Chapter 3 Reading BABU RUWAN Kin Soyayya by preety xayeesherth READ HAUSA Novels

BABU RUWAN Kin Soyayya by preety xayeesherth

Author :  preety xayeesherth Category :  African Stories & Novels

Chapter   3 / 6

6K to 9K   out of 17.2K words

tausayawa yarinyar nan.




SUKayi sallama sannan kowa ya kwanta.

*PAGE* 19-20


------------------------------------------------------------------


*WASHE GARI*

su fayal suntashi da huri domin tafiya scul
Domin daman yau ne zasu gama practical dinsu.

Bayan sun kammala komai sunyi wanka sannan suka shirya cikin shiga iri daya bak'a doguwar riga tare da farin gyale farin takalmi da farar jaka.

Amnah ce kadai ta tsaya yin kwalliya duk da dai bame yawa tayi ba itako fayal daman ba yi take ba iyaka karshen kwalliyarta shine tashafa farar hoda da farin manbaki.

Amman duk da haka kyanta kara fitowa yake sai kaga kamanma intayi kwalliyar muni zatayi.

Bayan sungama shirine sukayi breakfast karfe takwas daidai sannan suka nufi mota domin fayal jiki yayi sauki sose kaman ba ita bata jiya ba lafiya.

Amnah ce ke driving dinsu itako fayal sai tunanin abinda zatawa Amsard yau take.


Da isarsu makaranta akace musu ae yau lecturern bazai samu damar zuwa ba yayi tafiya so dole sai yadawo sucigaba.

Dan haka ynzu zasu cigabada lectures ne.


Ita dai fayal bataso haka ba domin kuwa yau taxomasa da tsarabar rashin mutunci ita practical dinma bai dame taba akan shirinta daya baci.



Fayal tacewa Amnah"kinga fa mutuminnnan baida mutunci fa".

Amnah tace"haba fayal yanada uxurine fa".

Fayal taja tsaki sannan ta huce ajinsu.

Sannan Amnah tabi bayanta.




💖💖💖💖💖💖💖💖
*malesia*


Amsard ne zaune adakinsa yafito DAga wanka yashirya cikin kananun kaya bak'in wando bluen riga sannan yasaka glass dinsa na likitoci.

Ankawo masa abincinsa sannnan yaci .

Bayan yagamane yadauko wayarsa yakira usman.

Bayan sun gesane usman yace"yauwa yallabe bani labarinku kai da madam".

Sai da Amsard yaja numfashi domin shi harma yamanta dawata wai fayal.
Sannan yace"kai dai baka mantuwa wallah".


Usman yasheke da dariya sannan yace"eh din naji nidai abani labari".


Amsard yakwashe duk abinda yafaru tsakaninsa da fayal yafawa usman.


*PAGE* 21,22


-------------------------------------------------------------------


Bayan yagama fadawa usman abin dayafaru tskaninsune.
Usman yace"oh Allah dai yakiyaye gashi yanzu baka da numberta balle muji yajikin"
Yakarasa maganar tare da dariyar mugunta.

Amsard yace"kai kama sameni wallahi yaushe zan karba number wannan jaririyar ai kabari kawai sai na nuna mata *Babu ruwan so* alokacin ne zata nemi numberta kai yarma dani gabaya".


Usman yakara dariya sannan yace"kaiiiii oga adaiyi magani awannan miskilancin naka".

Amsard yace"hmm usaman kennan karka damu kabi dramar nan asannu zatazo karshe bakaji yadda bature yake cewa *wonder shall never end* ba dan haka karkayi mamaki daga karshe"

Usman yace"toh shikenan oga Allah dai yaba da sa'a dawasa wasa hakan yazama gaskiya yatashi daga drama".




Amsard yace"kai dai baka da damuwa wallahi gwara kai ma bara natashi domin zamu shiga aiki".

Usman yace"toh yaushe zaka dawo neh?

Amsard yace"wallahi daga zuwana har aiki yamin yawa Amman karka damu inaga jibi nazo".

Usman yace"owk Allah yakaimu".

Amsard ya amsa da "Ameeeen".




Sukayi sallamah sannan kowa yayi wajen aikinsa .



💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖



Lectures akema su fayal Amman ita gaba daya hankalinta baya jikinta sai tunani take .

Ita kadai sai yatsina fuskarnan take .

Abinda akasaba bara adaina ba dai.


Tun 8 suka shiga lecturers Amman sai 4 akabarsu sufito domin sallah hada azhar da la'asar sukayi.

Fayal sai mita takeyi akan anki bari su huta itako Amman sai dai ta kalleta domin ita tariga tasaba da hali irin na fayal.

Aiko suna idarwa ba abarsu sunci komai ba suka koma lectures .


Gaba daya sun galabeta sai wajen 6.10pm suka fito wasu masallacinma har Anfara kiran Sallah.


Suna fitowa suka nufi motarsu domin komawa gida bashiri Fayal tamikawa Amnah key din motar domin acewarta tagaji bazata iya komai ba.




Aiko Amnah gudu take Amotar domin ita kanta tagaji ga azababbiyar yunwa Anhanasu ko cin abinci.




Suna isa megadi yabude musu get suka shiga sannan Ammnah tayi paking fayal ko daukan jakartama batayi ba tashige gida .



SAi Amnah ce ta dibomusu dukansu.




Fayal tanashiga tayi sallama tageshe da momy daga nan bata kara cewa komai ba tayi cikin dakinsu.




sannan Amnah tashigo da sallamarta bayan sun gesa da momyne .

Momy tace"sannu da alama yau practical din yabaku wahala".


Amnah tace"ai bama practical din mukayi ba domin lecturan bai zo ba.
kinsan mun kwana biyu ba lectures shiyasa yau muka dadde".

MOmy tace"owk toh sannun ku nima yau aiki yamin yawane wallahi sai yanzu nashigo naga bakwanan gashiba abinci".


Amnah tace"to bara nadaura mana momy".


Momy tace"kema fa kingaji da kin huta kawai anyi ordering ".


Amnah tace"A'a momy kinsan fayal batacin abinci waje bara kawai nayi".


Momy tace"oh Amnah kincika san sisternnan taki ".

Amnah tayi murmushi.

MOmy tace "to dai Allah yayi muku Albarka kuma Allah yakaramiki hakuri da juriyar zama da fayal".


Amnah ta Amsa da Ameeen .

SAnnnan ta tashi tashiga daki tacire kaya tasa wasu tayi sallah tukun tashiga kichin.

Batare da bata lokaci ba ta fere doya sannnan tawanke tukun tasa atukunya ta daura agas .


BAyannnan tayi gretin din kayan miya tafara soyawa ba mai bayan yadan soyu tazuba kwai.



Kafin tagama miyar har doyar tayi dashike agas neh.


Bayan takammala doya da miyar sos ne tukun ta hada musu fruit salat.


Tana kammalawa anakiran sallar isha tuni taje tayi wanka sannan tadawo domin shiryamusu abinci a dainin.


💖💖💖💖💖💖💖💖

Amsard yana cikin aiki chuku chuku har yanzu dai anata fama akan kafar nan duk da alamun sun fara samun nasara.




*PAGE* 23.

-------------------------------------------------------------------------

sai karfe 10pm su amsard suka samu fitowa daga dakin ofireshon .

Suna fitowa yanufi gidansa sannan yayi wanka tukun ya gabatar da sallah.


Yana idarwa yanufi kicin domin shi inba girkin hajiya momy ba gwara yayi da kansa inkaga Amsard yaci abincin waje to fa ba yadda ya iyane.

Dan haka bai damu da gajiyar dake jikinshi ba yafara aiki .
yadaura sanwar wake sannan yadaura shinkafa adayan gefen gas din .

sannan yakoma yafara gretin din kayan miya.

Batare da bata lokaciba shinka far nan suka tafaso dan haka yasauke su duka sannan ya wanke .
Ya zuba su a abin tsamewa .
Yadibo kayan miyannnan yasa atukunya asoyasu sose da manja sannan yazuba su kayan dan'dano .
Bayan yazuba ruwan yatafasa sannan yasa su shinkafa da waken nan.



yatafi fallo domin huta wa bai fi 40minit ba aiko yafara jin kamshi alamun abincinsa yadahu
Yaje yasauke sannan ya samo plet yasa .
yakoma falo.
Sannan yake firish dinsa yadauko drinks na lakaseraH
Yazauna dominci.


Arayuwar Amsard acikin abinci ba wanda yakeso fiyeda dafa dukan shinkafa da wake.


Adrinks kuma lakaserah.

Shiyasa ba ya kyashin yima kansa girki komai dare.




*PAGE* 24,25.
-----------------------------------------------------------------------

Amsard yagama abincinsa yaci kuma sannan yayi lafila tukun ya kwanta barci.


Suma su fayal sunci abinci tukun sukaje kwanciya.

Anan ne fayal take ta tunin Amsard dayaki zuwa azyciyarta tace kodai ma tsoro yajine yace zai tafi wajen aiki ana nemansa tana ta tunani dai iri iri daga karshe kuma tace"toh ma ina ruwana dashi mtsw".

Batasan maganarma tafito fili ba sai ji tayi Amnah ta shek'e da dariya .
Sannan tace "aiko da ruwanki tunda kina tunaninsa".

Rain fayal yabaci dan haka taje dogon tsaki sannan ta kwanta.

Sai tajima ita kanta haushin kanta take.


****WASHE GARI******
💖💖💖💖💖💖💖💖


Da Asusuba Amsard yatashi yayi sallah sannan yayi wa kansa breakfast .
Yayi wanka sannan yashirya tukun yayi break kafin 7 har ya kammala komai nasa sai tafiya asibity.

Da isar sa asibity akasanar masa Da ai feshen din sa ta farka .

Aiko yayi farinciki da jin hakan .
Batare da bata lokaciba yaje yaduba sannan yamata tambayoyi tukun yakoma office dinsa.



yau gaba daya fayal ta tashi jiki ba kwari ita kanta batasan meke damunta ba ita dai kawai taji jikinta ba kWAri .

Dan haka tanayin wanka ta zumbula doguwar riga sannan ta dauko hijab da glass dinta tasa .

Ko breakfast dinma takasa yi su momy sun tambayeta menene Amman sai dai tace musu bakomai.

Tun suna tambayarta har suka gaji sukayi shiru.


Ahaka suka tafi skul itada Amnah .

Fayal sai faman tsaki take wanda ita kanta batasan dalilin hakan ba.

Ita kuwa Amnah me zatayi banda kallo .
Azuciyarta kuwa cewa take"da alamu kinkusa chaza hali mu huta dan inAga kinkusa fadawa tarko".


Afili kuma tayi murmushi abinta.


Fayal ko sai sake yamutsa fuskarnan take ga tsaki.




Ahaka suka isa skul ba mai wa wani magana .


duk da dai daman hakan dabi'ar fayal dince .
Amman nayau din yafi nakullum.


Sun isa skul wajen 8 dan haka har anfara lectures ma Amnah tashiga sannan tace"excuse sir".

Sai da yabata izinin shiga tukunna tashiga .

Ita kuwa Fayal batama fito amotar ba sai ynzu duk da tasan sunyi letti Amman ko ajikinta .

Tafiya take kamar bazata taka kasa ba .

TaNa zuwa tashige lecture room din ko sallama babu.


Shiko lecture yace"tafita mai a aji tabari sai takoyo sallama tukun tadawo.



Aiko hakan ko ajikinta Dan hakama yasa tacigaba da tafiya kamar wadda kwai yafashe mata aciki.

kowa yakoma da kallonsa gareta ahaka har tabar ajin.



shiko lecturern sai da yazabga tsaki sannan yace"wallahi duk mace me irin wannan halin tausayima ni take bani gwara ku gyara halayenku ku huta.




Sannan yacigaba da lectures dinsa.



Amnah azuciyarta kwatakwata bataji dadin abin da fayal tayi ba domin koda yaushe infayal tayi wani Abu kanta yake dawowa sai yan ajin sutamata habaici.

Itakuma batason hakan
Shiyasa kawarta guda dayace akaf makarantar.




Fayal tana fita tayi mota tabude baya ta kwanta abinta ita har taji makarantar tafitan mata akaima.

KOMai yasa?
Ohooo Amsar da taba kan ta kenan.


Ahaka har tafara barci abinta.

💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖

Amsard yaga yau ba aiki sose a office dan haka yafara shirin komawa nigeria gobe.


MIsalin karfe 2 Yakira usman yafada mai insha Allah gobe zai dawo .

SAnnan usman yace"toh Allah yasa nidaman na zaqu kadawo aciga ba da drama domin naga mutuniyar ma amota ita kadai
DA alama dai yau ma ankuma da wani kenan".


Amsard yace"hmmm ai wannan yar sai dai Allah yakyauta Amman fa karka damu nakusa saita ta".

USman yasa dariya sannan yace"toh nidai kullum inama fatan sa'a ".

Amsard yayi dariya shima sannan yace"kadai ji dashi ageshemin da uwargida".

USman yace"aiko zataji domin nafara bata labarin dramar ku".

Amsard yace"kace kasani a faifai kenan".
Usman yasa dariya.

SAnnan AMsard yace"nidai sai anjima inashiri ne".
Sukayi sallamah.

*PAGE* 26,27.

----------------------------------------------------------------
Bayan usman sunyi sallama da Amsard .

Sai Amsard yacigaba da shirinsa nakoma wa nigeria.



Abangaren fayal kuwa tun karfe 9take barci sai 1 tafarka daidai da fitowar su Amnah kenan.


Amnah nafitowa ta hango motarsa abin yabata mamaki dan batayi tunanin ganin fayal ayanzu ba.

Batama ga abin mamaki ba sai da taga fayal da alamun tashi daga barci.


Azuciyarta tace"ikon God".

Niko nace sai kallo.

tana zuwa tace"fayal lafiya kuwa".

fayal ta yamutsa fuska har kungama kenan?

Amnah tace "eh wlh lecture usman ma yasanar damu insha Allah jibi zamu cigaba da practical dinmu".


Fayal tace"kwaji dashi dai".


Amnah tace"hhhh ai shiyasa kikaga mun fito da huri yau yasin da sai 6 inaga har sai kingama kumburah ma'.

Fayal taja tsaki sannan tace"ni kishigo mutafi ko malama".

Ita dai Amnah dariya take da dariyarta tashiga mota suka nufi hanyar gida.

Sun isa gida bakowa dahike momy ta tafi aiki shikuma dady yayi tafiyama.


Dan haka suna isa fayal tayi sallah tukun tadawo kichin domin daura abinci.

Duk irin halin fayal na kyaliya hakan baisa iyayenta sun sakalta ta ba .

Aduk sanda momy zatayi girki sai ta tabbatar da su fayal da Amnah na wajen.

Dan haka fayal tashiga kichin domin musu girki .

shinkafa da wake dafa domin itama shine abincin datafi so arayuwarta.

Tana kammala momy tadawo dan haka suka hadu a dainin domin cin abinCi.

Ananne momy tace"yadai maganar practical dinnaku gashima naga yau kun dawoma da huri".

Amnah tace"umm momy wai jibi zamu cigaba kinsan gobe sunday shiyasa kawai akabari sai monday inAga yau me practical din zai dawo shiyasama yau bamu jima a lectures ba".

Momy tace"owk su fayal ansha aiki ko maganar ma baza amin ba".

Fayal ta yamutse fuska sannan tace"hmmm momy".
Daganan bata kara cewa komai ba .
Sukuwa momy da Amnah suna hira sunacin abincinsu.

Itakuwa Fayal yadda batason yin magana haka bataso nakusa da itama su cika yi dan Haka da anfara cin abinci taga su momy sunfara bude dandalin hira sai tayi sauri tabar wajeN.

Toh yau mah haka tayi tayi tatashi tabar wajen.

Dashike sunsaba da halinta hakanma baya damunsu.

Fayal tana shiga daki Tadauko wayarta tafara game.

Domin datayi magana gwarah tata karatu ko game.

Suko su momy sai dasukaji sunyi nak tukun Amnah ta kwashe kayan da tA bata tatafi wanke'wanke .


Sai momy afalo dake danna wayarta.


Megadi yashigo da sallamarsa.
Momy ta Amsa.

Sannan me gaji yace"wai wani ne yace nakira masa fayal".

Shikansa asanyaye yake maganar domin yasan halin ta sarai.
Bayau akasaba zuwa wajenta ba tana hulakanta mutane .
Amman duk da haka kaman karuwa masoyanta suke.

Sai da momy taja dogon nufashi.
Domin ita kanta tsoron yartata take.


Sannan tace"waye ke kirinta?.
Megadi yace"wani ne yazo amota yana waje ".


MOmy tace"owk kace tana zuwa".

Megadi yace"toh sannan yatashi yatafi jikinsa asanyaye.

Momy takasa motsi sai tunanin yadda zata bullowa yartata take.


Daga karshe dai kawai ta yanke shawarar zuwa tasanar mata.


Momy nashiga ta tarar da fayal kwance tana game awaya.

TAyi sallama sannan fayal ta dago tukun ta Amsa.

MOmy tace"fayal ".

Fayal ta dago.
Tukun momy takara da cewa dadynki ya aiko wani dan abokinsa kije ku gesa".

fayal ta yatsina fuska sannan tace momy ni wallahi agajiye nake kawai Amnah taje su gesa".

DAkyar momy tajawo hankalin fayal dataje su gesa tukun tayarda.

Momy tabar dakin gaban ta sai faduwa yake.
Azuciya kuma tana addu'ar Allah yasa adace yau".

FAyal tadauko hijjabinta harda daukowa Amnah likaf tasa.

Tana fita!.



*PAGE* 28.

----------------------------------------------------------------------


fayal ta fito tana fitowa ta hango wani saurayi Tsaye tare da abokinsa sai washe baki suke.

Taja dogon tsaki tukun azuciyarta tace"hmm shirme".


Tafiya take kaman bazata karasa garesu ba.

Hakanne ma yasa basusan da fitowarta ba.


Sai da ta isa dai dai wajensu tukun suka ankarah.


Saurayin nan ne yafara magana dace"hajiya bako sallama ne?.


Abokinsa yace"kokuma tayi bamuji ba dai ko?.


Saurayin yace"oh hakane fa ashe kanata jana da hira ne".


Suka sheke da dariya dukansu .

Ita kuwa fayal abin ya kona mata rai taja dogon tsaki.



Tukun saurayin yafara dacewa"toh hajiya nidai sunana ibrahim Anakira da khaleel ni dan kasuwa ne kuma ina karatune har yanzu Kuma ni dan garinnan neh".


Yakara jan numfashi sannan yace"naganki ne wallahi Askul dinku nikuma naga bai kamata namiki magana acen ba shiyasa naxo nan".



Agaskiya inasonki sokuma na aure.


Khaleel sai washe baki yake waishi adole Amsa yake jirah.


Duk maganar nan yake itA fayal ko ajikinta ita haushinsa nema yakamata.

Gawata dariya dayake kamar anmasa kyauta.

Duk azuciyarta take ta fadin hakan.


Abokin khaleel yace"kodai kunya hajiyar tamu take neh".


Shiko khaleel har yanzu dai washe baki yake.


Sai Alokacin fayal tadago ta kare musu kallo sannan taja dogon ciki tafara tafiya.




Shikuwa khaleel da Abokin sa tsayawa kawai sukayi suna ganin ikon Allah.


Tafiyarta take hankalinta kwance kamar ba abinda yafaru .


Sai da tashiga cikin gida tukun abokin khaleel yace"kaga dai abinda nke gujemaka kenan ko?



Sai da akace kar muzo kowa yafadamana halinta Amman kai kaki yarda wai adole sai ka gwada sa'arka toh ai kuwa yau ga sa'arnan kazo gun wadda ko kalloma bamu isheta ba".




Shidai khaleel yakasa magana domin har ynzu abin mamaki yake basa.



*PAGE* 29,30.


-----------------------------------------------------------------------

Bayan shigar fayal gidane .
Su khaleel kuma suka tafi.


****WASHE GARI*******


Amsard yakammala shirinsa tsaf domin tahowa nigeria.


Yagama komai sannan ya yatafi domin hawa jirgin safe.


yazuwa kuwa ba ajima ba suka kammala kome jirginsu yatashi.

Wata yar budurwace ta nufo inda Amsard yake .

Tana isa tace masa"excuse sir".

Tukun Amsard yadago yakalleta .

Tace"can i sit pls".
Cike da shagwaba take maganar.

Shikuwa yarasama me zaice mata kawai sai ya girgiza kai.
Alamun eh .


Aiko tana ganin haka tayi saurin zama kusa dashi.


sai magana take me da turanci Amman yaki kullata .

Domin shi Amsard yatsani macen data fiye iyayi.


Baima san tanayi ba duba jaridar hannunsa yake.


Gashi kana ganinta kasan jinin hausawace amman tazo taname wani yare.



Sunfi minti goma ahaka sai daga karshe taga dai ba sarki sai Allah tukun tace"haba oga magana fa nake tun tuni kaki kulani".


Akara na biyu kenan daya dago tukun yace"au daman kin iya hausa neh?
AI nazata daga turanci sai turanci".


Budurwar nan tayi murnushi tukun tace"Ai kaine nake tunanin bakajin hausa shiyasa nama turanci".


Amsard yace"owk".


Budurwar nan takara dacewa"sunana zubaidat Amman anakirana da zuby
Sannan kuma ni yar asalin jigawace Amman ina karatu A malesia".



Amsard yace"owk barkanki dai".



Zuby takara dacewa"inbazaka damuba inaso nazama sistern ka".


Amsard yamata shiru.


takara dacewa"pls kuma me sunanaka?


Amsard yace"sunana Amsard kuma ni dan garin katsinane nima karatune yakaini malesia sannan nafara aiki".


Zuby gaba daya tabawa Amsard hankalinta sai dataga yatsaya da magana tukun .

Tace"wooow Amman gaskiya sunanka yamin dadi kamar yadda kake da kyau hakama sunanka yake.

Toh pls kayarda nazama sister ka mana".

Amsard"yace owk".



Zuby takuma cewa"toh kadan bani numberka mana dan Allah".


Amsard yace"owk sannan yafadamata ta rubuta sai da takirasa taga yashiga tukun ta katse .
Sannann tace"toh kayi save mana".

Amsard baice mata komae ba yayi saving tukun yacigaba da karanta jaridarshi.



Zuby ta lurah dacewa Amsard bai son magana sose shiyasa tun tana jan sa da hira har tayi shiru tabarshi.




Ahaka har suka iso nigeria zuby ta tsaya tukun tame sallama tare da yafadamata a inda yasauka zatazo domin tasamesa.


Amsard yamata kwatance makarantar su fayal tace "aiko gobe zatazo insha Allah".


Aha sukayi sallama kowa yayi hanyarsa.

Abangaren su fayal kuwa yau ana hutu tunda sukayi sallahr asuba ita da Amnah suka koma barci sai wajen 12.30 suka tashi.



Suna tashi kuwa sukayi wanka tare da sallar azahar tukun suka fito geshe da momy.

Amnah ce tafara fita .
Tana fita tahango momy naduba takardu ahannnunta.

Amnah tageshe da momy .

MOMy ta amsa cikin sakin fuska .

Sannan fayal tafito ta geda momy.

Momy ta Amsa.

Sannan momy tace"toh tunda sai ynzu Allah yayi kuka tashi ai sai ku daura girki".

FAYal ta hada rai kaman zatayi kuka.

Amnah tace"uhymm momy yunwa fa nakeji nidai".


Momy tace"aiko zakuyi bayani tunda bani nace kuta barci ba".

Fayal tace"uhumm momy".

MOMy tace"toh kudan ban tausayi dai ga abinci ku cen kuje kuci".

FAyal tayi murmushi tare da fadin"owk momy".

AMnah ma tawashe baki tare da tashi domin zuwa cin abincin.

FAYal ma tabi bayanta.

SUNa zuwa kuwa sukaga AShe dambu momy tamusu.
DAman tasan Amnah dason dambu shiyasa take yawanyi.

AIkuwa AMnah tana gani tace"woooow sannan tajuya gun momy da gudu turungumeta tare da fadin "nagode momy nah".

Momy tayi murmushi tukun tace"u ar wlcm my daughter".

SAnnan AMNah takoma sukafara cin dambu sai washe baki take tana ta surutu itakuwa fayal sai yatsina fuskar nan take tana ci kaman dolE.

DUK DAtanaso amman bata nunawa.


Itakuwa Amnah sai zakan abinta take.


*PAGE* 31,32.

-----------------------------------------------------------------------

Fayal ce tarafara tashi tabar Amnah tanacin abinci
Haka kawai taji tana farincikin da ita kanta batasan dalilinsa ba
Ahaka ta wuni cikin farinciki wadda ko su momy sai da abin yabasu mamaki.

Kawai binta suke da ido
Sai kallo.

Amsard ya iso jigawa karfe 4.00 ina isowa yakira usman awaya domin yazo yadaukesa.

Batare da bata lokaciba kuwa Usman ya iso
Yana isowa Amsard yahangosa dan haka yasa yakarasa wajen sa.

Amsard nazuwa yace"a lallai usy kanaji dani naga saurinka fah".

Usman yayi murmushi sannan yace"ba dole naji dakai ba tunda kakusa angwancewa".

Amsard yadan daki bayan usman sannan yace"kai ko baka da dama gwara kai nikam muje kasaukeni amasaukina insamu inyi wanka dan wallahi nagaji".

Usman yayi dariya

3 / 6