Author : Khadija KMU Category : Love
bai san sunanta ba don haka yace ke ki tashi mun iso shiru Hurriya tayi
saida yayi mata magana kusan sau uku sannan ta bude idon wadanda sukayi mata nauyi Sosai har
lokacin tana jin jikinta na kwankwatsa Kumurci yace ki fito munzo kuma kada kiyi ma mutane kafiya
da rashin kunya don kece zaki sha wahala Hurriya da batajin karfin jikinta kwata kwata don ko yadda
take numfashi zaka iya lura tashi tayi ta rungumo kayanta saidai tana tafiya biyu ta sake su Kumurci
da yayi gaba yaji karar kayan da tasaki don haka ya juyo ya kalleta sannan ya daukar mata kayan
suka fita duk da suna zuwa ana sallahr magriba don duhu har yafara Bayyana Amman bazaka iya
gane cewa rana ce ko dare ba saboda haske da ya wadaci ko ina a babbar masarautar Qamar
Masarautar kanta abun kallo ce girmanta gari guda ne tunda ga floor din dake kasan masarautar da
ginin da akayi mutum zai gane cewar masarauta ce maiji da tsantsar dukiya kuma da karfin mulki
.saidai Hurriya ba Abu daya wanda ya burgeta don kallo daya tayi ma komai wanda bata kara kallon
wani Abu ba
Su Bintu da su karime kam Murna sukeyi kamar su ciji duwawunsu basu san masarautar Qamar,
bawuri bane da ya kamata ace ya burgesu ba ko su kasance masu farin ciki Don masarauta ce wadda
take cike da tsantsar zalinci da rashin imani.Kusan duk wadanda sukazo dasu sakin baki suke suna
kallon ko ina.
Tasa keyarsu akayi ana bugunsu kamar tumaki suka shigo ciki inda ba abinda kake gani sai dagorawa
dake tsaitsaye fuskar su hade kamar zasu je yakin basasa hannunsu daya narka narkan bulali Dayan
kuma hannu dogayen bindigu kowane,Ba wanda bai firgita ba da ganin wadanan dogarawan don
fuskar su babu alamun sassauci
Hurriya da da kyar take tafiya saboda zazzabin da take wani bakin dogari ne ya sakar mata bulala
wadda saura kadan ta fadi da kyar ta cigaba da tafiya
Kumurci da yaga banda dukansu ba abinda akeyi yayi dauriya yace basu bane bayin ,Dukansu tsaya
sukayi suna kallon Kumurci saboda dokar masarautar ce duk wanda yafi ka matsayi dole kabi
umarninshi kuma duk abinda zaiyi ba wanda ya isa ya dakatar dashi saidai idan har akwai wanda
yafika matsayi zai iya hanaka to
Kallon Kumurci suke da idanunsu masu sawa mutum ya shiga zullumi Kumurci da duk ya tsure yace
Allah ya gafarce ku Kumurci yana Neman sassauci. Saminu ne ya iso don kusan duk yafi su matsayi
ya kallesu yace lapya?cike da rusunawa ya fara mashi bayanin abinda ya faru wani kallo Saminu yayi
masu wanda nan take suka bar wurin ya kalli Kumurci yace ka shiga dasu ciki kuma duk wanda ya
tareka kace ni na baka umarni shiga dasu daga ciki sannan ya bar wurin.
Kallon su shaho yayi da yan matan da suka taho dasu da mazan,saitin Hurriya ya kalla yaga tanajan
numfashi da kyar ta hade gwiwar ta da kanta,tunda aka tsaidasu ta kwanta Kumurci ba karamin dadi
yaji ba lokacin da yaganta da hijab ya tabbata da ace ba hijab jikinta da yanzu wani ya shiga dakinshi
da ita gashinta kuma da tuni an datse saidai cikin ikon Allah ta rufe duka jikinta harda kusan rabin
fuskarta.
Tafiya sukayi inda suka kara nitsa kansu cikin masarautar sakin baki kusan Dukansu sukayi don
haduwar masarautar tafi bayyana yanzu akan wurin da suka baro a baya kuyangu ne da bayi da
hadimai wadanda basu da iyaka kowa da hidimar da yake kuma kusan kowa da kalar uniform din
dake jikinshi wasu green and red wasu green and orange wasu green and yellow wasu green and
blue.
Su karime kam yau sun samu Tv don suna kashe ma kwarkwatar idon su haka suka rinka tafiya don
daga inda suka baro zuwa inda sukazo yanzu tafiya ce Mai wani irin nisa don dukansu sun gaji shaho
yace a kira uwale uwar bayi ta raba masu aiki tun yanzu Kumurci ya daure yace ai kasan ka’idar abun
dole sai sunkai gobe saboda jakadiya tana shiyar uwargijiyar ta yanzu to bari na nemo uwar bayi
Shaho ya tafi don nemo uwar bayi ba tare da wani bata lokaci ba sai gashi sunzo fuskar ta ba annuri
bare fara’a Kumurci ne ya gaisheta cike da girmamawa ya mikasu wurinta Kumurci Kallon Hurriya
data gama galabaita yayi cikin aljihun shi ya fiddo paracetamol da ibuprofen ya bata kin karba tayi
don kusan sau uku yana mata magana ta amsa Amman ko kallon inda yake batayi ba bare har ya
sanya ran zata amsa a ranshi yace zaki sha wuya ne a masarautar nan don duk kafiyar ki sai kin
ajiyeta don dubunki ma sunyi sun gama
Kumurci ya dora mata maganin saman hijab sannan ya juya ya bar wurin,su karime kam sai kallon
yadda ta zukana sukayi she looks so pale and weak yanayin da ba wanda ya taba ganin ta dashi
tunda take rayuwarta she’s always strong and fierce don haka Dukansu da mamakin yadda take suke
sai Abu na biyu da ba wanda ya taba ganin ta dashi wato hijab tunda duk wanda ya kwana ya tashi ba
wanda ya taba ganin Hurriya da hijab a unguwar su shiyasa suke kallonta da mamaki uwar bayi ce ta
kallesu tace wai Lapia kukayi tsaye kallon mazan tayi tace zata kira halliru ya shigar dasu ta kalli su
Bintu tace su tafi.
[12/02, 4:53 PM] Khadyn Sp: Masarautar Qamar
By Khadija (KMU)
Page 11&12
Uwar Bayi ce gaba suna biye da ita tafiya sukayi Mai nisan gaske kafin su iso wani babban gini kallon
wurin su Bintu suka rinkayi ita dai Hurriya ta kosa ta kwanta don kiris ya rage mata ta daina tafiya
saboda kasusuwan ta da suke kwankwatsa kusan dukan su itace karshe wurin tafiya uwar bayi ce ta
shiga dasu cikin ginin wanda yake da bangare iri da iri a ciki
Kuyangi ne kowace da uniform dinta suna hidimar su tunda suka shigo yan matan dake zaune suke
binsu da wani irin kallo Hansa’u ta tabo barira tace kinga mun samu sabbin zubi yau Barira da take
kallon Ko wanne a cikin su daya bayan daya cikin izza da takama tace uwar Bayi daga ina aka samo
mana sabbin tumakai su sa’ade da karime duk suka bude baki Hurriya da tanajin sun saidai ta kanta
takeyi Uwar bayi kam batace komai ba ta wuce suka bi bayanta
Hansa’u ta kalli barira tace kinga yan mata tsala tsala nifa harna hango wacce tayiman Barira yadda
take zaka dauka wata diyar sarkice saidai kawai saboda tafi su mukami kuma tanada saurayi a cikin
dogarawan don haka take baza nata mulkin a inda ya kamata cikin izza da mulki tace kudai bi a
hankali kada wata acikin ku ta shiga gonata sannan ta tashi tana wani juyi wanda kamar dagan gan
takeyinshi su Hansa’u Dukansu biyota sukai abayanta.
Uwar Bayi wani babban daki ta kaisu wanda yake da Bayi kusan duka manya mata ma ko ina
shimfede da katifa kowa kallonsu yakeyi da tausayi don ace yara da kuriciyar su sunzo azzalumar
masarautar nan don neman abun duniya but basusan cewar lalatar rayuwar su sukazo yi ba don a
masarautar tasu miye ba a aikatawa na kazanta babu shi Duk abinda baida kyau shi akeyi ga zalunci.
Uwar Bayi ta kalli yan matan da tazo dasu tace to nidai ga makwanci don haka ku nemi inda zaku
kwanta kafin gobe tayi a rarraba maku wurin bacci Dukansu godiya sukayi mata sukaje neman
wanda zai taimaka yadan rabasu kafin zuwa goben da tace.
Hurriya kam tana duke bata motsa ba bare tayi i tunanin tafiya Uwar bayi ta kalleta tace kiyi maza
kije ki nemi wurin kwana ko ki kwana a kasa tunda ba’a gidanku kike ba Hurriya dagowa tayi ta
kalleta wani irin kwarjini tayima Uwar bayi Uwar bayi batace komai ba ta tabe baki ta fita.
Bintu kam har tasamu wurin kwana matar Mai kirki kamar ma budurwa ce ita ta kara Bintu kuma
katifar katuwa ce zata ishesu su biyu Tunawa Bintu tayi da Hurriya don ba taganta ba tunda suka iso
a hankali ta fara o dubata kafin ta hango ta zaune a tsakiyar dakin cikin sanyi sai kallonta akeyi da
sauri Bintu ta nufi inda take tace Hurriya a hankali ta dago idonta da sukayi jajir ta zuba ma Bintu
hankali tashe tace Hurriya mike damunki baki lafiyane? Subahanallah ta dora hannunta saman
goshin Hurriya & tureta tayi da sauran karfin daya rage mata tace How dare you touch my Royal
Body maganar na fita da karkarwa saboda kyarmar da takeyi Bintu tace kiyi hakuri don Allah
hankalina ne ya tashi dana ganki haka Bintu tasan cewar Hurriya na bala’in sonta duk da cewar bata
nunawa amman idan Bintu na mata labari hankalin ta duka take bata ko Daga yanayinta zakasan
tanajin dadin ko wani irin labari Bintu ta bata kuma tasan har abada bazata samu kawa irin Hurriya
ba don ako da wani lokaci itace Mai tsaya mata tsayin daka a rayuwarta ta kwatar mata yanci a wurin
kishiyar uwa da shikanshi mahaifinta don ba wanda baisan irin muzgunawar da suke mata saidai
Hurriya ba ruwanta haka zatazo tazage su tass kuma tayi masu babban kashedi na idan suka kara
matsa mata zata dauko masu hukuma kuma sunsan halinta saboda ta taba dauko ma Larai da baban
Bintu yayi magana tace a hada dashi saida Bintu tayi sati daya a wurinta lokacin abinci duk idan zasu
ci sai ta tambayi Bintu mizasu siyo kuma duk abinda Bintu ta gani tanaso sai ta siya mata shi wani
lokacin da kanta take tambayar Bintu Abu kaza yayi maki idan tace Eh zata sai mata shi kamar
batasan darajar kudinta ba kuma idan har Bintu tazo bata kara kwana a katifa sai a kasa saboda
Hurriya ba wanda ya isa ya taba koda hannunta don tasan wannan halin nata duk wanda yayi gigin
taba ta sai ta sauke mashi mari Bintu ma kafin su saba kusan sau uku tana Marinta saboda yawan kai
hannu jikinta daga bayane saidai ta tureta tayi mata kallon kada ta kara.
Kallon Hurriya tayi tace mata sanyi ke shigar ki muje ki kwanta banza tayi da ita Bintu kuka ta fashe
dashi tana ma Hurriya magiya ta tashi sanyi Amman ina kusan duka mutanen dakin kallonsu suke
Bintu kam da taga Hurriya taki tashi sai ta kwanta kasan siminti tana kuka tace mata don Allah ki
tashi idan har baki tashi ba nima anan zan kwana Hurriya kallonta tayi cikin muryarta mai cike da
rashin karfi tace Bintu ki shekara a kasa idan kin tashi Bintu da tasan wacece Hurriya tayi mata sanin
da ba wanda yayi mata shi don tabbas Hurriya dagaske take ta shekara kwance a siminti itadai
batasan mi ya faru a rayuwar Hurriya ba daya maidata haka kamar dutsi
Fashewa da kuka Bintu ta karayi sannan ta tashi tanayi mata magiya kallon yanayin Hurriya tayi
wanda banda hakoranta dasuke gabgab ba abinda sukeyi wani kuka ta kara fashewa dashi mai
tsuma zuciya ta fara hadata da Allah mutane duka kallonsu sukeyi suna mamakin irin son da Bintu
keyi ma Hurriya ita kuma Hurriya ta kafe kamar kafurar farko sa’ade tace kibar shegiyar ta mutu
kowa ma ya huta kafura Mai bakin hali Karime tayi caraf tace tun ba aje ko ina ba karshen karuwa
yazo namu dai muyi kallo duk jiji da kan mutum dole ya ajiye shi don ubanshi zaici yayi anan.
Hurriya duk tanajinsu duk da ciki ciki sukayi maganar ta yadda bazata iyaji ba ,saidai sunanta fa
Hurriya Faisait Hamood. Magana daga nesa komin kasa da murya da mutum zaiyi sai taji ta kamar
gizo gizo haka take Allah ya bata kunnuwa kamar ba irin na mutane ba saboda kaifin ji da suke dashi.
A hankali ta fara wani irin tari harda sarkewa salati Bintu ta rinkayi tana kuka da tarin ya tsaya ba
abinda take sai karkarwa Bintu a hankali ta rage tsawonta tana kuka tace ki taimakeni Hurriya ba
kanki zaki taimaka ba Hurriya tunda nike baki taba musu da duk abinda nace inaso ba sai kinyi mani
shi don Allah ki taimakeni ki tashi ba don halina ba Hurriya kallon Bintu tayi da idanunta masu kyau
saidai sun rikida sun koma jajawur saboda azaba don har jijiyoyin idonta ana gani
Hurriya tashi tayi a hankali ta fara takawa saidai kafafunta banda kyarma ba abinda sukeyi Bintu ta
dafata saboda kada ta fadi tureta tayi da sauran karfin da ya rage mata har Bintu na faduwa kasa
tana binta da wani kallon cikin muryar ta da ta shake tace kina hauka ne ,Bintu kuka take tana girgiza
kanta tace Aa to sai ta kasa maganar tana Neman faduwa Bintu da sauri tazo ta tarbeta kada tafadi
kasa daga Hannunta Hurriya tayi da basu da karfi sosai ta wanka mata mari tana kallon Bintu da sai
kuka take sannan ta sake ta
Mutane kallon dramar kawai suke wasu lokaci daya Tsanar Hurriya ta kamasu saboda rashin
mutuncinta suna jin tausayin Bintu wasu kuma zaginsu kawai suke suna cewa marar sa mutunci zasu
zubda hali daga zuwansu duk munsan ma’anar abinda kukeyi hmm mutane sun iya judging din
abinda bashi bane Har sun manta da cewar yau su Hurriya da Bintu suka zo bare suyi irin hallayar da
suke magana.
Hurriya da kanta ta taka sukazo har inda Bintu ta samu wurin kwana Bintu kam dadi ta rinka ji don
har ta goge hawayen ta.
Habiba kallo daya tayi ma Hurriya ta washe mata baki tace sannu yanmata Hurriya ko kallon inda
take batayi ba bare ta sanya ran zatayi mata magana
Bintu kallon Hurriya tayi tace bari tayo alwala, waje ta fita sannan ta dawo ta gyara hijab dinta ta fara
rama sallolinta har tagama Hurriya idonta a rumtse yake don ta jinginar da kanta jikin katifa.
Bintu bayan tagama addu’arta ta kalli Hurriya tace in samo maki abinci Hurriya daga mata kai tayi
alamar Eh Kallon habiba Bintu tayi tace ina zan samo mata abinci Habiba tace muje in raka ki kitchen
ki amso naku abincin to inji Bintu don haka tabi bayan Habiba suna tafiya akan hanya sai habiba ta
dan wuce Bintu itakuma Bintu tana ta tunani tana tafiya.
Habiba juyowa tayi baya sai taga Bintu na tafiya kamar wacce zata fadi dawowa tayi ta rike mata
hannu gam tace kina tunaninta ko ?kada ki wani damu zaki samu wadanda suka fita komai a
masarautar nan wacce zata kula dake kuma ta soki sai ta farayi mata tafiyar tsutaa acikin hannu tace
Ko nima idan kika bani dama zan maye maki gurbinta Sai ta tsunkuli Bintu a waist dinta tana kashe
mata ido daya itadai Bintu kallon ta kawai takeyi ba tace uffan ba don batasan inda zancen nata ya
dosa ba kallon habiba tayi tace muje ko naga lokaci na tafiya Dariya habiba tayi tace gaskiya kinason
wannan yar tawalwalar ki nima inason inga ana kula dani haka shiyasa nike kaunar ki don daga gani
kinada kulawa ko kukan da kikayi mata kadai ya isa ya nuna hakan
Gaskiya inasonki nagode kawai Bintu tace sannan tace muyi sauri kada tayi bacci murmushi habiba
tayi ta rike mata hannu suka fara tafiya da fan dan sauri sauri itadai Bintu tanajin yadda take mata
tafiyar tsutsa da hannu har suka kai babban kitchen din da ake dafa ma bayi da kuyangi da masu aiki
abinci ba’a wani hantare su ba saboda sanin sune sabbin ma’aikatan da suka zo don suna bukatar
Abinci don habiba tayi masu bayani
Plate biyu aka basu cike da tuwo habiba ta amsa ita kuma Bintu tayi tsaye tana kallo ana miko mata
plate din Habiba ta kalleta tace ki amsa mana bata fuska Bintu tayi tace ba shinkafa ne? Kallonta mai
bada abinci take da mamaki tace ke yar Gidan maysiyata ki amsa idan ba haka in maida ki kwana da
yunwa shegiya har MU zakiyi ma iyayi alhalin agidan ku ba lallai kina samun kalar shi ba Habiba ta
mintsinota Bintu ba domin ranta ba haka ta amshin abincin saboda tasan ba lalle cewar taci tuwon
ba
Suna zuwa suka ga Hurriya ta kara dukunkune wa don ta kara makurewa wuri daya kamar da alama
sanyi takeji Bintu tace Hurriya ki tashi ki ci abinci A hankali ta bude fuskarta tana kallon Bintu da take
kuka a hankali tace ya akayi kuma?Share Hawayen ta Bintu tayi tace Hurriya don Allah ki ci abinci
kada ki ce bazaki ci ba akwai nisa fa inda muka amso kuma kinga baki lafiya tana sakin baki kamar
karamar yarinya Dan tsotsar bakinta Hurriya tayi kamar daman sararta ce ta daga mata kai
Cike da jin dadi Bintu ta miko mata tuwon Habiba dai tana kallon ikon Allah kwano ta samu ta debo
ruwa sannan taba Hurriya ta wanke Hannunta ta fara cin abincin a hankali ta dan ci ba laifi tanajin ta
koshi ta ture plate din ta kalli Bintu ,da sauri ta kara miko mata kwano ta zuba mata ruwa ta wanke
hannunta Habiba cike da kaudi da son ta samu shiga tace Hurriya ga magani kisha na ciwon kaine Da
zazzabi Hurriya ko kallon inda Habiba take batayi ba don a hankali ta sanya hannuta cikin hijab
aljihun wandonta anan ta fito da magungunan da Kumurci ya bata hannun Habiba har lokacin yana
tsaye tana bata magani cikin muryar ta da take da alamun rashin lafiya tace Bintu bani Ruwa.
Da sauri Bintu ta bata ruwa ta shanye maganinta kallon habiba Bintu tayi tace kiyi hakuri tana da
wuyar sabo ne Amman tana da kirki zaku saba In Sha Allah .Bari in tafi in samo wurin kwana sai
Hurriya ta kwanta tare dake,Habiba murmushi tayi cikin yanga tace yi zamanki ki kula da abarki ba
mai takura maku nizaje inda nima za’a kula dani,dadi sosai Bintu taji ta farayi mata godiya don tasan
idan har Hurriya ta kwanta Habiba ta kwanta kusa da ita kilan za’a iya tashi aga habiba kwance
saboda irin dukan da Hurriya zatayi mata kuma itakanta Bintu bazata taba bari ta kwana kasa ba
saboda sanyi.
Habiba ta fita tace matsiyata kuma ashe kunsan harka muje zuwa ta nufi dakin Su Hansa’u Aiko tana
shigowa sukazo suka zagayeta sukace mata habiba ya bakin nan nagansu tsalatsala guda habiba tayi
tace ayiri to ku kwantar da hankalin ku don ba wata wahala da zamusha wannan karan wurin jawo
hankalinsu tace ai yan gidan matsiyatan suma duk sun san harka don wadda na bama makwanci ma
baki gansu ba kamar zasu cinye juna nan ta kwashe labari ta basu tass dariya suka rinkayi suka ce
gobe zasu zo ta nuna masu yan matan suna fata ma Allah ya sanya akawosu dakin Barira duka tana
jinsu Amman batace komai ba don shiru tayi.
Bintu kallon Hurriya tayi da ta fara gyangyadi tace ki kwanta ni zan kwanta kasa daga mata kai
Hurriya tayi ta kwanta dukun kune cikin hijab dinta bacci ne mai wahala ya dauketa Bintu kam
tagumi ta buga tana kallon Hurriya don ta hango wahalar da zatasha a masarautar nan don Hurriya
bata durkusa ma wada sadai da alama waddanin sunyi yawa a