SAFARA A TAƁO FATIMA MUHAMMAD GURIN *GUREENJOH* *ADABI WRITERS ASSOCIATION* *PAID BOOK* "*TSOKACI* Wannan littafi nawa mai suna SAFARA A TAƁO zai taɓo fannin da muke ganin ba komai bane, a wannan tafiya za mu fahimci Soyayya ba murmushi kadai ba ce; jarabawa ce," "aure kuma ibada ne, sannan rayuwa darasi ne daga Allah." *GARGAƊI* haƙƙin mallakar SAFARA A TAƁO na Fatima Muhammad Gurin ne. Ban amince ba ban lamunci a sauya min labari ko ta wani ɓangare ba ko a yi amfani da shi ba tare da sani ko izini na ba. *001* SHIMFIƊA "Shi aure sunnah ne mai girma na manzonmu annabin rahama annabi Muhammad (S.A.W). ya yi mana nuni da cewa zai yi matuƙar alfahari da hayayyafarmu ta hanyar aure a ranar gobe ƙiyama, sannan aure ibada ce sai dai kuma ba dole ba ce! don ka yi aure ba shi zai saya maka tikitin shiga aljannah ba kuma ba shi zai saya maka na wuta ba illah iyaka ya zama tsani wurin ƙaruwan ladar da zai iya kai ka zuwa aljannah ko ma halaka da zai iya jefa ka zuwa wuta." "Manufar aure da cikarsa shine zancen ubangiji na samun soyayya da natsuwa ta yadda za'a gina addini a kuma taimaki juna ta yadda za a yi rayuwa ta addini kuma a ji daaɗin duniya, kenan dole dai a samu ƙauna da tausayi a aure saboda ana tsufa ne tausayi na maye gurbin" wannan ƙauna da aka gina tun farko. "Numfashi mai matuƙar nauyi ta furzar tana sake damƙe sitiyarin motar dake hannunta inda ta ƙara ƙarfin gudun giyar da 30 tana tsula uban gudu a shimfiɗaɗɗen titin na birnin legas, ba za ta ce maganganun Momma ba su sosa mata rai ba sai dai ta riga ta yanke wa kanta hukuncin cewa babu kalar maganar da za'a yi mata ya mayar da ita ruwa a cigaba da gara ta tamkar taya, ba za ta taɓa yin aure ba a wannan duniyar, babu kuma kalar baƙar magana ko shaguɓe da zai tunzura ta zuwa ga MAZA, Me yasa ake auren? ai don kar a yi zina ne to ba za ta yi zina ba don haka ba za ta yi auren ba, dalilin tsanar aurenta ya sa ta zauna ta samu cikakken ilimi kan littafin 'Al'ulamul uzzab Allazina afdhalul ilmu alal zawaj' ta karanta cewa malamai ne har talatin da bakwai da duk sun koma ga mahallaci ba tare da sun yi aure ba ciki har da mafiya shahara a fagen ilimi irin su Imamun nawawi da ibn taimiyya." "Da wannan ta kafa hujja ta jingine kalmar aure bare soyayya, babu abin da ta tsana a yanzu" haka kaman 'Maza!' Har ta kai ga mahaifinta ma ta ƙauracewa idanunshi kaman yadda ta shafe sama da shekaru biyu ba tare da ta sanya shi a idanunta ko ta ji muryarshi ba. "Ta tsine wa kalmar So' don guba ne da ta sha shi ya illata ta, ta yarda ɗari bisa ɗari cewa duk wata hidima da za'a yi wa so ba ya taɓa bin ka da alkhairi sai dai ya saka maka da sharri...So bashi da kama ba shi da sabo, bukata ce kawai ta ɗan adam saboda babu so idan babu dalili. Dalili kuwa daidai yake da buƙata a duk sadda wannan buƙata ta cika shikenan kuma soyayyar ta tarwatse tamkar an wullar da kofin tangaran ne ƙasa. So tamkar kogi ne da muddin ka sake ka saka kanka ciki zai iya nitsar da kai kila ma ya zama sanadiyar yanke maka duk wata ni'imar" rayuwa da Allah ya tanadar maka a bayanshi. Leɓenta na ƙasa ta datse da ƙarfin gaske tana danna horn mai uban ƙarfi jikin tamfatsetsen kamfanin da aka rubuta da manyan baƙaƙe """MB MUSTAPHA AUTO MOBILE INDUSTRY LIMITTED""" "Wasu masu uniform kalar shudi har biyu ne suka wangale kofar ma'aikatar ta ƙutsa ciki tana parking inda kawai yayi mata don ji take tana rasa numfashinta, kwakwalwarta tuni ya birkice idanunta suka sauya launi ainun, ɓalle marfin motar tayi ta fito tana taku biyu zuwa uku ta ji jiri na shirin ka da ita tayi hanzarin dafe bambar motar tana runtse idanuwa da ƙarfi kirjinta na" sama da ƙasa. """Madam! Kaman baki yi parking bisa ƙa'ida ba...""" Ta ji wata murya ta furta mata. "Ba tare da ta ɗago ba ta harba makullin motar saitin inda ta ji Muryar a zafafe ta ce ""Gashi sai ka yi yadda ya dace ɗan iya!""" "Shirun da ta ji na tsawon mintuna ne ya sa ta ɗago sai idanunsu suka sarƙe, kusan seconds" goma suka ɗauka suna kallon juna hannayenshi zube cikin aljihu bai ko motsa ba inda key ɗin ke yashe a nan ƙasa. """Ke kika yi kayan ki don haka ke za ki gyara""" Cikin masifa ta ce """Idan ka damu ka gyara ka aikomin da key Design nd strategic planning team. Idan baka damu ba kuma ka bar shi a inda ka ganshi.""" Tana kai nan tayi gaba zuwa enterance na babban skyscraper ɗin ta shige ciki da yake glass ne yana kallonta har ta shige elevator ya mayar da kanshi kan key ɗin sai ya saki murmushin mamaki da kuma kaɗuwa yana furta """Unbelievablee!""" ******** "Babban gida ne wanda ya amsa sunansa babba sai dai duk girmansa tarin mutane na nesa da kusa sun cike shi dam daga ciki har waje babu masaka tsinke, hidima ake yi ba na wasa ba yara na kai kawo kaman yadda a ka yi baje kolin abinciccika kala daban daban masu ci na ci, hayaniya ne ko ta ina wasu daga waje kuwa a manyan canopies na 'yan gayu da aka kakkafe" maza ne birkij kaman yadda daga farkon Layin har zuwa karshensa motoci ne iri daban-daban "ga dukkan alamu gagarumin hidiman biki ake, daga chan cikin kuryan wani ɗaki kuwa 'yan mata ne zasu yi su goma sha kowacce na harkokin gabanta masu kwalliya na yi masu sa kaya na yi, masu hira na yi masu cin abinci na yi gabaɗaya ɗakin surutu ne har wani baya iya jin maganan wani." "A chan cikin bargo kuwa wata buduruwa ce lulluɓe daga ƙafafu har kai ban da hasken wayan da ke riƙe hannunta ya haske fuskarta tarrr za ka zaci bacci take ko wani abin, sai dai ga mamaki na duk irin raɓa da sanyin ɗakin ita wacce ke lulluɓen wani irin wahallen gumi take tsatsafowa, jikinta na wani irin tsuma take rubuta" """Sagir ka rufamin asiri... Kar ka sa zuciyata ta buga idan abin da kake cewa ya tabbata wallahi sai dai wata Hibban ba ni ba, ashe soyayya na iya juyewa ya zama tsantsar ƙiyayya? Na roƙe ka da girman Allah da manzonsa ka rufa min asiri.""" "Kuka sossai take yi marar sauti tana kallon fuskan wayar har wani saƙon ya sake shigowa ɓul! ""Ba ni da su ba ni da dalilin su, duk savings ɗina na tura maka Meyasa kake so sai ka lalata mini suna ne? Anya ka taɓa so na kuwa? Ashe soyayya kan iya zama RUWAN GUBA? Idan ka ɗanɗana min wannan gubar wallahi ba zan rayu ba ka taimakeni Sagir, ko don iyayena da mijin da ake gab da ɗaura mana aure!""" Ta tura da saƙon emoji na roƙo da hawaye. Ko buɗewa bai yi ba alamu farkon kawai ya karanta tana shirin sake magana taji ana jan bargon da sauri ta kife wayan. Dariya 'yan matan ɗakin suka kwashe dashi wata daga gefe tace """Su Hibbah sarakan cika baki da tsiwa yanzu duk bakin ya mutu za'a yi kewan Momma da Daddy""" Wata buduruwar da suke tsananin kama irin kama me tsananin nan da babu bambamci ta matso ta dafa kafaɗunta """Twinie ke ce fa kike bani ƙwarin gwiwa, ke kike tausata a kan rabuwarmu shine yanzu zaki fara" "kuka? Kina so ki ga nima na fara ko? Haba tsigalen Momma""" "Dariya duk aka yi ita kam sai ta ɗaura kanta akan kafaɗar ƴar uwartata kawai ta rushe da wani sabon kuka da ya ɗaga hankalin ɗayan itama ta fara, wacce ta yaye bargon da babbar macece tace" """Haba Hudah kema fara wa zaki yi? Kun ga kukan nan ya isa Hibbatullahn Momma biyunin Hudallah 'yar tsigale yi haƙuri haka ko So kike a kaiki gidan Mahmud da fuska a Suntume? Tashi shiga wanka maza kan a gama ɗaurin aure maza su fara shigowa""" Da kyar wacce na ji sun kira da Aunty Kubrah ta tura Hibbah bayi yayin da me kwalliya ta cigaba da yi wa Hudah. "Har ta fito wanka bata daina hawaye ba tun 'yan matan na tsokananta har suka dawo tausaya mata da alama Amaren uku ne bayan 'yan biyu akwai wata da take diban kamanni da su cikin ɗakin sai dai ita sam bata ba da fuska akan abin da ke wakana ɗakin ba kwalliyarta kawai ake mata, ko da aka zo kan makeup ɗin Hibbah hawaye ya hana sai da ɗaya daga cikin yanmatan ta kira Aunty Kubrah" """Yanzu kam zan saɓa miki dake da kukan, Haba! ki ga yadda kike so ki ɓata wa 'yar uwarki tata kwalliyar dubi Amal yadda nata yayi mugun kyau duk ina shegen taurin zuciyar naki?""" Da kyar aka samu hawayen ya tsaya aka fara makeup... "Chan daga wajen gida kuwa inda maza ke cike maroka na aikinsu aka soma ɗaura aure, Amal da ta kasance babba aka fara ɗaurawa da mijinta Zubair, aka ɗaura na Hudah da take bi wa Amal waenda Uba ne suka haɗa da 'yan biyun kuma ita Hudah ita ce Hassana da mijinta Mu'azzam, dai dai za'a fara batun ɗaura na Hibbah wani friend ɗin shi dake operating waya ya waigo ya taɓa shi, Juyowa yayi yana cewa" """Kai dallah bar taɓani ina so in ji sadda za'a ƙulla aurenmu da My soul ta yadda ba zan taɓa mance wannan rana mai tarin albarka ba.""" """It's something very urgent Mahmud da ya shafi ɗaurin auren naku""" "Matsowa yayi Abokin nashi me suna Abdhameed ya miƙa masa wayar a hankali cikin wani irin sanyin gwiwa ya soma scrolling sai da ya ƙarewa pictures shidda curr kallo har jikinshi ya ɗauki tsuma tamkar Wanda aka watsawa dusar ƙanƙara a tsakiyar sanyi, wani irin gumi suka karyo mishi rubutun da aka rubuta daga saman ya bi a hankali kan wayan ya zame daga hannunshi, daidai kunnuwansa na jiyo masa ina nemarwa ɗana Mahmud auren 'yar ka Hibbatullah da wani irin karfi da karaji ya furta" """Ku Dakata!!!""" "Gabaɗaya hankulan mutane ne ya dawo kanshi ""Meyasa? Me yasa zaka dakatar da masu ɗaurin auren?""" "Babanshi ya faɗa yana kare mishi kallo tuni ya birkice ya cire hula da babbar rigar ya yasar ""Na Fasa wallahi Na fasa, Ni ba mazinaci ba ne ba zan taɓa auren mazinaciya ba wallahil azeem""" """Kana cikin hankalinka kuwa??""" """Lafiyata ƙalau ku tashi mu tafi""" Ya dakawa duk Ƴan uwa da abokan shi dake zagaye dashi tsawa. "Tuni wasu sun fara gani don a Facebook ne kuma yana daga cikin App da ake saurin ganin abu saboda yanayin yaduwar shi da wuri, mari Babanshi ya tsinka mishi" """Ba Za ka mai da ni ƙaramin mutum ba, wallahi ka yi kaɗan, me kake nufi Mahmud?""" Wayar Abdul ya fusgo ya miƙawa baban """wannan...Wannan azzalumar macuciyar ita ce Hibbatullah ashe ban sani ba kura ce ita lulluɓe da fatar akuya ina yi mata kallon biri a ayaba take kallona, Wlh ta zalunceni inda Allah ya so ni ban kai ga aurenta ba amma tirrr tirrr na yi Allah wadai da ranar da na fara ganin Hibbah""" Zuwa yanzu kuka yake yi sossai. "Alhaji Mudassir Madaki da hankalinshi ya soma tashi ya miƙe tsaye yaje ya warci wayan da ya kusa faɗuwa daga hannun mahaifin Mahmud sai idanunshi suka mishi mummunar gani, bai iya ya kalli guda biyu ba wani irin mugun jiri ya diɓe shi sai ganinshi aka yi a ƙasa tuni hankula suka tashi wuri ya ruɗe, da gudu wani matashin yaro ya shigo parlorn yana kallon mutanen da wannan ke nunawa wannan abu a waya wata ke nunawa wata, kayuna biyu uku a harhaɗe a parlorn wasu na rike baki yayinda wasu ke salati, sam ba ya fata Momma ta ga wannan tashin hankalin da gudu ya haura nan ma abu ɗaya ne daidai zai shiga ɗakin Mahaifiyar tasu ya ji An" tsala ihu... """Mun Shiga Uku Mun Lalace... Innalillahi wainna ilaihi rajiun Allahumma Ajjirni fi musibatin Yaya" "Fatee! Yaya Fatee""" "Momma da suke magana da Aunty Kubrah ihun Anty Asiya ya sa duk suka juyo kanta har karo tayi da su suna shirin riƙota wayan ta nuna wa Momma da hanzari ta karɓa sai ta ga kaman idanunta basa gani da kyau daga ita har kubra sun gani sau kusan uku kan kafafunsu suka soma rawa, hannun Momma ne ya ja sama sabon Feed ya fito inda idanunta suka sauƙa a kan rubutun" """An fasa ɗaura auren Hibbatullah ɗiyar gidan shahararren ɗan siyasan nan Mudassir Madaki saboda hotunanta na banza da suke yawo media... Inda a take angon ya ce ya fasa ya haɗa da" "baƙaken maganganu masu ɗaci ga amarya har ga zuriya wannan dai an yi abin tirrr""" Daidai nan Mumtaz ya shigo wayan tuni ya saɓule daga hannun Momma tana shirin faɗuwa Mumtaz ya sake riƙe ta.. """Da gaske ne Mumtaz? Da gaske Mahmud ya fasa auren Hibba? Da gaske ne Hibba ce a wannan hotunan? Hibba dai Hibba da na haifa a cikina na kuma ba tarbiya dai-dai gwargwado?""" "Kuka kawai ya fashe dashi, jijjigashi ta fara ""Ita ce ko? Da gaske ita ɗin ce?""" Kan ya furta wani magana kawai ta sume mishi ta fi shi kiba ga nauyin jikinta ya sake daga ita "har shi zubewa kawai suka yi ƙasa yana kuka akan muryarshi kaman ba namiji ba, Yau ina ma" da ace shi ne gaba da Yaya Hibba? Ina ma... A chan kuwa ɗakin yammatan amarya wata ƙawar Amal ce ta fara gani inda ta matsa jikin Amal "ta nuna mata, dariya sossai Amal tayi suka tafa" """Hmmm Biri ya yi kama da mutum ai rashin kunya da fitsarar ba na banza ba""" "Wayan ta karɓa tana sake dubawa fuskanta falll fara'a tace ""Allah sarki Mahmud ashe niyar cutanka aka yi bawan Allah""" "Da karfi take maganan hakan ya sa gaban Hibbah ya shiga dukan ɗari-ɗari ba tara tara ba, numfashinta har sama sama yake." "Daidai Hudah ta ɗauki waya bayan ta gama karanta saƙon mijinta akan an ɗaura tana murmushi ta ɗan leƙa Facebook inda ta ci karo da sabon tashin hankali wani iri. Miƙewa tayi tsaye kaman wacce aka buga da kulki girgiza kai ta fara tana sake kallon hotunan sai dai duk inda aka je aka dawo ta riga ta sani ta tabbatar da wannan ɗin jikin yar uwar ta ce don duk wani shaida ko taɓo na Allah da ta san Hibbah da su gasu nan baro baro bare a ce edit ne, kanta ne yake neman bugawa a yayinda duka yan matan suka nufeta suna tambayar menene?" Salati kawai take ja na duk adu'ar da ta zo Bakinta kowa ya santa da natsuwa da tsantsar kama kai da haƙuri ba kamar 'yar uwarta ba da ta zama mafadaciya marar haƙuri sai dai bata taɓa sanin halayen Hibban zasu iya jefata irin wannan mummunan yanayin ba. "Ihu wacce ta warce wayan tayi nan fa aka fara kalle-kalle kowa da kalar tashin hankalinshi yayin da wasu na ciki ke ciki, jiki a saɓule Hibbah ta karɓi wayan sai duk suka zuba mata ido suna kallo ɗakin ya zama tamkar wanda mutuwa ya ratsa saboda shiru, idanunta ta runtse da ƙarfi tana jin yadda zuciyarta ya buga da wani irin tsananin ƙarfi, suma ma ashe wani rahama ne, gabaɗaya jikinta ya tsumee kaman mutum-mutumi haka ta zama da wani irin ƙarfi Hudah ta" chakumeta """Ki ce min ba ke bace?? Sis ki ce min editing aka yi? Twinie this. this would never be you" "No. No please No wayyy""" Duka take kai mata tana kuka take maganganun cikin Wani irin yanayi mai matuƙar wahalar fasaltuwa """Ni ce Huda.""" Abin da Bakinta ya furta kenan Hudah ta tsinka mata mari daidai Shigowar Aunty Kubrah wacce Yaya ce ga mahaifiyarsu hannunta riƙe da murdaddiyar wayar wuta ta rufeta da azababben duka tana kuka sossai. "*Littafin nan na kuɗi ne ki biya Naira Ɗari biyar (500) kachal domin kasancewa cikin masu kwasar tarin ilimi, faɗakarwa da zazzafar soyayya mai cike da sadaukarwa da aka zube ciki. Za ki biya ta wannan asusun" 0545475847 Gt bank Fatima Muhammad Gurin Sai ki tura shaidar biya zuwa wannan layi 09039206763 Ko kuma katin MTN na Naira 500 cikin wannan layi na sama sai ki tura da shaidar biya ta same layi. Sai na ji ku* Note: Da dare ne zan dinga posting da rana zan bi in dinga karanta comments naku so please a ba ni haɗin kai mu tafi lafiya kaman yadda muka fara lafiya. Na gode sossai. Gureenjoh SAFARA A TAƁO FATIMA MUHAMMAD GURIN *GUREENJOH* *ADABI WRITERS ASSOCIATION* *PAID BOOK* *002* "Dukan kawo wuƙa Aunty Kubrah ke yi mata gabaɗaya ɗakin an rasa mai ƙarbar ta sai ma masu kuka don kusan friends ɗin cousins nasu ne, ganin har jini na fita a jikinta ya sa Hudah da take ji kaman jikinta ake zubawa bulalun ta shiga da gudu ta rungume 'yar uwarta tana kukan fitan rai kaman yadda Hibbah ke yi, sam ba zata taɓa cewa zafin bulalar ya fi na zuciyarta ba, zuciyarta" gabaɗaya ji take ta tarwatse kanta ya mata nauyi a wurin bata da maraba da saƙago don bata "fahimta, bata ji kuma bata gani abinda kawai ke dawo mata tamkar a talabijin bayan hotunan sai" fasa Aurenta da Mahmud yayi. "Wani irin balae'en rikici ne ya barƙe a gidan abin ka da kishiyoyi kuma dama Momma a wuyansu take a maƙale, hakanan Hibbah tafi kowani ɗa a gidan shiga ido masu Allah ya ƙara na yi masu Allah ya kyauta ma suna yi, Alhj Mudassir ne ya shigo gidan bayan an samu ya farfarɗo mutum ne shi mai tsananin zafi da faɗa bashi da sauƙi sam, kuma kap cikin yaranshi babu wanda yake yiwa son da yake yi wa Hibbah, shine zata ɗibi ƙasa cikin trela ta watsa mai a ido? Shine za ta muzanta a gaban dubban jama'a? Shi zata kunyata a idon duniya? A haukace ya ci karo da su Mumtaz da Aunty Kubrah da wasu 'yan uwan Momma sun dauƙeta ranga ranga don duk irin dabarar da za'a yi an yi ta ƙi farkawa hankalinsu ba karamin tashi yayi ba, ba" shiri ya juya suka nufi asibiti. "Fitansu gidan kaman sabon gurmi ne don tuni su Hajiya Kamila sun cike gidan da zagi da cin mutunci babu mai bakin magana bare amsa cikin 'yan uwan Momma don kunya tabbas Hibbah ta bar masu abin kunya, Daddy Rabi'u ne babban wan Alhj Mudassir ya shelanta cewa biki ya watse kowa ya kama gabanshi kawai a bar 'yan gida komai da zai faru ya riga ya faru kafin awa ɗaya gidan ya zama sai su ya su ahalin gidan kuma har lokacin Hibbah bata bar wani irin kuka da take yi daga ƙasan zuciya ba tana yi tana girgiza kai hannunta ɗaya akan zuciyarta da take ji kama zai tsagata ya fita kunnuwanta na ji mata irin rashin kunyar da ƙanwarta Aina'u ke yi mata, wai yau ita ce Aina'u dai Aina'u dake bi ma Mumtaz a haihuwa take gayawa magana duk saboda kuskurenta... Duk saboda wautarta..." """Wallahi kika kashe mana uwa sai kin bi ta, ashe baki da tausayi? Ta ji da sharri da bala'in" Hajiya Kamila da Hajiya zakiya ta ji da baƙin taurin kanki da rashin jin maganar ki da kullum sai "kin ja mata magana a gidan nan kuma yanzu ke da abin kunya ita da mutuwa? Ba zai yiw """ """Will you shut up Aina'u??""" "Hudah ta daka mata tsawa tana kuka akan muryarta, itama Aina'un cikin tsawa tace" """Ba zan yi shiru ba Adda Hudah ba ita kaɗai ba ce! ba ita kaɗai Momma ta haifa ba, ashe ba zata sararawa uwarmu ba? In ta mutu mu waye zai ragar mana? Tirrrr tirr da halinki Hibbah"" Tana kai nan ta fice tana kuka sossai." "Tuni su Amal dama sun tattafi sashen iyayensu gurmi da mayar da magana ya saura Hudah ne da Hibbah Ta kasa barin 'yar uwarta duk yadda mijinta ke kiranta a waya ta kasa dagawa, ta" kasa shiru da kukan da take yi Dukda na Hibbah ya fi nata sau hamsin sai dai ciwon ƴar uwar "haihuwar ta nata ne, dama sun saba duk abin da zai samu daya na sharri ko alkhairi tare suke" raba wa amma Hibbah ta fi janyo musu abin kuka Hudah mai haƙuri ce tsantsa. A chan asibiti kuwa likitoci ne suka rufu a kan Momma saboda ganin sun ceto rayuwarta abin ya daketa sossai hakan yayi sanadiyar hawan jininta ainun da suke tunanin in ba sa'a ba zata iya samun paralyze. Sai safa da marwa Daddy Zubair da ya tuko su yake yana call Shi ɗin babban DSS ne yana ganin ko da yadda za'a yi a taking pictures ɗin down kuma ayi tracing daga inda ya fito don ya shiga mota zai tafi office kenan ya ga su Alhj muddasir ɗin afujajan tsabar rikicewa duk motocin sun bari gida suka fito da kafa shine ya tsaya kawai aka sanya ta ciki. """Yaya ka kwantar da hankalinka don Allah kar kaima ka shiga wani hali komai zai yi daidai in shaa Allahu""" Alhj Mudassir dake hadiye wani irin baƙin ciki ya kalli Daddy Zubair hawaye na shirin sauƙo mishi yace """Zubair ba zaka gane ba... Nan""" Ya nuna kirjinshi """Kaman zai fito nake ji, why Hibbah?? Meyasa Hibbah zata mana haka? Me na ragi yarinyar nan da ta zaɓi tozarta ni a idon duniya, yanzu abokan gaba sun samu makami a kaina rasa kujerata kila zan yi, hakan bai wani dameni ba kaman yadda mutuncin gidana da sauran ahalina ya zube don ko za'a mutu wani ba zai taɓa yarda cewa ita ɗin ba 'yar iska bace kaddara ma bata taɓa aikata hakan ba kenan""" Tari ya fara """sakayyar kenan? Na nuna mata ƙauna fiye da duk 'ya'yana na fifitata na bata duk wani gata" "sannan na bata tarbiya Zubair sakayyar da zata yi min kenan""" Kan a ankara jini ya fara fita masa a hanci hankali tashe Zubair ya riƙe shi yana jijjiga shi """Yaya..! Doctor...!! Someone please helppp""" Ai da gudu aka yi kanshi shima aka tura shi emergency. "A mugun zuciye Zubair ya fita asibitin haka ya isa gidan kaman zai tashi sama ya haura ɗakin yaran, har lokacin kuka suke wani irin hankado kofa da yayi shi ya saka su duka Miƙewa tsaye, wani irin bugawa zuciyoyinsu yayi." """Ashe ke ƴar iska ce? Kashe mana ɗan uwa kike so ki yi? Hibbah me kika nema a duniya kika" "rasa da kika zabi wannan hanyar? Don ubanki kin ce aure kike so ne aka ƙi yi miki?"" Girgiza kai kawai take yi don sun san irin zafi da tsananin shi, shi a gidanshi matanshi ma tsoron motsi me karfi suke" """Don ubanki ki buɗe baki ki yi min magana..! Kin ce a miki aure an ki?"" ""Aaa.a..ah""" """Uban me ya saka ki aikata hakan?"" ""Wal """ "Wani gigitaccen marin da ya so kurumtata ya sauƙe mata, zata iya rantsuwa ta yi suman wucin" gadi ta dawo kan ta gama ganin taurarin marin ya rufeta da mugun duka da belt da ya zaro... Ihu take yi Hudah na taya ta ganin zai iya kashe mata 'yar uwa kuma babu mai taimako Alhali mutanen gidan sarai zasu iya jin su yasa tayi shahada ta riƙe kafafunshi da ƙarfi """Don Allah...Don darajar Allah kayi hakuri Daddy Z, tayi kuskure amma kayi haƙuri jikinta ya" "farfashe ka tausaya don Allah..!""" Hudah yarinya ce mai hankali da ladabi kowa ya sani tun haihuwar su akan mixer su don ba'a gane wacece wacce a cikinsu sai da suka fara wayo halayensu ya sha bambam nesa ba kusa ba. """Waye shi ɗin kika ba wa jikinki??""" """Ba...ban yi b...a""" Cikin wani irin wahala take kakaro maganan """Nace uban waye kika tambaɗe dashi har yake da shaidah kan ki..?""" "Tsawar da ya daka mata ya haɗu da mummunan yanayin da take ciki na jiki da zuciya ta buɗe baki da niyyar magana sai numfashi ya ƙi fita, tamkar mai ciwon asthma haka take kokuwa da numfashinta hannunta ɗaya dafe da zuciyarta tana dannawa saboda ji take kaman ana daddatsawa she's disappointed, betryed, deeply hurt duka a lokaci ɗaya tun tana fahimta har ta" zo ta daina fahimtar komai ta tafi luuuuuu ta faɗi ƙasa kanta ya bugi jikin gado shima ya fashe... Daddy Rabi'u da ya shigo da hanzari saboda shiga da yayi magana da masu aiki akan su zo su gyara gidan "Fitowan da zai yi sai ya ga motar Zubair kuma ya san shine ya tafi da su Momma asibiti hakan ya sa ya hauro da hanzari kar yayi aika aika kowa ya sanshi da zafin zuciya irin Alhj muddasir amma nashi ya haɗu da aikin khaki da yake ya ninka na Alhj muddasir ɗin ihun da Hudah ta tsala daidai faɗuwar yar uwarta yasa ya shigo da gudu, ɗaukarta kawai yayi suka fito da gudu gudu zuwa mota iliya yayi hanzarin buɗe mishi suka shiga da ita kusan duk matan da yaransu kowanne na kofar side ɗin shi suna murmushi yayinda Aina'u ta riƙe autocinsu da suma 'yan" biyu ne maza Fadil da Fareed a jikinta tana kara karfin kukanta. Itama Hibbah emergency aka yi da ita Dr. Najeeb Kabir ne yayi kanta da wasu nurses aka rufu don ceto ta. "A chan ɓangaren Momma an samu ta farfarɗo da kyar an yi mata allurar bacci likitocin suka fito suka kwantar musu da hankali haka ma na Daddy dama yana da 'yar matsalar zuciya amma ba chan ba kuma yana kan samun kulawa kan wannan abu ya faru shima an samu ya lafa ya yi bacci, duk da basu damu da sanin Halin da Hibbah ke ciki ba sai dai kukan Huda da yadda take ta je-ka-ka-dawo sai ya basu tausayi, nan Aunty Kubrah ta janyota jikinta tana rarrashi sai da aka samu awa kan Dr. Najeeb ya fito ya dube su sai dai sam bai yi magana ba don ya karanci yarinyar ya fahimci daga gidansu ne koma mene ya sameta don tana farkawa da haƙuri ta fara" tana ambatan sunayen Momma Daddy da su Aunty har ma da Hudah. "Office nashi kawai ya wuce riƙe da file ɗinta a hannunshi, zama yayi yana sake karantar file ɗin da yanayinta nan ya kira wata Nurse ya ba da umarni a je a yi mata gwajin kirjin nan ya gani don kaman ta samu issue da numfashinta, sam bai natsu a kan lamarin ta ba don haka kawai yanayin nata ya mugun taɓa shi Dukda bai san laifinta ba sai zirga-zirga yake yi a ɗakin babu kowa kusa da ita ko a kanta har aka kwana, Washegari da safe yana tsaye kanta ya zuba wa fuskarta da take ta zubar da hawaye idanu cikin salon dakiya da magananshi ya furta ""Hibbatullah...!""" "Bata ko motsa ba bare ta nuna alamun ta ji ƙiran da yayi mata, his gaze are still fixed on her ya" ce """Kashe kan ki kike son yi ne kam? Baki san komai na bawa rubutacce ne ba kuma karɓar kaddara na daga cikin imani ba? Kuka babu abin da zai janyo miki sai wani wahalan Look at this...""" Ya ɗaga file ɗinta yana nuna mata """Numfashi ba ya isa huhunki yadda ya kamata, zuciyarki tana nan a kumbure kika ci gaba a wannan hali mutuwa za ki y...""" """Da sai na fi kowa farin ciki, da hakan ya fiye min wannan rayuwar marar future... Ni da fanko duk ɗaya muke saboda ko na rayu zuciya da ruhina sun jima da mutuwa don haka ka kyaleni in mutun kawai ko zan huta..!""" "Ta ƙarasa da fashewa da kuka, iska ya furzar yana kallonta zai yi magana sai aka turo ƙofa Hudah ce bayanta mu'azzam ganinsu bai sa Hibbah ta daina kuka ba sai ma kifewa da tayi ta ɓoye fuskarta tana sake fashewa da sabon kuka.. Wani irin abin kunya ne wannan wani irin kuskure giyar soyayya ya sa ta aikata? Taya za ta fara haɗa idanu da mijin 'yar uwarta? Ba za ta iya ba ta tabbatar likitan nan ma da ke nuna tausayawarshi gareta bai san me ta aikata ba ne ko kuma hotunan tsiraicinta da ta tabbatar miliyoyin mutane zuwa yanzu sun gani bai riske shi" ba ne. "Ficewa ya yi da ga ɗakin ganin Hudah ma ta fara nata kukan sam baya son kukan mace shi mutum ne mai rauni da tsananin tausayi, ya je wuce Nurse station ya ji wata Nurse tana faɗa wa wata" """ke wallahi yarinyar nan ce a amenity room 8 duba da kyau ita ce wacce gabaɗaya media ya ɗau dumi a kanta sabon update nata ya bayyana, ai ita ce wacce aka fasa aurenta a jiya an ma ce mahaifinta har tsine mata yayi...""" "Runtse idanu yayi yana jin ba daaɗi har ranshi a hankali ya wuce su zuwa office ɗin shi," wayanshi ya zara ya shiga Facebook ko scrolling uku bai yi ba ya gamu da hotunan da sauri ya kife kan wayan yana ambaton sunan Allah. "*Littafin nan na kuɗi ne ki biya Naira Ɗari biyar (500) kachal domin kasancewa cikin masu kwasar tarin ilimi, faɗakarwa da zazzafar soyayya mai cike da sadaukarwa da aka zube ciki. Za ki biya ta wannan asusun" 0545475847 Gt bank Fatima Muhammad Gurin Sai ki tura shaidar biya zuwa wannan layi 09039206763 Ko kuma katin MTN na Naira 500 cikin wannan layi na sama sai ki tura da shaidar biya ta same layi. Sai na ji ku* Note: Da dare ne zan dinga posting da rana zan bi in dinga karanta comments naku so please a ba ni haɗin kai mu tafi lafiya kaman yadda muka fara lafiya. Na gode sossai. Gureenjoh SAFARA A TAƁO FATIMA MUHAMMAD GURIN *GUREENJOH* *ADABI WRITERS ASSOCIATION* *PAID BOOK* *003* """Hibbah...!""" Hudah ta ƙira ta tana dafa bayanta. "Bata amsa ba, ba kuma ta motsa ba sai kukan da har yanzu bai tsaya mata ba take rerawa a hankali." "Kallon mijinta tayi hawayenta na zuba ta mishi alamun da ya je waje, juyawa yayi ya fita bayan ya sauke gauron numfashi." """Twinee kar ki juya bayanki gareni, ki juyo ki kalleni 'yar uwarki ce da duk tsanani ba za ta taɓa gudunki ba, ki sani duk wani jarrabawa ko ƙaddarar rayuwa bai isa ya raba mu ba tunda a tare Allah ya hallice mu. Na zo ga kafaɗata ki tashi ki yi kukan kar ki yi ke kaɗai...""" "Rawar da muryarta yake yi ne ya yanke maganar, Juyowa Hibbah tayi ta yunkura zaune tare da" ɗora goshinta kan kafaɗar Hudah """Twinee na aikata shirme..! Na yi babban wauta ban sani ba!! Ban san ya zan yi ba mutuwa kawai zan yi Twinee ta ya zan fara cigaba da rayuwa??""" Hanci Hudah ta ja hawayenta na ɗiga a bayan Hibbah tace """Ba zan ɓoye miki ba twinee am very disappointed in you! Na matuƙar raina wayonki a wannan ɓangaren, ban taɓa zato zaki iya aikata hakan ba! Iyayenmu sun shiga cikin tsananin fushi sun kasa sauraron uzurin da zan miki Dukda na san uzurin nawa duk shirme ne tunda kin juye min twinee, kin zama min baƙuwa wacce ban sani ba daga jiya zuwa yau. Tashi twinee tashi ki faɗa min...""" Ɗago kafadunta tayi ta riƙe ta tana kallon cikin idanunta """Da gaske ne..? Twinee da gaske kin watsar da tarbiyarmu? Yanzu a haka sagir ya san ki matsayin mace?""" "Idanunta ne ta ji sun yi mata duhu jinin jikinta na tsitsinkewa, kwakwalwarta na maimaita mata tambayar 'yar uwar haihuwar ta..." """Innalillahi wainna ilaihi rajiun..!""" Da Hudah ke ta maimaitawa jikinta na ƙarasa mutuwa hawayenta na kara gudu su suka dawo da ita cikin tunanin da ta faɗa sai dai bata ce ko tak ba bayan kukanta da ya tsaya chakkk. Sun fi mintuna uku cikin wannan hali kan Hibbah ta ce da ƙyar """Hudah Daddy ya tsine min ko?""" Girgiza kai hudah tayi """suna fushi ne shiyasa basu zo inda nake ba ko?""" """Hibbah ko wanene dole yayi fushi! Daddy yayi wa Mu'azzam umurnin ya ɗaukeni mu tafi tunda an riga an ɗaura aure don na dame su da magiya da roƙon su yi haƙuri, ya ce kar in sake zuwa gidanshi sai ya neme ni ya ce Mu'azzam kar ya bar ni in zo inda kike amma nayi ta roƙon shi har ya amince ya kawo ni!""" "Gefe kawai Hibbah ta zubawa idanu fuskarta very pale, a yanzu hawayen sun tsaya mata tun kalaman Hudah na ta rasa ƙimarta a waje ya dake ta a lokacin ji tayi bata buƙatar proving ma wani taliki cewa ba hakan bane ko hakan ne. Allah da ta yi wa laifi shi za ta nemi gafarar shi ba mutanen duniya ba..." """Kan ku tafi ku tsaya a sallameni, na riga na ji sauƙi. Shine alfarma na karshe da zan roƙa a" "gareki twinee don ba ni da waya ba ni da card ɗina ban san ta ya zan biya bills ɗin ba"" ""Me kike nufi alfarma na karshe ina za ki je??""" Hudah tayi hanzarin tambaya zuciyarta na tsinkewa. Ga mamakin ta sai ta ga murmushi mai nauyi a fuskar Hibban """Ina kike tunanin zan je? Gidanmu mana! ina da wani wurin ne bayan nan??""" "Numfashi mai nauyi Huda ta sauƙe kan ta ɗauke idanunta tana lissafin abin da Hibbah ke kissimawa a ranta, wani lokacin bushewar ido da rashin damuwa akan ko ma menene na Hibbah na bata tsoro. Wa zai kawo za ta dake a yanzu yanzu kaman ba wacce ta yini kuka jiya ta kwana cikin fitar hayyaci kuma ta tashi da kuka ba!" Miƙewa tayi daga ita sai doguwar riga marar nauyi gashinta da ya sha gyara a hautsine sbd yadda jikinta yayi tsami gefen idanunta jini ya kwanta na duka da kyar take motsa jiki haka Hudah ta zaro mayafin doguwar rigar dake jikinta tunda ta ɗora hijab har ƙasa a kai ta yafa mata suka fito a tare. "Mu'azzam da ke zaune idanunshi zube wuri guda ya waigo jin motsin su, ganin su biyun ne ya" sa ya miƙe tsaye """Sannu Biyuni ya jikin?""" "Ba tare da ta kalleshi ba ta ce ""Alhamdulillah na gode""" "Huda ta isa gangarshi ya riƙo hannunta suna magana a hankali wanda bata jin su, kallon da ta" musu sai ta ji wani abu ya soki zuciyarta tunanin Mahmud ya shiga bijiro mata har sai da tayi ta gaske ta iya daidaita tsayuwa da numfashinta a lokacin Mu'azzam ya kalleta """Ki zauna Biyuni bari na yi magana da likitan""" Zama suka yi ya tafi. A chan office na Dr Najeeb yana zaune yana duba wani file idanunshi sanye da farin tsiririn glass na ƙarin karfin ido ganin Mu'azzam ya sa ya rufe file ɗin tare da miƙa masa hannu suka gaisa. """Batun patient ɗin mu tace ta ji sauƙi ita gida zata shine na zo in tambayi ko za'a iya" "sallamarta?""" "Yana ɗan gyara zaman madubin idanunshi ya ce ""Wacce kenan?""" """Hibbatullah Mudassir Madaki""" Ɗan kallon shi yayi sai yanzu ma ya tuna fuskan don kallon fisha ya mishi da zai baro ɗakin """A gaskiya sallamarta a yanzu haka akwai hatsari Dukda zata iya tafiya ɗin amma bisa sharuɗɗai guda biyu. Na farko shine a kiyaye shigar ta damuwa sossai don tana developing wani kalar matsala da numfashinta damuwa na triggring ciwon, sannan bamu gama bincike ba za ta ke zuwa check up duk bayan sati biyu. Matuƙar kuna son lafiyarta da gudun matsala a tabbatar duk wani damuwa ba'a sanyata ciki ba please""" Kai Mu'azzam ya gyaɗa """Za mu yi ƙoƙarin hakan Dr.""" Sallama ya bashi ya fita ya biya bills ɗin kan ya koma wurin su. Suna zaune har lokacin babu mai cewa kowa komai a cikinsu don kowa da abin da yake saƙawa cikin ranshi. """Muje Hudah""" "Miƙewa suka yi tana daga baya yayinda suka jera a hankali har wajen asibitin. Taxi ne ya tarar mata huda ta buɗe mata baya ta shiga idanunta cike da hawaye, Allah ya gani bata son ta bar yar uwarta ta koma gidan, bata san me zai iya faruwa ba ba kuma lallai in ta kira ta samu labari ba, gashi Daddy yayi mata umurnin kar ta koma gidan sai ya neme ta muddin ta take kuma ta shiga uku haka tana ji tana gani drivern ya ja yar uwarta suka wuce, Mu'azzam ya janyo ta" zuwa motanshi ta fashe da kuka sossai. Rungumeta yayi tayi kukan ma'ishi kan ya ɗago fuskarta yana share mata hawayen """Hudah kun fa girma, Its high time da zaki daina sa damuwan 'yar uwarki cikin naki, saboda kun zauna ciki daya na wata tara kun kuma girma tare ba shi zai saka komai na rayuwarku ya tafi iri ɗaya ba. Ita ta yankawa kanta kazar wahala don haka ki kyaleta ta fige abarta ita kaɗai...""" "Wani irin kallo take Binshi dashi amma Bakinta ya kasa furta ko da kalmar A ne, gani take duk abin da zata faɗa ma ɓata bakinta za tayi akwai abin da ya isa ya hana zuciyarta shiga damuwa idan yar uwarta na cikin damuwa? Me yasa yake nuna kaman ba komai ba? Meyasa yake nuna mata kaman ba ɗaya suke ba? Leɓenta ta datse kawai ta zubawa titi idanu ya ja motar a" hankali ba tare da ya sake cewa komai ba. "Ta ɓangaren Hibbah drivern na jan motar hawayen dake maƙale ƙasan idanunta suka shiga sauƙa a hankali, ba kukan abin da ya faru da ita take ba tana kuka ne na rabuwa da 'yar uwarta da basu taɓa rabuwa da juna ba, duk inda zasu a tare suke zuwa haka duk inda zasu kwana a tare suke kwana, a yau 'yar uwarta ta tafi ɗakin mijinta ita kuma za ta koma ɗakinsu da suke su uku ta cigaba da rayuwa ba tare da ta san makomarta ba Tuna Mahmud da irin kalamanshi" "da alkawurranshi ta shiga yi, irin burin da suka ci na rayuwar da za su gina a tsaftaceccen gidansu na sunna, hawayenta sai suka ƙara gudu, zuciyarta ke zafi sossai ba na komai ba sai na rasa wani ɓangare nata don haƙiƙa ta ƙaunaci Mahmud da dukkan zuciyarta amma ƙaddara" ya rigayi fata ga shi yayi mata kololon nisa da bata tunanin har abada zai waiwayota. """Hajiya Hotoro ta ina?""" "A hankali ta iya furta kalmar ""GRA""" Cigaba da tafiya yayi tana kallon hanya ganin zai wuce ta nuna mishi Layin da gidansu yake ya "shiga kadan tace ya isa, sauƙa kawai tayi don already Mu'azzam ya bashi kuɗi ta shiga takawa" "a hankali ta nufi tamfatsatsen gate ɗin na gidansu. Babu kowa a gaban gate ɗin alamun masu gadin suna daga ciki, buga gate ɗin tayi sai taji ana tambayar waye? Bata ce komai ba don Bakinta nauyin magana yake ta sake bugawa sai aka buɗe" """Ah Hajiya Hibbah ce ashe, sannu da dawowa""" Bata ko kalleshi ba ta wuce shi ta nufi ciki. "Turus ta ɗan yi hangar mutane a tsaitsaye kaman hargowa ma ake wanda ta tabbatar bai wuci a kanta bane su Hajiya kamila ke kumfar bakin nan don ita da yaranta ne har da Amal dake amarya suke ta yada maganganu, bata tsaya ba ta nufi sashen mahaifiyarta a hankali tana tafiya ne kaman wacce kwai ya fashewa a ciki, kanta har juyawa yake jin irin maganganun da suke yi dab za ta shige ta ji Atika wacce Amal ke bi ma a haihuwa tace" """Ga shegiyar chan macijiyar sari ka noƙe...""" Nadiya wacce ita ce babba tayi hanzarin cewa """Ji yadda take abu kaman ta Allah ciki fall iskanci, wallahi Hajiya kar ki yarda saboda ita a ce an" "ɓata ma yarinyar ki babban ranarta irin wannan?""" "Tuni dangin Hajiya kamilar suka karɓa aka cigaba da zage zage da cin mutunci har da gadon iskanci tayi ai mahaifiyarta ma aikin gidansu kenan buzaye sadaka yallah dama me aikinsu idan ba yawon ta zubar ba? Runtse idanu tayi da ƙarfi tana dafe kofar sashen nasu, da a da ne ko sama zai haɗe sai ta daka tsalle ta isa tsakaninsu ta gaggayawa kowacce su abin da ya zo Bakinta amma ban da yanzu da ita ce silar komai, duk baƙar da za'a gayawa mahaifiyarsu ko su a yanzu ita ce sanadi... Da kyar ta iya tattaro sauran ƙarfin da ya rage mata ta tura kofar sai ta yi turus ganin Momma da family dinta zaune a babban parlorn ƙasan duk suna zaune ne jugum jugum ta yadda za ka tabbatar akwai abin da ke damunsu don fuskokinsu bai ɓoye ba, Tv ba'a kunne yake ba kuma babu mai magana cikinsu yayinda zage-zagen Hajiya kamila da dangin ta Ke ratsowa har cikin parlorn yana shiga cikin kunnuwansu yana isa ga zuƙatansu" yana soya su. "Duk idanu suka zuba mata yayinda Momma ta runtse ido alamun bata ƙaunar ganinta, duk ta yi wani iri kaman ba mommansu sarauniyar ado da gayu ba, tana sanye da doguwar hijabi farar fuskarta ya zama jajazir idanunta duk a kumbure alamun kukan da tayi a kanta babu misali hawaye ne ya gangaro mata, da kyar ta iya gaining courage" """Aunty kubrah ina kwana?""" "Bata amsa ba sai ma tsaki da ta ja ""Aunty Asiya ina kwana?""" "Itama bata ce komai ba kaman bata ji ba ma. ""Momm...""" """Kar ki kuskura ki ƙira sunana da kazantaccen bakin nan""" Kanta ta sauƙar ta kalli Zaitoon 'yar Autar Hajiya kubra kenan kuma ta girme ta tace """Sannunku Yaya Zaitoon""" Tana kai nan ta juya ta haura don duk cikin mutanen parlorn ita kaɗai ce babba da ita kuma ita ne take ganin ya dace ta gaisar bayan iyayensu mata daga ƙannenta har yaran Aunty Asiya babu wanda yace mata ci kanki. "Ɗakinsu ta wuce ta tura ta shiga a gyare yake tsaff kaman ba a ciki ake ta bidiri jiya ba, kai tsaye ƙasa ta zauna tana ɗora kanta bakin gadon nasu tana sakin tsiririn kuka. Daga inda take tana jin hayaniyar su Hajiya kamila da bai lafa ba har sai da Daddy ya dawo anan ta fahimci suna masifa ne akan ta ɓata musu auren Amal tunda daddy ya ce ba za'a sake wani event ba kuma akwai wanda suka shirya bayan ɗaurin aure ciki har da dinner amma duk ya hana, Amal sai kuka take tana cewa za'a raina ta ya za'a yi aurenta kaman na marar gata tana sake zuga mahaifiyar tasu dake ta zuba tijara Daddyn kuwa na shigowa ya tsefe su tasss ya kira Alqaseem ya zo ya ɗauki Amal ɗin, Atika da Nadiya yace kan ya fito su tabbatar sun bar mishi gida haka Duka sauran dangin Hajiya kamilar su fitar mishi daga gida. Nan ta kawo bore ta saka ai bai isa ya raba ta da 'yan uwanta ba in gaskiya ne Meyasa bai kori dangin Momma ba dayake ita ce matar so ya barta da 'yan uwanta ita kuma zai kora mata 'yan uwa. Sai da ya musu jan ido ya tabbatar mata idan ya shiga ya fito ya same su har ita zai hada ya kora idan" kuma tana kokonta ta hana su tafiya kan ya shige sashenshi. "Sanin halinshi yasa duk suka koma sashenta da baƙin ciki suka fara shirin tafiya, bai jima sashenshi ba ya fito shi da Alqaseem da bai jima da zuwa ba bayan ya fito ma sai ga Daddy Rabi'u da Uncle zubair suna shigowa sai da suka ga fitanshi da Amal dake ta kukan bakin cikin irin wannan aure da aka mata duk saboda wata banza Hibbah kan su ukun suka yi sashen" Momma. """Na je asibiti na samu an sallamo yarinyar nan ta dawo ne?"" Daddy Rabi'u yayi maganan kai tsaye yana kallon su Momma." Aunty Asiya ce tace """Ta shigo bai jiman nan ba""" """Ke Aina'u ƙira ta""" Daddy ya ba da umurnin hakan. Tana nan zaune inda take kanta a kife bakin gado Dukda irin ciwo da nauyin da yayi mata har tana ji kaman zai faɗo taji an banko kofa ko sallama babu taji Muryar Aina'un na cewa """Wai ki zo""" "Tana kai nan tayi waje, daidai Zaitoon na hauro wa da su Mumtaz, fareed, fadeel da kuma yaran Aunty Asiya su huɗu Asma'u, Hawwa, ummu aimana da khalid a parlorn saman suka" zauna da alama iyayen ne suka musu umurnin barin parlorn ƙasan za su yi magana. Hijab ta ɗora akan kayan jikinta da bata damu da ta cire ba duk ta yi wani irin zubewa lokaci ɗaya har tana jin iska na ɗaukarta don rabonta da abinci zata iya cewa tun shekaranjiya shima banda snacks da ruwa bata iya cin wani abu mai nauyi ba tsabar irin tashin hankalin da Sagir ya sakata ciki. "Wuce su tayi bata kalli kowa ba ta nufi ƙasa kafafunta har rawa suke yadda take jin idanu a kanta na iyayenta, a hankali take jin kunya na sassara duk gaɓoɓinta a yanzu a haka kila a tsirara suke kallonta Dukda hijabin da ta suturta kanta dashi amma kila su hoton chan shine a idanunsu kuma hakan ne, zuciyoyinsu zafi yake musu kunyar zamanta cikin ahalin su na rufe su, barin ma Momma da ta san bata musu sakewar da za su lalace ba, bata taɓa tunani akwai wani yaudara ko daaɗin baki na maza da zai watsar mata da Hibbah ba sai gashi kaman daga" sama ta shayar da su ruwan mamaki da tsoro. Chan nesa da su ta zube bisa gwiwowinta ko ɗaga kai bata yi ba bare ta haɗa idanu da ko da "ɗaya daga cikinsu ne har ma ta ga irin kallon kunya, haushi, baƙin ciki da suke jefanta da su." """Uban wa ya biya kudin asibiti har aka bari kika taho gida?"" Uncle zubair ne ya jefa mata tambayar a harzuke da ita." Tambayar ya saka dole ta ɗago idanu tana kallonshi tunani yake samarin banzanta ne suka biya mata bills na asibiti? Har suna tunanin lalacewar tata ta kai haka? """Kina kallona da soyayyun idanunkin nan da babu kunya a ciki? Na ce uban wa ya biya miki bills ya kuma kawo ki gida da aka ce a mota aka sauke ki?""" Sheshekar kuka Momma ta fara Aunty Kubra ta dafata tana bubbuga kafaɗarta. Murya a hankali tace """Mu'azzam ne""" Wayanshi ya zaro ya shiga kiran Mu'azzam din sai da ya tabbatar shine kan ya katse kiran hawayenta na sauka bisa hijabinta rashin yardar da ta chusa musu a zuciya ya kai a yanzu su kasa yarda da duk wani zancen Bakinta alhali sun san cewa ita bata iya ƙarya ko ɓoye ɓoye ba? """Hibbah""" Babanta ya kira sunan a hankali ta ɗago irin abin da take gani a cikin idanunshi ya sa ta tafi daga durkushe da take ta zauna a kan duwawunta tana fashewa da kuka mai cin rai. """Hibbah Meyasa kika zaɓi lalacewa bayan irin yardar da muka baki? Meyasa Hibbah? Me kika nema ban miki ba? Kuɗi? Sutura? Ci ko sha? Don Allah ki faɗa min ta inda na Gaza da na chanchanci hakan? Meyasa kika zaɓi kunyata ni cikin duniya?""" Irin yadda yake magana ya karya kowa a parlorn bata yi magana ba bayan kukan da take. Uncle zubair ya shiga tambayarta uban waye ta ba kanta da har take iya yi mishi hotuna tsirara ta tura mishi kaman rainon Turai? Bata ce komai ba duk yadda suka yi ta ƙi magana har maruka ya tsitsinka mata amma ta ƙi cewa komai bayan kuka sai kuma su yi haƙuri da ta kan furta a shaƙe. """Zubair ka kyaleta""" Uncle Rabiu yayi umurnin Aunty Kubra tace """Ki je ki tattaro wayoyinki da duka katunan bankinki ki kawo, tunda hanyar da kika zaɓa kenan waya ko karatu basu zame miki dole ba sai ki ta zama a gida amma ba zaki ci gaba da fita kina lalata mana zuri'a ba""" "Miƙewa tayi taje ta kawo musu komai nata na gadget system, ipad, waya da car key sai Atms" ɗinta. Daddy Rabiu ne ya zabi yi mata nasiha sossai akan ta tuba ta shiryu ko don mahaifiyarta da take cikin tashin hankali da damuwa ga tsangwaman kishiyoyi da ya ninku a kanta. Bayan tsawon lokaci da suka dauka kowa na faɗa mata abin da ya zo kanshi ko bakinshi inda mahaifiyarta da mahaifinta suke zaune baki shiru aka sallame ta ta miƙe ta haura tana tafiya da kyar. Ko da ta isa ɗaki a kan gado ta zube tana runtse idanu a hankali ta janyo bargo ta rufe har kanta jikinta rawa yake sossai kan ta ji an shigo an zauna a gangarta an kuma dafa ta. "*Littafin nan na kuɗi ne ki biya Naira Ɗari biyar (500) kachal domin kasancewa cikin masu kwasar tarin ilimi, faɗakarwa da zazzafar soyayya mai cike da sadaukarwa da aka zube ciki. Za ki biya ta wannan asusun" 0545475847 Gt bank Fatima Muhammad Gurin Sai ki tura shaidar biya zuwa wannan layi 09039206763 Ko kuma katin MTN na Naira 500 cikin wannan layi na sama sai ki tura da shaidar biya ta same layi. Sai na ji ku* Note: Da dare ne zan dinga posting da rana zan bi in dinga karanta comments naku so please a ba ni haɗin kai mu tafi lafiya kaman yadda muka fara lafiya. Na gode sossai. Gureenjoh SAFARA A TAƁO FATIMA MUHAMMAD GURIN *GUREENJOH* *ADABI WRITERS ASSOCIATION* *PAID BOOK* *004* Tun fitowarsu daga gidan take kuka take kuma kwashewa Hibbah Albarka yayinda Alqaseem ke ta ƙoƙarin ganin ya rarrasheta. """Haba my love! Har yaushe za ki tsaya a kanta kina ɓata precious hawayenki uhmm?""" """Ba Za ka gane bane amma Hibbah ta jima tana kwacemin abin da yake ni ya kamata in same shi, ta jima tana dakile min farin ciki a gidan nan a aurena ma bata bar ni ba?""" Ya riƙo hannunta ɗaya yana ɗan murza wa a hankali """A yanzu kam kin mata nisa My love kin manta ke matar aure ce? Matar ma ta Alqaseem Abba? Ko ta ina kin ƙere mata don haka ki kwantar min da hankalinki ki manta da wacce duniya duka suke kan jefa mata maganganu marasa daaɗi, ke fa a yanzu ko a gaban Allah ma kin fi ta" "daraja""" "Numfashi mai nauyi ta sauƙe sai ta tuna yadda hibban ta shiga gida a haukace, ta tuna wai yau Hibbah ce ake zagi a kan idanunta amma bata tanka ba tuni murmushi ya maye gurbin damuwa dake fuskarta ko a haka ta gode Allah, ta tabbatar a yanzu rayuwa sai yayi wa Hibbah kunci ba a gida ba ba kuma a waje ba ko ina zai zama ƙuna a gareta hakan kuma ya haskaka ranta, ta" tabbatar duk gidan sai sun yi murna daga ɗakin su har ɗakin Hajiya Zakiya. "Bata sake jinta cikin natsuwa da farin ciki ba sai da ta kalli gidan da Alqaseem ya shigo da ita da sunan nata, kalar motocin da suke jere wasu a rufe, kalar irin tsari da tsaruwar gidan sai taji zuciyarta kal lallai ta yi dace da ta zaɓi Alqaseem dama chan ta tsammaci hakan daga gareshi saboda irin motoci da yake hawa da kuma shigar da yake ta fara kula shi, tana so ko ta wannan ɓangare ta nunawa su Hibbah ita ɗin ta ƙere musu, kyaun nasu na banza ne tunda daga mijin da Hudah ta aura zuwa wanda yake shirin auren Hibban ya fasa duk basu kai nata dukiya ba ko" a farce kuwa. "Cike da farin ciki ta taka ƙasan shimfidadden interlocks da yayiwa gidan kawanya hannunta ɗaya cikin na Alqaseem ya taimaka mata ta ƙarasa sauƙa ya rufe gambun motar suka nufi ciki duk haƙorinta waje wane gonar auduga, bata ƙara tabbatar da yana da dukiya ba sai da suka shiga ciki Dukda duk kayan ɗakin mahaifinta ne yayi mata bisa ra'ayin ta sai dai deco da interior Designs na parlorn sun tafi da ita ga wasu chandliers da bata taɓa ganin ma kalar su ba a duniya Dukda nata mahaifinma mai arzikin ne. Har ɗaki ya raka ta" """Ki shiga kiyi wanka ki samu ki huta ko baby? Ko in zo in yi miki da kaina?""" "Ta karya wuya tana cewa ""uhm uhmm""" Yayi murmushi yana kashe mata ido kan ya juya ya fita ya barta da blushing har da juyi cikin tsananin farin ciki. **** "Su Hudah suna isa gidan da yake mallakin Mu'azzam mai ɗauke da ɓangarori biyu wanda ɗayan ya kasance na mahaifiyarshi ce da suke kira Hajiya sai ƙanwarshi da suke tare falmata, kai tsaye sashensu yayi da ita saboda ta huta don ba karamin sara mata kanta ke yi ba ga damuwa fallll zuciyarta yana tura kofar suka yi ido biyu da Hajiya da falmata da suke zaune cikin parlorn murmushi suka sakarwa juna ya matsa Hudah ta shigo kanta ƙasa ta tafi wurin" kafafun hajiyar ta shiga gaisheta. """Sannu Hudah""" "Hajiya ta amsa da shi yayinda falmata ma ta yi mata sannu. ""Ki isa ciki ki huta bari zan yi magana da Mu'azzam din""" "Miƙewa tayi ta nufi corridor da ta gani Dukda bata san ma kan gidan ba, ɗakuna biyu ta gani sai dai duk wanda ta taɓa a rufe Juyowa tayi da niyyar dawowa cikin parlorn ta faɗawa Mu'azzam" din kila ya bata makulli sai ta tsinkayi Muryar hajiyar tana cewa """Ni dai Allah ya gani ba don kaddara da ya riga fata ba da baka amshi wannan yarinya ba, tabbas ba don sai da aka ɗaura wannan abin ashhan ya faru da biyunta ba da na hana, ina dalili? Haɗa zuri'a da gurbatattu? Kaima ka san abokin ɓarawo baya rasa zama ɓarawo ka san" "ko tare suke yi na wanchan ɗin ne ya fito fili?""" "Maganganun ba ƙaramin duka suka kai mata ba a zuciya, jiri ya nemi ɗaukarta saboda tashin hankali tuni idanunta sun rine sun sauya hawaye na sintiri bisa saman fuskarta, kallon da aka juye yi musu kenan? Ashe ana judging wani da laifin wani? Innalillahi wainna ilaihi rajiun..! Take ta nanatawa ta juya da sauri ta bi wani karamin hanya da ta gani sai ya kaita zuwa ga kitchen ta ga wani kofa ta buɗe ta fita haraba ce mai faɗi yana dauke da bishiyar almond wanda muka fi sani da umbrella ƙasan bishiyar an zagaye da interlocks kai taje ta zauna tana kuka sossai, ta jima cikin wannan yanayi kan ta ji motsi sai tayi hanzarin share fuskarta Dukda idanunta basu ɓoye yanayinta ba ta yi yunkurin daidaita fuskarta ta miƙe tsaye daidai lokacin da Mu'azzam ya" tura kofan ya fito. """Hudah! Ashe kofofin rufe suke shine kika zo nan?""" Ta gyaɗa kai murya a sanyaye ta amsa """Na duba ganin a rufe shiyasa na tsaya kallon gidan kan ku gama magana da Hajiya""" Ya matso ya riƙe hannayenta """Fatan yayi miki ɗari bisa ɗari? Ko akwai abubuwan da kike so a chanza?""" "Ta ɗan yi murmushi da bai kai ciki ba tace ""Komai yayi masha Allah""" Janta yayi suka koma ciki ya kaita har ɗakinta ya tafi toilet ya tare mata ruwan zafi daga heater a bucket ya surka a jikin pampo ya kai wurin wankan ya ajiye kan ya dawo ɗakin """Ki shiga ki yi wanka bari na duba ko falmata ta kawo abinci sai ki ci ki sha magani ki samu ki" "huta ko? Na tabbatar kan nan ba zai rasa ciwo ba ga hidimar biki ga kuka""" Murmushi ta ƙaƙaro again """Na gode sossai""" "Fita yayi ta miƙe ta zame kayan jikinta tana karewa ɗakin kallo daidai misali komai yana nan a tsare kuma kayan da Daddyn nasu yayi musu na ji ne da gani, gidan ba zata kira shi cikin na manyan kusoshi ba sai dai masha Allah yana da kyaunshi kuma a tsare yake, harabar bashi da girma don ba zai ɗauki motoci biyu ba sai dai ɗaya, an zagaye gidan da wasu koraye da jajayen furanni masu tsari babu mai gadi don haka ta ciki suke rufewa da jamlock idan ka kira sai a je a buɗe maka, mai gidan kan fita da key idan ya dawo ya kan buɗe ya shigar da motar shi ciki kan ya koma ya rufe, parlornta na da ɗan girma madaidaici dashi da ya ɗauke kujerunta da dining table ɗinta mai six chairs ba tare da ya takure ko ya matse chan chan ba, kitchen ɗinta ma madaidaici ne da aka shirya mishi carbinates farare masu kyau sai kayan kitchen da iyayenta" mata suka yi matuƙar kokari a kai sun zuba abubuwan zamani da yaaayi kusan babu abin da zata nema ta rasa na aiki idan ta ga dama ma ba sai ta yanka komai da wuka ba don komai na gayu ne Aunty kubrah ta sayo su birjik daga Lagos nata da na Hibbah. "Ɗaki ɗaya aka bata don haka ɗaki ɗayan mahaifinta yayiwa kaya don na Mu'azzam da kanshi yayi kayanshi saɓanin wanda aka yiwa Hibbah na dakuna biyu da parlor biyu, inda na Amal dakuna har uku. Ko ɗarr bata ji ba don mahaifinsu kaya uku yake yiwa kowacce idan ɗakin naki uku ne a zube miki idan ɗaya ne a saka ɗaya a baki full kudin biyun ki nemi abin yi ko sana'a ko wani abin haka yayi musu, Dukda an yi ta cecekuce akan yanayin gidan na Mu'azzam ta nuna musu yana da rufin asiri kuma tana son shi a haka don shi mai zuciyar yi ne, don haka hankali kwance ta auri kayanta sai dai bata taɓa tsammatar irin kalaman hajiyar shi a kanta ko gidansu ba, har ta gama wanka ta fito ta shirya bata daina sake-saƙe ba tana gama sanya doguwar rigar" ya shigo ɗakin. Ta isa ta miƙa hannu da niyyar ta karbi tray da ya riƙo da kular abinci a kai ya zagayeta ya wuce yana furta """wa ya gayamiki amarya na aiki a ranar farkonta gidan miji?""" "Murmushi ta ɗan yi ya ajiye a gaban rug carpet ya zauna yana nuna mata gefenshi, a hankali ta taka taje ta zauna, da kanshi yayi serving ta karɓa ta fara ci a hankali tana juya kalaman mahaifiyarshi na ɗazu ta zura mishi idanu tana son jin ra'ayinshi a kan hakan sai kuma taji da ma bata tafi ba a dazu ta tsaya ta ji shi me yake tunani? Hure mata idanu yayi ta ɗan yi murmushi tana sauƙe idanun ƙasa har lokacin ita kaɗai ta san me ke wakana cikin zuciyarta." ***** """Hibbah! Ki tashi ki sanya wani abu a cikin ki, zama da yunwa ko azabtar da kai ba shi zai sauya abin da ya riga ya faru ba, don Allah ki cire duk wani damuwa ki fuskanci Allah ki nemi yafiyarshi ki nuna nadama ki kuma nemi gafarar iyayenmu shine babba ba kuka da damuwa ba"" Ta ƙarasa tana janye mayafin, fuskar hibban da ya zama jajazir ya kumbura sossai ya bayyana idanunta a rufe, bandegi da aka zagaye kanta daga goshin ya ɓaci da jini saboda yanayin motsin fuskarta na buɗe ɗinkin dake a wurin ba tare da ta sani ba Dukda tana jin zafi da raɗaɗi" daga wurin amma bata damu ba don na zuciyarta ya ninka hakan sau dubu. A hankali tace """Yaya Zaitoon ba na jin yunwa""" """Dole ki ji yunwa Hibbah yaushe rabon da ki ci abinci? Kin san Hudah ce ta kira ni ta sa na mata alkawarin za ki sa wani abu a cikin ki? Don Allah ki tashi ko tea ne ki sha gashinan kinji?"" Hawaye ne yake gangara daga gefe da gefen idanunta zuwa cikin kunnuwanta har lokacin bata buɗe idanu ba ta san kowa ya tsane ta dama, kowa kyamarta yake ji a yanzu kila har Hudah ɗin ma a ƙasan zuciyarta nadamar zamansu ciki ɗaya take, ina ma za ta iya mayar da lokaci baya? Ina ma ana iya hasaso gaba kan bawa yayi wani kuskuren da zai sauya komai har ya kai ga" buɗuwar baabin wani sabon ƙaddarar ba tare da shiri ko tsammani ba? """Hibbah!!""" "Zaitoon ta ƙira tana jijjiga mata kafada, a hankali ta buɗe idanunta dake a suntume ta yunkura Zaitoon ta taimake ta ta kai zaune, tea ɗin ta shiga bata da kanta tana sha a hankali duk yadda tayi ma da ta ci cake slice ɗin ko samosa da ta haɗo da su ta ƙi iya tea din ta sha rabin kofi kan ta furta a hankali" """Na gode""" Ta koma da baya ta kwanta. "Yinin ranar gabaɗaya Zaitoon a ɗakin tayi shi Dukda daga ita har Hibbah ba magana suke yi ba amma bata bar hibban cikin kaɗaici ba kuma wanzuwarta ya hana kukan da hibban take yi akai akai, babu abin da ke ɗaga su sai sallah yayinda Hibbah ke kwance kawai zuciyarta blank ita Zaitoon tana operating waya ne, Dukda irin abin da take cin karo dasu a Twitter da tiktok na cin mutuncin Hibbah da zuri'arsu zuciyarta a kuntace cikin ƙuna da damuwa shikenan kuma mutane abin da suke jira kenan, babu mai tunanin wani hali wacce abin ya sama take ciki, babu tunanin ta yaya hakan ya kasance an haɗa da ita da iyayenta da basu ji ba basu gani ba ana zagi ba tare da an hango laifin shi saurayin da ya fitar da komai ba, akwai laifinta tabbas tunda Its willingly amma kalaman sun yi mata muni har bata sanin hawaye na gangaro mata chan ta ji" Muryar hibban """A kaina ne ko?""" Ta Yi saurin share fuskarta """A'a Hibbah wani abin tausayi ne na gani anan""" Murmushi mai cike da ciwo ta ɗan yi wanda ko Bakinta bai buɗe ba tace """Uhmm Yaya Zaitoon ba sai kin ɓoyemin ba, na san halin mutanenmu na yanzu Jira suke, kaman adu'a ma suke abu ya faru da mutum mai muni da za'a yi ta yaɗawa, ko ban hau media ba zuciyata da kwakwalwata sun gama karanto min irin munanan kalamansu gareni ba ga mace ba, ba namiji ba, ba babba ba ba yaro ba duk zasu mance tasu matsalolin su rufu akan wannan.""" Zaitoon ta share fuska tace """Abin nan yana min ciwo Hibbah, ba tun yau ba na kan ji tsoron yadda mutane kan haɗu a kafar sadarwa da gayya a tasa mutum musamman mace a gaba da kalar zagi da cin mutunci wanda ko kusa addininmu bata koyar da hakan ba, wani abin ma sirrinka ne amma wani na chan yana neman bankaɗowa duk don ya samu mabiyar da idan zai mutu a yau da wuya ɗaya daga cikinsu yayi mishi Adu'a bare ya bishi har kabari ya taya shi zama, irin wannan cin zarafi ya tura mutane dayawa cikin halin tashin hankali da damuwa haɗe da ciwo mai tsanani, wani fa za ki samu shima da nashi zunuban amma na wani chan yake hange, wata uwar ma da nata lalatacciyar gabanta take zagin wata uwar daban da bata iya ba yarta tarbiya ba wlh media na iya kai mutum wuta idan ba mu yi hankali ba""" Ta ƙarasa da tsananin damuwa. "Shiru kawai Hibbah tayi don a zancen ta fahimci abinda ya saka Zaitoon kuka iyayenta ake tuhuma da rashin bata cikakken tarbiya alhali basu Gaza mata ba, kaiconta a matsayin 'yar da ta janyowa iyayenta tozarta, wani irin turiri take ji yana huruwa daga cikin zuciyarta me amfaninta a duniyar? Bata chanchanci cigaba da rayuwa ba bare tsammanin farin ciki, ta gama" taɓewa. Me soyayya ya ja ta ta aikata? Ina alkawarin da Sagir yayi? Ina rantsuwarshi na cewa iya idanunshi hotunan za su tsaya? Me yasa yayi mata hakan? Wani irin masifaffen kuka ne ya kwace mata ta shiga dukan kanta da ƙarfin gaske tana ihu da gunji. """Hibbah! Hibbah!! Hibbah keeee!!""" "Ihun kiranta da kokarin natsar da ita da Zaitoon take ne ya janyo hankalin Aunty Kubra da ta zo wucewa ta kofar ɗakin da sauri ta shigo, halin da ta iske Hibbahn ya sakata a cikin damuwa ya kuma karya mata zuciya da sauri ta ƙarasa ta rungumeta tayi luub jikinta tana kuka sossai da sossai, a hankali Aunty Kubra ke shafa bayanta" """Na yi kuskure Aunty amma wallahi na yi nadama, wallahi nayi nadama... Zuciyata rabewa zata yi gida biyu mutuwa zan yi! Me yasa mutane za su zargi iyayena da laifin da na aikata? Me yasa na zama 'yar kuka mai janyowa iyayenta jifa? Me yasa Sagir yayi min haka bayan duk alkawarurrukanshi gareni? Na zaci Mahmud zai zama yana da bambanci da shi sai dai kashhhh shima ya kasa sauraron uzurina ya tsinewa ranar da ya sanni, ya saka kafa ya shure duk soyayyar da yake ikirarin yana yi min. Kuskure ɗaya takk ashe yana iya kashe mutum? Aunty ko ban mutu ba ba zan moru ba, ba zan iya sake farin ciki ba, tarihi zai rubuta cewa Hibbah ta gama wanzuwa cikin mutane masu walwala cikin shekaru sha tara kachal a duniya..."" ""Shhhhhhh! Shhhh Hibbah ki yi shiru ki daina wannan sambatun babu wanda ya fi karfin jarabawar ubangiji ke kuma naki da haka ya zo...""" """Babu ruwan ubangiji ni na ɗora wa kaina Aunty... Duk komai laifina ne Allah...! Allah Allah na" "tuba""" "Yadda take yi kaman zata mutu ya sa Aunty Kubra dake zub da hawaye duban zaitoon ""Zaitoon dubo Abdallah da Nasir suna ƙasa maza maza su zo su ɗaukar min ita zuwa mota mu koma asibiti""" "Duk sai ta ruɗe ta shiga damuwa, da sauri yaran nata samarin waenda su ne Zaitoon ke bi ma a haihuwa suka shigo bata bari ma sun yi magana ba tace" """Maza..! Maza ku taimakamin da ita zuwa ƙasa bari na ɗauko mayafi ku hanzarta Abdallah"" Nasir shi kaɗai ma ya ɗaga ta chak don bata da wani kumari suka yi waje numfashi take ja da kyar hawaye kuwa wane pampo hannunta dafe da zuciyarta da take jin ya kusa fashewa a haka suka zo suka wuce Momma dake zaune a parlorn ƙasa da kallo kawai ta bi su har suka fice, Fitowar Aunty Kubra da mayafi bayanta Zaitoon ne ya sa ta sake mayar da hankali kansu har" suka fita bata ce musu komai ba kuma bata motsa ba. "A waje Nasir ya sanyata cikin motar da Abdallah ya karɓa na Momma tun zuwansu auren kasancewar Hotel ne suka sauƙa saboda su rage saukin zirga-zirga sai suka karbi motan, Daddy da ke tsaye suna magana da Uncle zubair dake tabbatar mishi a yanzu an yi kokari an sauke duka hotunan sai waenda suka yi saving suma idan har za su ɗora to automatically zai goge kanshi ko ya ja musu shafewar shafinsu gabaɗaya, ganin yadda suka fito ya sa dole suka" mayar da hankali kansu. "Zuciyar Daddy ne ya karye, ya ɗan cije lips yana kallonsu ba tare da ya motsa ba har suka bar" "gidan, numfashi ya sauƙe ya mayar da kanshi ƙasa a hankali ya furta" """Jarrabawa ne! Allah ya ba mu ikon cinyewa duka. Zubair ka bi su please a san menene problem ɗin kuma ku yi magana da likitan""" Kai ya gyaɗa kan Daddy ya juya ya nufi sashenshi shi kuma uncle zubair ya fice daga gidan cikin tashi motar. "*Littafin nan na kuɗi ne ki biya Naira Ɗari biyar (500) kachal domin kasancewa cikin masu kwasar tarin ilimi, faɗakarwa da zazzafar soyayya mai cike da sadaukarwa da aka zube ciki. Za ki biya ta wannan asusun" 0545475847 Gt bank Fatima Muhammad Gurin Sai ki tura shaidar biya zuwa wannan layi 09039206763 Ko kuma katin MTN na Naira 500 cikin wannan layi na sama sai ki tura da shaidar biya ta same layi. Sai na ji ku* Note: Da dare ne zan dinga posting da rana zan bi in dinga karanta comments naku so please a ba ni haɗin kai mu tafi lafiya kaman yadda muka fara lafiya. Na gode sossai. Gureenjoh SAFARA A TAƁO FATIMA MUHAMMAD GURIN *GUREENJOH* *ADABI WRITERS ASSOCIATION* *PAID BOOK* *005* "A wannan karo jikin ya rikice mata sossai don abu ne da bata taɓa kawowa ba, abu ne da ya" zame mata tamkar mafarki yadda komai yake suɓucewa daga hannunta a hankali tamkar yadda ake warware zare daga jikin maɗaukarta ko bakin saƙi da aka katse. "Dr. Najeeb ne bisa kanta da sauran nurses da suke taimaka mishi wurin kula da ita har sai da suka shafe sama da awa biyu komai ya daidaita ta yi bacci, ko da ya fito su Aunty kubrah ya shiga yi wa faɗa yana kara jadadda sai da ya ce a kula da ita amma gashi a ranar da aka sallame ta aka sake dawo da ita jiki babu daaɗi, yana da right ɗin kin karbanta ko ma yayi" reporting nasu tunda kasheta suke da niyya. "Basu iya cewa komai ba ya ce duk za su iya tafiya don ba za ta farka ba sai safiya, jiki a" sanyaye Aunty Kubra da su Nasir suka juya zuwa gida don dama uncle Zaid an ƙira shi ya tafi ko da suka koma gida basu samu su Aunty Asiya ba. Zaitoon ke tambayar Momma """Su Asma'u fa?""" Momma da take zaune shiru ta amsa cikin sanyayyiyar murya mai dauke da damuwa """Sun fita da mamansu gidan Hudah da ke za su koma Nasarawa gobe da safe, sun je su mata sallama su kuma ga gida though Daddy ya haɗa su da su farida duka akan Hajiya kamila na da" "saƙo suma kuma ya ce su je su ga gidan 'yar uwar su daga nan za su tafi gidan Amal""" "Aunty kubrah ta kai zaune tana duban zaitoon ""Je ki dafa min ruwan shayi please""" Miƙewa tayi ta nufi ƙasa yayinda Aunty Kubra ta kalli Momma da ke kallonta """Dole fa za ku sassautawa kanku ku kuma sassautawa yarinyar nan duba da irin halin da ta shiga wanda na tabbatar da son ranta ba za ta so hakan ta kasance ba, abubuwa ne fa suka haɗe mata goma da ashirin Fatima. Ga rashin masoyi kema kin san ƙunar shi, ga kunyar mutanen duniya ga fushin ku. Idan ba kuna so ta mutu bane ku binne ta don Allah ku rage" "wannan zafi da kuka ɗauka wallahi komai zai iya faruwa da ita a cewar likitan""" Momma ta mayar da kanta ƙasa hawaye na gangaro mata a hankali tace """Toh Yaya Kubra da haihuwar irin Hibbah ba gwara ɓari ba? A yanzu ma don ta mutu ba komai bane, raɗaɗin mutuwan da sai ya fi sauƙi da abin da nake ji a Yan """ """Kul Fatima! Kul na ce. Idan baki gode Allah ba ba zaki butulce mishi ba, 'ya'yanmu rahama ne a garemu kar ki manta tun kafin ki san menene a cikinki Allah ya riga ya rubuta duk abin da zai faru da wannan ɗa daga haihuwarsa zuwa mutuwarsa, ki yi istigfari kuma ki tofar da baƙin miyaun don naki mai sauƙi ne, waenda suke tattare kayansu daga gaban iyayensu su shiga duniya su kuma iyayen su ce me? Kin tabbatar da tana aikata abin da kuke zargi? Kawai hoto da kuka gani shikenan? Toh wallahi ki yiwa kanki karatun ta natsu. A yanzu ne ya kamata ki janyo ta jiki tunda har ta gane ta yi kuskure kuma ta yi nadama idan kika ture ta duniya faɗi ne da ita tsaff sai ta dulmiyar da ita cikinta kuma a hakan ma baki tsira ba don sai Allah ya" "tambayeki.""" "Jikin Momma ne ya sake yin sanyi, ashe a duk sadda ɗa zai aikata kuskure ya kuma gane ba kyamatarshi ko ture shi daga jiki ba ne zai sa ya chanza ya zama shiryeyye, irin yanayin da aka fita da ita ta tuna ta tabbatar da tana da yadda zata yi da ta goge afkuwar wannan rana amma inaaa wani abin baya taɓa goguwa tawadarshi ya riga da ya bushe. A hankali take jin za ta iya" sassauto wa daga irin fushin da ta dauka mai tsanani da Hibbahn. *** "Su Aunty Asiya kam da gidan Hudah suka soma, doguwar mota ce wanda yawanci na 'yan makaranta ne masu saka uniform, su wurin sha biyu ne ciki" Mujiba da ta kasance Autar su Amal a ɗakin Hajiya kamila bayan Nadiya da Atika. "Sai Nasiba, farida da Baby waenda su ne yaran Hajiya zakiya kuma Nasibar ce babba tana ma sa'anni ne da Mumtaz." "Sai Mumtaz da shi ke bi ma su Hudah a haihuwa bayan shi akwai Aina'u, Fareed da fadil daga" ɗakin mamansu. "Sai Aunty Asiya da yaranta Asma'u, Hawwa,Ummu Aimana da khalid." "Suna isa kofar gidan Hudah driver yayi parking suka shiga saukowa Nasiba ce ta fara tambayar ""Gidan kam ba shi da haraba ne da za'a sauƙemu a waje bainannasi kowa na kallon mu?"" Babu wanda ya tankata sai ƙannenta da suke dariya ƙasa ƙasa, Asma'u ce ta kira Hudah sai gashi ta zo ta buɗe suka shigo ciki tana rungumar Asma'u ɗin" """Ashe tafiya ya tashi da wuri haka Aunty?""" Tayi directing maganan zuwa ga Aunty Asiya dake jifan ta da murmushi. """Eh Hudah, tafiyan ya zo bagatatatan saboda jarrabawa da su Aimana za su fara jibi Litinin"" ""Allah sarki! Amma za mu sha kewanku. Mu isa ciki""" "Ta ƙarasa tana riƙo Twins da suka rungumeta suna murnan ganinta, ta ɗan kalli su Nasiba da sai taɓe baki suke Baby ke cewa" """Tabdijamm""" Dukda sun yi gaba suna ji Mujiba na cewa """Wannan shine koma baya a tashi daga birni a koma kauye. Allah ya kyauta wallahi""" Suka yi dariya da su Farida Dukda a tsakaninsun ma ba shiri bane na a zo a gani amma gwara tsakanin dakunan biyu da na Momma kam. "Ko da suka shiga parlorn su Aina'u sai yabawa suke su kuwa sai kushewa suke cikin kwainane da zallar iskanci, bata kula su ba ta tafi ta kawo ruwa da drinks ta ajiye musu, saƙonta na wurin Momma Mumtaz ya ajiye mata ta yi godiya tana kallon Aunty Asiya tace" """Twinee na fa? Baku kamo ta ta rakoku ba? Ko bata fara kewata ba?""" Fareed yayi carab yace """Tana ta kuka muna ta mata magana ta manna mana sha tara ko Fadeel?""" Kai ya gyaɗa yace """Ai dai Sister(Aina'u) ta ce bata da lafiya ne. Yaya twinee kin san me ke damunta?""" Hudah ta ɗan murmusa kaɗan Dukda damuwa da take dannewa ta ce """Ciwon kai ne Fadeel, ai ba ka ce za ka zama Dr ba? Toh sai ka fara da ita ko autan Momma?"" Kai suka gyaɗa daga haka zancen ya tafi don Momma ta ce bata so su gayamata Hibbah ta koma asibiti." Kaman suna kan ƙaya samm sun ƙi barin ma su wani zanta suka miƙe suka fito suna cewa "suna jiransu a mota, Aina'u ta ce" """Aunty kina jin abin da yaran nan suke yi?""" Ta Yi murmushi """Ba sai su yi ta yi ba su suka sani wallahi, sun kuma ci sa'a da ni suka fita da da Yaya Kubra ce da yanzu wani zancen kuma za'a shiga. Yaran su Hajiya kamila kam sai Fatan shiriyar Allah""" "Daga haka basu sake kawo maganansu ba, Hudah ta kaisu suka gagga gida tare da yi mata" "Adu'a, daga nan suka isa sashen Hajiyar Mu'azzam tana zaune suna kallo da falmata suka" "gaisa a tsaitsaye kadaran-hadaran kan a ce su gama su fito an kusa cika unguwar da horn wanda su Mujiba ne suka saka driver ya dinga dannawa har sai sun fito idan kuma suka ƙi fitowa zuwa adadin lokutan da suka diba sun rantse sai sun tafi komai Daddy zai yi yayi in sun je gida, sai kuma gasu sun fito Hudah ta rako su har wurin mota suka shiga ta dubi su Nasiba tace" """Ku gaida gida""" "Daga haka ta juya ta koma, ta san da Hibbah na nan wannan magana ma da ta musu da sai ta kusa kasheta da masifa kuma ba zata juri rainin nan ba sai dai iyayensu kullum su shiga musu" kuma ba zai ƙare kan hibban kaɗai ba har Momma. Daga yanayin unguwar da suka shigo ya sa Mujiba ta shiga washe haƙora """Kun ga inda ake batu... Ka fito cikin arziki ka kuma dulmiya cikin dukiya mai sunan dukiya, irin" "ci gaban da kowacce ke mafarki amma fa masu asali da nagartaccen tushe gaba da baya don mai rabin asali yayi kaɗan""" """Ke!""" "Mumtaz ya furta yana waigowa a hasale, ta Harare shi tana jan tsaki. Ya waiga kawai yana dan" datse haƙori. """Zancen gaskiya fa ka bari a yi ta babu ruwan ka ehee""" Baby ta faɗa Asma'u za tayi magana Aunty Asiya ta girgiza mata kai akan su yi shiru don dole basu ce komai ba. Murmushi Aunty Asiya tayi cikin yanayinta na sanyi wanda babu abin da ya raba su da Momma sai Aunty Kubra kuma ta fito a wuta don ta fi citta zafi ka taɓo ta har ma su kan ce ita Hibbah ta ɗauko ita kuma ta kan ce Uncle zubair dai da Babansu amma ita kam ba ita ba. "Ba ƙarya gidan Amal kam gida ne da ya amsa sunansa gida, komai ya ji wane a wani ƙasa dama ko a lefe nata ya sha bambam da na su Hibbah, ganinsu ya sa ta ji daaɗi har ƙasan ranta ba fa kuma wai na wani abu ba sai na alfahari tana jin a yanzu ne baƙin ciki zai kashe su har ma su koma suna ba da labarin irin gidan da suka iske ta ciki, a yangance ta musu iso suka" zazzauna. """Aunty ke kaɗai?""" Ta murmusa """Yana nan yana saman shi yana hutawa ne, shiga kitchen ki kwaso muku abubuwan taɓawa kin san duk masu aikin ya basu hutu saboda mu samu sararin hutawa mu biyu""" "Mujiba tayi dariya tana miƙa mata hannu suka tafa kan tayi kitchen cike da yanga, su Baby basu ɓoye hassadarsu ba kuwa don fuskokin su gashinan dai ga yanayinshi yayinda su Mumtaz kuwa ko a kwalar rigar su, arziki irin haka kuma sun saba shigarshi tunda mijin Aunty Kubra mai kuɗi ne sossai su kan je hutu akai akai wurinta Lagos." "Bare ma su basu da saka ido akan abin wani don Momma ta mugun koya musu gudun duniya," mai fusgar ce dai ɗaya da suke da ita da ta zama kaman zakkah a ɗakin nasu. Kafin su bar gidan sai da aka kusa dambatuwa don sossai iyayin Mujiba da Amal ya harzuka su Nasiba karshe ma Aunty Asiya ce tace duk su tafi kawai. Amal tace Mujiba ta zauna zata sa a mayar da ita haka suka bar gidan su Asma'u da Aina'u dai nasu dariya don rigimar dariya ya basu kaman ba sune yanzu suka haɗe kai suna kokarin ci musu mutunci ba amma dubi hassada karara tsakaninsu. Har suka isa gida kowa ya kama gabanshi babu wanda ya tanka a tsakaninsu sun kuma san rigimar kila ba zai kare ba kuma har iyaye matan sai sun tsunduma ciki. **** "A hankali ta shiga buɗe idanunta da suka matuƙar yi mata nauyi tana jin yadda gaɓɓan jikinta ke sassara wa, bata iya gani da kyau don haka bata fahimci inda take ba dishi dishi take iya hango shi tsaye bisa kanta yana jefanta da wani irin kallo lips ɗinta na rawa a hankali ta furta ""Maa..hmudd""" Da sauri ta runtse ido jin tsawarshi bisa kanta """Kar ki sake ambaton sunana da wannan kazantaccen bakin ashe musuluncin naki da kike nunawa a baki ne bai kai zuci ba? Kin cuce ni Hibbah kuma wallahi ba zan taɓa yafe illatarmin da zuciya da ruhi da kika yi ba, kaman yadda nake azabtuwa da rashin ki kuma ba zan iya auren ragowar wasu kartan titi ba haka kema ba zaki samu natsuwar zuciya ba...ke ce! Duk abin da zai sameki daga yanzu ke ce silar komai...""" "Da karfin gaske yake magana har tana jin yadda yake amsa kuwwa a cikin kanta, kunnuwanta ta dafe tana so ta yi ihu mai karfin gaske ko duniya za su fahimci zaucewa ne kawai ya rage mata kuma shima ya iso, Mahmud ya san me take ji kuwa? Ya san yanayin da take ciki kuwa?" Da ƙarfi ta ji.... "*Littafin nan na kuɗi ne ki biya Naira Ɗari biyar (500) kachal domin kasancewa cikin masu kwasar tarin ilimi, faɗakarwa da zazzafar soyayya mai cike da sadaukarwa da aka zube ciki. Za ki biya ta wannan asusun" 0545475847 Gt bank Fatima Muhammad Gurin Sai ki tura shaidar biya zuwa wannan layi 09039206763 Ko kuma katin MTN na Naira 500 cikin wannan layi na sama sai ki tura da shaidar biya ta same layi. Sai na ji ku* Note: Da dare ne zan dinga posting da rana zan bi in dinga karanta comments naku so please a ba ni haɗin kai mu tafi lafiya kaman yadda muka fara lafiya. Na gode sossai. Gureenjoh SAFARA A TAƁO FATIMA MUHAMMAD GURIN *GUREENJOH* *ADABI WRITERS ASSOCIATION* *PAID BOOK* *006* "Da ƙarfi ta ji an jijjigata wani hannu kuma ya rufe mata busasssun lips ɗinta, sai ta shiga ji ana kiran sunanta cikin sanyi da kulawa." """Hibbah! Hibbah Mafarki kike...Babu wani Mahmud a kusa da ke, buɗe idanunki ki ji ni""" "Numfashi take saukewa a hankali, kan ta buɗe idanun ganin ɗakin asibiti da kuma fuskan likitan da ba za ta iya tuna sunanshi ba ya sa ta tabbatar da mafarki ne kawai abubuwan da suka haɗe mata da irin kaunar da suka shimfida da Mahmud suka sa shaidan ke mata wasa da hankali, a hankali ta sake lumshe idanu tana ɗan muskutawa, chan ta ce" """Don Allah ƙarfe nawa?""" A ɗan hankali tayi maganan tuna akwai Sallar Magrib da isha a kanta don ta ga garin yayi duhu sossai da shiru alamun dare ya fara nisa. Wayanshi ya ɗan matsa ya ɗago ya kalleta """ƙarfe biyu na dare""" Ta ɗan buɗe idanun da har lokacin suke mata nauyi tace cikin Muryar mara ƙarfi """Ni kaɗai ce ko?""" "Numfashi ya sauƙe don kila tana tunanin yadda za ta kai kanta bayi ne tayi alwala kuma a wannan karo da gayya ya hana kowa zama da ita ba don komai ba sai don ta samu natsuwar zuciya da yake tunanin ta gaza samu daga kowa a zuri'arta, wani ko wata za su iya ganin abin da ya sameta da sauƙi amma macen da ta san kanta da mutuncinta kuma ta fita gidan tarbiya" dole ta shiga makamancin halin da ta shiga a yanzu. """Hibbah...!""" Ta kalleshi kaɗan ta kawar da kai don ita kanta kunyar kanta take a wannan yanayi da take ciki na fitar hayyaci. """Za ki iya cewa ina ruwana ko kuma me ya dameni da damuwar ki amma fa akwai ɗin, ni likitan ki ne kuma zan so miki samun lafiya da fita daga barazanar ciwon dake shirin shigo miki da ƙarfi. Ina so ki ba ni hankalinki na mintuna ki kuma saurari abin da zan fada miki""" Pale eyes ɗinta ta zuba mishi ba tare da ta ce komai ba """kowa na kuskure amma kar ki kuskura ki bari wannan kuskure ya bi ki har ƙarshen rayuwarki, ba zama nagari ke hana kuskure ba, kuma babu son zuciya a kuskure rayuwa ce ke koyar da darasinta ta wannan hanyar. Hibbah Madaki rashin kuskure baya taɓa gina mutum, darasin dake ciki shi ya kamata ya zama miki tushe da tubalin gina wata rayuwar. Kar ki taɓa tsanar kan ki saboda kuskurenki ki daina hukunta kanki ki ɗauke shi abin da ya wuce sai ki ga kin samu" "wata babbar damar ta gyara""" Sossai kalaman ke samun matsuguni a ranta tana jin su tamkar wani magani dake watsakar da tarin damuwarta. Bai tsagaita ba ganin yadda jikinta ke sanyi ya cigaba """Na tabbatar bayan ahalinki kina fuskantar barazana daga mutanen dake zagaye da rayuwarki especially social media da suka mayar da kalmar ""Update"" wani abin burgewa suke faɗin abin da alfahari da dariya a kan fuskokin su ba tare da sun san irin makomar da hakan kan zame musu ba saboda Allah bai bamu damar yi wa ƙaddarar wani dariya ba, annabi da ya nuna harshe sai yayi mana gargadi a kanta da Kuffa alaika haza don tabbas harshe na iya kai mutum ga wuta. Ina so ki sani duk irin kyau ko mugun halinki mutane za su yi magana amma wallahi No one owes you an explanation, any irresponsible person can judge by what they see without thinking twice saboda tsadar damar hankali da tunani da suka gaza samu""" Ya isa dab da ita har tana iya shakar kamshin turarenshi cikin taushin murya yace """Wallahi sau dayawa akuyar da ta hau kan katanga ita duniya ke gani baki san komai ba a kan irin rayuwar da mutane ke yi wasu dayawa suna nan dankare da kashi a karkashinsu amma suna yiwa wani dariya. You have to flight this situation and do what is right for yourself not to please anybody don daga zarar kika yanke hukunci don burge wani ko saisaita wani bayan" "Allah daga sannan kuma rayuwarki ya gama tabarbarewa.""" "Murmushi ya saki cike da taushi irin na kwararren likitan da ya san aikinshi, a hankali ta ɗan yi murmushi wanda zata iya cewa rabon ma da tayi irinshi tunda Sagir ya fara mata barazana yana amsar duk wani abin da ta tara don fansar abinda daga karshe bai fansu ba tunda gashinan a duniya." """Thank you""" "Ta faɗa chan ƙasa, ya gyaɗa kai sai ya juya ya fita." "Ba'a jima da fitanshi ba sai ga wata Nurse mace ta shigo ta taimaketa zuwa bayi bayan tayi tsarki tayi alwala ta fito ita ta kawo mata hijabi da sallaya ta zauna a zaune ta rama sallolinta tana idarwa ya shigo hannunshi riƙe da mug ya miƙa mata, ba musu ta karɓa harda cake da ya haɗa kuma ta shiga ci a hankali har ta ji ya isheta ta sake mishi godiya don yana zaune ne yana azkar rike da counter, sai da ya ga ta kwanta kan yayi mata sai da safe ya fice, bata tsaya" dogon tunani ba bacci yayi awon gaba da ita. "Ko da ta tashi da safe misalin ƙarfe bakwai bayan ta koma da tayi sallah jikin sossai ya sake ta, nauyin da zuciyarta yayi mata ainun ya rage haka take jinta kaman bata da wani damuwa saboda ta riga ta karɓi kuskurenta kuma ta shirya gyarawa, da kanta ta shiga toilet ɗin ta ɗan wanke bakinta da fuskarta ta fito, tana fitowa ana turo kofan ɗakin Dr Najeeb ne bayanshi wata" babbar macece sai wata budurwa da zasu iya yin sa'anni suka shigo. "Fuska a sake ta gaishe shi ""Ina kwana Dr.?""" Yana murmushi ya furta """Masha Allah! Jiki yayi kyau Hibbatu. Kin tashi lafiya?"" Ta gyaɗa kai kan ta dubi matar tana ɗan duƙawa tace" """Ina kwana?""" """Lafiya ƙalau Hibbah ya jikin dai?""" Tace """Alhamdulillah da sauƙi. Ga wurin zama""" "Tayi maganan tana nunawa matar mai cike da fara'a kujera ta kuwa zauna, yarinyar da suka shigo da ita ma tayi mata sannu ta amsa." """Ummana ce, dama dai ana ji da ni da duk na kwana a asibiti kuma zan kai rana sai an turo min abin kari da nace ta haɗa da ke shine tace bari ta zo da kanta ta samu ladar duba marar lafiya""" Murmushi kuwa tayi """Sannu Umma mun gode sossai Allah ya ba da lada""" Murmushi Umman tayi """Ameen ɗiyata. Nihla saka mata abinci ta samu ta ci ko zata ƙara jin karfin jikin""" "Yarinyar da ta kira da Nihla ta shiga zuba mata kuwa, farar shinkafa ce da kidney sauce sai kunun gyaɗa babu musu ta amsa ta shiga ci a hankali daidai sallamar su Aunty Kubra, Zaitoon, Ya Nasir da Momma." "Sai da ta nemi ƙwarewa ganin Momma a asibitin, a hankali ta ajiye spoon ɗin kanta ƙasa Aunty" Kubra ke furta """Masha Allah! Barkanmu jiki ya fara kyau sannu Hibbah""" "Kai ta gyaɗa tana furta ""Ina kwana?""" """Lafiya ƙalau Alhamdulillah, baki ganmu da wuri ba sai da muka ajiye su Asiya a airport ne ya" "karfin jikin?""" Ta amsa da Alhamdulillah. Ta ɗan dubi Momma kan ta gaisheta da mamakin ta kuma ta ji ta amsa har tana karawa da ya jiki ta amsa da sauƙi a hankali. Duk zama suka yi suka shiga gaisawa da Umman Dr. Najeeb har godiya suka yi mata kan ta miƙe tana yi musu sai anjima ta fice. "Zaitoon ta zauna a gefen ta tana ƙara sakata cin abincin da ta koma ci a hankali ganin mommansu a ɗakin sai taji kaman wata bakuwar ce ta daban ba mahaifiyarta ba, Sun jima sossai har ta gama cin abincin suna hira Dukda daga Nasir, Zaitoon da Aunty Kubra ne ke" involving ɗinta shima sama sama take amsawa. "Bayan fitansu daga ɗakin Nihla ta kalli Dr. najeeb tana furta ""Ya Njeeb ba wannan ce yarinyar da media ta ɗauki magana...""" "Kallon da yayi mata ya sa tayi shiru Umma da tun suka fara zancen a gida da sauran ƙannenta biyu mata ta kwaɓe su kuma tausayin iyaye da ita kanta Hibbahn ne ya rufeta don har cikin sallah ta saka ta a Adu'a, ta harareta" """Wallahi ku kiyaye yamaɗiɗi da kuma dariya da ƙaddarar wani ba fata ba amma babu wanda ya" "san inda rana zata faɗi...""" """Umma ki yi haƙuri""" Ta girgiza kai tana cigaba da yi mata nasiha har ya raka su mota ya koma office. **** Kaman yadda kowasu Amare ke tafiyar da dararensu na farko gidan miji haka ta ɓangaren Amal da Hudah ya tafi don sun sha soyayya da kauna ba ƙarya tare da alkawarurrukan da babu wanda zai san da tabbatar cikinsu ko akasin hakan bayan Mahalicci. "Ko da gari ya waye Mu'azzam shi ya taimakawa Hudah ta sake kintsa gidan, bayan sun gama suka nufi sashen Hajiya don kai mata gaisuwa suka sameta zaune da falmata suna shan ruwan bunu ganinsu ya sa hajiyar ta gyara zama suka duƙa ƙasa suka shiga gaisheta cikin girmamawa" """Muna ta zuba idon abin kari kuma shiru?""" "Ta jefa tambayar ga Mu'azzam, ba shi kadai ba har Hudah sai da ta ɗago ta kalleta ganin sun" hada ido ya sa tayi ƙasa da kai. """Ban gane kuna kallona ba? Yanzu a tunaninka da tsufana da komai kana da mata sai na shiga kicin na yi girki? Idan ma bata zo da babban tukunya bane to ta zo na bata aron shi don girki dai yanzu ba za mu sake yi a wannan sashe ba""" Ya ɗan sosa kai yana furta """Wai na ce Hajiya ko za'a dan bari ta kwana biyu kan ta fara? Ga falmata ba sai tana yi ba idan ma ta fara ɗin sai su haɗu suna yin bibbiyu""" """ita ta ce maka falmata na zaman banza? Yanzu da ka gantan nan makaranta zata shiyasa take shan wannan bunu, kuma dai wannan aiki ai na me ɗakinka ne tunda itama gidan wani zata ta samu nata ladar""" Ganin zai sake magana Hudah ta ɗan ja gefen riganshi tana ɗan murmushi """Ki yi haƙuri Hajiya in shaa Allah yanzu zan je sai in yi in kawo""" "Bata amsa ba sai taɓe baki da tayi ita kuwa ta miƙe zai bi bayanta hajiyan ta tsayar da shi, tana zuwa kuwa ta shiga kitchen ta hau girki don komai tana da shi na gararta cike a karamar store ɗin nasu, sam zuciyarta ɗaya ta gama ta zube a warmers masu kyau ta kai musu, bata yi mata tayin zama ba itama kuma bata nemi zaman ba don tana so ta sake watsa ruwa ta fice, a takaice bata ga idanun Mu'azzam din ba sai wurin sha biyu da arba'in shima alwalar azahar ya" shigo zai wuce masallaci. ** "Ita dai Amal ƴar gata ce saboda komai Alqaseem ne yayi mata a ranar yana cika ta da soyayya yana riritata wane kwai, komai daga kan gado ake mata sai ta ji kanta na sake yin girma, ƙauna da tarin soyayyar Alqaseem ɗin na ƙara mamaye mata zuciya da bargo tana jin ta fi kowace" mace sa'a. *** "Kwanan Hibbah biyu a asibitin wannan karo kuma Alhamdulillah har Daddy da kanshi ya zo sau ɗaya, sossai Dr. Najeeb ya tsaya mata kuma yayi mata ƙoƙari wurin ganin ta samu lafiya, haka mahaifiyarshi kan kira a waya ya haɗa su ta gaisheta da jiki mace mai kirki da sanin darajar dan Adam, bai sallame ta ba sai da suka yi alkawarin duk sati biyu za ta ke zuwa asibitin ana duba" lafiyarta. Dukda ba za'a ce ta manta komai ba amma sossai damuwar ya ragu mata kuma idanunta zuwa "yanzu suka bushe da zubar da hawaye, ko da ta koma a Washegari Zaitoon dake debe mata kewa suka tarkata suka koma legos abin su, ya saura su ya su a gidan." "A koyaushe tana ɗaki a kwance bata sakewa da ƙannenta bare a kawo zancen ma Fitowar ta zuwa harabar gidan ko hulda da wani ko wata daga waje, tsakaninta da Aina'u gaisuwa tunda ɗaki ɗaya suke haka Momma da Daddy duk za ta sauƙa ta gaida su kan ta dawo ɗaki sai kuma Washegari da safe, ta zube sossai kuma ta yi duhu kaman ba Hibbah sarauniyar gayu ba, kasancewar cimanta ba kaman da ba ya sa ramar ma bai ɓuya ba tana kewan 'yar uwar ta" sossai tana so ko muryarta ne ta ji amma tana tsoron karbar aron wayan wani ta kirata. "Yau ya kama Asabar a sashen Daddy ake karyawa don haka Momma da ke da girki da masu aikinta chan suka jere duk wani abu da za'a bukata wanda zai ishe duk ahalin kan ta dawo ta shirya cikin atampharta doguwar riga da ya ji ɗinki tayi ɗaurinta daidai da shekarunta su sarka da abin hannu duk bata bari ba ta fita fess da ita a buzuwarta, sai da ta haɗa kan yaran ta tura su kan ta haura zuwa inda ta san za ta samu Hibbah don ko jiya sai da suka sake tattaunawa da Aunty Kubra akan hankalinta bai kwanta da barin Hibbahn a gidan ba saboda ta san har yanzu suna chusguna mata, ita Momma ta kawo uzuri da cewa sai a hankali zata manta Dukda tabo ne da babu ranar warkewarshi don har meeting ta je cikin last week an yi mata zancen da ya sosa ranta akan hakan. Ta dai yi wa Aunty kubrahn Alkawarin sake sassauta wa don haka" da kanta ta tura kofar. Hibbah dake jingine da gado hannunta riƙe da counter ganinta ya sa ta ɗan zabura ta miƙe zaune da kyau. """Kin manta yau Asabar ne?""" Sanyi ta ji a ranta don bayan gaisuwa da ya jiki wannan ne karon farko da magana mai tsawon words biyar ya shiga tsakaninsu da momman tun bayan tarwatsa aurenta da Sagir yayi. """A'a zan sauƙo yanzu""" "Kai momman ta gyaɗa tana juyawa ta ce ""Make sure kin yi looking presentable"" Tana kai nan ta fice." "Miƙewa Hibbah ta yi dama ta yi wanka sai ta nemi doguwar rigarta wani simple egyptian Abaya peach ta saka ta saka gyalen ta duba fuskarta a madubi duk ta susuce don haka ta ɗan murza powder tare da saka lip balm ta fito a hankali take tafiya iska na ɗaukarta har ta isa ga sashen na mahaifinsu, da sallama ta shiga kusan kowa ya hallara hakan ya sa ido duk suka dawo kanta musamman su Hajiya Zakiya da Hajiya Kamila da tunda abin nan ya faru basu sanyata a ido ba" kuma basu nemeta ba. """Ina kwana Hajiya?""" """Aw ashe fa kina gidan, ni wlh na ma manta da baki yi aure ba baiwar Allah sannu!""" "Momma ta ɗan runtse ido ta buɗe, Daddy zai yi magana Hajiya Zakiya tace" """Ina za ki tuna da ita tunda ta zama matar kulle, ni na zaci ma mahaifiyarta ce ta hanata zuwa gaishemu don bamu kai zama iyaye a gareta ba""" Momma bata ce komai ba kuma dama yaranta da ma mijinta sun san ba lallai ne ta ce ɗin ba idan ba makura suka kaita ba. Daddy ya ce """Mamana Meyasa bakya zuwa gaishe su?""" Kanta ƙasa tace """Kayi haƙuri Daddy, dama ban samu ƙarfin jikin bane amma zan gyara""" "Duk sai da suka sake kallonta hatta Daddyn da yayi magana lallai rayuwa mai chanza mutum, ya san da a da ne zata iya tuburewa akan bata yi laifin komai ba ai itace bata da lafiya basu je sun gaisheta ba amma ji yadda take bada haƙuri basu so hakan ba amma dai suka danne, ta zauna kusa da Mumtaz shi ya miƙe yayi serving nata tace thanks a hankali ta shiga wasa da" cokalin. "Sun jima sossai a sashen don ko da aka gama cin abinci parlor suka dawo kowa na laying bukatunshi da burin shi na gaba ga Daddyn Dukda ita Momma ta karanci akwai dan abinda ke damunshi har dai duk suka gama suka watse Hibbah bata ce komai ba, sai da ta ji shiru ma ta" "san an watse ɗin don ta yi zurfi cikin tunani, ta miƙe don fita kenan ta ji Daddy ya kira sunanta.." "*Littafin nan na kuɗi ne ki biya Naira Ɗari biyar (500) kachal domin kasancewa cikin masu kwasar tarin ilimi, faɗakarwa da zazzafar soyayya mai cike da sadaukarwa da aka zube ciki. Za ki biya ta wannan asusun" 0545475847 Gt bank Fatima Muhammad Gurin Sai ki tura shaidar biya zuwa wannan layi 09039206763 Ko kuma katin MTN na Naira 500 cikin wannan layi na sama sai ki tura da shaidar biya ta same layi. Sai na ji ku* Note: Da dare ne zan dinga posting da rana zan bi in dinga karanta comments naku so please a ba ni haɗin kai mu tafi lafiya kaman yadda muka fara lafiya. Na gode sossai. Gureenjoh SAFARA A TAƁO FATIMA MUHAMMAD GURIN *GUREENJOH* *ADABI WRITERS ASSOCIATION* *PAID BOOK* *007* """Na'am Daddy""" Ta amsa a sanyaye tana komawa zaune. "Momma da take kallonsu sai ta ji zuciyarta ta sake karyewa, ta san irin kaunar da mahaifinta ke mata, ta san irin kusanci da fahimtar juna da suke dashi bata san wani irin ƙaddara bane ya ratsa rayuwar ɗiyarta amma a yanzu tana fata ko ma menene ya tsaya iya hakan." Ko ma menene tana Adu'a Allah ya sa ta hankalta da darasin da rayuwa ke son koya mata. """Yaushe za ki koma asibiti checkup?""" Ta ce """Ranar monday ne""" """Toh Allah ya kaimu, batun makaranta nake son in miki 'yar uwarki zata koma Litinin ya kamata a ce kema kin koma ɗin""" Da ɗan sauri ta kalleshi don bata taɓa zaton zai bari ta cigaba da fita a gidan da sunan karatu ba ko Momma mamaki ne ya rufeta. """Kina mamaki ko? Ai ƙaddarar da ta ratsa ba zai sa in katse miki neman iliminki ba Hibbah, ki koma makaranta ki yi karatu ina fata a wannan karo za ki natsu wurin mayar da hankali akan abin da yake daidai. Akwai driver zai na kai ki ya ɗauko ki, wayoyinki kuma zan duba sadda ya" "dace sai in mayar miki""" """Na gode sossai Daddy""" "Ta amsa fuskarta na nuna sakewa alamun ta ji daaɗin zancen komawa makarantar, bayan ta musu sai da safe ta fice Momma ta dube shi." """kana gani ya kamata ta koma makaranta a yanzu?""" """Me zata zauna ta yi mana a cikin gidan Fatima? Babu abin da zai hanata karatu tunda tana da burin yin abin ta kuma ta fara nisa sai dai zan tabbatar mun saka idanu a kanta ƙwarai da gaske Dukda na san mawuyacin abu ne ta sake maimaita kuskurenta na baya! Fatima na yarda da kaddara ce kawai ta faɗa mata amma ban yi zina ba kema haka na tabbatar Allah ba zai" "jarrabemu da dattinta cikin zuri'a ba""" Numfashi ta sauke tana furta """Allah ya tsare mana su gabaɗaya. Ameen""" "Shiru suka yi na tsawon mintuna kan ta sake cewa ""Anya babu abin da yake damunka Daddyn yara?""" Ya sauke gwauron numfashi zuciyarshi babu daaɗi yace """Abubuwa suna damuna Fatima, Dukda ɗaya ya fi ɗaya tsayamin a rai fiye da shekaru ashirin da tara zuwa talatin na kasa manta kuskuren da na aikata, na kasa cire abin a raina""" Fuskarta ya nuna damuwa ta san abin da ya faru da Hibbah ne ya tado mishi miƙin abin da ya faru da jimawa wanda ko ita a lokacin da ta aure shi labari ne ta ji kuma ba kasafai yake maganan ba sai in ta ciyo shi a rai ta ce """Allah yana sane da wannan lamarin kuma zai yi ikon shi a kai, ka ƙara haƙuri ka san wannan matsalar ne ya janyo maka ciwon zuciya da kake fama da shi ka daure ka danne kar kuma wani abin ya sake faruwa da kai""" Kai ya gyaɗa. """Ya kuka yi da 'yan jam'iya?""" Murmushi ya ɗan yi marar zurfi """Siyasar nan karshe jingine ta zan yi in koma kasuwanci da dama shi na fi wayo, sun fara min wasa da hankali suna kokarin ja na a ƙasa daga partyn masu adawa zuwa namu, gani suke muddin aka zo zaɓe sai an sake tono lamarin Hibbah wanda dole zai rage kima da yawan adadin daraja ta da mutane za su gani har su zaɓe ni a karo na biyu amma ban damu ba." "Komai da zai faru Allah ya riga ya kadarta""" Tunda ya ce haka ta san ya gama yardarwa zuciyarshi ne cewa hakan shine tsarin Allah kuma ba zai taɓa bari a fuskarshi a yi wa ƙaddarar yar shi dariya ba. Sun sake taɓa hira kadan kan ya fice masallaci ita kuma ta koma cikin gida. "Hankalin Hibbah ya sake kwanciya ganin iyayenta sun sassauto sossai don cikin kashi ɗari na haushinta da suke ji a yanzu bai wuci kashi talatin ya saura ba don dukkanin su ba gwanayen midiya ba, tunda kuma Daddy Z ya tabbatar an sauke ya kuma kafa tsatsaurar tsaro akan wanda zai ake ɗora videon hankalin duk wani masoyinta ya kwanta, ranar monday bata je" school din ba sai da ta shiga asibiti ta yi sa'a babu layi ta samu ganin Dr Najeeb. Sossai ya dinga janta da hira na musamman yana sakata responding har da murmushi sun dau lokaci a session ɗin kan ta fito kuma ya ji daaɗin ganin improvement a al'amarin ta sossai da sossai kenan ta cire wa kanta tarin damuwar da ya nemi binne ta daga nan school ta ce driver ya kaita. "Ko da ta isa makarantar wayanshi ta karɓa ta kira huda ""Twinee""" Ihu ne kawai hudah bata saki ba na jin muryarta """Twinee ke ce? Kullum na roki Momma ta ba su Fareed waya su kai miki sai ta hau ni da faɗa Aina'u kam ma bata daukar wayana tsantsar yadda na addabe ta, shi kuwa Mumtaz kullum sai ya wani ce baya gida ya kike?""" "Murmushi Hibbah ta yi tace ""Ina cikin school kina ta ina?""" """Don Allah? Daddy ya barki?? Alhamdulillah!!"" ""Katin driver muke cinyewa faɗa min kina ina?"" ""Ina department namu""" """Ok gani zuwa""" "Ta katse ta miƙa mishi kan tayi godiya ta fita, kai tsaye hanyar SLT ta ɗauka Dukda ba department ɗinta bane amma saboda Hudah kusan bata shiga school din ta fita bata je department ɗin ba, abin da ya so firgita ta yadda ake ta kallonta har tana tuntunɓe ɗago kan da zata yi ta ga wasu kaman suna yi mata video ko hoto da sauri ta janyo hijabinta ta rufe har rabin" fuskarta gabanta na dukan uku-uku. "Ko kan ta isa SLT department ji tayi bata numfashi da kyau, da sauri ta juya don komawa mota sai ta ji ana yi mata magana bata tsaya ba bare ta saurara don kalaman ya fi yanayi da jaje ko kuma tuni akan miƙinta, Meyasa mutane suke haka? Me yasa burin mutanen yanzu su yi mocking ɗinka akan kaddararka? Shiyasa kashe kai ga yaran turawa ya zama ruwan dare, damuwa da depression ya kashe mutanenmu na arewa bila adadin ba tare da an sani ko an farga ba musamman a native wurare irin kauyuka da basu yarda cewa akwai wata cutar ta" damuwa ba. "Ko da ta koma mota wani irin kuka take yi tana ja wa Sagir Allah ya isa, tana kuka tana cursing ɗin shi da zuri'arshi gabaɗaya don ta san mutane, wannan tambari ba zai taɓa mantuwa a gare su ba har karshen rayuwarta, driver ya yi kokarin yayi mata magana sai dai duk bata wani sauraronshi ta rikice gabaɗaya, a take tsana da kyamar makarantar ya shige ta, Hudah ce ta kira Layin drivern jinta shiru ya ɗaga a ɗan ruɗe yana gayamata halin da suke ciki, da sauri ta bar department ɗin ta nufi wurin da ya ce mata suke zuciyarta na tsitsinkewa, bata zaci haka Hibbah ta fito ba da ta ce ko facemask ne ta saka don itama sai da ta nemi facemask ta saka Dukda daga an mata magana ta amsa ake gane ba Hibbah bace amma wasu kallon birds of the" same feathers suke musu. Ko da ta zo rungume Hibbah tayi tana rarrashi wasu cikin friends da ake hi/Hello duk sun mammatso jikin motar yayin da wasu suke daga nesa. """Malam Bala ja motar nan mu tafi daga nan don Allah, duk ba don Allah suka taru ba sai don gulma""" "Ta faɗa tsiririn hawaye na bin idanunta ya ja suka bar makarantar, sai da suka yi nisa yayi parking a gefen hanya yana ɗan waigowa don har lokacin kuka Hibbah take yi wanda ke fita daga ƙasan ranta." """Hajiya Hudah ko asibitin za mu koma?""" """Eh, kaimu asibitin goshinta kaman garwashi aka ajiye don zafi""" Girgiza kai tayi za tayi magana Hudah tace """Shhhh ki yi shiru don Allah, ba za ki koma gida ki je ɗaki ki kwanta a wannan yanayin ba. Ki yi" "haƙuri twinee ki sassauta wannan zubar hawayen.""" "Bata ce komai ba sai majina da take ja, kanta har kaman zai faɗi haka suka isa asibitin Dr Najeeb suka nema yana ganinta hankalinshi ya tashi" """Me kuma ya faru? Yanzu fa barinta asibitin nan""" "Ya jefawa Hudah tambayar yana nuna mata kan gadon da za ta kwantar da Hibbahn, ba don kayan jikinta ba zai iya rantsuwa ba ita ba ce Hudah ce ba lafiyar don lafiya lau suka rabu tana kuma walwala ba laifi." """Dr. Makaranta ne ta shiga akan zata koma lectures yau, ka san mutane wasu burin su su nuna sun santa ko suna da alaƙa da ita, wasu burin su ganta kawai bayan ibtila'in da ya afka mata yayin da wasu da basu santa ba ake kiransu ganinta tamkar sabuwar halitta su ne suka rudata har ta shiga wannan hali""" "Ranshi bai mishi daaɗi ba don har a fuska bai ɓuya ba, wucewa yayi ya fara kokarin haɗa" allurai anan Hudah kuma ta shiga ƙiran Daddy. Hankalin daddy ma sai da ya tashi jin abin da ya faru nan ya ce gashi zuwa asibitin shi da Daddy Rabi'u. Kusan mintuna arba'in ya ɗauka kan bacci mai nauyi ya ɗauketa under heavy medications. Dole ta shiryawa hakan dole a yanzu kaɗaici da laying low shi ya fi chanchanta da rayuwarta ko kuma ƙaura zuwa wani garin don samun kwanciyar hankali. "Yana fitowa su Daddy suka tare shi, sossai mutumin ya yi mishi girma a idanu don wani nauyinshi ya ji yana ji, ƙasa miƙa hannunshi ga Daddyn da ke miko mishi na shi yayi sai ɗan rankwafawa tare da gaida Daddyn cikin girmamawa, iso yayi musu har cikin office nashi. ""Likita menene matsalar ne da daga ta shiga ruɗu haka sai jikinta ya nuna? Wani Sabon ciwo" "ne kuma ya kamata?""" Dr Najeeb ya ce """Wato Alhj abin da ya fara faruwa da ita abu ne da za mu ce ya yiwa zuciyarta girma, duba da ta fito cikin gidan mutunci, tana da tarbiya daidai gwargwado, tana da tarin mu'amala kwatsam a ce koina ya ɗume da zancen da har yayi sanadiyar wargaza aurenta bayan gangami da shiri da aka gama, dukan da abin yayi mata a zuciya shi yayi sanadiyar da numfashinta baya ratsa huhunta yadda ya kamata, a gudun kamuwarta da wata cutar ta daban ya sa dole take kan medications ga mental Health ɗinta da is not stable. Wannan dalili ne ya sa daga hankalinta ya tashi numfashin ke gagararta da kuma saukar mata da ciwon kai mai tsanani. Idan har za ta kiyaye dokokin asibiti kuma za ta nesanta ga damuwa komai zai zama daidai amma idan hakan" "na faruwa akai akai akwai possibilityn kamuwarta da kowani irin cuta ma""" "Numfashi mai nauyi Daddy ya sauƙe yana tuna matsalar shi daga haka ya fara, kenan zuciyar Hibbah irin tashi ce, ya san irin wahalhalu da ya shiga a baya saboda wautar shi, har yanzu yana tsanar kanshi ba kuma ya fata a ce mummunar ƙaddarar shi ko ya ɗauka a son zuciya ne ke shirin dawowa kan 'yar shi da tafi soyuwa a ranshi. Wasu kalamai ne ke dawo mishi cikin kunne da sauri ya dafe kunnuwan yana duƙawa, Daddy Rabiu ne ya dafa shi Dr. Najeeb ya miƙe ya kawo mishi ruwa Daddy Rabi'u ya karɓa ya bashi ya sha, sai da ya ɗauki lokaci kan ya ɗan natsu ya miƙe tsaye yana yi wa Dr. Najeeb godiya ba tare da ya mayar da hankali kanshi" ba suka fice. """Hudah ki je Malam bala ya mayar da ke gidanki mamanku na hanya""" "Da sauri ta kalleshi sai dai bata iya ta yi magana ba amma Allah ya gani bata so komawa gida ba tare da Hibbah ta tashi ba, ko fa gaisawa basu yi ba. Kaman ta yi kuka haka ta fice." Daga Daddy har Daddy Rabi'u babu mai magana suna zaune ne kowa da abin da yake saƙawa har Momma da Mumtaz suka shigo ko zama basu kai ga yi ba Ƙiran Hajiya kamila ya shigo "wayarshi, har kaman ba zai ɗauka ba sai kuma ya ɗaga da sauri ya miƙe tsaye yana Salati..." *** "Hudah na isa gida ta iske Hajiya zaune kan plastic chair a tsakar gidan tana shan iska, kallonta" take har ta isa ta duƙa tana miƙa mata gaisuwa. """Ina shi Mu'azzam din? Ya ce zai je ɗauko ki""" Ta jefo mata maganan ba tare da ta ko amsa gaisuwar ba. """Toh kila mun yi saɓani dayake ba daga makarantar nake ba, mun je sai Hibbah bata da lafiya na kaita asibiti""" Wani kallo Hajiyar ta watsa mata. """Shine kika kasa kiran mijin naki ki tambaya?""" "Shiru ta yi, har ga Allah bata kuma san me zata ce ba don tana ganin ko me zata faɗa kaman ba yarda hajiyar zata yi ba don tun farko ma bata yarda da maganan ba, kwafa hajiyar tayi tana gyara zama." """Dole ki min banza! Ba ni da ikon tambayar ki ko? Toh shikenan tashi ki je bari wanda ya" "ajiyekin zai zo shi dolenshi ya ba ni amsa ko ya ƙi Allah""" "Hudah ta miƙe ta nufi kofarta, a kwanakin nan ta juri abubuwan da bata taɓa zato ba daga hajiyar, tun tana ɗauka normal ne har take ganin kaman ba haka ya kamata abubuwa suke tafiya mata ba a matsayin sabuwar amarya da tayi auren soyayya, Adu'a take Allah ya bata juriya don ita bata taɓa bambance tsakanin Mommahnta da Hajiyar ba a ranta shiyasa ko Hibbah bata yi niyyar kaiwa kokenta ba akan hajiyar Dukda kanta a ƙulle yake." Tana shiga ɗakinta ta tsaya chakk ganin wardrobe ɗinta buɗe kayakinta wasu a kan gado wasu a ƙasa duk ninkakkun an wargaza """Me wannan??"" Maganar ya fito mata ba tare da shiri ba." "*Littafin nan na kuɗi ne ki biya Naira Ɗari biyar (500) kachal domin kasancewa cikin masu kwasar tarin ilimi, faɗakarwa da zazzafar soyayya mai cike da sadaukarwa da aka zube ciki. Za ki biya ta wannan asusun" 0545475847 Gt bank Fatima Muhammad Gurin Sai ki tura shaidar biya zuwa wannan layi 09039206763 Ko kuma katin MTN na Naira 500 cikin wannan layi na sama sai ki tura da shaidar biya ta same layi. Sai na ji ku* Note: Da dare ne zan dinga posting da rana zan bi in dinga karanta comments naku so please a ba ni haɗin kai mu tafi lafiya kaman yadda muka fara lafiya. Na gode sossai. Gureenjoh SAFARA A TAƁO FATIMA MUHAMMAD GURIN *GUREENJOH* *ADABI WRITERS ASSOCIATION* *PAID BOOK* *008* """Yaya wai ga chan Amal ta zo da kuka gida wiwi wai an kama maigidanta"" ""Mene??""" "Daga Daddy Rabi'u har Momma suka faɗa a tare cike da mamaki da kaɗuwa. ""To wai a dalilin mene?""" """Kamilar bata yi min bayanin komai ba wai Amal ɗin ta kasa natsuwa""" "Mommah ta saki salati ""innalillahi wainna ilaihi rajiun""" Shawara suka yi za su je gidan su ji me kuma ya faru kwata kwata auren wata biyu kenan an fara zuwa gida kuka da tashin hankali? Tafiya suka yi suka bar Momma na kula da Hibbah. "Ko da isar su gida sun samu har lokacin Amal na a haukace fuskar nan suntum saboda kuka, Hajiya kamila ma ta yi mai isar ta yaranta na gidan aure har sun iso, sun tasa Amal ɗin a gaba ta ƙi magana kiran Daddyn ne ya saka Hajiya kamilar ta saka Amal a gaba suka nufi parlorn na Daddy da har ya ƙira Daddy Z sun iso tare." "Amal na ganin daddy ta fara sabon kuka ya ce ta zo ta zauna gefenshi, nan ta iso ta zauna ""Daddy sun zo sun kama shi sun kuma yi seizing takardun gidanmu""" Ta ƙarasa cikin kuka """su waye su?""" """Ya ce wai hukumar custom ne don dama ya ce sun riƙe musu kaya, kuma ya tattara kuɗi ya saka ciki har da bashin banki yanzu kayan na chan wurinsu bankin kuma lokacin biya ya yi ba'a biya ba shine suka karɓi takardun gidan. Don Allah Daddy do something""" Daddy Z ya ce """Would you shut up! Kaman ya yayi wani abu? Me kike tunanin zai yi?""" """Calm down Zubair, ai ba zamu zuba ido komai yayi ta faruwa ba tunda aure ya haɗa. Yanzu a ina suka kaishi?""" """Nima ban sani ba Daddy"" ta sake faɗa tana kuka." Hajiya kamila da ita kam haushin Daddy Rabi'u da Zubair take ji na yadda take ganin kaman su suke hanata rawan gaban hantsi a gidan kuma duk suna goyon bayan Momma a komai a cewar ta don ko suna ganin tana da yara maza ne ta yadda ko Daddy ya mutu za su taya su cin gado ta yi tsulum ta ce """Ni sai nake ga duka waennan tambayoyi ba ita ya kamata a yiwa ba, ka ga ita amarya ce ko fara zagayen gidajen 'yan uwanshi bata yi ba bare sanin abokanshi ko wani a wurin aikinshi, Daddyn yara a ƙira ko waliyyanshi ne a samu wani abokinshi sai a ji duk bayanan da ya" "kamata""" "Daddy Z yayi kwafa ba tare da ya ce komai ba don shi dama ba son yaron yake ba, kuma tunda Hajiya kamilar ta mishi rashin mutunci akan wai yana bakin ciki Amal zata auri mai kuɗi ne yake so ya hana ya cire kanshi a shirgin auren Daddy ne yayi assigning aka yi binciken, yanzu ma halin ko in kulan ya nuna bai tofa ba har suka gama magana daddy ya ce taje ta bar kukan nan" "komai zai daidaita in shaa Allah, nan suka fice suka bar su su uku." """Zubair me kake gani ne? Don wannan dai ɓangarenku ne hukuma""" Murmushi yayi """Yaya ai kuma kuna iya damawa duk ɓangarorin, duk kuma abin da kuka yanke sai a yi"" Ya zame kanshi, Daddy yayi murmushi don ya fahimta." """Shikenan zan ƙira shi mahaifin nashi yanzu sai in ji duk yadda komai ya kasance. Allah ya sa" "muna da abin da zamu iya yi""" "Suka amsa da Ameen, sun tattauna kadan kan suka watse." **** """Hudah!""" Mu'azzam ya shigo sashen yana kiran sunanta. Tana daga kitchen tana haɗa abincin rana ya sameta """Me ya faru ne? Hajiya ke cewa kin gaya mata magana ko mene? Sannan nayi ta kiran layinki" "bakya picking Allah ma ya sa na ƙira hajiyar ta ce min kin dawo tuni""" Numfashi ta sauƙe tace """Eh na dawo, ina school ɗin Hibbah ta shigo to sai kuma ta samu attack na ciwonta muka tafi asibiti a ruɗe duk na sha'afa ban kira ka ba don har Daddy ya sa aka dawo da ni ma bata farka ba.""" "Fuskarshi ba yabo ba fallasa yace ""Hibbah Againn! Toh Allah ya bata lafiya"" Ta amsa da Ameen." """Ka duba abu a wardrobe ɗina ne?""" "Tayi tambayar tana cigaba da soya kayan miyan dake kan wuta. ""A'a me ya faru?""" """Shikenan""" "Ta faɗa ba tare da ta kalleshi ba, har ya juya zai fita ya dawo." """Hudah na sanki da biyayya da kuma sanin ya kamata don Allah bana son kawo karar nan da" "Hajiya take yawan yi akan ki, kinga ita uwa ce kuma shekaru ya ja sai ana yi ana haƙuri da su""" "Karo na farko kenan da ta ji wani irin haushi na taso mata akan lamarin hajiyar, dannewa tayi" tace """In shaa Allah""" "Ya fice, aikin ta cigaba da yi tana tunanin rayuwarta a gidan tare da suruka da kuma ƙanwar miji" har ta gama girkin ta saka a kula ta kai musu nasu ta jera nata a parlor ta nufi ɗakinta don ƙiran Momma ta ji jikin 'yar uwarta. **** "Alhamdulillah ko da Hibbah ta farka bata farka da kukan ko damuwa ba, Momma ta taimaka mata ta wanke baki tare da alwala ta zo tayi sallah kan Momma ta zuba mata abinci har lokacin Mumtaz na nan sai sannu yake mata kuma ta ji daaɗin kulawar tasu, ta ci abincin ba laifi kan Mumtaz ya je ya sanar akan ta farka bai jima da dawowa ba sai ga Dr. Najeeb da wasu nurses" biyu. "Fita suka yi don a duba ta, ya dubeta" """Kin karya min alƙawari""" "Ta ɗan yi murmushin yake ""Alkawarin da ban san na ɗauka ba?""" """Eh ke baki sani ba amma ni na daukarwa kaina cewar ba za ki sake kwana da damuwar komai ba kuma da yardar Allah sai gashi kin karya min shi.""" "Ta ce ""Hmmm""" """Da kamar wuya ko? Yanzu ina ne ke miki ciwo?""" Ta girgiza kai """Babu kawai zuciyata ce bata yi mini daaɗi""" """Za ma tayi in shaa Allah, kin san babu abin da ya fi ƙarfin Allah ko?""" Ta gyaɗa kai yace """Toh oya ga wayana buɗe qur'ani ki karanta shine abincin ruhi kuma kina gamawa tabbas zuciyarki zata yi daaɗi""" "Nurses ɗin sai mamaki suke ganin yadda suke hirarsu su biyu shi kam ma ya manta dasu, shi da bashi da yawan magana sai wasa idan yayi ra'ayi ga addini da ya samu daidai gwargwado" kuma shine kan gaba a komai nashi. "Babu musu ta karɓi wayan, ya kalli nurses ɗin yace" """Patient ɗin mu bata bukatar wata allura ko ruwa a yanzu mu dan bata lokaci""" "Fita suka yi, shi kuma ya ja kujera ya zauna yana kallonta tayi bismillah tana karatun ba da ƙarfi chan ba a hankali take yi sautin na fita kaɗan kaɗan ya ɗan lumshe ido ya buɗe a kanta har tayi ayoyi goma na farkon suratul yunus da ta chanka, sai ta sauƙe numfashi ta ɗago suka haɗa idanu a hankali ta mayar da kanta ta ƙara biyar kan tayi sadakallahu azeem ta miƙa mishi ya ce" """Masha Allah! Ƙanwata ashe Malama ce""" Ta ɗan yi murmushi """Ɗaliba dai""" """A haka ɗin? Ko dai kin san gwanaye basa faɗa"" ""Ai ban isa zama gwana ba sai dai Gwangwani""" Dariya yayi jin abin da tace. """Alhamdulillah na ji daaɗi da baki bari kuncin rai yayi overtaking yanayinki ba, Dukda na san" "akwai shi a chan ƙasan rai""" """kaman yadda ka faɗa abincin ruhin nan da ka bani yayi aiki ƙwarai nima kuma bana son ganin iyayena da 'yan uwana a damuwa ta dalilina. Wannan attack da na samu ma akasi ne don na san kaman yadda ya tuna min da abin da ya faru suma kuma ya tuna musu wanda ko a fuska suka nuna hakan ba zai min daaɗi ba""" Kai ya gyaɗa """Haka ne, Allah ya yaye ya baki lafiya amma please ki koyi shanye maganganun mutane, don dole za su yi kar kuma ki ce za ki dinga rufe kanki a ɗaki kina tunani be the Energetic and strong Hibbah""" "Murmushi tayi Tana godiya ya juya ya fice, Momma da Mumtaz suka dawo." "Anan Mumtaz ya kira Nasir ya bata yayi mata ya jiki, Momma ma Aunty Kubra ta kira don sun dameta da kira ta ba Hibbar itama ta yi mata ya jiki da wani nasihar haka su Aunty Asiya duk" sun yiyyi waya kan Hudah a karshe. """Twiny kiyi haƙuri Daddy ya kora ni baki farka ba""" Ta Yi murmushi """Ai ya yi daidai ina Amarya ina zaman asibiti, na dai ji ba daaɗi bamu ko yi magana ba"" ""Zan roƙi Mu'azzam ya kawo ni mu yini churr muna hirar da muka kwana biyu bamu yi ba"" ""Toh Allah ya sa ya bari da kuwa na ji daaɗi, musamman zan girka miki favorite ɗinki"" Hudah ta kwashe da dariya Momma da Mumtaz na taya ta sai Hibbah ta Shagwaɓe fuska ""A ke ɗin? Wacce ta tsani girki?? Lallai da kuwa an yi ruwa da ƙanƙara""" """Zan kuwa baki mamaki Allah"" ""Ki ba wanda bai sanki ba dai""" Haka suka yi ta hira karshe Momma ta kwace wayarta. "Da yammacin aka sallameta don ta sake fiye ma da yadda suka zata, ya dai tabbatar mata bayan kwana bakwai ta dawo nan suka tarkata suka yi gida." ***** "Abinci ne a gabanshi sai dai ba ci yake ba bayan wasa da spoon ɗin da yake ta yi a ciki, hankalinshi tuni ya yi nisa har bai ji Shigowar Ummanshi madaidaicin parlorn mai ɗauke da kaya masu kyau da tsari daidai ba sai da ta ɗan taɓa kafadanshi tana zama." """Najeeb lafiya kake kuwa? Me ya faru?""" Ya girgiza kai """Babu Umma, gidan naki shiru ina 'yan matanki?""" """Sun tafi makaranta. Ka dai san ba zan amince cewa komai lafiya ba ko? Ka ga nisan da kayi a tunani? Har fa na shigo parlorn nan baka sani ba Najeebu menene?""" Shiru ya yi ta gyara zamanta a hankali ta cigaba da cewa """A iya sanina baka da wacce ta fi ni kaman yadda nima ba ni da wanda ya fi ka Najeeb, idan kana cikin matsala kaman dukkanmu muna ciki ne don kai ne komai namu a gidan nan duk abin da zai same ka kaman mu ne zai sama don haka ka faɗa min matsalar sai mu shawara a" "tsakaninmu mu kuma roki Allah mafita""" "Idanunshi da suke yanayi da nata ya ɗago ya ɗan kalleta yana tankwashe kafa ya ce ""Umma aure ne nake so in yi amma ina tsoron amincewarki""" Ta ɗan zaro ido """Me zai hana ni amincewa Najeeb? Ko kana tunanin zan hanaka ne saboda ɗawainiyarmu da na Ƙannenka dake kanka? Wallahi ko daya zan so ka yi, shawarar dai da zan baka shine ka samo 'yar gidan mutunci kuma masu rufin asiri da zata iya haƙuri da kai a kowani yanayi, na san hidima na yi maka yawa ƙwarai da gaske amma don ƙarin mace ɗaya cikin rayuwarmu ba" "komai ba ne.""" Kanshi ya shafa yana sauƙe ajiyar zuciya. """Umma ai na samu matar""" """Toh fa! Abin ashe na wuri ne ka ce mu fara shiri. Wacece?""" Tayi maganan da wasa fuskarta ɗauke da murmushi """Umma Hibbah ce nake So! Wannan yarinyar da kika duba a asibiti, wacce aka fasa aurenta watanni biyu baya""" Ɗan shiru ta yi kan ta ce """Ka tabbatar kana sonta Najeeb? Ko dai tausayinta kake? Ba zan taɓa baka shawarar ka aureta saboda kana tausayinta ba don idan saboda hakan ne babu inda alaƙar taku zai tafi Dukda na san ana gina so daga tausayi, idan don ibtila'in da ya sameta ne zai wuce don abu sai dai idan bai faru ba yau da gobe sai Allah duk kowa zai manta, zata cigaba da rayuwarta kuma ta nema" "wa kanta farin ciki.""" """Umma wallahi ina sonta har cikin raina, sam tausayi ba shine ya gina min soyayyarta ba na ji ina sonta tun kan in san me ya sameta, sanin me ya sametan kuma bai sa na ji zuciyata ta sauya ba sai ma gaba da take yi, zan iya cewa a 'yar zaman da take yi asibiti na fahimci kyawawan hallayarta, natsuwarta da ma mutuncin gidansu Dukda miliyoyi a yanzu na kallonsu marasa mutuncin amma a idona daban nake kallo saboda ba zan taɓa hukunta ta ko iyayenta" "bisa kuskuren da ya faru a rayuwarta ba""" Numfashi Umman ta sauƙe a hankali tace """Shikenan, in shaa Allahu Idan Abban naku ya shigo sai in sanar mishi amma baka ganin ta fi karfinka Najeeb?""" Dariya ya ɗan yi marar sauti """Dariya ma na baka? Wannan yarinyar fa mahaifinta mai kuɗi ne, ita ɗin 'yar gata ce gaba da baya zaka iya da bukatunta? Ko zata amince ta aureka alhali ta san sun fi mu ta kowani ɓangare?""" """Umma babu abin da suka fi mu, yadda suke ci su sha mu ma nan muna ci kuma mu sha haka bukatu babu wanda bama saukewa daidai gwargwado bare ma na gamu da mahaifinta" "mutumin kirki ne da duniya bata dameshi ba""" "Ta dai yi shiru ba kuma don wai tana ƙin Hibbah ba sai don tunanin tazarar matsayin su, Dukda Alhamdulillah sun kasance cikin masu rufin asiri don ci sha da sutura bai gagare su ba, Abban su Najeeb tsohon ma'aikacin gomnati ne da yayi retire sai pansho da yake karɓa, a lokacin da yake aikin ne ya tsayawa Najeeb ya yi karatu kasancewar shi mai hazaƙa da son yin Allah ya taimaka yana jamb a SS3 ya zama hightest scorer a gabaɗaya Kano inda ya samu scholarship ta dalilin wannan ya tafi china ya karanci fannin likitanci, shima bai zauna ba don yana karatun ne yana duk sana'ar da ya samu su kan taimaki juna idan yana takure bashi dashi Abban ne zai" kurkurda ya tura masa haka shima idan ya samu bai taɓa mantawa da su ba zai turo. "Tunda ya tafi bai waiwayi gida ba saboda scholarship ɗin babu batun zuwa gida idan zaka je sai dai idan kaine zaka yi kudin jirgi ka je ka dawo don haka ya zauna shekara shidda churr sai da ya zama cikakke kuma kwararren likita a fannoni da dama kan ya dawo, ko da ya dawo bai sha wahala sossai wurin samun aiki ba saboda kwazonshi nan ya karɓi ragamar kula da su," kannenshi duk suna makaranta a yanzu haka ga ɗawainiyar gidan. "Miƙewa yayi da tray ɗin abincin ya fita zuwa kitchen ɗinsu dake tsakar gidan ya ajiye kan ya dawo parlorn ya ɗauki wayanshi ya fita zuwa ɗakinshi dake ta mashigar gidan jikin madaidaicin gate ɗin nasu wanda haɗe yake ciki falle ɗaya mai girma da toilet ciki, komai na ɗakin neat and clean saboda tsaftarshi sannan yadda aka tsara ɗakin ma yayi kyau sossai Dukda ba kayan alatu aka zuba masa ba a kan katuwar katifarshi mai tudu sossai da ya sha shimfida ya kai kwance yana kallon saman ɗakin cike da tunanin y ta yadda zai fuskanci Hibbah, yana da tarin abubuwa da yake son ji daga gareta amma yana ga gwara ya bi komai sannu a hankali har ya" cimma nasarar saninta sossai. "Najeeb bai yi ƙasa a gwiwa ba ya cigaba da bi da ita ta dabara yana nuna mata kulawa yana janta da hira da wasa, tun bata wani sakewa har ta zo ta fara sakewa dashi sossai kasancewar bata da wani abokin hira, babu wayanta kuma bata zuwa ko ina sai ya zamana tana tattauna" wasu abubuwan da shi matsayin friend ɗinta. "Hajiya kamila fitina sossai ta tayar wa Daddy saboda damuwan Amal, har gani suke wai bakin ciki ake yi mata da samun miji irin Alqaseem shine aka je aka yi masa asiri don ya rasa dukiyar shi gabaɗaya, shi kuma Daddy yana goyon bayan hakan tunda yana da yadda zai yi ya gagara" "Amal har da ciwo, dole Daddy ya nemo mahaifin Alqaseem ɗin don jin abin da ke faruwa." Ko da suka zauna dattijon ya ce mishi ai Alqaseem ɗin na legos har yanzu amma komai ya kamalla na chuku-chukun sakeshi suna tsammanin ma a sabuwar wata zai dawo. "Daddy yayi adu'a da Fatan kiyaye gaba kan suka rabu da dattijon, Hajiya kamila da fitan mutumin ya sa tayi zuruf ta fito daddy ya kalla" """Hankalinki ya kwanta ai ko? Toh sai ki kyaleni na sha iska""" Fuuuu ta wuce kaman iska ya bita da kallo yana girgiza kai. "A tsakar gidan ta gamu da Hibbah da dawowarta asibiti kenan, sanye da hijab har ƙasa da" yanzu da su take fita ta ƙura mata idanu har Hibbahn ta zo zata wuce tace """Aniyar moɗa dai sai dai ta bi randa ki kaiwa tsohuwarki saƙon cewa duk malaman buzayen da" "ake bi sai an sake shiri. Ta ji da rufa rufan cikin da kuke ta yi ta kyalemin yarinya ta sha iska a gidan mijinta...""" "Hibbah bata yi magana ba ta raɓata don wucewa Mujiba ta fusgo hijabinta har wuyanta na shaƙe wa, tana waigowa ganin Mujiba ce bata yi wata wata ba ta zabga mata mari idanunta na rinewa a take ihuuu mai ƙarfi da Mujiba ta kwala shi ya janyo hankalin jama'ar gidan tuni aka" fara fitowa. "*Littafin nan na kuɗi ne ki biya Naira Ɗari biyar (500) kachal domin kasancewa cikin masu kwasar tarin ilimi, faɗakarwa da zazzafar soyayya mai cike da sadaukarwa da aka zube ciki. Za ki biya ta wannan asusun" 0545475847 Gt bank Fatima Muhammad Gurin Sai ki tura shaidar biya zuwa wannan layi 09039206763 Ko kuma katin MTN na Naira 500 cikin wannan layi na sama sai ki tura da shaidar biya ta same layi. Sai na ji ku* Note: Da dare ne zan dinga posting da rana zan bi in dinga karanta comments naku so please a ba ni haɗin kai mu tafi lafiya kaman yadda muka fara lafiya. Na gode sossai. Gureenjoh SAFARA A TAƁO FATIMA MUHAMMAD GURIN *GUREENJOH* *ADABI WRITERS ASSOCIATION* *PAID BOOK* *009* """Za ki gayamin idan ni sa'arki ce da za ki fusgoni haka! Ko haifata kika yi? Bar ganin kura ta yi" "lafiya kiyi tunani karnuka suna da damar kawo mata raini. Wallahi har yanzu a Hibbata na...""" Hannu da Hajiya Kamila ta kawo mata ta buge tana yin baya dukan ya bi iska. """Nima dukana zaki yi Hibbah? Don na faɗi gaskiya shine za ki sauƙe kan Mujiba? Ƙarya nake" "ba cikin ne jikinki ba? Idan ba shi bane uban me kuke ɓoyu kullum a hijabi?""" "Momma ta lumshe ido, sam bata taɓa kawo da Hibbah ake tashin hankali ba don ko da ta ji magana sama sama bata yi niyyar motsi ba amma jin ihun Mujiba da karfin gaske yasa dole ta" "fito sai ta iske Hibbah tsulum a tsakiyarsu, Amal da ta fito ne tace" """Ai na gayamiki Hajiya idan ba ciki ba me zai sa su yi ta nuku-nuku? Wallahi na san fitan hoton nan kaɗai bai isa ya sa Hibbah natsuwa haka ba sai dai in da biyu ai kin gani gashi tana nuna miki halinta""" "Nusaiba da Baby da suke tsaye daga sashensu suna kallo tare da mahaifiyarsu suka haɗa baki ""Ciki??? Tabbbbb""" Nusaiba da ita ce ta ɗora da """Aiko wallahi in haka ne ba'a gidan nan ba don ba za'a hana mu auruwa ba saboda waenda su sun riga sun saba sai dai Daddy ya zaɓa wallahi don dai da irin Hibbah a zuri'a gwara babu..""" Hajiya Zakiya tace """Ai tunda ya ɗauko uwarsu ya san me ya kwaso yana murna da ta zuba mishi maza ba bai sani ba duk gayyar 'ya'yan Kuka ne...""" """YA ISHEKU DUKA!!!""" Daddy ya daka musu tsawa. """Ku ɓace min da gani tun kan in sassaɓa muku kamanni""" "Yaran duk suka watse, ya dubi Hajiya kamila yace ""Duk ku uku ku zo nan""" "Yana kai nan ya juya ya koma parlornshi, sai mita Hajiya kamila ke yi har suka isa suka" "zazzauna, Momma dai shiru bata ce uffan ba." """Abin naki ya kai a gaban idona kike jefar ɗiyar cikina da ciki out of wedluck? Kamila ko kunyar ubangiji ba zaki ji ba? Wallahi ko da wasa na sake jin wannan kalma a gidana zan ɗauki mummunan mataki a kanki, duka yaranmu basu fi karfin kowace iriyar kaddara ba, kuma idan baki kiyaye bakinki ba sai Allah ya hukuntaki bisa dariyar ƙaddarar Hibbah da kike har kika mayar dashi abin zagi da habaici. Na gayamiki wannan ne karo na karshe da zan ja kunnen ki" "akan aibatamin yara da mata ta mummunar hanya""" """Amma Alhj a fa gaban idonka yarinyar nan ta yi min rashin kunya har ta nemi ta kai min hannu duk baka gani ba sai don na ce tana da ciki, idan ba ɗakin saurayi taje ba wani saurayin ne zai samu hotunanta har ya yaɗa duniya tana sanye da panti da breziya?""" "Runtse ido Mommah tayi don maganan ya daketa da har take sake ganin hotunan da ta gani ranar da aka fasa auren Hibbah ɗin da sauri ta miƙe ta fice daga parlorn hatta kalar pant da bz din dawo mata yake a kai yana sakata ganin jiri, Daddy yayi shiru kawai idanunshi da suka sauya sossai akan Hajiya kamilar, ta ja kwafa ta tashi ta fice ko a haka bukatarta ya biya ta baƙanta ran matar son, don wulakanci zai wani ce kar ta sake aibata mishi mata ta ga ita ɗin ma igiyoyi ukun ne kanta, sai da ma ta fara samu kan ita wacce yake fifitawar yana ganinta uwar" Maza ta samu. Hajiya Zakiya da take kallonshi tayi murmushi kaɗan kan tace """Ka yi haƙuri gaskiya kalaman sun yi tsauri in shaa Allahu ba zaka sake jin su ba, bari na je na ba ita Fatimar ma haƙuri ai duk ba zamu yi wannan fata ba ko don 'ya'ya mata da muke dasu mu ma""" Numfashi ya ɗan sauƙe kan ya gyaɗa kai a sanyaye ya ce """Don Allah ku dinga tausayin yarinyar nan Fatima, ko don saboda haƙuri da take dashi da" "kawaici ga girma da take ba kowaccenku""" Ta ɗan taɓe baki kan ta miƙe """In shaa Allahu. Na barka lafiya""" Tana kai nan ta fice tana kwashewa yarinya da ya kira Momma dashi albarka. "Ita kam Hibbah tana shiga parlor ta ci karo da Aina'u da Mumtaz bata ko tsaya yi musu magana ba ta haura abin ta, dawowar Momma duk ya sake saka jikinsu sanyi ganin yanayinta Aina'u tace" """Ni kam Ya Mumtaz anya Adda Hibbahn nan!""" """Kul! Kul nake gaya miki kallonki kawai nake yi dama na fahimci gani gani da kike yi mata, bari kiji su Hajiya kamila ko da Hibbah ko babu ita za su ja Momma a ƙasa, ki daina ganin kaman saboda Adda Hibbah ne tun kafin ma a haife ta a haka suke kawai Hibbah ba zata iya shiru bane mu kuma mun zabi mu yi shirun a lokuta da dama amma sau dayawa Adda Hibbah na burgeni ta yadda take kare mahaifiyarta with all her might. Sannan kaddara ce ta faɗa mata har ke baki fi ƙarfi ba kar ki ga don kin yi tsawo kin kamota ko kin fara kula samari shi zai sa ki raina ta don abin da ya faru da ita, tana bukatarmu duka a gangarta don haka don Allah Aina'u ki" "natsu ki fahimci yadda ya kamata ki tafiyar da alakarku da yayarki da ta fi kowa shan wahalarki""" "Yana kai nan ya tashi ya fice ya barta da tunani, hakika bata kyauta ba a duk abubuwan da suke faruwa ta bari shaidan ya saka mata jin haushin 'yar uwarta tana tunanin kawai zata kashe musu uwa ne alhali ita ma ta san zafin uwar tunda tata ce itama, sannan da gaskiyar Mumtaz idan su ba zasu iya karbarwa uwarsu faɗa ba ita ta zaɓi hakan don babu wanda zai ga ana taka" uwarshi ya kyale musamman idan irin Momma ce da bata ƙaunar hayaniya. "Miƙewa tayi ta nufi sama wurin Hibbahn, sai ta samu ta watsa ruwa kenan ta fito ganin" Shigowar Aina'un bai sa ta tsayar da abin da take yi ba har ta iso gangarta ta zauna """Addah Hibbah don Allah ki yi haƙuri da abubuwan da suka ta faruwa, na san ban kyauta ba""" Murmushi ta yi """Ba komai Aina'u, ke kalar naki nuna jin haushin kenan ga shirmena na fahimceki""" Numfashi ta sauƙe ta cigaba da zama gangar yayartata dama ɗaki daya suke kwana daga lokacin kuma suka cigaba da shirin su kaman baya Dukda dama kusancinsu ba kaman ita da Hudah ba da suke komai tare. "Fara raka Hibbah asibiti da Aina'u ta yi shine sanadiyar fara wayar Dr. Najeeb da Hibbah sossai suka samu kusanci sanadiyar wayan don idan ya kira Aina'u za ta bata su sha hirarsu, maganar makaranta kam tace ba yanzu ba so Daddy ya saka an yi mata deffering semester ɗin kila" bayan watanni uku ko huɗu ta ji zata iya komawa. "A yanzu watanni biyar kenan churr da watse zancen aurenta, har yau mijin Amal dai bai dawo ba tana gida tun ma Daddy na fahimtar zantukar mahaifin nashi har ya daina fahimta a gida kuma sun matsa mishi lamba akan yayi wani abu ai asiri ne aka yi don a rabata da shi da kuma" gidan aurenta. "Ta ɓangaren Hudah zamanta dai ba zata ce ga wani tarin farin ciki da ta tsinta ba saboda matsawar hajiyar Mu'azzam da Falmata, a hankali ta fahimci falmata ce ke zuwa ɗakinta ta ɗaukarta mata kaya ta saka, ranar da ta fara fahimta bata ce komai ba da zata tafi makaranta ta cewa Mu'azzam idan zai fita ya tabbatar ya rufe mata sashe kuma ya tafi da key yace" """Akan me? Bayan ga su Hajiya a gida? Bamu yarda da su ba kenan ma idan za mu kama rufe" "sashe kan mu fita""" """Ba maganan yarda bane, kowa na da nashi privacy ɗin ɗakin baccina ko naka ba abin da zan iya sakaka dashi bane bare bana son abin da zai janyo min magana har a ga laifina don haka don Allah kawai ka rufe ɗin""" Bai ja ba ya rufe suka fita Haba ko da suka dawo hajiyar shi duka ne kawai bata kai musu ba. "Irin maganganu da tayi ta yada wa ya sa dole ya ba Hudah haƙuri akan za su bar mata key ɗin ko da sun rufe, sam bai fahimci abin da take so ya fahimta ba har saida ta sake ganin falmata da kayanta a ranar Hibbah ta je gidan da Aina'u don a yanzu ta kan fita sa'i da lokaci kuma Daddy ya bata wayoyinta da car key ɗinta don duk gidan ita kaɗai ce take tuka mota saboda masifar son injuna da Allah ya yi ta dashi tun tana karama ita ko wasan baby doll bata yi sai na" motoci da parts ɗinsu. Irin kallon da Hudahn tayi ta bin Falmata da shi ne ranta na nuna a fili ya ɓaci ya sa Hibbah ta yi magana """Twinee! Lafiya ko? Tana miki wani abu ne?""" Numfashi ta sauƙe """Ban san ta ina zan ɓullowa wannan al'amari ba twinee, yarinyar nan idan ta tashi kawai sai dai ta shiga ɗakina ta daukar min kaya ba tambaya ba komai sai dai in gani jikinta""" """Kan bala'i! Kuma ta dawo da shi ki dauka ki sa??""" Girgiza kai ta yi """Ko ta dawo dashi dauka nake in mayar mata har gaban mahaifiyarta amma abin na yawa, na rasa ta ina zan fara daukar mataki in yi magana Hajiyarshi tace ina musu gani gani don mahaifina ya fi su arziki alhali wallahi ban taɓa kawo ko da hirar abin da ya shafi iyayena bane a gabansu""" Ta ƙarasa tsiririn hawaye na gangaro mata """Ni ban san me na tsare musu ba, aikin duk da nake musu na abinci safe, rana dare duk gajiya ko jiggatar school bai dame ni ba amma kin ga kananun maganganu da yawan kaiwa Mu'azzam" "ƙarata da har yake ganin ina yiwa mahaifiyarshi rashin kunya abin na damuna""" """Ina zuwa!""" Ta faɗa tana ƙoƙarin Miƙewa da hanzari Hudah ta mayar da ita zaune. """Ina za ki je? Ki rufa min asiri Hibbah don Allah""" Da kyar Hudah ta hana Hibbah fita don ta san wallahi tsaf zata je ne ta samu falmata ta tsefe ta don yanzu hibban da ce ba wacce kaddara ya so ruguzawa ba. "Aunty Kubra Hibbah ta ƙira a labari take ce mata ai aiki ya yi wa Hudah yawa ga girki ga kula da gida ga makaranta tana jiggata don Allah ta sa Momma ta dinga tura mata mai tayata ayyukan ko da yini ne take yi, ta kuwa yarda da shawarar Hibbahn suka sake hira kadan suka yi sallama suka fito, ko hajiyar bata je ta gaisar ba don haushinsu take ji suka bar gidan wanda hakan sai da ya zama abin magana a wurinta ai Hibbah marar kunya ce, dama fitsarar da ake cewa ta yi ashe kaɗan ne tunda gashi ta zo ta musu a gida, sossai Mu'azzam din ya chanzawa Hudah" amma haka ta ba su haƙuri. "Bayan kwana biyu Momma ta yi wa Daddy bayanin batun mai taya Huda aiki ya kuwa amince aka tura ta, ranar da ta je hajiyar ta sa Mu'azzam ya sallame ta akan basa buƙata wato sun raina shi ne ma da arzikinsa da har za su ɗauki mai aiki su ce babanta ne zai dinga biya, idan yana bukata zai ɗauka da kuɗin shi wannan abu ya matuƙar cika Hibbah, aiko ranar da ta tabbatar Hudah na school ta san ba zata samu Mu'azzam a gida ba ta shirya tsaff ta nufi Gidan" Hudar bayan ta cewa Momma asibiti zata. "*Littafin nan na kuɗi ne ki biya Naira Ɗari biyar (500) kachal domin kasancewa cikin masu kwasar tarin ilimi, faɗakarwa da zazzafar soyayya mai cike da sadaukarwa da aka zube ciki. Za ki biya ta wannan asusun" 0545475847 Gt bank Fatima Muhammad Gurin Sai ki tura shaidar biya zuwa wannan layi 09039206763 Ko kuma katin MTN na Naira 500 cikin wannan layi na sama sai ki tura da shaidar biya ta same layi. Sai na ji ku* Note: Da dare ne zan dinga posting da rana zan bi in dinga karanta comments naku so please a ba ni haɗin kai mu tafi lafiya kaman yadda muka fara lafiya. Na gode sossai. Gureenjoh SAFARA A TAƁO FATIMA MUHAMMAD GURIN *GUREENJOH* *ADABI WRITERS ASSOCIATION* *PAID BOOK* *010* "Ta isa gidan kai tsaye sashensu hajiyar ta yi, ta kuwa sameta tana zaune tana hutawa. ""Barka da hutawa Hajiya""" Ta faɗa tana zama. """Yauwa, ya aka yi kika tashi da wuri yau? Ko tun dama chan kina tashin yawonki kawai kike tafiya?""" Ido ta ɗan tsayar a kanta """Ai Hajiya ban isa yin wannan hali ba don gidan da na fito ya fi gaban nan""" "Da ɗan sauri ta kalleta don bata zaci samun amsa ba kaman yadda ta saba da Hudah, kuma sam bata fahimci cewa ba Hudar ba ce." """A ina kenan aka saba da yawon?""" """Uhmm ai ba za'a ji mutuwar sarki a bakina ba, dama makulli na zo amsa wanda Mu'azzam ya baki""" "Ido ta zaro cike da mamaki kala biyu, a gabanta take kiran sunan Mu'azzam gatsal? Sannan ita zata faɗawa magana a fakaice?" """Ko ba'a ji a bakinki ba ai an sani ne don an ce kura ma ta san gidan mai babban sanda, don" "nan kam baki ga tambarin hakan ba. Sannan batun makulli ina ga ai shi Mu'azzam din kika ce ya ba ni saboda haka ki jira ya zo sai ya karɓar miki.""" """Meyasa? Na ga gidana ne kuma sashena ne, kayan dake ciki kuma nawa ne ko kina tsoron ba" "ni in ƙi dawowar ne a rasa na zuwa saane?""" "Da sauri hajiyar ta miƙe tsaye, itama Hibbah ta miƙe tana kallonta a ido ""Ni kike ƙira ɓarauniya? Da ni kike sa'insa?""" Ta ɗan yi farr """Ni??? ai ban isa ba, ina son albarkarki ba zan taɓa kiranki ɓarauniya ko yin sa'insa da ke ba na ga dai hira ce tsakanin uwa da ɗiya muke y. """ """Allah ya sawaake in haifi irinki, dama tun farko ba son wannan aure na Mu'azzam nake ba gashi nan ba'a je ko ina ba kina nema ki min rashin kunya ki kalli cikin idona don tsageranci ki zage ni! Toh wallahi zai dawo ya sameni aure zan masa""" "Taɓe baki Hibbah ta yi tana jin haushin Mu'azzam din na kamata fiye da Hajiyar don duk laifin shi ne, shi ya kamata ya taka ma mahaifiyarshi da ƙanwarshi birki idan dai tabbas yana kaunar matar shi, wani irin auren soyayya ne wannan? Ana ganin kaman Hudah ta yi aure tana hutawa" ai da zama da irin hajiyar Mu'azzam wallahi gwara mata ta tabbata bata da aure. """Ina bukatar key a yanzu dai sashena ne kafin ki kawo wacce zaki kawon""" Har lokacin mamaki da kaɗuwa bai bar hajiyar ba ta zaci Hudah shiru shiru ce kuma natsatsiya ta yadda bata ko ɗaga ido ta kalleta yau ita ce take kallonta cikin ido? """Hajiya!""" "Ta sake kiranta tana kallonta sai kawai hajiyar ta ɗauki keyn ta jefa mata, ta tsuguna ta ɗauka ta" ɗago ta kalleta a ranta tana cewa za ki gani. "Ta fice daga sashen ta nufi na Hudah ta buɗe ta shiga, kai tsaye kitchen ta je ta shiga girki wata iriyar shinkafa ta dafa kofi uku ita ba danya ba ita ba nunanna ba ta zabga yaji don atturugu goma sha wani abu ta zuba ta yadda sai ka ɗanɗana za ka gane, ta juye a warmer ta ajiye." Cikin natsuwa ta girka wani farin macroni da sauce ta zuba kuloli daban ta kai parlor ta dibo kaɗan ta zo ta zauna tana ci kenan sai ga Falmata ta shigo ita da wata yarinya da daga gani rashin kunya ne fal cikinta. Basu yi sallama ba don haka bata ko ɗago ta kallesu ba. """Hudah! Hajiyar kika je kika yi ta yi wa rashin kunya? Ashe baki da mutunci? Nan ɗin fa gidan yayana ne, guminshi ne ba na uba...""" "Ɗago ido da tayi ta kalleta a zafafe shi ya katse mata maganar, ran Hibbah ya zo wuya Dukda ta so ne ta yi maganin abin da fatar baki amma tana ganin sai ta karya yarinyar nan dake tsaye" hankalinta zai kwanta. """Dama a cushe muka karɓeki ba don muna so ba, ga abin kunya da aka zabga lokacin biki da har yanzu kunyar ma a ce mun haɗa zuri'a da gidanku nake... Kinga 'yar dangi kuma ɗiyar mutunci ita ce zata shigo ta zama matar ƙwarai don na tabbatar ba zata taɓa yi wa uwarmu fitsara irin naki ba...""" Maganar farkon a gunguni ta yi na biyun ne tayi shi a fili kuma da kyau amma duk Hibbah ta ji. """Fita a parlorn nan"" Ta faɗa cikin gargaɗi." """Sai ki gayamin idan da shi kika zo a ƙunshin gararki"" Remote ta ɗauka ta chanza channel ta kalli Raliya ""Shiga ki duba gidanki ne ke a very soon..""" Abincin Hibbah ta ajiye daga Raliyar har Falmata sai gwaruwar kansu suka ji wuri guda ƙuuuummm. "Kan su gama fahimtar bomb ne ya sauƙa ko menene ta rufe su da duka, sun kasa kare kansu" ta nemi wayar wuta ta shigesu ihu kawai suke na neman agaji da taimako don basu taɓa tunanin za ta iya dukansu ba har su biyu. """Na rantse da girman zatin Allah ko kofar sashen nan kika kara takowa bare har cikin parlorn nan ko zuwa cikin ɗaki don min bincike ko ɗaukar min kaya sai na yi miki abin da ya fi wannan ai ba hauka bane. Baki da hankali? Ke ba mace ba ce? Baki san boundaries ɗinki ba baki san zuru ba?? To ki dawo ki cigaba da rashin kunyar ki ga idan na cigaba da kallonki...""" Hauka sossai ta nuna musu ai a tsiyace suka tsira da kyar jiki duk ciwuka da tabbuna. "Gyare parlorn ta yi tana haki ta nufi kitchen ta ɗauki kular shinkafar ta bi bayansu, kuka ta samu suna risga ganinta ya sa har rige-rigen shige wa ɗaki suke don sun tsorata, hajiyar ta miƙe" tsaye """Hudah! Hudah falmata kika kama da duka kaman kin haife ta? Uban me suka miki haka? Ko" "ma me suka miki uban wa ya baki damar taɓa min yarinya?""" """Idan da sun zauna iya matsayarsu da yanzu kila suna nan jiki bai ci na jaki ba, amma dayake marasa kunya ne sun gane kurensu." "Hajiya bari na fito miki a mutum, wallahi ba duka ba sai in kakkarya falmata in watsar kuma babu abinda aka isa a yi min muddin ta sake taka kafarta sashena da rigima ko rashin kunya. Wallahi wannan kaɗan ne muddin ta sake taɓa abin da yake nawa ba tare da sanina ba, you guys should be on your length ku barni na sha iska a gidana habaa!""" Hawaye ma take ji tsabar bakin cikin da take ji wa Hudah. Hajiyar ma ta tsorata don idanunta sun kasa ɓoye wa """Toh fa dama mai aljannu Mu'azzam din ya ɗauko mini ni Tani..."" ""Sai dai Mayu don aljannu ma kila sun yi kaɗan""" "Tana kai nan ta fice ta bar hajiyar baki sake, ai da gudu taje ta rarumo wayanta ta shiga kiran Mu'azzam yana ɗauka ta hau ihun ya kawo musu ceto Hudah zata kashe su a gidan don dab" "take da ƙone su su mutu, hankalinshi ya tashi a fujajan ya baro wurin aikin nashi yayi gidan." "A hanya ta gamu da Hudah zata je karɓo key, ido ta zaro ganinta." """Hibbah! Me kike yi a gidan nan? Meyasa ban ga motarki ba? Daga fa sashen Hajiya na ganki...""" "Janta Hibbah tayi suka yi parlornta suka zauna ""Hibbah me ya faru? Baki yi wani abin ba ko?""" """Falmata da wacce uwar mijinki ke son aura mishi na daka! Na yi musu jina-jina"" ""Innalillahi wainna ilaihi rajiun na shiga uku! Garin yaya? Aurena kike so ki kashe?""" Ta miƙe tsaye da sauri tana maganan tuni hawaye sun wanke mata fuska """kin san Allah har ke sai in tsinka miki mari a yadda nake ji na ɗin nan, aka gayamiki shiru shiru ko haƙuri su ne zai sa su soki ko su ƙaunaceki? Ko kina tunanin su za su ceceki daga makirce makircensu? Da ma tana sonki ne gwara gwara, amma matar nan kiri-kiri take bad mouthing gidanku, family ɗinki """ Hannunta ta kama """Hudah ba ina kushe duka iyayen miji bane don akwai nagari ƙwarai, ba kuma zan zagi kannen" miji ko yayyunshi ba amma irin naki matsiyata ne da sai da wuta ake dawowa daidai Mijinki tun farko yana da laifi da bai tsaya miki a matsayin wacce yake so ya kankaro miki daraja daga wurin mahaifiyarshi da ƙanwarshi da yake da iko da ita ba tunda bai yi hakan ba ke ya kamata ki tashi tsaye and show them their limits. Kar ki sake wani girki mai daaɗi ki kai musu ki dinga "dafa hauka da shirme idan sun yi complain ya sameki ki ce baki saba girkin yawa ba shiyasa tun farkon auren kullum suke kai mishi kara girki ba daaɗi, idan sun gaji za su dawo yi da kansu" "tunda falmatar hannunta ba haila yake ba""" "Dukda Hudah na fahimta sai dai ita tana tsoro, bata ƙaunar tashin hankali sam kar a ce ta zama" fitsararriya.. """Kina ji! Duk yadda aka yi na san yana hanya ki tabbar kin fetsere idanunki kin fitar mishi da abin da ke cikinki akan cin kashin ƙanwarshi, shiru na cutarki a lokuta da dama kuma dole ki magantu, duka kuma ki ce sun zo dukanki ne har cikin parlor kika kare kanki duk abin da ya ga zai iya ya yi Zan tafi just act like ni ce ke kema kuma kin san duk abin da zan iya farin sani""" Tana kai nan ta ɗauki katon hijabinta ta ɗora kan wando da shirt na jikinta ta ja Jakarta ta fice don tunda ta zo daga kitchen sai parlorn ta zauna ko hanyar dakunan bata gani ba. "Ta bar Hudah da kaɗuwa, a firgice take zaune kaman a ce kyat ta ruga Miƙewa tayi ta nufi ɗaki ta cire kayan jikinta ta sauya da riga da wando don ba zata so ma Mu'azzam ya fahimci Hibba ce ta aikata komai ba don wlh sai ya kai wa Daddy ƙara an mata rashin mutunci a gida wanda" ba zata so ba. "Tana gama shiryawa ta zauna bakin gado ta ji ihun Mu'azzam yana kwala kiran sunanta ""Hudah! Hudah!!!! Hudahhhh""" "A bakin kofa suka kusa karo ya ɗaga hannu da niyyar kai mata mari nan ta tsaya chakk tana kallonshi, sai hannun ya tsaya a iska shi bai sauke ba shi kuma bai maretan ba, mamakin" hakan bai ɓuya a fuskarta ba """Mari na zaka yi? Ni zaka mara Mu'azzam?""" """Hudah mahaifiyata har ta yi lalacewar da za ki ke sa'in-sa da ita kina gayamata duk abin da ya fito bakinki? Hakan bai isheki ba ki kama Falmata ki daka haifarta kika yi? Duk wannan rashin kunyar da fitsaran ina kika kwaso su? Dama Hajiya ta jima tana ce min da kyar suke iya cin" "abincinki ban taɓa yarda ba sai yau kashe su kike yunkurin yi???""" Idanu ta zuba mishi karo na farko da ranta ya zo mata wuya a abubuwan da yake yi akan Hajiya "da falmata, ai idan da gaske yana ƙaunarta kuma yana so su yi zaman lafiya ba wannan hanyar" ya kamata ya bi don sulhunta su ba. """Tunda ka gama abin da ya kawo ka za ka iya tafiya""" Ta faɗa tana juyawa ya fusgo hannunta tayi baya baya """Me kike nufi? Ga banza na magana? Wai me ke damunki ne Huda?""" """Komai ma!!! Komai ma na damuna Mu'azzam na gaji! Na gaji da yadda kake zuwa ka hauni da faɗa a duk lokacin da ka jiyo zancenka ba tare da ka ji ta baki na ba, bari ka ji in faɗa maka abu guda ɗaya being respectful doesnt mean tolerating disrespect, kai na kawowa zancen ana shiga min har uwar daka ana daukar min kaya a wardrobe ka sani na kuma sani babu mai hakan sai kanwarka me ka yi a kai?? Kana ganin yadda nake wahala da aikace aikace da school ka san hatta kular da nake kaiwa su Hajiya abinci a haka suke dawo min dashi ko in bi in dauka ba tare da an wanke ba. Na kawo mai aiki sun kora Duk ban damu ba, duk abin da Hajiya ta faɗa maka ba ka second thought za ka hau kai ka zauna kayi ta faɗa da kananun maganganu duk ban damu ba abin ya kai har kanwarka ta zo nan ta ce zata dakeni in zuba ido in kallesu? Ba zan iya" "ba...""" "Yanzu kam kuka sossai take yi sai jikinshi ya yi sanyi, zai taɓa ta ta ture hannun ta juya ta ɗauki" hijabinta da jakanta ya tare hanya """Ina za ki je?""" """Gidanmu za ni ai da aka aura maka ni ba'a ce harda Hajiya da falmata aka aura maka ba, gwara mahaifina ya san na yi wallahi na gaji...ban damu ba ka auro huɗu ka ajiye su cigaba daga inda na tsaya""" Ta cigaba da maganan cikin kuka sai hankalinshi ya sake tashi. """Me haka Huda? Don Allah ki tsaya mu fuskanci wannan matsalar wallahi ban san abubuwan" "duk sun kai haka ba, ban san suna miki ciwo haka ba! Don Allah ki yi haƙuri...""" Ture shi take ya bata hanya ta fice ya rungumeta """Ki yi haƙuri, ki ƙara haƙuri don Allah idan baki tayani da haƙuri da mahaifiyata ba wa zai taya" "ni?""" """Wacce zata aura maka, matar so, 'yar gidan mutunci kuma mai hankali""" "Tayi maganan tana sake ture shi ta raba kanta da jikinshi tana kuka har lokacin wiwi, duk bai san tana iya birkicewa haka ba dama an sha faɗa mai haƙuri bai iya fushi ba lallai ya fusatata. Da sauri ya fita ya rufeta ta waje" Ta janyo Jakarta ta fiddo waya ta shiga ƙiran Hibbah tana picking tace """Ke twinee kin koyamin daru...""" Labarin abin da ya faru ta bata """Yauwa! Haba! Ko ke fa? Sai yanzu na tabbatar mun kwanta tare a mahaifa na tsanmiki rigimata kaɗan""" "Dariya suka yi a tare ""Yanzu me abin yi?""" """Ki cigaba da hawa kar ki sauka sam don na tabbatar hajiyar ba zata barshi da takuri akan ki ba, idan kika ga abin ba na kare bane ki birkice sai ya raba muku gida kawai ko ki koma gidanku, kin san maza zuma ne sau tari wuta ne maganinsu""" Sun sake magana sossai kan suka yanke ta kwanta abunta dama ba wani yunwa take ji ba tuni bacci yayi awon gaba da ita. Shi kam ya rasa yadda zai yi a parlorn karshe yayan mahaifiyar tashi ya ƙira ya bashi labarin duk abin da ke faruwa nan ya ce da dare zai zo sai ya ajiye su duka ya ji me ke faruwa. Ko da dare yayi a parlorn Hajiya ya tara su Hudah kanta a ƙasa bayan ta gama faɗa mishi duk abin da ke faruwa da irin cin kashin da falmata ke mata ya dubi Hajiya. """A gaskiya baku kyauta ba Tani, sam wannan abu da kuka yi ba hankali ko lissafi a ciki wannan yarinyar 'ya take a wurinki ya kamata abin da za ki yiwa falmata shi zaki mata, na tabbatar ba za ki so a yi wa taki 'yar haka ba to Meyasa za ki takurawa yar wani?""" Ya dubu Hudah """Kin yi min daidai da kika lallasa 'yan banza gobe ma su ƙara""" """ke kuma falmata wallahi ko da wasa na sake jin kin mata abin da ya shafi rashin kunya ko zuwa sashenta kin daukar mata abu ba da izini ko saninta ba wallahi Ummaru zan taho da shi ya miki dan banzan duka mu koma, marar kunya kawai""" """kaima da laifinka anan! Meyasa ba zaka tsawatar mata ba? Su fa duka mata ne karkashinka suke yaushe suke da tunanin da y dace? Kanwarka ace tana gida amma kwanon abincin da zata ci sai dai ta ci ta ba matarka ta wanke? Ina girmamawa ta matar wa da kanwa anan?""" "Ta inda yake shiga ba ta nan yake fita ba, karshe ya dubi hajiya" """idan bakya son ta kawo 'yar aiki sai ku yi girkin ku ta yi nata shine abin da na gama finalizing ina Fatan duk kun ji ni? Idan kuma kuka cigaba da wannan tashin hankalin dole ku tarkata ya kama muku haya ku koma in yaso ita ta cigaba da zama anan""" Mu'azzam ya tafi raka shi yayinda Hudah ta miƙe don bin bayansu tana kawar da kai a kallon banzan da Hajiyar ke jefanta ita dai ko a haka ta ji daaɗi kuma Hibbah ta wanke mata zuciya don kallon irin tsoron ta da ya shiga falmata kaɗai nishadi yake bata. **** Tana kwance tana chatting saboda yanzu rayuwarta ya ɗau seti hankalinta kwance Dukda dai ta chanza handles na duka flatforms ɗinta kuma ta goge komai da komai nata na hoto a media sai dai kalle kalle don ko hira ba yi take ba ta ji wayanta ya ɗau ƙara ko bata ga sunan ba ta san Dr Najeeb ne don sun yi zai kira ɗin by that time. """Amincin Allah ya tabbata a gareki"" Ya faɗa cikin kulawa da natsuwa ""A tare da kai Dr. Barka da dare""" "Ta amsa da ɗan murmushi don sossai a yanzu take jin daaɗi da natsuwar waya da shi kaman ya asirceta ne da bata rabo da murmushi a duk sadda wani abu nashi yayi popping saƙo ne ko kira ne ko ma tuni ne akan abin da ya shafi addini da ba ya rabo da shi, abin da yake burgeta da shi yadda bai taɓa tambayarta komai dangane da rayuwarta na baya da ya danganci inda" matsalarta ya faro ba he's so matured fiye da zaton ta. """Barka dai Hibbatullahi ya gdn?""" """Gida lafiya ƙalau ina Umma?""" """Kullum dai sai kin min tambayar Umman nan gata to ku gaisa!"" Tana shirin cewa ya bari ba yanzu ba kawai ta ji sallamar Umman..." "*Littafin nan na kuɗi ne ki biya Naira Ɗari biyar (500) kachal domin kasancewa cikin masu kwasar tarin ilimi, faɗakarwa da zazzafar soyayya mai cike da sadaukarwa da aka zube ciki. Za ki biya ta wannan asusun" 0545475847 Gt bank Fatima Muhammad Gurin Sai ki tura shaidar biya zuwa wannan layi 09039206763 Ko kuma katin MTN na Naira 500 cikin wannan layi na sama sai ki tura da shaidar biya ta same layi. Sai na ji ku* Note: Da dare ne zan dinga posting da rana zan bi in dinga karanta comments naku so please a ba ni haɗin kai mu tafi lafiya kaman yadda muka fara lafiya. Na gode sossai. Gureenjoh SAFARA A TAƁO FATIMA MUHAMMAD GURIN *GUREENJOH* *ADABI WRITERS ASSOCIATION* *PAID BOOK* *011* "Ko kan ta ce wani abu ya miƙa wa ummar waya cike da girmamawa ta gaisheta don tana tuna karamcin matar, ta yadda take amsata kaman ta santa sossai ya ƙara mata ƙauna da ganin" girman matar har ranta. Sun ɗan jima suna magana kan ta ce ta gaishe mata da mamanta daga nan suka yi sallama ta miƙawa Dr. Najeeb wayan. """Umma na da kirki da tausayi..""" Ya ɗan yi murmushi yana barin parlorn """Hakane, umma ta kan ce duk wanda so ya kama ko ya saka shi aikata ba daidai ba sai an yi mishi uzuri""" """ba kowa ke da wannan fahimtar ba, wasu ma basu yarda da cewa akwai soyayyar ba, barin ma iyaye waenda suka girma.""" "Hibbah ta gyara zamanta tana ji shi yake tambayarta ""Me kika dauki so?""" Murmushi ta yi idanunta na ɗan juyawa ta ce """Ka san kowa da yadda ya ɗauki So amma ni na dauke shi rayuwa, na kan yi shi da dukkan zuciyata saboda Allah ma ya ce idan za mu yi so mu yi saboda shi!""" "Ta lumshe idanunta da suka cika da kwallah tana tuna irin tarin soyayyar da ta yi wa Sagir wadda har ya ruɗe ta ta aikata kuskure mai girma a rayuwarta, tana tuna irin son da ta yiwa Mahmud bayan ta koyawa zuciyarta tsanar Sagir ta chusa shi da tunanin shi zai mata jigo ko ya" zama wani katanga a rayuwarta sai shima ya fita kaman iska cikin rayuwarta. """Laifi ne mutum ya yi soyayya saboda Allah? Ko laifi ne mutum ya baiwa soyayya muhimmanci fiye da rayuwa?""" Ta tambayi Dr Najeeb hawaye na silalo mata """Kaman yadda kika ce Hibbah kowa da yadda Allah ya yi shi, wani kan yi so sama-sama ta yadda ko rabuwa ta zo cutarwar ba za ta yi yawa ba, some people love slowly ta yadda zai ɗauki lokaci kan su saki jiki su kuma yarda da son karan kanshi, wasu kuma kaman ke love with their whole chest once their heart connects." This isn't weakness. This isn't foolishness. "This is simply how Allah created your heart. Ki ɗauki duk waenda kika rasa a baya cewa ba su ne Allah ya tsara miki rayuwa da su ba saboda babu mai auran matar wani, ki shiryawa abin da" "zai faru kuma gaba""" "Numfashi ta sauƙe ta ji daaɗin kalamanshi sai dai ko da ta tuna Hudah da irin soyayyar da suka yi da Mu'azzam kan aure har zuwa auren ta tuna yanayin da take ciki na takura da damuwar uwar miji sai ta sake jin kalmar soyayyar na zama mata kamar ƙarya ko wani almara da ba ya ɗore wa, ta sake tuna Amal da irin nata soyayyar da yadda auren ke shattering a kan idanunsu duk sun susuce sun rasa Makama, ta tuna matan Daddy Z ta yadda basa shiri a tsakaninsu rigimar yau daban na gobe daban amma shi mijin idan ya tashi kowacce gasa ta yake, ta tuna Momma Dukda tana auren mijin da yake ƙaunarta amma kishiyoyi basu taɓa bari ta ɗauki sati a" gidan ba tare da ta yi kuka da dana sanin auren ba... """Anya akwai kwanciyar hankali a cikin soyayya zuwa aure kuwa?""" Bata san ta jefa mishi tambayar ba sai da ta ji yana murmushi """A cikin soyayya akwai tarin mafarkai da haƙuri ke taka rawa wurin wanzar da su cikin rayuwar aure Dukda a yanzu auren ya zama abin da ya zama sai dai ba hakan zai sa ka yankewa kanka rahama daga ubangiji ba. In faɗa miki wani abu?""" "Tana gyara kwanciyar ta ta gyaɗa kai sai kuma ta amsa ""Ina sauraronka""" """This might sounds simple for you but it means alot to me, i've been keeping this in my heart a" "while now ban shirya faɗa ba, amma zuciyata ta gaji da ɓoye gaskiya. Hibbah...""" "Tana iya jin yadda zuciyarta ke pounding da tsakanin ƙarfi da yadda kalamanshi ke taɓa wani ɓangare da bata so ko kusa ko alama wani abu ya sake isa gareshi ba, a hankali ta amsa idanunta na lumshe cike da kwallar da bata san na menene ba tana sake ƙamƙame pillown da ta janyo ta rungume" """I have feelings for you. Kuma ba na wasa ba i just want to be honest, Ina sonki... Not forcefully," "but sincerely daga cikin zuciyata""" "Hawaye kawai taji suna cigaba da gangaro mata na rashin Makama, shin amincewa za ta yi? Ƙi" za ta yi? Me zata yi? Duk bata sani ba jin sautin kukanta ya sa ya ce a hankali """Ban faɗa don ki ɗaga hankalinki ko ki yi ta kuka ba, just take your time Ok? Zan fahimceki kuma zan yi respecting duk wani amsa da za ki ba ni kawai ina so ki sani ne... Za mu yi magana kin ji?""" Kai ta gyaɗa tana sauraronshi ya katse kiran. Ta yi kuka mai isanta kan ta miƙe ta shiga toilet ta wanke fuskarta ko da ta fito ƙasa ta yi wurin Momma. "Kusan sati biyu da maganar nasu bai sake tado mata maganan soyayyar ba ya kan kirata dai su gaisa ko su ɗan yi hira tunda yanzu ta daina zuwa asibitin saboda lafiya da ta samu, yau ya kama Lahadi bayan ta gama abin da take ta nufi ƙasa wurin Momma a kitchen don kama mata aiki tunda Aina'u bata nan tana gidan Daddy Z tun jiya da su Fadil. Momma na ganinta ta ce ""Yauwa dama yanzu nake shirin kiranki, ki je ki ɗaki akwai saƙon Hudah a kan gado please ki kai mata ki ce mata daga Aunty Kubra ne za ta ƙira ta, sannan ki biya wurin Husna ki karɓo min saƙo sai ki taho da yaran nan Aina'u na da exams gobe ko takarda ɗaya bata dauka ba bare ta yi focusing a karatu""" "Kai ta gyaɗa tare da juyawa jiki a mace kaman yadda take jinta tun tashin ta yau ta koma saman ta shirya, yau dai bata zurma hijabi ba ta saka doguwar riga ta yafa gyalen ta ɗauko" saƙon ta fito jiki a mace ta sake yi wa Momma sai ta dawo ta fice. "Ko da ta iso gidan hudan a waje tayi parking ta sauka ta nufi ciki, a kitchen ta sameta tana" "ƙoƙarin ɗora abincin rana ""Oyoyo Twinee""" Ta je tayi hugging ɗinta """Me na ga duk jikinki a mace haka? Me yake faruwa twinee? Ko Dr Najeeb ɗin ne?""" Jan hannun Hudar ta yi har parlor suka zauna """Hudah ban san ya zan yi ba wallahi, ni duk na rasa makama ba zan iya ƙin Najeeb ba saboda" "zuciyata ta riga ta kamu da son shi amma ina tsoron outcomes ɗin, ana cewa zuciya bata da" "ƙashi i started to blame my heart for racing for him idan na rasa shi shima fa?""" """No Hibbah ki daina wannan tunanin" "Najeeb is kind, you admire him, you feel safe with him. Your emotions built a world around him on top of all that mahaifiyarshi na ƙaunarki bata taɓa kallon flows ɗinki a abinda zai hana su haɗa zuri'a da ke ba to na me ɗaga hankalin? Saboda kin rasa samari biyu da kika taɓa ƙauna baya? Wannan ba hujja ba ne su ɗin ba su ne Allah ya nufa za ki aura ba sai tsani ƙaddarar haɗa ki da Dr. Najeeb da suka zama ki daure ki bashi dama yadda ya kamata""" Numfashi mai nauyi ta sauƙe tana jin kalaman Hudan suna sake tasiri akan abin da take ji a ranta. """Shikenan zan bashi dama, i pray komai ya tafi smoothly""" Hudah ta amsa da Ameen tana murmushi """Ke na ga kin ɗan faɗa menene? Har yanzu waenchan basu fita hanyar ki bane ko?"" Hibbahn ta faɗa tana sake kallon Hudah da ta ɗan ƙara haske ta rame kaɗan." """Hmmm Hibbah ki bar wanda ya ce baya sonka tun farkon fari, Falmata dai ta shiga taitayinta don bata sake shigo min nan ba amma duk sanda zan je gaishe da Hajiyar Mu'azzam idan kika ji irin kalaman da take jefana da su sai kin yi min hawaye, har Mayya kirana take ina so in rabata da ɗanta da danginta abubuwa iri iri dai amma ya zan yi ne? Ni kuma nawa jarabawar" "kenan""" Bata da daman cewa kar ta je gaisheta tunda gida daya suke kuma ko Mu'azzam din ba zai ji daaɗi ace ko gaisuwa baya shiga tsakanin Hudar da mahaifiyarshi ba amma da ita ce tana gayamata A sai ta kai mata har Z don wanda bai kama girmanshi ba bata ga amfanin girmama shi ba. """Girki fa? Har yanzu kina yi da su?""" """A'a tun bayan abin da ya faru kaman yadda kika ce ne na cigaba da yau labta Maggi gobe mai ta gaji ta ce mishi ya ce in bari basa so tunda ni goyon sakalci ne ban iya komai ba za su dinga dafa abinsu tun daga nan ban sake ba, sai yau da bata da lafiya jininta ya hau shine Mu'azzam din yace in yi girkin dare da su""" Hibbah ta ɗauki saƙon tana ajiyewa gabanta tace """Toh ai shikenan, Allah ya kyauta ya kawo karshen zamanku da alkhairi"" ""Ameen fa, menene wannan?""" """Momma ta ce in kawo miki wai daga Aunty Kubra ne za ta ƙira ki"" Buɗewa take tana murmushi don ta fahimci abubuwan su na mata ne ""Dole a ce za'a kira ki ni ce kenan ba za'a yi wa bayani ba. Ku kuka sani""" "Ita dai Hudah dariya take ta adana kayanta ta dawo suka taɓa hira akan school ne ma Hibbah na cewa har yanzu bata ji tana son komawa ba, kila sai gaba ko ma ta yi transfer don makarantar ya fice mata a kai daga karshe dai ta tafi ko sashen Hajiyar bata kalla ba duk yadda" Hudah ta so taje ta gaisheta ta ƙi tayi tafiyar ta. "Kai tsaye gidan Daddy Z ta tafi ta kuwa samu suna rigimar da suka saba idan dodon nasu baya gida, wai ana yi wa Aunty Husna sata a kitchen na abubuwanta na girki don a sace zuciyar Daddy Z yadda ta sace shi yake ƙaunarta da bata girma, fareed ya ce ai Aiman ake aika babban ɗan Amaryar Aunty Maryam shine uwar sai ta mishi duka da munafurcin da yayi musu wurin Aunty Husna." Kai tsaye fareed taje ta janye ta koma kan kujera ta zauna tana kallonsu sai ta rasa wai akan Daddy Z wannan dodon da ko dariya baya yi suke ɓata lokacinsu da karfinsu ita wallahi tana ga ta chanchanci a mata dan banzan duka idan aka ga tana faɗa akan miji har mamakin masu yi kan saurayi ma take. Aina'u dai ta yi zuru zuru kaman yadda yaransu suka yi amma ganin Hibbah ya sa hankalinta ya ɗan kwanta """Za ka zo ka sameni ne munafuki kawai shiyasa Aunty Zakiya bata ƙaunar ko inuwar da kuka" "tsaya saboda ta san kun iya kissima husuma da haɗa wuri""" """wowowowo ɓarawo dai ya ji kunya kuma ahir ɗinki har abada ba za ki iya irin girkin da na iya ba, shiyasa mana Baban Ammar kullum ya ci abincin wata sai ya sha magani ashe concoction ake haɗa mai""" """A haka ɗin dai ya ganni har ya auroni ya kawo miki ke da kika ƙware a girkin...""" Tana kai nan ta ja tsaki ta buɗe kofarta ta shige. Hibbah ta girgiza kai tace """Sannu Aunty Husna""" Yadda ta faɗa ɗin ya saka Husna da Aina'u fashewa da dariya. """Me kike min sannu? Ko ke ce za ki yi abinda ya fi haka, matar nan tana raina min wayau dayawa""" Miƙewa Hibbah tayi tace """Aina'u je ki shirya yaran nan za mu tafi yanzu, kai kuma da kunnuwanka kaman na felfelar jirgi ka cigaba komai ka gani sai ka yi magana watarana sai an zubar da hakwaran nan ka zama" "wawulo za ka gane""" "Tayi maganan tana jan lips ɗin shi ya fashe da kuka, Aina'u ta janye su suka yi sashen Aunty" Husna inda anan suka sauƙa tunda suka zo dama. Ita da Aunty Husnar ɗakinta suka nufa tana cewa """Aunty ni fa akan mijinkun nan ba zan zauna ina faɗa ba, da ma yana kasheni da soyayya ne to amma in ta hayagaga idan kuma ya dawo ya zama kaman hadari ba da ni ba dambe da mahaukaciya""" Dariya Aunty Husna tayi tana cewa """Hibbah ba za ki gane irin su Baban Ammar ba... Kuma wallahi ya dawo sai na sanar da shi sata take son koyawa yaranshi ba junanta rashin kunya da fitsara ba!""" """Wai Aunty Husna haka kowasu kishiyoyi suke ne ba zaman lafiya? Ba Za ku haɗa kai ku zauna lafiya ba?""" """Ai idan kin ga an samu haɗin kai sai duka ɓangaren suna so, da farko na so ƙwarai mu zauna lafiya da Maryam sanin halin Baban Ammar amma matar nan ƙarfi da yaji take son fitar da ni daga kan 'ya'yana alhali ita ta zo ta same ni, da farko gori take min da bana haihuwa ne ya sa ya aurota sai kuma na riga ta haihuwa na haifi ma namiji hakan bai isheta ishara ba ta cigaba da makirce makircenta tare da yayarta duk don su fiddani alhali basu sani ba Baban Ammar ba zai taɓa iya rabuwa da ni ba... Kuma ko a yanzu ina kan tabbatar musu da aurena mutu ka raba" "ne takalmin kaza dole su haƙura su kyaleni""" "Ita kanta Hibbah ta san matsalar daga Aunty Maryam ne don tun da ta zauna gidansu wurin Auntynta Hajiya Zakiya da uwa ɗaya uba ɗaya suke bata da mutunci, sun sha yin rigima da Hibbah tun tana secondary don ta jima a gidansu har auren ma Daddynsu ne ya aurar da ita tare da su Nadiya yarinyar Hajiya kamila, kusancin Aunty Husna da Momma ke sake rura wutar rigima tsakanin Maryam din da Husna Dukda ita Husna da zuciya ɗaya ta so zama da ita tun farko." Har gwara yanzu ma abubuwan sun yi sauƙi da kullum Daddy na nan yana sulhu don Uncle Z rigimar shi sai shi koro Maryam ɗin yake ko ya daketa ayi ta ɗauki-ba-daɗi. """Kowani aure dai da nashi ƙalubalen wasu na kuka silently wasu muryoyinsu ya fita, Allah dai ya" "sa mu dace. Ga sakon ki inji Momma""" """Ameen ya rabbi. Kai amma na gode ƙwarai zan kirata""" Hibbah ta gyaɗa kai bayan su Aina'u sun shirya suka fice daga gidan suna shiga gida Aina'u ta shiga ba Momma labarin abin da ya faru a gidan na Daddy Zubair ita dai haurawa tayi abin ta sama. "Tana shiga ɗaki sai ga call na Dr. Najeeb kuma dama ya ce mata next call dinshi amsa ne zai yi demanding amma zai zo ne har cikin gida, gabanta ya ɗan faɗi a hankali tayi picking yace mata ""Ga ni cikin unguwarku ina fata kin shirya tarba ta?""" Hannu ta sa ta dafe zuciyarta dake beating very fast... "*Littafin nan na kuɗi ne ki biya Naira Ɗari biyar (500) kachal domin kasancewa cikin masu kwasar tarin ilimi, faɗakarwa da zazzafar soyayya mai cike da sadaukarwa da aka zube ciki. Za ki biya ta wannan asusun" 0545475847 Gt bank Fatima Muhammad Gurin Sai ki tura shaidar biya zuwa wannan layi 09039206763 Ko kuma katin MTN na Naira 500 cikin wannan layi na sama sai ki tura da shaidar biya ta same layi. Sai na ji ku* Note: Da dare ne zan dinga posting da rana zan bi in dinga karanta comments naku so please a ba ni haɗin kai mu tafi lafiya kaman yadda muka fara lafiya. Na gode sossai. Gureenjoh SAFARA A TAƁO FATIMA MUHAMMAD GURIN *GUREENJOH* *ADABI WRITERS ASSOCIATION* *PAID BOOK* *012* "Gaban madubi ta ƙarasa ta dafe, kanta a ƙasa tana ƙoƙarin saita gudun da zuciyarta ke yi kaman zai ratso kirjinta ya fito, haka kawai take jin kaman jininta na hawa bata san me zata yi ba, she's feeling not safe about this kaman something is not right, ta ɗauki tsawon lokaci kan ta iya saita kanta ta ɗago ta kalli madubi, babu abin da ta ƙara ko ta chanza haka ta juya ta nufi" "ƙasa hannunta riƙe da wayanta, a parlorn ta tsaya kusa da Momma tace a hankali" """Momma na yi baƙo ne yana so in fita mu gaisa..!""" Da sauri Momma ta ɗago tana kallonta amma ganin tension a yanayinta da alamu tana cikin sarkakiya ko wani damuwa ya sa bata ce komai ba bayan """Sai kin dawo""" "Juyawa kawai tayi ta fita cikin sassarfa tana fita harabar gidan motarshi na shigowa daga bayanshi Nadiya babbar 'yar Hajiya kamila kuma ita ce babba a gidan gabaɗaya a yaran Daddy ta shigo bayanta goye da ɗiyarta, motar na parking ya fito yana kallonta ta mayar da kanta kan" "yatsunta tana wasa da su, shi kuwa ya narke a kallonta maganan Nadiya ya katse su..." """Hibbah baƙo aka yi?""" "Juyawa yayi kaman yadda Hibbah ta ɗago tana kallonta, ta san da gayya ta tsaya ba arziki ne ya tsaida ta ba." """Eh, sannu da zuwa""" Ta faɗa tana ɗauke kanta a lokacin Dr. Najeeb ya jefa mata gaisuwa ta amsa ta sake kallon Hibba """Ya kufayin jikin dai? An ce wai ɓari kika yi ne ko Haihuwa ma?""" "Daga Dr. Najeeb har ita da sauri suka kalleta sai Hibbah ta mayar da kai kanshi shima ya ɗan juyo yana zuba wa yanayinta idanu, sossai ta haɗe rai tace" """Idan kin faɗa domin ki ɓata ni ne shi wannan da kike gani tunda abinda ya sameni ya faru bana rufa sati biyu bai ganni ba idan ma haihuwar ne shi ya kamata ya fara sanar wa don na tabbar shi zai karɓa kan ya iso kunnuwanku. Dr. Mu isa ciki na barka tsaye Afuwan!""" "Tana kai nan ta juya ya bi bayanta bayan ya juya ya kalli Nadiyar, seating room na Daddy ta" "mishi iso suka zauna kanta ƙasa zuciyarta na ƙuna akan abin da Yaya Nadiyar ta yi mata, numfashi ya sauƙe a hankali ya ce" """kin manta you promised ba za ki bari maganar kowa ya yi hitting ɗinki Hard ba? You are a strong woman Hibbah sincerely speaking yadda kika amsa mata ya burgeni ƙwarai i like ur confidence""" Ta ɗan kalleshi cikin sigar Harara yayi dariya itama ta yi murmushi bai tambayi alakar su da Nadiyar ba kuma bai damu ya sani ba abinda kawai ya sani bata son Hibbah kuma shima baya sonta ko wacece ita ga hibbar. "Miƙewa Hibbah tayi ta kawo mishi ruwa da lemu daga frigde na Daddyn ta tsiyaya mishi five alive a glass cup ta miƙa mishi, fararen yatsun ta dake ɗauke da jan lalle da ya rufa maroon" sharr ya bi da kallo. """Thanks love!""" "Ta ɗan yi murmushi kan taje ta zauna inda ta taso, sai da ya kurba kan ya ce ""Ya kike? Kin yi min wuyar gani""" """Eh ai ku ganinku sai dole, in ba dole ba wa zai so rashin lafiya?""" "Suka yi murmushi a tare ""Hibbah""" Ta kalleshi """I Miss you...""" Zuciyarta ya doka ta mayar da kanta ƙasa """Na zo ne in ji amsata shin wannan ɗan bawan Allahn ya samu karɓuwa? Ko in je in rungume tramsfomer?""" Dariya ta yi shima ya cigaba da murmushi yana kallonta. """Ɗan umma ya yi nasara akan Hibbah. Don Allah ka riƙeni amana do not betray me kar ka ƙarasa zuciyar da ta riga ta gama tsatsagewa tarwatsewa ne kawai ya rage """ Ta ƙarasa hawaye na silalo mata """Amsarki kawai ta isa na cigaba da kasantuwa a cikin farinciki a raina lallai na yi babban dace wanda ba zai misaltu na iya bayyanawa ba, na zamo mafi sa'a da samun ki kuma na miki alkawari mutuwa ce kawai ta isa raba wannan alaƙa sai kuma wanda ya haɗa""" "Daga wannan lokaci Hibbah ta buɗewa Najeeb zuciyarta ya shiga ya yi kane kane, soyayya suke zubawa ba na wasa ba yayi nasara ƙwarai wurin mantar da ita duk wani burbushin damuwarta, Momma ma hankalinta ta kwanta ƙwarai ganin yadda Hibbah ta dawo da" walwalarta kaman komai bai faru ba Dukda har yanzu ta ƙi komawa makaranta. Safiyar Asabar ne sun gama karyawa suna zaune gabadayansu kawai Hajiya Kamila ta dubi Daddy """Jiya mijin Amal ya kirata Alhamdulillah komai na warwarewa bisa tashi tsaye da muka yi mu ma, ya ce ta shirya komawa wani sati zai zo har nan ya ɗauketa""" "Amal ɗin da ke zaune tana ta murmushi Hibbah ta kalla ta ɗauke kai. Daddy ya ce ""Toh Alhamdulillah tunda komai ya warware dama haka ake fata sai ta hau shiri"" Momma ta musu barka suka amsa a gatsine." Hajiya kamila ta sake cewa """Sai Nadiya ta ce ɗiyarta ba lafiya tana so Mujiba ta je ta ɗan kama mata aiki samu ta kaita asibiti""" """Meyasa sai Mujiba? Sauran yaran kam ba ƙannen Nadiya bane? Meyasa kuke so a koyaushe" "ku ga kun raba mini kan yara ne kam kamila?""" Hibbah ya kalla """Ki shirya ki je gidan Nadiya ki kama mata aiki ta kai yarinya asibiti""" Har ranta bata so ba amma wacece ita da zata Musa? A hankali ta amsa da Toh ta miƙe ta fice daga parlorn ko ta je ma rigima ne zai biyo baya su da ba'a raba su da rigima. "Sama taje ta ɗauko wayanta da car key ɗinta ta fice daga gidan kai tsaye ta nufi Gidan Nadiyar, tana shiga parlorn a kan idanunta Mijin Nadiyar na tsinketa da mari har ɗiyar hannunta na faɗuwa a ƙasa ta fasa ƙara, wani irin zaro idanu Hibbah tayi ganin Nadiyar jiki na rawa ta shiga kokarin bashi haƙuri shi kuwa yana sake harzuƙo wa yana yunkurowa zai sake" Kai mata hannu. Wani irin tsalle hibba tayi ta dira tsakiyarsu ba tare da ta sani ba ta sa hannu ta ture shi da ƙarfin gaske """Baka da hankali ne? Kai dabba jakin wani garin ne???""" Da ƙarfi tayi maganan har Nadiya na maƙalewa bayanta cikin kuka. """Wacece ke da za ki shiga abin da babu ruwanki? Ke kin san wan...""" """Ko uban waye kai baka da right na sa hannu ka daki matar aurenka, kai ko ma wanene kai you are very, very stupid...""" Hannu ya ɗaga zai daketa ta mishi ihu """Kana taɓa ni wallahil azeem daga yau ba zaka sake marmarin taɓa wata mace a duniya da sunan duka ba, zaka ga danyan hauka da jahilci wanda ya ci uwar naka Gidanka gidan 'yan" dambe ya zama da zaka daki uwa ka daki 'ya? Idan damben kake ji ka je ka shiga wrestling "mana ka yi da maza masu jini a jika!""" "Ta juya ga Nadiyar dake shaking cikin kuka take cewa ""Ke kuma wa """ Ta ja dogon tsaki ta ma kasa ƙarasa wa ta kusa zaucewa wani irin namiji ne Nadiyar ke aure? Ashe da suke ta pretending tana zaman lafiya tana cikin jin daaɗi suna yi ne don kawai kar a musu dariya? Ba gara dariya ba da zama ciki assault? Bare ma wa zai yiwa ƙaddarar wani dariya idan ba su ba jahilai da kwakwalwarsu ke dankare da tarin wawanci da rashin sanin ciwon kai? """Yaya Nadiya tashi mu tafi""" "Ta ɗauki yarinyar da har lokacin bata yi shiru ba jikinta rau kaman wuta za su fita ya ce ""Wallahi Nadiya kina fita a gidan nan a bakin aurenki""" """Sai me??? Sai me?? Dama wannan aure ne? To hell with you da auren naka da ma gidan gabaɗaya. Ki tashi mu tafi """ Yadda take tafasa za ka zaci ma ita ce yayar Nadiyar ce ƙanwar. "Janyeta tayi suka fice daga gidan Nadiyar na ta kuka har mota ta ja ta bar gidan, rasa ma me zata fara yi tayi don yarinyar na bukatar ganin likita haka kuma tana son ganin Daddy cikin gaggawa." "Asibiti ta fara yi wurin su Najeeb kan ta isa ma ta kirashi akan suna zuwa ganin Pediatric dr saboda yarinyar ma is at state of emergency, duk abin bukata ya sa aka tanada suna isa aka karɓi yarinyar Nadiyar na tsaye daga gefe tana kuka, kallo ɗaya yayi mata ya ganeta bai cewa Hibbah komai ba har sai da yarinyar ta zama stable ya zo yana tambayar" """Meyasa yarinyar nan zazzabi na jikinta ba'a iya an kawo ta asibiti ba sai da ya ci karfinta har ya" "ƙone ruwan jikinta? Wasu irin iyaye take da su da basa aiki da hankali?""" A matsayinshi na likita faɗa ya ringa yi Hibbah ta kyale shi da Nadiyar da take ta kuka kawai tana roƙon ya taimaka yarinyarta kar ta mutu ta rasa yara har biyu cikin sakaci irin wannan da tsoron mijin nata. ya ce """idan ta mutu ma ai sakacinki ne ba na wani ba""" Yana kai nan ya wuce Hibbah tayi murmushi ta juya gareta. """Na kira Daddy ya ce ana samun kan Amatun mu je gida yana son ganinki""" Bata ce komai ba jiki a sanyaye ta juya suka fice. "Babu hijabi duk abin da ya faru sai da Hibbah ta faɗawa Daddy da Brothers ɗin shi dake zaune, shi dai Daddy Z bai ce komai ba don ya riga ya fitar da kanshi a abinda ya shafi yaran Hajiya kamila tunda ta ce ba ruwanshi Daddy Rabi'u ne ya ce" """Ke Nadiya dama hakan ya jima yana faruwa ne baki iya kin kawo batun gida ba?""" Hajiya Kamila dake ta maka mata Harara ta kalla kan ta mayar da kanta ƙasa tana zubar da hawaye. """Ba magana ake miki ba kin mayar da mutane banza??""" "Daddy Z ya daka mata tsawa, jiki na rawa tace" """Eh Daddy amma Hajiya ce ta hanani faɗa muku saboda bata son kishiyoyi su yi mata dariya idan aurena ya mutu""" """Ba ka ji dabbanci da rashin hankalin ba? Ba ka ji ba Yaya...""" Daddy ya faɗa cikin tsantsar takaici ya juya ga Hajiya kamila """Wace iriyar uwa ce ke? Ni da na haifi yaran nan kin taɓa gani na saka su gaba ina jibga har sai da na aurar da su da girmansu, iliminsu daidai gwargwado da hakwaransu talatin da biyu wani chan gardi yaje yana jibgarsu ki ce kar su faɗa? Dariyar banza dariyar wofi... Yanzu idan da Hibbah bata je gidan ba sai kenan ya kashe yarinyar ita ma ya kasheta a banza?""" Ta inda yake shiga ba ta nan yake fita ba zuciyarshi har zafi zafi yake mishi saboda bacin ran Hajiya Kamila da ko a fuska bata nuna wani damuwa ba hasali ba wani haushin Hibbah da "Nadiyar ne ya zo mata wuya, tana ganin ai Nadiyar ta gama sunce mata zani a kasuwa ne." """Zan yi ƙarar wannan marar mutuncin wallahi he must pay na taɓa yarinyar nan""" "Daddy Rabiu da shine waliyyinta ya faɗa a hasale, Daddy ya sallame su suna fita Hajiya kamila ta bi Nadiya da zagi da masifa hibbah na kallonsu har suka ɓace mata kan ta girgiza kai ta nufi nasu sashen." "Ko a mafarki bata yi tunanin rashin wayon Nadiya ya kai ta zauna wani na jibgarta ba, da ilimin ta da gatanta da komai saboda karamin tunaninsu, ta tuna fa itama Nadiyar auren soyayya suka yi da Baban Amatun don tana tuna har choculates da sweets yake kawowa in ya zo hira a raba ayi ta iyayi a wurin wasa musamman su Amal, ashe soyayyar duk na bogi ce to anya akwai auren da yake da daaɗi kuwa a wannan duniya? Ita dai duk inda ta juya matsaltsalu take" hangowa dake ƙara tsinka zuciyarta da al'amarin mazan da ma kanshi rayuwar auren. """Ke lafiyarki kuwa?" Taji an faɗa daga bayanta da sauri ta juya... "*Littafin nan na kuɗi ne ki biya Naira Ɗari biyar (500) kachal domin kasancewa cikin masu kwasar tarin ilimi, faɗakarwa da zazzafar soyayya mai cike da sadaukarwa da aka zube ciki. Za ki biya ta wannan asusun" 0545475847 Gt bank Fatima Muhammad Gurin Sai ki tura shaidar biya zuwa wannan layi 09039206763 Ko kuma katin MTN na Naira 500 cikin wannan layi na sama sai ki tura da shaidar biya ta same layi. Sai na ji ku* Note: Da dare ne zan dinga posting da rana zan bi in dinga karanta comments naku so please a ba ni haɗin kai mu tafi lafiya kaman yadda muka fara lafiya. Na gode sossai. Gureenjoh SAFARA A TAƁO FATIMA MUHAMMAD GURIN *GUREENJOH* *ADABI WRITERS ASSOCIATION* *PAID BOOK* *013* """Yaya Nasir? Yaushe a gari?""" Tayi tambayar tana murmushi yace """Tun jiya sai dai Hotel na sauƙa, aiki ne ya kawo ni branch namu na nan. Lafiya kike kam?""" "Suna ƙarasa wa cikin babban parlorn tace ""Lafiya ƙalau fa, ya ka baro su Yaya Zaitoon?""" Momma dake fitowa tace """'yar uwarki kawai kika sani ko? Nasir barka da shigowa ya Yayata?""" "Daga shi har Hibbah suka yi dariya, Aina'u da ta fito taje ta kawo mishi ruwa da snacks nan suka zauna suka shiga hira abinsu, zai dan yi kwana biyu amma ba gidan zai zauna ba saboda idan suka sauƙa gidan basa jin daaɗin su Hajiya kamila don haka suke sauka Hotel abinsu ko sun zo gidan ziyara ne, ya jima don har bayan isha yana nan tana tsaye da Dr. Najeeb da zai" koma bayan hira da suka yi ya fito tace """Dr. Ga yayana Yaya Nasir""" Miƙa mishi hannu yayi suka gaisa kan tace """Wai zaka wuce kenan?""" Kai ya gyaɗa """Zan tafi sai zuwa wani sati ma kila zan sake shigowa saboda daga gobe aikin da ya kawo ni zan fara""" """Toh Allah ya taimaka sai da safe""" "Ya je ya ɗauki motar Momma ya bar gidan, basu jima tsaye da Dr. Najeeb ba ya tafi shima tana" bashi saƙon gaisuwa zuwa wurin umma kaman yadda itama bata taɓa gajiya da aiko mata da saƙon gaisuwa ba. Tana shiga cikin parlor ta tarar duk ba kowa ma sai mai aikin dake gyarawa ta haura sama kai tsaye zata shiga ɗakinsu Fareed ya kirata """Momma wai ki zo Yaya Twinee""" "Kai ta gyaɗa ta juya zuwa ɗakin momman ta samu ma Aina'u na janyo fadeel akan su tafi taje ta shirya su su kwanta yana ƙi, masifeshi tayi da sauri ya riƙe hannun Aina'un suka fita Momma ta dube ta" """Ki dinga kokarin bin yaran nan a hankali mana don Allah ji fa yadda duk kika tsorata min ɗa""" Ta taɓe baki kaɗan tana zama """Momma Allah raini ne ban cika so ba, ki ga fa abin da yake yi wa Aina'u kaman wata sa'arshi amma kin san ina son yara""" Momma tayi kwafa kan ta ce """Shi wannan dake zuwa wurinki waye ne?""" "Dukda tana tsammanin titseyen sai dai da taji daga bakin momman sai da gabanta ya faɗi," kanta ta mayar ƙasa """Momma Dr. Najeeb ne""" "Fuskar Momma a ɗan washe tace ""Wannan likitan dake duba ki a asibiti?""" Kai ta gyaɗa Momma ta ce """Masha Allah yana da hankali kuwa, ga mahaifiyarshi mai kirki ko ba ita muka samu a ɗakin asibiti kwanaki chan da baki da lafiya ba ta zo duba ki?""" """Ita ce Momma, ai kirkinta ya wuce nan, har fa layina ta karɓa wurinshi ta kirani rannan daga" "haka nayi saving idan nayi kwana biyu ban ƙira ba ita za ta ƙirani mu gaisa""" """Masha Allah! Allah ya kara mata lafiya"" Hibbah ta amsa da Ameen." """Babanku ya ce ki ce mishi ya iso idan da gaske yake saboda ya ganshi ba sau ɗaya ba ba sau biyu ba yana zuwa wurinki.""" "Da sauri ta ɗago tana kallon Momman ""Mene? Ba da aure yake sonki bane?""" Kanta ta mayar ƙasa gabanta na cigaba da bugawa """Da aurene ya jima ma yana min maganar turowan ni ce dai nake ta kwana kwana, Momma tsoro nake ji sai in ga kaman shima auren ba zai yiwu ba!""" """Me zai hana shi yiwuwa Hibbah? Ke ba mace bace kaman kowa? Kuma ina ce babu abin da bai sani ba akan abin da ya faru a baya hatta mahaifiyarshi ma ta san komai to tsoron me kike?""" Numfashi ta sauƙe """Hakane zan faɗa mishi Momma""" """yauwa. Ki cire duk wani shakka ko tsoro a ranki babu abin da zai hana ki samun farin ciki, akan ciro mace ma daga gidan karuwai a aureta kuma ayi zaman lafiya da ita bare ke da hotuna ne" su ɗin ma kuma ba tumbur haihuwar uwa ba. Zuwa yanzu duk komai mu barshi a baya mu yi "adu'ar Allah ya tabbatar muku da alkhairi a tsakaninku""" Kai Hibbah ta gyaɗa bata wani cigaba da zama ba ta yiwa momman sai da safe ta wuce ɗakinsu. Shirin bacci tayi tana ƙarewa kaman yayi timing sai ga ƙiran shi """Ka je gida lafiya?""" """Ba ƙalau ba""" "Yayi maganan kaman baby ""Subhallah wani abu ya faru ne?""" Kai ya girgiza """I wished cewa da na dawon nan ke zan tarar zaune cikin kwalliya ki tarbe ni da murmushin nan naki mai kyaun gani da narkarwa""" Murmushi tayi mai sauti """Soon in shaa Allah, yanzu ma da albishir a baki na"" ""Haba? Faɗi mu ji""" """Uhmm uhmm sai an ba ni goro fari kallll""" """Na ji za ki ga goronki fari kalll ni dai ba ni in shaa"" ""Daddy ya ce ka turo""" Karamin ihun murna yayi """Yessss Alhamdulillah Alhamdulillah""" Murmushi take yi jin farin cikin da ya shiga haka suka cigaba da soyewa kan su yi sallama ya tabbatar mata zai tuntubi Baba gobe da safe suna saka date na zuwan nasu zai faɗa mata ta faɗawa Daddyn. **** "Da ciwon kai yau ta yini tana girkin ranan ma tana jin jiri jiri na damunta, miyan tayi tasting taji ba gishiri ta dibo ta ƙara ta sake tasting bai fita ba ta sake ƙarawa Dukda kadan ta yi niyyar sawa saboda Hajiya dake fama da hawan jini a kwanakin don haka bata buƙatar gishiri mai yawa amma jin miyan bai fitar da gishirin ba kuma ta gaji da ƙarawa ya sa ta rufe ta ƙarasa duk" abin da zata yi ta zuba na su hajiyar ta fito da su a basket ta nufi wurin hajiyar. "A ƙasa ta zauna ganin Mu'azzam shima zaune yana matsa mata kafafu, ganin abincin yace ""Yauwa Hajiya dama yanzu kika gama zancen yunwa kike ji ga yarinyar nan bata gama girki da wuri ba bari na zuba miki wannan kawai sai ki ci ki sha maganin""" Zai ja basket ɗin Huda ta matsa gangarshi ta buɗe ta shiga serving a natse bayan ta gama ta ajiye gaban Hajiyar ta koma ta zauna. Cokalin Hajiya ta ja tayi bismillah a fili ta kai loman farko... Wani irin furzarwa ta yi tana kakari """Ba ka ga ba Mu'azzam? Ba ka gani ba? Na ce maka matarka bata ƙaunata kasheni take son yi ka ƙi yarda yanzu idan ba baƙar mugunta ba me na labta gishiri alhali ta san ba ni da lafiya??""" A ɗan ruɗe Hudah tace """Hajiya me yasa zan kashe ki? Wlh ko kadan gishirin abincin nan bai fita ba, wallahi ba zan iya" "cutar dake ba ko menene kuwa kika min...""" Mu'azzam ya janyo cokalin ya ɗanɗana abincin da sauri ya furzar yana kallon Hudah """Amma baki san an hanata cin gishiri haka bane? Meyasa za ki zarge ta da miki karya Hudah alhali gaskiya ce? Wannan gishiri ko ke ba na tunanin za ki iya cin abincin nan...""" Hajiya na sharce hawaye take cewa """Ai wannan watarana sai dai ta zuba min maganin ɓera in ci in mutu...""" Da sauri Hudah ta karɓi cokalin ta ɗanɗana hawaye na cika idanunta ganin irin kallon da suke mata ta ɗanɗana bata ji komai ba """Wallahi ban ji komai ba, yanzu menene a abincin nan?""" "Haushin musun da take yi ya kama Mu'azzam bai san ya rufeta da masifa ba kaman zai ari baki, a rikice ta ɗauki abincin tana cewa bari taje ta chanzo taku biyu ta yi zuwa uku ta faɗi a wurin a sume." **** "Nasiha Daddy da Daddy Rabi'u suka saka alqasim a gaba suke mishi na haƙuri da rayuwa da kuma jarrabawa don ya ce musu kusan ya rasa komai nashi sai dai adu'ar Allah ya dawo mishi da arzikin, sun tausaya mishi ƙwarai daga Daddy har Daddy Rabi'u sun bashi kyauta masu" tsoka akan ya riƙe hannunshi kan aka turo Amal don su wuce. "Har tsakar gidan su Hajiya kamila suka rakota, baki har kunne cike da nishadi ta shiga jar motar dake parke yana jiranta, shima Alqasim ya shiga suka fita a gidan a hankali." Suna fita daga gidan ya riƙo hannunta cikin kulawa """My love na yi kewarki""" Ta langwabe tana kwantar da kanta jikin kafaɗarshi """Ba zaka gane yadda nayi kewarka ba don faɗa ma ɓata baki ne Sweetheart""" Murmushi yayi yana shafa kanta suka cigaba da zama ganin ba'a ɗauki hanyar gidansu ba sai ma wani uban tafiya da suka ɗauka ya sa tace """Ina kuma muka nufa Sweetheart?""" """Gidanmu za muje, kin san abin da ya faru a yanzu haka gidana bai dawo hannuna ba zan kaiki wurin su Inna ne ku zauna tare kafin komai ya daidaita ina fata za ki bani haɗin kai?""" Kai ta gyaɗa tana komawa kishingiɗe """Babu matsala my love ai mahaifiyarka tamkar tawa take, Fatana dai Allah ya dawo maka da" "duk abin da ka rasa cikin sauƙi.""" "Ya amsa yana murmushi, tun suna tafiya tana gane ma hanyoyin da ake bi har ta ɓace, ba su suka tsaya ba sai cikin wani ƙaramin kauye mai dauke da jar ƙasa da ma gine gine irin na jar kasa, yara ne yuuuuuuu suke biye da motan suna ihu daga marasa wando sai masu majina duk sun yi futu futu kaman dodon wasannin yara." """Ga qasimu! Ga qasimu...""" "Kallonshi tayi cikin tsantsar mamakin da ya kasa ɓoyuwa a fuskarta ta kalli kofar gidan da suka tsaya da buhu ne madadin kyauren wani wurin ma a fashe kwata ne mai girma da sai ka tsallake kan ka shiga cikin gidan, hankalinta a tashe tace" """Ina ne nan Alqasim?? Me muke yi anan?""" """Yanzu fa na gama ce miki wurin inna zan kawo ki ku zauna kafin komai ya warware"" Idanunta kaman za su faɗo ta kalli kofar gidan ta sake kallon Alqasim a rikice ""Naan. nan shi ne gidanku?""" """Eh mana anan aka haifeni, nan ne gidan iyayena""" """Innalillahi wainna ilaihi rajiun Na shiga uku! Alqasim mayar da ni gidanmu, mayar da ni gidan iyayena wallahi ba zan iya zama anan ba""" Buɗe kofa yayi ya fita ya zagaya ya buɗe ɓangaren ta ya janyo hannunta """Ai kuma zancen kike so, tunda kina aurena ai zama a gidanmu dole...Na ma yi miki da sauƙi da" "kika kwashe watanni gidanku""" "Turjewa take tana kuka akan ya saketa ita gidansu zata tafi shi kuma yana janta har ƙasa ta zube tana kuka ita ba zata iya shiga ko gidan bane shi kuma ya dage sai da ya kaita har ciki duk matan kauyen suna tsaye ana ta kallonsu, yana shiga innar shi ta taso" """Lafiya kuwa Qasimu?""" """Inna bata da lafiya ne a kawo ruwa ta sha ko zata watsake""" "Da hanzari innar taje ta kwalfo ruwa a randa ta kawo mata, ganin jan ƙasa dake kwance ciki ga ruwan jajazir kawai ya tayar mata da zuciya duk kwanon tsatsar lamba ne haka ya kai mata baki da karfi ta Buge ya faɗi sai amai." """Ashaaa Ashaaa jikin ashe yayi tsanani haka? Taho in taimaka miki zuwa ɗaki""" Ture matar tayi tana ihun kar ta taɓa ta cikin kuka da karaji. **** """Ai tunda kika zaɓi kashe aurenki ki dawo ki zo muna haɗa kafada babu abin da ba za ki gani" "ba, ba dai ni kika zaɓa a yi wa dariya a gidan nan ba? Za ki faɗa min idan bakin ciki kike da ni...ki wuce ki ɗaura mana abinci babu mai miki girki ki ci a gidan nan""" Kallon Mujiba ta yi """Hajiya fa kina ji yarinyar na min rashin kunyar da ta ga dama kuma ki ce ba zan yi magana ba? Gidanmu fa na dawo amma daga kan shara, wanke wanke da girki, gyaran dakinki hatta wanki duk yaran nan sun nade hannu sai ni zan yi? A kaina aka fara mutuwar aure? Idan ban bar baban su Amatu ba mutuwa zan yi kafin ki gane ina cikin ƙuncin rayuwa?""" Miƙewa tayi ta nufeta cikin masifa da tsawa """Da kina gidanki uban wa zai saka ki hakan? Tunda kin zaɓi ki kashe auren ai kin shiryawa zama da ni da bauta mini don duk wanda ya ki sharar masallaci zai yi na kasuwa tunda ba ladar za ki samu anan kaman dakinki ba... Mujiba kuma ba zata yi ba ke za ki yi don ubanki""" "Gabaɗaya hajiyar ta sauya mata, bata da sukuni da farin ciki a cikin gidan kaman wacce ke gaban kishiyar uwa, abu kaɗan zagi da cin mutunci bata la'akari da yanayinta ko ciwon dake cinta a cikin rai kuka take yi sossai kaman 'yar goye don ta fara gundura da zaman gidan tana" jin gwara dukan Mijinta da irin abin da mahaifiyarta ke mata. Miƙewa kawai tayi ta fice daga sashen tana kuka sossai ta nufi sashen Momma duk irin kira da ihun da Hajiya kamila ke mata akan ta zo kar ta taka kafanta wajen gidan bata waiwayo ba ta fice. Momma na zaune da su Hibbah suna hiran su kawai suka ji Shigowarta ko kan Momma tayi magana taje gabanta ta tsuguna tana kuka """Subhallahi... Nadiya? Lafiya me ya faru haka? Menene?""" """Momma haka kowace bazawara ke fama ne ko ni ce kaɗai? Momma ba gwara in koma in cigaba da karɓar duka ba da irin maganganun Hajiya marasa daaɗi? Momma ki ba Daddy haƙuri ya sa a bar ni na koma kawai na gaji wallahi ba zan iya cigaba da zama da Hajiya ba""" """Ki natsu Nadiya, a yanzu wannan kukan duk saboda Hajiya kamila ne? Share hawayenki ba za ki koma gidan da za'a cigaba da assaulting ɗinki ba har abada, ki tashi ki je ki zaɓi ɗakin da za" "ki zauna babu mai takura miki anan bare ya gayamiki baƙar magana kin ji?""" "Kuka kawai ta sake fashewa dashi tana ɗora kanta kan kafafun momman saboda abu ne da bata taɓa zato ba, duk irin cin kashi, rashin kunya da fitsaran da suke yiwa matar nan ta iya samun wuri a zuciyarta ta yafe musu kuma take marabtarsu a gangarta? Lallai zuciyarta mai kyau ne dole ta nemi yafiyarta sun zalunce ta bisa rashin sani da hurewan kunnen Hajiyarsu da" ta nuna musu Momma bata taɓa ƙaunarsu ba kuma burin ta shine ta raba su da mahaifinsu... "Wayan Hibba da yayi ƙara ya sa ta mayar da hankali kai tare da ɗauke kanta daga magaganun su Momman, Dr. Najeeb ne picking tayi tare da sallama suka gaisa a natse yace" """Babe kin kusa zama tawa... Tawa ta har abada""" "Murmushi tayi softly ""Allah ya nuna mana""" """ba za ki tambayi me yasa na ce hakan ba?"" ""To me yasa ka ce hakan?""" """Na riƙe maganata tunda bakya son ji""" """Da gaske ina son na ji""" """Su Abbana za su zo wani sati lahadi in shaa Allah, za'a zo a tambaya min aurenki"" Kunya ne ya rufeta ta rufe fuskarta tana dariya a hankali." "*Littafin nan na kuɗi ne ki biya Naira Ɗari biyar (500) kachal domin kasancewa cikin masu kwasar tarin ilimi, faɗakarwa da zazzafar soyayya mai cike da sadaukarwa da aka zube ciki. Za ki biya ta wannan asusun" 0545475847 Gt bank Fatima Muhammad Gurin Sai ki tura shaidar biya zuwa wannan layi 09039206763 Ko kuma katin MTN na Naira 500 cikin wannan layi na sama sai ki tura da shaidar biya ta same layi. Sai na ji ku* Note: Da dare ne zan dinga posting da rana zan bi in dinga karanta comments naku so please a ba ni haɗin kai mu tafi lafiya kaman yadda muka fara lafiya. Na gode sossai. Gureenjoh SAFARA A TAƁO FATIMA MUHAMMAD GURIN *GUREENJOH* *ADABI WRITERS ASSOCIATION* *PAID BOOK* *014* "Sossai Mu'azzam ya shiga cikin tashin hankalin ganin Hudah cikin halin da zai iya cewa su ne silar jefa ta ciki, tunda ya shigo da ita asibitin ko zama ya kasa yi sai zirga-zirga yake ya rasa ma wani irin tunani zai yi, shin yana cutar da Hudah kenan a zamantakewarsu? Zama gida ɗaya da mahaifiyarshi abu ne da ya kamata a ce ya cigaba kenan? Amma ita uwa ce haƙuri da su dole ne idan kana so ka ƙare lafiya yanzu idan ya yunkura da niyyar raba musu gida babu abin da ba zata iya yi ba wanda yana gani Allah zai kama shi akan hakan... Duk ya rasa Makama ko tunanin da ya kamata yayi akan wannan matsalar har likitar da ta shiga kan Hudah ɗin ta fito ta" wuce shi tayi office ɗinta ba tare da ta ce mishi komai ba. "Bayanta ya bi zuwa office ɗin ya samu kujera ya zauna ""Likita ya matata? Me ya sameta me ke damunta Dr?""" Kallonshi take yi cikin natsuwa tace """For now matarka da abin da ke cikinta duk suna cikin koshin lafiya amma kuka cigaba da wasarere da lafiya da kuma rayuwarta komai na iya faruwa a gaba, shin baka sonta ne ka aureta kake musguna mata? Ko kuwa ka gaji da ita ne ka zaɓi wannan hanyar yi mata kora da halin? Me yasa kuke haka ne kam? Kuna manta cewa wannan macen da ta amince ta aure ku always sacrife a lot don kawai tayi providing wa needs ɗinku ta kuma baku iyalin da za ku gani ku yi alfahari da, ta baku yaran da za ku bugi kirji ku ce naku ne, waenda za ku so su alhali" "itama ta baro nata gidan ne gaban iyayenta ba kuma don ba'a sonta b """ "Kanta ta juya tana jin kaman ta zub da hawaye, a carieer ɗinta na aiki ta san mata na going through alot, duk mace da zata gani da kalan problems ɗinta ba kuma don babu masu zuciyar imani da zama lafiya cikin soyayya da kauna kaman yadda addini ya koyar ba sai don poisoning mind ɗin maza da ake yi, komai namiji yayi daidai ne yayinda ko menene mace tayi na kuskure" it will be on her har karshen rayuwarta. """Dr. Wallahi ni da matata komai na rashin jin daaɗi ko baƙar magana na fatar baki bai taɓa hadamu ba, she's well trained and a respected lady i've ever came across...""" Katse shi tayi """Toh menene zai haddasa mata damuwa da shirin ɓari? Menene zai ke hanata cin abin da zai gina mata jiki da bata cikakken lafiyar da zata gudanar da al'amurranta yadda ya kamata? Idan ma baka sani ba you have to investigate ka kuma san hanyar gyara because wallahi alhakinta kake ɗauka wanda sai Allah ya tsayar da ku ranar gobe, making her your wife doesn't made her" "slave ina fata ka fahimta?""" "Kai ya gyaɗa a sanyaye, ya miƙe ya fito ya samu wuri ya zauna." "Ya fi awa biyu yana zaune kawai cikin rashin sanin Makama ko madafa, nan dai ya miƙe ya nufi ɗakin da take kaman ta ji Shigowar shi don bai jima da zama ba ta farka kuma da kuka ta tashi, he just stood up yaje ya ɗaga ta zaune ya ɗan rungumeta sai da ya bari tayi kukan sossai kan ya ɗago ta yana zama hannayenshi cikin nata kaman yadda idanunshi ke a cikin nata ya furta ""Ki yi haƙuri Hudah... Ki yi haƙuri don Allah""" Idanunta ta sauƙar ba tare da ta ce komai ba """Huda...""" """Just leave me alone ka ji? Ina buƙatar space""" "Tayi maganan tana zame hannunta a cikin nashi ta koma ta kwanta, Miƙewa yayi ya fita sai ya" tsinci kanshi da neman Layin Hibbah ya kirata kila za ta bukacesu a wurin fiye da shi. Hankalin Hibbah a tashe Dukda ya gayamata ba wani abu bane mai girma kuma ta ma farka haka ta fito rike da makullin mota """Momma! Mommaaa""" """Haba Hibbah menene kike kwala min kira haka kaman makauniya?""" """Momma twinee ce wai bata da lafiya she's on admission yanzu Mu'azzam ya kirani"" ""Subhallahi! Me ya sameta? Wai me yake damunta?""" """Nima ban sani ba Momma bari dai na je""" """A'a je ki ɗauko min waya in kira Babanku idan ya amince sai mu tafi tare""" "Kaman zata kifa taje ta ɗauko tun a hanya ta kirashi ko da ta iso ma yayi picking, Momma ne ta mishi bayani yace su je shima yana office amma daga chan zai biya ya duba jikin." Da sallama suka tura kofan ɗakin tana kwance jin Muryar Momma ya sa tayi saurin Miƙewa zaune Momma ta ƙarasa gangarta """Hudah! Sannu...""" "Rungume momman tayi ta fara sabon kuka, Momma na shafa bayanta har tayi shiru kan ta" ɗago ta """Menene na kuka haka Huda? Ai sai ki ƙarawa kanki ciwon sannu ya jikin?""" """Momma na yi kewarku ne sossai, Momma don Allah zan bi ku...""" """Ki ji shashanci, wa kika taɓa gani ya bar ɗakin aure ya koma gida haka siddan saboda yana" "kewar gida? Ki ka samu sauƙi dai ki kawo mana yini saboda mu ma mun yi kewarki sossai""" "Ta ɗan yi murmushi ta kalli Hibbah da idanunta suka cika da kwalla tayi mata murmushi, girgiza kai Hibbah tayi kan ta zo ta zauna ɗayan side ɗinta" """Wai me suka ce yake damunki haka twinee?"" ""Wlh ban sani ba, da shi suka yi magana""" "Duk sannu suka cigaba da mata, ta kwanta kan kafaɗar Momma tana jin kaman ta gudu daga auren ta koma gida gaban iyayenta don hankalinta ya fi kwanciya, ba kuma don bata son mijinta ba sai don gujewa matsaltsalun mahaifiyarshi da kauce wa karan zuƙa da ta sanya mata, waenda suke waje Adu'a suke su yi auren wasu kuma dake ciki da za'a ce a mayar da hannun" "agogo baya sai sun zaɓi zama gaban iyayen da auren, the life is not just balance." "Ko da Mu'azzam ya dawo ɗakin bata nuna komai ba ya zauna suka gaisa da Momma, bayan nan suka gaisa da Hibbah kan suka cigaba da taɓa hira har Daddy da Daddy Z suka shigo, Hudah ta yi murnan ganinshi don rabonta da shi an kwana biyu shima kuma yayi murnar ganinta Dukda ya ga ta sauya mishi sossai ta ɗan yi rama tace ai stress na karatu ne kawai, ledoji manya manya suka shigo dashi suka ajiye mata, chan sai ga Aunty husna saboda Daddy Z ya gaya mata ta dafo abinci ta taho dashi, tuni Mu'azzam ya tafi don jinshi yake a takure sanin za su zargi rashin ganin mahaifiyarshi a asibitin ko 'yar uwarshi tunda gida dai ɗaya suke rayuwa bare a ce basu kai ga sani ba ne tukun. Kuma ya koma gidan don ya ɗauko ko Falmata ne hajiyar ta ce babu inda za ta ai ita ce Hudar ta so gani kwance Allahnta ya ceceta reshe ya juye da mujiya, duk yadda zai mata nasiha nuna mishi take ta fishi jimawa a duniya kuma ta ɗauke shi a cikinta na wata tara ta haife ta shayar akan Hudah har ya haddace waennan" kalaman dole ya haƙura ya kyaleta. "Huda dai zata ce wannan jinya da daaɗi ya zo mata don Hibbah ta tare gangarta tana bata nishadi tuni suka ajiye Hajiya da damuwarta a gefe, 'yan uwa sai zarya suke cikin asibitin ana ganinta, abinci gasu nan koyaushe kula na shiga wani na fita daga gidan Daddy Rabi'u har gidansu da ma wurin Aunty husna, har umma da su Nihla kannen Dr. Najeeb sun zo sun duba ta wanda hakan ya ƙara kwantar wa da Momma hankali cewa Hibbah ta samu miji ta kuma yi dace, shi karan kanshi a asibitin yake raba dare tare da Hibbah wanda hakan ya ƙara musu tsananin kusanci, soyayyarsu ko a yanzu ka fara gani sai ya burgeka yadda suke daukar lamurran juna da muhimmanci. Nasir ma ya shigo sau kusan uku idan ya tashi aiki ya kan zo su" yi hira tare. Su Aunty Kubrah kam sai dai a waya. "Kwananta huɗu aka sallame ta, Hudah har kaman zata yi kuka a sadda Hibbah ta sauƙe ta a gida tare da Mumtaz da Aina'u, ji take kaman ta bi su kawai amma babu yadda ta iya haka suka tattaro duk tarukucen asibitin zuwa cikin gida, Aina'u da Hibbah suka gyare mata gidan suka yi girki Mumtaz na taya su da surutu a gefe daya yana neman tsokana suna ta dariya da nishadi" har suka gama girkin suka ci a tare. """Amma Addah Hudah za dai ki zo gida jibi bayar da twininki ko?""" "Mumtaz ya faɗa, hararshi Hibbah take yana dariya" """Dole na ai Mumtaz, na isa ban zo ba? Twinee fa guda za'a mallakawa Dr Najeeb ai da ni za'a ci a cinye in shaa Allah""" "Ita dai bata ce komai ba nan suka dasa hirar abubuwan da zasu yi idan bikin ya taso, har hibbah ta gaji ta tarkatasu suka yi waje ta dubi Hudah" """Don Allah kar ki sake saka damuwar kowa a ranki twinee, ko don lafiyarki ki daina bari maganganun hajiyar Mu'azzam yana taɓa ki tunda ba za ki iya rama wa ko daukar mataki ba...""" Kai ta gyaɗa """In shaa Allahu na gode sossai my love""" Hararanta tayi kan ta fice tana cewa sai ta ganta jibi ɗin. "Abu da rana idan aka saka nan da nan sai ka ga har ya yi, a yau ne dangin Dr. Najeeb suka" shirya tsaff don tahowa gidan Alhj Mudassir Madaki saboda nemawa ɗan su auren Hibbah. Ta ɓangaren Momma ta so ko Aunty Asiya ne ta zo amma abin bai haɗu ba dole daga ita sai matan Daddy Rabi'u da Aunty husna sai Nadiya da a yanzu take kara respecting Momma da nadamar rayuwar da tayi na baya ta kuma yi alkawarin nunawa mahaifiyarta ainihin Momma da suka yi missunderstanding saboda kishi da son zuciya Dukda mahaifiyartata a yanzu ba kula ta take ba tace in ta ga sun fara maganar arziki to ta yi baran baran da Momma ne ko kuma kar ta sake shiga mata sashe hakan bai sa ta bar wurin momman ba don ta tabbatar Allah ba zai kamata da laifi akan fushin da Hajiya kamila ke yi na marar dalili da ita ba. "Sun yi girki da snacks kala kala tare da drinks, an gyare parlorn baƙi daga Daddy har 'yan uwanshi babu wanda ya fita a ranar, Hudah tun safe ta zo Dukda bata yi wani aiki ba saboda laulayi da take fama dashi tana kwance ɗaki suna ta shan hira da Hibbah da lokaci lokaci take tsintar kanta cikin faɗuwar gaba, tana tuna a haka ranar da Mahmud ya turo gidansu don neman aurenta shekara ɗaya da watanni da suka wuce, tana tuna a haka Sagir ya turo aka nema mishi izinin zance da ita saboda shine Firstlove ɗinta kuma Momma ta ɗora su a lokacin kan ba zasu kula kowa ba sai da izinin mahaifinsu amma Sagir yayi using that against her, ya yi" poisoning mind ɗinta har ta amince da cewa neman izinin zance daidai yake da ba da aure... "Shigowar saƙo wayanta ne ya sa tayi saurin kai idanunta wurin tana dawowa daga tunanin da ta tafi, sunan Dr. Najeeb ta gani Dukda tana son yin murmushi wani abu dai ya taho ya danne mata zuciya ta janyo wayan cike da kasala ta buɗe saƙon gabanta na ta faɗuwar da ta rasa" dalili... "*Littafin nan na kuɗi ne ki biya Naira Ɗari biyar (500) kachal domin kasancewa cikin masu kwasar tarin ilimi, faɗakarwa da zazzafar soyayya mai cike da sadaukarwa da aka zube ciki. Za ki biya ta wannan asusun" 0545475847 Gt bank Fatima Muhammad Gurin Sai ki tura shaidar biya zuwa wannan layi 09039206763 Ko kuma katin MTN na Naira 500 cikin wannan layi na sama sai ki tura da shaidar biya ta same layi. Sai na ji ku* Note: Da dare ne zan dinga posting da rana zan bi in dinga karanta comments naku so please a ba ni haɗin kai mu tafi lafiya kaman yadda muka fara lafiya. Na gode sossai. Gureenjoh SAFARA A TAƁO FATIMA MUHAMMAD GURIN *GUREENJOH* *ADABI WRITERS ASSOCIATION* *PAID BOOK* *LAST FREE PAGE* """Labari mai daaɗi...Yanzu su Abba suka fice don nemo mini aurenki ina fata su dawo da labarin da zai fi kowani irin labari daaɗi a duniyata na an mallaka mini ke, a lokacin sai na fi kowa farin" "ciki""" "Numfashi ta sauƙe kaɗan idanunta na zube a kan screen ɗin, Hudah tace ""Ya dai?""" """Abban su Dr. Sun taho""" """Shine jikinki yayi sanyi haka? Chill up dear za'a yi komai a wuce wurin Ni da ma za'a yi miki irin surprise nan na daga zuwa tambaya a ɗaura da sai na fi kowa farin ciki""" Tsaki Hibba ta ja tana binta da banzan kallo ba tare da ta ce komai ba. "Tun bayan reply da tayi mishi na Allah ya kawo su lafiya ta cigaba da kwanciya idanunta a lumshe har ta ji karar buɗe gate da Shigowar motoci, tana ji Hudah na leke ta Window tana gaya mata sun iso amma bata motsa ba, ta san tana ƙaunar Dr. Najeeb har cikin ranta saboda a cikin maza samun kamar shi sai an tona, irin kulawar da yake bata, yadda yake fahimtar ta kusan fiye ma da Hudah da suka fito a tare, yadda yake fifita al'amurranta yake yi mata duk abin da ya san hankalinta zai kwanta dashi, amma ta rasa Meyasa ta kasa samun sukuni tana tuna lokacin neman aurenta da Mahmud irin zumudi da rawar kan da suka yi tayi har snacks da" aka ci a zaman ita da Huda ne suka yi amma wannan tana nan dai kwance kaman ruwa. Dafa ta Hudah tayi """Wai menene kin kasa kwantar da hankalinki Hibbah? Ko baki son shi ne?""" Murmushi tayi tace """Kin san Allah twinee? Ina kaunarshi fiye da yadda na ƙaunaci Mahmud a cikin raina a cikin zuciyata nake jinshi shiyasa nake tsoron samun tangarɗa don wallahi komai zai iya faruwa da ni""" """Meyasa kike son maganan tangarɗa ɗin nan ne? Me kike tunanin zai faru alhali ba wani mugun hali ko ɗabi'a aka shaideki da shi ba? Ƙaddarar da ta faɗa miki ma an san Allah ne ya riga ya" "tsara hakan kuma komai ya wuce to menene na ɗaga hankalin Hibbah?""" Miƙewa tayi zaune tana janyo hularta gaban Goshinta ta harde kafafu ba tare da ta ce komai ba. """Ki cigaba da ambaton Allah kila kawai nervousness ne"" Kai ta gyaɗa hannayenta duk sun haɗe da zufa." "Sama da awa guda kan suka shiga jin fitan motocin, da sauri Hudah ta miƙe taje jikin Window" sai ta saki murmushi """an gama komai twinee, bari na ƙira Mumtaz mu ji..""" "Kiran Mumtaz take tayi sai dai bai ɗaga ba, tana shirin fita ya shigo ""Ya an bayar?""" Cikin zakuwa Hudah ta jefa mishi tambayar yayinda Hibbah ke kallonshi """Ban fa sani ba korani Daddy Z yayi, kuma kin san shi idan na ƙi ma jikina ne zai gayamin" "amma da alamu an gama komai""" """Ina Momma?""" Hibbah ta tambaye shi """Yanzu dai Daddy ya ƙira ta ta tafi""" Juyawa yayi ya fice Hudah na bin bayanshi fuskarta cike da fara'a zuciyarta kal don ta san babu abin da zai hana a ba Dr. Najeeb Hibbah don ya cika yadda za'a so kowani namiji. "Ita dai Hibbah wayanta ta janyo tana leƙa media, ta san idan su Abba sun isa tabbas za ta ga kiran Najeeb ko saƙonshi na farin ciki wanda tana tunanin kila sai ta fi shi, kusan awa guda shiru Hudah ma bata dawo ba kuma bata son fita sam, kasa samun natsuwa tayi sai ta danna kiran layinshi sai dai har ya katse bai ɗaga ba, ta sake kira nan ma bai ɗaga ba haƙura tayi ta ba da mintuna kan ta sake ƙira don ta san dai baya nisa da wayanshi sai da ya kusa tsinkewa" kan ya ɗaga. """Hello!""" Ta faɗa chan ƙasa jin shiru bai yi magana ba. """Dr. Kana ji na?""" Nan ma shiru babu amsa chan ta ji ya ja numfashi da sauri ta miƙe tsaye """Dr. Kana ji na? Lafiya kam?""" "Duk ta rikice don bai saba mata hakan ba, wani zuciyar yace mata kila yana so yayi mata wasa ne" """Dr please talk to me yanzu ba lokacin wasa bane, ka san dai ba zan iya ɗaukar ko wani irin jan rai ba ko?""" Ji tayi kaman yana shirin kashewa da sauri tace """Kar ka kashe don Allah! Don Allah kar ka kashe menene? Najeeb talk to me""" "Kiris ya rage numfashinta ya bar jikinta a sadda taji ya ja numfashi irin na mai kuka ""Kuka?? Kuka fa?? Innalillahi wainna ilaihi rajiun...""" Chan ƙasa yace """Ki natsu pls...ki zauna""" """Ba zan iya natsuwa ba, ba kuma zan zauna ba har sai ka faɗa min me ya saka ka kuka? Daga ina ne matsalar? Su Abba sun ƙi amincewa da ni ne ko su Daddy sun hanaka ni ne? Don Allah ka yi magana..""" Da gaske kuka yake yi wanda ya ƙarasa hautsina natsuwarta. """Hibbah ki manta da ni a rayuwarki nima kuma zan yi ƙoƙarin mantawa da ke don ba za mu" "taɓa mallakar juna ba har abada...""" "Sossai maganan ya buga mata kai, wani abu kaman hajijiya ya ɗauketa ta tafi ƙasa a sulale" tana jin kaman kanta zai fashe don ba karamin shigarta kalaman suka yi ba """Ka...ka kuwa san me kake cewa? Taya zan fara hakan alhalin ka san zuciyata ta riga da ta saba da soyayyarka? Dr. Ka san condition ɗina wlh ka cigaba da maganar mantawa da kai a rayuwata numfashina zai iya tsayawa har abada... Menene matsalar? Ka faɗa min? Daddy ne" "ya ƙi baka aurena? Toh saboda dalilin me?""" """Ki yi haƙuri, al'amari ne da ba zai taɓa gyaruwa ba Hibbah...""" Katse shi tayi da ƙarfin gaske sautin shi na damuwa da kuka na sake hautsina mata kai a zafafe ta shiga jero mishi tambayoyi """Ka fi son mu cigaba da rayuwa a cikin ƙunci? Idan har da gaske kana so na, kamata yayi mu fuskanci matsalolinmu don mu sami maganin warakarta, ba zaka iya mantawa da ni ba Najeeb, ka manta zuƙatanmu a cikin juna suke? Ashe zaka iya wurgi da zuciyarka kenan?""" Kalaman ta karyashi suke baya kuma so ya kashe mata waya don zai sake ɗaga mata hankali "ne, sossai yake dauriya bai ƙarasa rasa kanshi ba." """Ba zai taɓa gyaruwa ba...Hibbah har abada ba zai taɓa gyaruwa ba...dole za mu yi haƙuri muna ji muna gani, ba zan iya kwatanta ciwon da kike ji a ranki ba haka nima ba zaki iya sanin abin da nake ji a raina ba but please ki daure Hibba... Kar ki ɗaga hankalinki saboda lafiyarki hibba please""" Wani irin zafafan hawaye ne suka shigo gangaro mishi kaman yadda tuni suka wanke fuskar hibbar. Cikin kuka da fitar hayyaci take furta """Ya kake kokarin magana da wacce ka san bata ji, kuma bata gani akan soyayyarka? Shin menene dalilin da zai sa mahaifina yayi watsi da farin cikina babu dalili? Ashe ma kana da ikon sake halittar wata zuciyar kenan, dole ne idan ana son in rabu da kai in kuma cire soyayyarka daga zuciyata sai an fasa ta an tatse duk wani jini dake cikinta saboda da kaunar ka jini ke" "harbawa dukkan sassan jikina. Wallahi ba zan iya ba mutuwa zan yi...""" "Wayan ya zame a hannunta zuwa ƙasa saboda jikinta dake tsananin rawa, tana ji yana kuka daga inda take sai hankalinta ya sake dugunzuma da gudu ta miƙe ta nufi parlorn sama don sauƙa tana son wani ya faɗa mata menene kan ta ƙarasa zaucewa...sai ta ci karo da Momma dake tahowa fuskarta cike da damuwa da sauri ta tare Hibban itama jikinta tayi ta rirriƙeta ""Momma! Momma wai Daddy ya hana Najeeb aurena? Meyasa? Me yayi? Momma Meyasa" "Daddy zai hana ni samun cikar farin cikina? Me yayi masa Momma talk to me please...""" Riƙeta Momma tayi """Ki natsu Hibbah please!"" ""Momma ba zan iya baaaa""" "Cikin kuka da ihu ta faɗi hakan idan ta tuna shima Najeeb na chan hankalinshi a tashe cikin damuwa da kaɗuwa sai ta ji ta ƙara birkicewa, shirin zagaye Momma take ta nufi ƙasa don tunkarar Daddy Momma ta sake riƙo ta" """Momma don Allah zan je ne in ji me yasa Daddy zai min haka? Me nayi ne nikam? Don Allah" "yayi haƙuri ya yafemin...""" """Mahaifinki ba ya cikin yanayin da za ki iya magana da shi Hibbah! Ki yi haƙuri""" "Momma ta faɗa tana janyota ta rungumeta saboda ta samar mata natsuwa don duk jikinta babu inda baya rawa, kuka ta sake fashewa da shi don bata tsammaci hakan ba tana kuma son sanin dalili" """Da gaske ne kenan Daddy ne ya hana aurena Momma? Da gaske ne ya rabani da Najeeb? Shikenan ni kuma haka za'a yi ta zuwa ana fasawa ana bari na da ciwo cikin zuciyata?" "Momm...""" "Numfashinta ke yankewa hakan yasa maganan ma daukewa hankali tashe Momma take kiran sunanta tana jijjigata amma tuni ta fara haki da kokarin janyo numfashin sai dai bata da control ɗin shi tuni ta kai ƙasa a sume, salati da ihun kiran sunanta da Momma ke yi ya fito da Hudah da ta ɓoye kanta ɗakin Momma tana kuka sossai don tana fitowa ta samu labarin wurin Aina'u, ta kasa komawa ɗakin ne saboda bata san yadda zata fuskanci 'yar uwarta ba, ashe da gaske abin da take ji a jikinta ba alkhairi bane? Ita kanta ta rasa dalilin da zai sa Daddy ya hana Najeeb auren Hibbah, halin da ta isko su ya sake ɗaga mata hankali da gudu ta zo ta kama" hibbar ta taya Momma suka yi ƙasa. "Mumtaz da Aina'u da suke zaune cikin jimami da damuwa a tare da Nadiya da ta zabga tagumi itama tana jimamin al'amarin Hibbah ganinsu yasa duk suka miƙe suka dunguma waje, Daddy Zubair ne da ya fito shima fuskarshi babu walwala ganinsu a hakan ya sa ya taho da sauri ya buɗe musu motar shi suka shiga basu tsaya ko ina ba sai asibiti tuni Daddy Rabi'u da matanshi biyu a tare da Aunty husna ma suka rufa musu baya cikin damuwa da jimamin Al'amarin da ba'a" taɓa zato ko tsammani ba. **** *BARI DAI MU DAKATA A NAN. LITTAFIN NAN YANZU MA AKA FARA TAFIYAR SHI DON DA SAURAN RINA A KABA... ME KUKE TUNANI YA SA AKA YANKE HUKUNCIN RABA NAJEEB DA HIBBA? SHIN WANI AZAL NE AKAN HIBBAH DA TAKE GANIN BATA DA SA'AR SOYAYYA A RAYUWARTA? ME ZAI FARU A GABA? WA ZAI KARYA MATA RECORD? WA KUMA ZAI FUSKANCETA YA BUƊE BAABIN DA TA RUFE KIRIB A RAYUWARTA NA SOYAYYA KO AURE? MUTANENA KU BIYO NI DON JIN YADDA ZA TA KAYA! ME ZAI FARU DA AMAL A KAUYE? SHIN HAJIYA ZA TA SO HUDAH KUWA? "*Littafin nan na kuɗi ne ki biya Naira Ɗari biyar (500) kachal domin kasancewa cikin masu kwasar tarin ilimi, faɗakarwa da zazzafar soyayya mai cike da sadaukarwa da aka zube ciki. Za ki biya ta wannan asusun" 0545475847 Gt bank Fatima Muhammad Gurin Sai ki tura shaidar biya zuwa wannan layi 09039206763 Ko kuma katin MTN na Naira 500 cikin wannan layi na sama sai ki tura da shaidar biya ta same layi. Sai na ji ku* Note: Da dare ne zan dinga posting da rana zan bi in dinga karanta comments naku so please a ba ni haɗin kai mu tafi lafiya kaman yadda muka fara lafiya. Na gode sossai. Gureenjoh 16 "Kanshi a jingine jikin katifan nashi da tunda ya zamar da wayan bai sake ko da motsi ba har lokacin wasu hawayen da bai taɓa tsammanin zai iya zubarwa ba yake zubarwa cikin zafi biyu da ya haɗe mishi, ji yake kaman kanshi zai tsage saboda girman abin da ya ji a yammacin ya shallake duk tunaninshi, sunan Allah yake ta ambata cikin neman sassaucin birkiceccen" yanayin. "Tura ƙofan ɗakin nashi aka yi, bai motsa ba don rudanin da yake ciki bai sa ya ji ma ƙarar da" "kofan yayi a sadda aka turon ba. Dafa shi yaji an yi tare da ambaton sunanshi ""Najeeb!""" "Wani kakkauran miyau ya haɗiye yana jan zuciya, Muryar kowa baya son ji ciki har Ummar tashi... Meyasa? Meyasa ta aikata mishi abin da ta aikata? Shi me yayi da ya cancanci karɓar" hukuncin laifin da bai san an yi ba? """Ka yi haƙuri Najeeb...""" "Umma ta faɗa tana zubar da hawayen da tun dawowar su Abba basu daina zuba mata ba, rayuwarta na baya take tunawa tana jin ina ma da zata iya mayar da hannun agogo baya? Ina ma tana da iko akan rayuwarta? Da bata zaɓi ƙaddarar ta ya kasance a haka ba. Da bata bari rudin soyayya ya kwasheta ta tafka kuskure da ya shafi har ɗan ta mafi soyuwa a ranta ba." """Umma ta yaya? Ta yaya hakan ya kasance? Ya kuke tunanin zan yarda da maganganunku sama-ta-ka? Me nayi da ba za ki iya sanar da ni abu mai girma haka a rayuwata ba sai yanzu da na gama sallamar da soyayyata wa Hibbah? Umma ba ni nake ji ba sai ita...bata fa da lafiya! Zuciyarta already a karye yake taya kike tunanin zata sake karbar wani namijin kuma a" "rayuwarta ba tare da fargaba ko damuwa ba?""" Kai take girgizawa ba tare da ta kalleshi ba hawayenta na ƙara gudu tace """Ka yarda da ni idan na ce maka ina jin kwatankwacin abin da kuke ji a raina nima, sam ban zata ta haka komai zai bayyana maka ba, na zaci komai ya wuce, na yi zaton na shafe baabin duk wani taɓo ko gibin da rayuwa ya darsar mini a baya ashe ba haka abin yake ba ashe da sauran rina a kaba!""" """Umma ta ya Mahaifin Hibbah ya zama Mahaifina? Ta ina?""" Ajiyar zuciya ta sauƙe tana goge hawayenta da bai daina zuba ba kuma har lokacin bata kalleshi ba don bata ƙaunar ganin mummunar yanayin da ɗan nata yake ciki ta shiga cewa. """Ka san yanayin rawuyar gidanmu, Dukda mun kasance ba masu hali ba mahaifinmu mutum ne mai zafin gaske da tsananin aƙida hakan ya sa gidanshi komai yake a tsare bisa ra'ayin da yake so ba son ran ɗa ba, ina aji biyu na secondary na haɗu da Mudassir da ya zo bautan ƙasa makarantarmu inda sabo ya shiga tsakaninmu kasancewa ta ɗaliba mai kwazo da hazaƙa, tun muna sabo har soyayya ya zo ya kullu a tsakani ko kan ya gama shekara guda cikin Daura ina jin cewa ba zan iya rayuwa ba a tare da shi ba, shima kuma yana ƙaunata sossai Dukda ya faɗa min su ma fafutuka suke da iyayensu don karatun ma da yayi under scholarship ne saboda kwazonshi kuma idan ya gama wannan bautan ƙasa bashi da takamammen aikin kamawa haka" na ji na gani na tura shi wurin mahaifina. "Tashin farko Babanmu ya ƙi amincewa a cewar shi ba zai kai ni har Kano ba tare da ya san wani kwakwarar sana'ar Mudassir ba, bautan ƙasa ba abu bane da zai rike mace shi kawai baya ma so, ya fi kaunar yayanshi suna kusa dashi idan ya juya zai gansu kuma ya ga halin da suke ciki don haka Mudassir yayi hakuri ina da manema a cikin dauran zai turo su in zabi ɗaya daga ciki yayi min aure tunda abin da nake so kenan, nan na daka tsalle na dira akan sai Mudassir tun ma bai san rigimar da nake yi ba har ya isa kunnen shi, an kai ruwa rana don har makarantar ma an hanani zuwa, nayi kuka har da ciwo kaman ba zan rayu ba amma na kasa fawwalawa Allah in bi maganar iyaye duk saboda SO wanda bashi da tabbas! shi kanshi Mudassir bai haƙura ba yayi ta zuwa ana mishi wulakanci iri iri a karshe na tubure bisa goyon bayan mamana na tafi wurin danginta a mai aduwa kawunaina suka ɗaura aurena da Mudassir""" Hawayenta ta sharce """Ban san cewa kofar wani baƙar kaddara na buɗewa rayuwata ba sai da muka baro Mai aduwa zuwa daura mahaifina ya hane ni shiga mishi gida, ya kuma yi rantsuwar babu shi babu ni har abada ya sallama wa Mudassir, ban sani ba ƙaddarar shan wahala ne, rabon samunka ne ko sharrin dake bibiye da wasu soyayyar ne amma tunda muka shigo cikin Kano na ji auren ya fice" min daga kai. "Iyayensu mutanen kirki ne, Yaya Rabi'u a lokacin shi ke ciyar da gidan kasancewarshi dan kasuwa yayinda Zubair yake ma secondary a lokacin na gomnati, idan an samu abincin safe to babu na rana dare da kyar ake ci ga jinya mahaifiyarsu na kwance Dukda ba ranga ranga ba amma suna yawon asibiti, farkon aurenmu akwai sauran kudin service nashi da ya tara ya fara business amma a je a je bukatu ga iyaye ga iyali ya zo ya karar da kuɗin tas ya shiga buga bugan inda yake bin 'yan siyasa, ban shekara biyu ba mahaifiyarsu ta rasu shima mahaifinsu da watanni takwas ya bi bayanta ba jinya ba komai sai Rabi'u ya janye ciyar da mu dama chan saboda iyayenshi ne da ya ɗauke su dole, yana dai taimakawa amma ba komai da komai ba shima kuma da nashi iyalan kwatsam muna cikin wannan hali na samu ciki kai tsaye Mudassir ya nuna baya so lokacin ba na ciki bane saboda yaushe ya gama fama da ni bare ya fama da harkar yara, ban damu ba na biye mishi muka barar har aka sanya min tsarin iyali da yayi ta sakani jinya iri iri yayinda hankalin Mudassir ya komawa siyasa bai damu da halin da nake ciki ba, ina son zuwa gida amma mahaifina ya riga ya yi min katanga da shi sai dai a waya da mahaifiyata da naga zan iya mutuwa da jinya ga jini da nake zubarwa a koyaushe na tafi aka je aka cire min ba tare da sanin Mudassir ba, watanni uku bayan nan na samu juna biyu kwatsam sai laulayi na fara a sannan har Mudassir ya samu kujerar member saboda irin kwazonshi da zafin nama, nuna min yayi ban isa ba mun yi rigima sossai akan cire wannan tsari kan muka zo kan batun zubar da ciki akan har yanzu bai shirya ba, na ja ya ja nan ya ce min sai dai in zaɓa" "ɗan ko auren...""" Shiru tayi tana tuna irin halin da ta shiga a lokacin kallonta kawai Najeeb ke yi yana sake jin gabaɗaya zuciyarshi na baƙi da ɗaci. """Ka kwatanta yadda macen da ta sadaukar da iyaye, karatu, gata, lafiya da kuma yarantarta akan namijin da a karshe ya juya mata baya zata ji cikin zuciyarta, na razana da kalamanshi sanin cewa ya san bani da inda zan je da ya wuce gidanshi tunda da shi na rufe ido zan yi rayuwa, ganin halin da na shiga ya sa ya fice ya kyaleni, na sabi mayafi na tafi gidan Yaya Rabi'u inda na kai mishi karar komai don har lokacin da yaranta ta don ma na daina makaranta tun daga auren da har a lokacin ban ƙare secondary school ba, ya ajiye mu yayiwa Mudassir faɗa sossai inda bai ce komai ba har muka dawo gida daga nan ya ɗauke min, ba zan iya wassafa maka irin zaman doya da manjan da muka dinga yi ba har sai da cikin ka ya kai watanni biyar inda na gaji, na lalace na ƙare a sannan shi kuwa kudi ya fara zama mishi sossai, har gida ya gina amma ya ƙi mayar da ni saboda bama shiri don kawai ina dauke da jininshi a jikina na kuma nace sai na haife, na nemi da ya sakeni zan tafi don na gaji, ya nuna min ga mata dayawa a gari a yanzu yana da kuɗin auro hudu in na tafi babu abin da zai same shi, zuciyata ta gama karyewa haka na haɗa kayakina ya ba ni kudin mota da takardar saki na da" kuma gargaɗin har abada kar na neme shi tunda ba zan bi ra'ayinshi ba. "Na yi kukan da ban san adadi ba na shiga tashin hankali a sadda mahaifina ya nuna ba gidanshi ba kuma ai sai dai wani gidan don shi a 'ya'yan shi ma babu mai kalan sunana ya jima da binne ta a karkashin kasa, roƙon duniya da magiya na yi bai saurareni ba na wuce wurin dangin mamana su ɗin ma ba wani karfi bane amma na zauna da su har na haihu damuwa, yawan kuka ya haddasa min hawan jinin da da na zo haihuwa kaman ba zan rayu ba don jijjiga a sannan ne nake ta roƙon a tayani neman yafiyan Babana mutuwa zan yi, ganin fa jikina ya fi" karfin mai aduwa aka kaini Katsina a sannan ne mahaifina ya zo kaina daga nan ma Kano aka "tura mu na azabtu kwarai kan na haifeka, ya riƙe ka ya yi maka Adu'a a lokacin tausayina ya fi komai yawa a ranshi, ya amince cewa rabon samun ka ne ya sa na tubure mishi a yanzu gashi na shiga cikin nadama mai yawa don Sunan Mudassir ya tumbatsa matashin dan siyasa mai kuɗi a hannu, tuni ya sake aure ma ya manta ma da ya taɓa rayuwa da ni A yawace-yawance" "jinyata mahaifina yayi hatsari Allah ya amshi abin shi hanyar Kano zai koma daura na tsani mahaifinka fiye da komai da kowa a duniya saboda a ganina shine sanadin komai, ya wargaza min rayuwa ya wargaza min farin ciki saukin ta ma ba ta yadda kuka yi kama so bana ganinka" matsayin danshi sai dai nawa. "Na koma daura bayan tsawon jinya muka cigaba da rayuwa a gidan gado karkashin mahaifiyata itama ta rasu baka wuce shekaru uku ba, Abbanku abokin yayana ne ya kan je Daura ziyara yana matukar kaunarka, tun ma bana sakewa da yadda yake kaunar naka har na fara sakewa muna hira da gaisawa kan ya nuna yana so na, na so na ƙi don tabon muddasir wallahi da shi zan mutu a rayuwata amma sai su Yaya suka hane ni, a karo na biyu ba zan iya kin bin umarnin na gaba da ni ba haka ya auroni ya dawo da ni kano ranar da na dawo na yi kuka marar adadi don ina tuna sadda na biyo son zuciyata na zaɓi Muddasir akan komai da kowa nawa a ƙarshe" na haifi da marar ido. "Abubakar na kaunarka wane shi ya haifeka Dukda bashi da arziki amma mutum ne mai zuciyar yi sannan yana da rufin asiri ya nuna min soyayya har na haifi duka Ƙannenka uku, wallahi ban san Hibbah ta alaƙanta da muddasir ba, ban san cewa zata iya zama ɗiyar shi ba, na kuma ɓoye maka komai ne saboda ina so ka cigaba da rayuwa cikin farin ciki ba tare da tuna akwai wani da yayi abandoning ɗinka a baya ba, sannan tuna komai da ya faru kaman tono wani miki" "ne mai wayar warkewa""" "A hankali yayi hugging na mahaifiyar tashi ganin har jikinta na rawa saboda kukan da take yi," lallai dole wasu su tsani So! Wasu mazan sai ka rasa menene a zuciyoyinsu su kan manta duk wani hallaci na mace da sadaukarwarta... """Na fahimceki Umma! Ki yi haƙuri na ganin laifinki da na yi ashe kema a kaddararki akwai bautawa So da kuma cin amana mai zafi, umma na fi jin Hibbah fiye da kowa tambarin Mahaifinta sai ya sa ta sake tsanan maza don za ta tabbatarwa kanta da cewa lallai namiji ƙanin ajali da ake cewa gaskiya ne..""" "Ɗagowa umma ta yi tana ɗan murmushi da bai mamaye fuskarta ba ta miƙe kawai don Allah ya gani a yanzu ko maganar hibban bata so bare mahaifinta, shima kuma Najeeb ɗin ya ji cewa har abada ba zai sake shiga huldarta ba Dukda ƙanwarshi ce kuma bata da laifin komai amma" shi bai karɓi Alhj Mudassir matsayin uba ba. **** "A chan asibiti kuwa da kyar aka ceto Hibbah, ko da ta farka ta cigaba da kukan da maganganu sai da suka yi da gaske ta natsu amma da Momma tayi mata bayanin komai saboda babu abin boyewa a yanzu gwara kawai ta sani a maimakon ta samu hujjar yi wa Najeeb sai ta sake" "samun hujja a kan maza ashe duk halinsu ɗaya ne, ashe yaudara da son zuciyar bata bar kan" "kowa ba...tana tuna umma da irin kirkinta sai taji duk lamarin mazan ya sire mata, ko da Daddy ya shigo duba ta bayan gaisuwa bata sake magana ko kallonshi ba, shi karan kanshi ya zabge a kwana ɗaya jal saboda bai taɓa tunanin ta nan Allah ya kama shi ba, babu abin da yake son sake gani a yanzu irin fuskar Najeeb, babu kuma wacce yake son yafiyarta kaman Mahaifiyar Najeeb a wannan duniya, haƙiƙa ya zalunceta amma Allah ya gani ya jima da yin nadama kuma" ya neme ta bai sameta bane ya haƙura. "Jiki a sanyaye suka tarkata suka yi gida don Hibbah ta nace a sallame ta, Mu'azzam ma ya zo ya ɗauki Hudah da tayi wani iri saboda damuwar 'yar uwarta, ko da ya tambayeta an gama" komai na Hibba ce mishi kawai tayi eh don ba za ta iya dogon jawabi ba. "A chan ɓangaren Amal kuwa sai da ta gaji da zama a wurin da kuka da komai Dukda ita kaɗai ce a tsakar gidan don duk sun share ta haka ta miƙe don fita daga gidan ta nemi yadda za ta yi ta koma gidan mahaifinta sai dai ji tayi kaman an ɗaure mata ƙafafu, wani ƙunci da damuwa ya sake ziyartar zuciyarta, Innar Qasimu da ta fito jin motsinta ta nuna mata wani ɗaki" """Ga chan ɗakin ki ki shiga ki huta kan a gama tuwo""" Ga mamakin ta kasa Musa mata tayi haka ta nufi ɗakin jiki a saɓule. "*Littafin nan na kuɗi ne ki biya Naira Ɗari biyar (500) kachal domin kasancewa cikin masu kwasar tarin ilimi, faɗakarwa da zazzafar soyayya mai cike da sadaukarwa da aka zube ciki. Za ki biya ta wannan asusun" 0545475847 Gt bank Fatima Muhammad Gurin Sai ki tura shaidar biya zuwa wannan layi 09039206763 Ko kuma katin MTN na Naira 500 cikin wannan layi na sama sai ki tura da shaidar biya ta same layi. Sai na ji ku* Gureenjoh 17 Wanka ya fito sai dai tunda ya zauna da niyyar shafa mai bai motsa ba har Momma ta shigo "ɗakin bayan ta gama kintsa komai da yayi amfani dashi na abincin dare ganinshi zaune cike da damuwa a yanayinshi, zama tayi gangarshi ta shiga cewa" """Daddyn yara tunani ko damuwa ba su ne mashalar halin da duk muke ciki ba, ya kamata ka" "ƙarfafa wa kanka ko don saboda lafiyarka kar ka manta sai da lafiya ake komai""" "Numfashi ya sauke a hankali kan ya kalleta da idanunshi da suke a rine ""Fatima Ya Hibbah?""" Itama dai cikin 'yar damuwa tace """Idan na ce maka lafiyarta ƙalau na yi ƙarya, Hibbah banda kuka da damuwa babu abin da take yi tsawon sati biyu kenan ko magana sai ya kama dole take yi shima sai da ni amma ƙannenta kam ko kallonsu bata yi, dole ta shiga wannan hali dama duba da yanayin yadda kaddararta ya faro amma komai zai wuce with time za ta manta""" """Ina tsoro Fatima, ina tsananin tsoron alhakin Aisha ne ke bibiyar yarinyata ina tsananin son neman yafiyarta amma ban san ta yaya ba, dole mijinta sai yayi min umurnin zuwa gidanshi duk kuma sadda zan ƙira kina ji yana cewa Aisha bata shirya ganina ba in yi haƙuri, office na Najeeb kuwa sun ce ma ya cika wani course wani sati zai bar ƙasar nan kuma na san duk saboda su kaurace mini ne, a nan Hibbah ta kasa lafiya da sukuni duk na rasa Makama ba dole" "na shiga halin damuwa da tunani ba Fatima.""" Ta riƙo hannunshi ɗaya """Komai zai daidaita ni na gayamaka hakan amma sai ka kara hakuri da juriya, Allah da zuciya yake amfani kuma yana sane da cewa tun ba yau ba ka yi nadamar duk abin da ya faru a baya bisa kaddara da sharrin shaidan su ma in shaa Allahu za su sauƙo ne ai kai uba ne a gareshi kuma har abada hakan ba zai chanza ba""" """hmmm""" "Shine kawai abin da ya iya cewa, saboda ya kwantar mata da hankali ya sake kaɗan don duk cikin matanshi ita ce take a tare da shi take kuma kwantar masa da hankali bisa damuwar da ya jima ciki, Hajiya kamila kam ma banda kananun habaice habaice babu abin da take, kuma yana sane da duk takaicinsu me yasa Najeeb babban danshi ya zama namiji, idan ya tuna yadda ya ga Najeeb cikakke, kamilallen namiji mai kwazo akan aikinshi sai ya ji tamkar ya lalabo shi duk inda ya shiga ta karfin tsiya ya dawo dashi kusa dashi amma bashi da wannan dama don ya riga yayi wasa da ita tun a baya, a ɓangaren Hibbah ma da yake jinta tamkar rai yana iya taya" ta jin raɗaɗi da zafin rasa namiji irin Najeeb da ta sanyawa rai... "Tana zaune daga bakin gado da karamin hijabi a kanta hannunta alqur'ani ne take karantawa, Dukda ba kuka take ba sai dai fuskarta yana nuna halin da take ciki na rashin walwala, ta rame sossai ta kuma kara haske, turo kofar ɗakin aka yi bata ɗago ba sai da ta kai aya ta ɗaga ido ta" kalli Aina'u dake tsaye bisa kanta """Ya Nasir ne ya zo yana son ganin ki""" "Tsaki tayi a fili Aina'u ta juya ta fita, idan tace bata fara jin haushin Nasir ba tayi ƙarya Dukda ba wani abu yake zuwa mata ba bayan duba lafiyarta da kuma ƙoƙarin kwantar mata da hankali tunda abin nan ya faru sai dai tuni ta tattare maza ta yi musu kuɗin goro. Ta san Najeeb ba yaudararta yayi ba sai dai cin amanar da Daddynta yayi ne Allah ya rama wa Umma a kanta hakan in ta tuna sai ta ji kunci da damuwa sun sake mamaye ruhinta, qur'anin ta rufe ta miƙe ta" fito babban parlorn ta same shi zaune yana hira da su Fadeel. """Gashi oya a je a yi wasa""" Karɓar choculates da yake basu suka yi suka fice da gudu. "Ya kalleta jin ta yi shiru ""Ƙanwata ba gaisuwa?"" Numfashi ta sauƙe a hankali tace ""Ina yini Yaya Nasir""" Girgiza kai yayi haƙiƙa yana tausayinta don dole duk wanda ya ganta ko ya ji labarinta ta bashi tausayi. """Lafiya ƙalau. Yau da albishir na zo miki mai daaɗi"" Kallonshi kawai tayi da idanunta ba tare da ta yi magana ba." """Na san burinki na karatun Engineering babu yadda kika iya ne kike yin Biotech a Skyline to kuma kaddara ta yanke karatun don idan na tuna kin ce min kina jin kin bar makarantar kenan har abada shine da na ga an fara ba da Admission Unilag na nema miki kuma Alhamdulillah kin" "samu field da kike so...""" Ya ƙarasa maganan yana zaro farin paper daga cikin Brown envelope dake kusa da shi ya miƙa mata. "Haƙiƙa cikin sati biyun nan wannan ne abu na farko da ya sa zuciyarta ya washe, wani farin ciki ya ratsa ciki, a hankali murmushi marar nauyi ya ziyarci fuskarta ta ɗago tana kallonshi ya sakar mata murmushi" """Karɓa mana kanwata naki ne! Na san za ki buƙaci karatun kwarai saboda debe kewa""" Miƙewa tayi ta je ta sa hannu ta karɓa aiko ga sunanta nan raɗau kan takardar da ke nuna samun gurbin karatun ta. """Na gode sossai Yaya Nasir""" "Tayi maganan tana kallonshi ya mata murmushi yana jin daaɗin ganin walwala a fuskarta ""Yauwa kanwata ki cigaba da wannan farin cikin komai zai wuce kin ji?""" "Kai ta gyaɗa dole ne ta bar komai ya wuce ɗin tunda damuwa ko kuka bai isa sauya cewa Ubansu ɗaya da namijin da ta gama mafarkin rayuwar aure da shi ba, kuma ta ji za ta iya yin karatun don yanzu gidan da ma garin Kano ya sire mata daga zuciya babu abin da ke bata farin ciki daga rayuwar bayan alqur'ani da ta saka a gaba. Bai matsa mata ba ya yi mata sallama ya tafi yana cewa ta shirya komai don an fara lectures idan su Momma sun amince zai musu" booking flight tare don shima next week zai koma.. "Ɗaki ta wuce hannunta rike da Admission ɗin, ba ita ta sauƙo ba sai bayan Magrib ta samu Momma a ɗakinta zaune kan sallaya Dukda ta idar da sallah tana zaune ne zaman jiran isha hannunta da chasbi tana hailala, admission ɗin ta miƙa mata a hankali kuma karon farko da ta" yi magana mai tsawo da momman tun bayan abin da ya faru ta zama kurma karfi da yaji. """Momma Yaya Nasir ne ya nemar min admission a Lagos, course kuma da nake so Engineering ina fata a wannan karo ba za ku hanani cika burina ba kila aure ba ya daga cikin kaddarata na" "nan kusa.""" Cike da wani yanayi Momma take kallonta kan ta karɓi admission ɗin ta gani ta sake mayar mata """Allah ya sanya mishi albarka, kuma bani da wani matsala da hakan don na tabbatar kika je ma gidan Adda Kubra ne masaukinki za kuma ta baki duk wani kulawa da tarbiya fiye ma da yadda ni zan baki tunda dukkanmu itace ta ɗora mu bisa turbar da muke kai. Sai dai Mahaifinki nake ji, kaman yadda kika sani bashi da ra'ayin nesantar mace da gabanshi da sunan karatu wanda tun farko dalilin da ya hana ki tafiya Lagos ɗin kenan karatu amma ba zan hanaki ba ki kai mishi da" "kanki ki mishi bayani idan ya amince falillahil hamd""" "Daga yanayinta Momma ta san bata ji daaɗin batun kaiwa mahaifinta admission ɗin ba. ""Hibbah!""" Ta kirata a sadda ta miƙe za ta fice """Na'am""" Ta amsa tana dawowa ta zauna. """Ba zan miki dole ki daina fushi da mahaifinki ba kuma ba zan wanke shi nace ya aikata daidai ba amma ki sani matsayin uba yake a gareki, jigo kuma majingina da ya haifeka, ya ciyar dake ya shayar dake bisa sahalacewar ubangiji ya kula da duk wani hakki da tarbiyarki tun daga yaranta har kawo yanzu. Ubangiji da kanshi ya ambaci iyaye da irin girmansu wuraren dayawa. Ko kin san me kalmar Uffin take nufi da Allah ya ambata a suratu Isra'i? Yana cewa ""ubangijinka ya hukunta cewa kada ku bautawa kowa sai shi, kuma ku kyautawa iyayenku. muddin dayansu ko biyunsu suna da rai, kada ku taba ce masu ""tir"" (na nuna dan alamar fushi da su), kuma kada ku yi masu kuwa; ku yi masu magana mai karimci""" Ina miki nasiha da tuni cewa ki daina wannan fushi da mahaifinki ki kuma je gareshi da kalamai "ma tausasawa don neman yardar ubangiji kina ji na?""" Hawayen da suke zuba mata ta share kan ta yi godiya ta miƙe ta fice Momma ta bi bayanta da "kallo, kai tsaye ɗaki ta koma tayi Sallar isha tayi kuka sossai bayan ta idar ta miƙe ta fito har" lokacin da hijabinta mai girma ta nufi ɓangaren mahaifinta. "Yana zaune da Hajiya Zakiya bai jima da shigowa daga sallah ba, idanunshi na zube a kan Tv yayinda take zaune ta kame gefenshi cikin kwalliyarta kaman yadda suke gasa da Momma a Kwalliyar ganin yadda koyaushe tana cikin kwalliya da kamshi kusa dashi, tunda ya dawo ta mishi sannu bai sake magana ba takaici ne fal cikin ranta amma bata tanka ba, sallamar Hibbah" "ciki ciki da Shigowarta ya sa duk suka mayar da hankali kanta, chan nesa da su ta tsuguna" """Mama barka da dare, Daddy barka da dare""" Hajiya Zakiya tana murmushin keta tace """A'a Hibba ce? Barka dai ya jikin? Sai fa haƙuri rayuwar kenan""" "Murmushi tayi wanda bai mamaye fuskarta ba bata ce komai ba, Daddy ya ce ""Ya dai Mamana kina so mu yi magana ne?""" "Kai ta gyaɗa har lokacin idanunta na a ƙasa, jin shiru na seconds yasa ya fahimci bata son yin" "maganan ne a gaban Hajiya Zakiya don haka ya ce ""Zakiya ki ɗan je daga ciki bari mu tattauna da Hibbah""" """Haba Alhj! Yanzu Hibbah nawa take da har don za ka yi magana da ita sai na baku wuri? Na ga dai 'yata ce ko kuwa?""" """Yarki ce tabbas amma tunda kika ga bata turo mahaifiyarta ba kenan da ni take son Magana" "kai tsaye don haka ki yi respecting dicision ɗinta ki ba mu wuri duk cikinsu ko waye ne ya zo yana son Magana da ni personally kema kin san ni mai bashi dama ne""" """Ba girin-girin ba dai ta yi mai... In bata yi hankali ba haka za ta tsofe gida ana nan ana baza" "baƙin hali""" Tana kunkunin hakan ta fice fuuu shi Daady kam ma ko jinta bai yi ba Hibbah da ta ji ta ta bita da kallo har ta fita kan ta mayar da kanta ƙasa """Ehen Hibbah ya dai?""" """Daddy da ma Admission ne na samu a Unilag shine nake so idan ka amince min in tafi chan in yi karatun""" Idanu ya ɗan zuba mata zuciyarshi babu daaɗi ya tabbatar ya hanata ya shiga hakkinta dayawa bayan abubuwa da suka ta faruwa don ta nemi chanjin environment da kuma natsuwa ta hanyar karatu bai kyautu a ce ya hanata ba amma kuma shi ba wannan ne ra'ayinshi kan 'ya'yanshi ba... """Online ne kika nemi admission ɗin?""" Girgiza kai ta yi """Yaya Nasir ne ya nema mini, ya san yadda nake son karatun Engineering ɗin and he thought hakan zai saka ni farin ciki shiyasa""" Shiru ya sake yi kan ya sauƙe ajiyar zuciya chan dai ya muskuta ya kira sunanta """Hibbah!""" "*Littafin nan na kuɗi ne ki biya Naira Ɗari biyar (500) kachal domin kasancewa cikin masu kwasar tarin ilimi, faɗakarwa da zazzafar soyayya mai cike da sadaukarwa da aka zube ciki. Za ki biya ta wannan asusun" 0545475847 Gt bank Fatima Muhammad Gurin Sai ki tura shaidar biya zuwa wannan layi 09039206763 Ko kuma katin MTN na Naira 500 cikin wannan layi na sama sai ki tura da shaidar biya ta same layi. Sai na ji ku* Gureenjoh 18 """Hibbah karatun zai saka ki farin ciki?""" Kai ta gyaɗa """Zan cika wani buri nawa ne ta hanyar karatun Daddy""" Murmushi yayi """Lallai kin zama ta daban Mamana duk kin karye min record kina sa ana ta ganin laifina""" Ta kalleshi karon farko yana murmushi yace """Eh mana, kin manta ke kika fara mallakar mota a gidan nan saboda kaunarki da harkar motoci da ma iya sarrafasu? Yanzu kuma gashi za ki tafi har Legos karatu hala kina so baki ya kasheni kenan""" A hankali tace """Daddy ka amince kenan?""" Kai ya gyaɗa """Ya na iya tunda uwata tana so! Zan saka miki kudi account naki sannan zan aika miki sabuwar mota gidan Adda Kubrah don Allah ki mayar da hankali akan abinda ya kai ki kin ji?""" Sanyi sanyi ne taji ya mamaye mata zuciya saɓanin raɗaɗin da yake ciki na tsawon kwanaki fuskarta bai ɓoye ba cikin murmushi tace """Na gode Daddy Allah ya kara buɗi da arziki mai amfani""" "Ya amsa ""Allahumma Ameen""" "Ta sanar da shi ranar tafiyar da Nasir yace zai musu booking tare Daddyn yace ta ce mishi ya bari zai saya mata ticket da kanshi ta san yana so tayi farin ciki ne kuma ta sake Alhamdulillah kuma ya ci nasara don da walwala ta fito, ko da ta dawo sashensu sai da ta sanar wa momma" amincewar Daddyn kan ta nufi ɗakinta ta shiga neman Hudah. """Twinee sai yau kika tuna da ni?""" """Afuwan maman twins. Yanzu dai Albishir na kira na miki"" Hudah cike da farin cikin jin samun natsuwar twineen nata tace ""Goro fari kal""" """Next week zan tafi Lagos karatu""" "Wani irin ihun murna Huda tayi kaman ta tashi ta tiki rawa ""Da gaske twinee? Kuma Engineering ɗin?""" """Kwarai da gaske mechanical Engineering""" """Alhamdulillah! Alhamdulillah kaii na miki murna twinee sai dai kam zan yi kewarki kusa da ni""" "Hira suka cigaba da yi cikin kaunar juna, Hibbah na ta bata labarin abubuwan da za ta yi don ba karamin daaɗi tashin tafiyartan yayi mata ba bayan sun gama magana ta ajiye wayar tana tuna Najeeb cikin ranta ko wani hali yake ciki? Ko ya yake jin tsanar wanda ya kawo shi duniya? Ta san dai ba zai yafe wa Daddy ba don ko ita ce bata jin zata iya manta komai ta cigaba da karbar Daddy matsayin uba don bai ba wa kanshi matsayin ba, hakika ta ji wa Umma raɗaɗin yaudara, ta ji mata ɗacin don ta san menene heartbreak, wanne ne za ta ce ya fi mata sauƙi? Rabuwa da Sagir ko tonon asirinshi? Ko kuwa fasa aurenta bayan gangami? Ko kuma Rabuwa da Najeeb?" A wurinta duk babu gwara amma ta tattaresu ta mayar gefe ta fara shirin makaranta. **** "A chan ɓangaren Amal bata san me ya shiga kanta ba, bata san ina hankalinta ba ta dai san bayan karamar waya da yake hannunta ta kan yi waya da Hajiya kamila shima da kyar kuma gaisuwa kawai take ta kashe, duk wani abu nata na kuɗi ko accesories Qasimu ya karɓe, ɗakin da suke ciki bayan katifa shima yamusashe babu abin da ke kai, tun idan ta ci abincin gidan tayi ta amai da zawo har ta zo ta saba yana dan zama ruwan kuwa ya dafar da ita a sati biyu ta zama tamkar wacce ta sabawa rayuwar wurin kuma ta kasa kawo maganar wa Hajiya kamila bare ta yi yunkurin fita, tana yi wa Inna biyayya wanda take jinshi kaman tilas daga zuciyarta amma ta kasa dainawa haka Qasimu bata iya daga ido ta kalleshi tayi mishi musu karfi da yaji" ta lalace ta ƙare. Ciwo kuwa idan ta fara amai kaman ba zai tsaya ba don malaria ya Buge ta sossai da cholera saboda rashin sabo amma haka ake mata jike-jike a bata ta sha ba zancen magani ko chemist. Ta san ba daidai rayuwarta ke tafiya ba amma ba za ta iya yin komai a kai ba. **** """Ta amince za ka iya zuwa""" Sune kalaman Mal. Abubakar bayan tsawon sati biyu da kwanaki da Daddy ke mishi magiya a kullum akan yayi haƙuri ya bashi lokacin ganin Umma don yana son roƙon yafiyarta kan Allah ya karɓi ranshi don haka ya yi farin ciki sossai kuma ya nemi da ya bashi lokaci ya kuwa bashi ɗin. "Washegari da yamma ya ɗauki Momma da Yaya Rabi'u suka tafi wurin Umma ɗin, tarba mai kyau Nihla ta musu zuwa masaukin baƙi, ta gaishe su cikin ladabi bayan sun gama gaisawa ta kawo musu ruwa da snacks kan ta fice shi dai Daddy duk ya zama wani iri guiltness yayi mishi" yawa amma kuskure kam ya san ya aikata. "Suna nan zaune sai ga Abba da Umma tana sanye da hijabi har ƙasa fuskarta babu walwala, gaisawa suka shiga yi yayinda ita kam ko kallon ɗaya daga cikinsu bata yi ba sai da Momma tace" """Maman Najeeb barka da yammaci""" Tace """Yauwa barka""" Yaya Rabi'u ma yayi mata sannu kan ta gaishe shi a hankali """Haƙiƙa Aisha sai an cuceka ne ake furta maka kalmar haƙuri, na tabbatar a cikin mu babu wanda ya isa ya ce ya dandani kwatankwacin abin da kika ɗanɗana, a sadda na samu labarin barin ki rayuwar Mudassir gashi a zaune kuma Allah ne shaida har marinshi na yi, na gaya mishi magananu marar daaɗi na kuma yi mishi izini da ya biki ya nemi yafiyarki amma ya nuna min shi ya gama da baabinki, na tabbatar mishi hakkinki ba zai taɓa barinshi ba Dukda yana ganin yana da kuɗi kuma yana da damar auro mata masu yawa, a hankali ya rasa kwanciyar hankali da matan nashi guda biyu duk inda ya zauna ya kan fadi irin biyayya da ladabinki" "gareshi, ya kan yabi kunya da kawaici irin naki a hankali damuwa ya mishi rubdugu kuma ya" "rasa haihuwar da Kamila har ma ya ƙaro aure itama bata haihu ba sai ya koma nemanki, amma" bai same ku ba an ce masu gidan sun rasu kun sayar da gidan kun raba gado. Wallahi ko da ya dawo bamu iya gane kanshi ba don a lokacin ya tabbatar da ya rasa ki har abada. "Dukda daga baya ya samu haihuwan amma bai taɓa manta halin da ya jefaki ba sanadiyar hakan zuciyarshi yayi rauni da ake tunanin ya kamu da ciwon zuciya, ya rasa kwanciyar hankali da natsuwa daga matanshi kullum ana rabon faɗa kullu yaumin rigima har sai da ya auro Fatima kin ganta nan, itama bata tsira ba don ma ba rigimamma ba ce amma biyun chan sun haɗe mata kai haƙuri da kawaicinta ya ajiye ta har yanzu. Wallahi wallahi a sadda ya sake ki da a ce kin fara nemana da ba zan taɓa bari ki tafi ba amma a ba yadda na iya na hakura gashi bisa kuskurenshi 'ya'yanshi biyu sun fada soyayya ba don Allah ya sa da yayanki da ya san Mudassir ɗin aka zo ba da Allah kaɗai ya san irin kwabar da za mu yi ko hakan ya ishe mu" "ishara""" "Kanta na kasa hawaye na diga a hannunta dake kan kafafunta, ko ɗaya ba maganar da ya ɗaɗata da ƙasa don duk bata ma ji zata iya kallon Mudassir ba bare batun yafiya, Momma ta ɗora" """Ni shaida ce Umman Najeeb wallahi ban taɓa kwana a tare da Mahaifin yaran nan ba ba tare da ya tashi cikin dare ya nemi yafiya daga rabbi ba ya kan kuma roki Allah ya bayyanaki ko don ɗauke nauyin ɗa ko 'yar da ya wofintar a tare da ke ba. Ki yi haƙuri don Allah ki bashi daman" "zama uban da ya kamata ya zama a rayuwar Najeeb""" """Har Abada Najeeb da na ne ni kaɗai, sai kuma Abbansu da ya zame masa uba kuma bai taɓa goranta masa ko wofintar da bukatunsa ba, ya tsaya mana ta yadda Najeeb bai ma san yana da wani uban ba bare yayi tunanin maraici ko ya dandani zafi da ciwon banzatar da rayuwarshi da mahaifinshi ya yi. Duk yana ina? Duk wani wahala ko wani ɗan lokaci me amfani cikin rayuwar yaron nan bai sani ba, haihuwarsa, fara wayaunsa, soma taka kafafunsa a ƙasa, karatunsa ko cimarsa sai a yanzu da ya zama mutum har da rabi shine zai dawo mana? Bama bukatarshi. Na kuma amince da ganinku don in roke ku ku fita hanyar mijina da ahalina ku daina takura masa don Allah""" Tana kai nan ta miƙe ta fice daga parlorn ba tare da ta kalli ko dayansu ba. "Girgiza kai Daddy yayi yana mayar da idanunshi da suka rine ƙasa, ta yi gaskiya ya yi abubuwa masu yawa kuma bai ga laifinta ba, a hankali ya miƙe Abba na ta basu haƙuri da tabbatar musu" za ta sassauto suka nuna ba damuwa ai tana da damar fushi daga nan suka fice jiki a saɓule. **** "Ana gobe Hibbah za ta bar Kano zuwa Lagos ta je gidan Hudah ta sameta kuwa don laulayin ciki ya hanata zuwa school, ita ta mata komai na gidan suna taɓa hira" """Yanzu kam Hajiya ta daina damun ki ko? Don kwana biyu ban ji kina zancen ta ba""" """Da sauƙi kam Mu'azzam da kanshi ya min umarnin in dinga zuwa sau biyu kawai a sati ina leƙa ta, kuma idan na je ma daga gaisuwa bana bari wani magana ya hada mu bare ta yaɓamin magana, wallahi baki ga ba yadda take mishi na rasa me zan yi ta so ni duk ta ɗora mishi laifin" "komai fa tana ganin ni ce na shanye shi, shi kuma yana nuna mata matsayin mu ba ɗaya ba ita uwa ce ni kuma matarshi ce duk Allah ya riga ya raba soyayyar a cikin zuciyarshi ba ta yadda" "zai fifitani a kanta amma ta Ki amincewa""" """Hmmm ni duk hakan bai burgeni ba twinee da raba muku muhalli ya yi da sai na fi kowa farin ciki don wannan wata rana sai ta cutar da rayuwarki wallahi ki bar wanda ya ce bai sonki. Aka" "so ka ma ya ka ƙare bare akasin hakan""" Numfashi Huda ta sauƙe """Ni kuwa tawa ƙaddarar kenan kuma wallahi mai sauƙi ne akan na wasu ke dai a dai yi sha'ani" "Twinee""" Sakin zancen suka yi suka kama wani har dare kan ta koma da kyar suka rabu. Washegari da safe ta sallami kowa wanda sai a lokacin sallamar ne su Hajiya kamila suka sani Haba ina wuta su saka Daddy. Rigima maganganu babu irin wanda basu yi ba barin ma Hajiya Zakiya da yaranta kullum burin su su je wani wurin karatu ko Abuja ne Daddy ya ƙi amma dake ita ce 'yar ido ai gashi an barta har legos karatu. Ita dai bata bi ta kan kowa ba don bata da lokacinsu Aljihunta a cike don daga Momma har Daddy kudi mai yawa suka saka mata ta shiga motar Momma da Nasir ke jiranta da Driver su Mumtaz ma da Aina'u da za su musu rakiya har Airport duk suna motar suka fice daga gidan. "Kaman wasa kaman gaske mintuna arba'in ya sauƙe su a legos a Cikin airport suka samu Aunty Kubra, Ya Abdul da Zaitoon suna jiranta cikin murnan ganinta suka ture Nasir suna yi mata maraba hakan ya faranta mata sanin tana da wuri mai kyau a gidan yapendon nata da" bata da kamarta nan suka dunguma sai Gida. Toh ga Hibbah a Legos me kuma yake jiranta? Shin karshen matsaltsalun kenan ko kuma mafarin wani matsalar kenan? Mu je zuwa.... "*Littafin nan na kuɗi ne ki biya Naira Ɗari biyar (500) kachal domin kasancewa cikin masu kwasar tarin ilimi, faɗakarwa da zazzafar soyayya mai cike da sadaukarwa da aka zube ciki. Za ki biya ta wannan asusun" 0545475847 Gt bank Fatima Muhammad Gurin Sai ki tura shaidar biya zuwa wannan layi 09039206763 Ko kuma katin MTN na Naira 500 cikin wannan layi na sama sai ki tura da shaidar biya ta same layi. Sai na ji ku* Gureenjoh 19 "Dukda ba wannan ne karonta na farkon zuwa Lagos ba, a koyaushe Lagos sabon birni yake zame mata saboda wata duniyace mai cike da tarin mutane masu mabanbanta addini da kabilu daban-daban, gari ne mai tarin hayaniya da shiru a lokaci ɗaya saboda bambancin wuraren da irin tazarar su, idanunta na zube akan shimfidadden tekun da suke tsula gudu a samanshi tun tana jin hayaniya tana kuma kallon mutane har suka shiga cikin Victoria Island, a hankali komai ya sauya fuska shiru mai tsada ya biyo baya haka akwai bambancin tituna masu tsafta da kyau, gidaje ne a shimfide tsararru a Layin da kowanne ke faɗin labarin kuɗi ba tare da ya yi magana" ba. "Horn Drivern ya ke ta zabgawa har aka wangale mishi kyakyawar mashigar ya kutsa kai ciki," Sai da ya tsaya suka sauƙa kan ya ƙarasa da motar cikin jerin motocin da suke jere a parking lot na gidan. "Zaitoon ne ke janye da akwatinta, Aunty Kubra na riƙe da hannunta yanayin shirun Hibbahn na damunta ta san da hibbar da ce ɗoki da hargagi ya isa ya sa su yi faɗa da Abdul daga ɗaukosu daga airport zuwa yanzu saboda ya kan ce ba ya son rashin natsuwarta, amma yau har shi sai" da yayi mamaki duniya mai chanza mutum. Kai tsaye sama suka yi zuwa ɗakin da aka tanadar mata Aunty Kubra tace """Oya yi wanka sai ki sauƙo mu ci abinci ko don duk nan jiranku muke kan mu yi lunch""" "Murmushi ta ɗan yi ""Na gode Aunty""" Bata ce komai ba ta juya ta fice Hibbah ta nufi fararen curtains da suka zagaye ɗakin ta yaye tana kallon harabar unguwar daga inda take. "A hankali take tambayar kanta abin da ta shirya zama a wannan gari, Dukda bata da tarihi anan amma za ta gina makomarta da juriya haƙuri da kuma jajircewa, a matsayin ta na baƙuwa a yanzu ba tausayawa ta zo nema ko shelanta damuwarta ba ta zo ne don ta nemi sabuwar rayuwa." A hankali ta furta """Ya Allah kana ganin zuciyata, na shigo wannan gari da tarin burika cikin zuciyata, na zo ba da komai ba sai Fatan neman gobe mai kyau ya Allah ka dafa min a neman ilimina, ka kautar da duk wata fitina da za ta zo hanyata, ka ba ni juriya da ƙwarin gwiwar ganin karshen wannan abin da na ɗauko ba tare da karyewa ba""" "Sama take kallo tana mayar da hawayen da suka cika mata idanu kan ta sauƙar ta juya ta nufi bayi, wankan ta yi tare da alwala Dukda bata ji kiran sallah ba amma ta san ɗaya ya yi ko ya gota, tana fitowa ta buɗe akwatinta na kayan shafa ta yi shafan da za ta yi duka kan ta nemi Abaya marar nauyi ta saka ta saka hijab ta yi sallah kan ta zare hijabin ta ɗaura dankwalin rigan" ta fito ta nufi ƙasa. "A dining area ta same su nan ta jona su, Zaitoon na zuba mata abincin ta yi godiya ta janyo ta fara ci a hankali." """Motarki fa ya iso Hibbah sai dai ba zan so ki fara fita da shi ba da yanayin tukin legos har sai" "kin ƙware kin kuma san wurare""" Aunty Kubra ta yi maganan. """Aunty ai a ko ina ma zan iya tuki fa...""" Ta faɗa a ɗan karye Nasir ya ce """In dai harkar mota ne an bar miki kayanki"" Suka yi dariya a tare." Abdul ya ce """Dukda haka dai dole za'a dinga fita da ke kafin ki saba don kika ɓace bamu san me za mu cewa Daddynki ba""" Ta kalleshi with puppy face ya ɗan zare ido """Dama school din hanya na ne zan dinga dropping ɗinki kafin kwana biyu, karfe nawa za ki fara fita gobe?""" Still Abdul ɗin ne ke maganan. """Da safe kawai Ya Abdul, Ya Nasir cewa ya yi duk wani wahalana ni zan yi""" Suka yi dariyar yadda ta yi maganan Nasir yace """Ai na gama miki me wahalan yanzu duk sauran na ki ne sai shi shirya don wannan kashe jikin wallahi bai ganki ba a Engineering""" """Aunty Ya Nasir ya raina kwakwalwata tun a jirgi sai maimaita sai na dage da Engineering yake""" Zaitoon tace """Tabb ai shi zaman aji kawai zai nuna miki amma basira da baiwa kam sai dai ki nuna masa, kwantar da hankalinki tunda shi ma yayi karatun kema za ki iya""" Spoon Nasir ya ɗauka zai jefa mata ta tsuguna tana dariya saboda dama sun saba wasan saƙo da saƙo da shi. Aunty tace """Nasir ka daina raina min basirar yarinya za ta baka mamaki ne with time""" "Hiransu suka cigaba da yi har suka gama cin abincin, Hibbah ke tambayar Daddy don bata ganshi ba Aunty ke cewa ba ya ma ƙasar, daga nan parlor suka koma mazan suka fice huldodinsu ita kuma ta shiga waya da Momma da ta kira ta ji ya suka sauƙa, bayan ta gama" waya da momman ta kira Hudah suka sha hirarsu kan ta kashe. "Gidan yana da yanayin shiru wanda a da ba ya mata daaɗi kasancewar ta saba da gidansu mai hayaniya da yau faɗa gobe rigima amma a yanzu sai ta ji nan ɗin ya fi mata kwanciyar hankali, ɗaki ma ta koma ta yi bacci bata tashi ba sai la'asar tayi sallah kan ta shiga kimtsa kayanta a wardrobe na ɗakin ta gama ta jere kayan shafanta kan mirror ta gama ta haɗa bag da za ta fita" dashi gobe ta adana har da kayan da zata saka. "Tana ma shirin sauka sai ga Zaitoon ta shigo a kujeran ɗakin ta zauna suka shiga hirarrakinsu don ita Zaitoon ma aiki take hira suke yi har suka gangaro matsalar dangin miji da Hudah ke fama dashi Dukda basu sanar da iyayensu ba amma tana tattauna wani abin da Yaya Zaitoon," sossai tayi dariyar labarin dukan da tayiwa su Falmata da take bata Zaitoon tace """Wallahi kin ga irin matsalar Hudah to nata nafila ne akan na Mommynmu, ta fama a dangin Daddy kuma har yanzu tana fama dasu, gani suke ita ta hanani aure har suna cewa ta ce sai na yi masters da phd kuma na samu aiki ai dole maza su dinga jin tsorona """ Hibbah tace """Muna da wannan mentalityn a jininmu wlh Yaya Zaitoon sai a yi ta cewa maza na tsoron mata masu zurfin karatu alhali fa auren nan lokacinshi ne bai yi ba, kuma ma karatu ai ba laifi bane ga mace saboda duk namiji mai tunani ya san shi ta taimaka da karatun tunda 'ya'yanta ne za su amfana""" Zaitoon ta gyara zama """Abin magana ne kawai ba ya musu kadan Hibbah, ni wlh ban so Daddy ya tattaro su daga Bauchi ya dawo da su nan ba, kin ga chan sai mun bushi iska muke zuwa amma anan sai dai kawai ki gansu kuma ba za su tafi ba'a samu matsala ba kin dai san mommy hakurinta kaɗan ne. Har Allah ya isa tayi akan sharrin da aka mata na hanani aure wai sai na yi karatu""" "Ita dai Hibbah na mamaki, mutum da gidanshi da mijinshi a hanashi kwanciyar hankali, hirarrakin ma matsaltsalun auren suka fara ba auren ake gudu ba damuwar don cikin 100% na" mata a yanzu kaso bai wuci ashirin bane za su ce suna zaman daaɗi. "Ta sake sossai kafin dare har ta cire bakuntar da ta shigo da shi, da dare ta kwanta da wuri bayan sun gama dinner saboda samu ta gama komai da wuri kar ta ajiye Ya Abdul ya fara mata masifanshin nan, ai kuwa Washegarin kan karfe takwas ta gama komai, tana karyawa ya shigo" dining area ɗin ta ɗago ido ta kalleshi """Ina kwana Ya Abdul""" """Lafiya ƙalau ya gajiyan hanya?""" "Tace ""Alhamdulillah""" """idan kin gama mu je ko?""" "Ta amsa da to tana Miƙewa ta san Aunty Kubra na bacci a yanzu, da Zaitoon da saukowarta kenan cikin shirin tafiya aiki suka gaisa tayi waje sanye take da wani Black yasmin Abaya da ya amsheta sossai ya sha ado a bayan daga gadon baya har ƙasa da wani dark pink lace sai hannayen da gefen mayafin, ta yafa shi in a stylish way, daga takalmi har jakanta dark pink ne" da sauri ta iso ta shiga gaban motar suka fice daga gidan. "Tuni yake mata a hankali akan abin da ya kawo ta, yana so ta mayar da hankali da kyau ta yi karatu idan tana da wani damuwa ko na menene ta sanar mishi, taji daaɗin kulawar da suke nunawa na 'yan uwantaka a junansu don duk haka suke daga su Asma'u yaran Aunty Asiya har su Yaya Zaitoon da su Hibbahn iyayensu mata basu taɓa nuna suna da bambanci ba a abu" ɗaya suka ɗauke su. "Babban makaranta ne mai cike da tarin ɗalibi iri daban daban, ya shiga ciki ya nausa har gaban department ɗinta ya samu wuri yayi parking suka fito a tare." "Ta zaci ma wucewa zai yi amma sai ta ga ya bi ta har ciki, daga karshe ma shi ya shige gaba yayi mata komai da komai har kudin makaranta da suka je biya Atm nashi ya cire ya bayar, sai" da ya tabbatar ta gama duk wani abu mai wahala kan ya miƙa mata takardun hannunshi. """Ki samu ki je lectures na yau idan kin gama just wait for me a inda na yi parking Ok?""" "Kai ta gyaɗa tana karɓa ""Na gode sossai Ya Abdul""" Yayi murmushi """Ga wannan ki sayi wani abu in kin ji yunwa""" Ta ɗan zaro ido """Na fa fito da Atm ya Abdul kuma da kuɗi ciki""" "Bai matsa ba yace ""Toh na tafi a kula""" "Yana kai nan ya wuce ya tafi, cike da farin ciki ta nufi inda aka ce mata suna lectures yau." "Wasa gaske karatu ya kankama mata ba kama hannun yaro, bata da stress na ɗalibai don ko cokali bata dagawa gidan Aunty kubrah, duk yayyen nata suna nuna mata kulawa da damuwa hakan ya bata natsuwar karatun da karsashi, watanta na biyu kenan cikin birnin legos kuma har yau basu barta ta ɗauki mota ba Abdul bai taɓa gajiya da kaita da ɗauko ta ba, sossai yake bata kulawan babban yaya yayinda Nasir kuwa duk assigment ko wani abu da ya shige mata duhu" idan ta dawo shi take sawa a gaba saboda field dinshi kenan. "Bata da damuwar komai a yanzu sai karatun da ta saka a gaba, idan weekend ne Ya Zaitoon kan ɗauketa su zaga gari har su bakin ruwa da sauransu dai kuma tana kara sanin birnin legos ɗin don Abdul ya ce sai ta yi wata uku a garin kan ya barta tana fita da motarta, idan ta fara waya da Hudah kaman kar su yanke musamman in video call ne Dukda tana ta aikin laulayi daga ita har Ya Zaitoon sai su sakata a gaba da tsokana." "Mahaifinta sau daya ya kirata suka gaisa ya tambayeta komai lafiya ta tabbatar mishi da hakan," daga nan bata sake kiranshi ba sai dai Momma. "A chan Kano kuwa Daddy na zaune Hajiya kamila ta shigo ""Ni dai ban gane kan Amal ba Senator""" Ya gyara zama """Me aka yi wa Amal din?""" """Kullum fa idan na kirata muryarta baya yi min yadda yake da, kaman tana cikin damuwa ne ba zata iya fada min ba don Allah ko Mujiba ne ka bari in tura mata ko zata fahimci matsalar tata""" Girgiza kai yayi """Kuna da matsala ku mata, ai lafiya shi ke sa a ji shiru, me amfanin bankade bankaden? Da girmanta ai idan tana cikin matsala za ta neme mu ki bar yarinya ta yi zaman aurenta""" Duk yadda ta kaɗa akan ya bari ita kam ta tura ya ƙi. """Ita kuma Nadiya laifin me ta miki da kike gaba da ita kina matsayin mahaifiya a wurinta?""" Tana Miƙewa tace """An riga an shanye min ita kuma duk abinda zan fada ba za ka gane ba tunda kaima a shanye kake, idan tana son sulhu da ni ai ta san inda za ta sameni amma ta sani ba zan taɓa hulda da ita ba alhalin tana hulda da kishiyata""" Ta nufi kofa tana jinshi yana ambaton sunan Allah har da furta """Ya rabbi ka gyara zuciyar bayin nan naka. Me mata suka dauki kishi ne kam?""." **** "Kwance take rigib cikin zazzabi dake kassara sassan jikinta, bata san me ke damunta ba amma ita yanzu burin ta shine ta ga likita ko za ta samu sassauci, gashi kwana uku kenan bata sanya Qasimu a ido ba wani sa'in sai dai ta ji muryarshi kan ta fita ya yi tafiyar shi, yanzu ma fakonshi" take jin motsi da maganar shi yasa ta miƙe ta nufi waje don ta roke shi ya kaita asibiti. """Yanzu kam burinmu ya kusa cika, ciki ne da ita"" Innar ta faɗa da fara'a a fuskarta" "Tuni ya washe hakora ""Da gaske Inna?"" ""Kwarai ma kuwa""" """Kaiii amma na ji daaɗi ni Qasimu na kusa zama millionier, jinina kawai zan jira ya iso mu kamalla aikin nan Allah dai ya kaimu wata taran nan. Yanzu kam ki kula da ita Inna kar ta mana asara murna ya koma ciki""" "Sossai gabanta ya yanke ya faɗi, a gigice ta nufi komawa ciki sai tayi tumbul da tukunya ta tafi" ta faɗi tana tsaka ihu.... "*Littafin nan na kuɗi ne ki biya Naira Ɗari biyar (500) kachal domin kasancewa cikin masu kwasar tarin ilimi, faɗakarwa da zazzafar soyayya mai cike da sadaukarwa da aka zube ciki. Za ki biya ta wannan asusun" 0545475847 Gt bank Fatima Muhammad Gurin Sai ki tura shaidar biya zuwa wannan layi 09039206763 Ko kuma katin MTN na Naira 500 cikin wannan layi na sama sai ki tura da shaidar biya ta same layi. Sai na ji ku* Gureenjoh 20 Da wani irin hanzari suka bayyano sai dai mummunan faɗuwa ta yi ga tsoro da ya cika mata zuciya kaman ka ce mata kyat ta ɓace haka take makyarkyata ko jinin dake bi mata jiki bata gani ba sai da Qasimu yayi ihu """Jinin nawa kika zubar? Kin san me kika janyo min kuwa? Ke mahaukaciyar ina ce da kina" "tafiya bakya kallon inda kike jefa ƙafa?""" Inna da ta tsura mata idanu tace """Bai zuba ba Qasimu sai dai muka yi sake tana gab da lalata komai, dole a sake saka mata ido"" Zuwa yayi ya ɗaga ta tsaye yana kare mata kallo sai rawa jikinta ke yi amma ta kasa ambaton sunan Allah ma, bayangida ya kaita kan innar ta bi su da ruwa da kanshi ya wanketa yana ta mitar rashin natsuwarta da dabbancinta kaman yadda yake faɗa, ita dai idan za'a ce ta mutu ta dawo to tabbas za ta yarda don bata san ma wani hali take ciki ba, kalamansu sun mata girma." "Su waye su? Me suke so da ita? Meyasa suke so ta haihu? Tambayoyin da bata san wa zai amsa mata ba take jerowa kanta, cikin ladabin dole take bin maganan shi har ya mayar da ita ɗaki yaje ya kawo mata abinci mai kyau wanda ta tabbatar duk saboda cikin ne yake mata hakan, amma me za su yi da cikin? Tsoro bai barta ba haka tayi ta tura abincin ba tare da ta san ma kalar taste ɗin shi ba karshe ta fashe da kuka tana furta" """Na shiga uku ni Amal! Ina na kawo kaina? Ina kwaɗayi ya dibeni na zo? Wayyoo Allah wayyooo Hajiyata...""" Sossai take rera kukan da bata san ranar tsayuwan hawayen ba. **** "Ta ɓangaren Huda za ta iya cewa a yanzu tana cikin natsuwa don bata bari maganganun Mama da ma basu cika haduwa ba yana damunta, ta matukar so Mu'azzam ya yi aure amma yayanta ya ja mata tunga akan cewa muddin bai yi niyyar aure ba ba zata mishi dole ba, suna cikin haka" dai ya samu wani course da yake nema a Malysia inda zai wuce. "Hudah Dukda ta mishi murna amma hankalinta ba a kwance yake ba da nesanta dashi ba barin ma yanzu da hankalinshi ke a kanta yana bata dukkan kulawa, bata so ba amma ba yadda ta iya haka ya shirya komai ya tafi inda ya bar mata gidan da komai a hannunta matsayinta na matarshi ko da Hajiya ta tabbatar da abin da yayi Haba sai ta tada ɓalli ai idan Mu'azzam ya tafi sai abin da Huda ta ga dama zata musu. Ita ta haifar mata yaron ne da za'a ce komai nashi ya" zauna hannun huda sai dai su a tsammusu. "Rigima sossai har Hudah ta roki da ya tattari komai ya kai mata nan ya nuna ba zai yiwu ba," Dukda a ƙasan ranta ta ji daaɗin darajar da ya bata sai dai ta daure ta ce """Uwa fa uwa ce Habeebi, babu irin abin da za mu yi musu mu biya su akan wasu kyalr-kyale ba zan bari ka tafi tana wannan fushin ba""" """Toh ya kike so a yi Habeebti?""" Ta Yi murmushi """yauwa ko kai fa, ka tattari komai ka kai mata""" Girgiza kai yayi """Zan bata wasu kudaden sannan zan musu sayayyar nasu daban ki bar na wurinki"" ""Amma kuma za ka takura kai fa matafiyi ne kuma kana bukatar kudi a yanzu""" Girgiza kai yayi """Hakan shine kawai solution""" Kai ta gyaɗa tana murmushi ya ɗan yi hugging ɗinta """Na gode matar kwarai! Ki ƙara haƙuri da Mama please wata rana komai zai wuce""" Kai ta gyaɗa. Yadda ya ce haka yayi amma nan ma Falmata tace wa Hajiya ai abin da ya kaiwa Hibbah ya ninka nasu na su biyu tana zaune a parlor da cikinta da ya fito sossai hajiyar ta shigo """Sannu isassa, sannu shafaffa wato yadda nake jin labarin hatsabibancin mahaifiyarki shine" "aikinku ya biyo ta kaina da na yarona?""" """Subhallah! Allah ya tsare mu daga sharrin shaidan""" """Ni kike kira shaidaniya? Rashin kunyar ya kai in haifi ɗa ki aure kuma ki mallake in zo ina magana ki ce min shaidaniya?""" Girgiza kai Hudah ta yi """Ban isa in zageki ba Mama ko babu komai mun zama ɗaya saboda jininki ne ke yawo jikin ɗan cikina! Ki yi haƙuri amma daga ni har mahaifiyata ba ma Fatan ranar da Allah zai nuna mana za mu bi wani shagalalle bayanshi... Ban san me na yi miki ba amma don Allah ki yi haƙuri""" "Numfashi ta ja tana karewa parlorn kallo kan ta nufi kitchen, duk abin da zata iya ta haɗa a wani basket ta ɗauka ta fice Hudah bata ce mata tak ba, kuma ko da ya dawo bata ce mishi komai ba don a ranar da dare jirgin shi zai ɗaga ta mishi rakiya har Airport da drivern Daddy da ta roka ya zo ya kaita bata son dawowa motar haya airport ne zata sha wahala ga babban ciki, rungumeta yayi" """Zan yi kewarki maman baby""" """Zan yi fiye da kewarka Daddyn Baby, ka kula min da kanka Allah ya tsare ya ba da abin da aka je nema""" Ya amsa da Ameen kan ya juya ya shige ita ma ta juyo gida cike da kewanshi tun bai bar ƙasar "ba, barin ma in ta tuna azumin da za'a shiga baya nan ko ya zai yi da abinci sai Allah." **** "Ta ɓangaren Hibbah karatunta take hankali kwance, inda ta ji daaɗi Lagos ba kaman Kano bane babu ruwan kowa da kowa kuma babu ma wanda ya santa don ta shige ne cikin kabilu bare bayanta ya dawo yayi hunting ɗinta, ba zata ce kai tsaye ta manta da zafafan jarrabawowinta ba don ba abu bane mai mantuwa haka ba za ta ce ta manta da zuciyarta dake karairaye ba amma ta runtse ta cigaba da jajircewa don ko da First semester result ɗinta ya fita ma da First class ta fara a GP ɗinta straight A's saboda focusing da tayi atleast tana son ko bata samu aure ba kaman sauran mates ɗinta ta samu karatu ingantacce, kuma sossai su Ya" Nasir suka taka rawa a rayuwarta bisa wannan bigire. Suna shirye shiryen exams na second semester ana shirye shiryen azumi haka ta dukufa don samun karatun kan ibada ya zo ya hanata duk sai ta zabge kwana biyu don ko abinci bata mai da hankali a kai. "Kaman kullum yau ta sauƙo ne da misalin karfe takwas, Mummy na bacci Ya Zaitoon kuwa ta fita ma tun seven tana da important abu da za tayi a office ɗin da sassafen, sauri take itama don ta so makara sanin irin holdup na legos sai ta kai nine ma bata shiga school ba kuma 9:30" ajinta. """Ya Nasir Good morning..""" "Ta faɗa da ɗan sauri tana shirin wucewa ya ce ""Hibbah! Ba Za ki sa komai a cikinki ba za ki fita?"" ""Ya Nasir sauri nake wlh na yi letti""" Miƙewa yayi yana cewa """Waitt ko ruwan zafi ne ko tafi dashi""" Vacuum flask ɗin shi ya janyo ya haɗa mata tea mai kauri a ciki ya miƙa mata tayi murmushi "tana cewa ""Thank you""" Kan ta fice daga parlorn. Motarta ta shiga ta fice daga gidan sai dai dab za ta shiga Layin makarantar ta su motar ta ya tsaya a tsakiyar titi.. """ Innalillahi wainna ilaihi rajiun""" "Ta faɗa saura kiris ta saki kwalla ganin tayi ta kokarin kunnawa amma motar ta ƙi, fitowa ta yi wasu sai Horn suke mata saboda kan corner ne duk ta rasa yadda zata yi ba, ta buɗe bonnet ɗin tana kokarin dubawa based on experience da take da shi akan motoci sai dai matsalar" "kaman babba ne ta fahimta, Goshi ta dafe cikin rashin Makama." """Sharrin ƙarfe ko?""" Ta ji an faɗa daga gefenta ɗan waigowa ta yi sai ta ga wani matashi ne sanye da kananun kaya hannayenshi zube a aljihu yana kallon motar. "Bata yi magana ba don wani irin miskilanci ta koya idan ba na gida ba mutanen waje ko fara'arta bata cika bari su kalla ba, bata ce komai ba har sai da ya kalleta" """Baki ce komai ba! Na ga kuma kaman sauri kike...""" "Kai ta gyaɗa ""Ina da lectures""" """Ki ɗauki abin da za ki ɗauka ciki muje in kai ki makarantar sai in ƙira mechanic""" Kallon kai kuma a wa ta mishi wanda hakan ya saka shi dariya mai faɗi da har tana iya hangar fararen hakwaranshi. """Am just helping a sis out here ba da wata Manufar ba, kuma ba zan sace ki ko in sace miki" "mota ba, nima bakano ne ɗan uwanki don kin min kama da su ne ma ya sa na tsaya in taimakeki""" "Yana kai nan ya fiddo katin shi ya miƙa mata, bata da wani option ta karɓa don ko ta ce ta kira" Ya Abdul ma kan ya zo wani aikin ne kuma har ga Allah ta rasa lectures ɗin akwai matsala. """ENGR. USAIB MUHAMMAD INUWA""" "Sunan da ta gani kenan da Layin waya kala biyu, idan har da gaske shi dan Kano ne kuma sunanshi akwai Muhammad Inuwa za ta iya cewa ta san family ɗinsu ma kai tsaye harkar conatruction daɗadɗe sana'a ne cikin familyn don duk wani gini ko min girma ko kankantarsa muddin na gomnati su suke karbar kwangilarsa Dukda an ce yaran gidan basa ji kuma sakakku ne da suke ganin kuɗi shine komai amma wannan ɗin sai ta ga ya zama daban da abinda ake" "cewa, numfashi ta sauƙe dama ai ba koyaushe zantukan mutane ke zama gaskiya ba." "Motar ta buɗe ta ɗauki handbag ɗinta da tea flask ɗinta sai sunglasses da ta mayar idanunta ya zauna mata chass ta rufe motar ya tafi ya buɗe mata nashi da ya kasance prado ta shiga hannu ya miƙa akan ta bashi key ɗinta, girgiza kai ta yi" """Da ka barshi zan kira yayyena sai su turo a ɗauka kawai"" ""No please ki bar ni in cikita ladana""" "Ganin sai bata lokaci suke ya sa ta bashi ya zagaye ya zo ya shiga ya ja motar da speed, babu wanda yayi magana a cikinsu har ya kaita cikin makarantar ya kaita har gaban department" ɗinsu da mamaki ta kalleshi """Ya aka yi ka san department ɗina?""" Idanunta ya kalla yana murmushi """Yanzu fa na ganki gaban mota kina ƙoƙarin gyarawa, wace macen ce za tayi hakan idan ba" "makaranciyar fannin ba? Kuma ma gashi a saman takardarki""" "Ya kai idanunshi kan hardcopy na wani assigment da tayi wanda ke riƙe hannunta, numfashi ta ɗan sauƙe" """Thank you""" Ta faɗa kan ta buɗe murfin motar za ta fita """Ki ji! Ko Sunanki baki faɗa min ba idan na dawo da motar wa zan ce? Kuma ta ya zan ganki?""" """Hibbah""" Ta faɗa kan ta miƙa mishi wayanta ya sanya number ɗin shi ya ƙira sai da ya shiga ya miƙa "mata, ta sake cewa ""Thanks""" Ta fice da sauri. "Da idanu ya bi ta har ta ɓace kan ya saki murmushi, motar ya ja ya fice yana kiran makanikinshi ya mishi bayanin motar da zai je ya ɗauka da inda ya bar key ɗin a jikin motar, yana wayan ma ya zo ya wuce motar anan inda take yayi inda za shi." Tana fitowa daga lectures ɗinta na karshe yana ƙiranta kaman ya yi timing picking ta yi """Usaib""" Ya ɗan yi shiru kan ya ce """Ina inda na sauƙe ki sameni pls""" "Bai jira ta sake magana ba ya katse kiran, ta nufi wurin tana tafiya a gajiye don tun bayan tea da ta sha bata sake cin komai ba gashi ana neman biyu da rabi ne a lokacin, tana isowa ya sa hannu ta ciki ya buɗe mata motar, shiga ta yi ba kuma don komai ba sai don su yi magana ɗin" waje rana yayi yawa kuma kila shi baya son fita bare su nemi wani Inuwa su yi maganar. """Sannu da lectures Hibbah"" ""Na gode! Motar fa?""" """Ai motar nan taki babban matsala ne ta samu gyaran zai iya kaiwa gobe""" """Don ma goben weekend, bari na wuce gida sai ka ba ni Layin mechanic ɗin sai in ba Ya Abdul ya karɓo idan ya kammala""" Ya ɗan yi shiru har sai da ta ɗaga ido ta kalleshi kan yayi wani abu da idanu yace """mu je in kai ki gidan, goben ma kuma in shaa Allah da kaina zan kai miki motar har cikin gida don ba za ki hanani samun ladarki ba""" "Idanu ta ɗan lumshe a gajiye don dama tana tunanin yadda za ta hau motar haya da bata taɓa hawa ba tunda ta zo garin, kirkin Usaib kuma ya burgeta don ba kowa ne zai iya taimakon mace akan titi ba tare da ya santa ba, ya mugun taimakonta a yau and she must be grateful don lecturer ɗin safe test yayi kuma over 20 ya kuma ce ba zai sake wani ba sauran marks na C.A" ɗin zai yi deducting daga Attendance. Babu musu ta faɗa mishi inda zai kai ta. "Ya ja motar suka bar makarantar, shiru ne ya ratsa motar chan ya miƙa hannu ya kunna waƙa," ta buɗe idanu ta kalleshi sai ya miƙa hannu ya kashe yana furta """Sorry! Ban san bayan rashin son Magana ma har hayaniya kika tsana ba! Shirun ya yi miki??"" Cike da mamaki take kallonshi ba tare da ta ce komai ba...." "*Littafin nan na kuɗi ne ki biya Naira Ɗari biyar (500) kachal domin kasancewa cikin masu kwasar tarin ilimi, faɗakarwa da zazzafar soyayya mai cike da sadaukarwa da aka zube ciki. Za ki biya ta wannan asusun" 0545475847 Gt bank Fatima Muhammad Gurin Sai ki tura shaidar biya zuwa wannan layi 09039206763 Ko kuma katin MTN na Naira 500 cikin wannan layi na sama sai ki tura da shaidar biya ta same layi. Sai na ji ku* Gureenjoh 21 """Meyasa kake yin kaman ka sanni?""" Ta jefa mishi tambayar yana murmushi idanunshi a kan titi yace """Haba Hajiya Hibba, ai kallo ɗaya kawai ya ishi mutum karantar hallayarki...kuma kin san menene?""" Bata ce komai ba bayan idanu da ta kawar ya kalleta """Wallahi ba ƙaramin kyau murmushi zai miki ba, kin san Sunna ne ko?""" "Ta kalleshi yana sakin murmushin ""Haka Allah ya yi ni""" """Ko kuma haka kika mayar da kanki dai...ba zan ce na san menene matsalar ba amma duk wanda ya iya karantar mutum da kallo ɗaya zai san ba yadda kike a yanzu kike da ba. Am sorry idan na cika surutu ko shiga hurumin da babu ruwana""" "Bata ce komai ba sai zuciyarta da ya sosu, Meyasa wannan ke gani har hanji? Duk wani dariya ko fara'a da zata yi ko da kuwa da 'yan gida ne ita ta san akan fuska ne kawai don da ciwo a" zuciyarta amma wannan na ƙoƙarin karantota kai tsaye daga haɗuwa. Chan ya ji ta ce """Human relations sai ya fi maka kyau da Civil Engineering""" Dariya yayi """Har kin ɗagoni ke ma? Mutane kan ce ni maye ne ta fannin karantarsu abokaina ma Eagle eyes suke kirana wai ina gani har hanji amma duk ba haka bane, ina tunanin wannan instict ne na ɗan Adam da idan zai mayar da hankali kan mutane zai fahimci matsaltsalun dake kwance ƙasan kowani murmushinsu""" "Daga nan suka fara hira akan irin issues da muke da su na yawaitar masu tafiya da damuwa amma suka iya dannewa suka shanye har nuna mata yake duk wani damuwa ko matsala da bawa zai shiga kaman tsani ne da zai bashi damar wata rayuwar, sai ta ga ai nata matsaltsalun za su iya zame mata alkhairi don gashi sanadiyar hakan ta nufi cimma burin rayuwarta wanda a da babu irin roƙo, kuka da majiya da bata yi wa Daddy ba amma fir ya ƙi idan ba don ƙaddarar" ba ai da yanzu tana chan gidan Mahmud matsayin matar aure. "Usaib ya bi duk hanyar da zai bi har ta sake dashi Dukda ma ba chan ba sakewar, wani sa'in sai suna magana sai ta yi shiru tana ɗauke kai har suka isa gidan da kwatancenta, yayi Horn ana buɗe ya kutsa ciki bayan ya yi parking ya dube ta yana sauke numfashi" """Toh na kawo ki! Saura Motarki""" "Ta yi murmushi kaɗan da ya sa ya zuba mata idanu yana sake kishingida jikin seat ɗin ""Na gode sossai...you helped me alot""" """kila i am God sent!""" "Bata fahimci maganar ba ta sake cewa ""Ba Za ka shiga ko ruwa ka sha ba?""" """No next time in shaa Allah, yanzu akwai inda za ni""" Kai ta gyaɗa kan ta fice ya bita da kallo har ta ɓace ya ja motar ya bar gidan yana murmushi. Wayanta ne ya shiga ringing dab za ta tura babban kofan parlorn ta dakata tana dagawa kan ta tura da hannu ɗaya ta kutsa kai ciki """Aina'u... Yau kuma da ni kika tuna ne? Yaushe rabon in ga call ɗinki""" Aina'u tace """Hmmm Adda kema kin fa san yadda school yake sai a hankali, na kira ne in fada miki Daddy fa ba lafiya har ya kai ga kwanciya asibiti""" "Dukda gabanta ya faɗi bata firgice ba, kujera ta samu ta zauna ""Mene? Me yake damunshi?""" """Heart issue ɗin nan ne, har yanzu ya kasa samun Najeeb kuma mahaifiyarshi ta ƙi bashi haɗin kai na haƙura ko taimaka mishi wurin shawo kan Najeeb ɗin, tunda ya tafi ya ƙi dawowa""" "Wani abu mai nauyi ta ji ya danne mata zuciya, tunawa da Najeeb kawai ya sa ta ji idanunta sun cika da kwallah, sama ta ɗaga kanta tana mayar da su" """Allah ya bashi lafiya, zan kirashi anjima""" "Tana kai nan ta yanke wayar ta duƙar da kanta tana dafe zuciyarta, Meyasa Daddy ya aikata" abinda ke hunting ɗin shi? Meyasa yawanci maza suke abu ba tare da sun da outcomes ɗin ba? "Kiran Aina'u ne ya sake shigowa Dukda yadda take jin zuciyarta na tsere haka ta ɗaga ""Menene kuma Aina'u?""" """Ai ban gama maganar ba kika kashe, wai kin kuwa san Amal ta ɓace?""" """Ban gane ta ɓace ba? Ina gidan auren nata? Ko daga chan ne ta fita ta ɓata?""" """Wlh muma bamu sani ba, watanni kenan da Hajiya Kamila ta ɗaga hankalinta akan tana kiranta sai ta ji muryarta wani iri, ta tura Mujiba gidan ya fi sau goma bata samun kowa a gidan, tun su Daddy basu damu ba har suka damu don daga baya ma an daina samunta Wanda ya" amsa sunan mahaifin Qasim ɗin an je gidan wai gidan haya ne sun tashi kuma ba'a san inda "suka koma ba, ko garin su ba wanda ya sani yanzu Hajiya Kamila kaman zata yi hauka""" Ita kanta Hibbah sai ta ji hankalinta ya tashi """Innalillahi wainna ilaihi rajiun wani irin labari ne kuma wannan marar daaɗin ji? Ta ya za ta" "ɓace shiru kawai? Ko dai sun yi tafiya ne ba'a sani ba?""" """Anya kuwa Adda Hibbah, don Allah kuna exams ki zo Dukda dai gidan babu daaɗi kam amma ki zo pls kin jima bamu gan ki ba""" "Ta sauƙe numfashi wani sati ne za su fara exams itama tana so taje ko don saboda Hudah da take kan gaɓar haihuwa cikin kowani lokaci kuma tana kewan mahaifiyarta da 'yan uwanta. ""Zan zo, Allah ya sa dai Amal tana lafiya...Ubangiji ya bayyanata""" """Kar ki damu kanki fa, kila lafiyar ne ya ɓoye ta tunda ta auri mai kuɗi cikar burin ranta...""" "Tsaki Hibbah tayi duk rashin shirin su tana ƙaunar 'yan uwanta kuma bata Fatan wani mummunan abu ya same su, duk abubuwan da Nadiya ta yi mata da ta yafe mata yanzu su kan gaisa lokaci lokaci." """Ki gaida Daddy kan in kira"" Tana kai nan ta kashe wayar." Ta miƙe kenan don haurawa ta yi watsa ruwa ta zo ta nemi abin da za ta ci sai ga Mommy na "saukowa, ta kan ce Aunty kubrah amma zama a gidan da kasancewa tare da Ya Zaitoon sai Bakinta ya kama mommyn itama." """Sannu da gida mommy"" ""yauwa Hibbah kin dawo?"" ""Eh wlh na dawo duk a gajiye""" """Nasir ya ce ko tsayawa ki karya baki yi ba, Hibbah ki daina zama fa da yunwa gudun ulcer""" Murmushi take na maganan Auntyn """Toh Mommy, ashe kuma Daddy bai ji daaɗi ba?""" Tana zama tace """Ni ma bai jiman nan ba muka yi magana da Maman naki take gayamin abu ya kai ga kwanciya, Allah ya bashi lafiya ya daidaita lamarin""" "Hibbah ta amsa da Ameen kan tace ""Bari na watsa ruwa na zo Mommy"" ""sai kin fito""" "Ta ji Auntyn na faɗa don tuni ta nufi sama, wanka tayi ta sauƙo sanye da simple boubou na" "mesh material da yayi mata kyau kasancewarshi Red, sai ta samu Ya Abdul ma ya dawo suna tare da Mommy ɗin a parlor, abinci ta je ta zubo a plate ta dawo ta zauna" """Ya Abdul sannu da dawowa""" """Yauwa ƙanwata, ya school ɗin? Na shigo ban ga Motarki ba i thought baki dawo ba.""" Tana tauna abincin a hankali tace """Hmm wlh motata ɓaci yayi a tsakiyar hanya yau na kusa missing C.A"" ""Subhallah dama yana baki matsala ne?""" Cewar Aunty Kubra """ko ɗaya wlh, sharrin karfe ne kawai""" Ta amsa da hakan """Toh yanzu yana ina motar?""" Abdul ya tambaya """Na bar shi wurin mechanic gobe za'a dawo min dashi""" Kai ya gyaɗa """Goben sai in sauƙe ki""" """yauwa na gode sossai""" Hira suka cigaba da yi har Zaitoon ta shigo itama ta haura tayi wanka ta zo ta ci abinci ta jona su. "Sai dare Hibbah ta kira Daddy ya ɗaga suka gaisa ta mishi ya jiki, cikin kulawa ya amsa yana tambayarta karatu, a yanzu ita da Daddyn ba kaman da ba shima kuma ya san ta janye mishi don duk kiran da za su yi baya wuce gaisuwa, a da kuma shine abokin hiranta ta kasa sakewa" da labarin da ta samu.. """Daddy Allah ya baka lafiya""" Ya amsa da Ameen ya rabbi kan suka yi sallama. "Hudah ta ƙira suka sha hirarsu ta 'yan uwa tana katsewa sai ga kiran Usaib, sunan ta zubawa" "ido sama da mintuna biyu don har call din ya tsinke bata daina kallon fuskar wayan ba wani call din ya sake shigowa, sai da ya kusa yankewa ta ɗaga" """Hajiya Hibbah barka da dare, Allah ya sa ban katse miki wani abu mai muhimmanci ba""" """Ka kusa dai don yanzu haka karatu zan fita... Ya gd?""" """Lafiya ƙalau, Motarki ya gama gyaruwa da safe kike son shi ko da yamma?""" Murmushi tayi don ya bata dariya ma """Duk sadda mechanic ɗin ya kawo, zai iya bayar da key ga gateman"" ""Toh ya za'a yi kuma?""" """Da me fa?""" """Da kaina zan kawo shi har gida kuma ina son ganin mamallakiyar motar don ina da abu mai muhimmanci da nake so mu tattauna in shaa Allah""" "Shiru ta yi bata ce komai ba sai kuma ta kashe wayan kawai ta kifar a wurin ta miƙe da system ɗinta a hannu ta fice zuwa karamin parlor inda suke yin tutorial da Nasir, tuni ta manta da wani Usaib ta kai musu snacks wurin, chan ma Zaitoon ta zo tayi joining ɗinsu Dukda ba hira take musu ba su karatunsu suke ita kuma tana aiki a system har sha ɗaya kan ta koma daki don" "bacci, ganin 3missed calls ɗin shi bai sa ta ɗaga ba." "Washegari ma bata kira ba, Abdul ya kaita school kuma shi ya je ya ɗauko ta..." Da dare tana zaune cikin kujera sanye da Brown doguwar riga cotton kanta cream dankwali ne dogo ta yafa shi messy hannunta wayanta tana dannawa Dukda ta ga calls na Usaib har uku bata ɗaga ba. "Mommy na saukowa gateman ɗinsu na sallama ""Ya dai Alex?""" Mommy ta tambaya. """wani ne wai yana son ganin Hajiya Hibbah"" Ya faɗa da broken english ɗin shi." "Ido ta ɗaga ta kalleshi ""Ni?""" Kai ya gyaɗa """Ka ce mishi ban sanshi ba kuma bana maraba da zuwanshi, kar ya sake zuwa inda nake"" ""Alaja shine fa wanda ya kawo ki jiya kuma ki ce baki sanshi ba?""" Za tayi magana Mommy tace """Tashi ki je, babu kyau wulaƙanta mutum""" Kaman za tayi kuka ta kalli mommy amma ganin she's serious ya sa ta miƙe babu yadda ta iya ta nufi waje tana gyara gyalenta. "Tun da ta doso shi ya zuba mata idanu, Hibbah na da wani tsarin kyau mai natsuwa da shiga ido, komai nata abin burgewa maganarta akwai daukar hankali, kallonta kan saka shi shan jinin jikinshi daga saninta shekaran jiya zuwa yau duk ta mishi kane kane cikin tunaninshi ko ina ya" motsa ita yake hangowa. """Amincin Allah ya tabbata a gareki ya ke amintacciyar Allah""" Duk masifa da faɗa da ta fito da shi sai taji wani abu na sauƙa mata a hankali tace """Assalamu Alaikum!""" Zai yi magana ta katse shi """Usaib na baka layina ne ba don ka kira ni anyhow ba, na gode sossai da taimakonka idan kana" son kudin gyarar duk zan saka maka amma don Allah kar ka sake kusantar inda nake ko ƙiran "layina""" """Hibbah!""" Ya kira sunan a hankali Dole ta ɗago ta kalleshi idanunta da suka sauya ya kurawa idanu """Baki san abin da Allah ya ɓoye a haduwar mu ba, ba zan miki dole ba amma don Allah ko ba zaki bari in zo inda kike ba ki ba ni dama muna gaisawa har ki fahimci wanene ni, ba ni da mugun nufi a kanki Hibbah illa na alkhairi""" Gabanta yaje ya miƙa mata makullin motar """Ga makullin, ki yi tunani akan abin da nace...shi wanda zai nuna maka so ko yaya yake ya fi makiyinka, kar ki manta rahama da darajar da Allah yayiwa dan adam, kuma kema kina ciki. wani ni'imarsa ne za ki juyawa baya?" "Karɓar keyn ta yi ""Na tafi!""" Ta kasa cewa komai har ya fice daga gidan ta mayar da kanta ƙasa tana zubar da hawaye. "*Littafin nan na kuɗi ne ki biya Naira Ɗari biyar (500) kachal domin kasancewa cikin masu kwasar tarin ilimi, faɗakarwa da zazzafar soyayya mai cike da sadaukarwa da aka zube ciki. Za ki biya ta wannan asusun" 0545475847 Gt bank Fatima Muhammad Gurin Sai ki tura shaidar biya zuwa wannan layi 09039206763 Ko kuma katin MTN na Naira 500 cikin wannan layi na sama sai ki tura da shaidar biya ta same layi. Sai na ji ku* Gureenjoh 22 "Ciki ta koma jikinta a sanyaye, mommy dake zaune ta kalleta ""Kin gane waye ne?""" Kai ta gyaɗa """Mechanic ne ya dawo min da motata ne""" "Tana kai nan ta wuce ta haura, mommy ta bi ta da kallo ba tare da ta sake tankawa ba." "A gado ta kwanta idanunta na kallon sama, bata jima ba bacci yayi awon gaba da ita a haka" cikin tunanuka iri iri. "Ko da ta farka da safe ta manta wani batun Usaib ta tattareshi ta ajiye gefe, ta cigaba da huldar makarantarta tana kuma shirin exams da shirin zuwa Kano for the First time tun zuwanta Lagos ɗin, wasa wasa duk ta cire Usaib daga lissafinta tunda shima an ɗauki almost 3days bai nemeta ba, kwatsam ranar tana ma department ta tsinci text message ɗin shi, ta karanta ba tare da ta yi" reply ba ta mayar da wayan jaka. "Da dare ta sake riskar wani, gaisuwa ce amma mai salon jan hankali da sanya tunani kuma bata bari ya yi tasiri ba ta sake ajiye wayar bayan ta yi waya da Momma ta tabbatar mata an sallama Daddyn, Hudah ta ƙira bayan nan suka tattauna akan jikinta" """Twinee ba za ki zo gida haka ba? Bana so labour ya tashi miki a wanchan gidan ke kadai" "anything can happen""" """Mu'azzam ne bai amince ba, ya ce sai bayan na haihu tukuna sai in je gidan so mun yi magana da momma ma take cewa za ta turo min ko da ɗaya daga cikin masu aikinta ne sai ta tayani zama before then amma ko da na faɗawa Mu'azzam ya sanar wa mahaifiyarshi bata amince ba, ta ce za ta turo min falmata mu zauna tare idan na haihun sai in je gidanmu ko me za'a yi a yi amma ba'a gidan danta ba""" "Numfashi Hibbah ta sauƙe tana girgiza kai, wallahi sun samu Hudah ce ta inda Allah ya" "taimakesu kenan, tana da kauda kai da sanyi Dukda ita kanta Hibbah na da wannan halin" amma hakurinta ya kan ƙare ba koyaushe take daukar raini ba. """Shikenan Allah ya sauƙe ki lafiya, ina labarin Amal kuwa Allah ya sa an samu wani hint don wlh" "ina cike da tunaninta, Allah kaɗai ya san me take going through""" """Kin san Daddy ba lafiya, Daddy Rabi'u dai na iya yinshi don Hajiya kamila ta ɗaga musu hankali ainun, Daddy Z shi kuwa kin san shi da kafiya ya ce babu ruwanshi a cikin lamarin don lokacin da ya nuna bai so Qasim ɗin ba babu abinda Hajiya kamilar bata ce ba don haka yanzu" "su fama.""" Girgiza kai Hibbah tayi """Lokuta dayawa mu muke sayan matsalolinmu da kuɗin mu, Allah ya kyauta ya bayyanata"" Suka sake dan taɓa hira, Shigowar falmata ya sa ta yanke wayan, har yanzu tana jin shakka Hudar don haka Hudah ta ce mata ta zo ta hau gadon su kwana tare tunda ɗakinta ne ba na" "Mu'azzam ba, tana yatsina ta zo ta haye bata ce komai ba." "Hibbah ta dukufa karatun exams ɗinta kuma sun fara successfully har suka gama bata samu wani issue ba sam, ranar da ta kamallah tana fitowa ta ga sakon Usaib na Fatan nasara a jarabawar da ta gama, bata san Meyasa take jin zuciyarta na motsawa ba, tsawon sati biyu kenan baya gajiya da dropping mata text message Dukda ba amsashi take ba, bai taɓa kira ba sai dai duk sakon da yayi mata ta kan dinga maimaita saƙon a ranta da nazarin iya kalamanshi," wani lokacin sai ta ji kaman yana kallonta ne in yayi abin. "Da tunaninshi ta dawo gida, nan ta ƙarasa shirin ta don flight na safe za ta bi zuwa Kano." """Mommy don Allah ki sa baki a lamarin Amal din nan, Daddy bai cika lafiya ba Wanda ya kamata ya tsaya a kai kuma ya ce ba ruwanshi, Daddy Z na jin nauyinki kila zai saurareki ko don mu san halin da take ciki...""" "Hibbah ta faɗa kaman za tayi kuka don Aina'u ke ce mata Hajiya kamila har hawan jini ya kamata don tashin hankali, babu uwar da zata share sama da watanni takwas bata sanya" ɗiyarta a ido ba kuma ta yanke ji daga gareta kuma a ce hankalinta ya kwanta. """Gaskiya ne Hibbah! Ko ba don Hajiya kamila ba ya kamata Zubairu yayi wani abin amma zan kira ita mamar taku mu yi magana idan ya kama ko waje ne sai a kai case ɗin Dukda na san Alhj Rabi'u ma ba zai zuba idanu ba, matsalar rashin ji kenan ko yaya sai ya haifar da ɗa marar ido""" Zaitoon tace """Amma Hibbah kina ban mamaki, duk abin da 'yan uwan nan naki suke miki idan suka shiga matsala sai kin koka a tare da su?""" """Toh Yaya Zaitoon ya zan yi? Su ɗin 'yan uwana ne ko na ƙi ko na so kuma dai duk akwai hakkokin juna da Allah ya ɗora mana, na san da su ne ba zasu taɓa damuwa ba sai dai ma su min dariya amma ni kam ba zan iya ba""" "Sun san wannan don Hibbah tana da zuciyar tausayi Dukda taurin ranta, haka bata so wani abu" "ya samu mutum ko sanadiyarta ko ba sanadiyarta ba, she's just too plain." "Hira suka cigaba da yi Ya Zaitoon na faɗa mata yadda za ta yi kewarta a gidan har su Abdul suka shigo a tare da Nasir suka yi joining ɗinsu duk tsaraba suka bata na kaiwa gida, ta ji daaɗi kuwa tayi musu godiya. Washegari da safe Nasir ya kaita har Airport bayan sun yi sallama ta" shige arrivals tana tura trolley ɗinta. "Sanye take da wani crepe material da aka yi wa dinkin da ya zauna mata, Jersey vail ne tayi wani ado da shi da ya bayyana fashion jewelries ɗinta, fuskarta so clean and fresh lips ɗinta ta yi wani lip combo mai sauki sai sheki yake, bayan ta gama komai ta yi check in ta samu wuri ta" "zauna kan jirginsu ya ƙaraso, hankalinta na kan waya ta ji an zauna gangarta." "Dukda kamshin da taji da yanayin da ya bayyana mata cewa kallonta ake hakan bai sa ta ɗaga kai ba, chan ta ji an ce" """Idan da za'a ce min daga gidan sarauta kike babu abin da zai hanani yarda! Izzarki na ƙara" "miki kyau da aji hakan kuma na burgeni matuka gaya"" ""Usaib!""" "Ta faɗa tana ɗagowa sai suka haɗa idanu ya sakar mata murmushi, fuska ta ɗan kame" """Meyasa kake bibiyata?""" Ya ɗan wara idanu """It's just a coincidence ban yi tunanin cin karo da ke a nan ba, amma kin san dai Kano nima garina ne ko?""" """Na ji! Amma ya aka yi ka san na gama exams jiya idan ba bibiyata kake ba? Meyasa duk wani motsinka na nuna alamar sanayyata a tattare da kai?""" Yadda ta yi maganan da zafi ya sa ya sassauta murya """Hibbah don Allah ki natsu! Calm down please... Allah ya riga ya ɗaura min kaunarki tun daga sadda na ɗora idanuna a kan ki, sanin halin da kike ciki kuma na ɗauki hakan ne hanyar rage kewarki da nake ji tunda ba kulani kike ba. Ban san me ya faru dake ba a baya amma ki yarda da ni wallahi ina kaunarki fiye da yadda zan furta miki... Ki ba ni dama zan tabbatar miki da" "hakan Hibbah na roke ki""" "Yadda yake magiyar kaman his life depends on that ya sake karyar mata da zuciya, bata ce komai ba har aka sanar da shirin wucewarsu cikin jirgi, ko da ta miƙe kan ta ɗauki handbag ɗinta ya daukar mata suka jera a tare har cikin jirgin ga mamakinta ma seat ɗinsu a tare yake" tana daga jikin Window yana gefenta. "Ta kasa sakewa yayin da shi kuwa yake nuna mata kulawa a duk wani motsinta, har suka sauƙa Kano bai barta ba motar gidansu na jiranta sai da ya rakata har motan ya buɗe mata ta shiga kan ya tsaya daga jikin kofan" """Don Allah idan na ƙira kar ki min rowar Muryar nan taki mai kama da sarewa... Hakan kawai za" "ki min na san na samu wani matsuguni komin kankantarshi cikin rayuwarki""" "Tana kallonshi har ya rufe kofan ya tafi ta sauƙe numfashi, har ga Allah tana tsoro sossai irin sossai ɗin nan don ta san zuciyarta bashi da wani karfi a yanzu duk ya gama karyewa, sannan tana da babbar matsala da idan ta tashi so ta kan yi shi da dukkan zuciyarta ta yadda kuma idan komai ya rufe jinyar na ɗaukarta sama da watanni, har suka isa gida juya abubuwan da" suka ta faruwa tsakaninta da Usaib tayi ta yi. "Tana ganinta cikin gidansu ta sauƙa da hanzari tayi sashensu tana neman Momma, da gudu fadeel suka zo suka rungumeta har Aina'u, bayan sun gama murna ta shafa kan Mumtaz dake ta mata murmushi" """Wato ka zama saurayi shine ba za ka yi welcoming ɗina da hug ba! Ya yi kyau... Ina Mamana?""" "Duk fara'a ne cike a fuskokinsu jin momma tace ""Ga ni ta nan""" "Ya sa duk suka yi dariya Hibbah ta isa ta rungumeta ""I missed you so much Momma na!""" Ture ta tayi ta miƙe tana tura baki suna mata dariya. """Ya Hibbah duk makarantar ce ta ramar dake haka?""" "Mumtaz ya faɗa Momma dake murmushi tace ""Ta rame kam sai fari kaman faratu""" """Ka san wahalar karatun nan kuwa? Hmmm don ma Allah ya taimakeni Yaya Nasir na nan" "kuma guru ne ai da na kaɗe har ganyena""" Momma tace """Haka ake so ai! Allah ya taimaka ki je ki watsa ruwa ki zo ki ci abinci sai ki je ki gaida mutanen gidan""" Fuska ta ɗan kwaɓe amma bata ce komai ba ta nufi sama. "Bayan ta yi wanka ta shirya cikin simple gown ta mayar da gyalenta iya kanta ta fito zuwa ƙasa," "favorite ɗinta Momma ta yi coconut Rice da zobo hakan ya faranta mata kwarai, bayan ta gama" "za ta zauna Momma ta kora ta dole ta miƙe ta fice, Da sashen hajiya kamila ta fara..." "Tana zaune kan babban kujera Dukda Tv take kallo amma tunaninta ya yi nisa. ""Assalamu Alaikum warahmatullah""" Hibbah ta shigo bayan ta doka sallama. Da kyar ta amsa sallamar tana karewa Hibbah kallo ko da ta gaisheta sama sama ta amsa bata kara kulata ba har ta gaji ta miƙe ta fice. **** Tsawon kwana uku kenan da Hudahn ta cire kudi ta bata tunda duk karshen month ne yake turo "mata itama ta ba su, yau tana zaune sai ga Hajiya ta shigo." """Kudin abincinmu fa?""" Ta faɗa ko gaisuwar ta bata amsa ba. """Hajiya ai na ba falmata yau kwana uku kenan wai ta kai miki""" """Au a bayar da kaɗan kaɗan ɗin ma da kike ina miki shiru yanzu sharri za ki yi wa falmata ki lamushe kudin duka? Hudah ina fa sane da irin cin kudin Mu'azzam da kike a banza kina barinmu sake da baki! Ke kika haifa min shi ne ko yaya da sai abinda kika ga dama za ki yi da" "kuɗin shi?""" """Hajiya ki tambayi Falmata na riga na bata kudin nan don Allah""" "Tayi magana cikin ginshira da mitocin hajiyar, ta ji da nauyi da wahalar da take ji na wannan cikin ma mana!" """Lallai yayi kyau, zan kira Mu'azzam din idan shi ya daure miki gindi kike mana wulakanci akan kudin abinci zan ji""" Tana kai nan ta fice. "Bata motsa daga inda take ba har bayan mintuna talatin sai ga falmata ""Falmata ban baki kudi ki kaiwa Hajiya ba?""" """Na bata mana me aka yi?"" ""Shikenan!""" "Hudah ta faɗa kawai don bata ƙaunar dogon magana ""Ki shiga ciki ina da baƙo...""" "Falmata ta faɗa tana kallon hudahn, shiru tayi na seconds kan ta miƙe ta shige ɗaki." Sama da awa biyu kan ta fito ta samu falmatan zaune tana wasa da waya. """Falmata!""" "Ta ɗaga kai ta kalleta ""Na'am""" """Meyasa kike irin wannan soyayyar? Kin kuwa san duk namijin da ya gama lalataki a waje ba lallai ne ya iya aurenki ba? Abubuwan nan na yawa at First ban so magana ba saboda irin juya maganar ku amma ke matsayin kanwa kike a gareni kuma ke 'yar uwata ce mace wallahi ki" "yiwa kanki karatun ta natsu...""" """Me kike nufi ne Aunty Hudah?"" ""Ke kin san abinda nake nufi!""" """Don kawai ina kawo samari na nan muna hira shikenan sai ki fara yi mana fassara?""" Shiru tayi bata ce komai ba taje ta zauna """Wanda dai ya ƙi ji ba ya ƙi gani ba, idan kuma har kin ji ba za ki iya dainawa ba kar ki sake" "kawo min kowani dan iska cikin parlor idan ba haka ba...""" Tayi shiru bata ƙarasa ba. Da sauri falmata ta miƙe fuuuu tayi wurin Hajiya da kuka da komai tace Hudah ta mata sharri "wai tana tambadewa a waje saboda kawai ta kawo wanda zata aure har parlorn yayanta. Hajiya ta shiga masifa ai duk iskancin falmata ba zata zo har cikin gida ta yi ba, tattaruwa suka yi zuwa wurin hudan Hajiya ta tsefe ta tas har da ita bata haifi 'yar iska ba ta san wacece 'yar iska yan biyunta da ta kasa auruwa saboda fandarewa." "Maganganun sun yi wa Hudah zafi kwarai har bata san tana kuka ba, suka gama suka fice a tare abinsu kokarin Miƙewa take don wani irin jiri da Murdar mara ne ya kamata lokaci guda, kuma kuka take yi sossai duk yadda zata yi don ta miƙe ma ta kasa dama cikin gashinan kaman randa, ciwo kaman wasa nan ya riƙe ta da gasken gaske, wayanta na cikin ɗaki ta baro..." "Kafafunta sun ɗaure mata azaba babu inda baya ratsa ta, tun tana dauriyar ciwon tana ganin kaman zai lafa ta samu taje ta ɗauki waya ta kira gidansu a zo a kaita asibiti har ta sulale tsakiyar parlorn cikin azaba, da rarrafe ta samu ta isa ɗakin da kyar sai dai bata ga wayan ba duk inda take tunanin ta ajiye ko rudewa ne oho, tunda Momma ta haife ta bata taɓa jin azaba" irin wannan ba... """Innalillahi wainna ilaihi rajiun! Wayyo Allah...Allah ka kawo min ɗauki""" "Take ta nanatawa cikin azahar ciwon, ko sau daya bai lafa mata ba bare ta iya fitowa, tana nan cikin wannan hali falmata ta shigo ɗakin daukar kayanta da ke wurin wai ta yi zuciya tunda sharri Hudar ke mata" """Falmata taimakeni! Ina ganin nakuda nake don Allah kira min Hajiya mu tafi asibiti""" Kallon uku saura kwata ta mata """Yanzu ki gama mana rashin mutunci kuma ki zo kina 'yar murya don sharri salon ki hada mu rigima da Ya Mu'azzam ko?""" Lebenta ta datse da karfin gaske kan ta saki hawaye na silalo mata ciki azaba tace """Ki taimakeni falmata, kin san azabar nakuda kuwa?? Don Allah ki kira min Hajiya...zan mutu""" Tsallake ta falmata tayi ta fice ma daga gidan gabaɗaya ko sashen Hajiya bata kalla ba bare ta kirata ɗin. Tun Hudah na gane ma me take ciki har ta fice hayyacinta a wurin. "*Littafin nan na kuɗi ne ki biya Naira Ɗari biyar (500) kachal domin kasancewa cikin masu kwasar tarin ilimi, faɗakarwa da zazzafar soyayya mai cike da sadaukarwa da aka zube ciki. Za ki biya ta wannan asusun" 0545475847 Gt bank Fatima Muhammad Gurin Sai ki tura shaidar biya zuwa wannan layi 09039206763 Ko kuma katin MTN na Naira 500 cikin wannan layi na sama sai ki tura da shaidar biya ta same layi. Sai na ji ku* Gureenjoh 23 A natse take tuƙin Dukda hankalinta na ga hirar Aina'u da Mumtaz da suke labarin abubuwan "da suka ta faruwa a watannin da ta ɗauka bata gidan, wani ta yi dariya wani kuma ta ji ba daaɗi har suka isa gidan Umman da suka nufa." "A waje tayi parking suka nufi ciki su ukun, ita dai Hibbah ba zata ce ga abin da take ji akan Umman ba, ta san a da ta ji nauyinta da kunyarta kaman me matsayinta na sirikarta, mace ce mai son zumunci don a sadda take tare da Najeeb duk juma'a sai sun gaisa ko da ita Hibbah bata ƙira ba Umman za ta ƙira, tana son matar har ranta saboda bata yi judging ɗinta ba a kan abinda ya faru da ita a baya ba, ta so ta kuma ta kaunaceta da zuciya ɗaya amma kaddara ya sa basu da rabon zama matsayin sirikai don haka dole a yanzu ta ɗauketa uwa kuma ta nemi" alfarmarta wurin yafe wa Daddy. "Sallamarsu ya sanya Nihla fitowa daga kitchen ganin Hibbah ya matuƙar bata mamaki, a hankali ta amsa sallamar ko kan ta ce wani abu an buɗe wani kofa an fito kallon kallo suka tsaya yi da junansu, a hankali Hibbah ta zare idanunta ta mayar da kanta ƙasa tana jin wani abu da ta rasa menene yana taso mata, idanunta ta kifta tana mayar da kwallar da ya tarar mata." "Shi kuwa kauce wa yayi Umma dake biye da shi ta fito, lokacin Hibbah ta kirkiro murmushi" """Ya Najeeb ina yini?""" "Shi kadai ya san irin wahalar da ya sha na tsige Hibbah a ranshi, ya maye wanchan soyayyar da ta 'yan uwantaka don ko ba komai ita ɗin matsayin ƙanwarshi take Dukda bai amince har yau da cewa yana da wani uban bayan Abbanshi ba." """Hibbah! Ke ce? Sannu da zuwa""" Umma ta faɗa fuskarta a sake """Ku ƙarasa ku zauna mana kuna tsaye kaman baƙi? Ke Nihla kawo musu ruwa"" Cikin parlorn suka ƙarasa suka zauna suna murmushi." "Cikin ladabi suka shiga gaisheta tana amsawa har Nihla ta kawo ruwan, shi dai Najeeb bai iya" ya yi magana ba ma sai da su Mumtaz suka shiga gaishe su yana amsawa. """Umma ƙannena ne. Wannan sunanshi Mumtaz ita kuma Aina'u""" Cikin murmushi Umman tace """Masha Allah! Allah ya cigaba da raya mana su bisa kan tafarki""" Shiru ne ya ɗan ratsa kan Hibbah ta dake ta shiga magana """Umma wurinki muka zo... Umma Don Allah ba don mu ba ki daure ki yafe wa Daddy, wallahi ko a yanzu ya ga ishara...Daddy na cikin wani hali bayan buƙatar yafiyarki, umma ke uwa ce a gare mu duka kuma da ku muke koyi...umma kin san Amal yayata tunda aka damkawa mijinta ita an nemata an rasa? Duk wasu 'yan uwa da ya kawo a bikin an rasa su, bamu sani ba tana mace ko tana raye hakan ma ba wani alhakin bane yake biya umma? Ko kin san basu so auren Qasim da Amal ba amma mahaifiyarta ta nace dole aka yi? Umma ki dube ni da irin matsaltsalun da nake fuskanta wallahi duk sakayyar Allah ne Daddy ke gani a kan nashi yaran yana kuma taya mu jin zafin hakan da damuwa tunda gashi ya kasa lafiya! Umma Allah yana son mai yafiya daga cikin bayinsa ki daure ko da baki manta ba ki yafe ɗin shine kaɗai muke" "bukata kila rayuwarmu zai koma a daidai""" "Da wani irin sanyin murya ta ƙarasa maganan, tausayinta ne ya sake riƙe Umman, da sauri ta miƙe ta kama Hibbahn ganin ta zo gabanta za ta tsuguna." """Hibbah na yafe wa mahaifinku. Allah ubangiji ya yafe mana gabaɗaya kuma kar ki sa a ranki cewa laifinshi ne kuke girba, babu mai karɓar laifin wani a wurin ubangiji in shaa Allahu komai zai wuce""" Hawaye ne ke zubowa Hibbah ta rungume Umman tana cewa ta gode da ƙwarin gwiwarta gareta. Bayan ta ɗago ta share fuskarta ta kalli Najeeb """Yaya kaima don Allah ka yafe wa Daddy, tunda ya riga yayi nadama ko da ba zaka je inda yake ba, ko da ba zaka liƙa sunanshi gaban sunanka ba, ko da ba zaka bari ya sake ganinka ba don Allah ka yafe mishi alhakinka da ya ɗauka na tsawon shekaru... Allah yana son masu yafiya kuma sakayyarka na nan wurin ubangiji""" Miƙewa ya yi zai fice ta yi saurin cewa """Yaya Najeeb""" "Muryarta cikin kuka na saka shi jin tamkar ruwan ƙanƙara ne ake sauƙe mishi duka jiki, Dukda zuciyarshi dake tafasa amma kalamanta na shirin sanyayasu ya karya su bayan tarin jarumta da dakiya da ya haɗa na fuskantar ko ma menene kafin ya dawo ƙasar." """Idan Daddy ya rasu a yau za ka iya yafe wa kanka kuwa?"" Juyowa yayi ya zuba mata idanu." """Bashi da lafiya Yaya...""" "Tana kai nan ta ɗauke idanunta sai ta koma ta zauna, juyawa ya yi ya fice ba tare da ya ce komai ba." "Sun dan ɓata lokaci a gidan don har abinci sun ci kan suka yi wa Umma sallama cikin raha suka fito, tuni Hibbah ta turawa Momma sakon yafiyar umma zuwa ga Daddy ta ce ta mishi albishir." Har sun ɗauki hanyar gida Hibbah tace """Kaii bari mu je mu duba twinee yau throughout bamu yi magana ba""" Juyawa suka yi zuwa hanyar da zai sada su da gidan Hudah a waje suka yi parking duk suka sauƙa suka nufi ciki. Sallama suka yi a parlorn suka kutsa kai Mumtaz da Aina'u suka samu kujera suka zube Aina'u na cewa """Wlh bacci nake ji tsabar cikina ya cika a gidan Umma""" """ke kam ai dama ta inda kika ƙware kenan, kuma kina bacci tafiya zan yi in barki don ba zama" "na zo yi ba sai dai ki bi adaidaita...""" "Hibbah na maganan ne tana nufan hanyar kitchen kan ta fara kiran ""Twinee!! Twinee!!!""" Ganin bata kitchen ya sa ta juyo ta dawo ta nufi hanyar ɗakinta da sallama ta tura ta shiga sai taji ta yi tuntube saura kaɗan ta faɗa mata kan ta ja baya a firgice tana kallon figuren Hudah "dake kwance tamkar marar rai a ƙasa a wurin, bata san ta yi ihu ba" """Hudah!! Hudahhh!! Innalillahi wainna ilaihi rajiun Hudah???""" Ihun da take yi da karaji kiran Hudah tana jijjigata shi yayi sanadiyar shigowan Mumtaz da Aina'u suma duk hankalinsu ya tashi """Kamata Addah Hibbah mu fita mu tafi asibiti ba kuka za mu yi ba... Taimako take buƙata a" "yanzu""" Dukda ya nuna tana jinsu don tana numfashi kaɗan kaɗan sai dai tayi nisan kiwo tsabar ta jima cikin labour da ma ta haihu ne amma har lokacin azababben contraction kawai take fama da shi sai jini da wani ruwa mai ɗan kauri dake ta zuba mata. "Su ukun suka ɗagata Hibbah kuka take yi haka Aina'u Mumtaz dake shi namiji ne shi yayi dauriya, suna kaita mota Hibbah ta koma cikin gidan da gudu Mumtaz na kiranta ko ta waigo, sashen Hajiya ta nufa tana zaune parlor tana kallo sai ga Hibbah ta shigo ganin babu ciki ya sa ta san ba Hudah bace" """Lafiya za ki shigo min a fuja """ Katse ta tayi """Wallahi wallahi muddin na rasa 'yar uwarta a yau duniyar nan yayi mana kaɗan wurin shari'a, wallahi ko ɗan cikinta muka rasa sai na maka ki a kotu wani irin rashin imani ne wannan da rashin tausayi? Me ta yi muku da kuke so sai kun kasheta? Ki gaya min me ta taɓa miki da kika ɗauki karan tsana kika ɗaura mata?? Kawai don ta auri ɗanki?? Kawai don ta taya ki son naki???""" Hawaye take zubarwa har bata gani. Hajiya ta kasa gane inda maganganun suka dosa """Ke babu manya ne a gidanku? Ko rashin tarbiya za. """ """Ai Manyan ma suna suka tara wani babban bashi da maraba da ɗan goye! A koyaushe sai ku fake da shekaru kuna zaluntar mutum ku ce yayi shiru saboda kawai kun girma..! Ki rubuta ki ajiye wallahi Allah idan har wani abu ya samu Hudah wallahi sai kin biya..""" "Ta juya kawai ta fice, hajiyar ta miƙe ta biyo bayanta don yadda yarinyar ke zazzaro mata idanu" tana rantsuwa ya kaɗa ta. Tana zuwa gate a kan Hudah dake lifeless kwance bayan mota ta soma sauƙe idanu gabanta "ne yayi wani irin faɗuwa, Mumtaz tuni ya karɓe key ɗin daga hannun Hibbah ya shiga mazaunin driver sun bar wurin." """Na shiga uku ni Tani!!""" "Ta faɗa hannayenta duk biyu a kanta ""Me ya sameta??""" "Da sauri ta koma ciki a rikice tana kwala kiran Falmata sai dai har ɗakin Hudah ta shiga babu falmata, taka tsantsin jini da tayi ya ja ta zame tayi mummunan faɗuwa tana tsala ihu kugunta na amsawa, Dukda irin azabar da taji idanu tayi saurin kaiwa inda taji ruwa ya zamar da ita sai" ta ci karo da jini da kaman ruwan mahaifa bata san ta rushe da kuka ba. """Na shiga uku! Innalillahi wainna ilaihi rajiun idan yarinyar mutane ta mutu na kaɗe har buzuna"" Sossai take kuka, da kyar ta iya Miƙewa a duƙe take takawa tana kuka, ba kuka take saboda barazanar Hibbah ba ita dai ta san wallahi Hudah ta mutu ta shiga uku! Kai duniya! Yanzu fa ta gama ci wa yarinyar nan mutunci ashe tana fama da nakuda??" """Wayyooo Allahna! Allah ka bata lafiya ya Allah kar ka ɗauki ranta da tarin alhakinta a" "wuyanmu""" **** "Dare ne amma bai kai ga tsala wa ba, kwance take cikin azabar da yayiwa duniyarta yawa turtsetsen cikinta na kallon sama, ya fi wata a yanzu bata iya baccin kirki, damuwa yayi mata yawa Dukda a yanzu tana samun cima mai kyau da kulawa ta fannin lafiya amma hankalinta ba'a kwance yake da Qasim ba, duk ta ƙare ta lalace, kukan yau daban na gobe daban, zuciyarta ya kasa natsuwa da irin zaman da take na 'yan gidan yari cikin gidan gashi a ranta ta san da abu a ƙasa, idan ba matsafi bane Alqasim ɗan yankan kai ne kuma kwaɗayinta shine ya" ja mata. "Fitsari da ya matse ta ne sossai ya sa ta miƙe da kyar ta ɗauki buta ta nufi waje, ta san Alqasim baya nan amma tana fitowa ta ga Inuwa na shigewa ɗakin Inna da a yanzu ko tari bata yi sai da" "umurninta, zuciyarta ya kasa natsuwa a haka ta nufi kofar Window ɗakin ta maƙale" """Inna uwa kin tabbatar nan da awa ashirin da huɗu zata iya haihuwa mu samu wannan jaririn?""" Inna ta yi dariya """Ni fa na faɗa maka Alqasim Komai na rayuwarka a hannuna yake hakan ya sa na san da" "ranar zuwan gudan jininka duniya! Za ka yi kuɗi kaman yadda kake so da zarar mun sadaukar da wannan jariri ga abin bauta ya ɗanɗana zaƙin soyayyar kuɗi daga uwar har uban zai biya maka buƙata da gaggawa. """ Dariya ya shiga yi tana taya shi... """Bana fata aikin nan ya samu akasi inna uwa. Ke kin san irin gwagwarmayar da nayi na samu" "tarin kuɗi musamman na je cikin birni na dinga hayan motoci da kayan sawa wani ma a awa biyu dubu ashirin haka nake hayo mota in tafi hira har ta yarda zata aureni! Hayan iyayen bogi ma aiki, babu inda ya ban wahala irin gida Allah ya sa akwai abokina dake cikin masu gadin gidan wani mai kudin gaske a legos yake da zama gidan kuma sai a yi watanni shara kawai ke kawo ma'aikatan company su yi su tafi, shi ya amince ya ba ni hayar gidan da kuɗi masu yawa har muka zauna na watanni biyu zuwa uku kema kin san ko da na dawo nan ba ni da ko sule duk ya ƙare, saboda burina da nake son cikawa kuma mun yi nisa ya sa na koma babanta ya bani kuɗi masu kauri, na haɗa duk kayan da taje da su na sayar na soke kudin aljihu kin ga ai" "duk wannan wahala da sadaukarwar da na yi ya kamata a ce na samu cikar burina """ "Da sauri Amal ta bar wurin ta shige bayi tana ambaton ""Innalillahi wainna ilaihi rajiun...""" Jikinta babu inda ba ya rawa Qasim da Inna Matsafa ne? Kenan kasa fita da tayi a gidan kafa ta suka yi? Me kalamansu ke nufi? Soyayyar da take yi wa auren mai kuɗi da son kuɗin Alqasim shi zai sa aikinsu yayi nasara idan suka kashe Jaririn da zata haifa? """kaicona! Kaicona ni Amal...""" Cikinta ta rukunkume tana jin soyayyar yaron na ratsa ta kawai ta rushe da kuka """Allah ka taimakeni! Allah ka taimaki wannan taliki naka da bai san komai ba... Allah kar ka basu nasara a kaina ya Allah""" "Kuka take yi bilhakki da gaskiya, idanunta ta kai kan ginin makewayin, sai ta juya ta koma ɗakin ta haɗa tsunmakaran kayanta tamkar mutum ne ke a kwance duk adu'ar da ta zo Bakinta yi take, a tsorace take ainun haka ta sake fitowa cikin sanɗa ta koma bayin ta taka wani dutse tana ta adu'a ta samu ta tsallake Dukda wani irin ciwon kai da ya sauƙar mata da kuncin zuciya" haka ta cigaba da Adu'a tana gudu babu waiwaye.... "*Littafin nan na kuɗi ne ki biya Naira Ɗari biyar (500) kachal domin kasancewa cikin masu kwasar tarin ilimi, faɗakarwa da zazzafar soyayya mai cike da sadaukarwa da aka zube ciki. Za ki biya ta wannan asusun" 0545475847 Gt bank Fatima Muhammad Gurin Sai ki tura shaidar biya zuwa wannan layi 09039206763 Ko kuma katin MTN na Naira 500 cikin wannan layi na sama sai ki tura da shaidar biya ta same layi. Sai na ji ku* Gureenjoh 24 Ko da su Hibbah suka isa asibitin ƙin karbar Hudah suka yi """wani irin rashin hankali ne zai sa ku ajiye mace cikin nakuda sama da awannin da basu da adidi tamkar waenda basu taɓa shiga aji ba kuma bayan komai ya lalace ku dauko ta ku kawo mana ta mutu a hannunmu a ce laifinmu ne?? To ba da mu b...""" Ihun Hibbah shi ya saka Nurse ɗin dake ta masifa ba ji ba gani shiru """Wacce iriyar macece ke da baki da imani da tausayi? Baki ganin halin da take ciki? Haka kawai da gayya za mu barta ne cikin halin nakuda?? Ko kin ga mun yi kama da marasa ilimi ne??"" Tuni faɗa ya kaure Hibbah tana masifa tana kuka don rudewa, su kuma nurses ɗin sun ce ba za su karɓeta ba tuni Aina'u ta kira momma tana kuka ta shiga bata labarin abin da ke faruwa, momman na zaune da Daddy da kuma Daddy Zubair ta mishi albishir na yafiyar umma gareshi" kuma ya yi farin ciki sossai yana ta jerawa Hibbah albarka cike da tausayinta. "Ganin yadda Momma ta firgice yasa duk suka mayar a hankali kanta ""Wani asibiti ne Aina'u??""" Tana faɗa mata ta dubi Daddy """Daddy wai Hudah ce take nakuda ta jikkata asibiti sun ki karbarta ga chan Hibbah tana ta rigima da su""" """wani asibiti?""" Daddy ya tambaya yana daukar wayanshi tuni Daddy Z ya lalubo keyn mota Momma na faɗa mishi ya shiga yin kira suna nufar waje duk su ukun. """Hibbah!!""" "Ta ji an kirata, da sauri ta juya sai ta ga Usaib... ""Lafiya kam Hibbah!""" """Sisterna ce take labour kuma wai ba za su karɓeta ba don rashin imani da sanin kan aiki"" Ganin duk sun natsu sun daina mayar mata magana ya sa ta fahimci ko ba Usaib ne babba a" wurin ba yana tare da wani babba. "Ko kan ma Usaib ya ce wani abu wanda suke tare dashi da babban mutum ne ya shiga faɗa ""Ashe baku san aikinku ba? Wannan rigimar shi ya kamata patient na chan tana azbtuwa?"" ""Sorry sir!""" "Abinda suke ta faɗa kenan kan ya shiga kiran best likitansu na ɓangaren haihuwa ɗin tuni an yi labour room da Hudah suka fara shirye shirye kan likitan ya zo, kafin ma mintuna biyu sai ga likitoci har biyu sun shigo gabaɗaya mai asibitin ma ya iso don kai tsaye Daddy ya sa aka ƙira" shi. Usaib ya riƙe hannun Hibbah dake kuka ya kaita ya zaunar kan kujera ya ɗan tsuguna gabanta yana miƙa mata hankey """Stop crying hibbah Sister za ta samu lafiya, in shaa Allahu za ta haihu lafiya ƙalau kin ji?""" Kai ta gyaɗa tana karbar hankey ɗin amma hawayenta sun kasa daina gudu. "Shigowar su Daddyn shi ne ya sa ya miƙe ya koma gefe, Daddy kai tsaye gangarta ya zo ya" zauna """Hibbah twinee za ta haihu lafiya kin ji? Kuka ko damuwa ba su zai sa ta sauƙa ba sai Adu'a just pray for her shi take buƙata""" Nan ma kai ta gyaɗa suna nan cikin damuwa likita ɗaya ya fito """Ina mai gidanta?""" """Baya ƙasar..."" Daddy Z ya amsa ""iyayenta fa?"" ""Ga mu nan""" Momma ta faɗa cikin damuwa """Za ku saka mana hannu a wannan form dole za ayi mata aiki, yara biyu ne a cikinta sun jiggata saboda sun samu UCP (umbilical cord prolapse) wato Wata gagarumar matsala ta haihuwa wadda ba ta yawan faruwa amma tana da tsanani, inda igiyar cibiya ke zamewa ta fito gaba da jariri yayin nakuda wannan dalili ka haifarwa da yaro distress har ya rasa numfashi cikakke" "wanda kan iya kawo asarar yaron shiyasa sam ba'a so mace na nakuda tayi zamanta a gida.""" Hawaye kawai Hibbah ke yi ta yiwa Hajiya Allah ya isa ya fi cikin kwando. Daddy ne ya saka hannu yana jin babu daaɗi har likitan ya juya ya koma. "An jima sossai sun ɗauki awannin kafin suka fito da yaran guda biyu da suka fi yanayi da matattu, da gudu aka yi nursery da su don za'a saka su under oxygen ne a incubator, Usaib har lokacin bai tafi ba hakan kuma ya sa ya samu wani gurbi mai girma a ranta, yana tsaye da su har likitan ya fito sai dai bai ce komai ba ya je ya nemo wani likitan suka sake dawowa suka" wuce su. "An fi awa guda kan suka fito jikinsu duk a sanyaye ""Me ya faru Dr.?""" Mumtaz ne yayi tambayar hankalinshi na ƙarasa tashi. """Ku kwantar da hankalinku babu abin da ya sameta ko yaran sai dai suna cikin critical condition da suke bukatar adu'o'inku. Mun samu gama aiki successfully amma ta samu matsalar Haemorrhage (Zubar Jini Mai" Tsanani) "Wahalar nakuda mai tsawo ya sa mahaifarta ta gaji ta kasa matsewa yadda ya kamata, wanda ya haifar da zubar jini bayan haihuwan amma mun shawo kan komai sai Fatan ta farka lafiya""" Bayan sun wuce Daddy ya dubi Momma """Meyasa aka bar yarinyar nan ita kaɗai a sadda kuka san haihuwa ya karato mata? Wani irin sakaci ne wannan Fatima?""" """Wallahi ban san cewa ita kaɗai ba ce, Na tura jummala ta zauna da ita sai kuma ta dawor da ita, da na kirata tace min ai Mahaifiyar mijinta tace ƙanwarshi ta zauna da ita kuma itama a gidan take za su iya kula da ita, ban kawo komai ba wallahi""" Ta faɗa cike da hawayen tausayin Huda. Hibbah tace """Daddy wallahi babu inda Hudah za ta koma matuƙar da Mahaifiyar Mu'azzam zata cigaba da zama! Allah sai dai a haƙura da auren""" Daddy Z yace """Ban gane ba! Matsayinki na wa?""" Cikin kuka ta shiga cewa """Idan dai har duk muna ƙaunarta da lafiyarta kuma ba za ku amince ba, Daddy Z wallahi Hudah ta jure abubuwa dayawa daga uwar mijinta, sun zalunceta sossai zagi, kazafi, cin mutunci babu wanda basa mata har da sharri iri iri tana haƙura tana zama amma batun kassara lafiyarta kam sam ba zan iya zuba ido ta cigaba da shan wahala ba don su basu san zuru ba""" Hawayenta ta share """Daddy ka san cewa har cikin ɗakin baccinta suke zuwa su mata cin kashi? A koyaushe na yunkura don sanar da ku a daukar mata mataki sai ta ƙi tana ganin idan tayi haƙuri komai zai wuce, mahaifiyar mijinta ce ta hana a daukar mata 'yar aiki tsawon zamanta gidan ga karatu, ga aikin gida, ga ciki. Ita ta hana mai kula da ita zama wai ba dai a gidan danta ba kuma su sun kasa zama da ita su kula da lafiyarta, har yaushe za mu zuba ido bamu dauki mataki ba? Har" "sai ranar da muka je muka sameta gawa??""" "Daddy ya riƙo hannunta tare da kwantar da kanta kan kafaɗarshi tayi shiru tana kuka a hankali don abin nan yayi mata zafi ta tsorata ainun, shiyasa take jin maza kaman basu da amfani a rayuwarta don duk laifin Mu'azzam din ne ba na uwarshi ba ranta kuna yake tana ayyana" wahalar da Hudah ta sha gashi basu da tabbacin samun lafiyarta ko na yaran da ta haifa. "Duk su uku sun kadu da jin bayanan Hibbah, sossai suka shiga mamaki Momma na Ayyana irin zurfin ciki da hakurin Huda sai taji duk hankalinta ya sake tashi tana ganin har da sakacinta da" bata matsawa hudahn tana mata bin kwakwafi tana sanin me ke faruwa a rayuwar aurenta. Tuni Daddy Z ya gama yanke hukunci a ranshi kuma ya zaunu babu mai sauya shi don duk ya ji "ya kara ƙaunar Hudah da tausaya mata, samun mace mai hakurinta ma sai an tona." "Daddy Rabi'u ma ya shigo, sai dai duk basu yi maganan komai ba har dai aka tabbatar komai stable su Daddyn suka tafi suka bar Aunty husna da Hibbah don har Momma Daddy yace su koma gida zasu dawo ne idan ta farka kuma ma likitan ya tabbatar ba zata farka yanzu ba saboda anaestasia da aka yi mata mai karfi ne, karin jini har biyu ne a hannunta ta kowani" hannu shiga yake wanda a blood bank aka saya. "Sai a lokacin Usaib ya dawo gangarta yana miƙa mata ruwan sanyi, sai da ta kalleshi kan ta" "karɓa bata buɗe ba bare ta sha tace a hankali ""Ashe baka tafi ba?""" """Ta ya zan iya tafiya na barki cikin wannan hali Hibbah?""" "Ta kalleshi ya mata murmushi, ɗauke kai tayi ta buɗe ruwan ta shiga sha a hankali yana cigaba da kallonta." """Meyasa kowani aure idan ka kalla da yanayin matsalarshi? Meyasa abu da ake tunani an yi shi" "ne don a samu farin ciki da natsuwa ta har abada yake zama Tragedy wa rayuka dayawa?""" """Da Aure da rayuwa duk abu ɗaya ne hibbah, ba ta yadda za'a yi rayuwa ya tafi smoothly babu tangarda dole za'a samu matsala kuma a komai ba kowa ne zai soka ba tunda kin ga mafi soyuwan rai ma a wurin mahalaccin da yayi mu gabaɗaya ba kowa ne ke taya ubangiji" "kaunarshi ba wato Manzon mu annabi Muhammad (SAW). Hibbah aure shi ibada ne""" "Numfashi ta sauƙe ba wai ta gama gamsuwa ba, bata sake cewa komai ba chan tace" """Me ya haɗa Civil Engineer da asibiti?""" Ya fahimci me take nufi ya ɗan murmusa """Na zo wurin uncle ɗina ne, ƙanin mamana shi ke kula da asibitin so na kawo mishi saƙo ne" "muna fitowa kuma sai muka ci karo"" Kai ta gyaɗa." Ya ƙara ɓata lokaci wurin bata kulawa kan ya tafi. """Hibbah a ina kika samo wannan kuma da ya mace gabaɗaya a kanki? Kin ga yadda yake kallonki kaman zai maida ki ciki ya kare ki daga duk wata damuwar duniya?""" Ta kalli Aunty husna tace """Aunty ni har yanzu hankalina bai kwanta da shi ba Dukda yayi min abu guda ba zan taɓa mantawa ba, ya taimakeni a sadda nake bukatar hakan don ban san me zai iya faruwa da Hudah kan Daddy ya zo ba hakan ya sa ya samu wuri mai faɗi cikin raina amma ina tsoro Aunty""" Riƙo hannunta Aunty husna tayi """Haba Hibbah! Me nake gani kaman har kin karaya da soyayyar? Duk fa waenda kika ga kin rabu dasu ɗin nan ba su ne Allah ya rubuta za su zama mahadin rayuwarki ba, Usaib na kaunarki ki bashi dama please... Baki ga har twineenki ta zama uwa ba?""" """Uhmm""" Tace a hankali bata sake magana ba amma deep down ta ji zata iya ba Usaib dama a rayuwarta. "Hudah har dare bata farka ba, kuma Hibbah bata koma gida ba tana tare da ita sau huɗu tana" ganin call na Mu'azzam amma bata ɗaga ba. "Ta ɓangarenshi yayi ta neman Hudah bai sameta ba kuma ya san bata jimawa bata hau online ba saboda su yi magana ya duba lafiyarta amma ganin an ja tsawon lokaci ya sa hankalinshi ya fara tashi, ya kira cousin brother dinshi akan ya je gidan ya duba mishi lafiyarsu." Ko da ya isa gidan ya samu falmata na fama da Hajiya su je asibiti a duba mata kugun da ta kasa Miƙewa da kyau ta ƙi duk ta firgice damuwarta kar a ce Hudah ta mutu ta shiga uku. """Hajiya lafiya kuwa? Ina Hudah ɗin? Mu'azzam ne ya turo ni ya ce yana ta nemanku ba ya" "samu""" """Hudah na asibiti tana nakuda""" "Ta faɗa don a yanzu bata da abin boyewa kuma kwabarta ya riga yayi ruwa. ""Subhallahi! Wani asibiti ne?""" "Kuka kawai ta saka tana cewa ita bata sani ba, Mu'azzam ya kira ya faɗa mishi abin da ke faruwa duk ya rasa natsuwa ya shiga kiran Hibbah bata ɗaga ba, ya kira Daddy ma amma bai" "ɗaga ba, ya kira Daddy Rabi'u yana ɗauka ya ce mishi" """Mu'azzam ni na baka auren Hudah ko?""" Zuciyarshi na rawa ya amsa da eh """Toh ina so a yanzu ka ba ni takardar sakinta, za ka iya furta min yanzu ko kuma ka turo min a" "saƙo auren ya isa haka""" Yana kai nan ya yanke wayan don shi karan kanshi mai hakurin cikinsu ma ranshi ya mugun baci da abinda su Hajiya suka yi da ya zo da karar kwana sai dai kan gawar Hudah za'a kira su. Hauka ne ya saura Mu'azzam be yi ba ya shiga ƙiran Kawunshi yana dagawa ya shiga kora mishi abin da ke faruwa yace shi duk ya ruɗe bai san me ya faru ba Meyasa iyayen Hudah kai tsaye za su ce ya saketa? Kawun ya ƙira Daddy kai tsaye shima kuma sakin ya nema don yace yana son 'yar shi bai gaji "da ita ba, da kyar dai ya faɗa mishi duk abin da ya faru shima ya kira Mu'azzam ya faɗa mishi bai san ya fara zubar da hawaye ba." Daddy na katse waya da Kawun Mu'azzam sai ga Hajiya kamila """Amma Senator ni ce bola? 'Ya'yana sun fi juji banzatarwa? Ka duba yadda kake ta tada jijiyoyin wuya a kan Hudah da rashin lafiya ne! Amal ta ɓace wata da watanni kana zaune hankalinka kwance babu abin da kake na yunkurin dawo da ita... Hakan daidai ne a wurinka? Me nayi da na chanchanci wannan azababben hukuncin daga gareka? Meyasa ni da ka aureni a fari kake wulaƙantani son ranka?" Da kuka da ihu take maganan.... "*Littafin nan na kuɗi ne ki biya Naira Ɗari biyar (500) kachal domin kasancewa cikin masu kwasar tarin ilimi, faɗakarwa da zazzafar soyayya mai cike da sadaukarwa da aka zube ciki. Za ki biya ta wannan asusun" 0545475847 Gt bank Fatima Muhammad Gurin Sai ki tura shaidar biya zuwa wannan layi 09039206763 Ko kuma katin MTN na Naira 500 cikin wannan layi na sama sai ki tura da shaidar biya ta same layi. Sai na ji ku* Gureenjoh 25 Sossai ran Daddy ya ɓaci jin abin da take yi mishi bisa kai ya ɗaga ido ya kalleta """Ba dole a kullum ƙimarki ya dinga raguwa ba! Yanzu ke ya miki daidai ki tsaya bisa kaina haka kina min ihu? Kin fi ni son 'Ya'yana ne Kamilah ko komai zan yi sai a kan idanunki? Shirun da na yi miki ba wai don daaɗin rai bane sai don kawai ya zamana dai kin samu kwanciyar hankali amma tunda hawan jini kike so to sai ki samu wuri ki zauna in yi miki bayanin""" "Ko ɗarrr bata ji ba ta wuce fuuuu ta zauna idanunta kaman za su faɗi a kanshi, ai dole ya nemi" abin kare kanshi tunda ta kamashi dumu dumu yana fifita 'ya'yan Fatima a kan nata. """Kin san cewa iyayen bogi yaron nan ya kawo mana aka ɗaura musu aure? Ko kina da masaniyar cewa ko asalin sunanshi basu sani ba kawai acting suka yi ya biya su yanzu haka suna hannu amma ba za su iya ma ba da wani haske a kanshi ba? Ko kin san cewa gidan da yaje ya ajiye ɗiyar taki da kike bugun kirjin ya fi na ubanta kyau ba nashi bane shima haya ya karɓa na watanni asalin gidan na wani mai kuɗi ne yana zama legos? Me kike son ji kuma bayan nan?""" "Bata san ta fara shakuwa ba, jikinta ya ɗauki rawa tuni ta iso inda yake idanunta kaman za su" fito don firgita tace """Me kake nufi Senator?? Kenan shi ɗin ba mai kudin bane? Na shiga uku ni kamila ina ya kai min 'ya? Wayyoo Allahna Senator don Allah ka taimaka ka yi wani abu wlh bana so in rasa Amal... Ina ya kaita Meyasa ya zaɓi ya aureta?""" "Duk ta rikice sai kuka. Ya taɓe baki ba wai don bai damu ba sai don jin daaɗin halin da Kamila ta tsinci kanta ai ko ba komai a yanzu za tayi hankali ta san cewa annabi ya faku idan ita wata ce, wani irin rigima ne basu yi da Zubair ba kan auren nan akan kawai yana son yayi bincike yadda addini ya tanadar, har ce mishi tayi idan ya haifu kar ya sake kallon yaranta a matsayin Ubansu don ba shi ya haifar mata su ba ba zai mata iko da su ba, ya san yana da daman hanawa amma kuma muddin ya hana wani bala'in ne zai kunno kai da bai san iyakarshi ba" shiyasa ya kyale. "Yana iya tuna ranar da su Mujiba da Baby suka je gidan da su Aunty Asiya sun dawo an yi baram baram har faɗi suke yi kawai don Amal na auren mai kuɗi ko da yayi magana har gori ta mishi hakan kuma ya isheta ishara. Yana ji tana ta kuka da maganganu don a yaranta tana ƙaunar Amal kaman me, kuma ba wai yawa ne da su ba idan ta rasa Amal ta rage gadon da ta" ci buri wanda kuma sai Hajiya karima ma ta fi ta samu ba Momma kaɗai dake da maza uku ba. "Da ya gaji korinta yayi, ta fito tana kuka magashiyan haka ta isa sashenta ta shige bargo sai" zazzabi da rawar dari. **** "Ta Yi gudun da bata san iya adadinshi ba, tun tsakar daren nan har sai da Alfijir ya keta ta shigo wani ƙaramin kauye a gaban masallacin da ladani ke ƙira ta zube ta buɗe randar ta shiga afa ruwa tana jin cikinta na wani irin kugi sai da ta ji amai da Murdar mara kan ta daina, ɗan cikinta sai wani juye juye yake ta huta tukuna tayi alwala ta gabatar da sallah a sujuda sai kawai ta kama kuka" """Allah na tuba wallahi na tuba! Allah ka yafemin ka kubutar da ni daga wannan tasku wlh zan" "chanza, zan gyara zan zama ta ƙwarai""" Haka tayi ta yi wa Ubangiji alƙawari sai da taji motsin fitowan mutane ta ɗago tana sallamewa wa za ta gani?? "Qasimu da inna suna kallonta tana kallonsu, saura kaɗan numfashinta ya tsaya chak zuciyarta ya buga ya fashe tsabar tsoro da kaɗuwar da ta yi, ihu ta tsala da ya fara janyo hankalin mutane" tana kuka tana ihu tana girgiza kai... """Ke lafiya?""" "Girgiza kai kawai take ba magana, ganin sun nufota ta damke wani mutumi tana kuka" """Don Allah kar ku bari su tafi da ni! Kar ku bar su su tafi dani za su kasheni su kashe abin da ke cikina...""" """Su waye ne?""" Nuna su take da yatsa tana ja da duwawu baya baya. """Malam lafiya?""" Wani daga cikin mutanen da suka zagaye ta ya tambayi Qasim. Sai yayi fuskar tausayi hawaye na ziraro mishi yace """Matata ce bata da lafiya ne. Ta samu lalaurar hauka tun jiya muke neman ta da mahaifiyata sai yanzu muka sameta tsoron mu dama kar taje nakuda ya tasar mata ne a daji...""" Inna uwa na girgiza kai tace """Allah ya kiyaye ma don ban san me zai iya faruwa ba, sannu Amal""" Damke mutanen take tayi tana kuka """Wallahi ƙarya suke yi! Lafiyata ƙalau ni ba mahaukaciya ba ce don Allah kar ku bari su tafi da ni Lafiyata ƙalau na rantse!""" Sai rantsuwa take a gigice hantar cikinta kaɗuwa yake tana jin kaman za ta iya haife yaron a lokacin tsabar tashin hankali. Ganin yadda take yin wani ya girgiza kai """Sannu baiwar Allah! Abin tausayi ga ciki ga hauka""" """Ni ba mahaukaciya ba ce!! Nace muku ni ba mahaukaciya ba ce kar ku bari su tafi da ni kasheni za su yi...innalillahi wainna ilaihi rajiun Allahumma ajirni fi musibatin""" "Kuka har da majina take, wanda ke rike da ita ya dubi Qasim" """Kamata samu ku tafi amma don Allah ku kula da cikin nan kar ta samu matsala dashi tunda bata san ma me take yi ba!""" "Qasim na riƙe ta ta daka tsalle tayi baya tana sake rushe wa da kukan tashin hankali yau suka tafi da ita ta kaɗe har buzunta, babu wani expression banda na damuwa da sannu da Qasim ne ke yi mata tare da inna suka damƙeta da kyau suka shiga janta tana tirjewa tana ihun wallahi ita ba mahaukaciya ba ce da hankalinta amma hakan ma sai ya kara mayar da ita mahaukaciya a" idanun jama'ar. ***** "Hibba ta ƙi barin gangar 'yar uwarta wacce sai Washegari ta farka cikin hali na jinya, kaman ma bata gane wanda ke kanta har likitoci suka zo aka sake yi mata wasu allurai Hibbah ta kallesu ""Dr. Me ya sameta? Za ta samu lafiya dai kam ko?""" """Kar ki damu in shaa Allahu za ta watsake komai normal ne"" ""Amma bata fa gane ni ba yanzu da ta farka Dr.""" """Har yanzu alluran basu saketa bane dole ba za ta gane ki ba amma in shaa Allahu tana sake farkawa za ta gane ki""" "Kai ta gyaɗa idanunta na tara hawaye, bayan fitan likitocin sai ga umma ta shigo bayanta" Najeeb da Nihla. """Hibbah sannu! Ya mai jikin?"" ""Sannunku da zuwa umma""" Ta faɗa a hankali don a jiyan da daddare Umman ta kirata ta ji ya suka koma sai Hibbah ke faɗa mata ai ma bata je gida ba ita kam tana asibiti da Hudah an yi mata aiki. """Ya jikinta?""" Najeeb ya faɗa yana isa bakin gadon """Da sauƙi yanzu suka sake yi mata wani allurar, ta farka dai amma bata gane ni ba ma""" Hawayenta ne ya shiga zuba umma ta riƙo hannunta """Kar hankalinki ya tashi in shaa Allah za ta warke ta tashi garas kin ji?"" Kai ta gyaɗa Nihla ma tayi mata sannu." "Suna nan a ɗakin sai ga Momma ta shigo ita da Daddy, sossai suka shiga mamakin ganin Umma da Najeeb a ɗakin." """Hajiya Barka da safiya""" Momma ta miƙawa Ummar gaisuwa umma na murmushi tace """Barka dai Maman Hibbah ya mai jiki?""" """Alhamdulillah da sauƙi""" """Allah ya bata lafiya ya kuma raya abin da muka samu""" "Duk sun amsa da Ameen ""Alhj ina kwana?""" Kwarai ya ji mamakin gaisuwan da Umman ta ɗaga mishi ya amsa tayi mishi sannu da jikin Hudah da kuma Allah ya raya ta miƙe. """Mu za mu koma! Hibbah Allah ya bata lafiya sai na sake zuwa ko? Ban da kukan nan don ba shi ne zai bata lafiya ba Adu'a za ki mata kin ji?""" Kai ta gyaɗa kan ta miƙe don yi musu rakiya. "Najeeb da kyar dai ya daure ya gaishe da Daddy ba tare da ya kalleshi ba, ya amsa a hankali yana jin wani sanyi na sauka mishi a rai, kaunar Hibbah na kara mamaye ranshi saboda ba don ita ɗin ba da bai ga Najeeb ba har ya buɗi baki ya gaishe shi." "Tuni ya bi bayan su umma, Momma ta dubi Daddyn" """Ka gani ko Daddy? Idan ka yi haƙuri ka kara jurewa ka daina damuwa komai zai wuce ne" "kaman ba'a yi ba""" Kai ya gyaɗa kwarai haka ne kuma ya ji daaɗin Fitowar shi asibitin da safen. "Hibbah har mota ta raka su suka tafi kan ta juya don komawa ciki har ta ɗauke idanunta sai ta sake mayarwa kanshi ya rufe motar da ya fito daga ciki yana kokarin nufan cikin asibitin. ""Usaib!""" "Ta ambata a hankali, ya waiga ya kalleta tuni murmushi ya yalwatu a fuskarshi ""Hibbah! Ban kula da ke ba ai... me kike yi nan?""" """Rakiya na yi! Ina kwana?""" """Lafiya ƙalau ya kwanan asibiti? Ya twineenmu da jiki?""" "Wani daaɗi take ji idan ta ga yana damuwa da ciwon twineen nata gashi har ya iya zuwa asibitin don duba Hudah ɗin da safiyar bayan ko saninshi ma Hudar bata yi ba, har ciki ya mata rakiya ya shiga ya gaishe da su Daddy da Momma kan ya fice ba tare da ya jima ba tana so ta bi bayanshi amma bata so su Momma su ɗauki wani abu don bata so su san ma tana tare da wani a yanzu ɗin." """Hibbah ki je gida ki yi wanka ki ci abinci idan kin huta sai ki dawo""" Shagwaɓe fuska ta yi """Momma don Allah ki bar ni kusa da 'yar uwarta""" Momma ta harareta """Mu kin san bare ne... Ki wuce ki tafi gida ki je ki kimtsa kin ga yadda kika zama kuwa? Haka za'a ta shigowa duba Hudar ana kallonki?""" Babu yadda ta iya don Daddy ma bayan Momma ya bi a kan taje ta huta haka ta fito ga mamakinta har lokacin Usaib na nan. """Baka tafi ba?""" Girgiza kai yayi ta gyaɗa kai """Don Allah mu je ka sa su bar ni in ga yarana tun jiya nake zuwa sun hana ni..""" "Yadda tayi maganan a Shagwaɓe ya ɗauki hankalinshi sossai sai ta ji kunya, murmushi ya saki" ya miƙe ko don wannan Shagwaɓar dole ya cika roƙonta. "Kawunshi ya kira ya roke shi ganin babies ɗin kawai, ya kuwa ce su je suka nufi nursery aka kai su har jikin incubator da yaran suke kwance hancinsu duk da oxygen suna bacci, tana murmushi tana hawaye a lokaci ɗaya" """Alhamdulillah! Alhamdulillah!! Allah na gode maka da ka nuna min yarana na wurin twinee Allah ka basu lafiya ka raya min su""" Ya amsa da Ameen. "Daga nan suka fito don ba'a bar su sun jima ba, shi yayi insisting kaita gida don motanta Mumtaz ne ya tafi dashi jiya dama Daddy yace driver ya mayar da ita sai ya dawo don haka tace ya bari kawai zata tafi da Usaib." Yana janta da hira suna tafiya har suka isa gida. """Ƙarfe nawa za ki gama in dawo in ɗauke ki?""" """Da dai ka barshi ma don kaman da mota zan koma""" Yayi puppy eyes """Haba beautiful! Kar ki rage min ladar mana""" Ta kalli kanta """Ni da Momma ta gama cewa na yi kamar mahaukaciya kake kira beautiful? Zage ni dai""" Murmushi yake yi """Ko wani irin yanayi kike ciki ni a idanuna bana gani kyaunki kawai shine abin gani na, shi kaɗai ya isa disashe duk wani abu da za'a iya gani a tattare da ke...""" "Ta shiga blushing kunya na rufeta, yayi murmushin samun nasara a kanta don ya fahimci a" yanzu tana jin wani abu a kanshi ko da ko ba yawa. "Sallama ta mishi ta fito yana cewa za su yi waya, tana kokarin rufe motar sai ga Hajiya Kamila da Mujiba da Nadiya suna rike da ita saboda zazzabin da yake son fin karfinta don zuwa asibiti," kaman ba zata ce komai ba ta dubi Nadiya da suke shiri a yanzu tace """Yaya Nadiya Hajiya ba lafiya ne?""" """Wlh Hibbah nima ina chan shirya su Fadeel Mujiba ta zo ta kirani ashe ta kwana jikin ba daaɗi shine za mu je asibiti. Ya jikin Hudah?""" """Sannu Hajiya Allah ya kara sauƙi, Hudah jiki da sauƙi ta ma farka Alhamdulillah""" Mujiba bata ce mata komai ba itama bata ce mata ba ta zagaye su ta wuce don hajiyar ma ko bude ido ta ƙi yi don kawai kar ta yi magana da hibbar. **** "Su Hajiya Tani ana kwance da lankwasheshen kugu jiki take ji sossai zuciyarta kuma har lokacin a tsinke don sam bata san me ke tafiya ba, duk sun barta a suspense na tunanin wani hali ake ciki ta tabbatar idan an bincika jininta ba ƙaramin hawa yayi ba falmata dake zaune a gefen ta tace" """Ni dai wallahi Hajiya na gaji! Haba har yaushe za ki zauna a firgice saboda wata chan! Mu muka ɗora mata ciwon ne?""" "Girgiza kai Hajiya tayi falmata ba zata gane ba, motsi suka shiga ji mai ƙarfi." Zazzaro idanu hajiya tayi kaman a ce kyatt ta runtuma da gudu don ayyanawa kawai take "Hudah ta mutu an zo kamata, falmata ce ta miƙe ta fito daga wajen ta shiga cewa" """Hajiya kayakin Hudah fa ake fita dasu daga gidan nan!!""" Da ƙarfi tayi maganan tuni Hajiya ta shiga kokarin Miƙewa zani a hannu tayi waje a duƙe.... *Afuwan gobe na yi alkawarin pages 2 in shaa Allah idan na ce zan cigaba da ɗayan zan yi bacci ban gama ba wlh idanuna rufewa suke...* "*Littafin nan na kuɗi ne ki biya Naira Ɗari biyar (500) kachal domin kasancewa cikin masu kwasar tarin ilimi, faɗakarwa da zazzafar soyayya mai cike da sadaukarwa da aka zube ciki. Za ki biya ta wannan asusun" 0545475847 Gt bank Fatima Muhammad Gurin Sai ki tura shaidar biya zuwa wannan layi 09039206763 Ko kuma katin MTN na Naira 500 cikin wannan layi na sama sai ki tura da shaidar biya ta same layi. Sai na ji ku* Gureenjoh 26 """Idan baki yi shiru ba na rantse muna isa sai na baki mamaki! Kin zata za ki mana dabara ne ki saka fillow da zani bisa katifa ki tsere? Toh da sauranki yarinya...""" "Sossai take kuka suna janta, mutanen basu watse ba sai ma yawaita da suka sake yi wani daga" cikinsu yace """Kai! Ku tsaya!!""" "Dukda gaban Qasim da Inna ya faɗi haka suka tsaya suna Juyowa, tuni Amal ta takarkare ta fusge har tana faɗuwa tayi cikin mutanen tana roƙon kar su bari su tafi da ita kasheta zasu yi" makisa ne matsafa. """Ni wlh kaman na san fuskar wannan yarinyar, anya kuna da gaskiya kuwa??""" Ya kalli su Qasimu da suka biyo ta cikin mutanen don su sake kamata a hasale... Kan Qasimu yayi magana tace """Basu dashi, ku ƙira min iyayane za su tabbatar muku ina da layinsu wallahi makisa ne..""" """Waye mahaifin naki?""" "Wanda yace kaman ya santa ya tambaya ""Senator Mudassir Madaki...""" Ya zaro ido """kece kwanaki aka yi ta cigiyarki? Ya Sunanki?"" ""Sunana Amal""" Ta faɗa cikin kuka sossai tuni Qasimu da Inna suka fara shirin zamewa wani yace """Jama'a ku tare su kar ku bari su gudu""" "Damƙosu aka yi tana kuka take bada labarin wahalan da ta sha da kuma ƙudirinsu a kanta, abinka da akwai tarin Matasa kuma kauye ne daukar doka a hannu abu mai sauƙi ne tuni suka" yi wa su Qasimu rubdugu ashe irin su ne masu sace musu yara suna tsafi. "Kan a ce hukuma sun zo daga kasimu har innan babu wanda bai haɗa jini da majina ba, kamanninsu duk ya sauya, da alama ba za'a rasa kariya ko gocewar ƙashi a jikkunansu ba, ko da hukuma suka zo ma ba'a bar su ba don suspect na kidnapping ne ga attempt murderer tuni aka kwashe su har Amal aka dawo cikin gari ita kam kan a zo ma labour ya tasar mata sai" asibiti aka yi da ita emergency... *** """kai! Ina za ku kai kayan?""" """Mai gidan ne yayi mana umurnin kwashe su zuwa inda yake""" """Mai gida? Yaushe Mu'azzam din ya dawo? Ko chan ƙasar da yake za'a kai?""" "Hajiyar ta faɗa tana dafe kwankwaso da take jin kaman zai karye. ""A'a inda yake za'a kai ai yana gari""" Ta zaro idanu """Mu'azzam ne ke garin nan?""" A rikice ta yi tambayar tana kara jin fargaba na rufeta """Eh fa! Yana nan don baki da baki muka yi magana ya mana umarnin tattara duk abin da ke sashen matarshi mu kai mai gidan da yake""" A sake da baki suka barta suka cigaba da aikinsu. Falmata ta kalla """Falmata me kenan hakan yake nufi?""" Tace """Ni ina zan sani Hajiya... Mu je dai ki gwada kiran layinshi na Nigeria""" Kaman za ta yi kuka tace """Idan na kira me zan ce mishi falmata? Ban san wani hali matar tashi da abin cikinta suke ciki ba. Kila ma sun mutu ya gudu ne kar a ce da sa hannunshi shima in shafa mishi kashin kaza...""" Riƙo ta falmata tayi """Ki daina wannan sambatun Hajiya, ai da mutuwa tayi da zuwa yanzu mun samu labari dole. Mu je ciki zai zo ne Yaya Mu'azzam ɗin""" Da kyar suka koma saboda kwankwasonta dake ƙara tsami... **** "Hibbah na zaune gangar Hudah dab azahar sai gashi ta farka, da sauri Hibbah ta miƙe tsaye" tana kallon fuskarta """Hudah! Twinee kin tashi? Kin gane ni?""" Murmushi ta saki cikin yanayin ciwo kan ta ɗaga kai. Hawaye ne suka kwacewa Hibbah fuskarta dauke da murmushi tace """Alhamdulillah! Bari na ƙira su twinee""" "Da sauri ta fice chan sai gata da wasu nurses a gabansu Dr. ne, basu bar Hibbahn ta shiga ba" sai waje da ta tsaya. "Aunty Kubra da a ranar ta sauƙa Kano, gefenta Momma ne da Aunty husna sun fito daga ganin 'yan biyu a nursery fuskokin su a sake ganin cewa yaran suna kan samun lafiya, Hibbah na ganinsu ta isa gare su fuskarta kaman gonar auduga" """Twinee ta farka Momma! Ta gane ni...""" Alhamdulillah suka yi ta cewa suma suna jin farin cikin farkawar nata. "Bayan likitocin sun fita nurses suka fada musu cewa za su iya shiga, ta ci wani abu mai ruwa" sossai sannan a samu abu a goge mata jiki tuni suka shige ɗakin. """Sannu Hudah ya jikin?""" Ta ce a hankali """Da sauƙi Momma... Aunty kubrah kin zo?""" Aunty Kubra ta riƙe hannunta """Ai dolena in zo Hudah na yi jikoki bana son mommanku ta rigani kwace fadar fav granny ɗin"" Murmushi ta yi." "Aunty husna tace ""Sannu Hudah""" "Kai ta gyaɗa tana ɗan murmushi, Momma ce ta yi mata towel bath ɗin aka gyarata tsaf kan aka ba ta tea marar zafi sossai mai kauri ta sha, sai da ta huta kan aka bata faten dankalin turawa da yayi laushi tibis yayi ruwa gefe danderun nama da shima yayi laushi sossai Hibbah na" taimaka mata tana ci. """Ba Za ki tambayi yaranki ba?""" Hibbah tayi maganan jin tun dazu Hudar bata ce komai akan abin cikinta da bata gani ba. Hararanta tayi chan ƙasa kasa tace """Ke baki da kunya ko?""" Hibbah kam ta ƙi rage murya tace """Kunyar wa za ki ji? Momma ko Mummy ko kuma Aunty husna?""" "Aunty husna tace ""Kunyar me?""" Hannu Hudah ta kai tana jan Hibbah amma sai da tace """Kunyar tambayar yaranta wai... Tabb kunya? Bayan wannan uwar wahalan da kika sha?""" Cikin rashin cikakken karfi ta mitsini Hibbahn a cinya Hibbah ta saki ihu tana Miƙewa tsaye su "Aunty husna na musu dariya, itama Hudah murmushi take." """Ba don halinki ba sai don zuciyarki tayi sanyi zan faɗa miki babies nawa masu kama da ni sakk suna nursery suna kan samun kulawa, kina gama cin abincin nan za'a kawo su ki basu abincinsu suma""" "Murmushi Hudah ke yi, a ranta tana godiya wa Allah da ya nuna mata saukarta lafiya, tana" "godiya da ya kasance yaranta sun fito lafiya ƙalau don bata taɓa tunanin ba zata mutu da yaran nan a ciki ba, ɗaci ne ya ziyarci ranta tuna abin da ya faru tsakaninta da falmata a yayinda take" "cikin azabar nakuda, tsanar gidan ne ya shigeta da har take jin ba za ta iya sake taka kafafunta" ciki ba. "Bayan ta gama cin abincin ta sha ruwan dumi sai gashi an kawo yaran cikin kayakinsu na jarirai very cute sai kamshi suke, Hibbah ta karɓi ɗaya daga hannun Nurse ɗin tana rungumeta don wannan ne karon farko da ta riƙe su, yayinda Aunty Kubra ta karɓi ɗayar tana kokarin" taimakawa Hudar ta shayar da ita aka turo kofa.... **** "Hajiya kamila ta kwana babu lafiya don jininta ba ƙaramin hawa yayi ba, ko da suka zo asibiti gado aka bata aka ɗaura mata ruwa, Hankalin yaran nata a tashe dukkansu adu'a suke kar mummunar abu ya samu Amal, Nadiya ce ta kira Daddy ta faɗa mishi, hakan ya sa dole ya bar asibitin da Hudah take ya nufi asibitin da Hajiya kamilar take inda anan ne suke da NHIS kuma" anan ne ma Dr. Najeeb ke aiki. """Daddy!""" "Mujiba ta kirashi kaman za tayi kuka ""Mujiba ya jikin maman naku?""" Nadiya tace """Toh da sauƙi dai Daddy amma kam tana jin jiki, jiya bata iya ta yi bacci ba""" Yace """Hmmm Allah ya bata lafiya""" Dalilin da yasa yake ɓoye mata bincikensu akan Amal kenan amma ta ƙi natsuwa ta ɗaga masa hankali da maganganu marasa daaɗi da zarge zarge dole shima ba yadda ya iya ya faɗa mata ga abinda ta janyowa kanta. "Dr. Najeeb ne ya shigo reception ɗin, har ya wuce kaman bai gansu ba sai kuma ko me ya tuna ya dawo." """Ina kwana?"" Ya faɗa." Daddy ya saki murmushin jin daaɗi yace """Lafiya ƙalau Najeeb ya aiki?"" Yace a hankali ""Alhamdulillah""" "Daddy ya kalli su Nadiya yace ""Babban yayanku""" "Ta duƙar da kai tana jin kunyar maganar da ta taɓa yi a gabanshi a kan Hibbah, Mujiba ta gaishe shi ya amsa kan yace" """Waye ba lafiya?""" "Nadiya ce ta amsa mishi tana gaishe shi ya gyaɗa kai yace ""Allah ya sawwaka""" Kan ya wuce ya nufi office nashi. "Daga nan office Daddy ya wuce, yana cikin ayyukan shi da misalin karfe sha biyu da wani abu aka kira layinshi kaman ma ba zai ɗaga ba ma sai kuma ya ɗaga." """Assalamu Alaikum warahmatullah barka da rana""" "Ya amsa sallamar kan yace ""Yauwa barka dai!""" """Ina magana da Senator Mudassir Madaki ne?"" Ya amsa da""eh shi ne""" """Sunana Hussaini""" "Nan ya mishi bayani shi DPO ne akwai case da ya faɗo mishi da safen nan, case ɗin ya shafi 'yar wajenshi da ake ta cigiya wato Amal." Bai san ya miƙe tsaye ba. """A ina? Tana nan lafiya ko DPO?""" """Mun sameta hannun wasu mutanen kauye, su ma kuma sun samu nasarar tseratar da ita ne daga Matsafan mijinta da kuma Mamanshi, yanzu haka tana babban asibiti inda ta haihu ta samu ɗa namiji""" "Murnan da Daddy ya tsinci kanshi ciki sossai Dukda zuciyarshi da ya buga yace ""Mijinta? Kuma tsafi?""" """Kwarai da gaske ta tabbatar wa al'ummar kauyen cewa da kunnuwanta ta ji suna shirin ta haihu su kashe yaron su ba da jininshi""" """Innalillahi wainna ilaihi rajiun...! Gani nan zuwa DPO""" Ya yanke wayan yana kiran Zubair don su haɗu a chan a lokaci daya yana ficewa daga office ɗin. **** """Momma ina yini?"" ""Lafiya""" Ta amsa ba tare da ta daɗa ba. "Mu'azzam da ke gab da rushe wa da kuka ya dubi Aunty Kubra ya gaisheta ita kam ko ta amsa don ta hasala sossai da shi, Dukda ta san itama 'yan uwan mijinta sun sakata gaba amma dayake tana da supportive husband da yake tsaye sossai kan lamarin abin bai yi tsamarin da zai dameta ba kuma itama bara bar su ba suna mata take rama wa, amma Hudah ga haƙuri ya mata yawa, ga uwarmiji ga ƙanwarshi sannan tana gani babu abin da mijin zai iya yi tunda" uwarshi ce tana zaune kawai tana shan wahala. "Ita kanta Hudar Dukda ta shiga cikin tsananin mamakin kallonshi a Najeriya tunda ta mishi kallo ɗaya bata sake ba, Hibbah kam ba magana fuskarnan tuni ta haɗe shi tsaf, ganin basu bashi fuskar ko kallon yaran yayi bane bare ma magana da Huda ya sa ya fice daga ɗaki jikinshi a sanyaye, Allah kaɗai ya san irin tashin hankalin da ya shiga daga barowarshi Malysia zuwa Nijeriya, jin irin wahalar da Hudar ta sha sanadiyar mahaifiyarshi ya saka shi kuka ba adadi, ko ba don Huda ba idan tana ƙaunarshi ai ya ci a ce ta ƙaunaci yaranshi dake cikin Hudar, rasa ma" inda zai yi yayi haka ya zauna a cikin mota ya haɗa kai da stirring. **** Mukus Hajiya Tani ta yi a sadda babban wanta ke ta zuba masifa kaman zai ari baki. """Kina ganin don Mu'azzam na miki biyayya shikenan sai ki ta mishi abin da kika ga dama da tutiyar ke mahaifiya ce a gareshi? Wallahi ki gode Allah ma kin samu ɗan mai biyayya a irin yaran zamani babu mai zuba ido kina yi mishi hakan, ita kanta Hudar kin ci sa'ar samun 'yar arziki amma kin nace lallai sai kin ga karshen zaman lafiyarsu to ya zo """ Da sauri ta kalleshi """Eh ya zo! Ki kalleni da kyau iyayenta sun kafe lallai lallai ya sakar musu 'ya don ba daga sassake ta faɗo ba da gatanta, shi karan kanshi Mu'azzam din ya dawo a susuce amma ya tabbatar min ganinku shine karshen abin da zai zo ranshi a yanzu don baku kyauta mishi ba! Kuma ban ga laifinshi ba don tunda kuka nunawa 'ya'yanshi kiyayya shima bakwa sonshi ya min daidai sai ku rungume gidan ku sha zamanku""" Yana kai nan ya juya ya fice yana cigaba da masifa don sossai ranshi ya ɓaci musamman da Mu'azzam din ya je mishi yana zub da hawaye. "Miƙewa Hajiya tayi ta nufi ciki jikinta duk a sanyaye, da kyar take tafiya har ta shiga cikin uwar daka tana kiran Falmata ta kawo mata mayafi ta tafi gidan Yayan ta samu Mu'azzam ita Allah ya gani bata so kashe 'ya'yan cikinshi ba kai ko Hudar ma bata yi mata fatar mutuwa ba sai dai ta" tarar da Falmata a bayi tana ta sheka amai..... "*Littafin nan na kuɗi ne ki biya Naira Ɗari biyar (500) kachal domin kasancewa cikin masu kwasar tarin ilimi, faɗakarwa da zazzafar soyayya mai cike da sadaukarwa da aka zube ciki. Za ki biya ta wannan asusun" 0545475847 Gt bank Fatima Muhammad Gurin Sai ki tura shaidar biya zuwa wannan layi 09039206763 Ko kuma katin MTN na Naira 500 cikin wannan layi na sama sai ki tura da shaidar biya ta same layi. Sai na ji ku* Gureenjoh 27 """Falmata? Dama baki da lafiya ne?""" "Tana wanke fuska tace ""Zazzabi ne kawai Mama""" """Sannu taho ki ga mu tafi gidan Yaya ina son Magana da Mu'azzam""" Tana fitowa jikinta duk a mace take cewa """Mama dama ya zo shine ba zai nemeki ba sai ke za ki neme shi?""" Girgiza kai tayi """Falmata wani irin zuciya ce a kirjinki? Yanzu a duk abubuwan nan da suke faruwa baki ji kaman ni ce mai babban laifi ba? Ban kyauta wa Mu'azzam ba, idan ya ce ya rabu da ni kuma ta har abada ai dukkanmu mun kaɗe wa zai cigaba da kula da mu da rayuwarmu?""" Zama tayi tana share hawaye """Wallahi ban ƙi Huda da wani dalili mai girma ba, sharrin shaidan ne shine ya nuna min cewa muddin na zuba ido duk wani dukiya ta Mu'azzam da kulawarshi a kan Hudar zai tsaya, ina ganin kaman za ta saka shi mantawa da mu sai ita kaɗai da ƴaƴanta dalilin kenan da ya sa na hana su zaman lafiya amma yarinyar nan bata taɓa min komai ba...""" Tana magana tana zubar da hawaye. """Na san wahalar ɗaukar ciki, na san na raino na san me ake cewa nakuda amma don rashin imani mun kasa tallafa mata, ta nemo mai tayata mun kore ta, kuɗi wannan idan ta ba ni dayawa sadda Mu'azzam ba ya nan cewa nake dama dayawa yake aiko mata tana so ta talauta shi ta mallaki komai nashi, idan ta ba ni kaɗan in ce ai dayawa ya aiko ta choge sauran saboda baƙar zuciyarta, wace macece za ta juri abin da Hudah ta jure a zamanta da ni? Kaico na ni Tani wallahi ban kyauta ba""" Sossai take kuka tana tuna duk abubuwan da tayi ta yi wa Hudah. Falmata da ta samu sanyin tiles ta kwanta tace """Ni kuma dan banzan dukan da ta min ta kyauta kenan? Kin san Hajiya dukan nan ne ya sa na shiga ɗakin ma na samu tana nakuda ko na bi ta kanta don dama na yi alkawarin rama wa. Ta saka min ido akan samarina har da guntun wa'azinta alhali ta sani na sani soyayyar idan ba da" "haka ba mazan gudu wa suke""" """Falmata dama kin shiga kin ga tana nakuda kika yi tafiyarki? Kin kuwa san me zai faru idan da ta mutu? Nakuda fa??""" "A ɗan tsorace Hajiyar tayi tambayar, baki falmata ta turo ""Innalillahi wainna ilaihi rajiun...""" "Hajiya tayi ta maimaitawa zuciyarta na cigaba da tsinkewa, duk abin da falmata tayi ba laifinta bane nawa ne, koma menene da bata ga ina yi ba da bata yi ba, wace iriyar uwa na zama ni" Tani? Tana maganan a ranta tana kuka. Da kyar ta danne zuciyarta ta ɗauki mayafi don tafiya gidan Yayan Juyowa da zata yi don "tayiwa falmata magana su tafi ta ga ta yi bacci, bata kawo komai ba ta fice daga gidan sai dai ta je chan ɗin ma bata samu Mu'azzam ba haka ta gaji da zama ta tattara ta dawo." **** "Amal kam tunda ta sauƙa tana zaune ne babu abin da take son gani irin iyayenta, a firgice take" "kuma a razane don haka ana turo kofa ta zabure sai ta ga Daddy ne, da sauri ta sauƙo tazo ta" "faɗa jikinshi tana kuka sossai da neman yafiya, daga shi har zubair ta basu tausayi ta ƙare kaman wacce tayi ciwon yunwa duk ta yi baƙi kaman ba Amal ba, ko da labarin bayyanar Amal ya je ga mahaifiyarta kaman za ta zauce haka itama ta sa aka kawo ta asibitin sun yi kuka sun kuma gode Allah da bai ba Qasim dama a kanta ba inda tuni aka yi musu kyakyawar ɗauri" kuma ana shirin tura su kotu don shari'a. "Satin Hudah biyu da haihuwa aka sallameta, ba zata ce zaman asibitin bai mata daaɗi ba don a kullum tare suke da danginta da 'yan uwanta ana kulawa da ita tamkar Gimbiya, yaranta sun warke garas tana cigaba da kulawa da su da taimakon su Momma, idan ka ganta ba za ka ce ita ce ta haihun ba don tuni ta mayar da kyaunta dama aikin ake kulawa da da kuma jininta, Mu'azzam ya mayar da asibitin gida tun yana zuwa basa kula shi har dai ya shiga ba Momma da Daddy tausayi don ranan kawai zubewa yayi yana roƙon su su yafe mishi wallahi ya amsa" laifinshi su barshi ya ga Hudah da yaranshi. "Da kyar Daddy Z ya kyale suka fita a ɗakin, gaban Hudah ya nufa ya riƙo hannunta" """Na tuba Hudah! Wallahi na tuba ki yafe min don Allah! Na tafka kusakurai dayawa a zaman mu ina ganin don ni ban saɓa miki ba ai don mahaifiyata ta saɓa miki hakan ba zai zama cusgunawa a gareki ba, na sani tayi abubuwa masu yawa na kasa magana bare ɗaukar mataki ban san cewa har a irin wannan lokaci na rayuwa ko mutuwa za su iya aikata abin da suka aikata a gareki ba! Wallahi a yanzu a shirye nake da daukar mataki tuni na chanza miki gida kayakinki ma suna chan ko hanyar wanchan gidan ba za ki sake kallo ba bare ki zauna da Hajiyata. Na ma nemi mai aiki da zata dinga miki aiki kina kula da yaranmu kuma kina zuwa" "makaranta duk abinda kike so ki faɗa wlh zan yi miki""" Zame hannunta ta yi ba tare da ta ce komai ba don Daddy Z ya riga ya mata gargaɗi kuma ba zata tsallake maganar iyayenta ba a kan 'yancin da suke son samar mata. Yaran yake kallo yana zub da hawaye sai yanzu ya samu ya ɗauke su ya rungume cike da farin cikin da ke sauƙa mishi tamkar ruwan sanyi a ranshi. """Alhamdulillah! Alhamdulillah!!""" Murmushi ya saki ya kalleta """Kun yi musu huduba ne? Na ji Hibbah na kiransu da Amna da Yumna""" "Girgiza kai tayi bata ce komai ba, sai ya fahimci inkiya ce kawai a take ya yi musu huduba, ya ajiye mata yumnar" """Allah ya raya mana Kubrah"" Yayiwa Amna ma kan ya sauƙe ta ""Allah ya raya mana Fatima""" "Bata ce komai ba don dama ta san a yanzu ba zai yi gigin saka sunan mahaifiyarshi ba sai dai bata yi tunanin zai saka Aunty kubrah ba, ya matso yayi pecking goshinta" """Sannu da ƙoƙari Allah yayi miki albarka Hudah""" Idanu ta lumshe kawai tana hawaye bata ce tak ba. "Shigowar su Aina'u ya sa dole ya fice, dole kawai yake rayuwa shi kadai a sabon gidan da ya" "saya saboda Hudah ɗin, gida ne mai kyau don ba karamin shigo mishi kudi ke yi ba, Dukda ba" "za'a ce babban gida ba madaidaici ne amma mai kyau da ɗaukar ido komai na gidan kaman ka sace don kyau da walwalin gidan, ya kashe kudi sossai a kan gidan ba kuma don komai ba sai don ya wankewa Hudah zuciyarta da hakurinta, Mahaifiyarshi duk yadda ta so ta ganshi abin ya gagara ya ƙi bari sam, ya dai san ya tura musu kayan abinci da kuɗin cefene ta hanyar ɗan" Kawunshi amma bai je gidan ba sam. "Ko da aka sallami Hudah Daddy Z gidanshi ya kaita ya sa Aunty husna ta shirya mata ɗaki na musamman, akwai dattijuwar 'yar uwarsu da ya je ya daukota musamman daga kauye kasancewar mijinta ya mutu kuma bata da 'ya'ya Yadikko suke ce mata ya ajiyewa Hudar don" Aunty Kubra zata koma ita da Hibbah. "Sai da ta dawo gidan Daddy Z aka yi suna na ji da gani raguna bibbiyu aka yanakawa kowacce yarinya duk fa mahaifinsu ma bai sani ba, Dukda an riga yin sunan Amal da ba kowane ma ya sani ba bare ya je ta sakawa danta sunan Mahaifinta Mudassir tana kiranshi Ayman, sai gata ta" zo sunan Hudah. "Dayawa sun yi mamakin ganin yadda Amal ta chanza, bata iya ta daure ba ta nemi yafiyar Hibbah da Hudah dama ta jima da neman na Momma, ita kanta mahaifiyarta jikinta ya yi sanyi da abubuwan da suka faru, yayinda Hajiya Zakiya kuma gani ga wane ya zama mata ishara ta" fara rage baƙar kishi da musgunawa Momma itama da take. Yara da mahaifiyarsu sun samu sha tara na arziki daga 'yan uwa da abokan arziki bayan suna da sati daya Hibbah da Aunty Kubra suka koma legos saboda school na Hibbah. "Shi kam Mu'azzam ko da ya je asibiti bai sameta ba ya sake jin tashin hankali, gidansu ya je sai dai aka ce mishi bata nan, ya sake susuce wa yaje wurin Daddy Rabi'u yayi ta roƙonshi gafara akan zai gyara zai chanza ya yi alkawari tausayinshi ya sa Daddy Rabi'u yace ba komai za su yi" "shawara da 'yan uwanshi yanzu ya tafi kawai, haka ya tafi cikin tsammanin wa rabbuka." ***** """ke falmata! Falmata ke!!""" Hajiya Tani ke kiranta tana ture ta. "Idanunta da suka yamushe ta ɗaga take kallon hajiyar ""Wai menene Hajiya?""" """Lafiyarki kam? Wani irin ciwo ne wannan da kullum safiya kina nan kina bin sanyin tiles? Abinci wannan sai kin zaɓa kike ci me yake damunki ne?""" Tayi maganan da damuwa """Me kuwa zai dameni Hajiya? Malaria ce fa da typhoid"" ""Ban yarda ba ki tashi mu tafi asibiti""" """Ni dai don Allah ba sai mun je ba bana son allura ki kyaleni"" ""Wallahi sai kin je, tashi mu tafi""" Ta janyo mayafin ta ta tura falmatar a gaba gabanta sai faɗuwa yake suka tafi asibitin da suke da kati. Bayan falmata ta yi wa likitan bayani aka bata gwaji suka je suka yo. """Masha Allah, tana dauke ne da cikin wata biyu dama irin wannan ciwuka a First trimester normal ne sai da """ """Ciki Dr.??""" "Daga falmata har hajiyar suka faɗa a razane ko kan yayi wani magana Hajiya ta yanke jiki ta faɗi ihu falmata ta saki shi kam bai san bata da aure ba sai salati yake tuni aka yi emergency da ita, falmata kam banda kuka babu abin da take ta ƙi magana sai wayan hajiyar suka ɗauka suka kira Yayanta a lokacin ma yana tare da Mu'azzam hankalinsu duk ya tashi suka yo asibitin sai" dai su ma da mummunan labari suka ci karo tuni Mu'azzam ya rufeta da duka. "Da kyar aka kwace ta, da kyar da gaske aka samu Hajiya ta farfado sai kuka." """Ai ba kuka ne ya kamata ki yi ba duk laifin waye Tani? Laifinki ne shiyasa wasu mazan ke ganin auren 'yar da ta tashi gaban mace sai jarrabawa, irin ku ne ke sa ake yi wa single mothers kudin goro, kin kasa saka idanu akan yarinyarki amma kin kafawa surkarki karan zuƙa," "kin bar huruminki kin shiga na Allah dole ki ga ba daidai ba""" Cikin kuka tace """Innalillahi wainna ilaihi rajiun...! Allah na tuba Allah... Sai da Hudah ta faɗa tana roƙona akan rayuwar falmata da irin tara samarinta na ce hassada ce take mata da baƙin ciki da sharri ashe duk gaske ne! Na shiga uku""" Sossai take kuka da ya so ba wa su Mu'azzam tausayi Yaya yace """Shiyasa harshe ma abin kiyayewa ne kaman yadda annabi ya ce, baki bashi da kyau"" Tana tuna irin aibatawar da tayi ta yi wa Hibbah da zargin gidansu Hudah din cewa duk 'yan" iska ne ashe ga ɗiyarta na lalace wa gabanta bata sani ba. "Fasalta irin tashin hankalin da suka shiga ma ba zai rubutu ba, falmatar ta nemi ko a zubar suka sake shigar jikinta da duka Kawun nata ya cigaba tsawatar mata" Babu zancen zubarwa tunda haka ta zaɓa ta raine shi har ta haife kila idan suna ganin ɗan ya "zame musu ishara, haka suka tarkata jiki a mace zuciya na cigaba da kuna suka yi gida, Mu'azzam bai zauna ba yayi tafiyar shi." ***** "Hibbah da Usaib a wannan dawowartan wani irin ƙauna ne ya kullu tsakani don tuni ta ba da kai bori ya hau, Usaib in dai kalamai ne a bar mishi yana kula da ita sossai da riritata, kuma daga ita har Aunty Kubra da Zaitoon suna jin daaɗin ganin yadda yake nuna mata ƙauna ko a gaban waye." A tsakankanin ne ma aka zo tambayar auren Zaitoon wanda hakan ya ƙarawa family ɗin farin "ciki ƙwarai kasancewar zaitoon rabon ya ɗan yi nisa, tuni shirye shirye ya kankama na bikin" inda Hibbah ita ce kanwa kuma kawa na kusa don Ƙawayenta dayawa ma basa ƙasar... "*Littafin nan na kuɗi ne ki biya Naira Ɗari biyar (500) kachal domin kasancewa cikin masu kwasar tarin ilimi, faɗakarwa da zazzafar soyayya mai cike da sadaukarwa da aka zube ciki. Za ki biya ta wannan asusun" 0545475847 Gt bank Fatima Muhammad Gurin Sai ki tura shaidar biya zuwa wannan layi 09039206763 Ko kuma katin MTN na Naira 500 cikin wannan layi na sama sai ki tura da shaidar biya ta same layi. Sai na ji ku* Gureenjoh 28 "A yau Hudah ke cika arba'in daga ita har yaran sun yi kyau abinsu suna samun kulawa sossai daga Aunty husna da Daddy Z bata daka ta rigimar Amaryarshi sam don asali ita ba mai kaunar rigima ba ce, tana zaune tsakar parlorn Aunty husna tana ba Yumna abincinta ta jiyo sallama, sai da gabanta ya faɗi jin Muryar da ko a mafarki ta ji zata iya gane mai ita cikin seconds, da sauri ta ɗago tana kallon Hajiya Tani da ta shigo parlorn tana amsa sallamar a kan labbanta," "Aunty husna ta miƙe riƙe da Amna itama tana kallonta ""Lafiya?""" "Murmushi ta yi mai ciwo, dole a ce mata lafiya tunda ta yi girman hoti-ho ta zub da daraja da" kima da Allah yayi mata kaico rayuwa! Kaiconta da ta kasa fayyace gaskiya da daidai sai da komai ya chaɓe mata. """Lafiya ƙalau na zo wurin Hudah ne""" Hudah da kyar tace """Sannu da zuwa Hajiya, bismillah ki zauna""" Gaban Hudah ta matso ta zauna gangarta kawai sai ta fashe mata da kuka """Hudah ki yiwa Allah ki yafemin alhakinki da na ɗauka, ki yafe min uzzura miki da nayi ta yi na hana ki zaman lafiya a dakinki, na yi nadamar duk wani furuci a gareki a yanzu haka kunyar kaina nake ji...""" Hannunta Hudah ta riƙo Dukda zuciyarta rawa yake tana tsoron kar ma shigo shigo ba zurfi hajiyar ke shirin mata """Hajiya ba zan ce ban riƙe ki ba a wannan karo, ba zan ce baki kuntata mini ba amma wallahi ban taɓa ganinki da wani ido ba bayan na uwa hakan ya sa duk kalamanki kan zama masu kuna tamkar garwashi a zuciyata, ban auri Mu'azzam saboda in raba shi da ku ba, na aure shi ne saboda ina son shi kuma ina so in tayaku sonshi, na zaci zan samu wata uwar da zan iya shearing damuwata mu yi kuka da dariya a tare kamar wacce ta haifeni, na rabu da 'yar uwata" "da tunanin Falmata za ta zame min twinee a sabuwar rayuwar aurena sai dai kash duk mafarkina ya sauya daga mai kyau zuwa mummuna har nake jin bana sha'awar sake zama da Mu'azzam bare mu haɗa Inuwa. Idan da iyayen miji masu ƙiyayya ga sirikansu za su fahimta wallahi babu macen ƙwarai 'yar gidan tarbiya da za ta so raba ɗa da iyayenshi saboda kawai tana aurenshi. Matsayinki na uwa Hajiya wallahi na yafe miki, ina fata komai zai wuce a wurinki," "idan akwai inda na saba miki nima ina roƙo ki yafe min...""" "Kuka sossai Hajiya Tani ke yi lallai ta ga ishara ji yadda yarinyar da zata iya yin jika da ita ke faɗa mata gaskiyar rayuwa, bata san me ya hau kanta ba da ta kasa ganin good side of Hudah a kullum sai son ganin laifinta, da ta bi shawarar Hudah tun farko da falmata bata lalace mata a gida ba, ita kam ta ga illar furuci." """Na gode sossai Hudah! Na gode ƙwarai Don Allah ki yafe wa falmata ma, tana chan tana fama" "da azabar laulayi wanda ta janyo mana da zuri'armu magana a kanshi yau fari gobe tsumma kullum kuka da nadama bata isa fita ko kofar gida ba sai cin mutunci""" Hudah ta ji tausayin falmata saboda ta san zafin da ta taya Hibbah ji a sadda rudin samarin zamani ya rinjayeta wurin aikata kuskure a rayuwarta tana tuna yadda ko fita ya gagari Hibbah sai da niqabi ko facemask saboda mutane da bakinsu. Aunty husna tace """Allah ya kawo mafita ya sa silar shiryuwar kenan, mun kasa gane samarin zamani a koyaushe bukatarsu ɗaya ce ga mace, matukar baki bari suna taɓa ki ko kina tura musu hotunan jikinki ko ma kuna aikata laifin musayen kalaman da basu chanchanta ba to ba soyayya ba ce ko kuma baki son su ne, mata dayawa saboda suna so su yi auren gani suke ba komai bane sai bayan saurayi ya yaudari mace sai ya gudu ya barta wasu ma kan yi tutiyar ba za su auri 'yar iska ba... Na kasa gane Meyasa gani ga wane ya kasa zamewa 'yan matanmu ishara""" Girgiza kai Hajiya Tani ke yi Hudah tace a hankali """Allah dai ya dubi bayan mu ya shirya mana zuri'a"" Suka amsa da Ameen." "Wasa wasa Hajiya sai da ta yini gidan kaman ba ita ba, da yamma sai ga Mu'azzam shi bai ma san tana nan ba amma ganinsu tare ya matuƙar sanya shi farin ciki, roƙon Daddy Z yayi ta yi akan yayi haƙuri don Allah ya bashi Hudah wallahi ba zai taɓa sake aikata kuskuren da ya aikata a baya ba, kwarai a yanzu sun gamsu yana son Hudah don bai taɓa tsallake rana bai zo" gidan ya yi magiya ba. Hudah Daddy Z ya ƙira yayi musu nasiha a tare kan ya tambayeta """Kina jin za ki iya komawa gidan Mu'azzam Hudah?""" "Kanta ƙasa ta gyaɗa a hankali ""Alhamdulillah, sai ki fara shirin komawa""" """Daddy don Allah ina son sai bayan mun je legos mun dawo bikin Yaya Zaitoon""" Ya miƙe tsaye """Wannan tsakaninki da Mijinki""" "Yana kai nan ya fita, Mu'azzam ya matso ya riƙe hannunta" """Ko birnin Sin kika ce za ki je ki dawo kan ki koma dakinki ni mai amincewa ne Hudah bare auren ɗiyar Aunty kubrah, haƙiƙa macen ƙwarai daban take Hudah ribar haƙuri da Allah yayi ta maimaitawa shi kika samu tunda ya gama mallaka miki Mu'azzam daga kan zuciya zuwa gangar jiki da ruhi, da a ce baki yi haƙuri ba kina bin mahaifiyata a kullum kuna kai ruwa rana ko kina rama kalamanta mugaye a kanki da kin jima da ficewa daga raina saboda duk lalacewar" "uwa ita ɗin uwa ce! Na yaba miki kwarai na kuma gode da gudumawarki a rayuwata""" Murmushi tayi a hankali tace """Ba kowani abu bane hayaniya ke resolving and ai Hajiya ta gama min komai tunda ta haifa mini kai""" Shima murmushi yake cike da farin cikin yau Hudah ta kulashi don ta bi umurnin iyayenta ne ta daina kulashi itama har sai da yau Daddy Z yayi mata nuni da cewa zata iya tunda ya sahale musu komawa gidansu. **** "Ta ɓangaren Amal shi karan kanshi Daddy mamakin halin Amal yake Dukda an ce mai hali baya fasa halinshi Hajiya kamila dai jiya e yau don ta kasa cire hassada da kyashin Momma a ranta gani take ta fita a komai, a maimakon tayi kishi irin na matan annabawa kullum mita da ƙorafi, daga Nadiya har Amal su kan je wurin Momma da bata taɓa nuna musu kyara ko kiyayya ba, hasali ma tana son Ayman kaman Hudah ko Hibba ce suka haife shi, kasancewar babu Hibbah a yanzu rigima ya fi yawa tsakanin Hajiya karima da Hajiya kamila idan Hajiya kamila ta makawa Hajiya Karima magana akan yaranta suna zaune sun kasa auruwa ita kuma Hajiya karima sai ta rama kan nata yaran tana godiya ga Allah da nuna da irin auren jeka ka dawo" madoki ko matsafi gwara mata basu yi ba. "Daddy dai yayi iya yinshi akan gidanshi ya rabu da su, kuma Alhamdulillah yanzu har Najeeb kan kira shi ya gaishe shi amma bai taɓa zuwa gidan ba, ya kan kira momma ma su gaisa kasancewar ya san farar zuciyarta wanda hakan ma sai da ya tada hatsaniya tsakanin momman da Hajiya karima ai Momma ta yi musu shishigi saboda ta san shine babban ɗa komai na Daddy zai iya komawa hannunshi nan da lokaci kankani, ita dai Momma kaman koyaushe bata wani kulata ba inda daga karshe ma hankalinta ya karkata ga shirye shiryen auren Zaitoon" da ya zo musu da tarin farin ciki. "Saura sati biyu auren Momma, Aunty husna, Hudah da twins ɗinta, matar Daddy Rabi'u uwargidan, Mumtaz, Aina'u da Fadeel&fareed suka dira filin tashi da saukan jirgi na Namdi" azikwe dake birnin legos. A babban jeeb mai tsawo Ya Abdul da Hibbah suka zo tarar su don ta yi kewarsu kwarai musamman twins ɗinta na wurin Hudah da take jinsu wane ita ce ta haife su. Buɗe motar tayi za ta sauƙa Ya Abdul ya tsayar da ita """Wai ke kam zumudi ba zai ƙare ba Hibbah?""" "Ta waigo a wata gudan nan da doriya ta ƙara kyau da haske musamman skin care da ta chanza ga kulawa da take samu ga Usaib da yanzu bata jin da na biyunshi cikin zuciyarta na sangartata yana riritata sai ta zama tamkar wata sabuwar halitta, sanye take da doguwar riga Abaya pink bata saka gyalen shi ba sai ta ɗora Jersey vail a kai very simple but demure, Shagwaɓe fuska" tayi """Ya Abdul ka kuwa san yadda nake kewan su? Wlh kaman na fire na taro su daga Kano i just want to see my cute cute babies""" Yadda tayi maganan sai da yayi dariya. """Allah ya kyauta miki Hibbah! Toh ga su chan sai ki je ki gansu""" Zaro ido tayi tana kallon Window ganin su ɗin ne da gaske ta balle murfin motar ta fita da sauri ta nufi Mumtaz da Aina'u da kowanne ke rungume da yaro guda. """Oyoyo my babieessss""" Ta haɗa su su biyu ta rungume tana shakar kamshinsu. """I missed you so much Girls ina Fatan Nanny ɗinku Hudah ba ta wahalar min da ku""" "Duk dariya suka saki Hudah ta kai mata bugu Aunty husna na cewa ""Sannu Hibbah mu kam ba'a ta mu, sai ta yaranki""" Tayi murmushi tace """Sannunku da zuwa Aunty, Momma barkanku da isowa ai ni yarana kawai nake iya hange"" ""Za ki ji da shi Hibbah, don wulakanci yarinya ta gama wahalar nakuda da raino ki kirata Nanny?""" Tana dariya ta ce """Momma ai nannyn ce don biyanta nayi ta haifa min yaran, kyaunta ma in kirata surrogate mother""" Da wannan hira suka isa mota Abdul na musu sannu da zuwa. Daga nan basu zame ko ina ba sai gida inda Aunty Kubra da Aunty Asiya itama da familes ɗinta da tun jiya suka sauƙa suka shiga yi musu maraba cikin murnan ganin juna. "Tuni gida kam ya cike aka shiga fara hidima ba ji ba gani don Zaitoon ɗiyar gata ce, ita kaɗai" Aunty Kubra da mahaifinta za su aurar ita ce na farko kuma na karshe gata ƙanwar maza. "An yi events iri iri, a wurin Dinner ne Hibbah na zaune rungume da Yumna da Amna wasu 'yan uwan su Zaitoon suka zo wucewa sai suka tsaya kallonta" """Hibbah yaran nan sun yi miki kyau kaman ke ce mahaifiyarsu""" Ta Yi murmushi politely tace """Ai ni ce ɗin don abin da yayi twinee shi ya yi ni""" Ɗayar tace """Uhmm naka dai daban yake ai gwara ku ma ku zo ku shiga daga ciki kina zaune har 'yan" "biyunki na ta sulmiyo ƴaƴa""" Huda ta kallesu don yadda suka yi maganan doesn't sound right Hibbah ta yi murmushi """Soon in shaa Allah kar ku samu damuwa ina fata kowacce za ta shirya na ƙasan akwatin zuwa" "Kano""" Wucewa suka yi suna dariya ɗayar na cewa """Ka ji min Hibbah auren ne sai an shirya na ƙasan akwati?""" Da wasa suke dariyar amma Hibbah ta ji ba daaɗi ƙasan ranta ta kalli yaran sai kawai ta yi "shiru, Hudah don son kauda maganan tace" """Twinee ina labarin Usaib? Tunda aka fara bikin nan ban ga ya zo ba kuma ni ban taɓa ji kun yi waya ba""" Murmushi Hibbah ta yi """Ba Ya ƙasar ya tafi wani aiki Sydney amma muna waya ta facetime ke ce baki taɓa kula ba, ai na faɗa miki Usaib duk yadda zan fasalta kirkinshi ba zai fasaltu ba ko Aunty Kubra da yanzu za taji muna magananshi da ta fara yabon shi, ba zan ce ya fi duk samarina na baya ba amma daban yake ni har yana saka ni tunani don bai taɓa fushi da ni ba, bai taɓa nuna bacin rai kan wani abu da zan mishi ba kaman marar zuciya haka yake bi na... Saɓanin sauran samari wlh" "shi ba za ki same shi da son taɓa jikina ko maganan banza a gareni ba""" """Alhamdulillah""" Hudah dake ta murmushi ta ambata """In shaa Allahu kukanki ya zo karshe kaman yadda muke ta adu'a kullum twinee""" Tayi murmushi """Ai babu yadda Allah ba ya lamarinsa ni da kika ba ni labarin sauyawar sirikarki kwana nayi ina yi wa Allah kirari abin da ba zai yi ba babu shi wlh, Allah dai ya kara tsarkake mana zuciya ya ƙara mana imani""" "An sada Amarya da ɗakinta Dukda da nisa sossai tsakani don chan lekki gidanta yake, gida ne mai kyau da tsari an kawatashi fasali na kuɗin gaske mai kwanciya a rai, bayan auren da one week su Momma suka koma Hibbah kaman ta bi su amma babu hali saboda makaranta har" kukan rabuwa da su Amna tayi. "Idanunta sun yi Red haka suka dawo daga airport Ya Abdul da Ya Nasir suna ta aikin rarrashi," tana shiga ɗaki sai ga kiran Usaib... "*Littafin nan na kuɗi ne ki biya Naira Ɗari biyar (500) kachal domin kasancewa cikin masu kwasar tarin ilimi, faɗakarwa da zazzafar soyayya mai cike da sadaukarwa da aka zube ciki. Za ki biya ta wannan asusun" 0545475847 Gt bank Fatima Muhammad Gurin Sai ki tura shaidar biya zuwa wannan layi 09039206763 Ko kuma katin MTN na Naira 500 cikin wannan layi na sama sai ki tura da shaidar biya ta same layi. Sai na ji ku* Gureenjoh 29 """Subhallah! My Queen me ya samu idanunki? Kuka kika yi?""" "Tsabar Shagwaɓa sai ta sake fara sabon hawaye, ya runtse idanu yana ɓata fuska alamun baya son kukan yana gyara wayan yadda zai kalli fuskarta da kyau ya ce" """OMG Hibbah please...! Tafiyar su Momma ne ya saka ki hawaye?""" Kai ta gyaɗa """I will Miss my babies""" Murmushi ya saki """Kar ki damu soon zan ɗauke ki in mayar da ke Kano, in kuma baki nawa twins ɗin yadda babu mai raba ku har ki yi kuka kin ji?""" Baki ta taɓe kaɗan. """Ki fito waje ki karɓi saƙo"" ""Saƙon menene?""" """Ke dai ya ce min ya shiga harabar gidanku tun ma lokacin da kuke dawowa daga rakiyar su Momma fita ki gani""" "Dama bata cire komai na jikinta ba kuma rufe take daidai misali ta miƙe rike da wayan ta fito bata haɗu da kowa ba har tsakar gidan, wata mota ta gani mai ɗan duhun glass ta nufi motar tana cewa" """Na fito""" Glass na motar aka shiga saukewa kawai sai suka haɗa idanu ta zaro nata cikin mamaki Dariya yake mata ta zagaye ta shiga motar ta zauna. """What a surprise!! Yaushe ka dawo shine ko ka gayamin?""" Yana murmushi idanunshi a kanta yace """It's a surprise kaman yadda kika faɗa and bukatata ta biya da farin cikin wannan kyakyawar fuskar""" """Ka ga wani saɓani, twinee sai tambayarka take amma suna tafiya kana dawowa. Welcome back dear...!""" Shiru yayi yana ta kallonta kawai da idanunshi har sai da ta shiga jin wani iri a jikinta ta ɗauke idanunta ta sake mayarwa har lokacin yana kallonta tace cikin kunya """Me ya faru kake kallona haka?""" Cikin Muryar da yayi ƙasa yace """I missed you like Crazy my love... Ji nake kaman in rungumeki kaɗan ko zan samu sauƙin abin" "da nake ji a yanzu haka""" "Tayi murmushi bata ce komai ba, ya kai hannu a hankali ya riƙe hannunta da ɗan sauri ta kalleshi ya kankantar da idanu cikin yanayin tausayi yace" """Things are Hard for me please ki bari ko hannunki na riƙe ko zan samu sauƙi!""" Wasa da hannun ya shiga yi za ta zame ya saƙe rikewa """kin fa waye love, you are educated, smart and beautiful.. Riƙe hannu ba komai bane a" "soyayya, ba don gudun laifi ba i could have hug you...! Just a hug""" "Hannunta ta zame tana jin yadda gabanta ke ɗan faɗuwa yanayin fuskarta na ɗan sauyawa amma bata iya ta hana shi ko ta ce komai ba, ya matso ta sossai da niyyar rungumeta ta dakatar da shi sai kawai ta zame hannunta ta sauƙa a motar tayi cikin gida ba tare da ta ce" mishi komai ba. Ya jima yana kallon hanyar da ta bi kan yayi murmushi ya juya baya ya ɗauki wani gift box da bonquet da aka yi da 1-1k zai iya yin bundles huɗu ko biyar yayi kyau sossai ya fito ya ba mai gadi akan ya shigar mata daga nan ya dawo mota ya ja ya tafi. "A parlor ta zube bata haura ba ta riƙe hannunta da ya riƙe cike da tunani, she was a victim na yaudara, she once thought cewa riƙe hannu, runguma duk wayewa ce a soyayya and illar da hakan ya yi mata har yanzu bata warke ba, why suddenly Usaib zai fara hakan? Bai mata maganan aure ba bare ta ce ita ce ta ƙi sai ta gama school, ta rasa ma kalar tunanin da zata yi amma zuciyarta na tabbatar mata babu abin da Usaib zai nema a jikinta a yanzu don bai taɓa taɓa jikinta ba sai yau, kila yanayi ne na maza hakan da ya kasa controlling tana shirin Miƙewa" ta haura sai ga security ɗinsu da saƙon yana miƙa mata ma Aunty Kubra na fitowa. """Haa ina muka samu wannan kuma?""" Tana karɓa tace """Nima tambayar da nake mishi kenan Mommy yanzu na ganshi da su."" ""Ma Oga da kika dawo daga wurinshi yanzu shi ya aikoni""" """Usaib!""" "Ta faɗa a fili, shi kam ya juya ya tafi." "Mommy ta dube ta ""Ya dawo ashe?""" Kai Hibbah ta gyaɗa tana buɗe kwalin da tarin choculates da wasu sweets sai ɗan note ne ciki. """Am sorry love for not controlling myself earlier, ke kika ruɗa ni and i lost it am very sorry hope ba za'a yi fushi da bawan Allah ba?""" Murmushi ta ɗan yi kan ta ajiye saƙon ta ɗauki choculates ɗin da bonquet na kuɗin ta kai gaban mommy ta ajiye. """Me zan yi da su Hibbah? Ai wannan naki ne. Amma zan so in ga cewa soyayyar nan ba'a ja ta da nisa ba already kun fi watanni takwas zuwa tara a tare da Usaib, ina amfanin a zauna ayi ta soyayya bayan kuna da damar aure a yi mai hujja? Ya kamata ko isar da kanshi ne ya yi mahaifinki ya san da zamanshi Dukda mun yi zancen shi da mahaifiyarki kuma ta yi farin cikin hakan""" "A kunyace Hibbah ta ce ""Mommyyyy """ """Eh mana, ai gaskiya ce tunda zai iya zama nan zai iya kuma zama Kano aurenku ba zai hanaki karatu ba, ki samu ki gayamishi na ce yawon soyayyar nan a barta haka a fara zancen kai" "maganan gaba kuma""" """In shaa Allahu zan faɗa mishi Mommy""" "Ta miƙe da kayakin ta haura ɗakinta tana jin gidan ya mata girma, kewar Yaya Zaitoon duk ya cika ta." ***** "Hudah suna komawa aka fara shirye-shiryen komawarta dama bayan iyayenta ko su Hajiya kamila basu san matsala ce ya ajiye ta gida ba duk sun zaci wanka ne kawai ta zauna yi, kuma hakan ya yiwa Momma daaɗi don basu samu kofar gayamata maganganu marasa daaɗi a kan hakan ba, ko da Hudah suka zo suka kwana biyu duk ta bi ta musu sallama, har wurin Umma sai da ta je Dukda Umman ta fi shiri da Hibbah amma Hudah ma 'ya ta ɗauketa yini ta musu da dare Najeeb ya dawo da ita har ma ya tsaya ya ci abincin dare wurin Momma ya kuma ga" mahaifinshi wanda hakan ya saka shi cikin farin ciki ƙwarai da natsuwa. "Satin ta ɗaya da dawowa aka mata rakiya zuwa sabon gidanta da kowa yayi ta yabon gidan da yi musu Fatan alkhairi, sai Amal ta dinga tuna lokacin da suke mata habaice habaice akan zata zauna gida mai dakuna biyu da wurin parking ɗaya, a yanzu motocin da duk suka rakota wurin huɗu duk suna harabar gidan, tana rike da yaronta idanunta zube kan wasu sababbin furnitures da Mu'azzam din ya zubewa Hudah masu kyau, ga Hajiya Tani da kanta ta haɗa musu abincin tarba yayi ordering waenda ba za'a rasa ba, tana rungume da jikokinta ta shiga yi musu adu'a" akan sabon wurin da kuma rayuwar aure mai albarka. "Lallai Hudah ta yarda Hajiya ta sauya, har 'yan uwanta suka tafi tana tare da Hajiya da Yadikko" sai dare ɗan Kawu Mu'azzam din ya mayar da ita gida aka bar Angon karni da Amaryarsa Hudah. **** "Amal ta kasa riƙe kanta suna isa gida ta shige ɗaki ta fashe da kuka, sai da tayi ya isheta kan tayi shiru idanunta da suka kumbura suna kallon sama tana tuna ranar da aka yi shari'a na" ƙarshe da su Qasim. Tana tuna sadda ta fuskanceshi ya sauya ya chanza saboda azaba da baƙar wahala yana ɗaure da ankwa bayan an yanke musu hukuncin shekaru masu yawa gidan yari tare da tara bisa laifin kidnapping da kuma attempt murderer na infant da ko duniyar bai zo ba ta ce mishi """Kasim abin da ka zaɓa kenan? Yanzu menene ribarka? Yanzu kun yarda Allah ɗaya ne idan ba haka ba ina tsafin da bai iya ya ceceku daga girbar abin da kuka shuka ba? Laifina ne da na bi son zuciya na hangi kudi ba nagarta ba na aureka bisa son zuciyata amma shi wannan yaro me laifinshi? Me kake so in ce mishi dangane da mahaifinshi idan ya tambaya? Kaico na!"" Sossai take kuka wanda shima kukan yake yi kanshi ƙasa" Sai da aka kama su ya tabbatar duk wani tsafi ko tsubbanci a bayan ikon ubangiji yake suna da manya ita kanta Inna tana da manyan iyayen gida amma babu wanda ya bi ta kansu kar ma su "haɗa kai da su laifi ya shafesu, banda 'yan siyasa da Ƴan kasuwa da take hulda da su waenda" "za su iya fitar da ita amma kowa ya zame, tsafin ya kasa taimakon su zuciyarshi na zafi don bai san da gaske yana son Amal din ba sai da ta subuce nadama da kunyar ɗan shi na rufe shi don" a gaba dole duniya ta gayamishi ubanshi ya so yin kuɗi da shi tun bai san shi ba. """Ki yafe min Amal! Don Allah ki yafe min na san na aikata kuskure mai girma na niyyar kisa amma wallahi ban taɓa ba da wani a yi tsafi ba, zuciyata bata kekashe ba sai a lokacin da kwaɗayin arziki yayi min dafifi ciki, son kuɗi masifa ne matukar ba halal za ka dage ka nema ba wanda shi kuma sai da haƙuri da juriya, Ina so a ganni da muhimmanci ina so idan na isa wuri a san na zo, ina son daukaka da arzikin da zai saka manya dayawa dawowa karkashina ban sani ba ashe daga sanda tunanin son yin kuɗi mai yawa ya shige ni son zuciya ma ya aureni na yi" "nadama wallahi""" Idanunta ta ɗauke a kanshi """Ka yi wa Ubangiji alƙawari chanzawa kuma Allah ya sa nadamarka ta gaskiya ce wanda lokaci" "ne zai fallasa hakan! Na bar ka lafiya""" """Amal!""" "Ya kirata, ta waigo tana kallonshi" """Don Allah ko fuskar yaron ne ki nuna min don Allah""" """Baka chanchanci ganin fuskarshi ba Kasim, baka chanchanci komai daga yaron nan ba shi ɗin nawa ne ni kaɗai""" Tana kai ta tafi ta barshi yana kukan nadama. Yanzu ma shi take tunawa tana tuna ita kuma image ɗinta ya ɓaci anya akwai wanda zai iya aurenta bayan an san a farko auren kwaɗayi tayi ta haɗu da iftila'in Matsafi? Allah ya gani ta yi nadama kuma ta chanza tana roƙon Allah ya Musanya mata da alkhairinsa. **** """Hibbah karɓa kar ki tafi ciki babu komai""" "Da sauri ta karɓi silver cup ɗin mai hannu dake ɗauke da golden morn, Ya Abdul ne ya miƙa" mata. Momma ta ce """Kaman ka san yadda tayi letti ɗin nan idan ta fito ko kallon dining bata yi a je a yini da yunwa ta dawo tana kukan ciwon kirji""" Nasir dake breakfast yace """Ai mommy makaranta ba za ka yi shi ka gama babu wannan wahalallen ulcer ɗin ba, bare irin karatunmu""" Hira suka cigaba da yi don tuni ta tafi. "Yau take shirin ƙare exams na First semester 200lvl kwana ta yi karatu don Nasir ta saka a gaba har ya gaji ya gudu ya barta hakan ya sa ta yi letti sossai don haka Sharp Sharp ta wuce, idan ta tsaya traffic sai ta sha golden morn ɗin a haka kan ta isa ta gama sha ta sha ruwa tana" zuwa hall ta nufa kai tsaye ta gabatar da exams ɗinta hankali kwance tana fitowa a wannan ma sakon Usaib shi ya fara riskarta na mata barka da fitowa jarrabawa murmushi ta saki tana mishi reply a lokaci ɗaya tana nufar mota har ta yi nisa ta ji ana kiranta """Hey! Miss Hibbah""" Ta ɗan juyo course mate ɗinta ce Kausara yoruba ce kuma natsatsiya tana da kirki Dukda gaisuwa ke haɗa su sai wani aiki na makaranta. """Hi! Ya exams ɗin?""" "Ta faɗa da ɗan murmushi ""Alhamdulillah... Kin yar da abu""" "Ta miƙa mata Atm ɗinta da ya bi waya ya zame a sadda take zaro wayan daga jaka. ""Subhallah kai amma na gode you saved me from stress na bank""" "Ta karɓa tana godiya, ganin za ta wuce ta nemi su je ta rage mata hanya mana nan suka nufi" motarta suka fice daga makarantar. Bayan ta dawo gida tayi wanka ta yi bacci dab la'asar ta farka tayi sallah kan ta shiga shiri sai ga ƙiran Usaib. """My Queen ya gajiyar exams?"" ""Alhamdulillah wlh, kaman ka san kana raina""" Tun incidence da ya faru gab exams ɗinta da ta nuna mishi fushinta bai sake kai hannu jikinta ba da sunan soyayyar wayewa. Hakan ya sa a yanzu hankalinta ke kwance da shi tana jin cikin kowani lokaci za ta iya aurenshi. """Allah ya sa ba laifi Bawan Allah ya yi ba""" Ta saki murmushi """Laifin me za ka yi ai kai ba ka laifi, magana ne dai mai muhimmanci nake so mu yi"" ""Kina ina yanzu?""" Ta ce """Ina gida amma dama ina so zan je gidan Yaya Zaitoon ne sai kuma ina son zuwa shopping akwai abubuwan da ba ni da su. Za ka bari dare sai ka zo?""" Ya ce """No, ki bari zan zo sai in kai ki kin ga duk maganan da za mu yi kan mu dawo mun yi shi right?"" Kaman ba zata amince ba kuma sai ta amince." Tayi sallah ta idar ya kirata akan ya zo ta miƙe ta cire hijabin ta sanya gyalenta dayake atampha ce jikinta straight gown gyalen couscous ne ta yafa shi a kafada ta haɗa takalmi da handbag kalar gyalen emerald green ta gyara ɗaurin ta kan ta fito ta yiwa mommy sallama bata ma gaya mata ba da mota za ta fita ba Mommy na mata a dawo lafiya ta fice. "A waje ta samu motar shi ta shige ya ja suka fara tafiya a hankali cikin natsuwa, sai yabon shigarta yake da kyaun da tayi. Da gidan Yaya Zaitoon suka fara a chan sun sha hira daga ita har mijinta basu da matsala don haka sun jima sossai sun ci abinci tare kan suka fito ya kaita shopping dab Magrib ne bayan sun gama suna fitowa ana kiran Magrib, bata so Magrib ya mata" waje ba amma ya kama sai da tayi ɗin. Har sun shiga mota ya kunna wayanshi yana cire pin sai tace """Amma kaman ba gwara ka yi sallah a nan ba idan muka tafi kan mu isa ma lokacin zai iya fita."" ""Hakane lemme pray""" Ya ajiye wayan ya zari ruwan gora ya fice. Wayan ta kalla har ta ɗauke kai ganin zai mutu kuma ya shiga pin sai ta ɗauka hoton wallpapern na ɗauke mata ido murmushi ta saki ganin wani Eskimo dog ne fari tas karen ya yi mata kyau tana shirin ajiyewa ta ga wani sako ya shigo ta sama cikin wani group da ya ja hankalinta ta danna kai.... "*Littafin nan na kuɗi ne ki biya Naira Ɗari biyar (500) kachal domin kasancewa cikin masu kwasar tarin ilimi, faɗakarwa da zazzafar soyayya mai cike da sadaukarwa da aka zube ciki. Za ki biya ta wannan asusun" 0545475847 Gt bank Fatima Muhammad Gurin Sai ki tura shaidar biya zuwa wannan layi 09039206763 Ko kuma katin MTN na Naira 500 cikin wannan layi na sama sai ki tura da shaidar biya ta same layi. Sai na ji ku* Gureenjoh 30 """Playboys!""" "Ta maimaita sunan group chat ɗin, bugawar zuciyarta ne ke sauyawa a hankali a sadda ta shiga ciki tana ganin abin da suke tagging suke tattaunawa a kai, she's still calm ta danna hoton Dukda zuciyarta ya gama yardar mata da ita ce bata gaskata ba sai da ta gani ita ce zaune a parlorn Yaya Zaitoon an rubuta a ƙasan" """Clock it guys! Saura kiris you all make sure our bet is still on...""" "Lips ɗinta ke rawa a sadda ta buɗe baki da kyar ta maimaita ""Bet!""" Kwakwalwarta rudu ya shiga ta ma manta menene ma bet ɗin a hausance. Hannunta na wani irin tsuma ta janyo wayanta ta shiga contact sam bata san ma wanda ta kira ba ta dai ji namiji ne yana ambatar sunanta da kyar ta fusgo maganan """Don Allah me..ne..ne ma bet?""" """Chacha!""" "Abinda ta ji an ce kenan, tana scrolling tana gamuwa da duka pictures ɗinta da aka tura a group" "din, babu ranar da ta haɗu da shi da bai yi mata hoto ya tura proof na cewa the bet is still on ba." """Menene Chacha?""" "Abdul da ta kira ba tare da ta san ma shi ɗin bane ya ce ""Lafiyanki kam Hibbah?""" """Uhmm... Menene Chacha?""" """Duk wani abu da za'a sakawa kuɗi ko dai wani abu mai amfani ko ma kawai don ƙure wa abu a kan iya saka Chacha a kanshi idan ka yi nasara kai zaka ɗauki duk abin da aka ajiyewa wannan wasa""" "Zame wayan tayi tana kashewa, kwakwalwarta dab yake da bugawa ba'a maganan halin da" "zuciyarta ke ciki, bata iya gani da kyau da kyar take iya tsintar wasu messages ɗin." "Ta fahimci su bakwai ne a group din, dirty talks suke yi a kanta, a sadda ta koma farko abin da ya girgizata picture ɗinta ne da yayi escalating lokacin bikinta da Mahmud, farkon maganan kuma shine wanda ya tura musu ɗin ya fara" """Guys kun ga wata zazzafar update na ɗiyar wani Senator""" "Yabo da kuranta halitattarta suka shiga yi, wasu irin hawaye ne ke zuba mata uncontrollably, farkon maganan Usaib shine" """Ni jikin ya min wlh jiya har mafarkinta na yi, ko in nemeta in rage zafi ne tunda komai ya riga da" "ya faru na sani!""" Ɗaya daga cikinsu ya amsa da """Ka dai san wannan Babe ɗin zazzafa ce kuma a yanzu da abin nan ya faru she will never listen to you ko gidansu ba za'a barta ta sake fita ko wani kula samari a yanzu ba""" Wani ya ce """Kila ma ta shiryu fa don ai wanda ya saki updates ɗin ba shine ma mijin da ta shirya aura aka fasan ba""" Shi Usaib ya amsa """Koma menene to hell with it! I must taste her before my wedding don ba zan daina mafarkin jikin yarinyar nan ba matukar ba kashe kwaɗayi na nayi ba""" """You can't!""" "Wani ya faɗa a cikinsu ""Then try me""" Usaib ɗin yayi reply. """In ka isa kwallon shege ka gwada""" "Dariya ya tura, sauran suka cigaba da cewa ba zai iya ba shi kuma yana proving musu sai dai" "bai ga dama ba, a karshe ya amince don kawai ya nuna musu komai zai iya yi don ya sameta ya ɗanɗanata kaman yadda yake faɗa har da ko da kuwa aurenta zai yi ya saketa a ranar." "A lokacin bata san me take ji ba, tafasa take, panic ta samu, kuka zata yi ko ihuuu ta dai san" "zuciyarta na ciwo, dab yake da fashewa saboda yadda yake kumbura yake fesar mata da hucin" "zafi, kuma bata daina bibiyar chats ɗin ba, har ranar da ya samu taɓa hannunta sai da ya basu" "labari, daga farcen kafarta har gashin kanta rawa yake, ta jiƙe shakaf da wani irin zufa Dukda" yanayi na sanyi da ake ciki a legos na ruwa cikin ko wani dakika. "Bata san ya shigo ba sai fusge wayan da yayi a hannunta, ta ɗago idanunta da suka juye zuwa wata halitta ta daban ta kalleshi, numfashi na escaping daga Bakinta cikin hucin turirin zafi... ""Me kike yi min da waya?""" "Tambayar ya dirar mata a tsakar ka ta ji shi wani iri, Muryar yayi mata kama da na wani dodo ko" mummunan halitta na daban. Muryarta na fita cikin cracks da kana iya jin tsananin ciwon dake zuciyarta ta shiga cewa """A'a...! A'a... Wannan ba gaskiya ba ne...""" "Kallonta kawai yake bai ce komai ba ""Usaib ba gaskiya ba ne """ Hannayenta ta sa ta bubbuga kanta duk biyu da karfin gaske kila mafarki take amma raɗaɗin zafi da ya ziyarceta ya tabbatar mata da gaske ne ba mafarki ba. """Usaib Ni...Ni ce Abar chacharku? So You were playing me all this while? Usaibbb. """ Numfashi take sama sama tamkar mai ciwon asthma hawaye uku huɗu ke bin idanunta """Usaib so duka komai ƙarya ne?? Komai kƙarya ne? Ɗazu nan you Said you loved me. ! Ka ce" ba zaka iya rayuwa babu ni ba ! Ka ce za ka so ni har karshen numfashinmu what happened "to that usaibbbbb!""" Da ihu ta ƙarasa tana fashewa da wani masifaffen kuka mai rikitarwa. """Hibbah""" Ya ƙira sunanta shamlessly Kuka kawai take tamkar ranta zai fita """Ki yarda da abin da zan faɗa miki wlh da gaske ina son ki, da farko na yarda wasa ne amma after all what happened na faɗa soyayyarki kuma aurenki """ """Shutttt uppppp Usaib!!!""" Ihun gaske take yi akan muryarta. """ƙarya kake yi Ƙarya kake yi Usaib""" Cikin kuka ta cigaba """Ashe na zama wasan kwaikwayo ban sani ba Duk abin da ya faru tsakanina da kai a shirye" "yake tamkar shirin film, you came to me as coincidence ka shigar da kanka ta ƙarfin tsiya cikin rayuwata Usaib har na amince maka a tunanina mun kulla tsaftacecciyar soyayya ne ashe duk ba haka bane Usaib """ Ta dakata tana kuka sossai hannunta ɗaya dafe da zuciyarta bata damu da irin hawaye da majinar dake zuba mata ba she's deeply hurt ta ce da karfi """Ka yi hakan ne kawai just to have sex with me You shameless useless stupic lunatic" "being Usaib what happened to every single thing you've ever said to me?""" Bai wani shiga panic ba saboda dama asalin dan duniya ne Matasa ne da basu damu da "damuwar kowa ba sai jin daaɗin rayuwa," """Ni namiji ne Hibbah, Its our nature to feel lust on ur gender... Halittarki na gani na ji ya min na biyo ki, ni ban ga wani abin ɗaga hankali da ihu ba...! Kina tunanin akwai namiji da zai iya sonki da gaske a haka? Sai dai son abin da idanunshi suka gani na daga wasu sassa naki... Idan kika ce za ki ci gaba da zama a shirye preaching up and down you will live Lonely and die single my" "dear...""" "Bakinta sake hawaye na cigaba da kwarara mata ta ce ""U..s...aib""" """Yes I mean what am saying, kar ki yi tunanin ɗaura alhakin abin da ba ni na fara ba kaina, i was trying to do you a favour don babu lafiyayyiyar macen da zata balaga ta san namiji kuma ta dawo tace ta zauna pure babu abin da ke damunta na daga sha'awa b. """ Wani mahaukacin mari ta sauƙe mishi da sai da karar ya ratsa motar. Jikinta sai kaɗuwa yake numfashinta kaman zai fita tana kwato shi tana so tayi magana amma sai in-ina take tana jan ajiyar zuciya... Ya shafo marin ya ɗan yi pecking hannun da ya shafon ya saki murmushi. """Ban taɓa tunanin you are this shameless ba Hibbah, kina tunanin don kin fahimci manufata a kanki zai sa in kama kuka a tare da ke? Nah! Har yanzu kina da sauran karatu a kan da namiji my dear...""" Cikin wata hautsinanniyar murya ta shiga cewa """Na gode Usaib! Thank you for all the pains you've caused for me, Ina roƙon ubangiji da ya halicci namiji da mace yayi sama da ƙasa ya sa a yi wa ƙanwarka...! Ɗiyarka ko ma mahaifiyarka daidai da abin da ka yi mini Usaib...""" "Ta buɗe motar kawai ta fita, da karfin gaske take kokarin hada kuzarinta ta shiga tafiya ba tare da ta san inda take jefa kafafunta ba, sossai take tafiya tana kuka kaman mahaukaciya cikin murya mai sauti, kila za ta zauce, kila kuma mutuwa zata yi a yau don ciwon da take ji ya fi" kowani irin ciwo azaba a rayuwarta. Bata san iya adadin tafiyar da tayi ba ta dai ji ruwa na sauƙa a kanta bata damu ba har sai da ta ji kafafunta ba za su iya ɗaukarta ba kan ta sulale kan wani dutse ta zauna hannayenta na kaiwa ƙasa cikin ruwan da ya taru a wurin ta cigaba da kuka on top of her voice ko damuwar da "take ji zai ragu, kila in tayi ta kuka da murya za ta daina jin kanta kaman zai buɗe..." **** "Tun bayan kashe wayan Abdul ke ta kira bata picking, ya ɗago ya dubi Mommy ""Mommy ina yarinyar nan ta ce zata je ne?""" """Gidan Zaitoon sai shopping""" "Mommyn ta amsa hankalinta na kan Tv, Nasir ya ɗago ya kalleshi ""Wani abu ne Yaya?""" """Meyasa ta hau motar kasuwa bayan ga motoci a gidan nan?""" Sai a lokacin ma Momma ta kalleshi """Motar kasuwa kuma? Bata fita da mota ba?""" """Motarta na waje, na yi mamakin ganin call ɗinta don na ma zaci she's home""" "Yana maganan yana kiran Zaitoon ko da ta ɗaga bai amsa gaisuwarta ba yace ""Ina Hibbah?""" """Sun tafi ai tun yamma"" ""Su? Ita da wa??""" "Ya tambaya ""Ita da Usaib...""" """Whatt??""" Nasir ya faɗa mommy ta miƙe tsaye """Da yaron nan Hibbah ta fita dama bata faɗa min ba?""" "Abdul ranshi yayi mugun ɓaci haka Nasir, Meyasa za ta fita da namijin da ba ma muharraminta ba gashi yanzu har ana shirin isha basu dawo gida ba?" "Layinta suka cigaba da kira amma kiran duniya ba'a picking, Layin Usaib ɗin ya karɓa wurin Mommy suka cigaba da kira shi kam ma user busy yake ta saka musu duka sun gwada da layukansu samething. A lokacin Mommy hankalinta ya gama tashi don a jikinta take jin ba lafiya" ba. "Tracker Abdul ya shiga yana duba Allah sa location ɗinta is on, ganin inda take ya sake ɗaga mishi hankali da sauri ya zari keyn mota Mommy ta janyo mayafi Dukda sun so ta zauna amma ta nuna ba zata iya zama ba gwara taje ta ga me nene ke faruwa, Nasir ne a gaba mommy ta shiga baya yayinda Abdul ke driving da speed sossai, ruwan da ake ta tsula wa ya rage yawaitar ababen hawan hakan ya sa tafiyar mintuna Arba'in ya kaisu inda wayar ke blinking" Red. Basu damu da ruwan ba don damuwarsu su tabbatar tana lafiya? Ko da suka fito suka fara dube dube Nasir ne yayi tuntube da wayarta """Innalillahi wainna ilaihi rajiun...! Me ke faruwa? Na shiga uku ni Kubra me ya samu Hibbah?"" Mommy ta faɗa cikin kuka a sadda Abdul ya dawo da mayafinta da posanta ƙarami ga wayanta. ""ko kidnappers ne suka sace ta?""" Nasir ya faɗa shima tension ɗin shi na karuwa. Abdul da kiris ya rage ya fara taya Mommy kuka ya ce """No way! Ba kidnapping bane mu cigaba da dubata ina ji kaman bata yi nisa ba"" A tare suka cigaba da dubata suna kiran sunanta da karfi""" "Figure ɗinta Abdul ya fara hanga yayi tapping mommy yana nuna mata ita, da gudu suka ƙarasa kanta tana kwance a ƙasa a wurin cikin ruwan lifelessly don ta jima da passing out a rikice Abdul ya saɓeta suka yi mota a maimakon hankalin Aunty Kubra ya kwanta ai sai ya ƙarasa tashi kar a ce hibbah ta mutu! Garin yaya? Me ya sameta? Ina shi Usaib ɗin? Duk basu" sani ba gashi babu wani abu dake harbawa a jikinta na masu rai..... "*Littafin nan na kuɗi ne ki biya Naira Ɗari biyar (500) kachal domin kasancewa cikin masu kwasar tarin ilimi, faɗakarwa da zazzafar soyayya mai cike da sadaukarwa da aka zube ciki. Za ki biya ta wannan asusun" 0545475847 Gt bank Fatima Muhammad Gurin Sai ki tura shaidar biya zuwa wannan layi 09039206763 Ko kuma katin MTN na Naira 500 cikin wannan layi na sama sai ki tura da shaidar biya ta same layi. Sai na ji ku* Gureenjoh 31 """Mommy don Allah ki daina wannan kukan za ta samu lafiya""" "Nasir ya faɗa yana riƙe hannun Aunty kubrah da tun da suka zo asibitin sama da awa kenan bata daina zubar da hawaye ba, tuni Zaitoon da mijinta ma sun iso cikin mamakin abin da ya faru don dai sun san sun bar gidansu ma lafiya ƙalau." """Nasir na ji zata samu lafiya, fargabata me ya sameta? Idan wani illa yaron nan yayi mata me zan cewa iyayenta?""" Abdul ya ce """Babu abin da ya faru in shaa Allahu na ashsha Mommy, ina tunanin kawai yayi breakingup da ita ne""" """Breakup all of a sudden Ya Abdul? Amma idan haka ne bai kyauta ba, bai dubi ciwon dake damfare da zuciyar Hibbah ba, me ta mishi da zafi zai so ta ya saka zuciyarta koyon sonshi then ya yi dumping ɗinta??""" "Zaitoon ta faɗa bata san hawaye ma na bin fuskarta ba don ji tayi tamkar ita ce a takalmin hibbar, she went through a lot akan samari da maza, Meyasa wannan ma zai illatar mata da zuciya?" """Ina tunanin wani abu because last da muka yi magana she was tensed asking me menene Chacha, Maybe Godforbid wani abu daban ya hara daga gareta Allah ya tona masa asiri""" A zafafe Nasir ya ce """Amma tabbas idan ya tabbata haka ne sai na yi ƙarar yaron nan duk kuwa inda zai shiga a" "duniya, wani irin rashin imani ne wannan? Bet??""" A maimakon ma hankalin Mommy ya kwanta sai sake tashi ya yi don ko da likitoci suka fito wurin awanni uku a kanta sun tabbatar musu jikinta yayi tsanani ciwon zuciyarta ya ƙara stage ɗaya daga yadda yake so yayi weak sossai amma sun ɗora ta kan wasu medications tana kuma kan allurar bacci sai ta huta sossai za ta farka ko zuwa gobe da dare. "A dole suka bar asibitin suka tafi saboda private ce mai tsarin waje da ba'a barin patient relative kwana, Nasir ne ya nemi sanin babu wani external injurie ko wani assault a jikinta? Abdul ya gyaɗa kai cikin son tabbatar da babu abin da ya sameta ɗin bayan Breakup, likitocin sun tabbatar bayan matsalar zuciyar babu wani abu da ya sameta external sun yi godiya kan suka" bar asibitin. "Abdul ne ya hana Mommy faɗawa su Daddy halin da Hibbah take ciki akan a bari zuwa gobe a gani kar su gagara bacci sannan me za ta ce musu ma idan ta kira? Hibbah ta fita da wani an sameta a yashe? A bari a samu hujja mai karfi tukuna, haka bata kira ɗin ba amma ita kanta daren ta kashe shi kan sallaya tana yi wa Hibbah adu'ar samun lafiya da kuma bata abokin" zama na gari da zai share mata hawayen wannan rayuwa da tayi ta gani akan soyayya. "Washegari tun safe Mommy ta wuce asibitin yayinda su Nasir suka tafi aiki akan sai sun taso za su shiga asibitin, a ɗakin ta zauna tana tasbihi da nemawa Hibbah dake kwance cikin kayan asibitin fari mai ratsin baki baki lafiya. Kaman yadda likitoci suka faɗa sai misalin shidda na Yamma Hibbah ta fara motsi alamun farkawa, a lokacin duk su huɗu suna a ɗakin a hankali ta shiga buɗe idanunta da suka yi mata nauyi, ɗakin ta cigaba da bi da idanu nan ta fahimci tana kwance ne a gadon asibiti, lumshe idanu tayi tana tuna abin da ya wakana tsakanin ta da Usaib," wani irin zafi da raɗaɗi ne ke ratsa zuciyarta. "Sautin kukanta shi ya janyo hankulansu duka kanta Zaitoon ta fita da sauri don kiran likita yayinda Mommy tazo tana share mata hawayen dake bin gefen idanunta duk su uku suna jera mata Sannu, bata ce komai ba sai hawayen da ya cigaba da bin idanunta mommy na daukewa tana nata hawayen na tausayi har ma'aikatan jinyan suka shigo, su suka taimaka mata zuwa" zaune. """Hibbatullah Sannu!"" Likita macen ta faɗa" Idanu Hibbah ta ɗan buɗe ta kalleta kan ta ɗauke tana gyaɗa kai. """Ki yi kukanki let your worries out don rashin kukan shi zai kara affecting zuciyarki amma ki sani lafiyanki ya fi gaban komai, ki sani lafiyarki ya fi tsada fiye da duk wani abu da zai faru da ke a wannan rayuwa, kar ki ba da daman koma menene yayi miki illa ta har abada saboda duk wanda zai yi hurting zuciyarki bai chanchanci hawayenki ba, bai chanchanci ki sanya damuwanshi a ranki ba har ya azabtar dake. Na sani koma menene da ciwo amma focus on yourself, ki so kanki kema kaman yadda suka so kansu wurin cutar da ke, I am a talk therapist kofa a buɗe take idan kina son shawarwari ko kina son fitar da abin da ke ranki i promise to help" "but don't depressed yourself kin ji?""" "Sossai magananumta sun taimaka don ta ji ƙwarin gwiwa kuma ta tabbatar Usaib bai chanchanci hawayenta ba, abin da take yi wa kuka baƙin cikin galaba da ya samu a kanta na shigar da kanshi cikin zuciyarta ne, allurai suka yi mata a canula suka cire drip ɗin suka yi" umurnin a bata wani abu mai zafi ta ci ko ta sha. "Zaitoon ne ta taimaka mata tayi brush har lokacin bata ce komai ba, bayan sun dawo Abdul da ya haɗa mata tea mai kauri ya zauna bakin gadon ya dauki teaspoon ya shiga bata dashi, bata ƙi ba ta cigaba da karɓa, ganin ta kusa shanye wa Nasir ya zuba mata abinci, Abdul na gama" "bata ya karɓi kofin ya miƙa mishi plate ɗin, kaɗan ta ci ta kau da kai." """Hibbah""" Aunty Kubra ta kirata """Me ya faru Hibbah? Meyasa za ki min haka? Meyasa za ki fita da Usaib ba tare da kin sanar min ba?""" Idanunta ta ɗaga sama tana ɗan taune lip ɗinta so take ta mayar da kukan dake shirin zuwa mata amma hawayen sai da ya gangaro a hankali tace """Ki yi haƙuri ba zan sake ba Mommy, ban san cewa fitan zai ɓata ranki ba""" Riƙe hannunta ɗaya Aunty Kubra ta yi """Ba ɓata min rai yayi ba, Hibba yanayin da muka sameki ne ya tsorata mu Allah Astagfirullah da wani abu daban ne ya sameki ba fata ba ya kike tunanin zan fuskanci iyayenki? Ya kyautu in ce musu ban ma san da wani kika fita ba? Me Usaib ɗin yayi miki?""" """Mommy azzalumi ne shi ya cutar da ni ba zan taɓa yafe mishi ba duniya da lahira... Mommy ashe Usaib bai taɓa so na ba? Ashe tun farkon Shigowarshi rayuwata komai shiri ne? Ya tsara komai don kawai yayi winning ɗina ba ma ta hanyar aure ba sai ta hanyar banza? Ba laifinshi bane komai nawa ne kuskurena ne ke hunting ɗina...amma ai na ce na tuba Meyasa mutane ba za su ji a ransu cewa ba su na yi wa laifi ba Allahn kuma da na yi wa ina ji a zuciyata cewa ya riga ya yafe min? Meyasa mutane suke amfani da kuskure wurin illata zuƙatan bayin Allah?""" Hawayenta Aunty Kubra ta share mata """Jarrabawa ce Hibbah, tabbas komai mai wucewa ne. Duk wanda kika ga baki aura ba ba mijinki ba ne Hibbah ki ƙara haƙuri ki kuma godewa Allah da bai sa kin auri mai irin wannan zuciyar ta yaudara ba""" Girgiza kai take yi """Bana son su, ba zan taɓa sake son wani ba na gaji...ai auren ba dole bane Mommy"" Abdul ya katse ta." """Kar ki ce haka Hibbah, ai ba duk aka taru aka zama ɗaya ba. Sannan baki da laifi don kin sake buɗewa wani zuciyarki...""" "Ya riƙe hannunta ɗaya don girgiza kai take tana nuna mishi ba zai yiwu ba a hankali ya ce ""Allah ya kwantar miki da zuciya, ya baki natsuwa, ya maye miki duk wata damuwa da farin ciki. Take your time Hibbah ban ce dole a yanzu bane za ki so wani amma ki sani wannan hujjar ba shi zai sa ki ce ba za ki yi aure ba ko ba za ki sake son wani da namiji ba and please be gentle with yourself, kar ki bari wannan abu ya illata rayuwarki ko ya taɓa cigabanki a rayuwa if you" "feel diaturbed or get confused, If you ever need to talk about anything, I'm always here.""" "Sossai take samun natsuwa da family ɗinta da suke zagaye da ita, tana iya hangar damuwarta da suke tayata shearing a kan fuskokinsu don Nasir kam ma hawaye yayi ta yi sai da kyar ya yi" magana """Allah zai saka miki ƙanwata, ba ke kaɗai Usaib ya zalunta ba har mu ɗin nan ya ɗauki alhakinmu at First na yi miki murna duk a zatona wannan karo kin samu mai share miki hawaye ashe ban sani ba kallon biri muke masa yana yi mana na ayaba, ashe shi ɗin kura ne lullube da fatar akuya. Kaiconshi!""" "Sossai ya ji ciwon wannan abu, ya sassauta murya ""Hibbah kin san menene?""" Ta girgiza """Ki ce Alhamdulillah da Allah bai sa sai da kika aureshi kika gane wanene shi ba, you are too good for him, ki sa a ranki ba ya cikin ƙaddara ki na alkhairi because If he was meant for you u would have been his wife by now. Ki sanyawa zuciyarki cewa 'What is not mine cannot stay in my heart' ki cigaba da rayuwarki kaman komai bai faru ba Don't blame yourself, don't cry harder Ok?""" "Dukda bata ji kaman za ta iya daukar hakan ba komai ba don kaman kuna ne da ba zai taɓa warkewa ba amma wani ɓangare na zuciyarta yayi sanyi, kulawa da damuwar da 'yan uwan nata suka nuna mata cike da so suka kuma yi kokarin ganin sun raba damuwar a tsakaninsu yayi matukar tasiri a ranta, suna nan har dare kowa na bata baki kan Mommy ta kira Daddy ta" faɗa mishi abin da ke faruwa. "Shiru yayi cikin rashin jin daaɗi haƙiƙa tausayin Hibbah bai taɓa fita a ranshi ba, bata kuma taɓa fita daga cikin adu'o'inshi ba kuma yana da tabbacin Allah zai kawo mata miji nagari wanda zai mantar da ita duk wani damuwa ko kukan da take kan yi a yanzu cikin rayuwarta." "Wayan ya sa aka bata ""Daddy...""" Ta faɗa tana mayar da kanta ƙasa hawayenta na diga """Mamana... Ki yi haƙuri kin ji? Ki yi haƙuri ki ƙara haƙuri babu abin da ba zai wuce ba!"" Yadda muryarshi yake tausarta ya saka zuciyarta sake karyewa ta saki kuka a hankali ya cigaba da rarrashinta har ta yi shiru kuma ta mishi alkawarin ba zata bari abin da ya faru ya hanata karatu ba don a yanzu shi ne abu daya da zai taimaka wurin sakata manta komai da" dawo mata da farin cikinta a karshe ya kara da """Allah ya baki lafiya Hibbah, Allah ya baki karfin zuciyar karbar jarrabawarki. I pray May Allah give your heart rest and replace this pain with something softer and better Ameen""" "Itama ta amsa tana sake jin sassauci, ko da suka yi waya da Momma ma itama haƙuri ta bata" da Adu'a akan matsalarta. "Sai da dare yayi sossai su Abdul suka tafi da Mommy aka barta ita kaɗai, Hudah ce ta kirata don Amal ta kira ta sanar mata abin da ya faru, sai da ma suka zo fita Nasir ya ajiye mata sabuwar waya don nata ya lalace sim kawai ya cire ya mayar mata da icloud ɗinta don already ya sani, sun jima sossai suna magana kan suka yi sallama ta kwanta bata zurfafa tunani ba" kuma bata yi kuka ba kawai dai gata nan ne ga yanayinta har bacci ya ɗauketa. "Ta Yi kusan sati a asibitin don haka kawai sai numfashinta ya fara seizing, tayi jinya da har ta" "rame saboda damuwar na nan yana cinta, raɗaɗin cin amana bai barta ba duk yadda ta so ta" "mayar da komai ba komai ba, a yau suka sallameta wanda Nasir ne ke tare da ita a lokacin shi ya gama komai suka nufi gida, ko da suka iso sun samu Abdul da mommy dake shirin zuwa asibitin dama zaune a parlor suna jiran isowarta, sannu suka mata cikin kulawa ta amsa da murmushi kan ta haura sama tayi wanka ta fito ta kwanta a kan gadon ɗakin tana tuna last baccin da tayi da wayan da suka yi da Usaib kan ta fita, idanunta ta runtse kawai ganin tunanin zai sha kanta ta miƙe ta fito bata da karfin jiki don tana tafiya ne kaman za ta faɗi har ta yi joining su Mommy a parlor, a kan kujeran ta kwanta tana ɗora kanta kan kafafun Aunty Kubra" ɗin. Zame dankwalinta Aunty Kubra tayi tana cewa """Kanki ya tsufa Hibbah bari na warware miki kika kara jin karfi sai ki wanke ko?""" Kai ta gyaɗa tana lumshe ido Mommyn ta shiga warware mata dama kitson manya ne kuma gashinta mai tsantsi ne da ruwa kan iya warware mata kitso don haka da hannu ta dinga warware mata tana ɗan sosa mata wanda hakan tuni ya sa bacci ya sureta... "*Littafin nan na kuɗi ne ki biya Naira Ɗari biyar (500) kachal domin kasancewa cikin masu kwasar tarin ilimi, faɗakarwa da zazzafar soyayya mai cike da sadaukarwa da aka zube ciki. Za ki biya ta wannan asusun" 0545475847 Gt bank Fatima Muhammad Gurin Sai ki tura shaidar biya zuwa wannan layi 09039206763 Ko kuma katin MTN na Naira 500 cikin wannan layi na sama sai ki tura da shaidar biya ta same layi. Sai na ji ku* Gureenjoh 32 "Ba zata ce ga yadda zuciyarta ya yi healing ba amma ta sani ta yi iya kokarinta kuma su Ya Nasir da Abdul da ma Mommy sun bada gudumawa sossai da sossai wurin ganin zuciyarta bai buga ba da abin da Usaib yayi mata, kulawarsu ya ninku a kanta ko da aka dawo makaranta ta" cigaba da karatunta hankali kwance. "Abin da ya bata mamaki har Daddy Z sai da ya kirata yayi mata nasiha duk wani masoyinta a wannan karo ya nuna mata ƙauna, saboda tabbatar musu suna da muhimmanci ya sa a zahiri ta manta komai kuma alkawarin ta na ta gama soyayya bai tashi ba don a yanzu maza kallonsu" "kawai take, bayan su Nasir bata hulda da ko mazan department ne,lecturers karan kansu sun" san cewa ta washi maza don duk abin da lecturer yace kar a yi bata yi ma bare wani abu ya gifta har ya sa ta dangana da office dinshi don ba da haƙuri ko don gyara kuskure. "Wannan part da ta ɗauka sai ya sauya mata fuska a idanun al'umma a inda wasu da suke yawan ganinta suke tunanin cewa tana da girman kai ko tana da ji da kai, sam hakan bai taɓa damunta ba, A dept ɗinsu ma da mace ɗaya take hulda Kaosara da ta zama friend ɗinta na school din saboda hankalinta da rashin hayaniyarta ga kirki, a haka suka kashe wata semester" ɗin suka fara shirin shiga aji uku. "Duk bata je Kano ba dukda tana jin kewar su Hudah da twins ɗinta da koyaushe Hudah na kan videoring yaran tana tura mata, suna video calls sossai da har suke nuna ma sun santa don sun yi wayo sossai, hakan bai sa ta ji tana son zuwa Kano ba ta cigaba da zamanta a legos tana karatu bayan sun gama First semester 300lvl tana shirin zuwa Kano kuma aka tura ta IT." "Ranar da ta dawo daga school da takardar ITn a parlor ta zube tana ɓata fuska ""Ya aka yi?""" Nasir ya ɗago ya tambaya Mommy na zaune tana duba wasu kaya da take haɗawa na shirin haihuwar Zaitoon da a yau ko gobe. """Ni da nake cewa wannan karo zan je kano na yi kewar su shine aka tura ni IT""" Murmushi yayi yace """Sai ki bari idan kin gama sai ki je kin san yanzu karatun ya ɗau zafi kuskure kadan za ki yi ya taɓa miki shi, ina ne suka tura ki?""" Ta buɗe ta karanta """Laaaa Ya Nasir kamfaninku ne ma fa""" Ya karɓa ya duba sai yayi murmushi yace """Masha Allah ko ba komai a yanzu za mu dinga zuwa aiki tare kuma kina kurkure in sa spaner in ɗaure kanki""" Dariya tayi """Da yake kaina ya zama noti ko?""" "Dariya Mommy ke musu, Abdul ya shigo ya zauna yana cewa ""Wash!""" """Sannu Ya Abdul...""" """Yauwa Hibbah ya school ɗin?""" """Wai IT za mu fita ka ga ma Kamfanin su Ya Nasir fa aka tura ni kalan ya sa min ido"" Ya karɓa yana dubawa." """Kar ki damu da shi hai... Ki yi IT ɗinki cikin salama na sanki da jajircewa ki dage ta yadda idan kika tafi za su ce kaman su jefar da Nasir su ɗauko ki don iya aikinki""" Zare ido Nasir yayi ya ce """Mommy kina jin wani gaibu anan? Ki ma yarda da shi wallahi ki zo kina min 'yar murya na assigment ko practicals ki ga idan na kulaki""" "Mommy dariya take musamman yadda Hibbar ta ɓata fuska. ""Ya Abdul za ka jaza min""" """Ba wani, kar ya sha mamaki yana zaune ki zo ki fishi sau nawa ɗalibi ke zuwa ya fi malami kar" "barazanar shi ya baki tsoro""" "Nan suka cigaba da zolayar juna suna raha, jin kiran sallah ya sa duk suka watse." "A daren suna cin abincin dare suka samu kira daga mijin Zaitoon cewa suna asibiti nakuda ya tashi mata tun yamma amma bata jima da sauƙa ba ta samu baby boy, duk ajiye abincin suka yi suka fice zuwa asibitin, sun samu ma Daddynsu ya riga su isa don shi Zaitoon ta fara kira akan ta sauƙa daga office ɗinshi zuwa asibitin babu wani nisa, su ma baby suka je suka samu santalele namiji murna a wurinsu ba magana, barin ma Hibbah da take jin son yaron har cikin ranta ta ɗauke shi ta rungume ta ƙi ba kowa, ko da Zaitoon ta farka tsokananta Nasir ya shiga yi Abdul na karɓa mata ita dai Hibbah hankalinta na nan kan yaron, Mommy da Daddy suna zaune daga gefe suna magana ne ma ɗago ido tayi sai suka haɗa da Nasir dake magana" amma idanunshi na kanta. "Ɗauke kai tayi bata ma wani damu ba ta cigaba da kallon yaron na bacci peacefully, ji take kaman har lokacin ana kallonta ta sake ɗaga ido suka sake haɗa idanu, gira ta haɗe" """Ba fa zan baka shi ba""" Ya saki murmushi yana ci gaba da kallonta """Ki cigaba da riƙe shi, ban taɓa ganin abinda yayi miki kyau ba irin riƙe wannan jariri""" "Kai tsaye yayi maganan kuma da iya gaskiyar shi sai ta ji maganan wani iri, bata damu ba ta mayar da kanta kan Momma dake cewa" """Kin ga Hibbah baki isa ki fara koyawa yaron nan riƙo a hannu tun daga yanzu ba don karshe ni" "za ku bari da rashin bacci""" "Suka yi dariya, a daren sai ga wasu daga cikin dangi sun fara shigowa, tuni Hibbah ta yi hoton yaron ta Turawa mutanen Kano kira ne kawai ke ta shigowa ita kuma tana chatting tana murmushi don tayi snapping kanta da jinjirin ta turawa Hudah shine su Amna ke ihun Mommynsu na Legos ta haifa musu baby Hudah tayi recording ta tura mata shine take dariya, ɗaga kai tayi sai suka sake haɗa ido da Nasir yanayin kallon sai ya sa ta ji kaman ta takura," ganin yanayinta ya sa ya ɗauke ido daga kanta ta miƙe ta fice daga ɗakin. "Sai sha biyu da wani abu suka koma gida har da Zaitoon da ta dawo kenan sai bayan Arba'in, dama mommy ta gyara mata ɗaki na musamman da za tayi wankan jegonta anan suka yada zango nan ma da kyar suka shiga zuwa makwancinsu, Hibbah ta jima tana juye juye kan bacci" ya sureta. "Ko da gari ya waye da hidimar mai jego aka tashi a gidan, baki na ta zuwa barka mommy da Hibbah sun shiga busy da baƙi kuma basu sarara ba har ana gobe suna, mai lalle ce ke ta aikin yi wa Zaitoon yayinda Hibbah ta shigo ɗakin rike da tray da bowl na hadadden cowtail" """Mommy ta ce maza ki ci ki ba ni kwano""" "Yadda tayi maganan ya ba mai lallen da Zaitoon dariya, Zaitoon tace ""Da ke ce Auta wurin Momma kam da ban san yaya ba""" Tana murmushi tace """Toh ai yadda aka ba ni saƙo ne na isar, amma da gaske ya kamata ki dinga buɗe ciki kina kwasar abubuwan jegon nan kar ki bar min yaro da yunwa""" """Zaki ji dashi ne daga ke har yaron naki""" "Zaitoon tayi magana tana jan bowl ɗin ta shiga sha. ""Za ki zauna lallen ba?""" Ta tambaya ganin Hibbah na ta kallon lallen nasu. """Yayi min kyau amma ni kaɗan kawai nake so baƙi ba zan iya zama ja ba kam""" """Toh ta yi miki mana""" """Zan je Saloon yanzu idan na dawo tana nan sai mu yi""" "Ta miƙe ta fice, ɗaki taje ta kara kimtsawa cikin wani boubou gown da ya amsheta sossai ta kafa ɗauri ta yafa gyale ta fito kamshinta mai sanyi na tashi, mommy ta yi wa sallama ta fita harabar gidan tana yunkurin nufar motanta sai ga Abdul" """Sai ina Madam?""" "Ta waigo ta kalleshi tayi murmushi ""Saloon za ni""" """Mu je in kai ki""" "Bata Musa ba yayi gaba zuwa mota tana tsaye har ya kawo gabanta ya duƙa ya buɗe mata ta shiga ta ja kofar ta rufe, ya bi hannunta da kallo" """Ke baki yi lallen ba?"" ""Zan yi ne idan na dawo""" "Kai ya gyaɗa yana tuki cikin natsuwa yace ""Ja kuwa zai yi wa fararen yatsunki kyau""" Tayi murmushi """Ni matsalata da jan nan zama ne, shiyasa ma nace baƙi kawai zan yi""" Ya girgiza kai yana gyara zama tare a ɗaukar kwanar da zata sada shi da saloon ɗinta da ya san take zuwa tunda ta zo garin ya ce """Ki yi ja ko da a yatsu ne ina son ganin hakan""" "Kai ta gyaɗa har suka isa kasancewar ba nisa, ta ma zaci zai tafi sai suka sauƙo a tare, baƙin" less boubou ɗinta da fararen jumpha da ya sa sai ya basu wani combo na rich Kid Vibes. "Har ciki suka shiga ya samu wuri ya zauna, ta yi wa workers ɗin bayanin abinda take so suka kawo mishi tea kan suka nufi inda za'a wanke mata, tana son wanke kai don yana yi mata daaɗi kwarai idanunta a lumshe har aka gama suka nufi gaban mirror aka fara gyara mata, idanunta ta kai kanshi ta cikin mirror ta zaci ma zata ga yana operating waya sai ta ga gabaɗaya hankalinshi na kansu, matar ne ta tambayeta" """Is he your husband?""" "Ta Yi murmushi tana girgiza kai ""My brother""" """Wow! Very protective da alamu yana ji da ke""" Tayi dariya kawai bata ce komai ba. """Ina ma tunanin in yi kitso ne don idan na bar kan haka zai na damu na"" ""So should just do the braids?""" Ta kalli Abdul """Me kike kallona? Ko kina so in zaɓa miki ne?""" Girgiza kai tayi """Idan zan yi kitso zan ɓata maka lokaci ne""" Yayi murmushi """Ko kwana za mu yi indai buƙatarki ne bai zama ɓata lokaci a wurina ba, Ma'am..""" Ya ƙira mai kitson """A yi mata masu kyau, ina mai hawa biyun nan? Wanda gaban zai kwanta a karkace yayi kyau?""" Bayani yake tsakaninshi da Allah ita kuma mai saloon na ɗauka yayinda hibba ke dariya har suka gama fahimtar juna tana zaune suka fara kitson. "Sun ɗauki kusan awa biyu kan suka gama kitson ya fita sossai ya kwanta a kan nata yayi kyau sossai, idanun Abdul na a kan gashin nata dake sheki fatar kan ya fita da kyau ya ɗaga hannu ya jinjinawa matar." """She looks gorgeous. Thank you""" Kai ta gyaɗa tana murmushin yadda ya ji daaɗin kitson don har kyauta yayi mata bayan ya biya kudin service da aka yi wa hibban duka suka fice. "Gyale ta ɗora a kanta fuskarta kaman za tayi kuka take kallonshi ""Wlh zafi Ya Abdul""" Ya sa hannu ya karbi jakanta da ɗan kwalinta """Sorry zai daina ne bari na rage miki waennan kayakin""" "Suka nufi mota yana sake mata sannu cikin kulawa, shi ya buɗe mata gaba ta shiga ya zaga ya shiga wurin mai zaman driver ya ja suka bar saloon ɗin, bai kaita gida ba suka je ya saya mata popsicles wai sanyin zai sa ta manta da zafin kitson murmushi kawai take, ko da suka isa gida bata ɗauki dankwali da jakan ba shi ya tattara mata ta sauƙa ya zagaya suka jera suka nufi ciki, Nasir da ke tsaye jikin motarshi harde da hannu ya bi su da ido har suka ɓace ba tare da ya nemi yi musu magana ba tunda su basu lura da shi ba, lip dinshi na kasa ya ɗan lasa kan ya" zaga ya shiga motar ya ja ya bar gidan... "*Littafin nan na kuɗi ne ki biya Naira Ɗari biyar (500) kachal domin kasancewa cikin masu kwasar tarin ilimi, faɗakarwa da zazzafar soyayya mai cike da sadaukarwa da aka zube ciki. Za ki biya ta wannan asusun" 0545475847 Gt bank Fatima Muhammad Gurin Sai ki tura shaidar biya zuwa wannan layi 09039206763 Ko kuma katin MTN na Naira 500 cikin wannan layi na sama sai ki tura da shaidar biya ta same layi. Sai na ji ku* Gureenjoh 33 *Ba edit da safe za ku ji ni in shaa Allah* "Washegari an tashi da hidimar suna a gidan inda 'yan uwa da abokan arziki suka cike aka yi decoration masu kyau da tsari ciki da waje, yaro ya ci sunan Daddyn Zaitoon inda Hibbah ta saka masa inkiya Aryan, daga Kano dai ba wanda ya zo amma Aunty Asiya da babbar 'yarta Asma'u sun zo daga keffi, Hibbah bata wani yi makeup ba ta dai gyara fuskarta ta saka wani lace da ya zauna mata sossai fitted ƙasan shi yana da Tail amma ba mai tsawo ba, kalar lace ɗin mustard yellow ne da touches na wasu kalolin silver, navy blue da pink sai ta saka silver accesories da takalmi hill ta yi kyau sossai barin ma da ta ja dankwalin baya gaban kitson ta ya" ɗan fito ya sake haske fuskarta. "Fuskarta kadaran hadaran don yanzu tayi mugun rage fara'a kuma ta koyi miskilanci da magana, idan ba wai da chan kun saba bane ba lallai ta yi maka shi ba, bata jima da zama parlorn ba ana ta hira da serving abinci ta miƙe ta fito waje inda ta samu Zaitoon ana ta mata pictures da yaron da kuma mahaifinshi itama ta fiddo wayanta ta fara yi musu tana ɗan murmushi kaɗan don sun burge ta, daga bayanta ta ji" """Masha Allah kin yi kyau ƙanwata!""" Ta waigo sai ta kalle Ya Nasir ne tayi murmushi """Yau kuma da zolaya ka fito Ya Nasir? Kai ma ka yi kyau Tabarakallah wane ango""" Yayi dariya yana ɗan duƙawa tare da leƙar fuskar wayanta kamshinshi na cika mata hanci "kaman yadda nata ke kashe mishi gaɓɓai yace ""Kika sani ko na kusa zama angon?""" "Ta ɗan waigo don yadda yayi maganan yayi mata wani iri ""Hala budurwa ka yi ba labari Ya Nasir""" """Ga ki tsaye kin ga sai a yi 'yar gida kawai"" Wasa ta ɗauki ma zancen tayi gaba tana cewa ""Bari ka ga ayi min pictures da yarona""" Ya bita da kallo yana murmushi har ta karbi yaron aka shiga yi mata. Bayanta ya koma kasancewar navy blue Men lace ce jikinshi da ya amshe shi kwarai yayi mishi kyau sai suka zama kaman su ne parents ɗin musamman da ya duƙa kaɗan yana leƙa fuskar "babyn aka yi snapping, Asma'u ke cewa" """Wai kun ga yadda kuka yi kyau!"" Tana kara daukar su da wayarta." Ya ɗago ya kalli Zaitoon ya ce """Kawai sai Lil Sis ta bar mana kin ga yayi wasu iyayen sababbin ko My Ƙanwa?""" Za tayi magana suka ji an ƙira sunanta ta waiga ta kalli Abdul ya fito cikin shigar farar shadda mai sheki da ya mishi kyau ƙwarai tayi murmushi """Latest iyaye in the town duk kun cinye wannan sunan gaskiya""" "Ya kalli kanshi ya kallo yadda suke da Nasir da bai motsa ba bai kuma kalleshi ba ya ce ""Taso ki zo""" Ta miƙe tsaye ta nufeshi idanunshi a kanta har ta ƙaraso gangarshi yana cewa """Yauwa mu ga ɗan nawa kuma Babana na kaina...""" "Kanshi ya sanyo yana taɓa kumatun yaron da hannunshi sai yayi motsi yana ɗaga hannu, Zaitoon ne ta sa mai hoton ya ɗauke su fuskarta da murmushi, tana admiring yadda Hibbah za tayi kyau da goyo, ta rasa ma tsakanin Abdul da Nasir da wa hoton nasu ya fi haskawa da kyau," tsaki ta ji da sauri ta ɗan waiga tana Kallon Nasir za tayi magana ya juya ya bar wurin. "Su Hibbah kam sai da ta gaji da hotunan kan ta koma cikin gida, tana shiga parlor wayanta yayi ringing ganin Nasir ya sa tayi picking" """Ya Nasir""" """Ina jin yunwa sama min wani abu mana please"" ""kana ina?""" """Ina karamin parlorn da muke lessons""" Yanke wayan tayi ta nufi kitchen. "Sinasir mai zafi da ta ga ake yi ta ɗiba mishi da miyan haɗin shi chicken curry, kunun aya ta haɗa mishi da shi da ruwa ta nufi parlorn, yana zaune hankalinshi na kan waya ta shigo ya mayar da idanunsa kanta har ta ajiye mishi tana zama" """Hala ko karyawa baka yi ba Ya Nasir""" Ta sanshi yana da jin nauyin shiga jama'a idan kuma ba kai mishi aka yi ba ba zai ci ba ta yi mamaki ma da yayi mata maganan yunwar. """Da ke da Mommy ne ai baku ba ni ba""" Ta ɗan taɓe baki """Wlh ban san baka ci komai ba tun safe, yanzu dai ci wannan kar yayi sanyi""" Miƙewa yayi ya je ya wanko hannu ya dawo ya cire babbar rigar da ya saka ya zauna ya shiga ci ita kuma tana danna waya. """Kin san monday ya kamata ki fara zuwa IT ko? Acceptance letter ɗinki na ɗaki""" Ta waro ido """Da gaske sun karɓe ni?""" "Kai ya gyaɗa tayi murmushi ""Alhamdulillah! Na gode Ya Nasir""" Ya mayar mata da murmushi """Sai ki ƙara hazaƙa ina mai tabbatar miki da irin kwanyarki da kuma baiwa da Allah yayi miki ba" "za su so rasa ki ba bayan kin gama, har aiki za su iya baki""" Cikin jin daaɗi tace """Da kuwa na ji daaɗi Ya Nasir bana son gama karatu in koma aiki wani field daban don na san Kano babu irin waennan manyan kamfanin kaman nan legos, kuma dama i hate going back to Kano sai kawai in cigaba da zamana anan""" """Yeah sai kawai ki yi aurenki ma duk anan""" Ta ɗan ɓata fuska """Ana maganan arziki Ya Nasir""" Ya zaro ido """Auren ne ba abin arziki ba Hibbah?""" "Ta taɓe baki zai yi magana wayanta yayi ƙara ta duba, Ya Abdul ne" """Kina ina ne ina ta nemanki Hibbah?"" Calmly yayi maganan." """Ina nan cikin gida"" ""Sameni a garden""" Ta amsa tana yanke wayan. Ya kalleta """Me Ya Abdul ke so dake ne Hibbah?""" "Ta mishi kallon rashin fahimta ""kila wani abu zan mishi ba?""" "Har zai yi magana kuma sai ya fasa bai ce komai ba har ta fita ya mayar da idanunshi kan abincin yana jin yayi loosing appetite, me Abdul ke nufi? Meyasa tun farko ba ya jin haushin chusa kai da Abdul ke yi lamurran yarinyar sai yanzu?" Numfashi ya sauƙe ya miƙe ya fito ya nufi garden ɗin. "Ita kam tana zuwa ya tura mata Boba tea da loaded fries da alama sayowa yayi ko order ya ce ""Maza zauna ki ci na san kina nan kina yawo da yunwa fal ciki""" "Kuma fa tana jin yunwar kawai dai bata zauna ɗin bane bare ta ci gashi ya sayo abinda take so, kayanta ta kalla ya tayata kallo" """Ya Abdul kayan nan ba zai bar ni in ci yadda nake so ba fa, bari na je dashi ɗaki in na cire sai in ci""" "Ya girgiza kai yana mayar da kanshi baya ya jingina da kujerar ""No Hibbah! Je ki cire ki sauya da wani sai ki zo""" "Bata Musa ba ta juya ta nufi ciki, bata fi mintuna goma ta ta chanza zuwa wani boubou fabric peach da shima yayi mata kyau sossai ta ɗora gyale kanta kawai ba tare da ta sa dankwali ba, bata chanza jewelries ba amma ta sauya takalmi zuwa wani half shoe na mata mai kyau silver, tun daga nesa yake kallonta har ta iso sai ta ji ta takura har a yanayinta ya fahimta hakan ya sa" ya ɗauke ido ta zauna. """komai yana karɓarki Hibbah""" "Tayi murmushi kaɗan kawai ta fara cin loaded fries ɗin da fork da aka yi wrapping jikin package ɗin, sai kallonta yake za tayi magana akan kallon ta ƙware ya ɗauki Boba ɗin ya kai mata baki yana ce mata sorry daidai nan Nasir ya taho ta inda suke idanunshi ya sauƙa kansu." "Komai ya fito mishi fili wani irin zafi da ɗaci ya ji yana ji a lokaci guda, idanunshi har wani ruwa suka tara yana kallonsu bai motsa ba har ta miƙa hannu ta karɓi cup ɗin tana juya kanta daga fuskar Abdul ɗin ta yi sipping kan ta ajiye cup ɗin ta ɗauki tissue da duk yana cikin package ɗin" ta goge bakinta tana cewa """Alhamdulillah! Na gode Ya Abdul""" "Zai yi magana ta miƙe kawai ta bar wurin gabanta na cigaba da faɗuwa, dab zata fita ta kusa cin karo da Nasir ta kalli idanunshi ya kalli nata, bugun zuciyarta ne ya ƙaru da wani irin tsoro da bata san na me ba, da hanzari ta wuceshi shima ba tare da tayi magana ba kawai tayi ɗakinta" tana zubewa bakin gado hannunta dafe da kirjinta. """Me ke faruwa?""" "Tayi maganan a fili, ta jima zaune kan ta ture tunanin dake bijiro mata tana tabbatarwa kanta ba" "abu bane mai yiwuwa a wurinta don haka ba komai bane, ta miƙe ta fito cikin mutane har aka" gama hidiman ranar bata bari ta sake ganin ko dayansu ba wayanta ma a DND yake. "Yau Monday ta tashi da shirin fara zuwa wurin IT, cikin two pieces Dubai fabric ta shirya wandon palazo rigan kuma ya sauka har wurin gwiwar ta ta baya ta gaba kuma ya wuce cinyoyinta akwai belt da ta ɗaura daidai cikinta da yayi mata kyau sossai, baƙin Jersey tayi styling kanta yana bayyana jewelry ɗinta, ta saka agogo da zobuna a hannun hagunta na damar ta saka wani tsiririn gold bracelet da Aunty Kubra ta saya mata, jaka da takalmi duka bakake ta" ɗauka ta fito. "Tun da ta nufi saukowa Nasir dake tsaye jikin kujera yana duba time ya zuba mata idanu, shi bai san yaushe soyayyar yarinyar nan ya shige shi ba da farko tausayi take bashi, bayan breaking up da tayi Najeeb saboda babu aure tsakaninsu har hawayen tausayinta ya zubar barin ma irin halin da ta shiga wannan ne da ya sa ya nace ya kuma dage sai da ya sama mata gurbin karatu don ta chanza environment ta kuma ji daaɗin hakan don course da ya jima da sanin tana muradi ya samar mata, ko da ta dawo da zama legos sam bai kawo sonta yake ba kuma har ranshi yayi mata murnar samun Usaib tunda ya ga tana tsananin ƙaunarshi, kariyar" zuciyar da ta samu daga Usaib shi ya darsar mishi son wanke mata zuciya. "Ya ji soyayyarta ya danne tarin tausayinta da yake, ya ji cewa zai aureta ya mayar da ita uwar 'ya'yanshi ya kuma so ta ita kaɗai har karshen rayuwarsu, a yanzu da yake kallonta da wani idanu na daban saɓanin kanwa kuma jininshi sai yake kara fahimtar irin baiwar kyau da Allah yayi mata mai sanyi, yake kuma karantar tarin nagarta da take da shi da kowani namiji zai yi" burin samu. """Ya Nasir...!""" Ta faɗa a karo na uku don ya ɓace cikin tunani. "Kanshi ya mayar kan dining sai ya ga Abdul da Mommy suna kallonsu ya ɗan basar. ""Mu je ko? Kin sa na so makara""" """Haka za ku tafi bata ci komai ba?"" Mommy tayi maganan." """ko a hanya za mu samu wani abu mommy yanzu holdup kaɗai ya ishe mu ga nisa""" "Yana shirin fita Abdul ya ce ""Tsaya Hibbah!""" Juyowa yayi ya kalleta ita kuma idanunta na kan Abdul da ya miƙe da cup na hot choculate yana miƙa mata. "Murmushi tayi ta karɓa tana furta ""Na gode Yaya""" "Da sauri ta nufi kofa don Nasir tuni ya fice, bai kalleta ba har ta shiga ta zauna tana ajiye cup" "ɗin gefenshi don ɗaura sitbelt sai da suka fita daga gidan ya samu titi sossai ya juya ya kalleta ta ɗauki cup ɗin tana shirin sha, ya sa hannu ya karɓe bai ce komai ba ta kalleshi" """Me ke tsakaninku da Ya Abdul?""" "Yayi mata tambayar cikin ɓacin ran da take karanta a fuskarshi ""Kaman me fa? Me kake nufi?""" Window ya sauƙe yayi wulli da kofin ta ɓangaren karshen ruwa da suka zo ya mayar da glass "ɗin ya rufe, sai a lokacin ranta ya ɓaci" """Menene hakan kenan Yaya Nasir? Abinda zan karya da shi ne fa ka jefar? Ko ba ni zan ci ba ai abinci ne ko baka san babu kyau wulakanci da abin da za'a iya ci ba??""" """Na ce ba zan nema miki wani abu ki ci bane idan muka fita? Ko ya fi ni sanin yanayin cimarki ne? Na tambayeki menene tsakanin ki da Abdul?""" "Window ta buɗe tana mayar da kanta ta chan don ta samu iska ya shiga huhunta ranta tafasa yake, Meyasa za su fara yi mata haka? Anya sun yi mata adalci?" """Amma dai ka san Ya Abdul bai taɓa bari na fita gidan nan ba tare da na ci wani abu ba tun da na fara karatu a garin nan ko? Me abin jin zafi don ya ba ni tea zan fita da yunwa? Ya Nasir don Allah kar ka sa na fara jin da na sanin zuwa na garin nan don wallahi ban shirya wa wannan abin da kuke kokarin farawa ba! Idan hakan baka so in bi ka ne fine zan iya daukar motata in tafi wurin aiki amma kar ka sake min haka bana so...""" Ta ƙarasa tana jin hawaye na zuwar mata na bacin rai da damuwar da suke shirin sanya mata tana ƙaryatawa. "Sai a lokacin ya ji bai kyauta ba, jikinshi yayi sanyi ganin tana hawaye kuma ya san yayi ba daidai ba, goshinshi ya dafe kadan yana jin haushin kanshi" """Ki yi haƙuri""" "Bata ce komai ba ya fiddo hankey ya miƙa mata, kaman ba zata karɓa ba sai kuma ta amsa ta gyara fuskarta, motar shiru har ya tsaya gaban wani cafe ya karɓa mata hot cofee da ya san tana so da meatpie da kuma banana bread." Bata buɗe ba sai dai ta karɓa tana riƙe da shi a hannunta har suka isa ma'aikatar da tsarin shi "kadai ya ɗauki hankalinta, tamfatsatsen gate ɗin an yi rubutu da manyan baƙi" """MB MUSTAPHA AUTO MOBILE INDUSTRY LIMITTED""" "Aka buɗe musu gate suka shige zuwa harabar inda ma'aikatar ke ta shigowa wasu a machine," wasu a motoci wasu kuma a ƙasa... "*Littafin nan na kuɗi ne ki biya Naira Ɗari biyar (500) kachal domin kasancewa cikin masu kwasar tarin ilimi, faɗakarwa da zazzafar soyayya mai cike da sadaukarwa da aka zube ciki. Za ki biya ta wannan asusun" 0545475847 Gt bank Fatima Muhammad Gurin Sai ki tura shaidar biya zuwa wannan layi 09039206763 Ko kuma katin MTN na Naira 500 cikin wannan layi na sama sai ki tura da shaidar biya ta same layi. Sai na ji ku* Gureenjoh 34 """Hibbah..! Na yi kuskure. Hankalina ne ya gushe, zuciyata ta cika da zafin kishi, shi ya sa na aikata abin da bai kamata ba. Ina neman afuwa.""" Ya faɗa a hankali yana katse ta daga niyyar sauƙa da take a cikin motar. "Kaman mai ciwon wuya ta waigo ta kalleshi ""Kishi?""" Ya gyaɗa kai """Ba zan yi nauyin baki ba kar a yi min tsakiyar da ba ruwa, Hibbah ina ƙaunarki da dukkan zuciyata, ba zan ce ga ranar da hakan ta fara ba amma na sani a yanzu babu abin da nake ji fiye da ke a wannan duniyar, idan kin ba ni dama ko a wani sati ne a shirye nake da aurenki...." "Ba zan taɓa cutar da ke ba, ba zan taɓa karya miki zuciya ko ta wani ɓangare ba don Allah kar ki yi turning ɗina down""" "Jikinta rawa ya ɗauka, zuciyarta na wani irin motsi da ƙarfi ba na soyayya ba sai na ruɗu da ta shiga, a'a bata shirya ba bata shirya soyayya da kowa ba on top of that ma Ya Nasir?" """No please. !""" "Ta faɗa muryarta na cracking, hawaye na cika mata idanu ta cigaba" """A'a Ya Nasir kar mu yi haka da kai don Allah Ban shirya ba ka daure zuciyarka ka janye" "kalaman nan""" Ya waigo gabaɗayanshi idanunshi da suka sauya zube a kanta """Na yi iya jurewar da zan yi amma zuciyata ta kasa hakan, akwai wani abu nawa da bai miki ba ko wani hali nawa da kike so na chanza kafin ki iya saurara ta?""" "A lokacin hawayenta zuba suka fara, ganin halin da ta shiga kuma ta kasa magana sai" "hankalinshi yayi mugun tashi, shi ba abin da ya shirya mata ba kenan, bai san menene yasa take kuka saboda ya furta yana sonta ba, bai kai bane? Ko akwai wani aibu da yake dashi?" "Jakanta ya buɗe ya ɗauko wani farin roba ya fiddo da pills ɗinta guda biyu ya miƙa mata duk damuwa ya rufe shi, a tafin hannunta ya saka mata ta jefa a baki ta kurbi cofeee din da ya saya mata, hannunta ɗaya dafe da kirjinta take mayar da numfashi a kai a kai hawaye kuma na zuba mata" """Bana son jin wannan kalmar don Allah ka bari Yaya Nasir, ka bari...ka saka a ranka cewa" "bamu yi irin wannan zance ba please nima zan goge wannan moment ɗin cikin kaina""" "Da sauri ta fita tana barin duk abincin da ya saya ɗin, jakanta a hannunta ta samu tsakanin" wasu motoci ta share fuskarta fes kan ta fito daga bayanta ya ce a sanyaye. """Mu je""" "Kan ya wuce ta, ta bi bayanshi kawai bata ce komai ba har zuwa cikin tamfatsatsen building ɗin bayan sun gaisa da ma'aikatan front desk ɗin sama sama suka nufi hanyar inda elevator yake suka shiga ya danna hawa na biyar, bayan ya buɗe wani farin haraba ya bayyana yana da tsiririn hanya da dakuna dakuna ta glass take iya kallon girman halls din da bata san na menene ba har suka isa wani office da aka rubuta" "HR daga samanshi, ta san HR department saboda orientation da suka samu na fita IT da tsarukan kamfani a nan (Human resources) HR ake ɗaukar duk wani sabon mutum da zai shiga kamfani da sunan aiki kuma anan ake tantance wanda za'a karɓa da kuma wanda ba za'a karɓa ba." "Knocking yayi kan suka shiga ciki, wani dattijo dake zaune kan kujeran office ɗin ya tarbesu da fara'a hannu Nasir ya miƙa mishi suka gaisa kan ya faɗa Mishi ga ƙanwarshin nan ya kawo ta, wurin zama ya nuna mata" """Please Sit""" "Ta zauna, Nasir ɗin ya juya kawai ya fita bai ce komai ba." "Har lokacin bai dawo daidai ba bai ɗauka za ta iya samun attack saboda kawai ya furta yana sonta ba, bai ga aibu a bayyana mata abin da ke ranshi ba. Shi dai bai taɓa jin son wata ba bayan Hibbah kuma yayi alkawari ba zai taɓa haƙura da ita ba." "Idanunta ta saukar kasa bayan barin Nasir office ɗin, Meyasa? Meyasa Nasir zai ɗauko mata wani zance da ta riga ta rufe babinshi a rayuwarta? Me a cikin soyayya banda ƙuna da raɗaɗi? Ita kama bata shirya ba ko ta shirya kuma ba zata taɓa iya amincewa Nasir ba ba don bashi da" nagartar ba kawai ya fiye mata alkhairi zamanshi matsayin Yayanta. """Hey...""" "Tayi firgigit, dattijon ya ce" """Ina ta magana hankalinki ya yi nisa hope kina lafiya?""" Da turanci yayi maganan ta miƙe tsaye tana ce mishi lafiya ƙalau yayi haƙuri she was carried away. "Kujeran gabanshi ya nuna mata taje ta zauna. ""Submit your papers please""" Takardun ta fiddo ta bashi yana dubawa yake tambayarta me da menene ne? Ta shiga mishi bayani "IT letter ne, Cv da suka buƙata and passport." "Kai ya gyaɗa yana sake kallonta she's very bold and confidence babu wani tsoro ko panic a tare da ita hakan kuma ya burgeshi, bayan ya gama dubawa ya dube ta ya shiga mata bayani." """Kamfaninmu guda biyu ne, akwai Kamfaninmu na sarrafa ƙarfe MB MUSTAPHA" "production/manufacturing company da ke Badagry Express(Agbara axis) a chan ne duk wasu kayan aikin hannu da fasaha, samar da kayayyaki, da kuma ayyukan bita da injuna. A nan aikin" "ofis ne kawai ke gudana su tsare tsare da sauran rubuce-rubuce, za mu iya ajiyeki anan ko a" "chan ɗin base on what you want""" Cikin ladabi tace """Zan fi son chan ɗin sir na yi ta yin theories a yanzu ina son in yi experiencing field ɗina a yadda yake, ina son in koyi su yankan ƙarfe, narkar wa, ayyukan Gearbox tsarukan birki, tsarukan sanya inji, gyaran da ake yi idan mota ta lalace da duba injuna... Idan har ba damuwa a tura ni chan ɗin""" "Murmushi yayi ""Wow! Miss """ Tayi murmushi ta ƙarasa mishi """Hibbah Mudassir""" """Gaskiya am impressed, this shows kin san me kike yi kuma da gaske field da kika zaɓa za ki iya""" "Ta Yi murmushi politely Dukda yake ne, har da ma bata son cigaba da zuwa da Nasir ya sa ta" zaɓi chan. "Wasu rubuce rubuce yayi kan ya bata da address na ɗayan kamfanin nasu, ta karɓa yace ta kai ta ba Manager workshop zai kira shi kan ta isa ma." "Tayi godiya sossai ta miƙe ta fice, kaman ta nemi Nasir kuma sai ta fasa gashi ba da motarta take ba, Allah ya taimake ta kasancewar safe ne tana fita ta samu taxi, akwai nisa kuma kudin ya yi tsada don tafiyar awa biyu ne ma daga nan Ikorodu zuwa chan Badagry ɗin amma idan da daga gida ne ta fita ta bi ta wani hanyar ba zai kai wannan zagaye ba." "Kai tsaye chan ta yi wurin karfe sha biyu ta nemi maganer workshop ɗin ta bashi yayi approving kan ma ya shigar da ita inda zata fara aiki, anan kam tun daga waje ta san aikin ne ya kawo ta don junks ne birjik, injunan narka ƙarafa gasu nan daban daban kowa sanye da kayan da ya zama baƙi saboda aikinsu na baƙin mai, sababbin kayan aiki aka bata taje ta sauya duk gani" kawai ta yini yi karfe uku ta bar kamfanin ta nufi gida a gajiye cikin yanayi marar daaɗi. Ko da ta iso dab Magrib saboda holdup da sauran chunkoso Abdul na tsaye jikin motan shi da kaman shima yanzu ya dawo ya kalleta. """Sannu Ya Abdul""" "Ta faɗa ba tare da ta mishi kallo biyu ba tayi yunkurin wucewa. ""Hibbah! Ya kika dawo a taxi?""" """Daga Badagry nake ba Ikorodu ba, wurin IT ɗina manufacturing company ɗinsu ne"" ""Me ke damunki?""" """Babu gajiya ce kawai""" Yadda take maganan ba haka ta saba ba ko da kuwa ta gaji. """Ke da Nasir ne?""" "Da sauri ta kalleshi kan kawai ta yunkura don wucewa ""Babu abin da ya haɗa ni da Nasir gajiya ce kawai"" Tana kai nan ta wuce ya bi bayanta da kallo." A parlor ta samu su Aunty Asma'u da su Zaitoon sannu kawai ta musu ta haura suka bi ta da ido ganin yanayinta ba fara'a. Wanka tayi da ruwan zafi ta kwanta tana jin kirjinta na ƙara nauyi. "Har ta fara bacci don ba sallah take ba kuma bata sauƙa ba ta ji ana hayaniya da ɗaga murya, idan kunnuwanta daidai yake jiye mata muryoyin Nasir ne da Abdul, da sauri ta miƙe tsaye ta nufi ƙasa jin tsawar da Aunty Kubra ke daka wa...." Idanu ta runtse da karfi tana dafe stairs jin sunanta ne ke fita a bakin kowannensu """Ina magana kuna cigaba da yi min faɗa a gida? Nasir Abdulll da girman ku? A kan Mace kuke" "kokarin yin abin da baku yi ba tun kuna yara? Me ya haɗa ku da Hibbahn? Me ya faru??"" Sai huci suke suna kallon juna basu kula mahaifiyar tasu ba." Magana Nasir yayi Abdul ya sake yin kanshi kawai Hibbah ta fashe da kukan tashin hankali hannayenta a baki tana ganin yadda Zaitoon da Aunty Kubra ke shiga tsakaninsu... "*Littafin nan na kuɗi ne ki biya Naira Ɗari biyar (500) kachal domin kasancewa cikin masu kwasar tarin ilimi, faɗakarwa da zazzafar soyayya mai cike da sadaukarwa da aka zube ciki. Za ki biya ta wannan asusun" 0545475847 Gt bank Fatima Muhammad Gurin Sai ki tura shaidar biya zuwa wannan layi 09039206763 Ko kuma katin MTN na Naira 500 cikin wannan layi na sama sai ki tura da shaidar biya ta same layi. Sai na ji ku* Gureenjoh 35 """NASIR! Meyasa kake ƙoƙarin ganin ka dawowa Hibbah da abin da ya wuce a rayuwarta? Me yasa ka ɓata mata mood a yau? Don dai na tabbatar kai ne musababbin halin da na ganta yau ciki""" "Abdul ne ya tare shi da maganan daga yana parking motarshi da niyyar shiga cikin gida, dama ya yini ranshi ba daaɗi gashi Hibbah ta zo ta tafi ko nemanshi ma bata yi ba bare ta sanar dashi yadda suka yi ko ta sanar da shi zata tafi ranshi ya ɓaci da hakan kwarai, da wannan bacin ran" ya dawo kuma Abdul na tare shi da wata magana. """Ita ta faɗa maka hakan?""" Girgiza kai Abdul yayi """Ko kaɗan! Actions naka ne ya nuna min hakan please koma menene a ranka i will advice you to drop it saboda ba zan bar hakan ya kasance ba, ka fita harkarta kawai i think it will be better for all of us!""" Cikin jin zafin kalaman ya mayar da martani """Who do you really think you are? All my life da kake controlling ɗina yadda ka so nake biyayya ka zaci tsoro ne ko me ya saka hakan? You are not telling me what to do am not ur puppet""" Wuce shi yayi ya nufi parlor a lokacin Abdul ya hasala ya bi bayanshi zuwa cikin parlorn kafaɗarshi ya riƙo """Am talking to you! me kake ji da shi? Yaushe ka yi girman da za ka gayamin duk abin da ya fito bakinka don na ce ka fita harkar Hibbah?""" """Ya Abdul!""" Ya faɗa yana kallonshi cikin ido """You cannot hurt me and tell me how to feel, you've already hurt me for long ina tolerating duk abin da kake yi wa Hibba a kan idona kuma na san da gayya kake hakan i've never talk or complain don haka ban ga dalilin da zai sa in tsaya kana gayamin yadda zan yi da Soyayyata" "ba""" """Soyayyarka? Har yaushe hakan ya fara?""" Abdul dake controlling kanshi yayi maganan kan ya dafa kafaɗar Nasir """Listen duk wannan kana lalube ne cikin duhu, do not let a woman come between us, Soyayya will not tear us apart kai kanina ne kuma ka tsaya matsayarka""" """Wai me ke faruwa ne?""" "Mommy da Aunty Asiya suka miƙe tsaye duka suna nufar su, Zaitoon dake dining da Asma'u dake kitchen duk suka fito saboda ba'a hankali suke maganan ba. Babu wanda ya kula su sai wani kallo da Nasir yayiwa Abdul" """So ba za ka iya bar min ita ba ko da kuwa sonta kake kaman ka mutu? Hasali ma me naka? na ga dai Hibbah zata zo garin nan ban kasa da kai ba ban saka sunanka a cikin mai taimakona wurin sama mata admission ba""" "Hannu biyu Abdul ya sa ya ture shi da karfi ""Don't talk to me in this manner""" Harzukowa yayi """This guy are you okay?""" Daga nan fa suka shiga rigimar da ya sanya Hibbah saukowa ta maƙale jikin stairs hannayenta dafe da baki. """With due respect Abdul, I never want to fight you amma hakan ba shi zai sa na tsaya ina kallo ka shiga min gona ba""" Ya faɗa daga bayan Mammi ranshi na tafasa da abin da Abdul ɗin ke mishi. """Wai me yake damunku ne?? Yanzu a ajiye Hibbah a gefe misali wata macen ce haka za ku yi" "ta faɗa kuna tada jijiyon wuya??""" "Aunty Asma'u tayi musu tsawa ganin Aunty Kubra har ta fara zubar da hawaye don bata taɓa ganinsu cikin irin wannan hali ba tun tasowarsu ma, Nasir na da kiyaye Zafin zuciyar Abdul don shi baya son abin da zai saka shi ɗaga hankali ko a taɓa mishi lafiyar jiki, yana respecting Abdul don ko wasan nan da saƙo da saƙo basa yi da shi sai dai da Zaitoon amma rana ɗaya suna" kokarin hautsina mata kai?? A kan Hibbah?? """Aunty Asma'u Hibbah is not just a woman, she's my soulmate, she's my responbility tunda ni na kawo ta gidan nan and i will fight for her to the end""" Ihu ta yi da ƙarfi da ya sa duk hankalinsu ya koma kanta tana kallonsu tace """Stop this please! Ku daina..." "Dukkanku biyu ina son ku matsayin 'yan uwa kuma soyayyar da zan nuna muku ɗaya shi ne I will never let you guys fight over me ba zan zaɓi daya in bar ɗaya ba am making my choice kaman yadda dukkanku kuka yi don haka duk ku biyu ku kyaleni ku cigaba da zama matsayin yayyena babu wanda nake so kuma babu wanda zan aura.""" "Ta ƙarasa da zare idanu making it clear to them don ba za su raba mata kai ba! Ba Za su kasheta tun kwananta bai ƙare ba, wani irin masifa ne wannan? Sharrin Son duk ya kai haɗa wa" da ƙani irin wannan rigimar? Abdul ya kalleta shima cikin hasala da jin zafin kalamanta ya ce """Hibbah wannan ba abin da za ki yanke bane, you are not involved in any of this! This is between me and Nasir and na rantse da Allah i will deal with you Nasir... Za ka ce min kai ka kawota kai ka fara sonta is she your wife da ka kawotan?? Har kana da audacity na walking over me ina maka magana don raini? Me zaka yi idan na ce sai na aureta?""" Hannunshi ya fusge a na Zaitoon da take ta mishi magana akan yayi hakuri yayi shiru ya nuna shi da yatsa """A sannan ne kuma zan shayar da kai ruwan mamaki Abdul don wallahi sai dai idan bana" "numfashi za'a aura maka Hibbah""" "Da gudu Hibbah ta haura stairs, hijabi ta saka ta janyo wayanta da Atm ɗinta ta fito tana kuka sossai don ita kam ba zata cigaba da zama a wannan gida ba kuma, wani irin bala'i ne ke" bibiyar rayuwarta na maza? """HIBBAH!""" "Aunty Kubra ta kirata ganin ta nufi hanyar waje, sai a lokacin duk suka kula da ita ""Ina za ki je?""" Auntyn ta tambaya a karye """Zan tafi ne, zan bar musu gidan tunda kasancewata a cikin gidansu ya zama bala'i da masifa! Idan na cigaba da zama Aunty ban san me shaidan zai yi jagorar aikatawa ba, zan tafi ko Hotel ne na kama kan in shiga school in samu accomodation a hostel... Aunty ki yi haƙuri amma sai" "na bar gidan nan yau""" """Kun gani ko? Kun ga abin da kuke shirin janyowa ba? Toh ba Hibbah kaɗai zata tafi ba nima tafiya zan yi in kyale ku tunda gidan ubanku ne in kun ga dama ku kashe kawunanku ku" "binne...""" "Ta nufi bin Hibbah da ta yi kofa, da Sauri Abdul ya nufeta ya riƙo hannunta, Nasir ma jikinshi" yayi sanyi shi ba don ya kori Hibbah a gidan yake rigima da Abdul ba. """Ki yi haƙuri Mommy!""" """Ka sake ni in tafi tunda ni ce banza a idanunku yau! Gaba ban san me zaku iya yi ba don haka ku bar ni in tafi tun da lafiyata. Hibba mu je...""" Nasir yayi saurin zuwa ɗaya ɓangaren Zaitoon na kuka danta na kuka don hankalinta ba karamin tashi yayi ba itama. """Mommy Don Allah ki yi haƙuri... Ki yi haƙuri please kar ki ce za ki tafi saboda mu! Ba za mu" "sake ba in shaa Allahu""" Ta kalli Nasir ɗin hawayenta na zuba """Kun ba ni mamaki especially kai Nasir... Akan Mace?""" "Lip dinshi ya taune yana mayar da idanunshi ƙasa, Aunty Asiya ta zo ta kama Hibbah da ta juya za ta tafi tunda ta ga mommyn ta yi sanyi, kuka take tana cewa ta saketa ita kam zata tafi da kyar suka shawo kanta ta dawo sai dai zazzabi, jiri da ciwon kai a take suka rufu mata da kyar aka haura da ita stairs Mommy na kiran likita." Abdul zai yi magana ta daka musu tsawa """Ku fitar min daga sashe yanzun nan... Kuma wallahi kar na ƙara ganinku a sashen nan sai na" "neme ku Mutanen banza kawai""" Ganin ranta a matuƙar bace ya sa duk suka fice ba tare da ɗaya ya kula ɗaya ba. "Zaitoon ta ɗauki yaronta tana rarrashinshi har lokacin ita kanta bata dawo natsuwarta ba, kwakwalwarta ma ya chushe." Hibbah dai a daren sai alluran bacci ne suka sakata bacci da kuma karin ruwa ta kwana jikin ba daaɗi. "Aunty Kubra da Aunty Asiya suka zauna shawarar abin yi nan dai ta ƙira mahaifinsu tace mishi ya taho gida abu ne ya taso urgently ya tabbatar mata zai yi booking available flight ya dawo a goben, daga karshe Momma Aunty Kubra ta kira ta labarta mata duk abin da ke faruwa kar ta ji shi wani wuri ta ji ba daaɗi kuma dai tana da alhakin sanin komai kan rayuwar Hibbah ɗin." Cikin rashin sa'a Daddy na a tare da Momman a lokacin kuma ya ji komai kafin su gama waya ma ya ɗauki wayanshi tana gama call din ya ce mata """Gobe flight ɗin karfe tara za mu bi zuwa legos, idan ya kama mu dawo da Hibbah ne za mu dawo da ita""" Yanayinta duk ba daaɗi tace """Wani irin abu ne ke bibiyar rayuwar yarinyar nan? Daddy kana gani aka ce yanzu ta zaɓi daya ta bar ɗaya abu ne mai yiwuwa? Idan kuma akwai wanda take son a cikinsu ta ƙi bayyanawa kawai don ta raba wannan matsalar fa ita ce zata cutu fiye da kowa ma.. hasbunallahu wani'imal wakeeel""" Ta faɗa hawayenta na silalowa. Ya matso ya riƙe hannunta """Ina ji a jikina Hibba za ta dace da gidan aure, duk wannan wahalar zai kau in shaa Allahu" "haƙuri da ƙaddararta da tayi Allah ba zai barta haka ba, mu cigaba da yi mata adu'a""" Sun sake tattaunawa kan suka kwanta. "Da safen suka wuto legos, Su Aunty Kubra na zaune cikin damuwar zazzabin Hibbahn da ya ƙi sauƙa kuma ta ƙi yarda a je asibiti suka ji sallamar Momma, duk sun shiga tsananin mamaki," Aunty Kubra ta miƙe tsaye """Fatima...! Ke ce tafe?""" """Ni da Babansu Hibbah ne ma, hankalinshi ya ƙi kwanciya dole ya sa muka taho""" Iso ta sa Asma'u ta mishi ya shigo suka zazzauna bayan gaisuwa Aunty Kubra tace """Ku yi haƙuri! Abubuwa marar daaɗi na ta faruwa da Hibbah karkashin Inuwata, da ina da iko da na goge abin da ya faru jiya wallahi ban iya na runtsa ba Daddyn Hibbah...""" Hawaye ta share """Abin da baƙin ciki a ce wai a gabana cikin parlorna yaran nan da girmansu da hankalinsu da" "tunaninsu sun tsaya suna faɗa kan Hibbah da duk sun san ba cikakken lafiya ce da ita ba..""" """Hajiya Kubra ki daina ba da haƙuri da Hibbah da su Abdul duk naki ne kuma na tabbatar abin da za ki yi akan Zaitoon za kiyi fin haka kan Hibbah! Ita kuma kalar tata ƙaddarar kenan. Wani abu da baki sani ba shi SO a sadda ya gama tasiri jikin dan adam is unpredictable, shaidan ya taka muhimmiyar rawa amma so ne da suke yi wa hibbar ya jawo silar komai a ganina kuma" "tausayinta ne ya sa duk suka ɗauki damarar share mata hawaye. Suna ina?""" """Ban sani ba don na musu iyaka da inda nake for now, wallahi muddin Hibbah zata bar gidan nan nima sai na bar musu shi basu isa su hanata zama ba sai dai kuma idan su za su bar gidan gabaɗaya""" Daddy yayi murmushi """Duk hakan ma bata taso ba Hajiya Kubra, tunda kin ce Alhajin na hanya bari mu bari in ya iso mu karkare shawara""" "Kai suka gyaɗa cikin gamsuwa. ""Asma'u raka Daddynku ɗakin Hibbah""" "Dama yana so ya ganta, don haka bai musu ba ya miƙe Asma'u ta kai shi har ɗakin. Motsin kofa ya sa Hibbah bude idanunta da har sun faɗa ganin Daddy ne bata san ta tashi zaune ba, ya ƙaraso bakin babban gadon kawai fashe da kuka." """Daddy bana son gidan nan! Ba zan taɓa iya cigaba da zama ba don Allah ka tafi da ni Kano na" "fasa karatun...""" "*Littafin nan na kuɗi ne ki biya Naira Ɗari biyar (500) kachal domin kasancewa cikin masu kwasar tarin ilimi, faɗakarwa da zazzafar soyayya mai cike da sadaukarwa da aka zube ciki. Za ki biya ta wannan asusun" 0545475847 Gt bank Fatima Muhammad Gurin Sai ki tura shaidar biya zuwa wannan layi 09039206763 Ko kuma katin MTN na Naira 500 cikin wannan layi na sama sai ki tura da shaidar biya ta same layi. Sai na ji ku* Gureenjoh 36 """Hibbah ki natsu, saurareni ki ji""" Ya faɗa yana riƙota da kyau fuskarta cikin tafin hannunshi """Bawa ba ya taɓa tsallake kaddararsa, ba ƙaddarar ba ce abin duba a'a ta yadda ya karɓa shi ya fi muhimmanci a wurin ubangiji, a yanzu haƙuri za ki yi ki fuskanci ubangijinki da roƙon abin da ya fi alkhairi ba koyaushe idan abu ya faru ki gudu ba, idan kika bar gidan nan ina za ki zauna Hibbah har ki ƙarasa karatunki? Ko kin fasa cika burin naki saboda kawai yaran Aunyunki" "suna faɗa a kanki?""" Ta girgiza kai """Ok then fight it! Idan ɗaya za ki zaɓa ki zaɓa a wuce wurin, idan ma duk ciki babu wanda kike jin son shi nan ma duk ɗaya hakan kuma ba zai hanaki cigaba da zama da kuma rayuwa gidan nan ba, na tabbatar Yaya Kubra ba za ta taɓa chanza miki ba ko ta wani ɓangare""" Hakane babu laifin Aunty Kubra amma ta yi abin kwarai kenan na haɗa husuma tsakanin yaranta? Kaman Daddy ya ji me take cewa ya ce """Ba ki haɗa kowani husuma tsakanin yaran Yaya Kubra ba don ba ke kika ce su yi fada da juna ba, ba kuma kin kula su duka biyu bane a ɓoye ko hakan ya faru?""" Ta girgiza kai """Good ki yi Adu'a ki kuma bi abinda zuciyarki ke muradi na miki alkawari babu mai miki dole kin ji?""" "Nan ma kai ta gyaɗa ""Na gode Daddy""" Yayi murmushi ya miƙe ya fice. "Ta koma kwance shiru cikin nazarin kalaman nashi kuma ta tabbatar hakan ne ya dace, amma idan za ta zaɓa wa zata zaɓa? Nasir yayi mata abin da har abada ba za ta manta ba don shi ne silar wannan karatu da take, ya tallafa mata kuma bai taɓa barinta cikin duhu ba a duk abinda ya shafi course ɗinta, tabbas ba don Nasir ba bata tunanin za ta ma kawo nan da clear results" babu carry over da kuma CGPA mai kyau. "Abdul a zamanta gidan ya yi mata kyautatawa daban daban ciki har da kula da duk motsinta, karantar damuwarta da hana cikinta zama da yunwa a koyaushe, yayi playing role ɗin Perfectly" Toh cikin su biyun wa za ta ɗauka ta bar wani? Tayi ta nazari daga karshe ta yanke wa kanta "hukunci daga nan ma bacci ya ɗauketa, cikin dare ta farka sai ta ga Momma kusa da ita tana" "bacci ashe tare suka zo da Daddy bata sani ba, sauƙa ta yi a hankali ta shiga bayi tayi alwala ta" fito ta hau kan sallaya. "Ta jima ƙwarai tana roƙon Allah akan ƙaddararta, bata kai ga sallamewa ba Momma ta farka, itama alwala taje ta yi ta zo tana taya ɗiyar tata neman sauƙi da kuma dacewa, Hibbah ta gama duk adu'u'o'inta yayi da Momma ke zaune tana jan chasbi ta zame ta kwantar da kanta kan kafafun Momman tare da lumshe ido, a haka wani baccin ya sake ɗaukarta tana jin nauyin da zuciyarta yayi ya ragu sossai haka numfashinta ma na fita ba tare da ya sarke mata ba, dukkan" tsanani saukin na wurin ubangiji ta yi imani wannan ma zai wuce. "Ko da Momma ta tashe ta da asuba ta yi sallah a kan pillow ta ga kanta ta miƙe ta ɗaga pillown taje ta mayar kan ta shige toilet, bayan sun idar da Sallah sun ɗauki lokaci sossai suna karatun alqur'ani bayan gari ya ɗan yi haske suka rufe, ta gaishe da Momma, ta amsa cikin kulawa" itama tana yi mata ya jiki ta amsa da sauƙi. "Duk fitowa suka yi zuwa kitchen sun samu ma Aunty Kubra da Maids ɗinta na ta kokarin haɗa abin karin, ko da Hibbah ta gaisheta shafa kanta tayi tana tambayarta ya jiki cikin kulawa, itama ta amsa da lafiya ƙalau ta ji sauƙi, ganin ba aiki sossai kuma ta ji kukan Aryan sai ta koma ta yi" ɗakin da Zaitoon take. "Sun gaisa lafiya kan ta karɓeshi tana rarrashinshi ""Aryan me Mommy ta yi maka kake buɗe baki haka?""" """Ban mishi ba amma zan mishi ne Hibbah, yaron nan ya so kukan banza wlh jiya fa daga ni har Aunty Hasiya babu wanda ya yi baccin kirki a ɗakin nan, bayan mun yi sallah ne nace ta je ta" "huta amma kin ga na safen ma ba zai bari na yi ba""" """Kar ki ga laifinshi Yaya Zaitoon wa ya san iya dararen da kema kika hana Mommy bacci?"" Dariya tayi tana kallon yadda yayi luff jikin Hibbah da ke ta yawo da shi a hankali tana ɗan" "bubbuga shi, sun dan jima kan yayi bacci ta kwantar da shi tana ɗan murmusa wa." """Hibbah!""" Zaitoon ta kirata tana kallonta. "Dawowa ta yi ta zauna kusa da Zaitoon din tana amsawa ""Na'am""" """Ki yi haƙuri da abin da ya faru, na san ba lallai kin kula ba amma ni na jima ina hangen kwantaccen rikici tsakanin Yaya Abdul da kuma Yaya Nasir a kanki, ban san zuciyarki ba amma ina so ki sani wallahi duk wanda za ki zaɓa cikinsu ni mai baki goyon baya ne ɗari bisa ɗari, ke ce ke da alhakin kawo karshen wannan rashin jituwar daga kin zaɓa dole ɗaya ya haƙura""" Kai Hibbah ta gyaɗa """Na riga na gama yanke shawara Yaya Zaitoon, in shaa Allah kuma ba zan takura kaina ko kuntatawa kaina ba, shawarar da na yanke kuma na tabbatar shi ne daidai don na gamsu da adu'o'ina har ji nake tuni Allah ya gama amsa mini haƙuri kawai zan ƙara kaɗan""" "Kai Zaitoon ta gyaɗa duk wani hukunci da Hibbah za ta yanke sun karɓe shi don babu mai zama mata da mijin, babu kuma wanda ya san me take ji a ranta don haka komenene ta ce" babu wanda zai mata dole ko ya ji haushinta. "A ranar da misalin karfe sha biyu Daddy ya iso garin, har kuma lokacin Mommy fushi take da su Abdul ta kuma rantse ba dai su shiga mata sashe ba, sai da rana yayi sanyi suka zauna da Daddynsu Hibbah da dama shi suke jira basu juya a ranar ba sun fi awa suna magana kan ya kira su a waya yace kowa ya same shi a babban parlornshi, ko da duk suka shiga suka samu wuri suka zauna ya dubi Hibbah" """Hibbatullahi ashe ɗiya na iya tafiya ta bar gidan mahaifinta saboda wani dalili da bai kai ya kawo ba? Nan fa gidanku ne duk wani abu da za'a yi miki ban amince ki tafi ba muddin ba barin legos zaki yi gabaɗaya ba, duk kuma wanda ya ɓata miki ina so kawai ki ɗaga waya ki faɗamin" "ni kuma zan ɗaukar miki mataki kin ji?""" "Kai ta gyaɗa idanunta a ƙasa tace ""Ka yi haƙuri Daddy""" """baki yi laifin komai ba, hasali ma ga nan masu laifin ina amfanin girman Abdul? Nasir a haka kuke so har ta auri ɗaya daga cikinku kuna nan kuna kokarin dambatuwa a kanta? Irin tarbiyar da kuka tashi da shi kenan ko kuma nemawa mahaifiyarku ciwo da damuwa kuke? Wallahi I'm very disappointed in you guys""" "Faɗa yake ta inda yake shiga ba ta nan yake fita ba duk suna shiru, sai da ya kai aya kan Nasir ya ce" """Ka yi haƙuri hakan ba zai sake faruwa ba in shaa Allah""" """Ba ni za ka ba haƙuri ba Yayanka, mamanku fa Hibbah su ya fi dacewa ka ba haƙuri in da" "gaske kake""" Ya waiga ya ba Abdul ɗin haƙuri shima ya mayar mishi da kalaman haƙuri suka ba mommy haƙuri itama Hibbah suka bata haƙuri tace ba komai. """Daga rana irin ta yau kar in sake ji kuma kar in gani. Dangane da ke Hibbah""" Ta ɗaga kai ta kalli Daddyn """Ba Za mu yi miki dolen auren kowa daga cikinsu ba, ba kuma za mu tauye ɗaya saboda ɗaya ba don haka ga ki ga su ga kuma mu duka matsayin shaidu ki zaɓa tsakanin su biyu wa kike gani za ki iya rayuwa da shi ta aure?""" "Bata ɗago ba amma zuciyarta kaman zai fita saboda bugu, tana iya jin idanun kowa zube a kanta ana jiran jin respond ɗinta yayinda hakan ya haifar mata da gumi da bata san daga ina suke tsatsafowa ba Dukda sanyin Ac da ke kaɗa cikin parlorn ba kakkautawa, ta fi mintuna uku" shiru Daddynta ne ya kirata ta ɗaga idanunta da suka rine cike da kwallah ta kalleshi """Don't be Hard on yourself, kar ki ji komai kawai ki faɗi wanda kike so a cikin su biyun na" "tabbatar daya mai iya haƙura ne ya bar wa ɗaya""" Mommy ma tace """Hibbah kar ki ji nauyin kowa, rayuwar aure ba irin wannan rayuwa da muke yi ta yau da kullum" "ba ne, kar ki ƙwari kanki babu wanda zai ga laifinki don kin faɗi ra'ayin zuciyarki kin ji?""" Kai ta gyaɗa ta ɗan saci kallon Abdul idanunshi na kallon wani wurin amma tana iya hangen tension da yake ciki a kan fuskarshi. Ta mayar da idanu kan Nasir shi kam idanunshi na a kanta ta kawar da kai tana mayar da idanunta ƙasa tace a hankali """Daddy Duk su biyun babu"" ""Babu me?""" Ta ɗan yi shiru """Babu wanda nake so""" "A mugun sanyaye ta ƙarasa maganar, bata kalli kowa ba amma ta ji shirun da parlorn ya ɗauka na minti ɗaya kan Daddy ya sauke numfashi" """Shikenan Hibbah""" "Ya kalli Su Abdul da duk sun kasa wrapping kalaman Hibbahn na duk su biyun babu wanda zata iya aure, jiki a sanyaye suka ɗago suka kalli Daddy da ya kira sunansu" """Kun dai ji da kunnuwanku, daga yanzu na kashe maganan nan kashewa ta har Abada, ko da wasa kar in ji cewa kun tadota ku kyale yarinya ta yi karatunta cikin salama hope am clear?""" Suka amsa kan duk suka miƙe suka fice daga parlorn. "Itama Hibbah Miƙewa ta yi ta fito a tare da Zaitoon, bata cewa Zaitoon komai ba itama bata ce mata ba har suka isa parlorn Mommy ta haura ɗakinta kawai ta fara kuka kuma, sai da tayi ya isheta kan taje ta wanke fuskarta tana jin tabbacin hukuncin da ta yanke shine zaman lafiyar kowa." "Huda ce ta ƙira ta jin labarin tafiyar su Momma legos a wurin Aina'u don jin lafiya kam, bayani ta mata da hukuncin da ta yanke itama Hudah ta ba da goyon bayan hakan Dukda ba haka ta so ba, ta so zuwa yanzu Hibbah ma tana a gidan mijinta cikin so da kauna, zaman har yaushe ana nan kowani hidima ya tashi a dangi sai an yi maganar Hibbah na zaune har yanzu shiru Dukda ma ba zuwa kunnen Hibbahn yake ba amma daga Hudar har mommy basa jin daaɗin irin" maganan. """Aina'u ta je gidanki ne? Ko waya kuka yi?""" """Eh ta zo bana dan jin daaɗi shine ta zo ta kama min aiki"" ""Ba dai har kin yi wa su twins Gambo ba?""" "Murmushi kawai ta yi don haka ɗin ne cikin ya zo mata bazata babu yadda ta iya ne kawai, ta yaye su twins ta tura su wurin Hajiya Tani da a yanzu bata da kamar Huda, ko laifi Mu'azzam yayi mata ita ke daukar mata mataki, rayuwa ya chanza su sossai barin ma Falmata da ta gama shan tsangwama da wahalar rainon ciki fiye da watanni tara tayi nakuda ta san zafi da raɗaɗinshi ɗan ya zo ba lafiya a karshe ya rasu, ta ga rayuwa da ya sauyata kwarai da gaske ta yi ta neman yafiyar Hudah a lokacin ita ma ta yafe mata, daga nan rayuwarta ya koma neman ilimin addini da kiyaye dokokin Allah, ta natsu sossai sai Fatan samun miji da gari wanda zai iya" rike ta yadda take a wannan zamani. "Basu wani jima ba suka yi sallama Hibbah na mata adu'ar Allah ya bata lafiya, a daren su Daddy suka juya da Momma ita ta kai su har Airport sun sake mata nasiha kan suka wuce, ta dawo gida Washegari tayi sallama da Aunty Hasiya da Asma'u da su ma a ranar za su wuce" "kan ta tafi wurin IT ɗinta, sam bata sanya su Abdul a ido ba kuma bata damu ba ta mayar da" hankali kan sanin makaman aikin kuma tana jin daaɗin mu'amala da mutanen companyn saboda kirkin su da iya mu'amala. "Satinta na uku a IT Nasir ya bar ƙasar sun tafi da Mai kamfanin inda Nasir ɗin da kanshi yayi applying waenda ake nema da za su koma sabon company ɗinsu na Germany inda a chan za'a cigaba da supplying duk wani abu na company ɗin Nigeria, da farko an zaɓe shi amma ya ƙi a yanzu kuma willingly yayi kuma ya samu nasara tafiyar ya saura sati ɗaya ya faɗawa Mommy, at First ta so ta hanashi amma Daddyn su yace ta kyale shi ya je ɗin ba yadda ta iya yayi musu sallama ya bar ƙasar, Abdul da kanshi ya raka shi Airport suka sake ba juna haƙuri kan suka yi" sallama. "Duk Hibbah bata sani ba sai a bakin Zaitoon take ji bayan ma ya isa, sossai ranta bai mata daaɗi ba ganin yanayin da Mommyn ta shiga tana ganin kaman laifinta ne ya sa Nasir barin family dinshi a tilas zuwa wata ƙasa ta rufe kanta a ɗaki tayi kuka da nadamar zuwanta garin sau ba adadi, ita kam soyayya ya zame mata guba a rayuwarta, a duk lokacin da ta ce ta karɓa ko ta ji a zuciyarta tana son karɓa sai ya juye ya zame mata guba mafi muni, Dafi mafi hatsari da yake ƙara dulmiyar da tunaninta da kuma nesantata da wani abu wai shi rayuwar so da" kauna har zuwa aure tsakanin mace da namiji. "Idan ta fito ta ga parlorn shiru ko suka zauna cin abinci da Mommy da Zaitoon babu Nasir babu Abdul da yake ba da uzurin aiki a kullum har zuwa yanzu an saba da kai mishi sashenshi sai ta yi kuka, bata iya wani cin abin kirki duk ta tsangwami kanta har a wurin IT ɗin suka fahimta, Manager Workshop ɗin ya ƙirata suka zauna tace mishi bata jin daaɗi tana so ta je gida nan ya bata hutun 2weeks ta dawo." Ta roƙi Mommy akan tana son zuwa Kano a Lokacin Zaitoon ta yi Arba'in sai Daddy yayi musu booking tare akan daga chan za ta wuce Keffi ta kwanar musu biyu kan ta dawo legos ta koma gidan mijinta. "Sai dai Zuwanta Kanon ma bai samar mata sauƙi ba don a ranar da suka isa sun samu ana ta shirye shiryen da basu san na menene ba, sai da Hibbah ta kasa hakuri ta tambayi Momma ""Ni kam hidimar me kuke da shi ne Momma?""" """A Gobe ne za'a zo tambayar auren Ƙannenki Aina'u, Mujiba da Baby""" Da sauri ta ɗaga ido ta kalli Momma sai ta mayar a hankali bata ce komai ba... "*Littafin nan na kuɗi ne ki biya Naira Ɗari biyar (500) kachal domin kasancewa cikin masu kwasar tarin ilimi, faɗakarwa da zazzafar soyayya mai cike da sadaukarwa da aka zube ciki. Za ki biya ta wannan asusun" 0545475847 Gt bank Fatima Muhammad Gurin Sai ki tura shaidar biya zuwa wannan layi 09039206763 Ko kuma katin MTN na Naira 500 cikin wannan layi na sama sai ki tura da shaidar biya ta same layi. Sai na ji ku* Gureenjoh 37 """Allah ya sanya alkhairi""" "Ta faɗa tana ji musu daaɗi a ranta amma ta wani ɓangaren zuciyarta na shiga ƙunci, a al'adar gidansu irin wannan rana kusan kowa na family na nan, tayi tunanin zuwa gidan Huda don gujewa maganganun mutane amma sai Huda ta riga kira akan tana nan zuwa da sassafe." "Mutane basa iya gane cewa kowa da nashi ƙaddarar, ba kuma rashin kyau, nasaba ko cikakken" "asali ke hana aure ba shi kaman haɓo ne da idan ya zo sai an yi shi, kuma ba dole bane don haka idan ta zaɓi ƙin yi ba kowa ta cutar ba hasali ma ra'ayin kanta zata bi." "Haka ta kwana sukuku, Amal da Nadiya suna sashen don taya su hira amma bata iya magana sai tsakaninsu da Zaitoon da Aina'u da taga ta kara mata wani girma da cika ta zama cikakkiyar budurwa take bi da idanu, ga irin rawan kan nan na 'yan matan zamani sai ta tsinci kanta da yi mata adu'ar dacewa da miji nagari, Dukda Daga Hajiya Zakiya har Hajiya kamila basu mata ko da maganar banza bane ko kallon banza bata wani saki jiki ba bare ta je sashensu kuma duk" sun sakarwa Momma aikin ne na tarbar bakin. "Washegari tun safe sai ga iyalan gidan Daddy Rabi'u Da Daddy Z, chan sai ga Huda ma da 'yan biyun ta da suka kara wayo sossai, su ne ma suka taimaka Hibbar ta ɗan sake ana hira da ita, kan fa dangi suka fara isowa kuma yawanci sashen momma ne don ta fi sakewa da mutane da" faram faram. "Hibbah Momma ta kira akan ta dinga serving na duk wanda ya zo kar a zo a tafi da yunwa, ana cikin karamar hidima aka sanar da isowan maneman auren Mujiba, sun gama komai an saka date kuma sun aminta nan da december a lokacin 'yan matan ma sun gama 100lvl za su shiga 2 kaman yadda aka yi wa su Huda Aure a tsakankanin." "Su fadil ne suke ba da labarin ai sun tafi, chan na Baby suka zo su ma duk aka gama date ɗaya da na Mujiba kan na Aina'u ita dai Hibbah na rabon abinci fuskarta kadaran-hadaran ta kawowa wata Goggonsu dake zaune da 'yar uwarta" """Kema dai Hibbah sai ki dage ki fidda naki don da kunya a ce Ƙannenki suna aure kina zaune""" Ɗayar ta ce """Baki ga baƙin halin da take ba? Wa ya sani ko shine take yiwa samarin take kora su""" "Abincin ta ajiye bata ce komai ba ta juya za ta fita wata cikin dangi tace ""Taimakeni da Ruwa mana hibbah""" Ba musu taje ta ɗauko ta kawo ta zo shigowa ta ji matar na ba da labarin rigimar da ta haddasa gidan Pendonta har wata ke cewa """Dama daga ganin yarinyar nan bata ɗauki kanta kusa ba, in ba haka ba ina mace ina soyayya" "da wa da kuma ƙani? Ashe ta je ta gama wargaza musu gida""" Jimami suke ta yi. Wacce ta fara kawo zancen tace """Toh kin ga kenan aure ba kusa ba, tsorona Allah tsorona ta kwaso ma su Yaya Mudassir abin magana, ina zan iya zama goɗe-gode ina haɗa kafadu da uwata?""" "Bata son jin karshen maganan don kafafunta rawa suke, zuciyarta kaman zai fito idanunta sun sauya sossai ta saki ruwan a wurin ta juya kawai ta bar wurin tayi sama, ɗakin Momma ta je ""Momma ki ara min key""" Momma dake duba abu kuma ɗakin nata da wasu ƙawayenta tace """Ki duba saman bedside, wai ma kun gaisa da iyayenki?"" ""ina yininmu?""" "Ta faɗa a tare muryarta wani iri. ""Hibbah ashe kin zo""" Wata kawar momman ta faɗa kai ta gyaɗa tana nufar inda key ɗin yake """Hibbah a dage dai a fidda miji wannan karatu ba inda zai kai ki ga 'yar uwarki har tana shirin zama uwar 'ya'ya uku""" Bata ce komai ba don ta fara ganin duhu ta dauki car key ɗin ta fice daga ɗakin kai tsaye mota ta shiga ta bar gidan... "A hanya ta tsaya tayi kuka sossai sai da ta ji ta daina jin raɗaɗin da take ji kan ta fita ta wanke fuskarta kawai ta ji tana son ƙarasa wa gidan Umman Najeeb, chan ta je Umman tayi murnan ganinta ƙwarai Najeeb ma yana gida don sunday ne, ta samu ashe mahaifinsu Nihla na ta fama" da jinya bayan sun gaggaisa ta sha ruwa ta zauna shiru. "Daga Umma har Najeeb sun fahimci tana cikin damuwa, ya ce ""Na ji yau ake kai kudin su Aina'u ko?""" Kai ta gyaɗa bata ce komai ba. """Daddy ya ta matsawa in je, sai dai ban ji ina son zuwan ba Allah ya kaimu lokacin da lafiya"" Ta ce Ameen kawai." """Hibbah kaman ba ki jin daaɗi?""" A hankali tace """Kaina ne ke ciwo Umma""" """Ki shiga ciki ki kwanta bari na kawo miki magani da ruwa""" "Ba musu ta miƙe ta shige, Najeeb ya dubi umma" """Kaman tana cikin damuwa""" """ƙwarai nima na fahimci hakan, amma ka san mu mata a lokuta da dama maganganun mu kan yi tsauri ba tare da mun damu da ciwon da wanda ake faɗawa zai ji ba, na tabbatar koma menene a kan auren ƙannenta ne!""" "Najeeb ya ji duk ba daaɗi, Umman ta miƙe ta shiga dakin ta bata paracetamol ta sha ta zauna" tare da ɗora kan Hibbahn kan kafafunta tana shafa kanta har tayi bacci don jiya fargabar abinda za'a yi mata yau ya hanata bacci gashi kuwa sai da aka yi. "Umma ta baro ta ɗakin ta fita don sama mata abinda zata ci idan ta farka, tayi bacci sossai don sai dab Magrib ta tashi da wani ciwon kan ta wanke fuskarta don tana hutun sallah sai a lokacin ta tuna ko waya bata fito da shi ba, ta fito ta ci abincin da umma ta tanadar mata a lokacin ma ana ta kiraye kirayen sallah tace za ta tafi, Umma tace ta bari in an yi isha Najeeb ya mayar da ita, bata Musa ba Umman tayi ta mata nasiha a kaikaice, murmushi kawai tayi umma bata fahimci cewa ba rashin auren bane ke sakata cikin damuwa ba yadda mutane suke kallonta ne ke damunta ga sauyin da ta haddasa gidan Mommy babu mai fahimtarta kawai ita ce bata kan" daidai a koma menene. "Bayan isha Najeeb ya ɗauketa suka nufi gida, ƙasa haƙuri yayi da shirun ta yace" """Hibbah akwai wani abin da yake damunki ne? Ni ɗan uwanki ne kuma likitanki yanayin ki ya nuna stress da tarin damuwa feel free wurin bayyana min matsalar ki zan ba ki shawara iya iyawata""" Idanunta ta ɗan runtse ta buɗe suka shiga zubar da hawaye """Haƙiƙa ina cikin damuwa Yaya Najeeb amma ban san ta inda zan dosa ba, ba kowa ne zai fahimci abinda nake ji ba, Yaya Najeeb ina jin kaman idan na mutu sai na fi samun natsuwa da kwanciyar hankali akan in cigaba da rayuwa, wani sa'in ina jin kaman in Samu Daddy Kawai in ce mishi ya aura min koma wanene idan hakan shine zai sa in tsira daga mummunan tarkon da So ya ɗana min...""" "Kuka take yi amma ya fi ta jin damuwa a ranshi, kaddara ne ta riga fata idan ba haka ba da" Hibbah bata zubar da hawaye ba. """Hibbah!""" "Ta ja hanci tana share fuska wasu hawayen na kara zuba tace ""Na'am Yaya Najeeb""" """Kar ki yi gaggawa, kar maganan mutane ya dameki kwata kwata shekarunki nawa? Ko kin san akwai waenda ma suke fin talatin ba tare da ko auren fari sun yi ba? Bari ki ji Namijin da kika zaɓa fa shi ne zai gina rayuwarki ko kuma ya wargaza ta, wasu matan suna gaggawar yin aure saboda matsi da suke fuskanta daga dangi da jama'a, ko kuma ganin kaman ke kaɗaice kika saura cikin pairs ɗinki, Hibbah ba kowa ne ya kamata ki aura ba don ba kowa ne ya cancanceki ba saboda kawai yana sonki ko kina son ganin kin yi auren. Ina so ki sa a ranki cewa duk abin da kika yankewa ranki kina zaban salama ne ko akasin hakan nan da shekaru kadan masu zuwa, kar ki bari wani dalili ya sa ki yi zaɓen tumun dare ki cigaba da focusing kan rayuwarki, ki" "cigaba da Adu'a nagarin na nan zuwa""" "Ta gyaɗa kai duk abin da ya faɗa haka ne a hankali ta kalleshi ""Idan kuma na zaɓi ƙin yin auren na har abada fa?""" Shiru yayi don kalaman sun fito ne daga ƙasan ranta """Ina jin cewa maza bukatarsu ɗaya ne kawai a kan mace, idan zan yi aure ban samu farin cikin da nake fata ko buri ba gwara in zauna har abada ba auren Yaya""" """Hibbah aure ibada ne kuma cikar farin ciki ne, aure wani hanya ne na samun ladar da zai kai ki ga aljannah""" """idan irin nawa soyayyar ne ba zan taɓa dace ba Yaya, muddin kuma na kawar da ido kan gaskiya na tsunduma auren ba dai ya kaini aljannah ba kila sai dai ya kaini zuwa wuta, Meyasa mutane ba za su kyale ni in ji da damuwata ba? Bayan abin da na fuskanta da Usaib ashe Yaya Nasir da Yaya Abdul ba za su iya bari in huta ba za su nemi kasheni da rayuwata? Meyasa za su ɗora min guiltness na rabasu da ahalinsu? Meyasa ba za mu koma rayuwa kaman baya ba" "don na zaɓi cewa duk na hakura da su saboda gudun haddasa fitina? Me laifina don Allah?""" "Sossai ta bashi tausayi, jikinshi yayi sanyi, bashi da abin cewa amma ciki maganan ta ya fuskanci abin da ke cin ranta, ruwa ya bata ta sha, ya juya kan motar zuwa asibiti bata ce komai ba suka je office nashi ya bata wasu magunguna ta sha ba musu ta sha ɗin kan ya dube ta" """Kin faɗawa su Daddy da kika fito?"" Ta girgiza kai." """Ya kike jin zuciyarki Hibbah?""" "Ta girgiza kai don ba zai misaltu mata ba, wasu allurai ya haɗa yayi mata don numfashinta yayi" "nauyi sossai, duk ya damu ina ma yana da ikon fidda Hibbah cikin wannan hali? Ina ma akwai taimakon da zai iya mata na samun tabbatacen farin ciki?" "Idanunta a lumshe ta ji ya ƙira Daddy hankali tashe ya ɗaga yake sanar da shi ba'a ga Hibbah ba tun rana ta fita da motar Momma har yanzu bata dawo ba, nan ya sanar da shi ai tana nan gidansu amma yanzu tana asibiti faɗa Daddy ya shiga yi akan me zata fita bata sanar da inda zata ba? Idan wani abu ya sameta me za ta ce duk ta ɗaga musu hankali, tana jinsu bata motsa" ba har Najeeb ya gama ba Daddyn haƙuri. "Karfe takwas da rabi duk 'yan gidan suna asibitin har Hajiya kamila dake cewa kila bakin cikin ƙannenta za su yi aure ne ya tada ciwonta, duk tana ji amma dayake bata son Magana da kowa bata tanka ba bata bude ido ba, Aina'u tace" """Ai abin da Allah kuma ya nufa dole zai faru ba gwara ta sanyawa ranta salama ba? Ko za mu zauna mu jira ta ne har sai ta auru?""" Hudah tace """Ke?? Aina'u kina cikin hankalinki kuwa?""" "Bata ce komai ba, Zaitoon tace ""Fita a ɗakin nan Aina'u""" Ta juya ta fice don ita har ga Allah Hibbahn ta fara bata haushi Haba ba zata yi haƙuri da ƙaddararta ba kullum tana nan tana ɗaga musu hankali ji babban ranansu ta so lalatawa kuma su yi magana ace rashin kunya da falli. "Juyawa Hibbah tayi kaman cikin bacci ta fuskanci gini bata iya yin komai ba sai shiru, ƙarfe kusan goma suka samu ta sake ta farka suka yi mata sannu kan suka tarkata zuwa gida, Hudah kaman Mu'azzam da ya zo ɗaukarta ya barta ta kwana da twin sis ɗinta amma bai yarda ba" haka suka tafi su ma. "Zaitoon ce ta cigaba da yi mata maganganun kwantar da hankali kuma dayake tare suka kwanta sai bata yi dogon tunani ba ta yi bacci da kyar ta ci sati ɗaya a Kano ta bi Zaitoon suka tafi Keffi a kan daga chan za su koma legos, Dukda Najeeb, Mumtaz, Zaitoon da Hudah basu barta ita kaɗai ba sun taka muhimmiyar w rawa wurin ganin komai ya wuce a wurinta tana kuma nuna musu fuskarta komai normal amma ƙasan ranta tana fighting depression a hankali kuma tunanin ƙin aure ya gama shigarta ta fara bincike a kan sahihancin ƙin yin aure a musulunci a ta karanta alfanun a bincikenta na ɗayar ɓangaren ta ci karo da littafin 'Al'ulamul uzzab Allazina afdhalul ilmu alal zawaj' ta karanta cewa malamai ne har talatin da bakwai da duk sun koma ga mahallaci ba tare da sun yi aure ba ciki har da mafiya shahara a fagen ilimi irin su Imamun nawawi da ibn taimiyya." Ta Yi bincike mai zurfi da wasa da wasa don duk lokacin da ta bata gidan Aunty Hasiya tana kan karatun littafin ne. "Ana kwana ɗaya ya saura za su koma legos Aunty Hasiya ta fita da su sayayya da kyar ma Hibbah ta amince za ta je suka shirya suka fito, sanye take da Abaya lighter Brown yana da adon black zare, ta ɗaura Black jercy scalf sai ta jefa gyalen a kafaɗarta kawai hannunta riƙe da wayanta suka fita, ita da Asma'u da Zaitoon suke zagayen duba abin da za su buƙata yayinda Aunty Hasiya ke riƙe da Aryan tayi hanyar wurin abubuwan yara don mishi sayayya, wani matashi dake ta kallonsu sun Shigowarsu ya bi bayansu, sallama yayi musu ita dai Hibbah ko ɗaga kai bata yi ba, Zaitoon ta amsa ya ɗan yi murmushi" """Sunana Adam, don Allah Layin wannan nake so na tambaya i hope ba matar aure ba ce""" "Kallon wanda yake nunawa Hibbah tayi sai ta ga ita ce, ta mishi wani kallo kan tace ""Toh matar auren ce sai ka mayar da kwalamarka""" Zaitoon tace """Haba Hibbah! Wani irin zance ne wannan""" """Kar ki damu yayarmu ai na san faɗe ne kawai don bata yi kala da matar aure ba""" Ranta ne ya ɓaci ta harzuko """Da yake rubutawa ake a Goshi a lika ko? Toh na ce matar auren ce ka kyaleni ka kama kanka kuma tun kafin in yi maka rashin mutunci""" Hannunta Zaitoon ta riƙe ta ja ta gefe """Calm down Hibbah don Allah menene aibun wanda ya ce yana son ka? Idan ma bakya son shi ai ba haka ya kamata kina amsa shi ba""" """Me a cikinsu in ba ƙarya ba? Wani abu za ka tsinta a cikin son da ba na Allah ba sai don biyan buƙata? Ni dai ya kiyayeni wallahi ko in zabga mishi rashin mutuncin da ba zai taɓa mantawa ba""" "Duk yadda ya so ta kulashi ta ƙi numbernta ma da Zaitoon ta yi niyyar bashi tace wallahi tana bashi sai duk ta kaisu kotu shari'a ta raba su, sossai ta ba Zaitoon da Asma'u tsoro ganin za su ballo ruwa ya sa suka bashi hakuri ya tafi, karshen sayayyar da bata yi ba kenan ta fice ta jira su a mota, wayanta ta shiga ta mayar da settings ɗin inda idan bata da number ɗinka ba zai shiga ba ta cigaba da zama a wurin har Aunty Hasiya ta zo ta ji abinda ya faru, faɗa ta shiga" mata basu san mafarin ba kenan daga ranar duk namijin da zai mata magana rashin mutunci ke "raba su, tun ana yi mata faɗa har suka gaji suka zuba mata ido ko da ta dawo legos ma bata" sauya ba... "*Littafin nan na kuɗi ne ki biya Naira Ɗari biyar (500) kachal domin kasancewa cikin masu kwasar tarin ilimi, faɗakarwa da zazzafar soyayya mai cike da sadaukarwa da aka zube ciki. Za ki biya ta wannan asusun" 0545475847 Gt bank Fatima Muhammad Gurin Sai ki tura shaidar biya zuwa wannan layi 09039206763 Ko kuma katin MTN na Naira 500 cikin wannan layi na sama sai ki tura da shaidar biya ta same layi. Sai na ji ku* Gureenjoh 38 "Ta yi 3 good months tana IT daga ma'aikatan har shuwagabannin da suke nan manufacturing company sun yi matuƙar jin daaɗi aiki da ita, kasancewar abin da ya kaita kawai take bata shiga huldar da ba'a sanyata ciki ba, har Director HR department na main company ɗin ya zo kusan sau uku yana duba yanayin aiki da ita kuma ya samu good review Log book ɗinta excellent a" "jere, da kanshi ya neme ta chan company ɗin bayan ta gama da su." "Ta saka rana kuwa ta faɗawa Mommy akan za ta je mommy ta mata Allah ya tsare ta fice, ƙarfe 10 na safe ta isa kasancewar sun taɓa zuwa da Nasir ta gane har office ɗin shi bayan sun gaisa ya ƙara yabon hazaƙa da mayar da hankalinta kan ya tabbatar mata next time ko da service ne in ta fita suna bukatar ta don samun makaranta kuma masu hazaƙa a ɓangaren mechanical Engineering yana yi musu wahala, ta amsa kuwa dayake suna ba da allowance mai kyau bata ƙi ba tace ba damuwa in shaa Allah nan da 2yrs za ta dawo suka yi sallama da exchanging" contact ta tafi daga nan school tayi ta ɗan yi abinda ba za'a rasa ba kan ta wuce gida kai tsaye. "Ita da Mommy suka fi rayuwa cikin gidan don Daddy ba mazauni ba ne, Nasir kuwa sai dai ta jiyo suna waya da mahaifiyarshi shi kuma Abdul ba shigowa yake ba a yanzu kullum ma yana ɓangaren shi ko wurin aiki, idan wani abu ya shige mata duhu a karatun har kuka take idan ta tuna yadda Nasir ke taimakonta, wani lokaci ta haye wani lokaci ta faɗi haka ta cigaba da gurgurawa har lokacin da aka diba na auren su Aina'u ya iso, a yanzu ta rage waya da mutanen gidan sam hatta Hudah sai su yi kwana biyu kan su gaisa, tana kallo Aunty Kubra na ta shirye- shiryen tafiya Kano bata ce komai ba, Zaitoon ma ta zo gidan don su haɗu su wuce ranar da" Aunty za tayi booking flight Hibbah ta ce """Ku biyu fa za ki yiwa Mommy""" Kallonta ta yi """Ban gane ba? Kina nufin ba za ki ba Hibbah?""" "Kai ta gyaɗa ""Saboda?""" """Ina da wasu tests masu zafi a kwanakin idan na bari na tafi zan iya samun matsala""" "Ta faɗa ko a jikinta don bata shirya zuwa abinda za'a so kasheta ba, daga nan inda take idan ta yi musu Adu'a zai same su har i da suke don haka ta ce Allah ya basu zaman lafiya, haka Aunty Kubra tayi booking su biyu ba don ta gamsu da hujjar Hibbah ba suka wuce Kano, ko a jikinta ta cigaba da karatun ta da aka bada hutun christmas da New year ta cigaba da zama a gida cikin neman abinda zai mantar da ita wani matsala ko damuwa ta shiga kallon Series na The" Originals kuma tana jin daaɗinshi ƙwarai.. Satin su Aunty Kubra biyu suka dawo ita dai ta ƙira amaren waya ta musu Allah ya sanya alkhairi kuma da Su Zaitoon suka yi ta posting pictures na bikin duk ta yi ta resharing a nata status ɗin har yanzu kawar da za ta ce ta yi a jami'a daya Kaosara suma good terms sossai ranar da ta kunce mata shine ranar da ta ba wani guy dake ta bibiyarsu contact ɗin Hibbah tayi mata kaca-kaca da sai da ta ji tsoro tayi ta ba hibbahn haƙuri shima ta tsefe shi tsaff. "Ko da suka gama First semester 400 dole ta je Kano saboda riskar rasuwar mijin Umman Najeeb, ta ji musu rasuwar sossai ta tausayawa su Nihla, ita da Momma suka je gaisuwar ita" kam har kwana ta yi a gidan Washegari ta koma gida a ranar Momma ta ajiyeta. """Wai me kike nufi ne Hibbah?"" Ta mata kallon rashin fahimta ""Me ya faru Momma?""" """Tambayata ma kike? Yanzu kam na kula da gayya kike ƙin zancen aure... Haka za ki zauna Ƙannenki kowacce na shiga daga ciki tana barinki? Aina'u fa ciki ne da ita mai girma, Hudah har ta yi uku kowa na ganin ni nake ɗaure miki gindi kike zaune a gida har yanzu to ba zan iya ba, idan ma korar samarin kike gwara tun wuri ki san na yi kina ji na ko? Ba Za ki gama karatu ki cigaba da zaman legos ba sam""" Fuskarta a turbune ta ce """Haba Momma ashe kema kin fara daukar maganganun mutane na rashin kan gado? Auren nan fa lokaci ne ki bari lokacin yayi ai zan yi""" Cikin ko oho ta yi maganan. """Hibbah ko da lokaci ne akwai niyya don haka ki ɗaura damara""" Ta ɗan taɓe baki """Amal da Nadiya za su ɗaura aure watan goben azumi da za'a shigan nan""" "Ta sake taɓe baki cikin ko in kula tace ""Allah ya basu zaman lafiya""" "Momma ta amsa da Ameen ganin ko a jikin hibbar, numfashi ta sauƙe tana kallo Hibbar ta fice." "Kwananta uku tana zirga-zirgan gidan su Umma kan na hudu ta tafi Gidan Hudah, daga ita har yaran sun yi matuƙar murnan ganinta suka rungumeta suna tsalle, ta kalli ƙanin nasu mai kama da babanshi tayi pecking goshinsa" """Allah ya kare ka da mugun halin maza""" Hudah tayi murmushi """Wani irin Adu'a ne wannan?""" """babban Adu'a da kowani namiji ke bukatar nanaci tun daga za in goyo"" ""Hibbah me kika ɗauki maza ne?""" """Duk wani ma'auni da zan auna abin da ke raina dangane da su yayi kaɗan don haka ki kyaleni" "tun kan ki ɓata min mood""" Hudah ta ce """Hibbah ba duka bane suka taru suka zama ɗaya kar ki yi musu kudin goro kin ga Babansu Amna wallahi duk inda zan fasalta miki ya wuce nan, shi ɗin tamkar tsani ne a rayuwata da yake ɗaga ni zuwa kololuwar daraja, zan iya ce miki a zamanmu na shekaru biyar din nan da muke ciki bayan rigimar mahaifiyarshi a baya bamu taɓa samun babban matsala a tsakaninmu ba, akwai irin su dayawa masu son cigaban matansu, na gama karatu na gama service kafin Daddy yayi maganar sama miji aiki Mu'azzam ya kawo min appointment kuma aiki mai kyau, a haka albashina bai taɓa taɓawa ba kuma bai taɓa bari na sayi ko pad bane da albashina, ki" "kyautata mu...""" """Na ji Hudah kuma na miki murna har ƙasan raina, tunda ke kin samu ni ba sai na dami kaina" "ba""" """kin manta hadisin da yayi magana kan falalar 'ya'ya wurin iyaye? Su ɗin fa rahama ne ta ya za" "ki same su idan kina ƙin batun aure?""" """Ga naki ai su ɗin ma nawa ne ko ba za su min Adu'a ba idan na mutu?""" Ganin tana kokarin juya zancen zuwa mai zafi ya sa dole Hudah ta kyaleta don ta kafe kan ra'ayinta. "Ta jima a gidan tare da yaran amma bata bari Mu'azzam ya dawo ya sameta ba tayi tafiyar ta, bata je Gidan Aina'u ba don gudun abin bacin rai sai ita ne ma ta sameta a gidan ranar da ta zo ""Yaya Hibbah shine ko ki zo gidana?""" """Raba ni! Kin manta gidan surikai ne? Ko kina so a fara yi da ni a gari?""" Aina'u ta ɗan yi saka ka """Saboda kin zo gidana Yaya Hibbah?""" """Saboda dai bai kamata ba ina buduruwa a ganni gidan kanwata matar aure""" "Duk inda Aina'u ta fito sai ta tare a karshe kuma bata je ɗin ba, haka ta koma legos ta shiga final semester ɗinta watanni uku gaba suka gama a ranar ne ma momma ke sanar mata haihuwar Aina'u da kuma auren Su Amal da aka ɗaura ta musu murna tace za ta kira su duka" anan ma sai da Momma ta sake maganar aure don yana damunta kwarai duk sadda ta tuna. "Azumi a legos tayi shi tsaff ta ƙi zuwa Kano, bayan sallah suka shiga camp inda ta sa Daddynsu" Abdul ɗin ya yi hanyar da zai yi aka barta nan legos kuma PPA ɗinta ya zama MB MUSTAPHA AUTOMOBILE INDUSTRIAL LIMMITED "Ranar da taje reposting Director ɗin ya ji daaɗin ganinta sossai tuni suka yi accepting ɗinta inda wannan karo ya barta a main branch ɗin son ta koyi sauran ayyukan, a nan office dinshi ya fara ajiye ta da team ɗinsu ta fara aikin daga nan a hankali ya fara fahimtar irin kaifin basirarta sai ya tura ta design and strategic team don suna bukatar mai irin kwakwalwarta, ranar da aka kaita desk na musamman aka bata da system, akwai ma'aikata dayawa a ɓangaren daga chan sama" kuma akwai karamin office na glass da katon table mai dauke da system da wasu takardu. "Daga inda take tana iya hangar namijin dake zaune a wurin haka shima da zai ɗago zai iya ganin kowa a ɓangaren, wata matashiya da za ta iya girman ta ta ce mata" """Sannu""" """Hi i am Raliya and you?"" ""Hibbah""" """Nice meeting you""" Ta miƙa mata hannu suka gaisa daga nan ta mayar da hankalinta kan aikinta. Chan ta ga duk sun miƙe sun tsaya ɗago kai ta yi sai ta hangi matashi ɗazu ne ke fitowa hakan ya sa duk suka tsaya a tsaye itama ta miƙe har ya zo ya fita """Waye wannan?""" Tayi tambayar tana kallon Raliya """Kanin mai kamfanin shine babban manager na nan, Mahir Bashir Mustapha amma idan baki sani ba za ki dauka shine mai kamfanin don karfi da yaji shima MB MUSTAPHA ake kiranshi ga" "izza da jiji da kai fiye ma da asalin MB MUSTAPHA ɗin.""" "Hibbah ta ɗan taɓe baki daidai lokacin da yake dawowa idanunshi suka sauƙa a kanta, a hankali ya cigaba da binta da kallo tana dai tsaye amma sam ba shi ma take kallo ba bata sani ba gabanta ya iso ashe ɗago kan da zata yi don ganin ko ya gama wucewan ta koma ta zauna" sai suka haɗa idanu. """Wa ya kawo ki nan?""" "Yayi tambayar a yatsine kaman ba zai yi ba ""Director HR""" """Meyasa ba'a kawo min record naki ba? Meyasa Director ke shiga min hanci da kudundune?"" Cikin masifa yayi magana ranta a haɗe fuskarta ba digon fara'a jin irin hargagin da yake yi tace ""I am just a Co-member not a permanent staff kila shiyasa""" Tsaki ya ja da karfi ya juya ya bar wurin ta taɓe baki tana zama wannan kam idan nuna isa da gadarar ƙanin ya kai haka Allah andi yayan kuma gaskiya yaya Nasir ya yi kokarin aiki da su. "Har aka tashi bata bar kan desk da aka ajiyeta ba don aiki Raliya ta haɗa ta da shi take ƙarasa mata tana da fahimtar mutane sossai da kuma yanayin wuri, ta karanci Raliyar akwai son banza da son nuna ikon da bata dashi, ta karbi aikin ne ba don ya zama dole ba sai don bata son zaman shirun." Shi kuwa wanchan masifaffen bata san dalilin da ya sa duk ta ɗaga ido daga inda take za ta ga yana kallonta ba. "Haƙiƙanin gaskiya bata ji daaɗin Service kaman IT ba ba kuma don yawan aiki ba a'a sai don waenda suke zagaye da ita ta ji bata yinsu sam, Allah Allah take ta gama ta bar musu companyn, riƙe kanta take kar ta zabgawa Mahir ɗin nan rashin mutuncin da bai taɓa gani ba a rayuwar sskaltar shi, ita kuma Raliya ta fara jin haushin Hibbah ganin har ta saba da Director HR sossai ga Mahir da yanzu ko waye ne yayi mishi aiki zai ce bai yi ba a ba Hibbah ta gyara ta kawo mishi, har allowance suka ƙara mata ga ma'aikatan sashen kowa mutunci take da shi hakan ya darsa haushi da tsana nata a zuciyar Raliya ba tare da ta bari ya fito fili ba kuma tana" rikewa a ranta ne saboda sanin kwana kusa Hibbahn za ta bar su. "Bata taɓa ganin asalin MB MUSTAPHA ɗin ba kuma bata taɓa tambaya ba, hasali ma attitude" "na ƙanin shi ya sa ta tabbatar shima duk halinsu ɗaya, fuska ne kawai Mahir bai samu cikakke daga gareta ba amma da yanzu wani batun ake." Yau dai ya shirya tsaf don nuna mata abin da ke ranshi game da ita don haka ko da ta zo zata yi sign out ya ce ta jira yana son bata wani aiki. Tun karfe biyar har shidda da wani abu tana jiran shi sai da kowa ya bar wurin kan ya ɗago ya dube ta ta sake tamke fuskar tamau da har ya ji shakkarta sai dai ya dake ya shiga magana.... "*Littafin nan na kuɗi ne ki biya Naira Ɗari biyar (500) kachal domin kasancewa cikin masu kwasar tarin ilimi, faɗakarwa da zazzafar soyayya mai cike da sadaukarwa da aka zube ciki. Za ki biya ta wannan asusun" 0545475847 Gt bank Fatima Muhammad Gurin Sai ki tura shaidar biya zuwa wannan layi 09039206763 Ko kuma katin MTN na Naira 500 cikin wannan layi na sama sai ki tura da shaidar biya ta same layi. Sai na ji ku* Gureenjoh 39 *TWO PAGES NA SO YI NA GAMA WANNAN NA YI NISA A 40 KUMA BACCI YA CI KARFIN IDONA DA SAFE ZA KU JI NI IN SHAA ALLAHU. BABU EDITING A LALLAƁA* """ummm wani ɗan aiki ne anan nake so ki je ki ƙarasa, it's a proposal ga nan topic ɗin sai ki fidda duk abin da kike gani ya dace""" "Ya faɗa, sossai ta mishi kwarjini yadda ta kame fuskan ya ɗan sa ya sha jinin jikinshi don haka" ya fasa niyyarshi zuwa wani lokaci. "Bata sake fuska ba amma ta karɓa ""Zuwa yaushe?""" """Next week nake buƙatarshi but please yayi kyau as always""" Kai ta gyaɗa """Have a good night Sir""" Ta faɗa tana Miƙewa har ta riƙe handle na kofan yace """Ammm would you mind na yi dropping ɗinki off?""" "Bata waigo ba tace ""Thanks am with a car""" "Daga haka ta fice tana jan tsaki, don dai aiki ne ya sa zata yi saboda tana jin daadinshi yana debe mata kewa yana kuma mantar da ita duk damuwowinta shiyasa idan tayi ɗin sai ya fita" daban. Kai tsaye gida ta koma bayan tayi wanka ta ci wani abu ta fara reshearch ɗinta kan proposal ɗin sai da dare yayi sossai ta kwanta da safe ta sake fita aiki. "Ta Yi spending memorable time a service Dukda irin matsi da ta fuskanta daga Raliya ga yawan sa idon Mahir hakan bai hanata enjoying moments ɗin ba, bata damu ba don babu wanda ya taɓa hailing nata ko noticing irin iya aiki da kaifin basirarta ba ta ji daaɗin samun baje irin basirarta da take gani aka barta sai ta chanza musu companyn nesa ba kusa ba, sati biyu ya saura mata POP ba ita kaɗai ba har Raliya daaɗin barin Hibbah companyn take ji don tana ga wanzuwarta a nan ɗin ba karamin barazana bane ga ita, yarinyar ta fiye shiga mata ido gashi a" "komai baka isa karawa da ita ba, very classy nd intelligent she's just juleous of her in all ways." "Kiranta Mahir yayi, ta gama abin da take kan ta nufi office ɗin tun da ta doso ya zuba mata ido komai nata na sake tafiya da imaninshi yana motsa asalin namijin da yake, da kujera ya jinginu yana juyawa a hankali har ta iso, ya rasa yadda zai yi su saba Dukda ayyuka masu yawa manya da yayi ta sakata tana yi kuma komai na tafiya mishi yadda yake so bata taɓa sakewa ko wani hira ya shiga tsakaninsu ba, tana gama bayanin ta zata fita kuma fuskar nan babu wani" walwala. """Ga ni""" "Ta faɗa daga tsaye ""Sit please""" Ta zauna """Na ji 2weeks kachal ya rage miki a wannan company?"" ""Eh""" """What if na ce zan yi retaining ɗinki da matsayi mai girma? I like you, your confidence, your talent komai na aiki da tsarinshi kin iya delivering sannan blindly kin yi min hanyar samun kudade masu tsoka ba tare da saninki ba, i would like to repay you da samar miki permanent" "aiki da mu gaskiya""" Ya zaci zata nuna farin ciki da zakuwa sai ya ga har lokacin fuskar nan kadaran-hadaran """Zan yi tunani akan hakan but ba lallai ba because am not living here so i've go back home if necessary""" Yayi mamaki """Kina da wani damuwa ne Hibbah?""" Ta ɗan mishi kallon me naka? Kan ta girgiza kai """May i have your contact? As ur boss ya kyautu idan kina da wani matsala ko financialy ko personally just ki min magana i would like to help u out""" """I am sorry but bana tunanin zan bukaci ko ɗaya, can i take my leave?""" "Wacce iriyar yarinya ce wannan? Me take ji da shi? Ya yiwa kanshi tambayar idanunshi na a kan bayanta har ta bar office ɗin, lip dinshi na kasa ya datse yana sake jin kwalamarshi na" ƙaruwa a kanta dole zai san abin yi tabbas. Director HR ke presenting wani ɗan aiki gaban Marketing manager bayan sun gama batun aiki Marketing manager ya dube shi """Director ka kula watannin nan irin cigaba da muke samu a wannan company? Shi fa karan kanshi Chairman yabon Manager yake da sabbin tunanukanshi akan harkar kamfanin nan""" Director yace """Da ya san ba shi yake aikin ba sai ya yi mamaki kuma ranshi idan yayi dubu sai ya ɓaci, you know him baya son wani ya ɗauki Credits na wani a aiki, zakewar Mahir na nuna tamkar komai idea dinshi ne""" "Marketing maganer ya gyara zama ""Seriouly ba shi yake yi ba?""" Murmushi Director ɗin yayi """Ba shi bane wata Corp member ce Hibbatullah Mudassir Madaki young lady sai brains, i just" "kept quite kar ya ce an shiga tsakaninshi da ɗan uwanshi but with time i hope Chairman ya fahimta ba shi ke yi ba""" """then we have to retain this girl... I can't believe Corp member will have this kind of business" "strategy Musamman a harkar ƙarafa""" """Thats what am trying, komai nata ma na gaban Chairman da zarar ya saka min hannu shikenan we would recruite her""" Kai Marketing manager yake gyaɗa wa cikin Fatan ta samu gurbin aikin don ba za su so ta "subuce ba, daga nan kowa ya koma kan aikinshi." "Bayan kwana biyu kuwa tana zaune tana wani aiki ta samu ƙira daga Director ɗin, barin komai tayi ta tafi office nashi inda ya yabawa aikinta kuma ta ji daaɗi don kaman shi ne kadai yake noticing ɗinta a kamfanin a wurinta, ya kuma damka mata offer mai dauke da sabon salaries da ya bata dumbin mamaki, fara'arta bai boyu ba" """Thank you sir... Thank you so very much""" """You deserve it Miss Mudassir just keep on with ur hardwork""" "Ta sake mishi godiya ta miƙe ta fita ya bita da kallo don ganin ɗiyar cikinshi yake mata, itama ta tafi da yabon kyaun halinshi Dukda ba musulmi ba very nice dattijo." Bata faɗawa kowa ba ta zo ta shigar da shi k "Cikin desk ɗinta, ganin lokacin break ɗinsu ya yi kuma ma It's time for Zuhr prayer ya sa ta ɗauki paper bag ɗinta mai dauke da lunch ɗinta da kuma hijab ninkakke mai tsafta da kamshi ta fita, kai tsaye masallaci taje ɓangaren mata tayi alwala ta gabatar da sallah kan ta gyara fuskarta ta mayar da accesories ɗinta ta ɗauki abincin ta nufi dining Dukda akwai tsaftaceccen abinci kuma mai rai da lafiya da ake serving ma'aikatan ko wani lokacin lunch ta fi son nata dai" na gida saboda yanayin kyankyaminta. "Kuma doka ne bayan snacks ko ruwa ba'a yarda kowani ma'aikaci ya ci abinci cikin wurin aiki ba, idan ba zaka je lunch room ba akwai kananun kitchens kowani department mai dauke da frigde su coffee maker na babban table da zaka iya zama ka ci abinci, nasu ɗin shima bata son zuwa don wasu ma'aikatan department nasu maza da kan zauna a wurin kuma sun fiye kallo" wanda hakan a yanzu ke pissing ɗinta off don gudun rigima ya sa bata zuwa. "Tana zama bata fara cin abinci ba wani dan department ɗinsu ya shigo. ""Congratulations Miss Hibbah ashe an yi recruiting ɗinki... Am happy for you""" "Dan yake tayi tun tana mamaki har tsoro ya kamata dama haka suke yi ne ko menene? Meyasa kowa ya san batun samun offer ɗinta? She taught wannan sirri ne, akwai ma masu cewa they spent years suna nema da kyar suka samu amma ita ta samu cikin sauƙi gaskiya sun mata murna, abincin ne ta ji ya fita mata a ka ta ɗauka kawai ta fita ta shiga elevator zuwa floor da office nasu yake, tana isa kan desk ɗinta ta samu papers da ta adana na offer ɗin zube a kan" desk ɗinta an yi ɗai-ɗai da su. """What is this?""" "Ta ambata ranta na ɓaci fiye da yadda ta zata, idan akwai abin da ta tsana nan duniya a taɓa mata abin da yake nata ba tare da izini ba." """Miss Mudassir kin yi magana ne?""" Wanda yake ɗan dab da ita kan desk ɗin shi ya tambaya don sun san ba maganan ta cika ba ganin yadda take tsayen ya sa ya damu """Who did this?""" """Oh Raliyat ita ta fitar she tells us to congratulate you on ur offer, she's very happy for you""" Lip ɗinta na kasa ta taune kawai ta juya za ta fita sai ga Mahir yana zuwa ya fusgo hannunta cikin fushi har zuwa office ɗin shi suna shiga ta fusge hannun tana murdawa saboda zafin da ya shiga yi mata fuskarta har yayi ja tace """Me hakan? Wani right ne ya ba ka daman tabani?""" """Would you shut up?? Me ke tsakaninki da wanchan tsohon??? Na ce me ke tsakaninki da shi da na nemi retaining naki kika watsa ni shi kuma ya nema miki kika karɓa da gudu?""" Idan ta buɗe baki za ta yi mishi zagin da bai taɓa tunani ta iya ba don haka tayi shiru. """Tambayarki nake?? Uban me yake baki? Toh bari ki ji kar ki yi tunanin da shi da ke duka ba zan iya haɗawa in kora ba, tsaf za ki mishi sanadiyar wannan aiki tunda kamfanin ba na ubanshi bane...""" Juyawa tayi za ta fita ya sake riƙo hannunta tana Juyowa ta zabga mishi lafiyayyiyar mari da ya sa duk jama'ar department ɗin suka miƙe tsaye saboda glass ne kuma yadda yake mata hargowa a kai ya sa hankalin kowa na kansu. "Ba su kadai ba har shi ya shiga shock da bai taɓa shiga ba, lallai yarinyar nan ta cika" cikakkiya...shi Mahir Bashir Mustapha ta mara? """Idan ka isa a yanzu ka koreni, saboda ina aiki karkashinka ba shi ya baka damar iko da ni ba, and ka tabbatar kaf rayuwarka baka sake gigin kai hannu jikina da sunan taɓani ba don tabbas ba zan ƙi tsinka maka mari a karo na dubu ba matsawar ba zaka kama kanka ba""" "Tana kai nan ta fice ta tattare kayanta a kan desk ɗin zata fita Kiran Director ya shigo wayanta, kaman kar ta ɗaga don huci kawai take tana sake Harzukowa shi kuwa yana chan tsaye kaman" an dasa shi sake da baki. Picking tayi """Sameni office now!""" "Fita tayi ta shiga elevator zuwa floor ɗin da office nashi yake, tana zama kawai ta kama hawaye, bai ce komai ba sai wasu daga cikin manyan company ɗin da ya ƙira suka same su, ya" bata tissue ta share fuskarta """What happend Miss Mudassir?""" "Ranta na kuna ta mishi bayanin komai, sai ta ga kaman ɗauka yake a recorder, chan bayan mintuna masu yawa duk suna sanye da kananun eaepeace a kunnuwansu kuma sun natsu ta" ga Director ɗin ya ɗago ya kalleta """I am so sorry for what happened Miss Mudassir, I assure you hakan ba ya cikin tsarin kamfanin nan Chairman gets his hands on this and ya ce in baki haƙuri zai kuma ɗauki mataki kan Raliya that invades into ur privacy da kuma Manager kan abin da yayi and na tabbatar tunda ya faɗa" "sai ya cika.""" "Wato Raliya ce ta fiddo abinda ta ajiye ta nunawa kowa, bata bar office ɗin ba sai da matakin da aka ɗauka anan ta ji sanyi ta kuma ji ba zata bar companyn ba don da tayi niyyar in har ta fita ta fita kenan har abada, ta fahimci ko waye Chairman ɗin mutum ne mai adalci, yadda suka natsu suna magana da shi ta abin maganan da suka makala a kunnuwansu ya tabbatar mata mutum ne mai natsuwa da kuma rashin son hargagi sannan yana da adalci da bai bi bayan ƙaninshi da" ma'aikaciyar da ya jima tare da ita ba ya bi bayan gaskiya. "Washegari bata ga Raliya ba haka Mahir ma ta cigaba da aikinta hankali kwance sai bayan sati biyu ta yi POP ma aka sake kiranta suka bata haƙuri har su Raliya ɗin da Mahir karan kanshi amma irin kallon da yake mata ya sa taji a jikinta wani abu ya sauya, bata damu ba ta cigaba da" aikinta hankali kwance. Yau ta gama shiri zata fita kenan Aunty Kubra ta ƙirata """Ni kam Hibbah"" ""Na'am Mommy""" """Ina ce kin gama Service ɗin nan ne zuwa company kuma na me kike yi?""" "Shiru ta ɗan yi kaman ba zata ce komai ba sai kuma ta ce ""Ai sun ba ni aiki da su""" """Sun baki aiki Hibbah? Shine kika yi gaban kanki kawai kika cigaba da zuwa ba tare da mun sani ba ko iyayenki sun sani?""" """Mommy ni dai ba zan iya komawa Kano a yanzu ba, idan da za ki min alfarma da kin barni idan" "na shirya zan sanar su momman da kaina cewa na fara aiki don bana so su hanani""" """Hibbah!""" Gwiwarta ta kai ƙasa muryarta na kara sanyi da rawa tace """Idan na je kanon me zan yi ban da cigaba da jin kalaman Momma masu yi mini ciwo? Mommy duk fa ƙannena zuwa yanzu babu wacce take gida koyaushe hankalin Momma ba'a kwance yake ba tana ganin ni ce na ƙi auren alhali shi ne bai zaɓeni ba ni ma kuma na ji na hakura da shi na har abada, ba ita kaɗai ba family ba za su bar ni ba zama a gidan chan ba karatu, ba aiki" "sai dai ya kasheni Mommy please ki kyaleni anan don Allah""" Tausayi ta ba Aunty kubrah ɗin ta ɗaga ta """Hibbah ko shekara dubu za ki yi gabana ba zan kore ki ba kuma ba za ki gundure ni ba, ki yi haƙuri ki kara a kan wanda kike, na sha gayawa mahaifiyarki maganganun mutane ya daina tunzurata tana ɗaga hankalinta har tana miki kalaman da basu dace ba akan rashin aure amma ta kasa fahimta tana ganin kawai ina daure miki ne kina abin da kike so, na fi kowa fahimtarki kuma a yanzu ko ban fi kowa saninki ba na san fiye da rabi da kwatar halayenki... Ki cigaba da aikin ki idan kin shirya faɗa musu da kaina ma zan sanar musu kuma zan nuna musu da goyon" "bayana""" """Na gode sossai Mommy"" Murmushi Aunty Kubra ta mata ""Allah ya baki miji nagari Hibbah""" Bata amsa ba ta juya ta fice don tana ga babu amfanin adu'ar saboda babu nagari a ƙaddararta. "*Littafin nan na kuɗi ne ki biya Naira Ɗari biyar (500) kachal domin kasancewa cikin masu kwasar tarin ilimi, faɗakarwa da zazzafar soyayya mai cike da sadaukarwa da aka zube ciki. Za ki biya ta wannan asusun" 0545475847 Gt bank Fatima Muhammad Gurin Sai ki tura shaidar biya zuwa wannan layi 09039206763 Ko kuma katin MTN na Naira 500 cikin wannan layi na sama sai ki tura da shaidar biya ta same layi. Sai na ji ku* Gureenjoh 40 Tana iya karantar abin da ke fuskar Mahir gareta amma bata so zuciyarta ya tabbatar bayan "haushi da takaicin ta da yake ji akwai wani boyayyen abu da kai tsaye ba zata ce so ba, aiki yake tula mata wane wane kuma bata taɓa kasa yi ba." "Raliya ta gama cika ta batse da haushi, hassada da tsanar Hibba saboda tana ganin ta tare mata abubuwa dayawa a wurin aikin, tun kuma abin nan da ya faru Hibbahn bata wani sake mata ba, yau suna zaune kowa hankalinshi na kan aiki Raliyar ta buɗe jakanta ta fiddo wani" choculates guda biyu ta ɗan ja baya da kujerarta ta matsa jikin table na Hibbah ta miƙa mata """Ga choculates"" Girgiza kai Hibbah ta yi ""No thanks""" """Hibbah har yanzu baki yi haƙuri da abin da ya faru ba ne?""" "Hibbah ta ɗan kalleta ""Ya wuce ai Raliyat""" """Da ya wuce da kin daina wannan cin maganin, da ya wuce da ba zan baki abu ki ƙi karɓa ba, don Allah ki yi haƙuri ba da wata mugun manufa na sanar ba na zaci abin farin ciki ne da ya kamata kowa ya tayaki murna, ni na fi shekaru biyar tun ina gidan mijina nake neman aiki a kamfanin nan bai samu ba sai da kyar ke kin samu cikin sauƙi ai abin farin ciki ne abin kuma a" "yi shela ne""" Numfashi Hibbah ta sauƙe """Ni a komai nawa ina son Sirri... Ba komai ne kowa ya kamata ya sani ba haka kuma ni a ganina taɓa abin wani bai dace ba yana daga cikin abin da ya fi saurin ɓata min rai shiyasa kika ga na dauke miki ɗin, duk kusancina da Hudah twin sister dita sai ta tambayeni take taɓa abuna" "idan za ki respecting ra'ayina then ni banda wani damuwa da ke Raliyat""" "Ta Yi mamakin maganganun Hibbahn kuma ta ji wani haushi ya turnuketa, kwata kwata hibbar nawa take da zata dinga jero mata ka'idoji? Yaushe kwata kwata ta zo kamfanin? A fili kuma sai ta ce" """Zan kiyaye hakan""" "Karɓar choculates ɗin Hibbah ta yi tace ""Thanks""" Kowacce ta koma bakin aikinta. Sun cigaba da 'yar dabi da Mahir saboda bai daina nuna mata kwalama ba kuma haushinta na "marinshi da ta yi har yanzu yana ji, niyyarshi mai girma ne a kanta kuma lokaci kawai yake jira." Tana zaune tana aiki a desk ɗinta wayanta ya shiga ƙira ganin Director ne ya sa ta ɗaga da ladabi ta gaishe shi ya ce mata ta same shi office. "Ta miƙe ta nufi office ɗin yana zaune riƙe da wasu files ya miƙa mata ta karɓa ta shiga dubawa ""Sir ai wannan ni na rubuta shi, akwai issue da proposal ɗin ne?""" Ya ɗan yi shiru kan ya ce """Issue ɗin shi ne baƙin sun iso ƙasar nan daga U.S amma Chairman ya samu delay na flight har yanzu bai bar Germany ba, wannan deal ɗin na billions of naira ne muka yi musu jinkiri za su iya ba wani companyn mu kuma mu yi asara, Chairman ya yabi aikin amma a yanzu babu mai iya presenting sai wanda yayi going through kaman dai yadda Chairman ya fi sati biyu yana dubawa. A yanzu dole ne kawai ba yadda muka iya ke ce za ki gamsar da su cewa mun" "chanchanci wannan deal ɗin.""" "Gabanta ya ɗan faɗi, presentation?" """Sir magana fa kake na billions ni ban taɓa presentation ba bare har in san ko zan iya convincing turawa su ba mu aiki idan na yi failing fa?""" """Za ki iya Hibbah I trust you with this""" "Jikinta a mace kuma she's not confidence a kan zata iya, karɓan papers ɗin ta yi yace ta je ta shirya suna isowa za ta yi presenting." "Zaune yake a cikin airport ɗin ɓangaren da aka ware na First class cikin wani kyakyawar cushion, gabanshi tea flask ne da mug, kunnuwanshi maƙale da earpiece yayi shiru bayan gama jin tattaunawar da ta wanzu tsakaninsu bai tanka ba har sai da Director ɗin ya ce ""Sir are you there?""" Ya ɗan wara idanunshi kan ya gyara zama yana ɗora kafa ɗaya kan ɗaya yace """Are you sure about this decision? Kana ganin ya yi mu ɗauki ragamar wannan project mu ba wa this Little girl da bata da wani experience? Wait!!...""" Ya ɗan yi shiru kan yace """Kana nufin da gaske ita ce ta rubuta ba Mahir ba?""" "A jere yake maganan in confusion don baya tunanin bata aikin daidai ne, haka kuma idan ita ce da gaske ta rubuta ya jinjina mata amma Meyasa Mahir ya ce shi ne ya yi?" """Ita ta rubuta Sir and am very sure za ta iya""" """for how many years ka ce take tare da mu?""" """Ta Yi service 1yr yanzu da fara aikinta anan ta kusa 2yrs""" A lissafinshi duk wasu manyan project da suka samu nasara a kamfanin nasu da har yake ganin yanzu Mahir ya yi hankali yana abin da ya dace ashe duk ba shi yayi ba nata ke yake presenting mishi shi kuma ya bashi reward ɗin? Ranshi ya ɓaci amma bai nuna ba chan ya ce """Make sure ka yi connecting ɗina da meeting room idan za ku fara and ku kasance a wurin duka incase wani abu na saɓanin ra'ayi zai faru you should help her, kar Mahir ya shiga hope am clear?""" """""Sure sir""" Ya yanke wayan ya miƙe zaune da kyau ya ɗauki tea ɗin ya yi sipping har lokacin mamaki ne a ƙasan ranshi. "He just knew her name lokacin case ɗinsu da Mahir and confidence da ta samu na marinshi alhali ta san yana da alaka mai karfi da kamfanin ta burgeshi hakan ya nuna zata iya kare kanta a ko ma ina ne muddin abu ya haɗa da mutuncinta, ya sa an ɗauki mataki kan Mahir amma bai nemi ya ganta ba don ba kowani ma'aikaci ne ma ya sanshi ba, from then ba zai ce ya sake tuna wanzuwarta ba sai yanzu da Director ke suggesting tayi presenting abin da ta rubuta sai ya" fi tsari. "Jin ana anouncing tashin su daga Munich(Germany) ya sa ya tattare abubuwanshi ya wuce kai tsaye zuwa cikin jirgi ya samu seat ɗin shi ya zauna comfortable ya buɗe system ɗin shi ya shiga sake duba project ɗin da yayi mishi thorough check, kusan minti talatin yana abu ɗaya jin za su tashi ya sa ya mayar da fuskar system ɗin ya rufe ya ajiye ya ɗaura belt ɗin shi kan yayi" relaxing yana lumshe idanu. "Tafiyar 3hours suka yi suka sauƙa a Amsterdam don nan ne transit ɗinsu before heading to Nigeria, kasancewar chanza jirgin zai kai awanni sama da bakwai ya sa dole ya nemi Hotel nearby yayi booking ɗaki don hutawa kan lokacin tashin nasu, wanka ya fara ya fito ya shirya cikin kananun kaya yayi ordern abin da zai ci kan ya zauna ya kunna system ɗin shi ya ajiye kan wani tattausan farin center da duk jikinshi ya fi yanayi da fox hair, abincin ya ɗauka ya shiga" ci a hankali idanunshi na sauƙa kanta tsakiyar meeting room ɗin. "Presentation da take yi confidently, turancinta, dressing ɗinta so classy and attractive, motsinta su suka yi caughting eyes ɗin shi gareta, ya jima yana kallonta kan hankalinshi ya koma kan tattaunawar da suke yi ɗin, bayananta ba turawan kaɗai ba har shi karan kanshi ya gamsu, he just find himself smiling don ya san sun gama samun wannan deal ɗin and gbammmm! Baturen ɗaya yayi signing yace" """Deal assured...""" "Tafi duka meeting room ɗin ya ɗauka, suka mimmiƙe ɗaya daga cikinsu na miƙa mata hannu don gaisuwa ta ɗan yi murmushi tare da duƙar da kanta tana mayar da hannunta baya and they respect her for that har suka gama suka watse kan ya kashe system ɗin." """Woww she's good at her work""" "Ya Yi exclaiming tare da jan wayanshi ya saka alerm ya hau gado ya kwanta idanunshi lumshe har bacci ya ɗaukeshi, saura awanni biyu tashin jirginsu ya farka yayi wanka ya gabatar da sallah kan ya shirya ya fice daga Hotel ɗin ya koma Airport bai fi awa guda cikin airport ɗin ba" aka kira su don wucewa Nigeria. "A chan Nigeria kuwa, ba Su Marketing manager da Director ba har ita kanta fuskarta fal yake da" "fara'a saboda success ne a gareta bata taɓa tunanin zata iya ba, har ta shiga hall ɗin gabanta" "ba karamin faɗuwa yake ba, kafafunta suka dinga rawa sai ambaton Allah tayi ta yi kan ta samu ta dawo daidai har ta iya fara magana, kowa yayi mata congrats don abu ne da suka jima suna nema kuma kuɗi sossai zai kawo musu, tun ta shigo ana yi mata murna ta kula da Raliyat da" fuskarta babu digon walwala. "Bata damu ba taje ta zauna desk ɗinta tana murmushi har lokacin, idanunta ne suka sauƙa" "akan Mahir dake tsaye hannayenshi a aljihu yana kallonta, bata ɗauke ido ba sai ma baki da ta" ɗan taɓe don kullum adu'arta koma menene nufinshi kanta ya koma mishi. "Ita kam Raliya kasa riƙe kanta tayi, ta miƙe ta fice zuwa restroom ɗin su ta sha kuka ta wanke fuska ta fito, shekarunta sama da shidda kamfanin amma babu wanda yayi recognizing ɗinta, Matsayinta ne Hibbah ta zo kai daga tayata ayyuka ta kwace komai a yanzu kusan ta fita" sanuwa a kamfanin wanda duk kokarin pushing da take taga babu kowa gabanta. """Sister Raliyat lafiya kam na ganki haka?"" Hibbah ta tambaya." """Kaina ke ɗan ciwo""" "Ta faɗa har lokacin ba'a sake ba, ta kasa ko da pretending da take ne bare ta yi mata murnan nasarar da suka samu yau." """Sannu Allah ya baki lafiya""" Hibbah ta faɗa da zuciya ɗaya. "Sun tashi aiki ta wuce gida, bayan ta yi wanka ta shirya cikin kananun kaya na shan iska ta sauƙo ƙasa ta samu Mommy na zaune da wasu dangin Babansu Abdul, gaishe su ta shiga yi suna amsawa ba yabo ba fallasa ta wuce kitchen ganin ma tuwo aka yi gidan ta dafa indomie guda ɗaya da kwai ta juye bowl ta fito har zata koma sama mommy tace" """Hibbah ina za ki? Zo ki zauna tattaunawa muke akan yayanku Abdul yau ya kai goro kuma an" "bashi gashi ya ce baya so biki yayi nisa shine muke tattauna yadda za mu tsara bikin""" Fuskarta ne ya ƙara sake wa tace """Masha Allah, Ya Abdul abu ya zo kenan to Allah ya sanya alkhairi ni to Mommy in na zauna ai ba abin da zan muku contributing gwara dai in je in ci abinci in kama aiki ni ina ayarin a bi yarima a sha kiɗa""" Wata daga cikinsu tace """Kema dai ina kaza ina cin danko? Ai ki bari waenda suka san kan irin hidimar nan su yi magana, Alhamdulillah ma da ya samu mace wanke hannu ka taɓa ai mu jininmu ba'a yi mana abu sau biyu""" Mommy ta kalleta """Ba ku ba, faɗar manzo ne ba'a cizon mumini sau biyu a rami ɗaya hidima kuwa ai su suka fi mu sani duk wannan abu da muke suna tashi ita da Zaitoon tsaff sai su sauya shi yayi armashi"" Murmushi kawai Hibbah ta yi bata nuna ko a fuska ta fahimci me matar ke nufi ba ta yi wucewarta, idan tace bata yi kewar yayyen nata kusa da ita ba ta yi ƙarya har yanzu bata daina jin guiltness na chanza musu rayuwa ba, amma kuma ta yi mishi farin cikin wannan aure har" "ƙasan ranta tana kuma yi musu Fatan alkhairi. Danginsu na wurin uba ba yau suka fara jefa mata magana akan ta ƙi yaransu kuma ta kasa auruwa ba, ba yau suka saba nuna mata cewa ita ce tayi sanadiyar rusa walwalar ƴaƴan dan uwansu ba amma da yake aka ce duniya ba kowa zai taru ya so ka ba daga Daddy har Mommyn basu taɓa nuna mata wariya ko chanjin fuska ba" kuma suna gamsar da ita cewa babu laifinta a abinda ya faru baya ko kaɗan. Da safe bayan ta gama shiri tana karyawa Aunty Kubra ta kira sunanta """Hibbah! Ni kam a hankali fa na kula kina son chanza kanki zuwa wata chan daban""" Ɗaga ido tayi ta kalli Auntyn bata ce komai ba """Meyasa a komai kike ware kanki? Wai a ganinki kin yi girman da za ki kauracewa kowa naki ciki har da twin sister ɗinki da iyayenki? Idan batun aure ne shekarun naki kwata kwata nawa ne? Ke fa har yanzu karamar yarinya ce...me yayi zafi na daukarwa kai irin wannan tsatsaurar" "ra'ayin? Ko aikin ne da na barki kina yi ke shirin sauya ki?""" "Ta Yi shiru bata ce komai ba. ""Hibbah magana nake miki fa""" """Mommy ni dai ban san me zan ce ki fahimce ni ba, aikina bai chanza ni ba illa iyaka shine sanadin da murmushi ke wanzuwa a fuskata har yanzu, i just feel like i need a break ne daga kowa nawa ina ji na zama musu burden da koyaushe suna cikin damuwar ya nake? Me nake yi? Wani saurayi kuma na sake? Wani cin amanar ne ya biyo baya? Wasu kam ma jira suke wani abin ya faru a ba da labari cikin farin ciki, a yadda nake yanzu bana magana da kowa bana" "kuma hulda da kowa hakan ya fi min kwanciyar hankali Mommy""" Girgiza kai Mommy tayi """Sam wannan ba hujja bace iyaye da 'yan uwanki sun fi gaban nan Hibbah musamman mahaifinki da ya fi kowa damuwa da halin da kike ciki na kaurace musu karfi da yaji, ba wai ya bar ki bane shima ya daina kiranki tsawon lokacin da baki taɓa nemansu ba ya bari ne ki samu natsuwar da kike so ki neme su don ra'ayin kanki, kar ki ɗauki komai da zafi baki yi girman da za ki yankewa kanki hukuncin da kika yanke a yanzu ba. Na farko kin ce ba za ki taɓa aure ba har Abada na ji ki ne ba don hakan za mu barki ki yi ba, na biyu kauracewa danginki? Kenan" "idan ba gidan nan kike ba mu ma ba kulamu za ki yi ba""" "Faɗa ta cigaba da yi mata, daga karshe ta yi mata umurni" """koma me kika saka a wayanki ki cire mahaifiyarki na son Magana da ke ni ce nake hanata da tuni ta zo nan ta saɓa miki Hibbah, don Allah ki bi komai sannu a hankali kin ji?""" Kai ta gyaɗa ta miƙe tsaye jikinta a sanyaye """Na tafi aiki"" ""Allah ya tsare""" Auntyn ta faɗa tana binta da ido har ta fice. A mota ta zauna sama da mintuna biyar kan ta janyo asalin wayanta ba wanda take amfani da shi yanzu ba ta kunna ta kuma cire shi a DND Ajiyewa tayi ta tada motar tayi reverse ta fito daga gidan. "Sanye take da farin palazo trouser na kamfanin FENDI sai wani Red blouse da ta saka mai faɗi ya sauka mata har rabin cinya, farin scalf ne kanta ta saka shi kan ta ɗora rigar don haka wuyanta a rufe, fuskarta babu komai Bakinta lip balm ne kawai ta shafa mishi sai kwallin da ta sa cikin idanunta, jakanta da takalminta Red ne sai tayi kyau sossai kaman ka saceta ka gudu ga maganan da suka yi da Auntyn nan ya sauya mata mood fuskarta babu walwala sam shade" ɗinta ta ɗauko ta saka daidai wayanta na ringing. "Sai da gabanta ya faɗi ganin Momma ce, miyau mai kauri ta haɗiye kan ta ɗaga a hankali ta" saka a kunne """Kin kyauta Hibbah! Eh na ce kin yi dai dai tunda muka haifeki ai mun gama miki komai... Anya Hibbah! Anya?? Wannan baƙin hali dole ya kora miki samari har kike ikirarin ba zaki yi aure ba kuma na rantse baki isa ba ko kina so ko baki so aure sai kin yi shi don da ba'a yi da ba'a haifeki ba...""" """Momm """ """Ki rufe min baki kar in ɗaga bappanki daga nan yaje har chan ya sauya miki kamanni, yaushe kika yi girman yankewa kanki hukunci yadda kika yi ra'ayi? Mu za ki mayar 'yan iska da bamu san me muke ba? A kanki aka fara rabuwa a soyayya?""" "Hawaye ne suka cika mata idanu tana jin numfashinta na nauyi a hankali, stiring ta damke tana hana kanta kuka" """Momma """ """Na ce ki min shiru in gama magana na, idan kina son Magana da ni ki bari idan kin kira sai ki yi ba mu ne bamu da amfani a rayuwarki ba da kika yi blocking ɗin mu har mahaifinki kike rayuwarki yadda kike so ba? 'Yar uwarki nan ta zo tana kuka cikin damuwar kin yanke magana da ita ni na rantse ba zata bi ki ba tunda abin naki ya zama hauka, mahaifinku anan ba irin damuwar da bai shiga ba koyaushe bashi da wani sukuni saboda ke amma ba za ki yiwa kanki faɗa ki dawo ki yi aure ki natsu gidan mijinki kema ki huta mu ma mu huta ba ko? To ya yi miki kyau Hibbah Allah ya baki nasara""" Tana kai nan ta katse wayan. "Kasancewar traffic ne take ta ɗora kanta kan stiring tana maida zafafan kwallar da suka cike mata ido kuma taurin rai ya hana su zuba, kalaman momman sun mata tsauri ita ba Manufar ta ba kenan amma Meyasa ba za su fahimce ta ba? Horn da ake ta mata ya sa ta fusge motar da karfi tayi companyn ta shiga tayi parking anyhow tana fitowa numfashinta kuma ya so bata" matsala. "Bayan shigowarshi yana tsaye jikin motarshi yana magana da chief security ɗinsu ya ga Shigowar motar, yadda tayi parking ba bisa ka'ida ba ya ɗauki hankalinshi sun gama maganar sai ya sanya hannu a aljihu ya shiga nufar cikin companyn inda kuma nan ne motar tata take a" lokacin ta fito ta tsaya dafe da motar cikin mayar da numfashi. """Madam! Kaman baki yi parking bisa ƙa'ida ba...""" Ta ji wata murya ta furta mata. "Ba tare da ta ɗago ba ta harba makullin motar saitin inda ta ji Muryar a zafafe ta ce ""Gashi sai ka yi yadda ya dace ɗan iya!""" "Shirun da ta ji na tsawon mintuna ne ya sa ta ɗago sai idanunsu suka sarƙe, kusan seconds" goma suka ɗauka suna kallon juna hannayenshi zube cikin aljihu bai ko motsa ba inda key ɗin ke yashe a nan ƙasa. """Ke kika yi kayan ki don haka ke za ki gyara""" Cikin masifa ta ce """Idan ka damu ka gyara ka aikomin da key Design nd strategic planning team. Idan baka damu ba kuma ka bar shi a inda ka ganshi.""" Tana kai nan tayi gaba zuwa enterance na babban skyscraper ɗin ta shige ciki da yake glass ne yana kallonta har ta shige elevator ya mayar da kanshi kan key ɗin sai ya saki murmushin mamaki da kuma kaɗuwa yana furta """Unbelievablee!"".." "*Littafin nan na kuɗi ne ki biya Naira Ɗari biyar (500) kachal domin kasancewa cikin masu kwasar tarin ilimi, faɗakarwa da zazzafar soyayya mai cike da sadaukarwa da aka zube ciki. Za ki biya ta wannan asusun" 0545475847 Gt bank Fatima Muhammad Gurin Sai ki tura shaidar biya zuwa wannan layi 09039206763 Ko kuma katin MTN na Naira 500 cikin wannan layi na sama sai ki tura da shaidar biya ta same layi. Sai na ji ku* Gureenjoh 41 "Ya jima tsaye yana kallon key ɗin kan ya duƙa ya ɗaga, a lokacin Marketing maganer da" Assistant ɗin shi sai PA da Director HR suka isko shi. """Good morning Sir""" "Ya amsa gaisuwar da kulawa ya sake kallon keyn motar kan ya kalli Security dake ɗan nesa ya ƙira shi ya zo, key ɗin ya bashi ya gyara parking kan ya dawor mishi da shi suka nufi ciki yana daga tsakiyarsu yana tafiya cikin natsuwa da karsashi, har PA ɗin shi zai danna floor da office nashi yake ya tsayar da shi." """To Design nd strategic department please""" Ba musu ya danna floor ɗin elevator ɗin ya ɗan motsa kan ya shiga haurawa da su duka. "Ita kam Hibbah tana shiga elevator ɗin ta lumshe idanu sai abin da tayi yanzu ɗin ya shiga dawo mata, laifinshi ne ba nata ba idan ba haka ba ina ruwanshi da rayuwarta da zai shiga yi mata maganan wani parking tana ji da abin da ke damunta, wasu ma'aikatan department ɗinsu biyu ta ji suna magana akan dawowar Chairman wato CEO MB MUSTAPHA, har ɗayar na cewa dole abubuwa su chanza tunda har yau ya shigo cikin kamfanin da kanshi, bata wani damu ba tunda ta kula ya fi Mahir hankali kila ma tsoho ne kaman su Director da Marketing manager elevator na buɗewa ta nufi seat ɗinta tana gaisawa da waenda hanya ya haɗa su" sama sama. "Tana zama ta shiga kunna system ɗin tana gyara zaman table ɗin nata yadda take son gani Dukda she's totally moody maganganun Momma sun tsaya mata tamkar Ƙashin kifi a maƙogoro, tana nan tana tunanin ta ji Miƙewar ma'aikatan da sauri ta ɗaga kai ta ma zaci Mahir ne da ikon shi sai ta ga su Director ne da Marketing manager cikinsu ta ga wannan mutumin da" ta gama masifewa itama Miƙewa tayi tsaye haka kawai tana tsintar kanta cikin faɗuwar gaba. "Da sauri ta basu baya tana dafe kirjinta idanunta a waje ba dai shi bane MB MUSTAPHAN? Ta tsinci kanta cikin tambayar kanta ba tare da ta san amsar ba kanta ba, idanu ta ɗan runtse tana" jin yana amsa gaisuwar da ma'aikatan ke jefa mishi a hankali hankali har ya iso desk ɗinta. """Miss Mudassir Madaki??"" Ya faɗa" "She froze in place, ta kasa motsi she's extremely shy da abin da tayi mishi yanzu, looking him in the eye ta faɗa mishi duk abin da ya zo Bakinta was soo foolish of her." """Hibbah!!""" "Director ya ƙirata again, da kyar tayi gaining courage na Juyowa kanta ƙasa tace" """Good morning Sir""" "Ya tsinci kanshi da murmushi yarinyar is unbelievable dube ta kaman ba yanzu ta gama rashin kunya ba, gaban desk ɗin ya isa sossai har tana jin kamshinshi mai sanyi da daaɗin shaƙa na ratsa kofofin hancinta yana doke duk wani kamshi nata ya ajiye key ɗin gabanta" """I think you left something with me shine na kawo""" "Idanu ta runtse tana ɓata fuska cikin kunya, fuskar ya kalla yana dariya a ranshi ya juya kawai" ya bar department ɗin su PA na biye da shi a baya. Da ƙarfi ta koma ta zauna """Me na yi?""" Tsaki ta ja tana kallon keyn kaman ta kurma ihu. "Har ta tashi aiki kunya da tsarguwa bai barta ba, abin da ya faru ya mantar da ita faɗan" "Momma, bayan ta koma ta watsa ruwa ta ci abinci ta shiga aiki sai ga kiran Hudah." """Hibbah!"" Ta amsa ""Twinee""" """A'a Hibbah baki ɗaukeni rabinki ba in har za ki ɗauki tsawon lokacin nan baki ji ni ba kuma baki neme ni ba baki ɗaukeni da muhimmanci a rayuwarki ba""" """Hudah ba za ki fahimci duk abin da zan faɗa miki ba, babu mai fahimtar yadda zuciyata take ciki sai macen da aka yi mata rufdugu akan batun abin da bata da iko a kai, misali rashin haihuwa da rashin aure da wuri, a raina nake jin kowa ya gaji da ni, kowa ya gaji da shearing matsaltsaluna kowa ya gaji da tayani kuka akan ƙaddarata, ba ni da wani hanyar sama muku sauƙi sai cire muku damuwa a kaina ku fahimceni nima ba da gayya na gujewa ji daga gare ku" "ba""" """Wannan ba hujja ba ce Hibbah! Amma in kin ji a ranki hakan daidai ne shikenan""" "Tana kai nan ta katse ƙiran, wayan Hibbah ta bi da kallo hawaye na cika mata idanu." Sake kashe wayan tayi ta jefar gefenta ta kwanta idanunta a runtse. "Washegari ko da ta tashi ta gama duk wani shiri da zata yi na fita aiki ta sallama Aunty Kubra ta fice, kai tsaye production company ɗinsu ta wuce don akwai abin da zata duba tayi jotting wasu point mai muhimmanci a kai so ta fi so ta kalla physically ta tabbatar da abin da zata rubuta, favorite spot ɗinta a hanyar ta bi ta sayi small chops, meatpie, banana bread da su tigernut drinks, zobo package mai yawa ta ƙarasa companyn, bayan ta yi parking ta shiga ciki daga ma harabar waenda suka santa tun IT suka shiga gaggaisawa cikin fara'a tana basu abin da ta riƙo musu, har wurin Managar workshop ta ƙarasa ta ajiye mishi nashi yana yi mata godiya tace tana so ta duba abu ne idan ba damuwa ya ce mata ai ba sai ta tambaya ba taje kawai kai" tsaye. "Ta wuce shi kai tsaye zuwa chan ciki wurin ayyukan nasu, a hankali take takawa tana duba abin da ya kawota bayan ta gama ta bi ta chan baya don zagayowa a ƙasan wani katako mai ƙarfi ta hangi wata yarinya da ba zata wuce biyar zuwa shidda ba tsugune tana kwashe wasu Red flowers da iska ke kaɗo furen suna zuba ƙasa, katakon bai zauna ba daga ma yadda yake rawa don haka ta nufeta, dab za ta isa kanta kenan yarinyar ta yunkura fitowa ƙafanta ya buge ƙasan katakon yayi kanta zai faɗi kuma idan ya faɗi mata babu abin da zai hanata jin ciwo da hanzari ta shigar da hannayenta ta tare yarinyar tayi saurin fita sai katakon ya buge mata gefen fuska" da hannunta na hagu ta haɗu da glass Window ɗin ɗayan ɓangaren. """Washhhh...!""" "Ta zame tana riƙe hannun nata ta waigo a lokaci ɗaya tana tambayar yarinyar ""baki ji ciwo ba? Daga ina kika shigo nan?""" Shiru yarinyar tayi tana kallonta da cute eyes ɗinta da tsoro ya cika su. Ta tsuguna gaban yarinyar za tayi magana kenan yarinyar ta saki kuka ta juya zata gudu daidai shi kuma ya iso wurin yana ƙiran """Jasrah! Jasrahhhh"" Softly." Ganinta cikin kuka ya sa yayi hanzarin duƙawa yana riƙota """Jasrah Menene?""" Idanunshi ya ɗaga sai suka shige cikin nata tana tsaye hannunta na ɗigar da jini fuskarta ƙasan idanunta yana iya ganin kurjewa da tayi. """Subhallah! Me ya faru?""" Ya faɗa yana Miƙewa tsaye ya nufo ta hannunshi riƙe da yarinyar da taji ya ƙira da Jasrah. """Ba wani serious abu bane Sir, she got scared ne saboda ta kusa jin ciwo.""" "Tana kai nan tayi yunkurin wucewa ya ɗan matsa sai ta tsaya ""Jini kike zubarwa and you are saying is not that serious?"" Tayi shiru kanta ƙasa." """Follow me""" "Ya faɗa yana yin ciki hannunshi riƙe da yarinyar da take ta kallonta, bayanshi ta bi zuwa ciki har office na manager workshop da ganinta hakan ya shiga damuwa yana tambayar me ya faru yadda duk suka shiga damuwa da ɗan ciwon ya yi mata daaɗi hakan kuma ya burge MB MUSTAPHA ganin yadda take da kyakyawar mu'amala da su." "Manager ɗinne ya ɗauko First aid box yana nufar ta MB yace ""Give it to me""" "Ba musu ya miƙa mishi, ya kalleta fuskarshi ba'a sake ba ba kuma a haɗe ba yace ""Sit""" "Ba musu ta zauna ya saka auduga ya shiga goge mata hannun da ta miƙa mishi ɗin dauriya tayi tayi saboda mutanen dake wurin amma spirit ɗin ba karamin shiga yake ba, bayan ya gama ya ɗago sai suka haɗa idanu ta kawar da nata, ya sake saka sabon auduga ya kai fuskarta focusing only on the wound yana gogewa har ya gama ya janye hannunshi tace" """Thanks""" "A hankali, iya shi kaɗai ya ji kuma bai amsa ba, ta kalli Jasrah ta ɗan mata murmushi sai yarinyar ta matsa kusa da shi tana sake manne mishi." "Kallon da ya ga tana yi wa Jasrahn ya sa ya kalleta sai ya ga itama Hibbahn take kallo amma fuskarta yana nuna kuka take son yi ko ta yi wani laifi, bai ce komai ba ya miƙe ya kama hannun Jasrah yana yi musu sallama kunun aya guda ɗaya da ya karɓa cikin tayin da Manager yayi mishi kuma ya sanar da shi daga ina ya fito ya ɗauka yayi waje suka raka shi har mota ya bar" companyn. """Wannan ɗin wacece a wurinshi?""" Ta tambayi wani collegue nata da ya zauna inda MB MUSTAPHA ya tashi. """'Ƴar shi ce bata magana kurma ce, yarinyar sam bata da sabo bata san kowa ba bayan" "mahaifinta""" "Tausayin yarinyar ya sake rufeta, wani abin baka isa ka saya ba duk arzikinka don ta tabbatar" da kuɗi na sayan baki da tuni ya saya mata ta fara magana kaman kowani yaro. "Bata jima ba itama ta musu sallama ta tafi sai bata koma wanchan companyn ba don rana ya riga ya yi kuma jinta take wani iri hakan ya sa ta koma gida kawai ta watsa ruwa ta zauna ƙarasa aikin da ta fara, fuskar yarinyar take ta gani da yanayin Baban, bai yi kama da MB MUSTAPHA ba like bai yi kama da matashin da zai mallaki irin wannan kamfani ba, don ba zata ce yayi 40 ba, a duniyar kasuwanci zata iya cewa kutse yayi don at First ta zaci zata ga kaman Daddy ne ko irin su Uncle Z, bashi da fara'a sossai haka kuma ta kula bashi da yawan magana sai dai yana da kirki wa ma'aikatanshi daga yadda yake kula da sha'aninsu da kuma yadda" suke ƙaunarshi ta fahimci hakan. "Lallai Mahir sam bai yi halin Yayan nashi ba, wayanta ne ya shiga ringing tana dubawa ta ga Manager a fili ta furta" """Speaking about the devil then the devil appears""" "Sai da ya kusa katsewa ta ɗaga ""Good Afternoon Sir""" """Meyasa baki zo aiki ba?""" """Sabon project da aka bani aikinshi na tafi production company haɗa bayanai am still on it ma yanzu haka""" """Waye ya baki izinin hakan?""" "Ta ɗan haɗe gira kaɗan kan tace ""It's from the Chairman""" """Hibbah kenan...""" Ya yi wani dariya kan ya katse ƙiran. Ta riƙe wayan a hannunta tana mamakin dariyar tashi da bata raba ɗayan biyu da wata Manufar yayi ta. Numfashi ta sauƙe ta cigaba da aikinta. "Washegari da wuri ta isa office, ga mamakinta a tare da MB MUSTAPHA suka isa bayan ta gaishe shi ya amsa tayi elevator shima ya biyo bayanta ya shiga kunnenshi maƙale da earpod yana waya hannunshi ɗaya sanye cikin aljihun Orange suit da yake sanye da su da suka" "matukar amsarshi, jinginuwa yayi da jikin elevator ɗin yana cigaba da wayanshi." "Tana tsaye daga gefe bata ma nuna alamun tana sane da shi cikin elevator ɗin ba wadda hakan ya saka shi kallon bayanta da ta bashi, tana sanye da farin english gown da yayi mata kyau sossai ta ɗaura cream vintage scarf kafafunta wasu matsakaitan hill shoe ne cream colour" haka jakan hannunta. """Yeah... Yes am listening you can continue""" "Ya faɗa alamun ya ɗan yi losing focus a wayan for some minutes. ""Ok...Ok please give me a second""" "Ya isa bayanta bai san ya lumshe ido yayi sniffing kamshin da take fitarwa mai masifar daaɗi ba, sake magana da aka mishi a waya ne ya sa yayi tapping ɗin kafaɗarta kaɗan ta waigo yayi" mata alamar rubutu da hannu. "Biro da jotter ta fitar ta miƙa mishi bata ce komai ba ya karɓa yana ɗan jotting bai ma kula da tsayuwar lift ɗin ba sai da ya gama wayan ya ɗago ya ga bata nan daidai floor dinshi ya buɗu," numfashi ya ɗan sauƙe ya fita ya nufi office ɗin nashi rike da jotter da Pen ɗin. "Tana shiga department ɗinsu ta tarar da Mahir tsaye a wurin desk ɗinta, ta yi mamaki amma bata nuna ba ta isa tana ce mishi" """Good morning""" """Hibbah wato da Manufarki kika shigo shine ni kika mayar da ni ɗan iska kaman baki gane nufina ba, da me wanchan da kike bibiya ya fi ni??""" Ya faɗa yana waigowa. "Zama tayi ta yi baya kaɗan da kujerar ta ""Ban fahimceka ba Sir""" """Tun farko target ɗinki kan Mustapha Bashir Almustapha ne shiyasa kike nuna halin ko in kula akan signs da nake nuna miki na Ina sonki, idan ba haka ba Meyasa ya yarda da ke har ya sakar miki ragamar project da na tabbatar ba zai taɓa wasa da shi ba? Meyasa shekaran jiya ya shigo companyn nan bai fara zuwa ko ina ba sai mazauninki directly? Meyasa jiya kuka hada baki kuka ƙi zuwa nan kuka zagaye kuka haɗe a Production company? Meyasa yau kuka shigo a tare??? Idan shi da wata Manufar yake nemanki Ni Mahir Bashir Almustapha aurenki nake da" "niyyar yi in rufa miki asiri...""" Tsaki take son ja mai ƙarfi amma tana riƙe kanta """Anya ka san me kake faɗa kuwa?? Da ka san wacece ni ma ba zaka kawo wannan banzan zancen gabana ba, Please Mahir respect yourself idan har kana so na cigaba da ganin girmanka matsayinka na ogana, do not accuse me akan abin da baka sani ba kuma bai shafeka ba""" """Ni kuwa na sanki Hibbah ɗiyar Senator Mudassir Madaki 'ya ɗaya tilo da ta rage gidansu karankatakaf saboda ta gagara auruwa sanadiyar rashin shuka al """ "Wani irin Miƙewa tayi daidai an shigo department ɗin nasu idanunta suka rufe, magana take son" yi amma numfashinta ya shiga fusga hannunta ɗaya ta ɗaga tana nuna shi.... """MAHIRRR...!""" Husky voice nashi ya ambata da ƙarfi cikin kuma faɗa da tsawa. "*Littafin nan na kuɗi ne ki biya Naira Ɗari biyar (500) kachal domin kasancewa cikin masu kwasar tarin ilimi, faɗakarwa da zazzafar soyayya mai cike da sadaukarwa da aka zube ciki. Za ki biya ta wannan asusun" 0545475847 Gt bank Fatima Muhammad Gurin Sai ki tura shaidar biya zuwa wannan layi 09039206763 Ko kuma katin MTN na Naira 500 cikin wannan layi na sama sai ki tura da shaidar biya ta same layi. Sai na ji ku* Gureenjoh 42 """Mahir are you in your right senses? Menene ya baka ƙwarin gwiwar faɗawa employee ɗin mu duk abin da ya zo bakinka? Here you know ba sai na tuna maka ba we respect our employee and we behave around them... Whats wrong with you?""" "Shiru yayi bai ce komai ba, wani kallo MB ya yi mishi kan ya ce ""Leave...""" Zai yi magana ya daka mishi tsawa """Nowww tun ban ɗauki mummunan mataki kanka ba!""" "Dole ya fita ran nan a matuƙar haɗe bai isa ya tafi gida ba, don haka kai tsaye office na MB ɗin ya nufa ya tsaya daga waje, wani ɓacin rai yake ji, ji yake kaman ya yi bingidiga saboda tunanin mu'amala take da Mustapha alhali shi tana acting very Cole around him, bai sani ba ko don ta ga yana sonta ne take neman wulakanta shi, shi da alfarma ya so yi mata ya rufa mata asiri" bayan dogon binciken da ya yi a kanta. "He felt a Sharp pain da bai san na menene ba ganin yanayin da take ciki, idan ba zai manta ba ranar da ya soma ganinta ta fito daga mota that was her reaction is she sick? Ya tambayi kanshi cikin 'yar damuwa, gaban desk ɗin ya ƙarasa tana dafe da desk ɗin tana jan numfashi a hankali ""Miss Mudassir Madaki""" "Ya ƙira coldly, ɗagowa tayi ba tare da ta kai idanunta da suka cika taf da kwallah kanshi ba, jikinta rawa yake kula da hakan ya sa yace" """Ɗo you need any help? Should i call a Dr?""" Kai ta girgiza tana ɗan datse lips ɗinta hawayenta kawai suka shiga zuba. """Ya Salaam!""" "Ya furta deep down yana ɗauke idanunshi daga kanta, lip nashi na ƙasa ya ɗan lasa ya sake kallonta." "Side bag ɗinta take ƙoƙarin ɗauka ""Akwai maganinki ne ciki?""" "Don ya kula akwai abin da take buƙata kai ta gyaɗa, ya buɗe ya fiddo robar ya cire mata guda biyu kan ya je despenser ya dibo ruwa cikin disporsable cup ya dawo ya bata, ta sha yana tsaye" gefenta har ta dawo daidai ta zauna kawai ta sa tafukan hannunta ta rufe fuskarta. """Look i am very sorry da abin da ya faru but trust me ba za mu zuba ido hakan ya cigaba da faruwa ba, here we have rules and regulations expecially on behavioral acts we can even file a law suite idan ya kama da cin zarafi kar ki ji tsoron komai saboda akwai alaƙa tsakanin company da Mahir just say it out idan kina buƙatar a daukar miki mataki.""" "Ya faɗa cikin kulawa don kaman yadda zai kula da ɗiyarshi haka yake kulawa da ma'aikatanshi bai yarda a karkashin shi wani yayi kuka ba, bai yarda a tauye wani under him ba, ba kuma zai" taɓa zuba ido a fara hakan ba. "Girgiza kai tayi alamun bata so, don ko ta amince ta san idan aka je mayar da magana sai maganan ya fito abinda bata son ji, abinda ta riga ta rufe shi a rayuwarta abinda sai ta zaci ya" wuce sai duniya ta sake tuna mata. she already had enough of it. """I..I just want to leave here idan da hali"" Ta faɗa a hankali." "Sossai yanayin nata ya bashi tausayi ɗauke kai yayi ""Consider it done""" "Daga haka ya ajiye mata jotter ɗin da Pen ɗinta ya nufi fita daidai kuma Raliyat na shigowa suka kusa cin karo, da sauri ta matsa tana gaishe shi kai kawai ya gyaɗa mata ya fice ta shigo" tana bin Hibbah da kallo ƙasan ranta na suya. "Ko da yaje office disciplinary committee ya kira ya faɗa musu abin da yayi noticing and saboda respecting ma'aikaciyar ba sai an ƙirata an tona maganar ba First da ta mare shi aka yi bincike he was at fault an yi suspending ɗin shi yanzu bayan tattaunawa mai tsawo aka bashi query dole ya amsa before tomorrow idan bai dawo da shi ba kuma za'a iya dismissing ɗin shi saboda kokarin ta da zaune tsaye cikin ma'aikata, ranshi a ɓace ya ɗauki takardar ya fice kaman zai" tashi sama. A harzuke ya shigo tamfatsatsen parlorn murya a sama yake ƙiran """Mum! Mummm!! Mummm!!!""" Matar da ke zaune bisa dining area tana karyawa ta miƙe ta fito """Kai lafiyarka kuwa? Ko yaƙi ne? Me aka yi maka uban 'yan zuciya?""" """Na gaji! Mum na gaji da irin abin da wanchan uban 'yan faɗin ran ke mini kike hanani ɗaukar mataki... A yanzu wallahi ba zan dauka ba sai dai koma me zai faru ya faru...""" Yana huci yake maganan kaman zai kifa mata a kai. """Yanzu kuma menene yayi maka? Matsala ta da kai Mahir gajen haƙuri barin mishi office ɗin ka yi ka dawo gida ya ji daaɗin ture ka da kyau?""" """Ba zan sake zuwa ba Mum... Ta ya za'a yi yarinya in fara ganinta in fara sonta har marina tayi ya ɗauki mataki a kaina sama da wata biyu bani da albashi yanzu kuma a kanta ya ba ni query kuma na kula take-takenshi sonta yake wallahi ba zan yarda ba, a kan yarinyar nan sai dai mu" "tashi legos gabaɗayanta... Daga ita har shi wallahi sai na ɗauki mataki a kan su""" """kai Maher! Meyasa kwakwalwarka na kifaye ne? So kake ka wargaza min shiri? Ka zauna ka natsu ka min bayani yadda zan fahimta ban son shashanci""" "Zama yayi kaman zai Huda kujerar yana cigaba da huci, bayanin abin da ya faru ya shiga mata tayi shiru tana sauraronshi har ya kamallah tayi murmushi" """Daaɗina da kai wawanci""" """Meyasa a koyaushe baki da kalmar jefana da shi sai na wawanci da shashanci, kullum sai ki dinga nuna wanchan banzan ya fi ni kwanya da komai? Na gaji fa Mum wallahi zan ɗauki" "matakin da har ke zai shafa na rantse da Allah""" "Miyau ta hadiye tana kallonshi haushi take ji a duk sadda Mahir zai aikata wani shirmen, baƙin ciki cika mata zuciya yake a duk sadda ta kalli Mustapha da irin cigaban da rayuwarshi ke samu a kullum, ba haka ta so ba wai ƙanin miji ya fi miji kyau, amma a hakan ma bata huta ba a kullum kokarin ta na ganin yadda zata juye komai bisa karkashinta take Allah ya bata dakiƙin ɗa" "da baya tunani kaman na masu basira, tsaki ta ja..." """Wannan abu ba abin tashin hankali bane Mahir, hasali ma wannan abu da kake ba shi zai nisanta su ba sai ma ya kusanta su, ina so ka ba ni hankalinka ka ji, mace ba'a binta ta zafi kaman yadda kake yin nan wata macen kudi baya gabanta, kyautatawa da soyayya haɗe da kyauta zaka dinga yi mata sai ka ga ta fara kulaka amma ka ce yarinyar 'yar iska ce?""" Kai ya gyaɗa """Hotunan abinda tayi a baya shi ya yadu a duniya aka fasa aurenta na farko shekaru kusan takwas baya.""" Ya faɗa yana tunani """Toh kai yanzu har irin wannan matar aure ce da zaka dinga yaƙi akanta? Ka san me tayi tayi" "bayan nan?""" """Mum ko bana sonta tana burgeni komai nata classy ko da ba zan aureta ba nima ina so in ji ya take, bare ma wannan idan tana iskancin na masu aji ne sannan ko ban sameta ba wallahi ba zan yarda wanchan banzan ya sameta ba""" Mum tayi murmushi wani idea ke faɗo mata amma bata wani mayar da hankali kai ba ta bar shi sai tayi tunani mai zurfi a kai. "Za ta yi magana idanunta ya faɗa kan Jasrah dake rungume da teddy bear tana kallonsu ""Ke wuce ki ba mutane wuri kin zura mana idanu kaman sabuwar Mayya...!""" Ya juya ya buga mata Harara shima yana zare mata idanu da sauri ta juya ta koma har tana taɗiyewa """ƙaramar kwaro bari na kamallah da ubanki tukuna in ji da ke""" Ta faɗa fuskarta cike da tarin tsana. Wasu shawarwari ta ba Mahir tare da sake danne shi """Ka san abin da muke so ya sa na turaka companyn nan idan ba zaka iya kwato mana shi ba babu amfanin zamanka cikinshi, maimakon ka mayar da hankali wurin ganin ka zama jagorar komai kullum ƙara mayar da kanka baya kake shiyasa shi karan kanshi baya maka ganin mutum... Ka tashi ka koma ka basu haƙuri dukkansu kuma ka bi abinda na ce""" Ba don ya so ba ya miƙe ya fice daga gidan. **** "Tun abin ya faru bata motsa daga inda take ba, kanta na kan desk banda sara mata babu abin da yake, ba zata ce ga irin tunanin da take ba don ta gaji, ta gaji da komai ta gaji da rayuwar, ta yanke hukuncin zame kanta daga TAƁON da ta dulmiya na SO ashe dattin ba zai barta ba ya" cigaba da bibiyar sawayenta zuwa duk inda ta jefa kenan? """Miss Mudassir Madaki!""" Ta ji wani murya ya ƙirata "Ɗagowa tayi idanunta a rine Dukda ba kuka take ba. ""The Director wants to see you""" Ta miƙe tsaye ta bi bayanshi har office na Director ɗin. Bayan ta zauna ya dube ta """I just got a call from the Chairman This is your promotion letter, a yanzu kin zama Secretaryn Chairman congratulations...""" "Ta karɓa har lokacin fuskarta ba a sake ba ""Thank you""" """Ban sani ba ko kin san duties ɗinki na secretary?""" Ta girgiza kai saboda bata sanin ba. """Well zan sake tayaki murna saboda matsayin secretary ba matsayi ne na kowa ba, hakanan zamanki a wannan company bai yi tsawon da ya kamata a baki wannan matsayi ba amma Chairman yayi appointing naki da kanshi which am very sure ya san za ki iya ɗin ne." Cikin sabbin ayyukanki akwai Karɓar Sadarwa • Karɓar kiran waya • Amsa imel (email) • Karɓa da aika wasiƙu Tsara Lokuta da Ganawa • Shirya tarurruka • Tsara jadawalin shugaban kamfani • Tsara tafiya idan akwai buƙata Adana Takardu • Shirya da ajiye takardu (na hannu da na kwamfuta) • Kula da bayanan kamfani • Rubuta rahotanni da bayanan taro Karɓar Baƙi • Tarbar baƙi • Nuna musu inda ya dace • Taimakawa sassa daban-daban idan an buƙata Taimakon Taro • Shirya ajandar taro • Rubuta muhimman bayanai yayin taro • Rarraba bayanai bayan an gama "Ina fata kina ɗauka?""" Kai ta gyaɗa cikin tabbatarwa """Ina yi miki waennan bayanan nan ne Hibbah saboda aiki da Chairman sai kin yi da gaske, bashi da matsala amma kuma baya son wasa da aiki yana da zafi idan kika kawo mishi wargi a aiki don haka please ki kiyaye kin ji? Idan akwai wani abu da ya shige miki duhu ki tambayeni, akwai P.A yana jiranki zai kai ki sabon office naki""" Godiya ta yi mishi sossai kan ta miƙe ta fice har lokacin bata da wani ƙwari ta tafi department "ɗinsu rike da wani box da aka bata na tattare abubuwanta, tana fara tattarewa Raliyat ta miƙe" """Mun shiga uku! Hibbah lafiya?""" Maganan da tayi ya ja hankalin sauran co-workers ɗinta duk suka mimmiƙe fuskokinsu cike da damuwa a tunaninsu an koreta ne tunda tun Shigowarsu fuskarta ba walwala haka har yanzu kowa ya ganta ya san akwai abin da ke damunta. """I just got promoted"" ""Promoted??""" Raliyat ta faɗa da ƙarfi tana zare ido. """Yeah am now a Secretary to the Chairman""" "Murmushi da congratulations aka shiga yi mata ita kam Raliyat ta kasa motsi tsabar kaɗuwa, da sauri ta ɗauki waya ta fice ita kam Hibbah bata ma kula da ita ba bayan ta tattare komai nata tayi musu sallama ta bi P.A sai floor ɗin the CEO" "Floor ne mai girma, ba kana fita daga elevator zaka ganka ciki ba, sai ka bi doguwar corridor ta fita wata 'yar corner kan ka bayyana babban office na farko mai ɗauke da kofofi guda uku, a jikin kofan tsakiyan akwai desk mai girma da computer da telephone sai tarin files, shimfide yake da tattausan Brown carpet daga farko har karshe duk girmanshi, akwai Ac har biyu dake aiki 24/7 akwai doguwar kujera cushion daga gefe mai tsawo da resting chair sai center table mai girma da tsari gefen dispenser ne tsararre, gaban desk ɗinta ma akwai kujeru guda biyu" dake zaune. Chan inda take fuskanta katon plasma ne dake aiki tashar CNN. "Nuna mata wurin zamanta yayi ta mishi godiya ta ajiye kayan hannunta. ""This""" Ya nuna mata office da take dab dashi """Shine ofishin Chairman a yanzu duk wani mai son ganinshi a wurinki zai fara booking appointment sai kin sanar da shi ya amince tukun ki tabbatar da time ɗin, duk wasu schedules nashi zan baki sannan ke za ki dinga tuna mishi duk wani abu da yake da shi a rana before the time duk wani abu da yayi missing a rana ko ta mantuwa it will be your fault so you will be extra" "careful. Nan""" Ya nuna ɗayan office ɗin dake gefe chan """Shine nawa idan kina buƙatar kowani irin taimako ko kina da tambaya you should let me know, yanzu ki biyoni in baki schedules ɗin nashi and please wannan project da ya baki you should finish it on time because week ne ya saura tsakani har ya fara tambaya yana so ya duba before" "time""" """In shaa Allah zan ƙarasa da wuri""" """there... Restroom ne so be free yanzu nan duk naki ne""" "Ya ƙarasa da wasa ta ɗan yi murmushi ""Thanks""" Ya nufi office nashi ya shige. Wurin ta shiga bi da kallo sai ta tsinci kanta da murmushi ko ba komai yanzu za ta fi jin daaɗin aiki hankali kwance. Takardunta ta shirya tsaf ta janyo system ɗin ta sanya modem ɗinta ta mayar da aikinta wurin ta cigaba hankali kwance. Tana cikin aikin ta ji motsin buɗe kofa da fitowanshi da sauri ta miƙe tsaye sai dai bai kalleta ba hankalinshi na kan agogon hannunshi ya fice. "*Littafin nan na kuɗi ne ki biya Naira Ɗari biyar (500) kachal domin kasancewa cikin masu kwasar tarin ilimi, faɗakarwa da zazzafar soyayya mai cike da sadaukarwa da aka zube ciki. Za ki biya ta wannan asusun" 0545475847 Gt bank Fatima Muhammad Gurin Sai ki tura shaidar biya zuwa wannan layi 09039206763 Ko kuma katin MTN na Naira 500 cikin wannan layi na sama sai ki tura da shaidar biya ta same layi. Sai na ji ku* Gureenjoh 43 """Whattt?? Secretary??""" """Na rantse da Allah! kuma har ta fara aiki with immediate effect""" Ta faɗa cikin Muryar zuzuta abu """Ni za'a rainawa hankali? Ina zuwa zan ƙira ki""" Ya katse ƙiran yana juya kan motar ya koma gida ya je ya tsayarwa Mum tashin hankali akan ba zai lamunta ba sai dai a kori yarinyar kowa ya huta. """Ƙiramin mahaifinku""" "Ta miƙa mishi wayanta, Abban ya ƙira ya bata ringing na biyu ya ɗaga ""Hello Hajiya!""" """Alhaji...""" Ta faɗa cikin wata iriyar murya """Subhallahi! Me yake faruwa? Baki da lafiya ne Hajiya Hafsatu?""" """Wallahi faɗuwa kawai na yi alhaji na rasa hankalina yanzu haka ina kwance duniyar sai juya min yake...""" """Innalillahi wainna ilaihi rajiun garin yaya?""" """Hmmm jinina ne ya hau an ƙirani Mahir ya kusa kashe wani da mota da kyar case ɗin ya mutu yanzu dawowar Manu ƙanina kenan daga police station. Ban san yaushe Mustapha zai yi hankali ya daina haurawa Mahir da ya san ba haƙuri ne da shi ba, kullum ina faɗa mishi a komai shi ne babba ya dinga haƙuri taya hankalinka zai kwanta idan ka bar mu hannunshi amma ya kasa""" Tayi maganan a karye. """Shi ne ya tunzura Mahir ɗin ko?""" """Wai faɗa suka kusa yi kan wata chan ma tambadaddiyar yarinya"" ""Faɗa? Ina zuwa yanzu Mahir ɗin ya jirani a gida""" Ya faɗa yana katse ƙiran. """Duk yadda zaka yi laifin ya koma na Mustapha ka yi idan Babanku ya dawo na fi so a kullum ya" "dinga ganin baƙinshi yadda ya saba bai taɓa halin kwarai ko na arziki a idanunshi ba, hakan na" "baƙanta ran yaron fiye da tunaninka saboda yana kaunar mahaifinshi har ranshi""" "Kai Mahir ya gyaɗa suka cigaba da tattauna yadda za su ƙuntatawa Mustapha ɗin da bai san suna yi ba, yana zaune a office mahaifinshi ya ƙira kaman koyaushe duk sadda zai ga ƙiran mahaifinshi sai gabanshi ya faɗi don ya san ba alkhairi zai faɗa mishi ba, ya tabbatar dole kafin" a gama wannan waya idan ranshi yayi dubu to sai ya ɓaci. """Assalamu Alaikum warahmatullah""" """Ji yadda kayi sallama kaman mutumin ƙwarai amma babu... Ka sameni gida yanzun nan" "hankalinka kuma ya kwanta tunda ka sa jinin mamanku ya hau har ta suma""" Idanunshi ya lumshe yana jinginuwa jikin kujera daidai lokacin da Abban ya katse ƙiran a kan "lips dinshi ya furta ""Mahir..!""" "Tuni jijiyoyin kanshi sun bayyana, taune haƙorinshi yake a hankali cikin kokarin samar wa" kanshi natsuwa kan ya miƙe ya fice daga office ɗin ko kula da wanzuwarta bai yi ba. "Da kanshi yake driving don haka mintuna arba'in ya kawo shi Ikoyi, ɗaya daga cikin unguwanni mafi tsada cikin legos yana dauke da manyan gidage na alfarma yawancin mazauna unguwar 'yan siyasa ne da manyan'yan kasuwa sai manyan jami'ai da suka amsa sunansu. Unguwar shiru kaman babu wasu halittu masu rai haka ya dinga kutsa shimfidaddun titunan har kofar" gidansu yayi Horn aka buɗe ya shige ciki. "Ganin motar mahaifinsu ya sa ya san ya dawo gidan tuntuni, ciki ya nufa rannan a haɗe wannan dalili ya sa ya tsani zaman legos ya gwammaci yayi ta zama waje da ya dawo gida, bai san inda rayuwar gidansu ya dosa ba, ba zai ce ga abu guda da ya taɓa yi na laifi da ya sa mahaifinshi yi mishi mummunan shaida ba, Dukda ya san Mum tana mishi son da take yiwa Mahir amma bai san daga ina matsalar take ba kuma tana iya kokarinta wurin fahimtar da Abba amma son da yake yi wa Mahir kan rufe mishi ido da bai taɓa yarda da laifinshi ba kaman" yadda shi yake yarda da nashi ba tare da bincike ba. Da sallama ya shiga """Babana! Ɗagoka daga aikin mahaifinku yayi? Alhaji sai da fa na ce maka ka kyale yaron nan" "na san ba zai hukunta Mahir ba dalili ba""" """Dalilinshi na banza na wofi! Har shi ya isa ya isa hukunta wani? Yaushe shi yayi hankalin na hukunta wani? Ina amfanin hukuncin da ba zai haifar da ɗa mai ido ba tunda gashinan ke suka barki cikin jinya alhali lokacin da aka yi baki sani ba?""" """Mum ki yi haƙuri ban san hukuncin da na zartar kan Mahir zai ɗaga miki hankali ba...""" Ta katse shi """Sam ko kusa hukuncin bai ɗaga min hankali ba, damuwata yarinyar da ka shigarwa faɗan akan" "ɗan uwanka cewa fa aka yi tatacciyar 'yar iska ce duk Kano ba wanda bai sani ba, me kenan? Tsorona kar ta wargaza maka tarbiya a barwa jasra abin faɗa da dai za ka bi ta shawarata ko ka mayar da ita kaman kowani ma'aikaci da kallonka zai mata wahala ko kuma ka koreta kawai" "a samu maslaha mu ma hankalinmu ya kwanta""" Ya wara ido yana kallon Mahir. """Mahir ka ji tsoron Allah, ka sani sharri irin na zina bashi da kyau wallahi sai Allah ya bi mata hakkinta kanka kuma za ku tsaya ranar gobe da kai da ita yayi muku hisa...""" """Abba ba ka gani ba? Daga faɗan gaskiya a kanta ta mareni kwanaki ya hanani albashi wata har biyu Mum gata nan ta hanani na faɗa maka saboda kar na ɗaga maka hankali yanzu na dawo aiki tana neman ɗan uwana don na dakatar da ita ni yake cewa bani da tsoron Allah!""" Mahaifin nasu ya kalleshi ranshi bace """Yanzu akan yarinyar ka hana ɗan uwanka albashin wata har biyu ko kunyar mamanku baka ji ba Mustapha? Kai Allah ya wadaran naka ya lalace...tunda abin ya zo da haka ka je yanzu ka sallame ta ta bar ma'aikatan in ji gari""" Girgiza kai yayi """Abba kayi hakuri amma ba zan iya sallamar ta ba don bata yi laifin komai ba, ban ga dalilin da zai sa Mahir ya ɗauko zancen company yana kawo shi gida ba maganan hukunci kuma displinary committee su suka hadu suka ga ya dace su yanke mishi hukunci suka yi aikinsu." Sannan don Allah Abba da Mum ku daina ɗaga hankali ku akan yaron nan duk abinda ya faɗa "ku hau kai ku zauna """ Mum ta yi charab ta karɓa """Wannan gaskiya ne, Mahir shashancinshi na dayawa Abbanku ne ba zai yarda ba amma da ya barka ka cigaba da yin abinda ya dace a kanshi shine daidai""" Abban da ranshi a ɓace yace """Ke dama koyaushe mustapha baya laifi a idanunki Hafsatu, amma bai isa ya zauna yana yi min faɗa ba na tabbatar Mahir ba zai taɓa cutar da shi ba sai dai idan faɗin ranshi da taurin kanshi ne ya hanashi ganewa, ya yi maka kyau Mustapha! Ba ka nuna min cewa kamfani naka ne ban isa saka ka ba ko? Toh zan dawo da Mahir karkashina in bashi ragamar kamfanina nan kuma zan ga idan ka isa ka mishi iko... Idan ka ga dama ka tabbata da yarinyar""" Yana kai nan ya miƙe cikin fushi ya bar ɗakin. "Idanu Almustapha ya runtse Sharp pain na sukarshi a kirji, Mum ta riƙo hannunshi tana sake" kasa da murya """Ka yi haƙuri da Mahir Babana, watarana sai labari""" "Kwarai don ita ne kawai yake haƙurin da Mahir, don ita kaɗai yake iya ɗaga ido ya kalli Mahir amma Allah kaɗai ya san abinda yake ji a ranshi muddin ya kalli yaron." """Mum ki ba Abba haƙuri zan ƙara kiyayewa Mahir ɗin ya koma bakin aikinshi""" Ya faɗa a sanyaye kan ya miƙe ya fice. Mum ta bishi da kallo tana dariya a ranta bayan ya fita ta miƙe zaune """Ashe ma gwara da aka yi, kai Mahir ka koma bakin aikinka ka cigaba da kunno mana shi" "ubanshi na ƙara ji yana ficewa a ranshi""" Mahir yace """Amma Mum ba ga damar mallakar companyn Abban ya samu ba? Meyasa kuma za mu cigaba da farautar wanchan banzan?""" Murmushi tayi """Na fi son nashi Mahir saboda nashin sai ya fi taɓashi idan ya rasa akan na mahaifinku, sannan na mahaifinku ba mai wahalar samu bane ko ni nan kadai na ishe shi saboda kwakwalwarku iri ɗaya na kifi abu kaɗan ke zurma ku rami""" Rai ya haɗe komai sai ta zage shi hankalinta ke kwanciya ya miƙe ya fice. "Shi kam Almustapha na fita daga ɗakin inda ya san zai samu ɗiyarshi ya yi, tana zaune tana" wasa da puzzles ya shigo ganin shine ta miƙe da gudu taje ta rungumeshi ya shigar da ita jikinshi yana runtse idanu sanyi na mamaye shi. """Har abada bana fata ki san baƙin cikin dake tattare da hukunci mai ɗaci irin na uba marar uzuri kaman nawa""" "Ya faɗa chan ƙasa ta ɗago tana juya hannunta alamun me ya ce? Ya girgiza kai. ""Za ki rakani office?""" Kai ta gyaɗa ya janyo hannunta suka fice zuwa mota daga nan ya ja sai office nashi. Hibbah na zaune tana aiki suka shigo ta miƙe """Welcome back sir""" "Ya tsaya kawai ya zura mata idanu ba tare da ya sani ba, babu maganan da ke dawo mishi irin na Mum da take cewa ita ɗin tatacciyar 'yar iska ce da duk Kano an mata shaida... Girgiza kai" yayi snapping out of that thought cikin rashin yarda ya nufi wucewa ba tare da ya amsa ba don wallahi shi bai ji ma welcoming nashi da tayi ba. "A sanyaye ta koma ta zauna, kenan shi ɗin ma kaman Mahir ne? To amma Meyasa at First yake abu kaman ba haka yake ba? Wata zuciyar tace kila yana hakan don ganin idon mutane" ne anan ko ta faɗa babu mai yarda. "Wayan landline ɗinta ne ya shiga ringing ta ɗaga daga front desk ne na kamfanin gabaɗaya. ""Miss Mudassir Madaki you have a visitor here""" "Cikin mamaki tace ""Who could that be?""" """He said he's your biological father""" Da sauri ta miƙe tsaye """I'm coming please""" Ta katse ƙiran ta nufi office na MB kar ta fita bata faɗa mishi ba ya neme ta bata nan tayi laifi. "Knocking ta yi bata buɗe ba sai da taji an amsa ta buɗe ta shiga, wannan ne karonta na farko cikin office ɗin, duk yadda zata fasalta tsaruwar office ɗin ya wuce nan komai neat and clean abubuwan ciki daban da na ko'ina cikin companyn ta tabbatar rabi da kwata ba daga ƙasar nan bane, yana kwance cikin tattausan three seater da yayi mishi kaɗan saboda tsawonshi ya ɗora" kafafun chan saman kujerar yayi pillow da hannayenshi idanunshi a rufe. "Daga chan gefe Jasrah ce ke zaune gabanta kayan wasa ne da alamu akwai su enough a office ɗin nata sai wasa take, idanu ta ɗan tsura mishi don kaman ba shi ya amsa mata knock ɗin ba saboda kallo daya zaka mishi ka zaci bacci yake mai nauyi don ba wani motsi dake nuna" alamun idanunshi biyu. "A bazata ya buɗe idanu sai karab suka shige cikin nata, da sauri ta kawar tana basar da faɗuwar gaban da taji tace" """Sir Ina neman permission naka ne zan sauƙa ƙasa mahaifina ya zo yana son ganina""" "Kai ya gyaɗa mata amma da yake ba kallonshi take ba bata kula ba ta cigaba da tsayuwa, jin bai ji motsin fitan ta ba ya sa ya buɗe idanu a sanyaye yace mata" """You can go""" Ta juya ta fice. "Sauri sauri ta shiga elevator Dukda gabanta dake faɗuwa, yaushe rabon da ta ji ko Muryar Daddy ne? Sai a yanzu take jin tsananin kewarshi zuciyarta ya shiga tambayarta guje musu da tayi shine daidai? Laifin mazan da ya shafi mahaifinta shine daidai? Ko don ta ga ya barta ya zuba mata idanu? Elevatorn ƙasa na buɗewa ta fita da sauri sai tayi turus ganinshi zaune cikin" cushion na front desk ɗin yana jiranta. "Murmushi ya sakar mata ""Mamana?""" Sai tayi sauri ta isa jikinshi ta rungumeshi ta fara kuka. Ya ɗagota """Haba mamana ya za ki kama kuka a bainar nasi kaman baby? Kin fa girma kina da yara dayawa""" Ta miƙe tsaye """Daddy...""" Ya miƙe tsaye ta mishi jagora har zuwa karamin meeting room na ƙasan wanda na ganawa ne da mutunanen da ba zasu fi biyu ba. """Daddy ka yi haƙuri...""" Ta ƙarasa cikin sabon kuka. """Sam baki min laifin komai ba""" """Daddy dama ka san na fara aiki? Ya aka yi ka san companyn nan?""" Murmushi yayi """Haba mamana, yaushe na yi lalacewar da ba zan san komai a kanki ba? Ko don kin ga kin bar Kano shikenan kin bar idanuna ne? Duk wani motsin ki Hibbah a legos ina sane da shi... Na barki ne idan hakan shi zai sama miki kwanciyar hankali na barki ki gwada kebewar ki kuma tsunduma abin da kike so matukar hakan shi zai samar miki da natsuwa ya mantar da ke damuwarki""" Kuka take yi tana jin babu kaman iyaye a rayuwa. Ya shafa kanta ta riƙe hannunshi ɗaya. """I didn't do it on purpose Daddy... It really hurts me in a quite way idan na fuskance ku ko na ji Muryarku that fear of disappointment, yana da zafi sossai musamman idan kuna nuna min ba komai bane in sake haƙuri alhali you all hurt silently. Don Allah ka yi haƙuri Daddy duk laifina" "ne da ban biyewa Sagir ba da na jima da tsufa gidan Mahmud""" Girgiza kai yake yi. """Don't feel hurt Hibbah we are never disappointed in you... Mun fa san kaddara ko kin manta mu musulmai ne? Akwai wanda ya isa ya hukunta abinda Allah bai hukunta bane? Ki daina wannan tunanin za ki samu farin ciki, za ki auri namijin da zai so ki fiye da mu ke ɗin ta daban ce Hibbah You are more than capable, you are a smart girl haƙuri kawai za ki ƙara kaɗan we all believe" "sauƙi na nan zuwa and we love you No matter the situation...""" He just break her again sai ta kasa controlling hawayenta sheshekar kuka na kwace mata. "*Littafin nan na kuɗi ne ki biya Naira Ɗari biyar (500) kachal domin kasancewa cikin masu kwasar tarin ilimi, faɗakarwa da zazzafar soyayya mai cike da sadaukarwa da aka zube ciki. Za ki biya ta wannan asusun" 0545475847 Gt bank Fatima Muhammad Gurin Sai ki tura shaidar biya zuwa wannan layi 09039206763 Ko kuma katin MTN na Naira 500 cikin wannan layi na sama sai ki tura da shaidar biya ta same layi. Sai na ji ku* Gureenjoh 44 "Da kyar Daddyn ya samu tayi shiru, ya shiga tambayarta yanayin aikin nata ta ɓoye mishi duk" wani matsala sai alkhairi da tayi ta samu ya mata murna da Adu'a kan ya ce mata zai wuce don a yau zai juya Kano. "Kaman kar su rabu haka ya tafi ta raka shi har mota tana daga mishi hannu ta jima tsaye tana kallon bayan motar kan ta juya ta koma ciki a hankali sanyi ke mamaye ranta, haƙiƙa ta yi kuskure na yin kudin goro har da mahaifinta alhali shine mutum na farko da ke fahimtarta cikin" kowani yanayi. "Ko da ta koma ɗin aikinta ta cigaba da yi lokacin tashi na yi ta tattara tayi gaba bata jira MB da ko motsin shi bata ji ba, Washegari da safe bayan ta iso office ɗin tana fara ayyukanta ta ji an shigo mata ko da ta ɗaga kai sai ta ga Mahir ne, kanta ta mayar ga system bata ce komai ba har ya iso kujerun gabanta ya zauna a ɗaya." """Hibbah""" Bata amsa ba kuma bata daina aikin da take yi ba. """Hibbah please ki ɗan bani aron lokacinki kaɗan ki saurareni""" "Ta ɗaga ido ta kalleshi ""Ina jinka""" "Tayi maganan cikin ko in kula don ta tabbatar maganan bakinshi bai taɓa ma'ana ba, fuskarta a" kame wanda rashin sake mishi da take ke ƙara dagula lissafinsa. """Hibbah ki yi haƙuri da kalamaina na jiya, na tako har nan ne don in baki haƙuri in kuma sanar dake ba wai da wata Manufar nayi maganan ba kishi ne da haushin da nake ji na yadda kike kula wanchan banzan ni ba kya kulani alhali duk wani alamu da zai nuna miki sonki nake na riga na nuna miki kuma aurenki nake son yi shiyasa na yi bincike a kanki""" Sai da ya faɗi kalamar aure ta ɗago ta kalleshi kan tayi dariya kaɗan na ka ma raina ma kanka hankali. """Idan auren ne ma sai in rasa wanda zan aura sai kai Mahir? Ai duk namijin da zai iya gorantawa wani akan wani kaddara da ta sameshi ba mijin aure bane. Mu kaddara ma na amince da kai sai in aureka duk wani laifi da zan maka ka yi min gori ko ka zageni da abin da ba ni da iko a kai??...""" Zai yi magana ta katse shi """Please nan office ne wurin aikina ne ba wurin maganan wani aure ba and mind you ba ni da niyyar aure a yanzu yadda nake daga nan har karshen rayuwata, ko ma akwai Mahir wallahi ko da zan saura daga ni sai kai a wannan duniyar baka da tagomashin da har zan iya aurenka so please respect yourself and LEAVE ME ALONE""" Da babban murya ta ƙarasa tana kallonshi cikin ido saboda wani tsana da haushinshi da yayi mata tsaye a maƙogoro. """Haka kika ce?""" Bata amsa ba sai cigaba da kallonshi da take """Dama irinku baku da godiyar Allah alfarma nake kokarin yi miki kina runtse ido. Irinku ne kuke mutuwa babu aure saboda kin ɗauki kanki wata tsiya...""" """Leave I said...""" Ta faɗa tana Miƙewa tsaye tare da nuna mishi kofa. Ya miƙe yana mata wani kallo kan ya fice. Ta kai zaune tana dafe Goshi. Ba a bakinshi ta soma jin a yanzu duk wanda zai aureta sai dai yayi mata alfarma ba hakan kuma bai taɓa shaking ɗinta ba don bata zaɓi auren ba bare ta je a alfarma hakanan ko da auren tayi ta san ta fi ƙarfin alfarma daga waje har ciki. "A zafafe ta ɗago jin an sake shigowa tana furta ""Mah...""" "Sai maganan ya maƙale haɗa idanu da suka yi, sanye yake da navy blue suite da suka amshe shi ƙwarai da gaske tuni kamshinshi ya cika office ɗin, hannunshi ɗaya cikin aljihu ya cigaba da takowa fuskarshi ba wani walwala." """Good morning Sir""" Ta faɗa tana mayar da idanunta ƙasa. """Morning""" Ya amsa da kalma ɗaya yana wucewa office nashi. "Zama ta yi ta cigaba da aikin dake gabanta, ko mintuna biyar bai yi da shiga ba ta ji landline" ɗinta na ringing ta ɗaga ki zo kawai ya faɗa cikin harshen turanci ya ajiye. Ta miƙe ta ɗauki tab ɗinta da duk ta tsara schedules dinshi na ranar ciki ta nufi kofar ta ɗan yi knocking kan ta shiga yana zaune kan kujerarshi ya saka farin tsiririn medicated glass da ya kara fitar da kyau da kamalar fuskarshi idanun na zube bisa computer dake gabanshi yana sarrafa keyboard ɗin cikin salon kwarewa. "Gabanshi ta isa ta tsaya ""Ga ni Sir""" "Bai yi magana ba sai da ya kamallah abin da yake ya ɗan ɗago ya kalleta ""What are my today's schedules?""" """Da misalin ƙarfe 9:40am akwai meeting na board members which will take 1-2 hours, after that akwai lunch da za ka yi attending for M&S Metal company wanda sun ba da invites for over a month, daga nan. Sai one in one meeting da za ku yi da Shinghai Marketing manager from" "then you are closed for the day""" Ya bar abin da yake yana kallonta cikin analyzing abubuwan nashi na yau din kwarai ya tuna metal company ɗin nan sun bashi invites tun da jimawa kuma shi ma yayi accepting ne saboda akwai wanda yake son gani a taron nasu which is just part of business don haka ya gyaɗa kai. """Okay then zan fito around 9:40 ɗin"" Ta gyaɗa kai ta juya ta fice." Aikinshi ya cigaba da yi itama ta shiga kokarin ganin ta haɗa project nata da yake ta jira ta bashi saboda proposal ne mai girma da idan sun rasa zai zama musu asara a company. "9:10 ta fita da kanta zuwa meeting hall ta tabbatar komai intact an jera ruwa da lemo sannan wurin is very clean and neat sai kamshi yake tashi na freshners da Ac ta dawo office, bata jima da zama ba ya fito sai ga P.A ma ya fito, jotter da Pen ta ɗauka ta bi shi a baya kaman yadda" "P.A ya ba da tazara kadan suka zama suna take mishi baya har hall ɗin, tuni manyan sun iso ciki har da masu kula da Production company da kuma finance department saboda matsalar da ake samu na ɓace-bacen kaya da kuma kudade wanda tun yana kaɗan har abin ya fara yawan" da ya ga ya kamata ya zauna ya fuskanci daga ina matsalar take. "Sun fi awa biyu suna meeting ɗin, ita dai tana zaune amma bata tsoma baki ba sai rubuta wasu" "points ɗin da take musamman idan ya kalleta ya yi mata alama na she should jote down, bayan sun gama office suka koma." "A ɗan gajiye ta zauna don kanta har yana dan yi mata ciwo, bata cigaba da aikin ba ta janyo paper bag da ta zo dashi ta fiddo meatpie da pepper chicken ta shiga ci saboda ko karyawa bata yi ba sai lokacin bata ma iya ta cinye ba ta mayar da sauran ta sha ruwa kan ta tashi ta shiga toilet ta ɗan kama ruwa ta fito wanda daidai sha biyu, bata zauna ba ma sai gashi ya fito" P.A ma ya fito daga nashi office ɗin har tana kokarin ce musu Allah ya kiyaye ya dube ta suka haɗa ido. "Outfit ɗinta yake kallo Black straight skirt ne sai Light purple shirt mai dogon hannu da ta saka, takalminta hill ne Black Color haka jakan hannunta, abin hannu da abin wuyanta yana da colourn purple sai Black jercy scalf da tayi styling dinshi a kanta ya bayyana jewelries ɗin, she's" just Perfect for work and he likes it. """Make sure kin riƙo tablet, jotter and Pen""" "Ya juya, ta ɗan yi frowning da ita za su tafi? Ganin har suna kokarin ɓace mata ya sa ta ɗauka da sauri ta bi bayansu zuwa ƙasa." Gaba ta shiga shi da P.A ɗin a baya sai driver suka dauki hanya. Tafiya ne suka yi na kusan awa guda kan suka isa companyn ita dai tana bin bayanshi a jere da "P.A har cikin tamfatsatsen hall ɗin da aka tanada don event ɗin, ita ce ta nuna invites ɗinsu aka isar da su table ɗinsu duk suka zauna." Abinka da manya ba wani afrikan time lokaci na cika aka fara gabatar da taron kaddamarwa this is her First time na fitowa irin wannan taro and ya kayatar da ita ƙwarai barin ma da aka kirashi ya ba da takaitaccen shawara ko wani idea na sirri har da cracking jokes suka mishi wai sirrin cigaban companynshi da har yake damawa cikin manya. "Ko da ya karɓi mic murmushi ya fara kan gaisuwa sai taya murna kan ya gangaro kan shawarwari inda yayi emphasizing kan ma'aikata su ne company idan babu su to babu company sai kuma jajircewa da haƙuri, bayan ya gama wonderful speech ɗin aka shiga tafa" mishi ya dawo ya zauna kan aka yi musu presenting varieties na abinci. "P.A ne yayi serving dinshi tukuna yayi wa kanshi ya kalleta ""Miss Mudassir what would you like to eat?""" Ta girgiza kai """Bana jin yunwa thanks""" "Ɗaga ido MB ya yi ya kalleta sai dai bai ce komai ba ya mayar kan abincinshi tana nan zaune har suka gama, mocktail kawai ta sha sai ga wanda yake son su ganan ma ya isko shi har table suka shiga tattauna tana sauraro inda ta ji ya kamata tayi jotting sai ta rubuta." "Ko da suka fito azahar ya wuce a hanya ya sa suka tsaya suka sauƙa suka yi sallah kan suka ƙarasa company she's just very tired and headache ma ya matsa mata, ko da suka isa kai tsaye alwala tayi ta zaro hijab da sallaya da ta kawo musamman office ɗin ta gabatar da Sallarta da tana cikin yi ya fito ya fita ta idar tana azkar ya shigo suka haɗa idanu mistakely suka dauke a" tare ya wuce office nashi. "Kaman kar ta koma kan aikin nan na proposal haka take ji da kyar ta ƙarasa, isowar baƙin china ɗin ya sa ta miƙe tayi welcoming nasu kan ta basu wurin zama ta nufi office nashi tayi knocking" ya bata izini ta shiga ciki. """Sir baƙin nan na Shanghai sun iso za su iya ƙarasowa?""" Yana kishingide kan kujera ya miƙe zaune ya nufi hanger ya ɗauki suite da ya cire ya bar zallar farin shirt ɗin ya saka. """They can come in""" Ta nufi frigde ta fiddo musu ruwa da su drinks dan karamin wurin ganawa na office ɗin ta gyara ta ajiye kan ta fice shi kuma yana duba abu akan desk ɗin shi. "Iso ta musu har ciki sai da suka zauna shima ya zauna kan ta juya za ta fita ""Miss Mudassir...!""" Ya ƙira ta. Ta rasa Meyasa duk ya kirata sai ta ji karamin faɗuwar gaba bata sani ba ko daga Muryar shi ne ko me oho. """Yes sir""" """please get your jotter and have a seat""" Kaman tayi magana sai ta fasa taje ta ɗauko ta zo ta zauna wurin meeting ɗin nasu. "An jima ana zube ideas kowa na ganin abin da ya fi dacewa har aka samu matsaya, kanta ciwo yake tana rike da jotter ɗin amma hankalinta rabi baya kansu, biron hannunta ne ya zame ya" faɗi ta duƙa don ɗaukowa tana ƙoƙarin ɗagowa ta ɗan Buge goshinta da jikin table ɗin tace """Ashhh"" a hankali ta yi mamakin ganin ya kalleta ""Sorry...!""" "Ya faɗa ta gyaɗa kai don bata zaci ma zai kula ba, jotting ta cigaba da yi chan yace musu duk wani matsaya da suka tsaya a kai za su sake zama yanzu he need to rest and think over it again." "Dole suka musu sallama suka tafi, tana yunkurin wucewa ya ce ""Miss Mudassir... Are you Ok?""" Ta kalleshi da gajiyayyun idanunta """Am good sir ciwon kai ne kaɗan amma zan sha magani""" Kai ya gyaɗa har ta fita bai daina kallonta ba sai da ya gaji da kallon kofan ya juya ya nufi toilet don alwalar la'asar. "Tana idar da Sallah sai ga Raliyat ta shigo mata ""Har kun tashi ne?""" Take tambayarta """Yeah zan wuce kenan nace bari na leƙo mu gaisa in ga office"" Murmushi kawai Hibbah tayi, za tayi magana sai ga kiranshi ta miƙe ""Kina nan ba?""" Kai Raliyat ta gyaɗa """Yauwa bari na ga Boss yana ƙira""" Office ɗin ta wuce. "Tana shiga ta samu yana ɗan tattare abubuwanshi ""how is the headache?""" Ta Yi mamakin tambayar amma sai ta basar """Ya sauƙa thanks""" """Project ɗin nan kin gama kuwa?""" """Eh ya kamalla i will just Email it to you""" """Ok please do it gobe ne zan ga mutanen nan"" ""Yes boss""" "Har ta juya za ta fita ma sai ta ga table da suka tashi yanzu da abubuwan da suka yi amfani ta nufi wurin za ta tattare bata san tasowarshi ba har ta saka hannunta kan goran ruwa ta ji ya sanya hannunshi ya zame zuwa nashi ta ɗago sai suka haɗa idanu, baya ta ɗan yi tana kawar da kai" """You are sick just leave it""" "Kai ta gyaɗa ta juya ta fita ga mamakinta bata ga Raliya ba bata damu ba ta zaci ta daɗe ne ya sa ta gaji ta tafi, system ta duba tana kan ma file ɗin ne don haka ta mishi emailing kan ta kashe komai ta tattare abubuwanta daidai yana fitowa suka yi sallama.." "*Littafin nan na kuɗi ne ki biya Naira Ɗari biyar (500) kachal domin kasancewa cikin masu kwasar tarin ilimi, faɗakarwa da zazzafar soyayya mai cike da sadaukarwa da aka zube ciki. Za ki biya ta wannan asusun" 0545475847 Gt bank Fatima Muhammad Gurin Sai ki tura shaidar biya zuwa wannan layi 09039206763 Ko kuma katin MTN na Naira 500 cikin wannan layi na sama sai ki tura da shaidar biya ta same layi. Sai na ji ku* Gureenjoh 45 "*Na so mun gama littafin nan kafin ramadan amma abin ya ƙi haɗuwa in na ce zan yi rushing duk littafin ba zai yi daaɗi ba kuma ma'anar ba zai fita yadda nake sonshi ba, so za ku yi haƙuri" mu tsaya anan mu yi ibada. Da yardar Allah ranar sallah za mu cigaba* "A natse take tuƙin duk da irin crowdness na titunan legos idan yamma yayi glass ɗinta a dage yake har sama, Ac kuma ke aikin sanyaya motar tuni ta cire hill da ya matsa wa kafarta a yinin, waƙa tayi playing take sauraro har ta shigo cikin Layin unguwar nasu dab za ta sha kwanar ƙarshe wata mota ta shiga gabanta da sauri ta taka birki tana kallon motar cikin mamaki don da" alama da gayya aka yi hakan. "Bata sauƙa ba sai cigaba da kallon motar ta yi tana jira na ciki ya gama abin da yake ya bata hanya don bata cikin halin surutu saboda gajiya da kasalar da take ji, ganin abin na son zama rainin hankali tayi gefe za ta wuce ya" "Sake yin baya da motar ya tare mata hanya, kofa ta buɗe ta fito daidai lokacin da shima ya buɗe ya fito...chakkk haka ta tsaya kaman wacce aka yi wa pause, tuni duk wani fara'ar fuskarta ya ɗauke ta haɗe rai kwarai da gaske ganin wanda ke tsaye gabanta kuma kallonta yake yana" nufota. Tafasa zuciyarta ya fara har ya ƙaraso gangarta sai yayi ƙasa ya duƙa. """I'm not proud of what i did... Na rasa natsuwa, na rasa kwanciyar hankali, na rasa bacci Hibbah tun bayan da na barki na kasa samun sukuni, sai da kika subuce na san cewa na kamu da soyayyarki a gaske ba wasa ba... Wallahi wallahi ba zan iya rayuwa babu ke ba. Duk wata hanya da zan bi in manta ki na kasa, duk wata dabara da zan yi ki fita daga kwakwalwata hakan" "ya ci tura ki taimakeni ki yafe min Hibbah...!""" Kai ta juya tayi wani dariya kan ta kalleshi """Usaib! You have to be enjoying your win zuwa yanzu ai. Playboy ba you enjoyed toying me around ko wani season ɗin kuma kuka buɗe season 2 episode 1 saboda buƙatarta na banza" "bata biya ba?""" Kanshi ya duƙar har lokacin gwiwarshi na ƙasa """Na sani duk abin da zan faɗa ba za ki yarda ba, amma zan yi miki abu ɗaya shine rantsuwa da mahallicina wallahil azeem Hibbah babu yaudara a tare da ni a yanzu, na yi wasa dake a baya na sani amma ba ke kaɗai nayi wasa da ba har da zuciyata tunda gashi i didn't plan for it to go this far sai kuma ubangiji ya yi min talala ya ɗaura min sonki na gaske a cikin raina, I'm very sorry Hibbah ki yafemin please... I used you tamkar wata kaya gashi yanzu na kasa cire ki a zuciyata, ki bani dama in nuna miki a yanzu bawa nake gareki wallahi kome kika ce in yi zan yi" "Hibbah saboda in tabbatar miki da gaske nake""" "Har lokacin murmushi ne a ranta Dukda hawayen da take gani a idanunshi, dariya ma ya shiga" bata ba kaman farko da ya hasala ta ba. """Da gaske?""" "Ta faɗa tana harde hannayenta a kirji. ""Da gaske Hibbah komenene""" """Then ina so ka ɓace min da gani... Ka fita daga sabgata tun kafin in shigar da hukuma su yi mana tsakani Usaib... Ina so har abada kar ka sake nuna min mummunan fuskarka mai cike da tarin zalunci da mugunta a kai, your crocodile tears will never shake me har abada ka gama" "wasan kura da ni Usaib.""" "Muryarshi na cracking ya ce ""Hibbah Kuskure n. """ """Wannan ya fi ƙarfin kuskure sai dai tsantsar baƙar zuciya da mugunta Usaib. !""" Da tsawa ta ƙarasa maganar. """Hibbah """ Ta ji an ƙirata ko da ta juya Abdul ne """Lafiya kuwa?""" Hannu ta ɗaga mishi """Wannan matsalata ce Yaya Abdul ko lafiyar ko akasin haka""" Kaman ta kurma musu ihu saboda dukkansu wani irin haushinsu take ji kaman ta yi bindiga. """Usaib wallahi wallahi this should be the last time za ka nuna fuskarka a fuskata duk ranar da ka sake na rantse da ubangijin da ya halliceni a ranar sai na yanka maka sammaci hukuma ta yi mana tsakani.... Ni Hibbah ba zan taɓa sonka ba don daƙiƙi shi ke maimaita aji... Na rufe babin rayuwarka tun daga ranar da na gane wanene kai, wallahi ko ana mutuwa ana farkowa ko da sama zata haɗe da ƙasa sai dai ta haɗe amma ni da kai har duniya ta naɗe. Idan kuma kana" "ganin magana nake ka sake don Allah.""" "Ta juya rannan a haɗe kwarai da gaske ta shiga motarta ta danna Horn ta riƙe ga Horn ɗin ƙarar gaske, Miƙewa yayi ya je ya shiga mota ya fitar mata da shi a hanya yana kallon motarta idanunshi na sake cika da tarin kwalla na zallar nadama don shi kadai ya san abinda yake ji a ranshi na soyayyarta babu abinda bai yi don ya manta ta ba har ƙasar ya bari amma ya kasa, ta figi motar ta ƙarasa gida, ta fito tana shirin rufe motar Abdul ya shigo ko parking bai yi ba ya" sauƙa ya nufeta. """Hibbah lafiya kam?""" """Na ce babu ruwanka da ni Ya Abdul ko akwai??""" Da masifa ta harzuko idanunta kaman garwashi amma ta ƙi bari hawaye ya zubo don ta gama rufe baabin kuka akan kowani namiji. """Hibbah me yake damunki ne? Ko kin manta ni wa nake gareki ko don saboda kalmar So da ya" "taɓa ratsawa tsakaninmu shine a yanzu na zama abin raini?""" Mamaki ya bata har bata san ma ta yi dariya ba. """Yaya? Ya Abdul da da gaske ka ɗaukeni ƙanwarka da ko bayan na ce mu haƙura da batun so da ka cigaba da hulda da ni kaman kanwar da nake... Da baka tsiri gaba da ni ba Ya Abdul da duk baku ɗaura min nauyi da tsanar kaina akan ganin da nake ni ce sanadiyar chanza muku tsari da rayuwar da na sameku a kai cikin gidan nan ba, ni ba Ya Zaitoon ba ce don haka ni ba kanwarku ba ce""" "Tana kai nan ta juya ta bar wurin, haka ta shiga gidan ranta duk ba daaɗi ko da Aunty Kubra ta" "tambayeta ce mata kawai tayi gajiya ce da ciwon kai bari ta haura tayi wanka, a sauko lafiya tayi mata kan tayi haurawarta sama." Bata tsaya tunanin kowa ko komai ba ta tattaresu ta watsar ta yi wankanta ta ci abinci tayi Magrib da kyar ta jira isha tana idarwa sai bacci. **** "Ta ɓangaren MB MUSTAPHA daga office gidansu ya sa driver ya kaishi don yana son duba Jasrah saboda jiya da ya shigo Mum hanashi tafiya da ita tayi kuma da safe bai samu ya biya ya ganta ba, ya san idan ya wuce Banana Island inda asalin gidanshi yake ba lallai ya fito ba sai" gobe. "Ko da driver yayi parking sauƙa yayi kai tsaye ya nufi cikin babban sashen na Hajiya Hafsa inda take baza mulki da jin ƙanta tamkar matar sarki ko shugaban ƙasa, sai da ya ratsa parluka biyu kan ya isa karamin seating room ɗinta har ya ɗan zarta ya dawo baya ganin figure ɗinta dunkule" cikin kujera tana rungume da teddy bear ɗinta kuma ba bacci take ba. Gabanta yaje ya duƙa yana ɗagota zaune hannunshi kan ƙuncinta. """My baby... Ba ki ga Abba ba?""" Shiru kawai tayi tana kallonshi with blank expression. """Jasrah ba za ki min magana ba? Ko fushi kike na tafi na barki?"" Shagwaɓe fuska tayi amma bata ce komai ba." """Am very sorry yau kam tare za mu tafi in shaa Allahu ba zan barki anan ba. Shikenan?"" Kai ta gyaɗa sai ta sauƙo ta rungumeshi, yayi hugging nata back kan ya miƙe ta kankame" hannunshi suka nufi ciki wurin Mum. "Tana zaune bakin gado tana waya yayi sallama ya shiga. ""My son kaine tafe?""" """Eh Mum. Fatan kuna lafiya?""" """Lafiya ƙalau Alhamdulillah ya wurin aikin?""" """Alhamdulillah Mum ya karfin jikin?""" Ta amsa da """Alhamdulillah, ina ka samo wannan? Chan wurin wasanta ko? Tun ɗazu nake nemanta ma Mahir ya kawo mata choculates in bata nannynta wai tana chan playground ɗinta""" Yayi murmushi """Maybe ta gaji da wasan ne a parlor na sameta tana kwance""" """Zo Jasrah ki karɓi tsarabar Uncle ɗinki""" Kafada ta maƙe idanunta na cika da kwallah """Za ki gamu da ni ne ja'irar yarinya don kin ga babanki shine za ki tsiri min hali ko? Ai zai tafi ya bar mu ne""" Ta faɗa da wasa da dariya """Uhmm ai tare za mu tafi Mum ta yi fushi jiya na barta nan""" """Kai dai ba zaka barta ka samu hutu ba Babana? Yaushe zata barka kayi aiki da ɗawainiya?""" "Kankanme hannunshi tayi ta fara hawaye. Ya kalleta ""Ba komai Mum zan tafi da ita ɗin kawai""" """Toh ai shikenan. Mu isa dining ka ci abinci kan ku wuce""" Ya girgiza kai """No am not hungry... Bari mu wuce kawai""" Sallama ta musu ta raka su har parlor suka fice ta bi bayansu da Harara tana gatsine baki. "Yana fita suka ɗauki hanyar Banana Island a hanya Magrib ya same su suka tsaya ya shiga har cikin masallaci da ita suka yi sallah kan suka fito suka wuce, tafiya ne mai tsawo sai seven suka isa tsibirin shiru da natsuwar shi ya fi na dukkan unguwannin Legos, idan ka shiga kaman wani kasa ka shiga tituna shimfidaddu suka yi ta ratsawa har suka isa tamfatsatsen gidan nashi mai kyau da daukar hankali, bayan drivern yayi parking cikin jerin motocinshi suka sauƙa suka nufi ciki, daga driver sai cleaner suke rayuwa a gidan don shi ke girkin da zai ci idan ba saya zai yi" "ba, don haka gidan tsitt suka haura sama ya kunna mata cartoon kan ya shiga yayi wanka." Bayan ya fito ya yi shafe shafen duk da zai yi ya bule jikinshi da turaruka kan ya sanya pjmas "dinshi blue ne riga da wando mai yauki da sulbi, lofas dinshi ya zura ya fito yayi ƙasa tana zaune ganinshi ya sa ta miƙe da sauri tazo ta riƙe hannunshi tana yi mishi alamun yunwa take ji." Ya tsuguna ya shafa kanta """bari na dafa miki noodles za ki ci?""" Kai ta gyaɗa """Ok just give me a minute""" "Ta gyaɗa kai ya shafa kanta kan ya miƙe ya nufi kitchen, a duk sadda zai shigo kitchen ɗin sai yanayinshi ya sauya, abubuwa yake tunawa da kan taɓa mishi zuciya ƙwarai amma ya zai yi? Haka Allah ya tsara mishi." "Noodle guda ɗaya ya dafa mata da egg ya sa a karamin plate dinta ya kai mata har parlorn ta zauna ya shiga bata sai da ta cinye tas ya bata ruwa ta sha, hannunta ya kama suka haura sama yayi mata wanka ya sa mata fararen pjamas kan ya jata zuwa ɗakinshi, bata hira tunda lalurar nan ya sameta gwara ma da mahaifinta amma idan ka cire shi da ido kawai take bin" mutane kaman aljannu. "Gado ta haye ta kwanta, sai a lokacin yayi isha kan ya hau gadon ya janyo system ɗin shi ya buɗe Email da Hibbah ta aika mishi." "To his biggest surprise slides uku ne kaɗai masu kyau sauran ya ma kasa gane menene, wayanshi ya janyo sai dai bashi da layinta Director HR ya kira ya tura mishi layinta ya shiga ƙira amma ya ƙira ya fi sau biyar No answer." Numfashi ya sauƙe yana yi mata uzuri kila kanta ne ya matsa mata tunda ya san she's sick amma gobe ne da misalin karfe 9 meeting ɗinsu da mutanen nan. "Dole haka ya bari ya kwanta, da asuba bai koma bacci ba ya shiga kiran layinta nan kam user busy ranshi ya fara ɓaci, wanka yaje yayi ya sauka ya yi musu pancake da oat ya zo ya tashe ta yayi mata wanka da brush ya shirya ta cikin gown ɗinta ya saka mata hula suka sauƙo suka" "ƙarya, ko da suka fice daga gidan almost seven sai 8 ya iso office yana shiga tana shigowa." """Good morning Sir...!""" """Me amfanin wayanki idan za'a yi ta ƙira No answer and after that ba za ki yi returning calls ba?""" "Bata san shi bane ko da ta tashi da asuba ta ga calls ɗin bata bi ba sai tayi blocking Layin. ""I'm very sorry ban san kai bane...""" Bai jira ta gama sauƙe numfashi ba yace """Ki duba Email da kika turamin nan Its encrypted ki tura min mai kyau yanzu ASAP""" "Da sauri ta zauna ta buɗe system ɗinta ta shiga sai dai itama me? slide biyu tayi ta ga same abinda ya gani, ganin ta ɗaga ido ta kalleshi ya sa ya zagaya ta bayanta ya tsaya daga jikin" kujeran yana kallon system ɗin. """Whats happening?""" Ta faɗa tana ɗauko modem ɗinta sai dai na ciki kam ma babu gabaɗaya. """I thought kin ce kin yi abin nan intact? Then how comes hakan ya faru? You knew that clearly awa guda kachal ya saura mu shiga meeting ɗin nan whats wrong with you?""" Yadda ya hasalar ya sa ta kasa cewa komai gashi ta shiga rudu aikin da ta dauki kwanaki tana yi ko jiya lafiya lau ta gama me ya sameshi? "Wuceta yayi ya zagaya ya shige office nashi ranshi a ɓace, Goshi ta dafe" """Innalillahi wainna ilaihi rajiun... Gani yake karya nake yi mishi ban yi aikin nan bane?""" "Tayi maganan zuciyarta na zafi tuni hawaye sun fara zuba mata ita kam ta san ta yi aikin nan. Miƙewa tayi tana safa da marwa hannunta a Goshi, ba zata iya zuba ido su yi asarar project nan ba, no ba zata bari ya fara zarginta da karya ba, da sauri ta nufi office nashi yana tsaye kawai jikin tranparent Window ya zurawa birnin ido Jasrah na zaune chan gefe tana ta wasanta da tablet ɗinta ta shigo ta tsaya daga bayanshi yanayinshi kaɗai na nuna mata ranshi ya ɓaci" ƙoƙarin controlling kuma yake. """Sir...Wallahi na yi aikin n...""" "Katse ta yayi ""Then ina yake??""" Razana tayi da tsawar baya take ƙoƙarin yi sai takalminta ya taɗiye ta ba zato ta tafi zata faɗi.... "Littafin nan na kuɗi ne ki biya Naira Ɗari biyar (500) kachal domin kasancewa cikin masu kwasar tarin ilimi, faɗakarwa da zazzafar soyayya mai cike da sadaukarwa da aka zube ciki. Za ki biya ta wannan asusun" 0545475847 Gt bank Fatima Muhammad Gurin Sai ki tura shaidar biya zuwa wannan layi 09039206763 Ko kuma katin MTN na Naira 500 cikin wannan layi na sama sai ki tura da shaidar biya ta same layi. Sai na ji ku* Gureenjoh 46 Cikin azama ya sa hannu ya riƙo wrist ɗinta yana dawo da ita gaba don da ta faɗin ba abin da zai hana kanta bugu wa da center table ɗin bayanta. """Watch out!""" "Ya faɗa cikin kulawa, sakar mata hannu yayi bayan ta yi balancing idanunshi zube kan fuskarta cikin mamaki ya furta" """Are you crying?""" "Kanta ta kawar zuwa wani ɓangaren tana sniffing, taku biyu ya ƙara dab ita ya sa yatsunshi biyu" "yana dawo da fuskarta gareshi ""Hey Look at me...""" Yadda Muryar ya fito very cool and deep ya sa bata san ta cigaba da kukanta ba. Idanunshi ya ɗan zaro tace """Sir I wasn't lying to you da gaske na gama duka it was there jiya ko da ka ƙira nan, despite headache da na yi ta fama da shi jiya i made sure na yi aikin nan because i don't want any failure not from me...ni...ni ban san ya. """ "Katseta yayi don maganan sai breaking yake ita ta san ba makaryaciya ba, kuma ta wahala a" aikin nan ta ya za'a yi ta rasa shi lokaci guda? """Hey..! I am terribly sorry ban ce kin yi ƙarya ba, i was confused and tensed Thats why na miki" "tsawa but i trust you maybe issue ɗin daga system ɗin ne is ok Stop this crying""" Gently yake maganan yana jin damuwar halin da ta shigan sai yake ganin laifin kanshi. Fuskarta ta share tana kawar da kai cikin kunya don bata san zata iya zubar da hawaye haka "gabanshi ba, shi kuwa idanunshi zube a kanta he's diturbed har ranshi." "Zai yi magana aka yi knocking, numfashi ya sauƙe ya zagayeta ya koma kan couch ya zauna yana harde kafa ya amsa, P. A ne ya shigo ganinsu hakan ya sa ya ƙarasa ya zauna shima, kallonta MB ya yi" """Sit please""" Zama itama ta yi duk ta takura kanta. "P.A ya sanar wa abin da ke faruwa. ""Yanzu me solution?""" Ya tambaya bayan ya gama yi mishi bayani. """Huhhh Sir gaskiya da wuya mu samu wannan aikin we cannot convince them just using mouth" "ba papers, idan ma muka yi hakan za su daukemu kaman bamu san me muke ba ko bamu san makaman aikinmu ba""" "Kai yake gyaɗa wa hakane kam amma sai ya kalleta ""Miss Mudassir... Whats your opinion here?""" Ta ɗago fuskarta ba cikakken walwala tace """We just go for the meeting zan iya briefing ko summarizing abin da ke ciki because i put all my best there... Kana tare da su ni kuma anan zan yi kokarin in ga na dawo da duka slides ɗin na san ko sun amince ba a yau za su saka hannu ba if kenan that would be Ok""" Kallonta yake yi yana yaba kaifin tunaninta but ba za'a yi haka ba. """No! No one would snatched away ur Credits, ke za ki yi presenting ki yi convincing nasu tunda kin fi kowa sanin menene ke ciki, after then in sun amince za mu nemi su ba mu zuwa gobe za mu taɓa slide ɗin kaɗan kan mu gabatar musu idan komai ya tafi successful sai ki dawo ki yi" "ƙoƙarin recovering wanchan ɗin""" """Amma Sir...""" Ya katse ta """Shhhh..! For a while ina ba wa Mahir Credits ɗinki saboda rashin sani amma yanzu no one would do that, don haka save what ever you want to say and start preparing""" "Ya ƙarasa yana zuba mata dukkan idanunshi, bata da zaɓi illa ta fice daga office ɗin ta fara shiri kaman yadda ya faɗa." Ya dawo da kanshi kan P.A """I think someone altered with her system, because haka kawai slides ɗin nan ba zai lalace ba idan ma zai lalace ba shi kaɗai ba but komai na nan intact sai shi kaɗai? Something is definitely" "off""" """kafin kamalluwar meeting ɗin zan yi ƙoƙari na yi bincike a kai boss""" Kai ya gyaɗa kawai yana sake crossing fingers ɗin shi cikin nazari har P.A ɗin ya fice. Mintuna talatin suka wuce a daidai lokacin hall ɗin gabaɗaya na dauke da baƙinsu da kuma "waenda meeting ɗin ya shafa ciki har da shi yana zaune kan kujerar shi na musamman, ba zaka ce ga yanayinshi ba amma fuskarshi babu wani walwala as usual." A natse ta tura kofar glass ɗin ta shigo his gaze are fixed on her... She's so Calm tana maintaining gentle eye contact fuskarta with slight smile looking so warm and approriate muryarta ya fito calmly """Good morning..""" "Tsikar jikinsa yaji ta tashi akaro na farko arayuwarsa baisan sanda ya lumshe ido ba, yana sake jin muryarta na ratsa shi tana bayani ya kasa focusing har mamaki yake, a gefe ɗaya kuma ta samu wani gurbi mai girma a ranshi don yadda take presenting ɗin ko shi ya gamsu bare su, har aka gama meeting ɗin tunaninshi rabi da rabi idanunshi kuma basu bar kanta ba, bayan sun amince hall ɗin ya ɗauki tafi contract ɗin ya zama sealed za'a bi su da papers ɗin su sake" reviewing kan su saka hannu. "Sun yaba mata duka ana ta miƙa hannu for successfull meeting ta zame ta fice, ya ɗan bi" bayanta da kallo kan ya ɗauke kai. "Bayan gama watsewar kowa ya koma office sai dai bai sameta ba, yana shirin fita dubata P.A ya shigo" """Sir you have to see this..""" "Office nashi suka shige bayan ya zauna P.A ɗin ya miƙa mishi ipad, sai ga Hibbah na zaune kan sallaya Raliya ta shigo zuwa kiranta da yayi ta tafi office nashi, bayan barinta wurin Raliyar ta miƙe da azama ta nufi systems ɗinta, ta fi minti uku a kai tana yi sauri sauri duk alamun rashin gaskiya ya gama bayyana a yanayinta, ranshi ne ya ji yana ɓaci yanzu idan da sun rasa wannan kuɗi menene gain na wannan yarinya? Me Hibbahn ta mata da zata lalata mata duk" wani aiki ta kuma shirya ɓata mata suna? """Dismiss this girl now!""" "Ya umarta yana miƙa mishi ipad ɗin, da sauri ya fice ganin yadda ran boss ɗin yake a ɓace, al'amarin mutane na bashi mamaki, tsam ya miƙe ya fito yana sake duba hibban sai dai bai" "ganta ba, balcony ɗin office ɗin ya fito daga saman sai ya hangeta tsaye kawai ta ƙurawa waje" "idanu, da alama akwai abinda yake damunta." """You did well, Thank you""" "Magananshi ya dawo da ita duniyar mutane, numfashi ta ɗan sauƙe kan ta juyo ta kalleshi" """Ni ya kamata in gode maka Sir for trusting me""" Ba murmushi yake ba amma idanunshi basu bar kanta ba har ta kasa jurewa ta janye nata ta mayar waje. """Raliyat ita ce ta lalata miki aiki, I fired her for that hakan ba zai sake faruwa ba""" "Cikin kaɗuwa ta waigo tana tuna lallai ta shigo jiya, me ta yi mata da ta tsane ta haka da har take shirin ruguza mata aiki? Meyasa Raliyat ta kasa sonta tun zuwanta ma matsayin Service" kan ta fara aiki? """Sir da baka yi haka ba, kora shi ne last abin da zata yi expecting aikin nan shi ke riƙe mata da" "yaranta da ita kan...""" "Da tsantsar mamaki yake kallonta hakan ya sa maganar yankewa, ya ɗan matso har tana jin" numfashinta na sarƙewa da kamshinshi """kin kuwa san cewa da ke ce a yanzu Matsayinta? She did that on purpose saboda ta san cewa bana wasa da abinda ya shafi aikina sai dai bata san cewa ni ba mutum bane mai yanke hukunci cikin fushi da rashin tunani, Idan da tana tuna yaranta da kanta da bata yi hakan ba So" "do not question my decision Mrs Mudassir""" "Ya ƙarasa da Muryar gargadi kan ya juya ya fice ta bishi da kallo, haka kawai take jin gabanta na faɗuwa bata so hakan ba sam don irin wannan hassadar da tsanar baya tsayawa iya nan, hassada mugun ciwo ne da ya kamata mu nemi tsari da shi, fitowa tayi sai ta samu Raliyat kam" zube a ƙasa ga MB na nan tsaye tana ta bashi haƙuri cikin kuka hannayenta a harɗe. Tana ganin Hibbah ta matso da gwiwa """Don Allah Hibbah ki yi haƙuri...! Help me kar ki bari na rasa wannan aiki, wallahi duka familyna da shi muka dogara i spent years ina fafutuka kan na samu i cannot loose it just like that"" Sossai ta bata tausayi, ta kalleshi kaɗan fuskarnan babu alamun fara'a don dole ta mayar da kanta ƙasa saboda yadda zuciyarta ke bugawa da yanayin fuskar nashi, tsaki ya ja ya shige" office nashi ya kama Jasrah suka fito bai ko kalli ɓangaren su ba ya bar companyn gabaɗaya. """Raliyat ban san tsanar da kika yi min ya kai ki nemi wargaza min aiki ba amma na tabbatar ko a hakan yanzu kin ga ishara, wallahil azeem ba zan yi farin ciki da rasa aikinki ba ko ba don ke ba ko don iyalanki, ki yi haƙuri ki tafi zan yi magana da shi idan ya sauƙo ni kika yi wa laifi kuma wallahi na yafe, ki nemi tsari da hassada ki wanke zuciyarki za ki fi jin daaɗin zaman wannan duniya""" Tana kai nan ta koma wurin zamanta ta zauna. "Ficewa Raliyat tayi tana mata godiya cikin kunya, Hibbah aikinta ta fara bata bar office ɗin ba" sai da ta tabbatar komai ya kamalla tayi printing ta shigar office na MB ta ajiye mishi kan ta fito "ta rufe tana duba time, ƙarfe bakwai na dare abinda an tashi tun 4 yau ita ce har ta haura time ɗin tashi haka, kamfanin shiru bata ji komai ba ta zaro wayanta daga chargy sai ta ga missed calls dayawa na Mommy, da sauri ta kirata back" """Hibbah ina kika shige dare yayi har haka baki dawo gida ba?""" """Mommy gani nan tahowa wallahi aiki ne ya sha kaina kwarai da gaske amma yanzu nake tattara wa""" """Ki hanzarta in ganki gida, ina daaɗi mace ta kai dare haka waje?""" Fitowa tayi maƙale da wayan a kunne ta shiga elevator sai dai tana shiga ko rufuwa bai yi ba "wutan wurin duka ya ɗauke ""Subhallah!""" "Ta faɗa tana fitowa tare da kunna hasken wayanta, Allah andi me ya samu wutan ta ayyana hakan a ranta kan ta nufi stairs dukda ta san ba karamin wahala zata sha ba, saukinta ma gangarawa ne ba haurawa ba, tana tura kofan taji an turo ta baya har wayanta ya faɗi da ƙarfi hasken shi ya ɗauke, wani mummunan faɗuwa gabanta yayi kan tayi balancing ta ji an turata an danne bakinta tare da mannata da gini, tuni wani irin firgici ya rufeta ta shiga kokawar kwace kanta sai dai namiji ne karfin ba ɗaya ba, numfashi ta ɗauke jin hannunshi jikinta bata san ta gantsara mishi cizo ba ya sakar mata baki ta yi wani irin ƙara numfashinta na shirin barin" gangar jikinta... "Zaune yake cikin mota ya bar jasra dake kuka gidan su Mum yana mamakin Meyasa a koyaushe in zai barta gidan sai ta yi kuka zuciyarshi baya daaɗi da hakan kuma baya iya cewa Mum ɗin a'a idan ta nema, aure ne kawai zai kusanta su da 'yarshi ta daina damuwa da ɗaga hankalinta a duk sadda zai musu nisa amma shi wa zai aura? Ta ya zai sake fara son wata a" rayuwarshi?. Call din P.A ne ya shigo suka tattauna kaɗan don ya bar office ɗin ba shiri saboda ɓacin ran Raliyat ɗin nan. """Ka duba aikin yarinyar nan kan barinka office?""" """Na bar office 5pm amma bata tafi ba boss tace ba zata tafi ba sai ta gama aikin nan""" "Sai ya ji ba daaɗi, suka yi sallama ya ja motarshi amma sai ya kasa natsuwa ya shiga kiran layinta don tabbatar da ta je gida lafiya sai dai bata picking." Chief Security na companyn ya ƙira """Good Evening Sir!"" ""Yeah, how are you?""" Ya amsa cikin ladabi """Yaushe Hibbah ta bar company?""" "Ya tambaya, jin shiru alamun bai gane ba ya sa yace ""My secretary""" Ya gane ta kuma ya san motarta """Sir she's still in the building, ooppsss..."" ""What?""" He asked calmly """Wutan ne kawai ya ɗauke i have to go and check menene matsalar"" ""Kana nufin har yanzu Mrs Mudassir na companyn nan?""" """Am very sure sir motarta na nan""" "Wani irin damuwa ne ya rufe shi da ba zai iya cewa na menene ba, juya kan motarshi yayi ya ƙara mata speed, cikin mintuna ashirin ya isa companyn sai dai har lokacin babu wutan, duhu ne ko ta ina, bai tsaya tambayar Securities biyu dake tsaye suna jiran Chief ɗin ya dawo daga duba matsalar wutan ba ya bi stairs ya fara haurawa" "Ayyanawa yake yarinyar nan bata da hankali, ko tsoro bata ji ta zauna ita kaɗai har irin wannan lokaci? Aikin na aljanna ne... Kila ma tana tsoron duhu, kila bata da ma haske a kusa da ita" yana tura kofa ana dawo da wutan sai idanunshi suka mishi mummunan gani.... "Littafin nan na kuɗi ne ki biya Naira Ɗari biyar (500) kachal domin kasancewa cikin masu kwasar tarin ilimi, faɗakarwa da zazzafar soyayya mai cike da sadaukarwa da aka zube ciki. Za ki biya ta wannan asusun" 0545475847 Gt bank Fatima Muhammad Gurin Sai ki tura shaidar biya zuwa wannan layi 09039206763 Ko kuma katin MTN na Naira 500 cikin wannan layi na sama sai ki tura da shaidar biya ta same layi. Sai na ji ku* Gureenjoh 47 "Ta dunkule a jikin table tana jan numfashi da kyar da kyar abinka da farar mace duka jikinta yayi wani irin jajazir, gyalen kanta yayi wani ɓangaren gashinta a hargitse, doguwar rigar jikinta rabin shi a farke har yana iya kallon skin ɗinta, wani irin runtse idanu yayi wani abu marar fasaltuwa" na dirar mishi kaman miƙi a zuciya. "Da kyar ya iya ambaton sunan Allah ba ita ba har shi jikinshi rawa yake, hanzarin nufarta yayi yana zare rigar jikinshi bayan ya cire bottons biyu yana taɓata tayi ihu tana kiran sunan Allah a rikice shima a rikice ya riƙeta" """Calm down! Hibbah you are safe kalli ki ga babu abin da zai sameki...""" Ganin da gaske shi ɗin ne kuma she's safe ta fashe da wani masifaffen kukan da ya saka "idanunshi cika da kwallah, wayanshi ya zaro yana Miƙewa tsaye ya nufi gyalenta." Chief Security ɗin ya kira """Idan har kuka bari wani rai ya fita a building ɗin nan yau wallahil azeem dukkanku kun shiga uku""" "Yana kai nan ya yanke wayan ya nufota ya sanya mata scarf ɗin a kanta ta haɗa ta rungume a kirjinta tana kuka sossai, a wurin ya duƙa kanshi ƙasa wani irin mummunan abu ke shirin faruwa a karkashinshi? Meyasa hakan bai taɓa faruwa ba sai akan Hibbah? Meyasa za'a so lalata mata rayuwa? Ko ma an ci nasarar ne..." """No No hakan ma ba zai faru ba..."" Ya faɗa a fili yana kawar da tunanin." "Kokawar da take yi da numfashinta ya dawo da shi daidai, da sauri ya tafi despenser ya kawo mata ruwa sai dai bata iya ta sha ba, numfashinta kokarin barin gangar jikinta yake har lokacin" bata daina jijjiga ba dole ya riƙeta idanunshi kaman garwashin wuta. Ganin ba zata natsu ba kuma zata iya suma mishi yasa ya ɗauketa chak ya nufi elevator ko kula Chief Security da yake ta kiranshi hankali tashe bai yi ba ya sanyata mota suka fice daga kamfanin. "Private hospital mai kyau ya kaita, rabon da ya ji tashin hankali haka tun ranar da aka kirashi aka sanar da shi hatsarin Anam da jasra, yawo kawai yake a harabar hall ɗin yana jiran likitar da ta shigan ta fito, adu'ar shi da fatanshi Allah ya sa ba'a samu nasarar kassara rayuwarta ba," har karfe 9:30 kan likitar ta fito tana kallonshi """Are you her relative?""" Ya girgiza kai """She's an employee in my company... Don't tell me an samu nasara a kanta?""" Yadda yayi maganan sai da ta ji wani iri don damuwarshi bai ɓuya ba har a harshen shi. """A'a babu abin da aka yi mata amma tsoro da firgici ya jefa ta wani hali, kaman kuma dama tun farko akwai problem na kirji a tare da ita so abin ya haɗe sai ya zama severe amma komai is normal yanzu, idan ta tashi lafiya ƙalau""" Ta ƙarasa tana kallon builded body ɗin shi a zaton ta ma mijinta ne ko amarya ce firgicin daren farko ya kawo su asibitin duba da ko riga bayan farar vest babu jikinshi. Ita kuma farin shirt nashi dake jikinta ya ɓoye yagun rigar ta. "Ɗakin ya shiga bayan ta tafi ya zauna kai tsaye ya shiga kiran manyan ma'aikatanshi suka haɗa zoom meeting abinda ya ce kawai ya rufe company na 1week kowa ya zauna a gida, duk yadda suka so su ji wani bayani bai ce komai ba, da farko sun so ƙi saboda asarar da za su yi a satin na da yawa amma ganin ya hasala yasa suka yi shiru ya nuna musu ko da yardarsu ko ba da yardarsu ba ya yanke hukunci, bayan ya kashe ya kira wani friend ɗin shi babba ne a DSS ya" sanar da shi abin da ke faruwa. """A daren nan ba sai gobe ba ina so ku yi duk yadda za ku yi gaskiya ta bayyana, ban san me zan iya yi ba da hakan ta kasance don ba ita kaɗai ba har career ɗina sai ya lalace kowa zai iya rasa aikinshi sanadiyar wannan attempt ɗin, wallahi mubarak ko million nawa zan iya kashewa" "don ganin na kawo karshen koma waye yayi wannan yunkurin""" DSS ɗin ya tabbatar mishi a yanzu za su fara aikinsu ya kwantar da hankalinshi gaskiya kuma "zata bayyana, sai dai binciken har kanshi ba zai bari ba yace ya amince suka yi sallama." "Iyayenta yake tunanin ƙira sai dai me zai ce musu? Ta yaya zai samu layinsu? Cikin wannan tunani ta farka karfe goma sha ɗaya na dare, a firgice ta farka da hanzari ya miƙe tsaye daga zaunen da yake cikin cushion na ɗakin Amenityn ya nufi gaban gadon." """Ki ƙira sunan Allah za ki samu natsuwa...! You are safe, nothing will harm you in shaa Allah""" Ya faɗa cikin sanyi da raɗa. kaman yadda ya faɗa salati ta fara kan ta shiga jera sunayen Allah zuciyarta na karyewa sai kuma hawaye suka fara zuba mata babu kakkautawa """Lã ilăha illallähul-'Azimul-Halim," "Là ilaha illallähu Rabbul-'Arshil-'Azim, La ilãha illallāhu Rabbus-samāwati wa" "Rabbul-ardi wa Rabbul-'Arshil-karim.""" "take faɗa a fili cikin sautin kuka, bai hanata ba tana cikin idanunshi na a kan hannayenta da take ta squeezing a tare, wayanshi ya shiga ƙira, ajiyar zuciya yake sakewa a hankali kan ya zaro wayan yana dubawa ya ga Nasir" Picking yayi ya makala a kunne """Boss ka yi haƙuri na ƙiraka by this time ƙanwata ur secretary ban san ko kuna tare ba hankalin" "mahaifiyarmu a tashe har yanzu bata je gida ba""" "Kallon Hibbah yayi sai ya saka wayan a handsfree ""Nasir dama Hibbah sister ɗinka ce?""" """Yeah she's my cousin sister"" ""Ok gata nan muna ho...""" "Da sauri ta miƙa hannu ta katse ƙiran tana cigaba da kuka, idanunsu ne ya sarke nata na zubar" "da hawaye nashi suna nan Red har lokacin jijiyoyin kanshi duk a tashe. ""Meyasa kika kashe?""" """Bana so su sani...bana so su san abin da ya faru a yau!""" Ta ƙarasa tana kau da idanunta daga kanshi muryarta so slow sai breaking yake. """Why?""" """Don Allah kar ka faɗa musu...ina da dalilin boyewar, daga zaran sun sani ba lallai na cigaba da aiki ba kuma aikin nan shine abinda ke mantar da ni damuwowina, bayan nan ko ba don aiki ba shikenan Hibbah ita ce koyaushe ake tashin hankali a kanta? Ni kaɗai ce 'ya da a kullum wani abu ya faru a family mai muni sai an ji sunana? Me kake tunanin mutane za su ce bayan giɓin da rayuwata ke da shi a baya? Tunda bai yi nasara a kaina ba mu binne maganan ko don kare martabar kamfaninka...""" Ta ƙarasa idanunta zube a gini. "Sai kallonta yake yana jin maganganunta na ninka tsananin tausayinshi gareta, menene a rayuwarta haka? Me take going through? Bashi da mai bashi amsa, call din Nasir ne ya sake shigowa." """Nasir Hibbah tana asibiti ciwon kirji ne ya kamata lokaci guda but she's okay now gata nan..""" Zai miƙa mata ta koma ta kwanta tana juya mishi baya. "Nasir dama ya san da wuya ta amsa, muryarshi na bayyana damuwar da yake ciki yace ""Wani abu ya faru da ita ne na damuwa Ranka ya dade?""" """Nasir I cannot say gaskiya just make sure ka sanar da gida""" "Ya faɗa mishi sunan asibitin da numbern room ɗin, bayan ya kashe ya miƙe ya fice chan sai gashi ya dawo yana sanye da jallabiya fara tas, hannunshi da paperbag na kamfanin kayan sawa na Dior, tana nan lokacin a kwance ta dunkule wuri guda shesheka take fitarwa a hankali" tana tariyo rayuwarta tun daga farko. """Mrs Mudassir""" "Ya ƙirata, ta miƙe zaune tana Juyowa" """kukan nan ya yi yawa please, ba zai yi maganin komai ba illa iyaka ya kara miki ciwo kan wanda kike ciki""" """Ba zan iya hana kaina kuka a yanzu ba, me na yiwa rayuwa da ba ya min adalci? Meyasa wani marar imani zai yi wannan mummunan yunkurin a kaina? I pleaded...I screamed...I fought amma ko dar bai ji na zai iya tausayamin ba, had it been Allah bai jefomin kai ba kila da yanzu na bar duniyar bcs ba zan iya ɗauka ba kuma! Zuciyata zafi take kaman zata fito...Sai yaushe" "ne zan samu farin ciki? Sai yaushe rayuwa zata tafi mini daidai? Ko dai ba ni rabon hakan ne?""" "Ya isa gangarta ya zauna har tana shakar kamshinshi mai sanyi, kallonta yake sossai kan ya ce ""Kowa kika gani da irin jarabawar da yake dauke dashi kawai dai na wani ya fi na wani ne, sannan bawa baya taɓa yanke rai da rahamar ubangiji saboda shi ɗin maji kan bayi ne, da zan faɗa miki wanene Mustapha Bashir Almustapha da kila zaki ce Alhamdulillah... Ki tashi ki watsa" "ruwa ki sauya kayan nan tunda bakya so a san abinda ya faru""" Saukowa ta yi idanunshi na kan kumatunta da yake iya ganin shatin yatsu alamun marinta aka yi ya ɗan datse lips yana dauke kai har ta shige toilet dake ɗakin. "Kan kujera ya koma ya zauna, ta fi mintuna talatin kan ta fito, doguwar farar riga ne da ya zauna mata kaman ya san size ɗinta, sai gyalenta da ta mayar kanta don dama black ne, fuskarta very pale tana tafiya a hankali saboda babu inda baya yi mata ciwo a jikinta har ta zauna bakin gadon sai ga nurses sun shigo, allura suka yi mata suka sake sa mata wani ruwan, bayan sun fita ta kwanta tare da lumshe idanu sai ya samu kanshi da barin kallon wayan da yake yana" zube mata lumsassun idanunshi. "Hibbah is dangerously fine, Effortlessly classic," "Unapologetically gorgeous. The kind of beauty that doesn't ask for attention, idan yana kallonta sai ya kasa dauke idanunshi a kanta kaman wani magnet ne ke maƙale da ita da suke sarrafa kwayar idanunshi ga kallonta, knocking da aka yi da turo kofan lokaci guda ya saka shi ɗauke idanun don dole ya kalli kofar, babbar macece ce ta shigo a rikice bayanta wani saurayi sai" wata hannunta riƙe da na wani karamin yaro. """Hibbah! Hibbah me ya sameki? Garin yaya kika kare a gadon asibiti daga zuwa aiki?"" Aunty Kubra ke faɗi tana kamo hibban, buɗe idanunta tayi ta miƙe zaune sai ta kwanta jikin Aunty Kubra ɗin chan ƙasa tace" """Kirjina ne ke ciwo amma da sauƙi mommy ki kwantar da hankalinki""" "Numfashi ta sauƙe ganin tana magana kuma dai da alamun da sauƙi ɗin don jikin babu zafi sossai, sai a lokacin suka kalli MB MUSTAPHA dake zaune, Abdul ya miƙa mishi hannu suka gaisa ya gaishe da Aunty Kubra ta amsa tana kallonshi" """Hala wurin aikinku guda? Sannu bawan Allah mun gode da kulawar da ka bata Allah ya biya""" "Murmushi ya ɗan yi kan ya miƙe ""Hajiya zan tafi tunda kun zo..."" ""Mun gode kwarai""" "Sai godiya take mishi tuni ya fice, sai a lokacin Hibbah ta ɗago ta kalli Mommy tace" """Mommy Shine fa MB MUSTAPHA ɗin""" Zaitoon tace """Shi ne?? Dama ba wani babba ba ne? Ikon Allah wlh yadda nake jin sunan nan na zaci tsoho ne""" Mommy tace """Toh sunan mustaphan ne yayi kala da na tsoffi""" Zaitoon na dariya tace """Kawai yadda Ya Nasir ke labarinshi da yadda yake girmamashi ne sannan mommy yana wuya fa ki samu irinshi matashi mai irin wannan arziki da yake da shi a karan kanshi ba na mahaifinshi ba""" Abdul yace """Hakane kam don wannan da wuya idan yayi 38""" Mommy tace """Ni yadda ya burgeni bashi da girman kai, ji yadda ya kula mana da Hibbah... Allah ya saka mishi""" Suka amsa da Ameen. "Hibbah dai tana jinsu kawai, sai da mijin Zaitoon ya zo daukarsu don ta bar motarta gida ne ta biyo su saboda tun safe ta je gidan tana jiran zuwan Hibbah su gaisa ta tafi shine fa basu ga Hibba ba hankalinsu ya tashi, da abinci ta taho don ta kira Maids ɗinta sun yi varieties saboda" gidanta ya fi kusa da asibitin akan gidan Mommy komawa da kuma dawowa ma aiki ne. "Mommy ne ta lallaɓa Hibbah ta ci wani abu, Abdul yana ta yi mata sannu sai dai ta gyaɗa kai daga karshe ya musu sallama ya tafi sai da safe zai dawo shima kaman yadda Zaitoon ta ce, mommy da Hibbah ne suka kwana asibitin ta yi iya kokarinta wurin ɓoye damuwarta kar su mommy su gane sai da ta tabbatar mommy ta yi bacci taje tayi alwala ta zo ta shiga gabatar da nafila tana kaiwa Allah matsalolinta da roƙon shi ya yaye mata ya kuma tona asirin koma waye" "ne ya far mata, da kyar ta dawo gado bacci ma sai ɓarawo ne ya sureta." "Shi kuwa MB MUSTAPHA company ya wuce don su Mubarak suna chan DSS da ya ƙira ya same su a CCTV room, an ɓata CCTV ɗin sai dai wani kwararre daga cikinsu yayi restoring abinda aka goge, duk ma'aikatan Securities da suke kamfanin daga yamma an kama su an tafi da su office na DSS ɗin don bincikarsu saboda babu yadda za'a yi hakan ya faru babu mai cleu, sai da yaji da ma bai zo ya samesu ba, sun samu ganin mutumin da ya shiga building ɗin sai dai bakaken kaya ne jikinshi full ko ina a rufe sai bayanshi kawai da hular facing cap da ya" saka. "Lokacin daukewar wutar da shigansshi office ɗin kai tsaye ya tabbatar musu komai was planned, ihunta, kukanta da roƙon da take mishi sai marin da yayi mata a sadda ta cije shi su suke ta yawo kan MB MUSTAPHA, idanunshi suka sake rinewa Dukda babu abinda suke iya kallo banda duhu don ma CCTV ɗin ba ruwanshi da Nepa da ba abinda zasu iya gani har Muryar ba zai naɗa ba, waya suka ji yayi an sanar da shi wani abu yayi saurin ficewa yana" "dukan gini, yana kuma fita daga office ɗin basu ga inda yayi ba." "Ɗaukan Original clip ɗin suka yi suka fito zuwa office ɗin, jakanta na nan ƙasa da wayanta da ya ci screen saboda irin faɗuwar da yayi, nan ma sun dan yi bincike kan suka tafi bayan sun dan tattauna da MB ɗin, office nashi ya shige ya zauna yana ɗora kanshi kan desk dinshi abubuwa ne goma da ashirin suke mishi yawo amma tausayi, damuwa da son sanin wacece ainihin Hibbah Mudassir Madaki su suka fi yawa a ranshi, ɗago kai yayi sai ya ga proposal da ta ajiye mishi wani abu ya sake rufe shi yana jin kaman zai yi zazzabi karshe a office ɗin ya kwana har garin Allah ya waye, da kanshi ya fita ya garkame companyn bayan ya tattare kayakinta ya shiga motarshi ya bar companyn kar ma wani ma'aikacin da bai san da batun break da ya bayar" ba ya zo ya sameshi saboda babu wanda zai so ganinshi a yadda yake. "Gidanshi ya wuce Dukda urge na son zuwa ya ganta da yake ji, wanka yayi daga shi sai" bathrobe ash ya zo ya kwanta a kan tattausan gadonshi yana lumshe idanu a haka wani baccin ya sake ɗaukarshi. "Littafin nan na kuɗi ne ki biya Naira Ɗari biyar (500) kachal domin kasancewa cikin masu kwasar tarin ilimi, faɗakarwa da zazzafar soyayya mai cike da sadaukarwa da aka zube ciki. Za ki biya ta wannan asusun" 0545475847 Gt bank Fatima Muhammad Gurin Sai ki tura shaidar biya zuwa wannan layi 09039206763 Ko kuma katin MTN na Naira 500 cikin wannan layi na sama sai ki tura da shaidar biya ta same layi. Sai na ji ku* Gureenjoh 48 "Ƙarfe tara na safe ya farka, sai da ya sake wanka kan ya shirya cikin kananun kaya kasancewar akwai sanyi ya ɗora leather jacket akan rigar tashi, wayoyinshi ya zara not minding yunwa da" yake ji ya nufi fita daga gidan yana danna ƙiran Mubarak. Kusan ringing na ƙarshe yayi picking """How far Mubarak?""" Numfashi Mubarak ɗin ya ɗan sauƙe """Duk yadda za mu yi da su mun yi amma sun ƙi magana duk nuna they are innocent suke" "amma zamu cigaba da bincike ka kwantar da hankalinka MB""" Tsiririn tsaki ya ja yana shiga bayan motar da Driver ya buɗe mishi don yau din baya jin karfin driving da kanshi. """Shikenan please ku yi hakan""" Yana kai nan ya katse ji yake kaman basu bincikesu yadda ya kamata ba. "Yana kallon ƙiran P.A ɗin shi amma bai ko yi niyar picking ba, sai da suka fara shiga gari kan Driver ɗin ya tambayi inda za su." "Wani mall ya ambata, kusan tafiyar mintuna arba'in ya kai su ya sauƙa ya shige ciki for almost" hour kan ya dawo. "Sunan asibitin ya faɗa da location ya ɗan kishingida jikin seat ɗin tare da mayar da idanunshi ya rufe, har suka isa bai motsa ba sai da ya ɗan jima zaune ma kan ya fito ya shiga ciki hannunshi ɗaya sanye cikin aljihu, kaman kar ya ƙarasa yake ji don wani zuciyar na mishi gargaɗin kar" "zakewar yayi yawa, wani kuma na tabbatar mishi da hakan dole ne a gareshi." "Knocking yayi, ba'a jima ba aka buɗe Zaitoon ce ganinshi da safe haka sai ta ji ashe ma jiya kallon tsoro ta masa Dukda idanunshi sanye da glasses mai duhu hakan bai hana kyau da" charisma ɗin shi fita ba. Matsawa ta yi tana mishi sannu da zuwa ya shiga. "Mommy da Jadwa wacce ita ce ake shirin aurensu da Abdul kuma jin Hibbah ba lafiya ne ta taho gaisheta suka mishi sannu da zuwa ya amsa yana gaida mommy ta amsa cikin nuna jin daaɗin kular da ya ba Hibbah, itama Jadwa ta gaishe shi ya amsa ba tare ma da ya wani kalleta ba, sai a lokacin ya ɗan kai idanunsa kanta jin ta furta" """Good morning""" "Cikin tsiririyar muryarta da ya kara shige wa ciki. ""How are you feeling today?""" Ta amsa da lafiya ƙalau. Bai wani jima ba ya miƙe yana ji Mommyn na maganar kila a sallamesu ma ai don jikin da sauƙi yayi mata adu'ar samun sauƙi ya ajiye ledar hannunshi a kan table ya fice. "Zaitoon ce ta ɗauka bayan fitanshi, wayar Hibbah da ya fashe ne a saman wani kwalin na" Iphone. """Wannan kam wayan ya faɗi ne haka Hibbah baki sani ba?""" "Kai ta ɗan gyaɗa bata ce komai ba, ko da Zaitoon ta buɗe kwalin wata sabuwar Iphone 17 air" "ɗin ce silver sak irin nata ɗin da ya fashe. ""Gaskiya mutumin nan na da kirki ainun""" Mommy tace """Gashi har ya shiga hidima shi da ba shi ya fasa ba, Allah dai ya saka mishi da alkhairi"" Suka amsa da Ameen." "Jadwa ce ta karɓa ta sanya mata sim ɗinta a sabuwar ta miƙa mata, jakanta na office kuma" router ɗinta na ciki na Zaitoon tayi connecting ta fara saka icloud ɗinta. "Karfe Ɗaya na rana aka sallamesu don ta ji sauƙi Dukda dai kirjin na mata ciwo sa'i da lokaci, duka 'yan gidansu da suka san bata da lafiya sai da suka ƙirata suna yi mata gaisuwa, kuma haka ya ɗan yi cheering mind ɗinta, ko da suka je biyan bills aka ce musu ai an biya da safen sun san aikin MB MUSTAPHA ne don haka Adu'a kawai mommy ta mishi suka fice a motar Zaitoon da driver ya kawo abinci da safen ya bar mata nan don jiya chan gidan mommyn motar" "ya kwana, Abdul na chan wurin aiki bayan ya sauƙe Jadwa ya wuce." "Tana isa gida wanka ta yi da ruwa mai zafi sossai ta sake gasa jikinta ta fito ta fara shiri a hankali har ta gama cikin cotton doguwar riga, ko motsi tayi kamshi ne ke tashi jikinta haka ta kwanta ta lumshe idanu babu irin tunanin da bata yi ba har bacci ya sureta a haka, ƙarfe huɗu da 'yan mintuna ta farka taje tayi alwala ta zo ta gabatar da sallah a lokacin Jadwa ta shigo ""Na leƙo ai ɗazu kina bacci""" """Ina kwanciya baccin ya sureni fa ba shiri""" Ta amsa fuskarta a sake """Eyyaa sannu! Allah ubangiji ya kara sauƙi ni zan wuce""" "Miƙewa tayi sanye da hijabin Jadwa na ce mata ta bari ma ba sai ta raka ta ba ita kuma tana cewa ba komai ai zata miƙe kafa ne har gaban motar gidansu da ya zo daukanta ta raka ta ita da Zaitoon, sai da ta shiga Zaitoon ta ajiye mata leda da mommy ta bayar a bata tayi godiya" kan suka fice. """Tana da hankali sossai na yi wa yaya Abdul murna"" Hibbah ta faɗa da 'yar murmushi expression ɗinta blank." """Aikam dai tana da hankali sossai, saura mu ga ta Yaya Nasir"" ""Allah ya sa kar ya kwaso mana baturiya to""" "Suka yi dariya a tare, ko da suka shiga Zaitoon wurin Mommy ta yi yayinda Hibbah ta nufi ɗaki, tana shiga taji ringing na wayanta kan ta ɗauka ma ya yanke, dayake sabon waya ne bata yi setting na silence unknown caller ba tukuna, ta buɗe tana kokarin duba number ɗin aka sake" ƙira. """Hello""" Ta faɗa tana zama. """Hibbatullahi Mudassir Madaki kin tsira a karon farko, amma ba komai a juri zuwa rafi dai...by" "the way na ƙira ne in yi miki gargaɗi..."" Ta miƙe tsaye" """Wanene kai? Kuma me kake nema da ni?""" Dariya yayi da alama Muryar an sauyata ne ko ta hanyar na'ura ko kuma daga maƙogoro. """Kin riga kin san me nake nema ai, na san babu abinda yake baki tsoro irin sake bayyanar hotunan da kike tunanin sun ƙare, ina da su har da waenda aka yi amfani da irin jikin da fuskar tsaff aka haɗa kyawawan videos da maza daban-daban...""" Idanunta ta ɗan zaro sun rine tuni """Me kake so da ni? Meyasa za ka ɗauki alhakina? Me na yi maka?""" """Duk kin san amsar yarinya, abin da ya kamata ki tambaya shine... In faɗi sharudai na za ki bi, kuskuren bin sharaɗina daidai yake da ki wayi gari da ganin videos ɗinki na playing automatically a billboard na matsiyaciyar kamfaninku, sai kowani ma'aikaci yayi Allah wadai da ke, sai kin zaɓi mutuwa fiye da rayuwa. """ "Hawaye ne suka shiga zubo mata babu shiri, waye ne zai yi Blackmailing ɗinta bayan yunkurin mugun nufinshi gareta?" """Me me kake so?""" """Yauwa 'yar gari, ina so ne ki saka wanchan bastard boss naku ya daina bincike a kaina, ina so ya zare hannunshi a lamarinki you will never fool me a tafin hannuna kuke duka, wallahi idan" "bai dakatar ba za ki sha mamaki""" Kitttt aka katse ƙiran. """Hasbunallahu wani'imal wakeeel innalillahi wainna ilaihi rajiun""" Ta Yi ta maimaitawa idanunta zube wuri guda na tsawon mintuna talatin kan ta sanya kanta cikin pillow ta fashe da wani kukan. "Ta Yi kuka har ta ji ba daaɗi kan ta miƙe ta ɗauko wayan ta shiga duba Layin MB MUSTAPHA sai dai bata da shi kasancewar ranar da ya kira bata yi saving ba, ta duba Layin Raliyat ta kirata sai dai a kashe. Babu irin tunanin da bata yi ba Usaib ne da bai samu cikon burinshi a kanta ba yake son tarwatsata? Raliya ce ta cigaba da riƙe tsanarta a zuciyarta take son ganin bayanta?" Ko Sagir ne har ya fito daga prison yake son ƙarasa kasheta? "Director ta ƙira shima not reacherble, ta sake gwada Layin da ya ƙirata yanzu switch off wayan ta jefar tana binne kanta a tsakankanin kafafunta tana sake fara sabon kuka, ko da Allah zai sa ta bar aiki kamfanin MB MUSTAPHA bata fata ko da wasa ta barshi a tozarce, tana tuna irin baƙin ciki, damuwa da ɗimuwa da ta shiga a baya na irin Blackmailing ɗinta da Sagir yayi da watsa hotunanta, zubewar ƙimarta da na gidansu idan irin hakan ya sake faruwa ya zata yi?" Dole ne ta samu MB MUSTAPHA a yau din nan. "Layin Nasir da rabon da su yi magana har ta manta ta duba sai dai ashe na Nigeria ne da sauri ta miƙe ta nufi ɗakin mommy, suna zaune da Zaitoon suna duba wasu kaya don shirye shiryen auren Abdul ake sossai saboda ya ƙarato." """Mommy Don Allah ina son numbern Ya Nasir"" Ta faɗa tana iya kokarinta wurin ɓoye damuwarta ""Me ya samu idanunki haka Hibbah?""" """Mommy bacci na tashi ne""" Ga wayan duba ki dauka. Da sauri ta ɗauki wayan ta fice tana gujewa idanun Zaitoon da ta san ba haka ta barta yanzu ba. Ringing na ƙarshe yayi picking """Yaya Nasir..""" """Hibbah?? Ke ce kike kira na da Layin Nijeriya kai tsaye? Mu je WhatsApp mana"" ""No ba sai mun je ba, Layin MB MUSTAPHA nake so ka turomin""" """Lafiya kam?""" """Lafiya ƙalau pls yanzu don Allah""" "Tana kai nan ta katse ƙiran, cikin mintuna ta ga Layin tayi copying kawai ta shiga kiranshi." """Ya ilahi..""" Ta ambata tana Miƙewa tsaye layinshi not reacherble da alama a DND ya saka. "Duk yadda zata yi ta yi amma ta kasa samun shi, tayi kuka har ta gaji ko da bayan isha ta sha magungunanta don kirjinta da yayi mata nauyi bata san ta yi bacci ba." "Washegari har makara tayi don magungunan akwai na saka bacci sossai saboda ta samu isasshen natsuwar zuciya, wanka tayi ta shirya cikin shirin zuwa office don dole ta samu MB MUSTAPHA ta dakatar da shi akan binciken da yake, ta gwammaci ta bar kamfanin gabaɗaya akan sake shigar hotunanta duniya, ko da ta fito a shirye tsab mommy ta dubeta" """Ya dai? Sai ina?"" ""Mommy office""" """Haba Hibbah, yaushe kika samu lafiyar zuwa office? Ba Za ki huta sossai ba?""" """Mommy Don Allah kar ki hanani zuwa wallahi na ji sauƙi babu abin da zai faru"" Mommy dai bata so ba amma magiyar Hibbah ya sa dole ta haƙura." "Sai da ta fita ta tuna motarta ma ba ya gidan yana kamfani, tana shirin juyawa ta karɓo keyn mommy Abdul ya yi mata Horn." "Kaman kar ta je sai kuma dai ta nufi motar ta tsaya daga gefen da yake ""Ina kwana""" """Lafiya ƙalau Hibbah ya jiki?"" ""Alhamdulillah da sauƙi""" """Ko in ajiye ki office ɗin? Na kula chan kika yi kuma kaman Motarki bai dawo ba ko?""" Kaman ta ƙi amincewa sai kuma ta tuna idan ta tafi da motar Momma wa zai dawo da shi har ta samu ta ɗauko nata? Zagayawa tayi ta shiga ta zauna ya kunna suka ɗauki hanya. """Hibbah""" Ya ƙirata jin shirun motar yayi yawa kwarai. """Na'am""" """Hibbah ina so don Allah ki yi haƙuri, ina mai baki haƙuri bisa abubuwan da muka yi ta yi a baya zuwa ɗauke miki da muka yi, hakan ya faru ne bisa dalilin nemawa kaina sauƙi ba don na tsaneki ko na daina daukar ki matsayin kanwa kuma jinina ba, kin riga kin haramta mana a" "dokance ina mai roƙon ki da ki sake ba ni damar kasancewa ɗan uwanki kuma abokin shawara kaman yadda muke a baya""" Kanta ta sauƙar tana hadiye hawayen da suka cika mata idanu. """Na zaci ka tsaneni yaya Abdul hakan ya sa nima na tsani kaina na amincewa da nayi na biyo" "Ya Nasir Lagos gashi na rusa kyakyawar alaƙa da zamantakewarku...""" """Kin taɓa ganin inda aka tsani jini? Ke fa kanwata ce Hibbah komenene ya faru babu mai chanza wannan matsayin, mu ne muka yi miki laifi amma yanzu a wurina komai ya wuce Ki yi" "haƙuri da tsatsauran hukuncina na yi hakan ne don in warke ciwon rasaki""" Numfashi ta sauƙe """Shiekanan Ya Abdul Allah ya cigaba da haɗe kanmu ya kara mana karfin zumunci""" Yayi murmushi """Na gode kwarai kanwata""" Basu sake wani hira ba har ya sauketa gaban company sam basu kula da gate ɗin a rufe kirib ba sai da har ya tafi ta nufi gate don shiga ciki.... 49 "Da tsantsar mamaki take kallon gate ɗin, me ya faru haka da shutting down company gabaɗaya?" Ta tambayi kanta sai dai babu amsa kuma babu kowa a arear. "Luckily tana nan tsaye sai ga motarshi, har sun Wuceta kaɗan sai ta ga an tsaya, bai fito ba driver ɗin shi ne ya sauƙo ya zo wurinta." """Good morning""" "Ya gaisheta ta amsa da turanci don yoruba ne baya jin hausa, ya sanar mata oga ya ce wai ta zo." Har ya ɗan juya tana tsaye tana kallon motar sai ta tuna ma irin neman da tayi ta mishi da kuma abin da ya kawota tuni ta kau da tunanin dalilin ganin kamfani a rufe kuma ranar aiki da safe ta nufi motar dama ya riga ya buɗe mata driver ɗin tabbacin Site da yake ta ɗayan ɓangaren ne don haka ta zo ta shiga. "Wani daddaɗar kamshi da kuma sanyi na Ac da har ya yo over ne ya bugeta, ta ɗan sauƙe ajiyar zuciya duk sanyin da ake zabgawa gari bai isheshi ba? Ta ɗan muskuta don hankalinshi na kan system kuma bai kalleta ba Dukda haka kwarjininshi duk ya cika motar dama ta saba duk suka fita tare a mota guda a takure take, a haka ɗin ma yawan zaman nata gaba ne idan" sun fita sha'anin aiki P.A ke zama da shi a baya. """Good morning Sir""" "Ya ɗan gyaɗa kai, seconds huɗu ya ƙara kan ya ɗan waigo sai suka haɗa idanu don kallonshi take, ta ɗan sauƙar da idanunta ƙasa tana jin tambayar da ya watso mata." """Me kike yi anan?""" "Ta kalli kanta ta kalli companyn, wani irin tambaya ne wannan? Me kuwa take banda ta zo aiki?" Ko dai ya koreta ne already? """Aiki na zo""" Ta harhada ta faɗa don har lokacin idanunshi da suka fitine ta suna kanta. """Aiki?? Yaushe kika warke?"" Ta ɗan bata fuska kaɗan ""Na warke Sir""" "Sai a lokacin ya kawar da idanu bai ce komai ba ya yi wa Driver ɗin umarnin su tafi. ""Si...r""" Maganan ya maƙale saboda kallonta da yayi har sai da gabanta ya faɗi Dukda ba Harara ba ne "ko mugun kallo, ta rasa courage ne kawai kafafunta har sanyi suka yi, yanayi ne da bata taɓa ji ba a rayuwarta." "Duk yadda ta so mishi magana ma ta kasa, sai da suka yi nisa driver ya tambayi ina za su je?" "Shiru ya yi abin shi ta fahimci da ita kenan ake, ina kuwa zata je tunda ya sakota gaba daga kamfanin shi banda gida?" """Victoria Island""" "Ta faɗa chan ƙasa babu abinda bata saƙa ba, ganin sun haye gada sun fara shiga ciki ta faɗa mishi Layin da zai bi har kofan gidansu." "A waje yayi parking sai ya fita ya bar su, motar ya ɗauki shiru sai kamshin junansu dake dukar hancin kowannensu, ya haɗu da unguwar very quite, weather ɗin kuma very cool da ya saukar da wani warmness yanayi mai sa natsuwa da bacci." "Jin kaman ba zai yi magana ba ta buɗe baki tace ""I called yo...""" "Daidai ya juyo shima yana cewa ""Me kika je yi company?""" Shiru duk suka yi. """You should go First"" Ya faɗa calmly." """Na je aiki"" ""Sure??""" Ta ɗan kalleshi """kika ce you called me? Me kike so?""" Ta ma rasa me zata ce duk miyaun Bakinta a kafe ta rasa dalili. "Wayanta dake hannunta ya zare, Luckily ba password shima dayake bai yi saving number ɗinta ba bashi da shi, abin da ya bashi mamaki ta kirashi sau talatin itama bata yi saving ba, da ɗan hanzari ya kalleta." """Me ya faru?""" "Yadda yayi tambayar sai ya sa hawaye cika mata idanu. ""Dama...Da..ma akan wannan abu da ya faru ne...""" Kallon Bakinta da take motsawa yana rawa a hankali ya cigaba da yi """Idan dai har akwai wani bincike da kake yi sir don Allah a barshi ba sai an yi ba...!""" Tana fahimtar kallon nashi a sadda ya juye zuwa tamkar Harara """Me kike nufi? Ni Almustapha a yi ƙoƙarin tozartani in zuba idanu? Never...""" Hawayen da take rikewa ne suka zubo ya zura musu idanu. """Hibbah!!""" "Wallahi har cikin kanta sai da ta ji ƙiran, ta kasa kallonshi banda hannayenta da take ta wasa da" su. """Look Hibbah... Kalleni nan ki faɗa min menene? Is someone threatening you?"" Cikin Muryar lallashi yayi maganan kaman mai magana da Jasrah." Ta girgiza kai """Haka kawai ne bana so, bana son abinda zai dawo ya ɗagawa iyayena hankali""" "Shiru ya ɗan yi yana kallon waje kan ya waigo ya kalleta ""Ok na ji... Zan daina bincike don ke!""" Lumshe idanu tayi tana sauƙe numfashi a hankali sai ya ce """Amma zan cigaba don kaina da kuma company ɗina, da a wani wurin ya faru kila bai shafeni ba amma cikin company ɗina har cikin office ɗina? No i must fish out the culprit.""" """Sir """ """Save it ko ma menene kike son cewa You can go home company na break sai monday za'a" "dawo aiki""" "Ya cire wayanshi a DND ya ƙira layinshi sai da yayi ringing ya kashe, ya shigar da contact ɗinta favorite kan ya mayar DND don numbobin da suke favorite ne kaɗai za su iya samunshi kuma daga Mum sai Jasrah sai Abbanshi sai ita na ƙarshe." Wayanta ya mayar mata kan kafafunta bai ce komai ba. "Ta kasa cewa komai haka ta fito daga motar don ko kallonta bai sake yi ba bare ya nuna alamun yana sauraronta, gida ta shiga kaman zata saki ihu." "A parlor ta samu Mommy da wasu aunties dinsu Zaitoon ta gaishe su zata wuce mommy tace ""Ya dai har kin dawo? Ko jikin ne?""" Ta girgiza kai """Ashe wai kamfani suna break sai monday za'a koma""" """kai gaskiya yaron nan yana da kirki, wani ma'aikata ne ake ba wa ma'aikata hutu haka? Ya" "kyauta wallahi za ma ki ƙara jin karfin jiki kan Litinin din""" Ita dai ta wuce bata ce komai ba kaman zata saki kuka. "Ko da ta shiga ɗaki sako ta sake gani da wani layi daban ba na jiya ba, shima gargaɗi ne." """Na shiga uku ni Hibbah... Yanzu ya zan yi?""" Tayi magana hannunta ɗaya na bisa kanta. "Ba zata ce ga yadda ta karashe sauran kwanakin ba, tun tana iya bacci har ta daina runtsawa saboda fargaba, a farko message sau ɗaya ake mata amma ya zama kullum yana ƙaruwa" yanzu sau biyar take ganin gargaɗi da jan kunne. "Tana zaune ranar Lahadi a waje hannunta bisa kumatunta aka wangale gate mota ta shigo cikin gidan, tana mamakin waye a taxi sai ga Nasir ya buɗe kofa ya fito." Miƙewa tayi ta nufe shi """Sannu da zuwa Ya Nasir""" "Yayi mata murmushi don shima sun shirya bayan ta karɓi Layin MB MUSTAPHA yana tambayarta jikinta a WhatsApp daga baya ya nemi afuwarta kuma ta yafe komai ya wuce. ""Yauwa Hibbah...""" Kayanshi ya fitar ta tayashi ja Dukda ba murna take ba amma tana ta murmushi saboda surprise ne da ta san mommy karan kanta zata ji daaɗi musamman da yace mata ai ya dawo ne yayi attending auren Yayanshi tayi murnar shiryawarsu wane. Su mommy da baƙin da har sun fara zuwa saboda auren wani sati ne suka shiga mishi maraba da murnar ganinshi ita dai ta koma inda ta taso don bata manta nightmere ɗinta ba. "Bata jima da zama ba aka sake wangale gate sai ta ga motarta, Miƙewa tayi ta tsaya har drivern yayi parking ya fito, shine wanda ya dawo da ita ranar da taje company ta hadu da su, gaisheta yayi ta amsa tana mishi godiya ya miƙa mata key" """Boss ne ya ce a dawor miki da ita"" ""na gode sossai""" Ta karɓa ya mata sallama tana ma ya tsaya ko ruwa ya sha ya ce mata ai boss na jiranshi yanzu. "Motar ta je ta buɗe ta ga handbag ɗinta na ranan da ta bari ta ɗauka ta sake rufewa ta nufi ciki, Washegari mutanen Kano za su iso amma bata wani farin ciki saboda gudun abin da zai iya" "faruwa, har rama ta yi tsabar faɗuwar gaba." Washegari monday da safe ta shirya mommy na ce mata ba zata je tarbar su Momma ba? Tace a'a tana da ayyuka bata karɓi izinin fashi ba yau haka mommy ta barta ta fice duk kuma damuwarta ta ga MB MUSTAPHA. "Yau kamfanin ya ɗauki hada-hada na jama'ar cikinta saboda sun dawo ne da karsashi da kuma karfin su saboda dan hutu da aka samu wanda har yau babu wanda ya san dalili banda MB MUSTAPHAN kuma shi bai huta ba don duk kwanakin ya yi aiki, kai tsaye elevator ta shiga zuwa office nasu an share duk an goge komai banda kamshi babu abin da ke tashi, zama tayi" tana harɗe hannayenta cikin jiran ya zo kawai ta sake ganin wani saƙo """Ba kin yi kunnen uwar shegu da gargaɗina ba? Toh ki jira zuwa gobe da misalin karfe 10 na safe kowani ma'aikaci na kamfanin nan sai ya ganki a mummunan yanayin da sai kin" "gwammaci mutuwa da rayuwa""" "Saƙon kawai take kallo zuciyarta na racing, bata ji Shigowarsu ba shi da driver da ya riƙo mishi jaka sai P.A har sai da P.A ɗin yayi mata magana ta miƙe tsaye da sauri sai idanunta suka shige cikin nashi." A hankali ta sauƙar tana gaishe su fuskarta cike da damuwa. "Ya amsa a kan lips ya wuce office nashi, P.A na biye da shi, zama ta yi hannayenta a goshinta duka biyu har P.A ya fito ya Wuceta zuwa office nashi, kiran landline daga office na MB ya sa ta miƙe ta nufi office ɗin ta ɗan yi knocking ta shiga, tana shiga wayanshi na ƙira..." """Yes...""" Ya amsa call ɗin. """Oh Yeah! Ga ni nan zuwa...""" "Ya faɗa yana Miƙewa tsaye ya nufi waje, har ya ɗan Wuceta ya waigo ""Give me a second pls""" Yana kai nan ya fice. "Zama tayi akan three seater ɗin, tun tana jira har bata san ta zame kwance ba bata san kuma bacci ya sureta ba saboda rashin bacci da bata samu a kwanakin don kwana miƙawa Allah lamuranta take a duk sadda damuwar wannan da bata san wanene ba ya hanata runtsawa." Shi kam ƙaramin meeting yayi da Securities dinshi na companyn ya manta ya tara su tun "sassafe sai da aka kirashi aka tuna mishi, bayan ya gama ya dawo office ɗin ko da ya tura ya shigo kai tsaye idanunshi kanta suka yi." "Hannayenshi ya zube a aljihu ya nufota ya tsaya daga gefen kanta yana kare mata kallo, she's so cute da bai san dalilin da ya sa yake ganinta very Unique and different ba, sai dai ya fahimci ta rame ba kaman lokacin da ta kwanta asibiti ba, kenan akwai abin da ke damunta? Alamunta sun nuna damuwa da gajiya...me ya janyo hakan bayan break aka yi bare ya ce stress na aiki" ne? "Tana sanye ne da farin straight skirt and blouse da yake da wani irin zane kaman jikin zebra amma skyblue ne da fari sai veil da ta saka a kanta sky blue haka fashion ear ring ɗinta da ya fito a yanayin wrapping na gyalen sky blue, takalminta ma da yake heel mai igiya shima sky blue ne ta yi kyau sossai don ya gamsu ya kuma yarda komai nata da tsari da kuma capacity take yi, a hankali ya ɗan taɓa hannun kujerar yana matsawa baya kaɗan" """Miss Mudassir!""" "Firgigit tayi dama baccin sace ta yayi da abubuwa dayawa a ranta ""I'm sorry sir ban san baccin ya ɗaukeni ba""" Ta faɗa tana Miƙewa tsaye. """Sit""" "Yayi mata umarni, sai da ta zauna daga karshen three seater ɗin ya koma one seater dake ɗan" dab da ita ya zauna yana crossing legs ɗin shi. """Hey kalleni! Menene matsalar ne?""" """Sir don Allah ba don ni ba ka daina wannan binciken pleasee""" Ta ƙarasa tana kallonshi idanunta cike tafff da kwallah. """Ki faɗa min dalili""" Ta lashi lips ɗinta da take jinsu dry duk yadda ta so mayar da kukanta ta kasa sai kawai ta sakar mishi kuka sossai. Hankalinshi ba karamin tashi yayi ba amma yayi kokarin maintaining calmness dinshi don "jikinshi har rawa yake, sai da tayi sossai kan ya miƙe ya ɗauko tissue..." """Hibbah!""" Ta ɗago tana jan hanci ya miƙa mata tissuen ta karɓa tana goge fuska. Duƙawa yayi dab ita """Ki cire batun shugaba nake a gareki, ni ɗin musulmi ne ɗan uwanki da zan iya taimakonki cikin kowani irin hali kika shiga... Na tabbatar haka kawai ba za ki ƙi sanin culprit ɗin nan ba sai da dalili hakanan a sanin da na yi miki abin da zai tsinka zuciyarki har ya ɗarsar da tsoro cikin kwayar idanunki ba ƙarami ba ne...""" "Sake ɗauke hawayen da ya tsirto ta yi, ya ɗan lashi lip dinshi na ƙasa yana ɗauke idanu daga" kanta. """I just want to help Hibbah not to cause another problem, ki faɗa min koma menene mu yi solving together""" "Ba wai bata son sanar mishi ba ne, ta ya zata fara sanar da shi akwai nudity ɗinta wurin wani?" Ta ya zata fara mishi wannan bayanin har ya fahimceta? Tana cikin tsaka mai wuya.. Wani irin faɗuwa gabanta yayi ganin ya zari wayanta kuma ta san babu password runtse idanu tayi da ƙarfi shikenan...! "Kai tsaye messages ya shiga layuka daban daban aka yi ta amfani da shi, abubuwan da ya gani sun kaɗashi wani irin kallo yake mata zuciyarshi na bugawa very very fast…" 50 "Kan office desk ɗin shi ya ƙarasa ya zari car key kawai ya fice daga office ɗin, bayanshi ta bi da kallo sai ta mayar da kanta ƙasa, jikinta yayi wani irin sanyi sukuku haka ta fito ta zauna wurin zamanta, tun tana saka tsammanin ganinshi har lokacin tashi yayi bai juyo ba, duk wasu meetings nashi na ranar cancelling suka yi, bata iya zama har bayan an tashi ba ta bar" companyn duk bai dawo ba. "Tana isa gida ta samu su Momma sun zo da Aina'u, Mumtaz sai yaran twineenta su uku 'yan biyu da gambonsu, oyoyo suka yi mata ta tarbesu fuskarta babu yabo babu fallasa" """Oyoyo my babies, kun iso?""" "Abir ya ce ""Yes Maami""" Ta Yi murmushi ta san yaron ya zaci ita ce Maamin nasu amma su Yumna kam Ammi suke ce mata. """Ina Mommana kuka bar min ita? Shi wannan kuma waye?""" Ta faɗa tana nuna wani ɗan yaro da ba zai wuce biyu da watanni ba. """Dole ki tambaya ai Addah Hibbah tunda kin yasar da mu duka ko maganan Kano bakya yi""" "Ta ɗago jin Muryar Aina'u, sai da ta kalli Aina'u sai ta sake kallon yaron ""Ashe Suraj ne? Na ga ya chanza min ne sannunku da zuwa""" "Ta faɗa kadaran-hadaran tana kawar da maganan da Aina'un ta fara, ciki suka nufa suna" "gaisawa da ƙanwartata, tana ta kallon yaran da mamakin girmansu." "Ɗakinta tayi da su inda Aina'u tayi parlorn da su Zaitoon suke nan da wasu 'yan uwa na kusa, ta Barsu nan bayan ta saka musu cocomelon a Ipad ɗinta ta shiga wanka, bayan ta fito ta saka su alwala su Amna dake sun fi wayo tsaf suka yi suka gabatar da Sallar Magrib kan suka fito shi dai Abir baya gane ba mamansu ba ce ya maƙalƙaleta, Hudah bata zo ba tana fama da aiki ga Hajiya Tani babu lafiya ita ke kula da ita so tafiya na barin gari haka ba zata iya barinta ba jikin babu daaɗi sam, bayan ta ɗaukeshi suka fito zuwa ɗakin Mummy don ta gaishe da Momma ta san nan zata same su duk su uku, kaman kuwa ta chanka suna nan zaune suna hiransu na 'yan uwa, sallamar ta ya sa Momma ɗaga ido ta bita da kallo sauran suka amsa, a kan carpet ta" kai zaune """Momma, Aunty Asiya sannunku da hanya""" "Suka amsa Momma kam chan ƙasa ta amsa Hibbah ta miƙa mata gaisuwa shima kaman bata so take amsa Hibbah bata damu ba don ta san tatsuniyar gizo dai bata wuce na koƙi, ta gaishe" da Aunty Asiya ta amsa kuwa da fara'a. """Aunty ina kika bar Asma'u baki zo mana da ita ba?""" Aunty Asiya tace """Wannan karo kam ban taho da ita ba exams suke ta yi ma"" ""Ya batun kudin aure za'a jinkirta har ki koma kuwa?""" "Mommy ke tambayar saboda zancen Asma'u da aka kawo ya tuna mata cewa gab take itama da aurar da diya tunda zancen kuɗin aure ake matsalar dai da aka samu lokacin da suke so su zo ɗin yayi ɗaya da auren Abdul shine mommyn ke tambaya, Hibbah ta ɗan yi murmushi ""Masha Allah ashe Asma'u ce next?""" """Dole ki tambaya ai Hibbah tunda kin fi gane cigaba da goga kafaɗa da iyaye, ko kunya bakya ji yanzu fisabilillahi?""" Aunty Asiya tace """Haba Adda Fatima! Me ya kawo wannan zance daga batun auren ƙanwarta? Allah ne fa bai" "kawo ba idan lokacin auren Hibbah yayi ai ko bata so sai ta yi""" """Ku daina kare ta dai Asiya, ba kuma Allah ne bai kawo ba bata yi niyya ba ne tunda ita ce bata" "sakarwa samarin fuska, kalli ki ga fa duk waennan yaran ƙannenta ne""" "Momma ta faɗa cikin jin haushin Hibbahn ta tabbatar da gangan ta ƙi batun aure, murmushi mai" nauyi kawai ta ɗan yi. """Hibbah tashi ki je abin ki""" "Mommy ta faɗa alamu faɗa take son yi wa momman kuma bata son yi gaban Jikoki da yara. Miƙewa Hibbah ta yi ta fice da yaran fuskarta ba yabo ba fallasa, abin da ya fi damunta ma wani mataki take kai da MB MUSTAPHA?" Ko da ta je parlorn da su Zaitoon suke ta samu suna ta hira Aina'u na nan tana zaune tana "chats, zama ta yi suka shiga hira yaran ma suka fara wasanninsu." """Addah Hibbah!!""" Aina'u ta faɗa karo na uku firgigit ta yi """Hibbah lafiya ana hira kina tafiya tunani haka? Sau uku fa ana ƙira baki ji""" Zaitoon ta faɗa da damuwa Numfashi Hibbah ta ɗan sauƙe """Lafiya ƙalau Yaya Zaitoon, kawai wani abin ne na aiki ya ɗauken hankali... Me kuke cewa?""" "Nan suka shiga maimaita mata hirar tun tana getting along ta sake zurmawa tunani ƙarshe dai haka ta bar su ta koma ɗaki ɗauke da Abir, tsaf ta shirya su su huɗu Aina'u na zaune tana kallonta har ta kwantar da su kan ta zo kan gadon ta kwanta" """Aina'u yi sauri ki gama abin da kike pls ki kashe mana wutan nan bacci ne fal idanuna gashi" "gobe ina da aiki""." """Baki ɗauki hutu ba ne?""" """Sai ranar mother's eve zan dauki hutun thursday da kuma friday da za'a yi dinner""" Miƙewa Aina'u tayi ta saka kayan baccinta kan ta kashe wutan ta zo ta kwanta """kin kuwa san batun zuwan Usaib wurin su Daddy?""" Bata san ta miƙe zaune ba """Ya je yayi musu me?""" Ta faɗa tana jin wani irin takaici da bakin ciki """ya je ne batun neman aurenki amma Daddy ya ƙi gaskiya ya ce mishi ya zo ku shirya ki tura shi" "da kanki""" Wani wawan ajiyar zuciya ta sauƙe """Duk wani ɗan air ya biyo bayan Usaib, me yake nufi? Wato ya zo nan na koreshi shine bari ya bi ta bayan fage to an ce mishi dole za'a yi min na aureshi ne?""" """Gab ake da miki dolen ai Adda Hibbah, don da ta Momma ne da an karɓeshi ita hankalinta ya" "kasa kwanciya da zaman da kike yi anan kike aiki ko batun auren bakya yi""" """Hmmm me a cikin auren Aina'u banda matsaltsalu? Ni a yanzu aure baya lissafina saboda duk mazan halayensu ɗaya kowa dan iskan kanshi ne""" Dariya Aina'u tayi da maganan na Hibbah """ba shi ke hana dacewa ba, ke dai ki yi Adu'a kuma ki fawallawa Allah sai ki ga kin samu mijin marainiya wanda zai mantar da ke duka wahalhalunki na baya ya lasa miki zumar soyayya da babu algus tuni zaki manta da wani batun tsanar aure ko maza""" Tsaki Hibbah ta ja tana juyawa. """Addah Hibbah wai kin san Daddy zai sake aure?"" ""Aure fa??""" Ta faɗa da tsantsar mamaki """Aure dai Ummin su Najeeb ce zata dawo to dai an samu an shawo kanta su Hajiya karima da Kamila ne ke ta rikici akan ba zasu yarda ba ummi da Momma sun haɗe musu kai tun kan ayi" "maganar dawo da ita ina ga an dawo da ita""" """hali dai zanen dutse Allah ya shiryasu, na ji daaɗi kwarai da wannan zance, Allah ya tabbatar musu da alkhairi, sauƙin ta ma su Amal duk sun dawo daga rakiyar iyayen nasu tunda sa'i da lokaci har waya muke da su duka har su Baby""" """Kin san mata da kishi bare suna ganin babu mai ɗa namiji cikinsu""" Hira suka cigaba da yi akan 'yan gidan nasu daga karshe bacci ya sure su. "Da safe bayan ta shirya Abir ya riƙeta kam ya hanata fita, a dole ta shirya shi cikin kananun" "kaya ta ɗaukeshi suka fito, a babban parlor ta samu Momma da Aunty Asiya ""Momma Good morning...! Ina kwana Aunty?""" """Lafiya ƙalau Hibbah shi wannan mummunan ya ƙi bariki ki huta ko?""" Inji faɗar Aunty Asiya """Kai Aunty yanzu fine boy nawan ne mummuna kina ganinshi wanke hannu ki taɓa?"" ""Uhummm faɗawa makaho""" Dariya Hibbah tayi Aina'u tace """Anya ba kishi a wannan lamarin? Ko don baya yi da ke ne sai da Mommy?"" Wasan kaka take mishi suke kare shi." """Ni zan wuce wurin aiki Momma sai na dawo"" ""Da shi zaki tafi?""" Cewar Momma """Toh ya ƙi zama bana so yayi ta kukan nan""" """Allah ya tsare"" ""Ameen""" Babban kitchen tayi ta kuwa samu Mommy bata barta ta tafi ba sai da lunchbox saboda ta san "bata karya ba, ko da ta fito mota kawai ta ɗauka suka nufi companyn." "Sai da ta isa take jin faɗuwar gaba da fargaba, her worst thought shine yadda MB MUSTAPHA zai dauketa a yanzu, idan hakan ya bijiro mata sai ta ji hawaye marar dalili na cika mata idanu, bayan ta ajiye Abir a chan gefe inda take hango shi ta kunna mishi cocomelon a Ipad ya kuwa natsu yana kallo ta je ta zauna tana kallon time, duk inda yake ta tabbatar gab yake da shigowa dunkule hannayenta da suke zufa tayi wani zuciyar na tambayarta" Me yasa kika damu kanki kike ɗagawa kan ki hankali akan abin da ya riga ya faru a baya? Meyasa kike jin tashin hankali don kawai zai san abin da dayawa suka sani? """There is nothing there Allah ya riga ya ga zuciyata""" "Ta faɗa a fili daidai lokacin da ta ji motsin kofar office ɗin gabanta ya wani irin faɗi har tana Miƙewa tsaye ilai kuwa shi ne ya ratso fuskar shi ba kaman koyaushe a murtuke hannunshi ɗaya a aljihu ɗaya kuma rike da hannun Jasrah dake sanye cikin berbie dress tayi kyau ainun don gadonshi tayi sai nata ya zama na daban, shi kam sanye yake da suite milk colour yayi mishi kyau sossai don kibkib jikinshi kaman a jikinshi aka ƙirkira ko kuma don shi aka yi musamman, tun kan ya iso ma kamshinshi ya cika mata hanci hakan kuma ya ƙara mata faɗuwar gaban da take ciki, bata motsa ba har ya iso dab table nata zai wuce tace cikin rawar" murya.. """Goo...d Mor...ning Sir!""" "Kai ya ɗan gyaɗa ba tare da ya kalleta ba ya cire wayanta dake aljihunshi ya ajiye kan table ɗin yayi gaba abin shi, sai da ta ga ya rufe kofa kan ta kalli wayan sai ta koma dirshan ta zauna tana dafe Goshi irin wannan uneasiness ɗin na fargaba da tsoro haɗe da rashin gaskiya a tare na sake rufeta, bai fa ce mata komai ba! Ko shima zai yi judging ɗinta kaman yadda aka yi mata a baya? Hawayenta ne ya ziraro tana raya to tunda har 'yan biyuna tayi judging ɗina waye ba" zai yi ba? """Maami! Maami!!"" Ta ji Abir na kiranta ""Na'am Abir""" "Ta amsa tana kawar da yanayin ta miƙe ta kamo shi yace zai sha ruwa taje ta bashi, ta ɓare" mishi snacks da ta riƙo mishi ta ɗora shi akan desk ɗin ta janyo wayanta bata buɗe ba ta ajiye kawai ta mayar da hankali kan aikin companyn. "Schedules ɗin shi na ranar bai tsaya ta faɗa mishi ba sai dai ta ganshi ya fita ya wuce ya sake dawowa ya shiga, duk meetings da sauran abinda zai duba yayi ba tare da ya tanka ta ba, ko da Jasrah ta fito ta ga Abir sai hankalinta ya koma kanshi, tun tana ɗari ɗari da mishi wasa har Hibbah ta haɗa su kan wani mat da ta shimfida musu, Jasrah ta zube kayan wasanta suka shiga yi a tare da Abir ɗin hakan ya bata damar dulmiya cikin tunanin da ya kasa barinta duk yadda tayi don yakice shi, azahar da ta kula yayi ne ta miƙe taje tayi alwala, sossai tayi ta zuba ruwa a fuskarta ko zata samu sauƙin zafin zuciyar da take ji bata bari ba sai da ta ga idanunta sun fara chanza launi, Abaya ne ta saka double chiffon purple, ƙasan Camisole ne baƙi da in tayi motsi ya kan bayyana, gyalen Abayar kawai ta ɗora akan tulin gashinta da ta kama shi da" "ribbon guda, hannayen rigar ma a nannaɗe haka ta fito wa idanunsu na sarƙewa cikin na juna." "Wuyanta dake waje ya ɗan kalla ya mayar da idanun ga fuskarta zuwa gaban goshinta da gashinta suka mammane saboda ruwa da suka sha, wani irin tururine da bai san na menene ba ya bijiro mishi tuni ya mamaye mishi zuciya raɗaɗin har kaman ba zai ɗauka ba, murmushi da" yake yi da su Jasrah tuni ya kau. Ba tare da ya sake magana ba ya miƙe ya fice daga office ɗin. "A sanyaye ta ƙaraso ta shimfida sallaya ta saka hijab tayi sallah bayan ta idar ta ajiye musu lunch tana feeding nasu su biyu ita kam ba wani ci take ba, kuma bata cire hijabin da tayi Sallar ba ta ma yi mamakin yadda Jasrah ta sake da ita yau ɗaya saboda Abir, har murmushi take ta" yi da 'yan tsalle tsalle na yara... Suna nan suna ci ya shigo ya wuce su bai ce musu komai ba ya koma office. "Hibbah bata san da gaske yake ba sai da aka ci wednesday ma sannu bai haɗa su ba, idan abin da ya kama a tambayeta ne sai dai P.A ya zo ya sameta amma shi kam boss ko kallonta sai ya zama a tsautsayi yake yi, kafin ta tafi ranar wednesday ta ba da letter akan ba zata zo thursday and friday ba, P.A ta ba wa kuma yana bayan ta tafi ya bashi bayan ya karanta ya" ajiye kawai kan desk. "Washegari tun safe ta tashi saboda mai lalle da ta zo zata yi musu a gida, bata son jan na gargajiya sai aka yi mata zanen khaleeji yayi kyau ainun a hannunta da kafafunta, bayan ta yi wanka ta karya almost 11 suka wuce makeup ita da Zaitoon ba su suka dawo ba sai da aka kira su akan za'a tafi hall na mother's eve wuraren 2, a hanyar su ta komawa da yake ita ke driving suna shan waƙarsu na Aure by morell Dukda tana maming fuskarta da fara'a idan ta tuna da shi sai ta ji wani abu a ƙasan ranta, gab da za su isa wurin wayanta ya shiga ruri ta janyo ta kalla" sai da gabanta ya ɗan faɗi ta basar. "Ko da bata yi saving layin ba ta san mai shi, MB MUSTAPHA ne! Me yasa yake kiranta? Ta tambayi kanta da kyar ta yi gaining courage ta ɗaga..." """Good Afternoon boss""" Ta faɗa in her cracky voice """Afternoon, on my desk akwai confidential file na Autralian automobile company I need them urgently.""" Cikin salon ba da umurni yayi maganan "Ta ɗan yi sakaka yana nufin ta kai mishi inda yake kenan? ""Na ɗauki hutu Yau ai ba na office""" She whispered. """Kin ba ni saƙon hakan?""" Ya tambaya not minding yanayin pleading voice ɗinta. "Ƙiris take jira ta fara hawaye cikin kankan da murya duk na son kar ya sakata dole zuwa tace ""Sir na fa ba P """ "She wanted to argue to insist, but his fierce voice stopped her…" """Ni kike yi wa aiki ko P.A ɗina?"" Ya tambaya da alamun jin haushi Bai jira amsar ta ba yace" """Duk inda kike make sure kin kawo min takardun nan in less than hour """ Yana kai nan ya katse kittt. "Wayan ta zamar fuskarta kaman zata kurma ihu ta kalli Zaitoon ""MB MUSTAPHA ne?""" Kai ta gyaɗa """Wai fa in je office in ɗauki takardu in kai masa kuma fa na ɗauki excuse"" Ta faɗa kaman zata yi kuka." Dariya Zaitoon ta fara """Amma kema kin nemawa kanki ne Meyasa baki tambayeshi kai tsaye ba kika ba wa wani P.A? Ai da gaskiyarshi shi kike yiwa aiki ko P.A?""" "Shiru tayi bata so ta yi kuka ta ɓata makeup ɗinta da babu abinda zai hanata fashewa da kuka, ina ko magana ba mata yake ba kawai don ya katse mata jin daaɗi zai wani aiketa ranar da ta" ɗauki excuse. "Haka taje ta sauƙe Zaitoon, tana gani ana ta zuwa ta juya kan motar ta fice daga wurin cikin" hanzari. 51 "Ko da ta je office ana gab da tashi duk wanda ta haɗu da shi sai ya bada compliment sai dai ta ji ana cewa 'You Look good Miss Mudassir' ko 'Masha Allah' sai dai tayi godiya ta wuce har ta isa office nata bata ko tsaya ba saboda sauri ta wuce zuwa nashi akan desk ɗin kuwa ta samu folder ɗin, bata tsaya ta buɗe ba ta ɗauka ta fito tana ƙoƙarin kiran layinshi ta ji inda zata kai sai" ta ga live location da ya tura mata. """Banana Island??""" "Ta faɗa kaman zata rusa ihu, fuskarta a kwaɓe ita wlh ko zuwa wurin ma bata taɓa yi ba, tayi dana sanin rashin kai mishi request na fashin nan ya fi dubu yanzu ana chan ana hidima ita tana nan, motarta ta fusga da ƙarfi ta sakar masa speed, sai da ta kusa hour a hanya kan ta isa Island ɗin daga ganinshi ma ba natural Island bane na ƙirƙira ne amma tsarin ba karamin kyau da daukar hankali yake da shi ba kaman ba ƙasar nan ba, shimfidaddun tituna da ƙawatattun gidaje sai ruwan dake dukan gefen titin daga ƙasa kana kallon wave ɗin zuwa yalwataccen" ruwan da ganin ƙarshenshi sai mahallici sun ƙara kawata tsaruwar arear. "Ga green plants da suka yiwa wurin kawanya a tsaftace irin ever green nan dake ba da kamshi da ni'ima na Musamman, bata tsaya mayar da hankali kan tsaruwar Island ɗin ba ta nufi titin da Google map ɗin ke nuna mata har ta isa kofar gidan tayi Horn, seconds biyu bata yi ba kofar gate ɗin ya buɗe da kanshi ta kutsa kai ciki, Security ɗaya ta gani zaune akan wani plastic chair, akwai motoci uku a harabar gidan wanda basa cikin wurin parking hakan na nuna alamun kila yana tare da mutane ne, taso wa yayi ya gaisheta ta amsa tana ɗan bin tsararren gida da kallo," komai a ciki screaming luxury yake. """Please can you give this to MB MUSTAPHA?""" Ya ɗan zaro idanu """Ma he knows you are coming he even open this door himself, just follow that walkway to the backyard you will find him there""" Ya faɗa yana girgiza kai don baya wannan karambanin duk wanda zai shigowa MB MUSTAPHA gida to tabbas da saninshi idan shi bai barka a waje ya zo ya karbi sakon ba then you must go in urself ka bashi. Fuskarta babu walwala she's pouting a zuciyarta kuma mita take tayi ta nufi ciki. "Yana zaune daga saman balcony kan wani Italian chair na hutawa gabanshi table ɗin da System ɗin shi a kai yana duba wani aiki a gefe chill energy drink ne cikin wani cup yana sipping, simple casual ne jiki shi riga da wando masu faɗi, rigar na da guntun hannu so ya bayyana murdaddun damatsanshi waje, hannunshi ɗaure da silver watch akwai kwantattun gashi masu taushi saman hannun nashi da ya basu wani kyau na musamman, daga sama yake zaunen so inda zata bi ta zo ta inda yake dole ta gabanshi zata wuce, shi zai iya kallonta amma" ita ba lallai ta kalleshi ba. "Ya san ta shigo gidan amma a yanzu takun sawayenta su suka ja hankalinshi zuwa kallon inda take, his eyes lifted... Idanunshi suka tsaya chak a kanta na ɗan lokaci fiye da yadda ya kamata," daga kan kafafunta da sautin ke sauƙa har cikin zuciyarshi ya fara kallo... "Cone heels ne maƙale a cikin fararen kafafunta masu bayyana jan lallen da ya kara ƙawata adon burgundy heels ɗin suna da igiya da ya ɗan zagaye ankle ɗinta jiki shi akwai wasu stones masu kyau da walwali, sama yayi da idanunshi zuwa jikin ɗinkin da kaman a jikinta aka ɗinka fitted gown ne colorn Black ne and burgundy, komai nata chip chip so breathtaking, a wuyanta ta makala burgundy veil shima don kar Momma tayi faɗa ne amma da ba zata saka ba kuma she will feel uncomfortable yawo cikin mutane haka, sarka da ɗankunne duk gold ne, ɗaurin ta" chip chip haka makeup ɗin was light amma ba karamin kyau yayi mata ba. "She continue moving with that same quite composure, files in hand, kowani motsi tana yi ne a hankali amma yana ɗaukar hankali ba tare da ta kula ba, patterns na lallen hannunta resting gently against her skin like art that wasn't trying to be seen yet demanded to be admired..." A hankali ya sauƙe numfashin da bai ma san ya riƙe ba ganin dab take da iso shi. """Focus Almustapha""" Yayi whispering amma tuni ya san zuciyarshi ta gama betraying ɗinshi. """Assalamu Alaikum warahmatullah""" She said calmly amma tana ɗan pouting alamun ranta a ɓace yake. Yayi kaman ba shi ya ƙare mata kallo from head to toe yanzu ba. """Wa'alaikissalam""" "Ya amsa ta ajiye files ɗin a gefenshi ""Ga su nan""" Tana kai nan ta juya zata tafi. """Hey!""" Ya faɗa sai a lokaci ya cire idanunshi ya sauƙar tarr bisa fuskarta. """Na sallameki?""" Ya tambaya yana Miƙewa tsaye hannunshi ɗaya riƙe da system ɗinshi ɗayan kuma drink ɗinshi. """Follow me with the file""" "Zara tayi ta bi bayanshi yadda ya umurta bata ce komai ba, cikin kofar wurin suka shiga zuwa wani walkway mai tsawo dake fidda kamshi, tafiya mai tsawo suka ɗan yi tana biye da shi a baya har ya buɗe wani kofa ya shiga, ta bi bayanshi ga mamakin ta wasu turawa ne zaune a ɗakin da ya fi kama da na meeting wato shi har halls na meeting yake da shi a gida ta ayyana, gabansu drinks ne da snacks kusan su shidda ne a wurin sai P.A tana bayyanuwa ido ya koma" kanta. "Me ya sa zai kawota meeting room da irin wannan dressing? This is unprofessional, yanzu kam abu kaɗan za'a ce ta fashe ko murmushi bata yi, da alama shi sun riga sun gana da shi dole ita" ta gaishe su. """You demanded my secretary and here she is, so za mu iya cigaba da meeting?""" Dama suna da labarin kwazonta da sanin makaman aiki sannan kowa ya san turawa da ka'ida sun ki yarda su yi meeting ɗin daga shi sai su da P.A sun ce dole akwai secretary saboda sa hannun ma nashi da nata ne. "Zama tayi ya cigaba da presenting ɗin meeting ɗin ko tak bata ce ba don hankalinta ma na kan ana chan 'yan uwa ana ta bidiri tana nan zaune kuma suna ɓata mata lokaci, bayan sun gama suka saka hannu suka sauƙo gabaɗaya don musu rakiya bayan sun fice daga gidan ta ɗan kalli" ɓangaren shi """Sai anjima""" "Ta faɗa trying Hard not to be emotional amma ta makaro don muryarta har rawa yake, ta juya kawai ta nufi motarta." "Shawarar zuciyarshi ya bi ya nufi inda take, ta shiga tana ƙoƙarin rufewa ya riƙe murfin motar" """Miss Mudassir!""" Ta ɗago bata ce komai ba amma idanunta ya saka ya ɗan lumshe nashi sai yayi baya ta ja murfin ta rufe tayi reverse ta fice daga gidan. "Driver dinshi ya kalla yace ya ɗauko mota, zasu mayar da P.A don bai zo da mota ba kuma" akwai inda yake son zuwa ciki har da gidansu. "Motar ya ɗauko ya shiga baya, P.a ya zauna gaba drivern ya ja motar suka bar gidan, irin ruwan legos ɗin nan mai zuwa babu notice ba hadari ba komai ya fara zuba, lumshe ido yayi yana jin ba daaɗi ƙasan ranshi ya hanata walwalwarta kuma alhali ya ga saƙonta Dukda ba shi ta" kawowa ba. """Ha! Wanchan ba Miss Mudassir Madaki ba?""" "P.A ya faɗa, a hankali ya buɗe idanunshi ya kai gefen hanyar itace tsaye gefen titi dab bayan sun fito Banana Island kaɗan, kuma ruwan taɓata yake, zuciyarshi ta ɗan buga parking driver ɗin yayi tun bai ce komai ba." P.A ne ya sauƙa ya je ya sameta """Lafiya Miss Mudassir?""" Ta ɗan yi jimm kan ta ce """I bumped into something fuel line na ya fashe""" "Ta amsa tamkar yadda take kwararriyar mechanic, ya ɗan yi jimm kan yace" """Give me the key zan kira a zo a gyara ki tafi Boss ya sauƙe ki""" """Na gode sossai amma zan hau taxi kawai""" "Ta faɗa bayan ta bashi key ɗin, ba lema a motar nata Allah ya sa ma ruwan ba da karfi yake zuba ba amma duk da haka yana taɓa fuskarta kuma yana bata mata kwalliya, jakanta kawai ta ɗauka da wayanta a motar ta koma gefe chan ta tsaya." "Tana gani P.A ya nufi motar MB MUSTAPHA da alama bayani ya mishi, chan ya sake dawowa wurinta don babu wani abin hawa ma dake gilmawa a wurin yace" """Miss Mudassir Boss ya ce ki je ki shiga ya kaiki please""" """Ni ba zan je ya kaini ba dama hakan yake so ya faru kuma ya faru ai sai ya kyaleni ko nan ma kamfaninshi ne?""" Shi dai P.A ya gaji da zuwa da dawowa ya kira MB ya gaya mishi bata san me yace ba ta dai ga P.A ya wuce zuwa motarta ya shiga ya zauna. "Seconds uku ba'a ƙara ba ta ga ya buɗe mota ya sanyo kafafunshi waje, ɗauke kai ta yi hannunshi riƙe da lema ya nufeta ɗaya hannun cikin aljihu yana taku a natse idanunshi zube a kanta a ranshi yana mamakin wai fushi tayi da gasken gaske." "Jin ruwan ya tsaya chak da taɓata ta san ya iso gabanta ga kamshinshi da ya gauraya da nata," iska ke busowa yana ratsa su gabaɗaya. """Hibbah!""" Yana wuya taji ya kirata da First name ɗinta kuma ya iya ƙiran sunan don ji take har ƙasan ranta ba tare da ta san dalili ba. Ta kasa ignoring ta ɗago ta kalleshi suka haɗa idanu. """Mu je in sauƙe ki""" Ya faɗa calmly """Ku je kawai na gode""" Ta faɗa tana yunkurin tafiya gaba yace """Waitt...kalli hanyar nan ko kwana zaki yi anan ba za ki samu taxi ba""" """Sir ku tafi kawai, ai yanzu lokacin tashi aiki ya shiga so Thank you i can manage""" "He looked down, a faint, almost imperceptible smile tugging at the corner of his lips. Fushi ta yi he looked back at her zai yi magana ta juya cikin sassarfa zata tafi." MB MUSTAPHA exhaled and this time around catching her hand before she retreat ganin da "gaske ruwan da ya ƙara karfi take shirin sake shiga, ta juyo ta kalli hannun ta kalleshi" """Leave me alone! Kana ganin laifina na rashin neman izinin fashin aiki a wurinka ka manta baka yi min magana? Ka manta you spent 2days looking at me kaman kashi? I knew what you found" amma you have No right to judge me ba tare da ka san me nake going through ba! I "thought...mahaukacin kwakwalwana ya bani kila kai daban ne za ka fahimceni but I'm mistaken, instead ka bar ni in ji da abinda nake ji kallon da kake min ya zama wani punishment daban a wurina, you made me hate myself for this two good days... You went too far again na taking advantage ɗina ranar da ya kamata na samu natsuwar zuciya you took it away Look at me now...! Ka yi farin ciki?""" "Ta ƙarasa hawaye na zuba mata, dama abin na cinta a rai kuma ta samu daman furzarwa." Idanunshi take ji har cikin ƙashinta bai sake hannunta da take ta ƙoƙarin kwacewa ba yace a hankali """I'm sorry... I'm really sorry if That's what i made you feel amma God knows ko ɗaya abin da kika lissafi ban yi su da gayya ko don in bakanta miki ba... Whoever work with me ya san wani iri ne ni i despise ganin employee ɗina cikin ƙunci bare ya zama ni na saka su da gangan. I have something important and urgently to disscuss with you shiyasa na ƙiraki i didn't really know cewa biki kuke ya hanaki zuwa.. I'm sorry once again""" "Kaman ruwa ne aka kwarara mata daga kai har kafafun haka jikinta yayi sanyi, me ta yi? Bakinta da baya iya shiru idan an mata abu shi ya kaita ga gayawa boss irin waenchan" maganganu ashe ba abin da ke zuciyarshi ba kenan? "Kunya ne ya rufeta, ya sakar mata hannu a hankali." """Mu je in sauƙe ki wurin bikin we talk on monday""" "Ya faɗa looking at her, kukanta ne ya taɓa mishi rai because ya rasa Meyasa bayan kukan" Jasrah kukanta ya zama na biyu da kan sauka mishi a zuciya wane ƙunan wuta. Bata yi musu ba a wannan karo ta bishi zuwa mota da kanshi ya buɗe mata ta shiga ta zauna ya zagaya ya shiga ɗaya ɓangaren. Tafiyar mintuna talatin suka yi ta ga driver ɗin ya shiga wani building bata yi motsi ba kuma bata ɗago ba har wata mace ta zo ta ɗan yi knocking glass ɗin ya sauƙe """Please retouch her makeup""" "Matar ta amsa cikin ladabi ta zagaya ta buɗe mata kofa, bata yi musu ba ta fice sai da suka shiga ta ga ashe babban wurin gyara ne na mata babu abin da basa yi, cikin mintuna da basu kai ashirin ba ta gyara mata kwalliyarta da hawaye da ruwa suka ɓata tuni ta fito fess ta rakota mota tana yi mishi godiya don ta riga ta ga kudinta, ita ce take yiwa Anam komai na gyara a" baya sanadin hakan ya santa sossai. "Ita ta faɗi wurin da ake eve ɗin sai ga su a kofar wurin fita driver yayi zata fita yace ""Hibbah!""" Ta ɗan waigo tana sake jin yanayin da take ji a duk sadda ya kira sunanta """Kar ki sake tunanin zan yi judging naki blindly please and I'am sorry one again""" Tana wasa da fingers ɗinta shima sai ya bi fingers ɗin ya zubawa idanu """Ka yi haƙuri for how i reacted, I...I...""" Maganan rawa yake """Is ok ya riga ya wuce and it's my fault after all""" "Jakanta ya ɗauka dake gefenta ya buɗe wani wuri daga inda yake zaune bundles na 1k guda uku ya saka mata ciki, za tayi magana ya yi saurin ɗora hannu a labbanshi" """Shhhh a sha biki lafiya""" "Ta ɗan yi murmushi marar faɗi ""Thank you Sir""" Ya gyaɗa kai ta fice daga motar tayi ciki. Sai da ya daina ganinta kan ya sauƙe idanu yana kallon hannunshi sai ya lumshe su yana jin tsikar jikinshi na wani irin tashi har driver ya ja suka nufi inda asali ya fito don zuwa idanunshi a lumshe… 52 """Hibbah!!""" Ta ɗan yi firgigit tana kallon Nasir da ke kiran sunanta. """Lafiya kike kuwa? Ko akwai wani abin da ke damunki ne tun da kika shigo wurin nan babu wani walwala a fuskarki""" "Ta ɗan yi murmushi kaɗan, duk tunaninta tafiya yake ga menene MB MUSTAPHA dama yake son sanar mata? Me yasa yake son Magana da ita kuma ya ce maganan ba na waya bane sai an natsu? She's just curious tsananta tunanin kuma yana tsananta mata son jin labarin har tana" ji kaman ta ƙira shi ma ta fasa zama wurin bikin ta je su tattauna. """Babu komai Ya Nasir""" Ta faɗa fuskarta na sake faint smile da bai wani kai ciki ba. """Kin dai san baki da lafiya please ki kiyaye, idan ma abin da ya kamata mu sani ne sai ki faɗa a magance shi da wuri""" Ta gyaɗa kai tana kai idanunta kan Zaitoon da su Aina'u da ke ta rawa a kan stage tare da amarya Jadwa sai fara'arsu suke. Ta ɗan sauƙe numfashi sai yaushe zata tsinci kanta cikin genuine farin ciki irin nasu dake fita daga zuciya ba kawai akan fuska ba? "Har aka tashi taron bata miƙe daga inda ta zauna ba sai dai tana kallon komai da murmushi su Momma sun taka rawar gani an ci kuma an sha komai irin na gidan arziki da mutunci, tana fitowa harabar kira na shiga wayanta ko da ta duba P.A ne ta ɗaga yace ta same shi a parking lot zai bata keyn motarta, kai tsaye chan ta yi da kyar ma ta gano shi don wurin fall yake da" mutane da motoci. """Ya aka yi ka san ina nan?""" Tayi tambayar da murmushi """Boss shi ya ba ni address ɗin ya matsamin akan lallai lallai a gyara a yi full tank kan ki tashi tafiya""" "Ta ɗan kawar da idanunta har lokacin fuskarta a sake tace ""Na gode, shima ka isar mishi da godiya ta""" Tayi maganan tana karɓar keyn ya juya ya fice yana ce mata sai Monday. "Ta saka a ranta kawai MB MUSTAPHA na da kirki kuma mutumin kirki ne bayan nan bata kawo komai ba, su Aina'u ta jira suka fito da yaran ta tattara su suka yi gida duk a gajiye take ga" ciwon kai saboda hayaniya. "MB ne zaune cikin owners corner ranshi tafasa yake, amma yana ƙoƙarin controlling shi kaɗai ya san me yake ji, ya yi tsaki idan bai kai ɗari ba zai yi tamanin daga inda suka fito kan driver ya" shigar da motar harabar gidansu yayi parking. "Sai da ya ɗan ɓata lokaci kan ya sauƙa ya nufi ciki, ba don yana son ganin Jasrah ba da babu abin da zai kawo shi gidan a yanzu, yana kutsa kai cikin parlorn ita ya fara hanga kwance kan tiles tana kuka a dunkule wuri guda wane kifin gwangwani, da mugun hanzari yayi kanta yana ɗagota" """Jasrah! Jasrah??""" "Ya ƙira sunanta muryarshi a shake, da sauri ta rungumeshi tana sake sakin kuka jikinta na" kakkarwa. """Me ya faru? Me ya sameki?""" "Yayi tambayar yana ɗago fuskarta a cikin hannunshi, za tayi mishi magana irin ta kurame Mum ta fito..." """Ha! Jasrah ba dai faɗo wa kika yi ba?""" Tayi maganan tana dafa kujera don samu ta zauna fuskarta da idanunta jajazir kaman ba Mum da ya sani ba. """Faɗuwa Mum?""" """Bacci tayi sai na ce a barta don in an ɗaga ta zata iya farkawa ta isheni da rigima ka ga nima ba cikakken lafiya ce da ni ba, to ina ga cikin baccin ne ta faɗo kaman har fitsari ta yi ma ko? Uwani!! Uwaniiii""" "Ta ƙarasa tana kwala kiran mai aikinta, da sauri ta fito bata bashi ma wani room na magana ba" idanunta kuma kirrr a kan jasran tace mata """kamata ki je ki yi mata wanka ki chanza mata kaya sai ki zo ki gyara wurin nan""" Kamata tayi amma hannunta ɗaya riƙe gam da na rigar babanta ta ƙi sakewa sai kuma hawaye take yi. Ya hadiye wani abu mai ɗaci kan ya shafa kanta yace tana kallon bakinshi don tana ji sarai magana ne bata yi """Ina nan ina jiranki ba zan tafi ba kin ji? I promise""" "Kai ta gyaɗa ta sake shi suka tafi, a kan kujera ya zauna yana ɗan dafe goshinshi abubuwa dayawa basa feeling right a wurinshi sai dai ya yarda da Mum ɗari bisa ɗari." """Mustapha babu labarin ɗan uwanka ko?"" Ya ɗago ya kalleta." """Mum ki daina damun kanki da batun Mahir, shi fa ba yaro bane""" Ta jefa mishi wani irin kallo a fakaici a ranta tana raya ta ya ba zan damu da ɗana ba idan ban damu da shi ba uban wa zan damu da? """Abin da Babanku ma ya faɗa kenan amma fa Mahir ka san ba cikakken hankali ke gareshi ba, sannan bai taɓa ɗaukan kwanaki bai leƙo gidan nan ba a jikina nake jin kaman shirun nan na" "kwana biyu ba lafiya ba.""" """Khairan in shaa Allah, ki cigaba da kula da lafiyarki Mum duk kin zama wani iri""" """Ta ya hankalina zai kwanta har in samu lafiya? Mahir kullum a rigima yake da kai baya ji Dukda na san kana nan kana haƙuri da shi, mahaifinku kullum ya buɗe baki baya faɗan alkhairi kanka babu ranar da ba za mu yi rigima ba saboda yadda abubuwanshi ke ta'azzara, kai kuma kana nan ka ƙi aure sai kawo mishi zancen kana kule kule a waje ake ka gayamin ina abu ɗaya da" "zai kwantar min da hankali anan?""" "Daga fuskarshi ta karanci maganar da tayi akan mahaifinshi ya taɓa shi, murmushi ta saki a fakaice bai yi magana ba." """Kar ka ɗaga hankalinka fa komai mai wucewa ne, a kawo maka abinci?""" "Ya girgiza kai ""No, am Ok""" "Ya faɗa kaman an mishi dole, bai motsa ba sai da Jasrah ta fito ya miƙe" """Zan tafi da ita Mum, Allah ya kara miki lafiya""" """Toh shikenan Na gode My son, Allah yayi albarka""" Bai amsa ba ya fice hannunshi cikin na Jasrah da yanayinta ke nuna jin daaɗin barin gidan. "Washegari friday Hibbah bata yi niyyar tashi da wuri ba amma kasancewar yau ne ɗaurin auren gidan ya cika da hayaniya, Miƙewa tayi ta watsa ruwa ta sanya wani aplique lace pink da purple ɗinkin doguwar riga da ya karɓeta wane, mayafi pink ta saka ta yi ɗaurinta, fuskarta babu komai a kai ta fito ta nufi kitchen duk abin da ma aka yi bata ji zata iya ci ba, indomie ta dafa ta fito da" shi riƙe a plate sai ta ji an kama gefen riganta ko da ta juya Abir ne da Yumna. """Heyyyy ina kuka fito haka?""" "Ta faɗa da murmushi tana rike hannun Abir ""Wurin Mommyn Suraj ita ta mana wanka"" ""Ina Amna?""" Tana chan ɗaki wurin Momma. Jansu tayi zuwa ɗakin da suka ce Aina'u take ta samu tana shirya Suraj ganin Hibbah ya sa tace """Yauwa dama nemanki nake Addah Hibbah a ina kuka samo wanchan drawing book?"" ""Muka samo?""" Hibbah ta tambaya in confusion """yaran nan sun ce a hannun Abir suka gani shi kuma ya ce wurin Jasrah wacece ita?""" Tayi maganan tana zama gefen Hibbah da ta zauna tana ɗora plate na indomie ɗinta kan kafafunta. """Jasrah ɗiyar Boss namu ce, da muka je da Abir they played together ban ma san ya ɗauko drawing book ɗinta ba, amma me kika bi kika damu?""" """Kalli nan Addah Hibbah""" Drawing ne da aka yi da Color wasu da fenti take nuna mata... """Kin san dai na yi karatu ne kan child art therapy abin da dayawa a arewaci bamu damu da shi ba, na san ba lallai kin san menene shi ba ma tunda ba field naki ba ne, Child Art Therapy (wato maganin yara ta hanyar zane da fasaha) wata hanya ce da ake amfani da ita don taimaka wa yara su bayyana yadda suke ji ta hanyar zane, fenti, ko wasu ayyukan fasaha musamman idan ba sa iya bayyana kansu da magana sosai, sau da dama yaran da suke cikin damuwa ko yanayi na rashin jin daaɗi su kan bayyana hakan ne ta hanyar zane musamman ida akwai" "tsoratarwa a lamarin.""" Hibbah bata san ta ajiye plate ɗin gefe ba tana kallon zanen dake ciki """Me kike nufi ne kam Aina'u? Kina nufin zai iya kasancewa Jasrah tana cikin damuwa? Kuma fa ita kurma ce bata magana""" """Definately Adda Hibbah, idan yaro na fuskantar ƙalubale zai iya yin zanen yanayin da yake ciki don fitar da tsoro ko damuwa daga ranshi, wasu yaran ko in ce wasu therapists kan ba yaro laka ko abubuwan ballewa da manne wa don kawai ya bayyana abin da ke ransa ta hanyar zanen sai ki samu abin da yayin nan shine ainihi a cikin ransa, ba kyaun zane ake dubawa ba" "a'a ma'anar ake karanta""" Hibbah tace cikin yanayin nuna damuwa """Amma mahaifinta na tsananin ƙaunarta haka a wurin mamanshi aka ce take Dukda am not sure ko mom nashi ɗin ce ko step mom, bai yi aure ba bare a ce tana fuskantar ƙunci wurin matar uba""" "Murmushi Aina'u tayi ganin har lokacin Hibbah bata gama gane menene ma shi art therapy ba ""Ki kalla Adda Hibbah duk fa zanen da ta yi bata yi da kala mai haske ba sai masu duhu sossai, ga wannan"" ta buɗe wani Page" """Ɗaki ne mai girman gaske sai zanen yarinya mace karama a mafi kankantar wuri cikin ɗakin zai iya kasancewa yana nufi duniyar gabaɗaya ya zama mata mai faɗi tana jinta ita kaɗai ce ciki, kalli wannan fuska ne amma babu idanu kuma cikin ƙunci, duba wannan ga ta ita kaɗai sai wasu mutane marasa fuska dake daga chan nesa sossai da ita, zane ne da suke bayyana ainihin abin da ke zuciyarta ba wai na raha ba, kaɗaici ne da damuwa ke damunta da idan ba'a" "dauki mataki ba komai na iya faruwa da ita""" Hibbah tace """Toh Aina'u yaro ba zai iya yin zane haka don kawai yana so ba?""" """Yaran da suke irin wannan zane sune irin waenda suka fuskanci tashin hankali ko suka rasa wani nasu, yaran da suke da matsalar sadarwa ko magana, yaran da ke fama da damuwa da tsoro, yaran dake da autism spectrum disorder ko ADHD." "Ban ce lallai lallai tana da damuwa ba amma don Allah ki san hanyar da zaki bi ki bincika""" Hawaye ne suka cikawa Hibbah idanu yanzu 'yar yarinyar nan ne za'a ce take fama da damuwa? Anya?? """Addah Hibbah ke mai ilimi ce, sau dayawa akan tauye yaro ko ki ga yaro ya tashi cikin" "gurbattaccen rayuwa saboda rashin mayar da hankali kansa, child art therapy na da matukar" "muhimmanci cikin al'ummar mu kuma yana da kyau mu kula sossai da yaranmu ta wannan ɓangare hakan ya sa na ji sha'awar karatu a ɓangaren, na san kanki ya ɗaure amma ki natsu ki mayar da hankali ko bayan na bar Lagos za ƙi kirani ki ce na ce... Ke kaɗai ce za ki iya" "taimakonta ni kin ga ko saninta ban yi ba bare in yi wani abu a kai""" """Na yarda Aina'u amma ta ya zan taimaka mata?""" """Idan da hali ki yi magana da babanta na fahimta, kar ki fito mishi kai tsaye sai kuma ki dage idan tana inda kike ki nuna mata ƙauna da tsaro, za ki iya bata kariya ta hanyar janta jiki har ta sake ta kuma aminta da ke, ki saya mata abubuwan zane kawai ki bata kar ki ce mata komai sai ki kula da abin da zata zana, idan ta yi ki yaba mata ki kuma ƙarfafata dole ne ta dangana da psychologist amma abu mafi muhimmanci shine ta bar wannan sorrounding da take fuskantar" "matsala ina fata kin fahimta?""" "Kai hibbah ta gyaɗa tana karɓar drawing book ɗin, daidai Zaitoon ta shigo ""Me kuke ta yi haka a ɗaki ne?""" """Ga mu fitowa Addah Zaitoon""" "Aina'u ta faɗa tana Miƙewa, Hibbah ta ɗauki indomienta da ya zama ƙanƙara ta mayar kitchen don abincin ba zai ciyu ba kuma, ta ɗauki Admiral A ta koma ɗakinta ta adana takardar kan ta fito, tsabar tunani da ta sanyawa kanta sai da kanta ya fara ciwo ko iya zuwa dinner bata yi ba haka suka tafi tayi kwanciyarta." "Ranar Lahadi su Momma suka juya, kuma Hibbah ba zata ce bata ji daaɗin tafiyar su ba don zata yi kewan yaranta da ta cika da shopping a jiya Asabar, za kuma tayi kewan Aina'u dake mata hiran gida amma Momma ba zata ce komai ba Dukda uwa uwa ce amma ta sosa mata zuciya ta bangarori da dama a bikin, ta fuskanci matsi wani lokacin har da tsangwama daga dangi babu abin da ya fi bata haushi irin yadda ake kwatanta da 'yan uwanta ko ƙannenta sai ka ce aure gasar tsere ne, suna manta cewa lokaci da kuma kaddara suna da tasiri. Tana yi wa Momma uzuri saboda lokuta da dama iyayen da kan matsawa yara batun aure ba don basa la'akari da abin da za su ji ba ne a'a damuwa ce da makomar 'ya damuwa ta gaskiya na son ganin 'ya ta samu rayuwa mai kyau, wani lokaci kuma ya kan zama tsoron maganan mutane" wanda mutum kuma ba'a iya masa mai iya masa sai mahallicinsa. "Cikin shirin office ta fito yau ta saka suite ne burnt Orange, wandon mai faɗi sai farar shirt mai dogon hannu da ta ɗora a sama kan ta kawo rigar suite ɗin ta ɗora a kai, farin jercy scarf tayi wrapping a kanta ya fitar da jewelries ɗinta kalar burnt orange, hill ta saka shima burnt orange ta ɗauki jakanta wannan colorn ta fito riƙe da keyn motarta, babu komai a fuskarta banda kwalli da lipgloss, sallama ta yi da Momma kan ta fice daga gidan ta ɗauki hanyar office gabanta banda faɗuwa babu abin da yake abubuwa dayawa zata fuskanta, menene zata iya ji daga MB MUSTAPHA akan rayuwarta? Ta ya zata taimaki jasrah ba tare da MB ya zargi shisshigi ko" chusa kai a lamarin ba?? 53 "Ko da ta isa office yau ta samu ya rigata zuwa, don haka zama kawai tayi ta fara duba schedules ɗinshi na ranan meeting ne kawai guda ɗaya sai zuwa chan Badagry kamfanin production ɗinsu akwai kayakin da zai duba ya kuma sa hannu a wasu files ɗin, sai da ta fitar da komai intact kan ta ɗauka ta nufi kofar office nashin haka kawai take jin faɗuwar gaba marar" dalili. Yana zaune relaxed cikin kujerar shi inda yake ɗan juyawa a hankali fuskarshi zaka kalla ka san "cewa akwai abin da yake damunshi amma bai bari ya taɓa aikinshi ba, kaman ma yana amfani da aikin da yake yin ne wurin kawar da tunanin da ke shan kanshi a kwanakin." A soft knock pulled him from his thoughts. """Come in.""" Ya ba da umarni softly ba tare ma da ya ɗaga kai ba. "The door opened, and there she was again." Sauyin bugun zuciyarshi da kuma takun sawayenta su suka sanar da shi wacece ko da bai "ɗago ɗin ba kuwa. For a brief second, sai da ya ji komai ya tsaya mishi chak it felt like the room shifted, like everything else dimmed just enough for her presence to take focus." "She stepped closer, calm as ever." """Good morning Sir""" Muryarta very soft and gentle ya ratsa dodon kunnenshi ya basar tare da ɗago kai zuwa ga kallonta don ya amsa gaisuwar. "But again... That pause marar control their eyes met ta saki murmushi ba tare da ta kula da tension dake building har cikin idanunshi ba, he bit his lower teeth a hankali cikin deep voice" ɗinshi yace """Good morning Miss Mudassir""" Ta ajiye papers ɗin """Ga schedules ɗinka na yau Sir""" "Ya gyaɗa kai yana mayar da idanunshi kan system ""I will check, thanks""" "Ta juya zata fita sai ta hangi Jasrah kwance a kan kujera cikin office ɗin tana bacci kan tayi magana yarinyar ta farka kuma ta miƙe da wani irin sauri tana zare idanu jikinta ya ɗauki rawa ganin kujerar ya jiƙe alamun ta yi fitsari, kasancewar idanunshi akan system suke bai kula ba da" sauri Hibbah ta isa ta riƙeta sai ta ɗago a firgice tana sake ƙara. Da sauri ya ɗago kan ya miƙe ya nufo su Hibbah ta riƙeta da kyau """Hey Calm down! Kar ki yi kuka baki yi komai ba...! Kar ki tsorata""" "Hannun Hibbahn ta riƙe kam ba tare da ta san tayi hakan ba tana kallonta, shafa kanta take yi" gently bata rungumeta ba saboda idan ta ɓata kayanta babu wasu da zata iya sakawa. """Is ok kin ji? Babu mai miki wani abin don kin yi fitsari, cikin bacci ne kuma yara dayawa suna yi Its fine kin ji?""" "Chakk ya tsaya yana kallonsu bai iso inda suke ba, sossai yake mamakin yadda ta iya natsar da ita Dukda tsoratar ya yi yawa, ta ya Hibbah ta fahimci tsoron fitsarin ne ya razanata haka? Me ma ya sa don ta yi fitsari zata razana? Something is definately off da ya kasa pointing ɗinshi, yana cikin tunanin ya ji motsin su sai ya ga Hibbahn ta ja hannunta zuwa toilet da kanta ta yi mata wanka ta dauraye kayan ta shanya suka fito jasran na ɗaure da karamin towel da ta" samu a toilet nashi da ya ji kayan alatu. "Sun samu cleaner na gyara wurin, shi kuma MB MUSTAPHA na tsaye jikin desk ɗin shi ya jingina da shi hannayenshi a harɗe a kirji, ba zaka ce ga abin da ke yawo a ranshi ba but fuskarshi babu wani walwala, suite nashi Hibbah take ƙarewa kallo Wine colour daga gani designer ne don bata taɓa ma ganin kalarshi ba, ya amshe shi kwarai da gaske." Kawar da tunanin ta yi """Sir, Allah ya sa kun riƙo wani kayan?""" Ya ɗan miƙe tsaye da kyau ya taka a hankali zuwa wurin wani bag ya fiddo kayanta ya miƙawa "Hibbahn ba tare da ya ce uffan ba, zama tayi ta kamo Jasrah da ke ta kallonta ""Bari mu sa kaya ko Jasrah?""" Kai ta gyaɗa mata har ta gama sanya mata doguwar rigar ta saka mata hula. """Yauwa, an gama. Saura mene?""" "Tayi tambayar da murmushi, sai jasran ma ta ɗan yi murmushi tana mata alama da hannu amma bata gane ba sai ta kalleshi aka yi sa'a yana kallonsu ne idanunsu suka sarke da juna, ta ɗan haɗe lips ɗinta kaman zata yi magana kuma tana ɗari ɗari sai ta ji ya ce" """She's asking of the boy u came with last week""" "Idanu Hibbah ta ɗan buɗe ""Oohh Abir??""" Ta tambayi jasran sai ta gyaɗa kai tana murmushi. """Abir ya koma Kano but akwai Ayman zan iya kawo miki shi ku yi wasa ko?"" Kai ta gyaɗa." "Ya matso ya dafa kafaɗar jasran ""Are you Hungry?""" Ta girgiza kai """Okay je ki yi wasanki""" Ta gyaɗa kai ta wuce da sauri tana jin daaɗi yau ta yi fitsari ba'a zaneta ko an mata mugunta ba. "Numfashi suka sauke a tare sai kuma suka juyo suka kalli juna ashe duk ita suke kallo basu sani ba, kaman zai yi magana sai ya fasa ya juya ya nufi komawa wurin aikinshi sai tayi saurin" cewa """Uhmm Boss am so sorry to ask, na san personal issue ne amma Jasrah """ "Ya waigo ya zuba mata idanu ta ɗan dakata kaɗan kan ta fitar da maganan ""Bata zuwa school ne like other kids?""" "Bata sani ba maganan ya sosa mishi wani ɓangare ne na rayuwarshi, ya ɗan lumshe idanu da" suke neman sauyawa a hankali yace """As you can see she's disabled""" Cikin sauri kaman jira take ya ce haka tace """But Boss ai akwai schools na special kids like he. """ """Enough please Hibbah """ Softly yayi maganan yana juyawa ya koma desk ɗin shi ya zauna. Ta ɗan sauƙe numfashi kan tace """Sorry""" "Ta juya ta fice, ya bi bayanta da kallo har ta rufe kofar ya lumshe idanun yana ɗan swinging kujerar." "Ta jima zaune cikin tunanin ta yadda zata yi maganar Jasrah duk inda ta waiga sai ta ga kaman bai yi ba amma ba zata kuma iya zuba idanu rayuwar yarinyar ya cigaba da tafiya a hagunce ba, bata ji ma Fitowar shi ba sai taɓa desk ɗinta da yayi ta ɗan razana kaɗan tana kallonshi, cire idanunshi yayi daga cikin nata jin wani abu ya bi tun kanshi har tsakiyar tafin kafarshi." """Mu je""" "Ya faɗa, ta miƙe ta tattaro takardun gabanta suka fice zuwa meeting hall." "Ya gabatar da meeting ɗin cikin ƙwarewa as usual kuma ya tafi successful ko da suka dawo basu zauna ba ya fito riƙe da hannun Jasrah suka fita a companyn zuwa mota, P.A bai biyo su" ba don haka yau dole ta zauna tare da shi a bayan. "At First she was feeling awkward kasancewar motar shiru sai ta ji jasra ta kwanta akan jikinta, ta sa hannu ta zagaye yarinyar cike da tausayinta bai kula da hannunta dake wurin ba ya kai zai" "taɓa jasran hannunsu ya haɗe, da hanzari duk suka janye sai suka kalli juna." Kawar da kai tayi tana zaro wayanta ta kunnawa jasran cartoons da su Abir suka ta gani a wayan zuwansu. Kaman daga sama ta ji Muryarshi yayi breaking shirun """Na ce ina da magana da ke but you didn't care to ask""" Ta ɗan kalleshi idan da ya san yadda maganan nan da yace yake da shi ke mitsininta a zuciya da daga ta shiga office nashi sai ya fara bata shi. """It's like today baka cikin yanayi mai daaɗi shiyasa ban yi maganan ba""" """Hakane.""" "Ya faɗa, wurin ya sake zama shiru kan ya ce" """About Jasrah bata zuwa makaranta ne saboda condition ɗinta, not because ita ɗin kurma ce sai don mental Health ɗinta""" "Har yanzu kanta a ɗaure yake, Meyasa ba zata iya zuwa school ba to? Ganin baya son zancen kaman dole ma yake yi ya sa ta kyale batun har suka isa suka yi abin da za su yi a Badagry daga nan wurin cin abinci mai kyau ya sa drivern ya kaisu, yadda suka jero su ukun dayawa sun ɗauki hankalinsu bayan sun zauna aka zo aka karɓi order ɗinsu, kiranshi aka yi a waya ya miƙe" ya fita waje. "Tana ta kallon jasrahn tana son yi mata maganan da ya shafi gida amma tana tsoron yarinyar tayi reacting da zai sa baban ya kafa mata alamar tambaya don haka ta yi shiru, ta mirror door take kallonshi yana tsaye hannunshi duk biyu cikin aljihu da earpod dake maƙale a kunnen shi" yake wayan. """He's very tall""" "Ta raya a ranta, ko da ta ga ya katse wayan ya kira driver sun yi magana kan ya nufi ciki sai ta ɗauke idanunta a daidai lokacin aka kawo musu abinci shi dirty jollof Rice yayi ordering ita kuma White Rice da gizzard sauce sai Jasrah da indomie, tana ɗaga kai ta ga driver a ɗayan table ɗin kenan ce mishi yayi shima ya shigo kuma shima order aka kawo masa Coconut Rice da abin sha." "Ta kan yaba hali da kuma kirkin MB MUSTAPHA a ranta, wanda bai zauna da shi ba zai mishi" kallon miskili kuma marar mutunci saboda bashi da wani walwala kuma bashi da magana amma he's very observant and his kindness is topnotch. "Bayan sun gama suka koma company Jasrah a wurinta tayi bacci, tana ɗan duba wasu files wayan landline yayi kira alamun shine, Miƙewa tayi ta nufi ciki ta shiga ta same shi yana tsaye jikin transparent glass ɗin da ya ci rabin office nashin idanunshi na kallon waje, hannunshi ɗaya a aljihu ɗayan yana rike da kofi da alama wani abu yake sha na zafi don mug ne ba glasscup" ba. """Yes boss""" Ta faɗa tana gyara tsayuwar ta daga bayanshi kaɗan. Ya ɗan waigo staring at her kai tsaye. """Ina so na yi magana mai muhimmanci da ke but bana son kuka, and ba na son ki sanyawa kanki damuwa da zai iya affecting lafiyarki""" "Ta ɗan hadiye miyau tana kara jin tsinkewar gaba ""Zan yi iya kokarina na ganin ban yi hakan ba Sir""" Ya ɗan sauƙe numfashi ya lumshe idanu ya sake warewa. """Sit""" He whispered Ta je ta zauna kaman yadda ya umurta ya juya ya bata baya """An kama culprit that attempt raping you!""" Maganan ya zo mata kaman sauƙar aradu bisa kai ta miƙe da hanzari idanunta duk a waje """What???""" "Sai ta ɗan runtse idanu, ya waigo ya nufota sai da ya zo gab da ita ya ce" """Sit down Hibbah! you just promised me ba za ki yi panicking ba. Kin san tun yaushe nake son mu yi magana ina tsoron halin da za ki iya shiga?""" "Damuwa ke fitowa da maganan har kan harshenshi, hankalinshi tashi zai yi ya sani muddin ya" ganta cikin mawuyacin hali. """Ta yaya? Ya aka yi kuka gane shi? Me na mishi ya ce muku?""" Ta jero tambayar duk a rikice. """A wannan zamani da muke ciki ba sai ka yiwa wani abu bane zai nemi ganin ya lalata maka tanadin rayuwa, mun samu nasarar kamashi ne ta hanyar text messages na Blackmailing da yayi ta turo miki, cikin layukan muka samu Layin da akwai a wayan ɗaya daga cikin Security na nan that helped him, shi ya kashe wutan companyn har ya iso nan cikin sauƙi haka kuma shi ya kirashi ya gayamishi na zo plan dinshi ya wargaje, ko da aka kama Securityn azaba ne ya saka shi faɗin wanene and mun samu nasarar kamashi tun kwanaki biyar baya yana ɗaure a yanzu" "haka""" "Kallon bakinshi kawai take da yake mata bayani, duk saboda me har yanzu bata sani ba. Ita ba shigan banza ko na bayyana sura muraran ba, ita ba rashin kamun kai ba to me zai sa wani yaji" sha'awar yi mata fyade? """Wanene? Na san shi?""" Ya ɗan sauƙe numfashi yana jiƙa lips ɗinshi da harshenshi """Yeah kin sanshi, idan na faɗa miki wanene i don't want you to think of anything, babu zancen yafiya dole sai an shigar da shi kotu ko don hakan ya zama izina a rayuwarshi, ko don ya koyi darasi ya kuma san rayuwa ba'a yi mata garaje""" """kotu?""" Ya gyaɗa kai yana kallonta Ta ɗan girgiza kai """Bana so, hakan zai sa lallai iyayena su san halin da nake ciki and it might ruin me aikin nan ba" "lallai in cigaba ba""" """then za mu yi shari'ar ba da saninsu ba amma batun a barshi bai taso ba""" """Don Allah wanene?""" """MAHIR BASHIR ALMUSTAPHA""" Ya zaro sunan a hankali yana kawar da ido daga kanta. """Mahir?? Mahir fa brother ɗinka ka ce?"" Kai ya gyaɗa mata in comfirmation" Hawaye ne kawai suka ɓalle mata ba da shiri ba. Bata san ta fara zaro magana ba """Shiyasa ban taɓa yarda akwai wani abu wai shi so na tsakani da Allah ba, idan da gaske tun farko so na yake why would he do that? Me na mishi da na chanchanci hakan? Kawai don na ce bana son shi? Ya Rabbbb """ Ta miƙe tsaye yayi hanzari Miƙewa ya tari gabanta """Hibbah! Hibbah Zauna please""" Cikin tsantsar damuwa yayi maganan Ta koma ta zube a zaune kaman robot. "Bata taɓa kawo duk rashin mutuncin Mahir zai iya yunkurin bin hanyar da bai kamata ba don cikar mummunar burinshi a kanta, ina kalaman nadama da yace yayi da neman yafiyanta da yayi? Allah ya gani bata taɓa zarginshi ba but a yanzu sai ta fahimci tun dama lalatar yake so" "da ita ba so ba, sossai take kuka kuma hakan ba karamin ɗaga hankalinshi yayi ba." "Ya ma rasa ta ina zai fara, kawai yayi tsaye idanunshi a rufe yana taune lip ɗinshi, jikinshi har" rawa yake.... 54 "The moment hit him harder... Bai san me zai yi ba, bai san ta ya zai taimaka mata ba, she's" breaking down. "Ta kasa controlling kanta, duk yadda ta so ta dakatar da kanta ta kasa." Miƙewa tayi tana so ta fita ta samu wani wurin tayi kukanta son ranta but he refused to let her go ya tsaya dab da ita just looking at her. """Hey..."" he utters quitely, his voice dropping immediately, instictively softer ""Hey, Its okay. """ "Ta girgiza kai da sauri like she's embrassed, kaman tana so ta daina amma ba zata iya ba. ""No...it's not... I'm sorry, i just..""" "Her voice cracked again, worst this time. Kawai sai ta sa hannu biyu ta rufe fuskarta and then" "she continues crying right there in front of him, in his office, in his space..." "He freeze for a second, ya sake lumshe ido, ko da ya buɗe ta zame kasa kan knees ɗinta tana" cigaba da kukanta. "Ya fahimci ba zai iya hanata kukan ba a yanzu, akwai tarin damuwar da take fitarwa wanda kaman bata samu damar fitar da shi ba da jimawa, rayuwarta take tariyowa tun daga fari, wani irin kaddara ne wannan? Bata fa rasa ko wani irin gata ba, bata yi kukan talauci ba, bata yi" kukan maraici ba amma ga ta tsakanin maza suna wasan kura da rayuwarta. "A hankali shima yayi ƙasa zuwa gangarta ya saka gwiwowinshi yadda tayi, Something in his" "chest tightens, sharp and immediate." "He's seen her strong. Unshakable. The one everyone else leans on. And now she's here, breaking in front of him like she ran out of places to hide. Ganin hakan ya sa ta fara ƙoƙarin sake tsayar da kukan a karo na biyu. Ya miƙa hannunshi a hankali ya sauƙar kan kafaɗarta," "steady, warm and real." """Hey...look at me.""" "She hesitates, then slowly lifts her head. Her eyes are red and lost." "Ya haɗiyi wani abu mai nauyi a hankali ya furta ""You don't have to be strong here"" ta girgiza kai" Wanting him to let her alone saboda irin kunya da nauyinshi da take ji ya rufeta. """Ba zan iya tafiya ko ina ba, not while you are like this. Not while you are hurt"" And its not a boss speaking anymore." "It's a man da ya riga yayi zurfi, wanda ke ƙoƙari desperately don ya tsaya matsayarshi while" everything in him wants to cross it. "Hannunshi kawai ya cigaba da bari a kafaɗarta presence ɗinshi ya wadatar, yadda take tsugune" haka shima ya kasance a tsugune. "Sai da ya ga ta fara sassauta kukan ya miƙa hannu kan table dake gab da su ya zaro tissue ya miƙa mata, ta karɓa a hankali hannunta na ɗan rawa." Tsam ya miƙe ya fita chan sai gashi da maganinta ya buɗe ya cire biyu ya ɗauko ruwa a cup ya sake dawowa ya tsuguna gangarta. "Hannunta dake ɗaure kan kafarta ya kama sai ta ɗago tana zuba mishi rinannun idanunta," maganin ya saka mata ciki ya saki. Ta kai bakinta shi kuma ya kai mata ruwan kan lips ɗinta ta kurɓa ya cire. "Zama tayi daga tsugunon ta haɗe kafafunta shima ya zauna gangarta, zata iya cewa a yanzu abin da take ji bata taɓa jinshi ba kab rayuwarta." Wannan shiru nashi da kusanci da ya bata na sanin ba ita kaɗai ba ce akwai wani a gangarta tayi kukan da ya fitar da duk wani tarin damuwarta musamman a tsakankanin da Mahir ya far mata. "Sai da ta natsu sossai kan ta ɗaga kai ta kalleshi, ya zubawa wani wuri idanu amma tana" kallonshi kaman jira shima ya mayar da idanunshi kanta idanunsu suka sarke. """I'm Sorry""" Ta faɗa a hankali kaman mai raɗa. Ya girgiza mata kai """You don't have to...I'm sorry not onbehalf of Mahir a'a on behalf of this company that made you like this""" Ta ɗan yi murmushi mai ciwo """Babu abin da wannan company yayi mini, dama a yadda nake na same shi. Ka yi haƙuri kar ka" "kai maganan nan court""" Kafin ta ƙarasa ma ya haɗe fuska yana girgiza kai """Not after he made you feel like this Hibbah! Zan yi magana da mahaifinki and i know zai fahimta dalilin nan kadai bai isa ya sa kin bar aiki a wannan company ba""" "Ta waigo with so much pity face tana karya mishi wuya ""Ayya dai Sir...!""" Yayi hanzarin ɗauke kai daga kallonta yana ɗan cize lips yarinyar nan bata san me take yi ba. "Chak ya miƙe tsaye yana komawa kan kujera ya zauna, itama ta miƙe tsaye daidai zata yi" magana aka yi knock. Gyalenta ta warware ta rufe rabin fuskarta don ba zata so kowa ya ganta cikin wannan yanayi ba. "Nasir ne ya shigo bayan an ce mishi come in, kai tsaye gaban MB MUSTAPHA ya iso fuskarshi" da fara'a yace """Good Afternoon Sir""" Hannu MB ya miƙa mishi ba tare da ya miƙe ba suka gaisa fuskarshi a ɗan sake yace """baƙin ƙasar waje, an gama biki lafiya?""" """Alhamdulillah Sir""" Sai a lokacin Hibbah ta san ma ya je ɗaurin auren. """Ya Nasir barka da rana""" Ta faɗa tana ƙoƙarin sake muryarta. """Hibbah gajiya ne na ji Muryar ki haka?""" Ta girgiza kai """Kaina ne ke ɗan ciwo""" Tana kai nan ta zagaya ta bayan kujeran ta fice daga office ɗin yana ce mata Allah ya kara sauƙi. "Tana fitowa ta samu Jasrah ta farka, ta kaita bayi tayi fitsari ita kuma ta wanke fuskarta sossai ta dawo da ita ta bata ruwa ta sha." Alama ta mata zata je babanta Hibbah tace """Yanzu Daddy na da baƙo ki bari ya tafi sai ki je ko? Ga wannan ki yi drawing mu gani""" Ta cire drawing book da colours ta bata. """Kina son sweet?""" "Kai ta gyaɗa, a jakanta bata rabo da abubuwan zaki ta fiddo sweet ta ɓare mata ta sanya mata a baki, zama tayi da kyau tana tsotsar sweet ɗinta tana zane ita kuma Hibbah ta ɗora kanta kan desk tayi shiru." "A haka Nasir da MB MUSTAPHA suka fito da alama rakiya ya mishi, duk su biyun ita suka zubawa idanu don bata san ma sun fito ba, Jasrah ta miƙe da gudu taje ta rungume babanta ya riƙe hannunta, yana kallon Nasir da ya nufi desk ɗin ya ɗan buga kaɗan." """Hibbah!!""" Ta ɗago da sauri. """Ya Nasir har ka fito?""" """Ina za ki san na fito kin tsaya tunani? Hibbah...""" """Yaya Nasir na faɗa maka babu abin da ke damuna, bacci ne fa kawai ya fara ɗaukata"" Daga Nasir har MB sun san faɗa ne kawai tayi." """Shikenan na wuce"" ""Toh sai na dawo""" "Ta faɗa tana kallonshi har ya fita don bata son kallon MB dake kallonta, ganin ya ƙi cewa komai" ya sa ta waigo ta kalleshi. """Kar ki ce za ki yi driving cikin wannan yanayin, idan lokacin tashi yayi you should wait for me""" Yana kai nan ya juya ya shige. "Kaman yadda yayi alƙawari ba zai bar maganan ba, bayan ya zauna ya duba file ɗinta da ya" jima a office ɗin ya ɗauki numbern Daddy ya kira shi. """Assalamu Alaikum warahmatullah barkanmu da rana Alhj, kana magana ne da Almustapha Bashir Almustapha""" Ya ɗan yi jimm kan yace """Wa'alaikumussalam warahmatullah Masha Allah kai ne Shugaban Ma'aikatan su Hibbah ko?"" Ya ɗan gyaɗa kai kan ya miƙe ya nufi jikin Windows ya tsaya yana chusa hannu ɗaya cikin aljihu, yana da siyasa a magana don haka cikin yanayi na fahimta yayiwa Daddy bayanin komai don sam ba zai aminta da wautar da Hibbah ke shirin yi ba, dole ne a kiyaye wasu matan daga sharrin Mahir tunda har zai iya attempting sau ɗaya akan kowace mace ma zai iya sake" gwadawa. "At First Daddy ya firgita ƙwarai kuma hankalinshi ba karamin tashi yayi ba, Momma ta tabbatar" mishi da lafiyar Hibbah babu abin da yake damunta wani irin dauriya take dashi haka? Damuwa duk ya rufe shi sai ambaton sunan Allah yake. """Allah ubangiji ya kawo miki karshen wannan ƙaddarar Hibbah, ubangiji ya cigaba da baki" "juriya, Allah ya sadaki da farin ciki marar yankewa a kusa ya Allah""" "Kwarai da gaske zuciyar Almustapha ya karye, rauni ya baibaye jarumtarshi har yana jin kwallah na cika mishi idanu Dukda har yanzu bai san tarihin rayuwarta ba amma daga kalaman mahaifinta ya san ta ga jarabawar rayuwa daban daban, daga irin kukan da tayi ɗazu ya san" cewa zuciyarta ya jima da tarwatsewa haɗa shi wuri guda kuma babban aiki ne. """Ka yi haƙuri Alhj, In shaa Allahu komai ya kusa zuwa ƙarshe""" """Na gode kwarai Almustapha. Amma shigar da kanka shari'ar nan zai zama kaman neman rigima ne da step-mom ɗinka hakan zai iya haddasa koma menene, ina so ka janye Zan taho da 'yan uwana za mu karɓa daga inda ka tsaya Adalci dole ne a samar shi, don babu wanda ya isa ya tozarta ɗaya cikin 'ya'yana in kyale, kuma na yi maka alkawari matukar ba Hibbah ba ce" "ta buɗe baki tace ta bar aiki a kamfaninka ba zan hanata cigaba da aikinta ba.""" Numfashi mai nauyi Almustapha ya sauƙe dama tashin hankalin shi kenan a ce Hibbah ta bar "aiki karkashin shi ta yi wa idanunshi tazara, godiya sossai Daddy yayi mishi kan suka yi sallama akan wani sati za'a fara court hearing." "Bayan ya gama ya nufi computers ɗinshi, har zai kashe ya ga saƙon Email ko da ya duba saƙon international conference meeting ne da dole ya halarta, shiru yayi yana zubawa date ɗin ido in 2 days! A kwanaki yana ta adu'ar ganin sakon meeting ɗin don ya samu ya halarta amma a yanzu sai hankalinshi ya rabu ya san zai iya dawowa kafin a fara zaman court amma kuma hankalinshi da natsuwar shi basu bashi ya bar Jasrah wurin Mum ba kuma Dukda bai ga wani aibu nata ba kuma ya san ita ɗin tana kaunarshi tunda ta riƙe shi tun bai san kanshi ba a lokacin da ya rasa mahaifiyarshi cikin kananun shekaru, ba zai ce yayi maraicin uwa ba sai dai ya ce bai yi dacen uba ba, amma for Jasrah yarinyar tana matukar bukatarshi har tunani yake ko ya tafi da ita?" Amma idan yaje da ita taya zai iya mayar da hankali kan abin da ya kaishi nan ma Its not safe. "Numfashi kawai ya sauƙe ba don ya samu solution ba ya tattare abin da zai tattare ya fito," kaman yadda ya faɗa tana nan tana jiranshi hannunshi riƙe da na Jasrah suka fice ana ta yi mishi sai da safe har harabar company. "Keynta ya karɓa ya ba driver dinshi shi kuma ya shiga nashi don driving da kanshi, she sat in front seat bayan ta buɗewa Jasrah baya ta shiga, a hankali ya yiwa motar key yayi reverse tare" da ficewa daga cikin kamfanin. "Sun dan yi tafiya mai nisa ba tare da ɗayan su yace komai ba, tana kwance cikin kujera" idanunta a lumshe ya ɗan kalleta. """Sleeping?""" "Ta wara idanun ""No!""" """Then tunani ko?""" He utters Softly. Ta ɗan miƙe zaune da kyau tayi shiru don ko ta mishi karya ma ya riga ya sani. """I couldnt help it ne but zan yi kokarin ganin na daina""" Ya gyaɗa kai """Do that please, I'm sorry you're going through this. Ba zan iya kwatanta yadda kike ji ba but you don't have to carry it alone""" "Ta saukar da kanta tana wasa da fingers ɗinta, bata san mizanin da zata ɗora MB MUSTAPHA ba Dukda tana da twin amma twin ɗinta bata zama comfort ɗinta ba a lokacin hardships ɗinta na rayuwa kaman shi ba, had it been yana tare da ita for all This while ta tabbatar kila zuciyarta ba zai sha wannan wahala da yake sha ba, kwata kwata yaushe ya santa amma duba yadda" yayi understanding ɗinta fiye da kowa a rayuwarta. """You are so kind i must admit that, thank you so much""" Yayi murmushi mai sauti ta ɗaga ido tana kallonshi. Shiru ya ratsa na fiye da seconds goma ya ɗan saki murmushi again mai yanayi da na wasa yace """Kallon fa?""" "Tayi saurin kawar da kanta, ya cigaba da driving with a smiling face." """Eheemm Please cancel all my schedules for this week, a sake fixing masu muhimmanci cikin" "wani satin""" "Ta ɗan kalleshi kadan ""Ko Meyasa Sir?""" Tayi tambayar cikin ladabi. """I am travelling to china probably gobe by noon"" ""China??""" """Conference meeting, ko za ki je?""" Ta girgiza kai """No ba ni ma da Visa""" Ya ɗan ware ido """Wow! Then next time or before then ma""" "Ta waiga kaɗan ta kalli Jasrah dake game sai kunci ya ziyarci zuciyarta, Allah ya sa ba wurin stepmom ɗinshi zai barta ba, kasa shiru tayi" """Jasrah fah? Za ku tafi tare?""" Ya girgiza kai """She's too young wa yawace-yawacen nan zata zauna wurin Mum"" Ta runtse ido abin da bata so ji ba sam, chan wani idea ya faɗo mata." """Ko za ka bar min ita before ka dawo? I promise to take good care of her""" Ya waiga ya kalleta ta gyaɗa kai with wide smile sai ya tsinci kanshi da murmushi ganin murmushinta genuinely a yanzu. """Za ki iya kula da ita?""" "Ta zare ido sai ta saki tsiririn dariya ""I'm not a baby, Boss!""" Shima dariya kaɗan yayi na yadda tayi maganan """uhmm, Ok then zan tambayeta idan ta amince fine bana tantamar barinta wurinki sam""" Kai ta gyaɗa she will not rush him da zata juya ta tambayi jasrahn a take amma ta bari zuwa gobe ta tabbatar idan zaɓin yarinyar zai bi she will never choose her evil grandmother. "Har kofar gidansu ya tsaya, ya waiga zai yi magana call din Mum ya shigo. ""Excuse me!""" "Ya ce kan yayi picking kuka take yi sossai hankali tashe. ""Mum! Lafiya? Are you okay?""" """Ina lafiya Mustapha? Ashe ƙaninka kam kama shi aka yi? Yana rufe a hannun hukuma kusan" "sati?""" "Ya ɗan lashi lip ɗinshi na ƙasa kaɗan, yayi kaman bai sani ba. ""Subhallah! Wai akan me to?""" """Wai wasu ne suka kai kararshi ya yi yunkurin yi wa ɗiyarsu fyade, and wai a company ɗinka ma" "hakan ya faru?""" "Ya gyara zama ""Mahir ɗin?""" """Kaima baka yarda ba bare ni, kila sun zaci bashi da gata ne suke shirin zaluntarmin yaro basu isa ba wallahi, ko ma hakan ne basu isa sun tozartamu ba""" Yayi murmushin mamaki wanda bai bari sautin ya fito ba. """Mum yanzu ina kan hanya, bari zan zo gidan in ji ta yadda za mu fara shawo kan al'amarin"" ""Toh sai ka zo, don Allah ka hanzarta kar Yarona ya sake kwana a wanchan kazantaccen wurin""" Ya gyaɗa kai ya katse ƙiran. "Ya ɗan kalli Hibbah da take sauraron komai, itama shi take kallo kafin yayi magana tace ""Sorry Sir, don Allah do you share same Mum with Mahir?""" Ya ɗan girgiza kai """My Mum passed away tun ban kai kaman Jasrah ba, i grew up a hannun Mum nashi but she loves us equally kawai dai shi Mahir i don't really know inda ya kwaso wannan rayuwa nashi"" Ta sauƙe numfashi tana girgiza kai no wonder ake zaluntar Jasrah bai sani ba, he thought Mum mutumiyar kirki ce, so she's a green snake Oh Allah!" """Hey""" Ta ɗan yi firgigit tana mayar da hankali kanshi. """Am sorry for ur Mum, in shaa Allah she's in a good and Perfect place ever"" ""Ameen""" Tana so ta sake mishi tambaya amma bata so ya ga shishiginta yayi yawa sai ta ɗan kalleshi kaman wanda baya so su rabu shima ya kalleta. """Sai gobe?""" "Tayi maganan kaman mai tambayar izini, ya gyaɗa kai." """Bye, kar ki manta banda dogon tunani and if you really feel like crying make sure u call me""" Tayi dariya tana buɗe kofa ji wani zance idan zata yi kuka sai ta kama kiranshi? He's unbelievable! Sai da ta rufe kofan ta ɗan rankwafo """Eyyaaa Sir a sake tunani batun Baby Jasrah i will love to babysit her na kwana biyun nan. Bye"" Tana kai nan ta ɗaga mishi hannu ta koma baya tana ɗagawa Jasrah itama ta ɗaga mata with" wide smile sai ta juya ta nufi cikin gidansu zuciyarta wasaii… 55 "Kai tsaye gidanshi ya wuce, sai da yayiwa jasra wanka ya shirya ta ya haɗa mata cereal kan ya wuce ɗakinshi ya kwaɓe kayanshi ya wuce toilet, a cikin wani stylish luxury tub with warm, bubbling water for relaxation ya shiga ya kishingida yana tunanin Hibbah, a yanzu zuciyarshi ta gama kamuwa, she lives rent free in his heart, bai taɓa tunanin zai iya son wata macen kwatan-" kwacin yadda ya so Anam ba sai gashi ba'a je ko ina ba Hibbah ta gama bin jininshi. "The worst part shine ta yadda zata fahimceshi ta kuma yarda cewa shi babu yaudara a lamarinshi, ta riga ta biyo taɓo mai wahalarwa da ba kafafunta kawai ko tufafinta ya lalata ba har zuciyarta ya gurɓata da dattinshi, amma ba zai taɓa haƙura da ita ba daga rana irin ta yau yayi wa kanshi alkawarin tsayawa kai da fata har sai ya ga ta zama mallakinshi, har sai ya zuba ruwa mai ni'ima ya wanke wahalallen SAFARA A TAƁO da tayi na tsahon shekarun nan don da shi kaɗai ta dace, kuma dama tashin ce ba ta wani ba shiyasa ubangiji ma bai bari ta auri kowa" ba kawo haɗuwarsu. "Da kyar ya yakice tunanika dake yaƙarshi ya yi wanka ya fito da alwala don Magrib ake shirin ƙira, cikin wata jallabiya emerald green ya shirya da ya amshe shi ƙwarai, ya feshe jikinshi da perfumes ɗinshi kan ya fito yayi sallah, ya nufi ɗakin Jasrah ya samu tana zaune kan sallaya" fuskarshi cike da murmushi ya duƙa a gabanta. Ya ɗaga hannu yana amsar adu'ar da take yi Dukda bai san na menene ba bayan sun shafa ya shafa kanta da murmushi """Mamana wa ya koya miki yadda ake Adu'a?""" Ta mishi alamu da hannu wai ɗazu tayi sallah za ta miƙe Maman Abir tace mata ta dinga yin Adu'a musamman wa parent ɗinta kuma ta dinga roƙon Allah ya kawo karshen duk wani azzalumi. "Ya ɗan juya idanu sai ya taɓe baki da ɗan murmushi ""To me kika roka mana?""" Ta ce ta roƙi Allah ya sa mommynta na Aljannah kuma Allah ya sa kar Daddynta ya sake kaita gidansu. Ya kamata ta miƙe tsaye """Babyna bata son gidan Mum ne?""" "Da sauri ta gyaɗa kai ""Why?""" "Sai tayi shiru, ya sauƙe numfashi" """Gobe Daddy zai yi tafiya, Ina kike so in barki wurin Mum ko wurin maman Abir?"" Ta ɗan zaro ido sai da ya lallaɓa ta kan tace" Wurin maman Abir ya gyaɗa kai. """Toh me kika ji Abir na cewa Mamar tashi?""" Tace Maami """Then from now on haka za ki na ce mata ko?""" "Ta gyaɗa kai cikin murnan ba zai kaita wurin Mum ba, shi kuma kallon tausayi yake mata." "Hannunta ya kama suka fice zuwa mota, da kanshi yake driving cikin natsuwa har suka isa gidansu almost hour on road saboda tazarar dake tsakaninsu, ko da suka nufi ciki gamgam ta" riƙe gefen rigarshi har zuciyarshi na motsi wato har ranta bata son zaman gidan. Da sallama ya shiga Mum dake zaune ta zabga tagumi ta miƙe tsaye da sauri """Almustapha tun yaushe na ƙiraka?""" Ya isa gangarta ya kama kafadunta ya zaunar da ita kan kujera tare da zama gefenta """Mum ko da kika kirani ina hanyar gida dole na ƙarasa na watsa ruwa nayi sallah kan na fito""" Ya juya ga mahaifinshi da ya kira Jasrah yana mata wasa don yana kaunar yarinyar sossai. """Abba barka da dare"" ""Yauwa""" Ya amsa ba tare da ya ɗago ba. """Alhj ba za ka mishi magana ba kana kallonshi? Ko har ka manta irin halin da muka tsinci Mahir a ɗazu? Wallahil azeem na tsani yarinyar nan tun kafin na ɗora idanuna a kanta na ji duk duniya bani da makiyiya kamar ta, ta tozartamu ta wulakanta min rayuwar ɗa""" Cikin ɗaci da kunar rai tayi maganan. Abba ya ce """Wallahi ban yarda da kai ba Mustapha, yadda ka washi ɗan uwanka shi yake haƙuri da kai ka kuma washi ganinshi kusa da kai babu abin da ba zaka iya yi mishi ba, ka gayamin kana sane da kama Mahir ko baka sani ba?""" "Ya ɗan ciji lip ɗinshi kaɗan yanayinshi na sauyawa yace ""Ban sani ba Abba""" Kura mishi idanu Abban yayi don ya san da wuya ya mishi karya sai dai in akwai abin da yake shiryawa. """Amma ka san an ce yayi yunkurin yi wa wata fyade?"" ""Eh saboda employee ta ce, na san da batun""" """An ce kai ne shaida na farko Meyasa baka sanar da mu cewa Mahir ba ne? So kake a kulleshi" "ya baka wuri ko?""" Ya sauƙe numfashi idanunshi na kaɗuwa """Abba ban ganshi da idona ba don ina shigowa yana guduwa, abin da kawai na sani na kaita asibiti na kira iyayenta""" Mum tayi caraf tace """Matsiyata! Kenan su suka kai ƙara amma me shaidarsu na cewa Mahir ne? Saboda kawai ya" "taɓa cewa yana sonta ka mishi shigar sauri? A yanzu wallahi ko kai Almustapha in dai na isa matsayin uwa a wurinka ba zaka taɓa auren yarinyar chan ba""" "Yayi shiru bai ce komai ba, Abba ya ce" """Za'a ƙiraka witness na tabbatar idan an je court """ Wani kallo ya ɗago yana yiwa Abban da ya sa ya katse maganan """Ba kin ga rashin kunyar ba? Yaro idanu a tsakar ka ina mishi magana yana bi na da kallon banza to wallahi umurni nake baka kar ka kuskura ka nuna ka san wani abu""" """Dole mu samu lawyer daidai da su basu isa su ɗaure min yaro ba, kai kuma My son za ka taimaka ka karyata kasantuwarka wurin da kaita asibiti, shari'ar nan babu inda zai je za a" "watsar a sakar mini yaro kuma ka tabbatar ka koreta""" "Cikin tsantsar mamaki yake kallonsu duk su biyu, bai yi zaton za su nemi fitar da Mahir ko ta" wani irin hali ba ciki har da sake zaluntar Hibbah idan suka samu dama. """Abba, Mum ina so don Allah ku bar shari'a tayi aikinta, idan yana da gaskiya ai babu mai tauye gaskiyar, abinnan a kamfanina ya faru dukkansu kuma ma'aikatana ne da hakkinsu ya rataya wuyana me kuke tunani zai faru idan na ba da gudumawa wurin zaluntar daya? Karya ba shine" "solution ba don baku koya min hakan ba kar soyayyar da kuke yiwa Mahir ya rufe muku id. """ """Will you shut up Mustapha? Kai a'uzubillahi! da na san haka za ka zama mai son kanka da ƙin jininka da ba zan taɓa saka maka sunan mahaifina ba don ba haka yake ba.. Kiyayyarka ga Mahir har ya kai haka? Me yayi maka da zafi don kawai ya zaɓi ya taimaka maka wurin gina rayuwarka? Ko ka manta nima ina da wannan kamfanin amma ya zaɓi yayi aiki da kai? Kullum yaron nan ya zauna zancen shi ku samu haɗin kai ka so shi amma baka taɓa kaunarshi ba..." "Anya ba duk shirinka ba ne na ganin ya bar gabanka?""" "Mum ta rushe da kuka, jijiyoyin jikinshi sai da suka mimmiƙe da kalaman mahaifin nashi gareshi, me ya ɗauke shi? Meyasa tun tasowarshi Abba bai taɓa kaunarshi ba da yayi laifi da bai yi ba duk hantara da zagi na cin mutunci?" Ba zai iya magana ba a yanzu don dacin da yake ji har kan harshenshi. Ya juya ya kalli Mum da rinannun idanunshi zai yi magana ta ɗaga mishi hannu """Matukar ka daukeni uwa Almustapha ba zaka tura yarona kurkuku ba, ban maka riƙon wulakanci ba ba zaka rama min alkhairina gareka da sharri ba, ka tashi ka tafi idan ka ga dama aka je kotun ka basu goyon baya""" Tana kai nan ta miƙe da sauri tayi ɗaki tana kuka sossai. Ya cije haƙorinshi yana haɗiye kakkaurar miyau Abba ya girgiza kai yana jefanshi da mugun kallo """Ka gani ko... Matar da bata taɓa ƙin ka ba, ta so ka tamkar ita ta tsuguna ta haifeka amma dayake kai mutumin banza ne ita za ka konawa rai, kullum a kareka take a wurina abu sai ya fi karfinta ne take sanar da ni wani abin ma sai dai in ga ta maka bata yi wa Mahir ba sai nine zan" "mishi sakayyar kenan yayi maka kyau...""" "Yana kai nan ya sauƙe Jasrah ya miƙe ya fice shima, idanunshi a kafe kan carpet na parlorn hannunshi har rawa yake, ranshi tafasa yake bai ma san me zai yi ba kuma ko wani irin tunani zai yi, ba zai taɓa bin bayan karya ba a ko ina, kuma ba zai taɓa bari a zalunci ma'aikacinshi ba" "ko da ba Hibbah ba ce, bai taɓa tsanar Mahir ba sai dai ya tsani halayenshi masu yawa...." "Taɓashi da Jasrah tayi ne ya sa ya ɗago ido ta mishi alama ka yi haƙuri da hannunta, ya gyaɗa kai sai ya ja ta ya sanyata a kirjinshi yana lumshe idanun da har yaji yaji suke mishi." "Sai da ya ji sassaucin abinda yake ji ya miƙe tsaye da ita a hannunshi suka fito zuwa mota, a hankali ya ja yana jin wani irin kaɗaici da damuwa na rufe shi, yayi tafiya mai nisa kan ya shiga wani shopping mall mai girman gaske, yana rike da hannun jasrahn ya saya mata kaya sababbi kala har goma da panties sabbi da kuma nighties, ya bi ta ɓangaren turare yana dauka mata idanunshi suka kai kan wani turare Shamukh by Nabeel unisex ne kuma turare ne mai tsada sossai ya ɗauka ya matsa ɗaya ɓangaren ya ɗauki dior sauvage set ɗin gabaɗaya da shi yake" amfani. "Gaba suka yi wurin kayan makulashe madara ne babba sossai ya saya kaman wanda zai barta tayi shekara, ya saya su cornflask da cereals da Jasrah ke yawan sha, sai wasu choculates masu masifar daaɗi da tsada ya kwasa, aka haɗa package na turaren da choculates ɗin daban, Dukda fuskarshi babu digon fara sai kallonshi ake, aka haɗa mishi nashi daban sai tarkacen Jasrah a trolley ya sa aka haɗa pink a wurin duk suka yi unboxing suka shirya kayakin suka kai mishi mota bayan yayi payment da Gold Atm ɗinshi na dollers, daga nan ya ja motar ganin" jasrahn na shirin bacci ya kwantar mata da kujeran tunda da ɗan tazara inda suka nufa. Tana tsaye kitchen ta gama saka kifinta a oven don grilling tana haɗa Mango lemonade ta ji "ƙiran wayanta, sakin blender ɗin tayi taje ta ɗaga. ""Boss!""" "Haka tayi saving, ɗagawa tayi gabanta na ɗan faɗuwa da bata san dalili ba. ""Hey...!""" "Ya faɗa chan ciki, muryarshi very deep." "Bata san ta rufe idanu ba, sai da taji abin da ke mitsininta ya daina tukuna ta amsa ""Barka da dare Sir""" Ya amsa """How are you?"" ""I'm good""" """About Jasrah, zan iya kawota yanzu?""" "Cikin sauri tace ""Yes sure Sir"" ""on my way""" Yayi whispering Softly kan ya katse ƙiran. "Ta bi wayan da kallo muryarshi ba haka suka rabu ɗazu ba Its like something is bothering him, fita tayi daga kitchen ɗin ta tsaya hannun kujera tana kallon Mommy tace" """Mommy ai kin san Boss namu ko?""" Mommy ta waiga ta kalleta """Almustapha ba? Na sanshi mana har fa gudumawan biki ya ba Nasir ya ba ni, wannan" "mutumin kirkin da ya kaiki asibiti ba?""" "Nasir yayi dariya Hibbah na taya shi. ""Me ya same shi?""" Nasir ya tambaya yana kallonta """Wallahi wai zai yi tafiya ne zuwa China gobe shine yake son kawo min Jasrah babynshi ta zauna da ni kan ya dawo""" Mommy tace """Ha! Bashi da mata ne?""" Nasir ya amsa """Ta rasu a hatsarin mota Mommy baki tuna bane amma na faɗa miki har hatsarin yayi sanadiyar kurumtar ɗiyar tashi""" """Innalillahi wainna ilaihi rajiun! Yanzu yarinyar bata ji?""" "Mommy ta faɗa da tsantsar tausayi ""Mommy tana ji amma bata iya mayarwa ne""" """uhmm umm hunnn Allah ya ji kan mamanta ita kuma ya raya ta lallai wannan Almustapha ya" "ga jarabawa lokacin""" Hibbah da ke tuna irin muguntar Mum tace """Kuma bashi da uwa a raye Mommy""" "Nasir ya kalleta don shi karan kanshi bai san mamansu ba ɗaya da Mahir ba, amma bai yi mamaki ba kuma kasancewar ita ɗin secretary ɗinshi ce ta fi kowa kusanci da komai nashi a" yanzu. """Yi sauri ki gama girkin naki ko zai samu ya ci""" Nasir yace """Allah ya sa ma ya ciyu, yadda ba'a saba shiga kitchen ɗin nan ba""" Tana ɗan hararanshi tace """Kaima ka san wuce nan, don ba na yi sai na bushi iska ba shi yake nuna ban iya ba ehe"" Dariya suke yi mata ta koma kitchen ɗin ta cigaba da aikinta." "Maganan mommy ya sa ta tsinci kanta da shirya mishi platter na kifin na musamman da bata yi ma niyyar haɗawa da dankali ba amma ta fere kadan ta soya ta kara ta saka gefen kifin, ta haɗa cowslow ta saka, dafaffen kwai ta yiwa yanka mai kyau kan cowslow ɗin kan tayi wrapping" da cling film. "Juice ɗin ta zuba a wani transparent jug mai kyau ta haɗa da mug ɗin, kiran wayanta ya sa ta" wanke hannu taje ta dauka tayi picking. """Muna waje"" Ya faɗa calmly Ta ce" """Give me a second ina zuwa Boss""" "Ta katse ƙiran taje ta saka hijabi pink ne kuma jalbab da ya amshe ta sossai ya fitar da karamin fuskarta, hand cream ta shafa a hannunta saboda cire duk wani karnin kifi Dukda da ma handwash mai kamshi ta wanke, fitowa tayi zuwa harabar inda motarshi yake Parke, bai kashe" "ba saboda Ac da alama, ɓangaren inda ta san Jasrah take ta buɗe" """Sannu da zuwa Sir""" """Miss Mudassir Madaki""" "Yadda ya kira sunan sai da ya sa ta ɗaga ido suka hada idanu, a hankali yake jin sanyi sanyi na" "shiga zuciyarshi, wannan ɓacin ran da damuwan wani abu mai kama da raɓa na mamayesu." Ta Yi saurin sauƙar da idanunta tana kiran Jasrah a hankali """Yadda ta yi baccin nan ba zata tashi yanzu ba, bari na daukar miki ita""" "Ya faɗa yana buɗe motar ya fito ya zagaya ta inda take, wani irin shiga hancinta kamshin shi yayi da ya sa tayi hanzarin yin baya, bai kula ba ma ya ɗauki Jasrah ta shiga gaba ya bita a" "baya har parlorn farko ya kwantar da ita kan kujera, sai ya tsaya a kanta ya zuba mata idanu." A yadda yake jin son 'yar shin nan Meyasa shi Abba baya jin haka a kanshi? Ba zai iya "kwatanta yi wa Jasrah kwatar abin da Abba ke mishi ba tun tasowarshi zuwa yanzu, har ya fara" tambayar kanshi daga ina ne matsalar ko daga mahaifiyarshi ne? Amma a labarin da ya samu Abba ya so mahaifiyarshi tamkar rai amma Meyasa shi ya kasa son shi? """MB""" "Ta kira da ɗan ƙarfi, sai ya lumshe idanu ya wara su a kanta, ta kawar da ido ganin yanayin idanun nashi sai ta tuna kiran Mum, ko daga wurinta yake ne ya sa duk ya hautsine haka yanayinshi na nuna baya cikin walwala?" """I'm Sorry for disturbing you, Dukda gobe muka yi na kawo ta yau""" Ta girgiza kai """Haba dai Sir ai ko barin min ita zaka yi na har abada ma zan so hakan, ka zauna please bari na kawo maka ruwa""" """Da gaske idan na baki ita kina so?""" Tayi murmushi jin tambayar nashi """Ina so mana wa zai ƙi this lovely pretty Princes""" Ta faɗa tana kallon Jasrah fuskarta da murmushi. Ya sauƙe numfashi baya son gaggawa da zai ce ya bata halak malak. Ya fara shirin fita tace """Eyyaa Sir Don Allah ka tsaya ko ruwa ne ka sha, Mommy ma tana so ku gaisa please""" "Ba zai iya resisting roƙonta ba don haka ya koma ya zauna ta wuce cikin natsuwa, kitchen ta je" "ta haɗo mishi tray ɗin tana fitowa ma ta same su da yaya Nasir ta ajiye akan table ta ja table ɗin gabanshi, komai ta saka a tray ɗin." Bata zauna ba ta tafi wurin mommy sai da ya gama cin kifin da bai ci na kirki ba sai lemonade ɗin ne ya sha sossai Nasir ya ƙira mommy ta fito suka gaisa ta ce Nasir ya dauki Jasrah ya kaita sama saboda ta san Hibbah ba zata iya ba. Suka tafi a tare aka barta da shi """Akwai kayanta a mota""" """Ok bari na bika sai na ɗauko""" Ya ɗan yi gaba ta bi bayanshi sai ya ja kafa sai da suka jera ya cigaba da tafiya a hankali yadda take nata. "Akwatin ta cire ya bata paper bag mai kyau ta karɓa ""Shi na Maamin Jasrah ne""" "Tayi murmushi ""Thank you""" Har ya shiga mota ta tsaya ta ɗaya ɓangaren. """Sir! Sai da safe""" Ya ɗan yi murmushi kaɗan """Thanks for healing me and thank you for the food""" Ta gyaɗa kai Dukda bata fahimci na farkon ba ta matsa ya ja ya fice. "Akwatin ta tura zuwa ciki ta haura da shi ɗakinta anan ta samu Jasrah na kwance kan gadonta, zama tayi ta buɗe Akwatin ta ta fitar da nighties sai da ta gama mitar sayayan da yayi na kayan madaran nan kan ta saka mata riga da wando ta kaita bayi ta sakata fitsari kan ta dawo da ita" ta kwantar kan gadon. "Paper bag ɗin ta janyo ta buɗe ta fitar da abubuwan ciki, turaren ta zubawa ido turare ne mai" tsada sossai numfashi ta sauƙe ta adana komai ta dawo ta kwanta kusa da jasran tare da yi mata Adu'a. 56 "Sanin Jasrahn na fitsari ya sa ta hana kanta baccin kirki ko wani bayan awa biyu zata farka ta sakata a toilet tayi har gari ya waye kuma bata yi a kwaancen ba, bayan ta yi Sallar asuba bata kwanta ba ta nufi kitchen ta duba abin da aka yi ta ga jasrahn za ta iya ci ta bada lunchbox akan" "a saka mata kar su je office ta ji yunwa, ta fito ta nufi ɗakin Mommy Don gaisheta." """Ina kwana Mommy""" """Lafiya ƙalau Hibbah ya kwanan Jasrah?""" """Lafiyarta ƙalau, yanzu zan tashe ta in mata wanka kenan""" """Da ita za ku tafi?""" """Eh Mommy ko na barta nan ba lallai ta sake ba""" """Anjima kaɗan su Aryan za su zo ki barta tayi wasa da yara 'yan uwanta""" Dukda tana ta tunanin kar jasrahn ta kasa sakewa bata ƙi ba ta dai kira Zaitoon akan a kawo "yaran da wuri, ta tafi ɗaki ta tashi jasrahn ta fara yi mata wanka ta zo ta shiryata kan taje tayi nata ta zo ta shirya Sharp Sharp don kaman zata makara yau kam." Hannun Jasrah ta kama suka fito zuwa dining ta saka mata breakfast """Jasrah Maami za ta je aiki ko, ga ipad ɗinki ki yi game ɗinki ki kuma yi waya da Daddy idan kina so, ga mommyna nan duk abin da kike so ki tambayeta ko?""" "Ta gyaɗa kai tana kallon Mommy da ke mata murmushi tace ""Ki sake abinki nan ma gidanku ne ko?""" Ta gyaɗa kai. Layin Jasrahn ta ɗauka don ipad ɗin nata mai simcard ne irin na yara daidai shekarun ta. Hibbah ta miƙe """Mommy na makara byeee""" Ta fice da sauri mommy na mata Allah ya tsare. Ba'a ko jima ba aka shigo da Aryan a parlor suka baje ƙasa mommy na zaune tana kula da su suna wasan su tuni Jasrahn ta sake har da dariya. "Ita kam Hibbah tana zuwa office ma ta shiga aikin gabanta, ta zaci zai shigo kan ya wuce amma shiru shiru don haka ta cire tsammani, jiyan nan ta ganshi wani iri hakan kuma ya tsaya mata a" rai bata san dalili ba. "Karfe sha ɗaya da 'yan mintuna ta kira Jasrah video call, sai da ya ma kusa katsewa kan ta" "ɗaga tana ta dariya har 'yar sauti na fitowa, Hibbah ta tsinci kanta da murmushi zata yi magana Aryan ya kwala kiran sunanta" """Aunty Hibbah!""" "Ta biye musu suna ta mata surutu, Jasrah ta gani tana ta kallon bayanta sai ta sake washe haƙori tana ɗaga hannu alamun hiii, da sauri Hibbah ta juya sai da ta ji zuciyarta ya buga, sai a lokacin ta shiga jin kamshinshi na shiga hancin ta a hankali." "Murmushi ya sakar mata da ya sakata zama wani iri a take, ya ɗan duƙo ta bayanta kusancinsu" "ya ƙaru, tuni bugun zuciyarta ya zarta na farko har zufa take ji a tafin hannunta amma ta dake." """Jasrah ashe yau kina gida abin ki?""" "Ta fara mishi alama da hannu tana gidan mommyn Maami ta basu abubuwan daaɗi kuma ga Aryan tana ta wasa da shi, zuciyarshi ya yi haske ƙwarai bai taɓa ganinta cikin wannan sakewar a gidan Mum ba, hankalinshi ya sake kwanciya da inda zai barta, yace su je su yi wasan su and ban da taurin kai ko faɗa, har tsarabar da zai kawo musu ya tambaya Aryan yace mota Ita kuma tace takalmin taya ya ɗan zare ido tayi murmushi tare da haɗe hannayenta alamun roƙo sai ya" gyaɗa kai yana katse ƙiran. Bai miƙe ba ya ɗan waiga kaɗan ya ce """Kina lafiya?""" "Cikin raɗa yayi maganan zuruuttt haka ya shige mata a bazata don ta tafi duniyar tunanin Sauyin da take ji a jini da zuciyarta da bata san na menene ba, baya tayi saurin jan kujeran sai ta kusa faɗuwa da hanzari ya sa hannu ɗaya ya tare kujeran." """Hey! Are you okay?""" Ta miƙe zuruf ta fice a wurin tana sauƙe numfashi sai kuma tayi hanzarin wucewa toilet. A jikin sink ta tsaya tana kallon mirrorn bayin. """Menene wannan? Me ke shirin faruwa da ni ni Hibbah?""" Ta girgiza kai da sauri """Ba zan taɓa karya alkawarin da nayi akan maza ba, ba zan yi aure ba kuma ba zan sake soyayya ba... Hakan ba zai taɓa faruwa ba""" "Ta tabbatarwa kanta kuma ta ja zaren, ta ɗan jima kan ta fito yana tsaye dab jikin kofar office nashi hannunshi a harɗe idanunshi na kallon kofar bayin tana fitowa suna haɗa idanu, ta kawar" kan ta tako a hankali """Ina kwana Sir""" Ya cigaba da kallonta kaman mai son karanto damuwarta amma bata bashi daman hakan ba ya ce a hankali """Kina dai lafiya kam ko?""." "Ta gyaɗa kai, ya ɗan sauƙe numfashi sai ya juya ya shiga office nashi, bai jima sossai ba ya" fito. """Zan tafi""" """Allah ya tsare ya kai ku lafiya Sir""" Ta faɗa cikin sound ɗin ma'aikaciya ga shugaba don ta yi alkawarin yanke duk wani alaqa na daban dake shirin ratsa wa har ya haifar da abin da ko mutuwa zata yi ba zata sake yi ba sai dai mutuwar ya ɗauketa. "Ya amsa da Ameen kan ya wuce ta ɗan bi bayanshi da kallo sanye yake da blue Suite da ya sake fito da hasken shi, gashin kanshi ya sake shan gyara haka fuskarshi takalaman kafarshi" "cover ce daga gani ta ci kuɗi sai sheki take, kawar da idanu tayi ta mayar kan system ɗinta." "Shi kam yana shiga elevator ya sauƙe numfashi a hankali tare da sa hannunshi ya shafa kanshi yana lasar lip ɗinshi tare da ciza shi, ji yake kaman ba zai iya tafiyar ba, ji yake ƙunci na sauƙar mishi yana mamaye zuciyarshi, kwana biyu zuwa uku zai yi amma ji yake kaman idan ya tafi ba zai dawo ba, bai yi niyyar zuwa office ɗin ba a yau yayi niyyar daga gida zai wuce Airport ne ko da suka fito har sun fara ɗaukar hanyar Airport ɗin ya ji ba zai iya tafiya bai sanyata a idanunshi" "ba, dole ya saka driver juyawa suka dawo babu wani abu da ya ɗauka ko ya manta itan ce dai..." Har elevator ya buɗe idanunshi a lumshe kamshin turaren ta ke dawo mishi cikin hanci har ya isa mota driver ya ja suka fice daga kamfanin zuwa Airport kafin ya gama duk wani da zai yi dab tashin jirgi kawai ya wuce ya samu seat ɗinshi na musamman a First class kuma rufe ba ta yadda na gefenshi zai ganshi ya kishingida yana sake lumshe ido. Ita dai Hibbah ko da ta tashi aiki gida tayi kai tsaye tana ta kokarin yakice abin da ke yawo a "kanta, sai da ta samar musu tsaraba ta isa suka rufu a kanta suna mata oyoyo da kyar ta saɓule ta shige ɗakinta don watsa ruwa." "Wasa wasa Aryan ya ƙi komawa ya ce shi kam gidan Mommy zai cigaba da zama, sun shaku da Jasrah a lokaci kankani kuma yana fahimtar alamominta har ma fiye da kowa a gidan, Washegari Hibbah ta tashi da ciwon kai bata je aiki ba sai ga Zaitoon ma ta zo, dama Nasir na parlor da yaran sai ga Abdul ma da Amaryar shi Jadwa da suke hutun cin amarci gidan ya zama" full house dole Hibbah ta fito parlor ta kwanta nan ana hirar tana murmushi. "La'asar ne liss tana kwance ta zamar da dankwalinta rabin kwantaccen gashinta a waje hannunta dafe da goshinta dake sara mata, doguwar riga ce jikinta mai yauki, Su Nasir sun tafi Sallar la'asar haka Zaitoon da Jadwa amma ita bata tashi ba don ranar ta fara fashi, ga ciwon ciki kaɗan kaɗan ga na kai da ya matsa mata ta ji ana taɓa hannunta dake kan cikinta, a hankali ta buɗe idanunta da suka ɗan rine sai a kanshi da hanzari ta janye tablet ɗin ta kife kan kujera" tana kallon Jasrah kaman za ta yi kuka. Jasrahn ta juya mata hannu alamun menene ba zata yi waya da Daddynta ba? Ta girgiza kai "Sai yarinyar tace ta ɗauka sannu zai mata ta gayamishi kanta na ciwo, bata ma gama bayanin" ba ta ji Aryan na kiranta alamun sun dawo daga masallaci sai tayi waje da gudu. Numfashi mai nauyi ta sauƙe sai ta janyo hularta gaba ta ɗan gyara zama kan ta ɗaga fuskar ipad ɗin. Yana zaune daga shi sai singlet da three quarter da alama da system ne yake wayan ya ɗaura "kan wani abu, hannunshi riƙe da coffee yana sipping don dare ne a wurinsu." "Ta tsinci kanta da kasa kallonshi, ya ce a hankali" """Maamin Jasrah! Ashe ba ki ji daaɗi ba?""" Tace ba tare da ta kalleshi ba """Headache ne kuma Alhamdulillah yayi sauƙi""" """Are you sure?""" Ya tambaya cikin kulawa ta gyaɗa kai. "Yana ta kallon fuskarta da ya fito mishi tarr a jikin system ɗin, idanunta sun ɗan kumbura kadan" ba sossai ba kuma fuskarta yayi Red haka lips ɗinta are Little bit dry. """Allah ya baki lafiya""" "Ta amsa da Ameen har lokacin bata kalleshi ba, ta sake cewa ""Ya meeting ɗin?""" """Yana tafiya yadda ya kamata jibi za mu kamallah""" """Allah ya taima. """ """Washh subhallah...!""" "Ya faɗa in a very silly way, da sauri ta kalleshi sai suka haɗa idanu, murmushi ya sakar mata da ya buga mata zuciya." """Ko ke fa""" "Ya faɗa cikin tsokana, fahimtar don ta kalleshin ne yayi haka ya sa da sauri ta katse tana runtse idanu sai hoton kirar jikinshi da yadda singlet ɗin ya zauna mishi, da kananun gargasa da suka bi hannayenshi suka sake dawo mata da sauri ta buɗe idanun saura kaɗan ta fara kuka menene wannan?" Ta miƙe ta bar tablet ɗin a nan tayi tafiyarta ɗaki. Tana shiga ta ga message nashi Adu'a yayi mata ya kuma ce kar ta je office har sai monday ta huta sossai. Ta ɓangaren su Mum yadda ta ɗaga wa Abba hankali ya sa duk ya kasa zaune ya kasa tsaye duk yadda yake tunanin yana da connection a ma bashi belin Mahir ɗin an ƙi. Ta tsinewa Hibbah har ba adadi sam ba zata iya jurar ganin Mahir cikin wahala ba ta saka Abban ƙiran MB don shi ne mai hanyoyi kuma cikakken dan zamani kila ya karɓa musu belin nashi amma layinshi baya shiga. Abban ya gaji ya tafi ya barta. "Ta ƙira office nashi ma P.A ne ya ɗauka shi yake sanar musu MB na China bata san ta lailayo ashar ta maka ba. Wayan ya zame a hannunta ta miƙe ta fara sintiri a ɗakin wani irin tururi na mamaye zuciyarta, tsanar Mustaphan na sake ninkuwa a ranta wato shi danta na rufe ma ko" oho ya kada kai yayi tafiyarshi wani ƙasa. "Duk yadda ta shirya mishi na ya sota ya bi ta sau da kafa sai hakan ya fara tafiya sai ta ga kaman ana rabata da shi, bai taɓa yi mata musu ba amma ta kula a yanzu zai fara kuma bai isa ba bata sha wahala a kanshi don ya rayu ba, bata sha wahala a kanshi don ya samu farin ciki ba." "Babu abin da bata kulla ba amma plan ɗinta dole yana nan ne zai tafi, lauyan da suka dauka zai" "kare Mahir ta ƙira ta fara jero mishi plan ɗinta shi karan kanshi sai da ya razana da lamarin ta, ta mishi alkawarin makudan kuɗi idan har shari'ar ta tafi yadda take so." Hibba na zaune ranar Juma'a da rana kawai ta ga kiran Daddy. "Ta ɗaga fuskarta a sake cikin murmushi ta shiga gaishe shi, bayan sun gama gaisawa yace tana ina tace tana gida ya ce ta same shi wuri kaza, wani karamin garden ne." Da sauri ta miƙe tsaye """Daddy kana Lagos?""" """Shhhh bana so kowa ya san da zuwana a gidan naku""" "Shiru tayi sai kuma zuciyarta ya fara bugawa Allah ya sa MB bai mata kwaɓa ba, ko da shike ai Daddyn kan zo ya ganta a office ma ya tafi ba tare da su mommy sun san zuwanshi ba kuma muryarshi very soft and gentle don haka hankali kwance taje ta saka hijabi ta fito ta nufi wurin mommy tace za ta karɓi saƙo yanzu ta dawo ta fice." "Rungume mahaifin nata tayi cikin farin cikin ganinshi ""Daddy na yi farin cikin ganinka kwarai wallahi""" """Nima haka Mamana, ba kin guje mu ba? Ya aiki ya su Mommyn naku?""" """Lafiya ƙalau Daddy, Ai ban isa gudar ku ba Daddy ku ne fa farin cikina""" "Kujera ya nuna mata ""Zauna""" Babu musu ta kai zaune """Hibbah!""" "Yadda ya kira sunanta sai da gabanta ya faɗi shikenan wallahi aikin MB ne, me yake kokarin janyo mata?" """Na'am Daddy""" """Ashe baki ɗauke mu iyaye ba? Kin san role ɗin mu kuwa a kanki a addinance? Meyasa abu irin haka zai faru da ke ba za ki kirani ba Hibbah?""" Ta kalleshi idanunta na cika da kwallah. """Daddy ba za ku huta da matsalolina ba kenan? Koyaushe Hibbah! Hibbah!! Har yaushe na Daddy? Ba wai Ban faɗa maka bane saboda baku kai matsayin sani ba, na ɓoye ne saboda gudun ɗaga muku hankali yadda na saba""" "Ta ƙarasa hawaye na zuba mata, ya riƙe hannunta" """Ba zamu taɓa gajiya da ke ba, kowa ya san rayuwa da irin ƙalubalen ta, bai kamata a nemi" "tozartaki ki ɓoye mana ba hibbah, dole za a bi miki hakkin ki mu kuma ji dalili.""" """Daddy za'a sake tsangwamata, sunana zai bi family, za'a kara saka alamun tambaya a kaina ya zama tamkar tambari ko ɓata suna! Wani ba zai taɓa cewa an yi kokarin yi wa Hibbah fyade ba sai dai yace an yi wa Hibbah fyade, wani ba zai yarda ba saboda kuskurena na farko a rayuwa wani zai ce ba dai fyade ba dama chan a watse take... Ina amfanin badi ba rai Daddy?" "Tunda bai yi nasara ba don Allah a bar shi""" Daddyn yayi iya kokarinshi wurin danne hawayenshi saboda tsananin tausayin yarinyar tashi. """Daga ni sai 'yan uwana biyu na miki alkawari ko Mahaifiyarki ba zata san zancen nan ba Hibbah, wannan bai kai dalilin kyale wanchan yaro ba, za mu shiga kotu ranar Talata zaman farko kuma ina so ki kwantar da hankalinki ki ba kanki ƙwarin gwiwa... Komai zai wuce ne don" "Allah bai yi abin da ba zai wuce ba. Mu je wurin uncles ɗinki""" "Ta goge fuskarta ta miƙe ta bi bayanshi har ciki ta wani ɓangaren ta hangi mutane uku zaune. Ko da ta isa tsuguna wa tayi ta shiga gaishe su suka amsa cikin kulawa Daddy Rabi'u har da janta da wasa wai ta yi kudi ta manta da su, Uncle Z ne ya tambayi lafiyarta tace mishi tana nan" lafiya. "Ashe na ukun nasu lawyernta kenan Barrister Abdallah alkali kuma MB ne ya nacewa Daddy akan lallai lallai su bar mishi aikin ɗawainiyar lawyer shi zai yi, daga zantawar da suka yi suka fahimci mutum ne shi mai kwazo kuma tsayayye akan aikinshi na kare hakkin al'umma." Tambayoyi ya fara yi mata a jere a jere.... 57 "Asabar da safe kasancewar ranar ne MB zai dawo ta ɗauki Jasrah suka tafi saloon, a chan aka" wanke musu kai ita dai bata yi kitso ba sai Jasrah ce aka yi wa kitson yara mai kyau aka saka "mata beats, aka yi musu jan lalle mai kyau daga nan suka wuce shopping sayayya sossai ta yi" wa yarinyar duk abin da ta nuna tana so sai da ta saya mata. Bayan ta shiga mota suka zauna ta kira Aina'u Bayan sun gaisa tace """Aina'u batun yarinyar nan Jasrah ne, kwananta kusan huɗu a wurina ta sake sossai kuma tana wasanta hankali kwance, kina ga zata iya warkewa har ta buɗi baki aka cigaba da tafiya a" "haka?""" Aina'u tace """Za ta iya amma fa sai dai idan ba'a sake alaƙantata da inda zata sha wahala ba, kenan idan natsuwa da farin cikinta zai ɗore kinga a wurinki tana samun kula sannan ga Aryan kika ce suna wasa, a wurin babanta daga kallo sai bacci da cin abinci take yi wurin Stepmom ɗin shi kuma azaba iri-iri, kaɗaici ne zai dawo mata daga ta koma wurinshi zata iya sake komawa halin kunci" "kuma da damuwa ta koma wurin kakan kuma kin ga bai san komai ba zai iya kaita""" """kenan dole mu nemi psychologist da zata taimaka wurin healing kuma dole ta cigaba da zama cikin yara 'yan uwanta?""" """Yauwa kin gane""" """Ba ta yadda zan kaita asibiti babanta bai sani ba, kuma bana son ya kasance ni zan sanar da shi Aina""" """Ki cigiba da kula da ita ɗin ai rana dubu na ɓarawo rana ɗaya tak zai iya zama na mai kaya""" Numfashi ta sauƙe bayan ta katse ƙiran ta kalli Jasrah dake game hankalinta kwance tayi kyau sossai cikin wando da rigarta blue and pink ga pink booth da Hibbah ta saka mata sai headband a kan kitsonta dake ta lilo. "Ita kuma Hibbah sanye take da wando Jean blue da farin bodyhug sai ta saka pashmina Abaya a kai, kanta farin jercy ta ɗaura shi sai ta yafa gyalen pashmina ɗin a wuyanta, tana shirin ta da motar wayanta ya sake ɗaukan ƙara, a hankali ta sanya hannu ta ɗauka sai ta ga" """Boss""" "Kuma Layin Nigeria ne, kenan ya dawo? Ta tambayi kanta sai ta kalli Jasrah da taji bata so su rabu ta yi picking." """Hello barka da rana Sir""" """Kina lafiya?""" Natsatse kuma dakakkiyar muryarshi ya ratsa kunnuwanta. """Alhamdulillah Sir""" """Ina dab da wurinku zan ɗauki baƙuwarki""" Ya faɗa. """Ba ma gida amma muna hanyar komawa yanzu"" ""Ok""" Yana kai nan ya katse ƙiran ta ja motar ta wuce. "Ko da aka buɗe mata gate da farar Maybach ta fara cin karo sai ɗaukar ido yake yana sheki a ranta ta raya MB ya iso kenan, ta samu wuri tayi parking ta zaga ta kwashe shopping na sun Jasrah na daga gefenta rike da tablet ɗinta suka nufi Parlorn da ta san anan zasu same shi, Dukda ta san ba wurinta ya zo ba kuma ɗaukar ɗiyarshi ya kawo shi amma ta tsinci kanta da karamar faɗuwar gaba da bugawar zuciya da ta kan rasa na menene, a hankali ta sanya kanta cikin parlorn kamshinshi da ya danne na room freshner da turaren wutan parlorn na kutsawa" cikin hancinta yana kara mata faɗuwar gaba. "Yana zaune da Aryan, Jasrah na ganinshi ta tafi da gudu ya buɗe mata hannu yana sakin tsadadden murmushinshi ta faɗa ya rungumeta, sai Hibbah ta tsinci kanta da murmushi tana" kallonsu cike da burgewa. "Four days da yayi bata ganshi ba, sai ta ga kaman watanni huɗu ne don ya kara mata" "freshness baƙi sidik ɗin gashin kanshi zuwa sajenshi sai sheki suke, daga ka ga skin ɗinshi ka ga kuɗi a kwance a hankali kuma yake tauna chewing gum." """Oya ga tsarabarku je ku nunawa Mommy, wannan kuma ki ba Mommyn""" Ya faɗa yana miƙa ma kowannensu paperbag Jasrah kuma guda biyu da gudu suka yi upstairs. "Sai a lokacin ya kai idanunsa da suka cika fal da kewanta kanta, his heart stopped for a bit" chakk ya miƙe ganin ta kawar da idanunta daga kanshi. "Cikin takunshi na zaratan maza ya nufeta tall, Calm and composed kaman koyaushe," "hannunshi duk biyu ya chusa a aljihu bayan ya isa dab da ita, ta mayar da kanta ƙasa not" knowing what to say or do. "“Kin kula da ita sosai…” he said quietly, his voice lower than she remembered. “You took really good care of her.”" "Ya sake faɗa zuciyarshi na mishi daaɗin yadda ya gansu da Jasrah, ba zai iya misalta yadda" yaji ba don he's very sure Hibbah za ta kula da ita tamkar uwar da ta haifeta. She looked down shyly. """It's nothing Sir, ai ɗa na kowa ne""" She looked down shyly. """It's nothing Sir, ai ɗa na kowa ne""" "He walked closer, too close da har tana jin kusancin ya ɗan yi yawa, ta taka baya kaɗan she" could feel her heartbeat shift daga bugawa a hankali zuwa sauri sauri. "“I trust very few people,” he continued, his gaze not leaving her face. “But with you… I didn’t" worry at all.” """Thank you""" Ta yi whispering. "Shiru ya ɗan ratsa tsakani, ya miƙa hannunshi slowly sai ta daskare cikin tunanin me yake shirin" "yi? Zuciyarta kaman zai fito he brushed something from her chin ""Snacks stain""" Yayi murmuring. "Amma hannunshi bai bar gefen fuskar nata ba Dukda yatsa biyu ne kachal, ta ɗan ɗago" "Their hearts pounding very fast, idanunsu suka sarƙe, something unspoken and dangerous na" shiga jikin kowannensu. Numfashinta har sarƙewa yake ta matsa baya tana kai hannunta inda ya taɓa ta shafa a hankali tace """Sir...""" Ya dakatar da ita ba tare da ya sake matsawa gangarta ba. """Stop calling me Sir, atleast not right now""" Ta ɗan kalleshi """Toh me zan ƙira ka?""" """Almustapha, Mustapha, Musty duk sunana ne"" Ta ɗan zaro ido ya saki smile." """Ta ya zan fara ƙiranka hakan?""" Yayi shrugging kafaɗa yana cigaba da tauna chewing gum ɗin shi in a very naughty way yace """Then sai ki nemi wani sunan but not Sir""" "Ta haɗiye wani abu da ya tsaya mata a wuya tuni tsikar jikinta ke tashi, za tayi magana sai ga" yaran sun dawo numfashi mai nauyi ta sauƙe kaman wacce ta tsere wa abin tsoro yayi mata wani kallo sai ya saki murmushi. """Bari na ɗauko Akwatinta""" Ta faɗa tana wucewa da sassarfa. Ko da taje ɗaki zubewa tayi bakin gado tana dafa zuciyarta. """Na shiga uku ni Hibbah! Kar ki yaudareni don Allah wallahi ban shirya ba""" "Hawaye ya cika mata idanu fall, da kyar ta janyo Akwatin jasrahn ta zuba mata abubuwan duk da ta saya mata ciki dama kayanta na nan intact ta janyo trolley ɗin ta shiga dakin mommy, wasu kayakin Mommy ta bata akan ta ba Jasrah da kayan ciye ciye dai har da su Dambun" nama. "Ta sauƙo har parlor suka gaisa da MB yana ta yi mata godiya ta nuna babu komai ko yaushe yake so ya kawota kawai, Aryan har da hawaye mommy ta riƙo shi yayinda Hibbah ta raka su har mota, suna fita ya sanya hannu dab nata tayi saurin zame nata ya riƙe Akwatin ya tura har boot ya saka, ita kuma ta buɗe gefen zaman banza wa jasrahn sai da ta shiga ta mayar mata" da kofa ta rufe tana ɗaga mata hannu. "Shima ya zaga ya shiga saboda motar tint ce ya sa bai ɗaga glass ba har suka gama sallamansu da Jasrah da saura kiris ta fashe da kuka, ta ɗan kalleshi ya ɗaga mata hannu ta" sauƙar da idanu tana matsawa baya ya ja suka fice daga gidan. "Washegari Monday ko da ta isa office ma ta same shi ya riga ta zuwa, dole ta haɗa files da zai" sa hannu ta shigar mishi. "Bata bari wani abu ya faru ba saboda gudun rudin zuciya ta fito fuskarta babu cikakken walwala wanda ya karanci hakan sossai amma bai takura ta ba, da rana sai ga su Daddy sun zo a office nashi yayi musu masauki ya sa aka cika gabansu da ruwa da lemu, sun jima ciki sossai kan suka fito a tare da Hibbahn suka raka su har mota shi daga nan yayi office na HR ita kuma ta koma office, ana tashi ma bata jira ya fito ba ta gudu yana tsaye jikin transparent glass na office nashi yana kallonta har ta fice daga kamfanin ya shafa kanshi yana ɗan murmushi, a fili ya furta" """Bari mu kashe wutar gabanmu mu gani idan hakan zai ɗore Hibbahhh""" "Washegari ta fita kaman mai zuwa office daga nan gida Court ta yi duk yanayinta babu daaɗi, ita bata so hakan ta kasance ba don ta san ko me zai faru ba zai mata daaɗi ba ko da kuwa" hukuntashin aka yi daidai da abin da ya aikata. "Ta samu su Daddy a wurin ta isa suka gaisa suna cikin gaisuwan ne Motar Abba ya shigo cikin kotun suna zaune a baya shi da Mum, kaman an ce ta ɗaga kai kuwa idanunta ya sauka kansu, ko ba'a faɗa mata ba ta gane makirar yarinyar nan ce da iyayenta, wani irin mugun kallo take" jefa musu har suka fito. "Ko kallon inda suke babu wanda yayi a cikin su Daddy gwara Hibbah ma sun haɗa idanu da Mum ɗin dake jefanta da kaskantaccen kallo, murmushi tayi mata tana ɗan kwantar da kai" hakan ya ƙara ɓula Mum ta ja tsaki Hibbah ta taɓe baki tana kawar da idanu a kanta. "Bayan lawyoyinsu sun iso kuma lokaci ya cika na fara sauraren case ɗin ga motar prison ya kawo Mahir ɗin sanye da orange kaya irin na prison wando da riga, duk kowa ya samu wuri ya zauna aka kai Mahir gefe ganduroban ya saka shi zama chan gefe a ƙasa, kanshi ƙasa banda" suya babu abin da ranshi yake yi. Alkalin na shigowa duk suka miƙe tsaye sai da ya zauna kan kowa ya koma zaune. "Bar. Abdallah ya gabatar da kanshi matsayin me wakiltar masu ƙara, bar. Yasir ya gabatar da" kanshi a matsayin mai kare wanda ake kara. "Karanto shari'ar aka yi ana tuhumarshi da laifin yunkurin yi wa Abokiyar aikinshi fyade, bayan nan yayi amfani da hotunanta har da forging fuskarta jikin kazantaccen video yana mata" barazana akan idan bata janye batun shigar da maganan kotu ba zai watsa duniya ta gani. "Bayan mai karanta shari'a ya zauna, Alkali ya gama rubuce rubucenshi kan yace za su iya" farawa da sauraren lawyer mai kare wanda ake kara. """My lord... Duk wannan abu da aka karanto babu gaskiya cikinta ko guda hasali ma ita ce tayi mishi baranazar idan bai nemeta ba za ta halaka ɗan uwanshi da yake matukar ƙauna kuma shi" "ne shugaban ma'aikatan""" "Daga Hibbah har su Daddy cikin ɗaurewar kai suke kallon bar ɗin dake shararo karya, ya cigaba" """Hasali ma my lord akwai shaida cikakkiya na yadda tayi ta turo masa hotunan da kanta don ta rinjaye shi, My client is innocent don ba a kanshi ta fara ba ta yi wa samari dayawa irin hakan a" "baya don biyan buƙatarta""" Wani irin Miƙewa Hibbah tayi Uncle Z ya kama hannunta ya mayar da ita zaune fuskarta a rikice take girgiza kai za tayi magana ya ɗora hannunshi a Bakinta.... 58 """Ko za ku iya gabatar da gamsashiyyar shaidar hakan?""" "Alkalin ya tambaya yana gyara glasses nashi, Miƙewa barrister ɗin yayi ya shiga presenting a projector, wasu messages ne da ya sake ɗaure kan Hibbah kuma ga layinta nan jiki WhatsApp" "message ne da date da komai girgiza kai take yi cikin kaɗuwa, duk su Daddy sun shiga ruɗani." "Bayan sun gama presenting Alkalin ya dubi barrister Abdallah ""ko za ka iya kare wacce ke karar akan wannan tuhuma?""" Ya miƙe tsaye ya juya ya kalli Hibbah ya sake kallon alkali """Zan so wacce nake karewa ta fito domin amsa wasu tambayoyi""" Ta gyaɗa kai bayan umurnin alkali ta fito ta tsaya aka sanyata yin rantsuwa akan faɗin gaskiya a duk abin da aka tambayeta. """Kin tabbatar da wanchan Layin naki ne?""" """Tabbas layina ne amma zantuka irin haka bai taɓa hadani da Mahir ba, ban san inda suka samo ba""" Ya gyaɗa kai """Zan so ki bamu labarin alakarki da Mahir daga shiganki ma'aikatan MB MUSTAPHA zuwa yanzu""" """Bautan ƙasa shine abin da ya fara haɗa ni da ɓangaren da Mahir yake, at First yana son" Magana na saboda yana loda min dukkan ayyukan da shi ya kamata yayi in yi a madadinshi "kuma ya karɓe Credits ɗin aikin daga sama, ban taɓa damuwa ba saboda ni mai son koyo ce kuma hakan na taimakamin in koya ɗin, ban fara sa'insa ko rigima da shi ba sai sadda ya nemi shiga rigar mutuncina na mareshi cikin fushi HR department su suka yi mana shari'a aka tsayar da kowa matsayarshi shi kuma aka yi suspending ɗinshi, bayan ya dawo sai ya sauya salo da ba ni haƙuri da kuma neman soyayyata na ƙi, daga dawowan MB MUSTAPHA ya fara zargin soyayya muke na kuma zaɓi MB saboda ya fi shi kuɗi wanda hakan tunaninshi ne don babu wannan zance tsakaninmu." "Watarana da safe ya zo min da bincike da yayi akan rayuwata ta baya har da shaida kasancewar ina da matsalar zuciya har yayi triggering ciwona Allah ya kawo MB ya taimaka mini kuma a ranar ya chanza ni daga ɓangaren design and strategic ya mayar da ni secretary ɗinshi, tun daga wannan rana ban sake zuwa ta ɓangaren su ba, kuma magana bai taɓa hadani" "da shi ba har ranar da aka far mini""" Numfashi Barrister Abdallah ya sauƙe """My lord idan mun fahimci labarin daidai tun farko shi ne yake nemanta ta hanyoyi daban daban don cimma mugun nufinshi, idan da gaske ita mai neman fitina ce a sadda yayi yunkurin taɓata ko rungumeta ba za ta ɗaga hannu ta mareshi ba, haka don ya dawor mata da hannun agogo baya ciwonta ba zai tashi ba. Ina so a ba ni dama in kira HR department da suka yi musu shari'a su tabbatar da zancenta kuma su ba da shaida akan kyawawan halayenta daga shigar" "ta ma'aikatan""" Director ya ƙira da wasu daga cikin manyan HR department suka yi rantsuwa suka kuma ba da kyakyawar shaida a kanta ciki har da ma'aikatan production company da tayi aiki da su lokacin IT duk sun ba da shaidar halin ƙwarai nata. Gyaɗa kai alkali yake cikin gamsuwa kan ya aika aka kira musu computer scientist ɗin su don tantace sahihancin sakonnin a karshe aka gano aikin Artificial intelligent ne a take aka soke shaidar. Murmushi barrister Abdallah yayi kan ya miƙe """My lord ina so a ba ni dama in gabatar da hujjata ta farko"" ""An baka barrister""" Ya tattaro wasu takardu kan ya juya """Ina son ganin Dr. Ngozi Ekechukwu idan tana cikin wannan court""" Sai gata ta miƙe ta fito tayi rantsuwa kan ya shiga tambayarta """A daren 11 ga watan Maris daidai ƙarfe 8 na dare ko za ki iya tuna abin da ya faru?""" Ta gyaɗa kai cikin harshen turanci ta shiga bayani """Ina cikin aikina kaman ko da yaushe aka kirani akan an kawo emergency patient cikin hanzari na nufi A&E don an tabbatar min her condition was critical, ko da na taho ganin Mustapha Bashir Almustapha na zaci mijinta ne ban tsaya tambayar ba'asi ba na shiga dubata, kayan jikinta were miserable haka jikinta akwai alamun duka musamman fuskarta amma zuciyarta ya fi" taɓuwa saboda matsalarta ina fitowa na rufe shi da faɗa anan yake sanar da ni fyade ne aka yi "yunkurin yi mata God sent him, kuma yana son statement na sanar da shi akan sai an kawo police ba'a kwana ba muka fitar da statement ɗin nan na harrasment da attempt raped""" Tayi magana tana nuna papers na hannun Barrister Abdallah shi kuma ya miƙa gaba don a isar kan teburin Alkali. Komai ya fita clearly aka ba Dr Umurnin zama. """Ko akwai hujjar soke wannan shaida da lawyer me kare wanda ake zargi zai gabatar""" Ya miƙe tsaye """Babu My lord""" Bayan 'yan rubuce rubuce yace """Ehen barrister Abdallah you can continue""" Ya miƙe """As you pleased My lord... Shaidana na gaba shi ne mai kamfanin da duk suke aiki wato Almustapha Bashir, idan kana kusa bismillah""" "Babu wanda ya ga shiganshi a cikinsu ganinshi kuma ya kada ƴar hanjin Mum, wani irin kallo" take mishi zuciyarta na tafasa ya tabbata daga Mustapha ya ba da shaida akan danta mummuna sai ta ga ƙarshenshi itama ta karfin tsiya. Bayan rantsuwa barrister ya tambaye shi """Karfe nawa ne lokacin tashin ma'aikatan ku?""" """4pm dot shine ka'idar tashin mu amma some work pass closing time saboda muna da tsaro""" Kai barrister ya gyaɗa """Kuna da tsaro? Toh me ya ajiye ita Hibbah ita kaɗai a office har irin wanchan lokacin?""" """Kaman yadda na faɗa maka barrister ana iya aiki pass closing hour""" """kenan da haɗin bakin Security ɗin naku aka shiga aka far mata? Ko kuma an san zata yi daren ne aka shiryawa hakan?""" "Sai a lokacin wani abu yayi clicking a brain na MB ya ɗago yana kallon barrister ɗin, bayani ya mishi akan he fired one of his employee a ranar saboda kamata da aka yi da laifin lalata aikin company don ta ɓata Secretary ɗinshi Hibbah, she claimed son zuciya ne kasancewar kuma" aikin urgent ne dole Hibbah ta kai dare don ta ƙarasa. Barrister ya juya ga alkali """My lord wannan shari'a ya ɗauke mu zuwa wata hanyar kuma daban idan ba damuwa muna roƙon da a ɗaga wannan shari'ah har sai mun tabbatar da Shigowar wannan ma'aikaciyar hannu don tuhumarta yadda ya kamata""" "Bayan rubuce rubuce alkalin ya amince da daga zaman zuwa sati guda, barrister Yasir ya miƙe ya roki da a basu belin Mahir don samun natsuwar cigaba da bincike amma a take aka ƙi" """The court May not Grant bail because of the seriousness of the offense... Courttt""" Ya buga gudumar duk aka miƙe ya fice jama'a ma suka fara fita a hankali. "Don kawai Mum ba za ta iya tsayuwa a fitar da Mahir a saka shi a motar kurkuku bane ya sa ta matsawa Abba suka yi saurin tafiya amma ta so ta ci mutuncin Mustapha, ta so ta mishi Allah ya isa na rainon da ta mishi don ya gama kaita makura a yau, ji take kaman ta yi bindiga don" kan su isa gida kuka take jikinta rau da zazzabi. "Ita kam Hibbah Daddy ne ya fito da ita hannunshi riƙe da nata don tunda kirjinta ya buga a gabatar da hujjar karya da lawyern Mahir yayi bata sake shakar numfashi daidai ba, ko gani da kyau bata iya yi, basu tsaya ba ya shigar da ita mota ta kwanta Ko motsin kirki MB MUSTAPHA ya kasa yi, zuciyarshi na mishi wani irin ciwo da zafi na ganinta cikin wannan hali, tausayinta da sonta na kara lullube duk wani sassa na jikinshi suna tsuma shi da son isa gareta ya rungumeta" har sai ta ji ta manta duk wani tarin damuwarta sai dai babu wannan hali. """Almustapha""" "Daddy ya ƙira shi, a hankali ya mayar da idanunshi da suka sauya kan Daddyn." """Za mu tafi zamu fara kaita asibiti daga nan zan kaita gida da kaina""" Ya ɗan sauƙe numfashi """Shikenan Alhj, amma ta huta kar ta sake zuwa office sai an kamallah wannan shari'ar don a" "haka ba zata iya tabuka komai ba, sannan don Allah kar a manta da batun riƙe alkawarinta na" "kar kowa ya sani a cikin danginta bayan ku""" Murmushi Daddy yayi """In shaa Allah za'a riƙe, Mun kuma gode ƙwarai da taimakonka a kan Hibbah""" """Abin da kowani shugaba ya kamata yayi kenan Alhj""" Daddy ya ɗan buga kafaɗarshi kan ya juya yayi joining nasu motocin su biyu suka fita daga court ɗin daya na Hibbah ɗaya kuma wanda Almustapha da ya ɗauki nauyin masaukinsu da kyar shi ya bayar da driver ya kaisu duk inda suke so. "Da idanu ya bi su yana jin kaman sun cire wani ɓangare ne na jikinshi mai muhimmanci suka tafi da shi, rufe idanu yayi rufff yana jin son kasancewarshi da ita na trippling mishi amma babu wannan hali, ya san sati da zai yi bai sanyata a idanu ba will be a worst week for him saboda ta" gama da zuciyarshi da ma tunaninshi. Bayan sun dan yi magana kaɗan da Mubarak da kuma Abdallah ya nufi motarshi driver ya buɗe masa ya shiga ya ja suka fice daga court ɗin. Kaman yadda Daddy ya faɗa sun je asibiti aka duba ta sun so kwantar da ita amma ta ƙi sam aka bata magunguna ya karɓi motar daga zubair yace ya bi su Yaya Rabi'u su koma masauki shi zai mayar da Hibbah gida. "Har cikin gida ya shiga sai da ya zauna Hibbahn ta kwanta kan ya ɗaga waya ya ƙira Mommy, mintuna uku basu cika ba sai gata nan ganin Hibbah a haka ya ɗaga mata hankali amma Daddyn ya tabbatar mata jiki ya yi sauƙi ta kwantar da hankalinta." """Na shigo ɗan wani aiki ne na biya in dubata kuma na samu bata jin daaɗi shugaban ma'aikatan" "na shirin dawo da ita ko kiran Nasir ne nace ya bari bari mu taho""" """Sannu Hibbah Allah ya baki lafiya, wannan ciwon kirjin dake matsa miki Allah ya yaye ya cire miki duk wata damuwa""" Daddy ya amsa da Ameen. "Mommy ta kira kitchen aka shigowa Daddy da abubuwa dayawa aka cika gabanshi, ta kama" Hibbahn zuwa sama bayan ta kwanta ta fito zuwa ɗakinta ta kira Zaitoon da Nasir da Abdul. Daddy bai tafi ba har dare akan ya ce musu gobe da safe ne zai tafi amma ba Kano ba Abuja za shi. Duk yaran Mommyn sun zo sun gaishe shi anan ne ma suke samun labarin ai auren Asma'u kam babanta wani watan ya saka akan babu abin da za'a jira. "Shi dai MB bai san ma inda zai yi ba, gidanshi ne ko gidansu ko office duk inda ya tuna sai ya ji baya son zuwa shi dai wurin Hibbah kawai yake son ganin kanshi amma ba zai takurata a irin" "wannan moment na rayuwarta ba, idan ya matsa ya tabbatar har shi za ta iya tsana." Gidansu yayi amma Mum ta dinga mishi kuka da maganganu marasa daaɗi har gorin uwa tayi mishi da ya saka shi tantamar anya ita ɗin ce? Ya yi mata uzuri saboda ya san zafin abin da ke tunkaro ta don haka ya fice daga gidan. "Hibbah tun da Daddy ya shigar da ita bata sake fita ko harabar gidan ba, komai na legos na fita mata a kai a hankali, ji take tana so ta bar garin, da Mahmud ya aureta tun farko da duk wannan abu dake faruwa bata sanshi ba kuma bata yi going through ba amma babu yadda ta iya da kaddara da ya riga fata, wayanta a kashe through out the week don bata son Magana da kowa," daga ta sha magani sai bacci don akwai na saka baccin har satin komawa court ya zagayo. "Ta fito tacewa Mommy zata tafi office, Allah ya tsare mommy ta yi mata don ta sake alama jikin yayi kyau, tana fita daga gidan ta kunna wayanta yau Yasmin Abaya ce maroon colour jikinta ta yafa gyalen kawai a kanta da bata wani damu da saka mishi hula ba ta dai yi parking gaban a kwance lublub. Kiran Daddy ne ya shigo mata, bayan sun gaisa yake tambayar ta fito ne su sun" kusa court tace mishi ta fito sai ya yanke call ɗin. "Tana shiga court ɗin motar MB na shigowa, driver ne ya buɗe mishi ya sanyo jiki waje sanye da baƙin shadda da ya wani irin haska shi cikin ɗinki na zamani da yayi, har hula ya saka da cover shoe dinshi mai tsadar gaske, haɗa idanu suka yi bayan tsawon sati ɗaya yana wahala da rashin ta, ya kashe darare dayawa bai yi bacci ba saboda tunaninta haƙiƙa a yanzu babu abin" da ya isa ya saka shi nesa da ita ko itan ce a karan kanta. "Shigar da idanunshi yayi cikin nata ya riƙe yana karantar yanayinta, ta ɗan faɗa kaɗan ta ƙara haske kuma fuskarta ya rage walwala, ya ɗan lashi lip ɗinshi na ƙasa kan ya shiga takawa cikin karsashi yana nufanta kuma har lokacin idanunshi basu bar kanta ba, sai da ya iso dab ita ya" tsaya ta sauƙar da nata ƙasa. """Good Morning Sir""" "Ya sauƙe numfashi mai nauyi muryarta mai sanyi na ratsa shi, a fusge yace" """Sir Againn...""" Bata ce komai ba sai gyalenta da ta kama nervously tana wasa da ƙasan. """Hey how is ur Health?""" He utters slowly and gentle cike da kulawa. """Na ji sauƙi... I'm Ok now""" """You don't look okay,"" he said, almost in a whisper, kuma cikin kokarin hana kanshi kai hannu" "ya riƙo nata, ba zai iya fasalta kewanta da yayi ba but he knows a situation ɗinta bata son gaggawa." Yadda yayi maganan something in his voice broke through her walls. """I'm just tired, na gaji da komai Sir i want peace, i want quite kila mutuwa shi ne abu mafi sauki da zai samar min da irin natsuwar da nake """ """Shiiiiiii""" "Ya faɗa da hanzari moving a little closer, just enough for his presence to feel warm, steady." Ta sauƙe idanunta cikin son hana kanta fashewa da kukan da ba ya tashi zuwa mata sai a kusa "da shi, kila shi kaɗai ya iya lallasan zuciyarta irin yadda take so, wani abu ya mitsineta jin Muryarshi" """Look at me,"" he said softly. She hesitated... then slowly did." "And the moment their eyes met, he spoke again, cikin raɗa da tabbatarwa" """You are not dying...not now not even hundred years masu zuwa, komai zai wuce kina ji na? Za" "ki yi farin ciki za kuma ki samu aljannah silar haƙuri da kaddara da kika yi, kar ki gaji continue" "enduring... Lokaci kaɗan ya saura""" "Her lips parted, but no words came out wani abu ta haɗiye then a tear slipped down her cheek" before she could stop it. "Without thinking twice ya sake matsawa har kamshin jikinsu na gaurayuwa, ya sanya thumb" ɗinshi ya ɗauke hawayen zai yi magana suka ji an ce.... 59 "*My BP had been dropping rapidly tun jiya fama nake da su gishiri, coke and ORS jiri da ciwon" kai bai bar ni ba so manage please* """AL-MUSTAPHA!""" "Yadda tayi maganan da ƙarfi ya sa duk suka juya suka kalleta, hawaye take zubarwa tana" kallonshi """Me nayi maka da zafi haka da zaka nemi dasa min ƙunci a raina? Bayan shirin ɗaure yarona" "da kuke yi ashe da gaske har da neman wannan ƙaskantacciyar munafukar kake?""" "Ya sauƙe numfashi yana ɗan matsawa baya, sam ba ya son irin maganganunta gareshi, yana kuma yi mata uzuri saboda da zafi ganin ɗanka cikin mawuyacin hali, yana adu'ar Allah ya sa ta gane cewa ba kiyayya ba ce gata ne na gyara yake ba da goyon bayan a ɗauka akan Mahir amma ita tayi nisa." """Mu...""" Hannu ta ɗaga mishi """Bana son jin komai daga gareka, ka kyauta Mustapha"" Daga nan ta wuce su da sauri tana kuka." "Abba da yake tsaye chan bayanta ya tako ya matso ba tare da ya ce komai ba, Hibbah tace muryarta a sanyaye" """Ina kwana?""" "Kallonta yayi yana jin idan ɗiyarshi ce tayi going through abubuwan da Mahir yayi ta mata ya zai ji? Last barin su court sun yi rigima sossai da Mum don bai san tana shirin juya shari'ar da kazafi ba har yake ce mata ya godewa Allah da kwarewar lauyer ɗin yarinyar idan ba haka ba da sun aikata kuskure, Dukda yana son Mahir kuma baya so ya ga ya wahala sai dai bai san halin Mahir ɗin na iya zama haka ba ko da ba'a ƙare shari'a ba alamu duk sun nuna shi ne babu" gaskiya a lamarin shi. """Lafiya ƙalau""" "Ya amsa mata kan ya wuce yana ɗauke kai daga Mustapha, kanshi a ƙasa har Abban ya wuce" ta bi shi da kallo tana karantar yanayinshi. """Mu je ko?""" "Ya faɗa bayan yayi snapping out daga matsalar shi shi ya san irin raɗaɗin zuciya da yake shiga idan ya ga Abba ko ya gaishe da mahaifinshi bai amsa ba, gashi yanzu ba Abba kaɗai ba har" Mum yana cikin Black list ɗinta. "Jerawa suka yi suka nufi cikin court ɗin, bayan kowa ya gama zama chan sai ga Alkali ya fito" duk suka miƙe tsaye bayan ya zauna aka karanto shari'ar da za'a cigaba. """Lawyer me kare wacce ke ƙara ko an samu gamsassun hujjoji bisa kwanakin da kuka nema na" "sake bincike?""" Barr Abdallah ya miƙe """My lord komai ya kamallah, a ba ni dama na fara gabatar da komai ɗaya bayan ɗaya"" ""an baka""" """Ina neman Raliyat a gaban court""" "Wata police macece ta saka ta gaba har wurin da ake tsayawa don amsa tambayoyi duk ta sauya ta rame, hannu ta ɗaga tayi rantsuwa akan faɗin gaskiya idanunta na zubar da hawaye a lokacin da Barr ya tambayeta za ta iya zayyane duk bayanin da ta mishi? Ta fara magana ""Haƙiƙa hassada mugun ciwo ne, shaiɗan ya darsa min hassada da kyashin Hibbah tun ranar da na kyalla ido na ganta cikin department ɗinmu tana aiki cikin ƙwarewa da kwazo, idan na tuna irin wahalar da na sha kafin na samu aikin na tuna ita kuma daga zuwa bautar kasa wai an bata aiki sai in ji baƙin ciki musamman da na kula zata yi min shigar sauri, tun ba'a je ko'ina ba har ta fara gabatar da manyan projects kuma kowa a kamfani ya fara saninta cikin lokaci kankani, daga nan na fara cusa kai a wurin Mahir ina sanar da shi duk wani motsinta sanin" shima yana da interest a kanta amma ita baya gabanta. "Ni na tunzuro shi ganin alaƙa na shirin sarƙewa tsakaninta da MB wanda ko ni da nake shekara na wurin takwas kamfanin magana bai taɓa hadamu na sama da seconds ba don gaisuwa ce kawai, a tare muka yi bincike akan past ɗinta inda muka fahimci duk wani hali da take ciki yayi amfani da hakan don yi mata barazana sai kuma Almustapha yayi intervening daga nan ma a maimakon tayi baya sai tayi gaba hassadata ta sake ninkuwa a sadda na samu labarin wai an mayar da ita secretary, har kukan baƙin ciki sai da nayi ni na samu Mahir nayi ta zuga shi akan bai kamata ya haƙura ba, idan ba zata bashi kanta ta sauƙi yadda take ba Almustapha ba ya kamata ya san hanyar da zai bi Almustapha ya koreta in ya so sai ya bi ta bayan fage ya neme" ta. "Ya yarda da shawara ta amma shima yana plan against nawa, a bincikenmu muka san tana aikin wani proposal mai muhimmanci, ni ce naje da salon gaisuwa tunda ban taɓa shiga office ɗin nata ba tunda ta koma na fara roƙonta yafiya, cikin sa'a MB ya ƙirata ta tashi nayi amfani da damar na ɓata mata aiki duk don a koreta amma sai reshe ya juye da mujiya a karshe aka koreni, a ranar ne nayi snapping back to reality Me zan yi gaining a cutar da Hibbah? Me tayi min da hassadata ta sa nayi sanadiyar aikina ga ni da yara da ni ce nake wahalarsu? Ina amfanin hassadar alhali Hibbah tausayi ma nake bata, na kasa fahimtar cewa ko da aikin nan ko babu ita ɗin mai rayuwa ce cikin wadata da gata. Sannan ta ji ciwon rasa aikina da nayi har ta shiga gaba wurin roƙa mini MB ko zai yi haƙuri in cigaba da aikina. Da wannan baƙin cikin na bar company daga nan ban san me Mahir ya cigaba da planning ba kuma amma wallahi na yi nadama kuma na tuba tuba ta gaskiya sharrin zuciya da kuma shaidan ne""" Ta ƙarasa da kuka sossai. Dayawa girgiza kai suke suna mamakin sharrin zuciya haka kawai mutum bai yi maka komai ba ka ta kulla mishi sharruka? """Za ki iya komawa ki zauna""" Taje ta zauna tana rufe fuska saboda kunya da damuwa. """Hujjana na gaba shine Security da ya kasance da haɗin bakinshi wurin aikata komai"" ""Bismillah Barrister""" "Alkalin ya faɗa bayan cigaba da rubutunshi. ""Yaya sunanka?""" """Sunana Victor""" """Ko za ka iya gaya mana gaskiyar sahihancin abin da ka sani?""" "Ya daku iya azabtuwa wurin DSS kan suka miƙa shi wurin police, sannan ga rantsuwa da yayi da bible ba zai taɓa iya yin karya ba don son zuciya ce ta kwashe shi amma shi ɗin kirista ne na ƙwarai." Cikin kuka da nadama ya fara bayani """Sir Mahir came to me a sadda nake cikin matsala da damuwar neman kudin haihuwar matata, za'a yi mata aiki ne ga bukatun asibiti ga kuma mother ɗina ma ba lafiya, salaries ɗina ba zai ishe ni ba a watan ko da ya zo min bugu ɗaya ya damka min dubu ɗari biyu ya kuma ce min aikin mai sauki ne idan na yi successful zai ƙara min dubu dari biyu." "Yana so in saka ido in ga sadda MB zai bar office, sannan in kula da Secretary ɗinshi har zuwa yamma don a yadda ya santa da aiki ba zata bari kamfani tayi asaran kudade dayawa na aikin da Raliya ta ɓata ba, yadda kuwa yayi hasashe MB ya fice da wuri a ranar, sai da na ga fitar duk ma'aikatan kan na kira Mahir na sanar da shi, ina cigaba da kula har ya kirani yace in je in cire fuse na kamfani babu musu na je na cire don na san shi tun safe yana cikin kamfanin bai fita ba, ko da na cire a wurin na ajiye na koma ta gaba ashe na je kashewa MB ya shigo, ganin motarshi ya sa nayi gaggawar kiran Sir Mahir na sanar da shi ya samu yayi escaping da kyar. I'm terribly sorry na amshi laifina a min sassauci ko don mahaifiyata da matata with our New born twins""" Cikin kuka ya ƙarasa shima dai da nadama. """Ko anan muka tsaya na tabbatar kotu ta gama gamsuwa da cewa Mahir mai laifi ne, shaida ta ta karshe shine sakonnin shi na barazana da calls nashi gareta wanda ya zama tamkar Blackmailing""" "A projector aka dinga saka sakonnin ana tantacewa da tabbatar da ba aikin AI bane karshe record na calls ɗinshi da bata san taya suka samu daga wayan ba da MB ya karɓa suka yi playing komai ya fita ga muryarshi, a lokacin hankalinshi da na mahaifiyarshi ya gama tashi ""Ina roƙon wannan kotu mai adalci tayi gaggawar yankewa Mahir hukunci ko don kariya ga" "sauran 'yan baya. Na gode Sir""" "Barr yasir ya zama tamkar an jiƙa tsumma a ruwa tsabar mutuwar jiki, ba ta inda zai bugi Barr" Abdallah. Bayan dogon rubuce rubuce Alkalin ya sa aka fitar da Mahir """Ka amsa laifinka na shirin aikata fyade da kuma Blackmailing na victim ɗin da hakan ya jefa ta cikin tsananin mawuyacin hali da ciwo?""" """Na amsa""" "Ya faɗa da kyar kunyar duniya duk ya tarar mishi, ya kasa ɗaga idanu ya kalli kowa uwarshi da ta ɗora shi kan mummunan turba ta kasa kareshi, da ta kasance mai kyakyawar tarbiya a gareshi da duk haka bata kasance ba, bakin ciki da hassada tare da sanya rai akan dukiyar MB da bakin cikin cigabanshi na rayuwa shi ya kaisu aikata laifuka masu yawa da a yanzu yake jin" suna daɗɗaure jijiyoyin shi. """Wannan kotu mai adalci bayan tsawon bincike da kuma tarin shaidu, ta yankewa Raliya tarar dubu ɗari biyu da kuma watanni uku a gidan yari na taimakawa ɓarna, ta kuma yankewa Victor wattani goma sha huɗu a gidan yari shima na taimakawa ɓarna, sai shi karan kanshi Mahir ƙarƙashin dokar criminal code Act za'a iya yanke mishi hukunci na laifukanshi guda biyu daban daban amma za mu yi amfani da consecutive sentence wannan kotu mai adalci ta yanke masa tsawon shekaru goma sha biyu a gidan kaso idan bai gamsu da wannan hukunci ba yana iya daukaka ƙara zuwa 12 ga wata mai kamawa. Courrrrtttt""" Aka buga guduma. "Kuka sossai Mum ke yi tana Miƙewa ta tafi zata faɗi da sauri MB ya nufeta zai taimaka mata don zuciyarshi ya matukar karyewa shi karan kanshi, ta sa hannu biyu ta hankada shi" """Kar ka taɓa ni Almustapha kar ka yarda hannunka ya sauƙa jikina """ Abba ta riƙo """A'a.... A'a ka ce min ba gaske ba ne... Ka ce min ba Mahir ɗina bane zai yi shekaru dai dai har sha biyu prison... Don Allah ka ce musu shekarun sun yi mishi yawa kwata kwata nawa yake? Bai fa aikata fyaden nan ba kuskura ne... A""" Bakinta Abba ya rufe jikinta na wani irin kyarma. """Shhhh ki yi shiru, ki natsu kar ki ja wa kanki wani ciwon""" Da kyar ya riƙeta akwai wasu danginta tsirara da suka zo duk laifin MB suke gani har suna cewa """Ɗan wani ai dama sai Allah, ka gama rainon ɗan maciji ya juya ya watsa maka dafi""" Suka taya Abba fita da ita don Mahir ma ana janshi yana kuka akan a sassauta mishi sharrin zuciya ne. "Iyalan Victor gaban Hibbah suka zo suka zube suna ta roƙonta yafiya, tace a hankali" """Na yafe mishi""" Kuɗi ta cire har 100k ta ba matar da ake rike mata da 'yan biyu ta kuma karbi layinsu akan zata neme su ta ji jikin mamanshi. """Eyyyyyyyoooo you have a pure heart ma, May God shower you with his blessings thank you, thank you""" Cikin kuka take sake mata godiya da kunya don kayi sharri ma a mayar maka da alkhairi ba ƙaramin kunya da nauyi yake ƙarawa ba. Raliyat ma ta nufeta ta tsaya don bata haƙuri sai Hibbah ta dafa kafaɗarta """Kin jima da neman yafiyata kuma na yafe, zan yi ƙoƙari bayan kin fito ki koma bakin aikinki" sannan ki ba ni Layin da zan samu iyalanki in tayaki kula da yaranki har ki fito fatana dai Allah "ya sa hakan ya zama izina a gareki, ki kuma dage da ibada da roƙon Allah ya cire miki duk wata" "hassada daga ranki""" Ta datse haƙori tana girgiza kai cikin zub da hawaye """Na gode Hibbah, Na gode sossai"" Layin ta bata aka wuce da ita itama." "Tuni su Daddy suna haraba, ta juya da nufin ficewa kawai idanunta suka faɗa kanshi har" lokacin yana zaune shiru. "Ta ji zuciyarta babu daaɗi amma ta san ba Saboda ita bane mugayen halayen Mum ke bayyana a gareshi dama tana so ɗin ya san matar bata kaunarshi, amma halin da zai shiga take dubawa, ta yi amfani da shi tun yana da ƙaramin kwakwalwa ta juyar da kanshi akan cewa ita ce mai" tsananin kaunarshi sannan ta zaga tana cutar da shi irinsu hatsarin su ya fi shaiɗan. "Dab dashi taje ta zauna, duk bai ji motsinta ba sai da tayi magana ""Sir!""" Ya buɗe idanunshi dake lumshe ya kalleta ta kawar da nata gabanta na ɗan faɗuwa duk sun shanye sun zama wani iri don a take duka tsikar jikinta suka tashi. Ta haɗiye miyau """Sir I'm so sorry sanadiyata ka sanya kanka cikin wata matsalar da har ake ganin ka rama halarci da butulci, lemme tell you something... Ko da hallacin Mum tayi maka wannan abu da ka yi ba sunanshi butulci ba sunanshi gyara kuma abin da ya kamata ne, wannan jarumta da ka yi a kan ɗan uwanka ba ya nuna kiyayyaka gareshi bane sai soyayyar shi, mai sonka ne kaɗai zaka yi kuskure mai girma ya karkato da kai hanya, baka ji abin da aka cewa prison ba? 'Gidan gyaran hali' i believe idan har Mahir yayi nadama ba zai yi wasa da damarshi a prison ɗin nan" "ba, zai gyara kuma zai chanza zuwa mutumin ƙwarai wanda duk Credits ɗin gareka ne.""" "Tamkar ruwan sanyi take zuba mishi a zuciya, kalamanta na fita da tsananin taushi da harshen lallashi yana tasiri a dukkan gabɓanshi a yau da ita ɗin ta halatta mishi babu abin da zai hanashi rungumeta tsammm har sai ya ji duka sauran damuwarshi sun ƙarasa guduwa." Idanu ya zubawa lips ɗinta da ta cigaba da cewa gently """Dole Mum za tayi fushi amma with time zata fahimce ka, so kar ka damu kanka ka ji?""" Yadda ta ƙarasa da lallashi tamkar da Jasrah take hakan ya sa tsiririn murmushi kubce mishi da "har ta iya kallon fararen jerarrun hakwarinshi masu haske kwarai, itama ta ɗan murmusa shyly" tana Miƙewa. Ya miƙe shima suka fito a tare bai dai ce komai ba amma da alamu ya manta da duk wata damuwa sanadiyar tasirinta a zuciyarshi. "Su Daddy idanu suka zuba musu har suka iso su, hakan ya sa Hibba taji nauyi da kuma 'yar damuwa kadan kar fa su Daddy su fara wani tunani na daban a kansu alhali ita dai hukuncin ta na babu ita babu aure na nan daram babu inda ya je." """Sannu da ƙoƙari Almustapha, Mun gode kwarai da gaske""" Ya girgiza kai cikin ladabi yace """Babu godiya a tsakaninmu Alhj kaman yadda na faɗa maka cewa abu ne da zan iya yiwa" "kowani ma'aikacina, bare ma Hibbah da ta kasance ma'aikaciya ta daban da wanzuwarta a kamfanin ya kawo mana tarin nasarori fiye da kowani lokaci""" "Uncle Z shi dai ya so a sakata a gaba ta koma gida gabansu kawai amma Daddy Rabi'u ya nuna yana tare da hukuncin Daddy a barta tayi yadda take so tunda anan ɗin ba wai ta watsar da tarbiyarta bane, ko shaida da aka bayar a kanta daga company ya tabbatar da she's doing well and tana nuna legacy na gidansu, sun fi karfinshi don haka dole ya sallamar, already flight nasu na yau ne karfe uku don sun san yau dai za'a karkare shari'ar so sun fi booking, ta so raka su Airport suka ce a'a ta koma gida kar tayi yamma sossai waje hankalin Mommy ya tashi dole tana gani suka tafi tana ɗaga musu hannu zuciyarta kal na yadda Daddy ya nuna he's very" proud of her and will always be. "Har zata nufi motarta MB yace ""Hey!""" Softly and Calm as always. Ta ɗan waigo sai ta ɗan yi pouting kaɗan tana murmuring abin da bai ji ba ya kalli bakin very cute ya ɗan datsi lip ɗinshi yana gyara tsayuwa """Ni kika yi wa Allah ya isa?""" "Ya ƙarasa da ɗan ɗage gira ɗaya. Ta zaro pretty eyes ɗinta gabaɗaya ""Ni? Yaushe??""" Tayi maganan a Shagwaɓe kaman za ta saki kuka. 'Ya a Salammm! Anya yarinyar nan bata yi mishi asiri ba? His heart started to pound very fast a hankali ya zaro kalaman """Me maraban Allah ya isa da zage zagen da ki ke ta yi?""" """Zage zage? Ni fa ba zage zage nake yi ba I'm just saying i don't like it when you call me Hey after all ga sunana""" Ya ɗan kama kunnen shi surrendering """Then ki yi haƙuri ba za'a sake ba""" Sai kunya ya rufeta. """Bye""" Ta faɗa tana nufar motarta da sauri ta buɗe ta shige bata jira motsin shi ba ta kunna ta fice don ta san zai iya cewa zai kaita and ba zata iya cigaba da tsayuwa da shi ba zuciyarta zai iya fitowa ta baki bata sani ba… 60 *Alhamdulillah! Na ji sauƙi na gode kwarai da adu'o'i. Masu comment ina matukar godiya expecially Habeebarh Allah ya saka da alkhairi i truly appreciate you. Ku yi comment da duk abin da ke ranku ku samu wani Page ɗin karfe sha ɗaya da rabi in shaa Allah idan kuma ban ga motsi ba sai gobe da daddare idan Allah ya kaimu* "Washegari ta ɗan makara wurin zuwa, tana fitowa sai ga Yaya Nasir shima ya fito a shirye. ""Yaya Nasir ina kwana?""" """Fine Hibbah kin tashi lafiya?""" """Sai ina haka da safen nan? Ko tafiya ne ya tashi ba shiri?""" """Haba dai na isa? Hutuna da sauran sati guda MB ya ƙira ni zan mishi wani aiki ne a ɓangarena""" Ta sauƙe numfashin jin daaɗi """Wallahi kaman ka san kyueyar driving nake fama da shi yau ɗin nan mu tafi kawai da motarka"" Suka nufi motar a tare yana cewa ai dama jiki da jini don ma tayi ta hutawa last week saboda rashin jin daaɗi da bata yi ba." "Yana tsaye jikin glass ɗin office ɗin ya zubawa gate ɗin kamfanin idanu ya jima tsaye wurin hannayenshi zube a aljihu, Wine colour suite yasa da ya zauna mishi dass haka takalmin kafarshi kalar suite ɗin ce da surkin baƙi agogon Richard miller ne kalar Wine ɗaure a tsintsiyar hannunshi, ban da sassanyar kamshin turarukanshi babu abin da ke tashi a office ɗin, gyara tsayuwa yayi a karo na ba adadi yana sakin tsiririn tsaki, babu abin da idanunshi ke mararin gani zuciyarshi ke yunwar arba da irinta, yau da alama ta makara wayanshi ya zaro zai ƙirata" sai ya ga an buɗe gate. "Motar Nasir ce ta shigo Dukda bai san motar ba ya dai ɗan zubawa motar idanu har ta yi parking yana shirin kawar da kai ya hangeta tana zaro jiki daga cikin motar, wani irin dokawa zuciyarshi tayi sai ta tattare ta matse wuri guda, har a fuskarshi yana nuna bai ji daaɗin ganinta gaban motar wani ba ko kuma yace kishi ya ji duba da yadda tayi wani irin kyau cikin fararen kayan da ta zaɓi sakawa yau, wando ne mai yanayi da palazo amma ba mai faɗi sossai ba ta ɗaura kan wani baƙin riga, sai ta ɗora farar saman wandon da ya sauka mata har wurin gwiwa Dukda bai da maɓalli ko zip, baƙin takalmi heel na hermes ne kafarta yana da surkin kalar diamond tana taku cikin aura da confidence ɗinta as usual, lip nashi da ya ɗan yi dry ya lasa yana kai idanunshi sama, baƙin scarf ne da ake cewa vintage ta mishi dauri a kanta yayi mata kyau sossai don ya bayyana bakaƙen fashion ear rings ɗinta hannunta riƙe da baƙin handbag" "na hermes, magana suke da Nasir fuskarta a sake cikin murmushi suka jero tare." "Idanu ya ɗan runtse bayan sun ɓace mishi, ba ya jin zai iya cigaba da danne abin da yake ji a kanta, sonta, mararinta, kishinta, tunaninta duk su ke shirin illata natsuwarshi." Knocking da aka yi kofarshi ne ya sa ya ɗago a hankali sai ya taka ya bar wurin ya dawo kan kujerar shi ya zauna kan ya ba da izinin shigowa. Nasir ne ya shigo suka gaisa yadda suka saba tsakanin shugaba da ma'aikaci ya bashi aikin da yake so a mishi a kamfanin sun ɗan jima suna tattaunawa kan Nasir ya miƙe ya fice. "Ya janyo system ɗinshi ya buɗe tare da fara 'yan wasu ayyuka amma hankalinshi na ga son ganinta, kaman kuwa ta sani ta saukaka mishi tayi knocking ta shigo." Bai ɗaga idanu ya kalleta ba har ta iso dab table nashi. """Good morning Sir""" Sai a lokacin ya cire idanunshi ya zuba mata sai ya fahimci har da nude makeup a fuskarta tayi mishi kyau fiye da koyaushe. """How are you?""" Ya faɗa a hankali yana jingina da jikin kujerar tare da ɗaura hannunshi kan haɓarshi yatsarshi ɗaya na ɗan shafa lips ɗinshi. """Alhamdulillah, wannan su ne takardun sauran proposal ɗin chan na production company muna" "buƙatar ka saka hannu kan in yi presenting""" "Ya kalli takardun sai ya kalleta ""Kin gamsu da ideas ɗin?""" Ta gyaɗa kai """Sure Sir, shigo da sababbin injuna wanda babu irinsu anan ko da zai zama da tsada sossai ribarmu ne don dole mu za'a kawowa duk wani aiki da ya shafi injunan daga manya da kananun ma'aikata har ma wasu garuruwan so ka ga babban nasara ce hakan ma""" Kai ya gyaɗa irin kallon da yake yi mata ya sa bata iya kallonshi ko sau ɗaya ba har ta gama "maganan, sai ma office ɗin da take ɗan juya idanunta a ciki." """Jasrah bata nan tana wurin Mum!""" "Bata san ta kalleshi ba idanunta na nuna firgici da tausayi, ganin zai iya karantarta ya sa ta" sauƙe idanun tana kirkiro murmushin yake """Da wani abu ne Miss Mudassir?"" Ta girgiza kai." """Ba komai""" "Ta faɗa a sanyaye, sai ta juya za ta fita" """Waitt!""" Ta tsaya tare da Juyowa """Zan duba wannan amma ba yau ba, ki shirya board meeting a gabatarwa sauran masu ruwa da tsaki a kamfanin idan kowa ya gamsu then we will risk our money for that""" "Ta gyaɗa kai ""Ok Sir""" "Daga haka ta fice, a kan kujerarta ta zauna tana raya Allah sarki Jasrah, hawayen tausayinta ne ya cika mata idanu Allah kaɗai ya san me take facing bayan rage da Mum ɗin take ciki na rufe ɗan ta, numfashi ta sauƙe tana tsintar kanta da yi mata Adu'a don bata san me za tayi ba, ba za" ta iya fara sanar da shi ba saboda bata da wani hujja ko shaida. Ta ya ma zai fara yarda? "Har gab lokacin tashi hankalinta ba'a kwance ba, sun fita zuwa wani meeting sun dawo, sannan" "ya yi ta yin baƙi yau ɗin har gab lokacin tashi, Nasir ne ya shigo ya kamallah komai bayan ya shiga ya gabatarwa MB ɗin ya fito." """Kin kamallah abubuwanki mu wuce?""" "Ya tambaya yana zama idanunshi a kanta, har abada ba zai daina jin bugun zuciya akan Hibbah ba, ko a yanzu da ta kalleshi suka haɗa idanu sai da ya ji zuciyarshi ta motsa, danne yanayin yayi bai bari ya zo kan fuskarshi ba tace tana mayar da idanunta kan computers ɗinta. ""Yeah na kamallah, bari na sallami boss ya san na wuce""" "Ta kashe tare da ɗan tattare wurin, sweet da ta jefa a Bakinta take ɗan tsotsa har ta haɗe komai ta nufi office na MB bata jima ba ta fito tana mamakin yadda ya amsata fuskarshi babu walwala, tun ta san shi bai saba haɗe mata rai ba amma bata kawo komai ba ta ɗauki handbag" ɗinta suka fice. "Nasir na cikin driving da ɗan speed ya ga wata baƙar BMW ta nauso da speed fiye da nashi," "haka ta zo ta wuce su tayi gaba kaɗan sai ta yi kwana ta tare hanyar. ""Haaa""" "Yayi hanzarin taka birki dab motar motarshi ta tsaya yana shirin fita ya ji ba'asi don Hibbah karan kanta ta tsorata kawai suka ga an buɗe kofar motar MB ya sauƙo mamaki ne ya rufe su duk su biyun, ya tako ya nufo motar cike da wani irin kwarjini da charisma yana zuwa ya buɗe" ɓangaren da take ya ɗan duƙo. """Akwai abin da ya taso and I need you...""" "Numfashi ta sauƙe a hankali kan ta juya ta kalli Nasir da idanunshi ke kan MB ɗin, ta ɗauki Jakarta MB ya matsa baya ta sauƙa da kanshi ya rufewa Nasir ɗin motar suka nufi motarshi, ta rasa dalilin bugun zuciyarta ko tsorata da tayi da action na MB ɗin ne ko kuma irin kallo da signs da yake nuna mata gab yake da bayyana abin da ba zata iya ɗauka ba ko da za'a tara mata duniya gabaɗaya ne, da kanshi ya zagaya ya buɗe mata mota ta shiga ya zago ya shiga ya ja" motar da speed sossai. "Motar ya fi yanayi da sabo saboda irin walkiya da shekin da komai na ciki zuwa waje ke yi, a hankali ta ɗan saci kallonshi ba tun yau ba idan yana driving da kanshi ɗauke mata hankali yake, yadda yake relaxing ko kuma idan zai yi kwana ya ɗan taso yana amfani da hannu ɗaya" cikin ƙwarewa da sanin ƙarfe hakan na kasheta. "Ruwa ne ya fara sauƙa da ƙarfi, hakan ya sa ya rage tafiyar a hankali kaman baya so, babu mai magana cikinsu kowa da abin da yake saƙawa ita dai idan ta fahimta zagaye kawai suke a tsakiyar birnin na legos, ga ruwa ana yi ga motar yayi wani irin shiruuu sai bugawar zuciyoyinsu" a hankali hankali. "Ta ƙi magana itama amma tana mamaki, a ƙarshe ta ga ya nufi unguwarsu wato Victoria Island," sun ɗan zaga a ciki kan ta ga yayi parking a gaban wani restuarant da yake da tsananin kyau "da ɗaukar ido tun kan su shiga ciki, an yi wani design da sunan daga sama VICI RESTUARANT." "A yanzu yayyafi ne ke ɗan zuba kadan kadan, ya sauka sai ya zaga ya buɗe mata, bata yi" "musu ba ta sanya kafafu ƙasa tana tunanin kila anan ne za su haɗu da client ɗin nashi.. Jerawa suka yi ciki hannayenshi zube a aljihu, bai tsaya ba suka nufi sama zuwa wani open space." "Kasancewar yammaci ne sannan ruwan sama ya tsaya, yanayin ya zama wani yanayi mai daaɗi da sanya natsuwa, iska mai sanyi da kamshi irin na ƙasa na busawa a hankali damp and fresh, akwai flowers masu kyau da wasu chandliers(Maroon) da suka kawata wurin, ɗigo ɗigon ruwa na mamaƙale jikin ganyakin wurin, falling one by one in a slow rhythm, tapping gently against the wooden floor." "It was almost empty. Don babu kowa cikin wurin, The soft glow of warm lights reflected off the wet surfaces, turning everything golden like the world had decided to soften itself just for this" moment. "Kujera ya ja mata ta zauna shima ya kai zaune. ""Order something""" "Ya faɗa yana nuna mata scanner dake ajiye kan table ɗin, wayanta ta fitar tayi scanning tana duba menu ɗin a natse shi kuma yana kallonta, sai da ta gama ta ɗan ɗago idanunsu suka" sarƙe. "She looked away her heart continue racing fast, ya duba nashi ya saka order... Basu fi mintuna biyar ba aka fara gabatar musu da order ɗinsu very classy and stylish komai suke dropping yana dauke idanu, bayan sun gama ta kalleshi yayi mata alamar bismillah, ba tun yau ba sun saba idan sun fita su ci abinci waje don haka ta ɗan sake da cin abinci gabanshi amma yau har ta yi nisa da cin abincin bata ji motsin farawarshi ba, a jikinta take jin ƙwayar idanunshi da ke ɗaɗɗaureta." Ta ɗan kalleshi he slightly raised his eyebrows looking at her showing openness irin wannan kallon dake fitar da duk wani saƙon zuciya irin i see you and i like everything i see... Non-alcoholic wine da aka zuba mata a wani glass cup ta ɗauka ta miƙe gabaɗaya ta tafi gefe ta tsaya tana kallon ƙasa iska na ɗan kaɗata kaɗan kaɗan hannunta ɗaya a cikinta a zagaye ɗayan na rike da wine ɗin da take sha a hankali. Har sanyi ta fara ji yadda iskan wurin yake haka kuma zuciyarta kaman zai fito mata saboda "wani irin bugu da yake, iska ta ja a bakinta ta fesar da ɗan sauri ta motsa jin sauƙar rigar suite ɗinshi a kafaɗunta" """You're cold,"" he finally said, his voice low, careful-almost like speaking too loudly might break the moment." Riƙe rigar tayi tana jin kamshinshi na shiga hancinta yana kara mata saurin bugun zuciyarta. Bata iya ta ce komai ba ya sa hannu ya karɓi cup ɗin ta inda take sha ya sa lips ɗinshi ya sha kaɗan. """That's my drink!""" "Ta Yi gaining courage na faɗa slowly. Ya ɗage kafaɗa kaɗan yana ɗan smiling ""Na sani...""" "Ya sake sipping kan ya miƙa mata ta karɓa ta kalli cup ɗin ta sake kallonshi. ""Me kake yi?""" "Bai ce komai ba sai kallonta da yake, gaba tayi ta saka hannunta ɗaya ta riƙe ƙarfen dake" "zagaye da wurin, shima yayi hakan amma ya ba da tazara da ita shi gabaɗaya ita yake facing ita kuma tana facing waje." """Sir...!""" """I don't want to be your boss anymore...""" "Ya katseta, ta ɗan juyo idanunsu suka sarƙe shima ya cigaba da kallonta iska na kaɗa su a tare ""I want to be your boyfriend, your halal husband, the love of your life...""" Idanu ta kyafta zuciyarta na wani irin tsere gudu ji take kaman numfashinta ya tsaya chak komai na duniyar nan ya daina motsi sai narkakkun idanunsa kawai dake kyaftuwa cikin nata mai ɗauke da tarin sakonni.. """Hibbatullah Ina sonki I love you so much Hibbah""" "Juya fuskarta tayi da sauri tana barin wurin, numfashi na kokarin seizing daga maƙogoronta," tsabar yadda taji tsigar jikinta duka ya zuba sai da zufa ya karyo mata Dukda sanyin dake kaɗawa. Da idanu ya bita ta koma gefe ta tsaya tana riƙe glass cup ɗin da karfin gaske kaman yadda ta "danne hakwaranta, jikinta ne ya amsa haka zuciyarta amma kwakwalwarta ya ƙi bata haɗin kai. Motsin takunshi taji yana matsota ya zo dab ita ya sa hannu ya zare kofin daga hannunta." """Hibbahh! Na ce ina sonki... Say something please, idan baki yi magana ba i don't think i can breathe...""" Cikin tsananin raɗa yayi maganan. Za ta sake barin wurin ya riƙo rigarshi dake jikinta sai ta zamar da shi tayi saurin nufar jakanta ta ɗauka ta fice a wurin cikin sassarfa hawaye na tsinke mata… 61 Cikin zafin nama ya taka ya sha gabanta. """You are not leaving alone Hibbah, idan magana ne bakya so zan iya yin shiru for tonight"" Yayi uttering calmly cikin Muryar rarrashi." "She stopped, yayi settling nasu ko kan ya isa jikin motar ta shiga har lokacin hawaye take" "sharewa, ta ma rasa kalar tunanin da zata yi, idan da za'a aunata a lokacin tabbas sai an sameta da hawan jini because she lost control over her heart and soul and she promised to" never give in don idan tayi kuskuren hakan ta kuma rasa shi tabbas babu tantama sai ta rasa ranta a yadda take ji. "Yana driving a hankali har kofar gidansu dayake ba wani nisa, shiru ya cika motar sai da yayi" "parking zata sauƙa ya danna lock, ta ɗago idanunta da suka birkice ta kalli fitinannun nashi da suka kankance akan soyayyarta." """Hibbahhh ba na faɗa miki abin da yake raina bane saboda in saka ki a damuwa ko ƙunci and" "don't think this moment as halluscination, AL-MUSTAPHA loves you...""" Ya ƙarasa cikin sanyi. """Ka buɗe min kofa in fita...""" Tayi maganan deep throat with her cracky voice. "Har ga Allah baya son kukan nan, but he's not hiding anything anymore." "Hannu ya sa ya buɗe mata ta fice daga motar ba tare da ta waiwayo ba har ta shige gida, ya koma ya jingina ya jima zaune a haka kan ya sauƙe numfashi dole ta yarda da shi, zai koya mata sonshi ko da ra'ayin ta ko babu ya ja motar ya nufi gida don bai tuna yaje ya ɗauko Jasrah ba ya san Mum tana fushi mai tsanani dashi amma ba shine zai sa ya shafi Jasrah ba a" ganinshi. "Raba dare Hibbah tayi bata yi bacci ba, ganin bata da mafita ya sa ta tashi ta fara nafila ko da tayi sujada rasa me ma zata cewa ubangijinta tayi, kawai tayi shiru wannan Bond ɗin na tsakanin bawa da mahallicinsa na ratsa ta." """Ya Allah!! I'm back again in the same situation I thought I had already escaped, I thought I was getting better but all of a sudden it all hits again...it hits harder than usual Allah idan da rabon wahalarwa ka nesantani da Mustapha, idan wani laifi nayi ya Allah na tuba ya ubangiji...""" Tayi kukanta enough har tayi bacci. "Ko da ta farka da safe ta farka da ƙwarin gwiwa, bata ƙi shirin office ba ta shirya ta fito bayan ta karya, motarta da jiya ya sha wanki ta ɗauka ta fice daga gidan, ko da ta isa company jikinta yayi wani irin sanyi har zufa tafin hannayenta ke haɗawa na anxiousness kan ta isa office nata. Bai kai ga shigowa ba haka ta gama ayyukanta ta ƙira meeting duk bai shigo ba, kuma ya san" da meeting ɗin tunda shi ne ma yayi mata izinin hakan. "Har suka isa hall shi suke jira, P.A ne ya ƙira shi yace su fara zai shigo." "Tun da ya ratso cikin meeting room ɗin bai zauna a kujerar da aka tanadar dominsa ba sai kai- kawo yake cikin yanayinshi na mazantaka da jarumta, bai damu da ko hakan zai iya causing distraction a meeting ɗin ba, he was trying really hard not to be distracted by her because God! Ta mugun tafiya da shi cikin Perfect atampha da ta saka a yau, everything about her nd the" dressing was damm exquisite wato kyau mai salo da tsari. Ita kuwa cikin ƙwarewa da iya aiki take jero bayanan proposal da ta gama tsarawa kuma ya matuƙar ƙayatar don tsitt hall ɗin ya ɗauka ana sauraranta tana gamawa aka shiga yi mata tafi ta dube shi a sadda muryarsa ke ratsa kunnuwansu """I'm betting my money on you, Miss Mudassir Madaki so don't let me down"" ""Yes Sir""" Ta amsa calmly cikin yanayinta na rashin son hulda da dogon magana sannan shes clearly avoiding him. "Chairman ya ɗan kara bayani, yana ƙoƙarin rufe meeting ɗin MB ya yi magana" """Miss Madaki please make sure immediately after this meeting ur proposal are on my desk ASAP.""" "Ta amsa respectfully ba tare da ta kalleshi ba, shan kamshi da kamewa haɗe da miskilancinta" "su ke ba da gudumawa wurin chusa wanzuwarta a zuciyarshi daga ɗaya zuwa casa'in da tara ba tun yau ba, kowani motsinta burge shi yake." "Hankalinta na kan system ɗinta tana jira duk su gama fita ta haɗa abin da zata ƙarasa ta sake printing ta kai masa don haka bata ɗago ba har sai da ta ji shiru sai kuma a hankali ta shiga jin kamshin turaren da babu wanda bai san mamallakinta ba yana kokarin hawa mata kai saboda irin sanyin kamshi da sanya natsuwa da yake da shi, yunkurin ɗagowa tayi sai ta kusa faɗa" mishi. "He leaned closer like gab da ita hannunshi ɗaya a bayan kujeranta ɗaya dab system ɗinta he cornered her locking their eyes, da sauri ta kawar da kai tana kamewa" """Excuse me!""" "Ta faɗa ba tare da ta kalleshi ba, zara-zaran fingers ɗin shi very clean da kuma alamun tsananin taushi da za su yi da ta zuba wa idanu ya zame sai ya fara wasa da fingers ɗin akan desk ta yadda dole ta kalleshi, he smilled she looked away a hankali ya ce" """I'm just reviewing ur work so why would i excuse u?"" ""It will be on ur desk in a jiffy boss""" Ta faɗa tana shirin Miƙewa a tunaninta zai bata wuri ya kuma ɗauke mayun idanun da yake binta da su sai ya ƙara kusancinsu yana lumshe idanu yana buɗewa saboda ƙamshinta na Valentino da kuma YSL dake ratsa shi har inda bai kamata ya je ba. He bit his botton lip nd widen his eyes cikin wani kalar murya ya furta """I'm not your boss, am just a man who think about you endlessly...""" "She freeze, maganan ya soketa sossai tamkar tsinin mashi a zuciyarta, ganin tayi shiru ya sa ya" matsa ta miƙe kawai ta tattaro abubuwanta ta fice ta barshi da binta da mayen kallo yana dan murmushi. **** "Kwance yake a gadon asibiti idanunshi na kallon sama, damuwa da tsananin ciwo duk sun" "bayyana a yanayinshi, mahaifiyarshi dake zaune tace tamkar za ta zubar da kwallah." """Wannan rayuwa dama da kuka daukawa kanku bai yi ba sam, yanzu wa gari ya waya? Eyee Usaib? Ka saka yarinya cha-cha ba tare da ka san zuciyarka ka jefa a ciki ba ya kake so yanzu mu yi maka? Mu zuba maka idanu ciwon zuciya ya kasheka ko mu kwato maka ita karfi da yaji?""" Mahaifinshi da shigowarshi kenan ya ce cikin faɗa """Haba Rashida! Haba don Allah! Za ki bar shi ya ji da abin da yake damunshi ne ko kullum za ki" "zauna baki da aikin yi sai yi mishi faɗa da masifa? Yayi kuskure kuma yayi nadama me kike so kuma?""" Ta share hawaye """Alhj ba zaka gane bane, zafin ganinshi cikin wannan yanayi shi yake tuna min da girman" "laifinshi, ka duba ita yarinyar fa da ciwon zuciya already ya sameta amma babu tausayi ko imani hankali kwance yayi cha-cha da rayuwarta gashi ai Allahnta baya bacci""" """Ki tashi ki fita kuma kar ki ƙara zuwa idan ba abin da zai kwantar mai da hankali zaki ce ba"" Cikin bada umurni yayi maganan dole ta miƙe ta fice daga ɗakin." Usaib ya waiga ya kalli babanshi """Abba wallahi na yi nadamar abin da na aikata, kuskure ne da wauta don Allah ku sake zuwa ku rokar min mahaifinta ya bani aurenta wallahi ba zan taɓa wulakantata ba""" """Kar ka damu zamu sake komawa in ta kama har legos ɗin za mu je mu roƙeta ta ceci" "rayuwarka Usaib""" Idanu ya lumshe yana jin sassaucin raɗaɗin da yake ji a ranshi.... 62 "Duk wata natsuwa ta yi mata ƙaura, zuciyarta na ta yaudararta zuwa ga abin da ba zata iya ɗauka ba, tsoro take ji hakan ya sa ta kasa karya alkawarinta Dukda irin tempting ɗinta da MB ke yi, she always avoid him as much as she can, sai ta yini bayan gaisuwa da maganar aiki bata bari komai ya shiga tsakaninsu, shi kuma ya zama mai haƙuri da kuma iya sanin taku, duk wani hanya da zai bi ya san ya kwanta mata cikin zuciya sai da ya bi a kwanaki biyu da suka" biyo bayan bayyana mata soyayyarsa bata ce komai ba. "Yau ta dawo da pending aiki kasancewar bata gama ba kuma za ta tura ta Email na clients ɗin ne da sassafe, ta raba dare bacci ne ma ya ɗauketa da asuba kuma a kan aikin ta tashi ƙarfe shidda ta gama, numfashi mai nauyi ta sauƙe tana shafa messy hair ɗinta, ƙoƙarin duba Email ɗin ta fara don tura musu sai dai bata gani ba, kuma tana tuna jiyan ya bata a rubuce da sauri ta miƙe daga ita sai wando da riga blue na bacci masu yauƙi, jakanta ta ɗauko ta zazzage duk neman da zata yi wa paper ɗin bata gani ba, ta ɗauki hijabi ta saka ta tafi mota nan ma ta bincika ko ta yar a wurin babu haka ta dawo ɗaki bata da wani option illa na ƙiran shi, har ga" Allah tunanin kiran nashi kaɗai buga mata zuciya yake. "Kaman zata yi kuka haka ta shiga ta nemo contact ɗinshi da tayi saving da boss, ƙira ta danna" "tana rufe idanu ta saka a kunne, dab da zai katse aka ɗaga." """Hey!""" "She just heard that bold, romantic morning voice echoring slowly through her ears, zuciyarta ya" kara ƙarfin gudu da kyar ta iya haɗa kalmar """Good morning Sir, please I misplaced the Email address of the client you gave me yesterday"" Yadda take maganan kaman da tsoro kaman kuma bata so ya saka yake ta lumshe idanu daga" kwancen da yake yana bacci. """Check i've sent it again""" Ko kan ya ƙara cewa wani abu tace """Thanks""" "She just ended the call and start crying, sai da tayi ya isheta ta ɗago ta duba inbox ɗinta ta dauki Email address ɗin ta tura musu kan ta tashi ta shiga wanka feeling very weak." Mommy ne ta sakata karyawa a sadda ta fito don haka dining ta wuce ta zauna tare da Nasir dake ta kallonta. """Ya Nasir ina kwana?""" """Lafiya ƙalau Hibbah kina lafiya?""" Kai ta gyaɗa """Ya shirye-shiryen komawa Germany?""" """Muna kai kaman kar in koma ma wlh gida daaɗi ne dashi""" Kai ta gyaɗa kawai ta saka abincin amma bata ci ba sai ta tafi duniyar tunani sai juya cokali take cikin egg sauce da gudun farar doya da ta ɗan gutsuro jikin fork ɗin. """Hibbah!""" Nasir ya ƙirata tayi saurin ɗaga kai ta kalleshi. """Lafiyanki kam ko? Its like kina da damuwa ni ɗan uwanki ne idan akwai wani da kike da damuwa da shi zaki iya sanar da ni kila in iya magance miki shi""" Ta sauƙe numfashi mai nauyin gaske """Kwarai ina da damuwa Yaya Nasir amma don Allah adu'arka kawai nake so shine babban taimakon da zaka yi mini""" Muryarta har yana rawa ta ƙarasa. "Tausayinta ne ya sake rufe shi ""Is it love again?""" Ta lashi lips ɗinta kan ta haɗe su ta matse amma duk da haka hawayen da take dannewa ne suka shiga zuba. """Hibbah I hope zuciyarki bata jefaki komar son maso wani ba a wannan karon?""" """Yaya Nasir zuciya bata da adalci sam, zuciyata muguwar zuciya ce ta manta duk wani azaba da raɗaɗin da ta ɗanɗana a baya tana kokarin sake ɗaukar dala babu gammo amma a wannan karo ba zan bar hakan ta kasance ba, i will never trust a man with my heart ever again sai dai zuciyar ta buga amma ruhi da kwakwalwata ba za su taɓa sallamawa ba muddin ina so na rayu" "a wannan karo""" "Tausayi take bashi fiye da zato, ya sani bata dace ba a fannin soyayya, abubuwa dayawa sun faru kuma duk a ciki ba ta inda ya ga laifinta amma ba zata azabtar da kanta da wannan hukunci tana kallo ba." """Hibbah Thats not an option, baki da iko da zuciyarki kuma shi So...""" Ta katse shi """Ya Nasir Please bana son jin komai akan shi""" Tana kai nan ta miƙe kawai ta fice daga gidan zuwa mota ta ɗauka ta nufi office. "Yau she dress simple but elegant two pieces ne rigar ya fi yanayi da dogon riga amma daga gefen hip ɗinta na dama har ƙasa an kwashe shi inda ya bayyana mahaɗin wandon kayan mai faɗi sossai, dogon hannu ne gareshi kuma akwai manyan bottons da kawai don ado aka yi su guda uku ta gefen chest ɗinta Layin da tsagun rigar ya bayyana, wages ta saka yau cream colour da birkin bag ɗinta shima cream me jikin kada, scarf ɗinta cream ta yi tarha da shi ta" kama da wasu pins very stylish don she can dress ta ɓangaren chan an bar mata. "A hanya gabaɗaya hawaye ta dinga yi marar dalili, shawara take yi da zuciyarta har ta isa office, sauƙa tayi tana fita daga mota shima yana parking yau da kanshi ya fito, Wasu ash suite ne jikinshi da suka amshe shi, as usual komai nashi mai tsada da ɗauke ido na attracting 'yan mata dayawa, bai tsaya ba don itama bata tsaya ba tayi saurin wucewa kaman bata ganshi ba ta shiga elevator ta danna floor ɗinsu tana Allah Allah a riƙe shi da gaisuwa ko zata isa office ta" shige toilet kan ya iso amma inaaa ta makara dab kofar zai rufe ya sa kafafunshi ya tare. "Ta runtse ido tana shakar ni'imtacciyar kamshinsa da ya shiga ratsa hancinta, gabanta faɗuwa yake amma bata bari jikinta ya nuna ba, dab ita ya matso yana kallonta with so much love and affection" """God! you are beautiful you know that?" "A girl like u needs to be cherished and loved, please let me love you hebbah...!""" "Ya ja sunan a hankali yana kasheta da kallo, dama kuka na kusa mata tuni ta sakar masa kuka" hankalinshi ya ɗan tashi damuwa ya bayyana a fuskarshi """Me ya sa idan na yi miki maganar da ta shafi so sai ki kama kuka Hibbah?""" Ta ɗago idanunta dake zubar da kwalla tace """Ka san kuwa wacece ni? Ko ka manta kalar hotunana cikin mummunan yanayin da ka gani a wayan Mahir? Why did you damaged that? Kaima so kake ka yi amfani da hotunan wurin cimma mummunan Manufarka a kaina? Ko don ka ga ina aiki a karkashinka ne Al-Mustapha?""" "Ya runtse idanunshi a daidai lokacin elevator ya buɗu, za ta fita ya riƙo hannunta ya dawo da ita" baya in a very tender way ya matsa sossai kusanta. """Hibbah Wallahi Allah ba ina sonki saboda wani abu bane ina yi miki so ne saboda Allah, trust me I love you wholeheartedly""" Ya faɗa cikin raɗa da murya mai taushi a maimakon ya sassautar da ita sai kuka ta sake sakawa. Hannunshi ya kai kan fuskarta ya share hawayen dake zuba idanunshi a kan nata.. """Batun hotunan kuma i've never seen that, ko da da gaske ke ɗin ce ban damu ba saboda ke" "ɗin tsurarki nake so ba kyau ko diri ba""" "Lips ɗinta rawa suke hawayen na ƙaruwa yana gogewa idanunshi sun rikice gabaɗaya, yana jin" wani yanayi da bai taɓa ji ba na shigarshi. """Bana sonka!""" Wani irin runtse ido yayi don kalmar ta sauƙar mishi tamkar guduma bisa kai. """Bana sonka!""" Ta sake faɗa still tana kuka. """Bana sonka kuma ba zan taɓa son ka ba don ni aure baya cikin kaddarata ka yi haƙuri ka nemi" "wata""" Tana kai nan ta zagaye shi ta fice daga elevator ɗin tayi toilet da sauri tana kuka. "Ya jima tsaye a wurin kanshi a ƙasa kan ya wuce zuwa office nashi, wani irin abu mai kaman zazzabi ke rufe shi, ba zai taɓa yarda ba, ba zai taɓa amincewa ya rasa ta ba, not after zuciyarshi tayi wannan zurfin a kanta, ina ma zai iya zubar da hawaye don ko ba gaskiya bane" kalmar da ta jefe shi dashi yayi mishi muni ƙwarai da gaske. "Safa da marwa kawai yake yi, Menene ya sa ba zata amince da soyayyar shi? Menene dalilin ta na rufe babin soyayya a rayuwarta bare aure? Girgiza kai yayi kawai ya nufi kofar ya fito itama ta fito kenan ganinshi ya sa ta juya zata koma toilet ɗin taku uku cikakku yayi ya sanya" hannunshi kan nata dake jikin handle ya rufe kofar. "Da sauri ta juyo tana zuba mishi rinannun idanunta ""Me kake so da ni ne Al-Mustapha""" "Hibbah's heart raced, her breath catching." A karo na biyu ya ji sunanshi a Bakinta zuwa kunnenshi wanda hakan ke dirar mishi kan zuciya ya tada mishi tsigar jiki a take. His eyes burned into hers. """Babu abin da yake coincidence a wannan rayuwa, duk wani wanda za ki haɗu dashi an riga an rubutashi cikin littafin ƙaddararki, hakan bai zama coincidence ba because that soul might be in your life to teach you, to heal you or to love you.. Hebbah I do love you and i want to heal you... Ki ba ni dama in koya miki yadda za ki so ni, ki ba ni dama in zama mai kama hannayenki in" "jagoranceki wurin fitar da ruhinki daga duhun da ta jima a ciki zuwa natsatsiyar haske""" Tabbas da za ta iya cire zuciyarta ta jefar da tayi hakan a lokacin saboda irin bugawar da take har tsoro take kar ta fashe amma sam bata shirya ba. """I don't love you, zan iya maimaita maka hakan sau ɗari idan za ka furta min kalmar So sau ɗari, Love taught me so many lessons through pain, bana buƙatarta a rayuwata i've been hurt enough to know better now. Excuse me!!""" Ta zagaye shi ta fice daga wurin gabaɗaya. "Idanunshi ya runtse for the very First time tun bayan rasuwar Anam yaji wani abu wai shi kwallah na cika mishi idanu suna mishi wani irin yaji yaji, dakiya ya nemawa kanshi baya son sanin wacece ita before zuwanta but stubbornness ɗinta na saka shi jin kaman ya kamata ya san wacece ita me tayi facing da take da wannan dakiyar ta kuma iya sanyawa zuciyarta" makullai masu tsauri. "Office yaje ya zauna amma ya kasa takuba komai daga ita har shi babu wanda yayi aiki a ranar," "zama tayi kawai ta shiga rubuta letter sai da ta gama tayi signing tare da sealing, ta ɗora kanta kan desk tana jiran right time, tana nan cikin position ɗin ya fito ya wuce da alama sallah za shi." Ta miƙe kawai ta shige office nashi ta ajiye takardar a gaban desk dinshi ta fito ta haɗa komai nata ta fice suna fitowa daga sallah tana barin kamfanin. "Office ya haura yana dafe kanshi dake tsananin sara masa, ko da ya isa ya zauna yana ɗora" hannunshi kan table ɗin takardar na faɗuwa ya miƙa hannu ya ɗauka sai ya shiga warwarewa. Resignation letter ne ga sunanta ɓaro ɓaro da wani irin hanzari ya miƙe tsaye yana kallon handwriting ɗin """No Hibbah.... I don't want you out of my sight, not yet...not so soon""" Wayanshi ya janyo ya shiga kiranta amma switch off jefar da wayan yayi yana zama tare da kama kanshi """Hasbunallahu wani'imal wakeeel""" 63 "Tun a hanya tayi booking flight na Kano, legos gabaɗaya ya fice mata a ka, lokaci lokaci kuma ta kan sa hannu ta share hawaye don ita kaɗai ta san irin tarin tarnaƙi da ke baibaye da" "zuciyarta, tana isa gida ta nufi ɗakinta tayi wanka ta wanke fuskarta don bata so ko ɗaya" "mommy ta fahimci irin damuwar da take ciki, ta fito ta shirya don sai dare ne ma jirginta zuwa" "Kano, wurin mommy ta nufa tana zaune tana kokarin gyara wardrobe ɗinta." "Karɓa Hibbah tayi ta fara gyara mata cikin hira take cewa ""Mommy ina so zan tafi kano in anjima""" """Lafiya kam Hibbah?""" """Lafiya ƙalau Mommy kawai na ji ina so in je ɗin ne don na jima rabona da zuwa"" Ta faɗa a sanyaye." Mommy ta sauƙe numfashi """Toh shikenan Allah ya kaimu, amma wurin aikin fa?"" ""Mommy na riga na gama komai da su""" "Kallonta kawai mommy ke yi ba don ta yarda ba, sai ta karanci tarin damuwa a fuskar hibbar da" ruɗu. "Ta jima sossai ɗakin Mommyn kan ta wuce nata ta har haɗa duk wasu abubuwanta masu amfani akwati biyu ta yi masu girma don bata tunanin har abada zata iya dawowa legos, duk yadda take kaunar zaman cikinshi dole ne ta bar shi na har abada." Magrib na yi tayi wanka ta shirya cikin Abaya baƙi ta yafa gyalen tare da daukar babban glasses "Dukda dare ne ta rufe idanunta da suka zama wani kala, jakunkunan ta sa aka zo aka fidda mata." "Mommy na tsaye cikin babban parlor aka zo aka wuce da su, Hibbah ta sauƙo hannunta riƙe da" "handbag ɗinta da kuma wayanta, flat shoe ne a kafafunta sassanyar kamshi ke tashi daga jikinta a sadda ta rungume mommy hawaye na gangaro mata." """Hibbah... Ɗago ki kalleni""" "Ta ɗago tana kallonta Mommyn ta zare madubin kan ta ja hannunta suka zauna. ""Ni ce ko yaran nan wani ya ɓata miki?""" Ta kakaro murmushi """Haba dai Mommy, ai ke uwa ce duk wani abu da za ki yi min ba zai zama bacin rai a wurina ba haka ma su Ya Abdul duk yayyuna ne ban isa su yi min abin da zan ji ina son barin gidan nan ba, zan dawo idan da rabo""" Sai a lokacin mommy ta fahimci da gaske Hibbah so take ta bar garin gabaɗaya bayan tsawon shekaru da suka yi tare. """Hibbah... Haƙiƙa raina yayi ba daaɗi da har za ki iya tattara kayanki gabaɗaya da sunan barin gabana ba tare da na sani ba sai at this dieng minute, idan ba mu bane menene? Daga wurin aikin ki ne?""" "Kanta ta duƙar tana wasa da hannayenta cikin kokarin mayar da kukan dake taho mata, sai" kawai ta rungume mommyn tana mai barin hawayenta zuba """Zan yi matukar kewanku mommy, har abada kuma nan ma gida ne a gareni, zan dawo in shaa Allahu""" Mommy ta saketa """Toh Allahu ya sha""" "Ta miƙe suka sake sallama kan ta fice mommy ta raka ta har mota tana mamakin sudden tafiyar na Hibbah, amma bata tsawwala ba kaman yadda hibbar tace nan ɗin gida ne da zata iya zuwa a koyaushe ta tafi a koyaushe amma duk da hakan tana matukar jimami da tafiyar Hibbahn don" bata ga alamun dawowa a yanayinta ba. "Ita kam Hibbah tana isa Airport ta gama duk wani abu da zata yi ta samu wuri ta zauna tana jiran jirgi, tunda ta zauna ko waya bata kunna ba, wani irin kewa da damuwa ne ke kara rufeta a duk sadda zuciyarta ya raya mata babu lallai fa ta dawo shin hakan shi ne daidai a wurinta?" Tana ba kanta tabbacin cewa ba kuskure bane amma zuciyarta na karyata zancen kwakwalwarta. "An yi anouncing isowar jirginsu ta miƙe rike da handbag ta nufi hanyar da za su bi don isa ga kofar jirgin, tana tafiya ne kaman ba zata kai ba har ta isa mazauninta ta zauna tare da ɗaura belt, tana nan shiru har jirgin ya fara kokarin tashi sai ta sanya hannunta ta rufe fuskarta tana sakin tsiririn kuka, ji take kaman ta yi mantuwa, ji take kaman ta bar wani abu mai matukar muhimmanci na rayuwarta anan amma babu waiwaye a gareta hakan shine natsuwar da zata" iya sama wa kanta. "Tafiya ne da ta yi shi cikin wani mummunan yanayi don kan ta isa Kano sai da wani zazzafar zazzabi yayi nasarar rufeta duk yadda take kokarin dauriya kasa wa tayi, na gefenta babbar macece ta kira First aid aka zo aka bata magani amma dai ba wai ta ji sauƙi ba haka ta cigaba da rawar ɗari bayan an sauƙa ƙasa tafiya tayi sai a wani emergency bed aka saukar da ita sai asibiti da wayanta aka yi amfani aka kira Daddy, ya shiga mamaki kwarai ko da ya samu" wannan labarin tuni ya miƙe Momma dake tare da shi a lokacin tace """Lafiya kuwa Daddyn yara?""" """Ba ƙalau ba, Hibbah tana kwance asibiti babu lafiya""" Cikin mamaki da kaɗuwa tace """Hibbah kuma? Yanzu legos ɗin zaka? Jikin yayi tsanani ne?""" Ya girgiza kai """Tana nan Kano, a cikin jirgi ne ciwon ya kamata"" ""Kano???""" """Kin ga yanzu ba lokacin tambaya ba ne Fatima za ki tashi mu je ne ko in yi tafiyata?""" "Ya ƙarasa zura jallabiyarshi ya ɗauki car key ya fice, dole ta zura babban hijabinta ta ɗauki waya ta bi bayanshi suka bar gidan ba tare ma da kowa ya sani ba." A hanya ta shiga kiran Yayarta """Dama yanzu nake shirin kiranki, ina ta neman Hibbah bana samu ta isa lafiya ko?""" """Hmmm da sauƙi dai Yaya Kubra, me kuma ya faru a legos ɗin? Bata sauka jirgi da kafafunta ba tana chan kwance ba lafiya muna hanyar asibiti kenan""" """Innalillahi wainna ilaihi rajiun da ma sai da na raya a raina ba ƙalau ba, tun da Hibbah ta tafi wallahi na kasa zaune na kasa tsaye, Fatima ko wani abu ne muka yi mata a rashin sani? Na san dai a yanzu bayan mu babu wani da zai iya ɓata mata rai haka ba samari take kulawa ba" "ba komai ba""" """Haba Yaya kubrah har Hibbah ta kai don kin ɓata mata ta tattara ta bar legos? Kila dai wani abin ko cikin baƙin hali da ta ɗora wa kanta na miskilancin banza ko 'yan uwanta kullum a complain da ita suke""" """Ku ƙarasa dai asibitin sai mu yi magana hankalina sam ba'a kwance ba""" "Ta katse wayar tana mita, Daddy ya waigo ya kalleta." """Meyasa kike haka ne ni kam Fatima? Yarinyar nan ba kya duba halin da ta tsinci kanta na kaddarorin rayuwa daga wannan sai wannan sai wannan ke kullum a baibai kike kallonta ba dole ta janye jiki da ku ba? Kina abu kaman ba ke kika haifeta ba don Allah?""" Ranshi a ɓace yake maganan yana jin haushin yadda take handling matsaltsalun Hibbahn. """Wani lokacin Alhaji yarinyar nan zantukanku take ji take kara sakankancewa da tutiyar ita ba za ta yi aure ba, kaddara ba ita ta fara dorawa kanta ba? Duk da bata aikata abin da ta aikata a baya ba da yanzu hankalinta kwance tana gidan wani, a kanta aka fara heartbreak? Zuzuta lamarin da kuke shi yake kara bata jin daaɗin yadda take so wlh, yanzu ka ga yadda Yaron nan Usaib ya zo yake ta magiya da a aura mishi ita ko shi aka aurawa ai bamu faɗi ba sai taje tayi ta" "haƙuri kowa ma ai hakurin yake""" """Kin san Allah Fatima?? Idan har kin san kalar maganganun da za ki cigaba da yi kenan zan" "sauƙe ki ki nemi adaidaita ki koma gida, wallahi bakin ciki nake ji wa Hibbah idan na tuna ta bar" "legos ne kila don ta samu natsuwar zuciya amma za ta zo tayi karo da ke""" "Tayi shiru bata ce komai ba don ta kula ya gama harzuka, ba zata ce bata jin zafin abin da ke faruwa da Hibbah ba amma da zata natsu tayi auren ai da komai ya wuce amma ita ce koyaushe ɗaga hankali akan soyayya, tana ji Daddyn na cewa ba'a isa a takura mata a gidan uban ta ba kuma Usaib idan ba ita tace tana son shi ba babu mai aura mata shi, tana shiru har" suka isa. Likitan dake kanta suka samu ya tabbatar musu stress ne da rashin bacci kaman akwai tarin "damuwa a lamarinta don haka tana bukatar hutu da kulawa, idan ruwan jikinta ya ƙare ta farka" za su iya tafiya. "Daddy na zaune kan plastic chair rike da hannunta yana ta kallonta cikin tausaya wa zuciyarshi fal Adu'o'i yayinda Momma ke zaune daga waje tana waya ne da Yaya Kubra sai da ta tabbatar ta kwantar mata da hankali kan suka yi sallama, ta jima zaune wurin kan ta miƙe ta shigo ta" "zauna chan kan wani cushion dake ɗakin, Hibbah bata farka ba sai wuraren 1 na dare." A kan mahaifinta ta soma sauƙe idanu sai ta lumshe ta sake budewa very weak tace """Daddyna?""" Ya amsa da murmushi """My princess kin farka? Sannu ko? Ya jikin? Ina ke yi miki ciwo?""" "Ta saki murmushi cike da ƙwarin gwiwa da jin daaɗin kulawar mahaifinta. ""Babu ko ina Daddy""" Ya miƙe ya fice Momma dai da kallo take bin su tana girgiza kai. "Har Daddy ya dawo bayan sannu da tace mata wanda sai a lokacin ne ma Hibbah ta san Momma na ɗakin itama tace mata yauwa basu ƙara magana ba, da likita ya dawo bayan ya gama dubata ya tabbatar za su iya tafiya ya kuma ce su samu wani abu su tabbatar ta ci kar ta" kwana da yunwa sannan a kula da ita sossai. "Da taimakon Daddy ta sauƙo sai dai bayan ta daidaita tace mishi zata iya tafiya, ya sake ta" "suka jera a hankali zuwa mota Momma na biye da su a baya, shi ya buɗe mata mota ta shiga Momma ta shiga gaba ya zagaya ya shiga suka fice daga asibitin garin shiru." "Har suka isa babu mai magana a motar, karar shigar su shi ya mayar da hankalin Umma kai da" "take daga sashenta ta farka fitsari, hijabi ta zura ta sauƙa ƙasa kan ta fito sun sauƙo..." """Alhj lafiya kuwa? Daga ina da tsakar daren nan?" "Ta faɗa bata kula da Hibbah ba, cikin damuwa take tambayar. ""Hibbah ce ta iso garin ba lafiya shine muke je daukota daga asibiti"" ""Innalillahi! Hibbah??""" "Sai a lokacin ta kalleta ta tafi ta kamata ""Sannu Hibbah, ya jikin?""" Murmushi Hibbah tayi hakika tayi matukar farin cikin ganin Umma matsayin matar Daddy a karo na biyu za kuma ta so ta zama ta daban cikin zuciyar Daddy ko don chanchantarta da hakan. """Da sauƙi Umma""" """Mu je ki watsa ruwa ki ci wani abin""" "Janta tayi zuwa sashenta yayinda Momma da kuma Daddy suka wuce sashenshi, hankalin Daddy a kwance don ya san Umma za ta kula da ita sossai fiye ma da Mommar." "Aiko suna zuwa sama ɗakinta ta kaita ta shiga toilet ta haɗa mata ruwa mai dumi. ""maza shiga ki yi wanka bari na duba miki kaya wurin Nihla sai kuma abin da za ki ci"" ""Umma tea kaɗai ya wadatar please""" Ta faɗa a hankali tana kokarin shiga wankan. "Umma ficewa tayi zuwa ɗakin Nihla dake ta bacci ta zaro mata wani sabon riga marar nauyi na bacci dogo ne daga nan ta wuce kitchen na sama ta haɗa mata tea mai kauyi tayi sandwich ta haɗa mata dashi kan ta ɗora a tray ta koma ɗakinta ta samu Hibbah na kwance bakin gado, idanunta a lumshe." """Tashi maza ki sa kaya ki ci wani abin""" Miƙewa tayi zaune ta karɓa ta ci kaɗan ta sha tea ɗin sossai kan ta saka rigar. """Hau gado ki kwanta kan da safe a gyara miki ɗaki""" "Ta hau kuwa ta ja bargo ta lullubu tare da lumshe idanu amma ta san ko da gigin wasa bacci ba ɗaukarta zai yi ba, chan ta kai hannu ta dafe kirjinta idanunta runtse tana ambaton Allah don wani takure wa da yayi wuri guda yana neman illatata, da kyar tayi bacci don tana ji har karfe" uku da rabi da Umma ta farka kan baccin ya ɗan sace ta kaɗan biyar kuma aka kira sallah umma ta tashe ta tayi sallah. Kanta na sarawa haka ta shiga tayi alwala ta zo ta gabatar da sallah kan ta sake komawa gado. "Ba ita ta farka ba sai karfe goma na safe, ita kaɗai ce a ɗakin don haka ta sauƙa ta shige toilet tayi wanka ta fito sanye da towel amma ta ɗora babban hijabin umma a kai, tana fitowa Umma na shigowa cikin yanayin marar lafiya tace" """Umma ina kwana?""" """Lafiya ƙalau Hibbah ya jikin dai?"" ""Da sauƙi sossai Umma""" """Ga rigar Nihla sabo ne sai ki saka Daddynku ya aika Airport a karɓo miki luggage ɗin ki"" Kai ta gyaɗa ta karɓa tana godiya ta saka bayan ta ɗan shafa mai ta shafa humrar Umman," "kasancewar bata da wani auki har chan abayar bai mata kaɗan ba, cib ɗinta gyalen ta ɗora a kanta sai ta bi bayan umma da ta fice ta barta ta shirya, tana saukowa daga stairs idanunta ya" sauka akan Nihla da take kuka Umma kuma na kallon TV ba tare da ta ce komai ba. "Dakatawa tayi tana karewa yanayin kallo ""Umma ba za ki yi magana ba?""" Nihla ta sake faɗa cikin kuka. """To me kike so in ce eye? Zan ce ki je ki rama ne? Ke na rasa Meyasa baki da juriya ko kaɗan, ba a komai ake mita ko ƙorafi ba na faɗa miki ba sau ɗaya ba ba sau biyu ba, Hajiya Kamila bacin ran nan take so ta gani shiyasa a koyaushe bata gajiya da dangantaki da agola...""" Motsin Hibbah ne ya sa Umma yin shiru ta ɗaga kai sai ta hangota tana saukowa. Bata nuna ta ji maganganun su ba ta sauƙo ta zo ta kwanta kan kafafun Umma. Nihla tace """Laaaa Aunty Hibbah yaushe a gari?"" ""Cikin dare Nihla kina ta bacci"" ""Sannu da zuwa, kin kuw...""" """Kar ki cika ta da surutu ba lafiya ne da ita ba je ki ɗauko mata abin kari ta karya ta sha magani""" "Ta miƙe kenan sai ga Baby idanunta na kan Hibbah cikin mamakin yadda ta ga ta koma very demure, ko da bata motsa ba kyau, ilimi, natsuwa da wani irin nagarta sun bayyana a yanayinta, ko da Daddy yace ta zo ta cewa Umma idan bakuwarta ta farka tace ta zo bata zaci Hibbah ba ce what?? Hajiya karima kullum ke kiranta da tsohuwar guzuma amma wannan ai" aka jere 'yan mata sweet 16 goma ba za'a zare irin mai class ɗinta ba. """Baby...!""" Umman ta kirata tayi firgigit """Umma wai Daddy ya ce idan baƙuwarki ta farka ta je..""" Tana kai nan ta juya da sauri har da sassarfa ta fice. Hibbah ta miƙe zaune Allah dai ya nuna mata ranar da halin mutanen gidan nan zai chanza gabaɗaya. """Umma bari na je na dawo sai na karya""" Ta faɗa a hankali kan ta nufi hanyar waje lofas me mai kyau kafafunta sababbi farare sol da Umma ta fitar mata. Tana saka kai parlorn na Daddy duk idanu suka dawo kanta… 64 """Haa su Hibbah ne ashe a gari? Aaa lagos ya karɓeki""" "Hajiya kamila ta faɗa cikin kasa ɓoye mamakinta na ganin hibban da yadda ta zama, kana" "ganinta za ka san bata zauna jiran wani ya bata ba, tana neman kuɗi kuma tana kashewa kanta don yanayinta ma bai nuna wahala ko talauci ko na miskala zarratin ba." "Ƙarasowa tayi ta samu wurin kafafun Daddy ta zauna ta ɗan ɗora kanta kan kafarshi shi kuma ya sa hannu yana shafa kanta, ta ɗan lumshe idanu ta buɗe tace cikin sanyin muryarta" """Ina kwananmu? Mun sameku lafiya?""" Sake baki duk suka yi suna kallonta. Hajiya karima tace """Lafiya ƙalau fa Mutanen Lagos, ashe ana ganinku""" Tace """Ai duk daaɗin dawa gida ya fi shi, Mama baki ji an ce kyaun tafiya dawowa ba?""" Hajiya karima ta ɗan taɓe baki wato dai har yanzu hibbar dai ita ce bata chanza ba kana gayamata za ta mayar maka. "Da tarin magana fal bakunansu amma tsoron idanun Daddy ya sa duk suka yi shiru, su Baby ne suka shiga gaisheta ta amsa a hankali kan duk suka watse, Momma dama ta jima da komawa" "sashenta, daga Hibbah sai Daddy ne a parlorn yana shafa kanta yace" """Mamana!""" Ta amsa a hankali """Menene kuma ya faru? Kar ki ɓoye min komai idan abu da ya kamata in baki shawara ne zan" "baki kuma zan tayaki da Adu'a zan ƙara akan wanda nake miki, wani abu ne ya faru a Lagos ɗin?""" "Hawaye ne ya cika mata idanu, ta ɗan datse bakinta kaɗan tayi shiru na lokuta dayawa kan tace a hankali" """Daddy na ajiye aikina""" Yayi shiru bai ce komai ba ta duƙar da kai hawayenta suka diga akan kafafunshi """AL-MUSTAPHA na shirin illata rayuwana Daddy""" Ta ƙarasa da shesheka. Ya yi shiru yana cigaba da shafa kanta cikin tausaya wa. """Kina son shi??""" "Tayi saurin girgiza kai, ya ɗan yi murmushi don ya tabbatar tana son shi sai dai bata so ne tayi accepting kar illar yayi mata yawa." """Shi fa?""" Ta gyaɗa kai. """Daddy bai san wacece ni ba, iyayenshi suna ganina a matsayin mai babban laifi a gare su ta yaya zai fara tsoma kanshi inda ya san babu mafita?""" """Allah yana madakata kuma yana da mafita akan koma menene Mamana, zan shawarceki da ki" "yi Adu'a sossai ki dage kwarai da gaske duk abin da Allah yayi daidai ne kin ji?""" Kai ta gyaɗa tana jan hanci. """Iyayen Usaib a karo na biyu sun samu Yayana""" Da hanzari ta ɗago fuskarta dake cike da hawaye tana kallon Daddyn. """Ki kwantar da hankalinki ba za mu yi miki dole ba, amma Usaib na cikin wani hali mawuyaci a kanki, Allahnki ne ya kama shi ya kuma jarabceshi da Soyayyarki da ba zai iya controlling ba, a yanzu sun nemi ki ga Usaib ko da sau ɗaya ne idan har baki ji kina son shi ko ki ji kin yafe mishi ba za su haƙura""" Za tayi magana ya ce """Shhhh Hibbah! Kar ki ƙi wannan roƙon na su, ko a haka aka bar Usaib ya ga ishara abin da nake so da ke shi ne ki cire duk wani damuwa a ranki ki sanyawa kanki ƙwarin gwiwa da farin ciki. Ki dinga haƙuri da sanyawa kan ki jarumtaka rayuwa tana koyar da darussa ta hanyoyi daban-daban. Wani lokacin za ki rasa wanda kake so, wani lokaci zaka rasa abin da kake nema, wani lokaci kuma duniya zata juya maka baya ne gabaɗaya amma ki sani babu wani bala'i da ya fi karfin zuciyar da ta ɗaura damuwarta ga Allah. Hakuri shi ne jigon cigaba na san" "kina yi amma ina buƙatar ki ƙara a wannan kadamin kin ji?""" "Kai take gyaɗa wa cikin sanyin jiki, hakika bayan Mahaifinta da ya zama ginshikinta kuma bangonta, majinginarta Almustapha shi ne kaɗai mutumin da is always ready to deal with all her mood swings and to say sorry even though Its not his fault... Bata san Meyasa a duk sadda za ta ji damuwa yana daga cikin na gaba gaba a faɗo mata ba duk yadda take kokarin ture shi duk wani motsinta bijiro mata da shi yake, maganarsa, mayun idanunsa, murmushinsa da iya" sarrafa lafazinshi ko ido a rufe ko a buɗe basa taɓa barin kanta. Daddy da kanshi ya hada mata breakfast ya tabbatar ta ci sossai kan ya kyaleta ta koma wurin Umma kuma a lokacin kayanta ya dawo har ma an haurar mata ɗakin da Umman ta gyara mata tsaff don ta zauna. "Kwanciya kawai tayi babu irin tunanin da bai zo mata ba kafin bacci ya ɗauketa ko da ta farka azahar, wanka ta sake ta yi alwala ta zo ta gabatar da sallah tana idarwa ta duba akwatinta ta" "zura wata doguwar rigar ta ɗaura gyalen ta sanya takalmi ta nufi waje, a parlor ta samu su" "Hudah da Aina'u ga yaransu, Nihla da kuma Ya Najeeb ganinta ya sa yaran duk suka yi kanta suna yi mata oyoyo ta rungumesu ɗaya bayan ɗaya zuciyarta na mata ba daaɗi da ta zo kan" Abir tana tuna Jasrah Allah kaɗai ya san halin da take ciki. Bayan sun gama ne tace su je su yi wasa anjima za ta basu tsarabarsu a ranta take raya dole ta fita ta saya musu don dai zuwan babu shiri bata riƙo komai ba. """Ya Najeeb yaushe a gari?""" Ta tambaya tana zama kusa da Hudah don an ce mata yana seminar a Abuja satin shi biyu kenan da tafiya. """Ko kuma ke zan tambaya yaushe a gari ba? Idanunki kenan?""" "Tayi murmushi tana kallon Hudah da ba zaka ce ita ce 'yan biyun Hibbah da basu da bambanci ba a da, yanzu Hudah ta yi kiba kadan saboda haihuwa ba wasa ba, halittarta ya chanza ba kaman Hibba dake buduruwa ba har yanzu." """'Yar uwa rabin jiki""" "Ta ɗan yi side hugging Hudar, Huda tace ""Ashe rai kan ga rai? Hibbah idanunki kenan""" "Tana murmushi kawai ta kalli Aina'u ""Aina'u ya kike?""" "Ta amsa mata da murmushi daidai nan sai ga Mumtaz da ya zama saurayi sossai ya shigo bayanshi autocin Momma ne anan suka zauna suka dasa hira ana ta tuna baya ana dariya, sossai Hibbah ta sake kuma har zuciyarta ta ji daaɗin wanzuwarsu haka Umma ce ta baza musu abinci da su snacks kaman biki kowa ya ci ya koshi sai yamma lisss duk suka watse bayan an gama planning yadda za'a sha shagalin bikin Ya Najeeb da nan da wata biyu ne" kachal. "Tana idar da Sallar isha wayanta ya shiga ringing, gabanta sai da ya faɗi a hankali ta miƙa hannu ta zari wayan sai ta sauƙe ajiyar zuciya ganin ba wanda take tunani bane." """Daddy ina yini?""" Ta gaishe da Yayan mahaifin nata cikin ladabi ya amsa """Na samu labarin zuwanki ina son ganinki yanzu ko Najeeb ne ki sa ya kawo ki""" Dukda yadda gabanta ke faɗuwa haka ta amsa da to ta miƙe bata cire hijabin ba ta sauƙo rike "da wayanta, ta samu Yaya Najeeb da Umma zaune a parlorn kasa tace ""Umma Daddy yana nemana, Ya Najeeb don Allah ko zaka kai ni?""" Umma tace """Toh sai kun dawo Hibbah""" Najeeb ya zari key dinshi ya miƙe suka fice. Shi yake ta kokarin janta da hira har suka isa gidan Daddy Rabi'u a babban parlornshi suka same shi bayan gaisuwa Najeeb zai miƙe ya basu wuri Daddyn yace """A'a zauna abin ka, ai na ji daaɗin ganinku tare""" "Zama yayi, Daddy ya kalleta ""Hibbah!""" "Ta ɗago tana amsawa a hankali ""Na'am Daddy""" """kin samu duk wani gata daga tasowarki zuwa yanzu, kin yi karatu mai zurfi kusan fiye da duk 'ya'yaye mata na gidan nan, kina aiki mai tsoka kina samu kuma fiye da zato a ganinki matsayin" "ki na 'ya mace mai ya saura miki?""" "Shiru tayi bata ce komai ba zuciyarta ke bugawa da karfin gaske, har sai da ya kara maimaitawa tace a hankali" """Aure a al'adance Daddy""" Ya tsinci kanshi da murmusawa kadan """A addinance fa? Feel free ki gayamin duk abin da yake ranki in ji Hibba don in san ta inda zan bullo wa lamarinki na kula daga ke har mahaifinki baku san zuru ba""" """Daddy shi aure ba dole bane, ibada ce da bai zama farilla ba, malamai kuma sahabbai dayawa sun kafa rayuwarsu ne a hanyar Allah da har suka koma gareshi basu yi auren ba...""" """Sahunsu kike son bi kenan?""" Ta duƙar da kai """Hibbah shi fa aure ba kawai alaka ba ce, mafaka ce ta kwanciyar hankali, cike da kauna da rahama, sutura da abokin ɗebe kewa. Ibada ce da ke kara kusantar da mu ga Allah, da kwanciyar hankali da natsuwar zuciya." "Kuma saboda a zamaninmu fitintinu sun yi yawa, aure yana hana fadawa cikin alfasha, yana" "kawo hutu da nutsuwa, yana tsare tarbiyya daga gurbacewa, yana kuma ba wa mutum garkuwa mai karfi""" Ya ɗan yi shiru kaɗan """Na san ki da taurin kai ba shawartarki nake ba, ina miki nasiha ne da kuma tabbatar miki ba za mu zuba idanu ki cigaba da zama haka da hujjarki na shiririta ba don darajar mace na ga ɗakinta, ina kuma ƙarfafaki ne domin ina miki sha'awar natsuwa da kwanciyar hankalin da ke cikin aure wanda ya dandana dandanonsa na gaske, ya san cewa ni'ima ce daga Allah. Kuma kadaici ko da ya yi kama da hutu, ba zai taba kai darajar kasancewa da wanda yake kaunarka," "yana maka addu'a, kuma yake zamar maka rufin asiri a rayuwa ba""" Hawaye take yi don ita duk kalaman ba wai sun kwantar mata da hankali bane illa iyaka ma ɗaga mata hankali da suka yi. """Iyayen Usaib sun zo kuma na basu dama da su turo shi ki ganshi idan bai miki ba fine amma ki" "sani wannan ne damarki na ƙarshe akan fidda miji Hibbah""" "Gabanta ya sake wani irin bugawa, da kyar tace" """Toh""" "Ta miƙe ta fice, ya bita da kallo ya dawo da kanshi kan Najeeb sun dan yi magana kadan kan ya miƙe ya bi bayanta ya sameta tsaye kanta jikin mota tayi shiru kaman wacce ruwa ya cinye." Buɗe motar yayi ta shiga ta zauna ya ja ya fice daga gidan. """Hibbah bana tunanin a wannan karo za ki zame daga tarkon iyayenmu, na san Usaib ya aikata miki kuskure mai girma amma ko Allahn da ya halicce mu muna yi masa laifi ya yafe mana, ki dubi soyayyarshi na gaskiya a kanki ba na bogin ba...""" Ta ɗan katse shi """Ya Najeeb duk abin da zan ce yanzu ba za ku gane ba""" "Shiru yayi bai sake magana ba har suka isa gida tayi sama, a wurin Umma ta kwanta tayi ta kukanta marar dalili har bacci ya sureta." "Washegari ko da taje gaishe da Momma ajiye ta tayi ta inda take shiga ba ta nan take fita ba, bayan ta gama faɗa ta dawo nasiha duk dai na son tabbatarwa hibbar muhimmancin yin auren" da gajiya da ganinta haka da tayi. "Da yamma tana kwance don yanzu ko ruwa bai kaita kwanciya ba gaɓɓanta duk a sake idanunta a lumshe, ta ɗan zube sai hancinta ya kara tsawo haka fuskarta ya kara haske, Nihla ce ta shigo tace" """Aunty Hibbah wai in ji Daddy kina da baƙo a parlorn baƙi""" Tsirirn tsaki ta ja kan ta miƙe zaune ta jima haka ta zari hijab dogo ta saka tare da flat shoe ta fito ta nufi ƙasan tana tafiya ne kaman wacce kwai ya fashewa a ciki har ta isa parlorn. "Kofar ta tura tare da sanya kai ciki Bakinta ɗauke da tsiririyar sallama, Usaib ne zaune cikin" parlorn ya ɗan faɗa kaɗan kuma dai alamun natsuwa sun bayyana a yanayinshi. """Hibbah Sannu da fitowa""" Ya faɗa kaman wanda ya ga daren lailatul kadr yadda fuskarshi ya yalwatu da fara'a don bai zaci zata fito ɗin ba. """Lafiya kake nemana?""" Tayi tambayar ba tare da ta zauna ba. """Hibbah...""" Sai ya zame ƙasa """Don girman Allah ki yafe min Hibbah, na yi kuskure mai girma na zaluntarki ba tare da hakkinki ba, na san na aikata ba daidai ba wanda har abada ba zan daina nadama ba ki yafe min please" "ko na samu salama""" Ta ɗauke kai daga kanshi tana taɓe baki kaɗan """Zan yafe maka ne Usaib akan sharadi guda ɗaya shi ne ka rabu da ni da rayuwata don ba zan" "taɓa sonka ba kuma a karo na biyu, I gave you the love i never got , and you gave me the pain i never deserved ba tare da la'akari da halin da zan shiga ba...""" Hawayen da yake dannewa ne suka zuba mishi """Hibbah ba zan iya rayuwa babu ke ba""" """Ba Za ka taɓa mutuwa don ka rasa ni ba tunda ni ma zafin abin da ka yi min na ƙara min rauni" "kan wanda nake da shi mai muni a baya bai kashe ni ba""" Ya miƙe tsaye yana dafe kujera """Idan har na hakura da ke za ki yafemin?""" """ƙwarai da gaske ko yanzu ka yi min alkawarin ficewa daga rayuwata ka bar ni na ji da abin da" "ke gabana wallahi zan yafe maka duniya da lahira""" "Cikin karyayyiyar murya ya ce ""Shikenan Hibbah na hakura"" ""Allah ya yafe mana gabaɗaya""" Tana kai nan ta fice daga parlorn. Ya jima ciki kan ya lallaɓa ya fice driver da ya kawo shi ya ja motar suka bar gidan yana jin "ƙwarin gwiwa, yana jin cewa ba zai mata dole ba ba kuma zai cutar da ita a karo na biyu ba, ya riga ya yardar wa zuciyarshi cewa ya haƙura da Hibbah na har abada." "Ta yi tunanin zuwanta Kano zai rage mata abubuwa da dama amma sai ya kara chushe mata," "ta kasa walwala ta kasa sakewa, damuwa ya yi mata yawa ita da karan kanta ta san cewa she is just forcing herself to lose feelings for someone she is already deeply in love with.." "Satin ta biyu suka shirya suka nufi Nassarawa bikin Asma'un Aunty Asiya, kusan har da Umma suka tafi da Nihla don taya Momma hidimarta, hakan ya mata daaɗi don a gidan hidimar wani ba shiga suke ba kowa tashi ta ficce shi amma zuwan Umma ya chanzawa Momma hakan su kan je hidimdimun juna hakan kuma na kara musu kusanci yana sanya zuciyarshi Daddy farin" ciki kwarai yayinda sauran matan suka dauki hakan munafunci da cusa kai. "Kasancewar wannan ne karo na farko Da Aunty Asiya za ta aurar tuni gidan ya cike fall da jama'a, har mutanen Lagos sun iso Zaitoon kaman za ta haɗiye Hibbah da masifa haka matar Abdul da shi kanshi sun yi mata mita har sai da Mommy ta tsawatar musu ita dai murmushi ne" nata wanda kowa ya gani ya san yaƙe ne.. Suna tare a babban parlorn na ɓangaren Aunty Asiya ana ta hira da raha sai ga Mumtaz ya shigo """Yaya Hibbah wai kina da baƙo a ƙaramin parlorn Abbansu Asma'u"" ""baƙo?""" "Tayi tambayar da mamaki. ""Ki je mana ki gani""" Ta ja tsaki za tayi musu Momma da ta fito ta dankara mata Harara dole ta miƙe "Gidan fa cike yake don gobe ne ake fara events kuma har su Daddy duk sun zo kasancewar alaka ne mai karfi tsakanin Daddy Rabi'u da Mijin Aunty Asiya ɗin don kaman uban gida yake gareshi, yanzu kawai sai ta kama ratsa manyan mutane tana zuwa wurin wani da bata ma sani ba." "A harzuke ta tura kofar parlorn ta sanya kai sai dai kamshin da ta ji ya saka jinin jikinta kafewa, numfashinta ya shiga fita da sauri sauri gabanta ya shiga dokawa, idanunta ta kafa a bayanshi tana kallo ko bai juyo ba, ko a mafarki ta ga wannan bayan ta san wanene... Miyaun Bakinta ne" ya kafe a sadda ya juyo idanunsu suka shige cikin na juna.... 65 "Tun ranar da ta bar office da sunan ajiye aiki bai ƙara taka kafafunshi office ɗin ba, komai ya bar wa P.A idan ya kama dole suna bukatar saka hannunshi sai dai su iske shi gida, shi karan kanshi bai san kalar zaman da yake yi a gidan ba, bashi da wani walwala kuma zuciyarshi na cikin tsananin kunci da kewa, he want to maintain his composure as the CEO he is ya gwada" pretending mantawa da ita zuciyarsa ta gama yaudararsa akan hakan. "Sau babu adadi ya kan janyo wayanshi ya nemi layinta sai dai ya kan kasa ƙira don bai san kuma me zai iya ce mata ba, bai san kalaman da zai mata ta aminta da gaske yana sonta fiye da yadda yake son kanshi ba. Wani lokaci kuma zuciyarshi kan ji kwaɗayin sanin ita ɗin wacece da take nuna past ɗinta yana da munin da ba za'a iya sonta saboda Allah ba sai don tausayi ko sha'awa amma ba ya so ko da wasa yayi bincike ko ya ji daga bakin wani Idan har zai sanin" daga Bakinta ne kawai yake son ji. "Yana kwance cikin yanayin rashin walwalar zuciya, Video call suka gama yi da Jasrah da take gidan Mom bayan sun katse yayi shiru yana tunanin yadda zai bullo wa al'amarin Hibbah, haka kuma wani ɓangaren na tuna mishi da har yau Mom bata bar fushi da shi ba, shin za su amince ma ya auri Hibbah idan ita hibbar ta amince?" Abubuwa ne goma da ishirin suka haɗe mai suka saukar mai da zazzabin da ya jima bai yi ba. Tura kofar ɗakinshi da aka yi ne ya sa ya ɗago kai cikin mamaki sai dai wanda idanunshi suka gani ya sa bai san ya ɗan miƙe zaune ba yana yatsina fuska kaɗan tare da aro jarumta yace """Ahmad!!"" ""Musty""" Wanda ya shigo ɗin ya faɗa yana ƙaraso wa bakin gadon. """Daga office nake me kake yi a gida ranar aiki Musty?""" "Yana ɗan gyara zama ya sa hannu ya dafe goshinshi ba tare da ya yi magana ba. ""Ba dai baka da lafiya ba ne?""" """It's just a Lil headache zai daina ne. Me ya kawoka Lagos ba sanarwa?""" "Ahmad yana taɓa temperature ɗinshi ya zame hannu yana kallonshi da mamaki ""You are burning up ka ce Lil headache? Yaushe rabon da ka ci abinci?""" Shiru yayi don gaskiya ba zai ce jiya ko shekaranjiya ba snacks sai coffee yake sha kawai ko biscuite. """Ka jirani ina zuwa""" Ahmad ɗin ya faɗa kan ya juya ya fice. "Mustapha ya koma ya kwanta yana lumshe idanu, ita kawai yake gani ta hana kowani motsinshi sakat." Kusan awa guda da fitan Ahmad kan ya dawo da bags masu yawa a hannunshi. """Ka tashi ka ci wani abu in yi maka allurai""" Zai yi musu Ahmad ya ce """Ka san Allah dama da fushinka na zo ko ka tashi ko in yi maka rashin mutuncin da baka taɓa zato ba""" "Karamin murmushi yayi ya sani shi mai laifi ne ƙwarai don haka ya miƙe zaune, abincin Ahmad" "ya jujjuye mishi haka ya ɗauki spoon ya ci kaɗan kan Ahmad ɗin ya haɗa allurai ya saka mishi canular yayi mishi wasu kan ya ɗora masa drip, yana kwanciya bai jima ba bacci ya sureshi." "Ahmad ya jima yana kallonshi kan ya tattare wurin gabaɗaya ya fita zuwa parlor yana tunanin yadda rayuwar Mustaphan ke tafiya a hagunce, tun da mahaifiyarshi ta rasu basu ƙara ganewa rayuwarshi ba har sai da ya auri Anam mace mai kirki da natsuwa, mace da ta san darajar 'yan uwanshi ta kuma san rayuwa ta yadda ta kan nusar da shi akan 'yan uwan mahaifiyarshi da yayi watsi da su shekaru masu yawa, ita ce ummul aba'isin nemansu ta kuma fara kokarin daidaita tsakaninsu amma mutuwa ta yanke yunkurinta, sun ji rasuwar ta fiye da zato kuma daga nan komai ya tsaya chak tsakaninsu da Mustapha. Yana wahala ya nemesu sai dai su su neme shi ya kan ɗauki lokaci mai tsawo bai je ga kowa ba cikinsu haka su ma dama ba zuwa" gidan mahaifinshi suke yi ba. Ahmad ƙanin mahaifiyarshi ne shine auta a ɗakin su ya girmi mustapha amma ba sossai sossai ba don haka kaman aboki yake a wurinshi madadin kawu. Sai da MB ya shafe sama da awa huɗu yana bacci kan ya farka ya samu an cire masa ruwan a hankali ya miƙe zaune sai ya ga Ahmad ɗin zaune yana waya murya ƙasa da alama ma da "matarshi ne yake magana, ganin MB ɗin ya miƙe zaune ya sa ya katse call ɗin yana kallonshi" """Ya jikin?""" "Ya ɗan lumshe idanu ""Na ji sauƙi"" ""Alhamdulillah""" "Shiru ne ya ratsa tsakaninsu na kusan mintuna goma kan Ahmad ya ce ""Yanzu kana jin daaɗin wannan rayuwa da ka zaɓar wa kanka Musty?""" "Ya san laifinshi don haka yace ""Ba Za ka gane b...""" """Babu abin da ba zan gane ba, baka da excuse na watsi da danginka ta ɓangaren uwa Mustapha...""" Shiru yayi feeling very guilty. """Na zo ne dama in ganka in ga lafiyarka, sannan kuma in faɗa maka a satin nan za'a fara bikin 'yar Uncle Abubakar na fari""" Ya ɗan yatsina fuska kaɗan alaman bai gane waye hakan ba. Cike da jin haushi Ahmad ya girgiza kai. """Ka san Bappa Hussaini?""" """Eh, ba shi ne babba a kaf familyn su Maamiey ba? Kuma za ku ce mishi Bappa saboda babban yayan Babanku kenan!""" """Shi dai wanda ba ya faɗar abu a family a tsallake, to danshi Abubakar ke aurar da 'ya""" Shi dai Mustapha ya san duka dangin mahaifiyarshi fushi suke da shi shiyasa suka jima da zare shi a abubuwansu dayawa kuma bai san su ba. """Zan ba da wani abu sai ka kai musu Allah ya sanya alkhairi...""" Wani irin Harara Ahmad ya sakar mishi cike da jin haushin shi """To hell with your money Almustapha! aka gayamaka kuɗinka muke bukata ne? Anya Almustapha??""" Idanu ya ɗan lumshe """Me kake so na yi Ahmad?""" """Meyasa wani lokaci kake abu kaman wanda aljani ya shafa ne? Yanzu kai har sai na faɗa maka abin da ya kamata? To ka tashi ka shirya mu tafi Nassarawa...""" "Shiru yayi kaman ba za shi ba, sai kuma ya ji kila zuwa chan ɗin zai rage mishi raɗaɗin rai da" damuwa da yake fama da shi don haka ya amince za shi. Ahmad da kanshi ya shirya mishi kaya yayi musu booking flight Washegari da safe suka dira a Nassarawa. "Drivern gidan Kakanshi ne ya zo ya ɗaukar su don Ahmad ya kira ya sanar da zuwansu, Dukda mahaifin mamanshi ya rasu haka ma mahaifiyarta amma akwai matan kakan nashi guda biyu sai kuma manyan yayyen mamanshi da suka haɗa uwa da uba da kuma waenda suka haɗa" uba kawai don family ne mai girma da iko a Nassarawa. "Kai tsaye gidan Bappa Hussaini aka yi da su don chan ɗin a cike yake da 'yan uwa, da kyar MB ya iya gaisawa da rabi kan ya sadu da Kakan nashi, dattijo ne na ƙwarai kuma mai dattako kowa faɗa yake yi mishi idan sun haɗu amma shi nasiha yayi mishi ya kuma nusar da shi" "amfanin zumunci, da kuma girmansu a gare shi, kan su bar gidan sai da kanshi ya ɗauki ciwo." Suna fitowa daga gidan sai ga Uncle Abubakar baban Amarya. """Yauwa Ahmad don Allah ga wannan kayi maza ka miƙawa Mamansu Asma'u sai ku wuce inda" "za ku dama neman ɗan aike nake""" "Karɓar Babban jumbo bag ɗin Ahmad yayi ya saka a boot suka shiga suka zauna MB na yamutsa fuska lokaci lokaci yana sanya hannu ya dafe kanshi dake sarawa, wani ɓangaren kuma yana ji da ya ɗauko Jasrah itama an ganta don hakika sashi mai girma na zuciyarshi ya" shiga farin cikin ganin 'yan uwanshi da saduwa da su hakika zumunci akwai daaɗi. "Yana kishingide yayinda Ahmad ke driving har suka isa gidan, buɗe musu gate aka yi ya shiga yayi parking ba ya son shiga ciki don haka ya buɗe motar ya fita ya bar MB kishingide idanunshi" a lumshe. "Mumtaz ya gani sai ya ƙira shi akan ya zo ya miƙawa Aunty Asiya sakon, sun zaga ya buɗe boot yana bashi kaman an ce MB ya buɗe idanunshi sai suka faɗa kanta, bai san ya miƙe zaune ba, at First ya zaci gizo ne idanunshi suke mishi kaman yadda suka saba, amma ko da ya rufe ya sake budewa ita ɗin suka nuna mishi, su huɗu ne suke tahowa daga gate ɗaya daga cikinsu ke magana ita kuma tana sakin murmushi akai akai, zuciyarshi ne ya shiga bugu da ƙarfi" ƙarfi sai da ya ganta ya tabbatar da yayi kewarta ba kaɗan ba. Sai da suka wuce ya buɗe kofar ya zuro kafafunshi waje ya sauƙo gabaɗaya. """Ahmad!""" """Kai fa baka da kunya ina kawunka amma ba wanda ya kaika iya kiran sunana gatsal""" Ahmad ɗin ya faɗa yana hararanshi. Ɗan tsaki yayi """Ni ba wannan ba, waennan da suka wuce suka gaisheka me alaƙarsu da gidan nan?""" Yadda yayi maganan da seriousness ya sa Ahmad cewa """Ko akwai wacce ta yi maka ne cikinsu? To dai duk matan aure ne""" """kana da sauran sani akan su don ƙarya kake""" Ya juya ga Mumtaz """Hibbah... Ka santa?""" Mumtaz yayi murmushi """Eh ai ita kaɗai ce budurwa cikinsu duk da suka wuce yanzu Yayata ce uwa ɗaya uba ɗaya"" Sai a lokacin ya hangi kamanni. Numfashi ya sauƙe mai nauyi" """Don Allah alaƙarku da gidan nan fa?"" ""Maman Amaryar sistern mamarmu ce"" Ya ɗan lumshe idanu ya buɗe." "Ba zai iya tafiya bai ga Hibbah ba, ba zai samu natsuwa ba muddin ya bar gidan bai ji sautin" muryarta ba. """Don Allah ko za ka yi min magana da ita?""" Mumtaz ya karɓi sakon yace yana zuwa ya wuce. Ahmad ganin yanayinshi ya sa yace """Amma ka santa ba tun yau ba ko?""" Kai ya gyaɗa """Labari ne mai tsawo da in mun zauna zan baka shi""" Kai Ahmad ya gyaɗa kan ya mishi jagora har karamin parlorn baƙin. *** "Nauyi girjinsa yayi saboda jin muryarta Dukda ga ta a kusa da shi zuciyarsa babu abin da take irin tuna illarda rashinta yayi masa a kwanakin nan, ya rintse ido zafin ciwon girjinsa na qaruwa fargabarshi rigimarta idan ta ƙara nesa da shi hakan zai fi azabtar da shi don ya san idan yayi" wasa rashinta na iya yin ajalinsa. Sonta daban yake cikin ransa ba zai taɓa ha'da soyayyarta da yake ji ba data kowa a "rayuwarsa, idanu suka ƙurawa juna suna sauraron bugun zuciyoyinsu." Ba za ta ce ga abin da take ji yana yi mata yawo cikin jini ba amma ko ma menene akwai tarin kewa da kauna ciki wanda take dannewa ƙarfi da yaji. "Motsawa yake yi yana nufarta a take sexy eyes ɗinta suka kara shige wa ba tare da ta san ta yi hakan ba tana kallonshi, shima ita yake kallo ko sau ɗaya bai kau da kai ba ta lumshe idanu ta sake buɗewa tamkar mai jin bacci ko mai magagin bacci don bata gama yardarwa kanta shi ɗin" "ba ne, ta ya ya san tana nan? Ta ya zai zo har cikin gidan nan ya sameta?" "Sassanyar kallon da yake binta da shi ya sa jikinta sakewa, dab ita ya tsaya hannunshi ɗaya cikin aljihu abu ɗaya ke mishi shamaki a duk lokacin da ya ji yana so ya fusgota cikin jikinshi sai ya tuna ba muharramarsa ba ce, ba zai iya hakan da gayya wa ubangiji ba... Kame wa zuciyarshi yayi ya tattare wuri guda ya ja numfashi a hankali da tarin kamshinta ciki kan ya" sauƙe ya buɗe lips ɗinshi ya ce """Hey...!""" Bata motsa ba har lokacin. """Hibbah...""" Ya saƙe kira his eyes not leaving hers for even a second. """AL-MUSTAPHA...""" """Yaaaa ilahi...Say it again!""" "Ya faɗa chan ƙasa ƙasa murmushi da bai san daga ina ba na ɗan kufce mishi, bai taɓa jin" "sunanshi ya tafi ya soki zuciyarshi ba sai da ya ji from her cracky, surprised voice da ya fita slowly and unbelievably." "Sai a lokacin ta tabbatar shi ɗin ne, kaman wacce ta farka daga bacci tayi baya kaɗan ya sake" matsota ta sake yin baya haka har ta mannu da gini tana kallonshi. """Me kake nema da ni ne? I thought na yi making everything clear to you ko ana so dole ne?""" "Ya lumshe idanu ya buɗe a kanta tuni sun ɗan jirkice ""Hibbah!""" "Ta kawar da kanta, he use his two fingers ya sa ƙasan chin ɗinta ya juyo da fuskarta gareshi ""Look at me magana nake miki""" That deep and calm voice ɗin shi yayi sending shivers all over her body. """Ina jina cikin Aminci ne a duk lokacin da idanuna suka yi tozali da kyakyawar fuskarki, ke ce ɗaya tilo tun bayan rasa Anam da zuciyata ta amince ta so, ta ya zan fara katangeta daga muradinta? Ke ce take so kuma ke ɗin nan zata cigaba da so har Abada...""" Idanunshi cike da tarin emotions yake kallonta. "Ta turashi baya tana komawa gefe, muryarta cikin rawa ta shiga cewa" """Na tsinewa kalmar So da ma soyayyar baki ɗaya I was already dead decades ago so ni ba mutum ba ce gawa ce don haka bana bukatar soyayya ka kyale min rayuwata MB MUSTAPHA ka fita daga cikinta bana kaunarka bana kuma sonka har abada kuma ba zan so ka ba don na gama so.""" Cikin karyayyiyar murya dake gab da fashewa da kuka tayi maganan idanunta zube cikin nashi "da take iya karanto ɓacin rai, fushi da hasala da irin kalaman ta gareshi." "Bayan duk abin da ta aikata bai ji kaman zai iya rage soyayyarta daga zuciyarshi ba, kalaman ta basu yi mishi komai ba kaman nesanta kanta da tayi da idanuwanshi na tsawon lokaci, matso wa yayi gabanta har tana iya shakar ni'imtacciyar kamshinshi da kan kara gudun bugawar" "zuciyarta, ya sanya idanunshi ya sarkafe nata cikin wani tone ya shiga cewa..." """Duk inda za ki shiga a faɗin duniya sai na lalubo ki Hibbah na yiwa kaina alkawari sai na saka ki farin ciki mai ɗorewa, sai na gusar miki da ɗaci da raɗaɗin da kika fuskanta a baya a kan SO, sai na ga kin yi dariya sai na ga kin samu ingantacciyar rayuwa ta fannin auratayya babu inda za ki gudu ki layance min na yiwa kaina wannan alkawarin kuma ba zan taɓa sarara wa ba har" "na cika shi ko kina so ko baki so""" "Tayi saurin kallonsa hawaye na tsere bisa fuskarta zuciyarta kaman zai ratso ya fito, bai bari ya" ga hawayen ba ya juya ya fice da sauri ta fashe da kuka mai tsuma rai tana kai wa ƙasa… 66 "Ta jima zaune a wurin tana kuka kan ta share fuskarta ta miƙe tsaye tana tafiya tamkar marar lafiya, sai yaushe ne ita kam za ta daina zubar da hawaye a kan maza? Sai yaushe rayuwarta zai daidaita kaman kowa? Ashe shawarar ƙin auren ma da ta yankewa kanta ba zai taɓa ficce ta ba?" Ko da ta isa parlorn bata tsaya ba ta wuce kowa zuwa ɗakin da suka sauƙa ta kwanta tare da runtse idanu cikin tunanuka iri iri amma kalamanshi sun fi komai yawo a jini da jijiyarta. "Shi kuwa yana ficewa mota ya koma ya samu Ahmad yana shiga ya zauna kawai ya dafe kanshi da yake sara mishi kaman zai tsage, Hibbah dab take da haukatashi bai san me zai mata ta fahimci da gaske sonta yake ba, bai san ta ina zai fara convincing ɗinta cewar shi ba kaman kowani namiji ba ne a rayuwarta ba, ba zai taɓa mayar da ita chakwakwalin taɓon da ta" fito ba sam a doguwar safararta da maza. """Ya dai Musty?""" "Ya ɗan haɗiye abu mai kauri kan cikin shakakkiyar murya ya ce ""Ahmad ina cikin matsala wallahi...help me out please""" "Yadda yayi maganan ya tabbatar wa Ahmad cewa da gaske yana cikin matsalar don kaman ba jarumin namiji kuma tsayayye ba, duk dakiya da dauriyar namiji idan ka ga abu ya karya shi" haka ba kaɗan ba ne. A hankali ya bashi labarin soyayyarshi da Hibbah briefly kuma ya nuna mishi ne cewa ta sha wahala sossai akan soyayya a baya har tayi give up da batun soyayya ko aure. """Kar ka damu zan san yadda zan taimaka maka akan hakan, ka kwantar da hankalinka a" "labarin da ka ba ni itama ta jima cikin Soyayyarka she just can't admit ne""" """Ni ma na tuna hakan amma the way she always Look into my eyes tace ta tsane ni Its freaking me out""" Ya faɗa yana kishingida ko yaya dai ya samu sanyi tunda yayi shearing matsalar shi da ɗan uwanshi. "Har suka isa masaukinshi basu sake magana ba don MB dai miskilancin nashi ne ya motsa, a gidan Ahmad din ya sauka boysquarters ɗin shi matarshi Zainab na da kirki sossai ta shirya" musu abinci iri iri kan su iso sai dai MB bai iya ya wani ci na kirki ba ya kwanta. "Washegari babu inda yaje har yamma da aka shirya wani cocktail party da dare, bai yi niyyar zuwa ba don haka bai ko tashi ba bare ya shirya, yana nan zaune yana ɗan duba wani abu a system ɗinshi ya shiga tunaninta, kila kuma fa zata je taron nan, he felt a surge of jealousy" kawai ya ji ba zai iya zama a gida tana cikin taron maza ba. "Tsam ya miƙe ya ya wuce toilet ya ɗauki lokaci sossai ƙasan shower ruwa na jiƙa kowani ɓulin gashi na jikinshi kan ya ja towel ya ɗaura a kwankwasonshi ya fito, a tsaye yayi duk wani shafe shafe da zai yi ya yiwa jikinshi barin turare kan ya nufi wardrobe da ya zube kayanshi ya shiga duba suite don theme ɗin Black ne and White, a banza ma zuwa office yana shiga da fice a" tsadaddun suites masu ɗaukar idanu bare a biki. "Tuni ya fito as the CEO he is, composure da charisma suna kuka, wani irin fitinannen kamshi yake fitarwa yadda kuma ya kame fuska zai tabbatar maka da wani abu na damunshi." "A jikin wata BMW ya samu Ahmad da matarshi don za su je su ma. ""I thought ka ce ba za ka ba?""" Ahmad ya faɗa yana kallonshi. """Change of mind""" Ya ɗan waiga yana kallon garage na gidan don gaskiya family ɗinsu na da karfi da dukiya ba laifi haka Ahmad ɗin ma na da kalar nashi dukiyar don babu wanda ya nade hannu ya zauna a cikinsu. """Ba ni makullin wanchan motar""" Ya nuna wata Prada baƙa komai nata baƙi ne har glasses ɗin. "Juyawa yayi ya kalli matarshi ""Dee ɗauko mishi""" Ta juya ta koma ciki ba'a jima ba sai gata ta miƙa wa mijinta shi kuma ya miƙa mishi. """Za ka iya gane venue ɗin dai ko?""" Kai kawai ya gyaɗa kan ya ɗan daga musu hannu ya nufi motar ya shiga ya fice daga gidan. "Ya ɗan jima yana zagaye a garin kaman ba za shi ba daga karshe dai ya nufi wurin yayi parking, duhu ya sauƙa already amma cikin wurin na da wani irin haske na tarin kwaya kwayan lantarki, motoci ne birjik a wurin kala daban daban masu tsada da ɗaukar idanu, ya buɗe kofa ya sauƙa ya nufi ciki hannunshi riƙe da car key ɗayan kuma sanye a aljihunshi har ya isa ciki, theme ɗin ciki Black ne and maroon wani irin ado ne cike da hall ɗin kowani table an tsara shi" yadda ya kamata. "Akwai mutane amma babu hayaniya don abu ne na masu akwai kuma akwai natsuwa da ilimi, enterance ɗin ta gaba ne don haka yana shigowa hankalin dayawa ya koma kanshi, tafiyar shi ya cigaba da yi har ya isa inda ya zaɓa wa kanshi zama ya ja chair ɗin ya zauna yana harɗe" kafafu. """Ke Hibbah! Wanchan ba CEO ɗin ku ba?""" Zaitoon tayi magana tana kallonshi. Tun da ya shigo ta ganshi amma sai tayi saurin ɗauke kai don wani irin faɗuwar gaba da ya "riske ta, ita karan kanta bata san me yake yi a wurin bikin ba ko menene alakarshi da bikin." "Bata yi niyyar zuwa ba amma su Zaitoon suka yi mata dole, sanye take da wani baƙin expensive lace da aka yi mata ɗinkin da ya zauna mata kwarai da gaske, jewelries ɗinta duka silver ne har takalmi heel dake kafafunta zuwa clutch ɗinta, dama ita ɗin gwanar saka high" heels ne Dukda tsawonta. Simple makeup ne a fuskarta haka ɗaurin mai sauƙi aka yi mata she looked snatched and she's just shouting money and class duk motsinta. Maganan Zaitoon ya sa su Huda duka mayar da hankali kanshi. """Masha Allah""" Hudah ta faɗa. """Hibbah amma wannan 'yan mata rushing suke a kanshi ko?""" "Ta juyo tana yiwa Hibbah magana, ɗan tsiririn tsaki ta ja bata kalli inda yake ba tace ""Wa ya san mishi""" Aina'u tace """Shi ne baban yarinyar chan Jasrah?"" Kai hibbah ta gyaɗa." """Allah sarki gashi bashi da mata amma wallahi kyakyawa ne""" Zaitoon tace """Ga kirki, ga halin ƙwarai don wlh samun matashi mai kukan kuɗi Natsatse kaman shi sai an bincika sossai, wai kun ga kirkinshi kwanciyar Hibbah a asibiti?""" Nan Zaitoon ta fara basu labari Tsam Hibbah ta miƙe don maganarshi da suke ma yana sa ta ji wani abu na yi mata yawo a "cikin jiki, gashi tana so ta kalli inda yake amma tana tsoron sharrin zuciyarta da ya kasa barinta ta sarara da bugu tun shigowarshi wurin." "Miƙewarta ya sa idanunshi spoting ɗinta, ya ɗan datse lips kaɗan yana ƙara kallonta da kyau yarinyar nan ta gama da zuciyarshi, a yanzu ji yake kaman ya sace ta kawai ya gudu da ita kowa ya huta, bai motsa ba glasses na idanunshi kuma bai bari kowa ya san me yake kallo ba" amma ita a jikinta take jin idanun nashi. Table da Abdul da matarshi suke kai a tare da wani abokin shi ta zauna. """Su Zaitoon sun matsa miki ko? Na sanki da rashin son surutu su kuma kaman rina haka suke da zuba""" Abdul ya faɗa yana kallonta. "Ta ɗan yatsina fuska kaɗan cikin yanayinta tace ""Har kaina ya fara ciwo Yaya Abdul""" Abokin shi dake kallonta yace """Very sorry irin wannan wuri ai ba naku ba ne"" Ta ɗan yi murmushi kaɗan." "Wani irin abu MB yaji yana yawo a jikinshi na fushi da kishin da bai ma taɓa sanin yana da shi ba, numfashin shi yaji yana fita da sauri sauri, hannu ya miƙa a tray da ake ta yawo da su da drinks kala daban daban ya ɗauki ɗaya ya kurbi kadan ko zai ji sauƙi yana saukewa idanunsa" suka sauƙa kansu. Abokin Abdul ɗin ya ɗauki drinks ya miƙa mata """Sorry ki sha wannan kila za ki ɗan ji dama dama""" "Bata so ta yarfa shi ne da babu abin da zai sa ta karɓa, ɗaga idanun da zata yi sai cikin na MB ya zare glasses ɗin yana jefanta da wani irin kallon da bata san na menene ba, hannu ta miƙa" ta karɓi cup ɗin sai ta ɗan kalli gayen tace """Thanks""" Wannan murmushi da take yiwa wani shi kuma take haɗe mishi rai ya ƙara tunzura shi bai san ya matse glass cup ɗin sossai ba sai da ya ji fashewarshi a hannunshi da sauri ya miƙe kawai ya bar hall ɗin. "Bata taɓa ganinshi cikin yanayin ba, ta tsinci kanta da rasa sukuni, Miƙewa kawai tayi itama ta" "fita daga hall ɗin babu abin da bata kitsa a ranta ba, me yayi provoking ɗinshi haka? Tana tafiya kawai ta ga mutum tsaye ya juya bayanshi." "Hannunshi ta bi da kallo MB ne kuma hannunshi jini ne yake ɗiga, a rikice ta zagaya ta" gabanshi tana riƙo hannunshi ba tare da ta sani ba. """Ya ilahi...MB ka ji wa kanka ciwo!""" "Zame hannun yayi don tamkar electric shock ne ya bi jikinshi, idanunshi da suka sauya sossai" "ya zuba mata sam hankalinta ba ya ga fuskarshi, hannunshi ta sake riƙo wa tamkar za ta fashe" da kuka ta ce """MB bleeding kake fah...""" Ya sake fusge hannun wannan karo da ƙarfi. """Ina ruwanki da ni? Ko mutuwa na yi a yanzu Hebbah ai ba matsalarki ba ce..."" Ya juya zai tafi tayi saurin shan gabanshi." """Ba Za ka tafi kana cigaba da zubar da jinin nan ba, broken glass ne fa a hannunka ko chemist mu je a cire a wanke maka please MB""" Bata hankara ba ashe hawaye take yi. "Yadda ya zuba mata idanu cikin sanyi ya sa jikinta sakewa, itama idanu ta zuba mishi tana" barin hawayenta cigaba da zuba dama me neman kuka ne aka jefe shi da kashin awaki. """Hibbahh!""" Ya ƙira sunanta a tsakankanin numfashinsa. Idanunshi na ƙara shige wa cikin nata a hankali ya ce """Why won't you admit it? Kashe ki zai yi ne idan kika yardarwa kan ki cewa you've fallen..hopelessly inlove with me?""" Ta ɗan runtse idanunta da suka gama jirkice wa ta buɗe. 'Sauran wasu babu wanda zai taɓa sonki gwara ma ki yarda na miki alfarma' Kalaman Usaib kenan a gareta a sadda ya kusa gamawa da rayuwarta bayan amincin da ta bashi. "'wannan...Wannan azzalumar macuciyar ita ce Hibbatullah ashe ban sani ba kura ce ita lulluɓe da fatar akuya ina yi mata kallon biri a ayaba take kallona, Wlh ta zalunceni inda Allah ya so ni ban kai ga aurenta ba amma tirrr tirrr na yi Allah wadai da ranar da na fara ganin Hibbah'" Kalaman Mahmud kenan a sadda ya wargaza taron ɗaurin aurensu. Runtse idanu ta sake yi da ƙarfi tana tuna irin matsaltsalun da ta shiga da irin munanan kalaman jama'a masu yawa a kanta. Muryarta na rawa sossai ta ce """Al-Mustapha an ce duk wanda zai dauƙeni rufa min asiri kawai zai yi ba don da gaske zai so" "ni ba """ "Ya ƙara taku biyu zuwa gabanta yana kallonta cikin karyewa don yana iya hango pains ɗinta daga cikin kwayar idanunta, yana jin zafin kalamanta na fita daga muryarta alamar har zuciyarta" raɗaɗi yake mata. Ta ɗan yarfa hannu cikin rashin sanin Makama ta ce """All my live i've just been used and dumped Meyasa zuciya bata da ƙashi ne?""" Ya saƙe ƙara taku biyu ya ɗago hannunshi mai lafiyar ya kai fuskarta ya sanya thumb ɗinshi ya "ɗauke hawayen dake kara zuba nonstop, cikin taushin murya ya ce" """Don't say that, duk namijin da zai iya cheating on you is an idiot, kuma basu chanchance ki ba""" Ta haɗe lips ɗinta tana ɗaga kwayar idanunta sama don hana kanta kuka ba zai gane abubuwan dake bijiro mata ba a duk sadda tayi yunkurin amincewa kanta cewa tana sonshi. Cikin taushin murya ya ce """Hibbah A girl like you need to be cherished and loved...let me love you Hibbah""" "Wani irin motsawa zuciyarta ke yi da ƙarfi, ya sauƙe hannunshi yana cigaba da kasheta da wani" fitinannen kallo mai tsuma jini ya ce """Everything I feel for you is real, my intentions are pure and burina shi ne in ganki cikin farin ciki da walwala, as well as making sure you have no doubt on how deeply loved you're. I know I'm not perfect, and i will never pretend to be, Amma na yi miki alƙawari I will always give you the best of me." "Even on the toughest days, I won't walk away. I'm always here and I'm not giving up on us ever...""" "Kafafunta ne suka ji ba za su iya ɗaukarta ba, zamewa take ƙoƙarin yi for the First time ya sa" hannu ya riƙe nata hannun yana kallonta ido cikin ido. Damshin da ta ji ne ya sa ta mayar da idanunta kan hannun da ya riƙe nata har lokacin jininshi "na zuba, idanu ta kai kan keys ɗin shi kawai ta zara ta riƙo ɗayan hannun nashi ta buɗe motar" "tana kallonshi, bai yi musu ba ya shiga ta zaga ta shiga drivers seat ta zauna ta ja motar ta fice daga wurin ba tare da kowa yayi magana a cikinsu ba, bata yi tafiya sossai ba ta samu chemist sauƙa tayi ta shiga chan ta fito da ƙaramar leda ta dawo motar ya lumshe idanu kawai yana" mamakin dakiyar zuciyarta da shirun ta. "Hannunshi ya ji ta kama ta saka wani ƙaramin aska ta zare glass ɗin daga lallausan tafin hannunshi, sai ta buɗe baki tana hura mishi iska a hannun a hankali, lumshe idanu yayi yana jin duk wani tsiga na jikinshi na tashi, a hankali ta goge ciwon kan ta saka bandage ta zagaye tafin" hannun. "Sai da ta gama ta kunna motar ta fita daga wurin, bai ce komai ba yana kishingide idanunshi a" lumshe. """Ina zan kai ka?""" Tayi maganan cikin dasashiyar muryarta. "Ya buɗe idanu ya zuba mata, yana kallon side face ɗinta Dukda fuskarta da ya sauya sossai, hancinta yayi Red kuma idanunta sun ɗan kumbura kaɗan wani irin kyau ta yi mishi da har ya shagaltu a hankali cikin raɗa ya ce" """God! You are beautiful Hibbah kin san da hakan?""" "Saura kaɗan ta saki kan motar amma ta riƙe, ta samu wuri tayi parking ta waigo ta kalleshi." """Ina zan kai ka?"" ""Ki kaini gidanku""" "Ya faɗa, ta zaci gatse yayi mata haka ta kunna motar ta nufi gidan Aunty Asiya har harabar tayi" parking kan ta sauƙa kawai ta shige ciki. Ya jima zaune a wurin kan ya ɗaga waya ya kira Ahmad yace ya zo ya ɗaukeshi abin mamaki tun da ta bar wurin ta samu wuri ne cikin duhu ta zauna tana kallon motar har Ahmad ya shigo gidan ya shiga motar ya ja ya bar gidan da shi ciki sai a lokacin ta ɗan sauƙe numfashi tana dafe zuciyarta. 67 "Tun da suka bar gidan Ahmad bai kuma sake gane kanshi ba, Dukda ya kyale shi bai matsa" "mishi ba don da kowa ke tambaya a family ina ya shiga ko ya tafi ne? Sai ya ce baya ɗan jin daaɗi ne amma yana nan, babu event da ya sake zuwa na bikin har sai ranar ɗaurin aure." "Kaman haɗin baki itama bata sake wani walwala ba, bata so ma ta fita kar ta haɗu da shi tunda ta kula yana da alaƙa da gidan Dukda Asma'u tace bata sanshi ba da su Zaitoon suke tambayarta hakan bai sa hankalin Hibbah ya kwanta ba, an yi mother's eve an kuma yi kamu" amma duk yadda aka yi da ita ta ƙi zuwa tun Momma na mata faɗa ma har su Mommy da "Umma suka ce ta kyaleta bata san me ke damunta ba, sun yi rarrashin har sun gaji amma ta" kasa faɗa musu komai. Yau da ake ta shirye shiryen ɗaurin auren da misalin ƙarfe takwas Mommy ta shigo ta sameta tana kwance. """Hibbah!""" "Ta amsa ba tare da ta miƙe zaune ba. ""Tashi ki zauna mu yi magana"" Miƙewa tayi ta kai zaune." """Ko da ba za ki faɗa wa kowa damuwanki ba bai kamata kowa kuma a gidan nan ya fahimci cewa ba ke ba ce Hibbar da kowa ya sani a baya, na kula kin jima da dorawa kanki miskilancin da ya ci uban ma wanda kika samu a kwanakin baya-bayan nan, bakya walwala bakya hira da" "kowa kullum a kwance a kwance tamkar ruwa, kin fi so ki ganmu cikin damuwan ne mu ma?""" "Ta girgiza kai idanunta na cika da kwallah, a kanshi ta rasa duk wani ƙwarin gwiwar ta, a kanshi ta rasa duk jarumtar da ta jima tana sakawa kanta, a kanshi zuciyarta ta ƙi bata haɗin kai, duk iya kokarinta na cisgeshi ƙarfi da yaji ta kula ba za ta iya ba amma menene kuma zai zama" makomarta idan ta aminta da shi? Abin da kenan ke bata tsoro yake ɗaure ta da jijiyoyinta. """Mommy ki yi haƙuri!""" Ta faɗa cikin sanyi hawayenta na zuba. Hannunta mommy ta kama """Ba haƙuri nake so ba, ina so ne ki fitar da abin da ke ranki ki huta Hibbah har yaushe za ki cigaba da wahalar da zuciyarki? Babanki karan kanshi na cikin damuwar wannan hali da kika tsira kuma gani duk muke kaman mun tauye ki, gani muke kaman mun kasa baki farin cikin da kika chanchanta""" """Mommy kun yi min komai ai, kun yi haƙuri da ni kun tayani rungumar kaddarata baku bar ni ni" "kaɗai ba on all my hardest days, ina so kawai ku cigaba da tayani da Adu'a ne Allah ubangiji ya yaye min abin da nake ji idan ba alkhairi ba ne""" "Mommy ta ɗan rungumeta kaɗan tana bata warmness na uwa da ta san ba lallai Momma ta bata shi ba, Dukda ta san Momma macece mai ƙoƙari akan yaranta da ibada na musamman saboda su don bata taɓa hutawa da sadaka da adu'o'i akan Hibbah da ta fahimci ƙaddararta mai zafi bane kawai dai bata nunawa ne a ganinta idan ta nuna ɗin sai dai ya ƙara karya hibbar ba dai ya ƙarfafata ba, a ganinta idan tana nuna mata bata jin daaɗin zamanta hakan kila za ta" kunce ɗamarar da ta ɗora wa kanta na babu ita babu aure a duniya. """Komai ya zo ƙarshe da yardar Allah Hibbah, ina da yaƙinin daga yau ba za ki sake kukan baƙin" "ciki ba""" Ita dai shiru tayi idanunta a lumshe kwance jikin Mommyn. Ɗagota tayi """Ummanku za ta kawo miki kaya ki yi wanka ki saka don Allah ki fita cikin mutane kin ji?""" Kai ta gyaɗa har mommy ta miƙe ta fice Hibbah ta bita da kallo kawai. "Bata koma ta kwanta ba sai ta bi umurnin Mommyn ta shiga wanka, ta jima ƙwarai cikin ruwa kan ta fito Allah ya sa akwai dryer don har gashinta sai da ta jiƙa ko za ta ji sanyi, ta zauna tana busar da kanta sai ga Umma da wasu kaya a leda fari, karɓa tayi ta busar mata da gashin da" kyau tana janta da hira kaɗan kaɗan har suka gama gashin ya kwanta sossai. "Kaya Umma ta bata bayan ta saka fararen inners, tayi murmushi kaɗan don dai bata san ina umma ta samu kayan ba duk kuma suna mata hakan ne saboda ta sake kaman kowa ko ba komai kuma ta ji daaɗi ko da ta saka doguwar rigar farar tsadaddar lace ɗin tamkar an gwadata" "cib da cib da jikinta, wani farin embroidry Mini Gyale ta bata ta saka." """Tabarakallah Masha Allah""" Umma ta faɗa tana ƙara mata turare kan kayan dake ta kamshi. """Umma kayan nan kamshi""" "Ta faɗa tana lumshe idanu don kamshin gwanin daaɗi ""Na kara miki shi ne a kabbasar Amarya""" Umma ta faɗa tana murmushi. """Bari na turo miki me ɗaurin da ta zo yi wa Asma'u tayi miki me kyau sai ki saka gyalen ki fito"" Tayi murmushi mai sanyi har Umman ta fita." "Chan sai ga me ɗaurin tayi mata very simple, bata sa powder ba ta saka lipgloss kawai da" kwalli don idanunta da suka ƙara girma saboda yar rama da tayi da haske sun yi fari sol. "Fitowa tayi kaman yadda su mommy suka buƙata ta shiga cikin 'yan uwa kowacce da kalar wankanta, Huda ta riƙe hannunta suna magana kasa kasa duk kuma mita take mata akan ta" sauya mata ba kaman da ba sai dai Hibbah tayi murmushi wani abin yanayi ke chanza shi. **** "Tsaye yake ƙasan shower da ke ta zubar da ruwa daga kanshi har tafukan kafafunshi, sossai yake jin wani irin uneasiness a cikin zuciyarshi, anya idan da gaske wannan masifaffen yanayin da yake ji akan Hibbah shi ne da gaske so kenan menene ya ji akan Anam? Ba Ya tunanin akwai wani laifi da Hibbah za ta mishi wannan abu da yake ji ya sassauto mishi daga ranshi, ba ya tunanin komin nisan lokaci zai warke daga mummunan tarkon so da ya faɗa na Hibbah, idanunshi da suke lumshe ruwa na tsiyaya akan lashes ɗin shi masu tsai ya buɗe sun ɗan rine ya miƙa hannu ya kashe shower ɗin kan ya tako ya zo ya ɗauki towel ya ɗaura daga" kwankwasonshi. "Cikin tafiyarsa na cikakke kuma kakkarfan namiji mai jini a jika ya fito daga bayin ya samu wuri ya zauna ya shiga shafe shafe tamkar mace saboda yadda yake kashewa jikinshi lokaci da kuma kuɗi shiyasa koyaushe yake nan tamkar ka lashe, kamshi kuwa ba'a magana don har" fatar shi ta gama riƙe fitinannen kamshinshi. "Fararen kayan da ya tanada saboda ɗaurin auren ya warware ya fara sakawa, sun sha guga sai walwali suke saboda haske, ya saka wando da ƴar ciki ya ɗauki hula ya kafata da kyau, ba karamin kyau manyan kaya ke mishi ba ko don baya son sakawa ne oho, ya ɗauki garen ya riƙe a hannu don dai shi bai san yadda zai saka ba, wayoyinshi ya ɗauka sai ya ga tarin missed" "calls na Ahmad, yana fitowa ya sameshi daga parlorn boysquarters ɗin." """Sannu ko?""" Ya faɗa yana dan harararshi yayi murmushi """Afuwan tuba nake booking flight ne ya daukeni lokaci sossai saboda network issue""" Miƙewa Ahmad yayi """Da gaske 12 ɗin za ka wuce legos?"" Kai ya gyaɗa suna nufar waje." Me zai zauna yi? Idan ma ya zauna zuciyarshi za ta cigaba da ingizashi ne kawai ya neme ta ya kuma san ita a wurinta zai zama tamkar takura ne and he can't risk that don haka gwara ya tafi kawai. "Ahmad bai ce komai ba har suka isa farar motarshi da ta sha wanki tana sheki, gefen zaman banza MB ya buɗe ya shiga kawai ya zauna, Ahmad ya shiga driving seat ya ja motar suka fice daga gidan." "Kaman yadda al'ada dayawa take a kofar gidansu Amarya ake ɗaurin aure wannan ma bata sauya ba, canopies ne masu yawa a kofar gidan cikin tsari da natsuwa aka tsara komai, motoci ne birjik a Layin unguwar har ya shiga wasu layukan mutane kuwa na nan dayawa ana ta ribibi" kaman yadda muka san kowani wurin ɗaurin aure. Suna sauƙa Ahmad yace """Kawo babban rigan nan in tayaka sakawa ina amfanin rike shi a hannu?""" "Bai Musa ba ya bashi ya taimaka mishi ya saka ya gyara mishi kunnuwan kan suka ƙarasa daga ɗan gaba gaba suka zauna, manyan mutane ne birjik a wurin, ga Kakansu wa ga wanda ya haifi mahaifiyar Mustapha ga yaranshi ga wasu uncles ɗinshi dayawa, ga su Daddy Rabi'u, Daddy da su Uncle Zaid kowa na wurin har mahaifinsu yaya Abdul da bai cika zama ba ya" samu halartar ɗaurin auren. Aka yi gabatarwa aka fayyace ma'aurata kan aka kulla aure bayan miƙa sadaki dubu ɗari biyar "aka shafa fatihar auren Asma'u da angonta Abdulwahab, bayan nan mai riƙe da loud speaker" ya cigaba da cewa a dakata akwai wani ɗaurin auren. Uncle Muhammadu wa ga Ahmad wanda shine babba cikinsu gabaɗaya ya dubi Almustapha """Miƙo min sadakinka nan!""" "Wani irin kallo na ban gane ba yayi mishi kan ya kalli Ahmad, Ahmad yace" """Ka bayar ko baka shirya mallakar sahibar taka bane?""" "Kanshi ya sake ɗaurewa. ""Ahmad me kake nufi ne?""" """Ina nufin ana jiranka ka biya sadaki a ɗaura maka aure da Hibbatullah bisa amincewar" "magabatanta""" "Da a tsaye yake babu abin da zai hanashi losing balance ya faɗi, wani irin tsalle zuciyarshi yayi," tuni ya sa hannu ya fara lalubar aljihunshi har lokacin a ɗan ruɗe yake. "Akwai kuɗi jikinshi sabbin notes na 1-1k amma ba zai iya biyan su kuɗin sadakin Hibbah ba, ɗayar aljihun ya laluba ya zuba Dollars ciki wanda kwata kwata 1,000 US Dollars ne guda biyar. ""Ahmad zan musu transfer""" Ya faɗa yana ƙoƙarin zaro wayanshi Ahmad ya riƙe hannunshi """Wannan ma ya isa idan ba sayanta gabaɗaya zaka yi ba""" "Ya karɓi $5,000 ya miƙawa Uncle Muhammadu wanda daidai suke da 7.5mil a kuɗin Nigeria tuni aka shiga gabatar da aure na gaba." "Cikin rashin tsammani, cikin yarda da hukuncin ubangiji, bisa sahalewar iyaye da tarin dumbin" shaidu tamkar almara kunnuwa dayawa suka ji shigar shafa Fatiha an ɗaura auren. AL-MUSTAPHA BASHIR ALMUSTAPHA DA HIBBATULLAH MUDASSIR MADAKI Alkawarin Allah ya cika. "Daga wajen Daddy hawaye ya dinga zubarwa yana godiya ga Allah, Almustapha ya sulale ya kai goshinshi ƙasa yana yi wa Allah kirari, ya roƙe shi kuma ya amsa masa ya mallaka masa Hibbah a yau cikin rashin zato ko tsammani." Ahmad ya shafa bayanshi kan ya ɗagoshi idanunshi kawai ya runtse yana amsa ba da hannun da ake ta mishi na taya murna. "A cikin gida kuwa, bayan an ɗaura auren Asma'u suna ta mata tsiya saboda loud speaker da yake ratsa ko ina, sai suka ji ana cewa a dakata za'a ɗaura wani auren da mamaki dayawa suka mayar da hankali, Momma, Mummy da kuma Umma da Aunty Asiya duk sun natsu zukatansu na harbawa har sai da suka ji an shafa fatiha tsakanin Hibba da Almustapha kan duk" "suka kai ƙasa Momma sai kuka, Umma karan kanta hawaye take." "Su Zaitoon ma duk sujuda suka yi na godiya ga Allah sai kuma kowa hawaye, ita kam Hibbah jin an ɗaura ɗin wani irin bugawa da zuciyarta yayi sai ya tsaya chak, tana jin hayaniya tana jin sautin kuka, tana ji ana rungumeta amma tana jin hakan ne tamkar daga wata uwa duniya ba duniyar da take ciki ba, har lokacin kunnuwanta na jiye mata sadakin da aka ambata da kuma" shafa fatiha da aka yi. Hudah ta jijjigata ganin ko motsi bata yi tamkar gunki ake rungumewa ana tayata murna. """Hibbah! Hibbah ki godewa Allah, ashe muna da rabon jin ɗaurin aurenki da kunnuwanmu?" "Ashe komai zai wuce tamkar ba'a yi ba?""" Da ido ta bi Hudah kaman bata gane abin da take cewa. Momma ce ta cire nauyi ta zo ta kama hannunta ta ja ta ɗaki suna shiga ta rungumeta Tsam a jikinta tana furta """Alhamdulillah! Alhamdulillah!! Alhamdulillah ya Allah da ka nuna min wannan rana da lafiyata""" Hawayenta dake sauka jikin Hibbah su suka sa jikinta ɗaukar wani masifaffen rawa. Zamewa take kokarin yi ƙasa Momma ta riƙota zuwa bakin gado suka zauna. "Bata iya ta furta komai ba sai rawa da jikinta ke ta yi hawaye kuma ya fara sintiri a kumatunta bata san me zata yi ba, jikinta kawai karɓan mixed emotions yake don haka ta kasa karɓar farin" "ciki, takaici ko kuma ma dai bakin ciki duk bata sani ba." "Magungunan ta Momma ta fidda ta bata ta sha, tuni ta sulale a kwance bata sake mintuna biyu ba bacci ya ɗauketa don suna da ƙarfi shiyasa ba koyaushe take sha ba sai zuciyarta ya shiga" cikin ruɗu. "A parlor kuwa bidiri ne ya buɗe kan ka ce kobo status na duka Ahalin Madaki ya ɗauka da congratulations Hibbah Allah ya sa gidan zamanki ne, wasu su yi in text wasu su saka hoton ta" su rubuta a ƙasa kowa na cikin walwala da farin ciki. Chan waje kuwa MB ne ya ja Ahmad suka koma mota. """Har yanzu ji nake tamkar mafarki nake yi Ahmad, ji nake tamkar zan farka in riski wannan lokaci a matsayin Almara, ni din nan yanzu mijin Hibbah nake amsawa? Ta yaya Ahmad ta yaya" "hakan ya kasance?""" Ahmad yayi murmushi yace """Tun bayan rasuwar matarka Anam muke cike da tarin kewa da tunanin irin rayuwar da kake yi, MB bamu ƙi uwar goyonka ba amma tabbas da mahaifinka ya amince mana da baka tashi hannunta ba don bata taɓa kaunar mahaifiyarka ko ahalinta da zuciya ɗaya ba amma duk kowa ya barwa kanshi wannan don kai uwa ka ɗauketa a baya ko magana marar kyau aka yi a kanta idan ka tafi baka sake waiwayarmu kuma. Duk mun san cewa mace ta gari ce kawai zata taimake ka wurin sanin girman ahalinka da muhimmancinmu a rayuwarka tsoronmu jinin mahaifiyarka kar ka dauko wata macen da zata sake ƙarasa lalata dan guntun alakar hakan ya sa da ka zo min da batun Hibbah na yi bincike a kanta sossai na ji abubuwa da dama wanda kai baka ma sani ba amma ba abin ne ya dameni ba don na san duniya babu abin da ba za'a ce ba da zarar wani jarrabawa ya sami bawa, tana da halin ƙwarai, tana da natsuwa da tarin ilimi" "kuma tana da nagartaccen asali da haka na samu Yaya Muhammadu da batun...""" 68 """Ya yi farin ciki da jin zancen barin ma da yaji ai akwai alaka mai karfi tsakaninta da matar Yaya Abubakar don haka ya same shi da batun ta kai tsaye shi kuma ya sake tabbatar da kyaun asali da halayyarta da ya sani, mun samu Baba Hussaini shima ya bada goyon baya, nan take Yaya Abubakar ya samu babban Yayan mahaifinta, ya yi farin ciki sossai amma yace zai yi shawara" Dukda shi kam idan ta shine ya bayar. "Ya tafi sun yi shawara da 'yan uwanshi mazan a yadda na ji har matan ya ajiye su kuma Mommy wacce ta zauna wurinta legos ta ba su labarin irin kyaun halinka, su karan kansu da aka fayyace musu wanene sun nuna sun san ka farin sani kuma suna Na'am da wannan aure mahaifinta ya nuna a bari sai nan da wata biyu a haɗa auren da Yayanta amma sai Yayanshi ya" "ƙi yace a ɗaura a yau in ya so wata biyun sai ta tare don idan abu ya zo a yi shi kawai. To ka ji""" "Wani irin hug MB yayiwa Ahmad sai ya fara hawayen da yake dannewa, rabon da ya zub da hawaye ya manta don yana da jarumta kwarai da gaske amma wannan hawayen sun kasa" "dannuwa, hawaye ne na farin ciki tsantsa da bai san ya zai yi da su ba." """Na gode Ahmad... Na gode kwarai Uncle Ahmad ban san da wace kalma zan yi amfani wurin" "gode maka ba amma tabbas ba ni da kamarka a wannan duniyan""" Ahmad ya ɗago shi yana murmushi """Anything for you son, me nayi idan ban cika maka burin zuciyarka ba? Ko ka manta kai ka ce in taimaka maka? tamkar babban yaya nake a wurinka don ban ɗauki Adda Rabi'ah Yaya ba, ita ɗin madadin uwa ta taka a rayuwata ban buɗi idanu na ganni da mahaifiyata ba, ita na sani...""" Ya ɗaga kai sama yana son hana hawayen shi zuba. Shi MB Dukda bai santa sossai sossai ba ko ba zai iya tuna yadda take sossai ba yaji tsikar "jikinshi ya tashi, a hankali yayi mata Adu'a Ahmad ɗin yana amsawa." Time ya ɗan kalla """Ahmad ba zan iya tafiya ban ga Hibbah ba a yau""" Ahmad yayi murmushi """Na sani shiyasa nake ta hanaka booking flight ɗin ai amma sai da ka yi""" """Idan zan ganta ko na mintuna ashirin ne zan tafi zuciyata tana cikin natsuwa da salama""" """Bari na ƙira Aunty Asiya mu ji ko za ka samu ganinta""" Aunty Asiyar ya ƙira bayan ta yi picking yake sanar mata MB zai bi flight na rana zuwa legos kuma Washegarin zai bar ƙasar zuwa Germany don P.A ya gama arranging musu komai yana so kan ya tafi ko na mintuna ashirin ne ya ga Hibbah. Tace tana zuwa ta katse ƙiran sun ɗan yi magana da mommy kan ta kira Ahmad """Zai iya ganin matarshi, amma yanzu tana bacci idan ta tashi zan ƙiraka don magani ta sha"" Idanu MB ya lumshe yana jin wani sanyin daaɗi na kwarara mishi a sadda Auntyn take furta zai iya ganin matarshi wannan kalma ya saukar mishi da abin da ba zai ce gashi ba na ni'ima." Murmushi ya ƙi barin fuskarshi ko na second har suka isa gidan Baba Hussaini da ya nemesu. "Sun samu ana meeting ne da manyan iyayen, ko da suka shiga nasiha sossai aka yiyyiwa MB, baba Hussaini ya ce" """Mun yi wa mahaifinka laifi Dukda da kaina na kirashi a waya ya amince duk abin da muka yi a kanka daidai ne zan ɗaga Muhammadu ya je da kanshi ya sake mishi bayani, Allah ya haɗe kanku ya baku zaman lafiya""" Duk suka amsa da Ameen cikin walwala da farin ciki. "Hibbah ta fi awa guda tana bacci kan ta farka amma da ta farka sai ta zaci ai komai ma da ya faru da ita ya faru ne a mafarki, bayi ta shiga ta wanke fuskarta ta fito ɗaurinta da yake da office" pin ne bai ɓaci ba sam. Gyalenta ta ɗauka ta yafa daidai Umma ta shigo ganin babu wani yanayi a tattare da ita she's just blank tace """Yauwa Hibbah ki fita ta karamin parlorn nan akwai tray da ruwa ki ɗauka ki kaiwa baƙo a" "ƙaramin parlorn Abbansu Asma'u""" Hankali kwance ta amsa kan ta miƙe Umma ta ƙara mata turare a bayan kunne da wrist ɗinta Dukda kamshin da take zubawa ta fice babu kowa a ƙaramin parlorn sashen don haka ta fita ta kitchen bata haɗu da kowa ba tray ɗin da aka shirya wasu natural drinks masu kyau da cup ta ɗauka ta fice. "Tana tura kofan ta sanya kai ciki da sallama kanta ƙasa har taje ta ajiye tray ɗin, sai ta ɗago idanunta da suka lumshe saboda bacci don gaida bakon kawai suka faɗa cikin nashi yana daga tsaye don tun da aka ce tana zuwa ya kasa komawa zaune, idanunshi ko sau daya basu bar kofa ba har ta shigo ita kuma sai da suka haɗa idanu ne ta shiga jin masifaffen kamshin nan" nashi da bata san me ya ɗauke mata hankali ba da tun farko bata ji ba sai lokacin. "Gabanta ne ya wani irin faɗuwa ta kasa ɗauke idanu a kanshi kaman yadda shima ya kasa dauke nashi daga kanta, shigar tashi da ya kasa cirewa saboda farin ciki sun matukar amsarshi har bata san ta shagaltu a kallonshi ba, shi ma kuma yadda tayi mishi kyau cikin shigar tata shi" ya hana shi iya motsa idanu daga kanta. "A hankali yake takowa yana nufota, takun nashi na tafiya ne da wani irin bugu na zuciyarta," "yayin da nashi zuciyar ke a ɗaɗɗaure, mayun idanunshi na manne da ita har ya zo dab da ita sossai." "Babu zato ya saka hannayenshi duka biyu ya riƙo nata, sanyin nata da damshin nashi suna" haɗuwa wuri guda. Cikin wata murya da ta maƙale a maƙogoro ya ce """Hey...wifey! Ba gaisuwa...?""" Zare hannayenta tayi tana ɗan kallonshi """Me kake yin nan?""" Ya wara idanunshi da wani irin fitina da bai taɓa sanin yana da shi ba ke building yace """Me kenan? Taɓa Matata?""" Kenan da gaske ne ba mafarki ba? Da gaske ne ta zama matarsa a yau ba almara ba? Ita dai Hibbah ita aka daurawa aure a yau sama ta ka? "A ɗan birkice ta juya idanunta na cika da kwallah ta nufi hanyar fita cikin sassarfa... Tana sanya hannunta jikin handle ta ji kirjinshi ya haɗu da bayanta ya saka nashi hannun ya murɗa key ɗin ya zare ya jefa aljihu, wani irin Juyowa tayi sai fuskarta ya shige kirjinshi don sossai yake kusa" da ita. Baya tayi yunkurin yi don mannuwa da kofa amma tuni ya riga ta sanya hannunshi na dama kan kwankwasonta ya fusgota ya mannata da jikinshi yana binne kanshi cikin wuyanta. "First halal hug, daga ita har shi ba za su iya fasalta yanayin da suka shiga ba, shiru kawai tayi amma sai ta ji wani abu na warwarewa a zuciyarta yana fidda sanyi da ya tunzuro kukanta kawai ta sakar masa lallausan kuka, ya kara sanya ɗayan hannun nashi ya rungumeta sossai" idanunshi a rufe yana jin kukan har cikin zuciyarshi. Jin ba zata daina ba ya sa ya raba ta da jikin nashi ya manna bayanta da kofan ya ɗan "rankwafo hannunshi ɗaya danne da kofar daga saman kanta kadan duk ya cika mata wajen da tarin kwarjini, kamshinshi har ya samu matsuguni a fatarta, wani irin kallo yake binta da shi." """Wifey..! Kukan nan fa?""" Yayi maganan cikin wata iriyar murya yana daga mata gira kaɗan. """I can't believe this...""" Maganan ya kufto daga zuciyarta. """You cannot believe what? Cewa kin zama Matar Almustapha?""" "Bata tanka ba, ya bi lips ɗinta da suka jiƙe da hawayenta dake gangara kan ya ɗan lumshe idanu cikin sanyi ya sanya hannu cikin aljihu ya fitar da sweet guda ɗaya ya ɗora kan tafin hannunshi." Duk su biyu kallon sweet ɗin suke kan ya ɗago birkitattun idanunsa ya kalleta. """Shi wannan shi ma shaida ne na tabbatuwar Almustapha Mijin Hibbahhh...""" "Bata iya ta motsa ba don ya hana aukuwar hakan, bata kuma kalleshi ba ya kai sweet ɗin" bakinshi ya bare ya saka kan harshenshi yana tsotsa a hankali cikin natsuwa idanunshi kuma basu bar kanta ba ko na second guda. Sai da ya tabbatar zaƙin ya narke ya haɗe da miyaunshi kan ya sa yatsu biyu ya ɗago haɓarta idanunsu suka sarƙe. Cikin mayen tarin soyayyarta yace """Hibbah ni karan kaina ina son tabbatar da cewa ba mafarki nake yi ba, ina son zuciyata ta gamsu da cewa da gaske ne ke ɗin na mallaka a yau...""" Yana maganan yana juya sweet ɗin a hankali cikin bakinshi idanunshi na kan lips ɗinta kan tayi wani motsi ko yunkuri ta ji sauƙar lips ɗinshi kan nata. "Za ta yunkura ya mayar da ita jikin kofan Softly yana shigar da harshenshi ya sarkafo nata, wani irin deep french Kiss da ya kwance mata duk wasu notikan kai ya shiga bata, zaƙin sweet ɗin na gaurayuwa da nata miyaun da nashi yana ƙarasa zauta shi... Da kyar ya iya barinta ta shaki numfashi wani irin tension na building a jininshi, duk wani kofofin jikinshi na aika mishi da wasu" irin saƙonnin da ya jima bai ji ba. "Mayun idanunshi ya saka yake kokarin neman nata amma sam ta ƙi bashi haɗin kan kallonshi, ya janyota ya sake rungumeta a kirjinshi cikin deep Calm voice ɗin shi da ya ɗan yi kauri yake furta" """I love you baby...ina masifar kaunarki Hibbah da duk zuciyata""" Ya sake rungumeta sossai tamkar za'a kwace mishi ita yace """I promise Hibbah I will always take good care of you, ba zan taɓa saka ki kuka da gayya ba, i promise I will always respect you no matter the situation and will always be there for you in every situation. Wallahi Allah I love you wholeheartedly""" "Sheshekar kukanta ke fita a hankali, a hankali ta sa tiny hannayenta ta mayar mishi da" "rungumar karon farko, nannauyar ajiyar zuciya ya sauƙe tamkar ba za su rabu ba haka ya sake" ta. """Zan tafi, ko akwai abin da kike buƙata?""" Ta kalleshi irin kallon nan na daga yanzu? Yayi murmushi yana sa hannu cikin aljihu tare da gyara tsayuwar shi. """You are my property kin manta ne? My treasure bana so kowa ya sake yi min hidima da abata""" Karon farko ta ɗan murmusa shyly """You're very beautiful Hibbah""" Kalaman suka fito cikin sanyi. """Idan na yi missing flight ke za ki ba ni wurin kwana""" Ya faɗa yana kallon time. "Bata tanka ba, ya sake matsawa dab ita yana zame hannunshi ɗaya da yake rike da nata ya" ɗago fuskarta. """Say something mana wifey...""" Da kyar ta iya fidda kalmar """Bana buƙatar komai""" Ya ɗan sauƙe numfashi """Zan saka miki kuɗi, take good care of yourself for me, bana so ki fita ko ina ba da sanina ba, bana so kowani jik and jak su kallemin ke a banza sannan banda kula kowa kin ji?""" Dariya ya bata har bata san ta yi murmushi ba shima ya murmusa. """ko ke fa, I will be going""" "Ta taka ta ɗauki drinks ɗin daya a hannunta ta miƙa mishi ya haɗa da hannunta ya riƙe, sanyin" "natural drink ɗin na ratsa su su biyun, bayan ya zame drinks ɗin ya kai bayan hannun bakinshi yayi pecking." "Ya taka ya sake sanyata cikin jikinshi a kunnenta ya raɗa mata ""I love you""" "Kan ya Wuceta ya fice don idan ya cigaba da tsayuwa bai san kuma me zai iya yi ba, ji yake" kamar ya haɗiye ta kawai ko zai huta da masifar begenta dake dukar zuciyarshi… 69 "Kaman yadda Baba Hussaini ya faɗa da Uncle Muhammadu suka koma legos, driver ɗin MB ne ya zo ya ɗauke su, fuskarshi har lokaci cike da tarin fara'a Dukda ba dariya yake ba amma a sake kuma lokaci lokaci idan ya tuna ta, kunyarta, motsinta, idanunta da yadda take fighting" feelings against him sai ya ji murmushi na subuce mishi ba tare da ya shirya ba. "Sun isa gidansu inda MB ɗin yayi mishi iso har parlorn baƙi, ciki ya shiga ya aika a kai mishi" "ruwa da abin taɓawa kan ya nufi wurin Mum don ganin Jasrah, da sallama ya tura kofar na" ɗakin Mum. "Yana sa kai ya ji Mum ɗin na cewa ""Zo nan""" Motsin Shigowar shi ya sa jasran da ke tsaye ta nufeshi da gudu ta faɗa jikinshi jikinta tamkar "yakuwa don sakewa, Dukda sanyin Ac dake kaɗawa a ɗakin zufa take zubarwa." "Ya rungumeta Tsam kan ya ɗago ta gabaɗaya yana kare mata kallo ""Jasrah... Are you sick? Why do you Look so pale?""" Jasrah ta kalli Mum a sace kan ta koma jikinshi tayi luff Mum kaman ba za ta tanka ba sai kuma tace """zazzabi take yi, ko zaka ce bamu iya kula da ita ba ne?""" """A'a Mum wai ban san tana zazzabin bane, Allah ya bata lafiya.""" Bata amsa ba ya shiga ya zaunar da Jasrah daga kan cushion ya nufi Mum ɗin ya zauna daga bakin gadon tare da riƙe hannayenta. """Mum har sai yaushe za ki daina wannan fushin da ni? Mum idan na tuna cewa kin sauya min sossai ba kaman da ba sai in ji babu daaɗi, tun tashi na baki taɓa irin wannan doguwar fushin" "da ni ba, ashe laifin Mahir ya kai ya shafe ni har ya chanza matsayina a zuciyarki?""" Ta kalleshi a yanzu bata iya danne tsanar shi ta danne ɗin a baya amma a yanzu da ɗan ta ke rufe shi yana nan yana yawo freely idan ta ganshi sai taji kaman ta shake shi ta kashe idan ya so itama a kasheta. """Babu abin da zaka ce min ya wanke laifinka a raina Mustapha, ban taɓa tunanin zaka sanya hannu wurin tura dan uwanka gidan kaso ba, na zaci soyayyar da na nuna maka zata sa ka ji cewa zaka iya yin komai a kan jinina amma kai ka fara nuna ban haifeka ba bani da wani option illa na bi da kai ta yadda ka biyo. Ga 'yarka ni dai ba zan iya yi mata mugunta ba idan zaka tafi da ita fine idan zaka bar ta ne ma duk daya""" Tana kai nan ta miƙe zata shiga toilet yace """Mum...""" "Ta ɗan waigo tana jefanshi da kallon tsana a fakaice. ""Abba yana son ganinmu gabaɗaya parlorn baƙi""" Yana kai nan ya miƙe ya kama jasra da ta riƙe shi gam suka nufi ɗakin na baƙi. "Sai da ta ga dama kan ta zo, gabanta sai da ya faɗi ganin Yayan Rabi'ah mahaifiyar Mustapha" amma ta danne. """Ina yini?""" """Mun same ku lafiya""" Ta amsa da lafiya ƙalau. Abba ne yace """Sai da dai ka taso ka zo da kanka Yaya, ai sanar da ni da kuka yi a waya ma ya wadatar ku ma kun isa da shi ne""" Uncle Muhammadu yace """Dukda haka dai Alhj Bashir ai gwara a fitar da hakki, auren ne ya zo Ba tare da kyakyawar shiri ba""" """Aure??""" Mum ta tamabaya cikin mamaki Abba yace """Eh Sun ɗaura wa Mustapha aure a ɗazu da safe ban dawo bane ya sa ba mu yi maganan ba"" ""Aure fa ka ce aka ɗaura masa?""" "Ta sake faɗa zuciyarta na zuwa wuya, reaction ɗinta ya sa duk suka zuba mata ido har Abba." """Ba wai auren na dole ba ne, don ai Almustapha ya fi ƙarfin a yi mishi auren dole da shekarun nan nashi, shi ya gabatar da ita yana so kuma iyayenta suka nemi a ɗaura tariyar ya kasance daga baya, na tako ne in kara yi muku duka bayani in kuma ba ku haƙuri kar ku ji abin daga sama ku ji babu daaɗi""" Yaya Muhammadu ya ƙarasa idanunshi akan Mum. "Ta sauƙar da kanta tana ɓoye abin da ke cinta a zuciya, sai kuma kawai ta miƙe ta bar wurin ba" tare da ta ƙarasa jin zancen ba. "Da kallo MB ya bi ta duk ta chanza mishi ya rasa hanyar da zai bi ta dawo kaman da, Dukda baya ganin laifinta don dole ta ji ba daaɗi akan abin da ya samu Mahir tunda shi ne ya tsaga" jikinta ya fito ba shi ba. "Bayan sun gama magana Uncle Muhammadu ya sanar da shi tariyar sai nan da 2months idan akwai wani event ko wani abu duk da zata yi ma zata shirya shi kan lokacin, Abba ya nuna" mishi babu komai. "Bayan barin Abba parlorn, MB ya nunawa Jasrah uncle ɗin nashi yace ""princess je ku gaisa da granny ɗin ki""" Ta taka a hankali ta isa gabanshi ta mishi gaisuwar kurame. "Yana kallonta da tausaya wa yake amsawa har wasa ya ɗan yi mata tayi dariya abinka da yaro, ta dawo wurin Babanta." """Jasrah zan ɗan yi tafiya ne gobe da safe babu hali in tafi da ke, amma i promise you daga" "zarar na dawo zan ɗauke ki gabaɗaya ki dawo ganina kullum kullum kin ji?""" "Idanunta suka cika fal da kwalla tana kallonshi, kallo ne da da zai fahimta na damuwa, gajiya da kuma takura ne, haka zuciyarta a karye yake da ya kasa gano matsalar ta, hawayen da ta fara ne Uncle yake cewa" """Haka kuke ne kullum sai ta yi rigima idan zaka yi tafiya?""" """Ai Jasrah rigima ce da ita, bata so ko office ne in tafi in barta nan"" ""Matarka na da aiki""" Ya ɗan yi murmushi mai sanyi ya ce """Ai Uncle ita kam bana tunanin zata yi mata kuka idan na bar su don already akwai shakuwa tsakaninsu""" Ya gyaɗa kai yana ta kallon yadda MB ɗin ke rarrashin yarinyar daga karshe ma tsawa ya daka mata har uncle Muhammadu ke mishi magana don ta ƙi sakinshi. "Nannynta ya kira ta ɗauketa tana ta kuka suka tafi, ya sa a ranshi zata yi shiru ne haka Mum zata je ta rarrasheta babu yadda ya iya ne da zai tafin da ita shima yana buƙatarta a kusa da shi." Da uncle Muhammad suka tafi gidanshi a chan zai kwana Washegari MB yayi mishi booking flight. "Abinci masu kyau yayi order, haka wuri na musamman ya sauƙe kawun nashi." Bayan sun yi wanka sun ɗan huta ya fito ya dawo wurin kawun nashi kar ya barshi shi kaɗai. """Wani lokacin kaddara da rabo shi ke kawar da wani abin don ya kawo wani abin to existing""" Uncle Muhammadu ya faɗa muryarshi da ɗan wani yanayi. """Hakane, shiyasa komai ke tafiya bisa ƙaddara don ni ban taɓa yarda akwai coincidence ba""" Murmushi Uncle Muhammadu yayi """Ka ga Hafsatu babu wanda ya zaci zuwanta wannan matsayi da take kai a yanzu""" Gyara zama MB yayi """Uncle dama chan kun san Mum ne kan zamanta Matar Abbana?""" Kallonshi Uncle Muhammadu yayi sai yayi murmushi """Sossai ma kuwa, itama ai cibiyarta Nassarawa ne amma iyayenta asalin 'yan Nijer state ne daga kwantagora, mahaifiyarta wanke wanke da 'yan aikace aikace take mana a gida yayinda Mahaifinta drivern Baba ne tun da jimawa kenan, ba ita ce babba ba tana da yayye biyu maza yanzu haka ma suna Nassarawa da iyalan su, saboda itace mace karama ya sa ko yaushe idan Mahaifiyarsu za ta zo aiki da safe gida sai ta zo da ita, idan mahaifiyarka ta fita wasa sai su haɗu su yi ta yi da haka suka tashi tare, tamkar ƙawaye don tun da Rabi'ah tayi wayo komenene zaka saya mata idan baka saya da Hafsatu ba sai ta gwale ka ta ƙi karɓa, ya zamana hatta kayan sallah da sauransu duk in an tashi yi wa Rabi'ah da ita da Hafsatu Baba ke" yi musu. "Da Rabi'a ta kai shiga makaranta haka ta dage sai da aka sanyasu tare da Hafsatu komai tare suke har suka gama secondary, a lokacin Baba da mahaifinta da suka yi tafiya cikin Abuja da mota suka yi hatsari a hanya duk su biyun Allah ya karɓi abin shi dama mahaifiyarmu da tsohon ciki hatsarin ya girgizata nakuda ya tashi ta haifi Ahmad ba shiri itama bata yi surviving ba tsakaninta da Baba sati biyu ne kachal tayi ta zuban jini, jininta da ya hau ya ƙi sauƙa ko" farkawa bata yi ba tunda ta haihu har ta cika. "Rabi'ah ta fi kowa shiga tashin hankali don ita kaɗai ce mace ma cikinmu, Allah kuma ya ɗora mata ƙauna da soyayyar Ahmad, ita ta rungumeshi duk idan aka mishi wanka to tana rungume dashi madara komai, da ta zo ta iya kula da shi ma sai sallamar me reno aka yi, ta zama uwa tun a kanshi don haka bata mayar da hankali kan neman admission ba, Mahaifiyarsu Hafsatu ta cigaba da mana aikace-aikace bayan ta fita takaba, rayuwa ya cigaba da tafiya a haka har Ahmad ya cika shekaru biyu a lokacin Mahaifinka ya bayyana, shi ɗin asalin dan Katsina ne amma maraya ne kuma shi kaɗai iyayensa suka haifa neman kudi ne ya kaishi legos yayi" struggling sossai har yayi karatu ya ginawa kanshi rayuwa mai kyau. "Ya haɗu da mahaifiyarka anan Nassarawa da ya zo aikin wani company, mahaifiyarka ta ƙi sam" "da farko amma ya nace kuma kaunar da yake yi wa Ahmad shi ya sa ta fara kula shi har yayi alkawari idan ya aureta zata tare da Ahmad gidanshi, mun amince don mun riga mun saka ma" "ranmu ma itace uwar Ahmad saboda ko matayenmu basu da ikon da take dashi kan Ahmad, an yi bikin su da mahaifinka aka kawota nan Lagos, zamansu ya ɗau daaɗi don Ahmad na shekara uku aka sanya shi makaranta mai tsada, yana rayuwanshi me kyau duk hankalinmu kwance" kwatsam sai ga Hafsatu da Admission a University of Lagos. "Mun yi mata murna, inda ta tarkata ta nufi Lagos duk ma zatonmu hostel zata zauna bayan tafiyan ta da kusan watanni biyu muka gano ashe gidan Rabi'ah take zaune, dukkanmu babu wanda ya ji daaɗin hakan bayan Ahmad da ba nashi ba a kara Hafsatu kai kuma har hidimar" transportation ɗinta shi yake yi. "Rabi'ah ne ta nuna ba komai ai kaman 'yar uwarta take ba bare ba, kuma me amfanin ta idan Hafsatu zata zo Lagos ta zauna a hostel, har ga Allah kowa baya so amma muka kyale batun, Hafsatu na aji biyu mahaifiyarta ta rasu ta zo Nassarawa da Rabi'ah da kuma Ahmad a lokacin Rabi'ah na da cikinka Watanni huɗu, yadda suke goga kafaɗa zaka ce dukkansu auren suke a chan, duk Hafsatu ta chanza har matata sai da tayi magana amma Rabi'ah ta nuna bata so," bayan sun koma Lagos rayuwa ya cigaba da tafiya. "Har lokacin da Rabi'ah ta haifeka inda dayawa daga Nassarawa an je suna ka ci sunan mahaifin mahaifinka Almustapha, Rabi'ah na kula da ku a tare Da Ahmad da ya shiga Nursery 2 a lokacin, kana da shekaru biyu sai ga mahaifinka da batun auren Hafsatu a lokacin ta gama" jami'a. "Rabi'ah ta jijjiga, ta kirani tana kuka take faɗa min wai Bashir zai auri Hafsatu, kowa sai da hankalinshi ya tashi amma muka dinga tausanta, muka dinga bata haƙuri dayake tana da sanyin hali da haƙuri haka ta haƙura ta zuba ido har aka yi auren Hafsatu da Bashir auren da ya rusa alaƙa dayawa don daga nan muka yanke duk wani alaƙa da ita da zuri'arta da suke nan Nassarawa, zaman su bai yi daaɗi ba sam Dukda Rabi'ah bata faɗan abubuwa dayawa amma ta lalace ta rame wani lokacin Ahmad ne zai kira ya faɗa mana gata bata da lafiya don haka kawai sai ta yanke jiki ta faɗi, tayi jinya a tsai tsaye ba tare da kowa ya sani ba sai labarin" rasuwarta muka ji. "Mun girgiza ƙwarai Mustapha don rasa Rabi'ah ya tayar mana da miki mai girman gaske amma babu yadda muka iya haka muka yi tawakkali amma Ahmad ya ƙi zama a gidan Dukda mahaifinka ya so cigaba da riƙe shi, duk yadda aka yi da shi ya ƙi yayinda Mahaifinka kuma ya ƙi aminta ya bar mana kai kaman yadda muka buƙata, babu yadda muka iya saboda ya fi mu" "iko da kai ya damakawa Hafsatu da bayan rasuwar Rabi'ah da watanni uku ta haifi Mahir""" "Idanun MB ne suka sauya sossai, bai taɓa sanin labarin mahaifiyarshi ba sai yau, kanshi ya ɗaure matuka don yana iya tuna Mum kan ce mishi 'yan uwan mahaifiyarshi basa kaunarshi shiyasa bata so ya dinga zuwa kar su dinga bata mishi rai, idan ya je kuma baya iya sakewa" musamman da dayawa suna aibatata shi kuma bai taɓa ganin aibunta ba. """Shiyasa dukkanku bakwa sonta Uncle?""" Uncle Muhammadu yayi murmushi kawai. """Ina ga kun yi kuskuren fahimtarta ne Uncle, ai da ta ƙi Maamieyna da bata riƙe ni da zuciya ɗaya ba kila rabon Mahir ne ɗin ne ya sa dole auren ya tabbatu""" Kai Uncle Muhammadu ya gyaɗa """Hakane kam, mu maza duk mun mata uzuri mun kuma manta cin amanar da tayi amma matan sun kasa mantawa shiyasa a koyaushe ka je basa iya faɗan alkhairi a kanta kai kuma mai uwa kayi fushi da kowa ka daina zuwa kwata kwata har girmanka""" "Shiru kawai MB yayi, ya fahimci akwai magana a bakin Uncle Muhammadu amma ya zaɓi yayi shiru kawai, wani hiran suka kama lokaci lokaci kuma wani abin na dawowa MB a kai yana dan jin wani abin ba daidai ba amma ya kasa pin-pointing, bayan sun dawo isha suka ci abinci tare" kan ya koma ɓangaren shi ya bar uncle Muhammadu ya huta. Ko da ya gama shirya abinda zai shirya ya hau gado ya kwanta sai ya janyo wayanshi ya shiga laluben number ɗinta.. "Sunan da yayi saving na Miss Mudassir ya fara shiga ya goge yana ɗan murmushi ya rubuta ""My priceless jewel """ Bayan yayi saving ya danna ƙiran tare da lumshe idanu yana sauraron karan shigar wayan… 70 "*Don Allah ku dinga min uzuri idan kun ga ban yi typing ba, haka kawai ba zan nade hannu in ki yin update ba, nima so nake na ga na kamallah wahalar da nake sha a kan chargy ya isheni haka, wutanmu ya ƙi zama masu chargy kuma wulakancinsu is on another level idan na tashi typing ne sai wayana yayi running down tass kan in sake samun chargy in yi wani typing din is" another struggle pls bear with me * ***** """Boss""" "Abin da ta ga yana yawo kenan kan screen ɗinta da hasken wayan ya sa ta mayar da idanunta kai, ita da Huda da kuma Yaya Zaitoon ne a ɗakin duk tana jin su bayan sun kai amarya sun dawo gama hirarrakinsu da mazajensu har suka yi bacci da jimawa sai dai babu wanda ta tanka, ba kuma ta motsa ba, ba bacci take ba kuma ba danna waya ba." Garin yayi shiruuu banda karar Ac babu abin da ke tashi a ɗakin alamun rayuka dayawa sun kwanta don samun hutun jiki da ruhi. "Kaman ba zata ɗaga ba saboda wani irin faɗuwar gaba da ya risketa na ganin kiran a bazata," "ya kusa katsewa ta kai hannu tayi picking tare da danne wayan akan pillow tayi shiru, shima shiru yayi for some minutes kan a hankali ta ji ya ce" """Amincin Allah su tabbata a gareki""" Ta ɗan lumshe idanu sai ta buɗe saboda scene na ɗazu ne ke dawo mata yana tada mata dukkanin tsigar jiki. """A tare da kai""" """Fatan Matata tana cikin aminci?""" Ya faɗa slowly cikin wannan Muryar tashi dake ƙarasa hautsina natsuwarta da take tattaro wa. Cikin raɗa ta amsa mishi da """You sound tired""" """I am"" yayi admitting ""Long day but ai Its worth it, don wannan rana yana daga cikin ranaku mafi" "daraja a rayuwata""" Idanunta a lumshe tana sauraron shi yana kai aya ta ce """Then sleep""" """I tried""" He pause """Amma ya ƙi zuwa""" """Meyasa?""" Ta faɗa cikin kokarin composing kanta. Ƙasa da murya ya sake yi in a way that made her chest tighten. """Because i kept thinking about you.""" "Ta rufe idanunta tana sauƙe numfashi a hankali, shiru ya ratsa tsakani har sai da yace" """Are you there?""" """Uhmm""" "Ta amsa kan ta ɗora da ""Ya ka samu Jasrah?""" """She's fine though ta ɗan yi fever but da sauƙi""" Gabanta ne ya ɗan faɗi ko dai Mum ta mata wani abu ne? A hankali ta ce """Is she with you?""" """No, zan tafi Germany gobe so babu amfanin ɗaukota just for today.""" Miƙewa tayi zaune a take hankalinta ya ƙara tashi. """Sir...""" """No please not after ina amsa sunan Mijinki""" "Tayi shiru tana wasa da fingers ɗinta, ita kam bata san me zata kirashi ba kuma, sakin batun" tayi ta ce. """Please can you send her over to me?""" "Bata san ta ya zata fuskance shi akan batun Mum ba don ta tabbatar sama ta ka ba zai yarda matar da ta raine shi tun ƙarami zuwa girma za ta iya zaluntar ɗiyarshi ba, ya riga ya bata matsayin uwa." "Ya ɗan yi shiru ta ɓangaren shi nazari yake sai dai ba zai yiwu bane, bai san ya Mum ta amshi ma batun auren ba don ma bata san wacece ba, kuma a ce har ya ɗauki yarinya ya tura mata it" sounds somehow zai ƙara lalata komai ne tsakaninsu da Mum. """Soon za ta dawo wurinki gabaɗaya because i have No plans of leaving her with Mum, a yanzu yayi wuri Mine kin ji?""" "Har ranta bata so ba, don damuwa sossai ya taso mata akan Jasrahn.." """Would you mind idan na tambayi Meyasa baka sakata school ba?""" Da tana school komin yaya zata samu sauki ta wani ɓangaren amma 24/7 tana tare da Mum har yaushe? Shiru ne ya ratsa tsakani har kaman ba zai ce komai ba kuma sai a hankali ya furta """It traumatize her... Sun yi hatsari da mahaifiyarta a hanyar kaita school, her Mum couldnt survive she survived but lost her hearing, bayan tsawon lokaci ta warke but school sai ya zama yana triggering mental Health ɗinta, she always feel unsafe in ta tafi tayi ta kuka kenan tana cewa children will be laughing at her and mocking her, wani lokacin da ba dariyar ma ake yi mata ba gani take ana yin tunda at First ko ji bata nuna ta yi kaman yanzu... For year muna batun lafiyarta tun da kuma ta zama stable am afraid na mayar da ita school kar ta sake" "maimaita wahalar da ta sha tsakankanin mutuwar mahaifiyarta.""" "Tausayinsu duk su biyu ne yake sauƙa mata a zuciya, ashe idan kana kallon ƙaddarar wani sai ka ce kila gwara kai, eh gwara ita mana da girmanta komai yake faruwa da ita yanzu wannan 'yar mitsitsiyar yarinyar har ta san me ake cewa jarrabawa, ko ba komai kuma ita tana tare da iyayenta especially Daddy he's a very good supporter to her amma ita Jasrah ta haɗu da sharrin Mum ta yadda Mahaifinta ma ya kasa gane whats going on in her life." Idan ya sani daga baya she's very sure he will be shattered. """Allah sarki! Allah ya ji kan ta I'm very sorry for your loss nd struggles""" """Thank you""" "Ya faɗa da alama wani yanayi daban ne ya taso masa shiyasa baya son zancen, damuwa yake shiga mai yawa idan yana tuna kowani yaro na chan yana building future ɗinshi ɗiyarshi na nan zaune ba don ba kudi ba sai don fear na jefa ta cikin wata matsalar kuma." """Zai wuce wannan ma, i promise to take very good care of her za ta warke watarana har ma tayi magana da bakinta""" Tayi maganan cikin son calming ɗinshi down kuma ta yi nasara don numfashi ya sauƙe har tana ji yace """In shaa Allah Wifey, i trust you with all my heart and soul"" Tayi murmushi shima ya murmusa." """Bacci...""" Ta faɗa a hankali bayan dogon shirun da ya ratsa. Chan ƙasa yace """Sleep well and sweet dreams... I love you!""" Bai jira amsar ta ba ya katse ƙiran don ya san ba zata amsan ba. "Shiru tayi kawai ko wayan bata cire ba, bata san Meyasa kalmar I love you bata mishi wuya ba, a duk sadda ya faɗa hakan zuwa gareta kuma ta kan ji kalmar ya shige mata cikin zuciya ya samu kyakyawar matsuguni ya zauna, a yanzu sai da ta ji duka jikinta ya amsa zame wayan tayi ta ajiye ta gyara kwanciya idanunta lumshe, ta jima kan bacci ya sureta cike da tunaninka" daban daban. ***** "Ta ɓangaren Mum bayan tafiyan Uncle Muhammadu Abba ɗakinta ya nufa ya sameta tana zaune kawai wuri guda, ganinshi ya sa ta fara hawaye hankalinshi ba'a kwance yake ba musamman abubuwan da Mahir ya aikata yayi breaking nashi ba kadan kadan ba bai taɓa zaton dan da ya haifa cikinshi will be as terrible as Mahir ba amma ya danne ƙwarai saboda ta samu kwanciyar hankali kar taje wani ciwon ya kamata idan damuwarta ya haɗu da pressure" dinshi. """Haba Hafsatu! A yanzu kuka da damuwa ba naki ba ne, me abin kuka don Mustapha yayi aure?""" """Ba zaka sani ba saboda kai ba ni ba ce Abban Mahir, dangin Rabi'ah za su iya yin komai don su kuntatawa rayuwata su hanani sukuni, suna so su nuna ni din ban taka matsayin uwa ba a rayuwarshi shiyasa suka zaɓa masa mata suka aura masa amma ai ba su zasu zauna da ita ba ni zan zauna da ita, idan sun hore mata kunne ta raina ni ko ta min wani abin fa? Sun kasa accepting cewa aurena da kai tsarin Allah ne ba son zuciya ba, sun kasa gaskata irin rainon" "gatar da na yiwa Mustapha na manta ɗa na har ya jefa kanshi wani hali ba tare da sanina ba""" Ya tako ya zo ya ɗan yi hugging nata yana buga bayanta. """Har Abada babu matar Mustapha da ta isa ta shigo ta rainaki, ke uwa ce a gareshi babu mai chanza hakan har shi karan kanshi, ki kwantar da hankalinki sannan ki yi tunani mai kyau akan nufinsu kila ba hakan ba ne, na san waye Baba Hussaini kema kuma kin sanshi ba zai dauki" "mace ya haɗa ta da Mustapha saboda wani mugun nufi ba""" "Tana kan kirjinshi ta jefawa jikin nashi wani mugun Harara a ranta tana jan tsaki, a fili kuwa tayi damarar yadda Anam bata sha da daaɗi ba haka wannan ma ba zata sha da daaɗi ba wlh, bata yi wahalar Almustapha don wasu banza su more shi ba idan ita ba zata more shi ba to gwara kowa ma ya rasa. Bayan Abba ya fita ta cigaba da planning na yadda zata wargaza wa" Mustapha rayuwa yadda ta ci buri tun kan ya wargaza na danta a bazata. "Kukan jasra ya sa ta miƙe ta fita, yarinyar na ganinta ta sha jinin jikinta ta shiga haɗiye kukan da kyar jikinta na ɗaukar rawa." Bata tsira ba don gabanta taje ta sauƙe mata wani kyakyawar rankwashi cikin masifa da tsana take cewa """Cigaba mana munafukar yarinyar, ya tabbata idan na gaji da wannan sabon salon iskancin naki in saka wuka in yanke wuyanki sai in ga uban da zaki yi wa nanuken...""" "Kuka take rike wa tana jan numfashi da kyar da kyar, Mum ɗin ta zare mata idanu ""Bani wuri algunguma..!!""" Da gudu ta wuce Mum ta samu wuri ta zauna tana tsaki. **** "Washegari a Nassarawa sun tashi da shirye shiryen watse wa don iyayensu mazan duk tun a jiyan suka juya, Mommy ta so ta tafi da Hibbah amma Umma ta yi ta roƙonta ta bar mata ita, ba yadda ta iya ta kyaleta Momma dai sai ido ne nata tsakaninsu, duk a tare aka kaisu airport sai dai lokutan tashin nasu daban daban ne, Zaitoon kaman ta bi su Hudah don haɗuwar sun nan yayi daaɗi kwarai har bata so su rabu aka ce ɗan uwa mai daaɗi amma ba yadda aka iya haka" suka rigasu wucewa. "Su ma lokacin tashin su na yi suka wuce Kanon dabo, ita dai Amarya Hibbah har lokacin ba wai ta sake bane kuma ba maganan kirki take ba sai ya kama, tana nanuke da Umma har lokacin ta kasa yarda da cewa ita ce yau, ita Hibbah da ta ba talatin baya ita ce yau matar aure, bayan duk wani gori, bayan duk wani struggles, bayan duk wasu maganganu sai gashi da Allah ya ce" lokacin yayi babu wanda ya iya dakatar wa sai da mai afkuwa ta afku. "Haƙiƙa ba zata ce bata son Mustapha ba don idan ta faɗi hakan ma ta yi karya, tana kaunarshi kuma tana farin ciki da aurensu ta wani ɓangaren, ta wani ɓangaren kuma tana tunanin sabon struggles da za ta faɗa don Mum ba zata taɓa sonta ba, ita ma kuma ba zata taɓa son matar ba, ta san kafin ta tona mata asiri ba karamin gwagwarmaya bane don MB ya gama bata yarda, haka kuma tunaninta ya tafi ta yadda zata koma cigaba da aiki a office daya da Almustapha" matsayin mijinta. "Har suka sauƙa Kano babu irin tunanin da bata yi ba, Mu'azzam ne ya zo ya ɗauki matarshi haka ma Aina'u duk basu bi su gida ba, daga Momma, Umma sai Hibbah da Mumtaz da kuma" su Fadeel ne suka yi gida. "Suna isa kuma suka tsinci gurmin da ya tashi a gidan nasu na aurenta, ta san dama za'a rina wai an sace zanin mahaukaciya wasu murna suke mata ana ta mata adu'o'i yayin da wasu kuma ke baƙin ciki duk basa gabanta don har sashen umma suka zo wai an zo mata barka da" taya murna da kansu suka gaji suka kyaleta. Almustapha ko da ya zauna a jirgi zai tashi ya gwada neman layinta bai sameta ba sai ya mata dropping message daga nan suka wuce bayan ya tabbatar Uncle Muhammadu ma ya wuce safely. "Ko da ta riski saƙon shi murmushi mai sanyi kawai ta tsinci kanta da yi, bata yi reply ba ta ajiye" wayan ta cigaba da harkokin gabanta. "Umma kaman jira take a dawo nan fa ta fara shiga da fita don gyara ɗiyarta yayinda Su Nihla suke maganan event da za su yi idan lokacin bikin yayi Dukda Amarya kam ta ce ita bata son komai ko da Daddy ya tambaya, sun yi sun yi ta ƙi bayan mothers eve da zasu yi a gidan babu abin da ta amince zata yi, shi dai Najeeb akwai dinner wanda abokan shi ne suka haɗa amma dinner ɗin ma a tsarin ranar da hibban suka tafi ne za'a yi." "Komai na bikin shi da Mommanshi suke yi umma ba ruwanta haka na Hibbah Momma kaman bata san suna yi ba hakan kuma ya kara musu wani kima da soyayya a wurin Daddy, wani irin" kuɗi yake fitarwa na auren nan nasu har matanshi suna kasa ɓoye hassada da bakin cikinsu. "Babu wanda ya takura Hibbah ko ya mata dole don yin events ɗin da tace bata so, su Hudah ne suka zaga suka fara shiryen shiryen cocktail party bata ma sani ba wanda har shi zai yi attending kuma kayan da zata sa Zaitoon ne ta ɗauki nauyi don ta san taste ɗin hibban da" measurement ɗinta.... 71 "Days turns to week and weeks turns to months wasa wasa magana ake na saura sati ɗaya tariyar ta, a tsakankanin abubuwa dayawa sun faru, ciki har Lagos an je an yi ma gidanta jere wanda cikin masu zuwa har da Hajiya kamila, ko da suka dawo Bakinta gama mutuwa yayi a yanzu kam ta riga ta sallamar Hibbah ta yiwa duka diyoyin su fintinkau, ita da suke zagi ta kasa auruwa, ita da suke jifa da maganganu, idan ta tuna auren Amal na farko yadda suka dinga cin mutuncin yaran Momma gashi yanzu daga Huda, Aina'u har Hibbah sun tsere musu duka da dacen gidan arziki sai ta kama kuka, wani abin idan ba Allah ba to waye? Duk hassada ko" kyashinka sai dai ka zubawa sarautar Allah ido. "Tsakaninta da MB da a satin ne ma yake shirin dawowa daga Berlin text messages ne don zata iya kirga sau nawa suka yi waya shima ba tana mayar da hankali bane, shi kuma ta ɓangaren shi yayi wani irin busy ne saboda ayyuka da suka chukurkude masa a chan tun dawowanshi Nigeria, a haka ma bai zauna a City ɗaya ba yau yana chan meetings gobe yana chan" launchings da sauransu. "Dukda haka tun wata ɗaya da ya wuce suka yi magana da Ahmad don shi ne ma ya kirashi bayan sun gama gaisawa yake sanar da shi abin da yake so na lefe menene shawararshi, ya tabbatar mishi akwai Matar Yaya Musa tana kawo kayayyaki masu kyau daga kasashe zasu iya" bata kwangilar haɗa lefen. """Ahmad Matata fa ba laga-laga ba ce she's very classy and tana da high taste a dressing ka tabbatar zata iya?""" Dariya sossai Ahmad yayi """Sannu me classy mata, idan dai zaka fidda kuɗi komai ba matsala bane""" Tsaki MB ya ja a lokacin """Kaima ka san wannan ba damuwa ba ne, I will send everything sai ku yi magana please emphasize on high taste materials""" "Bayan sun gama waya kudi sossai Almustapha yayi mishi wiring har saida Ahmad ɗin ya sake kira don tabbatarwa yana tambayar basu yi yawa ba, MB ya ce everything for his wifey." Tun daga sannan ma bai sake bi ta kansu ba ya cigaba da harkokin gabanshi. "Yau ya dawo daga office a matuƙar gajiye, bayan ya yi wanka ya zauna kan soft cushion na ɗakin nashi ɗaure da towel a kwankwaso, coffee ya haɗa yake sipping idanunshi na kan hasken system ɗinshi, tsaki ya ja yana komawa kishingide, wani irin kewanta yake ji da son ganinta, he misses her like hell don sun kai sati basu yi magana ba, sometimes ko yana so ya ƙirata sai yaji bai son takura ta yana son bin komai bit by bit ne har da kanta ta sallama mishi ragamar" rayuwarta. "Wayanshi ya ɗauka ya duba WhatsApp ganinta online ya sanya ya shiga kiranta Video call, tana kwance bayan doguwar gyaran jikin da zata iya cewa ta ma gaji da shi, wanka tayi ta saka doguwar riga simple bata sa hula ba don ta wanke gashinta kuma bata yi drying ba, nata ya ƙone sai ta bar kan ya sha iska ta hau gadon ta kwanta, rashin abin yi ya sa ta janyo wayanta ta" shiga WhatsApp magana ma suke da Zaitoon kawai ta tsinci video call ɗinshi na shigowa. "Zuciyarta ne ya shiga bugawa da ƙarfi har hannunta na rawa, ta rasa Meyasa wannan bugun zuciyar daga gareshi ya gagara barinta, wai adrenaline da hormones ne ke saka jiki rikice wa a sadda abin da kake so yayi approaching naka, Hudah ta fi kowa matsa mata da batun signs ɗinta a kanshi idan suna wani hirar ta kawo batun kasa sakewa da take idan yana wuri wai ita" "ga ta dangin biology ba, lumshe idanu tayi don calming kanta." "Ko da Hudah bata tabbatar mata tana son MB ba ita ta sani don duk wasu signs na soyayya ta jima cikinshi, strong emotions, attractions, overthinking, nervousness around him duk jikinta da kwakwalwanta sun jima suna karbar waennan sakonnin to a yanzu ma dai nervously ta ɗauki wayan a sadda ya kusa tsinkewa sai dai bata yi turning camerar ba ta kife wayan tare da saka" earpods don jin me zai ce. """Hey..!""" """Good Afternoon""" Ta amsa da gaisuwa. """Mu nan Evening ne Its already past 8 Sugarplum, kina lafiya?""" Ta sauƙe numfashi kaɗan. """Lafiyata ƙalau and you?""" """Bana lafiya""" Ya faɗa cikin wata murya da ya sa tsikar jikinta tashi a lokaci ɗaya. """Me ya same ka?""" Ta tambaya a hankali. """Turn on your camera Hibbah""" "Ta ce cikin Shagwaɓar da bata ma san ta yi ba ""No please my hair is messy""" "Ya sanya hannu a soft gashin kanshi and he messed up his soft, Black hair and said" """Turn and look mine is messy also!""" "A hankali ta juyo da wayan tayi turning camerar, da kyar ta kai idanunta kan shi ai da sauri ta kawar ganin daga shi sai towel, faffadar kirjinshi duka waje, yayi wani irin fresh skin ɗinshi sai yalki yake, haka kuma da gaske ya wargaza gashin kan nashi, kallo ɗaya ta mishi ta sauƙar da" idanunta. "Shima a ɓangaren shi ya shagala wurin kallonta, A hankali ya lumshe mayun idanunsa wanda zallar fitina yasa suka canza kala ya sake buɗewa yana bin ruwan da ke ɗan bin gefen wuyanta haɗe da gashi da suka mammane a wurin, wani irin kallo yake mata kasa kasa yana cije lips." Jin shiru ya sa ta sake ɗaga idanu ta kalleshi sai ta narke fuska da tsantsar shagwaba wanda ya kara mugun kasalantar da shi. """Ina sonki cikin kowani irin yanayi""" Maganan ya shige ta sossai musamman yadda ya zaro ta kaman an fusgo daga bakinshi... "Katse wayan kawai tayi tana runtse idanu, daga ɓangaren shi murmushi kaɗan yayi bai damu ba don ta kashe mishi wayan ya san ta rasa yadda zata yi ne kuma ko a haka sakon da yake so ya isa, ganin sakon Ahmad ya sa ya fita daga nata ya shiga faɗa mishi yake ya sanar mata jibi" za'a kai lefe daga Nassarawa sannan ya faɗawa Mum idan tana zuwa. Turawa Hibbah yayi saƙon kan ya fita ya ajiye wayan ya miƙe yaje ya shirya cikin wasu silk "cream pjmas, bayan ya gama har ya kwanta ya nemi layin Mum ya ƙirata." """Mum barka da yammaci"" ""Barka dai""" "Ta amsa ba yabo ba fallasa. ""Fatan duk kuna lafiya?""" """Lafiya ƙalau Alhamdulillah""" """Mum dama su Ahmad sun kira ni ne akan in sanar da ke cewa za'a kai lefe Kano""" Kaman jira ta shiga cewa """To me zan yi muku ni? Abin da ba'a yi involving na ba tun farko Meyasa ake gayamin batun kai lefe? Ai sun fi ni isa da kai don haka sai sun dawo""" "Har ranshi baya jin daaɗin rashin jituwarsu ba haka ta saba yi mishi ba, ta kasa haƙuri da shi" wanda hakan ke saka kunci a ranshi idan ya tuna. """Mum wallahi kina da matukar muhimmanci a rayuwata, ke na buɗi ido na gani a matsayin uwa Dukda ban zauna cikinki ba, kin bani duk wani gata da uwa zata ba ɗanta ko da Abba zai min wani abin ke kike kare ni, baki taɓa bari na yi kukan halayyar Abba gareni ba yanzu idan kema" "kika cigaba da fushi da ni Abba ya cigaba da tsanata yadda ya saba ina kike so na sa kaina?""" "Shiru ta yi kaman wacce maganganun suka shiga zuciyarta amma a zuciyarta tsaki ta ja tana raya ba zata taɓa kuma iya pretending akan tana son shi ba, aurenshi ya tsaya mata a wuya kuma burin ta na mallakar komai nashi zai iya komawa ga shegiyar matar da aka aura mishi" wanda ba zata taɓa bari ba ko da za tayi yawo tsirara ne kuwa... """Mum...""" "Kit ta katse wayan ya ɗan lumshe idanunshi da suka ɗan sauya ya buɗe, kiran wayan mahaifinshi ne ya shigo mishi ya zubawa Layin idanu yana kallo har ranshi baya farin ciki don" ya san ba zai kwana cikin walwala ba muddin yayi magana Da Abba a yau. "Abba bai taɓa kiranshi don karan kanshi ba tun mallakar wayar shi, faɗa, zagi ko masifa zai mishi akan abin da baya sanin ya aikata." Dab zai katse ya ɗaga ya saka a kunne idanunshi a rufe ruff ya shiga gaishe shi. """Anya kana son gamawa lafiya Almustapha?""" "Numfashi ya ɗan riƙe kan ya saki a hankali ""Abba ka yi haƙuri Dukda ban san laifina ba""" """Meyasa ka kai batun lefe chan dangin mahaifiyarka? Saboda ka nunawa duniya cewa Ita ba ita ta haifeka ba? Idan da uwarkace gidan zaka tsallaketa ka kai batun lefenka wani wurin har sai" "da za'a kai za ta samu labari?""" """Abba Mum fushi take yi da ni ko kan batun auren nan, bana so in kara mata bacin raina ya sa na tura kudin lefen nassarawa a tunanina da chan da nan duk ɗaya ne! Don Allah Abba ka dinga sassauta Kalamanka gareni ko ubangiji bai amsa ba zuciyata za ta iya bugawa watarana""" "Har lokacin idanunshi da suke motsi a rufe, idan ya buɗe babu abin da zai hanashi hawaye." """Almustapha ni kake faɗawa in daina yi maka faɗa? Then kam kai ka haifi kanka ba ni na haifeka ba, duk lalacewar Hafsatu ka san bata zalunceka ba idan ka butulce mata kai da ubangiji""" Yana kai nan ya katse ƙiran yana tsaki. Mum dake kuka ya kalla. """Ki daina zubar da hawayenki kan Almustapha, Allah ya ganar da shi, na kan yi mamakin" "halayyar yaron nan wai jinina ne da jinin Rabi'ah macen ƙwarai, Albasa bata yi halin ruwa b...""" Ta katse shi """Ka daina irin wannan maganan, na faɗa maka ne don ka matsa da tambayata dalilin kuka na amma ban ce ka faɗi bakaken magananu akan Almustapha ba, Na kasa mayar da hankali kan" "Mahir na bashi cikakkiyar tarbiyar da ta dace don in gina Mustapha kar ka lalatamin shiri""" """Ke da kike kare shi gashi ya watsa miki ƙasa a idanu Mahir da baki mayar da hankali kanshi ba ya kwaso halayyar da ta jefa shi cikin mummunan yanayi da ya ke ciki na miyagun abokai, kin ga kin yi biyu babu...""" Yana kai nan ya juya ya fice cike da haushin abin da Mustapha ke yi a yadda ya sani daga wurin matar tashi.. Shi kam Mustapha da kyar yayi bacci ranan saboda bacin rai. *** "Tun da ta faɗawa Umma batun kawo lefen suka shiga shiri fa, don baƙi sun fara isowa dama ranar kawo lefen gidan a cike makil da mutane, ko da Hibbah ta fito murmushi kawai ta ɗan yi da girgiza kai, same mutanen nan dai da suke gulma da zundenta, same mutane da suka taya duniya yaɗa labarinta, same mutane da suka gujeta suka kuma janye diyoyinsu daga gareta, same mutane da suka yi wa ƙaddararta dariya a yanzu sun zo su kashe kwarakwatan idanunsu" su kuma tabbatar da da gaske ne tayi auren. "Ko a jikinta don babu abin da ya kai bakin ciki a zuciyar makiyi irin ya ga cigabanka, ta tabbatar" "Almustapha ba zai yi abu da ƙaranta ba don shi ɗin idan zai yi zai yi ne wannan ta sani, ta kuma tabbatar a kanta ba zai yi kyashin kashe ko nawa ba ne." "Kaman kuwa yadda ta sani Baba Hussaini yayi shatar private jet da aka loda akwatuna masu masifar kyau da tsada ciki, mata ne manya na family guda uku sai matar Ahmad da shi kanshi suka jagoranci kai kayan auren, a chan Kano motoci ne masu rai suka zo suka tare su aka sake jero akwatunan da suka sha ado har gidan su Hibbah, tarba mai kyau suka samu ko da aka fara" fitar da akwatunan bakin mutane dayawa ya mutu. "Wasu daga cikin dangin Daddy ne suke ta guɗa, sai da aka jere set huɗu churr kan aka fara buɗewa, kayaki ne na ji da gani kowa sai sam barka lallai Hibbah ta yi Goshi, har key ɗin mota wanda kyauta ne daga kawun ango yana legos, key ɗin aka ba su." "Mommy da Umma suka haɗa 2m suka bayar tukuici banda uban kayan makulashe da snacks da aka har haɗa musu, an so su kwana amma sun ƙi sun ce jirgi na jiransu sai sun zo daukar" amaryar su da aka musu rowar ganinta. "Hudah ce da matar Ahmad suke sake tattauna batun cocktail party da zasu yi shi friday, don Layin Ahmad ta roƙi Mustapha da suke gaisawa ya bata ita kuma ta sanar mishi don su shirya a ɓangaren su." "Haka suka juya suka tafi suka bar su Mommy da kulawa da kaya, Aunty Asiya ta ɗauki mini Kit" da gwala-gwalai ne ciki ta tafi da shi saboda tsaro. Ita dai Hibbah tana daga sama tana kallon tsakar gidan don anan aka shirya aka gyara tsaff aka yi taron karɓan kayan har da decorating komai ya tafi smoothly cikin ban girma. "Washegari aka fara event na ango Najeeb da Amaryarsa Abida, sai nan Momma ta bayyana suka yi mothers eve ɗinsu cikin ban girma, Washegari Amarya tayi Kamu wanda su Hibbah suka je mata, wani red material da ya ji dinkin garari Hibbah ta sanya tayi kyau sossai Dukda banda gyaran jiki ba'a yi komai ba tukun daga kitso har kunshi sai Washegari, an sha kamun" amaryar Najeeb shima yayi kyau kuma sun yi hotuna. "Washegari aka tashi da chanchada mata kitso Dukda tayi ta nuna bata so amma Mommy ta sakata a gaba sai da aka fara ta tafi, ana kitso me lalle ta zo ta fara na soletape shima zaman tayi ta mita har aka gama, aka yi mata Black a sama da bayan hannu kasancewarta fara tuni ta" zuba wani irin masifaffen kyau. "Kowa ya ganta sai ya tanka har Zaitoon ta yi Adu'a ta shafa mata wai kar baki ya kamata, tace a fili" """Sai dai ya koma kansu Adda Zaitoon ni kam na yi azkar"" Suka yi dariya." Yinin ranar gabaɗaya gidan kacaniya ne ana ta raha yadda kowani gidan biki yake. "Ana yin Magrib Zaitoon ta shigo da wata kyakyawar mace janye da trolley Kit. ""Hibbah tashi""" "Ta faɗa kai tsaye. Hibbah ta miƙe zaune. ""Lafiya Adda Zaitoon?""" """Ga me kwalliya za ta fara yi miki"" ""kwalliyar mene?""" Ta tambaya cikin rashin fahimta """Na Cocktail party ɗinki da muka shirya""" Za tayi magana Zaitoon tace """In har dai kin daukemu duka da muhimmanci za ki tashi ba musu ki yi abin da muka ce, don musu ba zai chanza komai ba in kuma kina so ki watsa mana kasa a idanu ne then bismillah""" Baki ta turo tana Miƙewa zaune wallahi kanta har ciwo yake saboda kitson nan da ya takura "mata da zafi, haka taje ta zauna tana fushi aka fara yi mata kwalliya, kwalliyar bai yi nauyi ba amma ya fito tsaff tayi wani irin kyau na garari." "Fashion Designer da tayi making outfit ce ta shigo don fitting ɗinta, ita abin ma har mamaki yake" "bata, haka ta miƙe tsaye aka fara shiryata." "Ita ɗin fara ce ku hangomin ita cikin coffee Brown handwoven silk satin, yana da lace details Brown ɗin ya fi turuwa a stones da work ɗin inda aka yi layering ƙasan da wani cream mulberry silk, hand embroidry ne kayan, tun kan a gama fitting ɗin curvy and tall body ɗinta ya gama looking expensive and takeaway." "Bayan an gama sakawa ta zauna aka yi mata ɗauri mai masifar kyau, accesories ɗinta Hudah" ta fiddo. "Pearls jewelries ne simple but elegant, suka saka mata aka ɗauko french lace veil ɗinta That's crafted with premium material and detail handwork aka makala da kyau jikin ɗaurin ta sai ja yake ta baya heels ɗinta da shima designer ne coffee Brown me cream finishes ta saka sai aka bata clutch bag ɗinta shima coffee ne nd cream Color." (Ku hango Hibbah kawai a idanunku guys) "Wasu irin hotuna ake ɗaukarta ita karan kanta da ta kalli kanta sai da tayi hamdala wa ubangiji, sai kuma kuncinta ya gudu wani irin murmushi take da kowa sai da ya shiga mamaki Hudah ta" kai mata duka """'yar Is... Ashe kina son auren""" Ta saki murmushi """I must be a happy bride today twiny ko don idon makiya bare ma I am very happy, very very happy Alhamdulillah""" Zaitoon ce ta zo ta kamata ta fitar """Mu je parlorn baƙin Daddy ki zauna za'a zo a fita da ke don gidan nan kusan kowa ya wuce" "wurin taro""" "Bata Musa ba ta bita a baya har parlorn, a kan kujera ta zauna tana ɗora dogin fingers ɗinta da" "suka sha kyau cikin lalle kan cinyarta ta shiga wasa da su, fuskarta har lokacin da murmushi daidai ta ji an buɗe kofa, tana ɗagowa idanunsu suka sarƙe cikin na juna...." 72 "Ji tayi gabaɗaya gidan ya ɗauki shiru, not because he's loud, but because everything about him" "whispers wealth, class and power." "Sanye yake da Perfectly tailored grand Men lace, daga nesa ba zaka ce Men lace bane don sai ya matso ka iya hango kananun holes ɗin, yana da wannan shine and rich texture da ya bayyana tsurar tsadarshi daga kallo ɗaya kawai, coffee Brown ne, 'yar cikin tana da doguwar" hannu da ya saka mata wasu expensive links cibcib jikinshi. "Babban rigar na da faɗi sai dai dinkin na zamani ne, zanen dake gaban kirjinshi na rigar da aka yi da dark Brown is catching the light with every moment, fuskarshi ta bi da kallo slowly tana" sake mutuwa a kaunarshi. "He's tall, broad-shouldered, skin ɗinshi na wani irin glowing na hutu Dukda ba a zaune yake ba but he always take care of his skin, beard ɗinshi are neatly lined. Ya shiga takowa cikin tsantsar natsuwa idanuwansa dake lumshewa suna buɗu wa ko sau daya basu kau daga kanta ba no" "rush, no tension." "Idanunta ta ɗan saukar kadan suka tsaya kan sleek luxery watch dake daure a tsintsiyar hannunshi shima dark Brown, sai zobe guda ɗaya na azurfa ne amma dutsen Brown, ƙasa tayi da idanunta takalmanshi Italian leather shoe ne dark Brown, very clean and polished stepping" towards her with confidence. "Lumshe idanunta tayi tana shakar ni'imtacciyar kamshinshi da a yau ta ji chanji, karfinsu ya fi" "yanayi da oud, warm and deep fragrance da a take ya gama kashe jikinta tun kan ya iso." "Yatsunshi masu kyau kawai ta ga shigarsu cikin nata, soft and tender palms ɗinshi na haɗuwa da nata yana tsarga musu jini a tare, ɗagota yayi da hannun ba tare da ya iya magana ba ta miƙe tsaye." A hankali ya zame hannunshi ɗaya ya kai kan habarta ya ɗago fuskarta idanunsu suka sake "sarƙewa, ta ɗan daga nata don bugawar da zuciyarta yake ba zata iya jure kallon cikin idanunsa ba." "Ashe bata ma kula da well shaped hula da ake kira tangaran, Perfectly match da takalmanshi" "dake kafe kanshi ba, idan bata ce yayi mata mugun kyau ba then ta yi babban ƙarya." """Anya zan iya barin ki fita a haka Wifeyy?""" "Maganan ya fito very Calm amma cikin Muryar tana iya jin tension nashi, ya rasa ma me zai ce ya rasa ta ina zai fara yabon kyaun da tayi mishi a yau." """Ka zo lafiya?""" She asked Softly. Ya ɗan duƙa fuskarsu ya samu kusanci har suna shakar numfashin juna. """Kin yi kyau My starlight, irin kyau da ban taɓa ganin wani abu me kyau da shi ba, you Look stunning fiye da ɗawisu""" Ta tsinci kanta da karamin murmushi. """Ɗawisu na daga cikin halittar ubangiji mafi kyau a duniya""" """Kin fi shi Starlight..."" Ya katseta." Ta ɗan lumshe idanu kamshinshi yana kara shigar ta abin da yake mata a hannu yana sa taji tsikar jikinta na wani irin tashi don a hankali yake matsa su yana binta da mayen kallo. """Kai ma ka yi kyau""" Ta samu courage na faɗa a hankali. """Not as you Mrs MB MUSTAPHA""" "Ta ɗan motsa kaɗan zai yi magana aka yi musu knocking, bai sake hannunta ba Ahmad ya shigo." """Malam jiranku fa ake""" Baki ya taɓe """Kar ma ku jiramu don Allah ku watse dama bana so kowa ya kallarmin mata a haka"" ""Ai kuwa baka isa ba""" Murmushi kaɗan Hibbah tayi Yadda Ahmad ɗin yayi magana ya bata dariya shima kuma ya tare MB ɗin ne don ya san zai iya aikata cigaba da shanya al'umma. """Don Allah mu je""" "Ya sake faɗa yana kallon MB, waigo wa yayi ya kalleta." """Shall we?""." Kai ta ɗan gyaɗa ya daidaita da ita hannunshi cikin nata suka fara tafiya a hankali. """Masha Allah""" "Ahmad ya faɗa yana kallonsu don kyau sun yi kyau, and they are Perfectly made for each other." "Ko da suka isa Mota tana ƙoƙarin shiga dogon rigarta ya so sarketa tuni ya sa hannu biyu ya ɗauketa chak har cikin motar, idanunta a runtse cikin kunya har ya gama gyara mata veil ɗinta" "ya rufe kofar, ya zagaya ya shiga." Hannunshi na cikin nata babu mai cewa komai cikinsu amma shi ya san me yake yi wurin wasa da hannun nata slowly. Chan ƙasa yace """Lallen nan yayi miki kyau sossai, ban taɓa gani kin yi ba""" A hankali ta ce """Akwai zama ne ba daaɗi""" Ya ɗan murmusa kaɗan yana bin zanen lallen da yatsarshi ɗaya ya ce """Idan ya goge i will Sit u on my laps a sake yi miki wani ba za ki gaji ba""" Ta rufe idanu tana ɗan murmusawa. "Sun isa wurin taro dake cike da mutane, babu manya taro ne na samari da 'yan mata, abin da ya basu mamaki ganin kusan duka ma'aikatan MB MUSTAPHA AUTOMOBILE COMPANY, shi kam har wasu daga cikin Abokanshi ya gani wurin da ma wasu business friends masu irin" sana'ar shi da ake good terms. "Maza da mata ankon cream suka yi, mazan duk Men lace ne cream da hula irin na yarabawa mai kala biyu cream nd brown, takalmansu Brown, matan kuma lace material cream suka yi dauri da coffee sun yi kyau ita kanta ta sha mamakin ganin ƙawayen su na secondary har da" wasu na university da ta fara tayi dropping out. "Masu hoto sai aikin ɗauka suke har suka zauna, hall ɗin na screaming luxury wasu irin mixed kamshi ke tashi sai ka rasa wani turare ne ya fi wani, an fara gabatar da taro aka yi raye raye wanda su Zaitoon sun cashe kwarai na murnar biki, kan aka kira Amarya ta fito cikin 'yan uwanta su taka kaɗan, Hudah ce taje ta kamo ta shi dai MB ba yadda ya iya ne da babu inda" zata je tana nan rike da hannunshi. "Waƙar Dan Musa aka sakar musu na aure, suna Mamming suna takawa a hankali take rausayawa tana murmushi mai kyau, itama ta shiga bin wakan musamman lokacin da yake cewa" """Masu karyar cewa an fasa to an ɗaura kun ga ku kam da ma kun saba da abin kunya...""" Ba'a yi spray ba amma hall ɗin ya zama very lively. "Bayan sun gama ta koma zaune aka kira abokan ango da ango shi dai sai murmushi yake bai yi rawa ba amma friends sun yi har da P.A, bayan sun koma aka ajiye basket gabansu lokacin ba da gift, kudi kuwa sun ganshi don masu saka Dollars ma sun fi yawa sossai Hibbah ta ji daaɗin event ɗin saboda ta ga kara wurin jama'a, daga nan aka kira ango da amarya su yi rawa a cikin" hayaƙin masoya. "Yana rike da hannunta har tsakiyar hall ɗin, ko da suka tsaya kan ta yi wani yunkurin ya sa hannunshi yayi grabbing wait ɗinta zuwa gareshi, a bazata hakan ya sa ta kai hannunta ɗaya kan kirjinshi ta ɗago ido tana kallonshi aka shiga kashe su da pictures, murmushi yayi mata itama ta mayar mishi, sai ya shiga juyawa da ita a hankali ba rawar kai ba hayaniya itama tana juyawa a hankali hayaƙin ya baibayesu waƙar Ali jita ke tashi na" """Duka zuciyata... Ke kika mallaketa.. Ban iya gane mata in ba ke ba gwanata..an ba ni keee an bani ke! An ba ni ke kin ga an ba ni ke...""" Ya ji daaɗin wakar don kaman daga zuciyarshi yake fita. "Bayan nan aka kawo cake suka yanka suka ciyar da juna, daga nan aka ci aka sha enough kan aka watse taro wurin karfe sha biyu na dare." "Har cikin gida suka sauke su, ko da Ahmad yayi parking shi ya sauka ya buɗe ya riƙe hannunta" ta sauƙo. """Goodnight and sweet dreams my kids Mamee ฀" "I love you""" Yana kai nan ya matsa ta wuce tana murmushi kaɗan kaɗan. Washegari da ƙarfe tara aka ɗaura auren Najeeb da Amaryarsa daga wurin ɗaurin auren Almustapha ya wuto gidansu da tawagarshi don daukar Hibbah saboda da kanshi zai ɗauki matarshi.. "Yau shigan tsadaddiyar farar shadda yayi mai haske kwarai dake ta walwali, har da babbar riga," "bakaken takalmi, agogo da hula ya saka ko da suka ƙaraso iso aka yi mishi har parlorn Daddy" don ya nemi ganinshi. "A ƙasa ya samu Hibbah zaune cikin wani green luxury Laffaya, baya iya ganin me a ƙasan laffayar kanta a ƙasa hannayenta a fili rike da handky da alama kuka take yi, ya ɗan lumshe ido" ya buɗe kan ya samu wuri a kan tattausan carpet ɗin shima ya zauna Daddy ya miƙe ya riƙo hannun Hibbah ta miƙe tsaye suka taka a hankali har gabanshi ya kama hannunshi ya sa na Hibbah ciki. """Almustapha Na nemi ka zo da kanka ne ba don komai ba sai don in damƙa maka amanar 'yata da hannuna zuwa naka, ita ɗin amana ce mafi daraja da nake da ita a rayuwata, Hibbah ko a cikin yarana ta daban ce ta tashi cikin gwagwarmayar rayuwa ta yi battling kaddarori da dama ta kuma haye su bisa hukuncin Allah, ita ɗin me rauni ce tana bukatar So da jin ƙai daga gareka, tana bukatar Hakurinka domin aure ba tare da jarabawa ba baya wanzuwa, tana bukatar girmamawarka kaman yadda kaima za ta girmamaka, ka kula da ita da zuciyarta domin duk wata mace tana bukatar kulawa." Idan ta yi kuskure ka zama mai gyara a gareta cikin hikima ba da wulakanci ba. Almustapha rana ɗaya ka ji cewa wannan amana da na baka ba zaka iya rikewa ba don Allah kar ka wulaƙanta min ita ka dawor min da ita zan karɓa in kuma yi godiya. "Ina yi muku Adu'ar Allah ubangiji ya baku zaman lafiya, ya sanya albarka cikin aurenku, ya sanya soyayya da fahimta a tsakani ku kuma ya ba ku zuri'a ta gari""" "Zuwa lokacin sossai Hibbah ke kuka, Momma da suke zaune a parlorn ma hawaye take yi, uba" "irin na Hibbah are rare, yana son ɗiyarshi fiye da yadda zai so kanshi shes really her Daddy's princess from day 1." "Kukanta yana tafiya ne kai tsaye zuwa zuciyarshi yana kassarata, sam baya so riƙe hannun yayi da kyau cikin kulawa kaman wani abu mai daraja da riƙe shi da garaje zai iya fasa shi. Ya ɗago ya kalli Daddy..." """Na gode kwarai da wannan girmamawa da kuka yi mini na damƙa min amanar Hibbah Daddy, wannan amana ce me matukar nauyi da nake ji a zuciyata, in shaa Allahu zan yi iya kokarina wurin riƙeta da gaskiya, soyayya da kulawa kamar yadda ta cancanta, zan yi iya kokarina wurin" "kare mutuncinta, faranta ranta da gina zaman lafiya a gidan aurenmu.""" Hankalin Daddy ya sake kwanciya kwarai da MB ba zai taɓa wulakanta mishi 'ya ba. Daddy Rabi'u ne yayi musu nasiha haka mommy ta musu wani tukuna aka ce za su iya tafiya. "Zame hannunta Hibbah tayi da sauri taje ta faɗa jikin Daddynta tana kuka kaman ranta zai fita," shima da kyar ya iya danne hawayen dake cika mishi idanu Momma ta miƙe ta fice tana yiwa ɗiyarta adu'ar tabbataccen zaman lafiya... "Almustapha ne ya zo ya zame ta tana girgiza mishi kai cikin kuka take furta ""Da..d..ddyy""" Ya juya kawai ya shige ɗakinshi yana share hawaye... Rungumeta Almustapha yayi ta cigaba da kuka suna tafiya a haka har waje da kanshi ya sanyata mota kowa sai kallonsu yake. "Zaitoon, Hudah, Umma, Mommy, Aunty Asiya da kuma Matar Daddy Rabi'u ɗaya da Aunty husna su ne za su tafi da amarya inda suka shishiga motoci sai Airport." Ko a cikin motar tana kwance a kirjinshi hannunshi zagaye da ita yana bubbugata a hankali tana fitar da shesheka kadan kadan har suka isa Airport... "Private jet ne suka yi hiring guda biyu, shi da ita da Zaitoon da Hudah suka shiga ɗaya inda iyayen suka shiga ɗaya su Ahmad basu bi su ba don Nassarawa za su yi matarshi kawai ta shiga wurin su umma don akwai wasu 'yan uwa a chan masu taryar Amayar, yayinda ma'aikatanshi dayawa sun wuce tun sassafe, ciki har da P.A da ya sa ya je yayi arranging cars" da za'a ɗauketa zuwa gidansu. A cikin jirgin ma bata bar jikinshi ba da kyar ya samu nasarar sakata shiru su Zaitoon sai gulma "suke, shi dai hankalinshi da kulawar shi na kan gimbiyarshi har suka sauƙa birnin ikko." "Motoci na alfarma suka dibe su, yanzu ma ita da shi ne kawai motar su, ya ɗan ɗaga veil ɗin saman kanta a hankali ya furta" """Ɗaga ki sha iska One and only""" Ya leƙa idanunta sai ya kwaɓa fuska """Subhallah! ji idanunki fa sweetheart please kar ki sake wannan kukan ya isa haka""" "Ta gyaɗa kai, ya cigaba da shafa bayanta har suka isa tamfatsatsen gidan suka sauƙa sai a lokacin Umma ta zo ta kamata shi kuma ya matsa baya tsirarun 'yan uwanshi suka fito suna yi musu maraba, Mum da suka dauko da kyar tana hakimce zaman jiran amarya su suka musu jagora zuwa ciki don gidan gida ne da ya amsa sunanshi, ko da suka isa kofan sai da ta ɗan" dakata kan ta sanya jafarta na dama zuwa ciki bisa umurnin Umma Bakinta ɗauke da adu'o'i... (Wayyoo hannuna...) 73 "*Ku fara da wannan, ɗayan na nan zuwa in shaa Allah*" "Parlorn akwai 'yan uwa tsirara na Nassarawa, duk Miƙewa suka yi sun yi wa Amarya da dangin" "ta barka da zuwa, nuna musu gaban Mum suka yi." """Ga nan uwar ango ta ƙaraso ta nan ta miƙa gaisuwa""" "A gabanta Umma ta sa ta durkusa, Mum ta kirkiro murmushin yake da take ta saki tun ɗazu tace" """Maraba lale da shigowa wannan zuri'ar, Allah ya haɗe kanku ya ba ku zaman lafiya"" Aka amsa da Ameen." Ɗaya cikin gidan 'yan uwan Mahaifiyarshi ta taso """Bari mu ga fuskar amaryar tamu ai ba za mu tafi bamu ganta da kyau ba kar ta zo mu kasa gane ta""" "Da wasa take maganan don Abokiyar wasa take ga Mustapha, su Mommy na gaisawa da Mum a lokacin da wanchan ɗin ta janye mayafin laffayar da ya rufe fuskar hibban ta ɗan tallafo kumatunta tana ɗago kanta wasu na cewa Masha Allah, daidai lokacin da Mum ta kai idanunta" kanta Hibbah ta buɗe idanunta da suke lumshe suka shige cikin nata. Wani irin Miƙewa tsaye tayi kaman wacce tayi gamo da aljani idanunta na jefan Hibbah da wani "irin mummunan kallon tsana yatsanta na nuna ta tace ""Ke. Ke Almustapha ya zagaya ya aura??""" Jikinta har rawa yake saboda tashin hankalin da ta shiga. """Hajiya lafiya? Ko kin santa ne?""" """Wannan watsatsiyar? Wannan tambadaddiyar masharranciya? Wannan 'yar iskar ka...""" """Subhallahi menene haka? Wani irin kalamai ne wannan?""" Umma ta katseta tana miƙe wa tsaye. Kowa hankalinshi ya tashi ganin yadda Mum ɗin ta sauya lokaci guda wani irin ja fuskarta yayi har turiri take na baƙin ciki da takaici. Da sauri wata daga ciki ta fita tana neman Almustapha shi kuma yana tsaye daga tsakar gidan hannunshi a Aljihu yana waya da Ahmad da yake ce mishi ya tabbatar jama'ar nan sun bar gidan cikin lokaci kar su yi missing flight na yammacin da zai kai su Nassarawa a ranar. """Musty...""" "Kusan haka ne sunan da dangin mamanshi suke kiranshi da wuya su kira shi complete, waigo wa yayi yana kallon babban ɗiyar uncle Muhammadu da take aure a Nassarawar har da zuri'a." """Akwai matsala fa, ka zo!""" Gabanshi ne ya faɗi don bai san Mum na gidan ba. """Me ya faru?""" """Mamarka c...""" "Kan ta ƙarasa ya nufi parlorn da sauri, gabaɗaya sun rikice yadda Mum ke jefa Hibbah da munanan kalamai tana zagin ta tana tsine mata albarka kuma tana kukan baƙin ciki, baƙin cikinta na ta rasa komai Almustapha na samun abin da yake so, ya shammaceta bata taɓa zato ko tsammanin yarinyar Almustapha zai zagaya ya aure wacce ta tsana fiye da kowa da komai a duniya, ko tsanar da tayiwa Almustapha da Rabi'ah be kai na yarinyar da ta zura mata idanu" tana kallonta bata ko motsa ba. "Umma ce ta zo ta kama Hibbah ta dagata daidai Almustapha ya shigo idanunshi ya kai kan Hibbah ganin ba kuka take ba kuma ba alamun an yi mata wani abu ya sa ya shiga sauƙe ajiyar zuciya a kai a kai, idanunsa ya kai kan Mum da ta tsayar da nata kan shi tana jefanshi da wani" irin kallo da ya kasa fassarawa. """Almustapha! Almustapha!! me ka daukeni?""" Ya nufeta yana ƙoƙarin riƙeta """Mum ba sai kin tambayi matsayinki a rayuwata ba ke ɗin uwa ce a gareni kin cike mini gurbin Mammiey baki bari na yi maraicin uwa ba""" Ta fusge da ƙarfi... """kenan ina da muhimmanci a rayuwarka?"" Kai ya gyaɗa mata a sanyaye." """Zan iya saka ka abu ka yi?""" Nan ma kai ya gyaɗa mata idanunshi na cigaba da sauya wa. """Toh ina so a yau kar wanchan Yarinyar ta kwana gidan nan! Bana so ta ƙara mintuna biyu da" "aurenka kanta! Wallahi wallahi ba zan taɓa bari ka zauna da karuwar chan b...""" "Wani irin runtse idanu yayi gabanshi na faɗuwa fat fat fat ""Innalillahi wainna ilaihi rajiun..""" Daga mommy har su umma da su Zaitoon abin da suke maimaitawa kenan yayin da Hudah tuni ta fara kuka. Hibbah ko ɗarr bata ji ba sai ma murmushi da take jifan Mum ɗin da shi. """Almustapha ba zaka saketa ba???""" "Ta daka mishi tsawa, ya girgiza kai yana buɗe rinannun idanunshi" """Mum abin da ya faru a baya kuskure ne, kuma ba laifinta ba ne, Mum rabuwa da ita daidai yake da tarwatsa tawa rayuwar...""" Kai ta gyaɗa sai tayi wani murmushin bakin ciki a lokaci ɗaya tana hawaye. """Eh lallai! Lallai na raineka ka girma ka zama mutum Mustapha dole ka kalli tsabar idona ka ce ba zaka iya rayuwa ba tare da wanchan tsinanniyar ba da ta lalata rayuwar ɗan uwanka, yayi kyau. Amma ka sani muddin kana tare da wannan yarinyar babu ni babu kai har Abada, muddin" "baka saketa ba kar ka sake zuwa inda nake Almustapha""" "Tana kai nan ta juya ta fice tana kuka sossai, idanunshi ya saukar ƙasa zuciyarshi na cigaba da" "bugawa, dama ya san hakan zai kasance amma bai yi tunanin muninshi ya kai haka ba, Mum" "uwa take a wurinshi kaman yadda ya faɗa don ita ta bashi duk wani gatan uwa a rayuwa, wannan kam har abada ba zai cire ba yana ƙaunarta har ranshi saboda a wurinta kawai ya samu salama a yarantarshi wani lokacin har mantawa yake da ba ita ce ta haife shi ba, anya" yayi mata adalcin sakata hawaye? A hankali ya juyo ga Mommy da Umma da jikinsu yayi matukar sanyi barin ma Umma hankalinta ya tashi. """Ku yi haƙuri Mommy don Allah""" "Yadda ya faɗa ɗin sai ya basu tausayi har ita Hibbah, sai yaushe zai fahimci matarnan ba kaunarshi take ba ya daina damun kanshi da damuwarta?" "Bakin da ta ɗan taɓe sai a kan idanun matar Ahmad da take ta karantarta tun fara rigimar," Mommy ta ce """Kana ganin za mu iya barin Hibbah anan Almustapha?""" Da sauri ya matsa kadan gabanta yana girgiza kai """Babu abin da zai faru mommy kar ma ku kawo maganan juyawa da Hibbah don hakan ba mai yiwuwa ba ne Mommy""" Duk ya damu kaman sun ce sun tafi da itan ne. """Yaya Amina motocin da za su kai ku airport suna waje duk ku kwantar da hankalinku, Mun gode kwarai da hidima""" Suka juya don fara shirye-shiryen tafiya kowa da abin da yake saƙawa a ransa. "Umma ta kama Hibbah tana tambayarshi ɗakinta da hannu ya nuna musu suka nufi ɗakin dukkansu, ɗaki ne da ya ji komai na alatu saboda Hibbah ba karamin Goshi tayi ba, Daddyn su Nasir ne yace sam ɗiyarshi ce Hibbah tunda tayi Rayuwa mai tsawo karkashinshi shi zai mata kayan ɗaki, to mahaifinta ma bai naɗe hannu ba don ma yana iya yinshi ya danne soyayya da tausayawarshi ga Hibbah duk cikin 'ya'yanshi haka Daddy Rabi'u sai ta tashi da mafi tsaddodin furnitures dakuna har uku aka yi mata jere na ban girma haka parlor biyu tsaf aka jere mata da" tsadaddun kayakin waje. "Kitchen ɗinta ba'a magana, ga motoci biyu da ta tashi da kyautar su a auren ban da tsohon nata, a kan shinfidadden bed da aka lailaye da tattausan bedsheets suka zaunar da ita umma" dai bata natsu ba ta kalli mommy. """Adda kubrah kina ganin za mu bar Hibbah gidan nan karkashin wanchan matar? Kiyayyar uwar miji fa ba shi da daaɗi kwata kwata ga barazanar tsinuwa""" Hudah tace """Umma ai Hibbah ta fi kowa sanin menene Kiyayyar uwar miji tunda ni karan kaina gefe na koma na zuba musu idanu da Hajiyar Mu'azzam me rasuwa""" Hibbah tayi murmushi tana tuna rigimar su da waenchan mutane lallai a yanzu ma bata sauya ba bare ta san wannan matar hatsabibancinta ya wuce tunanin me tunani amma zata nuna mata ita ɗin 'yar yau ce. """Haka ne kam Hudah, ba za mu so tadawa kowa hankali akan wannan auren da kowa ke farin ciki marar misaltuwa da wanzuwarshi ba, by the way ba ita ta haifeshi ba Dukda na san tana da hakki a kanshi a yanzu sai dai tunda yana son ta kuma ya shirya shawo kan matsalar ba komai ba ne in shaa Allah""" Mommy ta faɗa tana kallon hibbar. Aunty Asiya da ke zaune kan lallausan sofa na ɗakin beige Color ta ce """Ku ne kuke ɗaga hankalinku ja'irar yarinyar ba gata nan murmushi take yi tun fara rigimar ba""" Zaitoon ta ce """Ayya Aunty to me zata yi? Abu ne ta saba ji"" ""Dukda haka da ciwo sossai Zaitoon!""" "Mommy ta faɗa har lokacin tana jin zafi, tana da faɗa bata da haƙuri sam kuma da Mum ta" cigaba da zage zagenta ga Hibbah ta sani zata iya retaliating su lalata komai shiyasa take ta danne zuciyarta. Duk sun ɗauka ma a kan rayuwarta na baya Mum ɗin ke darun cewa ba zai zauna da karuwa ba basu sani ba saboda har yau bayan su Daddy babu wanda ya san batun Mahir. "Ganin hankalin Hibbah kwance ya sa suka sake, sun fita sun zaga gida kam yayi kyau ƙwarai" "don in ka ce kyau ma ka rage, sai da suka yi Magrib suka kara kimkimtsa mata komai don mutanen kanon gidan Mommy za su kwana da sassafe jirgin su zai juya da su zuwa Kano." Ana yin isha sun gama saka sanyayyun turaruka masu masifar kamshi cikin burners da suke "kusufa kusufa na gidan, ga kamshin sabbin furnitures ga sanyin Ac ga na turarukan wuta sai ya ba gidan wani soft and cool kamshi mai kassara gaɓɓai da saka kasala." "Umma ta sa Hibbah sake wanka suka shirya ta cikin wani Atampha da aka yi wa dinkin straight gown mai kyau sossai ya ji stone works, gyalen da ya shiga da kayan ta yafa sai kamshi take zubawa yadda ya kamata matsayin Amarya, su Zaitoon fita suka yi Mommy da Umma suka saka ta gaba da sabon nasiha har sai da ta sake kuka, kaman kar su tafi don babu wanda ya zaci Hibbah zata yi irin kukan nan a aurenta duk yinin yau kuka ta yini yi har zazzabi na rufeta, jikinta ya ɗauki zafi kuma yunwa take ji tun safe tea ne kawai cikinta idan wannan ya tambaya ta ci abinci sai tace eh wane ya kawo mata don bata jin cin samm wani masifar kewar Daddynta take ji kaman ta gudu ta koma, ashe haka aure yake? Ashe tana da rabon jin yadda kowace" "mace take ji? Feelings nan daban yake, lallai aure ya tabbata yaƙin mata." "Tana nan zaune hannayenta na wasa da ƙasan vail na jikinta Dukda irin zazzabi da take ji da ciwon kai ga faɗuwar gaban da ta fara fama da shi tunda ta ji gidan ya ɗauki wani ni'imtaccen shiruuu baka jin motsin komai sai Ac dake fita a hankali, motsi ta ji bata ɗago ba sai da ta ji an" buɗe kofa an shigo a hankali ta ɗaga kanta sai ta ga shi ne ya shigo ɗakin. "Hannunshi riƙe da wani kyakyawar tray da ba zata ce ta san me akai ba, sanye yake da wani" "boyel mai yanayi da ruwan kalar sararin samaniya da ya matukar karbar skin ɗinshi dinkin zamani haka hulan zanna da ya ɗora akan soft hair ɗinshi kalar kayan ne, agogon hannunshi" "Black ne da zoben azurfarshi, tun kan ya gama ƙarasowa kamshinshi mai daaɗi ya shiga ratsa" "kofofin hancinta, har ya ƙarasa ya ajiye tray ɗin kan tattausan rug da ke malale a ɗakin, nufar ta" "yayi sai bugun zuciyarta ya ƙaru dab ita ya zauna sai yayi mata sallama, a hankali ta amsa." Hannu ya sanya ya ɗaga gyalen zuwa saman kanta sai ya sake matsawa kan ta yi wani motsi "ya janyota ya sanya cikin kirjinsa ya mayar da hannun a rufe, a tare suka sauƙe kyakyawar" ajiyar zuwa cikin wani kalar murya ya ce """Barka da shigowa gidan aurenki na har Abada Sugar, barka da matar ƙwarai, barka da matar kirki... Madallah da natsuwar zuciyar Al-Mustapha... You are my answered prayer Hibbah!"" Lumshe idanu tayi sai hawaye suka shiga zubo mata a bazata, bai san kuka take ba don bayanta yake shafawa a hankali sai da ya ji sheshekarta, hannunshi mai taushi ya sa a" kumatunta ya ɗago fuskarta """Subhallah! You are burning babe, baki da lafiya ne? Ina ke yi miki ciwo? Ko mu tafi asibiti?""" Sai kawai ta sake kara fashewa da wani irin kuka ganin yadda ya rikice daga jin zafin jikinta. """Na kasa amintar da zuciyata da kalamanka, na kasa sakin jiki da baƙo yanayin da ya mamaye dukkan ilahirin jikina zuwa bugun numfashina, is this real? Shin wannan ma zai tabbata ko na wucin gadi ne? Bana so in sakankance cewa komai ya wuce wani abu da zuciyar Hibbah ba zai iya dauka ba ya faru. Tsoro nake ji MB ina tsoro sossai...""" Ta ƙarasa cikin shesheka. "Yatsunshi ya sanya yana dauke mata hawayen cikin wani irin yanayi ya shiga cewa ""Kina kokonton soyayyata a gareki ne?""" Yanayin da yayi maganan ya sanyaya jikinta ta duƙar da kai. """Duk mazan da suka shigo rayuwata sun shigo ne da manufa, ban taɓa sa'a ba sai sau ɗaya shima ya kufce min ba tare da shiri ko tsammani ba, kana tunanin zan iya yarda da kalmar I love you kawai?""" Ya tari numfashinta """Ban san ko na faɗa miki ba hibba, amma ki sani duk namijin da zai iya samunki ya yi sakaci har ki suɓuce mishi is an idiot.""" "Ta kalleshi ya gyaɗa mata kai. ""Kin san mene?""" Ta girgiza kai """Zan cigaba da faɗa miki ina son ki har ki gamsu da cewa ke ɗin ce tauraruwar zuciyar Mustapha, wallahil azeem Hibbah soyayyata a gareki ba ta da iyaka. Na kuma yi miki alkawarin" "kowani yini zan cigaba da sonki fiye da jiya har zuwa ranar da numfashina zai tsaya""" "Komawa jikinshi tayi ta zagaye hannayenta a bayanshi sai ya karɓeta yana matseta kaɗan, zafin jikinta har a jikinshi ya fara ji sai ya ɗagota." """Tashi ki ci wani abu mu yi sallah babe ki sha magani, you are sick""" "Hannunshi ya sanya cikin nata ya ɗagota har tsakiyar carpet ɗin suka zauna, foil ɗin ya buɗe gasashen kaza ne da ke tashin kamshi ya buɗe ya gasu har kashin yayi laushi, tsokar naman yake sabulewa yana bata tun tana ƙin karɓa yana lallashi har ta fara ci a hankali sai da ta koshi" "kan ta kawar da kanta, sanyayyiyar fresh milk ya tsiyaya ya bata ta sha kaɗan." """Za ki iya yin alwala?""" "Kai ta gyaɗa ""Oya je ki yi ki zo""" "Ta miƙe cikin dauriya don har wani jiri take ji tana shiga bayin kuma zuciyarta yayi ta tashi amma haka ta daure tayi alwala ta fito, ko da ta fito ya tattare wurin shima da alama yayi alwala har ya shimfida musu fararen darduma tasss masu laushi, ta zo ta cire gyalen ta ɗauki hijabi ta saka tana zame dankwalinta, raka'a biyu suka yi saboda ya san bata jin daaɗi bayan sun idar ya dafa kanta yayi mata wasu adu'o'i kan ya miƙe sai ta zame ta kwanta a wurin ta dukunkune" cikin hijabinta. "Fita yayi chan sai ga shi ya dawo, ya sauya zuwa wasu Navy blue pjmas masu yauki riga da" "wando, hannunshi riƙe da ruwa me rangwamen sanyi da tray ɗan ƙarami wanda magani ne a" kai da cup. "A gabanta ya duƙa ya sanya hannu ya ɗagota ya bata maganin ta sha, za ta koma ta kwanta taji yayi sama da ita, hannu ta sa ta zagaye wuyanshi kanta na binne a ƙirjinshi har kan gado ya kwantar da ita sai ya miƙe ya nufi wardrobe ɗinta ya samo wani silk wine Color half gown na" bacci me tsiririn hannu ya dawo. "Tana kwance ta ji yana yaye mata hijabi bata motsa ba har ya cire, wani irin zabura tayi jin ya" saka hannu bayanta yana zuge zip na rigarta… 74 """Calm down babygirl! Zan taimaka miki ne ki cire wannan kayan ki yi bacci, I promise not to do anything other than that""" "Ta ɗan ɗago gajiyayyun idanunta da suke cike da wani irin bacci, gajiya da ciwo ta kalleshi." "Ya saki soft smile ba tare da ya shirya ba ganin tana mishi kallon wayo zai mata, ya ɗagota" kaɗan zuwa jikinshi calmly ya ce """Me ya sa zan yi rushing ɗinki kina cikin wannan halin Sugarplum? You are mine only. forever" "and always. I won't rush""" Maganan sai da yayi sending chillness down through her spine. Zame hannunta da ta riƙe nashi slowly tayi ya birkitota tare da matso ta sossai jikinshi lumsassun idanunsa da suka sake lumshe wa saboda abubuwa da suka carke mai na jifanta da wani irin kallo daya karya dukkanin garkuwar jikinta. "Rufe idanuwanta tayi ahankali numfashinta na fita da sauri qirjinta na sama Yana komawa, tana jin shi ya zame zip ɗin yayi ƙasa da rigan bayan ya cire mata ya saka mata wannan rigar tukuna ya zame under wear dake ƙasan kayan, tattausan hannunshi ta sake ji kan fatar bayanta da ya sa ta kame a ranshi murmushi yake yana jin bugun zuciyarta har a jikinshi ya ɓalle hooke ɗin bra ɗinta a bazata ta ji hannun ya dawo ta kafadunta ya cire hannunayen sai ya mayar gaba" slowly ya zaro bra ɗin idanunta ta ƙara runtsewa a kunyace. "Ya riqo qugunta yaqarasa matso da ita cikin jikinsa, still idanuwansa dasukai wani laushi suna kanta, ta ƙara rintse idanuwanta tana jan numfashi wutan ya miƙa hannu ya kashe musu tare da jan burgo ya lullubesu, a kunnenta ya raɗa mata" """Sleep tight Sugar""" "Tun tana ɗari ɗari da tsoro har ta saki jiki bata wani jima ba bacci ya ɗauketa, shi kam ya jima" sossai yana tunanin Mum da hukuncin ta kan bacci ya sace shi rungume da ita. "Shi ya fara farkawa da asuba, a hankali ya kai hannunshi wuyanta ya shafa jin ba wani zafi ya sa ya sauƙe numfashi ya zame ta ya miƙe zuwa bayin ta yayi alwala ya fito, ko da ya fito a zaune ya ganta sai dai ta cukwikuye blanket din a jikinta bai ce komai ba bayan murmushi ya fita, da sauri ta sauƙa ta shiga bayin tayi alwala ta fito ta saka hijabin da ya kai mata kasa daidai ya shigo kenan sanye da jallabiya ya ja su sallah, bayan sun idar ya janyota ya zame hijabin ya kwantar da kanta kan kafafunshi, hannunshi ɗaya a flat tummy ɗinta daya na shafa yiri yirin" kitsonta ya ce. """Good Morning Hayatee""" "Sai ta ji kunya ya kamata a hankali ta ce ""Ina kwana?""" "Murmushi yayi ya ce ""How are you feeling?""" Kai ta gyaɗa mishi kan ta ce """Na ji sauƙi""" """Good""" Yadda yake sosa mata kai tana lumshe da idanu tun tana jinshi har wani baccin ya sake "ɗaukarta, ya ɗaga ta chak zuwa gado ya kwantar bayan ya kwantar da ita ya gyara mata lullubi ya fita." "Da kanshi ya haɗa musu simple breakfast yaje yayi wanka tunda babu inda za shi Farar shirt da wata three quater Ash ya sanya sai ya zauna ya kunna system ɗinshi yana ɗan duba Emails, ya fi 30mins kan ya miƙe yana rufewa ya nufi ɗakinta Its already past 8 ya kamata ta ci abinci ta" sha magani. "Yana tura kofan wani sassanyar kamshi yayi mishi sallama, ya lumshe idanu ya buɗe yana" "saukewa kan gadon sai dai babu kowa kuma ta gyarashi tsaf kaman ba'a kwanta ba, idanunshi" "ya fara zagaye cikin ɗakin yana neman ta, chan ya hangota gaban madubi tana saka jewelries kanta na ga zoben da take sakawa a yatsanta ko buɗe kofar bata ji ba sai mannuwarshi da" "bayanta ta ji ya zagayo da hannunshi kan cikinta, duk su biyu idanu suka lumshe." """Kin tashi?""" "Ta ɗan gyaɗa kai, ya saketa yana juyo da ita ta fuskance shi. ""Kin yi kyau""" "Ta ɗan yi murmushi kaɗan ""Ya jikin?""" Kan tayi magana ta ji hannunshi a wuyanta sai da ta ɗan zabura yayi murmushi """Na ji sauƙi""" """Masha Allah, mu je ki yi breakfast""" Ya riƙo hannunta suka fito har dining da kanshi yayi serving nata kan yayi wa kanshi ya zauna bai takura ta ba suka karya. "Son yarinyar yake ji kaman zai mishi illah, duk idanunshi suna kan motsinta bini bini zai" "tambayeta tana bukatar wani abu? Is she Ok, sai ta ji zuciyarta ya gama sallama mishi..." "Wayanshi ne yayi ringing yana dubawa yanayinshi na ɗan sauya wa don Abba ne, da kyar yayi" gaining courage yayi picking. Wani irin Miƙewa tsaye yayi """Mene? Innalillahi wainna ilaihi rajiun yaushe Abba? Is it worst?""" "Hankalinshi ba karamin tashi yayi ba, ta miƙe tsaye daidai ya sauƙe wayan ta riƙo hannunshi" """Lafiya?""" Ya haɗiye wani abu """Jasrah ce wai ta ƙone sossai a hannu""" "Ai sai ta fi shi rikicewa tuni hawaye ya fara zubar mata, yau take so ta lallaɓa shi ya ɗauko mata ita Allah ya sa ba wani abu Mum tayi mata ba, da sauri ta juya zuwa ɗaki ta ɗauko mayafi, car key kawai ya ɗauka suka fito don driver ɗinshi ya bashi hutu saboda yana so ya huta da" "iyalinshi sossai, fita suka yi." "Tun da suka ɗauki hanya Hibbah lokaci lokaci sai ta share hawaye, zuciyarta na mata zafi tana ganin kaman Allah zai iya kamata da shirun da tayi bayan ta san yarinyar na cutuwa, ko da suka isa Abba na daga waje shi da Mum, tun daga nan suke jin ihun yarinyar sai Hibbah ta sake" "rikicewa Dukda shi ma bashi da natsuwa amma ya miƙa hannu ya riƙo ta, bai ce dai komai ba." "Suna nan tsaye aka fito da ita, daga dantsen hannunta zuwa wrist ɗinta zagaye da bandage," "tayi yaraf kan gadon da suka turo ta, tana ganin Babanta ta fara miƙa mishi hannunta me lafiyar" shi da Hibbah suka nufeta haka Abba. """Sannu Princess, Sannu!""" "Ya faɗa cikin wani yanayi, Hibbah kam har lokacin hawaye take, Dukda Jasrah na cikin azaba sai da ta murmusa ganin Hibbah, sai ta shafa kanta" """Allah ya baki lafiya Sannu""" Wani ɗaki suka tura ta don an yi mata allurar rage zafi ana so ta huta a ga yanayin kunan don fatar wurin gabaɗaya kwailewa yayi sai da suka je ma Hibbah da MB suka sake ganin wasu da suke daga cikinta duk sun duri ruwa digo digo dayawa. "Da kyar Hibbah ta ajiye hankalinta bata haukace wa Mum ba don ta tabbatar cikin zaluncinta ne, gaishe da Abba tayi ganin jasrahn ta fara bacci ya amsa cikin kulawa Dukda ba wai ya sake bane, aka kirashi office akan ana neman shi sai kawai ya fice, ganin ya tafi Mum ma ta juya ta" fice babu wanda yayi masa bayanin ta ya ta ƙone. Ran Hibbah ya sake zuwa wuya ta kalleshi tana hawaye. """Har yaushe? Har yaushe za ka cigaba da kau da kai yarinyar nan tana cutuwa?""" "Kanshi dake wani irin sarawa ya dafe kan ya ɗago yana kallonta cikin rashin fahimta ""Tana cutuwa Hibbah? Ta yaya? Tsautsayi ne f...""" """Ganganci dai, na tabbatar babu Tsautsayin da zai sa Jasrah irin wannan kunan, bata da rawan" "kai bare biri biri don Allah ka buɗe idanunka for once ka san da wa kake tare""" Fuskarshi ya kame maganganunta sake ruɗa shi suke. """Me kike nufi ne kam? Kina nufin da gangan a cikin gidanmu za'a ƙonata haka? Haba Hibbah" "kar kuma ki juya kiyayyar da Mum tayi miki zuwa something else mana""" "Ɗan wara idanu tayi tana kallonshi, ranta ya fara ɓaci tace a ɗan zafafe." """Sai yaushe zaka fahimci Mum ba sonka take ba? Sai yaushe za ka fahimci ita ɗin lumbu lumbu" "ce wutar ƙaiƙayi? Ka san irin kuncin da yarinyar nan take ciki k...""" """Shut upp Hibbah!""" "Da tsawa ya katseta yana zare idanu, ta ja numfashi tana kallonshi sai kawai ya juya ya fice daga dakin da sauri." Kan Jasrah ta mayar da idanunta tana jin sabbin hawaye na sake zubo mata. "Wayanta ne ya shiga ringing, tana dubawa ta ga Ahmad ne." Ta Yi mamaki Dukda ba chan ba dai sai ta ɗaga suka gaisa ya ce """Jiya Matata ke ba ni labarin abin da ya faru hope matar chan bata sake ɗaga muku hankali ba ko""" Cikin karyewar murya tace """Ta sake Uncle Ahmad, Ya kasa fahimtar matar nan bata son shi yanzu haka fushi yayi daga ta zalunci Jasrah na yi magana, MB bashi da saurin fushi amma akan Mum yanzu sai ku yi fada ba tun yau ba na kula da hakan, Uncle Ahmad ya kasa gane bata kaunarshi bata ƙaunar ko ganinshi""" Murmushi Uncle Ahmad yayi daga ɓangaren shi ya ce """Alhamdulillah da kika riga kika santa Hibbah, na jima da gane duk inda aka matsa da takurawa MB akan ya fahimci matar nan bata kaunarshi tsanar wurin yake ya kauracewa wurin, anan Nassarawa duk ya zo aka zage ta gabanshi ya tafi kenan sai mu mun nemeshi ina ganin kaman ba haka kawai ta barshi ba, matar nan hatsabibiya ce Hibbah, Makira wacce ba zata taɓa gamawa da duniya lafiya ba""" Muryarshi da ya fara rawa ne ya sa yayi shiru. "Sai ta ji wani irin ƙwarin gwiwa, ta ji cewa duk makircinta sai ta kawo karshen ta, ba dai ta shigo" gidan ba? Komai mai sauki ne. """Uncle Ahmad dama duk kun san wannan kuka bari ya bar Jasrah wurinta? Yarinyar is depressed damuwa yayi mata yawa da kananun shekaru, ka ga irin kunar da ta samu? I'm very" "sure da gayya ta mata wannan muguntar""" """Na sani Hibbah ban kyauta ba amma ya zan yi? Mustapha ba zai taɓa yarda ya rabu da ita ba, soyayyar karya da munafunci na Mum ya rufe idanunshi yana ganin bashi da kamarta a faɗin duniya, na yi mamaki da duk umurnin da take bashi a kanki baya iya cikawa, Hibbah kin san Meyasa na dage aka ɗaura auren ku?""" Ta girgiza kai kaman tana gabanshi. """Da na yi bincike na gano a kanki ne aka ɗaure Mahir kuma da taimakon Musty, wlh wlh da wata ce daban da sai dai ta sa ya taimaki Mahir kuma zai taimakan ya wanke shi, baya taɓa tsallake maganarta aurensu da Anam rabi rigima ne akan Mum, har sakin ta ya taɓa yi saboda Mum amma a kanki na ga sauyi sossai a yadda yake karbar maganan ta shiyasa na san ke ce za ki warware mishi wannan matsala da yake ciki, don Allah ki taimaka mana""" "Ta lumshe ido tana barin hawayenta zuba, ko bai roketa ba ta dauri damarar kawo karshen" Mum a gidan. Sun tattauna sossai sai da ta ga tashin Jasrah kan ta katse ƙiran. "Dr ta ƙira ya zo ya duba ta ya ce za su iya tafiya amma za su na zuwa kullum a dubata har na kwana bakwai ana sake wanke ciwon, Hibbah tayi kuka har kanta ya sake fara ciwo zafin kuna kadan ma yaya babba yake ji bare 'yar yarinyar nan? Tayi Allah ya isa mata ya fi cikin chasbi, ko da ta fito ta dauka bai yi nisa ba amma sai bata ga motarshi ba." "Ta kira shi 3missed calls bai ɗauka ba sai kawai ta fito da jasran suka fita ta tare taxi suka wuce kai tsaye zuwa gida, har haraba ya shigo da su ta mishi transfer ta sauƙo da jasrahn sai ta kalli motarshi mamaki ya kamata barin ma da ta shiga ta ganshi zaune a parlor hannunshi biyu dafe" da kanshi wayanshi na gabanshi yana kallo kenan ya ga kiranta ya zaɓi ƙin ɗauka. Wuce shi tayi da Jasrah zuwa ɗakinta ta kwantar da ita ta kunna mata kallon cartoon a system ɗinta kan ta tambayeta me zata ci? Ta Yi mata alama bata gane ba sai Jasrah ta nuna mata hoton indomie da aka hasko a cartoon ɗin kai Hibbah ta gyaɗa ta fice daga ɗakin zuwa kitchen ya bi ta da kallo daga inda yake zaune. "Indomie ɗin ta dafawa Jasrah guda ɗaya da egg ta kai mata har ɗaki, da kanta ta shiga bata tana kallon cartoon har ta cinye ta sha ruwa da magani, Hibbah ta fice don ajiye plate ɗin tana" ajiyewa ta ji an rungumeta ta baya. "Idanu ta lumshe, suka yi shiru na seconds kan ta ji Muryarshi yana furta" """Hibbah help me! Kai na ya ƙulle I don't understand what's happening, I'm sorry if I crossed the" "line earlier""" "Wani irin tausayinshi ne ya rufeta, ko da gaske akwai sihiri a lamarin Mum ne? Juyowa tayi ta" riƙo hannunshi. """Kayi haƙuri for how I addressed Mum, ita ɗin ai uwa ce kuma zan je da kaina in bata haƙuri in" "kuma nemi yafiyarta kila ta yafe mana gabaɗaya"" Murmushi ne ya bayyana a fuskarshi sai ya rungumeta ""Da gaske za ki je?""" Cike da tausayinshi ta gyaɗa kai """Thank you so much Sugarplum, I love you""" "Ta riƙe riganshi kam tana runtse ido, ɗago fuskarta yayi yana kallo ko kan ta motsa ya haɗe bakinsu, bata hanashi ba sai ma gudumawa da ta bashi wurin sarkafo wuyanshi da hannunta" tana kusantashi da jikinta… 75 Sai da suka ji kafafunsu na neman kasa ɗaukar su kan ya tsagaita sai kawai ya shigar da ita jikinsa ya rungumeta tsamm ya lumshe ido yana jin yanda soyayyarta ke son hana numfashinsa fita. "Sun jima a haka kan ya saketa bata yarda sun hada ido ba ta zaga da sauri ta fice daga kitchen ɗin ya bita da kallo yana murmushi, yinin ranar gabaɗaya sun karar da shi ne a kula da Jasrah da kasancewar ta da Hibbah ya kwantar mata da hankali barin ma da hibban ta yi mata" alkawarin ta bar gidan Mum kenan bari na har Abada. A dabarance Hibbah ta so ta ji me ya faru daga wurin Jasrahn amma har lokacin tsoron Mum da barazanarta bai bar yarinyar ba don rawa jikinta ya fara Hibba ta shafa kanta tana yi mata adu'ar samun sauƙi da kuma Allah yayi mata sakayya don duk wanda ya san kunan wuta ya ga Jasrah sai ya tausaya mata. Abba ne ya kira Mustapha sai yake sanar da shi ai sun dawo gida Hibbah za ta cigaba da kula "da ita, ya ce a ba Hibbahn." Bayan ta karɓa suka gaisa ya ce """Za ki iya kula da ita kuwa Hibbatullahi? Daga tariya kuma an ɗora miki ɗawainiyar yarinya?""" Cikin ladabi ta ce """Ai babu komai Abba zan iya kula da ita in shaa Allah"" Ta Yi mamaki da ta ji yana saka mata albarka." "Shi kuwa ɓangaren shi bayan ya katse ƙiran ya ɗan zubawa titi idanu, shi bai ga wani aibun yarinyar nan da Hafsatu za ta ɗauki kiyayya ta ɗora mata ba, ya san sanadinta Mahir ya shiga prison amma da bai aikatan ba ai ba za'a daure shi ba, hakan ya sa shi bai wani mayar da" hankali akan maganganun Mum ɗin na ya tirsasa Mustapha sakinta ba. Ko da ya isa gida ya samu Mum ɗin tana shiryawa wai za ta duba Jasrah nan yake sanar mata "ai an sallamesu matar Mustapha ta tafi da ita gidansu, ta jima tana kallonshi da gyale a hannu kan ta juya kawai tayi ɗaki gudun aikata wani abin da zai tona mata asiri." "Da misalin karfe bakwai ya shigo ɗakin, tana ba Jasrah cereal da tace take son sha idanu ya" zuba musu yana kara jin soyayyar Hibbah na Huda mishi jini. """Sannu da ƙoƙari Starlight""" Tayi murmushi tana ɗan kallonshi """Sannu Daddy, ka dawo lafiya?""" "Yadda ta ƙira Daddyn ya sa ya jefa mata wani kallo sai tayi murmushi, kan Jasrah ya shafa" """Princess ya jikin?""" Ta mishi alama da hannu ɗaya wai da sauƙi. """Allah ya kara miki lafiya Princess ɗina""" "Karɓar sauran yayi ya bata da kanshi har ta shanye sai ya ɗauketa suka fita, ajiyar zuciya" "Hibbah ta sauƙe tare da Miƙewa ta cire kayan jikinta da shirin shiga wanka, towel ta ɗaura sai kuma wayanta ya fara ringing." Ko da ta duba Umma ce sun gaisa take bata hakurin rashin kiransu Jasrah ce ta ƙone duk bata natsu ba sun je lafiya? Ta amsa da lafiya ƙalau sun ɗan taɓa hira kan ta ba Daddy da Hibbah ta roka saboda jin muryarshi. """Daddynah""" """Mamana, kina lafiya?""" Ta shiga amsa mishi da Shagwaɓa sun ɗan jima suna magana shima kan suka yi sallama ta "kashe, sai ta kira mommy ma suka gaisa ta mata ban gajiya, ta kira Momma ma daga nan ta kira Aunty Asiya, ganin lokaci ya tafi ya sa ta shige toilet don wanka." "Karamin towel ne pink da iyakarshi rabin cinyar ta, ƙasan kitson ta da suka ɗan taɓa ruwa sun" "mammane mata a wuya Dukda ta yi amfani da hular wanka, damshi ne sossai a jikinta hakan" "ya sa ta tsaya gogewa da 'yar karamar towel sam bata zaci zai shigo a lokacin ba, hankalinta" na kan abin da take kawai ta ji motsin buɗe kofa da Shigowarshi. "Sai da ya kusa losing balance a sadda idanunshi suka sauƙa a kanta, zuciyarshi ya shiga bugawa da sauri sauri kaman yadda nata ya amsa da ƙarfi, a rikice ta fara waige waige ko za ta ga abin da zata rufe jikinta, sai ya saki murmushi ya nufeta idanunsa da suka yi laushi lokaci" guda ko sau daya basu bar kanta ba. "Baya baya take yi yana takowa wurinta yana bin kyakyawar surarta da wani irin fitinannen kallo, santala santalalan cinyoyinta da kenan fresh suke sheki sun fi komai ɗauke mishi hankali, a hankali ya kai idanun saman kirjinta da towel ɗin bai wani haura ba rabin su a waje ta saka hannu ɗaya ta kare, kan wuyanta ya kai sai ya sauƙe wani kalar numfashi daidai lokacin ta" harɗe saboda baya baya da take. "Cikin azama ya sanya hannunshi ta bayanta yayi wa kwankwasonta kyakyawar riƙo, idanunta da suka firfito saboda tsoro da taji suka shige cikin nashi da suka fara yin ciki ciki, slowly ya manna ta da ginin bayanta ya bi yana ɗora kirjinshi kan nata, goshinsu ya haɗe haka ma" hancinsu a hankali yake goga nashi kan nata. "Wani irin bugu da kirjinta ke yi yana jinshi har kan nasa kirjin hakan ke kara rikita natsuwarsa, ta sa tafin hannunta da nufin ture shi amma ko gezau sai ma wani lumshe idanu da yayi don tafin hannun nata mai sanyi akan budadden kirjinshi ya sauƙa, sanye yake da fararen pajamas" riga da wando masu yauki kuma rabin kirjinsa a waje yake. Ɗayan hannun ta sake kaiwa sai ya haɗa tiny hands ɗin nata ya ɗaga sama and pinned it gently above her head against the wall yana chusa fuskarshi tsakankanin wuyanta ya shiga sakar mata kisses masu zafi da ruɗarwa. Cikin wani salo yana shafa sajenshi a wuyanta numfashinsa na ƙara ƙarfi yana sauka a fatar ta yana buɗe duk wasu kofofin sha'awarta. "Bakinta ta buɗe za tayi magana but before she could utter any word, he claimed her lips in a kiss that was desperate, raw, and filled with a terrifying need, irin mayunwacin Kiss ɗin nan da ya gama da ita a lokaci guda, tana da lafiya kuma shekarun ta sun kai jikinta ya amshi irin wannan saƙon har ma ya wuce, hakan ya sa gabaɗaya jikinta ya ɗauki rawa." Sakin hannayenta yayi ya kai ɗaya kan towel ɗinta ya sunce shi ya zame nan ƙasa ɗayan hannun ya kai kan waist ɗinta ya sake mannota da jikinshi yana cigaba da kissing ɗinta. Wani mugun dogon numfashi ta fusgo wanda saura kaɗan ya ɗauke saboda wani lafiyayyan tabi daya kai wa ƙirjinta. zame wa take ƙoƙarin yi ya tallafota gabaɗaya suka tafi a haka tana ganqame da shi tana kuma ƙara runtse idanuwanta saboda masifaffiyar kunya. "A hankali ya kwantarda ita a gadon sai a lokacin ya raba bakinsu yana kai idanunsa kan lafiyayyun dukiyar fulaninta da suka gama tafiya da imaninshi, wani irin more wa kallonta yake a haka lafiyarshi na wani irin harbawa wanda rabon da ya ji hakan tun kan mutuwar Anam." "Wasu irin hawaye ne da bata san na menene ba suke zubo mata jikinta babu inda baya rawa, Gashinta ya shafo tareda Kai hancinsa ya shago qamshinsa ya lumshe idanu buƙatarsa na qara tsanantuwa, harshe ya sanya yana lashe hawayen cikin salon da ke ƙara haukatata, sai da ya tabbatar sun tsaya kan ya zura hannu rage hasken ɗakin, a hankali kuma ta ji sauƙar harshen inda bata yi zato ba lokaci ɗaya ya shiga fidda numfashi da ƙarfi da ƙarfi jikinsa na fara rawa" kaman yadda nata ke yi. "Daga nan ba zai iya cewa ga abin da ya faru ba don gabaɗaya ya rasa natsuwarsa, shi dai ya san a mintuna arba'in zuwa awa guda ya shiga wata irin duniyar da bai taɓa sanin akwai ta ba, kwakwalarsa ta kasa ɗaukar yanayin har bai san irin ɓaran-ɓaramar da yake yi ba, chan nesa yake jin kananun kukanta da magiyarta amma bai iya ya dakatar da kanshi ba sai da wata irin natsuwa ta zo mishi ya ƙanƙameta kaman zai tsagata biyu, chan wasu hawaye masu dumi suka" shiga sauƙa suna bin wuyanta zuwa kan katifar. "Daga shi har ita wani wahallallen bacci ne ya ɗauke su na mintuna talatin kan ta farka a ɗan firgice wanda hakan shima ya farkar da shi, da sauri ya miƙe ya janyo wandon pajamas ɗinshi ya saka tare da kunna hasken ɗakin sai da ya firgita ganin irin yanayin da take ciki Dukda haka ƙoƙari take ta ja duvet ta rufe jikinta dake waje, hawa gadon ya sake yi ya janyota jikinshi cikin" wata irin murya ya shiga furta. """I'm very sorry Sugar, I'm sorry. """ "Duk ya rikice kuma, kuka ta sakar mishi ya ƙara rudewa ba shiri ya sauƙa ya shiga toilet ya haɗa mata ruwa mai ɗan zafi, ya dawo ya ɗauketa ita da duvet ɗin gabaɗaya don ta ƙi sake wa idanunta kuma a runtse sai jinta tayi cikin ruwa, tsiririn kuka ta sake sakar mishi tana rike" hannunshi. "Kanta yake shafawa yana kara lallashinta, sai da suka yi ruwa uku kan yace tayi wanka don ta" matsa ya je waje. "Fitan yayi ya yaye beddings ɗin gabaɗaya ya nufi ɗakinshi a chan ya wanke, ya shanya wani irin tausayi da ƙaunarta na kara bin sassa na jikinsa, wanka yayi yana fitowa ya sake saka wasu pajamas ɗin amma yanzu guntun wando ne da riga duk ƙaurinsa a waje, ɗakin ya koma bata fito ba zuciyarshi ya ji yayi babu daaɗi kila ta kasa ne don ya ga jarumtarta da kokarinta, wani beedsheet ɗin ya shimfida kan ya nufi toilet ɗin kai tsaye tana kwance cikin ruwan sai dai ba kuka take yi ba, jin motsin shi bai sa ta buɗe idanu ba har ya ƙarasa kanta ya ɗagota chak ya fito da ita yayi wrapping ɗinta a towel ya saƙe ɗaukarta har kan gado garin gyara zama wani irin" zafi ya ratsa ta bata san ta yi kara ba. """Wayyoo Allahnaa""" """Sorry, sannu Allah yayi miki Albarta Zumata""" "Yake ta maimaitawa da kanshi ya saka mata rigar bacci ya hado mata tea da magani ya lallaɓa ta ta sha sai rigima take mishi yana lallashinta, daga karshe ya janyota cikin kirjinsa ya rungume" "tare da rage musu haske, a kunnenta ya dinga raɗa mata wasu irin kalamai da suka kara narkar" "da ita a soyayyarsa, Lallai ta dace ashe wani jinkirin alkhairi ne." "Da kyar bacci ya iya daukarsa, sonta har yayi mishi yawa a cikin kirjinsa gata jikinshi amma" "ƙaunarta ya fitine shi, farin ciki ya kasa barin shi idan ya tuna moment ɗinsu na ɗazu, lallai a yanzu Hibbah ita ce rayuwarsa ba zai iya haɗa soyayyarta da komai ba a rayuwarshi." "Asubar fari ya farka sai dai fa zafin jikinta ne ya farkar da shi zazzabi ne sossai ya rufeta, ya shiga damuwa sai sannu yake mata har suka sake wanka ya gasata sossai suka fito ya saka mata wani cotton riga suka yi sallah, a kan cinyar shi ya ɗora kanta yana cigiba da yi mata" sannu har ta ji kaman kulawar yayi mata yawa. "Yana ta shafa kanta har ta sake wani baccin don yayi yayi ta sha ko tea ne ta ƙi, daga nan ya kaita kan gado ya kwantar tare da kissing forehead ɗinta ya gyara mata blanket kan ya fice, ɗakin Jasrah ya je don dubata saboda ya san bata wani iya baccin ba daga asuba yayi zata" farka ya samu kuwa ta tashin tana kuka. "Ya je ya ɗan yi hugging nata yana rarrashi kaman ya tayata kukan yadda take ta maimaita mishi hannunta na raɗaɗi, wanka yayi mata ya saka mata kaya suka fito ya bata tea ta sha kan ya kwantar da ita jikinshi yana ta rarrashi bayan ta sha pain killer har ta sake wani baccin ya" kwantar da ita sai ya miƙe ya shiga kitchen. Ya jima yana tunanin me zai yi kan ya yanke yayi Pasta mai ruwa ruwa and bit spicy saboda zai "taimakawa Bakinta, cikin lokaci kankani ya haɗa sai yayi pepper soup kaɗan na kayan ciki ya haɗa mata tea ya ɗauka ya nufi ɗakin." "Ga mamakin shi ya samu ta fito wanka, ajiye tray ɗin yayi ya nufeta." """Sannu Sugarplum, wurin daina zafi?""" Ta ɗan Harare shi kaɗan da idanunta da suka yi laushi kwarai suka kuma kumbura tana kokarin cigaba da tafiyanta a hankali sai kawai ta ji ya rungumeta ta baya sautin murmushinshi na fita. """A yafe min kar in lalace Love, wallahi Sonki ne sanadi, You bewitched me body nd soul I" "love…love….love u hebbah""" "Ta lumshe idanu wasu irin hawayen farin ciki suka shiga sauƙa mata, ya juyo da ita ya lalace a share hawaye ganin zai sake ɗaukar wani hanya ta dakatar da shi tana ɗan kukan Shagwaɓa, a kan cinyarshi ya zaunar da ita yayi feeding nata har ta koshi kan itama ta shiga bashi don ta san" "rabonshi da abinci tun jiya da rana, Dukda ya sha tea da asuban amma yana jin yunwar shima." "Bayan sun gama ya shiryata tace tana so taje ta ga Jasrah suka fito a tare har parlor nan ya bar su ya tafi yayi wanka, cikin kananun kaya ya shirya lokaci lokaci sai ya saki murmushi, ko da ya tsaya kallon kanshi a madubi sai ya ga ya fita a angon shi tsaff sai annuri da haiba ke fita daga" fuskarshi… 76 "Kwantar da kanta yayi kan cinyarsa yayinda Jasrah ke zaune tsakar parlorn tana kallonta," kitsonta yake shafawa yana wasa da jelar gashinta ya ce Softly yana kallon lumsassun idanunta. """Sugarplum!""" Ta buɗe idanunta a hankali tana kallonshi. """Gist me""" "Ta ɗan juya idanunta a hankali ""About what?""" """Rayuwarki na baya, i want to know everything if possible""" "Cikin natsuwa yake maganar, idanunshi a kanta sai ta yunkura za ta miƙe zaune yayi amfani da ɗayan hannun ya mayar da ita yana kama hannunta." """Idan har za ki takura you don't have to""" Ta ɗora hannunta kan nashi da ke kan flat tummy ɗinta tare da ɗan murmushi kaɗan. """Babu wani abin armashi a past ɗina sai tarin raɗaɗi, zafi da kuma yadda soyayya ta zamar mini nauyi da baƙin ciki mai girma a maimakon farin ciki, Sagir shi ne namiji na farko da ya tarwatsa min rayuwa, mun haɗu da shi ne a wani bikin dinner na ɗiyar kawar Momma wanda da ita muka je bikin, a lokacin muna zana waec ne, akwai kuma wannan rawan kan da falli irin na balaga musamman ganin yadda yake nuna mini so da kulawa, kalaman kwantar da hankali da kuma zuzuta irin kyauna zuwa kyaun halitatta irin wannan yabo da za ka ji lallai lallai wannan yana sonka, shi ne saurayina na farko kuma ko Hudah da muke kwana ɗaki daya at First bata sanshi ba, sai daga baya da zan fita paper daga nan ya zo mu je wurin shakatawa da sauransu kullum tana nunamin babu kyau tunda su Daddy ba wai sun sanshi bane amma na ƙi sauraron ta" saboda a ganina soyayyar gaskiya Sagir yake yi min. "One faithful Night muna hira yadda muka saba yake sanar da ni bashi da lafiya in taimake shi, na shiga damuwa nake tambayar shi me zan iya yi mishi, ya ce in dauki hotunan kaina naked in tura masa, na nuna mishi cewa ba zan iya ba don ba tarbiya ta ba kenan, ya shiga yi min magiya ko hannuna fa bai taɓa rikewa ba sau daya dai ba zan taimake shi ba? Na nuna mishi gaskiya ba zan iya ba, ya dawo ko half naked ne in tura masa, kalamanshi suna karya min zuciya sai naga kaman ban kyauta ba idan ban tura mishi ba Dukda ban san ta ya hotona half" naked ko naked zai samar mishi waraka ba. "Na roƙi yayi min alkawarin babu wanda zai gani, yace ko view once ne in tura masa." "Na duba Hudah dake bacci na miƙe na shiga toilet har ga Allah a raina bana jin abin da zan yin daidai ne amma haka na dake daga ni sai bra and pant na ɗauki hotunan na tura masa different pose kuma view once, godiya yayi min tare da zuzuta irin son da yake min a lokacin duk a zatona komai ya wuce, daga nan ya ribaceni har nake ganin tura masan ba komai bane, sau" uku cikin different styles ina tura masa daga nan na yi alƙawarin ba zan sake ba don daga baya "damuwa na rufeni, ina jin kaman ban kyautawa iyayena ba." "Mun cigaba da soyayya da Sagir ko sau ɗaya bai tado min wani zance ba har na shiga jami'a ina second semester muka rabu saboda irin kalaman batsa da abubuwan da yake tura min na ji zuciyata ta tsane shi ba zan iya cigaba da irin soyayyar ba a lokacin ya nuna min ban isa ba, wallahi bayan saman kirjina da cinyoyina Sagir bai taɓa ganin ko ina na jikina ba ga mamakina ya turo min hotunana tsirara, na kadu iya kaɗuwa, Dukda na fahimci har da edit amma sassan jikina dake jiki nawa ne, duk wasu shaida na jikina sun fito har da videos cikin yanayi mai muni, hankalina ya tashi na kirashi don jin ba'asin menene hakan yace ko in cigaba da soyayya da shi" ko ya turawa duniya. "A lokacin ina tare da Mahmud kuma Hudah ma ta samu Mu'azzam har ma sun gabatar da kansu, hankalina ya tashi nayi ta roƙon shi kar yayi min haka ba ni kaɗai ba har siyasan mahaifina da ƙimar gidanmu zai zubar amma ya ƙi aminta, he manipulated me and then used that against me ya fara Blackmailing ɗina akan idan ban tura mishi kudi ba zai tona min asiri ya yada duniya su gani, na shiga yanayin da ba zan so kowa ya shige shi ba saboda na kasa faɗawa kowa duk wani abu nawa valuable nake dauka in sayar in bashi idan an matsa da tambaya zan ce ya ɓata ne ko an sace, kowa ya sanni da kazar kazar da rigima saboda bana barin ko ta kwana kuma duk inda na shiga an san Hibbah ta zo wurin amma a lokacin magana ma wahala yake min, ya kuntatamin ba na wasa ba a haka daga karshe ranar ɗaurin aurena da" Mahmud ya saki abin da suke kira update... "Mafarin wahalata kenan...""" Hawayen da suka bi gefen idanunta ya sa hannu ya share mata ba tare da ya ce komai ba. "Bayan shiru na seconds ta cigaba da bashi labarinta daga nan har karshe, ta yi shiru bayan ta" "gama bashi labarin komai har zuwa Shigowarshi rayuwarta, numfashi ta ɗan sauƙe mai nauyi." """Najeeb Allah ne ya kaddaro rabuwarmu amma Usaib ya cutar da ni fiye da sauran... Ba zan ce ban ji ina son Abdul kuma na ji cewa zan iya rayuwa da shi ba amma sanin husuma zai kasance tsakanin shi da ɗan uwanshi na zaɓi in sake rusa kaina in yi saving alaƙarsu na hakura" "da duk su biyun""" Shiru ya ɗan ɗauki lokaci. "Shi kuma bai yi gaggawar magana ba, idanunsa na a kanta cike da tausaya wa da kuma zurfin fahimta da yake da shi a kanta, a hankali ya cigaba da shafa kanta kan ya furta cikin natsuwa da sanyi." """Duk basu taɓa chanchantarki ba, ubangiji ni yayi wa tanadi shiyasa waenchan suke shigowa rayuwarki suke kuma fita tamkar almara ko lokaci da zai iya shudewa har labarin su ya zama tarihi, Hibbah ki daina kallon kanki a matsayin wacce aka taɓa cutar wa...ina so ki fara kallon" "kanki a matsayin wacce aka adana domin wanda zai riƙeki daidai...""" "Ta miƙe zaune tare da gimtse hannayenta cikin nashi, idanunta da suka cika da laushi na a" kanshi tace """ko ba'a faɗa min ba yanzu na san na zo wurin da na dace, tabbas na sameka ne a lokacin da na daina neman wani abu wai shi So ko farautar aure, lallai na yarda wani lokacin Allah na ɓoye alkhairi a cikin jinkiri, don kawai ya koyawa bawa yadda ake haƙuri da kuma tawakkali...""" Matso shi ta sake yi sai ya gyara gabaɗaya ya fuskance ta tare da haɗe goshinshi suna musayar numfashi a tare a tare. Slowly ta cigaba """Ban san yaushe zuciyata ta fara sabawa da kai ba.. Amma na sani duk ranar da ban ji muryarka ba zuciyata tana jin kamar wani abu ya bata ko na yi rashi mai girma da nauyi. Ba wai saboda na saba da kai kawai ba... a'a, saboda kai ne mutum ɗaya da yake sa na ji kamar ina da daraja a zuciyar wani." "Sau da yawa ina boye yadda nake jin ka... amma gaskiyar ɗaya ce i've fallen for you, because if love had levels, then whatever I felt for you had gone far beyond it, Idan har akwai wanda nake so ya kasance tare da ni daga nan har ƙarshen rayuwata to kai ne Almustapha... Ina sonka" "soyayyar da ban san adadin shi ba""" "Hawayen ne ya surnano mata, ta sake buɗe baki zata yi magana kawai ya haɗe bakin nasu ya shiga kissing ɗinta Softly cike da tarin ƙauna da soyayya, ita ce ta zame tana kallon inda Jasrah take sai suka ga ma ashe ta kwanta ta yi bacci surarta yayi ta zaro ido kan ta yi magana sun" dangana da ɗakinshi. Hannunshi ta riƙe tana girgiza kai """Da zafi wlh...""" """Shhhh ba za ki ji zafi ba... That was First time shiyasa yayi miki ciwo it won't hurt you any more...""" """I trust you""" Ta faɗa a hankali tana ƙoƙarin sallama mishi cikin murmuring ya furta """I don't trust myself when it's you sugar """ "Daga nan duk suka rikice ya sake kwasar romo, sai albarka yake saka mata tana mishi rigima don sai da yayi mata zafi saboda ma ya fi jimawa yanzu da na cikin dare, a haka dai suka yi wanka suka fito, da yamma aka kawo mishi Cook da ya nema daga best culinary school in" Lagos saboda ya san Hibbah ba wai tana son girki bane and ta ji daaɗin hakan. Soyayya suke zubawa ba kama hannun yaro suna kuma kula da Jasrah a tare har yarinyar ta fara sakewa kaman kowani ɗa. "Satin Hibbah biyu tana kwance a kan kirjinshi yana wasa da favorite ɗinshi ta ɗan kama hannunshi cikin Shagwaɓa take magiyar ya bari da kyar ya kyaleta, tana langwabe jikinshi ta ce ""Rouhy!""" Ya amsa a hankali """Yes Baby""" """Ina so mu kaiwa Mum ziyara, it has been 2weeks kenan bata neme mu ba na san tana kewar" "Jasrah gashi ta ji sauƙi ya kamata mu je""" "Numfashi ya sauƙe baya kwana biyu bai je ba, duk ta ƙi sauraronshi abin na cin shi a rai Dukda" yana kokarin ɓoye wa amma sarai Hibbah ta fahimci abin da ke faruwa shiyasa tane so ta fara yaƙar Mum ɗin ta karkashin kasa. """Kina ga ba komai Sugar?""" Tayi murmushi mai sauti """Uwa take fa gare mu ai idan bata neme mu ba mu ya kamata mu nemeta Rouhy""" Ya gamsu ya ce su shirya goben sai ya kai su tace A'a ya bari za su je su biyu su mata yini. "Kaman yadda suka yi da shi Washegari da wuri ta shirya shi ya tafi office saboda ita bata koma ba tukun a gida take nata aikin P.A ya ƙarasa saura akan sai ta yi three weeks, abinci ta saka Cook ɗinsu girkawa in bulk, party jollof Rice, pepper turkey sai small chops da zobo ta haɗa mata komai intact, Jasrah ta fara yi wa wanka ta shiryata tsaf cikin wasu pink floral dress" yarinyar ta yi kiba ta kara haske kan taje tayi wanka. Wani dakakken lace ta saka ɗinkin boubou gown ta saka hill da ya shiga da shi ta zuba accesories kan ta yafa medium vail ta ɗauki handbag ɗinta da car key ta fito. Hannun Jasrah ta riƙe har mota ta sakata kan ta zagaya ta shiga ta kunna ya ɗan yi warming ta ja ta fita daga gidan zuciyarta fesss Dukda ta san ba alkhairi zata tarar ba kuma itama ba sulhu ne ko zaman lafiya zai kaita ba. "Mum na zaune parlor duk abin duniya ya cukurkude mata, Abba ya ƙi bata goyon baya, Almustapha ya nuna mata ba zai iya rayuwa babu Hibbah ba don haka ba zai saketa ba kenan komai zai iya faruwa kaman yadda ya fara faruwa lokacin Aman da ta so rusa mata shirin shekara da shekaru, Dukda ta tsani Anam amma tsanar da tayiwa Hibbah ya ninka na Anam sau dubu, Anam bata rusa rayuwar kwallin ɗanta ba. Tana nan tana shawarar ko taje kwantagora ne? Sai ta shiga jiyo sallama, har ta fara amsawa ganin Hibba ce ta yi mugun haɗe" fuska tana yanke amsar. """Lafiya kika zo min gida?""" Ta faɗa fuskarta a ɗinke tana Miƙewa tsaye. Hibbah tayi murmushi """Haba Mum ai kya bari in zauna, yanzu laifi ne ɗiya ta zo gidan iyayenta?""" """Wacece ɗiyar? Allahu ya tsareni da haihuwar 'ya irinki, da in haifi irinki Hibbah gwara na yi" "ɓarin ɗan in san ban haife shi ba kwata kwata""" Hibbah tayi dariya sai ta ɗan taɓe baki """Ai dama ni ban zo duniya don in burge irinki ba hajjajo, amma fa ki tabbata na fi wasu daraja" "da hali ciki har da ke da kuma ɗan ki dake kulle a gidan kaso""" """Kuttt... Ni kike kokarin zagi har cikin gidana? Ke kin san wacece ni kuwa? Kina ganganci da" "rayuwarki na rantse da Allah...""" Murmushi Hibbah tayi """Ki bar damuwa da rayuwata ki fara da naki don ni Hibbah ni ce zan kawo ƙarshen zaluncinki, ki" "kalle ni da kyau ki kalli kwayar idanuna bana tsoro bare shakkarki""" """Lallai yaro bai san wuta ba sai ya taka... Har yanzu baki san wacece ni ba shiyasa kika samu bakin fitsara da rashin kunyarki irin na 'yan yau, wacce bata kalleni cikin ido ba ma na kawar da" "ita bare ke da kike maƙale a wuyana...""" Dukda kan Hibbah ya ɗan ɗaure amma ganin ta fara provoking ɗinta ya sa ta gyara tsayuwa. """Har fariya kike da zalunci da mugunta? Ko aka gayamiki ban san wacece ke ba? Zaluncin da" "kika yi wa yarinyar nan kina ganin Allah zai barki ki sha haka kawai ne?""" "Mum da idanunta suka rine suka yi jajazir ta matso gaban Hibbah kaman za ta kai mata shaka," Jasrah ta koma bayanta tana damke rigarta yayin da Hibbah ta gyara tsayuwarta. """Mum abinci ne fa na kawo miki da kuma gaisuwa matsayinki na mahaifiyarmu""" """Ke! Me kika sani a kaina? Har kina tunanin don kin fahimci ina zaluntar Jasrah wani abu ne cikin manyan muguntana? Yarinya ki bar wasa da wuta don ƙunana babu daaɗi, uwar da ta haifi shi mijin naki ma na ga karshenta, da Allah ya tashi sai ya haɗa ta da banzan namiji marar fahimta, tuggu na da kissa irin nawa nayi ta amfani da shi muka gasa ta daga ni har mijin da take tunanin ba zai iya rayuwa ba ita ba karshe baƙin cikinmu ne ya buga mata zuciya ta faɗi tayi ta aman baƙin jini har ta mutu... Ita uwar wannan da kike gani ganin ta shiga hancina dayawa har ta fara claiming dukiyar da na tanadar wa kaina na rainon Shegen mijin naki da ban taɓa so ko ƙauna ba na sa aka yi min wasa da abin hawanta ta mutu, na so ɗiyar ta bita amma shegiyar tsawon kwana ne da ita amma zamanta a gidan nan na tabbatar ta gwammaci mutuwa sau dubu saboda bakin da kika ga bata magana ba wai bata yi bane tsoro da shakkar irin" "zaluncina su suka hanata magana kuma ba zata taɓa yi ba idan ba ni na sakata ba""" "Ta cigaba da zazzaro idanu tana kara matso Hibbah tace ""Ke bari ki ji shi mijin naki a nan yake""" Ta Nuna tafin hannunta """Kina cigaba da aibatani gabanshi hakan tsanar shi dake zai cigaba da hauhawa don ni na raba shi da dangin uwarshi, yana ɗauka son shi ne da kaunarshi ya sa na riƙe shi ko ɗaya na so ya lalace ne ya tambade, sai kuma ya daukaka yayi arziki Dukda haka bai baci ba don dashi da arzikin duka nawa ne ina ga hakan ya isheki shiri don na ga kin firgice sai ki zaɓi ko barin gidan da rayuwarmu gabaɗaya ko kuma MUTUWARKI """ 77 "Tsaye yake daga wurin zaman Hibbahn da bata nan ya ɗan jingina da jikin desk ɗinta hannayensa a harɗe yana sauraron P.A dake mishi bayani akan wasu ƙarafun motoci, Vibration na wayanshi da ke aljihu ne ya sa ya zaro sunan da ya gani na My Priceless jewel dake yawo ya sa bai tsaya ma wani dogon nazari ba yayi picking fuskarshi na yaltuwa da murmushi sai dai" ya ji tana cewa. """Mum abinci ne fa na kawo miki da kuma gaisuwa matsayinki na mahaifiyarmu""" "Har ya zaci ma ko kuskuren ƙira tayi yana shirin kashewa ya sake ƙiran ta ya ji Mum na furta ""Ke! Me kika sani a kaina? Har kina tunanin don kin fahimci ina zaluntar Jasrah wani abu ne cikin manyan muguntana?...""" Shiru yayi zuciyarshi na wani irin dokawa da ƙarfin gaske kunnuwanshi na ji mishi bayanin Mum "na irin muguntar da tayi daga kan mahaifiyarshi, mahaifinshi, shi da kuma Anam zuwa Jasrah, yarinyar da bata san komai ba, yarinyar da bata da hakkin kowa a kanta..." "Tsabar yadda ya kaɗu kafafunshi rawa suka fara, a take ya nemi numfashi ya rasa yadda Ac ke kaɗawa a office ɗin shi wani irin gumi yake zubarwa, wayar ce ta zame a hannunshi ta faɗi a rikice P.A ya tare shi yana furta" """Innalillahi... Sir.! Boss lafiya??? Boss""" "Tuni ya kai ƙasa hannunshi ɗaya a kirjinshi yana wani irin fusgo numfashin da yake gudu, rasa wani irin taimako zai bashi yayi, inda Allah ya taimaka sai ga su Director da kuma Marketing manager da MB ɗin ya nemi zama da su da sauri suka fita da shi ganin da gaske rasa numfashin shi yake shirin yi, abin yayi strokking heart ɗinshi fiye da yadda kowa zai zata asibiti suka yi da shi emergency kusan duka hankalin ma'aikatan ya tashi saboda duk wanda ya" ganshi ba zai yi tunanin zai kai anjima da numfashi ba. "Ita kuwa Hibbah Dukda ta shiga cikin wani irin kaɗuwa saboda bata san muguntar Mum ɗin ya kai wannan level ba, bata san matar za ta iya aikata kisan kai ba idanunta sun juye sun rine tamkar garwashi, ranta ya zo mata wuya Mum na sauƙe aya ta shiga jin saukan maruka hagu da dama, maruka ne da bata bari ma ta gama jin zafin ɗaya zata sauƙe mata wani sai da ta mata shidda a jere Mum ɗin tayi baya baya ta zube kan Center table sai ya tarwatse tuni wasu glasses ɗin sun shishige mata jiki, da kyar ta iya buɗe idanunta tana kallon Hibbah a goma" goma... """Ke har kin isa ki kasheni?? Ke ɗin nan kaskantacciya, wulakantacciya har kin isa ki kasheni? Idan kin ga na mutu to wannan kwanana ne ya ƙare kuma ubangijina shi ke da ikon hakan ba ke ba, su ma da kika samu nasara a kansu lokacin su ne ya riga yayi ko da hannunki ko babu za su mutu... Wannan maruka da na miki kuma ba na komai bane illah na zaluntar Jasrah da kika yi, kuma wallahi yanzu kika fara girbar abin da kika shu...""" "Maganan Hibbah ya katse ne ganin Abba tsaye jikin kofar sashenshi, jingine yake da gini amma jikinshi rawa yake, idanunshi kuma wasu irin zafafan hawaye ne ke gangarowa lips ɗinshi na" "motsi amma babu abin da ke fita, Hibbah ta tsuguna ta ja Mum kan glasses da suka shishige" mata duwawu bata ko damu da ihun da take yi ba har cikin ɗakin dake kusa da ita ta watsa ta ta "zare keys ɗin ta fita ta rufeta ta baya kan ta nufi Abba da sauri, a lokacin ya zame ƙasa dabas.." """Abbaa! Abba...""" Numfashi yake saukewa da ƙarfi karfi """Innalillahi wainna ilaihi rajiun... Inna lillahi wainna ilaihi rajiun""" "Take ta nanata mishi da kyar ya amsa sau biyu da sauri ta miƙe tayi waje Jasrah na nan tsaye tana kuka itama jikinta na rawa, driver da mai gadi ta kira da gudu suka zo suka ɗauki Abban zuwa motanta, Jasrah ta ɗauka driver ya shiga bayan ta bashi key ɗin ya ja da gaggawa suka" fice zuwa asibiti. "Kasancewar Abban na da hawan jini dole asibitin da ya saba zuwa Driver yayi da su aka karɓe shi emergency, Hibbah hawaye ya rufe mata idanu tsabar yadda suke zuba, ba ihu ko kukan take yi ba hawaye kawai take na tsananin tausayi da damuwa haɗe da tsoron ɗan Adam, Mum" azzaluma ce na karshe da bata taɓa ganin irin ta ba. Tana tsaye tana ta gwada Layin MB da ba'a picking sai kuma hankalinta ya sake tashi. "Ta kirashi ne don ya ji komai da kunnenshi saboda ta san ko faɗa zata yi ba yarda zai yi ba, amma bata zaci zai ji har batun kisan mahaifiyarshi da matarshi ba, tana shirin fita ta nufi office" ɗin a rikice ta kusa cin karo da P.A """Madam...""" """P.A MB yana cikin wani hali..""" Ta faɗa tana kokarin wuce shi ya yi saurin tare ta """MB na cikin emergency Madam ya samu heart attack"" Saura kaɗan ta faɗi tayi karfin halin dafe gini ""Innalillahi wainna ilaihi rajiun...""" """Ki zauna Madam kar ki faɗi..""" "Ya faɗa tamkar zai tayata amma baya son taɓa ta, da kyar ta iya zama tana cigaba da ambaton" Allah hawayenta na ƙara gudu. "Layin Ahmad ta nema don ba zata iya ba kuma, yana picking ta sakar masa kuka cikin tashin hankali, yana gaban Baba Hussaini da su Uncle Muhammadu ne ya ga kiran ko da ya ɗaga yana ji tana kuka Miƙewa tsaye yayi yana tambayar me ya faru take irin wannan kukan?" """Almustapha ya samu heart attack, Abba ma ya suma duk muna Asibiti Uncle Ahmad""" """Innalillahi wainna ilaihi rajiun me ya same su? Garin yaya hakan ya faru?""" """Hafsatu.. Wanchan azzalumar Muguwar ita ce ta kashe Mammieyn MB da baƙin cikinta, ita ce ta kashe Anam ita kam ma wasa da birkin motar ta suka yi duk don ta gaje dukiyar MB, duk don ta kawar da kowa a rayuwarsu ta zama me moransu ita kaɗai""" Zamewa yayi zaune. "Hawaye ne ya shiga zuba mishi yana girgiza kai dama ya sani, abubuwa dayawa sun faru a kan idanunshi na yadda Abban MB ba ya mata uzuri, makirci dayawa Hafsatu ta yi wa Mammiey, sata, zubar da ciki, sharri iri iri har kan abinci bata tsira ba, ya zamana Hafsatu ce ke tsammusu abin da za su ci shi da Mammiey MB kuma ya sha nono, yana iya tuna kullum idan Abban MB ya tashi shi zai kai Hafsatu makaranta yaje ya ɗauko ta tun kan ma ya aureta, duk wani abu da zai saya wa Mammiey a Hafsatu na waje biyu yake saya sai Hafsatu ta zaɓa take ba Mammiey amma hakurinta yayi yawan da ko ɗaga ido bata yi ta kallesu, ranar da suka kai haƙurinta karshe ta mari Hafsatu a ranar Abban MB ya rama mata har da gyara, a ranar ne zai ce ya fara ganin kukan Mammiey akan abin da suke kunsa mata na baƙin ciki tayi kuka har tayi ciwo daga nan ne kirji ya matsa mata wanda wannan ciwo yayi ta matsa mata yana ƙaruwa da baƙin" cikinsu har ta rasu bayan ta fice hayyacinta baƙin jini yayi ta fita hanci da Bakinta. """Za mu zo yanzu ki daina wannan kukan Hibbah, in shaa Allahu karshenta ne ya zo za su samu lafiya""" "Ya faɗa a hankali yana katse ƙiran, su Bappa Hussaini ya faɗawa a take suka buga Airport" shatan jirgi suka yi mazan su wurin biyar suka nufi Lagos har da dattijon. "Har suka isa daga Abba har MB babu wanda ya farka amma likitoci sun fito daga kansu, kuma" sun yi fada akan duk munin abu a san yadda za'a dinga faɗawa mutum abu irin wannan ke kashe mutum farat ɗaya. Kuka Hibbah ke yi """Wallahi ban sani ba, ban san munin abin ya kai haka ba sai da ta fara fayyacewa da ba zan bari ya ji a irin haka ba, Abba kuma ban san yana gidan ba...""" """Ba laifinki bane ɗiyata, Allah zai basu lafiya ki kwantar da hankalinki""" Uncle Muhammadu ke fada cikin rarrashi don tunda ta basu labarin komai kowa ya kasa magana. "Jasrah na kwance jikinta ta yi kuka har ta yi bacci, kunan take kallo tana kara zubar da hawaye." "Har yamma liss wurin karfe biyar MB ya farka, tun da ya farka idanunshi ke kallon sama ya kasa motsi bare yayi wani tunani mai kyau, wani irin zafi ke mamaye kirjinshi yana haifar da ɗaci a kan harshenshi, idanunshi sun cika taff da kwallah yana ɗan tuna wani abu na mahaifiyarshi da duk ya manta, yana tuna Anam bata ji ba bata gani ba marainiya ya aureta bayan ya aureta uncle ɗinta da iyalan shi da take wurin su suka yi hatsari a jirgin ruwa duk suka mutu, ta bashi duk wani kulawa da soyayya ta kuma bashi Jasrah amma a karkashin shi ya kasa kareta har" aka kasheta bai sani ba tsawon wannan lokacin. "Duk yadda ya so daurewa ya kasa wasu irin zafafan hawaye ne ke zuba mishi nonstop tuni fuskarsa yayi jajir kasancewarsa fari musamman idanuwansa da sukai laushi sosai," Kallo 'ɗaya zakai Masa jikinka yayi tsananin sanyi Dukda MB ɗin namijin gaske ne mai tsananin dauriya da dakiya amma zuciyarsa ta kasa ɗaukar wannan. "Sheshekar kukansace ta fargar da Hibbah dake zaune a ɗakin kanta ƙasa mazan sun tafi su yi sallah saboda lokaci dake shigowa, ta kira Abdul ya tafi da Jasrah wurin matarshi don da ya sanar wa Mommy tace zata yi abinci ta same su asibitin ya kai Jasrah wurin matar shi, bata" faɗa musu komai ba kawai ta faɗawa Abdul ɗin ne MB ba lafiya... Kanshi ta yi tana kallonsa cikin tsananin tausayawa idanunta na cika da kwallah. "Zaune yake shirin Miƙewa ta taimaka mishi, tana zama ganganshi yayi masauki kan kirjinta ya ƙanƙameta yana barin kukan fita saboda ba zai iya dannewa ba, ta cigaba da shafa shi hawaye" na zuba mata itama. "Sai da ta tabbatar wani nauyi ya ragu a kirjinshi kan ta ɗago shi. ""Ka yi haƙuri Rouhy! Ka yi haƙuri haka Allah ya tsara tun farko..."" Kai ya gyaɗa mata bai yi magana ba." "Hannunshi ta kama ya sauko tana tallafe da shi har toilet ita ta taimaka mishi ya kama ruwa yayi alwala suka fito, kayan asibiti ne jikinshi don tun zuwanshi ma suka sauya mishi suite ɗin jikinshi da su blue riga da wando, kan sallaya ta taimaka mishi ya zauna saboda sallolin da ke kanshi" tun azahar. "Ya jima yana rama sallolin ko da ya zo sujuda yana so yayi Adu'a kasawa yayi don ya rasa wani irin Adu'a zai yi, kuka ya sake farawa yana tuna Jasrah, yana tuna irin alamu dayawa da yayi ta gani amma bai ɗago komai ba, ya tsinci kanshi yana yi mata Allah ya isa, yana adu'ar Allah ya rama mata daidai yadda aka yi mata, da kyar ya sallame Sallar a lokacin su Uncle Muhammadu" duk sun shigo. Ahmad ne ya tallafeshi suka koma gadon ya saka mishi pillow a bayanshi. """Ka yi haƙuri Musty..!""" """Meyasa baka faɗa min Mammiey wahala ta sha da matarchan ba? Kana da wayo na tabbatar ka san komai Meyasa ka barni da ita tana zaluntata da cin amanar yardar da nayi da ita na damƙa mata amanar Jasrah? Sau nawa ta azabtar da yarinyar nan? Sau nawa ta shayar da ita raɗaɗi na mugunta kala kala? Ahmad ka cutar da ni...""" "Hawaye ne suka sake fara zuba mishi kaman yadda Ahamd ma ke hawaye don kowa ya ga yadda yake sai ya mishi kuka, kuma dole zai ji ciwo musamman na Jasrah." """Ban sani ba ko asiri ne a jikinka amma Musty idan zaka min adalci sau nawa muna faɗa da kai akan matar nan? Sau nawa kana zagina ka ci min mutunci ka kore ni ka yanke mu'amala da ni duk a kanta? Kar ka manta danne zuciyata nake nake sake mu'amalantarka saboda na san ita" "ɗin shaidaniya ce amma kake ce min kare ya lashe zuciyata?""" "Duk ya tuna, duk yana tuna yadda suke kwaɓar shi da jan hankalinshi akan Mum don duk Ahmad ya sanar da su irin halayenta tunda ya ƙi zama a gabanta amma duk ya watsar da su, idan ba asiri ba kenan shi ne wawa kuma tolotolo da ya kasa gane abin da suka so ganar da shi? Kanshi yayi zafi ƙwarai...zuciyarshi da kaman zai fita ya dafe Bappa Hussaini ya tako ya zo" ya kama shi ya kwantar da shi. Adu'o'i yayi ta mishi tun yana rawar jiki har ya sake yin bacci. "Duk yadda suka yi da Hibbah ta tafi da Mommy in ya so gobe ta dawo ta ƙi, karshe Bappa" "Hussaini yace su barta kawai, Ahmad ya kwana wurin Abba su za su tafi masauki zuwa safe, cikinsu babu wanda ya tuna Mum da Hibbah ta rufe a ɗaki." "Bayan sun tafi Mommy ma da ta kawo musu abinci da wasu abubuwa da Hibbah tace tana so suka tafi da Abdul don dare yayi, ta je ta watsa ruwa a cikin bayin Asibitin da kaman a gida saboda tsafta da kawatuwarshi ta dawo ɗakin ta saka doguwar rigar bacci ta ɗora hijabi a kai kan ta daidaita Ac, gadon ta hau gangar shi ta kwanta tare da rungumeshi kam, a haka bacci ya" sureta. "Cikin dare ya farka ya sake rungumeta kamkam yana sauƙe numfashi, haka ya kwana har" "asuba idanunshi biyu babu abin da bai tuna ba, a karshe ya yankewa kanshi shawara. Hibbah na farkawa ta ɗago idanunta sai suka haɗa ido da shi, idanunshi sun kumbura kuma sun sauya kala har lokacin basu dawo daidai ba." """Sannu ka tashi?""" "Ido ya lumshe mata don baya son Magana, ta sauƙa ta taimaka mishi suka shiga tare suka fito da Alwala daga zaune yayi Sallar shi bayan ya idar ya karɓi wayanta ya shiga qur'an App ya fara karatu, ya jima yana karatu har gari yayi haske." "Bayan ya sgama yayi Adu'o'i tukuna ya shafa yana Miƙewa a hankali sai ga likitoci sun shigo, duba shi suka yi sossai yace su sallameshi shi kam ya warke suka ki tare da tabbatar mishi jinin shi ya hau kuma babu karfi a jikinshi dole a sake yi mishi karin ruwa, ruwan suka hada suka fita" sai ga Ahmad ya shigo suka gaisa da Hibbah. """Ya jikin Abba?""" "Sai a lokacin ya ji Abba ba lafiya, ido ya zubawa Ahmad dake cewa" """Har yanzu dai bai farka ba amma sun ce komai stable kuma zai iya farkawa anymoment yanzu su Yaya Muhammadu suna wurinshi""" "Zama yayi yana tambayar MB ya nashi jikin? Da ido ya amsa sai kawai suka ji an buɗe kofar, idanu suka mayar kai Abba ne ana tallafe shi, yana ganin MB ya nufe shi har yana faɗuwa ya zube tare da fashewa da kukan da sai da ya karya zuƙatansu duka" """Ka yafemin Mustapha...! Don Allah ka yafe min...""" 78 "Drip ɗin ya zare ya sauƙo bai damu da jinin da ya fara diga a ƙasa ba ya ɗago Abban ya rungumeshi, jin kukan mahaifin nashi ya dinga yi har cikin zuciyarshi, Hibbah ba zata iya jure" kallon scene ɗin ba kawai ta fice hawayenta na zuba. "Da kyar Abba yayi shiru sai dai ya kasa cewa komai, duk Yadda MB ya so ya koma ɗakinshi a cigaba da mai treatment ya ƙi yace shi gida yake son zuwa, yana so ya je ya ji me yayiwa matar nan ta zaɓi ɗaiɗaita mishi rayuwa, idan ya tuna irin kalaman bakinshi marasa kyau kan MB sai ya ji kaman ya kashe kanshi ya huta, godiyarshi ɗaya dayake MB bashi a hakkin shi gashi ya gina kanshi ba tare da shi a image ɗin ba, Almustapha yaro ne da baya iya tambayar shi ko biyar a yanzu kuma ya tabbatar Almustapha ya fi shi arziki, to me ya fi wannan sakayya a wurin" ubangiji? "MB ma cewa yayi su sallameshi babu amfanin zaman, babu yadda suka iya haka suka basu sallama Mommy da ta kawo abincin da zai ishesu duka itama ta bi bayansu da Zaitoon da ta" shigo itama gaishe su duk suka dunguma sai gidan Abba. Hibbah ce ta dauki jakanta ta fiddo key ɗin da ta cilla ciki taje ta buɗe kofan. "Mum na yashe ƙasa kaman kayan wanki, ta azabtu iya azabtuwa da kishi da yunwa gashi ta kasa tashi saboda fragments na gilasai da suka yi numbing kafafunta, da kyar take ja da rarrafe shima iya gwiwa take shiga bayi ta sha ruwa don hannayenta duk akwai broken glass, kuka tayi tayi daga karshe tana tuna cikin azabtarwar da tayiwa Jasrah har da yunwa, tana tuna har da rarrafe akan gwiwa sai gwiwowinta sun kasa ɗaukarta kuma, tana tuna hatta ruwan gora hanata sha tayi sai gashi ita mai shan ruwan goran ta ƙare da tare ruwan bayi tana sha, abin mamaki" duk azaban nan da take ciki ta kasa bacci. "Ta Yi kuka ta tsinewa Hibbah har ba adadi kan ta ji buduwar kofan, Hibbah ce babu shakka ko wani abu ta sake shiga ta nufi Mum da taji gabanta na dukan tara tara saboda wani irin tsoron hibban da ya rufeta, fusgota Hibbah tayi ta sake janyota tana ihu har tsakiyar parlorn ta wullar" "da ita, kuka ta saki tana kallon Abba." """Na tuba Alhj Bashir, na tuba wallahi na yi nadamar duk abubuwan da na aikata muku ku yafemin! Mustapha ka ya...""" """Don't you everr!! Kar ki ƙara ambatar sunana da wannan bakin naki... Allah ya isa tsakanina da" "ke Allah Ya isa Hafsatu""" Ya faɗa yana runtse idanunshi don Allah ne kadai zai iya yi mishi sakayyar da zai gamsheshi don ya san ba ya zalunci kuma shi ne Alkalin alkalai sannan karshen hukunci na a hannunshi. """Hafsatu don Allah ki faɗa min me Rabi'ah ta yi miki da ta chanchanci wannan sakayyar? Me muka yi miki Hafsatu?""" "Abba ya faɗa yana sake tsiyayar da hawaye lallai shi lusari ne da ya kasa kare martabar matarshi da ya karbi amana daga hannun dangin ta, yana tuna abubuwa dayawa da suka ta faruwa yana iya tuna irin kallon da Rabi'ah ke mishi na mamaki da roƙo at thesame time a lokacin baya, kallo mai laushi dake nuni da tsantsar mamaki da kaɗuwa na halayyar shi amma duk ya kasa taimakon ta ya kasa mayar da wannan yarda har ta mutu. Anya zai iya cigaba da" rayuwa? """Rabi'ah bata yi min komai ba, hasali ma ta ɗauke ni ne tamkar jininta, bata taɓa nuna mini wariya ko kyama na kasancewar mahaifiyarmu mai aiki ba ce gidansu, suturun da take sakawa shi take sa dole a sayamin nima, makarantar da taje wanda na tabbatar ko da duka albashin iyayena aka hada ba zai kai ni ba ta sa mahaifinta ya sakani, amma shaidan ya ribaci zuciyata a kanta, tun kan zuwan Bashir rayuwarta nake jin haushi da tsanarta ganin duk wani gata ta same shi amma ni ban samu ba, ko a makaranta dayawa sun zaci yan uwa muke amma ni na kan nuna cewa babu abin da ya hada mu kaman ni ce mai mata alfarma amma bata taɓa damuwa" ba. "Ko da na ga Bashir a matsayin wanda zai aureta a take na ɗora wa zuciyata shine daidai ni ba Rabi'ah ba, na kuduri aniyar zama matarshi ko ta wani hali, an yi aurensu da Rabi'ah ba tare da zuciyata na so ba amma na kasa faɗawa kowa kuduri na sai wata rana da muka je Kontagora da mamanmu, akwai ƙanwarta da suke da dangantakar nesa ta kama ni ina kuka take tambayata nan na gayamata komai, ita ta ɗora ni kan hanya ta kaini wurin wani malami akan zai taimakeni a karkata hankalin Bashir kaina, aiki ne authetic kuma ni na amince aka yi komai amma yace in samu hanyar kusantarsu nayi ta tunani kan na nemi admission legos Allah kuma ya sa na samu ko da na zo a shirye na zo, ban sha wahala sossai ba Saboda Bashir ba namiji bane da ya damu kwarai da ibada har chan, idan yayi sallah yayi Adu'a shikenan Rabi'ah ce dai" mai dagewa hakan ya sa duk wani asirin da na zo da shi bai kamata ba sai Bashir. "Na juyo da hankalinshi kaina har ya aureni muka hadu muka cigaba da kuntatawa Rabi'ah, wallahi na yi nadama Rabi'ah ta mutu da bakin cikina kuma bata yafemin ba... Ahmad na da wayo ya ki zama wurina ya tafi da farko ban so riƙe Mustapha ba amma sanin idan ya tafi wurin 'yan uwan mamanshi zai samu gata da kulawa haka kuma ko yau Bashir ya mutu Almustapha sai ya fi ni gado gashi ban san me zan haifa ba sai na ƙira Antina taje min wurin malamin nan" da tunda ya min aiki akan Bashir bai taɓa karyewa ba. "Shi ya sanyawa Almustapha soyayya ta da ƙin duk wanda zai iya bakanta min ko ya aibata ni, makarin asirin kuma shine ya ji gaskiya daga bakina, a gefe ɗaya nayi amfani da kissa ina nunawa Babansu ina son shi amma halayenshi ba mai kyau bane, tunda yake magana mai daaɗi bai taɓa haɗa su ba sai cin mutunci, muna nan a haka blindly ya zaci bashi da kamata kwatsam ya zo da batun auren Anam, ban ki ba aka yi aure sai dai na kula dukiyar shi habaka yake har yana so ya fi baban sai hankalina ya koma kai na tura Mahir ya saka min ido akan duk wani motsin shi, anan ya fahimci Anam da kuma Jasrah za su iya yi min kafar baya, wata rana Anam ta kawo min abinci ta riski maganganuna kan Almustapha ta girgiza, na so ta ba ni haɗin kai mu ci arziki tare ta ƙi, a lokacin na kira Antina sai na samu labarin rasuwarta a hatsarin mota bayan ta ci azabar jinya, na taka na je Kontagora ban samu malamin dake min aiki ba kuma" dama na yanke alaka da duka yayyena don basu bani goyon bayan abin da duk na aikata ba. "Bayan na dawo na rasa yadda zan yi da Anam kar ta tona min asiri shawarar kasheta ne kawai ya zo min na yi hayan wasu thugs suka kunce mata birki ta je ɗauko Jasrah makaranta suka yi hatsari, Almustapha baya nan ni na je kansu sai dai dariya nayi a asibitin ina maimaita tugguna sai hada ido muka yi da Jasrah, yarinya ce mai wayau da basira a take na yi mata mummunan" barazana da wuka a wuyanta na tabbatar mata ta sake tayi magana da kowa sai na kashe "babanta a gabanta yadda uwarta ta mutu ba zata sake dawowa ba, ta firgita daga ranar ko ni" bata sake yi wa magana ba bare wani. "Ko da Almustapha ya bani ita babu irin abin da ban yi mata ba, ruwan zafin nan ma ni na watsa mata saboda bakin cikin auro Hibbah da Almustapha yayi sanin cewa ita ɗin za ta min wahalar sha'ani na kuma tsane ta ne saboda sanadinta Mahir yake cikin masifa. Waiiiii wayyoooooo" "Wayyoooooo na shiga uku. """ Ihunta ya katse labarin cikin azaba don kafarta ɗaya Hibbah da ba wanda ya san ma ta tashi ta kama ta tsunbula a tafasashen ruwa tana hawaye tace """Ki ji irin raɗaɗin da Jasrah ta ji na azabar wuta, gwara ma kuma ki saba don tabbas wutan" "Allah shine makomarki Makira azzaluma...""" "Almustapha ne ya miƙe yana jiri ya kamota sai ta fashe da kuka, wace irin macece wannan?" "Kuka take har jikinta na rawa wasu mutanen mugaye ne na bugawa a jarida, wannan matar anya ba shaidan ba ce a siffar ɗan Adam?" "Kusan kowa sai da yayi hawaye, Mommy dai ta kasa magana don kaɗuwa so mutum na iya" zama this wicked? A yi maka rana ka yi wa mutum dare. Baba Hussaini ya ce """Ita Rabi'ah da kuma Anam duk kwanansu ne ya ƙare babu mai shari'ah da ke akan hakan, za mu barki da ubangijinmu shi ya san irin hukuncin da zai miki ko a haka kuma kin ga sakayya don shi Almustapha da kika so ya lalace ya kasa albarka kin ga ya zama kafin Allah, ya tara nagarta, ilimi, dukiya da kuma iyali wanda ɗan cikinki bai samu ko guda ba hakan kaɗai ya" "isheki ishara, hakkin yarinyar da kika dauka duk ke da Allah...""" Abba dake kuka yace """Allah ya isa tsakanina da ke Hafsatu! Allah ya isa... Ki fitar min daga gida yanzu tun ban sauya miki kamanni ba...""" Nuna mata kofa yake akan ta fita don ta gama cutar da shi shi kam a rayuwa. "Ta buɗe baki da nufin magana sai dai ya ƙi fita, ta sake yunkurin hakan sai iska ke fita, a kidime ta kama wuyanta kaman me shirin gyara wani abu da ya karye ciki sai dai ko alama babu abin da ya sauya kallon su take amma babu mai digon tausayinta cikinsu." "Ta fara firgici, ta rikice... hannunta yana rawa, tana nuna baki kamar zata tilasta kalma fito wa Amma shiru kake ji wai an shuka dusa, irin shiru da ta daura wa Jasrah, irin shirun da ta ɗora" wa Anam na dole ta shafeta a bayan kasa don kar ta yi magana. Abba ya miƙe ya kira masu aikinsu yace su ja ta cillar waje ko da wasa ya ganta kusa da gidan duk ya koresu haka suka ja ta kaman kayan wanki suka yi waje da ita tana ihu. Nasiha sossai Baba Hussaini yayi musu ya kuma tabbatar Almustapha ya yafe wa mahaifinshi ya roki Abban da kar ya sa damuwa a ranshi idan ya ji damuwa ya fuskanci ubangiji shima ba laifinshi ba ne. "Bayan dogon nasiha suka tarkata suka tafi, Abba ya shige sashenshi Mommy da Zaitoon suka yi gidanta don Hibbah ta ce Jasrah ta zauna wurinta na kwana biyu Dukda Kaman Almustaphan bai amince ba yana son ganin yarinyar amma zuciyarshi ta riga ta karye he failed matsayinshi" na uba ya yi failing ɗinta. "Hibbah ce ta kamashi zuwa motanta ta ja suka nufi gida, har suka je gida bai ko buɗe idanu ba ko da tayi parking fita kawai yayi ya nufi ciki zuwa ɗakinshi ta jima tsaye parlor kan ta nufi ɗakinta tayi wanka ta saka riga marar nauyi ta fita kitchen ta duba abu mai ruwa ruwa ta haɗa ta kai mishi har ɗaki, yayi wanka yana kwance kawai da kyar ta samu har da kuka ta mishi ya ci" wani abu kaɗan ta fitar da kwanukan bayan ya sha magani sai bacci ya ɗaukeshi. "Har yamma tana kula da shi, kukan da take yawan yi har idanunta sun sauya kanta kuma yake" ta ciwo amma tana dauriya saboda shi. "Ya idar da isha ya zare farar jallabiyar ya bar iya wandon cotton mai taushi ya zauna daga bakin gado gwiwowin hannunshi daure a kan cinyarshi ya dunkule yatsun ya ɗora haɓarshi a kai, chan ya zame ya tallafi bayan wuyanshi da hannu biyun idanunshi a sama babu irin tunanin da bai yi ba, yana nan zaune lost in thought wutar dim light ce kawai ke ɗan haske ɗakin ƙadan" kadan. "The door cracked open, bai juya ba at First amma yana iya jin presence ɗinta tun ma kafin ya tabbatar da ita ɗin ce ta shigo, sassanyar turarenta, takunta cikin natsuwa su suka cigaba da" ratsa shi har ta iso dab da shi. """Baka yi bacci ba?""" Ta faɗa Softly don da yamma ya ci abinci kuma ya ce kar ta shigo daga ya yi isha zai yi bacci. "Maganan ta ya sa ya ɗago idanunsa da suka yi matukar laushi ya zuba mata, and for a second komai ya tsaya mishi chak, menene laifinta ita? Me tayi da ta chanchanci shearing damuwar shi da ita? Idanunta na nuna gajiya da kuma yawan kuka, tana mishi kallo ne na tausayi ba na neman wani abu ba kayan jikinta ya kalla ta saka na bacci amma freely ba wai don ta burgeshi" ba kawai ya zamar mata kaman dole ne tabbatar da lafiyarshi. "Shin ya kyautu kenan idan yayi mata hakan? A yanzu ita ce bangonshi, ita ce gabanshi da bayanshi a wurinta kaɗai yake da tabbacin samun salama." Ya sauƙe numfashi a hankali wanda bai san ma ya riƙe ba. """Hibbah... I'm sorry you didn't have to go through all this...""" Ta katse shi """I know! Amma babu yadda na iya saboda duk abin da ya shafeku kai da Abba da Jasrah nima ya shafeni Rouhy""" "Shiru ne ya ratsa tsakaninsu na mintuna, ta miƙa hannunta ta ɗora kan kafaɗarshi ya ɗan lumshe idanu ya buɗe ta ce a hankali cikin taushi" """Na san you have been carrying so much on your mind...""" "Ya katse ta with faint smile ""I'm fine Hibbah""" Ta ɗan runtse ido ta buɗe Sai ta sake matsawa kusa da shi ta sauƙar da hannunta daga kafaɗarshi zuwa cikin tafin hannunshi ta gimtse. "Sai kawai ya zame ya kwantar da kanshi kan kafaɗarta tayi baya ta jingina da pillow tana barinshi ya rungumeta itama ta sa hannu ta zagaye shi, tana jin nunfashinshi a jikinta a hankali yace" """I'm sorry I don't have to let this affect us""" "Tana shafa gashin shi zuwa sajenshi tayi wa kanshi peck tana kara rungumeshi a kirjinta tace ""Na sani, you are doing ur best to hold it but ka san bai kamata ba ko? You don't have to hide it from me""" Ya ƙanƙameta yana jin dole ya kawar da wannan damuwar don farin cikinsu a hankali ya furta """Ke ce rayuwata Starlight, ke ce farin cikina""" "Ta ɗago kanshi ta haɗe lips ɗinsu ta shiga tsotsa a hankali tana bin duk wani hanya da ta san za ta rage mishi wani abin ta ɓangaren ta, ta yi nasara don irin gudumawar da ta bashi bata taɓa bashi irinsa ba, sai da ya samu cikakken natsuwa ya sake kankameta yana jin yadda sonta" ke son hana numfashinsa fita… 79 "Safiyar Washegari ya tashi kaman babu abin da ke damunshi saboda ya yiwa kanshi alƙawarin binne koma menene Mum ta yi mishi, ko don saboda Hibbah, ba zai iya cigaba da ɗora mata pressure na damuwanshi ba kuma ko ba don hakan ba ma ya riga ya ci alwashin ƙin barin abin da Mum tayi ya taɓa shi don hakan ne zai cika burin ta na ganin ya rasa farin ciki da walwala don haka ya tattareta da duk abin da tayi musu ya watsa gefe, ya tabbatar karma is very real" kuma sai ya ci ta. "Yana tsaye yana ɗaura baƙar agogon fatanshi don sanye yake da wasu expensive Suit Black, ya saka White shirt a ciki ya ɗaura necktie ɗinshi ma Black da touches na White, ba karamin kyau yayi ba barin ma 'yar rama da yayi ya kara fitar da tsawon hancinshi lumsassun idanunshi" sun ɗan zurma ta yadda suka kara mishi wani kyau na musamman. Wani Black well polished shoe ya saka a ƙarshe kan ya juya da niyyar fita bayan ya kwashi Phones ɗinshi daidai lokacin aka turo kofan aka shigo. "Tsaye yayi da idanunsa kanta, tana sanye da wani ankara gown ne but straight cut, tsakiyar akwai roba da aka yi styling ɗinshi ya ɗan tattare kaɗan, rigar bai rufe sawayenta dake sanye da wasu nude Heels ba, ta saka scarf da ya tafi da takalmi da jakanta ya kuma rufe wuyanta don" rigan dogon hannu gareshi. "Kawar da mamakin shi yayi yace Softly ""Babe sai ina?""" Ta shigo ciki shima ya nufeta har suka haɗe ta sa hannu ta zagaye bayanshi kaman yadda ya "riƙo waist ɗinta ta ɗan karya wuya cikin tsiririyar murya tace ""office mana rouhy..""" Yayi mata wani narkakken kallo yana bin lip ɗinta da lip gloss kawai ta saka da kallo yace cikin raɗa da muryar tsokana. """Aikin da aka watsar min aka ce ba'a yi?""" "Ta ɗan binne kanta a kirjinsa tana ɗan kai masa duka cikin tsantsar Shagwaɓa take cewa ""Babeee Stop pls""" Yana kwaikwayon muryarta yace """Uhm uhmmmm hayatee ni da aka ce an tsaneni ba'a so na, ba'a son gani n...""" Ta fara bubbuga kafa yana dariya mai sauti yace """Shikenan sorry na bari, sorry My Sugarplum. But ai baki cinye hutun amarcin ba!""" Ta riƙe hannunshi suka nufi kofa tana cewa """Ai tunda ka gama na gama, haka kawai in zo ina sake da baki wata ta yi min wufff da kai""" Yayi dariya """Daga ke sai ke Sugarplum, daga ke babu ƙari.""" She shook off her head irin na ji whatever ɗin nan. "Motanshi suka shiga sai da ya buɗe mata ya zagaya ya shiga, ya kunna tare da adu'a a tare" suka fice daga gidan. "Yayi nisa da driving sai dai yana jin idanunta kanshi, murmushi ya ɗan saki yana cigaba da tuki" "bai ce komai ba sai da ya ji ba zai iya shiru ba kan ya ɗan waigo ya kalleta, duk ta juya bayanta na jingine da kofa ta zuba mishi idanu tana kallo." """Sugar... Kina so mu yi hatsari ko? Why are you looking at me like that??""" Ta sa hannu ta kama haɓarta unexpected tace """I can't help it ne Rouhy.. I'm looking at My tall, handsome and charming husband. The love of my soul... my forever..""" "Saura kaɗan ya bugi wani mota ya koma gefe yayi parking ta saki wani irin dariya da ya shagaltar da shi, lips ɗinshi ya kama yana tsotsa yana aika mata wani irin kallo na burgewa ita" kuma tana dariyar ta hannunta ɗaya a baki. """let me always see you laugh Sugar, Its my favorite thing in the world...""" Idanunta na cike da wani irin ƙauna take kallonshi tana sake murmushi. "Kunna motar ya sake yi suka nufi office tana cigaba da teasing ɗinshi yana dariya, ta ji daaɗi da ya mayar da komai ba komai ba, da karsashi ya shiga companyn hannayensu a sarƙe cikin na juna suna 'yar hira duk wanda ya gansu sai sun burge shi, ana ta miƙa musu gaisuwa a tare har" "office ɗinta, sai da ta raka shi ya zauna kan ta dawo nata." Aikin da ba'a yi shi cikakke ba kenan saboda ya kasa zama sanin tana dab da shi baya ganinta karshe office nashi ta dawo kan couch tana aiki yana nashi yana kallonta. "Da azahar shi ya tsayar da ita ya je yayi sallah itama ta yi, abinci da yayi order aka kawo musu shi yayi feeding nata har ta ce ta koshi itama ta karɓa ta yi feeding ɗinshi, bayan sun gama ta miƙe zata koma wurin aikinta ya riƙo kugunta a bazata yana ɗora ta saman cinyarsa tare a" zagaye ta da hannayenshi yana chusa kanshi cikin wuyanta yana shakar kamshinta. """Rouhy aiki faaa""" """yayi hakuri ya bar ni nayi enjoying matata""" "Tayi dariya tana shafa hannayenshi dake kan cikinta. ""Rouhy!""" Ya amsa chan ƙasa saboda kamshinta duk ya saukar masa da kasala. """Uhmm""" """Na yi wa Jasrah booking na appointment da wata physiotherapist and we need to visit her to night""" Ɗagowa yayi yana juyo da ita akan kafafun nashi suka fuskanci juna hannayenshi rike da kwankwasonta. """really? Dama abin da ke raina kenan""" "Ta ɗan ja hancinshi kaɗan ""Mamanta ta riga ka""" "Ya ɗora goshinshi kan nata yana goga hancinsu idanunshi a lumshe ya ce ""Than...""" "Bata bari ya ƙarasa ba ta kama lips ɗinshi ta shiga kissing, ya saki kwankwasonta ya dawo da" hannun kan fuskarta yana bata full support ganin yana shirin sakin layi ta tashi da sauri tana dariya ya jinginu da kujerar yana hararinta ta koma nata ta cigaba da aikinta tana mishi gwalo. "Tun daga sannan kasala ya hana shi aikin sai kallonta kawai da yake yana jin sonta na ƙarasa bin duk wani sassa na jikinsa, ƙarfe biyu client ɗinshi na karshe a ranar ta ƙaraso Hibbah ce ta fita ta shigo da ita, tun da ta ganta taji kawai bata son matar ta keɓe mata da miji amma haka ta" danne suka gaisa ta yi mata iso har office nashi. "Ya bar asalin seat ɗinshi ya dawo mini table ɗinshi na ganin private clients irin ta haka, tana shigowa ya ɗan miƙe tsaye yana welcoming ɗinta cikin policyn aiki da baƙon ka, ta saki" murmushi tana miƙa masa hannu. "Hannun Hibbah ta bi da kallo kan ta ɗauke kai ta mayar kanshi, yi yayi kaman bai gani ba ya zauna yana ce mata" """Please have a seat""" "Hibbah na daga tsaye tana kallon matar da a shekaru za ta iya girman hibban amma ba za ta kai MB ɗin ba, daga ganinta ka ga wayayyiya kuma irin 'yan duniyan nan waenda suka goge a" harkar kasuwanci suna ganin komai ba komai ba. Kujeran ta ta ja kusa da shi kaɗan tana leƙan abin da yake na buɗe proposal ɗinta da Hibbah ta haɗa a ranar. Hibbah bata je wurin su ba sai zama da ta yi kan kujera tana harɗe kafafu amma duka hankalinta na kansu. Bayani yake yi mata amma hankalinta ya bar kan aikinta ya koma kanshi sai wani kallo take mishi tana sosa gefen wuyanta da biro. """You are really charming MB MUSTAPHA, You know that?""" Tayi breaking awkwardness ɗin her eyes lingered not professional but interested. "Har ga Allah zuciyarshi sai da ya amsa na shakkar Hibbah, ya ɗago yana kallon ɓangaren da" "Hibbah take zaune yi ta yi kaman bata kallonsu amma ranta ya zo har wuya, ya sauƙe numfashi" """You have to focus on this idan har kina so mu gama komai a yau har ki juya""" Tayi murmushi tana crossing legs ɗinta """I don't mind kai wa har wani sati anan idan har da kai zan yi discussing business, I must say Its rare to see a CEO this composed under pressure.. Ko akwai wani abin ne bayan aiki you Look" "somehow""" "Unlike other Men yayi ƙoƙarin kame fuskanshi, babu dariya ko wasa a lamarinshi" """Composure is part of my job Miss Hayat""" "Yayi replying in steady voice don ya riga ya saba dealing da irin su, wasu matan kaman Mayu" daga sun sauƙe idanu kanshi sun zama mishi fitina kenan. """Then i will make sure komai ya tafi daidai, What did you say was ur suggestion?""" Tana maganan tana ƙara matsawa kusa da shi. Hibbah bata san ta dukunkune papers ɗin hannunta ba tana danne hakwaranta saboda yadda ranta ya zo mata wuya. "Yana sake yi mata bayani amma hankalinta duk ba ya kanshi, hannu ya sa ya bugi desk ɗin ""Can you focus for just a moment please""" Fuska a tsananin kame yayi maganan a lokacin bai da ma ƙwarin gwiwar daga kai ya kalli Hibbah ya san ta gama zuwa makogoro kuma yana da aiki a gabanshi na rarrashi. """What about outside work?"" Tana 'yar murmushi tace cikin mamaki" """Are you always this disciplined?""" "Shiru ne ya ratsa a yanzu, he is just choosing retraint saboda Hibbah da ke wurin. Za Ta sake magana suka ji takun tsinin takalman Hibbah, bata san ta miƙe ba ita karan kanta kawai ta ga ta nufi inda suke ne, babu hayaniya sai tsantsar natsuwa yadda ta kame fuska sai da ya sha jinin" jikinsa. Gangarshi sossai ta isa ta ɗayan gefen ta ajiye tablet da ke hannunta tana ɗora hannayenta kan table ɗin shiruu kan ta ɗago ta kalli matar. """Miss Hayat or whatsoever can you please step out?""" Calmly tayi maganan amma ranta tafasa yake saboda ita ɗin ba lusara ba ce da zata koma tana kallo wata na flirting mijinta ba. Da mamaki take kallon authority ɗin Hibbahn. Sai ta fahimci idanunta sun sauya sossai. """As the secretary??""" "Hibbah tayi murmushi tana Miƙewa tsaye ta harɗe hannayenta a kirji. ""As his Wife... I thought you are here to discuss business?""" Ta ƙoƙarin danne Muryarta """If you are here for something else then you are in a wrong office... Za ki iya tafiya""" "Shiru office ɗin ya ɗauka bai ce komai ba sai kallon Hibbah da yake a hankali ya miƙa hannunshi ya ɗora kan nata da ta mayar kan table ɗin, a hankali cikin natsuwa da kauna ya ce ""Relax mana baby! I'm yours""" "Ta tattare girarta wuri guda, Matar ta miƙe ta ɗauki handbag ɗinta kawai ta fice jin abin da ya" fada kenan tabbas matarshi ce. "Tana fita Hibbah ta zame hannunta ta nufi waje cikin sauri, bata yi nisa ba ta ji Muryarshi." """Hibbah! Come here.""" Calm and low. "Ta tsaya for a second kan ta waigo ta kalleshi idanunta har lokacin sun yi wani iri, ya miƙe tsaye" yana sassauta ɗaurin necktie ɗinshi a lokaci ɗaya yana zame jacket ɗin don wani zafi da yaji yana ji Dukda Ac da ke aiki. "His eyes locked on her. ""Ina da aiki""" Ta faɗa tana juyawa don ficewa ta ji Muryarshi ya katseta """You're my work right now""" "Ta ɗan riƙe numfashinta cikin jin haushi, ko sugar ɗin ba ya cewa bare Sugarplum ko Hayatee. ""Ba ni da lokacin wannan""" Ta faɗa tana kokarin ficewa taku uku mai kyau yayi ya mannu da kofar yana facing ɗinta idanunshi duk a kanta. """Da gaske? Da gaske ba ki da lokacina?""" Ta ƙara haɗe fuska """Ko dama na hanaka rawan gaban hantsi ne? Na takura ku ko?"" There it was wannan kishin mai zafi sai lokacin ya bayyana." Fuskarshi ya ɗan kame yana kallonta da mamaki kadan. Ya matso sossai he then leaned """You know me better than that Hibbah""" Ta ɗan zaro ido tana jin haushin kiranta da Hibbah da yake sai ta kawar da idanun. """Na dai san abin da idanuna suka gani""" Ya janyota sai ta kauce tayi baya tana mannu wa da gini ya yi mata rumfa yana kallonta murya chan ƙasa ya ce """and what did you see?""" Ta kawar da idanunta da suka cika da kwallah ta ce kaman za ta fashe da kuka """I saw a woman forgetting boundaries""" Muryarta na rawa ta ƙara da """Kai kuma kana zaune kawai watching her tana so ta lalata min kai""" Duk yadda ya so ya danne dariyar da ya taso mishi ya kasa he smiled yana chusa hannunshi ɗaya cikin gashin kanshi. """I was handling it Sugar...""" """Ko kuma kana jin daaɗi ba... You didn't Stop her!""" """Hibbah I was handling everything nan fa office ne, ita ɗin client ɗina ce ta ya a gabanki zan bari ta tsallake boundaries ɗinta?""" Idanunshi cikin nata ya sake ƙasa da murya yana kai hannu ya riƙo nata. """I'm your husband... And i don't cross lines, i wouldn't dare to do so Sugar... Not for anyone a wannan duniyar...""" "Her heart skipped, hawayenta ya gangaro." Ta zame hannunta ta share ta ɗan ja numfashi kan ta sake kallonshi """I know! Kawai dai..."" ""Is ok""" Ya faɗa Softly. """Kawai dai next time you don't have to intervene""" "Tana kallonshi tace ""Saboda?""" Muryarshi cikin tabbatarwa ya ce """Saboda dole kowa zai sani muddin yayi approching ɗina that I'm not available...""" Ta riƙe idanunshi cikin nata tamkar mai son karantar gaskiyar zancen a idanunshi. Sai ta sauƙe numfashi a hankali kafadunta na nuna relaxation don ta karanci gaskiyarshi. """You don't have to fight for me Sugar, I'm already yours sai yadda kike so za ki yi da ni...""" She smiled ya samu damar duƙawa ya haɗe lips ɗinsu shima yana dan murmushi. "Daga nan ya wanke kishin, amma ba'a cigaba da aiki ba suka tarkata suka tafi gida, ya ce mata" "zai hada Miss Hayat kawai da P.A su ƙarasa Dukda ita ɗin babbar client ce, a gidan ma haka suka lalace da ririta juna sai Magrib suka yi wanka suka shirya." "Gidan Mommy suka je a chan ma suka ci abincin dare Hibbah ta riƙo wani a hannu Dukda bai san me zata yi da shi ba, suka ɗauki Jasrah da ke maƙale da su suka yi asibiti sun ga physiotherapist ɗinta Vera likita ce mai kirki ƙwarai ta jima da Jasrah ɗin kan ta sallamesu a kan" za su dinga zuwa akai a kai kuma ta basu wasu pills da jasrahn za ta na sha. "Daga nan wurin Abba suka yi, MB ya ji tsoron yadda ya ganshi don babu ci sai ruwa kawai sai karatun qur'ani da yake, yayi wani irin sanyi da kyar suka samu ya ci abincin da Hibbah ta riƙo dama don shi ɗin ta riƙo, MB yace zai zauna wurinshi amma Abban ya ƙi sai yafiyar MB ɗin da" ya cigaba da nema Dukda ya tabbatar mishi ba sau ɗaya ba ba sau biyu ba da ya yafe mishi. "Daga nan gida suka yi, a haka rayuwa ta cigaba da tafiyar musu cikin tsananin so da kulawa, kullum kan su je office za su je wurin Abba su tabbatar ya karya kuma yana lafiya kan su wuce haka da yamma in sun taso za su zo su saka shi gaba ya ci kan su wuce gida, wani irin kulawa Hibbah ke bashi shi da Jasrah da a yanzu sun shigar da ita makaranta kuma physiotherapist ɗin" ta yi suggesting a kaita makarantar masu baki don zai taimaka mata tunda ba kurma ba ce. "Watannin Hibbah huɗu da aure kuma a lokacin sossai Jasrah ta sake ta dawo da tarin walwalarta magana ne dai har yanzu babu, Abba yayi sati biyu a Saudi don ya ce yana bukatar kusanci da mahallicinsa, MB ya tabbatar masa idan yayi wata ko ɗaya ne ya samu natsuwa za" su je duka sai su taho da shi. "Yau ya kama Sunday, Hibbah ce zaune tana kallon abincin gabanta da bata ko sha'awar ci don wari yake mata, kuma duk abin da tace MB yaje ya sayo ya je ya sayo amma duk daya wari" suke yi mata. MB ne ya janyota jikinsa. """Sugar ki daure ko kaɗan ne ki ci Wallahi ba zan iya cin komai ba ni ma matukar za ki zauna da yunwa""" "Ta narke ya ɗauko abincin a plate ya kai mata Bakinta sai ta kawar da kai. ""Akwai inda ke miki ciwo ne? Ko mu je asibiti ne Sugarplum?""" Ta girgiza kai ganin da gaske ya damun ya sa ta daure ta kai abincin Bakinta amma bata kai ga tunawa ba wani masifaffen amai ya taso mata. Da gudu ta miƙe sai ta nemi zamewa kan yayi azamar tare ta suka ji Jasrah ta kwalla kiran "sunanta ""Mamieeyy...!""" "Riƙota yayi suka kai ƙasa daga shi har ita idanunsu duka akan Jasrah da dumbin mamaki basu gama mamakin ba aman ya taso ta fara yinshi nan, banda ruwan sanyi da tayi ta sha Har da kankara ruwan kawai tayi ta amayarwa kan ta tsagaita jikinta duk ya mutu, ya ɗauketa zuwa toilet ya wanke mata jiki suka dawo parlorn da kanshi ya gyara wurin ita kam ta miƙawa Jasrah" hannu yarinyar har tana hawaye ta je ta kama nata """So..rr..y Mamieeyy""" "Ta sake faɗa sai kawai Hibbah ta fashe da kuka tana rungumeta ""Alhamdulillah! Alhamdulillah Alhamdulillah mamana ta yi magana Finally""" Ya ƙaraso ya haɗe su ya rungume yana lumshe idanu. Jasrah ta miƙe tana sharewa Hibbah hawaye """Ma..mieyy baki da lafiya ne.. Kike kuka?""" """Ina kukan farin ciki ne Finally bakinki ya buɗu Babynah, you have the sweetest voice Jasrah""" Ta rungume Hibbah tana cewa thanks. "MB ya matsawa Hibbah suka tafi asibiti tashin farko aka mishi albishir na cewa tana da juna biyu na sati har biyar, ta yi skipping period duk basu farga ba farin ciki a wurin su ba'a magana nan fa kulawar shi a kanta ya ninku, aiki ma ya hanata zuwa tana kwance a gida take mishi" shima idan ya je ba jimawa yake ba zai dawo duk ya lalace a kanta. "Wani rana tana kwance tana shan tsami gaye da ta sa Mommy yi mata ta ji knocking, ta miƙe" taje ta buɗe kofan tana buɗewa wa za ta gani...? *FINAL CHAPTER* """Oyoyo Daddy...!""" "Cikin tsananin farin ciki ta riƙo hannayenshi tana murnan ganinshi, ko da ya matsa Umma ce sai Hajiya Kamila, duk maraba ta shiga yi musu da tsantsar farin ciki suka shiga ciki Daddy na ta kallon gidan yana sam barka, ita kam ta gagara zama ta kawo wannan ta kawo wanchan, har ga Allah ba karamin farin ciki ta shiga ba na ganin mahaifinta gidanta abin da iyayenmu hausa" "suke ganin hakan ba daidai ba ne alhali hakan shi ya fi dacewa ga kowani uba sa'i da lokaci ya kai ziyara gidan 'yar shi don ganin halin da take ciki, zuwanshi kuma zai sanyaya mata kwarai" ya tabbatar mata da cewa don an aurar da ita ba shi ke nuna an watsar da ita ba kenan. Riƙo hannunta Daddy yayi don ta ajiye tray ta sake juyawa kenan ya ja ta ta zauna gefenshi murmushinta ya ƙi tafiya. """Daddy sannunku da zuwa"" ""Yauwa Hibbah, kina lafiya?""" "Ya faɗa yana kallonta da fara'a, ciki bai wani azabtar da ita ba don haka ta ƙara kiba sai dai ta" yi haske ne sossai. "Nan ta gaishe da su Hajiya kamila ta koma wurin Umma ta fara tambayar me aka kawo mata," kayan gargajiya ne fal jaka duk wani abu na ci sai da ta taho mata da shi don ta yi ta yiwa Umman mitar bata iya cin abincin kirki sai irinsu. "Daga nan ta fara tambayar mutanen gida, sai da Daddy ya tambayi maigidanta fah kan ta tuna bata sanar da shi zuwansu ba, wayanta ta ɗaga ta kira shi ya sanar da ita yana kusa dama bari" ya ƙaraso. "Hira suka cigaba da yi ta matsa musu sai da suka ci abinci, basu ma gama ci ba ya shigo shi da" Jasrah da ya dauko daga school da gudu ta ƙaraso ta rungume Hibbah """Mamieeyy oyoyoyo""" """Oyoyo my baby, kun dawo?""" "Kai ta gyaɗa sai ta nuna mata su Daddy ""Baki gaishe da su Daddyna ba""" "Da sauri taje har gabansu ta shiga gaishe su, Umma ta riƙota tana tsokanar kar ta kwace musu" "miji gidansu babu wurin ajiye ta, murmushi kawai MB ke yi yana yabawa nagartar bayin Allahn, lallai yayi dacen aure gidan mutunci." "A ranar za su juya ko da suka yi Sallar azahar Umma da Hibbah suka sake kebewa nan tayi ta jan hankalinta yadda ta saba matsayin Uwa da za su tafi Hibbah har da hawaye kaman kar su tafi, a jikin motar da zai kaisu gidan Mommy daga nan kuma sai Airport suka tsaya suka sake sallama kan drivern ya ja MB na tabbatar mishi da ya jirasu har ya kaisu Airport, bayan sun fice" ya janyo matarshi ya rungume yana rarrashi tana kara narkewa. "Bayan kwana biyu ya zo mata da Visa ɗinsu na barin Nigeria, Jasrah na school don haka suka yi shawarar kaita gidan Mommy itama bata damu ba don tana son gidan ƙwarai hankalinta a kwance yake tunda ta rabu da Mum kuma Daddynta ya tabbatar mata ita da ganin Mum har" Abada so a yanzu ta zama kaman kowani yaro within her age. "Sati ɗaya kan tafiyar su suka kaita gidan Mommy su kuma suka shirya a tsanake, sai da ya tabbatar company na good hands nd in good position kan suka ɗaga sai Germany birnin Berlin, a gajiye suka isa musamman ita da ta wahala saboda cikinta ba wai yayi kwari ba ne, shi yayi" "mata wanka ya shiryata tare da sanyata jikinsa suka yi baccin huce gajiya, basu fita ko ina ba" "sai Washegari suka shirya riga da wando ne jikinta sai ta ɗora double chiffon Abaya pink ta zagaye gyalen a fuskarta tayi kyau sossai, a haka suka fita zuwa company ta yi mamakin ganin" companinshi na nan ɗin ashe shima babba ne da ya amsa sunansa. "Nasir sai ganinsu yayi nan yayi ta ba da hakurin rashin samun zuwa bikin su da bai yi ba, Hibbah tayi murmushi tana ce mishi ba komai ai zai zo suna yayi dariya yana ce mata sannu rasa kunya, anan ɗin ma basu huta ba don duk su biyu sun yi aiki Dukda yana hanata amma tana ƙi satin su ɗaya yau yana zaune a office nashi na nan ɗin da duka glass ne, so yake ya kamallah duk abin da zai kamallah don gobe da safe za su wuce Maldives a chan ne za su yi" asalin honeymoon ɗin su sai gata ta shigo office ɗin. "Ɗaga ido yayi ya kalleta, riga da wando ne a jikinta sai ta ɗora coat mai girma wanda ya zo" "mata gwiwa yana da belt, takalmanta boot ne kanta scarf ne da ya rufe mata wuya, hannayenta cikin aljihun coat ɗin ta shigo." "Kai tsaye wurinshi ta nufa ganin ya mayar da idanun kan system yana ƙarasa aikin da ya fara, a" bazata ya ji ta zauna mishi a kan cinya tana zagaye wuyanshi da hannayenta biyu. """Sugarplum aiki fa nake yi..."" Ya faɗa idanunshi kan system." "Ta tura lips ɗinta alamun ina ruwanta, cikin taɓara da neman tsokana ta kai Bakinta kunnen shi cikin salo ta ɗan hura mishi iska tana furta" """What if i tell you that i need youuu?""" Wani irin kasala maganan ya sakar mishi ya kai hannunshi ɗaya kan waist ɗinta a hankali ya furta """Right now sugar?""" Ta ɗaga gira ɗaya tana mishi wani kallo da murmushi. "He puts his two hands on her waist pulling her closer, yana ƙoƙarin haɗe lips ɗinsu ta zame ta" miƙe tana dariya. """I'm just teasing you ne fah Rouhy... Ka yi aikin ka ni ka ga tafiyana""" Ta nufi kofa ba tare da ta kalli fuskarshi ba tana danne dariya. Tana saka hannunta da niyyar buɗe kofan ya mayar da shi ya rufe tare da murɗa key ɗin ya riƙo "kwankwasonta a kunnenta ya raɗa mata ""In kin isa me nake..""" "Shagwaɓa ta fara mishi tana zare ido ""A office ɗin Rouhy?""" """Ko ma a ina ne""" "Ta buɗe baki za tayi magana ta ji ya rufe da nashi, hannunshi ɗaya ya kai ya cire belt ɗin coat ɗinta ya jefar yana dawo da hannayen kafadunta ya zamar da shi ƙasa, ya mayar da hannayen kan waist ɗinta yana squeezing a hankali zuwa lower back ɗinta wani irin tingles yake sending down to her spine." "Shi ya fara laying backward kan tattausan Italian cushion ɗin kan ya mannata da kirjinshi yana cigaba da kissing ɗinta passionatly, who is she to resist his charming tricks tuni ta sallama tana bashi support, ya tura hannayenshi ƙasan shirt ɗinta yana squeezing fatar bayanta gently, ya sake juyawa ta koma ƙasa yayi mata rumfa yana bata kissing of her life daga lips ɗinta zuwa" neckline ɗinta. Kaman yadda ya faɗa bata isa ba daga neman tsokana sai da duk suka samu natsuwa kan ya riƙeta kam a kunne yake raɗa mata yadda yake sonta tana ta murmushi. A toilet nashi na office ɗin suka yi wanka ta matsa mishi da yunwa take ji aikin da ba'a gama ba kenan suka fice don nema mata abinda zata ci karshe a gida ya ƙarasa ya tura musu Washegari suka wuce maldives. "Moment ne da ba zasu taɓa mantawa da shi ba don Dukda tana fama da laulayi da changes da bata saba ba ta sake suka sha soyayya na bugawa a jarida, satin su biyu chan suka wuce Saudi Arabia, Dukda ta taɓa zuwa hajji sau ɗaya tunda Daddy na kai duka yaranshi hajji daga sun mallaki hankali amma wannan zuwan ta fuskanceshi daban, kai ko ma yau ne ka bar garin" ma'aiki ka koma gobe sai ka sameshi daban bare ita da ta jima sossai da zuwa. "Ibada suka yi sossai, ranar da suka ga Abba basu gane shi ba don ya samu wannan natsuwar na zama kusa da ma'aiki a kuma inda ya fi kusanci da mahallici, tuni duk damuwowinsa sun kau Dukda ba za'a rasa ɗaya zuwa biyu ba, satin su biyu suka juyo Nigeria har da Abban lokacin" cikinta ya fito sossai. "Ko da suka dawo rayuwarsu bai chanja ba wurin ƙauna da kulawa, Jasrah ta dawo wurin iyayenta, suna samun hutun makaranta suka tafi Nassarawa anan ne MB ya ga wata dattijuwa ɗiyar Baba Hussaini ce da mijinta ya rasu, tana da yara uku mata biyu da duk sun gama secondary suna neman admission sai babban su namiji da ba ya ma Kasar yana karatu Malysia, nan ya cewa Baba Hussaini ya kamawa Abban shi kaman wasa fa ashe da gaske yake, sai kiran Abban yayi akan yayi mishi mata Abba bai ƙi ba, sai yace in sun gama komai zai zo a ɗaura yana nan, MB ya ji daaɗi sossai hakan kuwa aka yi kan su koma Legos da Mama Juwairiya suka koma da yaranta Amirah da kuma Zainab don Abba ya ce shi ne ubansu a" yanzu ba zai bari su yi nesa da su ba. Hankalin Abba ya kwanta sossai da Mama Juwairiya don tana da halin ƙwarai kuma akwai "nagarta, tana kula da shi sossai kuma ko ba komai gidansu bai zauna shiru ba akwai Amira da zainab yana jin tamkar shi ya haife su." "Bayan watanni huɗu, Hibbah na zaune a ƙasa da turtsetsen cikinta tana shan 'ya'yan kuka, kallo take yi a lokacin MB ya shigo gidan da sallama, ta mayar da hankalinta kanshi ""Oyoyo Rouhy""" Ta ware mishi hannu. Jakanshi ya ajiye ya iso ta ya duƙa ya rungumeta """Sannu My baby Mamah! Ya nauyin jikin? Kina lafiya ko?""" Tambayar da baya taɓa gajiya da yi mata kenan cikin kulawa da tausayawa. """Lafiyata ƙalau""" Tayi maganan tana ɗan tura lips. "Yayi pecking lips ɗin yana bin ta da narkakken kallo ""Har yanzu fushin ne My Sugarplum?""" """Toh ba kai bane, ka hanani zuwa Kano ana chan ana shagali babu ni""" """Baby mana ki tausaya mana pls, kika cigaba da wannan fushi da ni zan bi duniya"" Yadda ya karkace yana maganan ya sa ta saki dariya." """Ko ke fah, ai Jasrah ta yi representing ɗinki kuma suna ne ko gobe sai ki ji ana batun kema za'a zo miki nan""" """Rouhy takwara fa na samu""" """Muka samu dai Baby ai takwaranki tawa ce""" "Tayi murmushi, yana taimaka mata ta miƙe suka nufi sama tana ce mishi" """Yaya Najeeb ya ƙira ni ya ce na yi maka godiyar hidimar da ka yi wa Baby Hibbah, Mun god..."" A hankali ya Juyota ya duƙa ya haɗe lips ɗinsu zuwa yanzu ta san koma me yayi mata baya son godiya, Rago ne Uda manya manya har biyu ya aika ma Najeeb, kayakin baby akwati uku na mamanta ɗaya na babanta ɗaya masu Shegen tsada yayi duk don an yi mata takwara matar" Najeeb da ta riga ta haihuwa. Gashi ya tura Jasrah ta tafi da Yaya Zaitoon da kuma Zainab da suke hutu don yanzu duk an zama daya hidimar Hibbah Mama juwairiyya ba'a barinta a baya. "Bayan yayi wanka suka yi sallah kan ya ɗora kafafunta kan cinyarshi yana mata massaging a hankali hankali har aka yi isha suka miƙe suka gabatar, da kanshi ya je ya kawo mata abin da take so wato Kunun tsamiya da shi take yawan sha yanzu, fruits kawai ya sha bayan ya gama suka koma kan gado ya kunna mata kallo a system ɗinshi tana kwance a jikinshi tana kallo shi" kuma yana aikin kallonta. Bayani take mishi akan film din da kdrama ne da yayi mata mugun daaɗi sai dai sam bata ji ma "yana nuna kaman yana kallo ba, ta ɗago daga jikinshi ta kalleshi sai suka haɗu idanu ta tura lips" """Rouhy film kake kallo ko ni? Drama ɗin nan fa is very interesting""" """Nothing is more interesting in this world than watching you...""" "She started blushing, ta sa hannu ta dafa hancinta sai ta kalleshi" """Are you by anyway laughing at My Big nose?""" "Ta ƙarasa saura kiris ta fara mishi kuka don idan taga yana kallonta sai ta ga kaman munin da tayi yake kallo fuskarta ya chanza hancinta kuma ya ƙara girma, he smiled yayi pecking" goshinta yana sanya fuskarta cikin hannunshi """Staring at your nose? No...I'm staring at the woman carrying my whole world inside her." "Kada ki sake tunanin ina kallon wani abu a jikinki da zai sa ki ji kunya, ajiya na ne fa nan, jinina" "ke girma a cikin jikinki, ta ya ba zan yi admiring macen da ta sadaukar da jikinta domin farin cikina ba? Ko me ya canza a jikinki, ya zama abin alfahari a gare ni... saboda ke ce Sugarplum!""" Hawaye ne ya cika mata idanu na tsantsar farin ciki da soyayya ta rungume shi yayi baya yana taimaka mata suka kwanta. """Kin san me nake kallo kuma?""" Ya yi tambayar yana kallon cikin idanunta ta kaɗa mishi su alamun a'a """ I was wondering how one woman can look this beautiful and still be creating life at the same time. That glow? That's what has me distracted""" "Ta tsinci kanta cikin murmushi mai sanyi, chan ƙasa ta kira sunanshi" """Rouhy!""" "Yana kallonta ya amsa ""Yes Sugar""" """You love me right?""" Yayi dariya mai sauti ya kai bakinshi goshinta yayi pecking """More than you can imagine Hayatee, I love you. Always have and always will"" Ta lumshe idanu tana jin soyayyarshi na kara gamawa da ita." "Cikin daren ta tashi da labour mai zafi, he didn't panic ya taimaka mata suka fita ya je ya ɗauko kayan haihuwa ya sameta a mota, tana da dauriya sai Adu'a suke yi a tare a tare har suka isa asibitin, aka shiga da ita ya tsaya daga waje yana jeka ka dawo tare da yi mata adu'ar sauka lafiya, Allah da ikonsa bata sha wahala sossai ba awa ɗaya da zuwansu ta haifi yaronta namiji, MB na tsaye kawai sai fito mishi aka yi da baby a kyakyawar showel, ya rungume yaron hawayen farin ciki na zubo mishi yana yi wa Allah mai kyauta da kuma kari godiya kan ya ɗago" ya tambayi matarshi fah? Suka ce ana shiryata ne lafiyanta ƙalau itama za ta fito yanzu. Sai da Asuba ya kira Mommy don dama bata tafi Kano ba ne saboda expecting na haihuwar "hibban da suke a kusa, kan gari ya gama wayewa mutanen Kano sun samu labari." "Murna kan murna, kasancewar lafiya ƙalau ta haihu ba wani matsala awanninta shidda a asibitin suka sallamesu suka yi gida, Mama juwairiyya da Mommy ke ta ina za'a saka ina za'a ajiye tuni sun fara kula da ita a tare, a ranar Umma ta diro itama suka cigaba da kula da mai jego da babynta, kafin ranar suna gidan ya cika da mutanen Kano da Nassarawa don kusan kowa ya zo su Hudah duk sun zo aka yi suna cikin kuɗi da tsantsar wadata Yaro ya ci sunan Daddyn Hibbah Mudassir suka sa mishi Jawad, Hibbah ta samu alkhairi kwarai da gaske don ko MB kayan da yayi musu da baby sai da su Mommy suka fara mishi faɗa, ya tabbatar musu ko duka dukiyarshi ya ba Hibbah wlh bai faɗi ba, haka Daddy ya fitar da ɗiyar shi da jikanshi kuma" "takwaranshi ba kadan ba, bayan suna da kwana huɗu Hibbah ta bi 'yan uwanta suka koma" Kano wankan gida cike da kewan mijinta da tausayinshi don da kyar ya haƙura zata je ɗin bayan ta yi ta mishi rigima yana sonta ya zai yi? Kawai dai ya san yawo ya kama shi ne daga Lagos zuwa Kano. 8 YEARS LATER "Hibbah da MB ne tsaye jikin mota sun zubawa doguwar ginin prison ɗin idanu, a yau Mahir ke fita daga prison don ko sau daya MB bai taɓa cire shi daga ranshi ba, ko yaya dan uwanshi kenan ɗaya jal da yake da shi a duniya, haka ma Abba basu taɓa mantawa da shi ba duk kuma irin halin da suka san ya tashi da shi sun sani ƙaddarar gurbatacciyar mahaifiya ne ya sameshi ba laifinshi ba, don haka MB bai taɓa manta ranar Fitowar shi ba ashe Hibbah ba na sane, ita" tace su shirya su tafi tare yaran duka suna gidan Abba za su jira su. "Kofar prison ɗin ne ya buɗu, idanunsu suka sauƙa kan wani kamilalle kuma Natsatsen matashi da ya fito sanye da doguwar farar jallabiya, fuskarshi a cike yake da suma amma a gyare kuma cikin tsari, kamalarshi ya fi yanayi da na malamai waenda suka san musulunci da sunnah suka" "kuma kwankwadi madararta, duk idanu suka zuba mishi kan MB ya bar jikin motan ya nufe shi." """MAHIR?""" "Mahir ya ɗago ya kalli MB sai ya ce ""Yaya..!""" Da sauri suka je suka rungume juna Mahir yana tsiyayar da hawaye. Sun jima sossai kan suka saki juna """Alhamdulillah Allah! Na gode Allah da ya nuna min chanzawarka Mahir""" Murmushi yayi yace """Nima na gode Allah kuma na gode maka da ka tsaya tsayin daka wurin ganin na zama mutumin kirkin, kila ba don kai ɗin ba da a yanzu ban san wani hali nake ciki ba da rayuwata""" Hibbah da ta matso ne tace """Ina tayaka murnan fitowa Mahir""" "Ya kalleta ta kara girma, ta sauya sossai ta yi wani irin kyau, alamunta suna nuna kula da dukiya sun zauna mata kwarai da gaske." "Ya kalli MB, MB yayi murmushi ""Ga Matata uwar 'ya'yana Mahir""" Mahir yayi murmushi """Kun dace da juna Yaya, ina Abbana?"" ""Yana gida yana jiranka""" "Nan suka dunguma zuwa mota, driver ke ja Mahir na daga gefenshi Hibbah da MB na baya har lokacin ransu kal na ganin sauyawar Mahir ɗin har suka isa gidan Abban da ya sauya sossai" saboda gyara da kula da yake samu. "Ciki suka nufa parlorn hayaniya ne fal cikinsa har waje suke jiyowa, suna kutsa kai Jasrah ta biyo Manar za ta daka MB yayi saurin dageta sama yana cewa" """Ya ilahi Me Ummanmu ta miki za ki daketa Adda manga?""" Ta tura baki """Daddy Manar bata ji, tun ɗazu fa sai tsokanan Inaaya take yi don ta samu yarinya mai haƙuri," "nayi ta magana sai tayi kaman ta bari ina juyawa za ta cigaba""" "Hibbah tayi murmushi don Manar wane Hibbah tana karama duk wani halin Hibba na tsokana, faɗa da rashin barin ko ta kwana duk ta kwashe." Inaaya 'yan biyunta ce ba karamin wahala take sha da ita ba sai ta tuna su da Hudah. Mahir yace """Masha Allah, yanzu duk nan zuri'arka ne Yaya?""" Jasrah ta kura mishi idanu tana tuna inda ta sanshi amma ta kasa tunawa shima yana kallonta yace """Jasrah?""" Sai tayi murmushi ta gaishe shi hawaye ne ya shiga zubo mishi. Hibbah tace """Duk ku zo ku gaida Uncle ɗinki Uncle Mahir""" MB ya ce """Ga Chan Jawad shi ke bin Jasrah, sai wanchan dake ta aikin zanen shi ne Abba kenan Bashir muna kiranshi Aryan sai twins Inaaya me sunan Momma(Fatima) da Manar me sunan Umma(Aisha)""." """Masha Allah, Allah ubangiji ya raya mana su cikin tafarki madaidaici""" suka amsa da Ameen suna zama. """Jasrah kira Abba""" Ta haura sama da sauri tana amsawa baban nata. "Yaran da ba'a mishi bayani ba ya nuna su biyu da suke ta wasansu suma ""Waennan fah?""" Hibbah ce ta amsa """jikokin Mama ne, Amaryar Abba wanchan ɗiyar Zainab Sa'idah sai karamin Shuraim yaron Amirah""" Allah sarki kan yayi wani magana Abba ya sauko. "Sai yaje ya rungumeshi suka shiga kuka a tare yana neman Yafiyar Abba Abban ma na neman yafiyarshi, da kyar suka yi shiru Hibbah ta sa Jasrah ta haɗe yaran suka yi baya suna wasa anan Mahir ya sake neman yafiyar kowa a wurin da ya cutar ciki har da Hibbah suka ce sun" yafe. "Ya san labarin mamanshi don haka bai tambaya ba, sai da ya natsu kwarai ya fi watanni uku da fitowa kan ya karbi kudi wurin Abba ya tafi Nassarawa neman Mum, ko ba komai tana da hakki" "a kanshi da dole ya saukar, gidan Yayanta ya sameta sun yi mata ɗaki daga chan gefen kofa" "gado na karfe me spring ɗin nan ne ɗakin sai katifa da ya tsotse kwarai, kafarta daya daure da sarka da iyakacinshi zai barta ta zagaye ɗakin a ɗakin take kashi da fitsari, daga bakin kofan ɗakin suke ajiye mata abin da suka samu don suma ba arziki bane da su kuma da tana da shi" ba taimakonsu tayi ba. "Ita da skeleton ba maraba, ta jeme ta kare ga rashin bacci da ya haifar mata da hauka yau tana lafiya gobe tuburan idan ta rufe da niyyar bacci babu wanda take gani sai Rabi'ah da Anam gashi bata magana ta azabtu kwarai, da kyar ta iya gane Mahir sun yi kuka sossai a tare tana mishi maganan kurame tana roƙon shi ya yafe mata kuma ya nema mata yafiya wurin su Almustapha da Abba, a hannunshi ta cika cikin mummunan yanayi yayi kuka yayi kuka kaman ba gobe haka yayi mata wanka ya suturtata ya kira su suka zo aka yi mata sallah aka kaita kan ya juyo ya dawo legos da labarin rasuwarta Abba da MB suka ce Allah ya yafe mata kawai daga" nan babu wanda ya sake batun ta. **** "Cikin wasu kyawawan Pajamas Wine colour Hibbah ta shirya tayi barin turare musamman inda ta san MB na son shaka a jikinta wuyanta da bayan kunnenta, don tsokana har da Red lip stick ta zizara tayi wani irin kyau kaman ka saceta don ba za ka ce ta yi haihuwa uku ba yara huɗu," gidan shiru alamun kowa yayi bacci ta nufi ɗakinshi.. "Yana tsaye jikin madubi shima wanka ya fito yana fesa turarukanshi ta buɗe kofan ta shigo, sassanyar kamshinta shi ya sanar da shi tana kusa sossai ya ɗaga idanu ya zuba mata ta cikin madubi sai ta sauya tafiya tana mishi wani irin yanga, kasa jure kallon madubin yayi ya juyo gabaɗaya yana dafe zuciyarshi" """Wayyoo Allahna Sugar za ki yi kisa""" Tayi mishi wani murmushin tare da blowing mishi Kiss a iska ya cafe yana sake mannawa "kirjinshi, ba zai iya jure yangarta ba ya nufeta ya rungume tsamtsam yana sauke numfashi." """Watarana sai sonki yayi ajalina Sugar! Zuciyata bugawa take da Sunanki, siffarki da tsantsar" "ƙaunarki""" Ta lumshe ido tana shakar kamshinshi a hankali tace """Ina kaunarka kwarai nima Rouhy, kar ka manta kai ne fa ka tsamo ni daga doguwar SAFARA A TAƁO da na ɗauko tun daga balagata bata ƙare ba sai da na ci karo da kai a hanyar ƙaddarata ka zare ni ka wanke ni fesss da farin ruwa na fita kal kan ka ɗora ni bisa jirgin sama wanda ba zan sake tuntube da taɓo ba bare ya ɓata ni har ya bakanta zuciyata...My plan was to never fall inlove again sai kwatsam na ci karo da ɗan kyakyawan saurayina, ya zama Mayen Hibbah, mai nagarta, mai kyakyawar murmushi da iya lafazi, mai kyakyawar nasaba, tall and charming, My 1" "in a billion I can't resist him dole ya mayar da Hibbah ruwa a soyayyarsa...""" Bata ƙarasa ba ya haɗe lips ɗinsu ya fara bata psssionate Kiss hannayenshi na yawo a jikinta yana birkitata a kaunarshi da kyar ya raba bakinsu ya ce """Sugar kin ja yau dai sai Rouhynki ya samarwa su Manar kanne twins maza in shaa Allah""" Daga nan suka yi kan gado cikin tsantsar ƙauna suka raya daren. Ya ƙanƙameta bayan lafawar komai """You always give me peace Sugar, kin bani abin da ko duniya aka hada babu mai bani irinshi," "thank you for being with me always... ina ƙaunarki! I love you Forever and always Sugarplum!""" TAMMAT BI HAMDILLAH "ANAN NA KAWO KARSHEN WANNAN LITTAFIN ABINDA MUKA RUBUTA DAIDAI ALLAH UBANGIJI YA BAMU LADA, WANDA MUKA KUSKURE YA YAFE MANA. A WANNAN TAFIYA IN AKWAI WANI WANDA NA SAƁAWA DA SANINA KO BA DA SANINA BA INA ROƘON YA YAFE MIN NIMA NA YAFEWA KOWA DUNIYA DA LAHIRA, ALLAH UBANGIJI YA HAƊA MU A WANI SABON LABARIN. NA GODE! NA GODE!! NA GODE KWARAI DA GASKE DA ƘAUNARKU GARENI ALLAH UBANGIJI YA BAR ZUMUNCI. I WILL MISS YOU GUYS LIKE" CRAZY MY PEN FAMILY ฀