mai gadi shima jikinshi narawa yashiga rokonsu su yakuri subarshi amman ko jinshi basayi saida suka tabbatar da sunmai lilis, he is totally weak baima iya motsi jini nafita daga hancin shi da bakinshi sanan suka barshi suka sakamai ankwa handcuff sanan suka jashi kamar ragon layya suka fita dashi daga dakin zuwa cikin motarsu.
Binsu har waje Mai gadi yayi shida Sadiya suna rokonsu akan susakeshi amma basubi takanshi ba, suna jefashi ciikin motarsu suka shiga direba yatada motar sukai gaba dashi.
Koda suka Isa police station fuskar Arham yay subu subu tsabagen mari kan dayasha, janshi suka karayi zuwa cikin station din suka bada report that lead them har suka mishi dukkan nan sanan aka jefashi cikin cell, babban su ya shigo cikin cell din rikeda wata zungurariyan takarda ya fara karanto mai offense dinshi na trying to murder Dr Waleed warbai. Janshi akayi zuwa toture room aka Fara tambayarshi why he strangulated Mr Waleed Warbai. Dago jajayen idonshi Amma baice musu komai ba. Fara dukkanshi sukayi tako Ina Yana ihu Yana " Don Allah kuyi hakuri, it was a mistake" kuka yafara yi Amma still basu barshi ba. Sai dasuka tabbatar da sun mushi lis har kasa daga lafanshi guda dayayi sannan Suka kawo mishi ruwan zafi suka bashi yasha.
Bayan sallan magrib Ammi da Mom da Mama suka shigo dakin dan sunje masallaci sunyi salla, ganin Waleed azaune yasa da sauri Ammi ta saki jakanta kasa tazo gadon tazauna gefen kafafunshi takai hannayenta kan fuskar Waleed, kaman zata fashe da kuka tace "My baby katashi, tell me meke maka ciwo eh? A ina kakejin ciwo ajikinka, tell me Waleed dina meka maka ciwo"? Tai maganan hawaye nata ruwa a idanunta tana shashafashi kaman zata cinyeshi, dan murmushi yamata ganin yanda tadamu yace "am fine Ammi karki damu, meya kawoku orphanage haka? Mama" yakira sunan Maman Arham ahankali yana murmushi, karasowa Mama tayi wajen zuciyarta tamata mugun nauyi, wani irin kunyan Waleed dinma taji tanaji jibi yanda danta yamai, yaron dake sonshi dake nufinshi da alkhairi ne yama wanan jina jinan, tsayawa tayi ahankali agabanshi, dan murmushi tayi mai kama da murmushin dole sanan ahankali tahada hannayenta biyu tace "Waleed dan girman Allah kayakuri abinda Arham yamaka, wlh naji kunyan halin......" da sauri Waleed yamika hannunshi mai lafiya yakama hannun Mama yace "Mama me haka kike cewa dan Allah? Please kidena bani hakuri, ninace miki Blood yamin wani abune"? Wani wawan harara Ammi ta watsa mishi, Mama tace "Arham yamaka abinda ba daidai ba, Arham bai kyauta ba, kalli halin dayasaka ciki, wlh naji kunyan abinda yamaka, kunyan kallonku dukama nike, Arham bai kyauta ba wlh, saisa nabama Ammi goyon baya takiramai yan sada amai lilis akaryashi kaman yanda shima yamak......" kafinma takarasa maganan Waleed yatareta yace "waya kirama Arham police"? Cikin fushi Ammi tana ballamai harara tace "nice nasa aje akamashi akaishi police amishi shima dukan dayamaka, ko angayamai banison kane dazai kama yamaka wanan dukan eh? Karfinku dayane yasan da shekara nawa ya girmeka dazai kamaka ya bubbuga haka saisa nasa inspector yasa aka kamashi akaishi Station amai wanan shegen dukan dayamaka" sosai idanun Waleed sukai wani irin ja ranshi yawani irin baci, cikin fushi yace "Ammi wai mesa in everything saikin shiga rayuwana ne eh? Friends fight don't they? Sabida munsami miss understanding da blood saiki shiga fadanmu har kisa akulleshi, ninace miki ki kullemin dan uwane eh"? Wani irin kallonshi Ammi take kaman ta rufeshi da duka amman bazata iyaba, wani irin kunci da haushin abinda Ammi tasa akama Arham yaji hakan yasa yace "Ammi call that inspector right away kicemai yasaki Arham" cikin fushi Ammi itama tace "bazanyi ba dan ubanka" Waleed zaiyi magana da sauri Mama datake ganin duk laifin ta ne komi tace "kaga Waleed abinda mahaifiyar ka tayi tayi gaskiya, daidai tayi wlh ko ansakoshi nida kaina saina sassaba mishi, dan haka kamabar maganan nan" gyada musu kai Waleed yayi cikin kunan rai yace "ok" wani irin yunkurawa yayi daga gadon yana cije baki sabida yanda bayanshi da kafadarshi da aka daure ke mugun ciwo, da sauri Ammi ta tareshi tace "kai ina zaka Waleed" ture hannunta yayi cikin karfin hali irin na maza ya shiga kokarin sauka daga kan gadon, rikeshi daga Mama har Ammi da Mom sukayi, fashewa da kuka Ammi tayi tace "Waleed wai mesa bakajin magana ne kacika taurin kai eh? Ina zaka, sokake daurin da aka maka ya turgude, Waleed kasheni kakeso kayi kahuta eh Waleed, mena maka? Mena maka nace da zaka tashi zakabar gadon da kake kwance kana ganin bamaka da karfin tashi" tureta yayi a haukace ya kabar da hannunta daga jikinshi yace "leave me alone Ammi, kurabu dani, I can't fight with my friend again, friends can't fight again? Eh dole saikun shiga, dole sai kin shiga komi nawa? Ko kasheni Arham yayi he's my friend, Ammi you have no right to interfere in my affairs, sabida Arham ya dakan saiki aikamai police su kamashi a kulle shi adaka haba Ammi, haba Mom" yay maganan yana kallon Mom itama yace "bakuji kunyan Mama datake nan tsaye dakuba kuna saka a chaza danta eh?" da sauri Mama zatai magana Waleed yadaga mata lafiyayyen hannunshi yace "Mama please kiyi shiru" sanan ya kalli Ammi yace "Ammi baki kyautamin ba, and inhar you feel wanan abun dakikeyi akaina shine son dakike min then guess what am not proud of the love you have for me am not, cus kinsa inajin kunyan abokina, my childhood friend, my only friend my blood Ammi, Ammi you hurt me today" yay maganan yana kwanciya a gadon ahankali tareda lumshe ido, shiru Ammi tayi tana kallonshi kalaman shi sun mugun sosamata rai, zatai magana Mom ta girgiza mata kai, dauke kai tayi tace "Waleed nikake ma magana haka akan nace a hukunta Arham ko" tai shiru tana kallonshi ko bude idanunshi Waleed baiyiba, ciro wayarta tayi takira Inspector agaban su tace asaki Arham din sanan ta katse wayan, sanan ta kalli Mom tace "stay with him nizan tafi gida" tana maganan tadau jakanta cikeda fushi tafita daga dakin zuciyarta kaman zai tsage yafashe, Mom zata bita Mama tace "bari nina bita ki zauna dashi" juyawa Mama tayi tafita daga dakin, Mom kuma ta zauna kan kujera takifa kanta kan gado tai shiru tana tunani.
Koda Mama tafito har motar Ammi direba yajata sunyi gaba, awani irin hankali Mama takarasa motarsu, baya tabude ta shiga direba ma baya cikin motar da alamu masallaci yaje, fashewa da kuka tayi sosai, intace dukan da Arham yama Waleed bai mata ciwo ga wlh tai karya, ta bala'in jin ciwon dukan nan kaman me, Waleed d'a ne wlh, dan halas d'a na kwarai, tasan harga Allah tanaso aramamai amman da Waleed yafarka yayma Ammin shi maganganun nan saida ranta ya sosu, bala'in sosuwa ma, Waleed d'ane da kowace uwa zatai alfahari dashi aduniyan nan, taji kunyan abinda danta yamai wlh taji kunya, tasan Ammi tagaya mata maganganu amman ko kadan bataji zafinsu ba dan tasan ciwon dakake ji in wani yakama maka d'a yadaka ba gaira ba dalili, Arham bakin halinshi da bakin zuciyanshi tamai yawa, kuka tayi mai suna kuka amotar nan hakanan ma taji bazata iya komawa cikin asibitin tahada ido da Waleed ba, tana zaune direban ta ya shigo yace "Hajiya yakuri ina masallaci ne mutafi?" gyadamai kai tayi tace "eh mutafi", tada motar direban yayi suka fita daga gidan marayun.
Direban Ammi nakaiwa gidan bamata jira yabude mataba tabude tafito, ahankali take tafiya dan bamata gani sosai, kanta wani irin bugawa yake kaman ana dukanshi da gatari, falo tabude ta shiga, yar aikinta da gudu tafito tana mata sannu da zuwa ko iya amsata bata iya tayiba tawuce stairs tai sama ahankali tabude dakinta ta shiga, yarda jakanta tayi anan tsakiyar dakin tawuce kan gadonta da kyar ta zauna tamika hannunta ta shiga tattaba saman kan side drawer dinta wani goran magani ta dauka da sauri, sanan ta bude taciro wasu kwayoyin magani na masu hawan jini guda biyu ta jefa abaki ta hadiye sanan tadauko bottle water ta kurbi ruwa kadan tasha, kanta na bala'in ciwo, tadafe kan da duka hannayenta ba'awani dauki lokaci ba bacci yay awon gabada ita.
***
Wuraren karfe biyun dare cikinta yawani irin murda mata da sauri tabude idanunta rass ta tashi zaune tznabin dakin da kallo, fuskarta ta taba taji tahada wani uban zufa kaman wacce tai dambe dudda uban AC dake dakin, tashi tayi ahankali ta dauki wayarta ta lalubo number Waleed tana yatsine fuska sabida ciwon maran datakeji, dailing number shi tayi amman bai shigaba, hartai bacci taga bai dawo ba gashi number ta bayi shiga hakan yasa tamike tsaye ahankali da kyar tana daga kafarta tabude kofa tafito daga dakinta, dakin Waleed tabude taga baya ciki hakan yasa tai stairs tafara tafiya ahankali zata sauko, wani irin ciwo dataji ya tokare mata mara yasa ta kurma wani mahaukacin ihu. "Mai gadiiiiii" zama tayi awurin tana wani irin nishi kafin tasake kwalama mai gadi kira, akaro na uku ne yaji yafito daga dakinshi yana share idanunshi dake cikeda bacci, ganin daga flat ake kiranshi yasa yay flat din yabude kofa ya shige hango Ilham daga ita sai doguwan rigan bacci yasa yay wurinta da sauri yace "Hajiya sannu haihuwan ce bari nakira miki dakta awaya" zai ciro wayarshi tace "kabarshi bayi shiga, kiramin duk wanda zaka iya kira azo a kaini asibiti azaba nikeji mai gadi" takurma wani uban ihu da saida ya firgita yace "Hajiya salati zakiyi, salati ake" juyawa yayi ganin bamatasan inda kanta yakeba ihunta kawai take, saida ciwon yadan sarara sanan ta nemi number Arham amman harya gama ringing bai dagaba, sau biyar takirashi amman shiru, dialing number Ammi tayi shima bayi shiga, ganin haka yasa tai dailing number Mummy ta, ringing daya Mummy ta tadauka fashewa da kuka tayi tace "Mummy mutuwa zanyi, Waleed bai dawo gidaba number shi bayi shiga, ina kiran number Maman shi itama bata shiga, dagani sai mai gadi agidan, kuma bai iya tuki ba balle yakaini asibiti, Mummy mutuwa zanyi" tafashe da kuka sosa daya ruda mahaifiyarta, anatse tace "kinga ba'a kuka in ana nakusa, be strong kinji yar albarka, ga Babanku nan yanzu zai kawoni wurinki just stay where u are kinji am coming" ta katse wayan, daidai mai gadi na shigowa yace "Hajiya wlh duk basa bude gate kinsan anguwan manya ne nan" ko jinshi batayi tahau ihu tana kuka sosai mai gadi yama rasa maizai mata sai dialing number Waleed yake amman bata shiga.
Wani ruwane yafashe mata dayasa tahau ihu. "mai gadi zan mutu kataimaka min wayyo Allah na kataimaka min dan Allah, daidai lokacin akai knocking kofar gidansu, da gudu mai gadi yafita yana zuwa yabude gate iyayen Ilham dinne mamanta da Babanta} da mota, Mmummy ce ta shigo tai ciki tafito da ita aka sata a motar Baba sanan takoma ciki taje ta nemo akwatin haihuwan ta adaki sanan tawuce takai motar ta shiga baban su yaja motar sai hospital.
Bakaramin wahala tasha ba sai wuraren karfe 8nasafe ta haihu, ta haifo danta namiji katoto mai bala'in kamada Arham kaman yay kaki ya tofar.
[11/1, 11:48 PM] Re@lš¤ K@usy š: š« _TWO DIFFERENT WORLD_ š«
āļø M SHAKUR
3ļøā£1ļøā£
Shirya yaron akayi aka fito da fitoda shi aka kawoma Mummy shi, ahankali Mummy ta karbe shi tana murmushi tace "miji nasamu ko kishiya"? Dariya nurse din tayi tace "miji ne Hajiya" karbanshi Mummy tayi tana kallonshi yaron kato dashi Masha Allah.
Daidai mijinta yakaraso tace "Alhaji kaga mijina masha Allah dawa yay kama"? Dan dariya Alhaji yayi yace "ai kamanshi daban da uwar da baban, hala sai nan gaba zai dauki kamanni, sake gwada namban mijinta dana mahaifiyar shi kiji ko zasu samu yakamata" number Waleed tafara dialing amman bai shiga har lokacin hakan yasa tai dialing number Ammi, lucky wayar ta shiga, wayar na gab da katsewa Ammi ta dauka, kafin ma Ammi tai magana Mummy tace "kawata lpy kuwa? Tun jiya da daddare muke kiranki dagake har Waleed baya shiga wlh hankalina yatashi" dan murmushi Ammi tayi tace "Waleed ne yadan sami hatsari wlh yana asibiti agidan marayun shi har karyewa yayi akafada, ban fadima Ilham bane kinsan mai ciki ba'a daga musu hankali haka, nikuma ina dawowa gida magani nasha na kwanta sabida hawan jinina yatashi, Mom ce awurin shi amman yanzu nai wanka shiryawa ma nike nakaimusu breakfast" da sauri Mummy tace "innalillahi wa innailaihi raji'un, ashe abinda yafaru kenan Ilham takira takira mijinta bayi shiga daga karshe saidai takira mu mukazo gamunan a asibiti wlh tasami karuwa yanzun nan amman tun cikin dare mukazo, anmiki miji fa, baki ganshi ba dan lukuti dashi" Mummy tafada cikeda farin ciki sabida tasan yanda Aminiyarta keson jika, Ammi mutuwan zaune tayi tama kasa magana, hakan yasa Mummy ta kyalkyace da dariya ta kalli mijinta tace "Alhaji tayi mutuwar zaune fa" sukahau dariya sanan tace "ki shirya saiki biyo kiga jikanki kafin ki kaima su Waleed abinci, Allah yabashi lpy, anjima dazaran an sallameta zamuje mu gaidashi"
Ammi kasa yarda da abinda aka gayamata tayi hannunta har wani irin rawa yake tai dialing number Mom dake zaune dakin tana kallon Waleed da tun jiya daya lumshe ido yaki budesu bacci mai nauyi ya kwasheshi yanzu muka yatashi dan tasan yana jinta sarai wlh, kaman bazata dauki wayan Ammi ba saikuma ta dauka takai wayar kunnenta, wani irin zabura tayi tace "Ilham ta haihu?" rass Waleed yabude idanunshi jin ance Ilham ta haihu, katse wayan Mom tayi tana murmushi sanan ta kalli Waleed dake kallonta ta tabe baki tace "mara kunya aika bude ido dakaji matarka ta haihu, suna asibiti ta haihu ansami namiji" ahankali yadan saki wata yar kyakkyawan murmushi sanan ya yunkura zai tashi, kafadarshi kawai da akai dauri kehanashi motsi yanda yakeso, da taimakon Mom ya iya tashi, Mom tace "me kakeso?" ahankali yace "office dina zani, I want to shower na chanza kaya naje nagansu" taimaka mai Mom tayi yamike tsaye ahankali suka fito waje, nurses sai gaidashi suke gyadamusu kai kawai yake, haryakai kofa yatuna alkawarin dayama Widad, Mom ya kalla yace "am coming Mom" sanan yay hanyar dakin datake, hannunshi yasa yabude kofar ahankali yashiga yana kallonta ganin tana bacci, ahankali yakarasa gaban gadon ya tsaya akanta yana kallon fuskarta kaman yatasheta dan taganshi saikuma yafasa yajuya kawai yafito tareda kullo mata dakin sanan yafito yay office dinshi shida Mom suka shiga ciki, dakin shi ya shiga yay bayi, brush yayi sanan yay wanka da ruwan zafi, jikinshi ciwo yakemai bana wasaba bai taba fada a rayuwanshi ba ko saisa Arham yay galaba akanshi oho, fitowa yayi yadauko wani jean yasaka da kyar sanan yadauko wata riga sai saka yakasa sawa, kwalama Mom kira yayi hakan yasa ta shigo, wani scissors yanuna mata, saida suka yanke hannun rigan daman sabida hannunshi yay balance sanan tasamai rigan ta shinfidamai dadduma yay sallolin da ake binshi sanan suka fito, Mom kejan motar suka dauki hanyar asibitin da Ilham take, parking sukayi suka fito sanan suka fara tafiya har zuwa dakin datake akwance.
Bude kofan Mom tayi ta shiga, Ilham na kwance kan gado, fuskarta ya kumbura suntum tsabagen kuka, sai Mummy dake zaune kan kujera rikeda jaririn da aka shirya yay kyau, Mummy na ganinshi tace "subhallahi, innalillahi wa innailaihi raji'un, Waleed wanan wani irin hatsari ne kaga yanda jini yataru a idanunka kuwa, jibi wuyanka da fuskarka sannu Waleed" kanshi akasa duk take maganganun nan ahankali yace "ina kwana Mummy" "ina kwana Waleed, ya karfin jiki? Allah yabaka lpy kaji, Allah yasa kaffara ne sannu" gyada matakai yayi suka shiga gaisawa da Mom sunama juna barka, karasawa gaban gadon yayi yana kallon Ilham data tsareshi da ido itama tana kallonshi tana mamakin abinda yasame shi haka, dan murmushi yamata ya shafa goshinta da hannunshi saida ta lumshe ido tabude su ahankali ta kalleshi, murya chan kasa yace "thanks for giving me a baby khadija, Allah yamiki albarka" gyadamai kai tayi tareda mika hannunta takama lafiyayyen hannunshi tarike gam, cikin muryanta da baya fita sosai tace "what happen to you Babyna"? Baki yabude zaiyi magana Mom ta taho rikeda jaririn tace "wato agaban mu ake nuna mana sonkai ko kana nuna kafi damuwa da matarka kan yaronka dayazo duniya yauko" murmushi Mummy tayi ranta fess ganin Waleed naji da yarta. Mom tamikamai yaron tace "ga danka nan dauki abinka kaga yanda yay kama da abokin ka kuwa kaman yay kaki ya tofar" wani irin mummunan faduwa gaban Ilham yayi saikuma ta daure ta lumshe idanunta da sauri kaman wacce bacci ya sace, ahankali Waleed yasa hannunshi ya karbi yaron yana kallon fuskarshi sanan yazauna abakin gadon yana rikeda shi yana kallon fuskar jaririn dake bacci yana murmushi, ko Allah yasan cewan yanason Arham, so na domin Allah, Allah ya azurtashi da d'a amman sai yaron bai biyoshi ba bai biyo mahaifiyar shi ba saiya dauko kamannin amininshi hakan yasa yaji bazaima iya sakama yaron sunan mahaifinshi ba, dan da yace in namiji yahaifa zai sakamai sunan mahaifinshi but wanan da yaron ke kama da Arham dole Arham zai bama yaron kodan Arham yagane shibai rikeshi da komiba sanan har gobe har jibi shi dan uwanshi ne no matter what.
Bakinshi ya daura kan goshin yaron ya sumbaci yaron yana murmushi sanan yama yaron huduba ya karbi dabinon dasuka sayo da zasuzo yatauna yabama yaron yabashi ruwan zamzam, yadago kanshi ya kalli Mom yace "Mom sunan d'ana Arham Waleed Warbai" shiru Mom tayi tana kallon Waleed din for few seconds itama Ilham saida tabude ido gabanta nafaduwa ko Waleed yagane ne saisa yabama yaron sunan Arham sosai ta birkice saikuma cikeda siyasa tace "d'ana yawani kama yayi kama da abokin ka saikuma kawani bashi sunan shi" karban yaron Mom tayi tace "Allah ya rayaka Arham, daidai nan aka bude kofa Ammi ce ta shigo yar aikinta abayanta da