[3/15, 10:21 AM] Meerah 💞: 🤴🏻🤴🏻🤴🏻 prince khamal🤴🏻🤴🏻🤴🏻 🌹🌹🌹🌹🌹🌹 By 🌹🌹🌹 Meerah💞 🌹 Also known as 🌹 Samira Ayuba🥰🥰 Wannan page na sadaukar dashi gareki my lovely daughter ****Ihsan****** Allah yarayamin ke bisa tafarki madai daici. Dasunan Allah mairahama Mai jinkai 🅿️ 1️⃣_2️⃣ "Khamal kaunarka acikin jinin jikina take bazan iya rabuwa dakai ba, khamal kada kamanta dani arayuwarka zanyi zaman jiranka har kadawo gareni" Hawayen dake gudana afuskarta ta share tare da dauko wata leda acikin jakarta ta mika masa. "Ka karbi wannan Ina maka fatan alkhairi", bata jira jinta bakin saba tashige motarta tayi gaba Kasa cewa komai yayi saibin motarta da kallo wani irin kunci yakeji acikin ransa, tabbas wannan itace Rana mafi muni arayuwarsa, zancen zuci yakeyi yakasa Koda dogon motsi awajen, inama mutuwa ta riskeshi kafin wannan rana. Hawayen dake gudana a lallausar fuskarsa yashare tareda duban ledar da Afra tabashi nantake wasu zafafan hawaye suka gangaro afuskarsa, tareda murmushi Wanda hausawa kecewa yafi kuka ciwo, A hankali yafara daga kafarsa Yana tafiya kamar Wanda kwai yafashema aciki, tafiya yakeyi batare da yasan inda yadosa ba. Kai tsaye Tasha ya nufa, motar da yagani kusa dashi yashiga batare da yasan inda motar tanufa ba. Tafiya sukeyi acikin mota kowa da tunaninsa khamal dai hawaye kawai yake sharewa, a haka har aka isa garin Zaria, fitowa yayi yafara tafiya, kallo daya zakayi masa kasan yanacikin matsananciyar damuwa. Yayi yawo sosai acikin garin harya gaji datafiya, baisan inda zashiba baisan kowaba arayuwarsa sai iyayensa dasauran Yan kauyensu da wadanda sukayi karatu tare sai Kuma Afra wadda tazama wani yanki acikin rayuwarsa Marece yayi sosai kowa da sabgar gabanshi saidai akwai wani bakon al amari daya daurewa Kamal Kai shigowarsa wannan gari sbd duk Wanda yagani ahanya saikaji anakiransa da ranka yadade, wasuma harda sunkuyarda da Kai sukeyi alamar girmamawa wannan abu yana bashi mamaki sosai tunani yakeyi kodai al adar garince ahaka, da wannan tunanin yabar zancen. A wata inuwace yayada zango duk da sanyin marece dake kadawa baihanashi gumiba sbd tsabar tashin hankalinda yake ciki, yadade awajen domin har sallar isha'i ma dayaje masallaci yadawo anan yakara zama, yunwa ke addabarsa gashi bashida kudi, Wanda yarage masa sukenan yabiya kudin motar daya shiga. Aza kansa yayi bisa kunshin kayansa ya kishin gida, a haka bacci barawo yadaukesa Kamar amafarki yaji ana tabashi, firgigit yatashi tsorace ganin wani dattijo zaune kusa dashi yakara tsora tashi batun mikewa yakeyi dattijon ya riko hannun sa yace "ranka yadade..... By meerah 💞 [3/15, 10:22 AM] Meerah 💞: 🤴🏻🤴🏻🤴🏻prince khamal🤴🏻🤴🏻🤴🏻 🌹🌹🌹🌹🌹 By 🌹🌹🌹 Meerat💞 🌹Also known as 🌹 Samira Ayuba🥰🥰 08068971503 Na sadaukar da wannan page gareki mahaifiyata Allah yakara Miki lfy da nisan kwana💘💘 Da sunan Allah Mai rahama mai jinkai 🅿️ 3️⃣_4️⃣ Batun mikewa yakeyi dattijon yariko hannunsa yace: "Ranka yadade kazauna zamuyi mgn" Zama yayi, duk da cewa baya son ganin kowa akusa dashi, amma zaiso wannan dattijon ya taimaka masa Koda da abinda zaicine.... "Ranka yadade kozaka iya gayamin sunanka, Da Kuma labarinka" Kallonsa khamal yayi, tare da daure fuska, ya kauda kansa gefe, kamar bazaiyi mgn ba, dattijon harya fitar da rai dajin amsarsa, da kyar yabude baki yace "sunana khamal Amma abokaina sunfi kirana da 🤴 khamal" Gyada Kai dattijon yayi, yace "awane gari kake, Kuma a Ina iyayenka suke, dannaga da alamar Kai bakone agarin, Kuma ga dukkan alamu kana cikin damuwa, domin tunda kazo wajennan nake lura dakai" "Banida iyaye" yafada cikin kosawa da maganar. "Ranka yadade dare yayi , kataso muje gidana idan kaso gobe saikaje inda kakeso" "A'a bazan jeba, kabarni anan zanfi jindadin hakan"... "Karka damu dana bazan takurama da surutu ba, danna ga alamar bakason yawan mgn, kataso muje kaci abinci" Yafada Yana mikewa tare da daukar kunshin kayan khamal.... Binsa yayi abaya batare da yace komai ba Dan koba komai zaisamu yaci abinci, da wurin kwana.... Washe gari misalin karfe 9:00am khamal yafito daga cikin dakin daya kwan, da kunshin kayansa. Zaune yaga dattijon atsakiyar gidan, yace: "baba nizan tafi, nagode kwarai da taimakon da kayimin Allah yasaka da alkhairi" Mikewa tsaye dattijon yayi cike da mamaki, yace "yaro ina zakaje haka da safennan, ko kanada Yan uwa agarinnan ne"? "A'a baba bansan kowa ba a garinnan saikai, bazan iya zama anan ba sbd banason nadaura maka wani nauyi akanka" "A'a khamal bazan barka katafi ba harsai nasan ko Kai wanene idan da hali saina taimaka maka" Kallonsa khamal yayi sbd shi arayuwarsa Babu abinda ya tsana kamar lbrn rayuwarsa domin cike yake ban haushi, ko kadan khamal bazai taba bawa wani lbrnsa ba sbd shi kansa da abin ya faru akansa haushin kansa yakeji, balle kuma wani yasanda wannan mummunan lbrn ai tsabar sa kawai zaayi.... "Kamar yadda na fadama abaya banida iyaye, ni shegene dan tsintuwa ne, bansan kowaba, ahaka nataso harna girma" "Su waye suka reneka harka girma kasan ciwon kanka"? Gabansa ne yayi mugun faduwa, sbd shi ko amafarki baya fatan sake jin lbrn rayuwar da yayi tare dasu, cikin ransa yake furta natsaneku natsaku, inna laure Allah ya isa tsakanina dake.... Hawayen da suka gangaro masa ya share, yace: "sun rasu........ 🤔 "Allah yaji kansu yayi musu rahama, ka kwantar da hankalinka ranka yadade kaiba shege bane, Kai dane, dan sunnah kamar kowa, karka Kara Kiran kanka da shege" Zaro idanu yayi Yana kallon dattijon "bangane abinda kake fada ba, taya zakace niba shege bane bayan tsinta ta akayi acikin daji" Murmushi yayi tare da dafa kafadarsa yace "iyayenka anan garin suke Kai babban mutum ne ranka yadade, duk Wanda ya ganka yasan Kai jinin Mai martaba ne sarkin garinnan, sarki Ahmada Abdus-salam"........ By Meerat 💞 [3/15, 10:22 AM] Meerah 💞: 🤴🏻🤴🏻🤴🏻prince khamal🤴🏻🤴🏻🤴🏻 🌹🌹🌹🌹🌹 By 🌹🌹🌹 Meerat💞 🌹Also known as 🌹 Samira Ayuba🥰🥰 🌹🌹ELEGANT ONLINE WRITER'S✍️✍️✍️ (EOW)💘💘 Na Sadaukar da wannan littafi gareku masoyana Ina alfahari daku 💘💘💘 Da sunan Allah Mai rahama mai jinkai 🅿️ 5️⃣_6️⃣ "Iyayenka anan garin suke Kai babban mutum ne ranka yadade, duk Wanda yaganka yasan Kai jinin Mai martaba ne sarkin garinnan, sarki Ahmad Abdus-salam" Kallonsa khamal yakeyi ko kiftawa bayayi, farincikine fall aransa, Amma azahiri sai yace "baba dama iyayena suna raye shine suka yaddani adaji" wasu zafafan hawaye ne suka gangaro a lallausar fuskarsa. Hannu baba yasa yashare masa hawaye ya dafa kafadarsa yace "ba yaddaka sukayiba khamalu sace ka akayi, kazauna danna baka labarin zuwana masaurata" Zama yayi cike da sonjin lbrn da baba zai bashi game da iyayensa...... Kallonsa baba yayi sannan yafara da cewa "Ni sunana sanusi haifaffen garin zamfara ne muna rayuwa ne awani kauye dake cikin yankin zamfara, iyayena marasa karfine sosai muna Shan wahala sosai a kauyenmu, domin abincima ga gararmu yakeyi wani lkc, wannan dalilin ne yasa iyayena suka yanke shawarar dawowa nan garin Zaria wajen abokin mahaifina domin yasama mana irin aikin daya keyi agidan saurata, munzo cikin nasara kuwa inda aka dauki mahaifina aikin gadi nikuma da ban wuce shekara 10 ba akasani aikin bawa shukoki ruwa, ita Kuma mahaifiyata agida tazauna domin mahaifina yace bazatayi aikin bautaba" Kallon khamal yayi yace "kaji dalilin zuwana wannan garin" Khamal kallonsa kawai yakeyi batare da yace komai ba. "Haka mukaci gaba da aiki agidan sarauta harna kai shekara 25 cikin wannan shekarar ce nayi aure na auri Khadija Yar jakadiya wadda kewa matar sarki hidima, ahaka mukaci gaba da rayuwa acikin gidan"... Bayan wasu shekaru Mai martaba sarki Ahmad Abdus-salam ya Kara aure, sbd yasamu haihuwa domin shekararsu goma da hajiya Fulani Amma Allah baibasu haihuwa ba. Ya auri hajiya Nafisa Yar babban attajirine acikin garin Zaria, anan Mai martaba ya bada umarnin abawa mamata Khadija jakadancin hajiya Nafisa sbd yabawa da halayenta nakirki, a duk masarautar babu baiwarda takaita rikon gaskiya da amana, Bayan shekara daya da auren Mai martaba da hajiya Nafisa Allah yabasu haihuwar da namiji, Mai martaba yayi farinciki da wannan haihuwar sosai domin anyi shagali sosai aranar haihuwar, Mai martaba yayi kyauta wadda bata misaltuwa adalilin haihuwar 🤴🏻prince Yazeed, saidai kash...... a Daren ranarda aka haifi prince Yazeed a wannan ranar aka sace shi 😭😭😭" Kuka ne yaci karfin baba sanusi Wanda ya hanashi ida lbrn......😭😭😭 Nima anan zan dakata harna share hawaye na sbd batan yarima Yazeed 😭😭😭😭😭 By Meerat 💞 [3/15, 10:22 AM] Meerah 💞: 🤴🏻🤴🏻🤴🏻prince khamal🤴🏻🤴🏻🤴🏻 🌹🌹🌹🌹🌹🌹 By 💞meerah💞💞 🌹 Samira Ayuba🌹🌹 08068971503 🌹🌹 ELEGANT ONLINE WRITER'S✍️✍️✍️ Sadaukarwa gare ku masoyana Ina alfahari daku💘💘💘💘💘💘 Da sunan Allah Mai rahama mai jinkai 🅿️. 7️⃣_8️⃣ Hawayen dake gudana a fuskar sa ya share, kallon baba sanusi yayi yace "meya faru bayan batan prince Yazeed"... "A Daren ranar bawan da yayi bacci acikin masarautar sbd tsabar firgici da tashin hankali, Mai martaba sarki Ahmad Abdus-salam yayi Suma fiye da goma kafin gari ya waye 😭😭😭 likitoci sundade akansa kafin asamu yadawo hayyacin sa. Haka itama gimbiya Nafisa tayi jinya sosai a dalilin batan prince Yazeed. Gimbiya Fulani itama tayi kuka kamar ranta yafita ganin tana gab da rasa mijinta abin alfaharin ta a dalilin batan yarima Yazeed..... Bayan Mai martaba yasamu sauki har yadawo gida, yabada umarnin a daure matata Khadija, wadda itace jakadiya ga gimbiya Nafisa Kuma itace ke tare da prince Yazeed har lokacin da aka saceshi, wannan dalilin ne yasa Mai martaba ya bada umarnin daureta harsai dansa ya bayyana..... Bayan daure Khadija Nima na fuskanci hukunci Mai tsanani awajen Mai martaba, nayi watanni a daure sai daga baya aka sakeni. Mai martaba ya kamu da ciwo hawan jini, gimbiya Nafisa itama ta kamu da ciwo zuciya a dalilin batan yarima Yazeed. Baya batan yarima Yazeed da shekara 10 gimbiya Fulani tahaifi yarta Mai suna khausar, kausar nada shekara 3 gimbiya Nafisa ta sake haihuwar yarta Mai suna khairat. A haka rayuwar Mai martaba da gimbiya Nafisa ta kasance cikin kunci, sbd har yanzu Mai martaba bai samu haihuwar da namijiba".... Kallon khamal baba yayi yace "yau shekara 34 kenan da batan prince Yazeed, har yau babu Wanda yasake jin lbrn sa, anyi nemansa kamar hauka Amma Babu shi Babu alamarsa.. A yanzu haka nasan Mai martaba yaji lbrn zuwanka garinnan, Kuma Koda yaushe zaka iya ganin fadawansa sunzo nemanka, domin tabbas zasu San nina daukeka Kuma hakan zai iya jawomin wani hukunci Mai tsanani awajen Mai martaba, Amma Ina neman kasa Mai martaba yayimin sassauci ranka yadade", hawayensa yashare tare da sunkuyar da kansa kasa, dafasa Kamal yayi yace "ka kwantar da hankalinka insha allah Babu abinda zai sameka sai alkhairi" Da karfi aka banko kofar gidan, Saida suka tsorata musamman baba sanusi dayayi imanin sai Mai martaba yayi masa hukunci Mai tsanani.. Fadawa ne suka dinga shigowa gidan sunfi a kirga, domin Saida suka cika gidan gaba daya, kasan cewar ba wani girma ne da shiba.. Ganin haka yasa baba sanusi da Kamal mikewa tsaye, gabadaya fadawan suka russuna kasa suna kwasar gaisuwa, gaisheka ranka yadade Mai girma yarima, magajin sarki, jikan sarki, Mai martaba sarki yabada umarnin a zo tare dakai ranka yadade... Kallon baba sanusi yayi yace "baba Babu tabbacin cewa nine Wanda ake nema fa"😔 "Kamal babu Wanda zai kalleka yace kaiba Dan mai martaba bane domin kamar ku daya dashi Babu inda kabarshi, Kuma karka manta fa ka gayamin wadanda suka reneka a daji suka tsinceka, taya zakace kaiba Dan Mai martaba bane"? "Hmmmmm" dogon numfashi khamal yasauke, harga Allah yanason haduwa da iyayensa, Amma yanzu fargabar zuwa garesu yakeji ko menene dalili oho!! Nidai nace kabar wannan tunanin tunda baka da Mai baka wannan amsar. A kunne baba sanusi ya rada masa wata mgn wadda nikaina banji abinda ya gaya masaba, kallon baba sanusi yayi, gyada Kai yayi alamar yaji mgnr da yayi masa,. Kallon fadawan Kamal yayi yace "muje ko" tashi sukayi suka buda masa hanya, a hankali yafara daga kafarsa Yana takawa saikace Mai koyon tafiya, dama salonsa kenan, shiyasa abokansa suke kiransa da prince khamal, sbd komai nasa cikin kasaita yakeyinsa, idan baka sanshiba, a schl ka fara ganin sa zakayi tunani shi Dan wani babban mutum ne, alhalin Kuma shidin rainon kauyene, ilimi ne kawai yasa yake gudanar da al amuransa cikin wayewa da kasaita.. Harya fara tafiya yatsinki muryar wani bafade na cewa dakai zamu tafi baba sanusi, gabansa ne yayi mummunan faduwa, sbd yasan cewa yau kashinsa yabushe tunda Mai martaba yayi kiransa a fada, a dalilin kamasa da akayi da magajin sarki... Jikinsa ne yafara rawa kafin kace wani abu tuni baba sanusi yafara fitsari a wando 🤭 durku sawa yayi har kasa ya fara kuka mai tsuma zuciya.. Khamal ne yayi karfin halin danne dariyar sa yazo ya daga baba sanusi yace "ka kwantar da hankalinka insha Allah Babu abinda zai sameka idan Kuma har za'a hukuntaka a dalilin ka taima keni to tabbas ni zan dauki hukuncin da za'ayima" share masa hawaye yayi, a cikin ransa yanajin kaunar wannan dattijon, da Kuma tausa yinsa, "baba katashi ka cenza kayanka mutafi... Tashi yayi jiki babu kwari ya shiga bandaki yayi tsalki, yaje ya cenza kayansa.... Tafiya sukeyi acikin mota kowa da tunaninsa, khamal dai yayi nisa sosai a cikin tunani yanajin kaunar iyayensa acikin ransa amma yarasa dalilin dayasa yakejin faduwar gabansa na tsananta, nan take a binda ya faru dashi a kyauyensu yafado masa arai, gaban sane ya tsananta faduwa nan take yaji jikinsa yafara rawa, tabbas idan yabari akasan da wannan lbrin to korarsa zasuyi bazasu taba karbarsa ba, dafe kansa yayi danjin yana sarawa, Ina bazan taba bari wani yasan da wannan lbrin ba, Yafada cikin ransa.. Fadawane suka yi cincirindo a kofar gidan, duk Dan tarbar yarima, kirari suka hauyi masa har aka wangale get din, wani dandazon tarone yagani Wanda yaninka wadan da ke waje, ciki ko harda sarki, da matan sa danya kasa zama a fada sbd tsabar zumu din ganin farincikin sa 🥰 A yau kowa na cikin farinciki musamman Mai martaba da gimbiya Nafisa.... By 💞 Meerah💞💞💞 Comments and share 🙏🙏 [3/15, 10:23 AM] Meerah 💞: 🤴🏻🤴🏻🤴🏻 prince khamal🤴🏻🤴🏻🤴🏻 🌹🌹🌹🌹🌹🌹 By 🌹🌹🌹 Meerah💞 🌹 Samira Ayuba🥰🥰 08068971503 🌹 ELEGANT ONLINE WRITER'S ✍️✍️ Da sunan Allah Mai rahama mai jinkai 🅿️ 9️⃣_🔟 Daidai ta parking din motocin sukayi, a hankali Mai martaba ya budewa khamal motar cikin so da kauna, fitowa yayi ya rungume mahaifina sa, da mahaifiyar sa. Kallo daya zakayiwa wannan family kasan suna cikin farinciki.... AFRA Kwance take a makeken bed room dinta Wanda yasamu komai na more rayuwa. "Afra!! Afra!! Afra"!! Cikin tsawa da daga murya umma ke kiranta afalo, tanajinta amma ta share ta danta San bawata mgn Mai dadi za'ayimata ba. Hawaye ne kwance afuskar ta, tuntana sharewa harta gaji ta daina. Banko kofar akayi da karfi, "ke Afra wai ba kyajine anata kwala miki Kira Amma kin kyale" Batace mata komai ba sai kokarin mikewa da takeyi, wucewa tayi tabar umma tsaye adakin tana binta da kallon tsana, kamar ba itace ta haifeta ba. Afalo ta iske Abba zaune, itama zama tayi da kyar ta iya bude baki tace Abba Ina kwana. "Da ban kwanaba Zaki ganni? Iye!!! nace da ban kwana ba Zaki ganni, to bari infada miki na tsada miki miji nan da sati daya zaayi auren ku"... A tsora ce ta mike tsaye, "wlhi Abba bazan aure shiba, ni khamal nake so, shika dai zan aura" Tasss! Tassss! Umma dake kusa da ita ta wanke ta da mari har sau biyu, "bazaki aure shiba Dan ubanki" "Wlhi umma mutuwa zanyi idan baku auramin shiba" "kije ki mutu mana waya rikeki, to bari infada miki aure babu fashi, ko kina so ko baki so" Yana gama fadar haka ya fice daga gidan rai bace.... Da gudu ta shige daki ta fada akan kayataccen bed dinta, tana rusa kuka kamar ranta zai fita..... Umma dake tsaye a falon tana ta faman zabga fada ita kadai, tace "wai anya ba cenzamin wannan yarinya akayi a asibiti ba Anya Yar Dana haiface da cikina? Kallon kofar dakin da Afra ta shiga tayi tace, "wlhi Afra Koda Zaki mutu sai anyi wannan auren baki isa ki zubar muna da mutunci ba, mezakiyi da khamal? Matsiyaci, Wanda bai gaji azzikiba, Dan tsintuwa wanda da ba'asan a salinsa ba, bandama rashin hankali irinna Afra wadda ta haifeshi ta jefar a daji ke mezakiyi dashi? Sannan babban abin takaici shine ya watsawa wadanda suka reneshi, suka ilman tarda shi, kasa a do, ya kunya tasu a idon jama'a, ya to zarta su, ke mezakiyi dashi... Indai nice uwarki to wallahi baki isa ki aure shiba, sha sha Shar banza mara hankali wadda bata san abinda takeyi ba.... Duk abinda take fada Afra najinta a daki, Dafe kanta tayi afili tace a'a khamal, baka aikata ba Kuma bazaka taba aikata irin wannan laifin da ake zarginka dashi ba, wlhi Koda zan rasa komai arayuwata saina fitar dakai acikin wannan halin bazan taba barin ana zarginka akan abinda baka aikata ba..... Wayarta ta dauko tafara Kiran layin khamal, shiru ba'a daukaba, tunjiya take ta kiransa Amma baya dauka, wasu hawayene suka gangaro mata, kodai khamal yarabu da itane? Dafe kanta tayi, tafara tuna irin cin mutuncin da Abba yayi masa, da korar kare acikin gidannan, kuka tafarayi Mai daga murya, kamar mahaukaciya, umma ce tashigo dakin tana binta da kallo, abin duk ya daure mata kai, kodai Afra nada iskane bata saniba sai yau... Hawa gadon tayi ta jawo Afra jikinta, tana cewa "lafiyarki Lau kuwa" kallon ta Afra tayi tace "umma khamal ya rabudani yaki daukar wayata tunjiya" tureta umma tayi cikin zafin rai tace ai haka nakeso Allah yakara tayi tsaki tabar dakin... Afra tayi kuka a ranar kamar ranta zai fita, da kyar tasamu bacci yadau keta.. Afra tazama abin tausayi rabonta da abinci tunjiya, yauma bata da niyyar ci domin halin da take ciki Kamal daine zai iya fitar da ita aciki, gashi yatafi ya barta. Wasu zafafan hawaye ne suka gangaro a fuskar ta, bazan iya rayuwa ba idan har babu Kai khamal... Wani tunani ne yado mata arai, tashi tayi cikin hanzari ta dauki mayafinta da key din motar ta tafice daga gidan... Bata tsaya ko inaba sai kauyensu khamal, bakin garkarsu ta tsaya tana tunanin ta shiga kota fasa, saude tagani ta fito daga gidan rike da tulun dibar ruwa da alama rafi zata tafi. Tana ganin Afra tsaye akofar gidan ta koma da gudu cikin gida, fadawa tayi akan Inna laure dake tsintar wake, "ke meye haka Kuma Zaki fadomin idan nibaki tuna Zaki iya jimin ciwo, aiya dace ki duba Dan dake cikin ki" "Inna wannan yarinyar ce fa Yar birni nagani a kofar gida", "wacce yarinya Kuma?, Oh!! Ni laure wai meyasa Yan birni sukeda nacin tsiyane duk da ankori khamal din saita dawomin agida to mezanyi mata"? "Inna shikenan ta rabani da khamal" saude ce ke mgn tanata faman kuka kamar karamar yarinya, Inna Dan Allah kidawomin da khamal wlhi bazan iya rayuwa ba idan Babu shi.. "Ke dallani matsa kibani wuri ai duk lafin kine da kinyi abinda boka yace aida haka bata faruba, kika kiyi kika je wajen wancen sha sha shan".... "Wlhi Inna ba laifina bane nima naso na kwaci kaina Amma nakasa dan ya fini karfi"... Gaban Inna laure ne yafadi ganin Afra tsaye tana kallon su Kuma duk taji abinda suke Fadi. "Ke Kuma meya kawoki haka mayya anace, to karya kikeyi kurwar khamal tafi karfinki..... Murmushi Afra tayi tana Kara shigowa cikin gidan, tace " dama ban taba yadda da wannan sharrin da kuka yimasaba, ayau asirin ku ya tonu Kuma wlhi saina fallasa ku abainar jama'a. Tana gama fadin haka takama hanyar dakin datasan na khamal ne tashiga, dube dube ta hauyi cen taga wayarsa, ajiyar zuciya ta sauke tare da murmushi, daukar wayar tayi tafice daga gidan ba tare da tabi ta kansuba..... Ta bude motar ta kenan zata shiga ta hangi ado Yana tafiya, rufe motar tayi ta nufi inda ado yake.. Gaisawa sukayi cikin farinciki, Afra ta kalli Ado tace "Ado wai abinda khamal ya aikata gsky ne ko"? Nisawa Ado yayi yace "nima banyar da ba kokadan, Ina zargin Inna laure da saude akan abinda yafaru, domin saude tana tsananin son kamal, Koda ace tabbas ya aikata to ba ason ransa bane tirsasasa akayi" "Nima banyar daba Ado nasan khamal sosai a schl, bazai taba aikata irin wannan danyen aikin ba, Amma zan cigaba da bincike koma menene saina gano gsky, Kuma saina Nemo khamal duk inda yake afadin duniyar nan"..... Anan sukayi sallama takama hanya tashiga mota tabar wajen. Gida ta nufa cike da farinciki, afalo ta iske umma ta hade rai, itama hade fuska tayi tazo zata wuce ta gabanta taji tace "daga Ina kike"? Tsayawa tayi batare da tajiyoba tace "daga gidansu nusaiba" By 💞 Meerah💞💞💞 [3/15, 10:24 AM] Meerah 💞: 🤴🏻🤴🏻🤴🏻 prince khamal🤴🏻🤴🏻🤴🏻 🌹🌹🌹🌹🌹 By 🌹🌹🌹 Meerah💞💞 🌹 08068971503 ELEGANT ONLINE WRITER'S✍️✍️ Da sunan Allah Mai rahama mai jinkai 🅿️ 1️⃣1️⃣_1️⃣2️⃣ Daki ta shige ba tare da ta Kara cewa komai ba, itama umma binta da kallo kawai tayi.. Akan bed dinta tafada cike da farinciki, murmushi ne take ta famanyi, Allah sarki khamal a yau nasamu hujjar da zan iya bada shaida akanka, Allah ya tsaremin Kai a duk inda kake, Amin... Mikewa tayi ta nufi kitchen Dan samun abinda taci.. Lokaci tafiya yakeyi, ranaku na gudana, umma da Abba sai faman shirye shirye sukeyi. Ita Kuma Afra duk abubuwa sunyi mata yawa gashi bincike takeyi a halin yanzu, dan ta San inda khamal yake, ta kasa samu wani lbr Mai dadi akansa, domin ta bayar da cigiyar sa, harda kyauta Mai yawa ga Wanda duk ya ganshi Amma Ba bushi Babu alamar sa. Wadanda tasa nemansa sun tabba tarmata baya cikin garinnan, domin sun duba lungu da sako Amma basu ganshi ba... Umma ce tashigo dakin tace "ki tashi maza kishirya ga Wanda Zaki aura nan yazo a falon baki" ficewa tayi ta barta nan zaune.... A jiyar zuciya ta sauke, mikewa tayi ta dau Maya finta rai bace ta fita.. Zaune ta iska shi Yana jiran shigo warta, da sallama ta shiga, kamar bazai ansaba, sai Kuma ya amsa cen ciki batare da ya kalli wajen da take ba... Zama tayi a kujerar da ke kallon tashi, tana kallon sa, shima ahankali ya dago kansa cikin kosawa da kallon da take masa ya kalleta fuska daure Murmushi tayi tace "naji dadin zuwan ka sosai Kuma a yanayin ka Dana kalla inada tabbacin burina zaicika" Tsaki yayi yace "ba wannan ne yakawo niba tirsa sani akayi nazo Kuma nazo Dan haka Kinga tafiya ta" mikewa yayi yafara tafiya, batare da yace mata komai ba. "Nagode kwarai, naji dadin zuwan ka, bari na rakaka" binsa tayi abaya har wajen motar sa, dakanta ta bude masa ya shiga, daga masa hannu ta dinga yi tana murmushi harya bar gidan.... Daki ta koma cike da farinciki, ba laifi shima ya hadu, Amma bazai taba Kai Kamal ba. Wayarta ta dauko ta Kara Kiran wannan number kozata dace, haryanzu dai kashe wayar take, wani zafi takeji aranta tarasa dalilin dayasa khamal yaki bude wannan ledar data bashi. Kodai yagani kin kunna wayar ne kawai yakiyi? Hawaye ne suka gangaro mata, khamal meyasa zakayimin haka? Kodai kadaina sonane shiyasa ka watsar dani?? Kuka takeyi sosai babban tashin hankali ta shine yau saura kwana uku a daura mata aure gashi Kuma khamal yaki kunna wayar balle tasan inda yake.. Tana cikin haka wani tunani yafado mata arai da sauri ta dauki wayarta da Kira wani course mate dinta, Kira daya yadauka. "Aslm Hashim kana ina yanzu" yace "ganin bakin aikina kamar yadda kika sani", "madallah, Hashim wani aiki nakeson nabaka Dan Allah" "Wane aikine? Kinsanfa banida isasshen lkc", "karka damu Hashim zan ninkama kudin da zaka samu a wannan aikin da kakeyi" "Ok wanne aikine"? "Zan turoma wata number yanzu ka bincikamin inda zaa sami Mai wannan wayar" "Indai wannan ne karki damu aikinane yanzunnan zan bincika Miki", "ok to bari naturoma, saika turomin account number dinka" Bayan ta turamai bada dadewa ba saiya kirata, " hello!! Hashim ya ake ciki" "Na duba naga Mai wannan layin Yana cikin garin Zaria" gabanta ne ya fadi "Zaria" tafada azuciyarta batasan mgnr tafito filiba, saijin sa tayi yace "ehh! Acikin garin yake" "Hashim bansan kowa ba a Zaria, Amma inason Dan Allah ka tayani bincike wanine nake nema", nan ta labarta Mai komai yaji tausayinta sosai "Karki damu Afra inada wani friend acen zansa shi yabin cikamin komai" taji dadin mgnr sa sosai, kudi ta turamai 2.5million, Kuma ta tabbatar mai idan komai yatafi dai dai zata karamai, yaji dadi sosai, shiyasa yafara aikinsa Babu wasa.... Yau laraba baki na nesa Dana kusa sunzo domin halarta wannan gagarumin biki da aka shirya shi cikin kankanin lkc.. Afra kan sai safa da marwa takeyi a tsakiyar daki, domin tunjiya da sukayi mgn da Hashim bata karajin wani lbr ba awajensa, kota kirashi sai yace mata Wanda yasa aikin Yana cen Yana bincike har yanzu bai gama ba, Hankalin ta ya tashi sosai, a haka ta share tsawon yina tana saurare Amma Babu wani lbr Mai dadi. Washe garin ranar alhamis tunda safe ta Kira hashim kamar tayi kuka tace " Hashim gobene fa zaadauramin aure" murmushi yayi yace "karki damu Afra ansamu lbr Mai dadi" itama murmushi tayi cikin zumudi tace "angane inda yake kenan ko"? "Ehh ya gayamin acikin gidan sarkin garin yake" dafe kirji tayi tace "gidan sarki Kuma"? "Ehh ina tunanin kamar bauta yakeyi acikin gidan", "bauta kuma? Khamal dinane yake bauta awani gida" hawaye suka gangaro mata, cikin kunci da damuwa tace "Hashim yanzu taya zan iya fitar dashi acikin gidan" "Hanya mafi sauki da zamubi, itace kema saikin shiga gidan amatsayin baiwa" "What!!! Baiwa Kuma ni Afra nice zanje wani kazamin gida a matsayin baiwa" ajiyar zuciya ya sauke yace "matukar kinason khamal to dole ne kema ki zama baiwa a dalilin sa, Kuma fa ba a haka Zaki dawwama ba da zarar burinki ya cika to shikenan bauta ta kare" "Shikenan Hashim zanje, inason ka tsaramin komai gamai da tafiyata, inson samune yau na keson natafi kafin gobe sbd taro zaiyi yawa agidannan" "Ok zamuyi mgn dashi komai ake ciki zakaji kidai zama cikin shiri", "ok " nan sukayi sallama taci gaba da shirya kayanta,... Shiru bataji komai ba game da Hashim har magrib tayi hankalin ta ya tashi sosai ganin yadda gidan nasu yacika makil da mutane na nesa Dana kusa, tun tana Kiran Hashim Yana cemata ta Kara jira harya daina daukar wayar ta, ta shiga damuwa sosai ganin yadda al amura ke tafiya, gashi tanason saka kayanta a mota Amma tarasa haryanda zatabi Dan gidan ko Ina mutanene. Tanan tana jiran Hashim har 12:00am tayi bataji wayar sa ba, cikin tane ke kugin yunwa, fitowa tayi danta samu abinda taci, taga gidan shiru ba motsin kowa alamar sunyi bacci, taji dadi sosai da sauri ta koma dakinta ta dauko jakar kayanta ta fito cikin sanda Kar ajita, Sannu ahankali ta bude motar ta tasaka kayan ta rufe, ta koma kitchen ta dibi abinci taci... 9:00am saiga Kiran Hashim yashigo wayar ta cikin hanzari ta daga Kiran "ki fito yanzu komai ya daidai ta ke kadai muke jira" Tayi farinciki sosai, cikin hanzari tayi rubutu ga paper ta ajiye ta bude wayarta ta ciro layinta ta ajiye akan paper din ta dauki wayar ta da Maya finta ta nufi dakin umma.... "Umma zanje na tafo da wasu friends dina suzo biki Kuma basu gane gidanba", "to kiyi sauri karki dade kinsan baason amarya na yawo", "to umma yanzu zan dawo" Da sauri ta bar gidan, tana fita ta Kira hashim a sabon layinta, Kira daya ya dauka "Hashim ganin a hanya yanzu zan iso....... By 💞 Meerah💞💞💞💞 Share and comments [3/15, 10:24 AM] Meerah 💞: 🤴🏻🤴🏻🤴🏻 prince khamal🤴🏻🤴🏻🤴🏻 🌹🌹🌹🌹🌹 By 🌹🌹🌹 Meerah💞💞💞 08068971503 ELEGANT ONLINE WRITER'S✍️✍️ Da sunan Allah Mai rahama mai jinkai 🅿️ 1️⃣3️⃣_1️⃣4️⃣ Tsaye ta ganshi da alama ita yake jira, parking tayi awajen, shikuma Yana ganinta ya zagayo ya shiga.. "Muje ko" ya fada Yana kallon ta, "tare zamuje kenan", "ehh tare zamuje zan tsaya harsai naga kinshiga gidan sannan nadawo" Kallon sa tayi tana murmushi, tace "ngd kwarai Hashim Allah ya saka da alkhairi", "ba komai afra, ai dole ne na taimaka miki dannaga guy dinnan ya kamaki dayawa" ya fada ne cikin zolaya. "Kaidai bari Hashim wlhi bazan iya jure ganin khamal cikin wani haliba, na dau alwashin taimakawa khamal Koda zan rasa komai arayuwata" "Bazaki rasa komai ba Afra insha Allah Zaki iskeshi lfy ki dawo dashi lfy, iyayenki Kuma bana tunanin zasu iya fushi dake sbd tsabar sonda suke yimiki" Hmmmm dogon numfashi ta sauke tace "kaidai bari Hashim iyayena sundaina sona tun lkcn da na kawo musu khamal amatsayin Wanda zan aura" "Basu daina sonki ba Afra Kuma bazasu daina sonki ba, Afra inason kiyi nazari ki fahimci manufar iyayenki, suna sonki sosai, basu son ganinki cikin damuwa, Afra khamal bai dace da babbar yarinya irinkiba, wlhi nayi matukar mamaki daya iya ganin classic baby irinki yace yanaso, sbd ke ba matar talaka bace, ke Yar".........."ya isa haka Hashim" tafada cikinjin zafin maganar sa.. "Khamal bashine ya fara shiga rayuwata ba nice na shiga rayuwar sa, Hashim nice naga khamal nace inason sa ba shine yace yana sonaba"..... Hawayen dake gudana a fuskarta ta share "Hashim nice silar tarwa tsewar rayuwar khamal, nice sanadiyyar da yasa akayi masa sharri akan abinda bai aikata ba, bai taba aikatawa ba... Khamal mutumin kirki ne Amma a dalilina kowa nayi masa kallon fasiki, khamal ya tashi cikin gata da soyayyar iyaye Amma a dalilina yarasa komai".... "Afra me khamal yayi maki dakika aikata masa wannan abun" "A'a Hashim wlhi ban shiga rayuwarsa ba dannaga ya tozarta, wlhi kaunar sa nakeyi tsakani da Allah, tunsanda na fara ganin sa, bansan haka abin zaika sance ba dana hakura da sonda nakeyi masa, sbd ganinsa cikin farinciki yafimin komai arayuwa" Ajiyar numfashi Hashim ya sauke yace "Afra wai ya akayi kika samu soyayyar wannan guy din dannaga baya kula kowa a schl" Murmushi tayi tace "wlhi nasha bakar wahala kafinna samu soyayyar sa, harna fidda raina, na daina zuwa wajensa sbd kullum naje baya kulani, idan inayi masa mgn ko kallo na bayayi. Na dauki tsawon lkc Ina Kai kaina wajen sa Amma baya kulani, tun abokaina na bani shawara akan yadda zansamu soyayyar sa har suka koma cewa na rabuda shi, daga karshe dai mukayi fada dasu sbd na fahimci suna sone kawai surabani dashi.. Dana fahimci dai khamal bazai taba Sona ba arayuwar sa saina hakura na daina zuwa wajens, cikin ikon Allah sai gashi yazo wajena da Kansa, Ashe yawan nacewa Dana keyi a kansa da jure irin wulakancin da yakeyimin yasa Nima yafara Sona bai saniba Saida na daina zuwa wajensa ne yagane sbd ya shiga damuwa rashin ganina, nayi farinciki sosai wlhi awannan rana, tunda ga lkcn soyayya Mai karfi ta kullu tsakanin mu"..... Hmmmm "lallai na jinjina Miki Afra domin wlhi nayi mamaki sosai dana ganku tare, sbd kowa yasan khamal a skull baya kula kowa, Kai ko maza ma baya kulawa balle mata... Amma kinsan wani abu? Kowa fa ya dauka cewa sbd kudin kune yasa khamal yake sonki, saidai ni abinda ya bani mamaki shine agabana ya taba wula kanta wata yarinya a skull sbd tace tana sonshi Kuma itama babbar yarinya ce kamar ke, kowa Yana ji da ita a skull din, Amma hakan baisa khamal yasota ba".... Murmushi Afra tayi tace "zeeey kenan ai wannan kowa yasanta a skull din bata da kamun kai, shi Kuma khamal ya tsani ballagazar mace, wadda bata da natsuwa". ... "Hakane Kuma domin khamal gsky kowa yasan shi a skull yanada kamun kai da riko da addini" Da wannan firar suka iso garin Zaria, Kai tsaye gidansu abokin Hashim suka nufa, sun tarar dashi agidan sbd yasan da zuwansu, Kai tsaye wajen mahaifiyar sa yakai su suka gaisheta cikin girma mawa, dayake dama abokin Hashim salim yayi mata bayanin komai tun kafin suzo, Amma bai gaya mata cewa Afra ba baiwar gaske bace... Bayan ta basu abinci da ruwa sunci, tace "to 'yata tunda kunzo tashi zakiyi naje na hadaki da matar da take Kai bayi gidan sarki"... Jiki asanyaye ta tashi, wajen motar ta taje ta dauki iya abinda zata bukata acen tabar saura cikin motar, Salim ta bawa key din motar tace "ka ajiye min motar nan anan gidan zanzo na dauketa idan natashi bukatar ta" Amsa yayi yace "insha Allah zan ajiye Miki ita bisa amana" Kudi masu yawa tabashi, sanna ta ida turawa Hashim sauran kudinsa kamar yadda tayi alkawari, anan tayi sallama dasu ta tafi inda mahaifiyar Salim ke jiranta...... Babban gidane Wanda ya kunshi komai na more rayuwa tun a kofar gida zakasan cewa wannan gidan sarauta ne, Afra dai sai kalle kalle takeyi domin komai na gidan ya birgeta murmushi takeyi, sbd yauce ranar da zata hadu da masoyin ta khamal... Wajen wata mata aka kaita da alama itace shugabar bayi acikin gidan, ta karbi Afra hannu bibbiyu sbd suna da bukatar bawai asashen gimbiya Fulani.... Babu bata lkc ko aka kaita cen a matsayin hadima wacce zata dinga tsaftace part din gimbiya Fulani. Ana kaita ko gimbiya Fulani tace ayanzu zata fara aiki, Babu alamun tausayi kokadan afuskarta .... Haka Afra ta hau shara da goge wurare, abinda bata tabayi ba arayuwar ta, saidai da nikaf tashi go, dan batason khamal yayi saurin ganeta tafi son tayi masa bazata...... Tana cikin aikine tajiyu murya kasa kasa ana cewa "ranki yadade boka ya tabba tarmin idan har prince Yazeed yasha wannan gubar bazai Kara numfashi ba aduniya.... Wata dariya gimbiya Fulani tayi, irin dariyar da mugaye sukeyi idan sukaga alamar nasara...... By 💞 Meerah💞💞💞 Share and comments fisabilillah 🙏🙏🙏🙏 [3/15, 10:24 AM] Meerah 💞: 🤴🏻🤴🏻🤴🏻 prince khamal🤴🏻🤴🏻🤴🏻 🌹🌹🌹🌹🌹 By 🌹🌹🌹 Meerah💞💞 08068971503 ELEGANT ONLINE WRITER'S✍️✍️ 🅿️ 1️⃣5️⃣_1️⃣6️⃣ "Ni Fulani na rantse sainaga bayanka Yazeed Koda zantafi tsarara, yadda ban haifi namijiba agidannan Babu wadda zata haifawa sarki magaji" Jikin Afra duk yayi sanyi, "innalillahi" kawai take maimai tawa, dama haka wannan gidan yake? Tabbas zanyi iya kokarina bazan bari akashe wani Ina gani ba. "Ranki yadade boka yace asawa prince Yazeed wannan gubar acikin abin shansa, gashi Kuma akwai tsaro Mai karfi a part dinsa"... "Karki damu jakadiya kullum Yana zuwa nan danya gaisheni, kibari gobe da safe idan yazo sai abashi yasha" Saurin Kama aikinta tayi danjin alamar motsin tafiyar mutum, jakadiya ce tafito daga falon gimbiya fulani.. Ci gaba tayi da aikin ta wata zuciyar tace ta taimaki wannan yazeed din wata zuciyar Kuma tace ke fita batunsu, meye ruwanki dasu keda ki kazo daukar kamal. Da wannan tunanin ta gama aikinta gaba daya...... Fitowa tayi daga part din gimbiya Fulani, ta fara dube dube acikin ma sarautar ko zataga Kamal... Ta fiya takeyi bata San kowa ba batasan inda zataba, wasu bayi ne maza ta gani da alama fira sukeyi wuri ta samu nesa dasu ta labe tana binsu da kallo daya bayan daya Koda zata ganshi..... Data ga Babu shi cikinsu saita Kara gaba, Afra tayi yawo sosai acikin masarautar har magrib tayi Amma bata ga khamal ba, haka ta hakura ta koma masaukin ta.... Washe garima haka tafito tunda safe Saida tayi yawon neman khamal kafin taje wajen aikin ta..... Shiko khamal yanacen wajen Mai martaba bai fitoba tunsanda yaje gaishe she, sbd Mai martaba akwai shi dason fira, duk da khamal bayawan surutu gareshi ba Amma haka yake sake jikinsa yayi fira da mahaifinsa, saidai tunjiya yanajin wani bakon Al amari acikin zuciyarsa, domin bugun zuciyarsa ne yakaru Koda yaushe jiyake kamar Afra tana tare dashi, yanason bawa mahaifin sa lbrn Afra da irin sonda yakeyi mata Kuma yanajin tsoron bayyanar sirrin daya boye Wanda bayason kowa yasani.... "Prince khamal" Mai martaba ya fada Yana kallon khamal, "na'am daddy" ya fada Yana kallon sa, "inason ka daukeni kamar abokinka ba matsayin mahaifiba, khamal banason kadinga boyemin damuwar ka komai girmanta haka komai kan kantarta, khamal ka gayamin meyake damunka Danna lura dakai tunjiya kana cikin damuwa" Murmushi yake yayi Wanda hausawa ke cewa yafi kuka ciwo, yace "ba komai daddy", kallon sa daddy yayi yace "yaushe kafara yamin karya, Yazeed" yafadi sunansa na ainihi babu alamar wasa a fuskar sa "kafadamin gsky meyake damunka"? Ganin yanayin mahaifinsa yasan babu wasa a fuskar shi yace " daddy dama wata yarinya ce wadda mukayi soyayya da ita abaya shine nakejin kamar tana kusa dani" Kallon sa Mai martaba yayi yace "wacece ita" nan khamal ya bashi lbrn Afra tun farkon haduwar su har irin korar Karen da Abba yayi masa lkcn dayaje gidansu... Daddy ya tausaya masa sosai yace "wanene mahaifinta, kafadamin nida kaina zanje na nema maka aurenta akaro na biyu" Gaban khamal yayi mugun faduwa domin yasan cewa zuwan Mai martaba gidansu Afra to tabbas allura ce zata tono galma " a'a daddy anriga anyi mata miji, har ansa ranar aurenta" hawayene suka gangaro masa domin wannan kalmar daya fada bakaramin tayar masa da hankali tayi ba, kardai mgnr sa tazama gsky, idanko hakan ta kasance to tabbas zai iya hadiye zuciya ya mutu....... Mai martaba bai Kara cewa komai ba sai binsa dayayi da kallon tausayi, lallashinsa yafarayi kamar karamin yaro...... Gimbiya Fulani tayi jiran shigowar khamal shiru bata ganshi ba har rana tayi babushi Babu alamar sa, haka ta hakura dole badan taso ba... Sannu sannu Afra Saida ta share sati daya agidan bataga alamar khamal ba, Kiran Hashim tayi awaya tace ya Kara bincika mata koya fita daga gidan Dan haryanzu bataga alamar sa ba. Babu bata lkc Hashim ya Kara bincikawa ya tabbatar mata da yana cikin gidan haryanzu, jikinta yayi sanyi sosai hartaso ta koma gida ta tuna da cewa guduwa tayi idan ta koma batasan irin hukuncin da zasuyi mata ba. Zaune take cikin lambu tana wasa da furanni motsin mutum taji abayan ta, tana wai wayawa, ta dafe kirji da sauri, innalillahi mezan gani haka tafada cikin ranta da mugun tsoro a zuciyar ta..... "Keee meya kawoki nan wajen ko Kinga wurinnan yayi Miki Kama da wajen zaman bayi" ajiyar zuciya ta sauke tana godiya ga Allah dayasa bai gane taba da yau kashinta ya bushe, taba fuskarta tayi taji bakin abinda ta shafa Yana nan baifitaba, shiyasa ma bai ganeta ba... "Kayi hakuri dan Allah wlhi ni bakuwa ce bansan komai ba acikin dokokin gidannan, tana gama fada tabi ta gefensa ta wuce tana murmushin jindadi, yau bakin paintin nan datake shafawa ya ceceta.... Shi Kuma Nasir tsaye yayi Yana binta da kallo kamar yasanta Amma bakin abinnan data shafa yasa ya kasa ganeta, hankalinsa ne yakasa kwanciya, jiyayi yanason sanin kowacece ita, bin bayanta yafarayi, sannu a hankali hartaje masaukinta shiga dakin tayi shikuma ya koma cike da sake sake aransa...... Wanene Nasir? Meyasa Afra taji tson ganinsa? Kubiyoni danjin cigaban lbrn Nice taku har kullum Meerah💞 More comments more typing 💘 [3/30, 1:44 PM] Meerah 💞: 🤴🏻🤴🏻🤴🏻 prince khamal🤴🏻🤴🏻🤴🏻 🌹🌹🌹🌹🌹 By 🌹🌹🌹 🌹 meerah💞💞💞 08068971503 ELEGANT ONLINE WRITER'S✍️✍️ Da sunan Allah Mai rahama mai jinkai 🅿️ 1️⃣7️⃣_1️⃣8️⃣ A gefen iyayen Afra ko basu San Afra ta guduba sai gab da daurin auren, mutane har sun hallara.. Umma ce taji shiru bataji motsin Afra ba tunda tace mata zata fita gashi har rana tayi ko break fast bataga tayi ba, "zainab" umma ce takira ta, da sauri tazo, "umma gani" "Jeki Kira Afra tazo taci abinci, "to umma" zainab ta fada tana tafiya dan cika umarnin umma. Tana shiga dakin taga ba kowa, zama tayi tana jiran fitowarta daga bayi, a tunanin ta tashiga toilet ne, idonta ne ya sauka akan wata paper da sim card a saman, dauka tayi ta bude danta ga a binda ke jikin paper din, gabanta ne yayi mummunan faduwa ganin abinda aka rubuta a paper din, da sauri ta fito tana Kiran, "umma!! Umma!! Afalo ta tarar da umma zaune tare da baki, Mika mata takardar tayi tana share hawaye, Itama umma bakaramin tsorata tayiba da ganin halin da zainab ke ciki ba, Jikin umma na rawa ta fara karantawa kamar haka... Umma, Abba kuyi hakuri ku gafarce ni wlhi bazan iya auren wannan mutumin ba, zanje neman khamal duk inda ya shiga afadin duniyar nan... Na barku lfy 😭 Umma na gama karanta wa tayanke jiki tafadi, mutanen da ke wajen sun rikice gaba daya, fadar irin tashin hankali da suke ciki bata lkc ne, ruwa suka yayya famata, Bada jimawa ba ta far fado, kuka tafarayi Mai tsuma zuciya... Afra karki tafi kidawo wlhi zangoyi bayan a auramiki Wanda kike so, umma tayi kuka sosai kamar ranta zai fita, cikin wannan halin ne ta kira Abba ta sanar dashi halin da ake ciki, shima dai sumar yayi awajen taron daurin aure, mutanen da suka halarci taron su suka yayya famasa ruwa,. Bayan ya farfado ne yasanar dasu halin da ake ciki.. Iyayen ango dashi kanshi angon ransu yayi matukar baci, musamman ma angon Wanda yaji yafara son Afra tun lkcn da yazo gidansu yaji ta birgeshi. Dangin ango sunyi fada sosai a wajen, shidai abba baice komai ba Dan ta 'yarsa yakeyi babu ruwanai dasu tunda sune sukaja mai yarasa 'yarsa wadda ita kadaice 'yarsa aduniya 😭 Gida ya koma yabar mutane nan tsaye, masu zaginsa nayi, masu tausaya masa nayi. Yana shiga gidan a falo ya zube kamar kayan wanki, hawaye nabin fuskar sa, umma ce tazo kusa dashi tace "Alhaji shikenan munrasa 'yar mu, munrasa farincikinmu Dana sani daban goyi bayanka ba, Dana sani Dana goyi bayan 'yata, wlhi bazan iya rayuba idanna rasa Afra" kuka takeyi sosai, Abba dai baice komai ba hawaye ne ke gudana a fuskar sa, kallo daya zakayi masa kasan cewa Yana cikin matsanan ciyar damuwa... Ahaka suka kasance cikin kunci da Dana sani, umma kullum fada takeyi Abba ne yaja mata tarasa 'yarta, shikuma Abba baya kulata Dan acewarsa duk halinda take ciki baike Wanda yake ciki ba...... Fulani ce keta faman safa da marwa a makeken falon ta Wanda yasami komai na more rayuwa, jakadiya ce ta shigo da sauri ta russuna a gaban gimbiya Fulani tace "ranki yadade prince Yazeed baisha abinda muka bashi ba" A razane gimbiya take kallon ta "wannan wacce irin banzar mgn ce kika zomin da ita? Mutum daya ya gagareki, yau sati daya kenan kina yimin alkawarin zaisha Amma kinkasa cikawa" "Ranki yadade akwai tsaro mai karfi a sashen yarima, Kuma idan yazo nan duk abinda aka bashi bayasha, Amma nasamo wata hadima wadda ke Kai abinci sashen yarima Kuma tayimin alkawarin zata zuba masa abinda muka bata" "Kije ki gaya mata matukar bukatar ta tacika to zan mallaka mata duk abinda takeso "an gama ranki yadade" Afra dai tana gefe tanajin su, sukuma basuma sanda ita awajen ba, jijjaga Kai kawai tayi, aranta tanason taima kawa wannan mutumin Amma tanajin tson abinda zaije ya dawo, addu'a ce kawai zata cigaba da yimasa Allah ya kareshi daga sharrin makiya na boye dana fili, Saude ce ke zaune a tsakiyar gidan, ta hada uban tagumi, hawaye na gudana a fuskar ta, Inna laure ce tafito da d'aki tana bin d'iyarta da kallon tausayi aranta tace duk nice silar shigarki cikin wannan halin, kallon baba Sani tayi tace "mlm hukuncin daka dauka akan khamal yayi tsauri koma mezakayi masa baidace ka koreshi ba, Khamal baya da kowa a duniyar nan saimu yanzu Ina zashi wazai bashi wurin zama"? "Ya isa haka laure banason ki koma yimin mgnr nan khamal dai ba d'ana bane, Kuma kema ba d'anki bane, Kuma hukuncin dana dauka akansa shiya zab'awar kansa shi" "Mlm khamal fa d'ana ne kamar yadda saude take d'iyata haihuwarsa ce kawai banyi ba Amma Nina raineshe tun yana cikin zanin goyo, Kuma Ina kaunarsa kamar yadda nake kaunar y'ata saude" bai koma cewa komai ba ya fice daga gidan, "Inna Dan Allah kidawomin da khamal wlhi bazan iya rayuwa ba idan Babu shi" dafa kafadarta Inna laure tayi tace "kiyi hakuri insha Allah bazaki mutuba khamal zai dawo gareki" share mata hawaye tayi tare da rungumeta, itama hawayen takeyi, harga Allah tana kaunar khamal kamar Dan da tahaifa a cikinta... Bayan fitowar Afra daga sashen gimbiya Fulani, haka kawai taji yau tanason zagayawa cikin masarautar Ko zataga khamal, haka ta dinga yawo, harta giji ko alamarsa bata gani ba, wani rafi ta tsinka nisa da ita, haka kawai taji tana sha'awar zuwa wajen, takon mutum taji abayanta kamar ana binta, aiko haka dinne, wai wayawar da zatayi caraf suka hada ido dashi, ta razana sosai da ganinsa musamman dataga alamar wajenta zaizo, taso tayi karfin halin danne hawayen da keshirin zubo mata sbd tsabar firgici Amma takasa, Kara sowa yayi ya tsaya daf da ita yana mata kallon tuhuma........ By 💞 Meerah💞💞💞💞 [3/30, 1:44 PM] Meerah 💞: 🤴🏻🤴🏻🤴🏻 prince khamal🤴🏻🤴🏻🤴🏻 🌹🌹🌹🌹🌹 By 🌹🌹🌹 Meerah💞💞💞 08068971503 ELEGANT ONLINE WRITER'S✍️✍️ Da sunan Allah Mai rahama mai jinkai 🅿️ 2️⃣1️⃣_2️⃣2️⃣ Murmushi tayi cike da farinciki "ohh ni Afra meyasa ma na boye banfito nafada masa Ni dince ba, a'a bazai yiyu na fito a haka da wadannan kayan ajikina, ta dubi kayan da aka bata na hadimai, alhmdlh Allah nagodema daka bayyana minshi, Ashe shine ake cema prince Yazeed danaji jakadiya nafada, nan take ta tuna da kullin da suka shirya masa, da sauri tabar wajen, ta nufi sashen gimbiya Fulani, a guje take ko hanyar ta bata gani, jinkawai tayi tayikaro da mutum. Saukar Mari taji a kuncenta "ke wacce irin dabbace haka zakizo ki bangaje ni"? Kausar ce take mgn cikin zafin rai. "Kiyi hakuri ranki yadade wlhi ban kula dake bane" mtseew "taya Zaki kula dani bayan bakida hankali babu kwakwalwa akanki, banza, jaka, dabba" tana gama fadanta ta wuce, Afra dai batace komai ba, ranta ya baci sosai Amma ba yadda zatayi dole tayi hakuri, ci gaba tayi da tafiyarta, daidai kofar shiga falon ta tsaya tana tunanin ta inda zata fara, tabbas jakadiya ta bawa hadima wannan gubar Kuma gashi khamal ya koma part dinshi, tabbas idan banyi saurin dakatar dashiba zaisha wannan gubar, da sauri tabar wajen.. Gudu takeyi sosai harta kawo part dinshi tanashirin shigane dogarawa suka dakatar da ita, sukayi mata alamar ba'ashiga dakai, magiyi tashiga yimusu Amma Sam suka hanata shiga, haka ta hakura ta koma gefe ta zauna tanata faman kuka.. Bangaren khamal kuwa Yana komawa part dinshi kishin gida yayi ajikin kujerar dake cikin k'aya taccen falon, Nasir yaso yaja khamal da fira Amma Sam yaki daga karshema cewa yayi ya fita yabashi waje yanason ya zauna shikadai, jiki babu kwari ya tashi yabar wajen. Hadimar ce ta shigo dauke da abinci da lemo ahannunta, ajiyewa tayi agabansa zuba masa tayi niyyar yi sai ya dakatar da ita yace lemo kawai yake bukata, tsiya ya masa tayi ta mika masa yace ta ajiye zai dauka, tana ajiyewa tabar wajen cike da fargaba.. Daukar lemon yayi zaikai baki kenan saiya ga photo Afra ya bayyana a fuskar tv dake jikin bangon dakin, sanarwar nemanta ne akeyi tare da aza makudan kudi ga duk Wanda ya ganta.. Cup dinda ke hannun sa ya fadi kasa ya fashe sakamakon rawar da jikinsa yafarayi, nan take ya zube awajen Babu numfashi...... Hadimar najin karar fashewar abu tasan maganin da ta zuba masane yafara aiki, da sauri ta lek'o ta ganshi kwance Babu alamar numfashi a tare dashi, murmushi tayi tace yau taka takare khamal saidai wani bakaiba, da sauri ta kwashe glass dinda ya fashe ta sauke lemon ta dauko wani ta aje awajen, nan take ta kurna ihu...... A guje fadawan gidan suka shigo, Babu bata lkc suka daukeshi suka nufi asibitin dake cikin masarautar dashi.... Afra na gefe tana ganin anwuce dashi nantake ta yanke jiki ta Fadi, itama daukarta akayi aka wuce asibitin da ita... Bayan likitan ya gama duba khamal ne itama ya dubata.... Mai martaba ne tare da gimbiya Nafisa wato ummi suka shigo office din doctor, Mai martaba yace "doctor meya ke damun son ne? sbd bada dadewa ba tare muke dashi a fada, lafiya Lau yacemin zaije yayi wanka ya dawo, Kuma Babu alamar koda zazzabi tare dashi" Ajiyar zuciya likita ya sauke yace "Allah yabaka nasara khamal yanacikin matsanan ciyar damuwa, tabbas akwai abinda yake so, domin Yana gab da kamuwa da ciwon zuciya, sai dai Kuma akwai wata yarinya da aka kawosu tare itama matsalar su dayace" Hankalin ummi yayi matukar tashi, "likita kayi wani abu Dan Allah ka kubutar min da dana, shine farincikina" kuka ne ya katse mata maganar. "Likita yanzu menene mafita banason wani abu yasame shi" Mai martaba ya fada cikin matsanan ciyar damuwa.. "Allah ya baka nasara abu dayane zaayi masa Wanda zai kub'utar dashi, shine anema masa abinda yakeso tun kafin wani abu ya sameshi, sannan itama waccen yarinya tata matsalar tamafi tasa domin ita harta kamu da ciwon zuciya sbd matsananciyar damuwa" "Wacece ita"? daddy ya fada Yana kallon likita, "Nima bansanta ba da alamar baiwace dannaga tufafin bayi ajikinta, saidai a yadda naga yanayin jikinta ko kadan batayi Kama da bauwa ba domin Babu alamar wahala koka Dan ajikinta" "Zamu iya ganinta kuwa" Daddy ya fada Yana kallon likita, "ehh zaku iya zuwa tama farfado" tashi sukayi sukaje dakin da take.. Zaune take akan gadon hawaye nabin kuncinta, tana ganin ummi gabanta yayi mummunan faduwa, hawayen da takeyi tuni suka bace sbd tsabar tashin hankali.. Itama ummi kallon ta takeyi da sake sake azuciyar ta.. Saurin mikewa Afra tayi ta russuna kasa ta duke kanta Dan ummi ta daina kallon ta, gai shesu tayi cikin girmamawa kamar yadda taga kuyangi nayi. Daddy ne ya amsa cikin sakin fuska domin shikan yaji yarinyar ta kwanta masa arai, dama khamal zai yadda daya hada auren su .. "Kamar nasanki ko" ummi ta fada tana kallon Afra dake sunkuye a kasa, dago kanta tayi ta kalli ummi tace "a'a ranki ya dade kila da kamace kawai kika gani" Hmmmm numfashi ummi ta sauke tace "ba Kama bace Ina tunanin kamar kece Afra wadda akaso Nasir ya aura" Rassssss gaban Afra ya hau dukan uku uku cikin inda inda tace aaaa' aaaa rannnnnnki ya daddddde bani bbbace Ina gggganin kama ce kawai, Ni sunana Hajara iyayena a cikin wani kauye suke Wanda ke cikin jahar kaduna", (kauyen su khamal kenan ) "Nima Afra danake mgn acikin garin kaduna take", "ya isa haka gimbiya tunda tace ba ita bace ai shikenan, toma idan itace mezaisa tazo gidannan"? Daddy ya fada. "Ranka yadade wlhi da kaga wannan yarinyar da zaka rantse da Allah itace anan, Kuma zata iya zuwa gidannan sbd batasan cewa Nasir Dan kanwarka bane" "To shikenan koma dai menene ya isa hakanan, ko itace koba ita bace tunda harta zonan babu ruwanmu da ita, tunda ita ta kawo kanta aikin bauta anan" "Amma ranka yadade atunanina yadace asanar da iyayen ta sbd dazu naga ana sanarwarta aginda television" "Bazan sanar da kowa ba, sbd mahaifin yarinyarnan ya wulakanta mu awajen daurin auren, daga karshe ya tafi gida ya barmu kamar wasu wawaye awajen" Yana gama fadar haka ya fice daga dakin, itama umma bin bayansa tayi. Suna fita Afra ta lallaba tabar asibitin, gaba daya cikin tashin hankali..... By Meerah💞💞💞💞 Share plssss 🙏🙏🙏🙏 [3/30, 1:44 PM] Meerah 💞: 🤴🏻🤴🏻🤴🏻 prince khamal🤴🏻🤴🏻🤴🏻 🌹🌹🌹🌹🌹 By 🌹🌹🌹 Meerah💞💞💞 08068971503 ELEGANT ONLINE WRITER'S✍️✍️ Da sunan Allah Mai rahama mai jinkai "Wacece ke" ya fada fuskar sa babu alamun wasa, jikanta har rawa yakeyi sbd tsabar tsoro, shikenan yau asirinta ya tonu, idan iyayenta suka San inda take tabbas bazasu kyale taba, Fuskar ta taji ya taba yanason ya share bakin data shafa , da sauri taja baya tace "ni hadima ce acikin gidannan bansanka ba ban taba ganin kaba ka kyale ni" tana k'okarin guduwa ne yayi saurin riko hannunta, tafiya ya farayi Yana rike da ita, taso k'wace hannun ta Amma ta kasa, Bakin tafki ya tsaya yakalleta baice komai ba ya duka ya d'ibi ruwa ya watsa mata a fuska, nan take bakin ya wanke, murmushi yayi Yana kallonta yace "Afra kenan da kina tunanin zan kasa ganeki ne? Tun ranar Dana fara ganinki nasan kece na kyalike ne kawai dannaga iya gudun ruwanki, Afra meyasa kika gudu ranar daurin auren mu"? "Nasir nasan nayima laifi Amma Dan Allah ka gafarce ni, wlhi zuciya ta tayi nisa a son wanin ka, bazan iya zama dakai ba amatsayin mijina" "Kinsan baki Sona meyasa kika bari aka hada aurenmu, meyasa danazo gidan ku kika nunamin kulawa bayan kinsan basona kikeyiba"? "Niba wata kulawa Dana baka, kawai dai ina ganinka ne na fahimci kamai baka Sona shiyasa naji dadi, harna nuna farincikina" Hmmmmm "Afra kenan agabana kike cewa baki sona ko" kallon ta yakeyi cike dajin zafin kalamanta, batace komai ba "Afra " Ya fada Yana kallon ta "Ni inason ki" da sauri ta d'aga kai tana kallon sa " a'a ni akwai Wanda nake so", "wanene kike so Kuma meya fini dashi da har Zaki gudu ranar daurin auren mu" Mutane ta tsinkaya suna tafowa wajen da suke ganin yarima ne da fadawansa yasa ta tsaya kallon sa danta ga wanene su gimbiya fulani keson kashewa, tunda nesa take ganin kamar khamal dinta Amma ta kasa gasgata hakan, Kallon Nasir tayi tace "wanene wancen Kuma naga kamar wurinmu zaizo" juyawa yayi shima dan yaga wata mgn akansa, murmushi yayi yace "wannan shine magajin wannan masarautar" "magajin masarautar Kuma" cike da mamaki ta fada, "ehh sunan shi khamal Kona ce miki prince Yazeed, yadawo ne bayan tsawon shekaru da batansa tun yana jariri" Taji dadi sosai dajin wannan mgn murmushi ne ya bayyana afuskar ta, Kara kallon sa tayi ganin yakusa kawo wane yasa tayi saurin b'oyewa bayan wata bishiya anan kusa dasu.. "Mekake yine anan nazo wucewa ne natsinke ka shiyasa na tafo" khamal Ya fada yanata faman dube dube kamar Wanda keneman wani abu "yarima lfy dai ko me kake nemane"? "Nasir kanshin turaren Afra nakeji awajennan", "Afra kuma, wacece Afra "? Kallon sa khamal yayi yace "wani yanki ne na rayuwata" ya fada Yana kallon Nasir "Kamal mgn fa mukeyi akan Afra ba akan rayuwar kaba"? "Nasir bazaka gane matsayinta awaje na ne ba, Amma duk yadda kake tunani ta wuce nan" Ajiyar zuciya Nasir ya sauke domin shi duk baya gane wannan yaren "kaga yarima mutafi kawai" Nasir Yafada Yana rike hannun khamal Dan bayason yaga Afra dake labe awajen, shiko khamal sai dube dube yakeyi, ganin haka yasa fadawansa suka ringa dube dube awajen, "wai me kuke nemane" Nasir Yafada Yana kallon su, wani ba fade yace "ranka yadade Nima naji kanshin turaren" k'wace hannun sa yayi yace kaga Nasir yi tafiyarka kawai zan zauna awajennan" Nasir yace "yarima Anya lfyr ka qlau kuwa? Inaga kamar kanada shafar aljanu, bari naje na gayawa Mai martaba, harya fara tafiya khamal yayi saurin rikeshi yace "nifa lfy ta lau Babu abinda ke damuna" To idan har da gaske lfyr ka Lau to mutafi dannaga alamar akwai aljanu awajenna, Nima tunda nazo naji kaina na ciwo" "Nasir wacce hadima ce na tsinkeku tare kafinnazo nan" ajiyar zuciya ya sauke yace "yace wata yarinya ce nagani anan shine nace ta wuce tabani waje nan ba wajen zaman kuyangi bane" Kamal bai Kara cewa komai ba, suka cigaba da tafiya.. Afra na ganin sun wuce ta lek'o tana kallon Kamal harya bace mata, share hawayenta tayi tace "Allah sarki masoyina Ashe Kaine magajin sarki nazo Ina nemanka acikin bayi" By Meerah💞💞💞💞💞 [3/30, 1:44 PM] Meerah 💞: 🤴🏻🤴🏻🤴🏻 prince khamal 🤴🤴🤴 🌹🌹🌹🌹🌹 By 🌹🌹🌹 Meerah💞💞💞💞 08068971503 ELEGANT ONLINE WRITER'S ✍️✍️ Da sunan Allah Mai rahama mai jinkai 🅿️ 2️⃣5️⃣_2️⃣6️⃣ Gimbiya Fulani ce zaune a falo itada jakadiya kowannen su cikin bacin rai, gimbiya tace "Anya yarima yasha gubar nan kuwa"? "Ranki yadade hadimar da tabbatar min cewa yasha gubar, ranki yadade atunanina gara akoma wajen boka ya koma bada wani mgn" Gimbiya tace"Kije kikara karb'o wani, a wannan karon banason a samu matsala" tashi jakadiya tayi don ta cika umarnin gimbiya.. A bangaren gimbiya Nafisa kuwa, jakadiya tayi yawo a cikin masarautar Amma bata ga Afra ba, haka ta koma ta sanar da gimbiya. Gimbiya tace "shikenan jeki kawai gobe zansaka fadawa sunemamin ita duk inda tashiga.. Afra na kwance bisa tsohuwar katifar dake cikin dakin, da sauri Dije ta shigo dakin tace " Hajara yanzu naga jakadiyar gimbiya Nafisa na nemanki" a tsora ce Afra ta kalle ta tace "na shiga uku, Dan Allah Dije karki fadamata Ina nan, wlhi banason komawa gida" kuka tafarayi, Dije dai sai lallashinta takeyi Washe gari Afra kamar bazata fita ba jiki a sanyaye tayi lullub'i ta fita Dan kar a ganeta, kamar yadda tasaba haka taje tayi aikinta tana dawowa akan hanyarta ta haduda fadawa su uku taji tsoron ganinsu sosai, binsu tayi sukaje kamar yadda aka umarce su.. Da sallama ta shiga falon, gimbiya Nafisa ita daice zaune a falon, durkusawa tayi har kasa ta gaisheta cikin girmama, ta amsa gai suwar ba yabo ba fallasa.. Nasir ne zaune a falon sa wayar sa ya dauko ya Kira Abba mahaifin Afra bayan sun gaisa Nasir yace "Abba naga anyi sanarwa jiya cewa haryanzu ba'aga Afra ba" Abba yace "haka ne Nasir muyi nemanta ko ina Amma ba'aganta ba" "Karka damu Abba insha Allah zan nemo ta duk inda tashiga" Abba yaji dadin maganar sa sosai, daganan sukayi sallama, murmushi yayi yace "Afra kenan wlhi dole Zaki aureni ko kina so kobaki so.... Kallon ta ummi tayi tace "Afra zan tambayeki banaso kiyimin karya idan kika kuskura nakamaki da laifin karya to zanyi miki hukunci Mai tsanani, ki gayamin menene dalilinki na zuwa gidannan"? Sunkuyar da kanta kasa tayi yaukam zata fadi gsky koma mezai faru yafaru, "ummi dama nazo nan ne dannnn........ " Tayi shiru kunya ta hanata ida maganar, "Fadamin mana" sukuyarda kanta tayi kasa tace " wanine nazo nema a gidannan" "wanene shi" ummi ta fada a takaice. Cikin jin kunya ta fadawa ummi komai tsakanin ta da khamal Amma bata fada mata garga din da Nasir yayi mata ba ta daice bata son yasan tana cikin gidannan harsai komai ya daidai ta.. Ummi taji dadin lbr da Afra ta bata, saidai bazata ce komai ba sbd bata tunanin Mai martaba zai amince da sake kulla alaka tsakanin sa da mahaifin Afra... Afra tajima a part din ummi, domin ummi taso ta dawo nan da zama ta daina bauta a gidan Amma taki a mincewa, haka ummi ta kyaleta badan taso ba, By Meerah💞💞💞💞💞 [3/30, 1:44 PM] Meerah 💞: 🤴🏻🤴🏻🤴🏻 prince khamal 🤴🤴 🤴 🌹🌹🌹🌹🌹 By 🌹🌹🌹 Meerah💞💞💞 08068971503 ELEGANT ONLINE WRITER'S✍️✍️ Da sunan Allah Mai rahama mai jinkai 🅿️ 2️⃣3️⃣_2️⃣4️⃣ Suna fita daga dakin Afra dakin da aka kwantar da yarima suka je kwance suka tarar dashi, Baba Sanusi da Inna Khadija suka iske cikin shiga ta alfarma, domin bakaramar kyauta maimartaba yayiwa Baba Sanusi ba a ranar da akazo kirasu shida khamal, a wannan ranar ne aka saki Inna Khadija, a cikin masarautar Mai martaba yabasu kayataccen gida. Suna zaune gefensa, cikin girmamawa Baba Sanusi da Inna Khadija suka gaishesu, ummi da Mai martaba sunji dadin ganinsu sosai, sunjima zaune awajen kafin Prince khamal ya farfado. Arfa na fita daga asibitin bata tsaya ko inaba sai dakinsu na kuyangi, gabanta sai faduwa yakeyi, Dije dake kwance saman katifar dake cikin dakin ta kalle ta tace " Hajara lfy kuwa na ganki duk a firgice" bata ida mgn ba saiga Nasir ya banko kofar dakin da karfi. "Keee!! Fita kibamu waje" Yafada cikin bacin rai Yana kallon Dije, tuni jikin ta yafara makarkata sbd tsoro, da sauri ta fice daga dakin. Kallon Afra yayi fuska daure yace "meye tsakaninki da Yazeed"? shiru tayi bata bashi amsa ba, tsawa ya daka mata da sauri ta kalle shi a tsorace, " nace wanene Yazeed a wajenki"? Kauda kanta tayi gefe itama ta daure fuska tace "masoyi nane Kona cema mijin da zan aura" A jiya zuciya ya sauke, aransa yanajin kamar ya shaketa sbd kishi, kallon ta yayi yace "bazaki aure shiba matukar Ina nufashi aduniya wannan alkawari nane" murmushi tayi Wanda hausawa ke cewa yafi kuka ciwo, tace "wlhi baka isa ka hana aurena da khamal ba, shinake so Kuma shi zan aura, a gabanka za'a dauramin aure dashi" "Shikenan kije ki aure shi, nikuma nayi miki alk'awarin saina saka rayuwar Yazeed cikin matsananciyar damuwa, Kuma kisani wlhi duk ranar da kika sanar da Yazeed ko Mai martaba dalilin zuwanki gidannan nikuma a ranar zan sanar da mai martaba da duk bayin dake cikin gidannan cewa khamal fasiki ne, mai saka alkhairi da mugunta, zan fadawa kowa cewa khamal ya yiwa kanwar sa cikin shege, 'yar wadanda suka reneshi tunyana jariri, suka ciyar da shi, suka tufatar dashi, suka ilman tarda shi, suka nuna mishi so da kauna, karkiyi mamakin sanin wannan lbr danayi domin mahaifinki ya fadamin dalilin da yasa yaki aura mikishi" Kuka Afra ta farayi tana rokonsa dayayi hakuri ya barta ta auri Wanda take so, Amma yak'iya yace dole ta aure shi koyasa Mai martaba ya kori khamal daga gidan, daga hakanan ya fice ya barta nan tana kuka... Ummi ce zaune a k'aya taccen falon ta, ta kasa zama ta kasa tsayi, ita dai bata yadda da zuwan Afra gidan ba kota halin yaya tana sonjin dalilin zuwan ta gidan, babban abinda ke daure mata kai shine lkc daya prince khamal da ita suka yanke jiki suka fadi kuma likita yace duk abu gudane ke da munsu, to meyake faruwane? tabbas akwai wani abu, kallon jakadiya tayi da shigo warta kenan falon, amsa mata sallama tayi tace, "jakadiya inason ki binci komin wata yarinya acikin masarautar nan wadda aka Kai asibiti tare da Prince khamal", "angama ranki yadade" jakadiya ta mike Dan cika umarnin gimbiya Nafisa... Khamal ne keta faman safa da marwa a dakinsa, hawaye na bin fuskarshi, shikade yasan irin radadin da yakeji acikin zuciyar sa, yanason yaje nemanta Kuma yana tsoron bayyanar sirrin sa a wajen iyayen sa, zama yayi a bakin gado yana tunanin inda zai samu mafita, tunawa yayi da kyautar da Afra ta bashi lkcn da suka rabu, da sauri ya mike tsaye yaje ya dauko ledar, murmushi yayi Yana bin ledar da kallo cikin farinciki, zama yayi yana shirin budewa saiga Nasir yashigo dakin, aje ledar yayi Yana amsa sallamar Nasir dake kokarin shigowa.. Kallon sa Nasir yayi Yana murmushi Wanda hausawa kecewa yafi kuka ciwo domin shikadai yasan radadin da yakeji a zuciyar sa, "ya jiki" Yafada Yana kokarin zama kusa dashi, "naji sauki" khamal ya fada Yana kallon sa, "Nasir meyake damunka naga yanayin ka ya cenza gaba daya, Kuma meyasa bangane ka asibiti ba har aka sallameni", "Banajin dadin jiki nane" Nasir ya fada yana kauda fuska gefe, "meyake damunka? Meyasa bakaje kaga likita ba? kayimin bayani idan bakason zuwa asibiti saina dubaka a gida" "A'a yarima rashin lfy ta baya bukatar ganin likita" dafa kafadar sa khamal yayi yace Nasir ka gayamin damuwar ka, ni Dan uwanka ne Kuma aminin ka" Kallon sa Nasir yayi yace "yarima ciwon so ne yake damuna, na fada cikin soyayyar wata yarinya" murmushi khamal yayi yace "matsalar mu daya ce nida Kai, Nasir saidai Kai kanada damar da zaka mallaki abinda kake so amma ni banida wannan damar" Gyara zama Nasir yayi yace "khamal tawa matsalar tafi taka sbd Kai wadda kake so tana sonka Amma ni bata sona, bata kaunata, wani take so daban bani ba" "Nasir meyasa zaka fara son yarinyar da bata sonka"? Kamal ya fada Yana kallon sa, Hmmm "Kamal bazaka gane bane, lkc daya naji nakamu da sonta" ajiyar zuciya khamal ya sauke yace "me sunan yarinyar Kuma wacece" "Sunan ta Hajara, itace yarinyar da aka fasa aurena da ita" kallon sa Kamal yayi cikin yanayi Mai wuyar fassarawa yace "Nasir karasa wazaka so sai wadda ta gudu ranar da za'a daura muku aure"? "Kaga kamal mubar maganar nan nizan nemota duk inda take Kuma saina aure ta ko tanaso ko bata so" ajiyar zuciya khamal ya sauke yace " kana da babban aiki a gabanka" daukar ledar yayi ya maidata wajen da ya dauko ta.. "Kamal ya sunan yarinyar da kake so, Kuma a ina take"? Nasir ya fada Yana kallon sa "sunan ta Afra a kaduna take, munason junan mu sosai iyayenta ne suka hanani auren ta" "me yasa suka hanaka aurenta bayan Kuna son junanku"? "Sbd ni talaka ne Kuma d'an k'auye, sukuma Mai kudi irinsu suke so" "haba khamal yanzu Kai babban mutum ne na tabbata matukar zaka koma tabbas zasu baka auren ta akaro na biyu" "A'a Nasir bazai yiyu na koma wajenta ba sbd anyi mata aure" Kallon sa Nasir yayi aransa yace ba'ayimata aure ba yanzu dai za'ayi mata, " ok ni zanje na kwanta bacci nakeji" Nasir ya fada, Yana kokarin ficewa daga dakin Yana murmushin mugunta..... By Meerah💞💞💞💞💞 [3/30, 1:44 PM] Meerah 💞: 🤴🏻🤴🏻🤴🏻 prince khamal 🤴🤴🤴 🌹🌹🌹🌹🌹🌹 By 🌹🌹🌹 Meerah💞💞💞 08068971503 ELEGANT ONLINE WRITER'S✍️✍️ Da sunan Allah Mai rahama mai jinkai 🅿️ 2️⃣7️⃣_2️⃣8️⃣ Zaune yake a garden sassanyan isaka na kadawa tare da bugun zuciyar sa, da nesa ya tsinki fadawa na tafe dare da Afra wadda ya aika a kiramasa ita. Zama tayi nesa dashi kadan, kallo daya zakayi mata kasan tana cikin bacin rai, murmushi yayi yace "amarya ta ba mgn"? Ko kallon sa batayi ba balle yasa ranzata bashi amsa, matsawa yayi daf da ita ya rike hannun ta Yana shafawa cikin so da kauna yace "Afra nasan baki Sona a yanzu inason kiyi hakuri ki bani damar mallakar zuciyarki ina tabbatar miki cewa wata rana zaki soni fiye da yadda nake sonki" Wani kallon raini tayi masa tace " Nasir wlhi bazaka taba samun abinda kake so ba a wajena dan bana sonka bana kaunarka, ni d'an uwanka nake so Kuma shi zan aura, Ina tabbatar ma cewa baka isa ka hanani auren khamal ba wlhi" saukar mari taji a kuncenta cikin zafin rai ya mareta har Yana shirin kara mata wanine tayi saurin kaucewa. "Karkiyi tunanin ganin Ina lallabaki zaisa ki dinga fadamin maganar da duk tazo bakinki, to baki isaba Kuma bazan lamunta ba, Kuma wlhi duk lkcn da kakiyi kokarin hana aurena dake to wlhi sainasa mai martaba ya kori khamal daga masarautar nan" Yana gama fadar haka ya tafi yabarta nan sai faman kuka takeyi, tana nan zaune a wajen ta tsinki prince khamal tafe tare da fadawansa da kanwar sa khairat, da sauri tabar wajen tun kafin suganta. Kamal na isowa wajen ya tsaya cakk Yana dube dube, khairat tace "yaya lafiya kuwa? Meyake damunka"? Kirjinsa ya dafe yace "khairat inajin kamar Afra tana wajennan" kallon sa tayi cikin rashin fahimta tace "yaya wacece Afra Kuma" baice mata komai ba ya fara dube dube lungu da sako, Suma fadawan neman ta sukeyi awajen, ita dai khairat binsu da kallon mamaki kawai takeyi.. Sun dauki tsawon lkc suna neman ta har wuraren da ke makwaf taka da wajen Amma babu ita babu lbrn ta, jiki a sanyaye ya zauna a wajen, kallo daya zakayi masa kasan Yana cikin damuwa sosai.. Tunawa yayi da cewa Afra ta b'ata yanzu haka ba'asan inda take ba, wasu zafafan hawaye ne suka gangaro a lallausar fuskar sa, lkc daya Kamal ya cenza gaba daya, wani zazzabi ne ya taso masa nan take jikin sa ya dau zafi, da kyar da taimakon fadawan sa da kanwar sa ya isa part din ummi.... Yana shiga dakin ya kasa zama ya kasa tsayi magana yakeyi a zuciyar sa, yanzu kamar ni Nasir ace wata mace ta kalleni tace wai bata sona, hmmmm wlhi Afra baki isaba dole Zaki soni, dole ki aureni, bazan taba bari ki auri wancen shashashan ba, wayar sa ya dauko ya daddana ya Kara a kunnen sa, gaisawa sukayi da mahaifinsa cikin so da kauna yace "Dad dama akan maganar wannan yarinyar da kukeson hada aurena da ita" banji abinda akace ba a daya bangaren naji dai yasake cewa "Dad wlhi nakamu da matsanancin son yarinyar nan, Dan Allah Dad kusake nema min aurenta a karo na biyu" Cikin zafin rai naga yayi jifa da wayar da alama dai mahaifinnasa bai amince da bukatarsa ba. Zaune ummi take tare da hadimanta sunayi mata fifita dayar Kuma tana ciremata b'awan ayaba tana mika mata, ganin prince khamal tayi fadawa sunshigo rike dashi, da sauri ta mike tsaye taje ta karbeshi ta rungumeshi tace "son meyake damunka jikinka yayi zafi hk" zaunar dashi tayi a saman kayatattun kujerun falon, ta kalli khairat tace" meya sameshi haka naga yanzu fa kuka fita dashi lfy Lau"? " Ummi nima bansan meyake damun yaya khamal ba, daga zuwanmu fa garden yace yaji kanshin turaren Afra, yafara dube dube a wajen daga nan Kuma sai zazzabi".. Jinjina kai ummi tayi ta fahimci komai, Amma batace komai ba, cewa kawai tafi fadawa suje su dauko mota a tafi a sibiti dashi, babu bata lkc ko aka tafi dashi cikin kankanin lkc likita yayi masa allurai daban daban, yajima yana bacci sakamakon allurar da akayi masa kafin ya farfado, Gimbiya fulani ce tare da jakadiya sunata faman kulle kullen su ta yadda za'a sakawa prince khamal guba acikin abinci wadda boka ya koma basu, shawara sukeyi ta yadda za'a sake saka masa ita, Wanda yayi daidai da shigowar Afra falon, sunji tsoron ganinta amma dayake sunada karfin iko saisuka danne cikin tsawa gimbiya tace "keee meya kawoki nan a daidai wannan lkc"? Kara shigowa Afra tayi cikin izza da kasaita tace "nazo nanne danna taimaka muku, dazu naji Kuna mgn cewa zaku sake bawa wata aikin daban sbd baku yadda da waccen ba, to nizanyi, ni zan zubawa yarima wannan gubar matukar zaku samamin hanyar da zan iya shiga part dinshi" Ajiyar zuciya jakadiya ta sauke tace "indai wannan ne toba damuwa kibani nan zuwa gobe zanbi duk hanyar da zanbi danki shiga part din" fulani dai batace komai ba sbd ta yadda da jakadiyar ta 100% Yana farkawa daddy ya kalleshi yace "son wacece wannan afrar ne datake son ta cutarmin da gudan jinina", murmushin yake yayi yace "Daddy itace wannan yarinyar wadda nabaka lbrn ta kwanaki" tashi yayi yana kokarin ficewa a dakin ummi tace "son ina zakaje Kuma kaida baka da lfy"? Murmushi yayi Wanda ya Kara fito da kyansa fili yace "ummi naji sauki fa sosai lafiya ta Lau" itama murmushi tayi tace "duk da haka kadawo ka zauna zamuyi mgn dakai" baice komai ba ya dawo ya zauna, ummi ta kallesa tace "son kayi mana bayanin komai gameda yarinyar gobe insha Allah zamuje munema maka aurenta" gabansa ne yayi mummunan faduwa da sauri yace a'a basai kunje ba sbd tariga tayi aure" A jiyar zuciya Nasir ya sauke jin furucin khamal lallai dolene ya tashi tsaye idan ba hakaba yanaji Yana gani zai rasa Afra..... By Meerah💞💞💞 More comments more typing [3/30, 1:44 PM] Meerah 💞: 🤴🏻🤴🏻🤴🏻 prince khamal 🤴🤴🤴 🌹🌹🌹🌹🌹 By 🌹🌹🌹 Meerah💞💞💞💞 08068971503 ELEGANT ONLINE WRITER'S✍️✍️ Da sunan Allah Mai rahama mai jinkai 🅿️ 3️⃣1️⃣_3️⃣2️⃣ Zaune khamal yake tare da Baba sanusi a gidan sa dake cikin masarautar, sbd Baba Sanusi yace masa yana son mgn dashi shiyasa ya bishi gidanshi, kallon sa yayi yace "Yazeed inason ka tsaya ka natsu akan abinda zan gaya maka, khamal na yarda da tarbiyyar ka halayenka da dabi'unka, inason kasan da cewa wannan masarautar tanada ka'idodi, dole ne ga duk Wanda zaizama sarki a sameshi da nagarta, wannan masautar batayi sassauci ba ga duk wanda yake shirin zama sarki kuma aka kamashi da laifi wanda zai iya zubarwa da masarautar nan mutunci, hukuncin da akayanke akansa shine kora domin bazai gaji sarki ba Kuma 'ya 'yan sama bazasuyi sarauta ba, kaji wannan kadan kenan daga cikin hukuncin da aka tana darwa wanda ya aikata wani mummunan laifi, sannan bin doka wajibine ga kowa musamman ma sarki dole yabi doka Koda kuwa shikad'aine d'ansa" Khamal kam jikinsa yayi sanyi sosai duk da sanyin ac dake ratsa ko Ina a falon bai hanashi yin gumiba muryar Baba Sanusi yaji yana cewa "khamal inason kafadi gsky gobe komai dad'inta komai d'acinta kada kaji tsoro" khamal kam bai iya cewa komai ba, sunjima a wajen Baba Sanusi yana kara masa karfin gwaiwa, da bashi shawar warinda suka dace dashi, daga hakanan sukayi sallama. A bangaren gimbiya fulani kuwa jakadiya tagama komai Afra kawai ake jira ta kaiwa yarima abincin sa na dare, babu b'ata lkc ko ta shirya tsaff saidai kuma tanajin matsananciyar damuwa, har zata fita ta tunada gargadin da Nasir yayi mata akan karta kuskura ta bayyanawa Kamal kanta idan kuma taje to tabbas zai gayawa kowa abinda khamal ya aikata, gabanta ne ya shiga dukan uku uku nan take tsoro da fargaba suka kamata, Kuma ba damar taki cika umarnin gimbiya fulani, jiki ba kwari ta dauki bakin abinda take shafawa a fuska ta saka nikaf ta fita.. Zaune khamal yake a k'ayataccen falon sa, dumawa da kunci sunyi masa yawa, har cikin ransa yanajin kunyar yadda zai bayyanawa mutane cewa kazafi akayi masa bashi ya aikata ba, hawayen daya ke gangaro masa ya share, da sauri ya daga kansa danjin kanshin turaren Afra a cikin falon sa, tsaye ya mike yafara takawa zuwa inda take tsaye, ita Kuma mutuwar tsaye tayi ta kasa daga kafarta, muryar shi taji Yana cewa " Afra kece " ya fada Yana murmushi, har cikin ransa yakejin farinciki, hannu ya daga dan ya cire mata nikaf d'in. A razane yaja baya da karfi ganin yadda fuskarta ta koma abin tsoro, tana ganin ya razana tace "khamal kada kaji tsoro nice Afra d'inka nice Afra, ganin sa kawai tayi yana kokarin zubewa a wajen, da sauri ta rikeshi ya fada jikinta ba numfashi, ta tsorata sosai da ganinsa haka, ihu ta kurma duk fadawan part dinsa suka shigo da karfi, Kama Afra sukayi suka sakata a kurkuku shi Kuma khamal aka wuce dashi asibiti. Nasir yaji dadi sosai da ganin halin da khamal yake ciki domin shi a wajensa wata babbar damace awajensa, a fili ya furta, Allah ya kaimu gobe khamal tabbas gobe zaka fada cikin tarkona, wata mahaukaciyar dariya yayi irinta mugayen mutane idan suka ga alamar nasara.... Ummi najin halinda d'anta yake ciki da sauri tanufi asibiti, tana zuwa ta tarar likita na dubashi, dole ta hakura badan tasoba ta zauna jiran fitowarsa tana nan zaune saiga Mai martaba da gimbiya fulani har da Nasir da sauran fadawan sarki. Likita ya tabbatar musu cewa lfy Lau yake torone kawai saidai yayi masa allurai masu karfi zai iya dadewa bai farka ba. By Meerah💞💞💞💞 https://chat.whatsapp.com/CdUQrjfQGnNKkl6cH8WwUL [3/30, 1:44 PM] Meerah 💞: 🤴🏻🤴🏻🤴🏻 prince khamal🤴🏻🤴🏻🤴🏻 🌹🌹🌹🌹🌹 By 🌹🌹🌹 Meerah💞💞💞 08968971503 ELEGANT ONLINE WRITER'S✍️✍️ Da sunan Allah Mai rahama mai jinkai 🅿️ 2️⃣9️⃣_3️⃣0️⃣ Mai martaba yayi gyaran murya yace "Yazeed dole ne kagaya mana inda yarinyar nan take domin bazamu iya ganinka cikin wannan halin ba mu kyaleka" baice komai ba, fulani dake zaune a wajen tace "ni a ganina a kira wannan dattijon da aka samesu tare wata kila ya fadamashi wata magana game da yarinyar nan" gimbiya Nafisa tace "hakane gimbiya tunda munyi munyi ya fadamuna yaki, Kuma yakasa cire ta aranshi" Mai martaba yasake kallon khamal a karo na biyu yace "son yanzu kana ganin matsayi na a wajenka da kima ta basu kai ka gayamin damuwar ka ba"? Jiki a sanyaye khamal ya kalli iyayen sa da Nasir dayake zaune a wajen tundazu baice komai ba, a hankali ya buda bakin sa yace "daddy ummi, ya kalli gimbiya fulani yace yace mamy banida kowa a duniyar nan a yanzu sama daku kune farinciki na, ku nake kallo naji sanyi a raina, idan ina tare daku to banida wata damuwa a rayuwa ta, tabbas kune kuka haifeni, yayinda wasu suka raineni, suma Ina matukar kaunar su a rayuwata sbd sunban kulawa sosai, sun Saida kadarorinsu dannayi karatu, sun sadaukar da farincikin su dannayi murmushi, ya kalli Daddy yace gobe zan fadamuku komai game da rayuwa ta, bazan boye muku komai ba" Ummi ta kalle shi cikin so da kauna tace ni Kuma gobe zan bayyana maka wani abu Wanda zai sanyaka cikin dauwa mammen farinciki" Kowa yayi murmushi dajin kalaman ummi Banda Nasir dayake ta faman hada gumi, tabbas dole yasan abinyi kafin gobe, itama fulanin danata tunanin da takeyi aranta domin tabbas dole burinta ya cika kafin gobe..... Baba Sanusi ne zaune a fada a gaban Mai martaba yace "ranka yadade a ranar da prince khamal ya kwana gidana bai fadamin komai ba akan rayuwar sa ya dai cemin wadanda suka raineshi sun rasu" Mai martaba yayi gyaran murya yace "sanusi inaji ajikina akwai lbr maradadi Wanda d'ana yake b'oyewa bayason musani, ni babban damuwa ta itace kardai a ce wani abune ya aika ta sbd kasan wannan gidan namu bama barin abin kunya komai kankantar sa, Kuma a ka'idar wannan masarautar dole ne Wanda zai gaji sarki yakasan ce nagar taccen namiji, dokace wadda muka gada tun kaka da kakkani cewa duk wani magajin sarki ya kuskura ya aikata wani abu Wanda zaisa kimar masauratar nan ta zube to wajibine a fitar dashi daga wannan masarautar, domin bazai gaji sarki ba Kuma 'ya 'yansama bazasuyi sarauta ba" 🤔 Mai martaba ya ida maganar ne hawaye na gudana a fuskar shi, yasake cewa "yanzu mekake tunani kenan idan akace khamal ya aikata wani abu Wanda zaisa a yimasa wannan hukuncin" kukane yaci karfin mai martaba sbd tausayi da kaunar danna shi.. "Kayi hakuri ranka yadade inaji a jikina yarima bazai taba aikata maka mancin haka ba domin yaron kirki ne duk da ba dadewa nayi tare dashi ba amma na fahimci yana da riko da addini sannan ga ladabi da biyyaya, sannan baya kula kowa musamman ma mata domin ko hadiman dakeyi masa hidima baya kulasu, ranka yadade insha Allah gobe zakaji alkhairi daga bakin mafi soyuwa awajenka, Kuma farincikin ka" Mai martaba yaji dadin kalaman Baba Sanusi sosai, domin shima zai iya bada shaida akan yarima saidai bazai iya kareshi ba idan har wani mummunan abu ya aikata, sbd dokar wannan masarautar ce, babu wani sarki da ya isa yataka wannan dokar komai sonda yakewa d'ansa" Zaune take tana kuka tana juya gubar data amsa a wajen jakadiya a hannun ta sbd tasamu ganin Rabin ranta, kuka takeyi sbd tsabar fargabar abinda zai faru da ita bayan taki cika umarnin gimbiya fulani, tana cikin hakane wani tunani yafado mata a rai da sauri ta tashi tsaye taje ta samu wani busashshen iccen sarbejiya ta daddake shi ta kulle a leda, taje ta zuba wannan gubar a cikin dankaramin toilet dinsu ta dawo ta zauna cikin farinciki.. Nasir ne nagani yanata faman safa da marwa acikin dakinsa sai faman kiraye kiraye yakeyi a waya saidai yahana na dauko muku rahoto domin ya kulle kofar, ta jikin kofar na tsaya dannaji meyake shirin aika tawa... Da sauri na ga ya fito ya nufi dakinsu Afra, zaune ya iska mata, fuska a daure yace ki shirya gobe zamuje gidanku Kuma a giben za'a daura muna aure" yana gama fadar haka ya fice da sauri... A jiyar zuciya Afra ta sauke tace lallai dolene na cika aikina kafin gobe, dolene na bayyana a gaban khamal kafin gobe... By Meerah💞💞💞 [3/30, 1:44 PM] Meerah 💞: 🤴🏻🤴🏻🤴🏻 prince khamal🤴🏻🤴🏻🤴🏻 🌹🌹🌹🌹🌹 BY 🌹🌹🌹 Meerah💞💞💞 08068971503 ELEGANT ONLINE WRITER'S✍️✍️ Dasunan Allah mai rahama mai jinkai 🅿️ 3️⃣3️⃣_3️⃣4️⃣ Washe gari Afra ta tashi da matsanan ciyar fargaba, da fuduwar gaba, a zuciyar ta takejin kamar wani abu ya faru da kamal ko yana shirin faruwa dashi, lkc guda ta rude tafita hayyacinta, gashi an tsare ta a kurkuku babu damar taje taga halin daya ke ciki, adu'a tashigayi tana rokon Allah ya kare mata masoyin ta kamal, wasu zafafan hawaye ne ke gudana a fuskar ta.. Khamal yana kwance haryanzu bai farfado ba daga nannauyan baccin dayakeyi, karfe 10:00am Daddy da ummi harda mamy da Nasir duk suna cikin dakin da aka kwantar da khamal suna jiran farfa dowarsa, wani bafade ne ya shigo ya faɗi kasa yayi gaisuwa ga mai martaba da gimbiya yace "Allah ya baka nasara yanzu wani mutum yazo yace yana son mgn dakai" Batare da ɓata lkc ba mai martaba ya bada umarnin a shigo dashi, da sallama ya shigo ya faɗi kasa yayi gaisuwa kamar yadda aka saba a masarautar yace "Allah ya taimaki sarki nazone da wani babban lbr mara daɗinji", hawayen munafurci ya share, kowa ya matsu yaji abinda mutumin zaice, shikuma Nasir sai fama murmushi yakeyi, mutumin yace "Allah ya baka nasara wani mummunan lbr ne akazomin dashi shine nace bari nazo na sanar dakai halin da akeciki" cikin kusawa da sonjin lbrn mai martaba yace "kafadamin meke faruwa" Mutumin yace "ranka ya dade wani mutum ne dazomin da lbrn wai prince khamal korar sa akayi daga kauyen su adalilin kamasa da akayi da laifin yiwa kanwar sa cikin shege ƴar waɗanda suka reneshi" Innalillahi wa inna'ikaihir-raji'un kowa yake mai maitawa acikin dakin, tuni mai martaba tari ya sark'eshi daga nan ya zube a wajen sumamme. Ummi kan kuka ba'a magana a wajen, harda mamy dake kukan farinciki, suma kannen khamal khausar da khairat da suka shigo daga baya sunji komai, suma kuka sukeyi sosai, Nasir kam ko alamun hawaye babu a idanun sa. Koke koken da akeyi ne a wajen yayi sanadiyar farkawar khamal, yashiga damuwa sosai ganin suna kuka, dubawa ya karayi sosai baiga Daddy ba, a tunanin sa wani abune yasame shi shiya sa kowa ke kuka, shima babu ɓata lkc ya shiga rera kukan sa, ba tare da ya tambayi kowa ba abinda ke faruwa... Likitoci sundade akansa kafin su samo numfashin sa ya dawo nomal, haka suka yini acikin a sibitin kowa sai kuka yakeyi, sai marece aka sallami Daddy, kai tsaye fada suka wuce domin Daddy yace kowa yaje cen yanada mgn, ciki ko harda mutumin daya zo da wannan mgn.... Bayan kowa ya hallara a fada, mai martaba ya umarce mutumin daya sake mai maita abinda ya faɗa, babu ɓata lkc mutumin ya mai maita kamar yadda ya faɗi a baya, gaban khamal ne ya shiga dukan uku uku kunya duk ta kamashi, tabbas yau itace ranar da yake gudu tuntuni, yauce ranar tonon asirinsa, muryar Daddy yaji yana cewa "khamal kaji duk abinda ya faɗa"? wani gumi daya taso masa a gushi ya share, aransa yace yau komai zai faru saidai ya faru zan fadi gskyr abinda nasani, "ehh Daddy naji abinda yace" ya faɗa kai tsaye "gsky ne ko ba gsky bane"? Daddy ya faɗa yana kallon sa, "ehh Daddy gsky ne amma.............. " daka tarda shi Daddy yayi yace bana bukatar jinkomai daga bakinka, ka tashi ka fice ka barmin gida bana bukatar ganinka acikin gidannan" yana gama faɗar haka ya tashi ya fice. Ummi tasowa tayi tanata faman rusa kuka kamar ranta yafita, tace "khamal meyasa ka aikata wannan abun? meyasa ka aikata abinda zaiyi sanadiyyar nisan tani dakai?, khamal meyasa zakayi wannan mummunan aikin bayan kasan wannan masarautar ta yanke hukuncin korar duk wani yarima daya aikata irin wannan abin" kara rungumeta yayi yace "ummi ban aikata ba wlhi sharri akayimin" yana mgn yana kuka kamar ransa zaifita, sundaɗe a haka kafin khamal yayi karfin halin tashi ya nufi part dinshi, kayansa ya shiga har hadawa yana gamawa ya dauki jakar har yakai bakin kofa ya yatuna da kyautar da Afra tayi masa, da sauri yaje ya dauki ledar yana kallon ta yana mumushi, mota ya shiga ya tadata ya fara tafiya batare daya san inda ya dosa ba, harya fice daga gidan Daddy na kallon sa asaman bene, har cikin ransa yanajin zafin rabuwa da ɗansa, amma ba yadda ya iya wannan dokace yazama dole ya yanke hukunci kafin hukuncin ya dawo kansa, hawayensa ya share yace ina matukar kaunarka khamal Allah ya tsaremin kai a duk inda zakaje ... Afra ko tana cen tana kuka tana faman bubbuga kofar kurkukun amma bawanda ya kulata acikin fadawan, a haka ta kwana har gari ya waye... BY MEERAH💞💞💞💞💞 [3/30, 1:44 PM] Meerah 💞: 🤴🏻🤴🏻🤴🏻 prince khamal 🤴🏻🤴🏻🤴🏻 🌹🌹🌹🌹🌹 BY 🌹🌹🌹 Meerah💞💞💞💞 08068971503 ELEGANT ONLINE WRITER'S ✍️✍️ Dasunan Allah mai rahama mai jinkai 🅿️ 3️⃣5️⃣-3️⃣6️⃣ Tana cikin bacci taji alamar taɓa kofar, da sauri ta mike tana fadin "don Allah ku fitar dani daga cikin wajennan, wlhi ba kashe shi nayi niyyar yiba" baice mata komai ba harya buɗe kofar yace ta fita, da sauri kuwa ta fita harda ɗan gudunta. Tana fita bata tsaya ko inaba sai part ɗin khamal, tana zuwa taga ba kowa a wajen harda masu gadi duk suntafi, tayi tunanin yana fada, kai tsaye cen ta nufa, da zuwanta fadawa suka dakatar da ita suka ce hadimai basa shiga, sbd mai martaba yana ganawa da iyalin sa.. Badan taso ba ta hakura, waje tasamu ta xauna tanajiran fitowar khamal, wani tunani ya fado mata arai nan take ta tashi, ta nufi hanyar fita daga masarautar, tana cikin tafiya taji wasu fadawa na mgnr khamal akan abinda ya faru dashi jiya, wajen su taje ta kara tambayar su, cikin kwarin gwaiwa da son bada lbr suka fada mata komai, kuma sun tabbatar mata mai martaba ya kore shi... Innalillahi wa'inna ilaihiraji'un tayi ta nana tawa a bayyane, duk ta rude tarasa meke mata daɗi kwallar data taru a idon tane ta gangaro, taso ta danne raɗaɗin da takeji acikin zuciyar ta hartaje gidan su Salim amma ta kasa, kuka ta dingayi bakin rai hartaje gidansu Salim... Tana zuwa ko ta iskeshi a gidan tare da mahaifiyar sa, hankalin su ya tashi sosai ganinta cikin wannan halin, tambayar ta suka shigayi, meyake faruwa? Bata boye musu komai ba ta sanar dasu halin da ake ciki, hakuri suka dinga bata harta daina kukan. Dakyar momy ta lallaɓa ta tayi wanka taci abinci. Salim ne ya bata shawara akan taje fada ta sanar da mai martaba cewa khamal bai aikata abinda ake zarginsa da shiba, haka kuwa a kayi shirya wa tayi tsab cikin shiga ta alfarma, key din motar ta ta amsa ga hannun Salim, tana tada motar bata tsaya ko inaba dai fadar mai martaba sarki Ahamd Abdus-salam. Shigarta gidan yayi daidai da fitowar iyalan giban baki daya ciki ko harda mai martaba, tsyawa sukayi cak suna kallon ta daidai wajen da suke ta parker motar ta, ta fito cikin takunta na kasaita da nuna isa, gimbiya fulani na ganinta gabanta ya shiga dukan uku uku, ko kallon ta Afra batayi ba dan bata da lkcn ta, wurin ummi ta wuce ummi na ganinta tazo ta rungumeta, su dukansu kuka sukeyi gwanin ban tausayi.... Mai martaba yace "meya kawoki gidannan? me kikazo nema"? hawayenta ta share ta kalli Nasir da tundaxu ita yake kallo yana hara rarta, kauda kanta tayi gefe kamar ma batasan yanayiba tace "Ranka ya dade, nazo nan ne a dalilin khamal, bansan cewa shi yarima bane saida na dade acikin gidannan ina nemansa" mai martaba yace "mekikazo nema a wajen sa bayan kin gudu daga gidan iyayenki, kenan kinxo nan ne danki kara lalatamin yaro ko"? a jiyar xuciya ta sauke tace "ranka ya dade khamal ba fasiki bane kamar yadda kuke tunani, khamal mutumin kirki ne, baya kula mata, baya shiga sha'aninsu, wlhi sharri akayi masa bai aikata ba, kuma nice silar shigar shi cikin wannan halin, a dalilina akayi masa wannan sharrin baijiba bai gani ba"...... Duk wajen kowa ya maida hankalinsa wajen ta, ita kadai ake saurare, mai martaba yace "meye alakarki dashi dahar kika jefashi cikin wannan halin"? Tace "ranka ya dade yanxu xanbaku lbrn kamal tundaga kuruciyar sa" sunji dadin mgnr ta sosai hakan yasa mai martaba ya bada umarnin kowa ya koma cikin fada danjin lbrn kamal.... **** KHAMAL****** Khamal yaro ne mai kokari da hazaka tunyana karami, Baba Sani shine ya tsinci khamal a cikin daji, yaji dadin ganin yaron sosai, sbd Allah bai basu haihuwa ba shida matar sa Inna Laure, sun shafe tsawon shekaru masu yawa dayin aure amma ko ɓatan wata bata taɓa yiba, wannan ne dalilin dayasa sukaji dadin tsintuwar yaron a cewar su, suma yanzu sun zama iyaye, sun nuna mushi so da kauna tamkar ɗanda suka haifa da cikin su, sun sashi makaranta sbd sunga yanada kokari da hazaka, duk da cewa a kauyen ba wanda ya damu da yayi karatun boko. Haka rayuwarsa ta kasance harya kammala karatunsa na primary, babu ɓata lkc suka biya masa yaje makarantar kwana (boarding) yana aji biyu ne Allah ya bawa Inna Laure ciki ta haifi ɗiyar ta wadda taci suna Saude, haka rayuwa taci gaba da tafiya har khamal ya gama secondry, bayan saka makon jarabawar su yafito, khamal yaci jarabawar sosai, bakaramin daɗi iyayensa sukajiba saidai suna son yaci gaba da karatu amma basu da zarahi Saida khamal yayi shekara ukku da gama secondry sannan Allah ya bawa Baba Sani ikon samun amfanin gona mai yawa, sune yasaida harda ɗayan gonarsa, yacika ya biyawa khamal yayi karatu, inda ya karance bangaren (health). A haka rayuwar sa ta kasance, yana gab da kammala karatu ni kuma na shiga skull din course daya muke karatu da shi, saidai shi ya kusa gamawa nikuma a lkc nafara, ananne Allah ya hadamu muka farason junanmu... Bayan ya kammala karatunsa ne muka yanke shawarar yazo gidanmu danya nemi izinin aurena, saidai anyi rashin sa'a domin mahaifina yace bazai bawa talaka aurena ba, duk da haka bamu rabuba sbd muna tsananin son junanmu, domin kuwa har kauyen su nake xuwa muyi hira, a she kanwarsa Saude tana masifar sonsa tun tana boyewa harta fito fili ta fadamasa, yace mata shi yanada wadda yake so kuma ita xai aura, wannan furucin yayi matukar ɓatawa Inna Laure rai, daga nan suka dinga shiga bokaye dan khamal ya farason Saude, saidai hakan bata faruba domin nidashi kullum kara sonjunanmu mukeyi.... Inna Laure macece mai masifar son abin duniya wannan dalilin ne yasa ta dinga sa Saude karɓar kudin samari, da hakane tasamu ciki, inna Laure bataji haushin ganin cikin ba sbd tana tunanin wata damace suka samu wadda Baba Sani zai tirsasa khamal auren Saude, saidai basuci nasaraba domin Baba naji abinda ya faru saiya kori khamal batare da yayi bincike ba.... A yanxu haka nasan wanda yayi mata ciki, wani saurayinta ne mai suma Dauda, shiya fadamin da bakinsa cewa shine yayi mata ciki" Dogon numfashi Daddy ya sauke lkc ɗaya yaji kewar ɗansa ta dawomai, meyasa shima ya yankewa khamal hukunci ba tare da yayi bincike ba...... BY MEERAH💞💞💞💞 [3/30, 1:44 PM] Meerah 💞: 🤴🏻🤴🏻🤴🏻 prince khamal 🤴🤴🤴 🌹🌹🌹🌹🌹🌹 By 🌹🌹🌹 Meerah💞💞💞💞 08068971503 ELEGANT ONLINE WRITER'S ✍️✍️ Da sunan Allah Mai rahama mai jinkai 🅿️ 3️⃣9️⃣-4️⃣0️⃣ Mahaifin Nasir ne ya fara mgn da cewa "da farko dai muna baku hakuri game da abubuwanda suka faru a baya" nan ya faɗa musu duk abinda ya faru tun haɗuwarsu da khamal har zuwan Afra har ɓatan khamal, basu ɓoye musu komai ba, daga karshe yace "munzo nan ne dan nemawa ɗanmu khamal auren Afra, idan ya dawo sai a ɗaura aure", Abba ya ƙara gyara zaman sa yace "bakuyi laifin komai ba, duk abinda ya faru laifinane, nine na matsa sai anyi wannan auren, dan haka ina kara baku hakuri, kuyi hakuri da abinda ya faru, sannan idan har Afra tanason khamal to na bawa ɗanku auren ta" murmushi sukayi gaba ɗaya, mahaifin Nasir yace "muna godiya sosai Allah yasa hakan shiyafi alkhairi". Mai martaba yayi gyaran murya yace "Da farko dai ina nemawa Afra gafara a wajenku, sbd duk abinda tayi tayi ne danta ceci ɗana khamal, nagode!! nagode!! sosai Afra Allah ya taimakeki fiye da yadda kika taimaki ɗana" murmushi Abba yayi yace " ranka yadade Afra batayi muna laifin komai ba, ko kaɗan bamu riketa a zuciyarmu ba sbd laifin mune, nine naso cutar da rayuwarta ta hanyar haɗata da wanda bata so,na gane kuskurena, wlhi a yanzu koda khamal ba ɗan kowa bane zan yadda na aura mata shi tunda shi takeso" Nasir kam yaji haushin mgnr Abba sosai musamman wajen da yace bashi Afra ke soba. Ummi tace " ina neman alfarma a wajenku, inason ku bani Afra na tafi da ita, idan khamal ya dawo sai tadawo ayi mgnr auren su" Ajiyar zuciya Abba ya sauke yace "tabbas da nan da cen duk ɗaya ne a wajena banida matsala da zuwanta cen, saidai inason abari ta kammala kara tunta, idan ta kammala sai ayi mgnr auren su" mai martaba yace "ba komai ta zauna anan taci gaba da karatunta, sannan aure baya hana karatu haka karatu baya hana aure, ko bayan auren zata iya cigaba da karatunta" Kowa ya amince da mgnr mai martaba, antsaida mgn cewa da khamal ya dawo za'a daura auren.... Da haka suka cigaba da hirarsu cikin farinciki, sun dade a gidan kafin sutafi, gidansu Nasir suka kwana, washe gari tunda safe suka nufi garin zaria. Afra kam suna tafiya ɗakinta ta koma ta kira Hashim domin ita ta matsu basu tafiba tasamu taji halin da masoyin ta yake ciki, kira daya ya dauka da sallama, amsawa tayi a takaice cikin raunin murya tace "Hashim ya ake ciki" ajiyar zuciya ya sauke yace" Afra gsky akwai damuwa" gabantane yayi mummunan faɗuwa cikin tashin hankali tace "meya sameshi" saida yayi shiru na ɗan lkc yana tunanin yadda zaifara yi mata bayani,yace "Afra Khmal yana cikin tashin hankali, sbd yana cikin wani daji mai matukar haɗarin gaske, domin duk wasu mugayen mutane acikin dajin suke, sbd yana da wuraren ɓoyo, ba lallai neba ace khamal yana nan raye acikin wannan dajin, idan kuma yana raye to tabbas yana cikin mawuyacin hali". By Meerah💞💞💞💞 [3/30, 1:44 PM] Meerah 💞: 🤴🏻🤴🏻🤴🏻 prince khamal🤴🏻🤴🏻🤴🏻 🌹🌹🌹🌹🌹🌹 By 🌹🌹🌹 Meerah💞💞💞 08068971503 ELEGANT ONLINE WRITER'S ✍️✍️ Da sunan Allah Mai rahama mai jinkai 🅿️ 3️⃣7️⃣-3️⃣8️⃣ Hawayen fuskar sa ya share yace "Allah sarki son kayafemin wannan laifin dana aikata, na kori ɗana, kuma farincikin, tabbas khamal kaine rayuwata idan babu kai to tabbas zan rayune tamkar gawa a cikin duniyar nan, kayi hakuri ka gafarceni na tabka babban kuskure a rayuwa ta" kallon Afra yayi yace "ngd sosai ƴata, ngd da irin kulawar da kika bawa ɗana, bazan taba mantawa da karamcin da kikayi muna ba, insha Allah zaki rayu tare da khamal, ni zantsaya muku komai rintsi, Allah dai ya bayyana shi" kukane yaci karfinsa ya kasa ida mgnr. Itama gimbiya Nafisa kuka takeyi sosai da kyar tayi karfin halin cewa "ranka yadade yanzu ba lkcn dogon surutu bane, kamata yayi kasa anemo munashi duk inda yashiga" Batare da ɓata lkc ba mai martaba ya bada umarnin aje anemosa duk inda yake, haka akayi ko, fadawa da police duk sunbazu ko ina lungu da sako acikin garin zaria, saidai kashhhhh, ba'asame shiba, har ƙauyukan garin saida aka duba amma babushi babu alamar sa... Mai martaba da gimbiya Nafisa sunkara shiga cikin tashin hankali mara misaltuwa, khairat da kausar ma sunzama abintausayi kallo daya zakayi musu kasan cewa sunacikin matsananciyar damuwa... Afra taso ta koma gidansu Salim Amma ummi ta hanata zuwa, badan tasoba ta kwana a gidan cikin kunci da damuwa. Washe gari haka kowa ya tashi a gidan bamai kuzari kowa jan jikin sa kawai yakeyi babu kuzari, shikan Nasir yana cikin farinciki sosai dan a cewar sa gara kowa yarasa, tunda shi Afra bata sonsa Kuma iyayensa sonce ko ita daice nace a duniya bazai aure taba, to shima khamal bazai aureta ba, hmmmm Nasir kenan kamanta da hukuncin Allah kenan. Mamy kam tunda taga Afra taji dalilin zuwanta, hankalinta ya tashi sosai domin ta tabbatar sai Afra ta tona mata a Siri, gashi ta kasa ganinta balle ta roketa ta rufa mata asiri, itama jakadiya duk abubuwa sun da gulemata gaba ɗaya dabararta ta ɓace domin ta tabbata saitaje kurkuku idan asirinsu ya tonu..... Afra ce zaune a ɗakin da ummi ta bata, wanda ke kusa da ɗakin khairat, tunani takeyi taya zata Nemo khamal? Nan take ta tuna da kyautar data bashi, da sauri ta dauki wayar ta tahau Kiran layin amma a kashe, mikewa tayi da sauri ta fita daga d'akin, a falo ta tarar da ummi da khairat zaune kowanne da tunanin da yakeyi. Ummi na ganinta tace "ƴata kinfito"? cikin kulawa Afra tace "ehh ummi" shafa bayan kanta tayi cikin jin kunya tace "ummi inason naje part din khamal na duba wani abu" gyada mata kai tayi alamar tatafi kawai batare da tace komai ba, kallon khausar Afra tayi tace "khausar muje ki rakani mana" tashi tayi tabi bayanta suka tafi. Suna zuwa kai tsaye dakinsa ta shiga ta hau bincike, amma bataga komai ba sai wayar sa dayake amfani da ita, "Aunty mekike nema ne? naga sai bincike kikeyi bakice na tayaki ba" Murmushi tayi tace "wata leda nake nema wadda na bashi lkcn da zamu rabu dashi a k'auye" "leda Kuma Aunty wacce irin leda?, menene aciki"? Murmushi Afra tayi tace "wata babbar wayace aciki da kudin da zaiyi amfani dasu a hanya, shine na bashi danna dinga sanin duk halin da yake ciki, saidai haryanzu bai kunna wayar ba domin nakira wayar kashe shine nazo na duba koya barta a gida, gashi na duba ko Ina bangan taba" "Karki damu Aunty yaya Yana matukar kaunarki bazai taɓa barin kyautar da tafito a wajenki ba, murmushi sukayi cike da kaunar junansu, part d'in ummi suka koma, suna zuwa ummi ta kalli Afra tace "daughter yadace ki koma wajen iyayenki kinemi gafarar su" sunkuyar da Kai Afra tayi tace "dama inason na koma amma nafison sai anga khamal sannan" murmushi ummi tayi irin nasu na manya tace "a'a daughter bazai yiyuba gobe insha Allah zamuje wajen iyayenki, nida kaina zan nema miki gafarar su sannan na nemi alfarmar abani ke kidawo nan har khamal ya dawo" Murmushi tayi ta sunkuyar da kanta, kunya duk ta kamata, ba tare da tace komai ba ta tashi tana murmushi, itama ummi murmushin takeyi, harda khairat dake kallon su ba tare da tace komai ba sai murmushi kawai. Afra na komawa daki ta dauki wayar ta tashiga Kiran Hashim, ring d'aya a nabiyu ya dauka da sallama, ansawa tayi suka gaisa cikin girmamawa, tace masa yasake bincika mata wannan number daya bincika mata kwanaki, nan ta fad'a nasa duk abinda ke faruwa, ya tausaya mata sosai aransa yace " Allah sarki Afra samun masoyiya irinki a wannan zamanin abune Mai matukar wahala, ya tabbatar mata da cewa zai bincika mata. Washe gari Mai martaba da ummi harda khairat da khausar ne suka raka Afra zuwa gida, tare da sauran bayi, motoci biyar suka dauka sai garin kaduna, a gidan su Nasir suka sauka suka tafi tare da iyayen sa harda shi kansa.. Umma da Abba zaune suke a falo cikin kunci da damuwa, wayar Abba ce ta hau ruri ganin sunan Maigadi ne yasa ya dauka a kasalance, yace "kabarsu su shigo ko suwanene" kashe wayar yayi batare da yaji abinda Mai gadi zaifad'a ba. Karar motocine ta cika gidan gaba daya, ganin haka yasa su umma fitowa Dan suga meke shirin faruwa, suna fitowa sukaga motoci sai shigowa sukeyi, galala suka tsaya suna kallon ikon Allah. Afra ce ta fara fitowa da gudu ta karasa wajen iyayenta tayi hugging dinsu, Suma cikin farinciki suka rungumeta suna murmushi, "Afra inakika shiga kika barmu? Kiyi hakuri my daughter naso na cutar da rayuwarki ta hanyar had'aki da Wanda bakiso" Abba ne ya fad'a Yana share hawayen sa, kafin Afra tace wani abu karaf idanun sa suka sauka kan mutanen dake wajen, gabansa ne yayi mummunan faduwa ganin amininsa wato mahaifin Nasir, harda shi kanshi Nasir d'in, daure fuska yayi lkc guda yana shirin yin maganane idanun sa suka sauka kan Mai martaba, zaro idanunsa yayi cikin in ina yace "Afra wanene wannan mai Kama da khamal"? "Ma haifinsane" ta fad'a tana kallon Abba, kunya duk ta gama Kama Abba, gaishesa yayi cikin girmamawa yace su shiga ciki, shiga sukayi kowannen su Yana yaba kyawon gidan da tsaruwar sa, tabbas gidan ya had'u iya had'uwa, ya wadatu da komai na more rayuwa..... By Meerah💞💞💞💞 [3/30, 1:44 PM] Meerah 💞: 🤴🏻🤴🏻🤴🏻 prince khamal 🤴🤴🤴 🌹🌹🌹🌹🌹 By 🌹🌹🌹 Meerah💞💞💞 08068971503 ELEGANT ONLINE WRITER'S✍️✍️ Da sunan Allah Mai rahama mai jinkai 🅿️ 4️⃣1️⃣-4️⃣2️⃣ Kuka takeyi sosai a ɗakinta, wanda yatayar da hankalin su umma dake falo zaune, da sauri suka shigo ɗakin, rungume ta umma tayi tace "daughter meya sameki? me akayi miki"? lkc ɗaya tajera mata tambayoyin. "Umma khamal ne" tayi shiru bata ce komai ba, cikin tashin hamkali umma tace "meya sami khamal ɗin"? "umma waii......." tayi shiru takasa faɗar abinda Hashim ya faɗa mata, sau kuka takeyi, cikin ɗaga murya Abba yace "zaki faɗamuna gsky ko kuwa"? bata ɓoye musu komai ba ta faɗa musu yadda sukayi da Hashim, innalillahi wa'inna ilaihiraji'un kawai su umma ke maimai tawa, jikin umma duk yayi sanyi, hawaye nabin fuskar ta tace duk laifin kane Alhaji daka yadda anyi aurennan tun farko da duk haka bata faruba" Dafa kafaɗar Afra yayi yace ki kwantar da hankalinki ƴata insha Allah zannemo mikishi duk inda ya shiga" kallon sa tayi tace "Abba dan Allah kabarni naje na nemoshi wlhi idan nazauna a gida zuciyata zata iya bugawa" Cikin mamakin ta Abba yace "Afra bakida hankali ne, taya zakice na barki kitafi cikin wannan dajin kina mace, to babu inda zakije, ni zansa a nemosa duk inda ya shiga, saidai banason kifaɗawa iyayensa halinda ake ciki domin na fahimci suna matuƙar sonsa, idan kika sanar dasu zaki iya jefasu cikin wani hali" wayar sa ya ɗauko ya kira police yasanar dasu halinda ake ciki, ya tabbatar musu idanhar suka samo shi a raye to zaibasu makudan kuɗaɗe, yana gamawa ya kalli Afra yace ƴata ki kwantar da hankalinki insha Allah zasu dawo dashi, sundaɗe a ɗakin suna lallaɓata har bacci ya ɗauketa, a ɗakin umma ta kwana tare da ita, tana kula da duk wani motsinta, shima Abba bawani kwanan kirki yayiba domin kusan ma tare suka kwana a ɗakin suna kula da ƴarlelensu... Washe gari Afra ta tashi da matsanancin rashin lfy, ga aman jini datake tayi, da sauri suka dauketa sai a sibiti, likita ya dubata sosai, daga karshe dai ya tabbatar musu tanada ciyon zuciya, idan har ba'ayi mata abinda take soba to zuciyar ta zata iya bugawa, sbd ciwon yaci karfinta.. Yini ɗaya ta share harda dare kafin ta farka sbd magunguna da allurai masu karfi da akayi mata, washe gari da farkawar ta abinda tafara faɗi shine " Abba anga khamal" murmushin karfin hali yayi yace ƴata ki kwantar da hankalinki insha Allah khamal yana cikin koshin lfy, zai dawo gareki" hawaye na bin fuskarta tace " Abba dan Allah kabarni naje neman sa" tunawa yayi da mgnr likita badan yasoba yace "Afra idanna barki kije zakiyi farinciki"? da sauri ta amsa da "ehh Abba, zanyi farinciki sosai" tafaɗa tana murmushi, shima murmushi yayi yace "shikenan dakinji sauki zaki tafi" da sauri ta mike tsaye tace "Abba naji sauki fa lfy ta lau" da kallon mamaki ya bita yace "a'a daughter kibari ki kara jin sauki sai a sallamemu, likita ne ya shigo ya dubata yace jiki yayi kyau sosai za'a iya sallamar su, haka ko akayi Abba ya shirya mata tafiyar tare wasu jami'ai guda biyar, babbar damuwar sa shine haryanxu waɗanda suka je da farko babu su babu lbrn su, badan yasoba haka ya hakura dole ya barsu suka tafi... By Meerah💞💞💞💞 [3/30, 1:44 PM] Meerah 💞: 🤴🏻🤴🏻🤴🏻 prince khamal 🤴🏻🤴🏻🤴🏻 🌹🌹🌹🌹🌹 By 🌹🌹🌹 Meerah💞💞💞 08068971503 ELEGANT ONLINE WRITER'S✍️✍️ Da sunan Allah Mai rahama mai jinkai 🅿️ 4️⃣3️⃣-4️⃣4️⃣ Kwanan su Afra biyu da tafiya shiru babu lbrn su, idan aka Kira wayarta tun tana ringing ba'a d'auka harta Kai saidai aji wayar kashe, iyayenta sunshiga cikin damuwa sosai, Abba ya kira mahaifin Nasir yasanar dashi halinda akeciki, Mai martaba da kansa yazo kaduna ya jajantawa Abba yayi masa alk'awarin zaisa a nemosu duk inda suke. Haka ko akayi Mai martaba ya tura mutane masu d'inbin yawa ciki ko harda fadawa da jami'ai saidai kash Babu lbr mai dad'i sun tarar da gawawwakin Jami an da Abba ya tura akan hanya wasu ko acikin daji Amma basuga Afra ba sunyi yawo sosai a cikin dajin Amma Babu alamar akwai wata rayuwa acikin dajin, da haka suka koma gida jiki Babu kwari suka sanar da mai martaba halinda ake ciki, aranan anyi koke koke a gidan, hakama gidansu Afra abin ba'a mgn.. B'angaren Afra kuwa aranar suna shiga cikin dajin suka tarar da wasu manyan y'an ta adda suka k'wace komai nasu suka kashe Jami an baki daya ita Kuma suka kaita wani bayan dutse suka ajiye ta, shugabansu yayi niyyar keta mata haddi Amma saiya fasa yace sukai ta su ajeyeta, tayi kuka sosai tayi musu magiya su kyaleta Amma fir suka k'i, dare nayi ta duba taga kowansu yayi bacci, a hankali ta dinga tafiya da sand'a tana ganin tabar wajen ta fara gudu, muryar wani taji yana cewa gatacen ta gudu aiko ba shiri ta K'ara gudu, sun dad'e suna biyarta da gudu Amma basu kamata ba, tana cikin gudu tayi tuntub'e da wani dutse ihu ta kurma da k'arfi saida dajin ya amsa, kafarta taji ciwo sosai dalilin hakane ta kasa gudu, juyawa tayi taga wad'annan mutanen da suka biyota suna fad'a da wani mutum kasan cewar duhune yasa bataga fuskar shiba, sundad'e sunayi daga k'arshe dai wannan mutumin yasamu nasarar halakasu gabaki d'aya. Tana nan zaune ta kasa tashi daga wurin da take, ganin mutumin tayi yazo wajenta ya d'auke ta yafara tafiya da ita, tsoro ya kamata sosai zuciyarta bugawa takeyi kamar ta tsage kirjinta. Bayan wani dutse ya kaita ya ajiyeta, d'aure mata k'afar yayi tabar zubar jini, ahankali ya bud'e bakinsa yace "meyasa kika biyoni nan, bakisan wajennan nada had'ari bane" Cikin farinciki tace "khamal dama kaine"? rungumeshi tayi tana murmushi tace "Alhamdulillah yau burina yacika", kallon sa tayi tace wlhi harna cire raina da sake ganinka arayuwata" Murmushi yayi Wanda ya K'ara bayyanar da kyaunsa yace "ni Kuma haryanzu bancire ran sake had'uwa dake ba, saidai k'addara ta gifta tsakanin mu inaji ajikina burinmu bazai tab'a cikaba" "burinmu zaicika acikin kwanakinnan" ta fad'a tana kallonsa da k'aya taccen murmushi a fuskar ta, da mamaki yake kallonta yace "Afra kinsan me kike fad'a kuwa"? tace "nasan komai khamal, nasan duk abinda ke faruwa, Kuma a halin yanzu iyayenka suna nemanka, sunyi nadamar abinda suka yimaka, sbd na fad'a musu gsky cewa baka da laifi" cikin mamaki yake kallon ta yace "Afra ya akayi kikasan iyayena" murmushi tayi tabashi lbrn komai harda abinda ke tsakaninta da Nasir bata b'oye masa komai ba, khamal yayi mamaki sosai domin bai tab'a tsammanin Nasir zaiyi masa haka ba, domin shi ya rikeshi da zuciya d'aya a matsayin d'an uwansa Kuma aminin sa. Baice komai ba sai kokarin mik'ewa tsaye dayakeyi, rik'eshi Afra tayi tace "khamal Ina zakaje acikin Daren nan"? Murmushi yayi yace "zanje na samo Miki y'a y'an itace domin sune kad'ai abinci acikin dajinnan" tace "a'a na koshi kadawo harda safe" yace "a'a kibari yanzu zandawo nasan kinajin yunwa, sbd nasan wad'ancen mutanen basu baki abinci ba" cikin mamaki take kallon sa tace "ya akayi kasan basu bani abinci ba"? tsayawa yayi Yana kallon ta yace "sbd Nima nayi zama a hannun su, basu tab'a bani Koda ruwa ba" ajiyar zuciya ta sauke tace " yanzu dai kadawo wlhi bazan iya zama a wajennan ba tsoro nakeji" jin tace tsoro takeji yasashi dawowa badan yasoba, zama yayi yana tsokanar ta, Haka suka kwana cikin dajin ko wannen su cikin farinciki. washi garima haka suka kasance kowannen su cikin farinciki, a wajen suka yini da sunji motsi da sauri khamal zaisa Afra ta boye shikuma ya haye icce Yana kallon abinda ke faruwa acikin dajin. Sunso fita Amma ba dama sbd kota Ina mugayen mutanen suna zagaye dasu.. By Meerah💞💞💞💞 [3/30, 1:44 PM] Meerah 💞: 🤴🏻🤴🏻🤴🏻 prince khamal 🤴🤴🤴 🌹🌹🌹🌹🌹🌹 By 🌹🌹🌹 Meerah💞💞💞 08068971503 ELEGANT ONLINE WRITER'S✍️✍️ Da sunan Allah Mai rahama mai jinkai 🅿️ 4️⃣5️⃣-4️⃣6️⃣ Zaune suke bakin wani rafi, suna kallon yadda ruwa ke gudana, wurin yayi matuk'ar birge Afra, kallon ruwan takeyi ta mayar da hankalinta baki d'aya a wurin, shikuma khamal hankalin sa na wajenta, ya kulada yadda take kallon wajen, murmushi yayi ya d'ibi ruwa ya watsa mata, zabura tayi da k'arfi ta tsorata sosai, shikuma dariya ta bashi ganin yadda ta zabura, ita Kuma haushin dariyar da yake mata taji ruwa ta d'iba itama danta watsa masa, yana ganin haka ya tashi da sauri, itama tashi tayi, yana ganin da gaske watsa masa zatayi ya fara gudu tana biyar sa, sundad'e suna gudu a dajin Saida Afra ta gaji sannan ya tsaya, rungumeshi tayi tace "habibina ina matukar k'aunarka" kara rungumeta yayi yace "nima ina kaunarki habibaty, kallon juna sukeyi cikin shauk'in so da k'auna, sauke kanta tayi kasa tace "naji dad'in zuwa dajinnan, Yana birgeni sosai, sannan kuma gashi Kana kusa dani, inajin kamar muci gaba da zama anan" murmushi yayi yace "idan mukaci gaba da zama anan taya zamuyi aure? Kinsan fa na matsu banga munyi aure ba" da haka suka cigaba da hirar su cikin farinciki, gwanin sha'awa. Abba ne zaune gaban Mai martaba suna tattauna yadda zasu sake neman y'a y'ansu, domin tunda basuga gawar suba basu yadda sun mutu ba, sun yanke shawarar nan da kwana uku zasu had'a rudunar jami ai domin a kaiwa wad'annan mutanen hari, Abba ya dad'e anan suna fira kafin yayi musu sallama ya koma gida (kaduna). Kwance saude take rai a hannun Allah ta dubi Baba dake zaune gefenta tace "Baba kayi hakuri ka gafarceni na aikata babban kuskure arayuwata nabiyewa son zuciya da Kuma zugar Inna, na fad'a cikin tsaka Mai wuya, Baba dan Allah ka yafemin Kuma ka nemamin gafarar yayana khamal, na cutar dashi, Baba khamal bashi da laifi, cikin dake jikina banashi bane" kukane ya katse mata mgn, cikin tashin hankali Baba yace "bangane mekike fad'a ba, idan ba cikin sa bane cikin waye"? "Cikin Dauda ne" ta fad'a a takai ce Innalillahi wa'inna'ilaihi raji'un Baba yake ta maimai tawa yace "Saude mekika aikata haka meyasa zakiyiwa d'an uwanki haka? Kin cutar dani Saude, kin rabani da d'anda nake masifar so arayuwa ta, meyasa zakiyimin haka? Me khamal yayi miki da zaki yimasa wannan k'azafin? Kin bani kunya saude wlhi kinyi abinda ban tab'a zato ba" cikin b'acin rai ya tashi da niyyar fita Inna laure tace "malam Ina zakaje haka cikin wannan yanayin"? Harararta yayi yace "bansani ba, nace bansaniba mutuniyar banza mutuniyar wofi, ki duba halin da kika jefa y'arki a ciki sbd kwadayin ki da son abin duniya, daga k'arshe kun rabani da d'ana yaro mai natsuwa da hankali da sanin ya kamata, meyasa idona ya rufe a wannan lkc? meyasa ban goyi bayansa ba? Laure wlhi ko kad'an baki cancanci zama uwaba, kin tarwatsa rayuwar y'arki da kanki, kin nisantani da khamal Wanda nafi so fiye da y'ar dana haifa da cikina" hawayen sa ya share, ya fice daga gidan cikin kunci da damuwa. Kai tsaye wajen Dauda yaje yayi masa fad'a sosai, daga karshe dai Dauda yace "aiba laifinsa bane Saude ce ta kawo kanta wajensa saboda ya bata kudi" ran Baba ya k'ara b'aci sosai, gida ya koma ya iske Saude kwance kamar yadda ya barta yace "ke Saude me kikayi da kud'in zubarda k'ima da mutunci da kika karb'a a wajen Dauda"? Muryar ta na rawa tace " Inna ce tace nasamo mata kudi zatayi zubin a dashe Kuma bata da kud'i shiyasa naje wajensa ya taima kamin, yace bazai baniba saina amince da buk'atarsa, da fari ban amince ba Saida Inna tace naje na samo mata kota halin k'ak'a ne" Tasss!! Tassss!! Karar saukar mari kakeji wanda Baba ya yiwa Inna Laura yace "kije nasakeki saki d'aya" Saude dake kwance cikin matsananci rashin lfy, nan take numfashinta ya sark'e kafin kace wani abu tuni rai yayi halinsa, innalillahi wa'inna'ilaihi raji'un, yaude Saude ta amsa Kiran Allah, saidai muyi mata fatan dacewa. Fad'ar halin da Baba ke ciki b'ata lkc ne domin ya shiga cikin tashin hankali mara misaltuwa, itama Inna Laure ba bayaba domin idan kaduba fuska zakace tafi Baba shiga cikin tashin hankali. Bayan anyi sadakar bakwai Baba ya shiga tunanin ta inda zai fara neman khamal, domin ya d'auki alk'awarin matukar yanada rai to saiya nemo khamal duk inda yake, ya nemi gafarar sa, yana zaune tunani ya fad'o masa da sauri ya tashi yasa babbar rigar sa da hula ya fita, bai tsaya ko inaba sai kofar gidansu Afra kamar yadda khamal yayi masa kwatancen gidan, baisha wata wahala ba wajen gane gidan kasan cewar gidane Wanda kowa yasanshi a gari. Sallama yayi Mai gadi ya amsa Yana yimasa kallon sama da kasa, yace "malam wakake nema a gidannan"? Da sauri Baba yace "mai gidan nake nema ayimin sallama dashi dan Allah" Kallon wulak'anci mai gadi yayi masa yace "kaga malam Alhaji dai ya gama bayar da sadak'a dan haka ka koma inda kafito" "Allah sarki yallab'ai niba sadak'a nazo nemaba, nazo nan ne dannayi wata muhimmiyar mgn dashi"mai gadi yace kaga malam Alhaji baya mgn da k'ask'antattun mutane irinka, kaga tafiya ta karka yadda na fito na tarar dakai a wajennan" Yana batun rufe k'ofar saiga Alhaji ya tako har get din, dan yana shirin shiga mota yaga maigadi na mgn da wani cikin d'aga murya, shine yazo yaga ko waye. Baba na ganinsa ya zube k'asa yana sharar hawaye yace "ranka yadade kayi hakuri nasan ka gargad'e ni cewa karna koma bari d'ana khamal yazo wajen y'arka, kayi hakuri dan Allah ka taimakamin" ajiyar zuciya Abba ya sauke yace "meke tafe dakai" share hawayen sa Baba yayi yace "nazo nan ne danneman taimako, inason ka kataimaka ka tambayamin y'arka ko tasan inda d'ana yake" Murmushi Abba yayi yace " wanne d'a kake mgn akai"? D'aga kai Baba yayi yalli Abba yace d'ana khamal nake tambaya" murmushi Abba ya sakeyi yace "ba naji lbrn cewa ka koreshi ba"? Baba yace "ehh ranka yadade nakore shi a kan wani dalili Wanda sai yanzu na gane gsky bashida laifi kazafi akayi masa, a yanzu na gane kuma inason na nemosa duk inda yake muci gaba da zama tare" Abba yaji tausayin Baba sosai, domin shima yayi nadamar korarsa dayayi a baya, saigashi a yanzu yafishi matsayi yafishi kudi yafishi komai na more rayuwa. Abba ya cewa baba su shiga cikin gida akwai lbrn da zai bashi, haka ko akayi a falon sa suka zauna Abba ya bawa Baba lbrn komai duk abinda ya faru har yanzu da ake nemansu gaba daya, Baba ya jajantawa Abba tare da yimusu addu'ar fatan alkhairi daga k'arshe yace idan za'aje wannan dajin asanar shi, shima zaitafi.. By Meerah💞💞💞💞 [5/12, 12:28 PM] Meerah 💞: 🤴🏻🤴🏻🤴🏻 prince khamal 🤴🤴🤴 🌹🌹🌹🌹🌹 By 🌹🌹🌹 Meerah💞💞 ELEGANT ONLINE WRITER'S✍️ Dasunan Allah mairahama Mai jinkai 🅿️ 4️⃣7️⃣-4️⃣8️⃣ Cikin sand'a suke tafiya ahankali kada suyi motsi babba ajisu, bayan icce suka lab'e suna leken mutanen dake wajen zaune da bindigogi a hannun su, kallon khamal Afra tayi tace "honey yanzu haka zamuci gaba da zama acikin jejinnan" kwallar da take shirin fitowa ta gangaro a fuskarta, kayataccen murmushi yasakar mata yace "a'a bazamu cigaba da zama anan ba Allah zai kawo muna dauki, ki kula da kyau kada kiyi dogon motsi zamu jira anan idan suka wuce sai muje na tuno kyautar da kika bani aranar nan saimu Kira gida azo afitar damu" itama murmushi tayi tace "shikenan honey matukar Ina ganin wannan kykkyawan murmushin a fuskarka to bazan damuba Koda zamuyi shekara awannan wajen" murmushi yayi Wanda ya bayyanar da fararen hakoran sa ya Kara fitar da ainihin kyansa yace " kin tabbatar Zaki cigaba da zama anan tare Dani"? Gyad'a Kai tayi tare da murmushi a fuskar ta, Ajiyar zuciya ya sauke yace " idan harkin tabbata to mukoma muci gaba da rayuwa anan" rike hannun ta yayi yajata alamar sukoma, da sauri ta rike hannun sa tace " a'a honey nafison mukoma gida sbd muyi rayuwar aure Mai cike da farin ciki, nakasance tare da wanda nake masifar so a rayuwata" murmushi yayi ya rungumeta yace "Ina matukar sonki Afra bazan taba iya rayuwa ba idan har bubuke a tare dani kinzamo jini da tsokar dake jikina, kasan cewa zama tare dake shine warwala da annurin da zai bayyana a fuskata da jikina baki daya, Afra bansan ta yadda zannuna miki godiyata ba, kin aje karatunki sbd ni kinbar iyayenki sbd ni kin sadaukarda rayuwarki duk sbd ni, Afra nayi miki alk'awarin kasancewa dake har karshen rayuwata acikin ko wanne irin yanayi, ke ta musamman ce a wajena bazan taba mantawa da halaccin dakikayimin ba" hawayene suka gangaro masa, Hannu tasa ta share masa tana murmushi tace "kadaina tuna abinda yariga ya wuce habibina soyayyarka dake gudana acikin jikina bazata tab'a barina nayi nesa dakai ba, duk inda kashiga a duniyarnan saina nemoka koda hakan zaisa narasa rayuwa ta, gara na mutu a lkcn da nake kokarin taimaka maka dana zauna a gida ciwon sonka ya kasheni" "Bazaki mutuba insha Allah, zamu rayu tare mu reni 'ya 'yanmu da kanmu" kallon juna sukeyi kowannen su cikin farinciki, suna cikin hakane Afra taji motsin wani abu a k'afar ta, da sauri ta duba, wata irin razananniyar ihu ta saki ganin maciji ya nad'e mata k'afa 🙄 da sauri Kamal ya riketa Yana kokarin guduwa da ita saiga mutanennan sun zagayesu kowanne da bindiga a hannunsa,🤦🏻‍♀️ D'auresu sukaye ga icce daya sukaje suka sanar da ogansu, yace abarsu nan d'aure har gobe a kashesu, haka ko akayi anan suka yini suka kwana daure, washe gari Afra ta kalli Kamal cikin mawuyacin hali domin d'aurin da sukayi misu ya azabtar dasu sosai, zuba kawai jini keyi a hannayensu da kugunsu da aka daure, tace " Kamal yau inacikin farinciki sosai a rayuwata" cikin razana Kamal ke kallon ta yace "Afra wanne farinciki kikeyi munacikin wannan halin"? "Kamal ina cikin farinciki sosai yau sbd yaune zan mutu inatare dakai, yaune zanmutu kaina yana saman kafad'arka, Kamal inason naji kalma daya kafin numfashina na k'arshe ya fita daga jikina" hawaye yana zuba a fuskarsa cikin tashin hankali yace "Afra kidaina fad'in wannan mgn wlhi zuciyata bazata iya jure jin wannan kalaman naki ba idan baso kikeyi zuciyata ta buga a wajennan ba" "a'a khamal zuciyarka bazata bugaba sbd Kai jarumine inada tabbacin hakan daga gare ka, Kamal kalmar danake bukatarji kafin numfashina ya fita itace kalmar daurin auren mu, dan Allah kada kabari a dauki gawata batare da andaura muna aure ba" 😭 "Ki daina fadin wannan mgnr Afra inaji ajikina Afra bazaki mutu kibarni ba, zamu rayu tare insha Allah" murmushi kawai tayi batare da tace komai ba tana kallon sa shima ita yake kallo, murmushi karfin hali shima yayi, shikadai yasan irin radadin da yakeji acikin zuciyar sa. Suna cikin hakane saiga mutanen sundawo tare da ogansu, karasowa yayi wajensu yace "kune kuka gudu daga hannun mu ko Kuna tunanin zaku tseremuna ne, hhhhhhhhh wata irin dariyar mugunta yayi yace "shiyasa nacewa yarana kada Wanda yaje nemanku da kanku zaku kawo kanku a wajennan sbd duk dajinnan zagaye yake da yarana duk inda kukaje sai sunkama ku", hhhhhhhhh yana gama dariyar sa yace ku halbesu, yaje yasamu wuri ya zauna. Mutun biyu suka saita bindiga, d'aya ya saitawa Kamal d'aya Kuma ya saitawa Afra, daga Kamal har Afra sun sadakat domin sun tabbata cewa yau itace ranar mutuwar su, wani mugun yawu suka had'iye da kyat suka rufe idanu suna jiran saukar alburushi a kansu. Harbin bindiga biyu saukar alburushi biyu a lokaci d'aya, 🙆🏻‍♀️ d'aya ya sauka a k'irjin Afra, d'aya Kuma ya sauka a bayan k'eyar wanda ya saitawa Kamal bindiga. Sbd tsabar tashin hankali Kamal harda gutun hawayensa ya runtse idanunsa gingingin atunaninsa shine aka harba, Saida yaji ansake harba bindiga sannan ya bud'e idanunsa ganin mutanen nan yayi kwance cikin jini kowannen su ya fad'i babu rai, murmushi yayi azahiri yace "alhamdulillah Allah ya kawomuna dauki Yana fad'i yana murmushi, jin Afra batace komaiba yasa yakai dubansa gareta, lkc d'aya ya fita hayyacin sa cikin razananniyar K'ara yace " Afra! Afra! Afra! Afra kitashi kada ki mutu kibarni" Afra kam jini ke gudana tundaga kirjinata har kasa kamar an bude fanfo, Da gudu maimartaba da Abban Afra harda Baba sani suka karaso wajen, sukuma jami'an da suka zo dasu sunacen suna gwabza fad'a tsakaninsu da wad'annan mutanen, daga k'arshe dai saura suka gudu aka Kama sauransu. Banyesu akayi Afra kam babu alamar numfashi a tare da ita, jijjigata Kamal ya shigayi yana kiran sunanta yana kuka yana gunji saikace mayunwacin zaki ya dad'e Yana jijjigata kafin numfashita ya dawo sama sama kallon sa tayi cikin mawuyacin hali tace "karka damu Habibi kadaina kuka ina nan tare dakai Koda na mutu ruhina bazai barka ba" "Afra kada kitafi ki barni wallahi bazan iya rayuwaba idan har babu ke, dan Allah kada kitafi kibarni " da gyar ta d'aga hannu ta share masa hawaye tace "bazan barkaba Habibi ina matukar sonka" kallon Mai martaba da Abba tayi dake tsaye suna kallon su tace Abba inason adaura muna aure a wajennan plsss" 🙏 Haka akayi aka tattatara fadawanda ke wajen harda jami'ai Mai martaba ya fidda kud'i naira dubu d'ari uku yabawa baba sani yace ya biya sadaki sbd shine waliyyin Kamal yayinda Abba yayi waliccin Afra haka aka daura aure kowa na kuka 😭 ana gama daurin aure Afra tace Alhamdulillah ko yanzu na mutu burina yacika tana gama fad'in haka ta sauke ajiyar zuciya daga nan numfashinta ya tsaya cek...... Anan zan dakata saimun had'u a shafi na gaba insha Allah By Meerah💞💞💞💞 Share fi sabilillah 🙏🙏🙏 [5/12, 12:28 PM] Meerah 💞: 🤴🏻🤴🏻🤴🏻 prince khamal 🤴🤴🤴 🌹🌹🌹🌹🌹🌹 By 🌹🌹🌹🌹 Meerah💞💞💞 ELEGANT ONLINE WRITER'S✍️ Dasunan Allah mairahama Mai jinkai 🅿️ 4️⃣9️⃣-5️⃣0️⃣ Fadawane cike a harabar asibitin tare da Jami'ai kallo daya zakayi musu kagane cewa suna cikin damuwa. zazzaune suke sunajiran fitowar likita, kamal kam yakasa zaune ya kasa tsaye, idanunsa sun kunbura sunyi ja sbd kukan dayayi kamar ransa zai fita, gabansa na tsananta fad'uwa domin shi ya tabbatar cewa Afra ta rasu Daddy ne yace sai ankawota asibiti. Lokaci sai gudu yake awanni na tafiya abu kamar wasa ya d'auki lkc tunsuna jiran bayanin likita harsun fidda rai domin likitocin sunkasa yi musu bayani, duk Wanda ya fito a guje yake wucewa basuda lkcn mgn. Bangaren Afra kuwa har dare likitoci na kanta sunkasa samo numfashinta ya dawo normal saidai yanzu an d'an samu cigaba domin bayan wasu awanni tana sauke numfashi guda, da wannan likitocin suka samu tabbacin bata mutuba. Jiki a sanyaye likitan ya fito, da sauri sukayo kansa kowa da tambayar da yake yimasa, a jiyar zuciya ya sauke yace "bata mutuba saidai haryanzu babu tabbacin numfashinta zai dawo, domin idan ta sauke daya zata iyayin awa uku kafin tasake sauke wani, kuci gaba da yimata adu'a domin ita kad'ai take buk'ata a wajenku" Yana gama fad'in haka yayi tafiyar sa, Kamal kam awajen ya fad'i sumamme. Gimbiya Fulani kuwa sai faman shige da fice take a wajen bokaye dan kada Afra ta farfado domin ta tabbata idanhar ta tashi to kashinta ya bushe domin banda rasa aurenta da zatayi saita fuskanci hukunci mai tsanani a wajen Mai martaba sbd sace Kamal datasa akayi tunyana karami. Zaune take a wajen boka tanata faman sharar hawaye tace "ka taimakamin kada yarinyar nan ta farfado wlhi idan har ta farka asirina ya tonu kashina ya bushe" boka yayi dariya irin tasu yace "kidaina damuwa indai wannan ne angama zanbaki kullin magani Wanda zakije ki aza akan filon datake kwance akai idan har kika aikata wannan to ita da tashe sai a lahira" hhhhhhh "amma akwai sharad'i" cikin hanzari tace "sharad'in mene fad'i koma menene zanyi matukar bukatata zata biya" kallon ta yayi a natse yace " dole saina kwanta dake sannan aljanu zasusa hannu acikin wannan aiki" a razane ta kalleshi sai a lkcn taji warin dayakeyi maradad'i kauda kanta tayi tace "a'a boka kafad'i wani sharad'in amma ba wannan ba" a fusace yace "tashi kibani waje bazaki had'ani da aljanu ba" ya fad'a cikin b'acin rai, harta tashi tsaye ta fara tafiya Kuma saita tuna abinda zai faru da ita idan taki amincewa, da sauri ta dawo tace "na'amince matukar bukatata zata biya" wangale k'aton bakinsa yayi yana dariya jajayen hakoransa suka bayyana wad'anda suka koma wata kala sbd daud'a, Tunda abinya faru tsakaninsu gimbiya keta faman amai sbd warinda ta Shaka wajen boka dakyar ta koma gida da kullin mgn daya bata, bayan komawarta ma aman bai tsaya ba tuntanayi sannu sannu harya galabaita ta tafita hayyacinta haka ta kasance cikin kunci da damuwa yau ta aikata abinda bata tabayiba tunda kuruciyar ta, gashi Kuma tarasa lafiyar ta. Nasir ne zaune a garden abin duniya duk ya taru yayi masa yawa, yanzu shikenan andaura auren Afra da Kamal jiyakeyi aransa dama Afra ta mutu kowama ya huta wata kwallar bakin ciki ya share, duk abinda ke faruwa har yanzu Nasir ba tafi asibiti ba balle yasan halinda ake ciki, yana nan zaune yayi nisa cikin tunani yaji motsin mutum a kusa dashi, a hankali ya sauke idanunsa akan kausar datazo tanata sallama baijitaba, tana batun zama kusa dashi taga yayi saurin mikewa fuska d'aure, itama d'aure fuska tayi cikin kosawa da wulakancin da yake yimata tace "Yaya Nasir laifinme nayi maka haka dazaka tsaneni, menene laifina dannace inasonka? Me Afra tafini dashine? Yaya Nasir wlhi Ina matukar kaunar ka acikin zuciyata" "ya isa haka banasonjin wannan shirmen naki nace banasonki ko anaso dole ne" tsaki yayi yabar wajen cikin b'acin rai, itakam kausar ko ajikin ta acewar ta yanzuma ta fara sonshi Kuma duk hanyarda zata bi ta mallakeshi Koda baya sonta saitabi, tana nan tsaye wani tunani ya fad'o mata arai da gudu ta nufi part dinsu, tana shiga ta iske mahaifiyarta gimbiya Fulani kwance babu lafiya tace "umma sannu yajiki"? Ta amsa mata cikin kulawa da so da kauna domin tana matukar kaunar 'yarta sbd ita kad'ai ta haifa, hawaye kausar ta share cikin shagwab'a tace umma Nasir ne yaketa wulakanta ni dannace ina sonshi murmushi umma tayi tace "kingaji da boyemin kenan, ainadade da gane kina sonshi domin ko a fada mukaje kin dinga kallon sa kenan" sunkuyar da Kai tayi tana murmushi, umma tace "inda wannan ne ki kwantar da hankalinka domin Mai martaba yadade dayimin mgnr ni nace abari saikun kawo kanku da kanku" da sauri kausar tace "umma Mai martaba ya amince da aurenmu"? Murmushi tayi tace "ai tun lkcn da aka fasa aurensa aka daura tare dake awannan wajen bayan mahaifin Afra yayi tafiyar sa awajen daurin auren, amma akace kar afadamuku sai kunfahimci junanku da kanku, shine dalilin da mahaifin Nasir ya turoshi gidannan danku daidaita tsakaninku" wani ihu kausar tasaki ta rungume ummanta da karfi tace "umma yanzu ni matar Yaya Nasir ce"? Tana fad'a tana murmushi, itama umma murmushi takeyi tace "kwarai kuwa kindad'e da aurensa a kanki baki saniba shima bai saniba" d'aga hunnuwa sama tayi tace "Alhamdulillah ashe dama andaura muna aure duk irin wahalar da nakesha akansa", "ehh kausar Nasir mijinkine" da gudu ta shige bedroom d'inta tanata faman tikar rawar murna. Afra kam saidai muce sauki sai awajen Allah domin kwana biyu ta share a haka tana kwance kamar matatta Abba da umma da sauran mutane duk sunfidda rai da farfado warta domin yanzu daga ummi sai mai martaba da Kamal ne kawai a asibiti sauran duk suntafi acewarsu gawace suke jinya, saidai shi Mai martaba baifaye dad'ewa idan yajeba, acewarsa tunda gimbiya Nafisa da Kamal suna nan toshi basaiya zaunaba, Ummi da Kamal duk acikin dakin suke kwana kasan cewarsa babban dakine saidai basu faye yin bacci tare ba domin likita yace a kula da ita sosai, wannan dalilin ne yasa idan wani na bacci to wani na zaune yana kula da ita haka sukeyi, yau ummi ce kwance tana kwana shikuma Kamal yana zaune a kujera kusa da ita, daganan bacci b'arawo yayi awon gaba dashi, A hankali ta bud'e idanunta nan take ta tuna duk abinda yafaru da ita har daurin aurensu, murmushi tayi takalli yadda yake bacci cikin natsuwa sannu a hankali tace "Alhamdulillah a yaunzu kazama mijina Kamal Ina sonka sosai, yunkurawa tayi ta tashi zaune dube dube tafarayi tana neman wayarta ta manta cewa tun acen daji ta barta cikin motarta, hankad'a filo tayi ko zata ganta awajen amma bata ganiba wani kullin mgn ta gani, d'auka tayi cikin rashin sanin komenene ta banye taga ba komai bane sai dakakken iccen Wanda aka aje a matsayin magani, gimbiya Fulani ta fado mata arai nan ta tuna da irin kullin sharrin dataso yiwa kamal, murmushi tayi tace zanyi maganinki Dani kike zancen, kugi taji cikin ta nayi mata gefe d'aya Kuma zafi takeji wajenda aka harbeta, dafe wajen tayi ta tashi ta shiga neman abinci, cikin saa ta ganshi saidai babu ruwa drinks ne kawai a frige, fita tayi waje kozata samu ruwa amma ina ma'ikatane kawai ke yawo acikin asibitin kowa yayi bacci,haka yasa dole ta hakura ta koma, zama tayi ta zuba abincin ta faraci, cikin bacci ummi kejin alamar motsin mutum kusa da ita a hankali ta bube ido, cikin bacci take ganin mutum zaune saidai bata ganin fuska domin tajuya mata baya, Kara bude idanunta tayi dakyau taga tabbas mutum ne ta d'aga kai taga Kamal yanata bacci a kujera, cikinjin tsoro tace wacece da karfi Wanda yayi sanadiyyar farkawar Kamal, lomar data debo takai baki ta jiyo ta hadiye tace "ummi nice yunwa nakeji" da sauri Kamal ya dubi gado yaga babu kowa yace "Afra kece" wata lomar takai baki ta had'iye sannan tace nice Kamal bari ingama cin abinci masifaffiyar yunwa nakeji.. Hamdala suka shigayi suduka itadai banda cin abinci babu abinda takeyi.. Kubiyoni a shafi na k'arshe insha Allah By Meerah💞💞💞 Share please 🙏🙏🙏 [5/12, 12:28 PM] Meerah 💞: 🤴🏻🤴🏻🤴🏻 prince khamal 🤴🤴🤴 🌹🌹🌹🌹🌹🌹 By 🌹🌹🌹 Meerah💞💞💞 ELEGANT ONLINE WRITER'S✍️ Dasunan Allah mairahama Mai jinkai 🅿️ 5️⃣1️⃣ -5️⃣2️⃣ Saukowa yayi da saman kujera ya dawo kusa da ita yace "Afra nayi farincikin ganin farkawarki, alhmdlh Allah na godema" ya fada cikin nuna kulawa da farinciki, hannunta ya jawo ya sumbacesa, fuskar sa d'auke da murmushi, itama murmushi tayi tace "honey yau babbar ranace a wajenmu burinmu ya cika inacikin farinciki sosai" gyaran murya ummi tayi tace "to marasa kunya a gabana babu ko Kara" kallon Kamal tayi tace "tashi kabata wuri taci abincinta" sosa k'eyarsa yayi ya tashi sum sum a kunyace ya zauna, ita dai Afra batace komaiba sai murmushi takeyi tana kallon sa danya bata dariya, kasan cewar ummi bata kallonta tana bayanta.. Washe gari tunda safe asibitin ta cika da mutane domin duk Wanda yaji Afra ta farfado sai yazo, likita ya kammala gwaje gwajen sa ya tabbatar da samun lafiyar ta, babu b'ata lkc ya basu takardar sallahma, Abba yace abashi ita sutafi idan tasamu lfy sai ayi biki ta tare gidan mijinta, haka kuwa akayi Mai martaba da ummi duk sun amince, saidai shikam Kamal baiji dad'in hakan ba, wannan dalilin ne yasa yace zaibi Baba sani gidan sa danya kasance kusa da Afra. Mai martaba ya yiwa Baba sani goma na arziki, duk da yaso yayi zamansa acikin masarautar Amma firr Baba sani yaki amincewa yace yafi son ya zauna acikin kauyensa, haka ko akayi tare suka tafi da kamal, duk abinda akeyi har yanzu Nasir da khamal basuyiwa juna mgn ba, Kamal yafita harakar sa gaba d'aya, tunda Afra ta bashi lbrn sa, shikuma Nasir haushin Kamal yakeji wannan dalilin ne yasa yaki zuwa asibiti Kuma da suka dawo yaki cemasa yajikinta, hmm wannan kenan. Suna isa gidan Kamal yaga gida shiru babu kowa yace "Baba Inna bata nan ne? Ina Saude tayi"? Ya jera masa tambayoyi lkc d'aya, baice masa komai ba ya bud'e d'aki ya dauko tabarma ya shimfid'a suka zauna, saida yayi gyaran murya yace "laure dai tana gidan su munrabu, ita Kuma Saude Allah yayi mata rasuwa, innalillahi wa'inna'ilaihi raji'un Kamal ya shiga maimai tawa, nantake hawaye suka wanke masa fuska, shima Baba yaji mutuwar ta dawo masa sabuwa, tare suka dinga kuka kamar wasu mata, sundad'e a haka daga k'arshe suka jajantawa juna tare da yi musu ta'aziyya, suna gamawa da sauri Kamal ya tashi ya nufi hanyar fita, dakatar dashi Baba yayi ta hanyar tambayar sa inda zashi, bai fad'a masa ba ya daice yanzu zai dawo, baijara yasakeyin mgn ba yayi gaba.. Da fitarsa ya shiga mota ya Kama hanyar kauyensu Inna laure, yayi sa'a kuwa ya tarar da ita a gida, tana ganinsa da murna ta tarbeshi itama maifiyarta da murnanta ta shiga tsokanar sa, shima yana mayar mata, inda sabo yasaba da zolayar kakarsa domin tunyana karami duk sanda yaje gidan saita tsokaneshi, Inna laure ta bashi hakuri harda kukanta domin harcikin ranta take kaunar sa, shima yana kaunarta sosai domin ta bashi kulawa a lkcn da yake bukatar kulawa, ta nuna masa soyayya a lkcn da aka nisantashi da mahaifiyarsa, wannan dalilin ne yasa bazai taba mantawa da itaba Kuma kome zatayi masa bazai gujetaba, yayi musu ta'aziyya sun roki juna gafara daga nan yace ta had'a kayanta yanzu zasu tafi, ba musu kowa ta shiga had'a kayanta domin tagaji da zaman gidan, ga masifar da iya uwani (mahaifiyarta kenan) keyimata akan korar Kamal datasa akayi akan fifikon data nuna akansa, iya uwani taji zafin abin sosai wlhi domin tana kaunar jikanta sosai, bayan ta shirya tsab tayiwa iya sallama suka fita, bakin kofar gida taga motar sa, ta wangale baki tana mamaki, tambayoyi ta shiga jera masa, baice komai ba sai bude mata gidan gaba dayayi yace ta shiga sutafi, ba musu ta shiga yaja suka nufi gida. Gabanta na fad'uwa sosai sbd tasan halin mijinta sosai da kafiya idan yace bayason abu, "Mutafi" kamal ya fada Yana kallon ta, ajiyar zuciya ta sauke tace "to" ya shiga gaba tana binsa a baya. Baba na nan zaune kamar yadda yabarshi, Yana ganinsu ya mike tsaye cikin b'acin rai yace "Kamal meya had'aka da wannan matar kuma"? Murmushi yayi yace "Baba wannan inna tace fa" kallon Inna baba yayi cikin b'acin rai yace ta fice masa a gida, Kamal yace saidai su fita tare amma bazai iyazama acikin gidan ba idan har Inna bata nan, sundad'e kafin baba ya amince tazauna, daga k'arshe dai gidan yakoma kamar da, kowa na cikin farinciki. Afra kam tasamu sauki sosai rauni ya warke har ansa ranar biki tare dana Nasir, sannu sannu lkc na tafiya ranaku na shudewa lkcn da aka aza yazo hausawa na cewa rana bata karya saidai uwar d'iya taji kunya, ba'a wani shagaliba abikin walima kawai akayi domin Afra ba mace bace maison hayaniya, da wannan dai aka kammala biki amarya Afra ta tare a gidan mijinta acikin masarauta yayinda kausar itama ta tare a gidan Nasir cikin garin kaduna, Nasir kam yadai d'auki zabin iyaye ne kawai badan yanason kausar ba, itakam kausar ta dauki aniyar zama Koda Nasir zaidinga wulakantata agidansa, Kamal ya gyarawa Baba sani gida ya mayar dashi ginar zamani ya zuba musu kayatattun kayan more rayuwa, sunyi farinciki sosai da wannan. Afra kam tasamu natsuwa da kwanciyar hankali acikin gidanta, Kamal Yana bata duk wata kulawar data dace, haka ummi tana bata kulawa daidai gwargwado. Gimbiya fulani kam tuni ta rasu a dalilin ciwon kanjamau data kwaso wajen boka, khairat Kuma ta koma karatu a kasar waje, itama Afra acikin garin Zaria aka sama mata skull taci gaba da karatu, kausar kam ba laifi tana fuskantar rayuwa cikin sauki domin Nasir baya takura mata balaifi Yana sauke mata duk wasu hakkoki nata, a'lak'a mai karfi ta kullu tsakanin Inna laure da ummi haka Daddy da Baba sanusi, suna ziyartar junasu lkc zuwa lkc.. Tammat bihamdulillahi littafi ya cika da godiyar Allah, Ina mika godiyata ga Allah subhanu wata ala daya bani ikon kammala wannan littafi lfy Ina Mika godiya ta gareku masu comments Allah yasaka da alkhairi Allah yabar zumunci. Muhad'u a sabon littafina na gaba mai suna MENAHAIFA ☠️☠️ horo story By Meerah💞💞💞💞 Share fisabilillah 🙏🙏