MAZAN JIYA Littafi Na Daya (1) Part A Marubuci: Abdulaziz Sani M/Gini Typing: Abubakar Saleh AlQuyraemey A wani zamani can baya mai tsawo da ya shude a cikin daular larabawa anyi wata kasaitacciyar kasa mai suna DARUL MAHABUR. Kasar Darul Mahabur na da matuqar girma da fadi kuma ta qunshi manyan birane a karkashin mulkin sarki guda daya mai sun MAHARAZ IBN SULEDENI. Birnin darul mahabur ya bunqasa da karfin arziki, yawan alumma da kuma kasuwanci har ya zama abin kwatance a ko ina cikin duniya. Sarki Maharaz ya kasance mutum mai tausayi, taimako da jin kan al'umar sa, Allah ya hore masa arziki mai dunbin yawa gami da kaifin hankali da kuma hasashen gaba yana da matar aure guda daya kacal mai suna SHALIFAT kuma basu sami haihuwa ba sai bayan shekara 11 da yin aure don haka a yanzu 'yar su qaramar yarinya ce 'yar shekara 8 a duniya wadda ta kasance kyakkyawa ta gaban kwatance ana kiranta da suna MULAIFA. Tun daga lokacin da Allah ya baiwa Maharaz da Shalifata Mulaifa sai suka dauki soyaiyar duniya suka dora akanta ya zamana ko quda basa son suga ya sauka a kanta.tun da mulaifa ta taso ake tsantseni da ita kuma komai sai dai ayi mata koda ruwa zata sha sai dai a bata a baki batun jin dadi dai da hutu masana sunyi bincike sun tabbatar da cewa a wannan zamani babu 'yar gata kamar mulaifa ko kadan sarki maharaz bai kasance Sadauki ba hasalima bai ta6a yin yaqi ba, amma yana da Sarki yakk wanda ake kira HIBRU IBN IMLAS. Hibru ya kasance babban masoyin sarki maharaz wanda a koyaushe a shirye yake da ya sadaukar da rayuwar sa don kare ta sarki da mutuncin sarki. Sai dai wani abin mamaki shi ne duk irin wannan kauna da Hibru ke nunawa sarki tazama a banza don sarki yaqi yaja shi a jikinsa.Sharifa matar sarki maharaz ta sha yi masa fadan akan sabo da me yaki yaja hibru a jikinsa amma bai ta6a gaya mata dalili ba.sun sha samun sa6ani akan hakan har ma rai ya 6aci, akwai ranar da ta harzuqa sarki baisan sa.adda ya mare ta ba. Cikin tsananin mamaki sharifat ta ruqe kuncinta ta dubeshi a lokacin da qwalla ya cika idanunta tace "Ya kai mijina kayi sani cewa 2n da ka aureni baka ta6a gayamin baqar magana ba bare zagi,amma yau gashi ka mareni lallai dalilin da yasa ka mareni shine yasa baka son kowa yasan sirrin dake tsakaninka da saduki hibru, ni kuwa nayi maka alkawari komai daren dadewa sai na bincika wannan sirri na san shi" Ko da jin wannan batu sai hankalin sarki Maharaz ya dugunzuma ya risina a gaban sharifat tamkar qaramin yaro sannan ya ce "Ya ke matata ki yafe min bisa dora tafin hannuna a kuma a lokacin bana cikin haiyacina hakan ta faru ki ina cewa tunda muka hadu ni da ke ban ta6a rokon ki alfarma ba hakane? Cikin sanyin jiki sharifat tace "Kwarai kuwa" Sarki ya durkusa bisa guiwoyinsa a gabanta ya rike hannayenta a lokacin da idanunsa suka ciko da kwalla sannan yace "Na roke ki don darajar iyayenki da soyaiya dake tsakanin mu da 'yar mu kada ki binciki wannan sirri domin ubangiji darbuza ya hanani yin hakan." sa.adda sarki maharaz yazo nan a zancensa sai jikin sharifat ya qara yin sanyi ainun kuma ta cika da tsananin mamaki daga wannan rana bata qara yiwa sarki maganar hibru ba. Shima sarkin yaqi sau daya ya ta6a yin aure a rayuwar sa kuma matar tasa ta sami shekara 7 da mutuwa amma ta bar masa da guda daya kyakkyawan matashi dan shekara 12 ana kiransa IMNAL. Ya gado mahaifinsa a fagen sadaukanta har ma ana ganin cewa nan gaba idan ya girma sosai sai yafi mahaifinsa jarumtaka domin 2n yana da shekara 7 yake dakawa maza gumba a hannu.duk sa,adda za.a fita yaqi dashi ake fita kuma yana taka muhimmiyar rawa irin wacce manyan mayaqan hibru ya raina abokan gaba sai yayi zamansa ya 2ra imnal ya wakilceshi wajen dakarunsa. Hakika duniya tana da fadi take haka kuma abin cikinta yawa gareshi a can wata nahiyar daban kuma akwai wani gawurtaccem sarki mai suna Dujalu Ibn Shardud wanda ke mulkin birnin hawaruldin. Sarki dujalu ya kasance mashahurin mayaki, sadaukin sadaukai yana iya yakar mutanen gari guda ya kashe su ya kama matansu a matsayin bayi, ya kuma kwashe dukiyar su a matsayin ganima ta wannan hanya ce ya mallaki garuruwa da yawa a qarqashin mulkinsa kuma yana tara dukiya mai qazamin yawa. Bugu da kari sarki dujalu ya kasance qasurgumin matsafi wanda babu kamar sa a nahiyar. A lokacin da sarki dujalu ya ga ya qasaita sai yai bincike a cikin halwar tsafinsa don yasan matsayinsa a akan sauran sarakan duniya. Sai da ya kwana arba'in sannan ya kammala binciken inda hankalinsa yai ma2qar tashi ya rasa abin da ke masa dadi a duniya. Ba komai ya gani ba illa sarki maharaz shine yayi dai dai dashi komai da komai. Koda sarki dujalu yaga wadannan al.amura sai ya kamu da baqinciki ya aiyana a ransa dole ne yayi 2nanin hanyar da zai bi ya rushe daular sarki maharaz ya zamana ya kawar dashi daga doron qasa kuma ya gaje dukiyarsa da mulkinsa ya hada da nasa domin ya zama babu kamarsa a duniya. Bisa wannan dalili ne ya sake shiga halwa ta kwana saba'in don ya sami mafita. Mafitar itace dole ne ya mallaki wandansu makaman yaqi na # mazanjiya wadanda zamaninsu ya shude shekarun baya, wadanda ba a ta6a yin mayaqa tamkarsu ba,kuma ba.a ta6a samun makaman yaqi masu qarfin sihirin nas ba. Makami na farko shine wata sihirtacciyar takobi mai suna Saiful Lujara mallakar Sadauki Hantaru na Birnin Kisra sai mashi mai suna Galilil Haras mallakar Sadauki Shaddadu na birni kufa. Sai wata hular tsafi mai suna lamsara mallakin sadauki hulkas na birnin romaniya . ☼☼☼☼☼☼☼☼☼ Ita dai takobin saiful lujara duk abin da aka sara da ita sai ya tsage gida 2 koda dutse ne ko qarfe, kuma koda shafar jikin mu2m akayi da ita sai ya mu2 saboda mugun dafin da ya ke jikinta. A yanzu haka takobin ta na can ajiye a qarqashin tsakiyar tekun Bahar dufiya a ƙarƙashin tsaron dakarun aljanu dubu 90. Tun bayan mutuwar Sadauki Hantaru wadannan aljanu suka dauko takobin daga gidan hantaru suka kawota tekun bahar sufiya suka ci gaba da tsaronta. Ba za su gushe akan wannan aiki ba face izuwa qarshen rayuwar su don aduniya ba su da abin bauta face wannan takobi. Tun a lokacin da bokan ya qerata mutum uku kacal za suyi amfani da ita. Yanzu mutum daya yayi amfani da ita ya bar duniya ba a san sauran mutum biyun da suka rage ba. Duk wanda ya mallaki wannan takobi har abada ba za.a cishi da yaqi ba koda zai shekara miliyan a duniya. Su kuwa wadannan aljanu guda dubu 90 an gutsuri ruhin kowannen su an sa a cikin sinadarin qarfen da akayi wannan takobi, shi ya sa suka mallaka rayuwar su a kan babu wanda ya isa ya iya rabasu da ita face yana cikin mutane 3 da ke da damar anfani da ita. ☼☼☼☼☼☼☼☼ Mashin Galilil haras mallakin Sadauki Shaddadu na Birnin Kufa, a halin yanzu yana ajiye a can wani kogon sihiri dake birnin kufa, fiye da shekara dubu tun da aka ajiye mashin ba wani mahaluki da ya sake shiga kogon. Shi dai kogon a cikin ƙarƙashin kasa yake mutum bai isa ya ga inda kofar kogon take ba face ya zo da takobin saiful lujara wajen ita ce zata sa shi a kan hanya ta shigar da shi har cikin kogon ta bude masa kofofi 99 ya isa inda aka ajiye mashin galilil haras. Haka kuma mashin na iya rikida ya zama abin hawan mu2m doki ko rakumi wanda ba zai gaji da tafiya ko yunwa ko kishin ruwa har kwana 40. ☼☼☼☼☼☼☼☼ Ita kuwa hular lamsara shu'umar hula ce wadda idan mutum ya sanyata yana iya ganin abin da ke gaban sa nisan tafiyar kwana 40 tamkar abin a gabansa yake, haka duk irin guguwar da akeyi ko tsananin ruwan sama ba zasu kusance shi ba. Sai dai ka ga yana tafiya amma babu su a inda yake. Hular lamsara na ajiye a cikin wani gida na kayan tarihi da ke birnin romaniya, in da aka ajiye kayan tarihin dukkanin sarakunan birnin wadanda suka shude, babu wani tsaro akan hular amma komai hatsabibancin mutum bai isa ya dauke ta ba face ya shigo dakin dauke da mashin galilil haras. Bayan sarki dujalu ya gama nazarin wadannan kayan yaqi na # mazanjiya sai ya cika da tsananin farin ciki yayi ta kyalkyata dariyar murna. Kashe gari kuwa da sassafe yasa a ka shirya dakaru miliyan dubu suka kama hanya suka nufi nahiyar da tekun bahar sufiya take domin dauko takobin saiful lujara, sannan su wuce birnin kufa da birnin romaniya don dauko mashin galilil haras da hular lamsara. ***************** A can birnin darul mahabur kuwa yau ne a ke bikin qarshen sheka na bautar gunkin darbuza. Tunda duku-dukun safiya dakin bautar ya cika da jama.a maza da mata duk inda mutum ya hanga sai dai yaga kawunan bil'adama ne rututu babu masaka tsinke, shi dai wannan dakin bauta yana da ma2qar girma da fadi.domin ya kai girman wani garin.A duk shekara mutane na zuwa daga dukkan sauran qasashen dake nahiyar domin neman tubarraki. Saboda haka duk shekara akwai wakilan wadan nan manyan sarakuna tara dake zuwa wadan nan dakin bauta. A wannan rannan rana sadauki hibru da dansa imnal sunzo bautar da wuri-wuri. Ba komai ne yasa hakan ba face imnal ne ya sa matsawa hibru akan lallai su zo da wuri don su kusanci gunkin darbuza. Maganar gaskiya ita ce ba don su kusanci darbuza bane sai don kawai yaje kusa da gimbiya mulaifa ta ganshi ya ganta. 2ni imnal ya sha alwashin cewa llai a yau ne zai furtawa mulaifa cutar da take addabar zuciyar sa tsawon shekara bakwai kuma a shirye yake ya dauki duk irin horon da za.ayi masa. Cikin sa.a kuwa su hibru suka kusanci inda gunkin darbuza yake ya zamana tazarar da ke tsakaninsu da inda su maharaz ke zaune ba ta wuce taku biyar ba. Gaba dayan dakin bautar tayi tsit,kuma kowa ya rufe idanunsa ya sunkuyar da kansa qas. Dama haka qa'idar dokar bautar take kuma sai an shafe a qalla sa'a guda a haka,sannan sarki maharaz zai miqe yayi bayanin jawabin da gunkin darbuza yayi masa, ma.ana ya isar da saqon darbuza ga jama.a. Dama duk shekara gunki darbuza yana bayani ne akan abubuwan da sa su faru a nahir na alheri ko na tsiya. Kua duk abin da ya fada suna faruwa ne ba a ta6a samun akasi ba. Game da abubuwan tsiyan da za su faru sai ya fadi abin da za ayi domin neman tsari ko sauqi. A wannan lokaci da kowa ya sunkui da kansa qas kuma ya rufe ido akayi tsit ne, imnal ya dago kansa ya bude idanunsa wato ya karya dokar bauta. Kawai sai ya miqe tsaye ya tafi cikin sand'a yana tsallake mutane har isa inda gimbiya mulaifa ke zaune su biyu rak. Kawai sai imnal ya zauna daf da mulaifa ya dauki hannunsa guda ya d'ora akan nata cikin firgici mulaifa ta d'ago kai don taga wanda ya ta6a ta, koda tayi arba da imnal sai ta qura masa idanu ta qame tamkar ba ta da rai . Nan take taji ta kamu da tsananin qaunar sa bata san sa.adda ta dafa hannun sa da nata d'ayan tayi masa murmushi sannan tasa bakinta akan kunnensa tayi masa magana a cikin rad'a "tabbas kaine imnal d'an sarkin yaqi hibru" ko da jin wannan ba2 sai mamaki ya kamashi don haka sai shima ya kara bakinsa a kunnenta yace "tabbas maganarki gaskiya ce amma ya akayi kika sanni alhalin nayi imani cewa baki ta6a ganina ba?". Mulaifa ta ce ansha bani labarinka a siffanta mini kamanninka. Na dade ina kwatantaka a cikin zuciyata.kamannin da nake gani a mafarkina su na gani a yanzu. Kai kuwa menene dalilin da yasa ka karya dokar bauta kazo har wajena? Shin baka tsoron sarki ya sa ayi maka horo mai tsanani? Imnal yayi murmushi ya ce ya ke ma.abociyar kyau da kwarjini ki sani cewa zuciyar da ta kamu da begen masoyi makauniya ce kuma kurma ce. Haka zalika ba ta tsoron komai a duniya muddin za ta sadu da abin begenta. Lallai na dad'e ina begenki a zuciya ta tsawon shekaru bakwai kuma a yaune nayi alqawarin sai na furta miki ciwon zuciya ta ko da kuwa bayan nai hakan za.a tsireni nan gaban miliyoyin wannan jama.a. Da taji wannan zance sai idanunta suka ciko da qwalla ta ce "godiya ta tabbata ga ubangiji darbuza wanda ya cusa min qaunar ka a zuciyata 2n kafin na ganka da ido na." ya kai masoyina ka sani daga ranar da na fara jin labarinka ni ma naji na kamu da tsananin qaunar ka kuma nima yau shekara bakwai kenan ina fama da begenka a zuciyata,bani da burin da ya kai na ganka da idanuna amma damar hakan bata samu ba sai yau. Da yaji wannan ba2 sai ya kamu da tsananin farin ciki kuma yaji sonta ya qaru a ransa d'ari bisa d'ari, kawai sai suka rungume juna.' a dai dai Wannan lokaci ne sarki maharaz ya d'ago kansa sama ya bud'e idanunsa sharkaf da hawaye.' ba zatao ba tsammani sai ya ga Mulaifa da Imnal a kankame da juna. A dai dai wannan lokaci ne sarki maharaz ya dago da kansa sama ya bude idanunsa domin ya yiwa jama'a bayanin sakon darbuza, idanunsa sharkaf da hawaye. Nima ganin yadda sarki Maharaz ya dago da jajayen idanunsa yayi matukar bani tsoro yasa na tsaya cak da typing, sai Allah Ya kaimu gobe mu cigaba. Zan ci gaba. Da fatan anyi sallah lafiya, sannan duk wanda yake son complete zai iya tuntubata ta wannan number 08138873799 kira ko whatsapp. MAZAN JIYA Littafi Na Daya (1) Part B Marubuci: Abdulaziz Sani M/Gini Typing: Abubakar Saleh AlQuyraemey Ba zato ba tsammani sai ya ga mulaifa da imnal a rugume da juna daf da shi al.amarin da ya matukar firgitashi kenan,kuma ya cika da tsananin mamaki, ya tambayi kansa, "ya ya akayi imnal ya tsallako yazo har nan inda muke? Kuma ya akayi mulaifa ta yarda dashi har ta rungumeshi alhalin ta kasance mai ji da kanta da kare martabarta"? Gama aiyana hakan ke da wuya sai mulaifa ta dago kai tayi arba da sarki yana kallonsu cikin razana ta janye jikinta daga na imnal. Al'amarin da ya sa shima ya juya kenan ya yi arba da sarki maharaz ya daka masa harara ba tare da ya ce da shi uffan ba. Imnal ya juya da sauri ya koma can wajen mahaifin sa ya zauna ya kara sunkui da kansa kas, ita ma gimbiya Mulaifa sai ta sunkui da kansa qas ta rufe idanunta zuciyarta na ta daka. A sannan ne sarki Maharaz yai ajiyar zuciya gami da gyara murya. Koda jin gyaran muryar tasa sai kowa ya dago da kai aka qura masa ido. Da aka ga hawaye na zuba a idanun sarki sai hankalin kowa ya dugunzuma,sabo da ba a ta6a ganinsa a cikin irin wannan hali ba. Sarki Maharaz ya qara yin gyaran murya a qaro na biyu sannan ya dubi jama.a cikin tsananin tashin hankali, domin mai girma darbuza ya gaya min cewa rayuwar dukkanin jama.ar dake wannan nahiya na cikin mugun hadari, sa6o da akwai wani gawurtaccen sarki mai suna dujalu wanda ke mulkin birnin hawarul din. Bincike ya tabbatar da cewa a halin yanzu da ni da sarki dujalu mun yi kunnen doki a qarfin mulki, arziki da girman kasa. Bisa wannan dalili ne kishi ya kama sarki dujalu ya sha alwashin cewa sai ya rushe daulata ya mallake mulkina da arziqina sannan sai ya mamaye duk kasashen da ke wannan nahiya tamu. Ba ma nahiyar mu kadai ba gaba daya duniyar yake son ya mallaka sabo da biyan wannan buqata ne sarki dujalu ya shiga halwar kwana saba'in ya samo mafita bita bisa samun biyan buqata. Mafitar kuwa ita ce dole ne yaje ya samo wadansu sihirtattun makaman yaqi guda wadan su zaqaquran sadaukai uku MAZAN_JIYA wadanda a zamaninsu ba a sami kamar ba. Wadannan mutane su ne, kaura Shaddadu na birnin kufa, sadauki Hantaru na birnin kisra, da kuma Hulkas na birnin romaniya. Wadannan barade sun cika MAZAN JIYA domin har yau har gobe ba a sami jarumai ba kamar su kuma har i zuwa qarshen duniya ba za a ta6a mancewa da tarihin su ba. Shi sadauki 1... Hantaru yana amfani da wata sihirtacciyar takobi ce mai laqanin Saiful Lujara, kome aka sara da ita sai ya dare gida biyu tamkar a sa wuqa a yanka lemon 6awo koda kuwa a takobi sai ya mutu saboda kaifin dafin da ke jikinta. 2...Shaddadu yana amfani da wani sihirtaccen mashi ne mai laqanin Galilil Haras, duk mahalukin da ya mallaki wannan mashi komai yawan abokan gaba shi kadai zai iya hallakasu da mashin, domin a duk sa'add ya cillashi cikinsu sai ya burma cikin mu2m dubu arba'in a cikin dakiku kadan, sannan zai dawo hannun sa. Mashin galilil haras yana da tsananin haske don haka komai duhun waje in dai aka shiga da shi sai anga komai ko da kuwa allura ce ta fadi qasa.bugu da qari mashin na iya rikidewa ya zama abin hawan mamallakin sa walau doki ko raqumi kuma ba zai gaji da tafiya ba, ba zai buqaci abinci ko ruwa ba har kwana arba'ing. 3... Hulkas shine mamallakin hular qarfe mai suna Lamsara. Ita lamsara ta kasance shu'umar hula ce in dai mutum yana sanye da ita yana iya ganin abin da ke gabansa, haka kuma duk irin guguwar da akeyi da tsananin ruwan sama ba za su kusanci inda yake ba. Wannan kadan ne daga cikin sihirin wadannan makamai na Mazanjiya. Akwai sauran sirrikan wadanda babu wanda ya san da su face masu su. Wato mazanjiya. A halin yanzu tuni sarki dujalu ya baro kasar sa tare da dakarun sa na yaqi ya nufi tekun bahar sufiya don dauko takobin saiful lujara. Daga birnin hawaruldin zuwa tekun bahar sufiya tafiyar shekara uku bisa doki ko raqumi ba tare da ya da zango ba." ko da sarki dujalu zai yi anfani da qarfin sihiri wajen yin wannan tafiya kuma koda akan aljanu za su tafi dole su shafe sama da shekara guda kafin su isa tsakiyar tekun bahar sufiya. Neman takobin saiful lujara a cikin kogin kuwa dai_dai yake da neman jaki mai qaho, wato dai mace ce da ciki zata iya haihuwa lafiya kuma zata iya rasa rayuwarta. A taqaice al'amari ne na sa'a da rabo, amma dai sai babbar sa'a sannan za'a dace. Idan har aka sami nasarar dauko takobin saiful lujara to lallai sauran makaman biyu ba za suyi wahalar samu ba sosai. Duk mutumin da ya hada wadannan makamai a jikinsa shi kadai tabbas ya cika GAGARABADAU kuma sai ya mulki duniyar na n gaba dayanta. Ba wai mutane kadai zai mulka ba hatta aljanu, dabbobi da dukkanin halittu sai ya iya sarrafa su har tsuntsaye kuma babu halittar da ba zai iya yin magana da ita ba, kuma ya bata umarni ta bi dole. Ya ku ahalin darul mahabur ku sani cewa ba mu ga ta zama ba, dole ne mu mike tsaye mu zage damtse don ganin mun riga sarki dujalu samo wadannan makamai guda uku. Idan kuwa mukayi sakaki ya riga mu samunsu to muna ji muna gani zai zo ya baje qasarmu ya kashe mazajen mu sannan ya gaje matan mu da 'ya'yan mu da dukiyoyin mu. Ya zama wajibi mu aika da wannan sako ga sauran kasashen da ke karkashin wannan nahiya tamu domin mu sanar da su halin da ake ciki kuma mu nemi gudunmawar su bisa wannan gagarumar tafiya". Sa'adda sarki maharaz yazo nan a zancen sa sai dakin yayi tsit tamkar babu kowa a cikin sa. Nan take dakin bautar ya watse jama'a suka tafi suna tattauna wannan lamari a cikin firgici da matukar damuwa. A wannan rana dai mutane ba su da hirar da tafi ba2n shirin sarki dujalu. Nan da nan labarin al'amarin ya fara bazuwa sauran garuruwa birane da qauyuka da kuma sauran qasashen maqofta. Duk jama'ar da ta ji wannan labari sa ta rude ta shiga shirye shiryen kare kai da bayar da dakarun gudunmawa izuwa birnin darul mahabur. Tun a wannan rana ne sarki maharaz ya aiki wasu zakwakuran hadiman sa na jinsin aljanu suka kai wasika zuwa dukkanin sarakunan da ke muli a nahiyar. A cikin sa'o'i kadan labarin ya riski ko in da ina sarakai suka firgice ainun kuma suka miqe tsaye wajen fara shirye shiryen tafiya. Wannan shine abin da ya faru a fadar sarki maharaz bayan ya sanar da jama'ar sa jawabin gunkin darbuza wanda aka saba yi a duk qarshen shekara a lokacin bauta. ☼☼☼ ☼☼☼ ☼ Al'amarin imnal da mahafin sa sarkin yaki hibru kuwa, tun da suka baro dakin bauta suka nufi hanyar gida sai duk suka yi shiru suna tunani a cikin zukatan su ba tare da sun ce kala ba. Shi dai sarkin yaki hibru ba komai ya ke tunani ba face kiyasta rayukan da za'a yi asara yayin wannan tafiyar gami da irin dukiyar da za'a 6arnatar. Haka kuma yana jimamin tafiyar da za.ayi abar mata yara da tsofaffi kawai a birnin ba tare da an bar musu dakarun tsaro ba wanda hakan na iya janyo komai ya faru, duk da cewar sadauki hibru ya san cewa bashi da mata, kuma bashi da sauran dangi a fadin kasar gaba daya sai yaji takaici da baqin ciki suka mamaye zuciyar sa saboda ya san cewa wannan gagarumin yaki da za'a fita ba karamar masiba bace da koma bayan ci gaban nahiyar gaba daya domin zai janyo karyewar tattalin arziqi kuma masoya za su rasa masoyan su, iyaye za su rasa 'ya'yansu 'yan uwa zasu rasa 'yan uwansu. Koda hibru yazo nan a zancen sa sai idanunsa suka ciko da qwalla saboda tausayin halin da jama.a za su shiga. Shi kuwa sadauki imnal ko kadan tunaninsa ba irin na mahaifin sa bane. Abin da yafara fado masa a rai shine wai shin ya za.ayi ya mallaki wadannan kayan yaki guda 3 na MAZAN JIYA? Koda ya gama aiyana hakan a zuciyarsa sai ya yiwa kansa dariya ya ce Amma fa bani da hankali akan wane dalili ne ma zan nemi abin da ya gagari manyan sarakunan duniya masu taqama da komai. Gama aiyana hakan ke da wuya sai gimbiya mulaifa ta fado masa a rai ya ce to wai shin yanzu za'ayi tafiyar nan tare da gimbiya mulaifa kuwa? Lallai zan kasance mai tsananin baqin ciki idan ba a tafi da ita ba. Idan kuwa aka tafi da ita sai na fi kowa farin ciki a fadin duniya. Haka dai imnal yayi ta saqe saqe a zuciyar sa har suka isa qofar gida. Dama imnal ne akan gaba har ya sanya qafar sa a cikin qofar gidan sai ya dakata ya waigo ya dubi hibru fuskar sa cikda alamun damuwa koda ganin haka sai hibru ya tsaya cak ya kura masa idanu sannan ya ce mene ne ya faru? Imnal ya ce ka gafarceni ya abba na nayi babbar mantawa dazu a dakin bauta sarki ya ce min na fada maka muzo ni da kai yana neman mu a fada da yammacin gobe. Ko da jin wannan batu sai hankalin hibru ya tashi yai shiru ya sunkui da kansa qas .daga can kuma sai ya dubi imnal ya ce ka gaya min gaskiya shin kayi wani laifi dazu a dakin bauta??? Jin wannan tambaya sai imnal ya sunkui da kanasa alamun rashin gaskiya ya ce qwarai kuwa nayi laifi. Domin na tashi daga inda nake zaune naje wajen gimbiya Mulaifa.... Koda jin haka sai hibru ya dafe kai yana mai ajiyar numfashi, sa'annan ya ce tabbas na san cewa ruwa baya tsami banza. Ni dai a sani na sarki bai ta6a neman shawarata ba sai dai kawai a gaya min cewa za'a fita domin naya shiri. Tabbas ka aikata babban laifi don haka dole ne ka fuskanci mai tsanani saboda wannan laifi don haka ni babu ruwana, tsuntsun da yaja ruwa shi yake duka. Koda jin wannan magana sai imnal yayi murmushi ya ce indai akana soyaiya ta ga gimbiya Mulaifa ne a shirye na ke don na kar6i horo koda kuwa na mutuwa ne, cikin tsananin takaici hibri ya dube shi a fusace, kawai sai ya wuce zuwa turakar sa ya bar imnal tsaye a kofar gida. Da yammaci kuwa fadar sarki maharaz ta cika makil da jama.a masu amsa gaiyatar tafiya yaki, duk da cewa adadin jama.ar da suka taru bai kai daya bisa goman masu tafiya yaqin ba sai da fadar ta cika ta batse sai da ya zamana duk inda ka duba kawunan bil'adama ne rututu. Tun a farkon yammacin ne sarkin yaqi tare da dansa suka amsa kiran sarki suka hallara a fadar, shi kuwa sarki maharaz bai fito ba sai da kowa ya gama zuwa. Da fitowar sarki kowa ya miqe tsaye don girmamawa a gare shi har sai da ya zauna sannan kowa ya zauna. Sarki ya dubi dubun mutane da suka amsa kiran sa sai ya cika da farin ciki, da ya duba 6angaren da su imnal suke tsaye sai ya murtuke fuska ya 6ata rai. Bayan fadawa sun zube sun kwashi gaisuwa ya rage sauran sarkin yaki hibru da dansa Imnal, kawai sarki yayi nuni da hannun sa izuwa ga wani badakare yana maiyi masa nuni da yazo da imnal gabansa, nan take badakare ya tasa keyar sa yazo da imnal gaban sarki. A wannan lokaci gimbiya Mulaifa na zaune daf da sarki. Koda taga an tasa keyar Imnal anzo dashi gaban sarki sai hankalinta ya tashi domin ta tabbatar da cewa lallai hukunci za'ayi masa. Gaba daya jama'ar dake fadar kuwa sai suka cika da mamaki suka zuba ido don su ga irin hukuncin da za'a yiwa Imnal yaron da ba.a ta6a ganin yayi wani laifa ba. A kullum shi da mahaifin sa ba su da wani abin da ya wuce biyaiya ga sarki, Sarki maharaz ya mike tsaye daga kan karagar mulkin sa ya dubi jama'a ya ce ya ku ahalin darul mahabur ku sani cewa wannan yaro Imnal d'a ga sarkin yakin mu hibru ya kasance mai ladabi da biyayya a garemu kamar yadda mahaifin sa ya kasance, kuma bamu ta6a kamashi da wani laifi ba, amma sai gashi a jiya ya aikata wani babban laifi wanda bamu ta6a zaton zai aikata shi ba. Laifin kuwa shine a jiya sa'adda kowa ya sunkui da kansa kas a dakin bauta sai shi ya miqe yaje inda nake zaune ya zauna kusa damu. Wannan shine karo na farko da wani mahaluki ya karya dokar maigirma darbuza a cikin kasar nan, don haka dole ne ayi masa hukunci gwargwadon laifin sa. Mai girma darbuza ya ce a daure imnal a sama jikin katako kuma a cikin rana tun daga hudowar ta har zuwa faduwar ta ba tare da an bashi ruwa koda makwarwa daya ba har tsawon kwana uku. Idan kuma ya sake aikata irin wannan laifi hukuncinsa zai zamo kisa ne. Koda sarki maharaz ya zo nan a zancensa sai idanun Mulaifa suka ciko da qwalla suka fara zubar da hawaye. Hibru da imnal kuwa ko a jikin su maimakon ma hankalinsu ya tashi sai suka kama murmushi domin sun san cewa wannan horo ba komai bane akan irin horon da hibru ya bashi tun yana dan karami. Sarki Maharaz yaci gaba da bayani .. Sai gobe za'a fara wannan horo ga Imnal, kuma washe garin ranar da aka gama horon ne zamu dunguma gaba dayan mu mu tafi izuwa gagarumin yaki da ke gaban mu. Domin mu riga sarki dujalu dauko takobin saiful lujara. Ina mai kira ga dukkanin jama'ar mu da a ci gaba da shirye-shirye babu sassauci domin tuni dakarun gudunmawa sunzo da yawan su mu kawai suke jira a tafi... Ko da gama wannan jawabi sai sarki Maharaz da Mulaifa suka shiga gida sannan jama'a kowa ya kama gabansa. Lokacin da imnal da hibru suka isa gida sai hibru ya aika imnal kasuwa don ya sayo masa zugazugi na wutar Qira sabo da nasa ya lalace. Imnal ya hau doki ya tafi kasuwa tun kafin ya isa kasuwar sai yaga duk inda ya ratsa jama'a na kallonsa suna magana akan hukuncin da sarki zai yimasa. Kafin ya isa kasuwar ne ya hadu da wadansu kuyangin gidan sarki suna tafe suna hira. Koda suka ganshi sai suka sha gabansa suka shiga yi masa kirari suna kodashi. Al'amarin da ya matukar bashi mamaki kenan ya dubesu ya ce ya ku wadannan kuyangi ku kuwa mai yasa kuke kodani haka alhali kuwa banyi wani abin al'ajabi ba? Suka ce ai kuwa kai ne kayi babban abin al'ajabi tunda har ka siye zuciyar gimbiya Mulaifa a halin bata ta6a nuna tana son wani da namiji ba face kai. A yanzu haka tana can gida tana kuka sabo da jin za'ayi maka horo na kwana uku bisa laifin da ka aikata. Babu irin rokon da gimbiya ba tayi wa sarki ba akan ya janye wannan horo amma yaki, saboda bakin ciki ne shi yasa ta kasa ci ta kasa sha kuma ga dukkan alamu haka zata kwana a wannan hali yau. Sa'adda kuyanga ta zo nan a zancenta sai hankalin Imnal ya dugunzuma ainun ya rasa abin da ke masa dadi a duniya, sai kawai ya dubi kuyangin ya ce da su idan kun koma gida ku shaidawa gimbiya cewa wanda take kuka dominsa yana bakin ciki bisa zubar hawayenta da kuma rashin ci da shanta.. Lallai shi ma ba zai ci kuma ba zai sha ba a yau har sai yazo ya ganta ta kowane hali... Jin wannan batu sai kuyangin suka zazzaro idanu cikin tsananin mamaki wacce tayi magana dashi tace taya zaka iya shiga gidan sarauta har ka ganta ahalin akwai tsananin doka da tsaro? Imnal yai murmushi ya ce ko mutuwa ke tsaro a yau sai na ga gimbiya Mulaifa kuje ku gaya mata cewa komai dare ina nan tafe a yau. Koda gama fadin haka sai imnal ya kada linzamin dokin sa ya wuce izuwa kasuwa ya siyo zugazugin ya koma gida sannan ya ci gaba da taya hibru kera wasu sababbin makaman yaki tamkar babu wani abu da ke sosa zuciyarsa. Nima zan so ganin yadda Jarumi Imnal zai iya ratsawa ta cikin wannan tsaro na gidan sarautar birnin darul mahabur har yaje ya sadu da Gimbiya Mulaifa, masu karatu ko zan samu dan rakiya kuwa? Da fatan kuna hutun karshen mako lafiya, sannan duk wanda yake son complete na Littattafan yaki harma da na soyayya zai iya tuntubata ta wannan number 08138873799 whatsapp kadai pls banda kira 🥺 MAZAN JIYA Littafi Na Daya (1) Part C Marubuci: Abdulaziz Sani M/Gini Typing: Abubakar Saleh AlQuyraemey Da tsakar dare lokacin da gari yayi tsit ba kajin komai face kukan gyare. Da daidaikun sautin tsuntsaye, imnal ya miqe tsaye dama ko runtse ido bai yi ba bare yayi barci. Cikin sanda ya debo wadansu bakaken kaya ya sanya sannan ya rufe fuskar sa da bakin rawani, takalmin da ya sa kuwa na fata ne kasansa gashi ne yadda duk abin da ya taka ba za.aji sautin komai ba. Ko allura bai dauka ba a matsayin makami, ya bude kofar dakin sa ya fita ba tare da hibru ya ji motsin sa ba, maimakon ya bude kofar gidan sai kawai ya daka tsalle kamar dan biri ya dira akan katangar gidan, duk da cewa tsawon katangar ya kai kamu sittin. Kafin ya tafi ya tanadi kayam da ya cire daga jikinsa a cikin 'yar qaramar jaka kuma shifidar da ya kwanta sai yatara tsummokarara yai musu siffar mutum ya lullu6esu tamkar mutum ne a kwance. Dama tuni ya daure dokinsa a kofar gida bai shiga da shi ciki ba saboda dama yasan cewa zai yi amfani da shi yayin da dare ya raba. Koda imnal ya dirgo daka kasa daga kan katangar sai yaje ya kwance dokin ya haye kansa ya zabureshi ya nufi hanyar da zata kai shi gidan sarki tuni ya aiyana a ransa ba zai wuce rabin sa.a ba zaije ya dawo. Cikin matsanancin gudu imnal ya ci gaba da tunkarar gidan sarautar sai ya sauya hanya domin ya 6ullo ta bayan katangar gidan, cikin kakanin lokaci ya hango katangar gidan da sauri ya sauko daga kan dokinsa ya daureshi a cikin bishiyoyi masu duhuwa sannan ya 6uya a cikin duhuwar, ya kurawa katangar idanu yana kallon dakaru kuma yana nazarin hanyar da zai bi ya shiga gidan ba tare da wani ya ganshi ba. Al'amarin da ya qara tayar da hankalinsa kenan domin bai ga ta yadda hakan zata iya faruwa ba. Sai imnal ya dan jima yana nazari sannan dabara ta fado masa. Nan take ya hau kan bishiya ya karyo itatuwa sannan ya sauko ya daddaure itatuwan da 6awon bishiya yayi siffar mutum mutumi ya dora shi kan dokin sa ya kora shi, dokin ya fita da gudu ya wuce ta gaban wadannan dakaru dake tsaitsaye a bayan katangar. Ko da suka ga mutum a sukwane ya wuce ta gaban su sai suka bi shi gaba daya da gudu domin su kure masa gudu, damar da imnal ya samu kenan ya fito da gudu daga cikin duhuwar da ya 6uya.. Ko da ya rage saura taku uku ya riski katangar sai ya daga tsalle yai sama tamkar tsuntsu ya kama karshen katangar, yana kama katangar sai ya ji ta da tsananin santsi har hannun sa ya su6uce zai fado sai ya sake jefa daya hannun nasa ya kamo katangar ya dafa kafafun sa sama ya dirga akan katangar, koda ya leqa qasan katangar izuwa cikin gidan sai ya ga akwai tsawo sosai in yace zai fada zai iya karyewa. A dai dai wannan lokacin ne ya jiyo dawowar dakarun da suka bi dokin sa sun dawo da gudun tsiya. Nan fa zuciyar imnal ta buga da karfi domin ya san cewa babu mamaki sun bi dokin ba su ga kowa a kan sa ba sai itatuwa, sai baban su ya ce lallai ma ko waye mai dokin nan ya raina mana wayo, sai ya daka ma sauran dakarun tsawa ya ce kowa ya koma malafar sa ya ci gaba da aiki don akwai alamar zuwan baki gidan nan. Imnal ya ringa bin katangar har ya hango wani tafki a jikin katangar daga cikin gidan sai yayi sauri zuwa wajen keda wuya sai yaga bakin tafkin 12dakaru ne suke kaiwa da komowa, amma sai yayi ta maza ya daka wawan tsalle sai ya fada cikin tafkin nan ji kake Zundum.. Al'amarin da ya juyo da hankalin kwamandan dakarun nan sai ya umarce su da su shiga cikin tafkin su lalubo abin da ya fada su fito da shi. Nan take suka bi umarninsa suka shiga tafkin nan.. Koda imnal ya ji dakarun nan sun shigo cikin ruwan, cikin zafin nama ya samu guda daga cikin dakarun nan ya suburbudeshi ya bishi da mazga, nan take ya suma sai ya cire kayan jikin sa ya sanya masa shi kuma ya sanya nasa, sakamakon dakarun duk kayan su iri daya ne. Can sai gaba daya suka yo sama su shaida ma sugaban ba su ga kowa ba, sai ya ce kowa ya koma ma6uyar sa imnal ne na karshe ya fito daga cikin tafkin ya ruga izuwa cikin wani sashen gidan sarautar. A lokacin da imnal ya fito daga ruwan ne ya ruga akayi akasi shugaban dakarun ya waigo kawai sai ya hango imnal ya ganshi dan karami kamar wada. Al'amarin da ya ba shi mamaki kenan domin ya san cewa duk cikin yaran sa babu gajere ko wada. To ya ya akayi aka samu wannan? . A gigice shugaban dakarun ya ruga izuwa bakin tafkin kawai sai yaga nasa badakaren a saman ruwa a sume.Shugaban dakarun yayi sauri ya kwala wa yaransa kira suka firfito daga malafar su a guje suka taru a gaban tafkin. Ya dubesu yace lallai muna da baqo a cikin gidan nan ku bazama neman sa. Nan take dakarun suka bazu izuwa kowanne sashe na gidan sunan dube dube. Lokacin da imnal ya ruga cikin gidan sarautar yana la6e la6e sai ya rasa hanyar da ya kamata ya bi saboda bai san 6angaren turakar gimbiya mulaifa ba. Kawai sai ya bi kan wata matattakalar bene da gudu. Da zuwa ya ga dakaru za su gan shi sai ya nemi wuri ya 6uya. A haka ne yayi ta wuce dakuna barkatar yane leke leke ta cikin tagoginsu. Wani lokacin sai kaga saura kiris a ganshi sai kuma ya duka kasa ko ya shige cikin wani lokon ya 6uya. Yana cikin haka ne ya hango wani daki kofar sa a bude kuma fitila a kunne. Koda ya leqa tagar dakin sai ya hango kuyangin nan guda biyu a zaune cikin tararrabi idanun su a bushe babu alamar sunyi barci ko suna jin sa, cikin zafin nama imnal ya fada dakin ya rufo kofa. Koda kuyangin nan biyu suka ganshi sai sukayi sauri su kashe fitilar dakin, cikin rada daya daga cikin su ta matso dab da shi ta ce hakika ka cika mai sa.a yaya akayi ka shigo cikin gidan nan ka tsallake duk tsaron waje da na ciki? Imnal yayi ajiyar zuciya ya ce ni dai yanzu bani da lokacin amsa tambaya ,abin da nakeso da ku kawai kuyi mini jagora izuwa inda turakar gimbiya take. Cikin hadin baki suka ce"ta6dijan ka rufa mana asiri indai ba so kake a hallakamu ba shin ba ka jin guje gujen dakarun tsaro ne? Nan din nan ma da kake ciki hadari ne ga rayuwar mu idan aka shigo aka ganka. Abin da zamu iya yi maka kawai shine mu baka zanen taswirar gidan nan mai dauke da nunin inda gimbiya take" Imnal ya ce na gode da hakan ma maza ku bani. Cikin rawar jiki daya daga cikin kuyangin ta dauko taswirar wadda ke zane akan wata busasshiyar fata ta miqa masa ta ce "Wannan ita ce gudummawar mu a cikin soyaiyarku kai da gimbiya" Koda jin haka sai murna ta kama imnal yace "Ni kuwa nayi muku alqawari duk ranar da burin mu ya cika ni da gimbiya sai na 'yantaku na ba ku kyautar dukiya irin wacce ba.a ta6a baiwa wani ba" Gama fadin hakan keda wuya sai suka ji ana kwankwasa kofar dakin da qarfi ana yi musu tsawar su bude. Kafin kuyangin suyi wani yi wani yunkuri sai suka ga imnal ya daka tsalle sama kamar dan biri ya naushi saman rufin dakin wanda akayi shi da katako mai kaurin gaske. Take saman ya 6urma ya fice fit ta cikin sa. Koda imnal ya tsinci kan sa a saman rufi sai ya ci gaba da gudu akan dakuna. Ba zato sai yaji ana harbo masa kibiyoyi cul cul cul ! In ba don karfin gudun sa ba da tuni an sameshi, sai da yayi tafiya mai tsayi a sama sannan ya hango wani tafkeken tafkin wanka mai dauke da ruwa garai garai gunin ban sha.awa.kwatsam sai ya hango gimbiya Mulaifa a tsaye a gaban tafkinkwatsam sai ya hango gimbiya mulaifa a tsaye a gaban tafkin ta daga kai sama tana duba madubi. Koda imnal yaga babu kowa a kusada ita sai ya yadako tsalle ya fado cikin tafkin kafin ya fito daga tafkin tuni itama ta daka tsalle ta biyoshi ciki kawai saita danna shi izuwa kasan tafkin sukayi nutso ta wuce gaba yana biye da ita sai gasu sun biyo wani kwararo sun fito saman wani sabon tafkin wadda yake tsakiyar cikin turakarta babu kowa awajen face kuyangi fitowar keda wuya daga cikin tafkin sai kuyangi 2 suka rugo suka yafa musu mayafan goge jiki har izuwa wannan lokaci mulaifa bata dubi fuskar imnal ba balle tace dashi wani abu kuma fuskarta a murtuke take tamkar wadda aka aikowa sakon mutuwa. Al'amarin daya jefa imnal cikin mamaki kenan amma sai yayi shiru baice komai ba bayan an gama tsame lemar dake cikinsu sai Mulaifa ta sake kama hannun imnal zuwa dakin baccinta da zuwa sai dukkanin kuyangin da suke ciki suka fito waje suka rufo kofa nan take Mulaifa ta sharawa imnal mari ta fashe da kuka ta rungumeshi tana mai cewa saboda mai zaka saida rayuwarka kace sai kazo ka ganni a wannan dare, shin mun rabune har abada baxamu sake saduwa ba inda tsautsayi yasa ka hallaka da tuni nima na kashe kaina. Sa'adda imnal yaji wannan batu na mulaifa sai gabadaya jikin shi yayi sanyi nan take yaji kaunar mulaifa ta kara mamaye zuciyarsa kawai saiya janye jikinsa suna masu fuskantar juna yace yake abin begena kiyi sani cewa sa'adda na samu labarin halin da kika shiga sbd hukuncin da aka yanke min sai hankalina ya dugunzuma, naji bazan iya yin komai ba sai nazo na ganki burina na ganki da idanuna koda kibiyoyi dubu zasu nutse a cikin gangar jikina, sa'adda imnal yazo nan a zancen sai mulaifa ta sake rungumeshi cikin tsananin farin ciki tana mai cewa tabbas kaine zaka zamo abokin rayuwata gama fadin hakan keda wuya sai sukaji Sarki Maharaz na kwankwasa kofa yana cewa a bude alamarin daya dugunzuma hankalin imnal da kuyangun ita kuwa mulaifa ko a jikin ta kawai saita dafa imnal da dan yatsanta guda na hagu take imnal ya rikide yazamo kofin zinare irin wadda ake saka furanyi aciki faruwar hakan keda wuya sai mulaifa ta umarci kuyangin nata su bude kofar. Sarki maharaz ya shigo a fusace yana haki nan take ya kama kalle-kalle yana nazarin ko wace kusurwa batareda yace komai ba. daga can sai Mulaifa ta duci sarki tace babu wani bako daya shigo wajena koda jin haka sai sarki maharaz yayi murmushi ya matsa dab da Mulaifa ya dafa kafadunta yace yake yata a iya sanina baki taba min karya ba ashe za'a wayi garin ranar da zaki min karya saboda soyayya inaso kisani cewa na fahimci akwai soyayya tsakanin ki da imnal dan sarkin yaki tabbas shina nake zargi da shigowa gidan nan ahalin yanzu na tura dakaru zuwa gidan sarkin yaki idan sukaje suka iske baya nan tabbas toh shine yazo... hukuncin kisane zai tabbata akan shi maimakon horo. Koda mulaifa taji haka sai hankalinta ya dugunzuma amma saita dubi sarki maharaz batare da nuna wani damuwa ba tace ina mai tabbatarka imnal na gida a kwance, sarki maharaz yayi murmushi har ya juya zai fita sai idanunsa suka kai kan wannan kofin zinaren sarki maharaz ya kura kofin kurawa kofin idanu yana nazarinsa, a lokaci ne zuciyar Mulaifa ta fara bugawa. Lokacin da sarki maharaz ya kurawa kofin zinaren nan idanu yana nazarin sa a lokacin zuciyar Mulaifa ta fara bugawa da karfi bayan sarki maharaz ya gama nazarin wannan kofin saiya juyo ya dubi mulaifa yace yaushe kika samu wannan kofin? Nide asanina bantaba sayo irinsa ba mulaifa tayi murmushi tace ai musamman na aika birnin shamrun aka kera mini shi koda jin haka sai sarki maharaz ya karisa inda kofin yake ya daukeshi yana mai jujjuya shi a hanun shi yace amma fah ya bani sha'awa sosai shin zaki iya bani kyautarsa mulaifa tayi murmushi tace ya abbana ai komai kake so daga gareni basai ka tambaya ba dauka yakamata kayi kawai amma akwai wanda zaifi dacewa dakai nasa akera maka shi zaizo nan da kwana Bakwai, yayin da sarki maharaz yaji wannan magana sai jikinsa yayi sanyi kuma ya kasayin gardama kawai saiya ajiye kofin sannan ya sumbaci goshin gimbiya mulaifa ya fice daga cikin turakar. Fitarsa keda wuya sai kuyangi suka rufe kofar turakar. ita kuma mulaifa saita ruga ta dauko wannan kofin zinare nan take ta karanta wadansu dalamisan tsafi ta tofa akan kofin faruwar hakan keda wuya sai kofin ya tarwatse kamar an watsa hoda, sannu a hankali hodar ta dinga disashewa ta bace bat kawai sai gimbia mulaifa ta tafi izuwa kan gadonta ta kwanta domin sai a sannan ne hankalinta ya kwanta. Al'amarin imnal kuwa shide kawai ya tsinci kansa ne kan gadon cikin dakinsa kawai sai yaji ana magana da mahaifinsa hibru a kofar dakin ga dukkan alamu ran hibru a bace yake domin yana magana ne cikin daga murya da fushi maganar da imnal ya fara ji daga mahaifinsa itace, yanzu niza ayiwa haka to kusani cewa tun safe ina tareda dana kuma yanxu haka yana cikin dakinsa yana barci wata kakkausar murya tace "Ya shugabana kayi hakuri mu yan aiken sarki ne dan haka bai kamata kaga laifin mu ba saboda bin umarni ne, yanzu dolene ka bude mana mugani idan yana ciki musan amsar daza muje mugayawa sarki, idan kuma bazaka bude ba dolene mu bude da kanmu". Koda jin haka sai hibru yayi ajiyar zuciya yace ai bama sai takai haka ba. Nan take ya bude kofar dakin aiko saiga imnal yanata sharar barci abunsa kamar ma baisan abinda akeyiba sai jikin dakarun sarki yayi sanyi babban cikinsu mai kakkausar murya ya dubi hibru yace ka huta lafiya ya shugabana kawai saiya juya ya fita daga cikin dakin sauran dakarun kuma suka rufa masa baya, cikin hanzari hibru yaje ya kullo kofar gidan sannan yadawo cikin dakin imnal ya dubi imnal yace yakai dana tashi muyi magana nasan idanunka biu kuma tabbas ka fita daga cikin gidan nan cikin dare. Koda jin haka sai imnal ya mike zumbur ya kurawa hibru idanu cikin mamaki sannan ya sunkuyar da kanshi kasa cikin alamun kunya da rashin gaskiya. Koda ganin haka sai hibru yace yakai dana kayi sani cewa duk wanda ya rigaka kwana dolene ya rigaka tashi a ka'idar rayuwata duk tsakar dare nakan farka na duba ko'ina na gidan nan kuma na fita kofar gida na kwanta, tun kafin a haifeka nake wannan al'ada kuma mahaifiyar ka batasan inayi ba, yauma kamar kullum hakan tafaru kuma dana duba cikin dakinka sai naga baka nan kuma dana duba waje sai naga babu dokinka, hakan ya tabbatar min dacewa ka fita cikin daren nan abinda bansani ba ina katafi? yanzu na samu amsar inda kaje tunda dakarun sarki sunzo don su tabbatar da cewa ko kaine kaje gidan sarki yakai dana mai yasa kake jefa kanka cikin rigima da tashin hankali mai kajeyi gidan sarki shin kamanta ne cewa kanada babban kaifi kuma a gobene za'ayi maka hukuncinsa. Sa'adda hibru yazo nan a zancensa sai jikin imnal yayi sanyi, daga can sai yadago kai cikin alamun nadama yace yakai abbana ka gafarceni kayi sani wannan kuskuren danayi bayin kaina bane zuciya ce ta ribance ni ina mai tabbatar maka ayanzu nida gimbiya mulaifa bazamu iya rayuwa ba idan bama tare da juna. Koda jin wannan batu sai hankalin hibru ya dugunzuma ya mike tsaye ya juyawa imnal baya lokacin da idanunsa suka ciko da kwalla, imnal ya mike tsaye ya zagayo gaban hibru ya tsaya kawai saiya durkusa bisa gwuiwoyinsa ya kama tuba da neman gafara hibru kuma kama kafadan imnal yayi suka fuskanci juna a lokacin da hawaye ke zuba da idanunsu hibru yace yakai dana bakayi min laifin komai ba kayi sani cewa in bah soyayya ba da nine sarkin wannan birni namu, amma saboda na zabi soyayya nayi watsi da mulki in badan soyayya ba da maxan jiya guda uku wato jarumi hulkas mai hular Lamsara, Kaura Shaddadu na birnin Kufa mai mashin galilul haras da sadauki Hantaru mai takobin Saiful Lujara da basu mutu a banza ba tabbas soyayya tushen wahala ce sai mai sa'a da rabo ke tsallake shaukin cikinta ina tsoron kada rayuwar ka ta kare irin yadda tawa takare da kuma yadda ta mazan jiya takare, ya kai dana kayi sani cewa na ziyarci bokaye da dama kuma sun tabbatar min dacewa zaka samu daukaka anan gaba. Da wannan furuci nake maka sallama sai ka je ka kwanta ka rintsa muga abinda zai faru dakai gobe, gama fadin hakan keda wuya sai hibru yaja kofar dakin ya rufe Imnal ya koma kan gadonsa ya kwanta. Tab! Gaskiya nima fa na fara tsorata da sha'anin soyayya dan haka zan ajiye dukkan wasu kalamaina na soyayya a wajen guda tunda ga jarumai ma masu dakakkiyar zuciya sun mutu a banza saboda tafarkin soyayya ballantana mu 🤔, amman dai wace irin shawara zaku bani shin na cigaba da soyayya ko kuma na hakura da ita gudun kada abinda ya faru da mazan jiya ya faru da ni. Shin kana bukatar wani littafi na yaki kawai tuntubeni ta wannan Number ko kuma kayi mani magana da profile dina 08138873799. Zan ci gaba. MAZAN JIYA Littafi Na Daya (1) Part D Marubuci: Abdulaziz Sani M/Gini Typing: Abubakar Saleh AlQuyraemey Al'amarin sarki hibru kuwa tunda duku dukun safiya ya shirya abincin kalaci ya shiga dakin imnal sai ya iske shi acikin mafarki har yana surutai a fili, ba komai yake ambato ba face sunan gimbiya Mulaifa yana fadan kalamomin soyayya. Hibru ya daki kafar imnal yana mai daka mishi tsawa yace mai kakeyi har yanzu baka tashi ba, to kasani saura kiris mu makara zuwa fada, kashirya ka sameni a falo muyi kalaci, gama fadin hakan keda wuya sai hibru ya juya ya fita, shiko imnal sai yayi sauri ya kimtsa ya riski hibru a falo sukayi kalace sannan suka fita kofar gida domin su tafi izuwa fada. Da fitowarsu sai hibru ya shiga cikin bsuma ya kamo dokinsa da nufin su hau tunda na imnal baya nan, har sun yunkara zasu hau sai imnal ya hango nashi dokin ya tafo da gudu shi kadai, cikin gaggawa imnal ya rugo ya riske shi kawai sai yaga wasika a karkashin siddin dokin cikin zafin nama ya zare wasikar ya boyeta acikin rigar sa saboda kar hibru ya gani, nan take imnal ya hau kan dokin shi shima hibru hau kan nashi suka tafi fada. Fada ta cika makil babu abunda mutum zai gani sai kawunan bil'adama lokacin da hibru da imnal suka shigo cikin fadan kowa ya gama halatta har sarki kuwa sai da yazo, kuma a wannnan lokaci shi ake jira a hankali suka cigaba da tafiya bisa kafafunsu suka durfafi inda sarki yake. Sarki maharaz da gimbiya Mulaifa na zanne sun zubawa su hibru idanu shi dai sarki maharaz fuskar sa acike takeda murmushi amma na mugunta ita kuwa gimbiya Mulaifa fuskarta acike take da tsananin damuwa kamar zata fashe da kuka. Koda hibru da imnal suka zo dab da karagar sarki sai suka zube kasa suka kwashi gaisuwa. Sarki maharaz ya amsa gaisuwan cikin murmushi yana mai kauda kai ga kallon su kawai saiya dubi wadansu karti biyu majiya karfi da suke tsaye a gefe daya yayi musu inkiyar su cika aikin su, nan take kartin biyu suka kama imnal suka daure shi ajikin wani murtukeken ice mai gwafa dake kasa sannan sai suka yayyage rigar jikin imnal da karfin tsiya suka daga murtukeken icen sama suka soke shi acikin rami mai zurfi saiga imnal a sama. Koda kammala haka sai sarki maharaz ya miki ya fiskanci gabadayan jama'ar da suke fadan yace yaku jama'ar darul mahabur, kamar yadda kuka sani fiye da shekaru talatin da suka gabata muna bautan mai girma darbuza a kasar nan, ba ataba samun wanda ya karya doka ba, sai a wannan karon da imnal dan hibru ya aikata wannan laifi kusani mai girma darbuza shiya yanke hukunci dakansa hukuncin kuwa shine za ayita shara masa bulala har sai fatar jikinsa da kwoilewa kuma ana zuba mishi gishiri acikin shi har sai ya suma. Ba za'a kunce shiba sai ya kwana, kuma babu ci babu sha har na tsawon kwana uku. Koda sarki maharaz yazo nan a zancensa sai gimbiya Mulaifa ta fashe da kuka ta kama rokon sarki maharaz da ayi wa imnal afuwa, sarki maharaz ya dakawa mulaifa tsawa yace kinaso nima nayi laifi ne ga mai girma darbuza, lallai ni mai biyayyane ga mai girma darbuza idan kikaga ba ayiwai imnal wannan hukuncin ba to tabbas bana nunfashi ne, nan take sarki maharaz ya sake duban karti guda biyu kawai sai suka daiki bulala da gishiri acikin wani katon kasko suka hau kan wani dogon munbari mai matattakala, Wanda yake dab da inda aka daure imnal suka fara cika aikinsu, yazama cewa daya ya fara zabgawa imnal bulala shi kuma dayan yana manna mishi gishiri a fatar jikinshi, maimakon jama'ah suji imnal na ihu da kuka sai sukaga ya kurawa gimbiya mulaifa idanu yana mai murmushi, ita kuma mulaifa in banda kuka babu abunda takeyi awannan lokaci a sannan jamma'ar dake wajen suka tabbatar da cewa akwai soyaya tsakanin imnal da gimbiya Mulaifa. Kafin ajima bayan imnal yayi kaca kaca da jini, komin rashin imanin mutum idan yaga yadda akewa imnal dolene ya tausaya mishi, lokacin da Mulaifa taga azabar da akewa imnal ta wuce ta hankali sai ta mike zumbur ta ruga izuwa gidan sarauta kash!! inda gimbiya Mulaifa tasan muhimmancin zamanta awajen da bazata tashiba domin kallon fuskarta da imnal keyi shi ya hana shi jin zafin azaban da akeyi mishi, aiko tana shigewa gidan sarauta imnal yaji tamkar numfashinsa zai dauke sbd azaba amma saboda juriya da jarumtaka saida imnal ya shafe sa'a uku acikin wannan hali sannan ya suma, duk abinda ke faruwa sarki yaki hibru na tsaye a gefe yana kallo yana murmushi tamkar zuciyar sa bata sosuwa akan abinda ke faruwa, a badine zuciyar hibru a tafasa take kamar zata kone saboda takaicin da bakin cikin ganin yadda sarki ya rufe Ido yake horar da dansa, babban takaicin dake damunshi shine yasha bakar wahala awajen taimakon sarki maharaz harma ya kusa rasa ranshi a lokacin da sarki maharaz yake neman haihuwa ruwa ajallo yau gashi sarki bai damu danashi danba. hibru ya tambayi kanshi wai menene amfanin biyayyar dana kewa sarki, akan wani dalili zan cigaba dayin bauta ga Wanda baisan halacci ba, na kubutar da rayuwar yar shi amma shi gashi yana so ya salwantar da dana hakika lokaci yayi dazan daina wannan bauta a yayin da muka bar gida don tafiya wannan gagarumin yakin, adaidai wannan lokacin da sadauki hibru yazo nan azancensa imnal ya suma saboda azabar da'ake masa. Koda kartin biyu sukaga ya suma sai suka daina masa azaban suka sauko daga mumbarin a sannan ne sarki maharaz ya sake mikewa cikin farin ciki yace yanzu mun cika umarnin mai girma darbuza hankali ya kwanta dan haka da sallami kowa, shiko mai laifi za'a bar dakaru masu tsaronsa don karwani yakawo masa dauki lallai ahaka zai kwana uku batare daci ko shaba koda gama sai sarki ya juya da nufin ya shiga gidan sarauta kawai saiya hada idanu da sarki yaki hibru nan take maharaz yaji zuciyar shi ta buga da karfi, bakomai ne haddasa haka ban face tunda sarki maharaz suke tare da hibru bai taba ganin ya harare shiba sai ayau bayan shigar sarki maharaz cikin gidan sarauta fada ta watse babu kowa face and wadansu dakaru 300 wadda suke tsaron imnal. Shiko hibru saiya tafi can nesa kadan da filin fadan yayi sumfuda ya zauna inda yana iya hango imnal, nan fah hibru ya shiga sakar zuci wata zuciyar tace dashi ya afkawa wayennan dakarun dake tsaron imnal ya kashe su sannan ya kunce imnal ya tafi dashi in yaso subar kasar gabadayan su, wata zuciyar kuma sai tace dashi ai bai kamata yayi hakan ba tunda shima yayi imani da darbuza zaifi kyau ya bari sai antafi yaki sannan sukama gabansu haka dai hibru ya cigabada zancen zuci ya kulla wannan ya kunce wancan har yamma tayi likis bai gusa daga inda yake zaune ba kuma bai nemi abinci koh abin sha ba har dare ya raba hibru nanan zaune a inda yake bai gusa ba cikin halin damuwa da bakin ciki kuma koh alamar bacci a idanunsa babu a lokacin ne hibru yaji tsani sarki maharaz da darbuza domin baiga amfanin biyayyar dayake mishi ba. Adaidai wannan lokacin ne iska mai sanyi ta soma kadawa wadda ta zoma sanadin farfadowar imnal daga doguwar suman da yayi, imnal ya bude idanunsa da kyar yana gani dishi-dishi sai kawai yaji wata irin izababbiyar ishirwa nan fah ya fara kiran ruwa! ruwa!! tun yana fadi a hankali harya bude makokoron sa yana fadi da karfi koda hibru ya jiyo sautin muryar imnal yana kiran ruwa saiya mike zumbur a firgice ya lalubi sulkar sa ya yunkura da sauri da nufin ya ruga zuwa inda imnal yake kawai sai yaga matarsa wato marigayiya mahaifiyar imnal ta bayyana a gabansa cikin tsananin tsoro hibru ya fadi kasa ya kama ja da baya yana mai nunata da dan yatsa yana karkarwa. Koda ganin haka sai marigayiyar ta dube shi cikin murmushi tace kwantar da hankalin ka yakai sadaukin zamani kayi sani cewa niba matarka bace na kasance cikin jinsin aljanu sunana luzaira yar salbas, nazone gareka acikin suffar matarka domin nasamu damar hanaka abinda kake son yi domin idan ka kaiwa imnal agaji wannan lokaci tamkar ka ruguza cigaban rayuwar sane, cikin rashin yadda hibru ya dubi luzaira yace ta yaya zan yarda dake kuma akan wani dalili zaki min wannan taimako shin bakya ganin halin da dana yake ciki ne sakamon kishirwar dake addabarsa. Koda aljani luzaira taji wannan batu sai tayi murmushi tace duk irin wahalar da imnal zaisha bazai mutu ba bincike ya tabbatar da cewa danka zai girma ya shahara a duniya nan gaba lallai ya zamo wajibi ka yarda Dani idan har kana son ka cika burinka na rayuwa inko kaki acikin bautar sarki maharaz zaka mutu, ina sanar dakai cewa a duniya darbuza bashida wani makiya wadda yawuce ubana sarki salbas mai mulkin birnin Shulai a kullum suna farautar juna Kuma wannen so yake ya kama dayan su a raye domin samun sinadarin da zasu cika burinsu, nazone sbd mu taimaki juna zan taimake ku kusamu yancin kanku daga sarki maharaz da aljani darbuza, ni kuma da taimakon kadai zan iya taimakawa mahaifina domin mu kama darbuza a raye sa'adda aljana luzaira taxo nan a zancen ta sai hibru ya sake rudewa kuma ya cika da mamaki yace yanzu kina nufin darbuzan da muke bautawa aljani ne kamarki? Luzaira tace ko shakka babu tace ai dayawan ku bil'adama mu kuke bautawa sbd kuna ganin munayin abunda ku bazaku iyaba hibru yayi ajiyar zuciya yace to yanxu tayaya zan iya taimakonki ke kuma tayaya zaki iya taimakona? Aljana luzaira tayi murmushi tace har abada bazaka taba kubuta daga cikin bautawa sarki maharaz ba sai an karya wani asiri daya maka shidai wannan asiri anyi shine silin gashin kirjinka guda daya kuma an bunne shine a cikin wata tsohuwa rijiya gaba-dubu (1000) dake can karkashin wani kogi dake birnin sin, itadai wannan rijiya duk duniya babu mahalukin dazai iya shigarta sai ni da abbana mu kadai, tabbas zanje na tono wannan asiri amma sai idan kayi alkwarin cewa zaka hada karfi da karfe dakai da danka imnal ku dauko takobin saiful lujara da mashin galilul haras da kuma hular lamsara kun bani su a hanuna, ina tabbatar maka dacewa bincikena ya nuna min cewa sarki dujalu da sarki maharaz bazasu iya dauko wayennan makaman ba amma kaida imnal zaku iya, lokacin da aljana luzaira tazo nan a zancen ta sai hankalin hibru ya dugunzuma daga can saiya dago kai ya dubi luzaira yace wato de yanxu bangare ukune suke son mallakar wayan nan kayan yaki na #mazan jiya bangare na farko shine sarki dujalu sai sarki maharaz sai na uku kuma keda abban ki, abinda na fahimta shine idan muka samu nasarar dauko wadannan makamai nida dana muka damka miki zaki rikesu ne amfanin kanki ke kadai koko zaki kaiwa abban ki? Kuma tambaya ta biyu agareki itane shin kina nufin mai girma darbuza bai san da zuwanki ba, kuma baisan duk abun dake faruwa tsakanin mu? yayin da aljana luzaira taji wadannan tambayoyi saita bushe da dariya sannan ta murtuke fuska tace yakai sadaukin zamani kayi sani cewa duk wani boka da amsa sunan sa bashida wani burin da yuce ya mallaki wadannan makamai na Mazan JIYA, karshe kuma batun aljani darbuza shin yana gani koh yana jin mu bai tasoba sbd idan yanada ikon ganina da banxo ba domin bazai taba bari nayi hulda dakuba. Sa'adda aljana luzaira taxo nan a zancen ta sai sadauki hibru yayi shiru yana tinani kansa a sunkuwe sannan ya dubi can inda ke daure a sama yaga ya sake suma na biyu, sai takaici da bakin ciki yasake mamaye zuciyar sa cikin karfin hali ya dubi aljana luzaira yace ki tafi sai bayan mun fito daga wannan yaki ki dawo izuwa gareni kiji amsar dazan baki idan zakizo kijo min acikin tsakar dare, koda fadin haka sai ya mike tsaye ya kwashe shimfidar sa ya nufi hanyar dazata kaishi gidan shi ko sau daya bai sake waiwayowaba balle yaga halin da imnal ke ciki. Bayan tafiyan hibru sai aljana luzaira ta tashi sama taje daidan fuskar imnal ta hura mishi iska a bakin ta wadda tasa gashin kansa ya tarwatse yana kadawa acikin iska tamkar ana guguwa mai karfi take imnal ya farfado yana mai ajiyar numfashi aiko yana bude idanun shi sai yayi arba da luzaira ta kura masa idanu tana murmushi babban abun mamaki shine duk ciwon dayakeji ajikinsa ya gushe haka yunwa da ishirwa ma duk sun gushe batare da fargabar komai ba imnal ya dubi aljana luzaira yace wacece ke? kuma menene ya kawoki wajena? ina mai rokonki da kadakiyi kokarin fitar dani daga cikin wannan halin danake ciki. Koda jin haka sai aljana luzaira ta bushe da dariya ta tankwashe kafafunta tamkar tana zaune a kasa bisa buzu ta fiskanci imnal sosai sannan tace yakai jarumin gobe kayi sani cewa lbrn yana tsawo amma idan kanaso kasan ni wacece ka tambayi abbanka bayan ka kubuta ka tambayeshi lallai ni mai amfani ne ga cigabar rayuwar Ku ina mai yimaka sallama yakai jarumin gobe sai gani na biyu in mun sake saduwa, gama fadin hakan keda wuya sai aljana luzaira ta bace bat kaman bata wanzuwaba awajen. Bayan Kwanaki uku fadar sarki maharaz ta cika ta batse bakomai ne ya haddasa haka ba face ayau ne za'a dugunzuma bakidaya dakarun birnin dana sauran kasashe makwabta wadanda aka gayyato saboda yin gagarumar tafiya izuwa kogin bahar sufiya don dauko takobin Saiful lujara saboda yawan jama'ah da kyar sadauki hibru ya kutsa ta cikin jama'ah ya isa inda aka daure imnal da zuwa sai ya iske imnal lafiya kalau acikin hayyacin sa, kuma babu yunwa ko ishi atare dashi cikin hanzari hibru ya hau kan wannan dogon mumbari ya kunce igiyar data daure hannayen imnal sannan ya sabo shi a kafada ya sauko kasa, gabadaya dandazon jama'ar dake wajen suka zubawa hibru idanu duk inda yabi sai kaga ana darewa ana bashi hanya ana masa jinjina da kirari domin ansan yaune rana irin tasa wato ranan dazai jogaranci rundunar mayaka izuwa yaki, dayawa daga cikin mutanen garin sunyi bakin cikin hukuncin da aka yankewa imnal dan hibru kuma sun san cewa imnal gwarzon mayaki ne wanda ake takama dashi yanzu gashi raunata shi a lokacinkirari daza tafi yaki a lokacin da akewa hibru da dansa kirari ne sarki maharaz da yar sa suka fito daga gidan sarauta, nan fah kallo ya koma kansu kowa ya zuba musu ido cikin matukar mamaki bakomai ne ya haddasa mamakin ba sai ganin irin shigar da sarki maharaz yayi dakuma irin wacce mulaifa tayi dukansu sun sanya jajayen sulke sun rataye takuba a bayansu komai na jikin su jane hatta dawakansu kowa yasan sarki da mulaifa basu kasance mayaka ba amma ansan cewa sarki maharaz kasurgumin matsafi ne, lokacin da hibru ya isa inda dokin sa yake saiya zaunar da imnal a kasa ya jingina bayansa a jikin gini ya bude wata jaka ya fiddo da garin magani ya mika masa sannan yace karbi wannan ka shanye ya kai dana domin raunukan sudaina maka zogi, imnal ya dubi hibru cikin murmushi yace ya abbana ai babu inda yake min ciwo a jikina kuma ko kadan bana jin kishirwa da yunwa koda jin haka sai hibru ya dubi imnal cikin mamaki yace menene ya kawo maka agaji a tsakanin dare uku zuwa wayewar gari? Imnal yace wata aljana ce mai suffa wadda kasha kwatantamin data mahaifiyata kuma tazomin a cikin suffar mutane ba aljanu ba tace a wajen ka zan samu labarin ta wacece wannar aljana ya abbana? Hibru yayi ajiyar zuciya yace kabar wannan magana tukunna har sai bayan kasamu lafiya gama fadin hakan keda wuya sai hibru yaji an busa algeta alamar sarki ya tsaya a gaban jama'ah zaiyi bayani da hanzari hibru ya mike tsaye imnal ya riko hannun hibru yace shin gimbiya mulaifa ma tafito kodajin wannan sai hibru ya dubi imnal a fusace yace na rabaka da gimbiya mulaifa amma ka ki to kasani cewa idan ka kara min maganar ta ko kuma kanuna min kana kaunar ta zamu raba hanya yayin imnal yaji wannan batu sai idanunsa suka ciko da kwalla ya dubi hibru yace ka gafarceni yakai abbana naimaka alkawari daga yau bazan sake maka magar gimbiya ba kuma bazan sake nuna kauna agareta ba. Cikin farin ciki hibru ya sumbaci goshin imnal yace ubangijin daya halicci darbuza ya albarkace ka gama fadin haka keda wuya ya nufi inda karagar sarki take har saida yaje dab da sarki ya tsaya sarki ya dubi gabas da yamma, kudu da arewa a lokacin da filin fadar yayi tsit tamkar babu mai rai a wurin sannan yayi gyaran murya yace yaku jama'ar birnin darul mahabur tare da jama'ar sauran kasashe makwabta a wannan nahiya tamu ina mai yiwa kowa barka dazuwa fadata kuma ina gdy dakuka amsa gaiyatata domin nuna kishin kasar Ku dakuma dukiyar ku data jama'ar ku Kamar yadda kuka sani cewa gagarumar masifa da bala'i na tunkarar mu idan bamu fita wannan yaki ba ina mai kira agaremu damu jajirce iya karfin mu dan ganin munje mun riski babban abokin gabar mu a can tekun bahar sufiya domin hanashi dauko takobin saiful lujara a can ne zamu yake shi don tserar da rayuwar mu da jama'ar mu kafin yasami nasarar mallakan kayan yakin mazan jiya kamar yadda kuke gani a yanzu nida yata munyi gagarumar shigar yaki alhali bamu kasance mayaka ba ko sadaukai kuyi sani cewa ayau munfito ne da dukkan karfin sihirin mu don tunkarar masafi dujalu a halin yanzu na baiwa yata mulaifa dukkan sihirina na tsafi guda dari tara da casa'in da Tara(999) na cikon dubun ne ban bata ba SBD wani dalili mai karfi na bata wadannan sirruka ne sbd ta taimaka min awannan yakin domin abokan gabanmu yawansu ya wuce misali ina mai sanar daku cewa yanzu haka sarki dujalu tareda miliyoyin dakarunsa sunyi nisa a tafiyar su ta zuwa tekun bahar sufiya kuma suna amfani da alkaluman tsafi wajen gajarce nisan tafiya muma zamuyi amfani da namu sihirin don gajarce nisan tafiyan yanzu nabaiwa dukkan ninku sa'a daya daku gama kimtsawa domin sa'a dayar na cika hadiman zasu iso daga karshe ina mai kira ga sarki yaki na hibru bn imlas dayazo yanzu ya sameni a cikin dakin gani domin muyi tattaunawa na musamma akan yadda yaka mata mu bullo wa wannan yaki koda sarki maharaz maharaz yazo nan a zancen sa sai filin fadar nan ya rude da sowa. Nan de sarki maharaz ya kama hannun gimbiya mulaifa suka wuce izuwa cikin dakin gani shiko sadauki hibru saida ya koma wajen imnal ya sanar dashi cewa zaije wajen sarki su gana.. Kuyi haƙuri kwana biyu kun jini shiru ko, wallaahi laifin Hadejawa ne dan kawai munje bakunta garinsu sai bari dai nayi shiru da bakina🤔🤔🤔 Shin kana bukatar wani littafi na yaki kawai tuntubeni ta wannan Number ko kuma kayi mani magana da profile dina 08138873799. MAZAN JIYA Littafi Na Daya (1) Part E Marubuci: Abdulaziz Sani M/Gini Typing: Abubakar Saleh AlQuyraemey Lokaci da hibru ya shiga dakin gani sai ya cika da tsananin mamaki domin sarki Maharaz kawai ya gani da gimbiya Mulaifa babu sauran yan majalisa, kuma maimakon yaga sarki akan kujerar daya saba zama akai sai yaganshi a kasa bama akan kujara ba, ita Mulaifa a dab dashi, koda hibru ya hada idanu da sarki sai yaga idanunsa acike suke da kwalla, al'amarin da yayi matukar girgiza hibru kenan, ya karasa gurin su sarki Maharaz jikinsa a sanyaye shima saiya zauna a kasa suka fuskanci juna, maganar farko da ta fito daga bakin sarki Maharaz itace yaya jikin Dana imnal? Kodajin wannan tambaya sai ran hibru ya baci bai san sa'adda ya dubi sarki a fusace ba yace ya shugabana kayi magana akan abun dayake gaban mu amma ba batun imnal ba, Yace domin ina ganin bashida wani amfani a wannan yakin da zamu je, mu barshi anan gida saboda yayi jinyar jikinsa. Koda gama fadan haka sai Hibru yaga hawaye ya zubo daga cikin idanun sarki Maharaz cikin razani Hibru yace ka gafarceni yakai shugabana idan har wannan furuci nawa ya kona maka rai. Koda jin haka sai sarki Maharaz ya tsam daga inda gimbiya Mulaifa ke zaune sannan ya dawo dab da Hibru ya dafa kafadunsa suka kurawa juna ido sannan yace yakai babban aminina kuma abokina, ayau ina mai neman gafara agareka duk abin dakaga nayi maka ko nayi ma danka ba'a kan kiyayya bane sai domin soyayya da kuma bin umarnin mai girma darbuza dana marigayi sarki hubaru, a halin yanzu baka kaunata acikin zuciyar ka, yakai abokina kayi tinani zuwa shekarun baya da suka gabata tun sa'adda muna yara kanana kawo izuwa girman mu da yadda akayi nazamo sarkin birnin nan da kuma yadda akayi kazamo sarkin yakina, lallai ayau ne zan fada maka wani sirri daban taba gaya maka shiba, amma sai bayan ka bawa Mulaifa labarin rayuwar mu ta baya da yadda akayi na auri mahaifiyarta, da kuma yadda na shiga tashin hankali bisa rashin samun haihuwa. Lokacin da sarki Maharaz yazo nan a zancensa sai idanun Hibru suka cika sharkaf da hawaye ya dubi Mulaifa cikin tsananin tausayi yace yake 'yarmu ki saurara da kyau kiji wannan labari mai dauke da dimbin abun tausayi da ban alajabi, kuma kisan irin dangartakar dake tsakani na da mahaifinki. Koda jin haka sai Mulaifa ta tattara hankalinta waje daya ta kurawa Hibru idanu. Shi kuma saiya shiga bata labari kamar haka "A wasu shekarun baya da suka gabata zamanin da sarki Ruzba ke mulki a wannan birni Darul Mahabur, nida mahaifinki mun kasance fadawan sarki ruzba wadanda aikin mu kawai tsaron lafiyar sarki, duk inda sarki zaije muna tare dashi kuma ko kuda bama bari ya sauka a jikinsa, mahaifin sarki ya kasance kasurgumin matsafi dan haka ya gaji tsafi kuma ya shahara, bisa wannan dama daya samune sarki ya zabe shi acikin dakaru masu tsaron lafiyar sa, niko mahaifina shine sarkin yaki birnin Darul Mahabur, a wannan lokaci tsufa ya riske shi har yakai baya iya fita yaƙi, awannan lokaci ban wuce shekaru sha biyar ba don haka ni nake wakiltar mahaifina a yakuna, sau uku muna tseratar da rayuwar sarki ruzba a lokacin da wani babban abokin gabarsa yake kawo masa hari don ya halaka shi, hari na farko a wani yammaci ne da sarki ruzba ya fita rangadi izuwa bayan gari inda muka shiga wani daji da ake kira Furuz, a rayuwar sarki ruzba babu abunda yake sha'awa kamar yin suu acikin kogi kuma dakan shi yakan shiga kogi yayi kamun kifi. Acikin dajin Furuz akwai wani babban kogi da ake kira bahar zur, shidai wannan kogi yana da girman gaske da muggan halittun ruwa a cikin sa, lokacin da mukazo zamu gifta ta gaban kogin tare da tawagar mu, sai sarki ruzba yace a tsaya a bakin kogin. Kodajin haka sai hankalin dakarun mu ya dugunzuma domin sun san halin sarki zai iya cewa sai an shiga cikin kogin yayi suuu. Nida maharaz ne kawai hankulanmu basu tashiba domin mun yarda da kanmu, kawai sai sarki ya dubeni ya dubi maharaz yace inaso na shiga cikin kogin nan nayi suuu. Don haka sai Ku biyoni ciki domin nasan cewa Ku kadai ne zaku iya biyoni. Nan take sarki ya sauko daga kan dokin sa ya dauki fatsarsa ya fada cikin kogi, cikin sauri nida maharaz muka bishi. A duk dakika biyar sai Maharaz ya dubi hannunsa domin ajiki yake ganin abinda ke karkashin kogin, da zarar yaga wani mugun abu ya tafo inda sarki yake saiya sanar dani sai nayi nitso a kasa na tarar da abun komai hazarinsa na kashe shi, acikin abinda bai kai rabin sa'a ba na kashe manyan kadodi biyar saida sarki ruzba ya shafe sa'a guda amma ko kifi daya bai kama ba, har ya hakuri da nufin ya daina ya fita da cikin kogin sai yaji fatsar sa tayi nauyi matuka ta yadda bazai iya dago taba, cikin mamaki ya dubi Maharaz yace yakai boka dan boka wai shin wani irin kifine na kamo mai girma da nauyi da har na kasa dago shi sama? Maharaz ya dubi tafin hanunsa yaga babu komai acikin fatsar cikin kaduwa da zaro idanu maharaz ya dubi sarki yace nikam banga komai acikin fatsar nan ba, tabbas muna cikin tashin hankali, duk yadda akayi wani abune mai mugun sihiri ya shiga fatsar ka, kafin ni koh sarki ruzba muce wani abu sai mukaga an fisgi sarki ruzba anyi kasa dashi izuwa karkashin kogin, ba shiri muma mukayi nitso izuwa karshin kogin, kawai sai mukayi arba dawani wani katon mutum ya shake sarki ruzba da hannu biyu har sarki ya fara kakarin mutuwa, cikin zafin nama na kafa hannayen wannan maridi na fara kokarin banbaresu daga wuyan sarki, nan kwanjin maridin ya kumbura idanun sarki ruzba sun kumbura ga kuma rashin numfashi shima Maharaz yana kokarin kashe maridin da karfin tsafi, amma duk abinda ya watsa mishi basa tasiri, kawai sai maridin ya juya baya ya gabzawa Maharaz naushi a fuska take Maharaz ya sulela sumamme ya tafi izuwa karkashin ruwa. Al'amarin daya dugunzuma hankalina kenan na tattara karfina gabadaya na gabzawa maridin naushi a kunnensa na hagu, sbd karfin naushin saida jini yayi tsartuwa ta kunnensa na hagu, ba shiri ya saki wuyan sarki ya kwarara ihu cikin zafin nama na kamo sarki ruzba sannan nayi kasa na kamo Maharaz sannan nayiyo sama, kafin maridin ya dawo hayyacinsa tuni na fito dasu bakin kogin muka zube wanwar a gabar kogin duk mu ukun muna cikin mugun hali, ni ina numfashi sama sama Sarki da Maharaz kuwa duk a sume suke, cikin gaggawa aka shiga yi musu fifita. Koda na mike tsaye sai naga wannan basamuden katon yayi fitar burgu tamkar an chillo shi daga cikin baka, take ya dira akan turba ya tsaya kyam kawai yana murmushi, har asannan jini na diga daga kunnensa, koda sauran dakaru sukayi arba dashi sai suka razana suka dinga fantamawa cikin daji, mutumin ya dubeni ya bushe da mahaukaciyar dariya wadda amsa kuwarta ya cika dajin, daga can sai murtuke fuska cikin kakkausar murya yace kai yaro kayi kuskure da kake zaton cewa zaka kare sarki ruzba, tabbas sai nayiwa sarki ruzba kisan wulakanci a gabanka kuma kaima sai nayi filla filla da sassan jikinka.. Kodajin wannan batu sai zuciyata ta kekashe gabarin tsoro na dubeshi a fusace nace karyarka tasha karya yakai wannan azzalumi, kai waye dakake tinanin zakayi mana kisan gilla. Maridin ya sake bushewa da dariya a karo na biyu sannan yace sunana Gilzam sadaukin sadaukai na maridan duniya, musamman sarki darbuza na birnin kailus ya dauko hayata domin na kashe sarki Hubru ayau, bisa yarjejeniya aduk kwanaki bakwai zai dinga bamu mutum dari nida iyalina muna cinyewa, domin naman mutane ne abincin mu, babu wani bala'i dazai hanani kashe sarki hubru ayanzu, idan kuma kuna gani zaku iya toh ku jaraba. Kafin na bude baki nace wani abu tuni gilzam ya zare wadansu zabga zabgan takubba guda biyu ya durfafo mu, girman kowace takobi ya wuce misali, nauyin ta kuwa saidai karti ashirin su dauka, dama tuni jikin sarki hubru dana Maharaz ya fara karkarwa sbd tsananin razanar da sukayi bisa ganin gilzam da kalamansa, amma sbd tsabar tsoro sun kasa mikewa ma su gudu. Cikin matukar karfin hali na zare tawa takobin na tunkari gilzam duk dayake ni kaina nasani gilzam yafi karfina nesa ba kusaba amma saina tari aradu daka... Gilzam ya nufo kaina gadam gadam nima na nufeshi acikin dakewar zuciya, takun sawun gilzam tamkar na toron giwa ne amma hakan batasa na razana ba, koda muka hadu ya kawo min wawan sara da takuba biyu da nufin ya fille min kai da kafafu saina goce da dukkan zafin nama na, takobin farko saita samu wata bishiyar dibino mai tsawo take bishiyar ta rabe gida biyu ta ratattake akasa, takobi ta biyu kuwa sai ta karci kasa, nan take ta haifar da girgizar kasa da zabtarewar ta, koda ganin faruwa wannan alamari sai hankalina ya dugunzuma na tabbatar dacewa yaufa na gamu da gamona. Sarki Hubaru da Maharaz kuwa sai suka sake tsurewa domin sun gama saduda sun san mutuwa tazo, niko danaga haka ban karaya ba sai na dada durfafan gilzam, shi kansa gilzam yayi mamaki dan bai taba haduwa da mutumin dabai taba razana akan shiba sai ni, abinda yafi daure mashi kaima shine na kasance yaro mai kuruciwa dan shekaru goma sha, cikin matukar fusata gilzam ya tasomin da dukkan karfin sa yana mai kawomin sara da suka da muggan makaman sa, nikuma ina gocewa amma ko kadan na gagara maida martani saboda karfin harinsa da zafin namansa ya ninka nawa, kaini kaina nayi mamakin yadda ma nake gocewa harinsa nan gilzam ya tashi hankalin dajin gabadaya ya haddasa kamawar wuta da girgixar kasa. Sai da muka shafe sa'a guda cif nida gilzam muna fafatawa shi baisami nasarar hallakani ba balle ya koma Kansu sarki hubru. Bayan ansamu sa'a gudan ne naji na fara gajiya, shiko Gilzam kamar a lokacin nema ya fara gumurzun, alamarin daya dugunzuma hankalina kenan na tabbatar dacewa saura kiris tawa ta kare. kwatsam! sai muka jiyo kururuwan mazaje daga bayan mu cikin sauri muka waiga sai naga ashe dakarun da muka fito rangadi dasune sukaje suna neman daukin sauran dakarun darul mahabur, sama da mutum miliyan biyu ne suka durfafo mu suna ihu da karaji, karar sukuwar dawakan suma kawai ta isa ta razana mutum ya dauka yakin duniya akeyi. Koda Gilzam ya hango wannan runduna ta durfafo shi sai yayi murmushi ya ruga garesu, tun gabanin su riske shi. Kaico!! yayin da Gilzam ya ratsa ta cikin dakarun saiya dinga zubar dasu tamkar yana shara, sai dai kaga takobinsa na datsa mutane tana raba dawakansu gida biyu, nanfa ya bude kasuwar daukar rai sai hangowa nayi jini na tsartuwa yana malala akasa, kafin na ankara tini gilzam ya kashe sama da dakaru miliyan daya da rabi da dawakansu. Ko da na hango wannan barna saina fusata ainun na falfala da matsanacin gudu Irin wadda bantaba yin irinsa ba, domin har ji nake kamar zantashi sama, na nufi inda gilzam yake wannan barna, yayin daya rage saura taku uku na isa gareshi sai na daka tsalle sama na sauka akan wuyansa, kafin yasa takobinsa ya kadoni tuni na soka masa wuka a kunnensa na hagu take wukar ta lume acikin kunnensa ya bullo ta daya kunnen. Gilzam ya kwarara uban ihu alokacin da jini yake shatata daga cikin kunnensa kawai sai yasa hannunsa guda ya kawomin wawura, niko na goce amma saida ya chakumo rigata, sai kawai ya cillani sama saida nayi tafiyar taku dari a sama sannan na maku akan wata bishiya na fado kasa a matukar galabaice, awannan lokacin ne naji Gilzam yana kururuwa mai matukar razanarwa bashiri sauran dakarun dabasu mutuba suka farfado sukayita faduwa daga kan dawakansu saida gilzam ya shafe dakika dari da arba'in yana kururuwa kuma yana kokarin zare wannan wuka dake cikin kunnensa amma ya kasa, daga can sai akaji yayi tsitt kuma sai ya sulale kasa ya durkushe bisa guiyoyin sa ya kame tamkar gunki, wato yayi mutuwa irin ta manyan mazaje. Koda ganin haka sai sarki hubru ya mike zumbur ya rugo da gudu zuwa inda nake kwance ya tasheni zaune ya rungumeni yana mai tsananin farin ciki da godiya a gareni. A iya rayuwar mu nida maharaz bamu taba shiga cikin harabar gidan sarautaba kullum saidai mujira sarki inya isa fada sannan mukuma aikin muna tsaron lafiyarsa amma awannan rana saida sarki hubru ya shigar damu har cikin turakarshi inda muka zamo yan kauye muka dinga kalle kalle. Nan take yasa aka kawo mana abinci da abun sha iri-iri wato dai ya shirya mana walima saboda farin cikin mun ceto rayuwarsa muna cikin more walimar ne muka hango abinda yasa muka tsaya cak gabarin ci da sha, duk gabadayan mu muka kame tamkar babu mai rai acikin mu. A lokacin da muka kame kamar babu rai ajikin mu bawani abu muka gani ba face wata kyakkyawar mace ta gaban kwatance ta nufo mu tana sanye da doguwar riga, wadda aka yiwa ado da zinare shekarunta basu haura goma sha uku ba, koda sarki ya hango wannan kyakkyawar budurwa saiya mike da sauri yaje ya taro ta sannan ya kariso da ita ya zaunar da ita abisa kujerar datake fuskartar tamu nida maharaz muka kura mata idanu muka kasa kauda kai har saida sarki hubru ya tabo mu muka dawo hayyacin mu kyakkyawar bata kalli daya daga cikin muba saita sunkuyar dakai tana mai murmushi kawai. Sarki hubru yayi gyaran murya yace yaku amintattun dakaru na kuyi sani cewa tunda na zama sarki awannan birnin babu wani da na miji da ya taba shigowa har cikin turaka ta sai ku, saboda muhimmanci aikin daku kayi min ayau dinnan na ceton rayuwata daga sharrin babban abokin gabata wato sarki dumbazu na birnin Kailus. Wannan kyakkyawar budurwar da kuke gani a gabanku 'yatace ta cikina, sunanta Sahira, tunda aka haifeta bata taba fitowa daga harabar gidan nan ba, kuma jama'ar gari basu san an haifeta ba, kai hatta hadiman cikin gidan nan basu san da haifuwarta ba kune mutane na farko da ta fara gani a rayuwarta banda nida mahaifiyarta. Tuntuni bincike awajen bokaye na ya tabbatar min dacewa, acikin bayina zan samu mutum biyu zarata wadda zasu kareni daga sharrin makiya, kuma daya daga cikinsu zai gaji sarauta ta, dayan kuma zai auri wannan kyakkyawar yata, kusani cewa ba'a son raina hakan zai faru ba, kuma banaso ace wani ya auri Yata wanda ba basarake ba amma babu yadda zanyi kaddara tariga fata. Koda sarki yazo nan a zancensa sai hawaye ya zubo masa sannan ya cigaba bayani... To nima jin wannan kalamai na Sarki Hubaru yasa nayi kikam Kasancewar na kamu da soyayyar Gimbiya Sahira kuma naji yana ikirarin ba zai bazai baiwa talaka yarsa ba 😢😢😢 Shin kana bukatar wani littafi na yaki kawai tuntubeni ta wannan Number ko kuma kayi mani magana da profile dina 08138873799. Koda sarki yazo nan a zancensa sai hawaye ya zubo masa sannan ya cigaba bayani inaso kusani cewa a duniyar nan babu abinda nakeso sama da yata sahira, to amma inaji ina gani zan rabu da ita domin bincike ya tabbatar min dacewa rayuwata gajeriyace abune mawuyaci na kara shekara biyar nan gaba a duniya, daga yau na damka muka sahira a hannunku na sani cewa a halin yanzu duk biyun kun kamu da kaunar sahira, to amma fa kusani cewa dole daya daga cikin ku ya hakura yabarwa dayan wadda duk ya auri sahira acikin ku bazai tabayin sarauta ba kuma zai sota samada komai a rayuwar sa, kuma saita rigashi mutuwa wanda yarasa sahira acikin ku shine zai gaji sarauta ta kuma zaiyi tsawon rai a rayuwarsa har yabar duniya haihuwa daya zaiyi sannan ya mutu yabar abunda ya haifa, babu wani tsafi ko wani kokari dazai sauya wannan kaddara akan mu inaso ku kwantar da hankalinku akan fitar da zuciyoyin ku bisa samun mulki koh auren yata domin lokacin ne zai banbanta komai da wannan kalami nake muku sallama daku tashi kutafi gidajen ku amma kafin sannan akwai kyauta ta mussamman yacce zan baku koda gama fadin haka sai sarki hubru ya dubi yarsa gimbiya sahira yace jeki ki dauko musu kyautarsu cikin fara'a sahira ta mike tsaye ta shiga wani daki tana tafiyar kasaita tamkar dawisu jim kadan sai gata tafito da wadansu jakukkunan fata guda biyu sahira ta matso gabanmu tabawa kowa jaka guda koda muka karba muka bude ashe zinare ne acike makil nan take muka zube kasa muna gdy sarki hubru ko kallon mu baiyiba saiya kama hannun gimbiya sahira yashige da ita izuwa cikin wannan dakin data dauko kudin shigewarsa keda wuya sai maharaz ya rude ya rikice sbd ganin wadannan kudade niko sai naji sam kudin basu dameni niba. Daga wannan rana wani abu sake faruwa ba sai bayan kwanaki goma sha bakwai da wata safiya sa'adda tafiya takama Sarki hubru izuwa wani kauwe da ake kira zumur domin yaje ya dubo wani tsohon abokinsa wadda ya kwanta ciwo tsawon wata uku, shidai wannan aboki na Sarki Hibru sunan sa abul husnu, kuma tun kuruciwa suka taso da sarki hubru abinda yasa yayi zamansa a zumur shine ya samu nasibi matuka a harkokin kasuwanci domin mutanen garin suna matukar kaunarsa sbd yawan taimakon sa da kuma kyautatawa ga talakawa, akarshe ma saida suka matsa mishi ya karbi shugaban cin birnin Sarki hubru ne dakanshi yazo ya nada shi a matsayin shugaban birnin akaxo akayi gagarumin biki bayan wata daya dayin bikin ne ciwo mai tsanani ya kama abul husuna lokacin da lbr ya riski sarki hubru sai hankalinsa ya dugunzuma aka nemi likitoti suyi masa magani saida likitoci sukai kwana goma suna lura da abul husuna basu gane irin cutar datake damunsa ba, bisa dole duka debi nasu da nasu sukaje suka sanarwa sarki hubru halin da ake ciki dajin bayanin likitocin sai hankalin Sarki ya kara dugunzuma akan hanyane sarki hubru ya tafi wajen wani amintaccen bokansa ya sanarda dashi halin da ake ciki, nan take bokan yayi bincike nan take yayi murmushi ya duvi Sarki yace ai wannan cuta ta abokin ka sharrin sihiri ne ba wani bane yayiwa abul husuna asiri sai tsohon shugaban kauyen zuhur sbd bakin cikin an sauke shi daga mukaminsa andaura abul husuna, shi dai wannan asiri an bunne shine a kofar gidan abul husuna. Abul husuna bazai taba warkewaba sai an tono asirin kuma idan an tonoshi take wanda yayishi zai mutu babu mai iya tono wannan asiri sai Sarki mai karfin mulki kamarka. Ya shugaba yazama dole kaje dakan ka kaje ka tono wannan asiri amma kada kaje sai randa asirin ya cika kwana casa'in da binnewa domin idan ka tonoshi kafin cikar kwana casa'in da wanda yayi asirin da wanda aka yiwa duk mutuwa zasuyi. Lokacin da bokan yaxonan azancen sa sai sarki hubru ya cika da mamaki daga can kuma sai ya dubi bokan yace toh yanzu idan naje kofar gidan abul husuna yaza'ayi nagane daidai inda aka bunne asirin boka yayi murmushi yace dazarar kaje kofar gidan kadaga kwagirinka na sarauta sama kasake shi, a duk inda kwagirin ya fado to daidai wajen zaka saka a tone kodajin wannan batu sai sarki hubru yadauko dukiya mai yawa yabawa bokan nasa yana mai matukar farin ciki sannan sukayi sallama sarki ya tafi gida. A ranar da abul husuna ya cika kwana casa'in a kwance yana jinya mukayi shiri tareda dakaru dubu arba'in muka tafi kauyen zumur saida mukaci rabin tafiya mun shigo cikin wata sahara inda babu gida gaba babu gida baya babu bishiyoyi ko duwatsu babu ruwa sai kawai mukaji wani irin tsananin zafi yana fesowa, nan da nan dawakanmu suka dimauce suka kama tutsu suna yada mahayan su suna fita da gudu wata irin gagarumar iska ta taso ta dinga daga mutane da dawakai suna yawo akan iska al'amarin daya dugunzuma hankalin kowa kenan keken dokin sarki maharaz saida ya rabu da kasa zaiyi sama kenan na rikoshi da karfin tsiya amma sai karfin iskar yafara rinjayata saida maharaz ya taimaka min sannan muka sauke shi kasa ni kaina inda badan maharaz ya taimaka min ba da tuni iska tayi sama dani munaji muna gani gagarumar iskar tayi sama da dukkanin abokan tafiyar mu tayita lulukawa dasu tun muna iya hango su har saida suka bace bat ya rage saura mu uku bisa turba wato ni da sarki hubaru wanda cikin keken doki bayan lafawar guguwar ne sarki hubaru ya fito daga cikin keken dokin ya tsaya a tsakiyar mu nan take na zare takobi na kama kallon gabas da yamma kudu da arewa ina jiran tsammani. Shiko maharaz sai yafara kallon tafin hannunsa yana karanta wadansu dalasiman tsafi faruwar hakan keda wuya sai mukaga wata katuwar inuwa ta lullube mu koda muka daga kawunan mu sama sai mukaga wata katuwar halitta tana saukowa daga sama mai tsananin muni da rashin son gani sannu ahankali halittar ta iso kasa-kasa yadda kana iya ganin cikakkiwar fuskarta koda mukayi arba da halittar sai duk mu ukun muka firgice ainun kamar zamu zabura da gudu dayake ita dai wannan halitta bakomai bace face wata sihirtarciyar dodanniya mai kawuna takwas kowani kanta guda girmansa yakaina katon dutse gabadaya kawunan takwas ajikin wuya daya yake shiko wuyan nata dogo ne har karawa kanshi tsayi yakeyi kamar yadda wuyan take kara tsawo haka hannayen tama ke kara tsawo ga dukkan alamu dai idanta mike hannunta guda daga inda take zata iya dauko abindake can bayan duniya daga kowace kusurwa kawai sai mukaga dodanniyar nan ta wangame bakinta guda ta kama gabadaya dakarun namun nan guda dubu arba'in harda dawakansu sunata zubowa kasa a mace anan tayita amarsu suna zubowa tamkar an dafa su acikin tukunya har tururin zafi ne ke fita daga jikinsu SBD tsananin zafin dake jikin dodanniyar bayan dodanniyar tagama amayarda abunda cikinta saita dube mu da idanunta kwala-kwala ta tuntsire da mahaukaciyar dariya maikama da saukar aradu, muka kara firgicewa muka hau kakumar junanmu lokaci guda ta turbune fuska tace kaicon yaku wadannan kananan halittu yau kun gamu da uwar dodannin duniya dayan ku bazai tsira daga bala'i naba duk saina zare muku ruhun numfashi, kuyi sani cewa sarki dumbazu na birnin kailas ne ya aikoni na hallaka sarki hubaru, labari ya riske ni cewa anturo gilzam kun hallaka shi to kusani cewa nina gagari dukkan sadaukan duniya da duk matsafan duniya, yau shekarata dubu tara ina tare mutane da aljanu a can dajin sarbusa ina cinyewa ankasa ganin bayana yanzu Sarki dumbazu yayi min alkawari cewa in dai na hallaka sarki hubaru zai dinga bani mutane dubu ina cinyewa basai nayi wahalar farautar suba, burina shine naci adadin mutane miliyan dubu saba'in a sannan ne zan iya haifan yayana wadanda bazasu bazama ko inaba a duniya sai sun cinye komai da kowa a kwana tara yazamana cewa babu wani abu mai rai a doron kasa saini dasu kawai. *********************** Mazan Jiya Part 11 #Cigaba Koda uwar dodanni tazo nan a zancen ta sai naji dukkan tsoro ya kau daga cikin zuciyata kawai saina dubi sarki hubru da maharaz nayi musu inkiya dasu fada cikin keken doki aikuwa sai sukayi wuf suka fada suka rufe kansu niko saina zare takobi na, na fuskanci uwar dodanni nace ai saiki fara gamawa dani kafin ki gamada sarki hubaru koh! nikaina nasan bakin rijiya yafi gaban wasan yara dan haka tsaurin ido kawai dakuma jarraba sa'a nayi amma ko kadan banasa ran cewa zan iya tabuka wani abu saidai nasan ance mai rai baya rasa motsi watakila nadan iya bata mata lokaci. Lokacin da uwar dodanni taji nayi wannan lafaji a gabanta saita sake bushewa da mahaukaciyar dariya a karo na biyu wadda har zaida walkiya tayita fita daga bakinta tartsatsin wuta yadinga fita cikin dacin rai da shammata ta mangareni da hannunta guda sbd karfin dukkan saida nayi sama na gwara baya ajikin wata bishiya ita kanta bishiyar saida ta tunbuko har jijiyoyin ta daga cikin karkashin kasa muka fadi kasa tare na baje wanwar a sume koh shurawa ban sake yiba azaton uwar dodanni kasusuwan bayana sun karye na mutu don haka saita zuro hannun ta a hankali ta balle kofar dakin keken dokin dasu sarki hubru ke ciki sukayi arba da fuskarta kawai saita kama musu dariya alamarin daya firgita su kenan mussan da suka hango a can gefe daya a kwance a mace ana cikin wannan haline na farfado akayi sa'a kuwa banyi yunkurin mikewa ba yadda hankalin uwar dodanni zai dawo kaina, a sannan ne tazuro hannun ta cikin keken dokin ta damko sarki hubru da maharaz tayi sama dasu da nufin takai kawunan cikin bakinta ta gutsure su kwatsam sai uwar dodanni taji motsi akan jelar ta abinda bata saniba shine nine na ruga na hau kan jelar naketa tsala matsanacin gudu domin na isa kan kafadarta kafin hannunta yakai bakinta, koda uwar dodanni taji motsin yana karuwa saita fara kai duka faruwar hakan ne tasa uwar dodanni tasamu jinkirin kai hannunta izuwa cikin bakinta ta gutsure kawunan su sarki hubaru koda taga motsin yaki karewa saita maida hankalinta wajen kai hannunta cikin bakinta guda saura kiris ta zuro kawunan su sarki hubaru a bakinta na iso kan kafadar ta aikuwa saina daka tsalle daga kan kafadarta nakaiwa hannunta sara wanda ke dauke dasu sarki hubaru take takobi na ya zabtare hannun nata ya fado kasa su hubaru suna cikin yankekken hannun nan kuwa ya kama tsartuwa da feshi daga cikin dulgul min hannun tamkar magudanar ruwa ta balle tsananin zafi da zogine da uwar dodanni tajine yasa tahaukace ta makance tahau kaiwa iska duka tana ruri da kururuwa mai tsananin firgitarwa, koda naga ta dimauce saina dinga saran sassan jikinta da takobina nikaina nayi mamakin yadda nasamu wannan nasara cikin gaggawa haka bayan sassan jikin uwar dodanni ya gama faduwa kasa sai sarki hubaru da maharaz suka fito daga cikin keken doki suka kuramin ido kawai suna mai matukar mamaki na sarki hubaru ya dube ni yace wai shin wannan yaro anya kuwa kai mutum ne tayaya kake yin wadan nan abubuwan alajabi wadanda sunwuce gaban tsammani. Koda jin haka sainayi murmushi na goge jinin dake jikin takobina na sumbaci takobin nace ya shugabana kaga wannan takobin inhar dai ina tare da ita bana shakkar tarar kowani irin bala'i asalinta ta kaka nane na uku indai kaga an cini da yaki to bana tarene takobin nan nayi imani da haka sarki hubaru ya kurawa takobin nawa ido dakyau ya girgiza kai baice komi ba. ayi hakuri da wannan zancigaba zuwa anjima. ********************** Mazan Jiya Part 12 #Cigaba A sannan ne muka dubi gawarwakin dakarun mu dake zube a kasa sai takaici ya turnuke mu bamu san sa'adda idanunmu suka ciko da kwalla ba nan take muka cinnawa gawarwakin wuta sannan muka hau keken dokin sarki hubru muka cigaba da tafiya har muka isa kauyen zumur bamu sake haduwa da wani tashin hankaliba kamar yadda bokan sarki hubru ya fadi haka alamura suka kasance da isarmu kofar gidan yadaga kwagirin sa na sarauta sannan ya sake shi ya fado kasa aiko sai kwagirin ya cake a karkashin kasa bai fadi kasa ba koda ganin haka sai sarki hubaru ya dubeni yace maza ka tone daidai inda kwagirin ya cake, nan take na cika umarni koda nayi rami mai zurfi kamu uku saiga wadansu layu ina fito dasu sai maharaz yayi nuni ga hannunsa akan layun take suka kone kurmus faruwar hakan keda wuya said juyo shewar mata acikin gidan take abul husuna ya fito daga cikin gida ya takawa da kafafunsa cikin koshin lafiya, koda yayi arba da sarki hubru sai yacika da tsananin farin ciki ya rugo gareshi suka rungumi juna abul husuna yace lale marhabin da aminina dama nayi mafarki zan warke daga wannan cuta a ranar daka kawomin ziyara. Koda jin haka sai sarki hubaru yayi murmushi yace aiko mafarkinka gaskiya ne tunda gashi ya tabbata nan take sarki hubaru yabawa abul husuna duk abunda yafaru tsakaninsa da bokansa akan rashin lafiyansa koda jin haka sai abul husuna ya cika da tsananin mamaki yace aiko shi makiyi bashida kama domin aduk fadin garin nan babu mai nuna min kauna samada tsohon shugaba ashe kaunar ta karyace da yaudara, rufe bakin abul husuna keda wuya saiga matar tsohon shugaban da yayan sa sun rugo da gudu suna kuka da zuwa sai suka zube a gaban abul husuna suka bada lbr cewa ga maigidan su can yayi wata irin mutuwa mai ban tsoro, koda jin haka sai sarki hubru ya dubesu yace kuje ku kone gawar maigidanku domin sharrin dayaso yayi abokina abul husuna ne ya koma kansa, koda jama'ah sukaji lafazin da sarki hubaru ya fada akan tsohon shugabansu sai duka hai tsine masa da murna akan muturwar sa, nan take abul husuna ya shigar damu cikin gidansa ya kaimu har izuwa turakarsa zaman mu keda wuya sai wata tsaleleliyar budurwa wadda muka gani tamkar hussainar gimbiya sahira ce sbd tsananin kyawu shi kansa sarki hubru baisan sa'adda ya kura mata idanu ba dan tsananin alajabi itadai wannan budurwa bambamcinta da sahira kawai tafita shekaru ne akalla zata girmeta kamar da shekaru biyu budurwa ta nufo mu da farantin abinci sannan ta durkusa har kasa ta gaisheda sarki hubru sannan muma ta gaishe mu sannan ta koma cikin gida har sarki hubaru ya bude baki zaice wani abu sai abul husuna yace kada kace komai yakai abokina wannan budurwa dakuka gani yata ce ta cikina sunanta husna kamar yadda ka boye yarka ga jama'ar kasar nan haka nima na boye tawa kuma bokan da yamaka bayanin cutata shine yasa na boye tawa yar kuma ya gayamun cewa duk ranar daka kawo min ziyara tare da matasa biyu masu tsaron lafiyar ka to acikin sune yata zata samu mijin aure sa'adda abul husuna yazo nan azancensa sai sarki hubaru ya cika da tsananin mamaki. Daga can sai sarki hubaru ya kallemu yace ku tashi ku fita inason ganawa da abokina. Haka muka tashi muka fice duk kuwa da cewa muna matukar jin yunwa kuma ga abinci mai rai da lafiya an kawo. Bayan fitarmu daga gidan Abul Husuna sai muka samu waje muka zauna muka yi shiru dayanmu bai ce uffan ba, daga can sai na dubi Maharaz nace da shi ya kai abokina nifa abubuwan nan dake faruwa da mu suna jefamu cikin rudani da rikittarwa, kaga dai ance dole a cikinmu ne daya zai auri Gimbiya Sahira sannan ance a cikin mune daya zai auri wannan budurwa Husuna, ina ganin tun yanzu ynaa da kyau kowanne daga cikinmu ya banbance zabinsa, kai yanzu a cikin yan matan nan biyu wacce ta kwanta maka a rai. Yayin da Maharaz ya ji wannan tambaya sai yayi murmushi yace ya kai abokina kayi sani cewa ai ni bani da zabi sai abinda ka zaba, dan kada na zabi wacce kake so a ranka, nikam duk wacce na samu babu matsala. Da jin wannan batu sai hankalin ya dugunzuma nace da shi a'a ba za a yi haka ba, inaso ka yi sani cewa idan ka auri gimbiya Sahira ba zaka yi arziki ba, kuma ba zaka yi sarauta ba, alhalin tun tasowarka baka da wani buri da ya wuce ka zama attajiri kuma ka yi sarauta, amman idan ka auri Husuna tabbas wannan burika naka zasu cika, saboda haka ka yarda ka auri Husuna ko dan ka cika wadannan urika naka. Koda Maharaz ya ji wannan batu sai ya rungumeni ya kuma fashe da kuka yana mai cewa lale maraba da abokin na gari wanda ke son ganin cikar burin abokinsa. Cikin kaduwa na janye jikin daga nasa muka fuskanci juna nace da shi "Ya kai abokina ina dalilin wannan kuka naka?" Maharaz ya sunkuyar da kansa kas y ce ban taba sanin cewa kana kaunata fiye da yadda kake kaunar kanka ba sai yau, tabbas ka dakusar da taka rayuwar dan daga tawa, tuni nima nayi bincike a wajen bokan mahaifina ya tabbatar mani da cewa kaine kadai zaka iya taimaka mani domin cimma burikana, idan kwa ka ki tofa sai dai na mutu a matsayin bawa, amman idan ka taimaka mani to kai zaka mutu ne a cikin bauta. Koda naji haka sai nayi murmushi nace na gwammace na mutu a cikin bauta muddin burinka zai cika, kuma nima nasan nawa burin zai cika tunda nasan zan gaji mahaifina sarautar Sarkin yaki. Maharaz yayi murmushi farin ciki sannan yace tabbas zaka gaji mahaifinka. Saida mukayi kwana biyu acikin kauyen zumur sannan mukayi shiri muka koma birnin darul mabur mu uku kacal, Sarki hubru bai yarda abul husuna yabamu yan rakiya ba mun isa gida lafiya amma sai muka iski wani babban abun bakin ciki wadda har izuwa karshen rayuwata bazan taba mantawa dashiba abunda muka iske shine tundaga komar gidan sarauta muka dinga arba da gawawwaki duk inda muka duba saidai muga jini na malala sai tarin gawa, a dimauce muka ruga izuwa gidan sarauta sarki hubru na kwalawa yarsa kira amma baiji ta amsaba gabadaya hadiman gidan ma babu wanda muka riska a raye a cikin turakar sarki hubru ne mukaga wata wasika akan gadonsa sarki hubru ya sunkuya yadauki wasikar, a lokacinda hannayen sa suke karkarwa cikin karfin hali yafara karanta wasikar kamar haka takarda daga sarki uban sarakai gwarzon sarki dodon mazaje wato sarki dumbazu na birnin kailus zuwaga kaskantaccen sarki mai taurin kai, babban abokin gabata hubru Ibn salkas ina mai sanar dakai cewa ruwa ba sa'ar kondo bane tabbas ina sama dakai, kodayake ka cancanci yabo domin yau shekara goma ina kokarin kasheka amma na kasa ayanzu na aiko gilzam da maridai yaranka sun hallaka su na turo uwar dodannin duniya itama sun hallakata toka sani zuciyar maza ta tafasa dan haka na taso dakaina na shigo har cikin masarautarka domin in halakaka da hanuna amma sai akayi rashin dace baka nan, abinda ya hanani na biyo bayanka shine binciken danayi a tsafi in nabiyoka ragas zanyi da yaranka, don hakane na yanke shawarar na dauke yarka sahira na tafi da ita izuwa fadata idan ka isa kai ubane mai son yarsa kazo har fadata ka karbi yarka idan bakazo ba zan yanke kan yarka na turo maka shi nan da kwanaki talatin idan kuma kana son yarka ta tsira toh kasa a yanko min kanka akawo min nan fadata koda sarki hubru yazo nan a karatun wasika saiya yanke jiki ya fadi a kasa sumamme. ********************* Mazan Jiya Part 13 #Cigaba A lokacin da sarki hubru ya fadi a kasa sume a dimauce muka rugo kansa munayi masa fifita sannan yadawo haiyacinsa koda ya bude idanunsa yayi arba damu saiya fashe da matsanacin kuka yana mai cewa narasa yata! narasa yata!! har abada, yaku wadannan mazajen fama na umarce ku daku gaggauta fille kaina sannan ku dauki kan kuje dashi wajen bokana shabulus Ibn mukaibar domin yabaku aljanin dazai iya kaiku fadar sarki dumbazu kafin cikar kwanaki talatin, lallai ku damka kaina ga sarki dumbazu domin yabaku yata sahira ku tafo da ita nan birnin darul mahabur. Sa'adda Sarki hubru yazo nan a zancensa sai tausayin sa yakama mu har idanuwan mu suka ciko da kwalla tsowon yan dakiku mukayi shiru bamuce komai ba kuma bamu birnin sarki hubru ba, koda ganin haka saiya daka mini tsawa yace shin bakuda kunne ne bakuji abunda nace ba, cikin tattausan harshe na dubi sarki hubru nace ya shugabana ai basai mun fille maka kai mun kaiwa sarki dumbazu ba inaso kabamu izini muje har can fadarsa mu yake shi mu kawar dashi, kuma mu dauko maka yarka mukawo maka ita nan fadar ka a cikin koshin lafiya. Koda jin wannan batu sai sarki hubru ya kwarara ihu ya tsalle ya tumu da kasa SBD tsananin fusata da tashin hankali har saida muka rikeshi yadawo cikin hayyacinsa saida kimanin dakiku dari uku da sittin suka shude sannan yayi ajiyar zuciya ya dubemu yace yaku manyan gobe inda kunsan masifar datake can fadar sarki dumbazu dakuma karfin sihirinsa da bakuce zakuje ku yakeshi ba ina tabbatar muku dacewa a halin yanzu kuma a wannan zamani duk duniya babu wani sadauki mai tsananin karfi tamkar sarki dumbazu kuma babu matsafin daya kaishi karfin tsafi hatta bokaye da aljanu shakkar sa sukeyi abinda yasa kukaga ya gagara hallakani a tsawon shekaru goma shine duk duniya babu wanda yasan sirrinsa sama dani kuma inada wani kambun tsafi wadda indai yana jikina dumbazu bazai taba haduwa daniba balle yasamu daman hallakani duk duniya mutum biyu ne rak masu irin wannan kambu daga ni sai shi sarki dumbazu asalin sarki dumbazu almajirin mahaifina ne shiko mahaifina gawurtaccen matsafine Wanda ya shahara a can wata kasa da ake kira mulubiya wato a takaice de niba dan asalin wannan birni bane yawon duniya ne yakawo ni nan har nasamu shiga awajen sarkin garin ya amintar dani harya aura min yarsa bayan ya mutu ne na hau karagar sa albarkacin wannan kambun tsafin da ubana yabani. Babban abinda ya haddasa gaba tsakanina da sarki dumbazu shine dumbazu yayi shekara ashirin yana yiwa ubana bauta har yasamu ya yarda dashi ya bashi sirrukan tsafi dayawa dumbazu yarike amanar amanar mahaifina hanu biyu har takai cewa mahaifina yadau keshi tamkar dan cikinsa don haka sai wata rana saiya kebe dashi cikin sirri yace dashi yakai dumbazu kayi sani cewa duk a cikin almajirai na babu wadda na yarda dashi dama dakai, kuma gashi yanzu tsufa ta riske ni bisa binciken danayi inada karancin kwanaki a duniya sbd haka zan baka wani sirri na karshe wadda kaine mutum na biyu dazai mallake shi bawani bane mutum na farkon face dana hubru wannan sirri dazan baka wani kambun tsafine wadda indai kana tare dashi babu wani mahaluki daya isa ya hallakaka komai jarumta karsa da karfin tsafinsa mutum ko aljan aduk sa'arda makiyinka ya tafi farautar ka bazai taba haduwa dakai ba saidai ku yita sabani babu wani tsautsayi dazai sameka muddin kana tareda wannan kambu, duk tsananin yaki ko matsifa zaka iya ratsawa ka wuce a yanzu haka tuni na daurawa dana hubru wannan kambu kuma kaima ga naka. Koda gama wannan jawabi sai mahaifina ya bude wata tsohuwar akwati ya dauko wannan kambu ya mikawa dumbazu hannun dumbazu na rawa ya karbi kambun ya daura shi a hannunsa na dama faruwar hakan keda wuya sai mahaifina ya dubeshi cikin tsananin damuwa yace kash! kayi babban kuskure sbd me kadaura wannan kambu a hannun ka na dama shin kamanta cewa komai na tsafi da hannun hagu ake yinsa inda kadaura wannan kambu a hannun ka na hagu da har abada baza a iya rabaka dashi ba amma yanxu bakin alkalami ya bushe a koda yaushe makiyanka na iya rabaka da wannan kambu. Koda mahaifina yazo nan a zancen sa sai ran dumbazu ya baci zuciyar sa takama tafarfasa yace tur!! dakai yakai wannan tsohon banza hakika kacika tsinanne kuma la'ananne meyasa tun farko bakace min karna daura kambun nan a hannun dama ba, wato na fuskanci cewa kana sane kamun wannan mugunta saboda danka ya fifita akaina, yau shekara ashirin kenan ina maka wahala amma shi danka baisan wahalan kaba ko guda tabbas ka cuceni kuma kaci amanata sbd haka nima dole naci amanarka yanzu take zan kashe ka kuma komai daren dadewa saina kashe wannan dan naka na cire kambun nasa, nasa a hanuna na hagu. Kodajin wannan batu sai mahaifina ya yunkura da sauri domin ya bude wannan tsohuwar akwatin nasa amma kafin hannunsa yakai kan akwatin tuni dumbazu ya zare takobinsa ya fille mishi kai nan take mahaifina ya sulale kasa matacce. Batareda bata lokaci ba dumbazu ya dauki wannan tsohuwar akwatin sihirin mahaifina ya tafi ya bazama gari nema na amma duk inda yaje sai ace dashi yanzun nan nabar wajen wato mukayita sabani kenan lokacin dana koma gida na iske gawar mahaifina saina sulale kasa sumamme nan take daya daga cikin almajiran mahaifina mai suna Kusad ya zuba min ruwa na farfado kodana bude idanu na nayi arba da Kusad saina tambaye shi a fusace nace wanene yayiwa uban nan nawa kisan gilla? nan take Kusad ya gayamin cewa shide yaga sa'adda mahaifina ya kira dumbazu cikin turakarsa suka kadaita kuma daga karshe ya jiyo dumbazu na daga murya cikin fushi daga can kuma sai yaji sautin sarar takobi kodajin haka sai kusad ya la6e a bayan kofar turakar kawai sai yaga dumbazu ya fito daga cikin turakar da sauri rikeda akwatin sihirin mahaifina dakuma takobin sa jini na diga a jikin ta. ********************* Mazan Jiya Part 14 #Cigaba Koda gama jin wannan batu saina rushe da matsanacin kuka domin nasamu tabbacin cewa dumbazu ne ya kashe min mahaifina babban abun bakin cikina shine nasan cewa har abada bazan iya daukar fansa ba akan dumbazu domin akwai ranar da mahaifina yace dani yakai dana ko a bayan raina kada ka kuskura kace zakayi kokarin ganin bayan dumbazu domin bazaka taba samun nasara a kansa ba saboda yafika karfin sihiri, kai baka samu komai ba daga cikin ilmina amma zan baka wata kariya wadda babu wani mahaluki dazai iya cutar dakai. Koda naji haka saina dubi mahaifina nace yakai abbana wai shin meyesa kaki ka koyamin ilmin ka na tsafi koda mahaifina yaji wannan tambaya sai idanunsa suka ciko da kwalla har hawaye suka zubo masa sannan yace kafin mahaifiyarka ta rasu ta rokeni alfarmar kadana koya maka tsafi, domin bincike yanuna cewa idan ka mallaki irin sirrukan tsafina bazaka taba haihuwa ba a duniya niko saina daukar mata wannan alkawari kuma na tabbatar dashi najin haka saina rungume mahaifina muka fashe da kuka har izuwa lokaci mai tsawo tun daga ranar da dumbazu ya kashe mahaifina bamu sake haduwa dashi ba, amma a kullum acikin farautar nema na yake har yagaji da neman ya tafi can wata nahiyar inda yadinga amfani da karfin sihiri yana yakar sarakuna yana mallake dukiyar su da mulkin su a hakane ya mallaki kasashe dayawa duk zamo a karkashin kasa guda mai suna kailus daidai da rana daya sarki dumbazu bai taba samun nutsuwa da kwanciyar hankali ba saboda kawai rashin samun daman hallakani, a kullum a cikin aiko aljanu da sadaukan bil'adama yake domin suzo su hallakani yakai hibru kayi sani duk lokacin dakaga kana samun nasara wajen kare rayuwata aduk sa'adda aka kawo farmaki ba takobin ka bane take baka sa'a face kambun tsafin dake jikin ka na hagu wannan shine asalin yadda gaba ta kullu tsakani na da sarki dumbazu ina mai tabbatar muku da cewa babu yadda za'ayi kuje birnin kailus kuci dumbazu da yaki face nayi abu guda wannan abu kuwa bakomai bane saidai nacire kambun tsafina nabaka kai hibru kasa a hannun ka sannan kaje ka tari dumbazu tabbas zaka samu nasara akan sa saidai ni daku munyi bankwana bazaku dawo ku sameni a raye ba domin ka'idar wannan kambu shine duk wanda yadaura shi a hannunsa to duk ranar daya cire shi bazai kara kwana uku a duniyar nan ba. Koda Sarki hubru yazo nan a zancen sai hankalin mu ya dugunzuma na dubi sarki hubru nace ya shugabana ina dalilin salwantar da rayuwar ka akan yarka. Kodajin haka sai Sarki hubaru ya zubarda hawaye sannan yace yakai sadauki dan sadaukai kayi sani cewa nifa sarki nayi arziki kuma na haihu duk abinda ake nema a duniya na same shi haka kuma shekaruna sun tafi yata fa yanzu ne take ganiyar kuruciyar ta SBD meye zan bari rayuwarta ta salwanta alhali kadai gareni idan na mutu itama ta mutu babu wani wanda za'a kalla a tuna damu idan bakuje kun ceto rayuwarta ba za ayi biyu babu domin bakin cikin rashin tane zai kashe ni anan ita kuma sarki dumbazu ne zai kasheta a can yanzu yanzu bada bata lokaci ba nakeso kuyi shiri kutafi izuwa ga bokana domin ya sadaku da hadimin dazai kaiku fadar sarki dumbazu domin ku yake shi amma kafun sannan ina mai dada jaddada muku alkwarin dake tsakanin ku kai hibru amanar yata na wajen ka domin kaine zaka aure ta kai kuma maharaz na damka amanar kasata da jama'ah ta a gurin ka domin kai zaka gaji sarauta ta gama fadin hakan keda wuya sai sarki hubru ya cire kambun dake hannunsa na hagu ya miko min hanuna na karkarwa na karbi kambun nasa a hanuna ina karba saina saka shi a hanuna wannan shine babban kuskure danayi a rayuwa ta domin na manta cewa duk wanda yadaura wannan kambu toh duk ranar daya cire shi bazai haura kwanaki hudu ba a duniya nan take mukayi bankwana da sarki hubaru yana kuka muna kuka domin munsan cewa mun rabu har abada bazamu sake ganin juna ba kaico babu ranar bakin ciki wacce tafi ranar rabuwa da masoyi tabbas mun shaku da sarki hubru koma munyi imani cewa yana matukar kaunar mu kamar yadda muke kaunarsa amma gashi munaji muna gani zai rasa rayuwar sa bamuda yadda zamuyi mu kareshi lokocin damuka baro fadar sarki hubaru muka nufi kofar gidan shaburus Ibn mukaibar rana ta fadi magariba ta doso kai muna isa kofar gidan muka iske boka shabarus a tsaye yana jiran isowar mu koda mukazo dab dashi sai mukaga idanunsa cike da hawaye yana kallon mu kawai alamarin daya karya mana zuciya kenan jikin mu ya karayin sanyi boka shabarus ya dube mu cikin sanyin murya yace lale da manyan gobe hakika kun baro masoyina a cikin mugun hali inda nasan wannan rana zatazo ta riske ni daban kawo iyanzu ba kuyi sani cewa a duniya banida masoyi tamkar sarki hubaru amma gashi an wayi gari inaji ina gani rayuwarsa zata salwanta babu abinda zan iyayi don kareshi yanzu bada bata lokaci ba zan hadaku da babban hadimi na wadda zai kaiku fadar sarki dumbazu acikin kwana goma sha daya maimakon tafiyar kwanaki saba'in da bakwai bisa rakumi ko doki batare da an yada zango ba koda gama fadin haka sai boka shabarus ya hade tafin hannunsa waje guda ya kama karanta wadansu kalmomin tsafi yana tofawa akan tafin hannun daga can sai yayi nuni izuwa kan kasa nan take kasa ta dare saiga wani narkeken aljani ya ratso ta cikin kasar ya bayyana a samanta aljanin nada suffa irinta tsuntsaye saidai kansa da wuyansa irin na biladama ne kuma fukafukansa guda goma sha takwas ne cikin rusunawa aljanin ya dukar da kai kasa ga boka shubarus ya kwashi gaisuwa shabarus ya dube shi yace angaishe ka mara'il labarus yakai mara'il labarus kasani cewa yaune ranar karshen aikin ka dani domin abune mawuyaci kudawo ku riskeni a raye. Koda jin wannan sai hankali aljani mara'il labarus ya dugunzuma ya dubi boka shabarus cikin damuwa yace ya shugabana ina dalilin ka na fadan haka boka shabarus yace yakai babban hadimi na kayi sani cewa zaka dauki sadauki hibru tare da boka maharaz ka tafida su izuwa fadar sarki dumbazu domin su yakeshi su kawar dashi, kodajin haka sai aljani Mara'il labarus yayi tsalle ya tumu da kasa ya kama kuka yana mai cewa haba ya shugabana laifin maina maka kakeso ka hallakani inani ina zuwa fadar shugaban bokayen duniya domin a yake shi, na roke ka daka yafemin wannan aikin kanemi wani yayi shi amma bani ba. Kodajin haka sai boka shabarus ya dakawa aljani mara'il labarus tsawa yace dolene kai zakayi wannan aikin domin kai kadai ne zaka iya idan kuma kace bazaka yiba yanzu take anan zan hallakaka kayi sani cewa sadauki hibru na tareda kambun tsafin sarki hubaru don haka babu wani tsautsayi dazai sa ku halaka saidai zaku iya shan bakar wahala, maza ka kwashe su ku tafi kuma ka tabbatar dacewa kun isa can a kwanakin dasuka gaza ashirin tabbas bazaku dawo ku riske niba domin a ranar da masoyina zai mutu nima zan mutu, koda gama fadin haka sai boka shabarus ya juya ya shige gidansa, koda faruwar haka sai aljani mara'il labarus ya suremu nida maharaz sannan ya bude fukafukansa yayi sama sannan ya fara tsala gudu nagaban kwatance muna gifta giza gizai tambar wucewar tauraruwa mai wutsiya saida muka shafe kwanaki tamkar wucewar tauraruwa mai wutsiya, sai da muka kwashe kwana goma sha takwas muna tafiya bisa aljani mara'il labarus a sararin samaniya batareda yasauko kasa ba don ya huta nikam a rayuwata bantaba ganin aljani mai juriyar wahala ba tamkar aljani mara'il labarus baisan yunwa ba baisan ishirwa ba balle lalaci a yammacin kwana na goma sha takwas dinne muka hango fadar birnin kailus daga can nesa kadan a gaban mu. Wohoho!! tabbas fadar ta isa da akirawota da matsayin aljannar duniya domin gavadaya ginin ta da gilashin lu'u-lu'u akayi shi babu abinda zaibawa mutum mamaki face ganin yadda aka gina gabadaya birnin na kailus a tsakiyar wani kogi abinda bamu saniba shine aljanu ne suka zuba tubalin ginin harya fito saman kogin nan duk inda zaka taka jauhar ne da zabar amma indaga sama ka taho kana iya ganin yadda ruwan kogin ya zagaye birnin gabadaya, aljani mara'il labarus bai sauko kasa ba saida muka iso dabda birnin sannan ya dira a bakin kofar garin babu kowa a bakin kofar balle muyi artabu damasu gadi kuma sai muka iske kofar a bude wanwar sannan mukaji garin yayi tsit tamkar babu wani abu mai rai acikin sa, alamarin dayayi matukar bamu mamaki kenan batareda fargabar komai ba muka sauko kasa daga kan aljani mara'il labarus na wuce gaba ina mai yafuo maharaz da aljani mara'il labarus da hanuna ina mai cewa kubiyo ni a baya, a lokacin ne na zare takobi na, na cigaba da tafiya ina mai duba kowace kusurwa kuma ina kasa kunne kozanji motsin wani abu daka iya kawo mana farmaki sumame saida muka shafe sa'a shida muna tafiya a cikin birnin kailus ko bera bamu ganiba rayayye duk mutanen garin da dabbobin su sun kame sun zamo gumaka babu abunda ke motsi hatta kasuwa damuka ratsa ta cikin ta mukaga mutane sunata harkoki amma kowa a kame yake yazamo gunki, wasu suna musayar kudi da kaya wasu kuma bakunan su a bude alamar cewa magana sukeyi hakadai muka cigaba da tafiya har muka iso kofar fadar birnin anan bamuga komai ba ko gunkin dakaru babu ma balle muji tsoron cewa zasu iya tashi akoda yaushe su farmana, kai tsaye muka kunna kai izuwa fadar har muka isa inda karagar sarki take amma bamuga kowa ba bamuga wani abu mai rai ba, kuma duk kofofin fadar nan a bude suke bamu riski guda daya a kulle ba dazuwan mu gaban karagar mulki sai muka dubi junan mu mukayi ajiyar zuciya a tare na dubi maharaz da aljani mara'il labarus nace yaku abokan tafiya kuyi sani cewa ruwa baya tsami banza duk yadda akayi an sanda zuwan mu kuma an yi mana tanadi, nikam ina ganin cewa wani tuggun aka shirya mana shiyasa bamuga komai da kowa ba kafun nagama rufe bakina sai kawai mukaji kofofin fadar na rufe kansu daya bayan daya sannan sai mukaji an bushe da mahaukaciyar dariya amma bama iya ganin mai dariyar nan nan fa maharaz yafara amfani da karfin sihirin sa domin yaga mai yin dariyar amma sai abu ya gagara nan take cikin mu ya duri ruwa duk da na tuna cewa ina tareda kambun tsafi wanda sarki hubru yabani amman sai naji banida nutsuwa da yadda dakai kwatsam sai mukaga wadansu dakarun aljanu ma'abota kwarjini daban tsoro sun bayyana dayawa ba adadi sunyi mana kawanya suna rikeda muggan makamai wadanda ko a labari bamu tabajin irinsu ba sbd razanar damukayi bamu san sa'adda muka kankame juna ba mu ukun, abin mamakin ma shine aljani mara'il labarus yafimu firgicewa domin duk ilahirin gabban jikinsa karkarwa sukeyi kamar wadda ake zukar jinin jikinsa, bazato ba tsammani sai mukaga sarki dumbazu ya bayyana tsulum akan karagar mulkin sa yana kyakyata dariyar mugunta sannan saiga sauran dakaru na bil'adama da duk fadawan sa sun bayyana suma sunayi mana dariya, al'amarin kashe mana jiki kenan mukaji nadama tazo mana bisa kawo kanmu izuwa wannan birni domin mun san cewa mun sayi ajalin mune da kudinmu, lokaci guda sarki dumbazu ya tsuke bakinsa yabar dariyar fadar tasa keyin tsit sarki dumbazu ya dube mu, mu ukun yace yanzu ku uku kacal aka turo ku yakeni wani haukane yasa kuke tunanin zaku iya karawa dani hakika yaro baisan wuta ba, yakai hibru kayi sannin cewa nayi nisa a halwar tsafi sanina ya wuce na maigidana mahaifin sarki hubru don haka wannan kambun tsafi daya baka ka daura a hannun ka bazai maka tasirin komai ba domin ka gamsu da bayani na a yanxu zan nuna maka wani abu, koda gama fadin haka sai sarki dumbazu ya bude damtsen sa na dama saiga irin wannan kambun tsafi wadda sarki hubru yabaiwa hibru nan take sarki dumbazu ya cire kambun ya jefa shi a cikin wani kasko take kambun nan ya kone kurmus, sarki dumbazu yasake kyalkyalewa da dariyar mugunta a karo sannan yace to kaga yadda nayi da irin kambun nan na hannunka ko dan haka wannan kambun darajar su daya da takarda banza a wajena amma idan baka yadda ba zakaga zahiri a yanzu, kafin na bude baki nace wani abu tuni sarki dumbazu ya dubi waddan nan zakakuran aljanu nasa yace ku afka musu naga iyakar jarumtakar su, nan take aljanun nan sukayi mana rubdugu nan fa aljanun nan suka haumu da sara da suka maharaz ya tare su da karfin sihirinsa yana kare harin su shima aljani mara'il labarus niko da karfin damtsena na taresu amma sai akayi min kwab daya na zube a kasa sumamme ko dakika arba'in ba'ayi ba aljanun sarki dumbazu sukayi fatafata da jikin aljani mara'il labaru, aljani mara'il labarus ya fadi kasa magashiyam ko ina a jikinsa yazamo kofar fitar da jini kawai maharaz ne yadan tabuka wani abu domin yasamu dakika kusan dari uku da tamanin yana fafatawa da aljanun nan sannan suka karya karfin sihirin sa sukayi masa sara tamanin ya baje a kasa ko shurawa bayayi. Lokacin dana farfado idanuna suka bude saina tsinci kaina a wata fadar a daure a jikin dirkar gini wata irin sarkar tsafice ta daureni koyaya na motsa sai naji sarkar ta kara matseni bisa dole na hakura na daina motsi bisa mamaki sai naga abokina maharaz a daure kusa dani yana numfashi sama sama kaida gani kasan cewa akan gangarar mutuwa yake, raunukan jikinsa guda tamanin na digar da jini shiko aljani mara'il labarus babu shima a wajen alamarin daya tabbatar min da cewa aljani mara'il labarus ya mutu kenan, bazato ba tsammani sai naga sarki dumbazu ya riko hannun gimbiya sahira yar sarky hubru sun tafo gareni sunata hira da dariya cikin nishadi nan fa na cika da tsananin mamaki nace a zuciyata saboda me sahira zata saki jiki da babban makiyin ubanta wadda a halin yanzu ya rabata da ubanta kuma yazamo sanadin ajalin sa sarki dumbazu yakai gimbiya sahira izuwa kan wata kujera ta alfarma ya zaunar da ita sannan ya tafo gareni saida yazo dab dani yadda muna iya jin numfashin juna sannan yace dani ga masoyiyar ka can tazamo tawa a yau zan sadaku da ita sannan na cika alkawari na wato na kasheta a gaban idanun ka tunda mahaifinta ya saba ka'ida ta bai baku kansa kun kawomun ba, bisa mamaki sarki dumbazu yaga na dubeshi nayi murmushi sannan nace matukar bil'adama na numfashi a doron kasa ako yaushe to baya yanke kauna da kubuta daga kowani irin bala'i, ya kai wannan azzalumin sarki maci amana kayi sani cewa lallai karshen lalacewa kuma har abada burinka bazai cika ba idan har amana da soyayya sun kasance ababen gaskiya lallai bazaka samu nasara akan gimbiya sahira ba. Kodajin wannan batu sai sarki dumbazu ya kyalkyale da dariyar mugunta yace yanzu kai a tunanin ka har akwai wani tsautsayi dazai sa nakasa samun nasaran abinda nasa a gaba duk duniya fa babu sadauki mai karfin damtse na babu matsafi mai karfin sihiri na wanene ya isa yaja dani nan take dumbazu ya shiga yiwa kansa kirari yana ihu da kururuwa a gabana yana cikin yin hakan ne na lura da wani guru dake kugunsa wadda ke dauke da layun tsafi akalla guda dubu, alkyabbar dake jikin sane ta rufe gurun amma saboda yana juyi da daga hannaye a gaban idona sai idanuna suka hango wannan gurun, cikin shammaci da zafin nama na sunkuya na kaiwa gurun nan chafka da bakina aiko sai nayi sa'a na chafke laya guda da hakorana na gatsa layar ta fashe take gurun nan ya bace bat itama sarkar tsafin da aka daure mu ta bace bat itama. Cikin zafin nama na zare takobina, haka kuma sai aba daya dakarun aljanun nan sarku Dumbazu sai naga suna narkewa kamar ana narka man shanu a kasko, kafin kiftawar ido duk sun zama ruwa a kasa. Su kuwa fadawan sarki Dumbazu sai duk suka firgice suka mimmike tsaye jiki na kyarma. Sarki Dumbazu ya tsaya kyam a waje daya ko motsi bai yi ba. Kawai sai ya suddar da kansa kasa yana mai zubar da hawaye, ni dai har wannan lokacin ina rike da takobina banyi yunkurin yin komai ba, daga can sai Sarki Dumbazu ya dago da kai ya dubeni cikin tsananin fushi fuskar nan tasa a murtuke, a wannan lokacin ne naga gimbiya Sahira ta mike tsaye zumbur tana kalle kalle a cikin fadar kuma tana kallon jikinta, ga dukkan alamu ta dawo cikin hayyacinta na ce a cikin zuciyata. Wato a da an juyar mata da tunaninta ta manta da kanta da kuma komai nata. Sarki Dumbazu ya kura mata idanu har wannan lokacin hawaye bai daina zub daga cikin idanunsa ba, kawai sai ya bude baki da kyar ya ce "Ya kai yaro hakika ka cuceni, ka ruguza Mani tsafin dana kwashe sjekaru da dama ina shirya shi, yanzu bani da suran sirrin tsafi a tare da ni, lallai sai na yi maka kisan gilla irin wanda ba'a taba yi ma wani a wannan duniyar ba, kayi sani cewa ko bani da sirrin tsafi ai in da na karfin damtse wanda babu kmaarsa a kaf nahiyar nan, dan haka maza bisa kanka yi kokari ka cice rayuwarka na gani. Cikin wani irin azababben zafin nama sarki Dumbazu ya zare takobinsa, takubbanma guda biyu ne ya kawo mani wasu tagwayen mugayen sara, duk da nayi sauri na kauce amman sai da takubban nan suka zarge rigar dake jikina, kuma suk yi mani dogon yanka akan kirjina har jini yana tsartuwa. Kawai sai na tafi da baya taga-taga zan fadi kasa ana layi. Koda Dumbazu yaga ya samu wannan gagarumar nasara sai ya sake dako tsalle domin ya dura a kaina da nufin ya gididdiba sassan jikina, amman sai na yunkura cikin karfin hali da matukar juriya na yi tsalle can gefe guda yayinda takubban nasa suka sari wata kujera take ta ragargaje. Nan fa muka ci gaba da azababben yaki yayi ta kokarin ya gididdibani ni kuma na himmatu ina mai kare hare-harensa, ina zuluyewa gami da kaucewa amman ko kadan na saka mayar da martani ko da sau daya ne kuwa. Domin zafin namansa da karfin saransa sun wuce misalin ta yadda bazan iya taresu ba har na mayar masa da martani. Sai da muka shafe sa'a tara muna wannan bakin Artabu Dumbazu ya kasa samun nasara a kain ni ma na kasa maida mashi da martani koda sau daya ne kuwa, hakika duk wanda ya fika jarumta to fa ya fika har abada, domin baka isa ka kamoshi ba. Koda sa'a tara ta cika muna wannan gumurzu sai gajiya ta riskeni har ya zamana cewa da kyar nake iya daga takobina na kare saran da Dumbazu yake kawo mani, shikuwa ko kadan bai gajiba domin kmar ma a sannan ne ya fara gumurzun. Yayi da yaga na fara sarewa sai ya cika da murna ya ci gaba da kawo mani hari a sannu yana murmushin mugunta, sai da ya kaini jikin bango ya tareni sannan ya buge takobina ta fadi kasa sannan ya labta mani wawan sara a cinya, ban san sa'ar da na kwarara uban ihu ba tare da durkushewa a kasa ba cinyata na zubar da jini. Dumbazu ya sake dankara mani wani saran a dayar cinyar tawa na zube kasa wanwar a matukar galabaice nan fa idanuna suka fara gani dishi-dishi. Dumbazu ya sake dag takobinsa da nufin ya fille mani kai, amman kawai sai naga hannun nashi ya sandare ya kasa labta mani saran, da kyar da sidin goshi na juya baya kawai sai naga wuka ta nutse a tsakiyar gdon bayansa jini na burbulowa ta tsakiyar girjinsa, tsaye a gaban Dumbazu gimbiya Sahira ce jikinta na karkarwa, a sannna ne na gane cewa ita ce tayi ta maza ta rugo ta caka wa Dumbazu uka a gadon bayansa. Nan take Dumbazu ya sullae kasa matacce ko shurawa bai yi ba, a sannan ne nima idanuna suka rufe na sume a wajen. Lokacin dana farfaɗo sai nayi arba da gimbiya Sahira tsugunne a gabana ta rusar kuka, raunikan dake jikin cinyoyina an saka masu magani, a gefe daya kusa da ni kuma Maharaz ne a kwance har wannan lokaci yana numfashi da yar duk da cewa an sa masa magank a jikin raunikan nasa. Koda na daga kina na dubi gabas da yamma, kudu da arewa sai naga ashe gaba daya mutanen birnin Karlus ne suka rufemu sun tsura mana idanu suna kallonmu kawai, a gefe daya kuma fadawan Sarki Dumbazu ne a tsaitsaye sunyi tsuru-tsuru kamar ace kyet su fice da gudu. Ashe duk mamakinmu suke yi yadda akayi har muka iya ffaatawa da sarkinsu, har ma kuma muka samu nasarar hallaka shi. Saida muka yi kwana arba'in muna jiyyar raunikan mu a birnin Karlus ni da Maharaz sannan muka warware, amman duk da haka bamu warke sumul ba, sai a sannan hankulanmu suka dawo jikinmu har na samu damar baiwa gimbiya Sahira llabarin dukkan abinda ya faru tsaninmu da mahaifinta gami da wasiyar da ya bamu mu shaida mata. Koda gimbiya Sahira ta gama jin bayanina sai ta fashe da matsanancin kuka kuma ta rungumeni tana mai ci gana da kuka. Da kyar na lallasheta daga can sai ta dubeni ta ce da ni tana so tayi wata magana ta sirri da Maharaz. Cikin matukar mamaki na dubeta nace da ita "Ke kuwa wace irin magana ce wannan da zaki yi da abokina wacce bakya so na ji? Koda taji wannan tambaya ai hawaye ya zubo mata ta ce ka yi hakuri ya kai mijina na gobe, wannan magana da zanyi da maharaz sakone daga mahaifina zuwa gareshi, kuma ya gargadeni da cewa komai rintsi da tsanani kada na kuskura na sanar d kai. Koda gama fadin haka sai gimbiya Sahira ta tafi wajen maharaz tayi masa rada a kunnensa, gabadaya jama'ar dake wajen babu wanda yaji abinda ta ce masa, faruwar hakan keda wuya sai kawai muka ga Aljani Mara'il Labarus ya sakko daga sama tare da tsirga a gabanmu, al'amarin da yayi matukar bamu mamaki kenan domin mu a zatonmu ya dade da mutuwa, hakan yasa ko neman inda gawarsa take ba muyi ba. Yayin da Aljani mara'il labarus yaga muna mamaki da ganinsa a raye sai ya bmau labarin cewar ai dama dogon suma yayi, lokacin daya farfado sai yaga babu kowa a wannan fada ta farko da muka fara shiga, dan haka sai ya tashi da yar ya tafi can bayan birnin Karlus ya boye knsa a cikin daji yayita jinya har saida ya warke. Koda jin wannan labari sai muka cika da farin ciki, a daidai wannan lokaci ne wazirin sarki Dumbazu ya zo gaba ya tsaya tare da cewa ya kai wannan sadauki mai abun mamaki, tunda har ka samu nasarar kashe sarkinmu, yanzu abinda ya kamata kayi shine ka maye mana girbinsa. Da jin wannan batu sai nayi murmushi n ce ai ni bnai da bukatar mulki ko dukiya, abinda nazo nema na samu, kuma ba komai bane face masoyiyata kawai, sai nayi nuni izuwa ga gimbiya Sahira, ita kuwa sai ta rugo gareni cikin farin ciki gami da murna ta rungume ni. Daga nan sai na dubi wazirin Dumbazu nace da shi mukam yanzu mun kammala aikin da aka turomu yi a birninku, saboda haka muna yi maku sallama sai ku zabi shugabanku a tsakaninku. Gama fadin hakan keda wuya sai Aljani mara'il labarus ya rankwafa bayansa muka hau mu uku muka zauna, sannan ya bude fuka fukansa guda 18 yayi sama da mu, kafin kiftawar idanu mun bace bat a cikin gajimare. Tun daga wannan rana sai naga abokina Maharaz ya daina sakin jiki da ni, ya daina yin hira da ni, hatta abinci baya yarda muci tare, al'amarin daya dugunzuma hankalina kenan na rasa binda ke mani dadi a duniya, a duk sa'ar dana tambayeshi shin ko nayi masa wani laifi ne? Sai yayi murmushi ya ce sam banyi masa laifin komai ba. Tsawon kwanaki 17 da muka shafe muna tafiya a sararin samaniya daga birnin Karlus zuwa birninmu na darul mahabur bamu yi hirar rabin sa'a ba nida Maharaz. Muna isa birnin darul mahabur muka iske sarki Hubaru da boka karlus sun mutu an binne su, muna kuka muka isa inda kabarinsu yake, sai da muka shafe sa'a uku cur muna a gaban karin muna kuka sannan da kyar aka kawar damu daga bakin kabarin aka tafi da mu izuwa fada. Kashegari da safe aka dora Maharaz akan karagar sarki Hubaru kuma aka daura aurensa da Husuna yar sarki Hubaru, bayan an gama bikin nadin Sarki Maharaz ne aka daura aurena da gimbiya Sahira sannan ya bani sarautar sarkin yakinsa, na cigaba da yin bauta gami da biyayya ga sarki Maharaz tsawon shekaru, kuma duk bukatar da ya zo mani da ita ina binta ga dukkan iyakar karfina ban taba nuna masa cewa na gajiya ba, na sha bakar wahala akan biyan bukatunsa musamman a lokacin da suka rasa haihuwa shida matarsa Husuna, domin sai da na kusa rasa rayuwata a kakarina na nemo masu maganin haihuwa. Duk wannan iyayya da bauta da nake yiwa sarki Maharaz bai taba yi mnai godiya ko sau daya ba, kuma gabadaya abotarmu da kusancinmu sai ya yanke su, ko magana bana samun damar yi da shi face in mun zauna dakin gani tare da sauran fadawa idan bukatar hakan ta taso. Har yau har gobe ban san dalilin da yasa sarki Maharaz ya nisanta da ni ba. Yake gimbiya Mulaifa wannan shine tarihin rayuwata data mahaifinki da kuma dangantakar dake tsakanina da shi. Masu iya magana suna cewa ranar wanka ba'a boyon cibi, yanzu dai gani ga shi kuma yace zai fada mani wani sirri wanda bai taba fada mani ba a yanzu, wanda shine sanadin da yasa ya nisanta abotarmu. Lokacin da Hibru ya zo nan a labarinsa sai hawaye ya zubowa sarki Maharaz ya matso daf da shi yadda suna iya jin numfashin juna sannan ya ce ya kai abokina hakika abinda kake zargi tabbas haka yake, idan baka manta ba a ranar da gimbiya Sahira ta kashe sarki Dumbazu acan birnin Karlus ta fada mnai wani sako a cikin kunne na cikin rada ko ba haka ba? To wannan sako ba wani abu bane face wasiyya daga mahaifinta wacce ya sanar da ita tun kafin sarki Dumbazu ya zo ya saceta, abinda ya fada mata shine, lallai ta sanar da ni cewar dole ne na nisnta da kai tun daga ranar da n zama Sarki birninmu na darul mahabur, idan kuwa naki to tabbas mulkina zai rushe, kaima kuma burinka bazai cika ba, domin ba zaka zama Sarkin yaki ba, kuma duk mu biyun ba zamu samu haihuwa ba har abada, bisa wannan alilai ne yasa na yanke abotarmu kuma na nisanta kaina daga gareka, amman a kullum sai na shiga turakata na kulle kaina nayi ta kukan bakin ciki ba tare da kowa ya sani ba. Ya kai abokina ka gafarceni inaso ka fahimta cewa dole ce tasa na aikata hakan a gareka bawai a son raina bane kuma dama ance kada na sanar da kai gaskiyar al'amarin sai a lokacin da naga gagarumin yaki ya taso wanda bamu da tabbacin samun nasara akan shi. Sa'adda Sarki Maharaz ya zo daidai nan a jawabinsa sai Hibru ya rungumeshi, take duk su biyun suka rushe da matsanancin kuka suna masu daɗa kwakumar juna. Mulaifa dake tsaye tana kallonsu sai ta kamu da tsananin tausayinsu, itama sai ta fashe da kukan aka rasa wanda zai rarrashi wani a tsakaninsu. Bayan sun jima a cikin wannan hali sai Sarki Maharaz ya janye jikinsa daga na Hibru suka sake kallon juna a karo na biyu sannan ya ce ya kai abokina kayi sani cewa abotarmu ta zama samu kamar yau muka fara ta, kuma ina neman alfarma guda daya a wajenka. Cikin murmushi Hibru ya ce fadi duk abinda kake so zanyi maka shi, sarki Maharaz ya ce ina so kabar yata Mulaifa tayi jinyar Sadauki Imnal a cikin wannan tafiya da zamu yi, lallai tare da ita za a yi wannan tafiya. N sani cewa Imnal yana matukar kaunar Mulaifa idan har tana tare d shi sai ya fi saurin warkewa, samun kafiyarsa da wuri shine samun kwanciyar hankalinmu, domin bincike ya tabbatar da cewa rawar da Imnal zai taka a wannan yaki ko ni da kai ba zamuyi rabinta ba. Da jin haka sai Hibru ya yi murmushi tare da cewa na amince da haka. Nan take farin ciki ya lullube Mulaifa da sarki Maharaz, har suka rungume juna tare. Sadauki Imnal na kwance a cikin dandazon mayakan da zasu fita yaki izuwa tekun Bahar Suffiyya, sai kawai akaga kuyangi da dakarun sarki Maharaz sun rako gimbiya Mulaifa suna masu ratsowa ta sansanin dakarun yakin, nan fa aka zuba ido aga wajen wa kuma gimbiya ta zo, kunyangin dake yi wa gimbiya Mulaifa su 12 ne, 6 na dauke da faratin abinci da abinsha iri-iri, ragowar 6 kuwa suna dauke da magunguna, shimfidu da kuma tanti. Kai tsaye gimbiya Mulaifa ta durfafi inda Sadauki Imnal yyake kwance, al'amarin daya baiwa kowa mamaki kenan a wajen, da isowar Mulaifa gaban Imnal sai ta durkusa daf da shi, ta dubeshi tare da sakar masa wani tattausan murmushi ta ce da shi nice baiwar daka bukaci mahaifinka ya samo domin yin jinyarka. Koda jin haka sai Imnal ya yunkura da nufin ya mike tsaye, amman sai Mulaifa tayi sauri ta danne kafadarsa ta maida shi kwance, Imnal ya ce wane ni na kalleki a matsayin baiwa, ai nine bawanki, haba ya shugabata ki kula fa domin kina gaban talakawanki kike kada kije kiyi abin kunya. Koda jin haka sai Mulaifa ta bushe da dariya tare da cewa ya kai masoyina, kayi sni cewa shi so makahone kuma kurma ne, wanda duk yayi zurfi a cikin kogin so to baya ji kuma baya gani, nayi nisa a cikin kogin kaunarka dan haka babu abinda zai sa naji kunyar wani mahaluki yayi kyautata maka. Ina son k saki jikinka ka daina dari-dari da shakkar komai, domin mahaifina ne ya turoni gareka da kansa kuma ya umarceni da nayi jinyar ka a yayin wannan gagarumar tafiya da zamu yi har izuwa lokacin da zaka samu lafiya ka warke sumul. Ina mai dada yi maka albishir da cewa a halin yanzu abotar mahaifinka da abbana ta dawo sabuwa kamar da. Nan take Mulaifa ta baiwa Imnal labarin duk abinda ya faru a dakin gani tsakaninta da sarki Maharaz da kuma sarkin yaki Hibru. Koda ta gama bashi labarin sai nan take yaji wani irin farin ciki ya lullube shi irin wanda bai taba jin kamarsa ba, kwatsam! Sai suka ji an fara busa algaita gami da kida tambura alamar cewa sarki ya fito daga cikin gida domin a fara wannan gagarumar tafiyar. Nan take kowa ya nutsu aka mimmike tsaye, masu dibar kya na diba, masu hawa dawakai suna hawa, wasu kuma ana tattara dukiya da guzuri ana laftawa rakuma, dawakai da kuma keken doki. Koda sarki Maharaz ya fito daga gidan sarauta sai aka ganshi tare da abokinsa sarkin yaki Hibru bisa kan fararen dawakai biyu, duk sunyi gagarumar shigar yaki kala daya suna tafe suna fira cikin nishadi abin gwanin ban sha'awa. Gabadaya jama'ar dake filin fadar sai suka cika da matuƙar mamaki, domin rabon da aga Maharaz da Hibru a haka tun kafin su samu sarauta, maimakon sarki Maharaz da Hibru su tsaya gaban jama'a suyi bayanin karshe na wannan tafiya, sai suka wuce kai tsaye wata hanya da zata kaisu zuwa dakin gunki darzuba. Da isarsu kofar dakin bautar sai suka sakko daga bisa dawaknsu, bayin dake biye da su sukayi sauri suka kama dawakan suka rike. Maharaz da Hibru suka shige cikin dakin bautar rike da hannun juna, a haka har saida suka isa inda gunki darzuba yake, isarsu keda wuya sai suka durkusa bisa gwiywoyinsu sannan suka suddar da kawunansu kas, kuma suka rufe idanunsu. Bayan sun dan jima a haka kawai sai suka yunkura da nufin su fece daga cikin dakin bautar, ba zato sai suk ji muryar darzuba yana mai cewa "Ku dakata mana tukunna yaku abokan asali, kuma masoyan gaskiya, sannan aminan zahiri. Cikin hanzari suka koma suka durkusa kamar yadd suka yi a farko. Darbuza ya ce hakika a yau ina mai matukar farin ciki da dawowar abotarku, domin kuwa kunyi hakuri da dukkanin kunci gami da takaicin da muka jarabceku da shi, domin inganta rayuwarku da nuna amincewarmu bisa karbar bautarmu da kuke yi ba dare ba rana. Nayi maku alkawari zan tsare rayukanku daga dukkanin irin masifun da zaku shiga a cikin wannan gagarumar tafiyar, kuma lallaı duk irin wahalar da zaku sha karshe kune zaku yi nasara, abinda bni da tabbacin yi maku alkawarinsa shine kare lafiyarku, dalili kuwa shine wanda kuke bautawa da wanda su sarki duzalu ke bautawa ya kasance mai karfi kamata kuma shine babban makiyina a duniya, tabbatas muna yi gaba mai tsanani kwatankwacin irin wadda sarki huburu da sarki darzuba suka yi kafin mutuwarsu. Ina mai sanar da ku cewa nima ina nan ina gagarumin shirin yaki domin tunkarar abokan gaba acan tekun bahar Suffiyya, wanda kokarinsa shine ya kare sarki dujalu kuma ya bashi ikon da nasarar dauko takobin saiful lujara, kmar yadda nima zan kareku kuma na baku nasara, wannan yaki da za a yi a bakin kogin bahar Suffiyya ba a taba yin kamarsa ba a tarihin duniya ba, domin sai anyi asarar dubun nan rayukan miliyoyin aljanu da biladama da kuma dukiya mara adadi. Dole ne cikin biyu ayi daya, kodai su halakamu ko kuma mu mu halakasu, amman ina da yakinin cewa mune da nasara domin nayi bincike har sau dubu dari amman banga komai ba sai nasara a garemu, da wannan kalami ne nake sallamarku sai mun hadu a bakin kogin bahar Suffiyya, lallai zamu gajarce maku tafiyar daga kwanaki masu yawa zuwa kwanaki kadan. Sa'adda darzuba yazo nan a jawabinsa sai Sarki Maharaz ya bude baki yayi godiya, shiko Hibru sai yayi shiru bai ce komai ba, tun sa'ar da darzuba yayi nisa a cikin jawabinsa sai zuciyar Hibru tta cika da wasiwasi ya tambayi kansa a cikin zuciyarsa ya ce wai shin wannan wane irin abune muke bautawa, wane ne haka muke bautawa wanda basji da cikekken yakini, ai bai kamata ace abinda ake bautawa yana shakkar wani abu ba, kai ni a ganina ma kamar akwai wani guda daya wanda yafi dukkaninsu karfi da iko, inya so sai ya yake su ya kawar da su dukkaninsu ya zamana cewa shi kadai ake bautawa. Nikam dama can zuciyata ta dade tana rawa akan wannan abin bautar na mu, domin sau tari yana barinmu muna shan bakar wahala, da kyar muke tsira da rayuwarmu, to yanzu kuma gashi shi da bakinshi yake cewa yana da kishiya gami da abokin gaba amman muje zuwa sannu bata hana zuwa sai dai a dade ba'a je ba. Nan dai Maharaz da Hibru suka mike tsaye suka fice daga cikin dakin bautar, kai tsaye suk koma bakin kofar fada suka sake tsayawa, bayan sun sauka daga kan dawakai sai sarki Maharaz ya wuce zuwa kan mimbari yayin da Hibru ke take masa baya, bayan sun hau kan mimbarin ne sun tsaya sun masu fuskantar jama'a sai Sarki Maharaz ya bayanin godiya ga jama'a uma yayi gaisuwa ga baki wadanda suka zo daga sauran makwabtan kasashe domin kawo agajin yaki bisa kare mutuncin nahiyar gabadaya. Daga nan sai yayi bayani ga jama'a inda ya kara masu kwarin gwiywa da karfafesu bisa mahimmancin wannan yaki da za'a fita. Yana gama wannan jawabi ne jama'a suka barke da shewa aka hau yi masa kirari. Nan take sarki Maharaz da sarkin yaki Hibru suka yi wa gabadaya jama'ar jagora, wato suka wuce gaba aka bisu duw a baya. Inda ace mutum na nan tsaye a wajen yaga wannan rundunar ke fitowa daga cikin birnin darul mahabur sahu sahu bisa rakuma, dawakai da alfadarai sai yayi tsammanin cewa gaba daya mutanen duniya ne suka fitowa saboda yawansu. Wannan shine abinda ya faru a birnin darul mahabur bayan kasashen dake nahiyar gaba daya sun hada kai sun fita gagarumin yaki dan kare buranensu daga sharrin sarki dujalu. ********************** Al'amarin Sarki Dujalu kuwa lokacin daya durfafi hanyar kofin bahar Suffiyya tare da dandazon dakarunsa na yaki mutum miliyan dubu daya da suke tafiya bisa wasu zaratan dakarun aljanu suma miliyan dubu daya. Wohoho! Hakika tashin hankali ba a samasa rana zuwa yake ba sallama, idan mutum yayi arba da wannan zuga ta rundunar sarki Dujalu zai iya haukacewa koma zuciyarsa ta buga fat daya, saboda tsananin kwarjininsu gami da bna tsoro, idan aka ce zasu iya tashin duniyar nan kaf a cikin sa'a daya su baje kaf biranen to ba za ayi mamaki ba, idan suna tafiya a kasa bisa turba aka hangosu daga nesa kamar zango dari sai mutum ya jiyo takun sawayensu wnda ke haddasa girgizar kasa, idan kuwa a sama suke tafiya sai kaga sun haddasa gagarumar guguwa wadda ke haddasa bishiyoyi su kama rangaji suna karyewa da zubewa kasa, koguna kuwa su kuma tambal-tambal suna zubewa kasa. Sarki Dujalu na da matan aure guda dari da goma sha daya, amman bai taba samun haihuwa ba, bashi da iyaye kuma bashi da sauran dangi face wata kanwarsa guda daya wacce ta kasance kyakkyawar budurwa ta gaban kwatance wacce suke uwa daya uba daya ana kiranta da suna Hursiyya. A duniya babu abinda sarki Dujalu ke tsantseni sama da kanwarsa Hursiyya, domin ko kadan baya kaunar abinda zai sosa zuciyarta ko kuma ya taba lafiyarta, duk inda kaga sarki Dujalu to fa sai kaga Hursiyya a damansa sam basa rabuwa da juna dare da rana sai dai kwanciyar bacci, kai wani lokaci ma akan cinyar sarki Dujalu Hursiyya ke bacci yana shafa gashin knta gami da raira mata wakoki masu dadin sauraro ko kuma yana bata 'abarai masu dadi da debe kewa, ko kadan Hursiyya bata da sadaukantaka kuma sarki Dujalu bai bata sihirin tsafin sa ba ko guda daya, wani babban abin mamaki a tare da ita shine gabadaya halayenta da ra'ayainta ya sha banban dana dan uwanta sarki Dujalu domin bata son zalunci sannan tana da yawon tausayi. A fagen kyautavkuwa tamkar indararo dan ko yaushe hannunta a bude ya ke, bisa wannan halayya tata ne yasa ta samu daukaka da farin jini a wajen talakawan kasar, har addu'a suke a boye suna fatan Sarki Dujalu ya mutu ta haye kan karagarsa saboda sun san cewa zasu samu yancin kansu. A rayuwar Hursiyya babu abinda ta fi so sama sauraron dadadan labarai, jarumtaka da kuma na abubuwan al'ajabi. Bisa halayen Hursiyya na jin kai da tausayi ne yasa sarki Dujalu ya tsani yin tafiya tare da ita, domin ita ce kadai mahalukiyar da take take masa burki wajen tafiyar da zalunci a harkokin mulkinsa. Kai sau tari ma ko zaman fada baya son yi tare da ita saboda tana yawan katse masa hanzari, kasancewar baya son ganin bacin ransa duk alfarmar data nema baya fasa yi mata, sau tari idan sarki Dujalu ya fusata saboda irin katse masa hanzari da take yi, ko yayi yunkurin dukanta sai ya kasa saboda alkawari daya daukar wa mahaifiyarsu kafin ta mutu, alkawarin kuwa shine ya rike mata Hursiyya bisa amana, kuma komai ta yi bazai hukunta ta ba, sannan zai kula da lafiyarta fiye da yadda zai kula da tasa lafiyar. A duk sa'adda Dujalu ya tuno da wannan alkawari sai ya cizi yatsa kwallar takaici ta zubo masa. A ranar da su sarki Dujalu suka shafe kwanaki goma sha takwas suna tafiya ne izuwa tekun bahar Suffiyya, sai suka yada xango a cikin wani kyakkyawan daji mai yawan ni'ima, Kasancewar yana dauke da koramai, bishiyoyi da kuma kananun dabbobin daji masu saukin farauta gami da kyawawan tsuntsaye, duk irin masifar dake cikin daji da zarar rundunar su sarki Dujalu ta ratso cikin daji sai masifar ta nemi mabuya saboda taga sa gudu maganin ki gudu. Bayan an kafa tantuna a cikin wannan daji mai ni'ima an ci abinci an huta sai Hursiyya taga sarki Dujalu ya kwanta yayi shiru ya shiga zurfin tunani, al'amari daya sosa Zuciyarta kenan ta dube shi ta ce ya kai dan uwana ina dalilin wannan tunanin naka haka mai zurfi, shin kana wasi-wasi ne akan samun nasarar mu ne akan wannan yaki da muka fito ko kuma kana tunanin yadda zuwa nan gaba zaka mulki duniya ne? Yayin da sarki Dujalu yaji wadannan tambayoyi daga bakin yar uwarsa Hursiyya ai yayi murmushi sannan ya sake gyara kwanciyarsa a saman lallausar shinfidarsa irin tasu ta sarakai, ya dubi Hursiyya cikin natsuwa yace da ita ya ke yar uwata kiyi sani cewa duk abinda ika fada ba shi nake tunani ba, ina naxari ne akan yadda soyayya takai Mazan Jiya zuwa ga halaka, har suka rasa komai na duniya, bisa wannan dalili ne nayi alƙawarin cewa bazan taba yarda naso mace fiye da kima ba, domin ita soyayya siradin mutuwa ce, duk wanda ya taka siradin ba makawa sau ya hallaka, haka nan kaidin mace yafi tsinin allura tsini kuma yafi kaifin zabira kaifi, komai jarumtakar mutum kuma komai karfin mulkinsa da karfin arzikinsa mace na iya maida shi rago, fakiri kuma bawa kamar yadda ta faru ga Mazan Jiya irin su Sadauki Hantaru. Koda jin wannan batu sai Hursiyya ta gyara zama sannan ta ce ya kai dan uwana na rokeka bisa darajar mahaifiyarmu ka bani labarin Mazan Jiya da yadda aka yi soyayya ta jefa su ga halaka. Dujalu ya gyada kai tare d cewa ai kin tambayeni labari mai tsawo, wanda in muka farashi ban san ranar gamawa ba, sai dai yana dauke da darasi mai yawa a cikinsa domin zaki samu ilimin zaman duniya, za kuma kiji yadda ake yaudara ta rashin mutunci gami da mummunan cin amana, sannan kuma zaki ji abin tausayi wanda nasan dole ne ki zubar da hawaye, ke idan kika ji wannan labari kin daina yarda da kowa a duniya koda kuwa iyayen da suka haifeki ne. Hursiyya ta sake gyara zama ta ce dan darajar tsafinka da darajar mulkinka ka gaggauta far banu wannan kasaitaccen labarin, ina mai tabbatar maka da cewa ko ina mai tabbatar maka da cewa koda zamu kwana kana jawabi bazan gaji ba, kuma bazan ji bacci ba. Sa'adda da sarki Dujalu yaji haka sai ya bushe da dariya sannan ya ce to shikenan bari na jarabaki na gani idan har zaki iya jurewa, Dujalu yayi gyaran murya sannan ya fara bada labarin da cewa: Kimanin shekara tamanin da suka shude, anyi wani adalin sarki mai suna Kusaidu a birnin Kisra, Sarki Kusaidu ya mallaki dukiya mai tsananin yawa, sannan yana da tarin mayaka Hakazalika akwai manya manyan birane a karkashinsa kimanin guda 40, sarkin Kusaidu nada matar aure guda daya jal wadda suka yi auren saurayi da budurwa ana kiranta Bazira, har bayan shekaru oma da aurensu amman nasu taba samun haihuwa ba, ko kadan wannan matsala bata damu Bazira ba. Amman shi sarki Kusaidu duk sa'adda ya kalli yawan dukiyarsa d kuma karfin mulkinsa ya kuma tuna cewa bashi da magaji sai yayi ta kuka, babu irin neman maganin da sarki Kusaidu baiyi ba amman abu ya gagara, domin saida ya ziyarci ko wanne bangare na duniya dan ganawa da manyan bokaye amman abu ya cutura. Lokacin da Fazira taga hankalin sarki ya ki kwanciya bisa ga matsalar rashin haihuwa, sai ta kadaita da shi ta ce ya kai mijina ka yi sani cewa a duniya bani da farin ciki sai naka, kuma bakin cikinka nawa ne, ni a tawa shawarar tunda dai ni ban haihu da kai ba me zai hana ka kara aure, ko a dace a samu biyan bukata? Koda jin wannan batu sai Sarki Kusaidu ya cika da tsananin mamaki ya ce da ita Kaicon ki ya ke mata ta, tun kafin muyi aure kika kafa mani dokar cewa daga kanki bazan kara ba, kuma na amince da haka ko kin manta ne? Da jin haka sai hawaye ya zubo wa Fazira ta ce ai wata larurar tana kawar da wata, nidai a halin yanzu na janye wannan sharadin in har soyayyata da taka ka tabbata gaskiya ce to ka yi aiki d wannan shawara tawa. Yayin da Sarki Kusaidu ya ji hkaa sai yayi shiru yana tunani ba tare da yace da ita komai ba har izuwa lokaci mai tsawo, daga can kum sia ya dago kai ya dubi Fazira ya ce ki dan bani kwanaki uku zan yi shawara tukunna. Koda jin haka sai Fazira ta cika da farin ciki kuma ta rungume sarki Kusaidu tare da sumbatar goshinsa kna daga bisani ta fice daga cikin turakar tana tsalle gami da murna, ba kaomai ne yasa Fazira farin ciki ba, sai sanin cewa sarki Kusaidu bashi da wani abokin shawara wanda ya wuce bokansa mai suna Boka Ardusa Bn Zabbar. Fiye da shekaru talatin sarki Kusaidu ake harka da boka Ardusa kuma ya yard da shi dari bisa dari, babu wani sirri nasa wanda bai sni ba. Sai dai abin bakin ciki da takaici shine duk tsawon wadannna shekaru boka Ardusa na cin amanar sarki Kusaidu ba tare da ya sani ba. Domin Ardusa ya mayar da Fazira matarsa ta sirri, wannan cin amana ya samo asaline tun daga lokacin Fazira ta so ta auri Sarki Kusaidu, kasancewarta yar wazirin mahaifinsa amma sai sarki Kusaidu ya nuna ko kadan baya sonta da aure, domin ya dauketa kamar kanwarsa ta jini, dalili kuwa shine a gidan su Fazira sarki Kusaidu yayi wasan kasa saboda akwai yayan Fazira sa'ansa ne, kuma abokinsa wanda suka shaku ainun har ya zamana cewa basa rabuwa dare da rana sunansa Asharab. Tun Fazira na karama jininta ya hadu dana Sarki Kusaidu take matukar kaunarsa, lokacin da Fazira ta cika budurwa sai masoyanta suka yi mata ca! Sabida ta kasance kyakkyawar gaske, ita kuwa sai ta tubure ta ce babu wanda take so face yarima Kusaidu. A wannan lokaci mahaifin sarki Kusaidu ne yake mulkin birnin Kisra, kwatsam! Sai aka wayi gari Asharab ya kamu da rashin lafiya har ta kaishi ga kwanciya, al'amarin daya dugunzuma hankalin Yarima kusaidu kenan ya koma gidan su Asharab ana jinyarsa kenan dare da rana ya zamana cewar yayi wa gidan sarki kaura gabadaya, a ranar da Asharab ya kwana tara yana jinya ne sai rai yayi halinsa, bakin ciki a wajen Kusaidu bazai fadu ba, domin sai da ya kwana uku bai ci abinci ba, kuka kuwa dare da rana haka ya dinga yi babu sassauci, nan da nan ya rame ya kuma lalace da kyar aka samu ya dawo daidai ya ci gaba da rayuwa kamar yadda ya saba, tun daga lokacin da Asharab ya rasu sai Kusaidu ya dauke kafarsa daga gidansu Fazira gabadaya ya daina zuwa, hakan ne ya tada hankalin Fazira ta dinga biyoshi har gida tana nuna masa soyayya, shiko ya dinga nuna mata cewa shifa kanwa ya dauketa ba masoyiya ba, har Fazira ta girma ta cika ya mace nan fa ta cigaba da kokarin janye hankalin Yarima Kusaidu amman ya ki amincewa da ita. Sai bayan da mahaifin Kusaidu ya rasune ya gaji sarauta sannan ta soma samun yardarsa albarkacin boka Ardusa. Shidai boka Ardusa hadimin mahaufin sarki Kusaidu ne, ganin haka ne yasa shima Kusaidu ya aminta da shi. A ranar farko da Fazira ta je wajen boka Ardusa da bukatarta ta son auren satki kusaidu, sai ya nuna mata bukatarta mai sauki ce amman fa sai idan ta yarda ta bashi kanta. Sai da Fazira ta shafe wata uku tana nazarin wannan sharadi a karshe dai taga cewa in har bata amince da sharadin boka Ardusa ba, to fa bazata taba samun damar auren sarki Kusaidu ba. Kawai sai ta abince d shi din, a ranar da abin ya faru ne Sarki Kusaidu ya amince da batun aurenta, da mako ya dawo aka daura auren amman duk da cewa Fazira ta auri sarki bata daina zuwa wajen Ardusa ba sun lalatrsu a sirrance, ita kanta Fazira ta yi mamakin yadda ak yi ta cigaba da yarda da boka Ardusa, abinda bata sani ba shine, ya asirceta ne babu yadda za'a yi ya bukaceta ta ki yarda. Haka dai Fazira da Ardusa suka cigaba da cin amanar sarki Kusaidu har tsawon shekaru sirinsu bai taba tonuwa ba. Bayan Fazira taji cewar sarki Kusaidu zai yi shawara sai ta saci jiki ta wuce zuwa gidan boka Ardusa nan ta sanar d shi abinda ya faru da sarki, ta kuma ce lallai ya baiwa sarki shawarar ya kara aure. Boka Ardusa ya kyalkkyale da dare tare da cewa amman ke meye hikimarki akan bashi wannan shawara? Fazira ta dubi boka Ardusa cikin nutsuwa ta ce da shi ka yi sani cewa har abada sarkk ba zai taba haihuwa ba, tunda matsalar rashin haihuwar daga gareshi ta ke, ni kuwa zan iya haihuwa, idan ya auro wata matar ina so kayi aikinka na bokaye kaga ta samu juna biyu, inyaso cikinka da nake dauke da shi a yanzu in na haifeshi sai ya tashi a matsayin dan amaryar sarki, kaga kenan danmu ne zai gaji sarautar, nasan tabbas zaka iya boye nawa cikin har na haihu ba tare da mutane sun sani ba. Lokacin da Fazira tazo daidai nan a batunta sai boka Ardusa ayi shiru, ya fada dogon tunani gami da nazari, daga can sai ya bushe da dariya harda buga kafa a kasa yana mai cewa Hakika ku mata ababan tsorone, ta yaya kika iya kulla wannan dogon makircin acikin dakiku kadan? Nikam tunda nazo duniya ban taba ji ko ganin yaudara da makirci irin wannan ba. Fazira ta bushe da dariyar murna tare da cewa ai bakaga komai ba sai nan gaba tukunna sannan ne zaka gane mu mata mune muke sarrafa duniya da duk abinda ke cikinta, muke haddasa zaman lafiya da rashinsa, kai ko yaki idan kaga ya barke ba zato ba tsammani idan ka yi bincike zakaga snadinsa mune. Koda gama fadin haka sai Fazira ta mike da sauri, tayi wa boka Ardusa sallama domin a wannan lokacin yamma ta yi likis, ta tashi tayi tafiyarta, kuma a wannan lokaci an kusa tashi daga fada, tana tsoron kada sarki ya nemeta bata nan. Kamar yadda Fazira ta shirya makircinta haka al'amuran suka kasance, wato sarki Kusaidu ya auro wata kyakkyawar budurwa jinin sarauta mai suna Shamilat acan wata kasa dake makwabtaka da birnin Kisra mai suna Darul Maabur. Wata uku da tarewar amarya Shamilat sai ga ciki ya bayyana, amman abin mamaki shine ko kadan amarya bata ji wani sauyi a jikinta ba, kuma bata yin wata lalura irin ta masu ciki. Sannu a hankali ciki ya rika girma har ya cika wata tara rana daya sai nakuda tazo wa Shamilat, mata suka taru akanta amman saida Shamilat ta kwana ta wuni tana nakudar bata haihuba. Al'amarin da yayi matukar dugunzuma hankalin sarki kenan ya kasa zaune ko tsaye. A lokacin da shamilat ta samu juna biyu irin farin cikin da sarki Kusaidu yayi ya wuce gaba tunani, domin sai da ya kusa zaucewa saboda tsananin farin ciki, ya rika kyautar dukiyarsa dare da rana, kai sai da takai hatta suturar dake jikinsa yana cirewa gami da baiwa barorin dake gidan sarautar, har sai da aka kulleshi a daki kuma aka hanashi fita. Yayin da nakudar amarya Fazira ta ki cinyewa sai ga uwargida Shamilat ta zo dakin haihuwa, da zuwanta sai ta kuri duk matan dake baiwa Shamilat agaji ta ce duk basu san aikinsu ba ma, kawai sai ta kulle kofar dakin ya zama cewa daga ita sai mai nakudar a cikin dakin, nan take ta shafa cikin amarya Shamilat ai kuwa sai hankalinta ya gushe ta suma, Fazira ta shafi nata cikin kawai sai ga tsohon cikinta ya bayyana kuma nan take nakuda ta zo mata, bayan kamar rabin sa'a Fazira ta haifo santalelen yaro kyakkyawan gaske, cikin hanzari ta gyara jikinta sannan ta gyara jaririn ta ajiyeshi daf da amarya, daga nan ta sake shafar cikin anarya a karo na biyu sai ga jinin haihuwa na zubo wa daga jikinta. Jim kadan amarya ta farfaɗo aiko sai ta ji jariri na tsala kuka a kusa da ita. Koda sauran mutanen gida suka jiyo kukan jariri sai suka rugo izuwa dakin haihuwar suna shewa gami da murna, cikin matukar mamaki. Ai kuwa labari na riskar sarki sai kuwa ya fito daga cikin turakarsa tare da fadawa dakin haihuwar ya dauki jaririn ya rungumeshi yana kukan farin ciki. Sai da aka kwana talatin ana bukukuwa da walimar farin ciki a birnin Kisra saboda murnar wannan haihuwa da akayi wa sarki Kusaidu. A kwana a tashi dan da amarya ta haifa mai suna Hantaru ya fara girma ya cikq shekaru biyar, Hantaru ya taso yaro kyakkyawa mai jarumtaka tq ban al'ajabi, domin tun yana da shekaru iyar yake iya daukar abubuwa masu nauyin gaske, idan kuwa yana wasan kokawa a cikin sa'anninsa babu mai iya kada shi. Kai sai da takai cewa yaran da suka girmeshi ma kada su yake yi. Lokacin da Hantaru ya cika shekaru tara sai ya zama cewa yana satar jiki ya shiga daji yin farauta shi kadai b tare da ya dauki makami ba, sai dai aka ya kamo damisa ko bauna ya shigo da ita gari a mace bisa kafadarsa. Nan da nan jarumtakar Hantaru ya bazu a ko ina a nahiyar, har aka dinga zuwa kallonsa ana mamakin sa, wani abin mamaki a tattare da Hantaru shine ko kadan bai damu da harkar sarauta ba, babu yadda sarki Kusaidu bai yi da shi ba akan ya rinka zuwa fada sun zama tare amman sai ya sulale ya tafi farauta. Baya ga farauta abu abinda Hantaru ke so sama da koyon yaki, dan haka sai ya like wa Sarki yakin birnin Kisra ya zamana cewa kullum yana gidansa yana koyon yaki. Aiko a cikin shekaru bakwai Hantaru ya zama gagarumin mayaki har ma yafi sarkin yaki shahara. Tun sa'ar da Fazira da boka Ardusa suka fa cewar gaba daya hankalin Yarima Hantaru baya kan sarauta sai hankalinsu ya dugunzuma suka shiga kokarin asirce zuciyara domin yayi watsi da harkar farauta data koyon yakin nan. Amman sai suka sha ruwan mamaki domin asirin da suke masa yaki yayi tasiri akansa. Ganin haka ne yasa Boka Ardusa ya dukufa akan binciken gano dalilin faruwar hakan, a cikin binciken nasa ne ya gano cewa nonon da Hantaru ya sha na amarya shine yya janyo ashin tasirin tsafi a jikinsa, domin ita amarya Shamilat tana da wata kariya a jikinta wadda mahaifinta ya shayar da ita tun tana jaririya, kuma babu abinda za a iya yi dan lalata wannan kariya. Koda ganin wannan al'amari sai bakin ciki ya turnuke boka Ardusa, domin ya fahimci cewa har abada Hantaru bai yi sarautar birnin Kisra ba muddin baiyi watsi da harkokin farauta ba ya kama na fada ba. Al'amarin sarki Kusaidu kuwa da amarya Shamilat hankalinsu yafi na kowa dugunzuma bisa ganin yadda dansu yaki damu da komai face harkar farauta da kuma yaki, ko kadan Hantaru bai shaku da sarki ba sai dai mahaifiyarsa Shamilat, kuma yana bata mafi yawa daga lokitansa a gidan abokansa yayan mafarauta na birnin, sai da sarki Kusaidu ya gana da boka Ardusa sau 10 akan wannan matsala, amman ko yaushe sai dai boka Ardusa yace da sarki ai sai dai ayi hakuri amma babu abinda za a iya yi. Boka Ardusa bai fada wa Shamilat dalilin da yasa tsafi baya tasiri a jikin Yarima Hantaru ba, dalili kuwa shine idan tasan da hakan hankalinta zai dugunzuma ta bazama neman taimako a wajen wasu bokayen kuma a haka asirinsa na iya tonuwa har sarki Kusaidu ya gane cin amanar da suke masa. Wata rana amarya Shamilat na zaune tare da sarki Kusaidu suna fira sai ta ce da shi ya kai mijina ka sani cewa tunda ka aureni ka raboni da kasarmu ban taba kaiwa iyayena ziyara ba sai dai su sukawo mani, ina son kayinmani izinin zuwa a wannan karon, nayi kokari nayi shiri na je. Idan da hali ma zan so na tafi da yarima domin yaga dukkanin danginsa na can. Yayin da sarki Kusaidu yaji wannan batu sai yayi ajiyar zuciya Ya ce yake mata ta kiyi sani cewa b laifina bane ki kai wannan ziyara, ina tsoron dazuzxukan dake kan wannan hanyar ne kafin a isa birninku, ni kaina sau daya nabi wannan hanyar lokacin da naje neman aurenki. Lokacin da zanje sai da akayi gagarumin shirin yaki na dakaru masu yawan gaske, kuma sai da Boka Ardusa yayi mani rakiya dan tabbatar da tsaro. Yayin da shamilat haka sai ta yi murmushi ta ce ya kai mijina indai dan tsautsayin hanya ne ka kwantar da hankalinka, ina mai tabbatar maka da cewa babu abinda zai samemu, domin tun ina yarinya karama iyayena suka bani tsari na musamman, bama ni ba hatta dana da ya sha nono na ya samu wannan tsari, kaima daka aureni ka samu wannan tsari, indai kana cikin hayyacinka to babu wani mahaluki daya isa ya cutar da kai. Ni nasan cewa baka son rabuwa da yarima daidai da rana daya shiyasa baka son nayi wannan tafiya Koda jin wannan batu sai hawaye ya zubo wa sarki Kusaidu ya ce Tabbatas kin fadi gaskiya yake mata ta, amman ki sani a halin yanzu babu abinda ke damuna sama da rashin shakuwata da Yarima, ko kadan bai damu da ni ba tamkar ba ni na haifeshi ba, duk shawarar dana bashi baya amfani da ita, har gwara ma ke naga yana matukar kaunarki, kuma baya son yaga bacin ranki. Sa'adda sarki Kusaidu yazo nan a zancensa sai tausayinsa ya kama Shamilat, ta dafa kafarsa ta ce kada ka damu ya kai mijina nayi maka alƙawari da zarar munje garinmu mun dawo zakaga sauyi a tare da Yarima zai kaunaceka kamar yadda ko wane da yake kaunar ubansa Hakazalika zai shaku da kai, sannan zai ajiye harkokin farauta ya rungumi na sarauta. Da jin haka sai sarki Kusaidu ya dubi Shamilat cikin tsananin mamaki ya ce Ta yaya hakan zata faru? Shamilat ta ce kakana shahararren boka ne wanda babu kamarsa a nahiyarmu, ina mai tabbatar maka da cewa ko Boka Ardusa aka sai dai suyi kunnen doki a karfin sihiri, kai ina da tabbacin kakana yafi Ardusa tarin ilimin tsafi, lallai nasan zai taimakemu ya juyo da hankalin yarima zuwa kan tafarkin da muke so. Yayin da sarki Kusaidu ya ji wannan batu sai ya cika da farin ciki kuma ya amince da batun tafiyar Shamilat. Tun kafin dare yayi Shamilat ta tura aka kira mata Yarima Hantaru tayi masa albishir da tafiyar da zasu yi a gobe ita da shi izuwa can mahaifarta ta darul maabur. Koda jin haka sai Hantaru ya cika da tsananin farin ciki domin a rayuwarsq bashi da wani buri da ya wuce yayi doguwar tafiya wacce zai ratsa ta cikin dazuka masu ababan hadari, kamar yan fashi da muggan dabbobin daji, ba dan komai ba sai don ya jaraba iyakar tsawagaron ku riyarsa da kuma shan wahalarsa, ya kuma ga iyakar karfin damtsensa, tunda ya ke sau daya ya taba halartar yaki a birnin Kisra kuma lokacin da yaje filin yakin ma saura kiris a gama da abokan gaba, a takaice dai Yarima Hantaru yana so yayi doguwar fafatawa da aboka gaba. Saboda tsananin dokin da yarima Hantaru yake saboda tafiyar da zasu yi tun a daren ya kimtsa kayansa sannan ya daura wa dokinsa sirdi sannan ya tanadi kayan yakinsa. Lokacin daya kwanta bacci sai idanunsa suka bushe ya kasa bacci saboda tunanin tafiyar ta gobe. Bisa wannan dalili ne yasa ya tafi dakin mahaifiyarsa Shamilat, da shigarsa cikin turakar sai ya isketa a zaune tayibshiru tana tunani sai faman murmushi take yi kamar wacce take magana da wani. Har Hantaru ya zauna kusa da ita amman bata san ya shigo ba, sai da ya dafa hannunta sannan tayi firgigit kamar wacce ta farka daga bacci, Hantaru ya dubi Shamilat cikin mamaki ya ce ya ke ummina tunanin me kike yi ne haka wanda har ya hanaki ki kwanta kiyi bacci. Sa'adda Shamilat ta ji wannan tambaya sai ta yi murmushi sannan ta ce Ya kai dana kayi sani cewa tsananin murna ce ta hanani na kwanta nayi bacci, saboda ina murnar cewa zanje naga kakana wanda ya haifi ubana Boka Sulbaini Bn Ukash. Kayi sani cewa a hannun Sulbaini na girma har nayi wayo, daga baya da za a yi mani aure aka rabani da shi, a ranar da za'a rabamu da shi munsha kuka tamkar ranmu zai fita saboda sabo da juna, rabona da shi yau shekara 16 kenan, nasan cewa yanzu ya kara tsufa ainun babban burina shine na sake saduwa da shi kafin rai yayi halinsa. Koda Shamilat ta zo nan a zanjenta sai hawaye ya zubo mata, take Hantaru yaji tausayinta ya kamashi har shima kwalla ta zubo masa, Hantaru ya rungume Shamilat gana mai cewa ya ke ummina ki kwantar da hankalinki domin naji a jikina cewar wannan kaka naki na nan a raye kuma tabbas zamu je mu riskeshi. Tsawon yan dakiku duk su biyu suka yi shiru babu wabda ya ce kala, daga can sai yarima ya janye jikinsa daga jikin nata suka dubi juna sannan ya ce Ya ke ummina shin ba kya bani labarin yadda rayuwar mutanen birninku take ba? Lokacin da shamilat ta ji wannan tambaya sai ta yi murmushi sannan ta gyara zamanta ta ce Mafi akasarin mutanen birninmu mafarauta ne da kuma makera, mahaifina shine sarkin makera kuma shine galadiman sarkinmu ana kiransa da suna Shuraim Bn Alkas. Tsakanin zuri'armu ta makera data mafarauta babu kyakkyawar fahimta ko zumunci mai karfi, kuma babu auratayya mai yawa. Babu abinda yafi burgeni a garinmu face wata al'ada da aka saba yi duk karshen shekara, al'adarvita ce za'a zabo budurwar data fi dukkanin yan matan garin kyau a sa gasar neman aurenta a tsakanin jaruman samari, masu ji da sadaukantaka. Yanayin gasar shine za a saki barewa a daji a kasa tsere duk saurayin da yafi kowa gudu ya kamonwannan barewa to shi zai auri wannan kyakkyawar budurwa. A lokacin da ake tseren gudun an yarda samarin su dinga bangaje juna duk wanda ya fadi kasa to ya fita daga cikin gasr kenan. Gabadaya mutanen garin banda al'karan gasar suna hawa kna wani dogon tsauni ne su tsitsaya dan su hango abinda ke faruwa, su kuwa alkalan gasar suna bin bayan mahayan ne, lokacin da shamilat ta zo nan a zancenta sai Yarima Hantaru yaji soyayyar darul maabur ta lullubeshi domin ya fahimci cewa can ne ya dace da yanayin rayuwarsa, dan haka sai ya sake cika da tsananin farin ciki. Yadda yarima yaga rana haka yaga dare, wato har gari ya waye bai runtsu ba, washegari da sassafe ya tashi tunma kafin alfijir ya keto yayi wanka ya kuma sanya tufafinsa, yana gama kimtsawa kuyanga ta kawo masa abincin kalaci, amman yana yin lokamar farko sai yaji ya koshi dan haka sai ya mike ya bar abincin ya tafi dakin Shamilat, yana zuwa ya iske ta, tuni itama ta gama shiryawa shi take jira kawai. Nan take kuyangi suka fito da kayayyakin Shamilat har da guzurin da zasu tafi da shi da kuma tsaraba, duk wannan abu da ke faruwa Zarifa bata sani ba sai a lokacin da sarki ya fito daga cikin turakarsa ya riski Shamilat da hantaru tsaye cikin turakarsa, kawai sai ta riske sarki Kusaidu yana bankwana da shamilat har yana rungume yarima Hantaru yana zubar da hawaye. A gigice zarifa ta taho da gudu ta karaso garesu ta kama hannu Yarima Hantaru ta rike tana mai cewa ya kai dana ina zaku tafi haka amman baku fada mani ba? Yarima ya dubi Zarifa a wulakance ya ce zamu tafi garin kakannina ni da mahaifiyata. Koda jin haka sai Zarifa ta ji zuciyarta ta buga da karfin gaske, har bata san sa'adda ta kama surutai ba tana cewa ai bai kamata ku tafi yanzu ba, zai fi kau ku bari ayi maku shiri na musamman. Yarima Hantaru yq ce ai babu abinda zai hana mu wannan tafiya a yau, sai dai fitar ruhi daga cikin gangar jiki. Gama fadin hakan keda wuya sai Hantaru ya kama hannun Shamilat ya ja ta suka tafi, barori ba biye da su da kaya niki-niki. Koda ganin haka sai Zarifa ta sulale tq fice daga cikin gidan sarautar ba tare da kowa ya sani ba. Cikin hanzari Zarifa ta haye bisa doki ta ruga izuwa gidan Boka Ardusa domin ta sanar da shi halin da ake ciki dan yasan matakin da zai dauka kada asirinsu ya tonu. Boka Ardusa na zaune shi kadai a cikin harabar gidansa ya zuba wasu alkaraman sihiri a gabansa yana nazari sai kawai yaga Zarifa ta shigo da gudu kuma a gigice har tana tuntube zata fadi kasa. Koda ta iso gabansa sai ta zube kasa tana mai faman haki, kuma ta bude baki zata yi magana sai kawai Boka Ardusa ya daga mata hannu yana mai yi mata nuni ta yi shiru. Bisa dole zarifa tayi shiru bata ce komai ba, kuma ta kura sama idanu har sai da ya gama yan tsubbace-tsubbacensa. Boka Ardusa ya juyo ya dubi Zarifa ya ce da ita ai nasan abinda ke tafe da ke, kuma tun a jiya nasan da batun tafiyar amarya Shamilat da danmu Yarima. Ki kwantar da hankalinki tamkar tsumma a randa domin babu abinda zai faru. Ina mai tabbatar maki da cewa muddin ina numfashi a doron kasa har abada asirinmu bazai tonu ba. Ki saki ranki kije kita bacci harda munshari, da sannu burinmu zai cika danmu ya zama sarkin birnin darul maabur. Koda jin wannan batu sai Zarifa ta kyalkkyale da dariya, can kuma sai ta hade fuska ta yi shiru kamar tana nazari. Boka Ardusa ya dubeta cikin damuwa ya ce tunanin me kuma kike yi, alhalin na fada maki cewar babu abinda zai faru? Zarifa ta yi ajiyar zuciya ta ce ni abinda nake tsoro shine kada yarima yayi zamansa acan birnin darul mahabur yaki dawowa nan gida, abu na biyu ni fa yanzu na shiga matsananciyar damuwa saboda dana yarima bai san cewa nice mahaifiyarsa ta gaske ba, shin kana tsammanin cewa nan gaba zai karbeni ne a matsayin uwa ? Boka Ardusa ya ce kwarai kuwa, kuma sai ya kaunace mu fiye da kowa a rayuwarsa nayi maki wannan alkawari, kedai ki ci gaba da hakuri al'amarine na lokaci, idan muka ce zamu yi wa lamarin gaggawa to fa lallai burinmu ba zai cika ba. Haka dai Boka Ardusa yayita lallamin Zarifa har hankalinta ya kwanta, suka aikata cin amanar da suka saba sannan ta tafi. Mazan Jiya Part 15 #Cigaba A lokacin da shumilat da yarima hantaru suka fita kofar gari sai suka kama hanya batareda fargabar komaiba su kwana nan su tashi chan saida suka bar birnin darul maabur da shiga su daji na fark6 wanda ake kira sujud sai shamilat taja linzamin dokinta ta tsaya shima sadauki hantaru saiya tsaida dokin nashin, shamilat ta kasa kunnenta bataji motsin komai ba sai tayiwa yarima hantaru magana cikin rada tace akwai muggan yan fashi a wannan daji kuma sun iya nada muggan tarkuna sai mun kula da kyau koda jin wannan magana sai hantaru yayi mata nuni data sauka daga kan dokinta batareda wata gardama b shamilat ta sauko shima saiya sauko daga kan nashi. kawai sai yasaki dokin nasa yayi gaba koda dokin nasa yayi tafiyar kamar taku talatin saiya zurma cikin wani wawakeken rami mai zurfin gaske saiga wadansu samudawan yan fashi suna mai rugowa daga cikin maboya suna zuwa bakin ramin suna tsayawa adadin yan fashin ya haura 300 dukkaninsu sun kasance majiya karfi kuma suna daukeda muggao makaman yaki sun shafe fuskokinsu da bakin shuni bayan yan fashin sun gama yiwa wawakeken ramin kawanya rai suka fuskanci cewa yaufa karensu bai kama zomo ba domin doki ne kawai ya fada cikin ramin babu mahayi akan dokin babu dukia cikin tsananin fushi shugaban yan fashi ya dubi sauran dakarun ya daka musu tsawa yace tsayuwar me kuke maza ku baxama neman mai wannan dokin kafin yagama rufe bakinshi sun tarwatse sun rarrabu acikin dajin, ashe dvk abin da akeyi hantaru da shamilat na labe acikin wani duhuwa suna hangowa koda hantaru yaga yan fashin nan sun rarrabu suna farautarsu sai ya cewa shamilat ta dada buya acikin wannan duhuwa shi kuma sai yakama wata doguwar bishia yakama hawa samanta hantaru yayi lamo acikin ganyen bishiyar duk dan fashin dayaxo inda shamilat ke boye sai hantaru ya diro ta bayansa ya masa mangara daya ya fadi sumamme sannan ya kwashe makanshi yayi sama dasu a haka saida ya sumarda sama da yan fashi 50 koda yaga zasu gano inda shamilat ke boye saiya sauko kasa ya dauke ta daga wajen ya ruga zuwa inda wawakeken ramin nan yake wanda dokinsa ya fada ciki!! wohohoh nan take hantaru ya shiga cikin ramin nan ya dauko dokinshi kafin hantaru ya juya ya daura shamilat akan dokinsa sai yaga yan fashin sun masu kawanya kimanin su 300 da doriya tuni shugaban yan fashin dora wata wuka mai tsananin kaifi akan wuyan shumilat cikin firgici hantaru ya dubeshi yana mai daka mishi tsawa yace ku kwashi duk abinda kuke so daga dukiya amma inamai gargadinku da kadaku kuskura ku tuba lafiyar mahaifiyata koda jin haka sai shugaban yan fashin yace aiko sai mun dauki fansar yan uwanmu daka sumar ka kwashe musu makamai yanxu xan kashe mahaifiyartaka sannan kaima nayi maka kisan gilla na kwashe dukiyar taku kafin hantaru ya budi baki yace wani abu tuni shugaban yan fashin nan ya dadara wukar nashin akan wuyan shumilat bisa mamaki sai yaji kamar akan dutse ya dadara cikin zafin nama hantaru ya zare wata wuka ajikin shi Cikin zafin nama hantaru ya zare wata wuka ajikinshi ya cillata ta cake a goshin shugaban yan fashin ya sulale kasa matacce koda ganin haka sai sauran yan fashin suka afkawa hantaru suna masu kai mishi sara da suka ta koina kaicoh! inda yan fashin nan sun san abinda zai biyo baya da dukkaninsu sun nemi gudu tsira. koda sukayiwa hantaru kawanya kawai sai yayi wuf yakama kafar daya acikinsu ya maidashi makaminshi da kuma garkuwanshi ya dinga tare sara dashi kuma yana maida martani dashh nan danan suka daddatsa dan uwan nasu duk wanda hantaru ya makawa dan uwan nasu sai kaga ya fadi sumamme koh matacce nan fah akarasa mutum daya daga cikinsu wanda zai iya koda lakutar jikin hantaru saboda tsananin zafin namanshi da karfin bugunshi kafin cikar sa'a dari biu duk ya bazar dasu akasa mattatu a sannane ne hantaru ya dubi shumilat cikin matukar mamaki yace yake ummina yaya akayi wuka ta kasa yanka ki? shamilat tayi murmushi tace shin kamanta cewa ubana sarkin makerane babu wani karfe dazai iya huda jikina koda kaima kanka karfe bazai cinkaba saboda kasha a nono shin kataba jarba karfe acikin ka? hantaru yace Aah amma barina jarraba yanxu nagani nan take hantaru ya zare takobinsa ya yanki dantsen hannunsa aiko sai yaga ko kortsanuwa bai yiba kawai sai ya cika da tsananin mamaki. batareda bata lokaci ba suka hau dawakansu suka cigaba da tafiya suna masu kada dawakan gaba suka bar yan fashin a zube a kasa matattu ru hantaru suka cigaba da tafia har tsawon kwana sha daya basu sake haduwa da wani mugun abuba da tsakar ranar kwana na shadayan ne suka shigo cikin wani bakin daji mai ban tsoro domin babu komai acikin shi tsaunuka masu tsawo da kwazazzabai da shigarsu cikin dajin hantaru ya aiyana a ranshi lallai baza'a rasa muggan halittu acikin shiba koda gama aina haka sai ya zare takobinshi yaceda shamilat ta dawo nashi dokin shamilat batayi wani gardama ba tayi yadda ya umarceta yin hakan keda wuya sai sukaga wadansu manyan gwaggon biri sunata fitowa daga cikin kogunan dutsen nan suka cigaba da bullowaa kamar bazasu kare ba koda ganin gwaggunan birin sai hankalin shumila da hantaru ya dugunxuma domin basu taba ganin birrai masu girma da muniba kuma koba komai sarkin yawa yafi sarkin karfi hantaru yasake kankame takobinshi dakyau yana ainawa arranshi cewa yau komin rintsi da tsanani baxai bari a taba lfy mahaifiyarshi ba adaidai wannan lokacin ne shamilat taji nadama tazo mata abisa wannan tafia zuwa birnin iyayenta nan take ta tunoda zancenda mijinta a lokacin da yake fadamata hadarin dayake kan wannan hanya. sannu a hankali birurrukannan suka cigabada matsowa suna yiwa dawakansu hantaru kawanya sukansu dawakan saida suka kama ruri da haniniya bisa gani birurrukan,shiko hantaru koh gizo baiyiba yaci gaba da rike linzamin dokinshi da hannu daya dayan hannun kuma na rikeda takobi wannan birran dai sunfi shekara arba'in acikin wannan dajin idan maza suka kama take suke kashe su inko mata ne sai su tafi dasu cikin gidajensu suna lalata dasu koda birurrukan suka tasan ma hantaru sai shima yayi kansu yana mai saransu yana bangajesu da kafa suna zubewa kasa bisa mamaki sai hantaru yaga ai takobi bata tasiri acikinsu duk sa'adda ya sara sai yaji kamar dutse ya sara nan fah birran suka fara kokarin su hallakashi amma sai yazamo musu alakakai yayinda hantaru ya gano nufin birran nan kuma yasan takobinsa batada wani amfani sai zuciyarshi ta harxuka yayi jifa da takobinsa cikin zafin nama ya goya shamilat a bayansa sannan ya diro kan dokin aka cigabada gumurzu mai ban alajabi domin duk inda hantaru ya kai duka saidai kaga birurrukan sun zube a kasa duk yawan nasu sai yaxamo na banza domin sun kasa koda lagutar jikinshi da faratunsu babban abinda ya tayarwa hantaru hankali dazarar ya zubar da birurrukan a kasa sai sumike zunbur su sake afka mishi runa masu kai mishi cizo da yakushi suko birurrakan sunyi matukar mamaki domin basu taba haduwa da shaidanin mutum irin hantaru ba, haka dai aka cigabada wannan fafatawa har tsawon sa'a daya shibai nakasa suba kuma bai kashe koda daya daga cikinsu ba ka suma basu hallakashiba tuni shumilat ta acikada tsananin mamakin bisa ganin jarumtakar hantaru domin bata taba tsammanin yakai hakaba babu abinda ya bata mamaki kamar yadda birurrukan nan suka kasa kai shi kasa wani lokacin har dandaxo sukeyi waje guda su tafo da gudu domin su hallakashi amma sai kaga ya tokare su ya watsasu. lokacin da hantaru yaga cewa lallai idan kara sa'a daya ana wannan gumurxun zasu iya samun nasara akanshi saiya chanza salon fadan kawai sai ya dinga kama hannayensu da kafafunsu yana cisgewa saidai kaga jini na tsartuwa na feshi nan birurrukan suka dinga kururuwa suna zubewa kasa a mace.. wohohoho!! maza maganin maza hakika birurrukan nan sunga bala'i domin kafin su ankara hantaru ya kashe samada guda duba biyar daga cikinsu saida takai birurrukan sun fara jada baya kai da sukaga abin yafi kafinsu rugawa sukayi cikin kogunan koda ganin haka hantaru ya yunkura da nufin yabisu cikin kogon dutsen sai shamilat ta gargadeshi kada ya bisu cikin kogon dutsen nan domin kowa a gidashi sarki ne, ka kyalesu kawau mu cigaba da tafiyarmu ai nasan ba zasu sake biyomu ba domin sun tsaga basuga jini ba. Hantaru yayinkwafa sannan ya ce kash! Ummina naso ki kyaleni na cigaba da yaki da burirrikan nan har sai naga babu dayansu da ya rage mai numfashi. Shamilat ta yi murmushi ta ce na gaisheka dana, hakika ina farin ciki da samunka domin ayau ne nasan cewa ina da namijin duniya kuma jarumin jarumai. Hantaru ya ce ai dukkan godiya ta tabbata a gareki da kika zama uwata na sha nononki har ya zama garkuwa a gareni. Hakika dole ne nayi alfahari da zuri'arki domin ina ganin cewa sadaukarnan tawa a wajensu na gadota. Shamilat ta sake yin murmushi ta ce tabbas mahaifina gawurtaccen jarumi ne na gaske mai tarwatsa maza a filin daga ina ganin cewa shi ka gado kuma gashi har ma ka fishi yarinta. ********************** Mazan Jiya Part 16 Labarin Sadauki hantaru mai takobin #saiful lujara na mazan jiya #Cigaba Kafin shumilat ta rufe bakinta sai sukaji sautin taku daga cikin kogon dutseo nan tamkar sawun giwa koda hantaru da shamilat suka waiga nan take hantaru yayi arba da abinda yarazanashi yayi matukar firgitasu ba wani suka ganiba sai wani katoton gwaggon biri wanda girmarsa ya ninka na wadannan birurru kan sau biyar katon goggon birin nan ya dunfafo inda su hantaru ya yana tafe yana nishi da gurnani takun tafiyar tasa na haddasa karamar girgixar kasa koda ganin haka sai shamilat ta kara rudewa tana mai jan hantaru tana cewa zomu gudu yakai dana tabbas bazaka da wannan birin ba hantaru ya cije ya tsaya cak sannan ya dubi shamilat yace ai faduwar gaba asaran namiji ce kede kijada baya ki zuba ido kiga abinda zai faru a rude shamilat ta juya ta labe a bayan wata bishia tana leke sukuwa birurrukan sai suka haukan duwatsu suka zuba idanu domin suga abinda zai faru tsakanin hantaru da shugabansu asannan ne hantaru ya gane cewa wannan narkeken birin shine shugabansu kuma yaransane sukaje suka kirawo shi a fusace shugaba birurrukan yayi kan hantaru lokacin da sauran yaran nashi suka fara wani irin gurnani runa mai mishi kirari kawai sai hantaru ya dunkule yan yatsunsa ya gyara tsayuwa, cikin shammaci birin ya gabzawa hantaru naushi a fuskanshi saboda karfin daushin saida hantaru yayi sama ya fado kasa kuma jini yayi tartsuwa daga bakinshi har hakorinshi guda ya fadi akasa take hantaru ya tashi a fusace zuciyarshi ta fara tafarfasa koda ganin haka sai sauran birurrukan ruka fara ihu suna shewa saboda nasarar da shugabansu yasamu akan hantaru alamarin daya kara fusata hantaru kenan baxato ba tsammani hantaru ya daka tsalle ya gabza mishi naushi a kasan cibiya kawai sai akaga birin ya kame kamar an zare duka lakar jikinsa nan take kuwa ya sulale kasa ko shurawa bai sakeyi ba hantaru ya daga kai sama ya dubi birurrukan na ya kwarara uban ihu nan take suka tarwatse suna masu fantamawa cikin daji batareda sanin inda xasu tsayaba, Kaicon inbada wuyya ta kai wuya ya za ayi wadannan muggan burirrikan har su guje wa biladama guda daya jal. Bayan birurrukan sun gudu sai shamilat ta fito daga bayan bishiyarda take ta rugo da gudu cikin farin ciki tana mai cewa hakika yau kayi bajintar da bayantaba mancewa da itaba suka rungume juna daga can sai shamilat da dauki takobin Hantaru ta sare kan wannan birin ta cire a cikin wani icce. Koda ganin haka sai Hantaru ya dubi mahaifiyar ta shi ya ce da ita ya ke ummina me kuma zakiyi da kan wannan birin? Shamilat tayi murmushi ta cw da shi ai d shi zan tafi, kuma zanyita ajiyar kokon kan wannan birin har iya tsawon rayuwata, domin abun tarihi ne wanda har abada bai kamata a manta da shi ba, ya dana kayi sani cewa kayi gagarumar bajinta wajen kashe wannan buri. Nan de hantaru da shamilat suka yada zango suka kunna wuta suna jin dumi saboda sanyin dake kadawa. kashegari da safe suka kada rakumansu sukayi gaba su hantaru suka cigaba da ratsa dazuzzuka iri iri a ranar kwana na goma sha biyar ne suka shigo cikin daji mai girman gaske abinda ya fara daukan hankalin hantaru shine gaba daya harabar dajin komai tsab yake babu kazanta a ko ina, sannan ga kuma wata irin iska mai ni'imah na kadawa koda ganin wannan wuri sai murna ta kama hantaru ya yunkura zai sauko daga kan dokinsa ba caraf! sai shumailat ta rike hannunsa tace kadaka sauka yakai dana wannan daji baza'a rasa aljanu acikin saba hantaru yayi murmushi yace yake ummina inaso kisani cewa wahala ga da namiji ibada ce, haka kuma tsoro tsanani ne na hallaka da rashi. Koda gama fadan haka sai hantaru ya sauko daga dokinsa ya xare takobinsa ya rike linzamin dokin ita kuwa shamilat saita dinga binsa abaya a hankali tana wauge-wauge kwatsam sai hantaru yaga wani katon lambu a gabansa wanda ke cike da yayan itatuwa iri-iri kamar su tuffa, inibi, fasa dabur dadai sauransu, bazato ba tsammani sai yaga wata yarinya budurwa kwance akan wata shimfida tana cin tufa fuskan a cike da annuri a iya rayuwar hantaru bai taba ganin mace mai kyan taba amma abin takaici daya dubi kafarta sai yaga kofato koda kyakyawar ta kalli hantaru rai ya kauda kai yaje ya sai ya kaufa fuska yaje ya tsinki tufa guda daya ya fara ci, alamarin dayabawa budurwar mamaki kenan ta bishi da kallo cikin takaici ta kuma shumailat rai taki shiga cikin lambun alokacin da hantaru yagama cinye tafar kawai sai yaji an rike hannunsa bawata bace face wannar budurwar daya wuce kwance,budurwar ta dubeshi cikin fushi tace haba bil'adama ka shigo lambu na babu sallama ka tsinki tuffata ka cinye. sa'adda hantaru yaji wannan sai kunya ta kamashi domin yasan baiyi da'a ba kuma bai nuna shi dane mai tarbiyya ba, cikin sanyin murya ya dubi budurwar yace yake wannan ma'abociyar kyau ki gafarceni hakika nayi kuskure amma ki sani kayan marmarin dake cikin lambun sunada daukan ido. budurwar ta bushe da dariya sannan ta murtuke fuska tace hakika kude bil'adama da rashin hakurh kuke to kasani cewa kaciwa kanka bala'i domin abune mawuyaci ka tsira da rayuwar ka ina yimaka albishir cewa ka fado cikin tarkon uwar mayu ta aljanu koda gama fadin hakan sai budurwar ta rikide ta dawo wata tsohumaw mummunar aljana mai matukar ban tsoro hantaru ya yunkuri da nufin ya kaimata sara sai yaji cikinsa ya murde ya fara ciwo kafin cikan dakika biu ya fara aman jini nan take fadi kasa sumamme. Koda shumailat taga abinda ya faru da hantaru sai itama ta fadi kasa sumammiya. lokacin da shumila ta farfado daga dogon suman datayi saita tsinci kanta acikin wanin irin gida an daureta da wata katuwar sarka shide wannan gida an gina shine da zallan duwatsun wuta kuma babu komai acikinsa face wata katuwar tukuba wacce aka hada guma guman itatuwa suna taci da wuta saman wutar an daura wani gado yayi jawur. kwatsam sai shamilat ta jiyo hayania daga can bangaren yammacin gidan sannu a hankali ya ringa karuwa yana cika dodon kunne daga can saiga dandazon wasu yayan aljanu sama dasu million 40 sun taho da gudu suna tsalle a tsakiyar su wannan mummunar aljanan ne dauke da hantaru su duka suka tunkaro inda tukubar wuta take koda ganin haka sai shamilat ta fahimci cewa cikin wannan gadon wuta aljanar nan zata daura hantaru shamilat ta kurma ihu tana kuka tana mai rokon aljanar kadata kona mata danta aljannar bata dubi shamilat ba saida suka iso dab da wutar sannan ta tsaya cak tana kyalkyala daria tace yake wannan bil'adama kiyi sani cewa idan ban gasa wannan danaki ba na baiwa yayana sunci duk mutuwa zasuyi ayau. kuma basu iya haura kwana 40 batareda sunci naman bil'adama ba kinga kuwa da bai fi ɗa ba. Kodajin haka sai shumilat ta fashe da kuka, aljanar ta sake bushewa da dariya a karo na biu tace ai gara kisha kukanki ki more kafin na dawo kanki domin idan na gasaki ni kadai zanyi walimanki domin yayana basa cin nama mace cikin tsananin fushi shamilat ta dubi aljanar tace tir dake wannan la'ananniar maiya inda dana acikin hayyacinsa yake dakin raina kanki domin baki isa kiyi masa komai ba sa'adda aljannar taji haka sai ta bushe da daria sannan ta dakawa shamilat tsawa tace ke bil'adama kiyi sani cewa agaban sarauniyar mayun aljanun duniya kike babu wani mahaluki daya isa ya hallakani sa'ar ki daya mijina baya nan ya tafi farautar bil'adama dayanzu kema mun gama dake dolene na hakura sai yadawo domin akwai yajin dazai tafo mana dashi wanda muke jin dadincin naman bil'adama dashi. ******************** Mazan Jiya Part 17 Labarin Sadauki Hantaru mai takobin saiful lujara na Mazan Jiya #Cigaba Gama fadin hakan keda wuya sai uwar mayu ta yunkara zata daura hantaru akan gadon wutan bazato ba tsammani sai sukaga hantaru ya mike zumbur ya daka tsalle sama daga kan tafin hannun ta kafin takai masa cafka cikin zafin nama ya gabza mata naushi a idon ta take hannun nasa ya burma cikin kwarmin idanun nata, koda ya zaro hannun nasa saiga kwayan idanun nata ya fado kasa nanfa jini ya kama feshi uwar mayu takama kururuwa tana katan tanwa saboda tsananin zafi da takeji a cikin idanun ta yayin da yayan uwar mayu sukaga abunda yafaru da mahaifiyarsu sai sukayi caa akan hantaru da nufin su yayyaga shi su cinye shi danye abinda basu saniba sun gamu da gamon su maimakon sadauki hantaru yayi amfani da takobin sa wajen yakar su sai yayi wurgi da takobin sa ya afka musu yadinga cafkar wuyan su yana gwara kawunan su nanfa kafun a jima hantaru ya hallaka sama da guda dubu dari a daidai wannan lokaci ne uwar mayu tadawo hayyacin ta koda taga mummunar barnar da hantaru yayi mata saita fusata ta runtuma sabon ihu da kukan bakin ciki shi kansa hantaru saida ya razana sakama kon jin sabon ihun datayi suko sauran yayan nata dasuka rage sai suka ruga izuwa bayanta suka tsaitsaya uwar mayu ta tunkari hantaru da mugun nufi shima sai ya tunkaro ta bada jin tsoron komai ba koda ya rage baifi taku goma su gamu sai hantaru ya ruga da gudu yayi tsalle sama yakai mata wawan naushi da nufin ya fasa daya idon cikin zafin nama uwar mayu ta kade shi da hannunta take hantaru ya maku da dirkar gini ya fado kasa a matukar galabaice koda uwar mayu taga hantaru a kasa ya kasa tashi saita rugo da gudu ta daga kafar ta sama ta kawo masa wawan taku da nufin ta mutsuke shi cikin zafin nama hantaru ya goce saboda karfin takun saida kafar uwar mayu ta nutse cikin kasa har gwuiwan ta uwar mayu ta zare kafar da sauri ta cigaba da kaiwa hantaru taku yana gocewa kafun ajima harabar gidan ya cika da ramuka ita kanta uwar mayu saida ta gaji ainun takama haki a sannan ne hantaru ya samu ya mike tsaye aiko sai suka kasa tsere ta dinga binsa tana kai masa cafka tana wangame baki domin ta hadiye kansa gabadaya aduk sa'adda ta karta mashi farata a jikin shi saidai taji kamar ana karta takobi akan dutse kuma ko korzanewa bayayi cikin dakika kadan gidan ya hautsine hankalin kowa ya dugunzuma domin gunguma gunguman duwatsu ne na wuta ke fadowa kasa su kansu yayan uwar mayu saida suka firgice suna neman mafaka itako shamilat tuni dirkar da'aka daure ta a jiki ta karye ta fadi sannan wani katon dutse ya fado akan dirkar lokacin da hantaru ya waigo yaga halin da shamilat ta shiga sai hankalin sa ya dugunzuma sabona yasan cewa idan ta dade a kasan wannan katon dutse na wuta kasa zata iya zaftarewa a wannan lokaci ne hantaru ya fusata don haka saiya daina gudun yama tsaya cakk awaje daya yana sauraron isowar uwar mayu gareshi koda uwar mayu taga hantaru ya tsaya cak ya daina guje guje sai murna ta kamata domin tasan cewa yanzu zata hallakashi bada bata lokaci ba kawai saita durfafe shi da dukkan karfinta cikin bakin zafin nama da isowar ta dabb dashi saita kawo masa wawan cafka da hannayen ta guda biyu cikin tsananin zafin nama hantaru ya sunkuya kasa ta kama iska kafun ta sake kai masa hari tuni daka tsalle ta cikin karkashin kafafun ta ya zagayo bayanta ya sake daka tsalle kafun ta waigo ya dira akan kafadar ta ya gabza mata naushi acikin kunnen ta aiko sai hannun nashi ya lume acikin kunnen ya futo ta cikin daya kunnen yana zare hannun jini yakama feshi take uwar mayu ta sulale kasa matacciya a matukar galabaice hantaru ya durshe kasa bisa gwuiwoyin sa saboda tsabar wahala a sannan ne ya lura cewa guma guman duwatsun wuta dasuka yita fadowa daga saman ginin sun hallaka gabadaya yayan uwar mayu dayan su bai tsiraba da rayuwarsa hantaru na durkushe yana haki sai kawai yajiyo ihun shamilat daga can kasan wannan katon dutsin daya danne dirkar ginin da'aka daure ta a jiki cikin zafin nama hantaru ya yunkura da saurin gaske ya ruga wajen ya kaimata dauki wani irin takun sawu mai karfi da hantaru ya jiyo a bayansa shine tsaida shi ya juya a firgice aiko sai yayi arba da wata jibgegiyar halitta mai tsananin kwarjini daban tsoro da muni bakomai ne wannan halitta ba sai mijin uwar mayu ya dubi yadda gidan sa ya rugurguje sannan ya hango gawar uwar mayu a can gefe daya can kuma saiga gawarwakin yayan sa kota ina kawai saiya takarkare ya kwarara ihu karar ihun tamkar ana ruwan kwaran kwatsa daga sama ak'amarin daya kara razana hantaru kenan musamman daya karewa mijin uwar mayu kallo sama da kasa ya tabbatar dacewa ruwa ba sa'an kwando bane a wannan lokacin ne kuma shamilat ta cigaba da kwala ihu ashe dutsen daya danne dirkar da take jiki ne yake kara dannawa kasa nan fa hankalin hantaru ya rabu gida biyu ya rasa abinda ya kamata yayi shin mijin uwar mayu zai fuskanta suyi yaki koko wajen mahaifiyar sa shamilat zaije ya ceto rayuwarta harya yunkura zai ruga wajen shamilat sai yaji an shako wuyan sa ta baya koda ya kama abun daya shake shi sai yaga ashe wata irin doguwar bulala ce mijin uwar mayu ya jefa mishi ta shake shi a wuya kuma ta shake shi ne ainun ya kasa cire ta mijin uwar mayu yafara janyo bulalar nan domin ya kawo hantaru gaban sa shiko hantaru saiya fara cijewa da dukkan karfin sa domin yasan cewa muddin ya kuskura yaje gaban sa ya damke shi saidai kuma mahaifiyar sa ta haifi wani amma shi tasa ta kare hantaru ya cigaba da cijewa amma saboda mijin uwar mayu yafi shi karfi nesa ba kusa ba saiya dinga jansa gabadaya al'amarin daya dugunzuma hankalin hantaru kenan ya saduda domin yasan cewa kwanan sa yazo karshe. ****************** Mazan Jiya Part 18 #Cigaba A lokacin daya rage baifi saura taku biyar ba mijin uwar mayu ya cafi hantaru da hannun sa sai wata dabara ta fadowa hantaru ya tuno da wata wuka dake sakale a bayansa cikin hanzari ya zaro wukar ya yanke wannan bulala data shake shi ya fada baya koda mijin uwar mayu yaga bulalar sa ta yanke sai yayi jifa da ita ya zare wani katon sungumi dake sakale a cinyar sa ya ruga izuwa kan hantaru suka kacame da sabon azababben yaki mai ban tsaro da ban al'ajabi wohoho!! tashin hankali ba'a saka maka rana saida hantaru da mijin uwar mayu suka kwana suka tashi suna fafata yakin bala'i hatta kasa tasha azaba domin saida mijin uwar mayu ya ratattaka komai dake cikin gidan nan da wannan katon makamin dake hannun sa tunda hantaru yazo duniya bai taba shan bakar wahala ba irin ta wannan lokaci sau bakwai yana suma a wannan fafatawa dayayi da mijin uwar mayu amma kafun mijin uwar mayu ya zaro shi daga cikin karkashin kasa ya karisa kashe shi saiya farfado su cigaba da gumurzu saida yazamana cewa hantaru ya samu karaya tara a jikin sa amma bai fasa yaki ba. Itako shamilat tuntuni ta suma ta nutse a cikin karkashin kasa batama san abunda dake faruwa ba ana cikin wannan gumurzun ne mijin uwar mayu ya samu nasarar yiwa hantaru wani irin wawan naushi a fuska nan take numfashin hantaru ya dauke ya baje kasa ko motsi bai sake yiba mijin uwar mayu ya tsaya cakk yana haki kuma ya kurawa hantaru idanu domin yagani ko zai motsa a wannan lokaci shima mijin uwar mayu duk jikin sa raunuka ne jini na zuba har jiri na diban sa yana layi tsawon dakika dari shida da sittin hantaru bai motsa ba. don haka sai mijin uwar mayu ya tabbatar dacewa ya mutu amma duk da haka hankalin sa bai kwanta ba saboda bai taba ganin bil'adama hatsabibi mai tsananin jarumtaka da naci da taurin rai tamkar hantaru ba, nan take mijin uwar mayu ya nufi kan hantaru kai tsaye da nufin ya cizge kansa da karfin tsiya ya cinye, koda yazo dabb dashi ya raba kafafun sa akan hantaru kuma ya sunkuyo da nufin ya kama kansa sai kawai yaji hantaru gabza masa naushi a ido, take hannun hantaru ya burma ta kwarmin ido ya fito ta keya take mijin uwar mayu ya fadi ta baya tamkar giwa uku sun fadi a kasa, lokaci guda. Da kyar da jan jiki hantaru ya isa inda dutsen nan ya danne shamilat hantaru yayi amfani da dukkan karfin damtsen sa ya dago dutsen sannan kuma ya shiga zaro wannan dirkar gini wadda ta nutse cikin karkashin kasa kuma shamilat take daure a jiki saida yasake shan bakar wahala sannan yasamu ya dago dirkar yana gama zaro dirkar yaga shamilat a mimmike babu abinda ke motsi a jikin ta nan hantaru ya kurma ihu kuma ya fashe da kuka domin a zaton sa ta mutu, wani iko na Allah sai hadari ya gangamo adaidai wannan lokaci nan da nan aka kece da ruwa, koda ruwa ya daki shamilat saita farfado a wannan lokaci kan hantaru na sunkuye yanata rusa kuka, kwatsam sai yaji shamilat tayi tari cikin zafin nama yadago kai koda yaganta a raye ya matsa gareta ya rungumeta duk su biyun suka fashe da kukan farin ciki. Saida su hantaru suka kwana arba'in a cikin wannan busashen gida na uwar mayu suna jinyar cikin su sannan sukayi shiri suka cigaba da tafiya, sannu sannu bata hana zuwa sai dai a dade ba je ba tunda su hantaru suka bar wannan daji dayayi mugun yaki dasu uwar mayu basu sake gamuwa da wani abu ba daya wahalar dasu har suka iso birnin darul habur da la'asar su shamilat suka shigo cikin birnin darul habur tundaga bakin kofar birnin shamilat ta cika da tsananin mamaki domin komai na garin yana nan kamar yadda tasan shi shamilat da hantaru suka yita kalle kalle suma suka zamo abun kallo a matsayin su na baki lokacin dasuka ratsa ta cikin kasuwa da makera sai hantaru yadinga ganin zaratan jarumai masu kirar karfi sunata kera makamai iri-iri wasu kuma sunata baiwa kansu horon kokuwa da gudu, daganin wadannan zaratan jarumai sai hantaru yasha jinin jikinsa yasan cewa lallai ya shigo nahiyar sadaukai inda sai yayi da gaske jarumtakar sa zata kwace shi, domin bai taba ganin samari masu girma da tarin kwanji irinsu ba abunda yafara fadowa hantaru a rai shine batun gasar nan na gudun kamo barewa nanfa ya shiga tunanin al'amarin a cikin zuciyar sa. Lokacin da hantaru yake ta wannan tunani itako shamilat farin ciki ne ya lullube ta sabona tsintar kanta a cikin mahaifarta in banda murmushi da kalle-kalle babu abunda shamilat takeyi hakadai suka cigaba da tafiya bisa dawakan su rakuman su na gaba, kwatsam sai daya daga cikin rakuman su hantaru yaje yana shinshina wata katuwar randa dake cike da ruwa yana kokarin ture marfin ta, dama rakuman na fama da kishirwa sunfi kwana talatin rabon su da shan ruwa domin sun dade a cikin sahara suna tafiya, ruwan dasu hantaru sukayi guzuri bashida yawa, a garin ture marfin randar ne rakumin ya bangaje randar gabadaya ta fashe karar fashewar randar ce tasa mai randar ya fito a fusace daga cikin rumfarsa rikeda takobi, koda yaga rakumin daya masa wannan barna sai yayi kansa zai sare shi cikin zafin nama hantaru ya zare takobin sa ya daka tsalle daga kan dokinsa ya dirka a gaban mai randar ya tare wannan sara takubban su suka hadu suka fitar da kara gami da tartsatsin wuta, nan fa aka tsaya ana kalon kallo tsakanin hantaru damai randar a iya rayuwar hantaru bai taba ganin saurayi mai tsawo da kauri da murdewar jiki kamar wannan saurayi ba, sannan yanada matukar kwarjini koda sauran jama'ar dake cikin kasuwa sukaga abinda ke shirin faruwa sai hankalin su ya dugunzuma kowa ya baro wajen sana'ar sa aka rugo inda su hantaru ke tsaye aka tsaitsaya ana kallo cikin tsananin fushi wannan saurayi ya dubi hantaru yace shin kazabi karasa rayuwar kane akan na rakumin ka hantaru yayi murmushi yace inason rayuwa ta, kuma inason rayuwar rakumi na idan saboda akan randar ka kakeso kadauki ran rakumi na toh gaskiya ka fadi kudin randar ka ko nawane zan biya kodajin haka sai saurayin yadakawa hantaru tsawa yace kai bako waye Kaine harda zaka nuna min gadara a cikin birnin mu lallai yau zakasan cewa ka tabo zaki uban dawa kuma dodon maza dakai da rakumin nakan duk yanzun nan takobi na zata sha jinin ku, kafun hantaru yace wani abu sai saurayin ya daga takobin sa cikin zafin nama ya kaiwa hantaru wawan sara a ciki da nufin ya tsarga shi biyu hantaru ya jada baya takobin ta sari iska nanfa suka kacame da azababben yaki, al'amarin dayayi matukar firgita shamilat kenan ta fara kuka tana rokon jama'ah dasu raba wannan fada amma babu wanda ya saurare ta face gudu da jama'ah suka ringayi domin wuri ya hautsine tsautsayi na neman afkawa kan kowa. Koda ganin haka sai Shamilat ta zaburi dokinta ta nufi gidan mahaifinta sarkin makera Shuraim ibn Alkasim domin tq sanar da shi abinda ke faruwa. Wohoho! Jarumtaka ta hadu da jarumtaka dole ne fafatawar ta zama abar tsoro, nan take Hantaru da saurayi suka hargitsa kowa da komai dake cikin kasuwar, suka rinka rushe rumfunan suna dagargaza dukiyar jama'a, nan fa jama''a suka dinga guje-guje da iface-iface, kafin a juma labari ya cika gari, Hantaru da wannan saurayi suka rinka kaiwa junansu sara da suka cikin tsananin zafin nama juriya da bajinta ba kakkautawa, sai da suka shafe kusan rabin sa'a amman dayansu bai samu nasarar koda kwarzanar jikin dan uwansa ba, har takubbansu suka dakushe. Al'amarin daya fusatasu kenan suka zubar da makamansu suka sake ruguntsumewa da azabben gumurzu da bugun juna da hannu da kafa, nan take kuwa kowa ya hada wa kowa jini da majina. A daidai lokacin ne Shamilat da mahaifinta Shuraim tare da wasu jama'arsu suka iso wajen a guje bisa dawakansu, aikuwa sai ga wata jama'ar da ban bisa dawakai a sukwane, ba kowa bane yake jagorantar su ba face sarkin mafarauta na birnin wanda ake kira zaharu ibn Dauwal, nan fa rundunonin nan suka ja tunga suna masu fuskantar junansu ga dukkanin alamu so suke su yaki junansu, abinda ya hanasu shine kallon fafatawar da su Hantaru ke yi. Zaharu ibn Dauwar shine mahaifin wannan saurayi dake fafatawa da Hantaru, kuma tsakaninsa da Shuraim gaba ce mai tsanani tun iyaye da kakanni, kuma ba komai bane ya haddasa wannan gaba ba face wannan gasa da ake gudanarwa duk karshen shekara ta tseren gudun kamo barewa, domin auren budurwar da babu kamarta a birnin, duk shekara idan aka yi gasar zuri'ar mafarauta ce take cinye gasar, zuri'ar makera basu taba cinye gasar ba, saboda an fisu zakwakurarun jarumai masu sadaukartaka. Shuraim n da wani da guda daya mai suna Hurais, a duk fadin birnin babu kyakkyawan saurayi kamarsa, kuma ya kasance mai matukar kwarjini a cikin al'umma, Hurais kanin Shamilat ne, dan Lokacin da aka yi mata aure bai wuce shekaru bakwai ba. Lokacin da Hurais ya girma ya zama saurayi sai soyayya mai zafi ta kulli tsakaninsa da wata kyakkyawar budurwa mai suna Marilat, wacce ta kasance kanwa ga wannan saurayi da ke yaki da Hantaru. Shi dai wannan saurayi ana kiransa da suna Rabbasu, ma'anar sunan shine mai karfin zaki. Bayan soyayya ta yi karfi tsakanin Hurais da Marilat sai iyayensu suka farga, nan fa iyayen kowanne daga cikinsu suka taka masu burki, aka hanasu ganin juna domin babu yadda za'a yi a bari suyi aure tunda akwai gabar asali a tsakanin dangin nasu. A asirce Hurais da Marilat ke haduwa a daji suna tattauna yadda zasu bullo wa wannan al'amari kan soyayyarsu, a karshe dai sai suka yanke shawarar cikin dare su sulale su gudu zuwa wani garin suyi aurensu. Aikuwa cikin tsakiyar dare suka sullae suka bar garin, koda gari ya waye sai aka nemi Hurais da Marilat aka rasa, nan fa rigima mai karfi ta kacame tsakanin dangin mafarauta da kuma dangin makera har ta kaisu ga yakar juna, wanda sai da takai cewa anyi asarar daruruwan rayuka, da kyar sarkin garin ya raba wannan rigima. A karon banza aka kamo Hurais da Marilat acan wani kauye waishi Gabril, a lokacin da suke daf da daura wa kansu aure. Daga wannan rana Hurais da Marilat basu sake ganin juna ba, a dalilin aka ne duk su biyun suka shiga mugun hali suka kwanta cuta, a karshe dai ciwo yakai ciwo rai yayi halinsa duk su biyun suka mutu a kuma rana guda. Marilat ce ta fara mutuwa, aikuwa Hurais na samun labarin mutuwarta sai shima ya hadiyi zuciya ya mutu. Bakin ciki a wurin dangin makera dana mafarauta ba sai an fada ba domin sai da kowannne bangare suka shafe kwanaki talatin suna kuka da bakin ciki na wannan abu daya afku, wannan shine sanadin daya kara zafafa kiyayya da gaba a tsakanin dangin guda biyu. Lokacin da rundunar biyun ta tsaya ana kallon ffaatawar da akeyi tsakanin Hantaru da Rabbasu sai kowa ya cika da tsananin mamaki, domin ba'a taba ganin jarumin da yayi gaba da gaba da Rabbasu ba har ya iya yakatsa ba sai yau, saboda tsananin jarumtakarsa da iya yakinsa. Koda yake shi kansa Hantaru ya raina jarumtakarsa domin bai taba haduwa da jarumi bil'adama kamar Rabbasu ba, kai ko yakinsa da mijin uwar mayu bai bashi tsoro ba kamar wannan gumurzu da yake yi da Rabbasu, domin ya tabbatar da cewa indai aka kara sa'a guda nan gaba sai dai cikin biyi ayi daya, kodai suyi ragas ko kuma daya ya kashe daya. Babban abinda ya tayar wa da Rabbasu hankali shine aduk sa'ar da ya sari jikin Hantaru sai dai yaji kara kal! Takobin nan bata tasiri a jikinsa sai dai wajen daya sara din ya dan kunbura. Shiko Hantaru abinda ya dugunzuma hankalinsa shine ko sau daya ya kasa samun nasarar yankar jikin Rabbasu. Ana cikin wannan hali ne kwatsam sai aka hango wani mahayi bisa wani farin doki ya durfafo wajen, tun kafin ya karaso wata irin iska mai karfi ta dinga tarwatsa mutane ba shiri aka buda masa hanya domin an gane kowane ne. Da isowar mahayin wanda ke rike da wata farar sanda sai yayi nuni da sandarsa izuwa ga hantaru da kuma Rabbasu, nan take duk su biyu suka zube kasa sumammu, wato suka yi rabuwar dole ga barin yakar junansu. MAZAN JIYA Littafi Na Daya (1) Part N Marubuci: Abdulaziz Sani M/Gini Typing: Abubakar Saleh AlQuyraemey A sannan ne mahayin dokin ya tsaida dokinsa ya dubi rundunar su Zuhairu da kuma ta su Shuraim yace kowa ya dauki nasa ku tafi gida, na raba wannan rigima a yanzu amman fa bata kare ba, domin za'a yi babbar fafatawa ta karshe nan gaba tsakanin Rabbasu da wannan bakon jarumi a ranar gasar tseren gudu, ta neman auren Gimbiya Larziyya, to nan ne za a yi wannan fafatawar ta karshe. Ko da gama fadin hakan sai mahayin yayi girgiza ya bace bat! Shi da dokinsa, b wani bane wannan mahayin sai kakan Shamilat wato boka Sulbaini ibn Hukaish. Bacewar boka Sulbaini ke da wuya sai ko wanne bangare suka dauke nasu, wato su Shuraim suka dauki Hantaru suka tafi, su kuma Zuhairu suka dauki Rabbasu suka tafi da shi. Lokacin da hantaru ya farfado yana bude idanunsa sai ya tsinci kansa bisa cinyar Shamilat ta zuba mashi idanu tana zubar da hawaye, a gefe daya kuma sai yaga wani dattijo dogo siriri kuma kyakkya a tsaye a kusa da shi kuma wata dattijuwar mace ce sun kura masa idanu suna murmushi gami da zubar da hawaye. Hantaru ya dubi ko wacce kusurwa yaga a cikin wani kyakkyawan daki yake, cikin matukar mamaki ya mike zaune zumbur! Ya dubi Shamilat ya ce yaya aka yi nazo nan, sannan wadannna mutanen su waye? Koda jin wannan tambaya sai Shamilat ta share hawayenta ta ce ya kai dana kayi sani cewa kakana boka Sulbaini ibn Hukaish hine ya zo ya raba yakin da kuke yi da wannan sadaukin saurayin, nan dai Shamilat ta baiwa Hantaru labarin Rabbasu da mahaifinsa Zuhairu da kuma irin gabar dake tsakanin zuri'arsu da ta su Rabbasu. A karshe ta shaida masa cewa boka Sulbaini yayi bayanin cewa za a sake fafatawa da Rabbasu ta hanyar tseren gudun kamo barewa, bisa takarar neman auren Gimbiya Larziyya. Sa'adda da Shamilat ta zo nan a jawabinta sai hantaru ya kuma cika da mamaki ya ce wace kuma gimbiya Larziyya? Kafin Shamilat ta bude bakinta ta bashi amsa sai Shuraim ya riga da cewa ya kai jikana Hantaru ka yi sani cewa ba wata bace Gimbiya Larziyya face yar sarkin garin nan namu Uhairu ibn Sabus, kuma a halin yanzu a gaba daya nahiyar nan babu wata mace mai kyawunta, ya kai jikana kayi sani cewa mahaifiyarka Shamilat ta bamu labarin jarumtakarka data gani da idanunta a yayin tafiyarku tsakanin birnin sarki kusaidu zuwa nan. Hakika kayi gagarumar bajinta irin wacce wani bai taba yi ba, domin fiye da shekaru hamsin baya, babu mai iya ratsawa ta wadannan dazuzzuka ya fita lafiya face ayarin dakaru masu yawa kuma masu karfin sihiri, amman kai gashi kai baka da sihirin komai face na kariya irin wanda muka shayar da mahaifiyarka tun tana karama, shi wannan kariyar kawai kake da shi. Haka dai aka cigaba da fira tsakanin Shuraim da Hantaru suna cikin tsananin farin ciki, daga karshe sai Hantaru ya dubi Shuraim ya ce ya kai kakana yanzu ya ya za a yi naga gimbiya Larziyya? Shuraim yayi murmushi yace wai shin me kake ci ne na baka na zuba? Ka kwantar da hankalinka zaka ga gimbiya Larziyya da idanunka amman sai bayan mun dawo daga gidan mahaifina boka Sulbaini, domin yace da ni lallai mu kaika gidan shi gobe da safe. Koda jin haka sai murna ta kama Shamilat dan dama bata da burin daya wuce ta sadu da boka Sulbaini, ba tre da bata lokaci ba Shuraim da matarsa Shaulat suka shiga hidimar shirya walima ta musamman dan murnar dawowar Shamilat da jikansu Hantaru. Nan take aka yanka rakumi da raguna guda uku, Sannan Shuraim ya aika wasu kuyanginsa kasuwa, suka je suka yi cefane. Nan fa aka shiga dafe dafe da soye-soye, daman tuni an aika da sakon gayyata ga yan uwa da abokan arziki da kuma makwabta. Tun kafin a gama shirye-shiryen jama'a suka fara hallara a gidan Shuraim, nan da nan kuwa gidan ya cika da jama'a, wasu abokan ma na Shuraim rabonsu da zuwa gidan an fi shekara goma, sai da kowa ya zauna a inda aka tanada sai kuyangi suka fara fito da abinci da na sha aka fara walimar, bangaren maza da ban haka na mata da ban. Sai da aka fara walimar annan Shamilat, Shaulat, Shuraim da Hantaru suka fito daga cikin daki suka fara gaisawa da jama'a, Shuraim na gabatar da Shamilat da danta Hantaru ga wadanda basu sansu ba, kuma suma bakin ana gabatar d su ga su Hantaru, ana gaggaisawa. Ana cikin wannan gaggaisawar ne sai Hantaru ya hango wata mace can tsaye, wacce ta rufe fuskarta da mayafi, idanunta kadai ke iya gani, ita dai wannan macen ita kadai ce, bata ci kuma bata shan komai, kuma ya lura da ita cewa Shuraim take satar kallo. Yayi tunani a zuciyarsa ya ce to shin wace ce wannan? Kuma me ya kawota wannan taro, tunda bata damu da komai ba na walima? Hantaru ya tambayi kansa. Bayan gama gaisheshe ne sai Hantaru ya saki wuri shima ya zauna ya fara cin abincin, a lokacin ne sai gaba daya samarin dake wajen suk zo suka lullubeshi suna masu yi masa jinjina bisa gagarumar bajintar da yayi ayau, na fafatawa yaki da Rabbasu. Al'amarin da ya baiwa Hantaru mamaki kenan ya ce wai shin shi wannan Rabbasu har shayinsa ake yi a garin nan? Wani saurayi mai suna Kumais ya ce ai a tarihin jarumtakar Rabbasu a nan grin ba a taba samun gwarzon daya taba tararshi ba, balle har su fafata yaki ba sai kai kadai, kai a takaicema gabadaya nahiyar nan babu kamarsa a sadaukantaka, sannan kuma bashi da imani ko kadan shiyasa kowa ke shakkarsa, babu mutum daya isa ya fada masa magana yaji face boka Sulbaini, shima dan babu yadda zai yi d shi ne, domin kura ta san gidan mai babbar sanda. Hantaru ya jinjina kai sannan ya ce wai shin Rabbasu yana shiga gasar gudun tseren barew da ake yi duk shekara ne kuwa? Kumais yabce ai Rabbasu bai taba shiga gasar ba, saboda baya son ya auri kowacce budurwa face gimbiya Larziyya. Ita kuwa Larziyya mahaifinta sarki yace ba zai aurar da ita ba, sai bayan shekarar da za'a yi gasa ta arba'in sannan zai aurar da ita. Wannan shekara da muke ciki itace shekara ta arba'in din, a yanzu haka saura kwanaki ashirin aidai ayi wannan gasa. A daidai wannan lokacin ne su Hantaru suka ga wannan macen mai satar kallonsu ta baro inda take tsaye ta durfafo inda suke tsaye. Koda ta zo daf da Hantaru sai ta mika masa wata takarda. Hantaru na karbar takardar sai kawai budurwar ta juya da sauri ta fice daga cikin gidan. Hantaru ya mike d sauri da nufin yabi bayanta, amman sai Kumais ya rikota yace da shi kafa ka bita, kuma kada ka duba takardar sai bayan ka kadaita a cikin dakinka kai kadai, cikin mamaki Hantaru ya dubi Kumais ya ce shi shin kasan wannan matar data kawo mani wannan takardar ne? Kumais yace eh nasan kowace ce, amman bazan fada maka ba, domin nasan ba zatayi bayanin kanta ba a cikin takardar fata baka. Koda jin haka sai Hantaru yayi shiru bai sake cewa komai ba, kuma ya sanya wannan ta karfa a cikin minti goma, kuma ya saki jikinsa aka cigaba da walima kamar babu abinda ya faru. Ita dai wannan walima tunda hantsi aka farata amman sai bayan magrib sannan kowa ya watse suka tafi suna son barka. Hantaru na zaune shi kadai a harabar gidan bayan kowa ya tafi aka barshi shi kadai a zaune yana tunani, ba tunanin komai yake ba face irin rayuwar daya baro acan birnin Kisra da kuma irin wacce ya tarar a birnin darul Habur, abinda Hantaru ya fara ayyanawa a ransa shine ina ma ace ba sarki Usaidu bane mahaifinsa, gwara ace mahaufina dan usulun wannan birni ne na darul Habur, domin rayuwata ta fi dacewa anan, da tuntuni na share hawayen kakannina na takaicin rasjin cin gasar d suke yi. Amman dai tunda yanzu na zo nan to komai ya zo karshe, ta kowanne hali a wannan shekarar nine zan zama zakaran wannan gasa. Lokacin da Hantaru ya gama ayyana haka a cikin zuciyarsa, sai yaji alamun ya soma jin bacci dan haka sai ya mike tsaye ya shiga cikin dakinsa, har Hantaru ya kwanta akan shimfida dmin yayi bacci sau ya tuno da batun wasikar nan da mace mai rufaffiyar fuska ta bashi. Hantaru ya mike zumbur ya zaro wasikar daga cikin aljihun rigarsa ya warwareta sannan ya fara karatu kamar haka: Takarda daga Gimbiya Larziyya zuwa ga bakon jarumi mai ban mamaki, ya kai taurarn shekara kayi sani cewa nayi matukar farin ciki da zuwanka wannan birni, kuma dama can na dade ina sauraron wannan rana ta zuwanka. Hakika wannan rana ta fiye mani komai a duniyar nan, ba komai bane yasa nake farin cikk da zukanka ba, face sanin cewa kai kadaine zaka iya yaye bakin cikin da ya addabi zuciyata tsawon shekara da shekaru. Ina mai tabbatar maka da cewa Sadauki Rabbasu ya dade yana sona, tun muna yara kanana, amman daidai da dakika ban taba jin ina kaunarsa ba, a kaidar wannan birni namu babu wanda zai auri wata mace kyakkyawa dole sai ya shiga gasar gudun barewa. Tunda sadauki Rabbasu ya zama saurayi bai taba shiga wannan gasa ba domin a kaina kadai yayi tanadinta, wato ya kudurce a ransa cewa ba zai shiga gasar ba sai idan akaina ake yinta. Tabbas bokaye da masu hasashe sun tabbatar da cewa duk sa'adda gasar aurena ta zo, indai Rabbasu ya shiga gasar babu wanda zai samu nasara akansa. Ni kam dadai na auri Rabbasu gwara ace na rasa rayuwata ma gaba daya. Ya kai Gwarzon jarumi ina mai rokonka saboda mahaifiyarka Shamilat da kuma kakanka sarkin makera Shuraim da ka taimakeni ka ceci rayuwata ka shiga wannan gasa, koda kuwa ba zaka samu damar aurena ba, ni dai babban burina shine ace Rabbasu ya rasani, idan har ka amince zaka yi mani wannan taimako, to mu hadu a dutsen kufainu dake can bayan gari a gobe da yammaci daidai lokacin faduwar rana domin naji amsata a bakinka, daga karshe ina mai kira a gareka daka rungumi kaddara bisa wani mummunan labari da zaka ji daga bakin kakan mahaifiyarka wato boka Sulbaini, domin labari ne mara dadi kuma zai yi matukar jefaka a cikin bakin ciki da damuwa. Lokacin da Hantaru yazo daidai nan a karatun wsikarsa sai hankalinsa ya dugunzuma ya shiga sabon tunani, har ya zamana cewar dare ya raba amman ya kasa bacci, abinda ke wa Hantaru zarya a cikin zuciyarsa shine wai shin wane irin mummunan labarine boka Sulbaini zai labarta masa wanda zai kefashi cikin bakin ciki. Abu na biyu kuma shine, ta yaya zai samu nasarar lashe gasar tseren kamo barewa na karshen shekara domin kubutar da rayuwar Gimbiya Larziyya. Haka dai Hantaru ya cigaba da wannan tunani a cikin zuciyarsa, bai gushe ba yana tunani har alfijir ya keto bai anakara ba. Bayan anyi kalacin safe kowa ya gama kimtsawa sai Salimat, Shuraim da Hantaru suka yi hawa suka tafi izuwa gidan boka Sulbaini, da yake akwai yar tazara tsakanin gidan Shuraim da gidan Boka Sulbaini basu isa can dinba har sai da hantsi ta yi. Gidan boka Sulbaini a bayan gari yake a saman wani katon dutse wanda ana iya hangoshi daga kowanne sashi, wato bangaren gabas da yamma, da kuma kudu da arewa. Daga nesa mutum zai iya hangoshi dan mitsitsi amman da zarar ya gabato sai ya fuskanci cewar yana da girma ainun. Lokacin da su Shuraim suka iso bakin kofar gidan boka Sulbaini sai suka sauka daga kan dawakansu suka dauresu a jikin bishiyoyi, sannan suka haye saman dutsen suka durfafi gidan boka Sulbaini. Shuraim ne akan gaba sannan Shamilat sai kuma Hantaru, da isarsu kofar gidan wanda hantaru ya kura wa idanu yana mashi kallon mamaki saboda ganin yadda aka gina shi da zallar dutse na murjani, sai Shuraim ya kunna kai, Shamilat ta bishi a baya. Koda Hantaru ya mika kafarsa zai sa a cikin gidan, sai yaji a daka masa tsawa wacce tasa tsigar jikinsa mikewa, bai san sa'adda ya janye kafar tasa ba kuma ya koma da baya, Shuraim da Shamilat ma sai suka razana suka koma da baya, kawai sai sukaga kofar gidan ta rufe da kanta. A sannan ne kuma boka Sulbaini ya bayyana tsulum a gabansu kamar walkiya, idanunsa cike da kwalla ya kurawa Hantaru idanu. Al'amarin daya daure wa Shuraim, Shamilat da Hantaru kai kenan, Shamilat ta dubi Sulbaini cikin matukar mamaki da damuwa ta ce Haba ya kai kakana, shin baka shaida ni bane? Ka tuna fa yau kusan shekara ashirin da doriya kenan rabon da muga juna, ina ta dokin nazo naganka domin na nuna maka dana, amman sai ka tarbemu da tsawa, Kaicona! Inda nasan haka zaka karbeni da bazamu zo gareka ba. Sa'ad da Shamilat ta zo nan a zancenta sai hawaye ya sake zubowa Boka Sulbaini ya dubeta cikin takaici da damuwa sannan ya nuna Hantaru da hannu ya ce Yake jikata abar kaunata, kiyi sani cewa wannan yaro ba jininmu bane, ina nufin ba kece kika haifeshi ba, kiyi sani cewa duk wanda ya kasance ba jinina ba idan ya shiga cikin gidan nan hallaka zai yi, wannan ne yasa na yi muku tsawa domin bana son ya hallaka. Koda jin wannan batu sai Hantaru, Shuraim da Shamilat suka zazzaro idanu, hankalinsu ya dugunzuma ainun. Nan take idanun Hantaru suka ciko da kwalla ya dubi boka Sulbaini yace wace shaida ce da kai wacce zata gamsar damu cewa ni ba jininku bane? Koda jin wannan tambaya sai tausayin Hantaru ya kama Boka Sulbaini har hawaye ya zubo masa, sannan ya ce tabbas kuwa nike da babbar shaida, na umarceku da kuyi duba izuwa wannan bangon gidan nawa domin ku ga yadda al'amarin ya kasance. Ba tare da gardamar komai ba su Hantaru suka dubi bangon gidan, shi kuwa boka Sulbaini sai yayi nuni da hannunsa izuwa bangon, take hoton birnin Kisra ya bayyana a kai, aka fara nuno wasu ababuwa da suka gabata tsawon shekara da shekaru, da farko a nuno lokacin da matar sarki Kusaidu wato Zarifa ta kadaita da Boka Ardusa ta ce da shi lallai ya baiwa sarki shawarar kara aure domin su cimma burinsu, wato suyi shirin da zasu baiwa sarki dan da suka samu ta hanyar lalata ta cin amanar sarki a matsayin dan cikinsa ba tare da ya sani ba. Daga nan aka nuno lokacin da sarki Kusaidu ya zo birnin darul Habur har ya shiga gasar neman aure kuma ya samu nasara a tseren gudun barewa, sanadin Salimat ta zamo matarsa aka daura aure ya tafi da ita birnin Kisra. Ina yi maku barka da wannan lokaci sannan ina baku hakuri na shiru da kuka ji hakan ya faru ne saboda rashin lafiya da na kwanta tun bayan sallah, amman yanzu AlhamduLillahi🙏🙏🙏 Ga masu son Complete Audio na Mazan Jiya Wanda Muhammad Umar Kaigama Ya karanta Ko Kuma Complete Document zasu iya mani magana ta whatsapp 08138873799 MAZAN JIYA Littafi Na Daya (1) Part O Marubuci: Abdulaziz Sani M/Gini Typing: Abubakar Saleh AlQuyraemey Sannu a hankali aka nuno yadda boka Ardusa ya saka wa Salimat juna biyu na sihiri da kuma yadda ya boye cikin zarifa na gaskiya har izuwa lokacin haihuwarta ba tare da kowa ya sani ba. Daga nan aka nuno ranar da Shamilat ta kamu da ciwon nakuda, ta kwana ta yini a ciwon nakuda, har sai da zarifa ta shiga dakin haihuwar ta kori matan dake yi wa Shamilat unguwar zoma, ya zamana cewa su biyu ne rak a cikin dakin. Nan take ta sumar da Shamilat ta kama tata nakudar, ta haifi santalelen jariri, ta ajiye wa samilat nata jaririn ta fice daga dakin haihuwar, daga nan ne fa sai jama'ar gari suka rude da farin ciki Salimat ta haifi da, daga nan aka ci gaba da rainonsa har ya zama Hantaru. Koda hoton duk wannan al'amari yazo daidai nan sai boka Sulbaini ya sake yin nuni da hannunsa izuwa ga bangon, take hoton komai ya bace. Nan take Hantaru ya kwarara uban ihu cikin takaici da bakin ciki, kuma ya fashe da matsanancin kuka. Itama samilat sai kawai taji jiri ya kwasheta, kafin su ankara ta sulale kasa sumammmiya. Cikin hanzari boka Sulbaini yayi tsafi ruwa ya zubo daga cikin yan yatsunsa ya yayyafa mata, sannan ta farfado ta fashe da matsanancin kuka mai tsuma zuciya. Sulbaini da Shuraim suka kamu da tsananin tausayin samilat har basu san sa'ad da suka kama kuka ba duk su hudun, haka suka yita wannan kukan. Sai daga can Hantaru ya zo gaba samilat ya durkusa bisa gwiywoyinsa ya kama kafadunta itama sai ta kama kafadunsa a lokacin da hawaye ke zuba daga idanunsu yace ya ke Ummina hakika yanzu na gamsu cewa ba kece kika haifeni ba, amman kiyi sani cewa har abada kece uwata domin nononki nasha na rayu har na girma, dan haka bazan taba daukar waccan ba da boka Ardusa a matsayin iyayena, kuma a halin yanzu ina jin cewa bani da makiya a duniya sama da su, kuma bani da wani buri a duniya da ya wuce na zare masu ruhin numfashinsu, domin sunci amanar mijinki sun cuci rayuwata sun kuma yi mani babbar barna da har abada bazata gyaru ba. Lallai bayan naci gasar tseren gudu sai na koma Birnin Kisra na kasheta ita da Ardusa sannan na fada wa sarki Kusaidu gaskiyar al'amari na ce masa ni ba dansa bane ga yadda akayi aka same ni. Bayan d Hantaru yazo nan a zancensa sai samilat ta rungumeshi, sannan ta fashe da sabon matsanancin kuka, shima sai zuciyarsa ta karaya ya cigaba da kukan, daga can sai samilat ta janye jikinta daga nasa suka fuskanci juna sosai ta ce ya kai dana ina son k tuno da tsantsar kaunar dake tsakaninka da sarki Kusaidu, ka tuna cewa ba a son ransa na taho da kai nan garin ba, saboda baya son rabuwa da kai daidai da na kwana daya, yanzu idan kaje ka sanar da shi gaskiyar al'amari yaya zai ji, kuma wane irin hali kake tunani zai shiga? Ina mai tabbatar maka idan yaji wannan labari zai iya hadiyar zuciya ya mutu, domin gabadaya zai ga rayuwarsa bata da wani amfani a duniya, tunda mutumin daya amincewa fiye da kowa a duniya wato boka Ardusa ya ci amanarsa. Sannan babban burinsa na duniya ya wargaje, tunda bai samu haihuwa ba, matarsa d suka yi auren saurayi da budurwa wacce yake kauna fiye da kansa, kuma ya bata amanar kansa tsawon shekaru yau itama ta ci amanarsa, ya kau dana ina mai rokonka da komai rokonka komai rintsi da tsanani kada ka bari sarki kusaidu yasan wannan sirri, idan har ka dauke ni a matsayin uwa ina so ka sani cewa ina kaunar mijina fiye d duk yadd kake tsammani, saboda haka lallai ina so na koma birnin Kisra na cigaba da rayuwa da shi cikin farin ciki, ban hanaka yiwa boka Ardusa da waccan mata hukunci ba, amman kayi sani cewa tana lafiyarta dai-dai yake da taba lafiyar mijina, idan kuwa kayi haka to babu ni babu kai sai dai ka sauya uwa. Sa'ad da Samilat ta zo nan a zancenta sai Hantaru ya rungumeta a karo na biyu ya fashe da kuka saboda bakin ciki da takaici domin yasan cewa ba xai iya ketare wannan doka ba data kafa masa. Bayan Samilat da Hantaru sun dade suna kuka na bakin ciki sai boka Sulbaini ya janyeshi daga jikin Salimat, sannan ya jashi gefe daya inda su Salimat ba zasu ji abinda zasu tattauna ba. Sulbaini ya dubi Hantaru cikin natsuwa sannan yace ya kai wannan Gwarzon jarumi, namijin Duniya, kayi sani cewa na hango maka mugun hadari a cikin rayuwarka da kuma mummunan karshe amman fa sai idan kayi sakaki soyayya ta rudi zuciyarka, na sani cewa Gimbiya Larziyya ta baka wasika a jiya sa'ar da aka yi walima a gidan Shuraim, kuma ta gayyaceka zuwa bayan gari tana son ku hadu a dutsen kufainu, ko ba haka bane ? Hantaru ya gyada kai cikin mamaki yace haka al'amarin yake. Boka Sulbaini yayi ajiyar zuciya sannan ya ce yakai wannan jarumi ka sani cewa Gimbiya Larziyya kyakkyawar mace ce ta gaban keatance dan haka da zarar ka yi arba da ita zaka ji ka tsunduma a cikin kogin soyayyarta, kuma zaka iya salwantar da rayuwarka kai data kowa ma dan kawai ka mallaketa, gargadin da zan yi maka shine, kada ka yarda ta umarceka da yin abinda zai sa ka rushe alakar dake tsakaninka da jikata Salimat anan gaba bayan kaci gasar tseren gudun barewa, idan kuwa ka kuskura ka aikata haka to kaima halaka zaka yi, kuma daukakarka zata tafi a banza, sai dai kawai a dunga tuno da kai a tarihi. Lokacin da boka Sulbaini ya zo nan jawabinsa sai hankalin Hantaru ya dugunzuma fiye da koyaushe, yayi shiru yana tunani har izuwa lokaci mai tsawo, daga can sai ya dago ya dubi boka Sulbaini yace lallai zan kiyaye bisa dukkan wannan shawara daka bani. Cikin farin ciki boka Sulbaini ya rungume Hantaru yana mai cewa madalla da da mai halacci ga jikata, wanda naso ace ya zamo jinin jikata. Koda jin haka sai Salimat ta taso da gudu daga inda take tsugunne ta rungume Sulbaini da Hantaru suka kankame juna su uku suka fashe da sabon kuka. Shuraim dake tsaye yana kallonsu shima sai ya fashe da kuka aka rasa wanda zai rarrashi wani a cikinsu. Shuraim, Salimat da Hantaru basu yi sallama da boka Sulbaini ba sai da la'asar ta yi, lokacin da suka zo yin sallamar ne sai Sulbaini ya dubi Hantaru ya ce da shi ya kai Gwarzon namiji ina son kayi sani cewa zaka sha bakar wahala a wannan gasar tseren da zaka yi, kuma kai da Sadauki Rabbasu kunnen doki zaku yi a cikin gasar, saboda haka sai kunyi gasar sau uku, kaga kenan dole ne ka zauna a wannan garin tsawon shekara uku, idan ma har zaka lashe wannan gasa to sai bayan kaje ka samo wata sihirtacciyar takobi wacce babu kamarta q fadin duniya. Tabbas kai da Sadauki Rabbasu zaku tafi neman wannan takobi, duk wanda ya riga dan uwansa mallakar wannan takobi to shine zai auri gimbiya Larziyya. Tabbas sai ka jajirce ainun sannan zaka iya samo wannan takobi da ake yiwa lakabi da Saiful Lujara. Asalin takobin Saiful Lujara wani hatsabibin boka ne ya kareta da ruhin wasu babaken aljanu guda dubu casa'in, a rabar da bokan ya kammala takobin ne ya mutu, sakamakon tsananin wahalar daya sha a kokarin kerata, saboda sai da ya kwana hudu ba ci ba sha, tsananin yunwa da kishin ruwa ne suka kasheshi, yanzu haka takobin na nan a cikin wannan kogon da bokan ya mutu, kuma babu wanda ke iya zuwa inda wannan takobi take saboda tsananin masifun dake cikin dazuzzukan kafin a ketare a isa kogon, da kuma shi kanshi bala'in dake cikin kogon face sadaukin da ya yarda da Sadaukantakarsa, kuma ya zamana cewa yana da matukar karfin sihiri. Daga lokacin da makerin takobin Saiful Lujara yya mutu kawo izuwa yanzu shekara dubu uku kenan, kuma a kalla sadaukai sama da guda dubu sun tafi dauko wannan takobi amman har yau har gobe dayansu bai dawo ba. Ya kai Hantaru ni kam nayi alƙawarin cewa zan taimaka maka da dukkan karfin sihirina, kamar yadda sarkin mafarauta zai taimaka wa dansa Rabbasu da dukkanin karfin sihirinsa domin yaje ya samu damar dauko takobin daraja ta Saiful Lujara. Ka sani cewa bani da wani buri da ya fi naga kambun gasar tsere ya dawo zuri'armu ta makera. Sa'ad da boka Sulbaini ya zo nan a zancensa sai jikin Hantaru yayi sanyi kuma hankalinsa ya dugunzuma domin ya fuskanci cewar duk wahalar da ya sha a baya kamar somin tabice akan wacce zai sha a nan gaba, saboda samun nasarar sa akan sadauki Rabbasu a wannan gasa da kuma dauko takobin Saiful Lujara wannan abu ba karamin jidali bane. Nan dai boka Sulbaini yayi wa Hantaru sallama a matsayin ba zasu sake saduwa ba sai nan da kwanaki goma sha takwas wanda ya rage saura kwana daya ayi gasar tseren gudun barewa. Ba tare da bata lokaci ba Shuraim da Salimat suka yi wa Sulbaini sallama gami da godiya sannan suka sakko daga kan dutsen suka kwance dawakansu duk su ukun suka hau sannan suka nufi hanyar gida. Salimat na waigen gidan boka Sulbaini wanda ke saman dutse, ta tuno da rayuwarta a gidan tun tana yarinya karama kafin rasuwar matar boka Sulbaini, abinda salimat ba zata taba mantawa ba shine kullum sai sunyi wasan yar boyo ita da matar boka Sulbaini, wani lokacin ma har wasan doki suke yi, ta hau gadon bayan Sulbaini tana sukuwa. A daidai wannan lokacin ne hawaye ya zubo wa salimat taji ace inama zata iya dawo da abinda ya wuce amman ina ai babu dama. A lokacin da su Hantaru suka iso mararrabar hanya ne, inda ta rabu gida uku; daya zata kaisu izuwa cikin gari, daya izuwa dajin kufainu, dayar kuma izuwa inda suka baro. Sai Shuraim ya nuna wa Hantaru hanyar da zata sadashi izuwa dajin kufairu. Yace ya kai Gwarzon Sadaukai wannan hanyar ita zaka bi kaje inda gimbiya Larziyya ta ke, maza kaje ku hadu, sannan ka tabbatar ka dawo gida da wuri kafin dare yayi sosai. Koda jin haka sai Hantaru yayi murmushi sannan ya dubu salimat ya ce zan tafi izuwa ga Gimbiya idan har kinyi izini a gareni ya ummina. Salimat ta mayar masa da martanin murmushi sannan ta ce jeka abinka ya kai dana, ina goyon baya dari bisa dari. Koda jin haka sai Hantaru ya zaburi dokinsa cikin farin ciki ya sukwaneshi izuwa cikin dajin kufairu. Yar gajeriyar tafiya hnataru yayi ya iso inda dutsen yake, tun daga nesa Hantaru ya hango gimbiya Larziyya a bisa dutsen a zaune tana sanye da wasu kurayen tufafi, masu tsananin kyau da ban sha'awa ta lullube kanta gaba daya da mayafin kayan. Koda Larziyya ta hango Hantaru ya durfafo inda take, sai ta mike tsaye, mikewarta keda wuya sai iska ta dauke mayafin data rufe kanta da shi ta yi kasa da shi, a wannan lokacin ne hantaru yayi arba da fuskar Gimbiya Larziyya, tsarki ya tabbata ga ubangijin daya daidaita gabban jikin gimbiya Larziyya, a iya sanin Hantaru ko a bakin ma'abota labarin duniya, bai taba jin wanda ya wassafa mace mai kyau na Gimbiya Larziyya ba, saboda tsananin kyawun fuskarta dana kirar jiki. Idan mutum yayi arba da ita sai yayi tsammanin cewa ba mutum bace aljana ce. Hantaru dai bai san sa'ad da ya ja linzamin dokinsa ya tsaya cak ba, daga kasan dutsen suka kura wa juna idanu suna sun murmushi. Nan take yaji kibiyar so ta sokeshi a kahon zuci kuma yaji cewa a haukansa ko mutuwa bata isa hanashi mallakar gimbiya Larziyya ba. Cikin natsuwa da tafiyyar kasaita Larziyya ta sakko daga saman dutsen kufairu, tazo daf da Hantaru ta tsaya sannan ta ce lale marhabun da Sadauki uban sadaukai, tauraron zamani mai haska duniya. Ya kai Hantaru ka yi sani cewa yauce ranar da tafi kowacce rana farin ciki a rayuwata, domin a yau nayi arba da masoyin zuciyata wanda na dade ina begensa tun gabanin naga fuskarsa, ina godiya daka amsa gayyata ta bisa muhimmiyar wannan rana ta saduwarmu. Shin daka ganni a yanzu kaji kana sona, kamar yadda na dade da kamuwa da kaunarka? Lokacin da Hantaru yaji wannan tambaya sai yaji dariya ta kubuce masa, itama sai ta kama dariyar kamar su duka biyun sun zautu. Lokaci guda suka daina dariyar kuma suka kura wa juna idanu, Hantaru yq ce yake wannan mafifiyar ma'abociyar kyawun, kiyi sani cewa babu wani mahaluki walau a mutane ko a aljanu da zai ganki bai kamu da tsananin kaunarki ba. Tabbas a yanzu ina ji a jikin cewa zan iya salwantar da rayuwata domin farin cikinki ko domin na mallakeki. Koda jin wannan batu sai Gimbiya Larziyya ta cika da tsananin farin ciki, nn take rungume hantaru suka kankame juna har izuwa wani lokaci mai dan tsayi, daga can sai ta janye jikinta daga nasa suka fuskanci juna ta ce ya kai masoyina kayi sani cewa yau saura kwana goma sha tara ayi gasar neman aurena, kaine kadai mutumin da zai iya share mani hawayena, ya hana Sadauki Rabbasu samun nasara a wannan gasa, idan har kaunar da kake mani ta gaskiya ce ina so ka daukar mani alkawarika guda uku a yanzu, alkawari na farko shine; duk wuya duk rintsi ba zaka janye takarar neman aure na ba, alƙawari na biyu duk alfarmar da na nema a wajenka zaka yi mani ita, alkawarina na uku kuwa shine a duk halin da muka tsinci kanmu ba zamu guji juna ba, idan har ka amince da wadannan alkawaruka to nima na yi maka alkawari cewa zan sallamar da rayuwata domin ka, kuma har abada babu wani da namiji da zai sanni ya mace face kai, haka kuma duk irin bala'in da zaka shiga zan bika mu shiga tare koda kuwa zan hallaka. Sa'ad da Gimbiya Larziyya ta zo nan a bayaninta sai Hantaru ya ji zuciyarsa ta buga da karfin gaske, abinda ya fara fado masa a rai ne shine batun alkawarin daya daukar wa mahaifiyarsa, Hantaru ya tambayi kansa a cikin zuciyarsa anya kuwa alkawarin dana daukar wa ummina ba zai zamo kishiyar wanda Gimbiya Larziyya ta ke so na daukar mata a halin yanzu ba kuwa? Nan fa ya rasa irin hukuncin da ya kamata ya yanke. Lokacin da Larziyya taga Hantaru yayi shiru bai bata amsa ba, kuma ya sunkuyar da kansa kasa yana tunani, sai ta dafa kafadarsa ta ce kai nake sauraro ya masoyina, wane hukunci ka yanke game da alkawarin da muka daukar wa junanmu. Hantaru ya dago kai cikin murmushi yace yake abar kaunata kiyi sani cewa kinzo mani da babban alƙawari, wanda yafi gaban na yanke hukunci yanzu take, saboda haka ina neman alfarmar ki bani lokaci nayi tunani. Koda jin haka sai Larziyya tayi murmushi sannan ta ce na baka lokaci, daga nan har izuwa ranar da za'a fara gasar neman aurena, amman sai kayi alkawarin cewa ba zaka yi shawara da kowa ba, sai da zuciyarka kadai. Hantaru ya maida mata da martanin murmushi sannan ya ce nayi alkawarin ba xan yi shawara da kowa ba face da xuciyata, cikin tsananin farin ciki Larziyya ta sake rungume Hantaru a karo na biyu sannan ta sumbaci goshinsa. Kawai sai ta tafa hannayenta biyu take wani bawan sarki ya fito daga cikin duhuwa janye da keken doki. Larziyya ta dubi Hantaru cikin wani irin murmushi mai dagula tunanin da namiji ta ce daga yau ba zamu sake saduwa ba sai ranar gasa, lallai a ranar ne zaka bani amsoshin tambayoyina, da wannan kalami nake maka sallama ya madubin zuciyata, sai lokaci yayi. Koda gama fadin haka sai Gimbiya Larziyya ta juya ta nufi inda keken dokinta yake tana mai waigen Hantaru, shi kuwa sai ya biya da kallo kawai ya kasa cewa komai har ta shiga cikin keken dokin ta zauna. Ina yi maku barka da wannan lokaci da fatan kuna cikin koshin lafiya 🙏🙏🙏 Ga masu son Complete Audio na Mazan Jiya Wanda Muhammad Umar Kaigama Ya karanta Ko Kuma Complete Document zasu iya mani magana ta whatsapp 08138873799 Bawan ya kafa linzaman dawakan dake jan keken dokin suka nufi hanyar cikin gari. Tun Hantaru na hango keken dokin har ya bace wa ganinsa, sai da Hantaru ya dade a tsaye yana mai nazari da tunani sannan shima jaye ya hau dokinsa ya nufi cikin gari. Da isar Hantaru gida sai ya iske tuni Salimat ta shirya masa abinci a ajiye a dakinsa. Bayan Hantaru ya zauna ne ya huta kuma ya ci abinci sai ya fada cikin kogin tunani, ya kasa yi wa kansa zabi bisa amsar da ya kamata ya baiwa Gimbiya Larziyya a ranar da za a yi gasa. Yana cikin wannan hali ne Salimat ta shigo cikin dakin ta riskeshi a cikin halin tunani. Cikin matukar damuwa Salimat ta zauna daf da shi sannan ta ce ya kai dana na sani cewa ka kamu da kaunar Gimbiya Larziyya domin babu wani da namiji da zai yi arba da ita ba tare d ya fada tarkon begenta ba. Ya kai dana ka fada mani dukkanin abinda kuka tattauna kai da ita, ni kuma zan baka shawara wacce zata fissheka a rayuwa. Koda jin haka sai Hantaru ya ji zuciyarsa ta buga da karfi ainun, kuma ta gargadeshi akan kada ya fada wa Salimat gaskiyar maganar da yayi da Gimbiya Larziyya. Hantaru ya dubi Salimat cikin murmushi yace yake ummina kiyi sani cewa babu abinda muka tattauna face kalmomin kauna gami da alkawarin zamu so juna da gaskiya. Koda jin haka sai murna ta kama Salimat ta sa masa albarka sannan ta mike tsaye ta fice daga cikin dakin. Kash! Hakika rashin sani yafi dare duhu, inda Hantaru yasan abinda zai biyo baya bisa boyewa Salimat gaskiyar al'amari da bai boye mata ba. Tabbas zuciya bata da kashi, kuma itace abar dake jefa mutum ga halaka dare daya. Daga wannan rana Shuraim da Hantaru suka rinka motsa jiki, yana nuna masa yadda ake yin wannan gasa ta tseren gudun kamo barewa a daji, a kullum sai su wuni suna gudu a daji, kuma suna gudun ne a bisa dawakai suna yakar juna domin daya ya jefo daya daga bisa dokinsa. A wannan lokacin ne Hantaru ya tabbar da cewa lallai Shuraim ya cika Sadauki domin yayi mamaki matuka da yaga irin juriyarsa gami da jarumtakarsa wajen shanye duka da kuma zafin namansa na kare sara da suka yayin da suke gudu a kan dokin, duk da cewa girma ya fara kamashi. Duk irin kokarin da Hantaru ke yi a wannan motsa jiki da suke yi, kullum.sai yaga Shuraim baya yaba masa, domin a kullum ce masa yake ya kai jikana ka kara kwazo domin har yanzu baka yi rabin kwazon da Sadauki Rabbasu zai iya yi ba yayin gasar, nasan yanayin gasar nan kuma nasan sirrinta ciki da bai, sannan nasan iyakar jarumtakar Rabbasu, bugu da kari duk shekara idan za a yi wannan gasa sai Rabbasu ya fito filin gasar ya zuba idanu yana nazarinta. Tabbas ya fika sanin sirrinta shiyasa nake da yakinin sai ya fika kokari dan har baka kara jajircewa ba, gobe zan gayyato samarin zuri'armu mu fita daji tare domin mu gwada wannan gasa tare da kai, a sannan ne zanga iyakar kokarin da zaka iya yi. Kashegari kuwa da sassafe samarin zuriar makera suka taru a gidan Shuraim sannan suka dunguma suk tafi daji domin jarraba gasar tseren barewa tare da Sadauki Hantaru. Ai kuwa ana fra wannan gasar sai Hantaru ya raina kansa, domin kuwa kafin ya farga tuni anyi masa fintinkau. Sabida samarin sun kware ainun wajen sarrafa doki, kuma kowannensu ya dade yana hora dokinsa saboda zuwan wannan rana. Sai da Hantaru ya zamo shine a can baya na karshe, koda ganin haka sai hankalin Hantaru ya dugunzuma, zuciyarsa ta harzuka ya tuno da gwagwarmayar da yayi a baya, ya kuma tuna cewa shifa sadaukine na kwarai, lallai idan bai dage ba ya ci wannan gasa ba, to kamar ya rasa Gimbiya Larziyya ne, kuma ya kasa karbo kambun gasa daga zuri'ar mafarauta wanda shine burin mahaifiyarsa Salimat. Hantaru yace da kansa a cikin zuciyarsa, me zanyi na saka wa da Salimat a rayuwa bisa shayar dani da tayi a matsayin dan cikinta? Kuma ta rikeni amana ba tare da tasan cewa ba dan cikinta bane ni. Abinda zanyi shine ya wanke bakin cikin zuri'arsu gabadaya wanda ya addabi zuciyarsu tsawon shekara da shekaru. Koda hantaru ya gama ayyana haka a cikin zuciyarsa sai ya kara zaburar dokinsa yayi masa kaimi ya kutsa cikin jaruman gasar nan yana bangaje wasunsu, bisa mamaki sa sai yaga yana matsawa gaba-gaba, sannu a hankali sai da riski wadanda ke kan gaba wasu zakwakuran samari jaruman gaske su uku, wadanda ya kasa wucesu, Hantaru ya dage iya karfinsa yana kai masu sara da suka da mangari, suma suna mayar masa da martani, amman saboda nacinsu sai ya kasa zubar da su a kasa, sai da suka yi doguwar tafiya a haka har suka fara hango barewar da aka saki tana ta tsula gudu ana so su cimmata. A karshe dai da hantaru da wadannan zakwakuran samarin jarumai uku ragas akayi, wato duk sun banke junansu sun fado kasa daga kan dawakansu, dayansu bai samu nasarar kamo barewar ba. Al'amarin daya dugunzuma hankalin Hantaru kenan, ransa ya baci kuma gwiywarsa tayi sanyi akan wannan gasa. Amman sai Shuraim ya karfafeshi akan cewar ya kara kwazo nan gaba akwai alamar cewa zai zamo zakara. Haka dai aka cigaba da wannan gasa ta baiwa kai horo dan tanadin ranar babbar gasa ta ainahi, ya zamana cewa a kullum sau biyu ake yin gasar safe da yamma, sai da ya rage saura kwana daya jal ranar gasar ta ainahi ta zo, a wannan rana ne Jarumi Hantaru ya samu nasarar banke wadannan zaratan jaruman guda uku ya zubar da su kasa, sannan ya cimma barewar da keso a kamo ya cafketa. Nan fa jama'ar zuri'ar makera suka cika da tsananin farin ciki, domin sun san cewa yanzu kam sun samu Gwarzon da zai karbo masu kambun gasa daga hannun zuri'ar mafarauta. A wannan rana kwana akayi suna walima, kadede-kadede gami da raye-raye, babu wanda yafi Shuraim da Salimat farin ciki a wannan rana, domin kuwa basu san iyakar dukiyar da suka raba wa jama'a ba. Wannan shine abinda ya faru a bangaren makera na birnin Darul Habur. ******************* Acan bngaren zuri'ar mafarauta kuwa lokacin da sarkin mafarauta Zaharu Ibn Dauwar ya isa gida tare da dansa Rabbasu a sume, tare da dukkanin jama'arsu, sai suka taru a cikn fadar Zaharu aka shimfide Rabbasu a bisa wata doguwar kujera, nan take Zaharu ya karanta wasu dalasiman tsafi ya tofa masa, nan take rabbasu yayi atishawa ya farfado, a dimauce ya mike tsaye zumbur yana mai kokarin kai duka, domin shi a zatonsa har yanzu yana fafatawa ne da Hantaru. Bisa ga mamaki sai yaga mahaufinsa tre da jama'arsu a tsaitsaye suna kallonsa kawai. A sannan ne ya dubi inda yake ya gane gida yake ba kasuwa ba. Cikin tsananin fusata Rabbasu ya dubi mahaifinsa ya ce ya abbana ina abokin fadana yake ne? Yaya akayi nazo nan gida? Koda jin wannan tambaya sai Zaharu ya bushe da dariya sannan lokacin guda ya murtuke fuska kamar wanda aka aikowa da sakon mutuwa, nan take kuma kwallar takaici ta zubo masa ya ce ya kai dana kayi sani cewa ba wani bane ya zo ya raba fadanku da wannan bakon saurayin ba face babban abokin adawata boka Sulbaini, wannan bakon jarumi ya kasance babban barazana ga zuri'armu gabadaya, domin yazo ne domin ya rabamu da kanbun gasar gudun tseren barewa, kuma shi gimbiya Larziyya ke son ta aura. Koda jin wannan batu sai Rabbasu ya kwarara uban ihu, wanda ya firgita kowa dake wajen, fuskarsa ta kama kakkarwa kamar zata zazzago ta fado kasa, cikin tsananin fushi ya dubi Zaharu ya ce ya kai abbana ka sani cewa yau shekaru sittin kenan ina tanadin neman auren Gimbiya Larziyya, ka sani cewa ina matukar kaunar Larziyya irin kaunar da in har na rasata to lashakka sai na rasa rayuwata, yaya kake tsammanin cewa zan bari wani yazo ya mallaketa. Zaharu ya dafa kafadar Rabbasu ya ce ka kwantar da hankalinka ya kai dana, kaima ka sani cewa babu yadda za a yi ina raye a doron kasa hakan ta faru, ina tabbatar maka da cewa yanzu lokaci yayi da zan baka gabadaya sirrinkan tsafina sabanin da dana baka rabi kawai, ka sani cewa abinda yasa ban baka sirrikan tsafina ba, shine kana da tsananin fushi da bakar zuciya, idan ka mallaki sirrin tsafina duka cewa zaka yi zaka yaki boka Sulbaini, duk ranar daka yaki boka Sulbaini kuwa a ranar wannan birni namu sai ya baje kowa ya hallaka. A halin yanzu bani da wani zabi face na baka sirrikan tsafinnawa tunda ni bani da ikon shiga wannan gasa, domin kare martabar zuri'armu da kuma mallakar gimbiya Larziyya. Abu na biyu dole ne mu baka sabon horo akan wannan gasa, domin ka samu karfi ninkin na da da kake da shi, dan kada abokin gabarka ya samu nasara akan ka, ka sani cewa da mutum dubu uku ake wannan gasa ta tsere, to amma daga yanzu kullum zaka rinka jarraba wannan gasa da mutane dubu shida, lallai indai ka samu nasara akan mutum dubu shida to ba makawa sai ka samu nasara akan abokin gabarka, wato wannan bakon jarumin daya zo. Koda jin haka sai Rabbasu ya cika da farin ciki. Daga wannan rana aka soma baiwa Rabbasu horo da mutum dubu shida, kuma kullum sau uku ake yin gasar, safe, yamma da dare. Tun a ranar farko Rabbasu ya rinka banke zaratan dakaru, duk inda ya ratsa ta cikinsu sai dai kaga maza na zubewa kasa, wani lokacin ma har dawakan nasu yake bankewa kasa, saboda tsananin karfin Rabbasu sai da ya lashe gasar nan. Daga ranar farko da aka fara wannan gasar zuwa ranar karshe kullum Rabbasu ne yake lashe gasar, kuma ko dau daya ba a taba kaishi kasa ba. Tabbas Rabbasu ya cika sadaukin Sadaukai domin yafi hantaru karfin damtse, a ranar karshe ana gobe za a yi gasar ainihi ta neman auren Gimbiya Larziyya boka Zaharu ya sanya dukkanin sirrikan ttsafinsa a jikin Rabbasu. Nan take Rabbasu yaji wani gagarumin karfi ya shige shi, tamkar zai iya nada gammo a ka a dora masa duniyar gabadayanta. Nan take ya cika da farin ciki, ya ji a zuciyarshi cewa dole ne ko ta halin kakama yaci wannan gasa da za'a yi. Acan cikin gidan Shuraim kuwa har dare ya raba amman boka Sulbaini bai zo ba kamar yadda yayi alkawari, al'amari daya dugunzuma hankalin Shuraim, Samilat da mahaifiyar Samilat kenan, domin sun san cewa muddin Hantaru bai samu taimako daga boka Sulbaini ba, babu yadda za a yi ya ci wannan gasa akan Rabbasu, saboda sanin cewa dole ne Zaharu mahaifin rabbasu yayi masa gagarumin shiri irin wanda bai taba yi masa ba. Haka dai aka kwanta cikin ta tarrabi da jimami. Al'amarin Sadauki Hantaru kuwa ko kadan baiji wata damuwa ta shigeshi ba, saboda koda yaushe yana da yakinin cewa indai yana cikin hayyacinsa babu wani tsautsayi da zai taba lafiyarsa. Hantaru na kwanciya sai bacci ya dauke shi, tamkar babu wani gagarumin abu dake gabansa a gobe, daf da ketowar alfijir ne Hantaru ya farka daga bacci, kawai sai yaga boka Sulbaini a zaune daf da shi idanunsa a rufe yana jan wani abu. Abinda ya daure wa Hantaru kai shine kofar dakin da tagar dakin a rufe suke ruf, to wai shin ta ina Sulbaini ya shigo cikin wannan dakin ba tare da ya sani ba, kuma ta ina ya shigo din? Koda ya tuna cewa iki ne na tsafi sai hankalinsa ya kwanta, hantaru ya yunkura da nufin mikewa zaune, amman sai Sulbaini ya nuna kirjinsa da tafin hannunsa, take Hantaru ya ji an danne shi da wani irin karfi na musamman wanda b zak iya dagowa ba. Bisa dole ya koma ya kwanta, faruwar hakan ke da wuya sai Sulbaini ya kammala wuridin tsafin da yake yi, kuma yayi tofi akan kirjin Hantaru, har a sannan Sulbaini bai bude idanunsa ba, koda ya tofa sai Hantaru yaji wani irin radadi da zugi na shigarsa, nan take gabadaya jikinsa ya kama kakkarwa, sannan wata irin zufa mai yawa ta rinka kwaranyowa daga jikinsa tana zubowa a kasa tamkar ana kwarara ruwa a wajen. Jim kadan sai zufar ta bace bat daga jikinsa, wanda ta zube a kasa ma ta bace. Nan take Hantaru yaji wani irin gagarumin karfi ya shigeshi, irin wanda bai taba jin kamarsa ba a rayuwarsa, domin ji yayi kamar shi kadai zai iya tunkarar gabadaya dakarun duniya, yayi yaki da su tsawon kwanaki arba'in ba tare da ya gaji ba. A daidai wannan lokaci ne boka Sulbaini ya bude idanunsa cikin murmushi yace bude idanunka ya kai sadaukin Sadaukai. Hantaru ya mike zaune daga kan gadon suka fuskanci juna, boka Sulbaini yayi gyaran murya ya ce Yanzu na gama nawa, na gama baka iyakar taimakon da zan iya baka, ya kai sadaukin Sadaukai ka yi sani cewa na baka dukkanin sirrikan ttsafinsa, ni yanzu babu abinda zan iya yi na tsafi, domin duk karfina ya koma jikinka, kamar yadda na boka Zaharu ya koma jikin dansa, idan har baka ci nasarar wannan gasa da za'a yi ba mutuwa zan yi, haka ma idan Rabbasu bai ci nasarar wannan gasa ba, boka Zaharu mutuwa zai yi, mu haka ka'idar tsafinmu ta ke. Ya kai Hantaru ka yi sani cewa dukkan burinmu mu jama'ar makera a kanka ya ke, dan haka ya zama dole ka zage damtse ta kowanne hali ka ci wannan gasa. Koda Hantaru yaji wannan batu sai hankalinsa ya dugunzuma ya dubi boka Sulbaini cikin tsananin damuwa ya ce Ya shugabana, sabida me zaka salwantar da rayuwarka akan wannan bukata, kayi sani cewa mahaifiyata na tsananin kaunar ka, yau idan aka ce babu kai zata iya shiga cikin wani hali, ina rokonka bisa darajar zuri'arku da soyayyarka ga kakana Shuraim ka cire wannan shiri na tsafi da ka bani, k barni da tsagwaran karfin damtsena, ina mai tabbatar maka da cewa t kowanne hali sai na lashe wannan gasa. Sa'ad da Hantaru ya zo nan a jawabinsa, sai kawai yaga hawaye ya zubo wa da boka Sulbaini daga cikin idanunsa, abinda yayi matukar bashi mamaki da tsoro kenan. Boka Sulbaini yayi ajiyar zuciya sannan ya ce yakai jikana ina so kasani cewa ni nasan abinda kai baka sani ba, akwai wani sirri babba wanda bazan iya fada maka shi a halin yanzu ba, kuma shine dalilin da yasa na sallamar da rayuwata dan samun nasararka, zaka iya sanin wannan dalili amman sai bayan mutuwata idan ka shiga dakin tsafina. Yace alfarmar da nake nema a wajenka ita ce kada ka kuskura ka fada wa mahaifiyarka Salimat cewa na baka sirrikan tsafina duka, domin idan ka yi haka zata iya shiga mugun hali ta rasa sukuni daga yanzu har izuwa ranar da za a kammala wannan gasa. Da wannan furuci nake maka sallamar karshe idan da rabon mu sake saduwa zamu sadu bayan ka lashe gasa. Koda kammala wannan jawabi sai Hantaru ya ji ya kamu da tsananin tausayin boka Sulbaini, dan haka sai ya rungumeshi ya fashe da kuka, kuma yana mai cewa da iznin abin dogaronka sai mun sake saduwa, da yardar su su ummana ba zasu zubar da hawaye ba. MAZAN JIYA Littafi Na Daya (1) Part Q Marubuci: Abdulaziz Sani M/Gini Typing: Abubakar Saleh AlQuyraemey Kafin Hantaru ya gama rufe bakinsa tuni boka Sulbaini ya ce bat daga cikin dakin, nan fa Hantaru ya nemeshi sama ko kasa ya rasa. Kashegari kuwa tunda duku-dukun safiya jama'ar birnin Darul Habur suka fara tafiya wani daji da ake kira Furja'al Maut, daga cikin birnin Darul Habur zuwa dajin tafiya ce ta rabin sa'a kacal, al'amarin daga daure wa jama'ar birnin kai shine shigowar baki daga kauyuka da birane da dama dan kallon wannan gasa, kai harma daga wasu nahiyoyi haka jama'a suka yita zuwa birnin Darul Habur tun ma saura kwana goma a fara wannan gasa. Al'amarin da ya janyo cunkoso a cikin birnin kenan na fatake dama yan kasuwa. Nan fa kasuwa ta bude, bisa tarihin birnin ba'a taba samun arki mai yawa a kasar ba irin na wannan shekarar ba, kuma ba a taba ganin yawan jama'a irin na wannan shekarar ba, sai da takaicewa babu masaukai inda baki zasu zauna, hakan yasa har a wajen gari kafa tantuna ake yi, kai ko ruwa mutum yake saidawa a wannan lokaci cikin kwana uku yake zama attajiri. Ba komai bane duk ya haddasa wannan al'amari ba face labari ya bazu cewa Sadauki Rabbasu ya shiga wannan gasa, wanda labarin jarumtakarsa ya bazu ko ina a nahiyar kuma an samu labarin cewa an samu wani bakon jarumi da ya iya fafatawa da shi har tsawon rabin sa'a b tare da dayansu ya samu nasarar komai akan dan uwnsu ba. Sannu a hankali jama'a suka rinka turueuwa a cikin dajin Furja'al Maut suna hawa saman manyan Duwatsu da tsaunuka suna masu tsayawa dan kallon wannan gagarumar gasa da za a fara a yau din. Shidai wannan daji na Furja'al Maut daji ne mai girma da fadin gaske, kuma duwatsu dake ciki sun kasance masu tsananin yawan gaske, wasu tsaunukan ma idan mutum ya hau shi sai a hangoshi dan mitsitsi tamkar dantsako. Kafin gari ya waye dajin ya cika ya batse da jama'a babu masaka tsinke, face wacce take a tsakiya wadda aka barwa dakarun gasa. Bayan jama'a sun shafe kusan sa'a uku a tsaitsaye suna jira, sai ga dakarun gasa sun tunkaro dajin daga can nesa, tawagar farko mutum dubu daya da dari biyar ne, sunyi shigar jajayen tufafi, dukkaninsu suna bisa fararen dawakai abin gwanin ban sha'awa, sannan suna rike da kulake na duka babu dayansu dake rike da takobi ko wani makami na karfe. Wannan zuga ita ce ta zuri'ar makera na birnin Darul Habur. A cikinsu gabadaya babu mai kwarjini da daukar hankali sama da Sadauki Hantaru, su kansu gabadaya dakarun wato yan uwansa sun sallama masa, kai da gani kasan cewa wannan karon sun fito gasar ne da matukar karfin gwiywa, kasancewar suna tare da shi, sai yi masa kirari da jinjina suke yi. Jim kadan da shigewar wannan tawaga sai kuma ga tawaga ta biyu wanda suma sun kasance su dubu daya da dari biyar, gaba dayansu suna sanye da bakaken tufafi haye bisa bakaken dawakai, babu wani mai haske a tare da su, saboda tsananin kwarjinin wannan tawaga sai da yan kallo suka razana, wasuma buya suka kamayi, saboda gani suke kamar zasu iya afka wa yan kallo a kowanne lokaci, suyi masu tamore, saboda ko kadan babu alamar tausayi ko digon imani a bisa fuskokinsu. A tsakiyar wannan tafiya Sadauki Rabbasu ne bisa wani jibgegen doki da yafi na sauran girma. Rabbasu ya shafe dukkanin jikinsa da bakin shuni, in banda jajayen idanunsa da ake gani babu abinda mutum ke iya gani a fuskarsa, sai faman huci da gurnani yake kamar tsohon mayunwacin zaki. Wani ayari daban na zuri'ar mafarauta na biye da su a baya, sunata buga tambura da ganguna kuma suna raira wakoki na jinjina da kirari ga sadauki Rabbasu. Duk mahalukin da yazo wannan daji na Furja'al Maut sai da hantar cikinsa ta kada a lokacin da Rabbasu ya kurma wani uban ihu, mai tsananin razanarwa face jarumi Hantaru wanda ya saba da kuruwar manyan aljanu da dodanni, shine kawai bai razana ba. Suma wannan tawaga ta biyi babu makamin karfe a hannunsu sai kulake, domin yanayin gasar kenan, ba a yarda a xo da makamin karfe ba. Bayan tawagar biyun ta cakude ne sai aka fara kallon kallo gami da harar juna. Wohoho! Yayin da manyan mazaje suka hada ido kuwa sai da zuciyar kowa a wajen ta buga da karfin gaske dan kada su kacame da azabben fada su tashi hankalin duwatsu da bishiyu dake wajen. Rabbasu da Hantaru suka kura wa juna idanu ko kiftawa basa yi, kowannensu fuskarsa ta kama gyatsine kuma jikinsu ya kama tsuma ji suke kamar su rufe juna da duka tun gabanin a fara wannan gasar. Wani akasi kuma da aka samu shine Rabbasu na daga hannun hagu shi kuma Hantaru na daga hannun dama, har ma wani lokacin idan aka yi turmutsutsu kafadunsu na gogar na juna. Jim kadan da cakudewar tawagar biyu sai alkalan gasar suka shigo cikin tawagar suna masu binsu daya bayan daya suka cajesu, aka tabbatar da cewa babu dayansu daya boye makamin karfe a jikinsa, ya zamana cewa in banda guraye da layu babu komai a jikinsu, to kuma sai kulkin duka. Gama hakan keda wuya sai alkalan gasar suka fice daga cikin tawagar biyi su hau kan duwatsu suka tsaitsaya kafin a busa kahon fara gasar. A daidai wannan lokacin ne kuma Hantaru ya hango gimbiya Larziyya a cikin taron yan mata can saman wani tsauni, tana danye da jajayen tufafi masu ratsin fari, wato dai tayi shiga irin dakarun zuri'ar makera, al'amarin daya baiwa kowa dake wajen mamaki kenan, aka shiga zunde da surutu ana cewa Me yasa gimbiya Larziyya zata yi irin wannan shiga, alhalin tana matsayin yar sarki, ai bai kamata ta nuna bangaren da take so ba daga cikin zuri'ar nan guda biyu ba. Duk da cewa kowa yasan cewa bata son Sadauki Rabbasu, dan ta tsaneshi kamar yadda ta tsani mutuwarta. Koda Gimbiya Larziyya ta hada idanu da jarumi Hantaru, sai ta cire amawalin data rufe bakinta da shi ta yi masa murmushi. Koda Hantaru ya maida mata da martanin murmushin sai ta daga hannunta ta yi masa jinjina, sannan ta rufe fuskarta kuma ta sake daure fuska tamau ta ki yarda ta kalli fuskar Sadauki Rabbasu. Wannan abu da gimbiya ta yi ba karamin bakin ciki ta dasa wa Sadauki Rabbasu a cikin zuciyarsa ba, nan take jikinsa ya kama kakkarwa kuma zuyarsa ta kama tafarfasa kamar zata kone. Acan gefe daya kuma sarki ne da yan majalisarsa tsaitsaye bisa dawakai bisa wani dogon tsauni sun zuba idanu kasa dan ganin yadda wannan gasa zata kasance. Dama musamman aka sassabe dogayen bishiyoyi na dajin domin a samu cikakken samun damar kallon gasar yadda ya kamata. Nan take wani dogon mutum ya hau kan wani dogon tsauni da babu kowa a kansa, koda ya kafa kahon a bakinsa ya busa, sai karar sautin kahon ta cika dajin gabadaya. Aikuwa sai gaba daya dakarun gasa suka zaburi dawakansu a lokaci guda aka zuba tseren gudu. Wohoho! Idan da ace mutum yana nan yaga yadda dakarun nan suka rankaya da gudu kura na binsu a baya sai yayi tunanin yakin duniya ne za a yi. Nan fa aka fara bugun jama'a da kulake, daman tuni an saki wata barewa a sanda aka fara gudun ta fice da gudu ta gaban dakarun nan, haka ko wanne badakaren gasa ya ci buri sai ya kamo wannan barewar. Kaicon maza! Lokacin da aka fara bugegebiya a tsakanin tawagar nan biyu, sai al'amura suka zamo abin tsoro kuma abin tausayi, domin sai dai aga an mako mutum.ya fado kasa, dawakai sun tattakeshi yayi raga-raga, wani lokacin ma har dawakan ake makewa su fadi kasa, wasu zaratan jaruman masu naci da tsananin juriya ko an maka masu kulki a kasa basa yarda su fado kasa, sai dai kaga jini na tsartuwa a fuskokinsu suma suna mayar da martanin duka. Al'amarin Sadauki Rabbasu da Hantaru kuwa, tun daga lokacin da suka fara gidun ne suka shiga bugun junansu, wato suna gudu suna gudu suna bugun junansu da kulake ga kuma duka ta ko ina, ta fuska, ta kai ta jiki, dukan da suke yi wa junan nasu wawan duka ne, wanda babu mai iya shanyeshi a gaba daya dakarun gasar, tunda suka fara bugun junnasu babu wanda fatar jikinsa ta tsage ko ta kwaile, sai dai kaji kara na tashi kamar ana bugun bugun dawa da tabarya, tim! Tim! Duk wanda aka zabga wa kulki sai dai kaga ya girgije ya mayar da martani. Kafin a samu tsawon dakika dari uku da sittin da fara wannan tsere an zubar da fiye da rabin dakarun a kasa, wasu sun kakkarya wuya sun mutu, wasu kuma sun kakkarye a gabban jikinsu, wasu kuma jikinsu yayi fatafata ba kyan gani, ga dukkanin alamu ba zasu yi rai ba. Komai rashin tausayin mutum idan yaga yadda mutane ke ragargajewa cikin wannan gasa dole ne zuciyarsa ta raunana. Sannu a hankali dakarun gasa suka rinka zubewa kasa har ya zamana cewa saura bai fi su dari uku ba, daga cikin su dubu uku. A wannan lokacin ne dokin Hantaru dana Rabbasu suka baiwa sauran dakarun rtaa mai yawan gaske, har ya zamana cewa suna iya hango barewar da akeso su cimmawa. Nan fa suka kara karfin gudu kum suka cigaba da kaiwa junansu cikin tsananin karfin hali da jarumta fiye da farko, aiko nantake kalaken naku suka kakkarye saboda tsabar bugun juna da suke yi, duk fuskokinsu sun kumbura, haka jikinsu ma duk ya kumbura, idanunsu ta kumbura hatta fatar idanunsu neman rufe idon take yi saboda itama ta kumbura abun ba kyan gani. Lokacin da Hantaru da Rabbasu sukaga kulakensu sun kakkarye sai suka ci gaba da naushin juna da hannu, a duk lokacin da Rabbasu ya naushi Hantaru a fuska sai yaga taurarin wuya, idan tsananin zafi da zugi ya shigeshi ya dimauce sai kaga yana layi kamar zai fado daga kan dokinsa, amman sai kaga ya makalkale dokinnasa shima ya takarkare ya ganza wa Rabbasu wawan naushi a fuska, saboda kasancewar Rabbasu ya fi Hantaru tsananin karfin damtse da juriya, ko Hantaru ya naushe shi baya yin layi sai dai ya shanye naushi kuma ya mayar da martani sau uku a jere kuma a lokaci guda. Kafin cikar dakiki dari uku Rabbasu yayi laga-laga da Hantaru, amman saboda tsananin naci da juriya Hantaru yaki yarda ya fado kasa, shi kuwa Rabbasu yayi mtukar mamaki yadda aka yi Hantaru bai fado kasa ba, duk d cewa ya galabaita ainun har ma kamar numfashinsa yana neman daukewa. Adaidai wannan lokacin ne gaba daya sauran dakarun suka ci kasa suda dawakan nasu, ya rage saura dokin Hantaru da na Rabbasu kadai dauke da mahayansu sunata tsala gudu. Mahayan na cigaba da gumurzu ga barewa a gabansu sun kusa cimmata. Duk wannan abu dake faruwa akwai wasu zaratan alkalan gasa su hudu suna bin dakarun gasa a baya cikin tsananin gudu, su dai wadannan alkalai dama can kwararrun mahaya dawakai ne wadanda babu kamarsu a gasar tseren doki a birnin kaf, kuma aminttatun sarki ne, suna aiki ne ba tare da son wani bangare ba daga cikin zuri'ar guda biyu. Lokacin da Sadauki Rabbasu ya waiga baya yaga gaba daya dakarun gasar sun zube saura su biyu tak, wato daga shi sai Hantaru. Sai ya harzuka ya kara kaimi wajen naushin Hantaru. Da dai yaga ya kasa kada Hantaru sai ya dage ya zabga wa dokinsa naushi a ciki, take dokin ya sulale ya fadi kasa tare da Hantaru. Dokin nan ku shurawa bai yi ba haka ya zama gawa, a wannan lokacin tuni Rabbasu ya fara kyalkkyala dariyar farin ciki, yana ganin cewa lallai shine zai lashe wannan gasa saboda ya kai Hantaru kasa, kuma tsakaninsa da barewar nan bai wuce kamu biyar ba. Ba zato ba tsammani sai kawai sadauki Rabbasu ya ji ana binsa a baya Daf! Daf! Ko da ya waiga baya sai yaga ashe hantaru ne ya biyoshi cikin wani irin azabben gudu na gaban kwatance, wanda ko dokin ma sai haka, har saura kiris ma ya riske shi. Cikin tsananin fushi da mugun nufi Rabbasu ya shiga kaiwa Hantaru duka ta bayan da mugun nufi, amman sai Hantaru ya rinka sunkuyawa yana kauce wa dukan, cikin matukar zafin nama Hantaru ya daka tsalle ya haye saman dokin Rabbasu ya rukunkumoshi ta baya suka fado daga kan dokin tare, kafin Rabbasu ya mike saboda tsananin nauyinsa ya ninka na Hantaru, tuni Hantaru ya mike ya gabza wa dokin Rabbasu naushi a fuska, nan take idon dokin ya fashe ya sulale kasa matacce. Nan fa hantaru da Rabbasu suka kasa tsere kowannensu na kokarin ya kamo wannan barewa, har a sannan alkalan gasa na biye da su kuma duk sunga abinda ya faru, bisa ga mamaki sai gudun Hantaru dana Rabbasu ya zo daya, ya zamana cewa suna hada kafada da juna an kuma rasa wanda zai wuce wani, kuma a hakan ne suka ci gaba d naushin juna amman a haka kowannensu ya ki yarda ya kai kasa. Yayin daya rage taku biyu kacal tsakanin su Hantaru da wannan barewa, sai suka daga tsalle sama a lokaci guda suka kai wa wannan barewar cafka, bisa rashin sa'a sai Rabbasu ya kamo kan barewar, shi kuma hantaru sai ya kama kafafunta, koda Rabbasu ya ja shima Hantaru ya ja sai barewar ta rabe gida biyu, a dai-dai wannan lokacin ne alkalan gasar suka karaso gabansu a guje bisa dawakai suka yi turjiya. Cikin zafin nama alkalan uka sakko daga kan dawakansu, mutum biyu suka rike Rabbasu, sauran biyun suka rike Hantaru kowannensu yana rike da rabin barewa a hannunsa. A wannan lokacin ne shima sarki da fadawansa suka iso wajen, sannan sai ga sauran jama'a yan kallo suma suna karasowa wajen. Sarki ya dubi alkalan gasar ya ce tsakanin Hantaru da Rabbasu yace wane ya fara kama wannan barewa da ta rabe biyu a hannunsu. Cikin hadin baki alkalan gasar suka ce a tare kuma lokaci guda suka kama barewar. Koda jin haka sai wuri ya yamutse da shewa murane suka hau fadin anyi ragas, anyi ragas... Nan fa dajin ya rude da hayaniya, sai da aka busa kaho sannan aka yi tsit tamkar mutuwa ta gifta, sarki ya dubi sauran jama'a ya ce sakamakon wannan gasa shine anyi ragas tsakanin Sadauki Rabbasu mai wakiltar zuri'ar mafarauta da Sadauki Hantaru mai wakiltar zuri'ar makera, saboda haka za a sake yin wannan gasa a shekara mai zuwa. Da jin haka sai jama'a suka barke da shewa gami da murna. Al'amarin Sadauki Rabbasu da zuri'arsa kuwa sai suka cika da tsananin bakin cika, Rabbasu bai san lokacin da hawaye ya zubo masa ba saboda tsananin takaici ya durkushe kasa ya kafa kansa a kasa. Shi kuwa Hantaru dama yasan cewa babu wanda zai samu nasara a wannan gasa tsakanin shi da Rabbasu, domin boka Sulbaini ya fada masa cewa sai sunyi wannan gasa sau uku babu mai nasara, wanda a karshe dole ne a tura su neman takobin Saiful Lujara dan kawo karshen gasar gabadaya a birnin na Darul Habur. Nan take Hantaru ya yanke jiki ya fadi kasa saboda tsananin galabaita, cikin gaggawa aka zo aka dauek shi aka sanya shi cikin kekn doki aka tafi da shi, saboda kumburin jiki da duruwar jini sai da aka kwana uku ana jinyar Hantaru sai a sannan jinin daya taru a fuskarsa da kuma jikinsa ya bace. Salimat ce tayita gasa masa jiki da ruwan dumi, kuma tana dafa masa magani yana sha, kafin jikin Hantaru ya dawo daidai a kullum idan ta dubw shi sai ta fashe da kuka saboda ganin irin tsananin wahalar da ya sha, hakan ne ma yasa ta tubure akan ba zata yarda a sake yin wannan gasa da Hantaru ba, sai dai su tattara yanasu-ya nasu su koma can birnin Kisra gidan mijinta. Da kyar d sidin goshi su Shuraim suka lallabata ta yard zata sake zama a garin har shekara ta zagayo. Wannan shine abinda ya faru a can birnin Darul Habur bayan anyi gasar tseren gudun barewa ta neman aure da aka saba yi duk shekara. MAZAN JIYA Littafi Na Daya (1) Part R Marubuci: Abdulaziz Sani M/Gini Typing: Abubakar Saleh AlQuyraemey ******* Acan birnin Kisra kuwa tun daga ranar da Shamilat da Hantaru suka bar gari sai sarki kusaidu ya shiga cikin wani mugun hali da bakin ciki, sannan yana yawan kuka bisa yawan begen yarima Hantaru da yake yi, abu kamar wasa sai sarki kusaidu ya kwanta ciwo kuma aka rasa abinda ke damunsa, domin sam bai fada wa kowa abinda ke damunsa ba. Lokacin da ya fahimci cewa idn ya kara jimawa a wannan hali to tabbas rayuwarsa zata salwanta, sai ya kira wadansu amintattun bayinsa su uku ya basu wasika yace suyi shiri su tafi can birnin darul Habur su kai wa matarshi wannan wasika. Nan da nan kuwa suk yi shiri suka kama hanya a sirrance ba tare da kowa ya sani ba, dalilin da yasa sarki Kusaidu bai yi shawara da boka Ardusa ba wannan karon shine yaga wani abu da yayi matukar daure masa kai, har yaji cewar ba zai kara yarda da shi ba har sai ya tabbatar da abinda yake zargi. Masu iya magana sunce shi laifi kuikuyo ne har abada yana bin mai shi, duk abinda mutum ke yi a boye komai daren dadewa sai asirinsa ya tonu, musamman abinda ya shafi cin amana da danne hakkin wani. Wata rana da tsakar dare sarki kusaidu na kwance a dakin uwar gidansa suna bacci, sai kawai wani dan mitsitsin tsuntsu ya shigo turakar ya tsaya a saman taga daidai saitin Zarifa yayi wani irin kuka tamkar yana raira waka. Koda jin wannan tsutsun sai Zarifa ta farka daga baccin da take yi kamar dama can idonta biyu ba baccin take yi ba, da mikewarta zaune sai ta dubi sarki Kusaidu ta tabbatar dda cewa bacci yake tunda gashi har yana sharar munshari, a hankali cikin sanda ta sakko daga saman gadon ta cire rigar baccin dake jikinta sannan ta saka tufafinta masu kyau ta nufi bakin kofa. Ashe sarki Kusaidu ba bacci yake ba, domin tun daga ranar da su Hantaru suka tafi birnin Darul Habur bai sake samun damar yin bacci daddare ba, sai dai kawai ya kwanta yayi lamo kamar mai yin baccin amman ba baccin yake iya wa ba, zuciyarsa cike da tunanin gami da begen dansa yarima Hantaru da kuma matarsa Salimat. Duk motsin da Zarifa ta ke yi yana jinta, kuma wani lokaci har bude idonsa yake yi kadan ya kalleta, da zarar yaga ta juyo sai yayi maza ya rufe idon nasa. Lokacin da Zarifa ta isa bakin kofar turakar, sai ta tsaya cak, ta juyo ta kura wa fuskar sarki Kusaidu idanu ta sake tabbatar da cewa bacci yake yi, sai da ta bata dakika sama da dari shida a kofr sannan daga bisani ta bude kofar a hankali ta fice daga cikin turakar gabadaya. A lokacin ne shima wannan mitsitsin tsuntsun da ya shigo wannan turakar ya fice da sauri, koda jin ficewar tsuntsun sai sarki kusaidu ya leka waje ta cikin taga, duk da cewa dare ne gari yayi duhu amman duk da haka sarki kusaidu ya samu damar hango wannan mitsitsin tsuntsun ta cikin ragowar hasken farin wata, lokacin da mitsitsin tsuntsun ya rikide ya zama wani aljani, bisa ga mamakinsa kuma sai yaga matarsa Zarifa ta haye bayan aljanin ya bude fuka fukansa ya tashi da ita sama, kafin kifta ido sun kule a sararin samaniya sun bace bat! Koda ganin wannan al'amari sai sarki kusaidu ya cika da tsananin mamaki, kuma hankalinsa ya dugunzuma ainun ya tambayi kansa a cikin zuciyarsa ya ce ina matata Zarifa ta tafi a cikin wannan dare, sannan wane ne ya turo wannan aljanin daya dauketa? Sarki Kusaidu ya kasa baiwa kansa amsar wadannan tambayoyi dan haka sai yayi shiru ya shiga sabon tunani, daga can sai yayi ajiyar zuciya ce hakika duk yadda aka yo matata Zarifa tana cin amanata ne, alhalin ni ina zaune da ita da zuciya daya, kuma ina kaunarta bilhakki, amman babu komai, koma mene ne take aikatawa a boye da sannu zan sani. Haka dai sarki Kusaidu ya koma ya kwanta ya ci gaba da tunanin su Hantaru da Salimat, bayan kamar rabin sa'a da kwnaciyarsa sai yaji an bude kofar an shigo, bai bude idanunsa ba, kuma bai yi wani motsi ba sai kawai ya ci gaba da kwarara munshari. A lokacin ne yaji an hawo gadon an kwanta, kamshin turaren data saba sakawa a jikinta ne ya sa ya gane matarsa ce Zarifa ta dawo. Nan take sarki Kusaidu yaji wani azabben bakin ciki ya shigeshi tamkar ya hadiyi zuciya ya mutu, amman sai ya danne zuciyar tasa ya hakura. Kashegari da safe sarki kusaidu bai nuna wa Zarifa wata damuwa ba, sai ma ya tashi da farin ciki yana mai cewa zarifa shi fa yau ya tashi da sha'awar fita rangadi. Koda jin haka sai Zarifa ta yi caraf ta ce aiko nima ina sha'awar fita rangadi sai mu fita tare kenan? Sarki Kusaidu ya dubeta cikin damuwa ya ce a'a gwara dai kiyi zamanki a gida domin wannan rangadin da zan fita ni kadai zan fita ba tare da dakaru ba, kuma zan iya yin nisan zango, kinga Kenan bani da tabbacin zan iya kare lafiyarki idan kika biyo ni. Cikin matukar mamaki Zarifa ta ce kai kuwa saboda me zaka fita rangadi kao kadai, shin ka mnta ne cewa kai sarki ne? Baka tsoron magauta su kawo maka hari? Sarki Kusaidu yayi dariya ya ce ai ni bana tsoron harin magauta domin na tabbatar da cewa ina tare da tsarin boka Ardusa, ke nake ji saboda baki da tsari irin nawa. Koda jin wannan batu sai Zarifa ta yi shiru bata kara tankawa ba. Ba tare da bata wani lokaci ba, sarki Kusaidu ayi shiri shi kadai, cikin batar da kammani ya fice daga cikin birnin Kisra. Sarki Kusaidu ya durfafi wata hanya da zata sadashi da wani kauye da ake kira da Raufal, daga cikin birnin Kisra zuwa kauyen Raufal tafiya ce ta rabin sa'a kacal, amman sai sarki ya zaburi dokinsa da sauri domin yana son ya isa kauyen cikin kakanin lokaci. Da isarsa kauyen kai tsaye ya wuce zuwa wajen wani bakon boka wanda bai wuce kwana uku da sauka a kauyen ana kiransa da suna Hulubul Auzar. Yau kwana biyu kenan rak da sarki Kusaidu ya samu labarin saukar boka Hulubul auzar, kuma ya samu labarin bokan ne a wajen wani amintaccen yaronsa da yake masa fatauci mai suna Ramzal. Ramzal ya tabbatar wa da sarki kusaidu cewa yaga bokan da ya fi boka Ardusa karfin sihiri, domin a gabansa boka Hulubul auzar ya warkr da wani mara lafiyya wanda ya shekara ashirin a kwance sakamakon wani asiri da aka yi masa, wanda yasa ya makance kuma ya kuturce, babu irin kokarin da boka Ardusa bai yi ba akan yaga cewa ya warkar da wannan mara lafiya amman ya kasa, sai ga shi a dare daya boka Hulubul auzar ya zo ya warkar da shi Lokacin da sarki Kusaidu ya iso kofar gidan da aka sauki boka Hulubul auzar sai ya iske bakan a tsaye ya zubo masa idanu fuskarsa cike da annuri. Tun kafin sarki Kusaidu ya karasa gareshi sai boka Hulubul auzar ya rugo da gudu izuwa ga sarki Kusaidu yana mai yi masa lale marhabun, kuma ya kama mashi dokin ya sauko, nan take suka shiga cikin gida suka kadaita a cikin wani daki. Har sarki Kusaidu ya bude baki zai ce wani abu sai boka Kusaidu ya tari numfashinsa ybace ya kai wannan sarki kada ka bata yawun bakinka wajen yi mani bayanin abinda ke tafe da kai, nasan kazo wajena ne domin nayi maka bincike bisa zargin da kake yi akan matarka Zarifa ko ba haka bane? Cikin tsananin mamaki sarki Kusaidu yace zancen ka dutse ya kai wannan boka mai daraja. Hulubul auzar ya dubi Sarki Kusaidu yace ya kai wannan arki mai daraja kayi sani cewa sau tari wadanda muka dauka a matsayin masoyanmu, kuma abokan shawararmu sune manyan abokan gabarmu masu son ganin bayanmu, mafi akasarin mutanen da muaka yi wa rana su kuma sai suyi mana dare, in mai bakin cikin sanar da kai cewa fiye da shekaru ashirin baya, boka Ardusa da matarka Zarifa suna cin amanarka ta hanyar lalata da junansu, kuma dan da matarka Salimat ta haifa Hantaru ba danka bane dan boka Ardusa ne da Zarifa. Ko da jin wannan batu sai sarki kusaidu ya dubi bokan cikin tsananin mamaki da rsahin gasgata zancen shi yace to amman ta yaya aka yi wannan abu ya faru haka? Maimakon boka Hulubul auzar ya bashi amsa sai kawai yayi nuni da hannunsa izuwa jikin bango, nan take hoton dukkan abunda ya faru tsakanin boka Ardusa da Zarifa ya bayyana akai, tun daga ranar da suka fara cin amanar shi kawo izuwa ranar da zarifa ta haifi Hantaru ta ajiye wa Salimat, yayin da Salimat ke nakudar sihiri wanda boka Ardusa ya sanya mata ba tare da ta sani ba. Koda ganin wannan al'amari sai sarki kusaidu ya fashe da kukan bakin ciki, yaji duniyar gaba daya ta yi masa zafi, kawai sai ya zabura ya zare wuka daga jikinsa ya daga sama zai burma a cikinsa, cikin hanzari boka Hulubul auzar ya rike hannunsa ya fisge wukar ya ce haba ya shugabana, ai idan ka kashe kanka makiyanka sun samu nasara akanka cikin ruwan sanyi, inason ka dauki dangana ka koma gida ka kuma cigaba da rayuwarka kamar yadda ka saba yi a kullum, sannan kada ka nuna wa zarifa sauyin komai, kada ka raba shimfida da ita, daga nan har izuwa ranar da amaryarka da kuma danka Hantaru zasu dawo gida, a sannan ne ido zai raina fata ayi maka ramuwar gayya, wacce tafi ta gayya ciwo. Kada kace zaia dauki wani mataki a yanzu akan Zarifa da Ardusa, domin ba zaka iya ganin bayansu ba, kuma idan ka matsa zasu kawar da kai ne su gaje mulkinka da dukiyarka a banza. Ko ni dinnan ban isa na kareka daga sharrin su ba. Ina mai tabbatar maka da cewa boka Ardusa ba karamin hatsabibi bane ni kaina ba zan iya da shi ba duk da cewa na fishi karfin sihiri. Alkawarin da zan maka shine zan cigaba da kare lafiyarka da kuma rufe sirrinka bazai taba sanin cewa ka san sirrin abinda yayi maka ba a yanzu har sai lokacin da Hantaru zai dawo gida. Tabbas Hantaru ne zai yi masu hukunci daidai da abinda suka aikata, domin har abada bazai taba karbar ba a matsayin iyaye, kuma ya tsanesu tamkar yadda ya tsani mutuwarsa. Daga wannan rana sarki Kusaidu ya cigaba da rayuwa mara dadi, ciwo kuma ya kara tsananta a jikinsa, kullum sai dai a kwantar a kuma tayar baya iya yiwa kansa komai, a duk sa'ad da boka ardusa yazo duba shi inya dubi fuskarsa sai yga kamar kura yake gani, ita kuwa Zarifa a duk sa'ad da tazo kusa da shi sai yaga kamar bakar macijiya ce take fasa kai zata sareshi, baban qbnida ya kara susuta sarki shine aminttatun bayinsa da ya tura zuwa birnin Darul Habur dan kai wasika ga matarsa Salimat tunda suka tafi basu dawowa ba har tsawon wata shida babu su babu duriyarsu. Al'amarin da ya kara jefa matsanancin ciwo kenan ga sarki Kusaidu, ya zamana cewar kullum fadawansa ma jira suke kawai ace rai yayi halinsa su san wanda zasu dora akan karagarsa. Babu abin takaici face kullum boka ardusa a turakar Sarki yake yini, shine mai nuna wa sarki kauna fiye da kowa, hatta masu baiwa sarki magani bai yarda da su ba, sai ya tabbatar da ingancin maganin sannan yake yarda a baiwa sarki maganin ya sha. Wannan hali da sarki Kusaidu ya shiga sai ya zamo tamkar samun dama a wajen Ardusa da Zarifa suka shagala da more rayuwarsu wajen cin amanarsa. A duk sa'ad da Zarifa ta bukaci boka Ardusa yayi bincike akan halin da Yarima Hantaru ke ciki sai ya kwantar mata da hankali yace ai yarima Hantaru yana nan lafiya lau, kuma zai dawo birnin Kisra a lokacin da sarki kusaidu zai mutu ya haye karagar mulkinsa. Lallai a wannan lokaci ne zamu sanar da yarima cewar mune iyayensa na gaskiya, kuma babu yadda zai yi dole ne ya karbemu a matsayin iyayen nasa, kuma ya girmamamu. Wannan kalamai na boka Ardusa ba karamin faranta wa Zarifa rai yake yi ba, sai kawai ta rungume boka Ardusa su ci gaba da sharholiyarsu. A zahirin gaskiya boka Ardusa yayi iyakar kokarinsa wajen gano halin da Hantaru yake ciki a cikin hallarar tsafi da mahaifiyarsa acan birnin darul habur amman abu ya gagara, duk sa'ad da ya matsa akan bincike sai madubin tsafinsa yayi bindiga ya tarwatse. Al'amarin daya dugunzuma hankalinsa kenan ya gane cewa lallai akwai wani babban bokan dake boye sirrin yarima acan birnin Darul Habur, abinda bai sani ba shine ba wani boka bnae face malaminsa a harkar bokanci wanda tuni ya dade d yin gaba har ma ya baiwa yan bayansa sirrinsa wato boka Sulbaini. Abinda boka Ardusa ya gano a cikin bincikensa kawai shine nan da shekaru uku masu zuwa yarina Hantaru zai dawo gida, wannan shine abinda yasa hankalinsa ya kwanta, ya amince da cewar zai cigaba da jiran dawowar yarima Hantaru. Kash! Hakika rashin sani yafi dare duhu, domin inda boka Ardusa yasan abinda zai biyo baya idan yarima hantaru ya dawo gida da ya kashe kansa saboda munin abin takaicin da zai samesu shi da farkarsa Zarifa. Acan kuwa birnin Darul Habur bayan kimanin wata daya da yin gasar neman auren gimbiya Larziyya, sai bangarorin biyu suka shiga shirye shirye gasar da za a yi nan da watanni goma sha daya masu zuwa, ya zamana cewa sun dage ainun dan ganin cewa idan lokaci yayi su samu nasara. Dare da rana kuma kullum Hantaru da Rabbasu cikin basu horo ake na kara wa jikinsu juriya da zafin nama gami da tsananin gudu, sai da takai cewa kowannensu na iya yin azabben gudu wanda a cikin rabin sa'a zai shafe tafiyar yini guda. Haka suka cigaba da baiwa jikinsu horo har tsawon wata goma sha daya, a tsawon wannan watanni tsakanin Hantaru da Rabbasu Babu wanda ya kara ganin fuskar gimbiya Larziyya saboda sarki ya sa an tsareta a gidan sarauta, babu wani mahalukin da ya isa yaje inda take, kuma itama bata isa taje ko ina ba. Da kyar da sidin goshi kuma a sirrance Gimbiya Larziyya ta samu damar aika wa da Sadauki Hantaru wasikar soayayya a cikin kwana talatin, duk sa'ad da wasikar ta riski Hantaru baya ganin komai a cikin takardar face kalaman kuka da bakin ciki bisa dalilin rashin saduwarsu, gami da baitocin waka na kara kaimi da kuma shawara kan lallai ya kara kaimi wajen ganin cewa ya samu nasara lashe wannan gasa da za'a yi ta neman aurenta a karo na biyu. Baya ga haka kuma a koyaushe tana yi masa tuni bisa alkawarin daya daukar mata guda uku, alkawari na farko; Shine komai rintsi ba zai janye ba, alƙawari na biyu kuwa shine duk alfarmar data nema a wajensa zai yi mata, alkawari na karshe wanda shine cikon na uku kuwa shine a duk halin da suka cintsi kansu a ciki ba zasu guji juna ba. Ko sau daya Hantaru bai taba saba wa aika wa da Gimbiya Larziyya amsar wasikarta ba, kuma a koyaushe yana kara tabbatar mata da cewa alkawarinsu yana nan babu abind zai tashe shi har abada. Sannu sannu bata hana zuwa sai dai a dade ba a je ba, hakika masu iya magana sunyi gaskiya da suka ce rana bata karya sai dai uwar diya ta ji kunya, a kwana a tashi sai ranar gasa karo na biyu ta dawo. Ai kuwa a wannan rana sai da hankalin gabadaya mutanen birnin Darul Habur ya dugunzuma saboda tsananin yawan al'ummar da suka cika wannan gari, tamkar mutane duniya ne suka hallara. A wannan rana anyi muguwar bakar gasa ta tashin hankali, wacce ta zamo sanadiyyar ajalin gaba daya dakarun gasar face na mutum biyu rak wato Hantaru da Rabbasu, suma din sai da kowannensu ya suma sau uku, kuma a karshe suka sake yin ragas kamar yadda al'amarin ya faru a gasar farko, wato a lokaci guda suka kama barewar gasa kuma suka tsinkata gida biyu. A wannan rana Sadauki Rabbasu kwana yayi yana kukan bakin ciki, haka dai ya rungumi kaddara bisa dole ya cigaba da hankoro zuwan Shekarar gaba. A takaice dai sai da aka yi gasa sau uku ba zakara sai ragas ake yi tsakanin Hantaru da Rabbasu, a ranar da akayi gasar ta uku ne shugaban alkalan gasar wato sarkin birnin Darul Habur wato mahaifin Gimbiya Larziyya ya yi bayanin cewa tunda dai wadannan zaratan jarumai sunyi ragas har sau uku akan gasar neman auren yarsa, to yanzu za suyi gasa ta karshe mai tsananin wahalar da ko dayansu yayi nasara ko kuma duk su biyun su hallaka, idan kuma suna ganin cewa b zasu iya yin gasar ba to sai dai duk su biyun su hakura da neman auren Gimbiya. Sarki yayi gyaran murya sannan ya cigaba da cewa ita dai wannan gasa ta karshe bata komai bace sai ta tafiya izuwa kogon mazabatul hirsham dake can karshen dajin hayatul Maut dan dauko takobin Saiful Lujara. Koda sarki ya zo nan a jawabinsa sai filin gasar ya rude da hayaniya da ka-ce-na-ce saboda sanin masifun dake dajin hayatul Maut. Dajin hayatul Maut yayi kaurin suna a ko ina a wannan zamani, domin dajine fiye da shekaru dubu da suka gabata babu wata halitta da ta taba shigarsa ta fito, duk abinda ya shiga cikinsa ya shiga kenan, har abada b za a sake jin duriyarsa ba, walau mutum ko aljan ko dabba ko tsuntsu, kai bama cikin dajin hayatul Maut ba, hatta gefen dajin ba a bi. Lokacin da filin gasar ya rudu da ka-ce-na-ce sai sarki yasa aka busa kaho kowa yayi tsit tamkar mutuwa ce ta gifta. A sannan ne sarki ya dubi Hantaru da Rabbasu wadanda ke duke a gabansa cikin mugun yanayi na galabaita mai kama da suma y ce Ya ku wadannan manyan zakuna ababan kwatance, kuyi sani d cewa daga yau har duniya ta nade ba za a manta da jaruntakarku ba, to amman fa ba zaku cika mazan jiya ba sai idan kunyi wannan gasa ta karshe, dayanku ya samu nasarar dauko takobin Saiful Lujara, shin kun amince zaku siyar da rayuwarku domin neman suna da neman auren yata? Koda jin wannan tambaya sai Sadauki Rabbasu yayi farat ya ce ya shugabana kayi sani cewa rayuwata bata da wani amfani muddin ban mallaki gimbiya Larziyya ba, kuma ban kare martabar zuri'ata ba ta mafarautan wannan Birni, saboda haka na amince na siyar da raina domin cikar burina da burin zuri'ata. Koda jin wannan batu sai jama'a suka sake barkewa da sowa, aka hau buga tambura da ganguna ana yiwa Rabbasu kirari da jinjina, sai da sarki yasa aka sake busa kaho sannan jama'a suka yi tsit a karo na biyu. Sarki ya dubi Sadauki Hantaru ya ce ya kai wannan namijin duniya ka ji abinda abokin gasarka ya fada, kai kuma me zaka iya cewa? Hnataru yayi ajiyar zuciya ya ce ya kai wannan sarki mai daraja, ka yi sani cewa a duniya babu wani abu mai daraja wanda yakai faranta rab masoyi, lallaı bani da masoyi wanda ya kai mahaifiyata da kuma abar begena Gimbiya Larziyya, mahaifinta bata da wani buri face ace yau kambun gasa ya dawo hannun zuri'arsu ta makeran wannan birnin, haka kuma masoyiyata bata da wani buri da ya fi ace yau nine zakaran gasar neman aurenta, bisa wannan dalilai dana wassafa na amince na sallama rayuwata domin faranta ran zuciyoyin wannan masoya nawa guda biyu. Koda jin haka sai jama'a suka sake barkewa da shewa gami da ihu, masu buga ganga nayi, masu busa algaita da tambura ma nayi. Sai da aka dan jima ana cashewa sannna aka busa kaho kow yayi shiru, saannan sarki yayi gyaran murya ya ce to jama'a kunji abinda zaratan jarumanmu suka fada, saboda haka kofa a bude take ga dukkanin jarumi wadanda suka ga zasu iya shiga wannan gasa wato su bi su Rabbasu izuwa dajin hayatul Maut dan shiga kogon Mazabatul Darshal a dauko takobin Saiful Lujara. Ko da mutum bai yi nasara ba, zai yi suna, idan kuma suna bai samu ba rayuwa zata salwanta, wanda duk yake ganin zai iya bin wadannan Sadaukai ya bayyana kansa yanzu. Koda gama fadin haka sai sarki yayi shiru ya kama kalle kalle yana mai duban gabas da yamma kuma kudu da arewa ko zaiga wani jarumin da zai fito ya kawo kansa, tsawon lokaci ba asamu mutum daya da ya fito ba. Ko da ganin haka sai sarki yace na sallami kowa da kowa, domin ta tabbata cewa wadannan zaratan jaruman guda biyu sune kadai zasu yi wannan tafiya, da wannan furuci nake sallamar kowa, sai kuma bayan kwana talatin zamu yi sallama da jarumanmu biyu domin su tafi dajin hayatul Maut, zamu ba jaruman mu adadin kwanaki arba'in wanda duk ya dawo daga dajin hayatul Maut dauke da takobin Saiful Lujara a cikin kwanaki arba'in din a cikinsu to shine zai zamo mijin ya ta gimbiya Larziyya, kuma ya cika namijin duniya Sarkin Sadaukai wanda har abada tarihin jarumtakarsa ba zata taba gushewa ba, kuma idan yaso zai iya mulkar duniya gabadayanta saboda sihirin dake jikin wannan takobi da ya mallaka ta Saiful Lujara. Koda jin wannan batu sai jama'a suka cika da tsananin al'ajabi kowa ma yaji inama zai iya saida rayuwarsa ya tafi neman wannan takobi. Nan dai mutane suka yita fadar albarkacin bakinsu, aka kwashi Hantaru da Rabbasu a matukar galabaice tamkar wadanda suka shekara suna jinyar cuta aka tafi da su gida, haka yasa taro ya watse kowa ya kama gabansa. A wannan karon ma Samilat ce ta yi jinyar Hantaru har tsawon kwanaki ashirin, sannan jikinsa y dawo daidai ya samu lafiya. A kullum dan Salimat ta dubi Hantaru ta tuna saura kwanaki kadan su rabu, Rabuwar da babu tabbacin su sake saduwa sai ta fashe da matsanancin kuka. Da kyar da sidin goshi Hantaru yake rarrashinta ya kuma bata baki sannan take daina kukan. A koyaushe Hantaru yana kara kara mata gwarin guiwa da cewa ya ke ummina kiyi sani cewa da zarar na dawo ne zamu koma can birnin Kisra tare da amarayata Gimbiya Larziyya ki sadu da mijinki, mu cigaba da sabuwar rayuwa, kuma a sannan ne zanyi wa boka Ardusa da mahaifiyata larifa hukunci da ya dace dasu bisa cin amanar mijinki da suka yi. A duk sa'ad da Hantaru yayi wannan furuci a gareta sai ta sake fashewa da kuka ta ce ya kai dana ka yi sani cewa har abada komi lalacewar iyaye, iyaye ne. Kada ka kuskura kace zaka hallaka Ardusa da Larifa bisa cin amanar d suka yi wa mijina, kai dai kawai ka tona masu asiri domin su zamo abin kwatance ga al'umma kuma darasi ga al'umma, ni dai bukatata a gareka ita ce, duk matsayin da ka kai a duniya kada ka gujeni, domin bani da wani face kai, duk da cewa banice na haifeka ba, ina jin a raina cewa ko a nan gaba bazan so dan da zan haifa kamar yadda na so ka ba. Ya kai Hantaru ka rike ni a matsayin uwa mahaifiya, kuma ka sani kamar yadda kowanne da ke son uwarsa, burina shine koda mai rabawa zata rabamu mu rabu da soyayyar juna. Yayin da Hantaru ya ji wannan batu sai ya rungumeta kuma ya fashe da kuka yana mai cewa har abada bazan gujeki ba yake ummina, kece uwata a zahiri, kuma kece uwata a badini. Kaico! Hakika kowa ya rasa masoyi yayi kuka, a duniya kaf babu abinda yafi farin ciki kamar samun masoyi, inda ace mutum na nan a lokacin da wadannan masoya suka rungume junansu sun kuka dan alhinin rabuwar da zasu yi nan bada daddewa ba, dole ne tausayinsu ya kmashi har ya zubar da hawaye, domin shakuwar dake tsakaninsu da sabo da juna ya wuce ayi misali face abinda zuciya ta kintata. A ranar da kwanaki talatin suka cika ne Hantaru ya gama shirya kayansa domin tafiya izuwa dajin hayatul Maut dan dauko takobin Saiful Lujara, lokacin da yazo yin bankawana da Salimat da kuma iyayenta, sai zuciyarsa ta karaya ya fashe da kuka ya kasa cewa komai a garesu, koda ganin haka sai duk su ukun suka fashe da kuka suma suka rungumeshi suna masu kankame shi a jikinsu tamkar ba zasu barshi yayi wannan tafiya ba. Kwatsam sai suka ji alamar motsin tafiya ana shigowa cikin gidan, cikin hanzari suka wauga suka yi arba da wanda ya shigo, ba kowa bane sai boka Sulbaini mahaifin Shuraim. Sulbaini ya tsaya cak yana kallon Hantaru shi kadai, a lokacin da idanunsa suka ciko da kwalla sannan sai ya dubi Salimat ya fara zubar da hawaye. Koda ganin haka sai Salimat da Hantaru suka ruga gareshi suka rungumeshi shi tare da fashewa da matsanancin kuka har zuwa lokaci mai dan tsawo, daga can sai Salimat ta janye jikinta daga nasa, suka fuskanci juna sosai sannan ta ce ya kai kakana mene ne dalilin da yasa kake kuka a yanzu, alhalin kaine ya kamata ka karfafi zukatanmu bisa wannan tafiya da dana zai yi. Sa'ad da Sulbaini ya ji wannan tambaya sai ya kama hannu Salimat ya jaya gefe guda inda babu wanda zai ji abinda zasu tattauna da ita, ya shiga yo mata wadansu bayanai, tunda ya fara bayanan Salimat ta fara kuka, aiko yana gamawa sai ta rushe da matsanancin kuka, kuma ta rungumeshi tana mai kankameshi a jikinta kamar wani zai kwace mata shi, da kyar Sulbaini ya cire jikinsa daga nata sannan ya taho gaba hantaru ya tsaya daf da shi har suna iya jin numfashin juna, Sulbaini yayi murmushi mai taushi ga Hantaru sannan ya ce ya kai namijin duniya kayi sani cewa nazo ne domin muyi bankwana, kuma nayi maka tuni bisa abinda na fada maka a baya idan baka manta ba, a ranar da kuka je gidana nayi maka gargadi akan kada ka kuskura Gimbiya Larziyya ta umarceka da yin abinda zai lalata alakar ka da jikita wata Salimat, bayan ka samu nasarar dauko takobin Saiful Lujara, idan ka kuskura ka aikata hakan tabbas zaka yi biyu babu a rayuwa, domin zaka rasa masoyanka kuma ka rasa daukakarka, har ya zamana cewa ka gwammace mutuwa da rayuwa, saboda haka ka kiyaye kuma kayi matukar nazari a duk lokacin da Gimbiya Larziyya ta zo maka da bukatarta. Lokacin da Hantaru ya ji wannan batu sai yayi murmushi yace kada ka damu ya shugabana, lallai zaka samenk mai kiyayewa bisa wannan shawara daka bani. Gama fadin haka keda wuya sai ga wani manzo yazo daga gidan sarki. Da zuwansa sai ya fadi gaban Shuraim ya ce ya shugabana sarki ne ya aikoni yace na sanar da kai cewa ana juran Hantaru a fada domin a sallamesu shida abokin tafiyarsa Rabbasu. Koda jin wannan batu sai Hantaru ayi wa mutanen gidan sallama karshe, ya kama doki ya hau ya tafi izuwa fada yana waugen su Salimat yana zubar da hawaye, suna zub da hawayen suma, masu daga masa hannu nayi haka dai har ya mace masu da gani. Lokacin da Hantaru ya isa fadar Sarki sai ya iske tuni Rabbasu na zaune a gefe daya cikin gagarumar shigar yaki yana muzurai tamkar zai ci babu, da zuwa sai Hantaru ya wuce gaban Sarki ya zube kasa ya kwashi gaisuwa, sannan ya koma gefe daya ya zauna shima, inda suka fuskanci juna shida Rabbasu. Koda suka hada ido sai Rabbasu ya daka wa Hantaru harara, wacce inda karamin jarumi yayi wa ita zai iya tsurewa ya kama gudawa, shi kuwa Hantaru sai yayi murmushi kawai ya kawar da kansa ga barin kallon Rabbasu. Ashe duk abinda ya faru sarki ya lura dan haka shima sai yayi murmushi ba tare da yace komai ba. Nan take sarki ya tura aka kira Gimbiya Larziyya ta zo ta zauna daf da sarki, a wannan lokaci fada ta cika taf da jama'a babu masaka tsinke face inda sarki da jam'arsa ke zaune. A wannan rana dai Gimbiya Larziyya ta ci ado na gaban kwatance irin wanda ba a taba ganinta da shi ba, kuma ta bar fuskarta a bude sabanin rufeta da take yiko gaishe. Wohoho! Lokacin da Gimbiya ta fito ta nufu inda karagar sarki ta ke tana yin tafiyar kasaita, sai ganadaya jama'ar dake fadar suka zuba mata idanu, kuma take suka dimauce saboda ganin tsananin kyawunta, da yawan jama'a basu san sa'adda yawu ya ka dalala da cikin bakinsu ba tamkar basu taba ganin gimbiya ba. Hatta Hantaru da Rabbasu ai da suka firgice suka bita da kallo, ko kifta ido basa yi, domin basu san cewa kyawunta ya wuce yadda duk suke zammani ba sai yau. Kai shi kanshi mahaifin nata binta yayi da kallo ya kama wasi-wasi a zuciyarsa yana mai cewa anya kuwa wannan Larziyyata ce, yaya aka yi naga kyawunta ya zarce na kullum a yau? Abinda sarki bai sani ba shine tsananin kwalliyar data yi ne gami da tsaba adon da ta yi, suka kara mata kyau na ban al'ajabi, domin idan kyau ya hadu da kyau sai idanuwa su kasa banbance wanda yafi wani. Bayan Gimbiya Larziyya ta zauna kan wata kujera ta alfarma wacce ke kusa da karagar sarki, sai sarki yasa hannu a cikin aljihunsa ya dauko wani dan karamin madubi na tsafi ya ajiyeshi a tskiyar fadar, sannan yayi gyaran murya ya ce ya ku jama'ar birnin Darul Habur, kuyi sani cewa ayau ne masoyan yata Gimbiya Larziyya wato masu neman aurenta, zasu yi gagarumar tafiya dan tabbar da gasa ta karshe a tsakaninsu, domin fitar da zakaran da zai zama mijin Gimbiya, kowa ya sani wannan gasa b komai bace face tafiya zuwa dajin hayatul Maut dan shiga kogon Mazabatul Darshal a dauko takobin Saiful Lujara. Duk wanda ya dauko wannan takobi ya zo da ita tsakanin Hantaru da Rabbasu shine mijin ya ta. Koda sarki yazo nan a zancensa sai fada ta rude da shewa, sai da sarki ya daga hannu aka yi tsit sannan ya dubi Hantaru da Rabbasu ya ce kunga wancan madubin tsafin dana ajiye a tsakiyar fada? Shine alkalin wannan gasa da xaku tafi, duk abinda zai faru a cikin wannan tafiya zamu gani a cikin wancan madubin saboda akwai dokoki da zamu shimfida maku a yayin wannan tafiya. Duk wanda ya karya doka daya daga cikin dokokin koda ya dauko takobin Saiful Lujara to ba zai auri Gimbiya ba, doka ta farko ita ce; Babu yaki a tsakaninku, wato ba a yarda dayanku ya cutar da dan uwansa ba. Doka ta biyu ba a yarda dayanku ya taimaki abokin tafiyarsa ba, abinda ake so shine kowa karfin damtsensa dana sihirinsa ya cece shi. Doka ta uku wacce ita ce ta karshe wanda duk ya samu nasarar dauko takobin Saiful Lujara, to kada ya tsaya ko ina face anan fadarmu. Da fatan zaku kiyaye wannan dokoki domin tabbatar da burinku, da wannan furuci nake maku bankwana da fatan samun nasara ga dukkan mai sa'a a cikinku. Koda gama wannan jawabi sai sarkk yasa aka kosassun dawakai kuma ingarmu guda biyu baki da fari, kowanne da guzuri akansa, ya dubi Hantaru da Rabbasu yace kowanne ya zabi wanda yake so. Cikin hanzari Rabbasu ya tashi tsaye yaje ya kama bakin dokin ya haye, shi kuwa Hantaru sai ya kama farin dokin ya haye. Nan take suka jera suna tafiya tamkar abokai suka nufi hanyar fita gari, jama'a na biye da su duu... Kamar kiyasai. Sai da aka raka su Hantaru har izuwa iyakar gari sannan aka tsaitsaya ana kallonsu suka kutsa kai cikin daji. Tun ana kallonsu har sai da suka kule suka bace bat! Hantaru da Rabbasu suka cigaba da tafiyya a jere suna ketawa ta cikin kwazazzabai da duwatsu, sai da suka yi tafiyyar sa'a shida cur dayansu bai ce d dan uwansa kala ba, sannan suka iso bakin wata korama. Anan ne fa dawakansu suka yi turjiya suka kama shan ruwa, saboda daman sun debo rana kuma sun gaji, su kansu su hantarun sun gaji kuma suna jin yunwa da kishin ruwa, amman saboda dakakkiyar zuciya irin ta mazan kwarai sai suka basar saboda kada suka cewa dayansu ya gaza. Lokacin da dawakan nasu suka tsaya a bakin gabar koramar suka kama shan ruwa, sai Hantaru da Rabbasu suka dubi juna, bisa ga mamaki sai suka yi wa juna murmushi. Rabbasu yayi gyaran murya ya ce ya kai abokin gaba ina ganin cewa ya kamata mu yada zango anan, domin mu huta kuma dawakanmu ma su huta, dan na lura cewa akwai gajiya a tare da mu. Hantaru yace kwarai kuwa ka zo da shawara mai kyau. Nan take duk su biyun sauka kayan su dake bisa dawakansu kowa ya kafa tantinsa, kuma suka bude jakar guzirinsu suka ci kuma suka sha. Bayan sun gama kimtsa cikin nasu ne sai kuma hira ta barke a tsakaninsu, inda Rabbasu ya dubi Hantaru yace ya kai bakon garinmu, kayi sani cewa ina da wata tambaya a gareka, wacce zan so ka bani amsarta bilhakki. Koda jin wannan batu sai Hantaru yayi murmushi sannan ya ce fadi duk irin tambayar dake bakinka ni kuma nayi alƙawarin zan baka amsa iyakar gaskiyata. Rabbasu yayi gyaran murya sannan ya ce ina son ka fada mani alakar dake tsakaninka da Salimat yar sarkin makera Shuraim, shin ita ce ta haifeka ko ba ita bace? Yayin da Hantaru yaji wannan tambaya sai ya cika da mamaki kuma yayi shiru kamar ba zai ce komai ba, sai ya ce alakata da Salimat itace ta shayar d ni, amman ba ita ce ta haifeni ba. Koda jin Wannan batu sai idanun Rabbasu suka zazzaro, kawai sai ya takarkare ya kwarara uban ihu cikin tsananin bakin ciki, ihun nasa ne ya firgita kananun dabbobin dake cikin dajin da tsuntsaye suka kama tashi da guje-guje wasu suna sauya ramuka, nan take kwallar takaici ta cika idanun Rabbasu ya dubi Hantaru yace hakika nayi babban kuskure da banyi cikakken bincike akanka ba, tun a farkon zuwanka garin nan, inda nasan cewa kai ba jinin zuri'ar makera bane da bazanyi wannan gasa d kai ba, da tuni na kashe kaina na da huta da takaici. Cikin tsakanin mamaki Hantaru ya dubi Rabbasu yace kai kuwa sabida me yasa ka fadi haka? Rabbasu yace saboda bincike ya tabbatar da cewa babu wani dan zuri'ar makera da ya isa ya samu nasara a kaina, duk da cewa har a yanzu baka samu nasara a kaina ba, in tsoron faruwar hakan a nan gaba, tunda kai ba zuri'ar jinin makera bane. Koda jin haka sai Hantaru ya bushe da dariya sannan ya ce ai kuwa babu makawa sai abinda kake tsoron faruwarsa ya faru, ina mai tabbatar maka da cewa nine zan karbi kambun wannan gasa ta neman auren Gimbiya Larziyya. Rabbasu shima ya bushe da dariya yana mai cewa ai Shikenan, muje zuwa mahaukaci ya hau kura, zanga ta yadda zaka lashe wannan gasa. Koda gama fadar haka sai Rabbasu yayi shiru bai sake cewa komai ba, shim Hantaru haka har dai suka gama hutawarsu suka cigaba da tafiya. Daman tun kafin su baro birnin Darul Habur an baiwa kowannensu zanen taswirar hanyar da zata kaisu zuwa kogon nan na Mazabatul Darshal, dan haka suna tafe suna duba wannan taswirar, haka dai su Hantaru suka wanzu suna masu keta dazuzzuka dare da rana wani lokacin ma basa kakkauta tafiya sai dai su kunna wutar icce su haska wa kansu hanya, wani lokacin kuma idan duhu ya kai duhu sai su hakura su yada zango. Duk inda tsautsayi yasa suka hadu da yan fashi ko muggan dabbobin daji, tofa komai yawansu cikin dakiku kadan suke ratattakasu su bi ta kansu, su kuma wuce tamkar anyi sassabe a gona, kai bama mutane da dabbobi ba, komai shedancin aljani da taurin kansa, da zarar ya hango Hantaru da Rabbasu sai kawai kaga ya ratse ya nemi maboya, domin yasan karo da shiryayyun maza irin su babu sa'a. Sai da su Hantaru suka shafe kwana goma sha tara suna ratsa dazuzzuka iri-iri sannan suka iso dajin hayatul Maut. Shi dai wannan daji na hayatul Maut ya fita da ban da kowanne irin dazuzzuka da suka saba gani. Tun a farkon dajin suka sha jinin jikinsu suka gane cewa sun shigo cikin bala'i da masifa wacce basu da tabbacin fita daga cikinta sai abinda hali yayi. Komai na cikin dajin ba irin wanda ido ya saba gani bane, gaba daya bishiyoyin dajin siffar dodanni garesu, su kuwa duwatsu suffar muggan dabbobi garesu, a cikin koramai kuwa sai suka rinka ganin aljani nata nukkaya da nutso, kai hatta ciyayin dake dajin hira suke da junansu, har ma suna yi wa junansu rada da zarar sunga su Hantaru sun matso daf da su. Koda ganin waɗannan abubuwa na ban tsoro, sai Hantaru da Rabbasu suka zare takubbansu suka ci gabada tafiya suna masu kallon gabas da yamma, kudu da arewa cikin nutsuwa domin suka ta inda za a fara kawo masu hari. Kwatsam ba zato ba tsammani sai sukaga wani aljani mai siffar guguwa ya taho a sama yanata kyakyata masu mahaukaciyar dariya mai kama da saukar aradu, hakika komai taurin kan mutum idan yaji wannan dariya dole ne ya razana, balle kuma idan yayi arba da aljanin wanda saboda matukar muninsa idan ka kalleshi zaka iya kama kumallo. Aljanin ya tsaya a cikin iska yana jale-jale kamar idan aka hureshi da iskar baki zai iya tarwatsewa, kawai sai ya dubi su Hantaru ya daka masu tsawa ya ce ku kanana kwari, wane tsautsayi ne yasa kuka siyar da rayukanku ku ka shigo wannan daji na hayatul Maut, shin baku da tarihin wannan daji ne? To ku sani cewa fiye da shekaru dubu duk halitar data shigo wannan daji ta ratso ta nan sunanta gawa, saboda mu tabbatar da tsaro ga takobin daraja ta Saiful Lujara. Lokacin da aljanin ya zo nan a zancensa sai Hantaru ya tari numfashinsa ya ce da shi Kai tsohon maketaci la'ananne, yau masu karya tasirinku sun zo, mukam mun shigo cikin wannan daji a raye cikin koshin lafiya, kuma sai mun fita a raye bayan mun dauke abinda kuka dade kuna gadi, wato takobin Saiful Lujara. Kafin Hantaru ya gama rufe bakinsa tuni Aljanin ya gabza masa wawan naushi a fuska, nan take hantaru ya sulale kasa sumamme, ya fado daga bisa dokinsa wata irin farar kumfa na fita daga bakinsa. Koda faruwar haka sai aljanin ya dubi Rabbasu ya daka masa tsawa ya ce Kai kuma maza ka kashe kanka ko kuma nayi maka abinda nayi wa dan uwanka. Rabbasu ya maida wa aljanin nan martanin tsawa ya ce karyarka ta sha karya dan haka ga maza nan bisa kanka, kawai sai Rabbasu ya tashi sama kamar tsuntsu ya bar bisa dokinsa ya afka wa aljanin yana mai kai mashi sara da suka cikin matukar zafin nama. Shikuwa aljanin sai yayi amfani da dan yatsansa guda daya jal a matsayin tasa takobin yana mai kare saran gami da mayar da martani, idan takobin Rabbasu ta hadu da dan yatsan aljanin nan sai kaga tartsatsin wuta na tashi, wata irin walkiya ta cika dajin baki daya, sai da suka jima a sama cikin iska suna wannan gumurzu dayansu bai samu nasarar koda kwarzanar jikin daya ba, al'amarin daya fusata aljanin kenan ya harzuka ainun, kawai sai aljanin ya rikide ya koma dan siriri kamar zare ya nannade jikin Rabbasu tun daga kafafunsa har zuwa kansa kawai sai ya shiga matseshi. Nan fa Rabbasu ya ji kamar za a rugurguza kasusuwan jikinsa gabadaya har bai san sa'ad da ya kurma uban ihu ba, sannan ya kama kumbura tamkar iska ake hura masa, nan fa shima aljanin ya fara rusa ihu domin shima ji yayi kamar Rabbasu zai tsinkashi gida biyu. Ba shiri aljanin ya rabu da jikin Rabbasu ya cilla izuwa can kololuwar sama tamkar daga cikin baka aka harba shi. Rabbasu ya daga kansa sama take ya zama haske ya bi aljanin da gudun tsiya, amman sai yaga ya kasa cimma wannan aljani domin karfin gudun aljanin yafi na tauraruwa mai jela. Ba zato ba tsammani sai aljanin ya sake rikidewa ya zamo wata irin masifaffiyar wuta mai tsananin zafi, ya juyo da baya suka kasa tsere da wannan haske, nan fa Rabbasu ya ji kamar daga cikin tafasasshen mai aka tsunduma shi, duk da cewa kuwa wutar ba ta taba jikinsa ba. Ba shiri Rabbasu shima ya rikide ya zama kankara, koda wutar da kankarar suka hadu sai duk su biyun suka rinka kururuwa wani irin sauti mara dadin ji ya dinga tashi, tamkar ana diga ruwa a cikin tafasasshen mai. Ba shiri duk su biyun suka rikito kasa kowa ya juye izuwa ainihin siffarsa. A daidai wannan lokaci ne aljanin ya shammaci Rabbasu ya narka masa dundu a gadon baya, take Rabbasu yaji tamkar kashin bayansa ya karye, kawai sai jiyayi yana kumallon wahala, shi kansa kumallon ji yayi kamar yan hanjin cikinsa zasu fito ta baki. Nan take ya baje a kasa sumamme, shi kuwa aljanin sai ya sauko kasa ya dira bisa turba yana mai kyakyata dariyar murna. Ba zato ba tsammani sai kawai yaji takobi ta tsargeshi gida biyu, tamkar yadda ake sa zabira a keta takarda, sai ga gangar jikin aljanin nan ta rabe gida biyu, ko wanne bangare ya fadi gefe daya. Ba wani bane yayi wannan aiki sai sadauki Hantaru, shi kansa sai kawai ya tsaya yana kallon takobin tasa yana mamakin yadda aka yi tayi wannan namijin aikin. Aljanin nan dai ko shurawa bai kara yi ba, Hantaru ya dubi Rabbasu wanda ke kwance magashiyan ko motsawa baya yi sai kawai ya kawar da kansa ya kama dokinsa ya haye ya cigaba da tafiya, yana mai tunanin cewa shikenan ya rabu da abokin tafiyarsa har abada, domin bai ga alamun zai iya rayuwa ba. Sai da Hantaru yayi tafiyar sa'a uku cur a cikin dajin hayatul Maut bai kara haduwa da wani mugun abu ba, kuma yana tafe yana duba taswirar hanya izuwa kogon Mazabatul Darshal. Kawai sai Hantaru yaga hanya ta bi dashi ta cikin kogon dutse mai tsananin tsawo da ba a iya hango karshensa, sannan da ya leka cikin kogon sai yaga mugun duhu ne da shi baya iya ganin komai, bisa dole hantaru ya sakko daga bisa dokinsa ya nemi icce ya kunna masa wuta, sannan ya sake hawa dokin nasa ya kunna kai cikin wannan kogo ba tare da fargabar komai ba tamkar yana shiga cikin gidansa. Shigarsa cikin kogon keda wuya sai yaga babu komai a ciki face kasusuwan bil'adama rututu a ko'ina, ta kai dokinsa yake bi yana takawa suna ruburbushewa, abinda ya daure wa Hantaru kai shine wanne irin mugun abu ne a cikin wannan kogo wanda ya hallaka miliyoyin rayukan bil'adama haka, ga dukkan alamu abun ya dade yana barna a cikin wannan kogo tsawon shekara guda shekaru, domin kasusuwan bil'adama dake wajen da yawansu sun gama bushewa, dan da zarar an takeau sai dai kaga suna ruburbushewa suna zama gari. Lokacin da Hantaru ya iso karshen kogon dutsen sai yaga a rufe yake ruf babu wata hanya ta fita, nan take ya fito da taswirarsa ya duba, kawai sai yaga hoton wata ƙatuwar rijiya a cikin kogon, kuma anyi nuni da cewa rijiyarce kan hanyar fita daga kogon, nan fa hantaru ya sakko daga kan dokiksa ya cigaba da haske haske da wutar iccen dake hannunsa, ai kuwa sai ya hango katuwar rijiya acan gefe daya koda ya hangota sai ya ruga da gudu izuwa inda rijiyar take, da zuwa wajen sai ya maida takobinsa a cikin kufenta kuma ya sakare wutar iccen a jikin bango, sannan yasa hannayensa biyu a bisa rijiyar da nufin budeta, nan fa Hantaru yaji kamar katon dutse yake son dauka. Al'amarin da ya dugunzuma hankalinsa kenan ya kara hade gabadaya karfinsa waje guda ya cigaba da kokarin daga marfin rijiyar amman sai abu ya gagara, domin ko motsawa ma marfin ma baiyi ba. Nan da nan Hantaru ya hada gumi yay sharkaf bisa dole ya yi tagumi ya koma waje daya ya shiga tunanin dabarar da ya kamata ya yi, yana cikin wannan hali ne yaji takun sawu ana shigowa cikin kogon, Hantaru ya mike tsaye zumbur yana mai zare takobinsa, sannan kuma ya dauko iccen wuta domin yaga mai shigowa. Ba zato ba tsammani sai kawai yaga ashe abokin tafiyarsa ne Sadauki Rabbasu, nan take Hantaru yaji farin ciki ya shige shi duk da cewa Rabbasu babban abokin gabarsa ne, amman ai ko ba komai tafiyarsa cikin wannan daji mai ban tsoro bata da dadi, gwara dai ace su biyun ne, dan haka sai ya ji yana murna da Rabbasu ya tsira da rayuwarsa. Yayin da Rabbasu yayi arba d Hantaru sai ya murtuke fuska tamkar yaga bakin kumurci kawai sai ya wuce cikin kogon ya kama haske haske yana mai duba taswirar hannunsa. Nan take ya gane wannan rijiya yake nema wato hanyar fita dag kogon, yace koda na fuskanci haka sai na koma gefe guda na zauna na zura masa idanu. Lokacin da Rabbasu yaga rijiyar sai ya sagale iccen wutar a jikin garu kamar yadda nayi sannan ya mayar da takobinsa cikin kube. Rabbasu ya tsaya akan rijiyar sannan yasa hannayensa biyu yayi amfani da dukkan karfinsa domin ya dauke murfin rijiyar, nan fa jijiyoyin jikinsa suka tashi suka yi birdin burdin, kwanjinsa suka kumbura, da kyar da sidin goshi ya daga murfin rijiyar kadan, amman sai murfin rijiyar ya rinjayeshi kasa dan haka dole ya sake shi. A wannan lokacin ne na tabbar da cewa indai batun tsagwaron karfin damtse ne to Rabbasu ya fini, tunda ni na kasa daga murfin rijiyar. Abinda kawai nake gani zan iya fin Rabbasu shine juriyar wahala, naci da kuma Sa'a. Rabbasu ya jaraba janye murfin daga bisa rijiyar amman sai abu ya gagara domin har saida ya jike sharkaf da zufa kamar yadda na yi a dazu, bisa dole Rabbasu ya hakura ya koma gefe shima ya zauna, duk su biyun sai suka zuba wa rijiyar idanu suna tunanin abinda zai ficcesu. Kwatsam sai muka ji wani irin gurnani na fitowa daga cikin rijiyar, tunda Hantaru yazo duniya bai taba jin gurnani irin wannan ba mai matukar ban tsoro, sannu a hankali gurnanin ya rinka karuwa ba shiri suka mike tsaye cikin razani suka ji kamar su ruga wajen kogon amman sai suka yi ta maza suka tsaya dan suka ko mene ne wannan abu dake cikin rijiyar. Kawai sai sukaga an naushi murfin rijiyar daga cikinta, take marfin yayi sama kamar anyi wurgi da faifai, ya fada can gefe daya, wani shirgegen dodo ne ya fito daga cikin rijiyar ya dira a gabansu. Koda kafafunsa suka taka kasa, sai gaba daya kogon ya kamar girgiza kamar zai ruguje, ni da Rabbasu sai muka zama yan mini-mini a gaban dodon nan kamar an ajiye yan tsaki a gaba muzuru, Hantaru da Rabbasu suka daga kawunansu sama suna kallon dodon nan cikin tsananin kaduwa da tsantsar al'ajabi jikinsu na kyarma. Gabadaya jikin dodon a murde yake kuma gashi da taurin gaske kamar dutse, yana da wani dogon kaho guda daya a tsakiyar kansa tamkar na dabbar karakanda, jelarsa kuwa murtukekeya ce mai tsawon gaske kamar ta kada, faratan yan yatsunsa kuwa zako-zako masu tsini da kaifin tsiya, koda Hantaru ya dubi dodon nan da kyau sai ya jinjina kai ya ce wannan zai iya halaka dakaru Miliyan dubu a lokaci guda, hakika yau mun gamu da gamonmu, dan abune mawuyaci mu fita daga nan. Koda dodon yayi arba da su Hantaru sai ya daga kafarsa ya shallakesu ya koma bangaren kofar da suka shigo ya tare hanya. Nan fa hantaru da Rabbasu suka dubi juna gami da yin ajiyar zuciya, duk da cewar a dokar wannan tafiya tasu, babu taimako juna amman yanzu ya zama masu dole su hada hannu domin yakar wannan dodo. Bayan anyi kallon kallo tsakanin dodon da su hantaru sai kawai dodon ya wangame bakinsa mai kama da rijiya ya bushe da mahaukaciyar dariya wacce ta kara furgitasu sannan yace ya ku wandannan kananan halittu, kuyi sani cewa yau kimanin shekara dubu kenan ina gadin wannan rijiya wacce ita ce hanyar da zaku bi domin ku shiga kogon Mazabatul Darshal, inda takobin daraja ta ke, duk mahalukin daya shigo wannan kogo walau mutum, aljan ko dabba to sai na zare masa ruhin numfashi, komai yawan ayarin dakaru muddin suka shigo to sunansu gawa, ku kuwa wanne tsautsayine ya shigo daku wannan daji, ko kuwa kuma kunzo ne domin daukar takobin daraja? Sa'ad da suka ji wannan tambaya sai Rabbasu yayi tsuru-tsuru ya kasa cewa komai, shi kuwa Hantaru sai yayi farat ya ce Ya kai wannan babbar halitta kayi sani cewa komai na duniya lokacine, tabbas ka yi sharafinka har tsawon shekaru dubu, to kayi sani cewa yanzu lokaci namu sharafin ne, a yau kuma a yanzu zamu halaka ka, sannan mu shiga cikin rijiyar nan mu wuce zuwa kogon Mazabatul Darshal mu dauko takobin Saiful Lujara. Koda Hantaru yazo nan a zancensa sai dodon ya sake bushewa da dariya a karo na biyu, wacce ta haddasa girgizar kogon gabadaya ya kama tambal-tambal, daga can sai ya tsuke bakinsa ya dubi Hantaru da kyau yace ai sai na gwada akan san na kwarai, mu zuba ni da ku asan gwani. Kafin daya daga cikinsu yayi wani yunkuri, tuni dodon ya kai masu wani wawan mangari, cikin zafin namq suka sunkuya hannun dodon ya bugin kogon, sai dutsen ya fara zubowa kasa, al'amarin daya firgita su hantaru kenan suka fara amfani da karfin sihiri, domin su hallaka dodon amman si sihirin nasu ya ki aiki, nan fa suka kasa tsere da dodon yana kai masu duka, mangari da kuma taku da hannu da kafa, duk inda kafar dodon ya taka sai ya haifar da rami zururu wanda zurfinsa ya kai kamu arba'in, fadinsa kuwa yana kai kamu ashirin, nan fa Hantaru da Rabbasu suka kama tsalle-tsalle a haka dai suka samu daman naushin fuskar dodo, amman duk sa'adda suka naushe shi sai suji kamar dutse suka nausa domin hannunsu ma sagewa yake, kafin a jima Hantaru da Rabbasu sun fara gajiya da galabaita, shiko dodon ko alamar fara gajiya bai yi ba tamkar ma kara masu kuzari ake. Ana cikin haka ne dodon ya samu nasarar damkar wuyan Rabbasu da yan yatsunsa biyu, nan fa Rabbasu ya hau reto da wutsil-wutsil, nan fa idanun Rabbasu suka zazzaro suka yi bulu-bulu ya fara kokarin cire yan yatsun dodon daga wuyansa amman sai ya kasa. A wannan lokacin Hantaru ya ruga izuwa can saman dodon ya hau kan kafadarsa ya dinga gabza masa sara da takobi a fuska, amman shi dodon ko kulashi bai yi ba domin ji yake tamkar susa yake mashi. Lokacin da Rabbasu yaji zahiri numfashinsa ya fara daukewa, ya tabbatar da cewa mutuwa zai yi, sai ya tattaro dukkan karfinsa ya kama dan yatsa daya na dodon ya finciko shi, nan take dan yatsan ya fice fit daga jikin hannun, aikuwa sai jini ya fara bulbula. Dodon ya kurma uban ihu ba shiri Rabbasu ya fado kasa. Hakika idan mutum yaga mutuwa babu abinda ba zai iya ba, Hantaru bai taba tsammanin cewa Rabbasu zai iya ceton rayuwarsu ba daga hannun wannan dodon, a wannan lokacin ne Hantaru ya dada sallamawa Rabbasu, ya tabbar da cewa ya cika Sadauki uban sadaukai. Yayin da dodon ya dubi dan yatsansa ya ga jini na shatata a jikin hannun nasa, sai ya haukace ya cigaba da kai masu duka da mangari ta ko ina, haka ya rika makesu suna gwaruwa da jikin bangon kogon, cikin kankanin lokaci Hantaru da Rabbasu suka galabaita ainun suka fita daga cikin hayyacinsu, har ya zamana cewa babu mai sauran kuzari a jikinsu, sai da dodon ya tabbatar da cewa yayi masu laga-laga sai ya sunkuya ya suri Hantaru yayi sama da shi da nufin ya soka kanshi a cikin bakinsa, cikin matukar zafin nama Rabbasu ya dauki takobinsa ya dagata sama tamkar an cillashi daga sama, kafin dodon ya soka Hantaru a cikin bakinsa tuni Rabbasu ya fada cikin bakin nasa, cikin tsananin zafin nama ya zarce zuwa cikinsa yasa wukarsa ya fara daddatsa hanjin cikinsa. A karshe sai ga shi ya faso ta duburarsa, kawai sai Hantaru yaga dodon ya kame wuyansa ya kame ya sake shi ya fadi kasa, yan dakiku kadan dodon yayi kasa tim! Hantaru dai bai san sa'ad da yayi wa Rabbasu jinjina ba, yace tabbas ka cika Sadauki uban sadaukai na sallama maka. Koda jin haka sai Rabbasu yayi wurgi da takobinsa, ya dubi Hantaru har kwalla ta zubo masa, yayi shiru bai ce komai ba. Al'amarin daya sa Hantaru ya dubeshi ya ce da shi ya kai abokin tafiya ina dalilin zubar wannan hawaye naka? Rabbasu ya koma gefe daya ya zauna yana haki bai ce komai ba, daga can sai ya dago kai ya ce ya kai namijin duniya kayi sani cewa bayan ka baro ni a baya a inda muka fafata yaki nan,sai da na jima a kwance kamar gawa sananne n dawo cikin hayyacina. Ina farfadowa sai na nemeka na rasa, sai kawai gawar aljanin nan na gani ta rabe gida biyu. Nan take na raina jarumtakata, kuma naji zuciyata ta buga da karfi, tsoro ya shigeni kuma na fara tunanin cewa abu ne mawuyaci na tsira da rayuwata a wannan daji na hayatul Maut. Domin na samu nutsuwa sai na dauki madubin tsafina na shiga binceke, koda naga abinda binceken nawa ya nuna mani sai na fashe da kuka, ba komai na gani ba face bani da sa'a ko kadan a cikin wannan gasa, kaine da sa'a kuma tabbas kai zaka karbi kambun wannan gasa. Cikin bincekena na gano cewa ba zan tsira da rayuwata ba a cikin wannan daji, kuma a yanzu haka mahaifina sarkin mafarauta na can a kwance cikin ciwo, haka ma kakan Salimat duk su biyun ba zasu rayuwa ba mutuwa zasu yi nan da yan kwanaki kadan masu zuwa, kaga kenan ni yanzu babu abinda zan tsira da shi a rayuwata, na rasa ubana kuma na rasa masoyiyata Gimbiya Larziyya, wacce tun muna yara kanana na kamu da tsananin kaunarta, amman sai ya zamana cewa ta tsaneni kamar yadda ta tsani mutuwarta, akan haka ne na sha alwashin sai na aureta ta kowanne hali. Ya kai wannan jarumi ka yi sani cewa tun da kuruciyata nake ta shiryeyen wannan gasa, nayita baiwa kaina horon yaki, tseren gudu da shanye horon duka, har izuwa lokacin dana cika saurayi. Yau gashi na wayi gari duk wannan tanadi da nayi ta zamo a banza, soyayyata ta kaini izuwa ga halaka, tabbas yanzu na yarda cewa kaine zaka zamo mijin gimbiya Larziyya dan haka ina mai kara kara maka gwiywa akan ka dada jajircewa wajen karasawa cikin kogon Mazabatul Darshal ka dauko takobin Saiful Lujara, ni kam tafiyata ta kare anan domin nayi nadamar zurfafawa a soyayya gashi kuma soyayya ta kaini ta baroni. Ya kai abokin tafiya kaima ina mai baka shawara da ka taka a hankali domin su mata da kake ganinsu suna da matsari, da wannan furuci nawa nake maka sallamar karshe gami da fatan samun nasara bisa abinda ka sa a gabanka. Koda gama fadin haka sai Rabbasu ya yunkura cikin zafin nama, ya kama kansa da hannayensa biyu ya murde wuyansa, nan take kuwa ya fadi kasa matacce. Cikin tsananin bakin ciki Hantaru ya ruga gareshi ya rungume gawarshi ya fashe da matsanancin kuka, duk da cewa Hantaru ya san cewa Rabbasu abokin gabarsa ne, amman sai yaji cewa kamar dan uwansa ne na jini ya mutu. Nan take hantaru yaji komai na duniya ya fice daga ransa, ya fara tunanin ya koma da baya ya hakura da dauko takobin Saiful Lujara. Sai da Hantaru ya shafe fiye da sa'a guda rungume da gawar Rabbasu yna ta shara kuka, sannan ya mike ya haka rami a wajen ya binne gawar Rabbasu, sannan ya rubuta sunansa da jinin dan yatsan sa a jikin duwatsun da ya rufe kabarin. Hantaru ya zauna a gaban kabarin ya shiga raira baitocin waka, da nuna jinjina da kirari ga sadauki Rabbasu, yana wakar yana zubar da hawaye har izuwa lokaci mai tsawo sannan ya mike tsaye ya tafi izuwa cikin wannan rijiya yana mai waigen kabarin Rabbasu yana cigaba da hawaye a haka har ya shige cikin rijiyar. Da shigar Hantaru cikin rijiyar sai kawai ya tsinci kansa a cikin wani makeken kogon dutse, wanda yafi wanda ya baro girma, tsawo da fadi sau uku, a cikin kogon akwai rijiyoyi guda dubu kowacce rijiya rufe take ruf da makulli, nan fa Hantaru ya kura wa rijiyoyin idanu yana ayyanawa a ransa cewa lallai takobin Saiful Lujara na cikin daya daga cikin wadannan rijiyoyi, abin tambaya anan shine a cikin wace rijiya takobin take? Kawai sai Hantaru ya yanke shawarar bude rijiyoyin daya bayan daya, nan take ya tunkari rijiyar farko gadan-gadan. Kaico! Rashin sani ya fi dare duhu, hakika inda hantaru yasan abinda zai biyo baya da ya hakura da bude wannan rijiya ta farko. Lokacin da Hantaru yasa takobinsa ya sare kwadon dake jikin wannan rijiya ta farko sai kawai yaga wata mutukekiyar macijiya ta taso sama, macijiyar na da kawuna saba'in da daya, girman ko wane kai daya ya kai na katuwar bishiyar kuka. Kafin hantaru yayi wani yunkuri tuni kawunan macijiyar nan guda saba'in da daya sun fasa kai sun gabza masa sara a sassan jikinsa ko ina da ina. Nan take wani irin dafi ya shige shi, jikinsa ya kama kakkarwa, kafin a jima ya jike sharkaf da zufa tamkar an tsamoshi daga cikin kogi. Hantaru ya sulale kasa magashiyyan kuma jikinsa ya cigaba da kakkarwa kuma ya fara kakarin mutuwa lokacin da wata irin kumfa ta fara dalala daga cikin bakinsa. Duk wannan abu dake faruwa macijiyar na tsaye akansa, ta zubo dukkan kawunan nasa a kansa, tana kallonsa kawai kamar jira take ya mutu ta cinye shi. Daga can sai ya sandare ya daina motsi, sannan ne macijiyar ta kara sakkowa da kanta kas da niyyar ta hadiye Hantaru. Ba zato ba tsammani sai kawai macijiyar taga numfashin Hantaru ya dawo, nan take ya amayar da duk wani dafi data saka mashi, wanda ya kasance bakikkirin kamar an jika shuni. Cikin zafin nama macijiyar nan ta wangane bakinta gabadaya dan ta hadiye Hantaru, amman sai ya rikede ya zama katon dutse, duk da haka sai da macijiyar ta hadiye dutsen. Koda sarki Dujalu ya zo daidai nan a labarin da yake baiwa yar uwarsa Gimbiya Hursiyya sai ya fuskanci cewar dare ya raba sosai, dan haka ya kamata su kwanta suyi bacci, amman bisa mamaki sai yaga idanun Hursiyya a kafe babu alamar jin bacci a cikinsu. Sarki Dujalu yayi shiru ya kafa mata idanu kawai yana murmushi. Gimbiya Hursiyya ta dubeshi cikin matukar damuwa ta ce haba ya kai dn uwana, sabida me zaka katse mani wannan labari, na rokeka dan girman iyayenmu daka karasa mani wannan labari domin naji yadda sadauki Hantaru yake dauko takobin Saiful Lujara, kuma naji yadda zai auri gimbiya Larziyya, sannan na ji yadda karshen rayuwarsa zata kasance a tafarkin soyayya. Haka kuma ina son jin yadda rayuwar sarki Kusaidu zata kasance da boka Ardusa, da Zarifa ma'abota cin amana. Lokacin da sarki Dujalu ya ji haka sai ya bushe da dariya ya ce yake yar uwata kiyi sani cewa a halin yanzu dare ya raba sosai, idan har zan cigaba da baki wannan labari har gari ya waye ba zai kare ba, zai fi kyau kiyi hakuri sai wani lokaci idan mun sake yada zango a wani wurin sai mu cigaba. Alkawarin da zan yi maki shine zanyi kokari na gama baki labarin sadauki Hantaru sannan mu shiga labarin Sadauki shaddar na birnin Kufa, wanda yama fi labarin Hantaru ban tausayi da ban al'ajabi. Cikin mamaki Hursiyya ta ce haba ya dan uwana ya za ayi a samu labarin da ya fi na Sadauki Hantaru ban tausayi da ban al'ajabi, ka sani cewa tunda ka fara wannan labari nake zubar da hawaye har ka tsaya ban daina ba. Sarki Dujalu yayi murmushi yace aikuwa idan kika ji labarin Sadauki Shaddadu sai hawayen idanunki ya kare saboda zuba. Yanzu sai ki tashi ki tafi izuwa cikin tantinki na sallameki. Cikin sanyin jiki Hursiyya ta mike tsaye ta fita daga cikin tantin sarki Dujalu, shi kuwa sai ya kwanta bisa shimfida ya mike kafafunsa ya kama aikin rago. Me zai faru idan rundunar mayaka ta sarki Maharaz da ta sarki Dujalu suka hadu a bakin gabar tekun Bahar Suffiyya dan dauko takobin Saiful Lujara? Waye zai samu nasarar mallakar makaman yaki guda uku, na mazan jiya? Ta yaya Sadauki Hantaru zai dauko takobin daraja a kogon Mazabatul Darshal? Wadanne irin abubuwan al'ajabi dana ban tausayi, da kuma jarumtaka ne a cikin labarin Sadauki Shaddadu na birnin Kufa da Sadauki Hulkas na birnin Romaniya? Marubucin yace mu hadu a Littafin mazan jiya Littafi na biyu.