*(¯`*•.¸,¤°´✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿`°¤,¸.•*´¯)* *MABARACIYAH* (mai harshen damo) тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιε. _haƙƙin mallaka_ _*sadi-sakhna*_ (Yar mutan Jama'are) Paid book #400 3131951977 Auwal sadiya First bank Mai turo kati kuma ta wanann number MTN 09035784150 Mutanen niger su tuntubi wanann number +227 97 21 16 15 Naƙara shafin free har zuwa page 20,zuwa lokacin inka shiryah kazo a fara dakai ranar juma'a. _____________________ Assalamualaikum barkan mu da wannan lokaci *ABMAR COLLECTION* ina nan na kawo muku kayana masu kyau da sauki👌🏻 KAMAR SU:- Atamfa, Atamfa Mai golden,💁‍♀️ Lace ,Shadda lace Yadi, Shadda Abayas💥 Kids wear Takalmi, jaka, mayafai💥 Sleeping dress, kananan kaya na gayu🔥kayan kitchen, DA DAI SAURANSU ina Sokoto ina tura kaya ko ina da izinin ubangiji mai son kayana pc ina maraba daku siyan daya ko sari👏🏻domin neman karin bayani sai ku neme ni ta wannan number waya👉08101521252 nagode kwarai da gaske💃💃 Free page 1••2 _shekara ɗaya baya_ Wata matace zaune a cikin taron mabarata wanda suke zama a bakin gidan bamu kudinnan domin samun abinda zasu sakawa cikinsu,duk wani lokacinma mutuwar zuciyace take kaisu. Karar wayar nokia ce tayi kara a aljihun wata yar matashiya,wacce kusan dukka wajen tafisu mummunar shiga sosai. Fitowa tayi da wayar da'aka ɗaɗɗaure da zare,da kyar ta daga wayar yanda hannunta yake karkarwa sosai. Can kaman na minti ɗaya tasaka wayar a kunne amma batace komai ba,da alama wani abu ake faɗamata. Sakin wayar tayi ta fadi a kasa tareda jera salati kala kala, "Talatu mai ya faru kike wanann salatin lafiya kuwa?" "Ahah kursiyyah,makwanciyata ce ta haya ta kirani wai ɗana bilyaminu dayake asibiti wai ciwonsa ya tashi,ance inbankai kudin aikin da wuri ba zai rasa ransa" Wata ce daga gefe kana ganinta kaga jarababbiyah, "Miye na damun kai oho,kefah kika ce yaronma shegene uhm" Talatu tana jinta bata kula ta ba,karisawa tayi inda layin gaba suke ta faɗa musu abinda yake faruwa,ƙin yadda sukayi da ita saida na baya sukace da gaskene tukunna. "Dan allah kuyi hakuri,ance idan ban kai da wuri ba zai rasa ransa,ku taimakeni na shiga gidan wajen alhaji dan allah,iya yaune kawai yake ganin mutane,inba hakaba bazan ganshi ba" Kuka tafara wiwi,wanda hakan yasa na gaban jikinsu yayi sanyi suka barta ta shiga. Securitynne suka bude mata kofar ta shiga tareda wasu masu neman taimako suma guda biyu da suke gaban layin. Bayan kaman minti biyar da shigarsu sukaji danger alarma ta gidan ta buga. Sauran masu neman taimakon hargitsewa sukayi,yayinda sauran masu tsaron kuma suka afka gidan da gudu. Duddubawa sukayi inda karar ta fito,wani hayaki aka saki wanda duk da hasken rana ta allah amma mutum baya ganin gabansa. Wani security ne ya kalli wata ƴar matashiya a cikinsu wacce bata wuce shekara sha takwas ba,ta fito daga cikin hayakin sai tari take. "Lafiya khamriyyah naga kin fito ina yallabai ɗin" "Ahhhh uhmm ban ganshi ba Ahamd,masu neman taimakon ma bangansu ba a ciki,inaga akwai matsala" "Oh shitt,duk mai muke haka tafaru,akan haka zamu iyah faɗuwa jarabawarmu tazama SSS fah,duk da muna matakin karshe,barina ƙira Dec. Sadeeq yanzu nan" Radio waya ya danna na security domin shaidawa headqauter su, Can komai aka faɗamasa sai ya kashe wayar yana kallon ta. "Yess wannan karon inaga zamuyi nasara khamriyyah,dasuka tashi guduwa da shi sun ɗauki mota a cikin gidan,kuma akwai na'urah mai bin diddigi a jiki" Saurin hawa mota suka yi,ahmad na tuƙawa da mic a kunnensa ana faɗamasa inda zasubi. **_____**_____** Tafiya suke motar cikin matsanancin gudu,kayan jikinta yagygygye tafara cirewa tana zubarwa a motar,ta kuma yiwa wacce take tuƙin magana,wacce itama yagaggun kayanne a jikinta. "Ki taka da sauri,mukai akan lokaci,sonake kowanne tafiya da motar nan zata yi ta dungayi ta barazanar ƙarewar numfashinsa na karshe a duniyah" A bakin wani kogi suka tsayah bayan sunyi tafiyah mai nisa a cikin jeji. Fitowa akayi dashi kansa a rufe da wani buhu,durkusarshi tayi a bakin ruwan dake gaban ta,tana sanye da baƙaƙen kaya sun yayyage kaman na mahaukata ,wanda tasamu damar sakasu a motar. "Safiyyah,miƙomin buhun nan yanzunna" "Toh shugaba" Cirewa buhun dayake kansa tayi tareda tsugunnawa suna kallon juna. "Ka ganeni Brr. Shehu ko kuma na tuna maka" Jikinsa ne yafara karkarwa kaman an jona masa shocking. "Dan .....al Allah kiyi hakuri na tuba,ki tunafah inada iyali dasuke jiran komawa ta gidan,mai yasa zaki zalunceni akan wata buƙata taki?" "Hhahahah zalunci shine abicina brr. Shehu,kuma yanzu kaima zan ciyar dakai shi " Karbar buhun tayi daga hannun matar sai motsi yakeyi, "Kasan menene a cikinnan?,nasan baka saniba,to macizaine masu mungun dafi da aka tunzurasu na tsawon sati guda,neman inda zasu huce sukeyi,......yanzu zamu saka kanka a ciki su samu abinda zasu juye dafinsu a ciki" Ihu yafara kan gari ya gari jin abinda take faɗamasa yana cikin buhun,saidai ko a jikinta saima ƙara nishaɗi da hakan yabata, "Kasam menene Brr.,ina son naga na kama mutum babba yakusa haifata inayimasa abu yana ihu yana neman taimakona,sannan inason yin basaja a cikin masu nemana ko wanda nake nema,wanann duk yafi bani nishaɗi,naga kana nemana ko kuma kana tsorona amma ina gabanka,a matsayin bakowa ba batareda saninka ba,hhhh wannan shine aikin MABARACIYAH ,matsoraciyah kuma abar tsoratarwah,....ohh ina ta baka labari,ashefah kai lokacinka yayi na manta ma kwata kwata,shine kai kuma baka tunamin ba ?" Duk shaƙiyancin datake yi shidai ya zuba mata ido,banda karkarwa da kuma gumi babu abinda yakeyi. Mata biyune masu matukar karfi,jikimsu daga gani suna ɗaga ƙarfe,rirriƙeshi sukayi tamau,yayinda ta buɗe bakin buhu ta cusa kansa a ciki babu alamar ɗanɗanon imani a ranta,saima murmushi da takeyi jin yanda yake ihu sukuma macizan suna saransa. Karar bingane yasaka ta tsayawa cak daga kallon wanda kansa yake cikin buhun,yayinda idonta ya sauka akan gefen kirjinta wanda jinin yake zuba ta wajen. Sakin buhun tayi tareda miƙewa tana dafe kirjin ta kalli wanda yayi mata harbin. Khamriyyah ceh wanda bayan tayi harbin hannunta sai karkarwa yake,abinka da wacce yinta na farko kenan. Haɗa ido sukayi ta ida suna kallon kallon,buɗe baki tayi duk da harbin dayake jikinta tafara magana cikin taurin zuciya, "Me kike nufi kenan da hakan,dan kin kawo karshena zaki iyah goge wanda nayi a baya ko kuma wanda zai faru a gaba,babu abinda xai fasu ƴar bincike,saima nace miki yanzu aka soma wasan................zamu haɗe masu bincike a salon daban" Dariya ta saka jini yana fita ta bakinta kafin ta faɗa cikin ruwan dayake gabanta. Ganin hakanne yasa suma sauran mabiyannata wanda suka sanye da kayan baran suka cikawa wandonsu iska saidai nasu jajayene ba baƙaƙe ba,daga ganidai idan zasuyi wami aikine suke sakawa. Kallon khamriyyah dec. Sadeeq yayi tareda cewa, "Aikin ki yayi kyau khamriyyah,duk da ke sabuwar shigace amma jarumtarki tana birgeni,daga yau nasakaki cikin sahun ƴan rukunina" Murmushi tayi na jin daɗi kafin ta saramasa, "Nagode sir,zan kasance mai cigaba da jajircewa,bazaka taba samun matsala daniba" Da gudu masu bada taimakon gaggawa suka zo da ambulance aka ɗauki brr. Shehu,wanda cikin ƙanƙanin lokaci har kansa yayi tulele kaman randa dan azaba. Asibiti aka wuce dashi da gaggawa saboda ƙoƙarin ceto ransa. Tare suka wuce asibitin duk da su dec. Sadeeq ɗin,yayinda wasu kuma aka barsu a kogin su nemo gawar mabaraciyah a ruwa,dan harbin da aka yimata a saitin zuciya ba lallai ne takai iyanzu ba da rai. A tsaye suke shida khamriyyah a ƙofar asibitin kowa yayi jugum da abinda yake sakawa a ransa. Wayar Dec. Sadeeq ce tayi ƙara wacce yake amsa kiran dayashafi rayuwarsa,hayatee yagani a jikin screen ɗin,wanda hakan yasashi yin murmushi. "Hello Amrah zan ƙiraki ina kan aikine yanxu haka mai muhummanci" Har zai sauƙe kiran tace "Tsayah baby,kasan dai kaine farin cikan koh?,sannan kuma kaine nutsuwata ,nasan dama kana aikin ai,yanzunnan naji wani batu,wai kun samu nasarar kashe wacce take kidnap ɗin manyan mutanennan" "Uhm Amrah a ina kikaji keda kike cikin gida" "Oh tambaya ma kake,ina matar shugaban masu bincike na jiha har ace a ina naji,yanzu dai ba wanann ba,kana lafiya babu abinda ya sameka koh?" "Lafiyata kalau,kefah ykk ya gidan" "Uhm babu ƙalau har sai ka dawo,koyaushe kace wani baka da time ɗin ƙirana,amma kullum kuna tareda wanann sabuwar ɗalibar taka,watan mu shida da aure har an fara maƙala maka abokiyar aiki mace,ni banasonta batayimin ba kwata kwata" Gyaran murya yayi tareda kallom khamriyyah wacce ta maze tareda kawar da kanta kaman bataji mai matar tasa ta faɗa ba. Ganin hakanne yasashi saurin komawa gefe kaɗan" "Kai Amrah wani abun ki daina faɗamin a wayah mana,yanzu kashi taji abinda kika faɗa,kimga ai bazata ji daɗi ba koh?" "Oh taji daɗi? daɗima zataji?,dama nasan kafara sonta ai,nibaka damu dani ba shikenan" Ta faɗa tana saka masa kukan kissah,lumshe ido yayi yana sauraron rigimar matar tasa,indai akan watane bata ɗaga masa ƙafa bare ta fahimceci,takasa gane cewar ita kaɗaice a ransa babu wata daban. "Kinga kiyi shuru haka,kinsan kukanki na ɗagamin hankali,yanzu barina koma dan iyalan sa sunzo asibitin,idan na dawo zamuyi magana,kimin massage ɗin abinda kikeso na taho miki dashi kinji" Yana gama faɗa ya kashe wayar tareda sumbatar wayar,iyah dasafe yabar gidan amma har yayi missing ɗin soyayyarta. Komawa wajen asibitin yayi,wanda shigowar wasu mutane kenan asibitin,babu abinda suka sai aikim kuka,musamman ma babbar macen,wanda da alama matarsa ce. "Innalillahi,yanzu bawan allah abinda yafaru da alhajin kenan?,ina gida sainaji mummunan zance kuma,da safe fah mukayi sallama dashi akan za'a kawomasa rahoto,sannan kuma zai gana da masu neman taimako,shikenan sai a yimasa haka,kowa yasan halinsa na kirki da dattako na mijina a garinnan,bai ci wannan ɗanyen aiki ya hau kansa ba,wannan yarinya akwai ƴar tsinanniya,inshallah baxata gama lafiyaba sai taga karshenta itama,yanzu duniya ta zamo babu dama mutum yayi taimako sai an kawar dashi,ni inada tabbacin cewar wlh duk yanda akayi abokan adawa ne suke aikata take wadannan ayyukan,kuma bilahillazi sai asirinsu ya tonu suma,Allah ya isah wlh bazan taba yafewa ba,haba wanann zalunci har ina" Dec. Sadeeq ne ya matso kusada ita tareda bata baki,dan duk sauran wanda suke wajen suma buƙatar wanda zai lallashesu suke,ita kaɗaice ma tasamu damar faɗar abinda yake cikin ranta. "Kiyi haƙuri mrs. Shehu,haƙiƙa abin da ciwo,saidai maganganun suma basuda amfani a yanzu,dan mun samu kawoshi asibitin da gaggawa inshaallah babu abinda zai faru...." "Abinda zai faru kan ai ya riga ya faru,malam naga fah yanda kamanninsa suka tashi daga yanda suke da aka dora a wayah,banda zalunci ta bushashshiyar zuciyah,ko wanda yayi mummunan aiki ban ta'ba ganin wanda akayiwa horo da macizai ba,wanann yarinyar duk yanda akayi ba mutum bace inaga shegiya tsinanniyah kawai,wlh itama sai anyi mata fiye da haka" Ƙara gunjin kukanta tayi tana bubbuga kirji, "Kiyi haƙuri hajiya,wacce kike magana akai ma ta mutu yanzu haka,ɗaya daga cikin abokiyar aikinmu tayi nasarar harbinta a kirjinta na hagun" "Ina gawar yarinyar take?" "Uhmuhm har yanxu ana kokarin nemota a cikin ruwan" Idonta ta tsayar akan fuskar khamriyyan wanda dec. Sadeeq ya nuna mata. Saurin karisawa wajen khamriyyah tayi tana kallonta ƙasa da sama. "Kkkece Dec. Khmariyyah wacce ta harbeta?" "Eh nice ranki ya ɗaɗ......." Tun kafin ta gama maganar hajiyan ta ɗauketa da wani bahagon mari,zata ƙara mata Dec. Sadeeq yayi saurin riƙeta. "Hajiya lafiyarki kuwa haka" "Tamabayata ma kake meyasa na mareta,to dayafi mari zanyi mata,ka duba irin azabar data gallazawa mijina,wanda yake cikinta yake shan ta har yanzu, bai ci kuɗin kowa ba bai kashe uban kowa ba. Amma ita data aikata hakan shine ta kasheta cikin sauƙi da salama,kuma wai gawar dazan gani ma nayi mata wani abu ko zan huce wai ba'aganta ba?" Dec. Sadeeq yana cikin riƙe da itah wani likita ya fito daga ɗakin da brr. Shehun yake. Saurin fincike hannunta tayi daga riƙon da Dec. Sadeeq ɗin yayi mata tareda nufar inda likitan yake. "Likita ya ake ciki,yatashi ina koh,ina ya tashi koh,ina so ka faɗamin yanzunnan" "Hajiya kiyi,haƙuri tukunna,mun samu nasarar ceto rayuwarsa,saidai kuma gaskiya babu alamar zaiyi tsawon rai,daga nan zuwa kowanne irin lokaci zai iya tafiya,dan gabaɗayah ƙwaƙwalwarsa ta cuɗanya da dafin macizai,munyi mamaki ma da bata narke ta zubeba dan gas......." "Ya isa haka likita da wannan mumummunar maganar taka,da bata zubeba kai ai saika je ka zubar da itah,yanzu dai zamu iya ganinsa ko yaya?" "Eh to hajiya a yanda yake bai kamata a bari wasu suje kansa ba,saidai kuma duba da halin dayake ciki,na mutuwa ko rayuwa bazamu iyah hanaku ganinsa ba,saboda idan muka hanaku ma har yanzu babu wani cigaba sosai" Tun kafin yagama bada bayani hajiya Delu ta nausa cikin ɗakin,turusss tayi a bakin ƙofah ganin yanda aka sossoka masa wayoyi a kansa masu yawa,ga kuma kannsa yayi suntumeme kaman na mutum uku,kuma yayi bakikkirin ya tashi daga kalar jikin mutum. Mutuwar tsaye tayi a wajen takasa karisawa,duk son ta da takarisa wajen abin gagararta yayi,dan karfim kuriwarta baikai yayi hakan ba sam. Hannunta ƴar ta taza mai shekaru sha biyar,babu abinda yake tashi a cikim ɗakin sai sautin ƙarar injin rayuwar da aka manna da jikin brr. Shehu,wanda bai san inda kansa yakeba. Takawa tafarayi a hankali yayinda karar injin ma yake ƙara sauti a kunnenta dadai da yanda take kusantarsa. Saida taje daff da inda yake kwancen kafin taja ta tsayah tana karemasa kallo. Waye zaice wanann halittar ta mutum ce kuma wai wanda da safema lafiyarsa ƙalau inba wanda yasani ba,gaskiya makashiyar bakaramin ƙwarewa tayi ba a harkar kisa. Zama tayi a bakin gadon dayake kwance tareda riƙe hannunsa ciki nata, "Mijina!,kaga yanda ta maida kai cikin abinda bai fi awanni ƙalilan ba,anya kuwa wanann mutum ce,mai kayi mata dazata yimaka haka,kuma wai abin takaicin ita ta mutu cikin saukakkiyar hanya,amma kai kuma kana shan wahala,wanann ba adalci bane sam,ka tashi ka amsamin kaji,ga ƴaƴanmu ma suna buƙatar ganinka,ka tashi kacemu su babu komai kaji barister nah......." Dukkansu kallon na'urar suke yanda layin rayuwarsa yake sauƙa da sauri sauri. Yarimyar ce ta tashi da sauri ta nufi ƙofah domin kiran likitan yazo ya gani. Hannunnasa da take riƙedashi taji ya kankame,wanda hakan yasa ta bashi hankalinta. Buɗe idanuwansa yayi da kyar,wanda kwayar idon ma tayi luhu luhu jajur,abun babu kyan gani,buɗe bakinsa yayi kaman mai son yin magana. "Mmmmmm....bbbbraciyah........." Daga haka taji hannunsa ya shika,daga gani yanason faɗan wani abu,ɗaga ido tayi ta kalli likitan wanda ya sunkuyar dakai alamar tafaru ta ƙare. "Likita ya kake tsaye,kazo ka dubashi mana,likitaaaa" "Kiyi haƙuri hajiya brr ya amsa ƙiram mahaliccinsa,kiyi duba da injin dayake gabanki" Juyawa tayi ta kallah,sai a sannan taga ashe injin ya tsayah cakk, "Ahah bahaka bane,wannan injin ƙaryah yakeyi,mijina bai mutuba bai ......" Tun kafin ta gama magana luuuuu ta faɗi ƙasa mataciyyah.. Saurin yin kanta likitan yayi shida yarijyar wacce itace ƴar babba a cikin ƴaƴan. Saurin ɗauƙarta akayi zuwa wani ɗakin a cikin asibitin. Yayinda shikuma marigayi brr. Shehu aka turashi zuwa ɗakin ajiye gawawwaki. Khamriyyah ce ta kalli dec. Sadeeq tareda cewa, "Gaskiyah abin ba yanda muka tsammaceshi bane,yanzu ogah ya zamuyi da gawar,da kuma ita hajiyan,dan yanda mutuwar ta zamo da kuma binciken" "Wane binciken za'a sake bayan an riga ansan dalilin mutuwarsa,saidai kuma saboda babban mutum ne case ɗin bazai mutu nasan a iyah haka. Yanzu abin da zamuyi shine muƙara tsananta binciken nemo gawar ita makashiyar tunda har yanzu sunce basu gantaba,kuma dama ga ruwan yana ambaliyah sosai,nemota zayyi wuyah sosai.....ahhh idan baki mantaba naji kaman yace mmmm....mabaraciyah koh,kafin ya mutu,shin ko zaki tuna wannan suna?" "Eh to yallabai lokacin da mukazo kaman kuna wani bincike akan case ɗin kisan wata ma'aikaciyar asibiti,wacce aka sameta anyi mata allurah da dafin macizi,kuma an rubuta mabaraciyah a duk jikinta da reza" "Tabbas hakane ashe kin tuna,kuma wannan ma haka muka karishi duban mu bamu gano hujjah ko ɗaya ba,dan hatta shatin hannu ɗaya na mutum babu a jikin gawar. Akwai lauje cikin naɗi gameda kisan guda biyu,waccar an ruvuta mata sunan mabaraciyah a jikinta,shikuma wanann yayinda yake gabar mutuwa ya ambaci sunan mabaraciyah,tabbas akwai kamanceceniya tsakaninsu. Inkuwa hakane to lallai kin cancanci karramawa ta musamman,wajen nasarar da kikayi na harbinta khamriyyah" "Nagode sir" "Karki damu,ki tsaya a wajennan tunda mrs shehu da kuma gawarsa suna ciki,zanje wani waje ina dawowa yanxunnan" "An samu wani abune har yanzu?” "Eh sargent umar ya ƙirani wai an ga gawar wata mata da harbi a ƙirjinta a can wani ƙyauye da nisa,to ina kyautata zaton itace,dan yanayin shaidun da alamar sunyi dadai,ki tsaya nan yanda nace miki,in case ko za'a buƙaceki" "Bakomai sir sai ka dawo" Ta ganin ƙulewarsa ta jawo wata ƴar karamar wayah a aljihunta ta kunnata,saida taga babu kowa a wajen kafin ta danna ƙira. "Hello shugaba Viper-lady" Aka faɗa daga ɗaya bangaren. "Yeess Vl3 ykk komai lafiyah dai koh" "Eh komai lafiyah,muna nan a tare iyah Vl1 ce kawai bata nan tana kan nata aikin ita ma" "Okay good,aikinku yana kyau da kuka taimaka min na kashe mabaraciyah,nayi nasarar kashe tsuntsu biyu da dutse ɗaya,na kasheta na shafe aikinta,sanann kuma ni nasamu yarda da kuma ƙarin matsayi daga cibiyar bincike,yanzu aiki da salo zai soma daga yanda yake. Mataye a shirya, Viper ta fito daga cikin raminta bayan tsawon ɗaɗewar datayi a ciki tana dakon jiran ranar fitowa,yanzu matar datayi mata kanainai ta hanata fitowa ta matsa. Lokacine ita ma daya kamata ta fito tayi nata sunan sanann tabawa zuciyarta abinda take muradi. Mun shiga episode 2 na wasan,bansan kozanyi wasan dayafi nata ko ahah" Tana kashe wayar ta zefata a aljihu tareda gyara ɗamararta da kuma hularta,wani mungun shu'umin murmushi tayi tareda cewa, "Micijiya zata shiga cikin rigar mai kamata,yayinda shikuma bai san tana ciki ba,yayi zaton mai taimakonsa ce,inda zaiyi ta faɗamata sirrin yanda zai kamatan. Mai zai faru?...shin tunda ta riga tasan ta inda zai kai farmaki zata barshi kuwa yayi nasarar. Salon Viper lady shima daban yake da na mabaraciyah. _sadi-sakhan_ *(¯`*•.¸,¤°´✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿`°¤,¸.•*´¯)* *MABARACIYAH* (mai harshen damo) тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιε. _haƙƙin mallaka_ _*sadi-sakhna*_ (Yar mutan Jama'are) Paid book #400 3131951977 Auwal sadiya First bank Mai turo kati kuma ta wanann number MTN 09035784150 Mutanen niger su tuntubi wanann number +227 97 21 16 15 Naƙara shafin free har zuwa page 20,zuwa lokacin inka shiryah kazo a fara dakai ranar juma'a. _____________________ Assalamualaikum barkan mu da wannan lokaci *ABMAR COLLECTION* ina nan na kawo muku kayana masu kyau da sauki👌🏻 KAMAR SU:- Atamfa, Atamfa Mai golden,💁‍♀️ Lace ,Shadda lace Yadi, Shadda Abayas💥 Kids wear Takalmi, jaka, mayafai💥 Sleeping dress, kananan kaya na gayu🔥kayan kitchen, DA DAI SAURANSU ina Sokoto ina tura kaya ko ina da izinin ubangiji mai son kayana pc ina maraba daku siyan daya ko sari👏🏻domin neman karin bayani sai ku neme ni ta wannan number waya👉08101521252 nagode kwarai da gaske💃💃 Free Page 3••4 _Shekarar yanzu_ Katsina____12:00pm Layin tsitt yake baka jin komai sai kukan karashiyah wanda sukan fito da daddare domin nemo abincin su. Daga ganin yanayin anguwar kasan masu hannu da shuni ne ke zama a cikinta. Bisa la'akari da yanda kowanne gida ɗaɗɗaine bashida get,ruwa,da kuma wutar nepa mai kyau. A hallayah irinta wannan anguwa akan rufe gidan kaman misalin karfe goma,hakanne ya sauƙaƙawa masu shirin shiga wani gida,wanda yafi kowanne gida a kusan wajen kyau. Su ukune sanye da baƙaƙen kaya,da kuma junduma junduman hijabai,a yanayinsu sunyi kama da mata,saidai kuma yanayin kujarinsu akwai shakku idam matanne,koma matanne to kuwa basuyi kama da masu zama a gidaba suna rainon yaransu. Ɗaya daga cikinsu ne ya kama katangar wajen ya hau,kaman dama danshi akayi wajen saboda tsabar ƙwarewa. Saida ya daidaita zamansa a wajen kafin ya mikawa na kasan hannu. Wani abu ya bashi a gwangwami yafara fesawa security ware tada zagaye gidan mai kaman spray. Saidai daga yanda yake rike abin cikin kulawa kasan abin da alamar hatsari a tattare dashi,koma ince fiyeda haka. Cikin abinda bai wice sakanni ba karfen wajen yafara narkewa kaman an zubawa kankara ruwan zafi. Saida suka tabbatar yabada wajen da mutum zai iya shigewa kafin dukkkan su suka hau,tareda afkawa cikin gidan. A yanayin yanda suka dire a tiles din gidan,yakai karar ya ankarar da hankalin mai gadin,saidai ko kadan hankalinsa ya tafi ga wata mata dayake mata magana a bakin get wajen misalin karfe 11:30pm,a cikin magagin bacci mai gadin yaji bugun kofar gidan,tsorone ya ɗarsu a cikin zuciyarsa,dan yasan ba kowa bane sai barayi,shikuwa yanda yake gudawar nan,ko iskan suka saita masa jefarshi zatayi. Har ya koma zai cigaba da kwanciyarsa dama ga sanyin da'ake,saikuma yaga rashin dacewar hakan,musamman da mutanen gidan suka yarda dashi suka bashi amanar kariyarsu. Tashi yayi cikin sanyin jiki ya nufi bakin get din,duk da daga kaga tafiyar dayake kasan ƙara ƙadance zata saka ya koma daga inda ya fito. Shuru yayi yana jiran yaji wanene,ga mamakinsa sai kuma yaji nishin mace,wacce take cikin mawuyacin hali. "Wayyooo,maga allah daga gidannan ya taimakamin dan allah" Saurin bude kofar yayi idonsa ya sauƙa kan wata mace,bazata wuce shekara ashirin da biyu ba,ga kuma ciki haihuwa ko yau ko gobe a jikinta. Kayan jikin ta da kuma yanda take maida numfashi ɗaya bayan ɗaya ya isa ya tabbatarwa da mutum halin data ke ciki. Karisawa wajenta yayi yadan bawa bakin kofar get din nisa kadan. Durƙusawa yayi a gabanta tareda tambayarta cikim tausayawa. "Baiwar allah lafiyah naganki a wannan wajen cikin yanayinnan da tsohon dare haka" Hannunsa ta kama na hagun wanda yake kusada ita,tamkar dukkan rayuwarta tana jikin hannunasa,numfasawa tayi da ƙyar kafin tace, "Bawan allah kai musulmine,kadubeni da idon rahma,a matsayina na ƴar uwarka musulma,wasune suke bina zasu kasheni,yanzu haka ƙishirwace ta kamani kaman zan mutu,shine na keso ka taimaka min da ruwan dazan sha dan allah" "Toh amma baiwar allah bakya bukatar inda zaki zauna kuwa,bai kamata ki zauna a waje ba,idan na shiga gidan ma kinga ke kadaice a wurin" "Ina bukatar hakan sosai,saidai kar na takuraka dayawa shiyasa kaga nace ka bani ruwan ma ya isa " "Ahah baza'ayi haka ba,a wanann halin dakike ciki rayuwarki nacikin haɗari sosai,shigo daga cikin na kawo miki ruwan" Har ta tashi zasu shiga sai idonta ya hango wucewar wani abu cikin gidan. Bata tantance menene ba kawai sai tayi Saurin kama hannun mai gadin wanda yake kokarin juyawa wajen da idonta ya hango,hankalinsa ya bayar kanta ganin yanda ta rike mararta tareda sakin ɗan marayan nishi. "Sannu baiwar allah,lallai kina ganin rayuwa kam,barina kawomiki ruwan koh" Ɗaga kai kawai tayi,dan maganar ma ta gagareta. Bace wa ganinta yayi ya nufi wani lungu na gidan,da alama anan zai samo ruwan. Zama tayi a bakin barandarsa inda ya barta tana maida numfashi. **______**_______** A hankali cikin sanɗa suka samu nasarar shigewa gidan,ganin yanda wata mata ta samu nasarar ɗauke masa hankali. A bakin kofar falon suka tsayah,inda ɗaya daga cikin su ta saka wani a bu a kofar makullin. Nan da nan kofar ta bude suka shige. Rarrabuwa sukayi kowanne yayi wani wajen,hanyar balcony daya daga cikinsu yayi inda zai kaita dakunan dasuke wajen,kara kunnensa yayi a jikin kofar domin jin wannene na mai gidan. Ganin sun dade amma basu ganoba yasa dayah daga cikinsu yah daga wayah tareda danna kirah "Ogah mun kasa gane a wanne ɗaki fah yake,gashi kince karmu kuskura mu bari wani ya ganmu,tayah zamu gane ɗakin dayake toh?" "Mtsww shiyasa fah nashiga aikinnan dan nasan sai kunyimin shirme,har yanzunku bazaku iyah gane yanda zaku fitar da kurege daga cikin raminsa ba,indai anan dabararku ta ƙare to zan san yanda zanyi daku,ƙanana ma in an basu aiki sun fiku iyawa, ku fito daga gidan kafin a ganku,zanji dashi ni,shiyasa fah nake aikina ni kadai babu ku" "Kiyi hakuri v-lady zamuyi yanda ya dace sosai,kinsan abinne sai a hankali" "Okay shikenan na baku minti ashirin ku fitomin dashi daga gidan,idan ba hakaba kuma zan tafi na barku ku kukasani" Daga ta kashe wayar tana sauke ajiyar zuciya,sai a sannan na kula ashe dukkansu matane,tsabar kawai kwarewane da kuma taurin zuciya yasakasu yin abinda ba kowanne na mijinba. Kiran sauran abokan aikin tayi tareda cewa, Ɗayace daga cikinsu tace "Kai ni tsiyata da itah idan wani ya ta'bota to ba sani ba sabo da ƴan uwanta,hmmm inka gane halintane zaka san ya take Hakane kam,yanzuma tace ta bamu nan da miniti ashirin,mai kuke ganin za'ayi,hmmm gashi tace karmu yi wani abinda zai ta'ba iyalansa,da tuntuni mungama da shi fah" Tafaɗa cikin ƙosawa,suma jugum sukayi,can sai taji ƙarar massage a wayarta, Dubawa tayi ganin an saka v- lady, "Yau yadawo kasar bayan wata biyu,dan haka dole idonsa biyu shida matarsa basuyi bacciba,a dakinsa zai zamo dole suke,saboda kowanne gida yawanci ɗakunan yara na kusada na matar gida. Dole zakuji dakin yafi kama turaren Emergency,saboda shine turaren dayafi amfani dashi,ku shiga daƙin,kafin tayi wani abu ku fesamata maganin bacci,shima ku fesamasa sanann ku kawo minshi ina jiranku" "Wow kuga yanda v-lady ta solver abinnan cikin ƙanƙanin lokaci,lallai dole mu sara mata,maza kuzo a kammala aiki" Sakin hancinsu sukayi domin jin ta ina turaren yafi ƙarfi a gidan,dukkan su samun kamsu sukayi a bakin wata ƙofah wadda take ƙarshen wani corridor. Dukkan su kallon kansu sukayi,tabbas hasashensu gaskiya ne,dan gashinan suna jiyo numfashinsu a ɗakin. "Vl4 ki tsaya ta gefen dama,ke kuma Vl5 ki tsayah ta gefen hagu,bari na shiga,ina shiga kowaccenku sai tayi kokarin fesamusu kafin suyi wani ƙoƙari,clear?" "Yesss Vl3,dukkan su suka haɗa baki. Tana buɗewa kuwa suka feshemusu fuska da spray ɗin,faɗawa sukayi ta bayansu akan gadon,shikamma uban gayyar daga shi sai gajeren wandon daya samu damar gyarawa lokacin da yaji motsin shigowarsu. Ɗaukar bargo sukayi suka jefawa matar tasa tareda kinkimarsa suka fita daga gidan. Ta bakin get din suka zo suka wuce abinsu hankali kwance, Haɗa ido sukayi da matar da take zaune a wajen,ko kallonsu batayiba sai aikin nishinta take,duk kuwa da cewar akan idonta suka wuce ɗin. Lokacin mai gadin ya kawo mata ruwan,ya tafi nemo mata magani suka wuce,shikuma sannan ya dawo. "Sannu baiwar allah ya jikin dai,ko nayiwa hajiya magana su taimaka miki,dan naga kaman ko haihuwa zakiyi" "Ahah baba ba haihuwa bace,kawai wahalar dana shane,watan haihuwar bai kama na tukunna,zan iyah amfani da banɗakinka idam babu laifi" "Lahh ba komai ki shiga,barina ɗan zagaya kafinnnan" "Toh nagode allah ya saka" Bata daɗe da shiga sashennata ba saigata ta fito tana gyara zaninta wanda duk ya yage ,kallon mai gadin tayi wanda yake tsaye tareda cewa, "Baba zan tafi,dan akwai tasha nan kusa,nasan yanzu wanda suke bina sun wuce,zan je da sassafe na kama hanyar ƙauyenmu,dan dama a wajen ƴar uwata nake anan" "Da naso kiɗan zauna ganin yanda kike,amma tunda kince haka shikenan,gsshi kuma bansan sunan ki ba" "Hhh baba kawai ka ƙirani da MABARACIYAH dan haka kowa ke ƙirana,dan nan ɗin ma barar mukeyi dana taho daga garinmu,saida nazo nagane ashe inada ciki na tsohon mijina da muka rabu" "To shikenan allah ya bada lafiya ki kulada hanya" Fita tayi a hankali kaman bazata iya kaiwa karshen layinba. *____*_____*____* Wata macece mai kaya riga da,zani na hausawa, ta fito daga wani lungu,kaɗan kaɗan ake ganin fuskarta saboda yanayi na dare sosai,a hankali take tafiya kaman mai tsoron kar wani ya ganta,saida tazo saitin wani lungun kafin ta shiga. Wata leda ta ciro a wani kango ɗan nesa da gidan data fito. Zanin jikinta ta cire ta jefar da kuma rigar,buɗe ledar tayi saiga baƙaƙen kaya sun bayyan irin na wanda suka dauƙi alhajin,saidai kuma nata akwai purple din macijiya (Viper)ta buɗe baki a bayan rigar ƙatuwa. Nan da nan ta saka tareda daukar rikagar sanyi mai irin kayan itama ta sakata,sanann ta ɗau Hula da kuma baƙin glass. Waya taciro a cikin aljihunta tareda yin magana cikin dakewa, "Kuna ta wajen ina yanzu haka,dafatan babu wanda ya ganku ko" "Eh V-lady babu wanda ya ganmu,muna karshen layin dakike tahowa". Tafiya kaɗan kuwa tayi saigata ga baƙar mota,buɗe baya tayi ta shiga,motar ta tashi ta nausa kan hanya,dan dama jiran shigarta akeyi . Sun dade suna tafiya har suka bar cikin gari suka shiga wani ƙyauye,a bakin wata bukkah suka tsayah a bayan garin. Dukkansu fitowa sukayi yayinda ɗaya daga cikinsu ta kinkimi mutumin zuwa cikin gidan,yayinda wacce take tuƙa motar kuma ta koma da baya zuwa cikin gari. Bukkar ƴar karamace bata wuce ace mutum ɗaya ne yake rayuwa a cikinta ba,saboda yanayin ƙanƙantarta da kuma yanda ta tsufah. Babu komai a cikin bukkar sai fili mai rairaiyi(ƙasa). Wani key wacce suke kira da v-lady din ta ɗauko tareda sakawa a wani dan abu dayake gefen bangon wajen kaman makunna. Tsakiyar ɗakinne ya buɗe saiga wani rami ya buɗe,dukkansu faɗawa sukayi cikin wajen.. Boyyayar hanyace ta karkashin ƙasa,wacce zata kaisu wani waje daban,sunyi kaman minti biyar suna tafiyah a wajen kafin suka bullo a fili mai ɗauke da wani gini babba,saidai ba lallai ya ɗauki hankalin mutane ba. Wasu matane a bakin kofar suka buɗemusu suka shiga. Abin mamaki da al'ajabi,gidan ko kaɗan baya kama da yanda yake ta waje,saboda kofah kofah ce dashi,sannan kuma da wurare daban daban. Wani ɗaki na karfe direct suka nufah da mutumin dayake rike a hannunnata, "Ku dakata ,ina naga kuna nufin kaishine,a zatonku daɗewa zayyi kuke nufin kaishi kejin masu jimawa,ku ajiyeminshi anan" Ajiyeshi sukayi suna kallon yanda yake sakin jiki saboda magananin bacci da har yanzu bai bar jikinsa ba, Kujera taja ta zauna tareda ƙaremasa kallo,hankalinsa ma wato akwance kaman bai san inda yake ba. Ɗaga hannunta tayi iyah ƙarfinta ta zabga masa mari. Wata gigitacciyar zaburah yayi kafin ya bude idonsa yana ƙwarewa wajen kallo. "Hajiya salah wayyo" Hada ido sukayi da itah ta ɗaga masa girarta ta hagun alamar kalleni da kyau. "Ƙaremin kallo dai doctor mai tashe,dan tsabar dama kai tantirine wato da sunan matarka zaka tashi daga bacci ko kuma inkaji wuyah koh,to ƙirata da kyau dan ba ganinta zaka sake yiba har abada,bari kaji bayani babbakeka zanyi a wajennan babu mai kwatarka,yau ma kuwa basai gobeba" "Wayyo to wacece keɗin ranki yaɗaɗe?" " raina ya daɗe? Ameen wanann shi ake fata,danna samuma naci karena babu babbaka ba,inason wanann addu'ar sosai. Har yanzu yallabai baka ganeni ba,ina ɗaya daga cikin masu tsaron dasuka kaika har gidanka cikin koshin lafiya jiyah,suka kuma yimaka fatana zaman lafiyah,saikuma gashi na laluba na kwamusoka bayan na kaika gidan. To ya kaji zancen yayi maka daɗi?" ,"mai kike buƙata,idan ƙudine zan baki number dazaki ƙira a baki,nasan kidnapping ɗina kikayi koh?" Kaga nayimaka kama da wacce take neman kuɗi,wato ku koma da kuɗi zaku fansheshi koh,duk abinda kuka yi idan aka nufo kanku saiku bada kuɗi,saboda kun saku kaji zaku saka musu tsaba koh" "To mai kike buƙata kika kamani,ko wanine ya aikoki daga cikin maƙiyina,sabod......." Sake gwaura masa wani marin tayi,idonta babu alamar tausayi. " yanxu yarinyah kina ta marina,kinsan fah nakusa jika dake,ke kuwa musulma ce kuma bahaushiyah,wane abune yasakaki yin aikin da namiji ma sai wanda aka tsinewa a cikin al'ummah yakeyi?" "Hhhhhhhhh inama mutanen dakuka mutu kuna nan kuzo kuji Dr. Bukar yana wa'azi,oh wato bai kamata nayi haka ba koh,to ai yawan shekarun daka bani su suke ƙara sakawa na ji daɗi zuciyata tayi sanyi idan na marekan,oh kai a iya marima kake tunanin tsayawata wai. Vl3 Vl4 Vl5 dukkanku ku fara dukansa da sandunan hannunku ƴan uwa har sai nace ku bari tukunna" Kaman jira suke kuwa suka fara dukansa kaman an aikosu gareshi,tun yana ihu har yayi shuri,abinka da jikin daya saba da hutun kasashen waje,tashi daya jikinsa yayi luhu luhu kaman jikin kazar turawa wanda aka figeta. "Ku dakata ya isa haka,nagaji daganinsa ma ni" "Wyyyo wayoo mmm....mai kike bukata ...kince ba kuɗi ba sanann kince ba aikoki akayi ba to me kike so" " anzo wajen gwanda da ka tambaya da bakinka,kasan mai nake so yasa na kamoka?......ƘODARKA nake so kabani,so nake ka cirota ka bani ita da hannuka,idan ka ciromin ita zan barka ka tafi abinka,idan kuma baka ciromin itaba nan da minti biyar zanzo na cira da karfin gaske,zabi ya rage ga naka,kokayi da kanka ko kuma ni nayi maka yanzu nan" Zaro ido yayi hankalinsa yayi matukar tashi,dukan da'akayi masa bai ɗaga masa hankali ba yanda cirar ƙodar ya ɗaga masa hankali. Jefa masa wuƙa tayi mai masifar kaifi gabansa,tareda jingina a jikin kujrar tana jiransa. "Wacece ke,lallai ke ba iyah mai bada tsaro bace kawai,ke watace daban,meyasa duk duniya baki biɗi ƙodar kowa ba sai tawa,hakan ma kuma na cire na baki yanzu batareda an bi ƙa'idoji ba na asibiti" Wata dariyar tasake sheƙewa da ita kafin tace, "Oh dama wannan ƙa'idojin suna nan kuma suna aiki? ,ni nayi zaton baka sansu ba ai,......minti biyu yarage maka ko buɗe cikin ka ka fitomin da ƙodarka kokuma na kar'ba na cira da kaina,sassauta maka nayi shiyasa nace ka ciromim da kanka,nima na iya cirar" Zuwa sannan ya kasa cewa komai,babu abinda yake sai kallo wuƙar take gabansa kawai......ƙarar tashin ta ne yasashi zabura yaja daa baya,saidai jikinsa bashida karfin yin hakan ko kaɗan. "Dr nawwarah(Vl6)fito ina son ganinki anan wajen yanxu" Fitowa tayi da kaya irinna su maryam a jikinta amma ita da ɗan ƙaramin glass fari a fuskarta. Razana Dr bukar yayi yana ja da baya,da alama ya shaida Vl6 ɗin, "V-ladies ku kaishi ɗaki a fara aiki,ina so ki ciremin duka ƙododinsa ki kawomin su nan,ku maye gurbinsu dana roba yanzunan,kawai so nake na gansu. Tashi ka bisu su ciromin ƙodarka" Fisgarsa sukayi aka shiga dashi ɗakin da dr nawwarah ta fito,tun tana jiyo ihunsa har yayi shuru. Can kaman zuwa minti goma saiga Vl4(safiyyah)ta fito da ƙoda biyu akan tire,duk jikinsu jini daga gani sannan suka fito dasu daga inda suke aiki. Ɗaukar ɗaya tayi daga kan tiren ta mitsitstsiketa a hannunta saida ta fashe jinin cikinta ya fito. Lumshe ido tayi tareda jan numfsshi kafin tace, "Aikin ku yayi kyau yan uwa,ina godiyah gareku" "Bakida buƙatar faɗan hakan ƴar uwa,an zama ɗaya kuma ana tare iya wuyah" Jefar da ita tayi ta take a ƙasa, "Wannan na fasata dannaji sauƙin raina,ɗayar kuma ku kaita ga asibiti a sakawa wanda yake buƙatar ........" Tun kafin tagama magana kira ya shigo wayar tata ,ɗagota tayi kusan fuskarta inda sunan Dec Sadeeq ya bayyana,murmushi tayi kafin ta ɗora wayar akan kunnenta. "Sir!!!?" "Ina kike khamriyyah maza ki sanar da sauran abokan aiki kan cewar akwai aikin daya bullo,dan yanzu labari ya ƙara zuwa mana Dr Bukar ya bata a darennan,ina jiran zuwanku office da karfe shida,bayan na gama bincike yanzu" Sauƙe wayar tayi tana ƴar dariya, "Ke Maryam (vl3),tunda Sabriyyah bata nan(Vl1),tana kan aiki ki ja ragamar duk abinda za'ayi,ni zan tafi muje mu kama wanda ya sace Dr bukar,bari naje gida na shiryah,sannan ki kiramin khairiyyahh (Vl2)ta turomin document din danace tayi min copy" Tafaɗa tana kara sautin dariyarta ta rainin hankali, "Angama v-lad....." "Ku daina kirana da viper lady idan ina yanayin wasa,ku kirani da ɗaya daga sunana kawai,kunsan inason a dunga ƙirana da sunaye da yawa" Tana gama shaƙiyancinta ta bar wajen,jijjiga kai maryam tayi tareda cewa "sai oga"cikin dariya da kuma yanda aikin shugabar tasu yake burgeta sosai,ita kanta tana mamakin yanda cikin sauki ogar tasu take sajewa da duk aikin da tasa a ranta sai tayi. Wani mashin da ɗauka a bayan gidan a cikin garage,wanda yawancin barayi suke amfani dashi saboda gudunsa. Wata hanya ta nufah a cikin jejin siririyah wacce zata kaita cikin gari a mintina kaɗan. Ana kiran sallahr farko ta shiga gidan,ɗan karamine madaidaici,amma kuma yanada kyau sosai. Banɗaki tashiga ta wanke jikinta tass,na aikin data kwana tanayi. Riga tasaka doguwa sannan ta jumbula hijabi shima doguwa. Sallayah ta hau tafara da kabbarar harama ta shiga sallah. A yanayin lokacin da kuma yanda take tayin sallahr ya tabbatar da ba asuba take ba,mai yiyuwa nafila take ko kuma biyan bashi na sallolin baya. Kiran assalatune yasata yin sallama kafin tashiga sallahr farillah ta asubar. Bayan ta idar ta naɗe tana addu'o'i kafin ta jawo qur'ani,suratul hijr ta buɗe ta fara karantawa cikin kwarewa,daga jin yanda take karatun kasan ba karamin haddar wajen tayiba,duk karatun cikin ruwayar warash takeyi,mamaki abin yabayar,domin a wanann zamanin da wiyah ka samu mace na yin ruwaya warash,saboda yawanci yanzu ƙira'ar hafs tafi yawa ga mata. Duba agogo tayi ƙarfe shida dadai,sai a sanann ma ta tuna da aikin da ogah ya ƙirata zasuyi na binciken 'batan Dr bukar. Hijabin jikinta ta cire da sauri da kuma rigar,wardrobe ɗinta ta buɗe bayan ta ajiye qur'anin. Kayan state security ta fitar,baƙaƙe amma kuma ba irinna ƴan sanda ba,cikin mintuna kaɗan ta gama shirin kana ta tsayah a gaban madubi tana kallon kanta. Abubuwa da damane suka bayyana akan fuskarta,alfahari,nadama,ƙunci,cikar buri da kuma rashin danasani. Ganin suna kokarin dulmiyata wajen da bata shiryah saka kanta a ciki bane yasa ta shafesu tareda ajiye wani murmushi akan fuskarta tana sarawa kanta da kanta ta madubin. Idontane ya sauka akan barge ɗin take kafaɗarta ta gefen dama,da sunanta da kuma status din ta,a duk sanda ta kallah sai ta tuna da alkawarin datayi wa ƙasarta a ranar daza'a rantsar dasu bayan sun gama training na shekarah uku. __nayi alkwari ni khamriyyah,zan tsaya tsayin daka wajen ganin na bada rayuwata ilimina da kuma lokacina wajen kare wannan ƙasa tawa da kuma al'ummar dasuke cikinta. Sannan zanyi yaki da zalunci da kuma kokarim kawo zaman lafiya da kwanciyar hankali ga yan kasata,sannan zan yi aiki bisa kan gaskiya da kuma amana___ Kana ganin fuskarta zaka hango tsagwaron tashin hankali lokacin data tuna da alkawarin datayi a gaban shugabanninta da ahalinta gabaki dayah. Saurin basarwa tayi tareda cewa, "Mtsw miye zan tsayah ina wani tada hankalina akan wata ƴar ƙaramar rantsuwa,ai ba dan inaso nayi ba,dan ganin idon mutanene,tunda nasan banshiga aikin dan nayi abinda suke fataba,kuma ɗanyen aikina bazan daina aikatawa ba,yanzu ma aka fara jin kukan marayu da zawarawa a garinnan billahillazi,babu abinda zai dameni kuma akan hakan,wacce na kashe mijinta saitaje ta auri wani,wanda kuwa na kashe ubansa sai ya tashi ya zage dantsen kulada kansa. Ƴan bantan uba,wato mu muna ta aikin garari sukuma iyayensu suna kulada su,idan muka kwashe iyayen sai a zama ɗaya kawai" Tana gama maganar ta saita yatsanta kaman bindiga akan fuskarta ta cikin madubi tace "Tassss ,bari kuma muje mu gwabza da ogah,dan shima nasan jan wuyane da kyar ake tsallakemasa,amma dai ba a wajena ba kam" Tafaɗa tana hure saman yatsarta kaman ta yi harbi dashi. Hularta ta dauka da dan karamin hijabinta sannan saikuma bindigarta,daga nan tayi waje abinta hankali kwance. _sadi-sakhna_ *(¯`*•.¸,¤°´✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿`°¤,¸.•*´¯)* *MABARACIYAH* (mai harshen damo) тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιε. _haƙƙin mallaka_ _*sadi-sakhna*_ (Yar mutan Jama'are) Paid book #400 3131951977 Auwal sadiya First bank Mai turo kati kuma ta wanann number MTN 09035784150 Mutanen niger su tuntubi wanann number +227 97 21 16 15 Naƙara shafin free har zuwa page 20,zuwa lokacin inka shiryah kazo a fara dakai ranar juma'a. _____________________ Assalamualaikum barkan mu da wannan lokaci *ABMAR COLLECTION* ina nan na kawo muku kayana masu kyau da sauki👌🏻 KAMAR SU:- Atamfa, Atamfa Mai golden,💁‍♀️ Lace ,Shadda lace Yadi, Shadda Abayas💥 Kids wear Takalmi, jaka, mayafai💥 Sleeping dress, kananan kaya na gayu🔥kayan kitchen, DA DAI SAURANSU ina Sokoto ina tura kaya ko ina da izinin ubangiji mai son kayana pc ina maraba daku siyan daya ko sari👏🏻domin neman karin bayani sai ku neme ni ta wannan number waya👉08101521252 nagode kwarai da gaske💃💃 Free page 5••6 A bakin office ɗinnasu ta ajiye mashin ɗinnata kafin ta shiga,kanta a sunkuye kana ganinta kaga gentle soul. Office din shugabannasu ta nufah,kasancewar babu kowa a headquater sai iyah wanda aka kira su aikin yin binciken. Ƙwanƙwasa ƙofar tayi amma kuma sai taji shuru,da alama bai iso ba kenan,ko kuma har yanzu suna wajen binciken,dan tun jiya ya ɗebi mazan suka tafi. Ƙarar wayarta ne ya katseta da tunanin inda Dec sadeeq din yake,ɗauka tayi ta kara a kunnenta, "Dec khamriyyah kina ina?" "Sir ina bakin office ɗinka yanzu haka" "Okay maza ki taho gidan Dr bukar muna can,akwai abinda nake so mu bincika,dan there is something odd about it" "Clear sir gani nan" Sauƙe wayar tayi tareda ɗan cija fatar bakinta,mai kuma aka samu da har Dec. Sadeeq ya ƙirata taje can,ba a nan zasu yi bunciken ba ne? Kardai ya gano yanda aka sace Dr bukar ɗin,kai bazaiyiyu ya gane ba,kwarewarsa bata kai har haka ba tukunna,duk da yana ganin shine shugaba amma har yanzu bai kama yatsana ba,idan naga ya gano sanja takun salo zanyi. Share tantamar dayake ranta tayi kafin ta nufi gidan Dr bukar ɗin. Tun daga bakin gidan yan sanda sunyi dafifi a wajen,duk da kuwa gari bai gama wayewa sosai ba. Mamaki abin ya bata ganin yan sandan ma harda masu babban matsayi,koda yake bawani abin mamaki bane kasacewarsa babban likita wanda ake ji dashi na ƙoda,da yake yawon buɗa ido akan aikinnasa a ƙasashe daban daban. Karisawa wajen tayi ta nunawa wani a wajen ID card dinta,saida ya dan sara mata kafin yabata waje ta shige. Cikin gidan ta shiga inda Dec sadeeq yake. Duk wanda abin ya shafa musamman ma Ƴaƴan sa sai kuka suke suda matarsa,masu dauriyar cikinsu ne mazan sukayo jugum kaman masu kar'bar gaisuwa. Kallo ɗaya khamriyyah tayi musu kafin ta karisa inda Dec. Sadeeq yake, "Barka da safiya Sir" "Sannunki da ƙokari,inasu Ahmad kuma ban ganki tareda suba," "shukurah tabada taakarda akan bata da lafiya" Kukan ɗaya daga cikin yaranne yakara tsananta tacika wajen da kuka,ga mutane dayawa kama daga yan uwansa da kuma mutanensa. Tashi khamriyyah tayi ta isa inda yarinyar take,ganin yanda yarinyar take kuka na rsshin mahaifinta ya sa wani dukan kirjin khamriyyan,saidai kuma ko kaɗan ta samu kanta da rashin nadamar abinda ta aikatawa ahalin. Dafa kan yarinyar tayi mai shekaru goma,in tace bataji tausayin yarinyar bama tayi ƙaryah,duk da batasan wani abu ba wai shi soyayyar uba. "Kiyi haƙuri kinji baby,dan kin rasa mahaifinki karki yarda zuciyarki ta karye,ki daure sannan ki tafiyar ta rayuwarki,ki kasance kullum cikin dauriya da kuma jarumta,babu wanda bazai iyah yin dauriya ba saidai in bai dage ba" Ɗaga kai yarinyar tayi tareda yi mata ɗan karakin murmushi. "Anty nima inason zama irinki,wacce take bada lokacinta wajen ƙoƙarin nemowa ahali dan uwansu idan ya bata" "To shikenan amma kiyi tunani kafin sannan sosai kinji,dan ba komai ne kake ganinsa a ido kuma ace cikinsa haka yake ba,karkiyi abu dan kinga wani yayi,saboda mai yiyuwa dalilinsa nayin hakan daban kekuma bakida masaniya akai,menene sunanki?" "Sunana Fadilah Bukar" Rutse ido khamriyyah tayi lokacin da yarinyar ta ambaci sunan ta tareda karawa da sunan dr bukar ɗin,abin akwai takaici,saidai kuma haka allah yaso fitar da ita daga tsatsonsa,duk ita ɗin ta tsaneshi amma kuma uban tane ita. Maganar Dec. Sadeeq ce ta katseta data ji yana cewa "Dec. Khamriyyyah,inaga akwai wani abu gameda kidnapping dinnan,Hajiya Salah tace ganin shigowar wasu mutane tayi masu baƙaƙen kaya,daga nan kuma bata sake ganin komai ba sai tashi tayi da asuba taga ba mijinnata. Sannan a katangar baya ta gidan akwai alamar shigowar mutane guda uku,sun diro cikin gidan,amma kuma babu alamar sun fita ta wajen. Duk yanda akayi ta kofar gidan suka fita,kuma babu alamar an buge ƙofar gidan,hakan yana nuna da key ɗim ƙofar aka buɗe" Dukkan su shuru sukayi suna kallonsa,idonsa yana kan khamriyyah dan yaji mai zatace,ɗaga girar ta tayi kafin ta ɗan waina idonta alamar tafiya tunani. Dolene nayi wani abun kaman ko yaushe,nasan dama zai gano wanann ƙana nan evidence din,dan haka banyi mamaki ba ko kadan saidai abu ɗaya shi....... "Dec. Khamriyyah naga kinyi shuru kaman mai tunani" Gyaran murya tayi alamar dawo hankalinta kafin ta hango mai gadi wanda yake ɗan nesa dasu yana magana da wani ɗan sanda. "Am baba mai gadi a yanda binciken ya tabbatar,an samu shaidun cewa masu aikin sace uban gidanka sun shigo gidanne ta katanga,duba ta yanda alamun durowarsu ta nuna,saidai kuma babu alamar sunyi amfani da hanyar har ila yau wajen fita. To hakan yana nuna cewa ta bakin get suka bar gidan,kuma babu alamar sunyi amfani da karfi wajen bude kofar ko kuma makulli. Kai in takaice maka bayani ma,zanen hannunka muka gani 'baro 'baro a jikin kofar. Shin mai kake a daren jiyah da har kunnenka yakasa jiyowa ƙarar fitarsu da kuma shigowarsu,sannan ina kaje a lokacin da karfe kusan 12:00pm na dare,dan yadda abin ya nuna zanen hannuka yayi akallah awanni shida a jiki,ko kuma daukar makullin sukayi a wajenka suka bude,sanann kuma babu duka ko barazana ka dauka ka basu?idan ba haka ba shin da haɗin bakin ka a.........." "Kiyi hakuri madam kimin rai,wlh ba haka bane yanda kike tsammani,ni ban haɗa baki da kowa ba hasalima bana wajen lokacin da suka zo ɗin. Wata mata tazo gidanann a daidai lokacin da kuka ambata,na ganta da ciki da kuma tana cikin mawuyacin hali,shiyasa naga yakamata na taimaka mata" Mamaki ne ya zagaye fuskar khamriyyah,wacce mata kuma yake nufi kuma da ciki sanann a duhun dare? "Wace irin matace da tsakar dare zatazo neman taimako?" "Nima Bansani ba madam,da farko naji tsoron taimakonta saikuma naga yanda take nishi daya bayan daya,hakanne yasa na taimaketa" "Daga nan kuma sai ka bar kofar a bude kuma?, ko me?" "Ahah tacemin tana bukatar ruwa,shiyasa natafi domin debo mata a fanfon baya,dan nawa ya baci,bayan na bata ne nayi kokarin ce mata ta zauna tunda tace ana biniyarta,saikuma tace wai akwai tashar mota gaba kadan zataje ta shiga" Tun kafin khamriyyah tasake bude baki tayi masa magana Dec. Sadeeq ya matso kusada mai gadin tareda cewa, "Shin akwai Ctv camera ne a gidannan?" "Eh Akwai amma guda biyuce kawai,daga ta bakin get din sai kuma ta wajen motoci" "Nuna min nagani yanzu" Hanyar wajen dakinsa yayi su khamriyyah na biyeda shi har dakin da suke. Dec. Sadeeq ne ya matsa gaba kadan ya kunna screen din abinda ya faru a jiya da daddaren. Ga mamakinsa har ma dana mai gadin babu komai daya nuna cewar wata mata tashigo. Abinda ya kara girgizasu shine yanda iya mai gadin ne a ciki,inda ya fito yana magana sannan ya matsa alamar mutum yashigo,har inda ya tafi zuwa debo ruwan,da kuma wucewar mutane da bakaken kaya. Bayan fitarsu kuma mai gadin ya dawo dauke da kofi a hannunsa ya miƙawa wani waje,kofin ne ya tsaya a iska kafin ya karkata alamar wani mutum boyayye a wajenne yasha. Dukkansu zaro ido sukayi kowa na kallon kowa,wanann abin akwai ayar tambaya a ciki. Shikam mai gadi jikinsa sai karkarwa yake dan ba karamin bugarsa abin yayi ba sosai. Magana ma kasa cigaba yayi,abinka da mai gudawa dama,tuni yayi hanyar bandaki yana duk addu'ar data zo bakinsa. Numfasawa Dec. Sadeeq yayi kafim ya kalli khamriyyah "Wannan abin akwai daure kai,a yanda na fahimta wamda suka daukeshi sunada alaka da matar da mai gadi yace yagani,duk da banida masaniya shin mutum ce ko aljan" Duk maganar dayakeyi khamriyya batace komai ba,dam itama akwai abinda take sakawa a ranta daban. Suna nan tsaye mai gadin ya fito daga bandakin yana zuzzura ido,jar yayi hanyar barin wajen ya tsaya cak jin maganar da Dec. Sadeeq yayi masa. "Shin kozaka iyah kwatanta mana yatake,ya kuma siffarta yake" Marairaice fuskarsa yayi kaman mai shirin rusa kuka. "Haba haba yallabai,yanzu karasa wace mace kake so ma siffanta maka sai aljana mai tsohon ciki hakanma,kalan na siffanta ta, mai ɗakina datake kauye ta haifi mai kamarta,yaudarata ma datayi na yafe haka" "To naji dalilinka,amma ko sunanta bata fadamaka ba" Sauke ajiyar zuciya yayi kaman bazayyi magana ba saikuma yace, "Cewa tacemin na kirata da MABARACIYA kawai,dan wai dama ita bara take" Shiru Dec. Sadeeq yayi yana cizar fatar bakinsa ta kasa kaman mai tunani,can kuma sai ya zabura tareda yin magana kaman wani zai rigashi. "Haka tace maka sunan ta MABARACIYA?,abin da mamaki,inkuwa itace to ai yakamata ace ta mutu,ko akwai wata bayan ita kai?" "Wacce magana kake ne sir" Dagowa yayi yana kallon khamriyyah wacce ta kureshi da ido. "Ahah babu komai,idam mun zauna zan miki bayani,yanzu dai yakamata mu koma headquarter dan akwai abinda nazarinsu sai a can" "Okay sir" Murmushi yayi kafin yace, "Aikiniki yana kyau Dec. Khamriyyah,kinda jajircewa da nuna bajinta akan aikiniki,hakanne yasa nafi jin dadin aiki dake" "Nagode" Shine abinda ta fada cikin karamar muryah,da alama taji dadin yabonnasa,duk da kuwa yanda zuciyarta ke kunshe da Abubuwa kala kala na abinda ya faru a gidan. Tare suka fito daga gidan,burka mashidin nata ta dungayi amma kuma sam yaƙi tashi,kallonta dec. Sadeeq yake wanda bai shiga motarsa ba yana ganim mai take,kafsewa tayi tareda juyar da kanta tana kallon gefe. "Meyasamu mashin din naki,uhm kuma mata da hawa mashin..." "Ogah toh keke zan hau inba mashin ba,ina naga kudin siyan mota toh" "Eh naji,bari mashin din bala zai tafimiki dashi zo na nasaukeki a headquarter" Amma sir daka barshi ma zan......" "Kinga na gama magana,ki barshi zai gyaromiki inyaso sai ya kawomiki can din" Ajiye mashin din tayi kafin ta nufi motar tasa,daga gani kasan dam babu yanda zatayi ne kawai. Tafiya suke a hankali babu mai cewa wani komai,wayar tace tayi kara ganin shugabansu ne yasa ta daga,a yanda take amsa wayar kasan ko a gabansa iya kaci kenan. "Yes sir ga shi nan ma sir din yallabai" Mikawa dec. Sadeeq wayar tayi tareda magana cikin girmamawa, "Gashi ogah,shugaba yace ya kira wayarka bai sameka ba tun dazu" Karba yayi ya saka a kunnensa yafara magana,can kuma ya kashe ya mika mata wayar "Dec. Khamriyyah kiyi hakuri zan ɗan bi ta gidana na dauko wasu takaddu kinji" Zaro ido tayi da alama maganar batayi mata ba sam. "Amma ogah kasan fah madam bazata so hakan ba,dan duk cikin ma'aikata matannan nice bata so saboda tana tunanin sosayya mukeyi dakai" Yar dariyah yayi kafin yace, "Karki damu babu abinda zai faru,zaki iyah zama a mota ki jirani har na fito,hmmm Amrah akwai kishi sosai" "To shikenan ogah babu matsala" Karkata motar yayi zuwa gidanansa,kaman yanda ya fada a motar ya bar khamriyyah,saidai kuma yazo fita ya kula da wani ciwo a kafarta yana zubar da jini,da alama lokacin da take burka mashinne ya yanke kafarta,komawa yayi ya zauna tareda kallon wajen "Subhanallah a Ina kika yanke kafarki haka" "Ahh ogah a wajen mashinne dazu,ba wani abune mai girma ba inna koma gida zan gyara wajen" "Ahah idan kika barshi zai iyah zama miki ciwo babba,shigo ciki ki gyara da first aid yanzu" "Amma ogah....." "Banaso idan na faɗamiki magana ko nanemi yimiki taimako ki dunga musawa fah" "Kayi hakuri ogah" Fitowa tayi a motar kanta a sunkuye har suka shiga cikin gidan,sallama tayi daga bayansa wanda yasa Amrah tsayawa daga rungume dec. Sadeeq din,sannan Murmushin datake ma ta tsaya dayinsa ta murtuke fuska. "Baby mai nake gani a bayanka,mai tazoyi kuma a cikin gidana bayan kasan bana......" "Kinga wify ba wani abu bane trust me,mashin dinta ne yasamu matsala gashi zamu je office yin wani bincike,toh abbah yace na ɗauko masa wasu takardune dasuke wajena shiyasa na zo gida yanzu,da farko nace ta jirani a mota saikuma naga kafarta da ciwo,kiyi hakuri tana gyrawa zata tafi a gidanki mai gida" Yafada yana jan hancinta,ajiyar zuciya tasake,saidai duk da haka hankalin ta bai gama kwanciya ba sosai. Dakinsa ya wuce domin dauko box din,yayinda khamriyyah ta zauna a ɗan bakin kujera har ya dawo,dan itama kanta yanda take daga gani kasan bata son zaman wajen. Daya dauko akwatin niyyar tsugunnawa yayi zai sakamata,suna hada ido da Amrah ya miƙawa khamriyyah akwatin saboda ganin kallon da amrah ta bishi dashi,sake komawa dakin yayi ɗauko abinda yazo ɗauka. Lokacin daya fito tagama gyara wajen,godiya tayimasa kafin suka fita daga gidan. A hanyar su ta zuwa office din har sun kusa isa wayarsa tayi kara daya saka a jikin charger mota,number Ahmad ceh dan haka ya dauka da gaggawa. "Ahmad menene ya ake ciki" "Eh dama wani massage ne yashigo wai yana cewa mu shiryah gobe zasu dawo da dr. Bukar din" "Da wane layi aka kira,kun samo karin bayani akan wanda ya turo sakon?" "Ahah ogah,munbi diddigin layin amma ya nuna layin baya nan (not exist)" "Oh shitt kucigaba da dubawa,yanzu barina sauke khamriyyah a gidansu,ta ɗan samu rauni,zan zo nasameka daga nan" A bakin kofar gidannata ya ajiyeta yana ta sauri,itadai kallo da idone nata kawai. Ko amsa Godiyar datake masa bai yiba yayi gaba. Itama shiga gidan tayi tana tafiyah dakyar saboda gajiyar data diba a ranar. Karo sukayi da wata yarinya mai kaman shekara bakwai,tana rike da kofi da cornplask a ciki. "Anty sannu da dawowa" "Ina diddy take da kuma fadeel saike kadai?" "Suna baya yana taya diddy wanke wanke" "Ke kuma kina nan kina shegen ci koh,bake yakamata ki tayata wanke wankenba?" "Yi hakuri anty bazan sake zama ban tayata ba kinji anty" "To naji bani waje toh,kuma kar wacce ta shigomin daki zan hutah,idan anty maryam da shigo da anty balki kice musu su jirani idan na gama hutawa zamuyi magana karki manta fah kinji" "Bazan manta ba,zance su tasheki idan sun shigo,sun tafi siyyar kayan abinci ne dama" "Kaiii fadeelah yaushe xakiyi hankali ne ƴar butar ƙaniyah kai" Takalminta ta cire tana niyyar ƙwaɗamata taruga da gudu wajen diddyn,dan ta taimaketa. Ƴar dariyah tayi da halayyar yarinyar kafin ta jijjiga kai ta wuce daƙinta. Ƙiran magribane ya tasheta daga baccin datakeyi,hamma tayi tareda yin salati kafin ta faɗa banɗaki. Wanka ta iyo da alwala,ta saka kananun kaya riga da wando,amma irin buje ɗinnan. Maryam ta samu da balki da kuma twins ɗin da diddynsu suna cin abinci ,karisawa tayi itama ta zauna,kallon ta sukayi kafin suka hada ido,da alama da abinda suke saƙawa,haɗe fuska tayi tareda cewa, " menene naga kuna kallona haka,sanjawa nayi kome?" "Ahah babu abinda ya sanja ogah,kawai dai sir ɗinnakine ya aiko miki mashin ɗinki,yace kuma ya jikinnaki,harda magani ma ya aiko,wanann kuwa ba folawa yayi ba kuwa?" " ahah kakar folawa kai,mai zanyi dashi toh,kun riga kunsan matsayinsa a wajena bayan shugabana ma,beside ma he is not my type,dan haka karna karajin kun hadani dashi" Tafada tana caka cokalinnata a cikin abincin,dukkansu shuru sukayi babu mai ce wa uffan sun sha ruwan jikinsu. Fadeelah ce ta tuntsire da dariya harda faɗawa kan ƴar dattizuwar dasuke ƙira da diddy. Tsaida idonta tayi akan yarinyar wacce ta har yanxu taƙi barin dariyah,saima nunata datake da yatsa. "Hhhhhh keki ga anty saikace wlh boss ɗin film ɗin Masheƙi" Kamo hannunta tayi zata daketa,aikuwa ta rutse idonta tareda cewa "Maaaama tahhhh" Saurin sakinta tayi jin ta ambaci mahaifiyar tata,tana ganin tasaketa kuwa ta tashi tayi ɗaki da gudu tana dariyah. "Ohhh allah Anty juwairiyah kin haifi ƴar da take shiga hancina da ƙudundune,allah ya shiryeta ke kuma allah ta jiƙanki" Suma sauran mutanen wajen ɗan murmushi sukayi,dan yarinyar bataji kam sam,inka gansu kaman ba cikinsu ɗaya da fadeel ɗin ba,ya zauna yayi shuru so gentle. Khamriyyah ce ta miƙe bayan ta cika cikinta,ɗakin ta nufah tana tafiyah tana musu magana. "Ƴan uwa ku shiryah mu wuce fah,am bar Safiyyah da nawwarah su kaɗai a can,dan ma Deen yana can,amma duk da haka lokaci yayi. Suma nasu ɗakin suka nufah,dayake gidan yana ɗauke da ɗakuna masu yawa,alama duk matan kowa da nata kenan. Cikin shiri suka fito da kayansu na aiki,kowa kuma riƙe take da babban hijabi wanda zasuyi basaja dashi. Fita sukayi tareda yiwa diddy sallama,akan sai gobe,fatan nasara tayi musu kafin sukayi waje,tafiyah fadeel yayi ya rungume khamriyyah tareda cewa , "Anty saikin dawo,karkiyi fushi da fadeelah ke kadai kawai takeyiwa wasa bayanni,tana sonki itama" Haɗiye kukan daya taho mata tayi tareda cewa "Karku damu yarana nima ina sonku sosai kunji,kaje ka kulada ita kafin na dawo kaji,ga nan diddy maza zatayi muki addu'a kafin ku kwanta." Saida suka shigo wajen aikinnasu kafin kowa ya cire hijabinsa ya ajiye. Ɗakin da aka kwantar da Dr. Bukar suka nufah,gefe kuma duka daƙuna ne kowanne da ɗan gado a ciki da banɗaki,saidai kofar a rufe take,wani daga cikin wanda suke ɗakunann yafara buga ƙofar yana magana. Kallon zainab khamriyyah tayi tareda tambayar wanene a ciki. "Uhm ɗan gidan minister ne da aka kawoshi jiyah" "Egnr Aisha Eemran?" "Eh itace,tun ranar yake ta......." "Bashshi dama dole yayi saboda bai san wahala ba ko kaɗan,yayi sa'a ma da iyah ajiyeshi akayi kawai a ɗakin,hmmm naji labarin itama yanda hankalinta ya tashi ai,ƴan rainin hankali,saina kai mata kansa naga tsiyah" Wucewa tayi ɗakin da suke aikin Dr bukar ɗin,yana kwance a jojjona masa wayoyi a jikinsa yana fitar da numfashi da kyar da kyar. Wani file dr nawwarah ta miƙawa khamriyyan tareda cewa, "Duk wani abu daya kamata ayi an zartar shugaba,buƙata shine a bashi ruwan zuwa anjima idan ya farka,daga nan kuma aiki ya kammala" "Sai ki dunga ƙirana da shugabarki duk kuwa da yanda kika girmeni a matsayi da kuma shekaru" "Hmmm dan bakisan yanda kike a zuciyarmu bane shiyasa kika faɗi haka,ke tamkar zinariyah ce da muka tsinceta a lokacin da muke tsaka da neman ko kwandala ce wacce zamuci abinci. Kin bamu ƙwarin gwiwa da kuma muradin yin abinda ko namiji bai isa bamuba,keɗin tamkar ɗayace da dubu,dan haka bake kika samemu ba mune muka sameki" Ɗan murmushin gefen baki tayi tareda cewa "Ki daina irin wanann zancen nawwarah,kin fikowa sanin na tsani abinda za'ayi ko a fadamin dazai jawo min karayar zuciya,yanzu dai aiki yayi kyau ina miki jinjina,barina je na ɗan ji da wancan ɗan gidan minister,dan in ba rufe masa baki akayi ba bazayyi mana shuru ba sam," Fita tayi daga dakin tareda saka wata fuska ta nufi ɗakin dayake. Can kaman wajen karfe shabiyu saƙo ya shiga mata kan cewar dr. Bukar ya tashi daga aikin da'akayi masa na cire ƙoda. Ɗakin ta nufah inda ta ganshi a zaune,kwana ɗaya har ya rame yayi baki,daga ɗan kansa akayi da pillow sai nishi yake bakinsa ta bushe. A gabansa ta tsayah tareda kama kunkumi tana dariyah,shima kuma sarai daga gani ya ganeta,buɗe baki yayi a hankali da kyar tareda cewa "Mmmmai ya ......fffaru dani a a anan wajen?" "Aiki mukayi maka yallabai,gani mukayi baka dace ace kamar ka kana amfani da ƙoda ba,ta roba zata fi maka kyau shiyasa muka ciresu muka saka maka na roba,to yanzu sai kayi mana godiya" "Ammmm..." Shuru yayi yama kasa cewa komai,babu abinda yake sai zubar da hawaye,dan a yanda yake bashida karfin halin aikata komai,hannun ya kai dayake rawa ya ɗora akan babban bandejin dayake kan ruwan cikinsa,tabbas ba mafarki yake ba hakane,sun cire masa ƙoda,dan ga alama nan ta nuna har a bakinsa najin kishirwa dayakeyi. "Oh sorry ba manta bari a kawomaka ruwa kasha,karka margaya tun yanzu" Ruwa ta tsiyanyo a kofi daga cikin butar faro,da kaman baxai karba ba,amma ganin ruwan mai kyaune kuma yana buƙata yasa ya buɗe bakinsa ta zuba masa. Kwat kwat yafara shan ruwan da kansa ya kawar da kai. Dr nawwarah ce tashigo ɗakin tareda cewa "Shugaba yasha ruwan ?" "Ehhh yasha fiyeda yanda nake tsammani ma kuwa,aiki yayi yanda muke so,yanzu kafin ya fara birkicewa ya kamata mu jefarshi su tsinceshi" Zaro ido yayi jin abinda suke faɗa,musamman da idonsa ya sauƙa kan fuskar dr nawwarah,wacce take masa kallom tsana. "Dr. To yanzu ya gaka yanda abun ya juyah,kasan ruwan da muka baka kuwa,ruwane mai dauke da sinadari mai karfi wanda temporary kidney baxata iyah excretion ɗin sa ba,mai kake tunani zai faru to a matsayinka na likitan ƙodar,nasan basai na fadamaka ba kasan result ɗin dazai haifar? Kafin nan ka more guntun lokacinka wajen tunanin,takaici,razana ,zullumi dadai sauran abubuwan dazasu kara worse ɗin ciwon,kan ka farga babu damar komawa da baya,saidai ka tunkari mutuwarka" Tunkafin ta gama maganar ma jikinsa yafara tsanani,kana ganinsa kasan ba karamin mawuyacin hali ya shiga ba sosai. Khamriyyah ce ta kalli su maryam wanda har sun shirya dama fita dashi. "Vl3(maryam) deen ya ɗaukeku a motah,ku kaishi gefen gidan Dec. Sadeeq ku ajiyeshi" "Shikenan V- lady,amma kince zaki tafi gidan,mai zai hana mu fita tare?" "Mashin ɗina aikin mai yake,beside ma banda ra'ayin zuwa,kudai kuyi yanda nace" Fita sukayi tareda nufar gidan dec. Sadeeq ɗin bayan sun saka shi a cikin boot,zuwa sannan har ya suma bai san inda kansa yakeba. A gefen wata katanga da take nesa kaɗan da gidannsa suka ajiye gawar. Har sun taka motar sun fara tafiyah,saikuma suka ga wata mata tazo kan gawar,da kaya a jikinta jajaye,babu abinda suke ganin a jikinta idonta kawai,ganin sun haskata yasa ta fasa yin komai a wajen ta zura da gudu bayan wasu gidaje wanda aka farasu ba'a gamaba. Maryam ce ta fita da gudu tabi bayan ta yayinda shima deen yabi bayan ta da sauri. Sun zuwa bayan wajen babu ita babu alamarta gashi kuma ba wani wajen da mutum zai buya a gurin. "Deen inaga fah aljana ce,dan baka ga kayan jikinta bama,ni wani iri nakeji ma" "Kefah kin faye tsoro,babu abinda xai faru,mutum ce daga gani kaman kowa,ina ruwan aljani da wani dr. Bukar toh,kawai dai inaga bacewa tayi" Saurin komawa mota sukai tareda barin wajen,gudun karsu dade a kamasu a wajen. Akwance yake Amrah tayi pillow da kirjinsa sai bacci sukeyi,dan jiya da daddare ma amai ta dungayi dakyar suka samu ya tsayah,shiyasa sunayin sallah suka koma bacci. Ƙarar wayarsa ce ta tasheshi daga baccin dayakeyi,itama kuma amrah ta motsa daga kwancen datake. Dayake tafi kusa da wayar ita tamiƙo masa wayar cikin magagin bacci,sunan data ganine yasa ta jan tsukah mai karfi. "Kekuma keda wa haka kike jan tsaki?" Ƙarbar wayar yayi,ganin sunan khamriyyah yasashi yin ƴar ƙaramar dariyah,yana shafah kanta wanda ta mayar ta sake kwanciyah tana tura baki. "Hell............what?,a gefen gidana kuma meyasa? Ganinna fitowa yanzu nan,ku tabbatar kun kula sosai" Saurin zame jikinsa yayi tareda jura rigarsa yafita da sauri. A bakin ƙofar gidannasa yasamu dandanzon ƴan sanda,sai ƙokarin ture mutane suke. Khamriyyah ce ta nufoshi da wata takarda a hannunta. "Barka da safiya ogah,ga can gawar yanzu muka samu bayani daga wani ɗan anguwar daya ganta,babu wanda yaje wajen isowarmu kennan" Ta gefenta ya wuce ba tareda yabawa abinda take faɗa muhimmanci sosai ba,burinsa ya isa ga gawar kawai. Tsugunnawa yayi a gaban wajen yana kare mata kallo,wata ƴar takarda ya ciro a gefen gawar fara,daukowa yayi tareda buɗewa. Rubitune irin na almajirai na warash,saidai kuma bana larabci bane,in ba wanda yayi zurfi a karstun nasu ba ba zai iyah karantawa ba bare rubutawa,dan dasu ake amfani ake ƙiran aljanu da kuma siddabaru. Duddubawa yake saidai ya gagara karantawa sam. Khamriyyah ce ta iso wajen tana kallon takardar a hannunsa,mikamata yayi tareda cewa "Duba ko zaki iya ganewa?" "Ahah yallabai,(ɗaga muryah tayi tareda nunawa mutanen wajen),akwai wanda zai iyah karanta mana wannan yaren kuwa" Shuru akayi sai daga baya wani almajiri ƙolo ya fito tareda ƙarbar takarda,a dole an ƙirashi wajen bincike. Duddu bawa yake alamar mai son gano wani abun,koda ba duka bane daga tasa fahimtar. Ɗagowa yayi tareda nunawa dec. Sadeeq wani waje a jikin takardar ta ƙasa. "Eh to nima ban iyah rubutawa ba amma kuma nakan gane harafi kaɗan kaɗan ba masu wuyah ba...........nan dai ta wajen ƙarshen MABARACIYAH aka rubuta dan na san na kalmar mabarata,nan mabaraciyane a rubuce. Amma nasan malamina zai iyah karanta muku wasiƙar. "Mabaraciyah kuma?" _sadi-sakhna_ *(¯`*•.¸,¤°´✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿`°¤,¸.•*´¯)* *MABARACIYAH* (mai harshen damo) тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιε. _haƙƙin mallaka_ _*sadi-sakhna*_ (Yar mutan Jama'are) Paid book #400 3131951977 Auwal sadiya First bank Mai turo kati kuma ta wanann number MTN 09035784150 Mutanen niger su tuntubi wanann number +227 97 21 16 15 Naƙara shafin free har zuwa page 20,zuwa lokacin inka shiryah kazo a fara dakai ranar juma'a. _____________________ Assalamualaikum barkan mu da wannan lokaci *ABMAR COLLECTION* ina nan na kawo muku kayana masu kyau da sauki👌🏻 KAMAR SU:- Atamfa, Atamfa Mai golden,💁‍♀️ Lace ,Shadda lace Yadi, Shadda Abayas💥 Kids wear Takalmi, jaka, mayafai💥 Sleeping dress, kananan kaya na gayu🔥kayan kitchen, DA DAI SAURANSU ina Sokoto ina tura kaya ko ina da izinin ubangiji mai son kayana pc ina maraba daku siyan daya ko sari👏🏻domin neman karin bayani sai ku neme ni ta wannan number waya👉08101521252 nagode kwarai da gaske💃💃 Free page 7••8 "Okay mun gode bawan allah,inshaallah zamu tuntubi inda malaminnaka yake domin sanin abinda yake jiki yanada matukar muhimmanci" "Bakomai ofisa ba nisa layin bayannan ne,kana zuwa kace Shazali mai almajirai,kowa ya sanshi sosai" Motar ambulance ceta iso wajen sai kara take na nuna bayyanarta,wasu mutanene suka fito daga cikin motar sanye da kayan aikinsu. Wajen inda gawar dr. Bukar take suka kariso domin tafiyah dashi checking,sanadiyyar alamomi daya nuna kala kala. Ɗagashin dasukayi ne yayi sanadiyyar bayyanar babban bandage din dayake cikinsa,da alama an kasheshine da hanyar yimasa wani abu a cikin. Saurin ƙarisawa wajen dec. Sadeeq yayi tareda cewa, "Kudan dagata pleace kaɗan" Buɗe cikin yayi tareda ɗora hannunsa akai, "Me'akayi masa a ciki to,lallai wannan lamari yafara bani mamaki yanzu. Maza a tabbatar an ɗauki hoton cikin" Ahmad ne yazo da sauri ya ɗauka da camera kafin aka sakashi a motar zuwa asibitin. "Kai Ahmad kabi bayansu asibitin muna zuwa yanzunnan,akwai wani waje dazamuje,ka tabbatar anyiwa gawar bincike yanda ya dace" "Yess sir" "Ke kuma dec. Khamriyyah zoki rakani,yakamata mu samu masaniya gameda wannan takardar,dan abin akwai ɗaure kai ciki" Binsa tayi a baya suka shiga motarsa tareda nufar gidan da ɗan saurayin yayi musu kwantancensa. Basu wani ɗade ba suka isa,kasamcewar a anguwar ne gidan. Maƙil suka samu gidan cikeda almajirai sai karatun maraice suke a jikin allansu,iyah muryarsu kakeji baka isa ka banbamce muryah wani ba da abinda yake faɗa. Wani yaro suka ƙirah daga cikin masu karatun,da kaman bazai zo ba saikuma yadai taso da allonsa a hannu. "Kai yaron malam ya karatu?" "Lafiyah kalau" "Yawwa idan malaminku yana nan kace muna sallama dashi kaji?" "Toh" Yana faɗa ya ruga cikin gidan da gudunsa. Suna nan tsaye sai kashi ya dawo tareda cemusu su shiga yana cikin zaurensa. A wani ɗan ɗaki yake zaune kafin a shiga cikin gidan,wanda muke kirada zaure a yaren hausa. "Salamu alaikum" "Wa'alaikumus salam" "Malam barka da safiyah,sunana Decetive Abubakar sadeeq,wananm kuma abokiyar aikina ce Khamriyyah. Wani abune na bincike ya taso wanda ya shafi sani da kuma ilimi irin naku a ciki,wanann ne yasa muka nufo nan tareda baran roƙon malam ko zaka iyah fayyacemana mai takardar nan ta ƙunsa?" Ya ƙarisa magana yana miƙawa malam shazali takardar. Ƙarba yayi yana ɗan duddubawa kafin ya ɗago ya kalli su khamriyyah. "Toh malam mai bincike nima lamarin yaɗan shamin kai,dan alƙalamin macece tabbas ya rubuta wannan kalmomi,abin mamaki anan shine ya akayi mace ta ƙware a rubutunnan,ko ɗaliban mu na nan,yanzu suka fara koyah basukai matakin wannan ƙwarewar ba" "Hmm ba kai kaɗai wanann abin ya ɗaurewa kai ba gafarta malam,kai yanzuma kasan da abin,mudai yanzu buƙata ka faɗa mana mai wannan takardar ta ƙunsa in akwai dama" "Bi'zinillah bazai gagaraba barina sake dubawa" Wani ɗan madubi ya ɗauko ya saka a kan takardar tareda nuna musu su matso su gani. Kaman dama jira suke,da sauri suka matso,matsowa yayi da sauri tareda saka idonsa akan takardar. Kallon malamin yayi da alamar tambaya akan fuskarsa. "Kagani rubutune na ajami da rubutun warash,amma kuma a juye yake,baya karantuwa sai tacikin madubi ga wanda bai iyah karantashiba da rubutashi,abinda kaga nasaka masa madubi saboda abune na bincike wanda kuna buƙatar ku sani dakanku" Miƙawa dec. Sadeeq madubin yayi da kuma taakardar,ga mamakinsa kuwa saiyaga tacikin madubin yana gane abinda aka rubuta akan takardar. Tashi yayi malamin tareda cewa "Barina baku waje ku karanta,zan zagaya almajiran can dama" Kallon khamriyyah yayi sanann ya ƙara kallon takardar. "Akwai biro da takarda a wajenki kuwa?" "Eh akwai ogah,bana tafiya babu jotter saboda rubuta bayanai" "Okay yayi kyau,idan na karantomiki ki rubutamin" _Mai kake tunani malam sadeeq mai bincike,a zatonka wanann harbin da abokiyar aikinka tayimin zayyi ajalina ? Lah lah,tabbas salo irinna aikina sukayi amfani dashi,amma bani bace nake aikatawa,kai kanka nasan kana tunanin nice,saboda nasan duk abinda suke shiryawa dama abinda kaima kake saƙawa,ni tamkar inuwa nake,ina a ko ina in ka wulga mai bincike. Sannan wanann kisan da akayi karma ka ambaci sunana,dan wanann ƙodarsa aka cire tareda maye gurbinta da ta roba. Dan haka inkana da hankali zaka san cewa wanann ba aikin mabaraciyah bane,aikinta da hanyoyin gargajiyah take amfani,sanann kuma ta wargaza wanda ba'a tsammanin wargajewarsa. Kasan ance *idan mikiyah tayi kuka kaza gudu take ta buyah*,to kaman hakane wacce take kisansu yanzu zasu gudu su buyah,kayimusu gargaɗi su tsimayi fasowata,dan akwai gagarumin aiki dazan gabatar a garinnan,in ka isa ka iyah bincike ka dakatar dani malam sadeeq. Abar nemanka MABARACIYAH._ Kallon rubutun khamriyyah takeyi bayan dec. Sadeeq yagama karantowa abinda yake cikin takardar,daga yanda take nazartar talardar kasan ta afka kogin tunani,sanann kuma daga gani mai saƙon ba iyah dec. Sadeeq aka turawa saƙon ba harda ita kanta. Sunyi kusan minti biyar babu wanda yayi magana a cikinsu,da alama suna ƙara tariyo abinne a cikim kansu,dan kowa danasa damuwar gameda saƙon dayake cikin takardar. "Sir mun riga mun samo abinda yake cikin takardar,yakamata mu koma asibitin nan,zaman haka babu abinda zai haifar" "Eh zamu koma,amma daga iyah takardar nan mun gano wasu satar amsa guda biyu a ciki" "Ogah satar amsa kuma?" "Eh,abun na farko mungano ba iyah ita kaɗaice take aikata mugun aikin da ake nemanta dashi ba,sannan abu na biyu mungano ita ɗin dole tayi makaranta ne a wata tsangaya ta almajirai,inba batayi makarantarba to lallai tanada alaƙa da wata makaranta irin tasu. Yanzu binciken mu dole zai haɗa da wurare na tsangayar almajirai,sannan dole kuma muƙara bincike wajen gano sauran masu aikatawar ma" "Amma.... Ogah ka yarda da abinda ta faɗa,anyah ba wasa takeson tayi da hankalinmu ba kaman yanda ta saba?" "Nima nayi tunanin hakan,ta farko ban yarda ba,amma kuma idan abinda tafaɗa gaskiyane ba fah,ya kikega zamuyi kenan,inaga idan har wanann ma na gagara gano wani abu akai to dole zan miƙa case ɗin nan zuwa gaba" "Baza'ayi har haka ba ogah zamuyi iyah matuƙar ƙoƙarinmu inshaallah" "Nan da wani satin inaga zan shigar da takardar tafiyah ƙarin karatu,danni ma na fara tantamar aikinnawa tundaga yanzu" Shuru khamriyyah tayi tana jinsa,dan tarasa abin cewa ma itah,duk abubuwa sun juyah lokaci ɗayah. Tashi sukayi suka tafi bayan sun yiwa malamin godiya. Asibitin suka nufah,dan tun a hanya ahmad yake ƙiransu wai result ɗin binciƙen ya fito. A bakin wajen yasamu iyalan dr. Bukar ɗin suna zaune sunyi jugum. Kallon su yayi a ransa yana cewa Yanzu su basuda aiki sai dauko gawar mutane sukai wa masoyanta,abin takaicinma sun gagara gano waye yake kisan, Wucewa sukayi ciki inda office ɗin likitan yake,a bakin wajen ya samu ahmad a tsaye da file ɗin a hannunsa,yana ganinsa ya miƙo masa. Karba yayi jikinsa har rawa yake wajen ganin menene a ciki. Idonsa ya zaro lokacin dayaga an rubuta yayi loosing kidney,kallon likitan yayi tareda neman ƙarin bayani. "Eh kaman yanda ka gani Detective sadeeq hakane ya faru,munyi bincike a gameda a cikinsa,inda muka gano bashida ƙoda ko guda ɗaya duk an ciresu,sannan kuma an maye gurbinsu da temporary,bayan hakan kuma an bashi ruwa mai ɗauke da sinadarin acid a ciki,wanda kuma ƙodar roba bazata iya taceshi ba,ko ƙoda normal ma mutum bazai iyah tsallakewa ba batareda yasha magani ba,sanadiyyar hakanne ta tsayah da aiki,shikuma ruwan ya shiga cikin jikinsa,wanann ne yajawo kalar duhu da jikinsa yayi. Kisa akayi masa na rashin galihu,sanann duk wanda yayi kisan nan ƙwararrene wajen bangaren ƙoda,sannan kuma masani a wajen tiyata,wanann case ɗin ba ƙarami bane detective sadeeq,wannan shine iya abinda muka gani a binciken da mukayi dai" "Nagode dr. Da ƙoƙari,in ba damuwa za'a iyah bawa iyalinsa gawarsa,mukuma muna buƙatar tafiyah" "Ba matsala hakan,zaku iyah tafiyah,Allah ya kiyaye gaba " Musabaha sukayi da dr kafin ya juya ya fito daga wajen likitan. Da hajiya salah yaci karo a bakin ƙofar idonta yayi jawur da hawaye,gefe kuma ƴaƴantane guda shida,maza biyu mata huɗu,kowanne kagani a cikinsu kasan yana cikin halin jimami,mai dauriyar cikinsu ma iyah dr. Muhseen ne wanda yanzu yake matakin shakarar farko na aiki a asibitin ubannasa. "Ya ake ciki,menene yace yayi sanadiyyar mutuwarsa?" Shuru dec. Sadeeq yayi ya gagara yi mata bayani sannan yarasa ƙwarij gwiwar miƙa mata file ɗin tagani da kanta. Ganin hakanne yasa khamriyyah karbar takardar t miƙa mata ,saboda taga ogananta yarasa ƙarfin gwiwarsa a lokacin. Dubawa takeyi amma takasa gani ko manene,ganin an saka case ɗin ƙodane yasa ta mikawa babban ɗan nata,saboda shima fannin wajen ya karanta irinna ogansa. Ƙarba yayi tun kafin ya gama karantawa hannunsa yafara karkarwa,idanuwansa suka firfito,kana ganin tashin hankali da razana a cikin idanuwansa cike fall,zafar da takardar yayi batareda yaƙarisa karantawa ba,domin hannunwasa ma bazasu iyah cigaba da riƙe takardar ba. "Menene muhsin mai ka gani a cikin takardar?" Shuru yayi shima ya runtse ido,ko buɗe ido ya kalleta ya gagara ballantana ya faɗa mata mai yayi arba dashi a cikin file ɗin. Kama rigarsa tayi tana jijjigawa,zuwa sannan tafara kasa riƙe kukan dayake cinta tun farkon faruwan ɗauke mijinnata, "Kayimin magana muhseen,idan shi yakasa yimin bayani kai bai kamata ka boyemin mai ka gani ba,kasan nafi kowa hakkin nasan mai yafaru da mijina!" "Ummah da kin....." "Karka fara wannan wasan dani,ka faɗamin mai ya faru yanzunnan,basai anjima ba" "Abbah ba haka kawai ya mutuba,sannan ba duka bane ko harsashi ya kasheshi ba ummah,ya mutune a sanadiyyar ɗauke dukkan ƙododinsa da akayi,sanann kuma aka maye gurbinsu da dana roba,ba'a barshi haka ba aka kuma shayar dashi ruwa mai ƙarfin acid da temporary kidney bazata iyah excretion ba,sanadiyyar hakan yakwana cikin azaba kafin safiyah ya mutu batareda wani ya kawomasa ɗauki ba......!" Sakin rigar muhseen ɗin tayi tareda zubewa akan tiles ɗin wajen,mai kuma zatace da irin wanann mummunan labari dataji,wanda gwanda ace a gabanta ya faɗi ya mutu dataji labarin abinda yafaru dashi,kuma batasan yafaruba bare tana wajen tayi wani abu. "Tabbas wannan zaluncine ummah,mai abbah yayimusu suka yimasa wannan ɗanyen aiki,a iyah sanina dashi bashida abokin gaba ko guda ɗaya,to menene dalilinsu na aikata hakan,wacece wanann mabaraciyar,sanann mai yasa take aikatawa manyan mutane wanann ɗanyen hukuncin?" "Uhm haƙiƙanin gaskiya muhseen ba mabaraciya bace ta aikata wanann kisan ba,saboda tabar mana takarda akan gawar kan cewa ba aikinta bane,amma tana dabb da aikata nata,mukanmu mun kasa samun ko alama ɗayah dazamubi wanda yake aikata kisan" "Tayaya Sadeeq zakace ba ita bace ta aikata kisan,dan kawai ta ajiye takarda tace ba ita bace sai a yarda da itah,to taya tasan an ajiye gawa a wajen dakuma mai ya faru inba itace ta aikata ba?,mai gadi da bakinsa yace muku tace mabaraciyah sunanta,kuma yanzu tace ba ita bace ta aikata,wannan zancen banzane zancen wofi,kawai kace ka gagara kamata kawai,kuna gani kun zuba ido tana kashe iyaye mutane kun kasa komai akai,to idan baxaku iya ba muzamu fara ɗaukanataki mu wanda abin yashafah,ya za'ayi ace ƙaramar yarinya mace ta dunga kashe manyan mutane amma ankasa yin komai akai,wannan ai zancen son kaine,kawai saboda kuna ƴaƴan manyan security an ɗaukoku an sakaku akan tsaron mutane,kuna yanda kuka ga dama,sukuma ƴan ƙasa ana ta kashesu......" "Kai muhseen ya isah haka,dec. Sadeeq yayi iyah ƙoƙarinsa akai,amma abin kam babu adalci a ciki,ya za'ayi mutumin da yake taimako yakeyiwa mutane magani,wasu kyauta yake basu ƙodar yau shine kuma za'a cirewa tasa dan mugunta?" Har dr. Muhseen ya buɗe baki zayyi magana khamriyyah tasha gabansa,dan takai maƙura wajen ɗaukar rainin hankalinsa, "Dakata malam,ya muna iya ƙokarinmu wajen bincikar wanda yake aikatawa kai kuma kana cimana mutunci,an faɗa maka nan asibitine inda mahaifinnaka yake isada iko a wajen,zakace dan yana dan mai bincike,kaima duk wanda yaganka ai yasan baka kai matsayinka baka akayi dan ubanka yana da faɗa a ji,da kaje kayi wani aikin mana ba irinna ubanka ba,kowa yasan kana cikin zafin mutuwa,amma bai kamata ka huce akanmuba,muda muke bada rayuwarmu dan taku. Da kake cewa wani zakaje ka ɗau mataki,to inka fasa,mu ai taimaka mana kayi idan ka kamota,kaga muma munhuta da tashin hankalin ace mana an ɗauke wani mutumin san........" Saurin janyeta dec. Sadeeq yayi suka bar wajen,gashi asibitine har dun fara tara ƴan kallo a wajen. Saida sukaje har bakin motarsu kafin ya sake hannunta yana kallon ta da mamaki,dama haka take da masifah da iyah ɗaukar bacin rai,abinda bai taba ganin tayiba tsawon kusan shekara ɗaya dasuke tareda ita. "Menene haka khamriyyah,muda muke kwantar da tarzoma kekuma kina ƙoƙarin kunnota,bakisan a cikin aikinmu akwai haƙuri ba" "Haba ogah baka ganin ɗan rainin hankaline ba" "To ke bakya ganin rashin mahaifinsa yayi" "To dan yayi rashin mahaifinsa sai....." "Ya isa haka,ga nan ahmad zai kaiki gida yanzu,kije ki huta kafin gobe na nemeki,dole zamu fara bincike akan wanann takardar,inaga dole zan barmuku aiki ma na tafi ƙarin sabon salo kona wata shidane" Yana gama faɗa mata haka ya koma cikin asivitin,bata tsayah jiran ahmad ba takama hanyar gabanta,dan har cikin ranta taji haushin abinda muhseen ɗin yayi,haka kawai baka san abinda ubanka yayi ba,kadai tunda yana ciyar dakai da tufatar dakai babu ruwanka,sai wani abu ya sameshi bazasuyi bincikeba sai zakin mutane,ba gudu baza da baya,babu wanda ya isa yahana ta cikar burinta kaf cikin duniya kuwa saidai mutuwa tayi. A bakin wani layi ta bayan wajen babu kowa wata mota ta tsayah ta ɗauketa. Shiga tayi tareda miƙewa a gidam bayah,deen ne yakalleta ta cikin madubi tareda cewa "Ran V-lady ya daɗe mai ya farune haka na kinyi jagwab dake,ko mutuminnamune ya birkita miki tunani" "Kai deen i am not in joke mood,ka kaini wajen khairiyyah ina buƙatar ganinta,tunda naga ta ɗauke ƙafah dazuwa gida" "Okay shikenan,hmmm mai kuma ya faru" Bata kulashi ba saima rufe ido da tayi tana jin sanyin motar dayake ratsata a jikin jikinta,kafin su karisa wajen har bacci ya ɗauketa,sai jin deen tayi yana tashinta ashe har ya iso wajen khairiyyan. Fitowa tayi tareda yimasa magana cikin ƙaramar muryah tashiga cikin cafe ɗin. Zama tayi a kan wata kujerah batayi mata maganaba ganin tana yiwa wasu aiki,saida ta gama kafin ta tashi tashiga wani ɗan ɗaki a cikin wajen. Tashi khamriyyah tayi ta bitah,wajen ɗan ƙaramin ɗakine mai ɗauke da computah guda uku,saikuma wasu abubuwan da wasu wayoyin. "Anty khmariyyah ykk ya aiki" "Cune baki khmariyyah tayi da alama sunan bayyi mata ba sam "Ji wani sabon salo kuma wai anty,lafiya ƙalau ykk ya aiki,jiya baki dawo gida ba lafiya dai koh" "Eh lafiyah kalau,wlh wani virus ne ya shigo mana,to kinga bazam tafi nabar su da aikiba,kwana mukayi muna aiki a wajennan,ya ayyuka suke tafiyah dai" "Lafiyah ƙalau,amma daya kamata ki ƙira wayah,banason naga kina kwana a wajennan keba namiji,duk da muna aikin kasada hakan bai bamu damar yin yanda muka ga dama ba" "Inshaallah mommy khamriyyah zam kiyaye" "Kaimata duka khamriyyah tayi,da alama tafara ƙosawa da zolayar khairiyyan,wanda kaman halintane hakan,eh naji dai kunsan alhakin kuladaku dukka yana kaina ko kuso ko kuma ku ƙi,dan haka daga yau idan wani abu ya faru ki tabbatar kin faɗamin" "Inshaallah kiyi haƙuri anty khamriyyah bazan sakeba nace ai,ina su maryam da su fareeda,ita batanan koh?" "Eh tana wajen aikinta,amma wanann satin zata dawo daga service ɗinta itama ta fara aiki,wato kinfi missing ɗinta akan balki koh?,nasan sabriyyah kam kuna wayah ai" "Uhm itama ba sosai ba,kinsan itah rashin ganinta yafi na kowa,baka isa ka ganta sanda kakeso ba,badan munsaka rai a wannan aikin ba dasai nace ni wlh na gaji,dandai zuciyata bazata samu nutsuwa ba idan banga mun cimma burinmu bane. Yawwa naji labari a wajen deen wai mabaraciyah bata mutu ba,dagaskene kuwa?" "Kai deen akwai gulma shiba mace ba,yaushe ya faɗamiki,keda baki fiyeson shiga sha'anin hakan ba" "Hhhhh jiya yake faɗamin wai dasuka je ajiye gawar dr. Bukar sunga wata mata ta ajiye wani abu akan gawar,dasuka bita kuma basu sameta ba duk neman da sukayi" "Kutt to amma nibasu faɗamin wanann zancenba,yaushe suka fara rufemin abu toh,mun samu takardar kuwa,kuma daga mabaraciyar tafito kuwa" "Tabbb to yanxu ya za'ayi,anya kuwa bazata kai farmaki kankiba,karki manta fah kece kika harbeta lokacin da ta yi ƙoƙarin kashe brr. Shehu,to amma meyema ya haɗata dashi,mungama target ɗin kamashi fah,kawai sai mukaga takamashi dakanta,nayi mamaki meyasa take bayyana idan zamuyi aiki?" "Karki damu khairiyyah zanji da wanann,yanzudai abinda yafi shine inaso kimin wani aikine shiyasa ma nazo da kaina banmiki aika bah" "Wane irin aiki kenan" "Ke bakya tsayawa kici ribar zance,kibari mana na gama yimiki bayani. So nake kiyimin hacking ɗin computar headquarter kisaka sunana a masu tafiyah ƙarin karatu a cikin wanann satin,zanje nacire paper zuwa gobe" Kallonta khairiyyah take da mamaki,dan ba karamin kaɗata zancen yayi ba,ƙarin karatu kuma a cikin satinnna ma" "Amma fah kinsan a ƙa'ida mutum sai ya tura takarda dakusan wata guda kafin a karbi takardar" "Shiyasa nace kiyi hacking ɗin wajen kaman yanda kika saba ki sakani cikin wanda zasu tafi a satinnan,kinda nimber ID na kiyi amfani dashi" "Okay angama anty khamriyyah,yanzu ina wani aikin,amma zuwa yamma zan miki,kafin na dawo gida" "Ki tabbatar fah kin dawo gida da wuri idan ba haka ba zaki ganni nazo ɗaukarki,kuma saikinyi sati ban barki kin fita a gidaba,wannan shine punishment ɗinki" "Baza'ayi haka ba ma,zan dawo inagama wannan aikin da'aka bani na wata masana'anta" Daga nan ƴar hirarsu suka fara ta ƴan uwa yaushe gamo,kafin khamriyyah tafito ta nufi makarantar su fadeelah domin ɗaukosu a makaranta. Tarar mai napep tayi tai masa kwatancen makarantar,har sannan kayanaikintane a jikinta,sai hijabai kawai data saka akai. Kasancewar shabiyi ake tashinsu kuma a nursery 3 suke,har sun fito suna zaune a bakin wata bishiya suna jiran mai ɗaukan nasu har sannan bai zoba,fadeelah sai kuka take wai ita yunwa takeji lokacin data ga khamriyyah tazo ɗaukansu. "Antyyyyyy....." "Menene fadeelah,har yanxu wai bazaki daina kuka a makaranta ba,kina ganin fadeel bayayi saike koh" "Ba shuraim ne ya kwacemin biscuit ɗina ba,babu abinda naci sai bredin da diddy tabamu da safe" Ƴar dariyah tayi ganin yanda ta dage sai kuka take,wanda da batayiba saida ta ganta tukunna. "To naji kiyi haƙuri tunda abokinku ne ina,kuma kema kirage tsokana da kuka,fadeel yana faɗamin irin tsokanarki ai a makarantar" Harara ta zanbgawa fadeel ɗin wanda yake zaune a bakin bishiyar yana ganin tijarar datakeyi. "Shima ai yana tsokanar zaice nikadai nakeyi,yau ma ai uncle saida yayi masa duka a aji" "Ƙaryah takeyi ita aka duka suna faɗa da wata ƙawarta" Kara kufulewa tayi musamman dataga khamriyyah ta yarda da zancensa,dan dama duk wata rigima ita takeyi "Kai ni ya isheni haka,kutashi mutafi gida,dama ba yunwar kikejiba ai tunda kika tsaya tsare tsaren mai yake faruwa" Wani mai adedetan taƙara tara suka tafi gida" A gajiye dec. Sadeeq yashiga gida yana sauƙe ajiyar zuciyah,kana ganinsa kasan ba ƙaramin abu bane yasashi haka. Akan kujera ya jube yana kallon P.O.P ɗin dayake saman falon,motsin zaman amrah dayaji a kusada shine yasashi ɗagowa ya kalleta, "Jarumina ya akayine naga ganka a gajiye,har yanxu akan case ɗin dr. Bukar ɗinne?" "Hmmm wanann case ɗin ai an rufeshi amrah,shima an kasheshi kuma har yanxu babu wani abu dayake nuna alamar zamu samu mai kisan,shikam ma dan rashin imani ƙodarsa aka cire fah duka biyun,nikaina dana dade ina bincike idan naga kisan da ake saina razana,kuma abin mamakin ma wai macece takeyinsa,yaya take oho,menene dalilinta har yanxu bamu saniba,kuma kinsam menene,da alama tanada alaƙa da makarantar almajirai,koma ba itaba to da akwai wani acikin irin makarantun dayake taimaka mata. Toh yanxu kuma mun sake binciko wai ba itah kaɗaice take kisan ba akwai wasu ma dasukeyi. Ni narasa ma yazanyi da wanann abun kwata kwata,a da na raina case ɗin danaji ance macece, amma yanzu kuma abin yafara gagarata amrah,inaga nafara kasawa da wannan case ɗin" "Karkace haka honey,inshaallah zaka iyah ka kwantar da hankalinka komai zai zo da sauƙi,kacigaba da jurewa jarumina" Rungumeta yayi a kirjinsa,da alama daman neman wanda zaiji ƙorafinsa yakeyi. "Nagode matata,yah babyn mu yake,naga yau jikinki da sauƙi sosai,ina fatan babu matsala ko" "Babu komai muna nan kalau,barina ɗebo maka ruwa tukunna,kafin na haɗo abincin" "Aha sannunki da aiki,nibanyi tunanin zakiyi bama yanda na fita na barki" "Ahah nasamu sauƙi miye zanyi ta kwanciyah,bayan nasan zaka dawo,ko a gidan su mamah baka son cin abinci yanzu bare a waje. "Maman ce ai yanxu ta daina girki sai masu aikine yanzu sukeyi,shiyasa na ajiye shafinsa a gefe guda" Bayan ta kawo abincin ma zancensu suka cigaba dayi irinna mata da miji,bai san lokacin da nutsuwarsa ta dawo masa ya manta da duk wata damuwa daya kwaso. A zaune suke yau ma da daddare suna cin abinci,saidai yau a hankali kwamce suke ci babu zancen wani da zasuje da daddaren. Khairiyyah ce ta fito da wata takarda ta miƙawa khamriyyan. Ƙarba tayi tareda buɗewa takallah. "Eh yayi kyau,amma nayi mamaki dasuka yi approve a yau ɗin,banyi zaton abin zai faru nan da nan ba" "Karki damu,kinsan niɗin bata wasa bance,sunan ki nasaka a jerij na huɗu,suna karbar biyar suka haɗa da sunanki,kinsan kaman banɗakina haka nake shiga wannan website ɗinnaku,babu abinda nake jin sauƙinsa kaman yimusu kutse a lamarinsu,na ɗauko bayanai. Wai tsayah kin karbi takardar ƙarin karatu,shin tafiyah ƙarin karatun zakije ko wani abune daban kika saƙawa wanda dole saikin bar wajen?" "Kai khairiyyah kin faye tambaya,ƙarin karatu zanje amma bata bangaren abinda ya shafi aikina bane,zanje sanin wani abune gameda wani lamari daya nake tunanin zai faru a gaba" Dukkan shuru sukayi musamman su fadeel daina cin abincin sukayi. "Anty tafiya zakiyi ki barmu?" "Ahah fadeel ba tafiya zanyi na barku wani waje zanje zan dawo kaji" Kallon dukkan matan wajen sukayi,khairyyah ce ta kasa hakuri saida tasake tambayarta. "Anty khamriyyah zancen serious dama dagaske kikeyi,amma wata nawa zakiyi toh" "Wata inaga zaikai shida zanyi,ya danganta da yanayin gama karatun,kafin na dawo kowa yayi normal rayuwarsa,nasan tunda ƙarin karatu zan tafi albashina zai dunga shiga,maryam ki dunga cirowa kuyi abinda yadace dashi,ku kula da kanku sosai" Dukkansu jugum sukayi,musamman su fadeelah da khairyya,dan kaman sun fi shaƙuwa da itah,dr nawwarah ce ta kalli khamriyyan wanda itama ta gama cin abincin. "Duk da bansan mai zakiyi ba amma nasan abune mai muhimmanci,karki damu inshaallah komai zai tafi normal,sannan zancen albashinki kuma kema ai zaki buƙata,menene amfanin kuɗin danake dashi wanda a yanzu bana ganinsa a wani abu fashe ruɗi na duniyah,zan cigaba da kuladasu dukka,za'a ɗauko mai gadi ma saboda tsaro,kafin allah yayi mana ikonsa" "Nagode sosai dr. Nawwarah da taimakonki,haƙiƙa bazanji dumuwar barmiki ahalina a hannunki ba" "Nima yanzu sun zama nawa ahalin,yaushe ne zaki tafi" "Jibi zan tafi ranar alhamis,idan gobe dec. Sadeeq yayimin sign,inkuma bai min ba dole saina jira ya amince" Dukkansu dariya sukayi a hankali,suna kallonta taƙasa "Da alama fah bawan allah nema yake ya fola fah,inkuwa hakane yana ruwa inya gano gaskiyah" "Ke maryam,wato tunda bakiyi magana ba saida kikaji zamcen tsokana koh,da har zance ina fareedah ashe fah mijinta ya dawo ɗazu,sun tafi gida." Ƴar dariyah khairiyyah tayi kafin tace, "Bawan allah kenan,duk da yasan gaskiyah amma bai hanashi sonta ba,Gaskiya samun miji kaman Badulmajeed sai antona" Kallonta balki tayi kafin tace, "Jimin khairiyyah mai saurin afkawa abu kaɗan,gaskiyar mai yasani,bai san harda itah a kisan da'ake ba,baisan tsakanin ta da khamriyyah,kawai fah yasan marainiyace kuma a nan gidan aka riƙeta,ki gayamin mai yasani toh" "Hakane kam,shiyasa daga yanzu nacireta koda wani abu zai taso,saboda kar a je ya shafi aurenta,zaman ta gidanta yafi wannan abin" Fareeda ce ta mike tareda cewa "Toh nikam saida safenku akwai abinda zanyi saina kwanta,fadeel maza tashi mutafi kwanciyah kaji mutumina" Tashi yayi yabita da gudu yanayiwa su khamriyyah bye bye,itakam fadeelah ana hirah harta kwantar da kanta akan diddy tana shirin bacci. Ƙwankwasa ƙofar office ɗin khamriyyah tayi dan tasan dole yana ciki,tunda lokaci yazo bata shigo da wuri Izini taji ya bata daga ciki hakan ta murɗa ta shiga da takarda a hannunta. "Ina kwana ogah" "Lafiyah khamriyyah ya hidimar aiki,naga yau kin makara koh duk gajiyar aikinne" "Eh to dama......wani abu na tsayah yi saboda akwai abinda nake shirin yi" "Mene....." Tun kafin ya gama tambayarta ta ajiye masa takarda a kan table,tareda kallon idonsa tana jira taji mai zaice. Ɗaukar takardar yayi yana karantawa,tun daga farko yasan takardar menene amma saboda tabbatarwa yasashi karantawa. "Me hakan yake nufi khamriyyah naga ya nuna cewar ƙarin ƙaratu,yaushe kika yanke wannan hukuncin haka" "Dama yallabai so nake kasaka min hannu,buƙatar hakanne yataso,naji kana cewa zaka tafi ƙarin karatu,to inaga gwanda naje akan kai ka tafi,beside ma ga matarka tana ɗauke da ciki,nasan bazakaso kayi nesa da itah. Kuma dama nayi shekara guda akan aiki,lokacin tafiyata ƙarin karatu yayi,musamman yanda muke ƙarbar case a watannin nan masu yawa" Shuru yayi yana nazarin bayanan nata,tabbas abinda ta faɗa gaskiyane,amma a wannan lokacin tace zata tafi gaskiya.... "Toh naji ƙorafinki,khamriyyah kije zanyi nazari kafinnan saina ƙiraki " "Amma yallabai wajen dazasu ƙarbeni yau suke buƙata na turamusu takardar tareda da takarduna,shiyasa na kawomaka,kayi hakuri ogah" "Naji amma duk da haka zan ƙiraki dai" Cikin sanyin jiki da alamar rashin samun nasara khamriyyah takama hanyar fita daga office ɗin,har taje bakin ƙofah taji yayi mata magana,wani murmushi tayi na sun nasara kafin ta juyo da sauri. Miƙamata takardar yayi tareda yimata fatan alkhairi. "Nagode nagode yallabai,allah yabaka abinda kake so" "To saiki dage,bakije kiyi ta shirmeba,fatan alkhairi" Da sauri ta fita daga office ɗin tana ƙafafa tareda farin cikin cikar burinta. Washagari dasafe ta haɗa kayanta ta tafi,bayan tasaka khairiyyah ta tura information ɗinta makarantar data keso su ƙarbeta. ****** "Fareeda yau fah kwana uku kenan har yanzu banga khairiyyah ba,ko gida bata dawoba ,naje wajen aikinta ma bata nan fah" "Mai kike faɗa maryam kin duba kuwa,mai yake faruwa" _sadi-sakhna_ *(¯`*•.¸,¤°´✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿`°¤,¸.•*´¯)* *MABARACIYAH* (mai harshen damo) тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιε. _haƙƙin mallaka_ _*sadi-sakhna*_ (Yar mutan Jama'are) Paid book #400 3131951977 Auwal sadiya First bank Mai turo kati kuma ta wanann number MTN 09035784150 Mutanen niger su tuntubi wanann number +227 97 21 16 15 Naƙara shafin free har zuwa page 20,zuwa lokacin inka shiryah kazo a fara dakai ranar juma'a. _____________________ Assalamualaikum barkan mu da wannan lokaci *ABMAR COLLECTION* ina nan na kawo muku kayana masu kyau da sauki👌🏻 KAMAR SU:- Atamfa, Atamfa Mai golden,💁‍♀️ Lace ,Shadda lace Yadi, Shadda Abayas💥 Kids wear Takalmi, jaka, mayafai💥 Sleeping dress, kananan kaya na gayu🔥kayan kitchen, DA DAI SAURANSU ina Sokoto ina tura kaya ko ina da izinin ubangiji mai son kayana pc ina maraba daku siyan daya ko sari👏🏻domin neman karin bayani sai ku neme ni ta wannan number waya👉08101521252 nagode kwarai da gaske💃💃 Free page 9••10 Daurah_____5:00pm Mutanene guda biyu mace dana miji zaune a bakin rafi suna hira,gefen ƙafarsu kuma ruwa yana wucewa,daga kallon yanda suke kasan suna jin dadin yanayin sosai. Kallon mutumin dayake zaune a gefenta tayi,kafin ta sau ɗan sansanyan murmushi. Doguwar rigace a jikinta baƙa,sai kanta ma ta nannaɗeshi da baƙin mayafi. Wanda hakan yafito da jar fatarta sosai irinta fulani. "Yah muzzanbil nayi mamaki danaga yanda kamaida wajenann,gaskiya wajen yanada tarina ni'ima,amma hakan fah rani yana zuwa zaku bar garin fah ku koma gun daban koh. Yaushe za'a daina wannan tashi tashin na almajiraine?inaga kuma lokaci yayi dazaku zamanta tsarin karatunku nan" "Lallai ma deejah har yanxu kina nan da ƙorafinki,yanzu idan muntashin menene zai shafeki a ciki" "Babu komai,kawai dai kasan bazan biku bane,kodah yake ni wani satin ma fah nake son shiga cikin garin katsina,wannan hutun jakin da kaya akai ya isheni haka" "Hmmm wai ke ba namijiba amma kina birkita hankalin manyan gari,nayimiki magana kibar wanann aika aikar amma sam kin ƙiji sam" "Bazan iyah dakatawa ba saina gama tukunna,a lokacin dana gama zan fito kowa yasan nice,kafin zuwan lokacin nashiryah kallon tsagwaron tsana a idanuwan wanda nayi sanadiyyar mutuwar masoyansu,nikaina nasan abin akwai babbar wuyah idan lokacin yazo" "Kwanaki kincemin na faɗamiki idan yadiko lami tazo ganin gida,to tazo jiyah a satinnan zata koma,maiyasa kike buƙatar zuwanta,wani abin kike ƙoƙarin shiryawa ko" "Hhhhh kai ya munzanbill mai ka maidani ne,kafin nan inaso ka ƙarisamin bayanin yanda ake laƙanin karshennan,saboda inada buƙatar sa a cikin shirina" "Deejah ina jiyemiki kiyi abinda zai jawo hatsari ga rayuwarki fah,wanann abin yakamta ki tsayah iyah haka" "Kayi haƙuri yah muzanbilu,nayi maka alkwari daga wannan nadaina bazan sakeba,amma matar sarkin katsina babu mai hanani illatata koda ban kasheta ba saita ƙwammaci a kashetan" Saurin zaburah muzanbilu yayi ya tashi tsaye tareda sunkuyowa yana kallon deejan,wacce ko a jikinta kaman ba ita tafaɗa ba. "Deejah!mai kika ce,naji kunnena yajiyo min wani gagarren aiki,mai kike nufi da hakan" "Basai ka tambayeni ba,lokacin da aikin ya kammala zakaji a kafafen yaɗa labarai cewar mabaraciyah ta kashe sarki Alhaji Bilyaminu muhammadu,mijin Hajiyah Fulani Ateekah." Wannan shine aikina na karshe akan manyan gari,daga nan kuma sai kaɗa hantar masu bincike kawai" Tunda tafara maganar munzanbilu yasaki baki yana kallonta haƙiƙa yanzu tafara bashi tsoro,anyah kuwa itah ce wacce yasani tana yarinyah. "Wayyyo jina nake kaman tsuntsuwa wacce ta fito a cikin keji,bayan shekara guda zanje aiki,hmmmm masu bincike da V-ladies ya zakuji inkuka yi arba da aikin MABARACIYAH wanann karon,yah muzanbilu kaidai kafaɗawa yadiko lami zam bita masarautar katsina inda take aiki idan ta tashi tafiyah. Daga nan sai aiki yasoma" Shigewa cikin gidan tayi tana tafe tana rera waƙa hankalinta kwance. *______*________*_______* Zabga mata mari yayi har saida jini yafita a cikin bakinta, "Ogah yace muyi ta dunkanki harsai kin faɗin gaskiyah,har yanxu bazaki faɗi abinda kuke aikatawa ba koh,yau kwana uku amma kinƙi cewa komai kega mai taurin kai koh." Duk dukanta dayakeyi babu abinda tace,saima ƙara tamke bakinta datayi,alamar b'ata lokacinsa kawai yake. Yana cikin dukanta ne dec. Sadeeq yashigo wajen,cell ne na ƙarfe,a wani waje killacecce da alama sai ana son tambayan wani mai babban laifi kafin akawoshi wajen. "Har yanxu bazakiyi bayani ba baiwar allah,dan kinga muna miki sako sako,to ki sani akan wannan case ɗin zamu iyah kasheki,kinsam tsawon lokacin damuka ɗauka muna neman koda karamar sheda akan wannan case,ɗin sai gashi tashi ɗayah mun samemi,ina so ki faɗamin mainene haɗinki da wannan logon na hoton macijiyah da muka gani a cikin laptop ɗinki,shine desame logo da aka samu a jikin gawar dr. Bukar. Sannan tsawon shekara guda ana mana hacking,bamu taba ankara ba sai wancan watan,wanann dalilinne yasa muka saka virus a website ɗin,abin mamaki kuwa saigashi mun sameki da neman mai gyaran irin wannan virus ɗin,hakanne yasa muka tura wani ma'aikacinmu yaje ya gyarah,yasaka alama a web ɗinki,wanda kina sake ƙoƙarin shiga web ɗinmu sunanki da inda kike zai nuna,abin mamaki kuma da ID ɗin ɗayah daga cikin ma'aikatanmu ake shiga tsawon shekara gudan,wanda kin boye information ɗin ID ɗin,duk yanda akayi muna da spy a cikin headquater ɗinnan bamu saniba. Inaso ki faɗamin wacece ke,sannan meyasa kike aiki damasu kashe kashen nan,nasan dole ke ɗaya daga cikinsu ce" Ɗago fuskarta khairiyyah tayi waccd ta sanja kamanni ta kalli dec. Sadeeq,ɗan ƙaramin murmushi tayi na ƙarfin hali kafin tace, "Babu amfanin faɗamaka tunda iyah bayanin daka samo kenan,dan koda na faɗamaka ba lallai ka ganeba,dan haka zai fi kyau kayi haƙuri da iyah saninka" Wani babban mutum a gefe bai bari ta gama magana ba ya gwabza mata duka,faɗuwa tayi akan gwiwoyinta saboda tsabar jifata datayi daga azabar dasuka gana mata a tsawon sati gudan. Buɗe ido tayi tana kallon cikin idon dec. Sadeeq ɗin bayan tasake tsayawa akan gwiwoyinta,da alama har sannan zuciyarta bata karaya ba. "Shin ke yarinyar mabaraciyah ce?" "Ya danganta daga yanda ka ɗauka,kawai amsa ce bazaka samu a wajena ba,kaman yanda ka taba kama ɗayah daga cikin yaran mabaraciyah ka kasa samun amsa" Zaro ido dec. Saddeq yayi,da alama bayyi tunanin tasan binciken dasukayi akan wata yarinya shekara ɗaya data wuceba. Bindiga ya fitar daga cikin aljihunsa ya nuna akan khairiyyan. "Har yanzu bakaji abinda waccer yarinyar ta faɗamaka ba,bazaka samu amsa daga irin muba da barazanar bindiga,saboda mu bada kuɗi aka sayemu ba,ka gane hakan mana" Zefar da bindigar yayi tareda cewa "Kinsan bazan kasheki ba saboda ina buƙatar bayanai,amma hakan bazai hana na hukuntaki ta mummunar hanya ba domin samun amsar danake nema ,ki jira dawowa ta,kafin sannan ki tabbatar kim tanadi amsoshin dazaki bani kafin ki rasa yatsunki na hannu dana ƙafa" Ƙarar wayarsa ne yasa shi fita waje domin amsawa. "Hello khaleel ya aiki da kuma kasar china?" "Lafiya ƙalau,amma babu daɗi ko kaɗan,na gama karatuna Allah Allah nake nadawo gida nima,saidai naga kaman da alama so suke suce nayi aiki anan kasar,nikuma hankalina gaba ɗaya yana kanku. Kayi kewata ma kuwa?" "Hmmm kajika da wani zance,kasan a duk ranar duniya sainayi kewarka ai" "Nasan da haka shugaban masu bincike,ya wannan aikin dakukeyi ne,har yanxu baku samu nasarar kamata ba?" "Har yanzu dai da saurah,saidai yanzu munkama ɗayah daga cikin yaranta" "To karfa kuyi wasa ta gudu irinna wancan lokacin,ni nayi zargin ma ina ga fah akwai wanda yake musu aiki a cikinku,shiyasa suke samun labaranku da shirin ku cikin sauƙi" "Eh nima nayi zargin hakan,yanzu inshaallah zamuyi yanda ya dace,yaushe zaka dawo kenan" "Hhhh inga nan da wani satinma idan nayi nasarar ƙar'bar takardata to zaka ganni a gida nigeria,barina kashe karna dameka da surutu kana kan bincike,sai anjima ko mai bincike,a gaishemin gimbiyah,kace mata tashirya ganin ƙaninta lokacin farko" "Hmmm ƙaninta kuma,yau kuma abinda ka ɗauko kenan,kowa ya ganka ai yasan ka girmeni" "Hakadai kace,sai anjima" Ƙitt yakashe wayar yabar dec. Sadeeq da kallon screen yana murmushi. Shukarah ce tazo da file a hannunta da sauri tareda miƙawa masa, "Ogah intargilent section sun bada shawarar ayi mata scaning ko akwai na'urah a jikinta,saboda duk wani abu da muke yanuna suna saneda hakan,wannan binciken ID ne da'akayi yafito,ansamo komai datayi yunƙurin 'boyewa" Da farinciki Dec. Sadeeq ya ƙarbi file ɗin tareda buɗewa bayan yagama jin bayaninta. Sunan dayayi arba dashi a jikin ID ɗin da'akayi amfani dashine yayi matuƙar girgizashi. KHAMRIYYAH,mai kuma ya hada khamriyyah da wanda ake zargi toh. Tsawon kusan shekara biyu duk da ID ɗinta ake amfani ana yi musu kutse,sun bi diddigi amma sun gagara gano waye yakeyi,saidai suga blank,wancan satin suka sanja computocinsu na tsaro babu wanda ya sani,gashi. Sun gano mai yake faruwa,hatta takardar da khmariyyah tatafi ƙarin karatu da ita wancan satij aka turata,gashi har ta shiga sahun masu tafiya a satin,kuma duk da tambarin viper akayi amfani wanda sune suke kasha kashen da'akeyi. Cire glass ɗin fuskarsa yayi bayan yagama tattara bayanan waje ɗaya,kenan duk tsawon lokacin daya yarda da khamriyyah zagon ƙasa takeyimasa,kai hakan yake nufi,bata tunanin yarda zai ɗauki abin. Baiyi wata wata na ya nufi sashen binciken nasu na na'urah dan har yanzu yagagara tantance bayanin. Har yazo dab dazai shiga wajen saikuma ya fasa ya nufi inda khairiyya take a ɗaure. To idan yaje wajenta ma mai zai cemata,faɗa mata zayyi yakasa gano wacce take yimasa zagon ƙasa na tsawon shekara biyu sai yanzu yagano ko me? Hannuwansa yasaka tareda murza cikin kansa,dan ji yake kaman ƙafafuwansa ma sunyi masa nauyi,share tantama dai yayi tareda nufar wajen horon. A ɗaure yasameta kaman ko yaushe kanta yana kallon ƙasa,motsinsa ne yasa ta ɗago ta kalleshi,ita kanta mamaki abin yabata ganin yanda kamanninsa suka sanja lokaci ɗaya,kaman wanda aka cemasa an yashe masa asusun banki. "Kee inaso ki faɗamin bayan khamriyyah wacece kuma wacce take yimana bin diddigi,inaso ki faɗamin tsawon wane lokaci kuka ɗauka kuna wannan shirin,dame dame kuka kitsawa " Cikin tsawa da tashin hankali yake maganar da alama hankalinsa baya wajensa. Ƴar dariya khairiyyah tayi kafin ta ɗora da cewa. "To danƙari,daga gano gaskiya ɗaya harka birkice haka,inaga inkagano wani daban,ina faɗa maka tun wuri zaifi kyau ka bar wanann binciken,dan ba'a kan kowa zai ƙare ba sai kanka,bazaka'iya jurar gane gaskiyaba idan ka cigaba da tonota nan gaba. Hmmm dan kagano khamriyyah ba ma'aikaciya ce ta gaske ba babu abinda zaka iya da hakan,kawai dazai fimaka kyau kasan akalar bincikenka kan wani waje daban ba nan ba ,wannan shawara nake baka mai kyau" Mari ya sheƙamata a fuska iya ƙarfinsa,dan daga gani yafara fita hayyacinsa,ga kuma ransa daya 'baci sosai. Wata macece daga cikin ma'aikatannsa tayi saurin dakatar dashi ta hanyar bashi wayarsa da take ringing. "Yalla'bai ga wayarka madam tana tana ƙirah" Tun kafin ya ƙar'bi wayar har ta katse,bai bi ƙirannata ba sai ya shiga wayar ya nemo number khamriyyah,kallon sunan yayi yana tuna masa abubuwa dayawa kafin ya daure ya danna ƙiran. Riniging ɗaya ,biyu tayi ya ɗaga. "Salam ogah barka da rana ya aiki" "Lafiyah ƙalau kin fara karatunne?" "Eh na fara ogah yauma nashiga aji fitowa ta kenan" "Okay toh ki dawo gobe inason ganinki" "Ogah lafiyah zan dawo?,ko sati ban cika ba fah da tafiyah" "Eh kidawo umarni nake baki,akwai wani abu mai muhimmancine da baxayyiwu a wayaba" "Ogah zancen kama khairiyyah ne dakayi ko kuma zancen gano cewa nice nake haɗa komai?,wannne daga ciki zamu tattauna oga. Karka damu oga inaga basai nazo bama,indai khairiyyah ce matuƙar zaka cigaba da bincike bazaka tsaya iya haka ba to ina mai tabbatar maka dakanka zaka jawo kanka abinda ƙwaƙwalwarka bazata ɗauka daidai ba,inada abinyi ogah a gaida madam saina dawo" Lokacin data kashe wayar yana jin dariyar ta ƙasa ƙasa,lallai wannan matar ta wuce inda yake tsammani. Wayar ya buga da tiles ɗin wajen,ta bada kara tatssss,duk abinda yake khairiyyah na kallonsa tana ɗaure,itadai ido nata kawai. "Fareedah inaso keda ahmad ku shiryah min body scanning yanxu,ina tunanin akwai na'urah tabbas a jikimta wanda khamriyyah takejin mai ake faɗa,zan je office kafin sannan ku shiryah komai" "Okay sir zamuyi yanda kace" Fita yayi daga ɗakin horon da sauri yabar khairyyah itada fareedah a wajen. Matsawa tayi gaban khairiyyan tareda cewa "Sis sannu ya jikin?" "Babu komai fareedah karki damu komai zai zo da sauƙi,tashin hankalin ɗayah shine ina tsoron su gano gaskiyar abinda muke 'boyewa fareedah,dan dukansu babu komai zan jure" "Ahah bazai yiyu kiyi ta jurewa ba khairyyah,dolene musan abinyi kafin lokacin,da inada damar yi da yanzu zan fiddaki daga nan wajen,saidai hakan bazai yiyu,duk wani matakin tsaro yanxu akanki yake,fitar bazayyi yiyu ba,dole sai anyi scanning ɗin babu yanda zamuyi" "Niba kaina nakeji ba idan anyi fareedah,sabriyyah nakeji bansan yazatayi ba,naga kaman anty khamriyyah tasan komai dayake faruwa,kece kika faɗamata koh?" "Eh nice na faɗamata shikuma yayi zaton wai camera ce a jikinki,sai naji daban faɗamata da wuri ba" "Ahah gwara dakika faɗamata ɗinma,kinga da yanzu tadawo dayace ta dawo ɗazu" "Hmmm tun jiyah taso dawowa ai,wai a dole saita ƙwatoki daga hannunsa,su anty nawwarah ne suka bata baki dakuma shawara,saboda idan ta dawo abin 'baci yayi,inaga yafima da bata garin,da abin sai yafi haka 'baci sosai. Kiyi haƙuri kinji khairiyyah inshaallah gobe muka tsara zaki fita anan wajen,barina je na shiryah scanning ɗin karyah zargi wani abun" Tana gama faɗan hakan ta juyah da sauri tabar wajen,tana tafiyah tana waiwayen ƴar uwartata,da alama bataso barinta a wajen ba,saidan babu yanda zatayi da al'amarin. Shuru dec. Sadeeq yayi a office ɗinsa tareda zuba uban tagumi,yarasa ma mai zayyi akan wanann abun. Tukun takardun dake gabansa ya kallah wanda ya gagara taba su bare yin wani aikin,karar buɗe ƙofar yaji amma bai ɗaga idonsa yaga mai shigowa cikiba,dan ba ta wanann yakeba a yanzu. Muryar ahmad yaji daya yimasa sallama. "Sir an gama shirye shiryen ascanning ɗin kaman yanda ka buƙata kai suke jira su fara" "Okay kace ina zuwa yanzunnan." "Kayi haƙuri da abinda ya faru" "Inbanyi haƙuri ba isaka zan tayar toh,haƙurin ai na dolene" Tashi yayi yabiyo bayan ahmad din suka fito daga office ɗinnasa. Wajenda ake scanning ɗin suka shiga wanda za'a gano wani abu a jikinka daka 'boye, Har lokacin da za'a fara idon khairiyyah yana kan dec. Sadeeq,da alama batason abinda za'ayin,saidai kuma idan tace kar ayi hakan bazai tasiriba saima ƙara musu ƙaimi,dan zasu gano da 'boye wani abin. Zaunar da itah akayi akan wata kujera sanye da wata doguwar riga wacce kalar ta bazai shafi aikinba Na'aurar scaner ce tafara daga ƙasa wajen ƙafartah,a hankali zuwa saman ta. Runtse idonta tayi lokacin dataji hasken na'urar a kan kirjinta,wanda hakan yaƙara sautin bugun ƙirjinta daga yanda ainihi yake. Ƙarar da na'urar tayine yasa ta tabbatar tafaru taƙare kawai,babu kuma sauran wani komawa bayah. Buɗe idonta tayi akan na'urar wacce ta nuna alamar ja akan saitin fuskarta,wanda hakan yake nuna kenan akwai abinda ta 'boye a fuskar. Sauran mutane kowa kallon fuskartata yakeyi,dan da alama babu wani abu ba daidai ba,saidai kuma ruwa bayah tsami banza,dole akwai dalilin hakan. Masu kulada binciken wajenne wata ta matso kusa tareda ƙarewa fuskar khairiyyah kallo,ɗan murmushi tayi da alama ta harbi jirgin abinda yake faruwa. "Ƴar da alama kaman fuska kika sa,kika 'boye ainihin fuskarki ta zahiri,koba haka bane?" Cikin sauri kaman wani zai rigata tabawa matar amsa da "ahah" Faɗaɗa murmushinta tayi jin da alama hasashenta yazama gaskiya. "Dec. Sadeeq mun gama maka binciken dazamuyi,yarinyar tana ɗauke da fuskar roba wanda ta 'boye ainihin tata fuskar,to yanzu aiki yarage naka ka gano shin ya ainihin fuskarta yake" Duk abinda suke dec. Sadeeq kallonsu yake,yama rasa abin cewa akan lamarin,mamakin sa ɗayah shin suwaye su,suna mata amma suka san irin wanann hanyoyin,hadda wani shirin na rufe fuska,da ba'ayi ascanning ba kenan haka zai ɗauka wanann ce fuskarta,tana fita saita wuce ya wuce ta maidashi wawa,allah yasa ma uwar gayyar itama fuskarta kenan. Musamman yanzu data san yaganota zata iyah cire fuskar tasake zuwa a matsayin wata daban. Kai gaskiyar amrah ne daga yanzu bazai ƙara ɗaukar mace aiki ba har ya jawota jikinsa irin yanda yayi wa khamriyyah,anyi na farko baza'a sake kumawa ba k.... Ƙarar yatsun da ahmad ya kyastah a saitin fusarsane ya dawo dashi daga makahon tunanin daya tafi,kallonsa yayi na ɗan sakanni ya tariyo mai yafaru kafin yayi magana. "Ahmad ku kaita izuwa ɗakin sirri,ban yadda wani yashiga ba bayan kai da kuma ma'aikatan wajen" Amsawa yayi tareda fara aikin da'aka umarceshi,a randa yana tausayawa shugabannasu yansa ya rasa nutsuwar sa akan case ɗin gabaɗaya. Ɗakin haske ne dashi sosai saikuma kujeru guda biyu kacal da tebur a tsakiyansu. Na ciki baya ganin na waje,amma kuma wanda yake waje ta gaban glass ɗin yana kallon na cikin. A zaune take ta sunkuyar dakai lokacin daya shiga ya zauna a kan kujerar da take kallonta,har sannan tana sanye da doguwar rigar da'akayi mata scanning da itah. "Har yanxu bazaki faɗamin gaskiya ba duk da nagano kusan rabin gaskiyarki" "Ai ba iyah rabi ka ganoba ma,ka gano babbar gaskiyar wanda nake jiyemaka ganota,yanzu idan nace karka sakani buɗe fusakata kaga wacece ni zaka yarda da zancena?" "Hhh kin fara yanzu tsorone saboda kar aga ke wacece,da hankalinki kwance saboda idan kin fita zaki cire fuskar dakika yaudaremu da itah,yanxu kuma kina jin tsoron mu buɗe asirinki ya tonu koh,to kisani alƙadarinki ke ya karye yau kuma anan wajen zai ƙarisa karyewa,kokina so ko baki so saikin cire abinda yake kan fuskarki kowa yasan ke wacece" Shuru khairiyyah tayi ta rasa abin cewa,saboda duk yanda zatayi masa bazai fahimta,ina amfanin baɗi babu rai dan haka kawai tasaka hannunta ta ɗaye gam ɗin daya haɗa fuskar da ainihin tata fuskar. Idan taƙi cirewa ma zasuyi mata ta ƙarfi. Duk abinda take dec. Sadeeq yana kallon ta har ta cire fuskar ta ajjye akan table ɗin. Ɗago idon da tayine shikuma yayi dadai da zaburarsa ya miƙe a tsaye,dukkan jikinsa rawa yake lokacin dayake nunata da yatsarsa,magana yake son yi amma kuma bakinsa yagagara furtawa. "Meye kake nuna ni toh yanxu,ka razana ne da ganina,saida nace karka tilastani cirewa amma kaƙiji na,toh yanxu ya kace sirikina?........" "Amrah......" "Hmmmm ji wani zance,amma dai kasan ka barta a gida koh,miye kuma kake ƙirana da sabriyyah,ohhh ashe da amrah kasanta kai bada ainihin sunanta ba. To bari nayi maka gwari gwari kafin kaje tayi maka kyakykyawan bayani,wannan ƴan biyun(twin)sabriyyah ce khairiyyah,tun lokacin daka aureta fita da ainihin fuskata ya haramta min saboda kai,duk da wani lokacin nice a gidanka ba ita ba idan zan saka camerah ko kuma nemo bayanai,sannan kusan duk taron da kake zuwa da itah nice nake binka ba itaba,shiyasa kayi ta mamakin ya akayi bana magana idan munje wani waje,saidai nayi ta komawa gefe,kokuma na nemi uzurin zuwa wani waje. Wanann shine dalili toh,yanzu kaji daɗi ka gano gaskiyah? Ko kuma har yanxu kawai gaskiyar da baka ganoba kake son sani. Gaskiyar ɗayace khamriyyah ce take shiryah komai wato babbar ma'aikaciyar ka,yayinda matarka daka fi so kuma itace ta biyu,nida ka kama kuma nice ta uku,sai wasu kuma da dama. Nasan yanxu ba tani zakayi ba ta matarka zakayi,kafin ka gama da itah nasamu na huta" Tana gama faɗan hakan ta murza ƙofar ta fita ta barshi a inda yake a tsaye kaman robot. *______*_______*______* Deejan ce sanye da kayan na saƙi kaman ko yaushe baƙaƙe,tafiya take kanta a sunkuye a wani titi dake cikin garin dauran. A bakin ƙofar wani gida ra tsayah,madaidaicine amma na masu ƙaramin ƙarfi. Ƙyauren gidan ta tura ta shiga a hankali bakinta ɗauke da sallama. Wata ƴar budurwace ta amsa wacce bazata wuce sa'arta ba shekara ashirin da biyu. Watace gada cikin ɗaki ta yi magana da ƙarfi ga wacce take tsakar gidan tana wanki" "Buntu wacece take sallama,in mai siyan barkonoce kice mata babu sai gobe za'a kawo" "Ahah inna deejah ce fah ƙanwar malam muzanbilu,wai yadiko lami take nema" "Au hoo tafita zuwa maƙwanta amma ta jirata yanzu zata dawo" Kallon deejah wacce aka ƙira da bintu tayi tareda sake fadamata,duk da taji abinda matar tace. "Waiki jirata yanzu zata shigo ta ɗan fitane" Ɗan murmushi deejah tayi wanda yake fito da ainihin kyanta da kamalarata. Dan shine babban abinda yasa mutane suke ganin mutuncinta,sannan kuma suke burin shigowa da ita cikin zuri'arsu. 'Lah bakomai barina zauna toh idan bazaki damu ba" "Ah ki zauna mana barina ɗauki miki kujerah" Zama tayi zefi zefi sun magana da bintu har yadiko lami ta shigo gidan da tsintsiyah a hannunta da kuma lade. Da alama sallama ta shigawa mutane ƴan uwa da abokan arziƙi. "Deejah kece a gidan ya muzanbilun yake,hala nasan aikoki akayi,dan rabona dake tun kina ƙarama" Ƴar dariyah deejah tayi dan ita idan ba muzanbilu ba bata saba da magana dasu ba,tsakaninta dasu sai murmushi kawai kokuma in an tambayeta ta bada amsa. "Uhm yadiko lami dama..........inason bikine garin katsina idan zakije,zaman haka ya isheni,shine nakeson ko tayaki aiki na dungayi a can" "To ba damuwa,dama shi muzanbilun yayi min magana akan hakan,yafi zaman banza kam,ina ga wannan nayi nayi tazo mu tafi taƙi bina" Tafaɗa tana nuna bintu da yatsa,wacce ta cune baki kaman ya faɗo ƙasa. "Kai yadiko lami,amma dai kinsan inason zuwa,kawai babane bazai barni na bikiba,kema yanda kina yayarsa da magana kikayi masa" "Wannan ubannaki ko ubana ne ai iyakaci,shiyasa fah zaman gidanku yake gagarata,gawara naje can ina aikina ina san'ata yafiyemin,nida dawowa ma inaga sai aurenki tukunna" "To yadiko lami yaushe zaki tafine?" "Wanann zuwan zamu tafine?,gobegobe nan nake son tafiyah,kije ki shiryha to mutafi,in munje bakya rasa wani aikin ba" "To nagode sai goben" "Ki gaida malam muzanbilun,kice zanzo ƙarbar maganin da daddare kan sanann yagama " Bawani shiri na azo a ganiba deejah tayi,ƴan kayantane sai shirginta wanda zata buƙata. Ɗakin muzanbilu taje,shikaɗaine yana zaune yan jan carbi da alama zikirin safiyah yakeyi,dan dama inyayi asuba baya komawa bacci. A gabansa ta tsugunna tareda sunkuyar dakanta. "Yah muzanbilu zan tafi yin aikina na ƙarshe,mai yiyuwa na dawo mai yiyuwa wanann karon ba lallai nadawo ba,saboda wanann ya sa'ba dukkan aikin danayi a bayah,saboda zan daɗe tareda wanann mutanen har sai nasamu cikar burina,ina matuƙar godiyah da kulawarka da kuma kyautatawarka a gareni,ina roƙon ka yafemin laifin danayi maka a zamana da kai" Saboda maganganun ta sun kashe masa jiki kasa magana yayi,sai ɗaga kai kawai dayayi mata,alamar yaji abinda tace. Sassafe taje gidan su yadiko lami ɗin,saboda karta tafi ta barta. Tasha suka nufah tana tafe tana binta a baya har suka shiga motar katsinan aka hau hanya,Allah ya tsare hanya. *_____*____*______* Yanda khairyyah ta bar dec. Sadeeq a zaune a wajen ya ɗade bai motsaba,sai can wajen awa ɗayah yaka ƙafafunsa ya fito a wajen,ba ta zancen khairiyyah yake ba wacce ta gudu,inma yakamata yanzu toh mai zaice?...yakam ƴan biyun matarsa wacce take aikata laifi?...bai kama kuma matar tasa ba tana gida?...bayan itace ta biyu ma a shigabancin yin hakan?. Wannan lamarin kwata kwata bai yi ma'ana ba. Bai kula kowa ba sanda yafito a wajen,suma kansu masu tayashi aikin sun rasa ƙwarin gwiwar dakatar da khariyyah daga fita a wajen,matar ogah ce shugaba kuma wayake ta ƙarama kuma. Hanyar wajen motarsa ya nufah ya buɗe ya shiga. Ikon Allah ne kaɗai da karewarsa ya kaishi gidannasa lafiyah. Tun daga bakin ƙofar babu kowa shuru. Taka carfet ɗin bakin falon yayi,mai makon hakan yasaka shi nishaɗi kaman kullum idan ya dawo ya tunada wacce zayyi arba,sai ya zamo kuma yau hakan ya juye zuwa fargaba da zullumi da abinda zai tarar. Bayyi magana ba duk da ƙwaƙwalwarsa tana matuƙar bukatar hakan,amma yazayyi da bakin wanda yagagara buɗewa bare ya furta komai. Kitchen yafata leƙawa babu kowa sannan ya ƙarisa ɗakin kwanansu,nan ma babu kowa,bai gazaba ya leƙa banɗaki nan ma babu kowa,fitowa yayi yana ƙarewa ɗakin kallo. Nan idonsa ya sauƙa kan wata takarda da wani littafi a kan table ɗin gefen gado.. Ƙarisawa wajen yayi ya ɗauki paper. ......Assalamu alaikum aminci ya tabbata a gareka mijina,nasan zakayi mamakin rashin ganina bayan ka dawo gida. Bazan iyah jurar jin kalmar saki daga gareka ba idan kazo ka taddani,tabbas da farko na aurekane don samun bayanai da kuma wani abu,amma kuma daga baya na faɗa kogin sonka a zahiri,wanda hakan yasa bazan fuskanceka ba har sai a karanta wanann littafin,anan zaka san tarihinmu da kuma dalilinmu na yin wanann aikin. Karka tambayeni labarin mabaraciyah wanann bansan nufinta ba sannan ba tare muke aiki ba. Daga matarka Sabriyyah(Amrah) Ajiye takardar yayi hannunsa yana rawa kafin ya buɗe littafin,da alama kundin tarihine na rayurwata ta ajiye masa ya karanta,duk da bashida ƙarfin yin wani karatu sannan amma kuma yana buƙatar hujjah. Da hotonsu yaci karo a farkon shafi su huɗu,khamriyyah,khairiyyah, sabriyyah,sai kuma wata buduwa a tsakiyarsu,bazasu wuce shekaru goma ba a lokacin,kawacce fuskarta ɗauke da murmushi,sannan basu san mai duniyar take cikiba. Shafin gaba ya buɗe kafin yafara karantawa.................. KASH.......anan fah na batinku ya ƙare my loves. Nasan kuna ɗauke da sinƙi sinƙin tambayoyi? #Mai dec. Sadeeq zai karanta a littafin sabriyyah,anyah kuwa abinda zai gani zai isah ya gamsar dashi yafasa kamata,uwa uba kuma ga ƙaramin cikinsa a jikinta,wamda yake nema ruwa a jallo ya haɗa jini dasu? #shin anyah kuwa khamriyyah ƙarin karatun ta tafi? # ya aikin da deejah(mabaraciyah )zata gudanar a cikin gidan sarautar katsina,zatayi nasara kuwa kokuma rishene zai juye da mujiyah? #Mabaraciyah da V-lady mutanene mabanbanta masu aƙida guda ɗayah,kowacce burin shine ɗaukar fansa,tukunna ma fansar menene da dole sai an kashe kaso mai tsoka na manyan gari? # a yayinda suka gama ɗaukar fansar shari'ah kuma da take jiransu a madakata zata ƙyalesu kuwa?. #Menene dalilin dayasa ta kirayi kanta mabaraciyah??????........ Dukkan wanann amsoshi suna nan a ɗaure tamau a cikin manhajar AREWABOOKS,naira 10 goma zaka dunga sakawa kana suncesu da kaɗan kaɗan . Kar a manta da follow da bada haɗin kai please. Taku _sadi-sakhan_ Ƴar mutan jama'are. *(¯`*•.¸,¤°´✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿`°¤,¸.•*´¯)* *MABARACIYAH* (mai harshen damo) тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιε. _haƙƙin mallaka_ _*sadi-sakhna*_ (Yar mutan Jama'are) Paid book #400 3131951977 Auwal sadiya First bank Mai turo kati kuma ta wanann number MTN 09035784150 Mutanen niger su tuntubi wanann number +227 97 21 16 15 Naƙara shafin free har zuwa page 20,zuwa lokacin inka shiryah kazo a fara dakai ranar juma'a. _____________________ Assalamualaikum barkan mu da wannan lokaci *ABMAR COLLECTION* ina nan na kawo muku kayana masu kyau da sauki👌🏻 KAMAR SU:- Atamfa, Atamfa Mai golden,💁‍♀️ Lace ,Shadda lace Yadi, Shadda Abayas💥 Kids wear Takalmi, jaka, mayafai💥 Sleeping dress, kananan kaya na gayu🔥kayan kitchen, DA DAI SAURANSU ina Sokoto ina tura kaya ko ina da izinin ubangiji mai son kayana pc ina maraba daku siyan daya ko sari👏🏻domin neman karin bayani sai ku neme ni ta wannan number waya👉08101521252 nagode kwarai da gaske💃💃 11••12 ____Garin daurah a shakerar 2008_____ Garin daurah garine ba wani babba sosai ba,amma kuma kowa dayake anihin cikyakykyen ɗan arewancin nigeriya to kuwa yasan labarin garin daurah da kuma irin tarihin daya ƙunsa a ciki. Kama daga tarihi harda tarihihi yazo mana da yawa wanda garin daurah ya shiga ciki. Duk kasancewarsa ba wani gari ne babba na azo a ganiba,amma garine da'ake cewa,Jinka yafi ganinka. Akwai gidaje dayawa kana da iyalai da yawa a garin,zaka samu wanann ya haɗu da wannan,wanann ma ya haɗu da wannan,saidai mu bama ɗayah daga cikin wanann ahali na garin,duk da muhallin mu yana cikin wannan gari amma kuma babu tabbacin muɗin ɗayah ne daga cikinsu. Dan mu tamkar tsuntsayen dasuka nemi alfarmar zama a shiƙar wasune saboda basuda iko da kuma ƙarfin yin tasu shiƙar,koda sunyi ma su ba ɗayane daga cikin su ba,saidai su rungumi iyah kansu,amma fah su barene a wannan wajen. Mai karatu bazaka fahimta ba koh,saboda nasaka ka a duhu,kayi haƙuri yanayin rubutunne yazo da haka. A taƙaice dai ba tareda zagayen ɗan wake ba danake dakai a cikin kwano,sunana Sabriyyah,na tashi na buɗi ido banida kowa banida wanda zangani a matsayin jinina sai ƴar uwata khairiyyah wacce muka zo duniyah tareda itah,amma inji wanda suka tsince mune suka tabbatar da hakan,dan ba uwace garemu ta bamu labarin yanda muka shigo duniya ba,uwar muce ta biyu data rainemu ta bamu wannan labarin. Dukkan gidan marayun na garin daurah haka yake cikeda tarin yara kala kala,wasu sunsan iyayensu guduwa sukayi suka barsu,wasu kuma 'bata sukayi shikenan aka kawosu nan,wasu kuma iyayensu ne suka haifesu bata hanyar aureba dan tsoron kunyar bazasu iyah fuskantar duniya suna tareda su ba suka kawo sunnan,ko kuma suka ajiye a inda za'a gani a kawosu wajen. Sai kuma rukuni irinna mu,wanda zai iya fin kowanne muni kuma zai iyah fin kowanne kyau,shine an kama wata mata ta ajiye mu a wajen da zamu iyah a hallaka a tsakanin kowacce daƙiƙi kuwa. Masu tsaron dare sun bita lokacin da suka ga ta zefa mu a cikin ruwa amma kuma basuyi nasaraba,nasarar ɗayace da sukayi nasarar fito damu daga cikin kogin,kana ganinmu kasan sabuwar haihuwa dan ko cibiyarmu ba'a rababa muna haɗe da juna nida khairiyyah. Shin itace mahaifiyarmu,in kuwa itace ta kawomu duniyah to tafi kowacce uwa tantiranci,wace uwace zata iyah kashe ƴaƴan ta har guda biyu. In kuwa ba ita ta haifemu ba to aiki aka bata na kashemu,kokuma ita tayi hakan dan wani kuɗirinta. Inkuwa hakane to duk wanda yayi hakan ba son mu a raye,da akwai lauje cikin naɗi gameda wannan abin!!... Babu abinda muke sai kuka,dan shikaɗai ne abinda allah yabami ikon yinsa a lokacin,gidan marayu na garin daurah aka kaimu,dan a lokacin shine waje mafi kusada inda aka tsince mu. Allah sarki uwar kirki jarumar uwa kuma jajirtacciyar uwa,wato uwar marayun gidan INNO,ta raini yara batasan adadinsu ba tsawon rayuwartah,tun tana da shekara talatin da mijinta ya rasu,ta fara aikin rainon yara marayu marasa galihu,duk da cewar bata ta'ba haihuwa ba amma kuma a sanina babu wanda ya kaita yawan yara da kuma wanda take ƙira a matsayin nata. Muma muna daga cikin rukuninta,shiyasa rayuwa tazo mana da sauƙi,ba kaman wanda suke sashen HAJJAH ba,hantara da ƙyara ma ya ishi mutum,kullum cikin masifah take da kuma cewa ita tagaji,musamman idan akace ba'a biyasu albashi ba,sannan zakaji masifarta sosai. Saidai duk da hakan tanada halin kirki,wanda yashiga yafita a lokacin to babh abinda zai faɗa sai rashin kirkinta,amma mu da muka tashi a gabanta munfi kowa sanin halinta,tanada tausayi sanann tana son mu sosai,matsalarta ɗayah bata son wasa irinna su Inno da kuma MAMAN YARA ,yanzu zakasha sanda idan ka kawomata wargi. Mukuma yara gagararru na gidan da muka ga haka sai yawancin wasan mu da tsokanar mu ta koma kanta. Dan dama sune abokan wasan mu ,a takaice dai iyaye kuma kakanni,saboda su debe mana kewa da kuma shaƙuwa ta iyaye da bamu samu ba. Inno itace ta shayar damu da madara,wanda gwamnati take bayarwa,duk da kunsan yanayin tsari na gwamanatinmu,idan ba'a kawo ba da kuɗinta take siya mana. A lokacin ita kuma Hajjah tana rainon Maryam da kuma shukurah. Saikuma Maman yarah tana rainon yara huɗu lokaci ɗaya,ciki harda Zaharaddeen da kuma faridah. Kasancewar kanmu ɗayah sai muka tashi tare kusan mu tarah. Rashin ji da kuma neman magana ba zancensa,dan inkaji gidan yayi shuru to fah bacci mukayi,inkuwa aka ce safiyah tayi toh bazaka sakejin shuru ba,musamamn idan muka saka Hajjah a gaba,tana binmu muna gudu,sauran suyi ta mana dariyah. Anty shamsiyyah ce ma da anty juwairah suke hanamu,ita anty shamsiyyah ƴar ɗakin mu ce wajen inno,anty juwairah kuwa ƴar ɗakin hajjah ce,. Allah baya haɗa biyu,ita anty shamsiyyah faɗane da itah,ita kuma anty juwairah sanyi ne da ita kaman ƙanƙara,idan hajja tana fadanta sai dai tayi shuru,gasu su ƙadaine a lokacin sukayi saura a manya a gidan,dan anyi auren sauran sa'anninsu,mazan kuma sun tafi bayan an basu sana'a,wasu kuma sun gudu neman kuɗi,yayinda wasu kuma aka ɗaukesu, Duk da cewa kowannne yaro burinsa a ɗaukeshi,sanann ana masa murna idan ya samu hakan,nikuma na tsani a ɗaukeni ko kuma wasu daga cikin ƙawayena,ita kanta inno bata son a ɗaukemu nida khairiyyah,dan tafi ji damu akan duk yaran data ta'a riƙewa,saidai babu yanda zamuyi idan aka tafi da sauran,saidai muyi kukan lokacin daga baya mu manta. Duk da mun taso gida ɗayah da yawanmu,kuma ba jini ɗaya ba,saidai kuma akwai tarbiyyar da su inno suke koya mana na haɗin kai da kuma rungumar junanmu. Shekarun anty juwairah a lokacin baifi sha biyar ba amma su suke mana wanki,kitso da kuma sauran kana nan abubuwa,musamman anty juwairah a akwaita da jan yaro a jiki,shiyasa muka saba da itah sosai,muke ganinta tamkar ƴar uwarmu ta jini. Shekarar mu biyar inno tace a kaimu makaranta mufara karatun boko,da kuma na arabi,dan a halin da muke ciki shine gatan mu bayan allah. Makarantar babu nisa sosai dan haka da ƙafa muke zuwa muna dawowa,a hanya kullum sai ansha faɗa hadda fasa baki,wani lokacin a tsakanin mu idan muka nufo hanyar gida,wani lokacin kuma da sauran yara ƴah makarantarmu. Yau ma kamar kullum an tasomu ƙarfe shabiyu,saboda yanzu mun shiga aji ɗaya na primary,su fareedah tun dazu suka tafi gida,su suna nursery three,, Nida deenne muka shawo kwana muna dariyah,yayinda maryam da khairyyah suke binmu a baya suna kuka sai sun rama dukan da mukayi musu. "Karka bari su kamaka su rama irinna jiyah,dan nakula maryam tana gudu sosai,amma waccan kam lusarar baya ce" Nafaɗa ina nuna khairiyyah wacce take can baya. Ita maryam ba sosai take kuka ba,amma khairyyah kam...sakaliyar inno kakeji,komai kuka zatayi wani inya gani sai yace nafita da shekara guda ba mintuna kaɗan ba,saboda yanda take sakaliyah ga son jiki,kuma ma da ƙarin taimakon inno,dan tafiji da ita fiyeda ni,in an jimu da itah toh tsokanar khairyyah nayi kokuma na ƙwace mata abun wasa. Binmu suke a bayah,takalminsu a hannu,khairiyyah kam hijabinta ma a hannu yake da jakarta. "Wlh sabrah idan baki tsaya na rama ba saina faɗawa inno" "Yeeee ki faɗa ɗin,iyakaci tace bazan bita ƙyauye ba,naji ɗin saina zauna a wajen anty juwairah" Na faɗa ina dariyah tareda yimata gwalo,hakanne yasake ƙularta ta fashe da kukan dayafi na da ma yawa. Nikuwa abinka da yaro daɗi naji nasaka ta kuka,a haka muke tafiyah har muka shiga gida. Ban nufi shashenmu ba sai nabi deen shashen maman yara,dannasan bazata bari inno tamin komai ba,ita kuwa da gudu ta shige ɗaki tana bubbuga ƙafa tareda jefar da jakar a ƙasa. "Innnnoooooo" Daga ɗakin madafah take jiyo ƙiran da khairiyyah takeyi mata,wanda hakan yasa ta fito tana cewa "Miyene khairin inno,yau kuma keda suwaye" "Ba....ba sabrah bace tah ta lakata min yawu kuma ta dukani a bayah ba lokacin da muka fito a aji,kuma nace ta tsayah na rama taƙi,danace zan faɗamiki sai tace ki faɗa ɗin wai" Kama baki inno tayi da ludayin miyah a hannunta tana ta'ba girkin da masu yin abincin sukeyi, "Kai kai wannan yarinyah,nasan yanzu haka tayi ɗakin maman yara,ƙyaleta kinji ƴar inno zan kamata,ina nan zatazo neman kunu ai bazan bataba ke zaki shanye dukka" Wata dariyah khairiyyah tayi jin za'a bata tashanye itah kaɗai babu ni,nikuwa ina jinsu a bayan labulen maman yara ina leƙowa" Ganin inno ta koma ɗakin abincinne yasa na lalla'ba na shiga ɗakin domin cire kayana,deen sai dariyah yakemin wai za'a dukani. Abinka da yaro ashe tana kallona na shige ɗakin,musamman da taji muna faɗan kayan da muka cire,khairiyyah tana cewa nata ne,nima ina cewa shina cire. Jijjiga kai tayi tasaka dariyah,hakan shikaɗaine farincikinta daya zaunar da itah a gidan,bata samu na jinin ta ba amma kuma tasamu na sauran mutane dasuka kasa riƙewa,itakuma ta zauna ta riƙe da zuciya ɗayah. Muna cikin faɗan kayanne inno ta shigo ɗakin,ina kallon ta na zaburah zan gudu ta riƙeni tareda cewa "Ina zakije kuma,wato zakiyi wanann ficewar taki sai la'asar ki dawo ko,inna ƙara gani kinyi wani abu kin bar gida zaki ƙwala,mai rashin ji kawai,bakida aiki zai zaluntar ƴar uwarki,maza ku wuce ku tafi wajen cin abinci an fara ci,idan kuma kuka tsayah faɗa aka cinye yau bazan baku nawa ba,kunun ma sai naƙi damawa" Da sakina tayi data gama faɗan ta shige ɗakinta,dan dama kowacce akwai ɗakuna a shashenta wanda yaran wajenta zasu na kwana,kumbura baki nayi tareda zangawa khairiyyah harara,saidai kuma bazan sake nayi gangancin dazata fada yin kunun ba,dan daga abincin rana banacin tuwon dare,shi nake yini ina sha,gwara ma khairiyyah tafini cin abinci,duk da wani lokacin ɗayane. Dan idan nayi wa inno tsiyah dayawa bata dama kunun sai dare,duk da ita nake sakawa a gaba nayi ta kuka,amma kuma nima yunwa tana isa ta. Fita mukayi daga ɗakin zuwa wajen da muke cin abincin. Wasu irin manyan faranti ne ,maza a nasu daban mata ma a nasu daban,a cewar dokar gidan ta hakane zamuyi zimunci idan kowa yana cin yawun kowa. Shiga wajen mukayi a kallah su kusa goma shabiyar,kowa ya kama cin abincin,layin kawanann mu mukaje inda su maryam da farida suke zaune,dariya ta na matse lokacin dana kula da kallon da maryam takemin,ita kuma fareedah ko a jikinta sai loma take,dama duk da fimu cin abinci,duk da ita a haife dama mun fita da kusan shekara biyu. Kallon fareedan nayi wanda ni lomata ɗaya ma a cikin abincin. "Fareeda ki daina cika bakinnan naki kaman bazaki ƙoshiba,rumbu kawai" Murguɗamin baki tayi ta muntsuna shi,dan dama duk gidan ta rufe ƙofah a rashin kunya da tsokana. "Naci ɗin waya hanaki ci dayawan" Hannun na miƙa zan kai mata duka muka haɗa ido da anty shamsiyyah wacce suke cin abinci a tire ɗayah itada anty juwairah,harara ta zanbagmin alaamar kar nayi. Amma hakan bai hana na bugeta kaɗan ba. Haka muka gama cin abincin babu wanda yasamu damar yin faɗa,dan anty shamsiyyah tana nan tadawo gida bayan tagama makarantar kwanan ta waccen satin. Har aka gama murnar dawowarta nidam banyiba,dan ninasan takura mana zatayi. Daɗinta ma aurenta za'ayi da ɗan gidan,amma a sashen hajjah ya tashi,yasamu aikin gwamnati yayi gininsa dadai misali,da yanuna yana sonta dama tun tana ƙarama sai aka saka musu rana. Bikin duk na cikin gidanne,mune sashen amrayah yayinda su maryam kuma ƴan sashen ango,. Murna ta ɗaya ce a bikin za'a mana sabon kaya kuma za'ayi su cin cin da nakiya,amma banda wannan babu ruwana da sha'aninsu,dan daga shi har ita amaryar ba shiri mukeyi dasu ba,sai yazo gidan sau uku bamu haɗu ba,kasona kawai nake samu na mintin dayake kawowa. Itama anty juwarah da take ƴar babba ba wani shiri take sosai ba,dan dama anty shamsiyyah tafita sosai,ko a makaranta ma tazarar shekarah uku ta bata,ita ta gama jss ita kuma ta gama sss,dukkan su hutu suke,amma bayan bikin anty juwairah zata koma ta cigaba da karatunta. Tunda satin bikin ya kama ƙawayen anty shamsiyyah suka fara zuwa gidan,duk yawancinsu wanda tayi a makaranta ne sai kuma na cikin gari kaɗan,dan dama ita tafi anty juwairah ɗaukar duniyah da zafi,shiyasa ma bawani shiri suke ba,koyaushe tana cikin cemata tafiye sanyi da ƙauyanci,itadai jinta kawai takeyi. Biki aka sha mai kyau ba laifi,amma ba damu akayi ba tunda sannan bamuda wani wayo,dan ko gidan amaryar ma bamuje ba,iyah anty juwairah ce taje kawai,oho nidama ba san zuwa nake ba,murna ta ɗayace sun bar mana gida zamuyi yanda muke so,musakata mu wala. Duniyah sabuwa ta koma mana,babu mai cewa mu bari,anty shamsiyyah ce ita kuma ta tafi,hajjah kuwa hmmm ai wannan mun raina mata wayo,idan bata nan har babu daɗi mukeji mun rada wacce zamu tsokana. Uh shekarun sun fara zuwa har muna aji biyar na primary,zuwa sannan mun ɗan wasu abubuwa,ba kaman da ba,dan yanzu mukan yi wankin kayan mu ƙanana,wani lokacin kuma har wajen girki muke shiga. Maman yara ce ta tafara cewa mudunga shiga muna ganin yanda ake,inno kuma ta hana,saidai kuma dole mu fara aiki,saboda kowanne lokaci za'a iyah tafiyah damu kokuma aure yazo mana da wuri,dan idan wani yace yana son ɗayar mu a kowanne shekarune indai ya kai sha huɗu to Baba Shahu saka ranar aure zayyi. Wannan shine ƙalubalen da zamuyi dakon tunkararsa idan yazo,duk da iyayen riƙon namu bazasu so haka ba amma kuma babu yanda zuyi idan ya faru. Ƙanana nan kayana na tattara ina sanɗa zan kaiwa anty juwairah danaga tana wanki,nasan ina zuwa inna roƙeta zata ƙarba,musamman idan nace zan tayata ɗiban ruwa. Inno ce ta ganni ina shirin wucewa,aikuwa kash rashin sa'a sai jin muryarta nayi. "Sabrah ina zaki da kayan dazaki wanke,kin manta wajen wankinne kike shirin wucewa" "Iye na'am inno dama ......uhm anty juwairah ce zata ɗan tayani na wanke" "Zaki kaimata dai irinna wancan satin,banace ku dunga wankewa ba,shine zaki kai mata saboda kinda tana wanke miki koh,to ƙaro dana khairi itama ki wanke mata" Tsalle nafara da dira kafa ina kukan tsiyah. "Kai inno kai inno ya za'ayi ace ni zam wanke mata wandon datake fitsari a jikinsu,ni wlh....." "Ke wlh me?...bazaki wanke ba ko mai,ba ƙanwarki bace,keda ba wata zaki kai ta wanke miki ba,ashe babu daɗi kenan....." Katsewa tayi da maganar jin muryar baba shehu yazo yana mata magana. "Shatu maza kizo wata yarinyah aka kawo,wani mutum ne ya kawota amma munyi munyi tayi magana taƙi,gashi mutumin ya riga ya tafi" "Toh ikon allah,yarinya ce ƙarama har haka?" "Ahah ba ƙarama ba ce,dan zata fi su khairi da kaman shekara guda koh fi ,saidai daga ganin yarinyar kaman taga rayuwa sosai" Juyawa inno tayi tabi bayansa domin ganin wacce yake magana akanta,nima ina za'a barni a baya gulma tana cina,da sauri nabisu dan ganin wacece,musamman danaji ance sa'armu ce,rabon da'akawo mutum mai ɗan girma tun muna ƙanana,hakan mazane guda biyu,shiyasa abin yabani mamaki. Binsu nake a baya batareda sun ganni ba,har muka ce office ɗin baba shehun,a bakin ƙofar na labe ina leƙawa kaɗan kaɗan,yarinyace kam kaman yanda ya faɗa,sanye da wata riga iya gwiwarta,da alama rigar ta daɗe a jikinta saboda dauɗar da rigar take tattare da itah. Gashin kanta dogone ya zube gaban goshinta wanda yana ganin fuskarta sosai,saidai duk da haka mutum sai ya hando farar fatarta datayi baƙi saboda dattin jikinnata. Babu takalmi a ƙafarta,duk ta farfashe kaman wanda tayi tafiyah akan ƙaya,a takaice dai in ka haɗu da itah a jeji zaka iyah rantsewa fatalwa ce. Saurin rufe bakin nayi domin karnayi babban motsi lokacin danaji baba shehu yana yiwa inno magana. "Gata nan Shatu ki shiga da itah ciki,nasan akwai yara a wajenki haka itama maryamu(maman yara),nayi niyyar kaita wajen Hajjah,saidai zamanta wajenta bazai yiyuba,saboda yarinyar tana buƙatar kulawa da ƙwantar da hankali idan ana so da dawo yanda take,kafin sannan ki kaita ciki ki shiryata ko kayan sabrah ta saka,zumuje asibiti a dubata,koda juwairah sai mu tafi. Ganin inno taja hannun yarinyar zasu fitone yasa na koma cikin gidan da gudu. Da deen mukayi karo a bakin ƙofah zai fita,saurin riƙo hannunsa nayi jikina har rawa yake wajen faɗa masa mai ya faru. "Kai dallah zokaji wata magana,bari kaji munyi sabuwar ƴar uwa,saidai kama take da fatalwa idan ka ganta" "Ƙaryah kikeyi,nasan ƙaryarki fah sabrah" "Mtsww bana son raini,ina maka ƙarya ne,ta barika ga yanzu inno zata shigo da ita,in da gaskene sai nayi maka duka uku,ko kayi bacci kuwa" Muna cikin maganar ne muka hango inno ta kamo hannun yarinyar sun nufo hanyar shigowa gidan,haɗa ido mukayi da yarinyar,duk da lokacin banida wani hankali amma kuma naga wani abu wai tashin hankali a cikin ƙwayar idanuwanta. "Ku kuma mai kukeyi a nan wajen,yar butan uwa ina kallon idonki ai kina leƙowa,wato kinzo kina yafa masa tun kafin mu ƙariso koh?" Tun kafin ta dungureni na shige gida ina dariyah,dan dama mun sabayi nida inno tawa takaina. Shashenmu suka shigo lokacin na koma wajen wankina,amma ban ɗauko na kharin da'akace ba,saboda naga inno ta manta da zancen. A bakin baranda suka tsayah da yarinyar wacce take ta rarraba ido a gidannamu,kaman wanda ta daɗe bata ga gida ba,ni inaga ma daga jeji aka ɗaukota. Maganar da inno take matane ta katsemu dukka dagani har itan a tunanin damuka faɗa. "Yarinyah menene sunanki?" Shuru tayiwa inno tana kallonta,da alama taji mai tace amma kuma bata mayar mata da martani ba" "Da alama kinji mai nace,ko bakya magana ne?" Jijjiga wa inno kai tayi,da alama tana maganar kenna ba kurmiya bace,amma menene haka ya hanata yin magana,allah ya tsaga maka baki dan kayi magana amma ka rufeshi kirif mai yasa?,mu gamunan sai anyi da gaske muyi shuru,amma ita maganar ce taƙiyi Ɗan karamin murmushi inno tayi mata wanda zaisa ta kwantar da hankalinta, "Ki saki jikinki kinji,nan gidanku ne kema kaman sauran yaran dasuka tsinci kansu a gidan,ki kwantar da hankalinki babu abinda zai sameki,ki ɗaukeni kaman uwar data haifeki,nikuma nayi alƙawari zan riƙeƙi tamkar ƴar cikina kaman yanda na riƙe sauran yaran" Ɗan murmushi itama yarinyar tayi amma har sannan akwai zullumi kwance a cikin idanuwanta. Rigar jikinta inno ta ɗaga zata ciremata tayi saurin riƙewa tana zare ido. Nida inno ƴar dariyah mukayi da muka gani mai take nufi,wato tana kunyar a ciremata riga,da gaskiyar ta muma tun yaushe inno ta daina yimana wanka,sai ita za'ace za'a yiwa wanka,ganin dariyar danake yimatane yasa ta ƙara sunkuyar da kai,inno ce ta kaimin duka tareda nuna min hanyar barin wajen. Fita nayi na nufi wajen su khairi,zuwa lokacin labarin zuwan yarinyar gidan ya zagaye ko ina na gidan. Saida aka kai ruwa rana kafin ta bari inno tayi mata wankan nan,a tunanina kunya takeji kaman yanda muke idan za'ayi mana,saidai kuma da alama hasashena ba daidai bane,mai yiyuwa tana boye wani abune a jikinta,wanda yazama sirrinta da take so ita kaɗai tasani. Komadai menene naga kaman ta yadda da inno,daga yanda ta ɗan sake da ita. Gyara mata jikinta tayi,tareda bata kayana ta saka,duk da ta ɗan fini a tsayi,saboda na ɗan fi khairi jiki amma kayan sun shigeta saboda yanda halin rayuwa yayi da itah,da alama idan bata tsinci kanta cikin hakan ba zata iyah fina ƙiba. Wanki mai kyau inno tayiwa gashinnata kafin yasamu damar yij kalar irinna bil'adama,haka zalika fatar jikinta wanda yanzu ta nuna kalar ta ba fara ba,kana kuma ba baƙa ba. Mashaallah tana da kyau dadai misali,wanda yanzu yasamu damar fitowa,saidai kuma ramar datake jikinta itama wani abune daya yi mata cikass. Hannunta inno ta riƙo suka fito daga ɗaki zuwa harabar gidannamu,inda kowa ke haɗuwa idan ya fito daga sashensu. Kallo ɗaya tayi mana tayi saurin sauƙe kanta,ganin yanda tarin yara suka kafeta da kallo,tunda suka fito wajen idona yake kanta,haƙiƙa naji daɗi da'akace a sashenmu zata zauna,koba komai na samu abokiya idan mukayi faɗa da khairi,dan haka kawai nakejinta a raina tamkar ƴar uwata. Baba shehu ne yafara magana,dan dama duk sanda aka kawo wani indai yanada wayo to zai faɗi sunansa muma mu faɗa masa. "To alhamdulillah,godiya ga Allah daya bamu wannan rayuwa mai albarka,kaman ko yaushe bama rasa amsar ɗaya daga cikin al'ummar musulmi zuwa wanann gida wanda ya tara yara marasa galihu,to yauma mun samu baƙuncin wata baiwar allah wanda aka kawomana ita an sameta a jeji a zaune. Muna fatan masu riƙon gidanann zasu riƙeta kamar yanda suka saba ga kowanne yaro idan ya faɗo hannunsu,duk da cewa ana biyansu amma hakan bashine yake nuna an biyasu dukkanin ƙoƙarinsu ga yara marayu ba,wannan sakamako ne da sai allah ne kaɗai zai biyata a ranar ƙarshe. Sannan ku kuma ina fatan zaku rungumeta tamakar ƴar uwarku,ku rayu tsintsiya maɗauri ɗayah" Dukkanmu haɗa baki mukayi wajen amsawa,cewar zamu karbeta a matsayin ɗayarmu. Bayan an gama jawabi ɗaya bayan ɗaya muke zuwa muna faɗamaata sunanmu,har aka zo ƙaina. Tashi nayi na isa gareta tareda kama hannunta. Kallona tayi da mamaki,inda ta sauƙe idonta akan hannunnamu kafin ta kuma mayarwa zuwa cikin idona,murmushi nayi mata mai nuna mun karbeta zuwa cikinmu kafin na yi mata magana. "Sunana sabriyyah ana cemin sabrah,ni ƴan biyun khairiyyah ce,nasan kinga kamarmu koh,ke kuma fah menene sunanki,har yanzu baki faɗamana ba?" Da gangan na tambayeta duk da nasan ba amsamin zatayi ba,dan inno ma ta tambayeta ɗazu amma bata amsa mata ba,ga mamakina sainaji tayi magana cikin dashashshiyar murya mai nuna ta daɗe batayi magana ba. "Banida .......ssssuna,bansan sunan ba" "Khamriyyah ,sunanki khamriyyah daga yau kinji" "Khamriyyah.....?" Sunan nata ta faɗa,amma kuma saitayi kaman tambayata takeyi,dariyah abin ya bani wanda hakan yasa ni yin dariyar. "Sunanki mai daɗi khamriyyah,gashi yana kama da namu,mai yasa kike tambayata,nasan zai miki kyau shiyasa nafaɗa miki,ki dunga amfani dashi kafin kisan naki kinji?" Ɗaga min kai kawai tayi amma ,Bata sakemin magana ba,da alama bata shiiyah yin surutun danake shirin jan ta dashiba. Juyawa nayi na kalli su deen tareda cewa, "Ku sunnan ta khamriyyah daga yau,ya kukaji yana kama da namu koh" Hajjah ce ta harareni tareda kauda kanta tana mita "Mtsww yarinya sai shegem iyayi,daga ganin baƙuwa harkin saka mata suna dan kinga bata dashi,uhm" Inno tana jinta kuwa ta cafe, "Abune mai kyau ai hajjah,yarinyar dama tanason wanda zai jata a jiki,saboda halin da take ciki" Tafiya akayi da itah zuwa asibiti kaman yanda aka faɗa,yayinda mukuma muka nufi yin wanka domin tafiyah islamiyah,bamuje ta safe ba saboda ranar lahadi ne amma ta yamma kam dole sai munje. A hanya na kalli maryam wanda tayi shuru tana zazzare idanu, "Uhm maryam amma ya kike gani musami wata ƙawar,kinga mun zama mu huɗu kenan koh,farida dama mun fita,maman yarace take cusata a cikinsu" Farida tana daga baya tana jin abinda nake cewa,aikuwa ta cafe. "Eh in kun fini kuma wacce aka kawo ɗin ai tafiku,dan haka idan kukayi mata raini kuma nayi muku" Binta nayi da gudu na buga mata jakar makaranta ta a bayanta,duk abinda ake deen,khairi,da maryam basu tankaba. Ganin abin yayi yawane ma deen ɗin ya kallemu tareda yin magana cikin faɗa, "Ku dallah ku kyalemu da zancen wata yanxu,ke sabrah wato kin manta da dukan malam garzali koh,hmmm sai ya kamaki kiyi ta ihu kaman an kasheki,amma kinfi kowa manta mai zamu tarar,gashi bamuje wajen anty juwairah haddaba,hmmm yau akwai duka" Tashi ɗaya abin ya faɗomin a rai,tunda na manta da hakan sai yanzu,idona ne ya fito nayi firi firi ina tuno yanda yake zambaɗamin bulalar idan bankai haddarba,kallon su maryam nayi wanda tun ɗazu su sun tuna da hakan,nikaɗaice na manata,nake biye farida wacce iyah haruffah ake koyamusu,kar'bar haddar ma tare suke bayarwa. Tuntsurewa da dariyah deen yayi yana bubbuga takashinsa wanda yake bada ƙarar wanduna da yawa. "Ihuuuu wasu zasu sha duka,nayi ciko tamau,kaya za'a daka,ku kuwa idan ya kamaku kowa sai tayi fitsari" Munji haushi abinda ya faɗamana saidai yau babu damar maida martani,dan cikin kowa ya ɗuru ruwa da tsoron malam garzali. Haka mukaje kuwa yayi mana duka,har aka dawo gida muna kuka,musamman khairi,tun inno tana rarrashinta har tagaji ta bari dan haushi. Basu anty juwairane suka dawo gidab na har wajen magriba,saboda saida akayi mata ƙarin ruwa tareda gwaje gwaje,iya maleria ce kawai take damunta sai typhoid saboda gurbataccen ruwa da tayi tasha. Ba laifi ta sauƙi sosai,dan iyah magani suka rubuta mata wanda zata dunga sha. A ɗakinmu aka ce zata dunga kwana kusada katifata. Tare mukaci abincin dare,saidai babu wanda tacewa komai har muka gama,muma bamuyi mata magana ba sai binta da ido kawai da muke,ganin sabon abu. Bayan mun shiga mun kwanta inno ce ta tofamaana addu'a kafin ta kashe mana wutar ɗakin,duk da yanxu mun iya addu'ar da kanmu amma kuma sabon yimana harda yaran da suka zo kafinmu yabi jikinta. ........cikin dare naji an tsala wani uban ihu mai masifar firgitarwa,zabura mukayi dukka muka tashi,musamman ma ni da nake kusada ihun. Khamriyyah muka gani a zaune har sanann bata bar ihunba amma dai ƙarar ihun ya ragu. Dukkan ilahirin jikinta rawa yake ga wani gumi daya rufeta shirkif kaman an watsa mata ruwa......... Taku _sadi-sakhan_ Ƴar mutan jama'are. *(¯`*•.¸,¤°´✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿`°¤,¸.•*´¯)* *MABARACIYAH* (mai harshen damo) тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιε. _haƙƙin mallaka_ _*sadi-sakhna*_ (Yar mutan Jama'are) Paid book #400 3131951977 Auwal sadiya First bank Mai turo kati kuma ta wanann number MTN 09035784150 Mutanen niger su tuntubi wanann number +227 97 21 16 15 Naƙara shafin free har zuwa page 20,zuwa lokacin inka shiryah kazo a fara dakai ranar juma'a. _____________________ Assalamualaikum barkan mu da wannan lokaci *ABMAR COLLECTION* ina nan na kawo muku kayana masu kyau da sauki👌🏻 KAMAR SU:- Atamfa, Atamfa Mai golden,💁‍♀️ Lace ,Shadda lace Yadi, Shadda Abayas💥 Kids wear Takalmi, jaka, mayafai💥 Sleeping dress, kananan kaya na gayu🔥kayan kitchen, DA DAI SAURANSU ina Sokoto ina tura kaya ko ina da izinin ubangiji mai son kayana pc ina maraba daku siyan daya ko sari👏🏻domin neman karin bayani sai ku neme ni ta wannan number waya👉08101521252 nagode kwarai da gaske💃💃 13••14 Dukkan mu kallonta muke yanda take nishi numfashinta yana sama da kasa,kaman da alama yana mata wahala wajen shagarsa. Gashi dukkanmu dagani har khairi da kuma sauran yaran an rasa mai matsawa kusada itah,ganin hakanne yasa na jawo khairi tareda yimata raaɗa a kunne ,na taje ta ƙira inno a ɗakinta. Bata daɗe da fitaba sai gata tashigo itada innon. Saurin ƙarisawa wajen ta tayi,wanda har yanzu razanar bata bar jikinta sosai ba. "Khamriyyah lafiyah kuwa,kinga ɗago ko kalleni,menene ya faru" Tana yi mata magana tana tofamata addu'o'i a jikinta,dan abinnata yayi kama da wanda aljanu suka ra'esu. A hankali take sauƙe sautin kukannata,har ya zamo iya ajiyar zuciya kawai takeyi,kallon inno take da kuma su sabrah,sai a sanann ma takula asheda mutane a kanta. Da alama kenan duk tambayoyin da inno tayi mata batasan tanayi ba. Mamaki abin yabani,wai dama haka masu aljanu sukeyi,danni ban taba ganin mai yiba,tunda mu iyah rayuwarmu to ta ƙarene dag makaranta sai kuma gida. Bamuda buƙatar yawo yawo irinna yara,dan idan wasanne har ma munyi yawa inaga. "Kalleni khamriyyah,yanzu kinajin mai nakecewa,in kinaji ki ɗagamin kanki" Ɗaga kan khamriyyah tayi,wanda hakan yake nuna taji abinda inno ta faɗa kenan. "Mai yafaru dake,ki faɗamin idan har kin ɗaukeni a matsayin uwa,kaman yanda na ɗaukeki a matsayin ɗiyata" Jijjiga kai khamriyyah tafarayi tana ƙara dawowa da kukannnata,saidai yanzu a cikin hankalinta takeyi,bana razana bane, Yanda take kukan da kuma abinda yake kan fuskarta,ya isa shaidawa mutum batason amsa tambayar da inno tayimata. "Kiyi haƙuri inno.....in in in ?" Daga haka ta gagara sake cewa furta wata kalmar bayan haka. Ganin tambayar bazai haifar da wani ɗa mai ido ba,saima ƙara saka ta kogin ɗimuwa,yasa inno sauke ajiyar zuciya tareda dafa kafaɗarta "Kiyi shuru ya isa haka to kukan,ki kwantar da hankalimki,inshaallah babu abinda zai faru,daga ni har sabin ƴan uwanki a shirye muke da mu tarbeki a cikinmu,sannan mu saurari kukanki,a duk lokacin da kika yi ra'ayin sanar da mu,in allahh ya kaimu gobe zan yi ƙoƙarin sanar dake wasu addu'o'i kafin a salak8 kema a islamiyyah." Ɗaga kai khamriyyah tayi,alamr taji abinda innon ta faɗamata,sannan ta koma ta kwanta tareda rufe jikinta ta mayafi. Juyowa wajenmu inno tayi tareda yimana magana muma,ganin yanda mukayi tsuru tsuru muna kallonsu " yanzu dare ya fara ku samu ku kwanta gobe da makaranta." "Toh" Shine kawai abinda bakimmu yasamu ƙwarin gwiwar fada. Da safe tashi mukayi har khamriyyan kaman babu abinda yafaru jiyan. Shirin mu mukayi kaman kullum cikin kayan makarantar tamu,har zan fita zuwa wajen karyawa khairi ta riƙe hijabina ta bayah. "Wlh baki isaba sabrah,haka kawai jiya ki sakawa hijabinki manja shine yanzu kuma ki ɗauki nawa,wlh ki ciremin" Juyawa nayi na kalleta,duk da nasan banawa bane,ammafah babu alamar zan karbi laifin ko kuma na cire hijabin saima ƙoƙarin ƙwace riƙon datakemin nakeyi. "Dallah ki sakeni,a gidan uban wa na saka manja a hijabinnawa,wannan ne nawa,saidai idan ke kika saka manjan" Faɗa muka fara har hijabin yana ƙoƙarin yagewa,inno ce ta fito daga ɗakinta da ɗan ƙaramin yaro a hannunta wato Abdoul wanda take riƙo,ɗaya hannunnata kuma da naira goma guda biyu na taran mu. Sakin baki tayi tana kallon yanda muke ta faɗa bayan ita kuma tana ciki tana nemo mana kuɗin break fast.. Ranƙwashi ta saki mana a kai kowa guda ɗayah,take kuwa khairi ta fasa ihu tana tsaramata abinda nayi mata. Kallona tayi nayi saurin kauda kai ina jiran mai zai biyo baya. "Hmmm wai sabrah nikam wannan faɗannaki na rashin gaskiya yaushe zaki daina ne?" "Ba nata bane hijabin nawa ne fah inno" "Wlh ƙarya take,ga can nata ita taci ɗan malele a wajen su Umaimah,ni banci ba" "Yi shuru nasan ita taci ai,to cire hijabin ki bata,ki dau naki ki saka,wani ne yahana ki kaishi wajen wanki,gashi yau monday,kai sabrah allah ya shiryeki" Cun'buna baki nayi bayan wulga mata hijabunnta,tareda fasa kuka ina zama a wajen. "Ni wlh to inno bazan je makaranta da nawa hijabinba,malam Ɗahiru dukana zayyi, koroni zayyi kona jema" Hijabin khairi ta ɗauka ta saka tareda ƙarbar nata kuɗin tayi waje,tunda an ƙwata mata hijabinta shikenan. Shigewa ɗaki inno tayi bayan ta zabga min harara,alamar aiki bai isheni ba. Bayan tashige nikuma tsayawa nayi ta burburwar ganin yanda khamriyyah ta tsiramin ido tana kallona,ashe tun sanda muka fara faɗan ma tana ɗakin tana kallommu,amma baxaka ce da mutum a wajen ba. "Meyasa kika yi shuru kina kallonmu" Banyi zaton zata amsamin ba sai naji tayi magana "Saboda sha'awa kuke bani sosai" Tunani na tafi a raina, "Sha'awa kuma,muna faɗa kice sha'awa?" Bata mayarmin amsar ba inno tafito daga ɗakin tareda kallona "Dallah tashi ki ciremin kayan nan inba so kike kiyi datti dasu ba,dama burinki kenan ki zauna a gida ai,in kika kuskura baba shehu ya ganki baki je makaramta ba bada ke zayyi ke kika sani" Jikina ne yayi sanyi,dan na tsani jin an ambata min kalmar za'a bayarni. Tashi nayi na cire riga da wandon na mayarda doguwar rigata wacce na cire. Komawa nayi kan kujerar da khamriyyah take na zauna mun kallon juna. "Khamriyyah meyasa bakya yin magana sosai?...." "Saboda bana buƙatar yin hakan,idan naji buƙatar hakanne nakeyi,saidai bawai buƙatar hakan yana daga cikin abinda nake so bane,saidan yana daga cikin kaɗdarata" "Ƙaddara kuma?....meyasa kike magana kaman manyan mutane,kowani babban ma da ƙyar zai gane" "Kamawa tayi shiyasa,sannan yawan magana ko yin magana bashi yake sakawa ka iya magana ba,saidai idam ita maganar tasoka da iyata" "Amma....." "Sabrah ke kuma kin kasance mai yawan tambaya sannan da manta damar da kike da itah rahama ce. Duk da kina gidan marayu amma kuma kinada uwar da ko ita ta haifeki iyakaci,kina da ƴar uwar da kuke jini ɗaya,sanann kinada kwanciyar hankali babu fargaba,uwa uba sunada muradin baki ilimi wanda zakije ki dawo kina gaban idonsu,meyasa kike wasa da hakan?..." "Kin ban mamaki,yanxu fah kika ce muna burgeki da muna faɗa,yanzu kuma kina cewa meyasa mukeyi?" "Kina burgeni saboda kin samu damar yin faɗa da ƴar uwarki,kina ban takaici saboda kin bari kina faɗa da ƴar uwarki" "Kinada abin mamaki,dole kiyi shuru,dan idan kikayi magana babu mai cewa ke yarinya ce" "Kema kinada abin mamaki da kika kasa tambayata meyasa banawa kowa magama saike kaɗai" Shuru nayi sai a sannan ma nayi tunanin hakan,bata yiwa kowa magana ba saini kaɗai meyasa toh. "Meyasa toh?..." Ƴar dariyah tayi kafin tace. "Karki damu haka kawai nake jin na yarda dake,amma maƙasudin dalilin hakan,bazan iyah faɗamiki ba,dannima bansan shiba tukunna" Rasa abinda zance ma nayi,dan gaskiyah wannann akwai wani abu tattare da ita. "Menene a rayuwar taki toh da kike cewa na more.....kodayake manta kawai kince bakyason yawan tambaya" Suna cikin magana ne,inno tafito daga ɗakin. "Tunda bazaki je makarantar ba ai saiki jata ku zagaya koh,ko kina nufin yau a nan zaki yini kai" Tashi nayi na miƙa mata hannu takama muka yi hanyar fita,dan dama sonake mu fitan,ina tsorone kar inno tace nayi shishshigi. Sashen maman yara muka fara zuwa,bamu daɗe ba muka fito,dan ma mun ɗan tsayah munci ƙosai data bamu,daga nan sai mukayi hanyar sashen hajjah. Turuss nayi har sannan muna sakale da juna na kalleta. "Kiyi a hankali,hajjah faɗane da ita sosai,zata iya kai miki duka ko kuma tayi ta miki faɗa,amma karki du tanada ɗan kirki,idan muna zaune zaki gane hakan" Ɗaga min kai tayi bayan tagama jin abinda nace,daga nan jata muka shiga ciki. Da sallama na shiga falon da ƙarfi,anty juwairah ce ta tashi da sauri daga kan kujerar datake kawance ta rufemin baki Magana tafarayi cikin murya ƙasa ƙasa,har sannan hannunta na kan bakina, "Kehh yi shuru haka,hajjah tana bacci,batada lafiya magani tasha,idan kika tasheta kinsan sauran" Ɗaga kai nayi kafin ta cire hannun ta akan bakina,gyara bakin nayi kafin na gaisheta. "Anty juwairah ina kwana?" "Lafiyah kalau wanann ƙawar takice kenan? Sabuwar ƙanwata" Tafaɗa dana ƴar dariyah idonta na kan khamriyyah,itama khamriyyam murmurshi tayi kafin ta gaisheta kaman yanda nayi. "Ke wai tukunna ma,meyasa bakije makaranta ba dukka sun tafi,ko dan ankawo miki sabuwar ƙawane,kefah dama in kika samu abu sabo..." "Ahah anty ba haka bane,manja na shafa a hijabin kuma ba'a wanke shiba shiyasa" "Hmmm in ɗan kamfaine ai kin iya kawowa na wanke miki,dayake hijabin makarantane sai kice kin manta,kuzo muje waje haka karmu damu hajja tana bacci" Tashi anty juwairah tayi ta fita muma mukabi bayanta har bayan gidan,inda muke shanya kuma ƴar bishiyoyi suke,ear piece ne a kunnenta tana tafe muna binta har muka je wajen wasu kujeru na dutse,zama tayi muma muka zauna. Cire abin kunnen nata tayi tana kallon mu ,musamman na khamriyyah hankalinta yafi komawa kanta. "Dagaskene sunan ki khmariyyah,kokuma ƙaryar sabrah ce" "Eh .....inaga sunana ne,koba nawa bane ma ina son yin amfani dashi tunda bansan nawa ba" "Kaman ya baki san naki ba,a ina kike kafin a kawoki nan wajen" "Bansani ba,ina rayuwane amma bansan wace kala ba,lokacin data faɗamin sunan naji ina sonsa sosai" "Kinada abin mamaki sosai,sannan daga gani kin fuskanci kaɗaici a rayuwarki da dama,saidai ina so kisani zamu kasance a duniyarki,bazakiyi kaɗaici ba daga yanzu" "Nagode anty juwaira,nima zan ɗaukeku tamkar ƴan uwa na jini,nayi alkawarin yin komai domin faranta muku da kuma yarda daku kaman yanda kukayi min" Rugumeta anty juwairah tayi tareda jin daɗi maganarta,dan kaman yanda nake jinta a raina haka itama anty juwairah n. Mun daɗe a wajen muna zaune,wani lokacin mu tashi muyi wasa mu dawo,ko kuma ita anty juwairah da dunga bamu labarin makarantarsu,dan hutun jss suke har yanzu mai tsayi,basu koma ba tukunna. Washagari dole na tafi makaranta tunda inno ta wanke min kayan,kuma da gargaɗeni da kada na sake zama a gida banje makaramta ba indai inaso naci gaba da zama tareda su. Tunda ga ranar anty juwairah ce takasance tana jan khamriyyah a jiiki,idan muka tafi makaranta takan zuwa wajenta ta koyamata abubuwa da dama. Idan muka dawo kuma a yita wasa,har zuwa lokacin tafiya islamiyyah,dayake satinta ɗayah aka sakata a islamiyyar itama. Lokaci da baifi wata guda ba mukayi wani sabo da ita sosai,musamman ma anty juwairah wadda take yini da ita a kullum,dama kuma gata mai son yara da haƙuri,sai hakan yaƙara saka shaƙuwa a tsakaninsu. Hutun su anty juwairah ne ya ƙare bayan wata ɗayah da satuka da zuwan khamriyyah,yazama dole ta koma domin ta cigaba da karatunta. Ana gobe zata tafi muna zaune a sashen hajjan wajenta inda take haɗa kayan makarantar,dan motar safe zata bi ta koma. Dukkanmu munyi jugum muna kallon ta,itama da alama jikinnata yayi sanyi na barin gidan. Khamriyyah ce ta rarrafa tareda kama bakin jakar tana tayata zugewa,fuskarta duk tayi wani iri da tafiyar anty juwairah,kallon ta anty juwairah tayi tareda dafa kafaɗarta. "Karki damu kinji babbar ƙanwata,wata uku kawai mukeyi mu dawo,yanzu zakiga lokacin yayi na dawo,zamu cigaba da karatun mu a lolacin,kafin sannan ga nan ƴan uwanki ku cigaba da zama dasu kuna wasa kinji" Daga kanta tayi hawaye yana bin kuncinta,a yanda na kulada ita iyah anty juwairah kawai ta fi sabawa da itah sai kuma nida inno da khairi. Deen ma wani lokacin zakaga suna magana dashi jefi jefi. Washagari muna gani anty juwairah ta shiga mota ta tafi,ba kaman ko yausheba wannan karon nafi damuwa da tafiyar tata,saboda nasan yanzu khamriyyah zata zauna a gida ita kaɗai. Da daddare bayan munci abinci muna zaune a ɗakin inno an saka fitilar ƙwai a gaba muna bada haddar izu ɗayanmu,dan ganin makarantar basuda tausayi wajen duka yasa inno take biyamana kafin muje mu bayar. Abin mamakin biyawa ɗayah akewa khamriyyah takawo tass,kaman dama tayi haddar wajen,saidai kuma da inno tambayeta cewa tayi batayiba,duk da abin da mamaki amma kuma Allah ba irin mutanen daya baya halitta da kuɗirar sa. Bayan mungama karatunne na kalli inno tareda yi mata magana. "Inno da an saka khamriyyha a makarantarmu,tunda anty juwairah ta tafi iyah ita kaɗai zata zauna a gidan kawai" Shuru inno tayi tana kallona kafin tayi min hararar wasa. "Uhm wanann,kin faye iyayi,to dama munyi maganar da baba shehu,har yafaɗawa shugaban makarantar ma,gobe zata fara zuwa,zasuyi mata interview sai su bata aji" Tsalle nayi na ɗale inno kafin na komo wajen khamriyyah na faɗa kanta muka zube a wajen muna dariyah. Itama dariyar take da alama taji daɗin hakan sosai. Haka muka kwana muna labarim makarantar dakuma mutanen dazamu hadata dasu washagarin Da'akayi mata interview bata wani ci sosai ba amma dayake tana da ilimi kuma primary ne sai aka barta kawai a ajinmu,wanda hakan dama mukeso dukka. Tafiyah tayi tafiyah wasa wasa khamriyyah tayi shekara guda da zuwa cikin rayuwarmu,duk wanda ya ganta bazaice itace a shekarar bayaba. Tayi kyau tayi ƴar ƙiba,duk da jikinta ba mai nuna girma ne sosai ba. Ance saika zauna da mutum kake gane halinsa,hakane wannan maganar,kaman yanda nakeda tsokana da kuma son mutane,surutu da kuma masifah. Ita kuma khariyyah tanada sanyin zuciyah da kuma rauni ba kaman mu ba gaskiyah. Yayinda shikuma deen yake da wasa da dariyah,duk da cewa baikaimu a haifeba amma kuma yanada tsayi sosai. Ita kuma maryam shuru ne da ita da kuma zurfin ciki. Idan anyi mata abu saidai tayi dariyah kawai. Duk cikinmu khamriyyah tanada wuyar sha'ani,duk da tayi shekara tareda mu amma har yau babu wanda yagane ainihin cikinta da halayyarta,tanada nutsuwa da lura akan abu kafin tasan wane irin mu'amala zatayi dashi. Wani idan ya ganta zaice sanyin rai gareta da haƙuri,amma haƙiƙanin gaskiya takan share abune idan bai kaita bango ba,amma idan har abu yabata mata rai to tanada zuciya da kuma ɗaukar mataki. Wannan dalilinne yasa kowa ke shakkarta a ajinmu,sanann za'ayi mata abu ta shanye amma banda jurar taba ɗayanmu ko kuma cemana ƴan gidan marayu,wannan bata ɗaukar so koda wasa. Wani lokacin idan ana faɗa ita su khairi guduwa suke,nice nake ɗan tsayawa najata mutaho gida. Haka rayuwar tamu ta kasance har muka zana jarabawar shiga matakin secondry ƙarama. Da gudun mu muka shigo gida muna murnar gama zana jarabawar,kowa yana ihu da murnar zamu shiga muma secondry. Turus dukkanmu mukayi ganin wasu mutane biyu mace da na miji,sun ɗan manyanta,da alama mata da mijine. Kallon mu suke ɗauke da murmushi a fuskarsu. Hajjah nagani tayi shuru da itah,da alama a sashen ta wannan mutanen zasu ɗauki yaro. Tantama tace ta share kuwa danaji maganar da baba shehu yakeyi,dama inkaga sabin mutane a gidannan toh wani za'a ɗauka a cikinmu. "Toh kungansu nan yaran sun dawo daga makaranta,duk da sun ɗan girma amma basu wuce ɗauka ba har yanxu" Faɗaɗa murmushinta matar tayi,jin abinda baba shehu ya faɗa "Hakane kam gasunan mashaallah,to wacce ce maryam a cikinsu toh" Tafaɗa tana ƙare mana kallo domin gano wacece maryam ɗin Dukkan idon mu sauƙa yayi akan maryam ɗin wacce tayi wuƙi wuƙi,tana kallon mutanen. Haƙika har a raina banason rabuwa da itah,saidai kuma ina yimata murna da samun wanda zasu ɗauketa a rayuwar nan kuma si kula da itah,musamman danaga alamar mutunci kwance akan fuskarsu. Kuma dama ance labarin zuciyah a tambayi fuska,duk da wani lokacin kansa labarin daba shine daidai ba akan fuskarta su. Jawota baba shehu yayi tareda turata gaban matar,ganin hakan yasa ta tsugunna daidai tsayinta,zuwa lokacin duk murnar data ɗebo daga makarantar ta zubar da itah,sai hawaye daya fara taruwa akan fuskarta. Share mata hawayen tayi tareda yi mata murmushi wanda yake nuna kada ta damu komai zaizo da sauƙi. "Ki kwantar da hanlinki inshaallah komai zai daidaita,munyi miki alƙawarin zamu riƙeki tamkar yanda zamu riƙe wanda muka haifa. Duk da cewa Allah bai bami haihuwa ba,amma kuma hakan bai hanamu sanin ya soyayyar samun ɗa take ba,mun sameki inshaallah zamu riƙeki yanda ya kamata maryam. Muna fatan kema zaki riƙemu tamkar iyayenki" Ɗaga kai tayi tana share hawayenta,alamar taji abinda tace ɗin. Tashi tayi tareda kallon hajjah wanda aka ce itace mariƙiyarta. "Mungama dama cike ciken takardar jiyah,yanzu muke son wucewa da itah cikin garin katsina,saboda akan hanya muke" "Toh ba matsala,dan allah ku riƙeta da amana,batada matsala ko kaɗan,yarinya ce mai nutsuwa" "Karki damu zamuyi iya ƙoƙarin mu sosai" Kayan maryam ta miƙo,dan dama tariga ta haɗa kayan tunda safe. Muna tsaye munyi soƙoƙo bama cewa komai,abin yabamu mamaki sosai,tashi ɗaya mun shigo da murna tare,lokaci ɗaya ita kuma za'a tafi da ita. Kallon mu take lokacin da matar ta kama hannunta suka fita daga gidan,binsu mukayi a baya cikin sanyin jiki,muna gani har suka shiga mota suka ƙulewa ganinmu kafin muka dawo gida. Murnar da muka shigo munayi na gama primary lokaci ɗaya ta koma ciki,kowa a cikin mu yayi jugum,cin abincima ya gagaremu,a duk lokacin da aka ɗauke ɗaya daga cikinmu a lokacinne muke tunawa da matsayinmu,wanda ba ɗaya yake da yaran da suke gidan iyayensu ba. Haka muka gama jimamin rashin ƴar uwartamu har muka daina,ganin duk abinda zamuyi bazata dawo ba ta tafi kenan. Zaman gida mukeyi kafin a sama mana makarantar sazamu tafi,sai murna muke dan munsan makarantar kwana za'a kaimu kaman sauran yaran gidan. Kwatsam sai mukaji baba shahu wai bazai kaimu makarantar kwana ba a gida zamuyi,roƙonsa mukai tayi amma ya ƙeƙasa ƙasa yace bazamuje ta kwana ba a gida zamuyi. Shirye shiryen tafiya makarantar muke har an siya mana uniform,shikuwa deen muna gani aka yi masa siyyah na kayan makarantar kwana zai tafi. Kallon khairi nayi wacce take zaune tana kallon maman yara tana yiwa deen shirin tafiyah makaranta,an siya masa abubuwa zai tafi mukuma bazamu je ba. "Wlh baba shehu baya kyautawa miye zai wani ce bazamujeba banda mugunta,ni wlh makarantar kwana nakeso " Tafaɗa tana matse idanu,nidai kallonta nakeyi nida khamriyyah,wacce ta gimtse dariyarta ganin abinda khairi takeyi. "Hhhhh yanzu khairi saboda sakalci dan bazaije makarantar kwana ba sai fara kuka?" "Eh ɗin ina ruwanki toh,kuma nace kuzo muje muyi masa kuka ina kun ƙi zuwa" "Kutt an gaya miki kowa irinkine,ba inda zanje" Khamriyyah ta faɗa tana sake shƙewa da dariyah,wanda yaƙara ƙular da khairyyah. Bayan wata guda da tafiyar maryam shima deen ya tafi makaranta,yazamo sauran mu uku kawai a sa'anninmmu,har sanann bamu fara zuwa makarantar da baba shehu yafaɗa zamu je ba,muna nan muna ɗan aikace aikace a gidan,tunda yanzu mune manya mata,anty juwairah tana makaranta. A zaune muke muna cin abinci suwaiba wacce itama a wajen maman yara take tazo ƙiranmu mu ukun. Gabana ne ya faɗi rass ganin mutane biyu mace dana miji,ko ba'a faɗaminba nasan mai ya kawosu sarai,dan abune da duk wani yaro na gidan ya sani,indai kaga mutane a gidan to wasu zasu ɗauka,yaran dun ƙarene har an zo kanmu ko me?... Katsewa nayi da tunanin jin mutumin yana cewa, "Eh gasunan kam ƴan biyune yanda kace,saidai guda ɗaya muke so zamu ɗauka daga cikinsu,wacce tafi farin siririyar zamu ɗauka" Kutt mai suke nufi,ai khairyyah zasu ɗauka,ina bazan iya rabuwa da ita ba,inno ma bazata iya ba. Jijjiga kai na farayi har sanda aka ce mushiga cikin gida,zasuyi magana,kafin azo ɗaukarta. Tun daga bakin ƙofar khairi take zabga uban kuka kaman ance mutuwa zatayi,nasan bana komai bane sai rabamu da za'ayi da ita. Kallonta nake amma banida ƙarfi ko ƙwarin gwiwar cewa tayi shuru,har muka shiga sashen namu wajen inno. Lokacin da labarin ya doki dodon kunnenta tashi tayi zumbur ta miƙe tana salati ,riƙo hannun khairin tayi tana dafa bayanta,daga cikin idonta zaga hango tsagwaron tashin hankali a ciki,da kuma fargabar rabata da za'ayi da khairin. Duk abinda ake dagani har khamriyyah babu wanda yace komai,saima kallonsu tamuke ganin yanda ta ƙaƙume inno tana zabga kuka. Wulgawar khamriyyah nagani tashiga ɗakinmu,bata daɗe ba sai gata ta fito da jakar kayan ta a hannunta. Duka kallonta mukayi da mamaki,har wacce take kuka shuru tayi tana kallonta. Inno ce tasami ƙarfin gwiwar yi mata magana. "Khamriyyah yana ganki da jaka ina zaki tafi haka?" "Inno binsu zanyi,zanje na faɗa musu su tafi dani su ƙyale khairiyyah,bazan iya jurar ganin sun rabata da ƴar uwarta ba,ko kuma su rabata da mahaifiyarta ba,wacce take sonta tamkar ita ta haifeta" "Amma.....khamriyyah baki daɗe da zuwa nan wajen,har yanxu kina buƙatar wanda zasu ɗebe miki kewa,kuma kinga bamu san halin da suke dashi ba,karki koma gidan jiya" Matsowa nayi kusada ita nima tareda dafata,tayi mana abubuwa da yawa,bai kamata bayan halin data shiga kuma tasake jefah kanta wani ba saboda mu. "Eh hakane khamriyyah bai kamata ki tafi ba bayan baki daɗe da zuwaba,sannan baki san wane kala bane,indan ta khairyyah ne karki damu da itah ni zan bisu su tafi dani in......." Saurin rufe mata baki khamriyyah tayi tareda jijjiga kai. "Kinfaɗi dalilin daya sa zan bisu,idan harke zaki tafi kibarta menene dalilin hakan toh,komin yanda zaki buƙaci wani a rayuwarki baikai ya ita ba,koda na barki kin tafi kina tunanin zaki ciresu daga rayuwaki ne?,kin manta abinda na faɗa miki lokacin dana ganku kuna faɗa,nafaɗa na ƙara faɗa kuna burgeni sabrah,kuma zan iya komai indai zan iya wajen ganin kun kasance tare. Zan tafi amma karki damu,ba kaman sauran yaran dasuke tafiya na ni zan dawo gareku,dan nan wajen yazama tamkar gidanmu inda aka binne cibiyata haka nake jinsa,kaman yanda nayi alƙawarin zam ɗaukeku tamkar ƴan uwana hakan bazai sanja ba ina kan baka ta" Matsawa tayi kusan inno inda suke zaune itada khairi. "Inno ke mahaifiyata ce,kuma har duniya ta naɗe bazan daina ganinki a hakan ba,kin rungumeni keda sauran yaran da suke wajennan,baku ƙyamceni ba,sanda nake buƙatar taimako kunyimin,dan haka nima bazan so ganin rabuwarki da ƴaƴanki ba,nice yakamata na tafi ba ɗaya daga cikinsu ba.Zan tafi ina muku fatan alkhari" Har ta kama hanyar zuwa office ɗin baba shehun na bita tareda rungumeta ta baya,waye zai min haka inba khamriyyah ba,ta kwammaci tayi komai akan su rabani da ƴar uwata,batasan itama banason rabuwa da ita ba,domin ta zama tamkar wani sashe na jikina. "Khmariyyah idan kika tafi keɗin kina tunanin zaji daɗi,anty juwairah ma datake makaranta bazata ji ɗadi ba idan ta dawo bata ganki ba" "Nasan bazakiji daɗi ba,haka itama anty juwaira bazata ji daɗi ba,amma rashin jin daɗinku shine zai tabbatarmin dazanyi ƙoƙarin dawows ku jirayeni zan dawo gareku,dan mun zama ɗaya" Baba shehu ne ya shigo daukar khairiyya da kayanta sai kuma yaga khamriyya riƙe da jakar kayan ta da'aka siyo mata,tun kafin yayi magana ta tura ni bayanta tareda kallon baba shehun "Baba shehu nice zan bisu ba khairiyyah ba" "Ke kuma?amma ai ita suka zaba,wanda suke so ai ita zasu ɗauka" "Amma saboda ita sukeso shikenan saisun ɗauketa kodah za'a rabata da ƴar uwar da ita kaɗai tarage mata,haka kuma ga mariƙiyarta wacce takejinta kaman ƴar ta? A tunani na muba bayi bane ƴan tattune,ahali na jini kawai muka rasa,hakan bai kai a maidamu marasa galihu ba,indai kai ka yarda to nice zan bisu ,idan basa buƙata toh suje wani wajen" Yanda ta tsayah tana zanzaro masa bayani babu alamar tsorone yasahi shan jinin jikinsa,tabbas gaskiya ta faɗa,su bazasu ɗauki duka biyun ba saidai su ɗau ɗayah,koda hakan na nufin rabasu ne. Karkata kai yayi tareda cewa "Shikenan hakane kam,zo muje toh,idan sun amince saiku tafi,idan kuma sunga basu aminceba shikenan sai suje wani wajen" Hannun baba shehun ta kama suka fita,har sunje bakin ƙofah ta juyo ta kalleni. Biyosu nayi a guje zan bisu office ɗin tayi saurin yimin alama na tsayah,nasan nufinta kar naje su ganni su ce ni zan bisu shiyasa ta hanani binsu. Ina kallonsu har suka bacewa ganina,shikenan nayi rashin ƙawata sauran guda ɗayan itama,taya zam manta da itah,kaman yanda tace zata dawo anya kuwa zata cika wannan alƙawarin,nacewa zata dawo garemu. Juyawa nayi na koma ɗakin mu na ƙwanta,duniyar nakeji tayimin zafi tana juyamin. Ko yaushe zamu daina sabawa da junanmu ana ɗaukemu,kumafah dolene a ɗaukemu saboda wasu su sami inda zasu zauna suma. .........hmmmm Taku _sadi-sakhan_ Ƴar mutan jama'are. *(¯`*•.¸,¤°´✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿`°¤,¸.•*´¯)* *MABARACIYAH* (mai harshen damo) тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιε. _haƙƙin mallaka_ _*sadi-sakhna*_ (Yar mutan Jama'are) Paid book #400 3131951977 Auwal sadiya First bank Mai turo kati kuma ta wanann number MTN 09035784150 Mutanen niger su tuntubi wanann number +227 97 21 16 15 Naƙara shafin free har zuwa page 20,zuwa lokacin inka shiryah kazo a fara dakai ranar juma'a. _____________________ Assalamualaikum barkan mu da wannan lokaci *ABMAR COLLECTION* ina nan na kawo muku kayana masu kyau da sauki👌🏻 KAMAR SU:- Atamfa, Atamfa Mai golden,💁‍♀️ Lace ,Shadda lace Yadi, Shadda Abayas💥 Kids wear Takalmi, jaka, mayafai💥 Sleeping dress, kananan kaya na gayu🔥kayan kitchen, DA DAI SAURANSU ina Sokoto ina tura kaya ko ina da izinin ubangiji mai son kayana pc ina maraba daku siyan daya ko sari👏🏻domin neman karin bayani sai ku neme ni ta wannan number waya👉08101521252 nagode kwarai da gaske💃💃 15••16 Abun ne nake jinsa tamkar a mafarki,shikenan khamriyyyah ta tafi,bazan sake ganinta ba,duk da tace zata dawo amma ban yadda da wanann zancen ba,duk yaron da'aka tafi dashi baya dawowa,nasan ta faɗaminne kawai dan na saki raina. Ina cikin tunani khairiyya ta dafani,ɗagowa nayi na kalleta ganin itama damuwarce a ranta. "Sabrah nasan kina kewarta koh,nima ina kewarta sosai,zata iyah komai damin mu,duk da ƙarancin shekarunta amma zata iyah tukarar abinda yafi ƙarfinta domin masoyanta." "Hakane khairi,muna mata fatan alkhairi a duk inda take" Bayan tafiyar khamriyyah da sati ɗayah inno tasamu baba shehu tayi masa magana akan ya kaimu makarantar kwana,nasan tana tsoron muma ta rasamune,ko kuma tana so murage kewar da muke ciki. Bayan tayi masa bayani kuwa ya amince da hakan,akan xai kaimu makarantar su anty juwairah wanda ita paper suke suna aji ƙarshe na matakin secondry. Munyi murna sosai amma ba kaman idan khamriyyah da maryam suna tare damu ba. A satin akayi mana shriri muka tafi,dan har an fara karatu. Ikon allah mai yadda yaso,da farko muna tunanin mu uku zamu tafi,sai gashi ashe mu biyune zamu tafi kawai. Kaya dayawa inno ta haɗa mana,su sukari,gari,ƙarago,da kuma ƴar madara,saboda in mukaji yunwa mu ɗan saka a cikinmu,duk da bamu san makarantar kwana ba amma kuma muna jin labarin wuyarta. Saidai duk da haka abinka da yaro mai son tafiyah makarantar kwana,munason zuwa. Baba shehune ya kaimu har makarantar da kansa,tundaga bakin ƙofar makarantar muke ƙaremata kallo,finally yau gamu a makarantar kwana zamu shiga cikinta,waiwayawa nayi na kalli khairyyah,itama niɗin take kallo tana dariyah. Office ɗin principle ya shige damu tareda kayanmu,muna zaune suka gama magana da malaman,aka bashi wasu takardu,yasaka hannu da sauransu,mudai namu idone kawai. Bayan sun gamane aka aika a ƙirah Juwairah usman,daga baya kuma mai aiken tadawo wai bata nan suna paper. "Toh kuna son makarantar kwana gashinan na kawoku,sai ku dage kuyi karatu,dan kun fi kowa sanin shine gatanku a yanzu. Yayartaku tana ɗakin jarabawa,idan ta fito zata zo ta ɗaukeku ku jirata a nan,ni zan tafi sai nazo muku visit. Kuka khariyyah tafara tana ƙiran inno,tsayawa yayi yana kallonta tareda rarrashinta,amma ganin zata bata masa lokaci yafa yi mata faɗa. "Jimin sakaliyar yarinyah,idan bazaki zauna a makarantar ba kizo mu tafi toh,duk uwarku ce ta lalata ku" Gani ya balbaleta da masifa tayi gum da bakinta,dariyah nayi ƙasa ƙasa. Haba dama khairiyyah ta iyah sakalci da kuka,inba hakan yayi mata ba bazatayi shuru ba. Sai can wajen ƙarfe huɗu anty juwairah ta fito daga paper,duk da muna son zuwa wajenta amma munsan kwanannan zata tafi ta barmu mu kaɗai. Da gudu ta taho inda muke tana ware mana hannu,muma da sauri muka tashi muka tareta muna dariyah. Rungumemu tayi dukkanmu, "Iyeee yaran inno sun girma sun shigo makaranta,ina sauran to naga ku kaɗai" Tafaɗa tana dudduba bayan mu. Murnar da muke muka daina muna wawwara idanuwa,dan bamu sam ma mai zamuce mata ba,raahin daɗi kam dole tajishi. "Uhm.....anty juwairah dd..dama wasu sun ɗauki maryam da kuma khamriyyah,wancan watan" Sakin mu tayi tareda yin jimm,idonta ne yayi ƙwal ƙwal kaman mai shirij kuka,sai kuma tayi saurin kawar dashi tareda jan hannuwanmu. "Ssshikenan kuzo mutafi ku huta kafin gobe ku tafi aji koh?" Bin bayan ta mukayi tana tafiyah,shuru babu wanda yace komai,kowa da abinda yake saƙawa a ransa har muka isa hostel ɗinsu. Shiiya mana kayanmu tayi a kwanar ta,tareda kaimana ruwan wanka da kuma abinci. Ƴan riguna ta fitar mana a kayan muka saka da daddare,anata hira tana nuna mu ga ƙawayenta,cewar ga ƙannenta sun zo. "Hmmm naji kunyi shuru baku bani labarin abinda ya faru ba,ina bakin surutun koh ya mutu kai?" Dariyah nayi tarede 'boye fuskata,tunda muka zo kam mun kasa cewa komai. Labarin abinda ya faru na bata,tareda sanar mata yanda za'a tafi da khairiyyah amma khamriyyah tace ita ta yarda a tafi da ita "Inno tayi ƙoƙarin cewa ta zauna,amma taƙi amincewa,a cewarta bazata juri rabamu da inda muka tashi ba,sannan bataso a rabani da ƴar uwata,itace ya kamata ta tafi ba muba" Dafa ni anty juwairah tayi idonta ya kawo ƙwallah tacd "Allah sarki maryam,kusan ni nayi rainonta,yarinya ce mai hankali sosai,ina addu'ar allah yasa ta samu gidan kirki dazasu riƙeta da amana. Khamriyyah kuma nakasa cewa komai,yarinyar tasha wahala a rayuwarta da take buƙatar wanda zasu tallafeta,duk da ita mutumce da bata nuna wahalarta,burinta kullum ta 'boye tace babu komai,saidai ma ta tallafeka. Duk da ɗaukar mutum a gidanmu kamata yayi a masa murna idan yasamu gidan kwanciyar hankali,saidai har cikin raina ina fatan khamriyya ta dawo garemu,amma kuma ina mata fatan allah yabata farin ciki,allah yasa su inganta rayuwarta ta manta da abinda yafaru da rayuwarta a baya" Sake rungumo mu tayi muna ƙara yin kukan rashin ƴan uwannamu. Hankalinmu kwance muke rayuwa da anty juwairan,babu wanda yake dukanmu ko kuma saka mu aiki,saboda muna ƙannen ta,rayuwar daɗi sosai. Satinmu biyu da zuwa ita kuma anty juwairah ta gama makarantar,bayan an ga jarabawa anyi bikin candy da komai. Sabon kuka muka kafa lokacin dazzata bar makarantar,khairiyya kam ma cewa tayi zata bita su koma gida,saida taga dole sai ta zauna kafin ta haƙura. Tun a daren muka fara ganin sanji a makarantar,ashe dama sauran ɗaliban da su anty juwairah suke ƙasansu haushin mu suke ji sosai. Kasancewar kowane ɗalibi yana punishment mu bama yi,da daddare muna kwance sai jin zubar ruwa nayi akaina mai shegen sanyi,zaburah nayi na tashi tareda sauƙe ajiyar zuciyah,wanda ashe itama khairyyah haka tayi. Wata bufurwace zata kai anty juwairah a haife da bulala a hannunta. "Hhhhh wato ku ga ƙannen sister juwairah koh,kowanne yaro zayyi aiki amma ku kuna zaune,dan ubanku wa kuka fi a makarantar nan" "Kiyi haƙuri" shine abinda na samu damar faɗa. "Haƙuri,naibishi da gudu ba wando,ƴam bantan ƙaniyah,ke Lawisah kwantar minsu yanzunnan,kowacce sai na yi mata bulala sha biyu,sannan kuma idan ku dawo daga aiki gobe akwai wankina yana nan zakuyimin shi" Duk haƙuri damuke bata haka tayi biriss damu aka kwantar mu kaman yanda ta umarta. Bulalar take ɗagawa tana zambaɗa mana muna ihu,bata daina ba har saida tayi mana adadin yanda tace tukunna. Fita sukayi daga ɗakin bayan sun gama zagemu tass,yaran dasuke ɗakin babu wanda yayi tari,duk da idonsu biyu sunga mai ya faru,saidai babu mai ikon cewa komai. Ajiyar zuciya muka cigaba dayi har bacci yasake ɗaukemu. Da safe da wuri muka tashi,jikin mu yayi tsami saboda dukan da muka sha a wajen sister Lubabatu,da mukaji ashe itace labour ɗin lokacin. Gugu gugu haka mukayi wanka da ruwan sanyi kafin muka saka uniform ɗin mu zuwa aji. Bayan mun taso kuwa hostel ɗin sister lubabatu muka wuce,yin wankin datace zamuyi jiya da daddare,haka babu imani tasaka mu kneeldown a rana na kusan awa guda kafin ya bamu wankin. Lokacin babu ruwa a makaranta ya ƙare,haka muka yi tafiyah mai nisa a inda aka kwatanta mana kafin muka samo muka wanke mata,duk jikinmu a tsorace yake karmu sake wani laifin. Lallai lokacin da anty juwairah take nan ba'a makarantar kwana muke ba sai yanxu tukunna. Watan mu guda babu itah har mun saba da duk wata wahala da ake gallazamana,mun bi sahun yaran wajen muma. Kwannan baba shehu yazo mana visit,ji mukayi kaman mu bishi gida muce mun fasa karstun,amma babu halin yin hakan,tunda muka fara toh dole sai mun ƙare. Sannan kaman yanda kowanne yara suke jurewa muma dole mu jure mu saba da hakan. Lokacin da mukayi hutun zango na farko murna kaman zata kashemu zamuje muga gida,kowa ranar kasa bacci yayi ana gobe hutu. Kaman yanda baba shehu ya faɗa mana kuwa ƙarfe sha biyu tayi masa a makarantar mu,kasancewar dole sai ya taho daga garinmu zuwa cikin katsinan,mudai sunan muna cikin birni,amma bama zuwa bakin get sai ranar dazamu bar makarantar zuwa gida. Tundaga mota da muka tsayah khairiyya bata tsayaba tayi cikin gidan da gudu tana ƙiran inno,nice ma nayi ɗan dauriyar ɗaukar jakata.. Ganin khairiyyah ta ɗale inno nikuma na ɗale anty juwairah wacce itama taji muryar khairiyyah ta fito. Dariyah aka dungayi tareda bada labarin yaushe gamo,inno ce ta katsemu ganin labarin bazai ƙare ba, "Kunga ya isa haka,muje kucire kaya kuci abinci ku huta tukunna,kafin koma menene sai ku faɗa" Wayyo gida daɗi rahama,kowa yabar gida gida ya barshi kam,can ayita dukanmu ana samu aiki,nan kuma yimana komai za'ayi. Result ɗinmu muka fitar daga jakar,tun kafin na gama cirewa naji anty juwairah ta fizgeshi daga hannuna,tana dariyah. Kallona tayi tareda dagani sama lokacin data nawa naci. Nice nayi na biyar 5,khairiyyah kuma tayi na bakwai 7. Saidai tafini cin math da computer,don ranta yana son subject ɗin sosai. Murna inno tayi sosai itada sauran iyayen mu ganin mun maida hankali mun dage sosai a karatun. Toh fah da hutu ya ƙare aka ce mana wani satin komawa duk sai muyi wani iri,dan shi deen har ya koma jiyah,shikam dai to ba ƙoƙari gaskiya,dan na kusan hamsin yayi a cikin su sittin. Haushi maman yara taji sosai,dan har dukansa tayi. Haka babu yanda mukayi muka tattara muka koma aka cigaba da gashi. _bayan shekara uku_ Abubuwa da dama sun faru,ciki harda jssce da muka zana,yau muke shirin tafiyah gida yin hutun wata uku. Yanzu mun saba da makarantar sosai,munyi ƙawaye sannan munyi suna saboda ilimin mu da kuma ƙarewa,da rawar kai komai muna ciki. Suhaila na kalle wacce take haɗa kayanta nace "Sully gobe sai a kama hanyar zariyah kenan" "Ai wannan dolene sabrah,ina zan tsayah,za'aje ayi dogon hutu kafin mu dawo kuma a cigaba daga inda aka tsayah" "Hakane kam allah ya kaimu lokacin da rai da lafiyah" Kaman yanda muka saba shigowa gida koyaushe yau kam bamuyi wanann gudun sosai ba,dan ba laifi an fara girma da kuma hankali,saidai murna kam baza'a rasa yi ba. Leƙawa nayi banga anty juwairah ba,sanann wani daban shima baba shehu ya tura ya ɗaukomu. "Ah inno banga anty juwairah na ina take?" "Hmmm yanzu kuka dawo ku huta tukunna koma menene sai kuji daga baya" Gabana ne yayi rass ya faɗi,mai yake faruwa haka,daga ganin yanayin mutanen gidan kasan ba ƙalau ba kam. Saidai tunda inno tace zamuji daga baya toh bamuda hurumin takurata sai munji a lokacin,duk da kuwa munason jin mai yake faruwan. Wanka na farayi sanann na jona khairiyyah a wajen cin abinci,lakutar abincin nakeyi nakasa ci sosai,zullumi da fargaba gaba ɗayah su suka cika min kirjina. Tashi nayi daga waken cin abincin nasha ruwa tareda zubawa inno ido,ko ban ce komai ba tasan mai muke son ji daga bakinta. Ajiyar zuciya tayi da alamun bataso wannan yazamo abinda zai tarbemu ba bayan dawowar mu,saidai yazama dole mu sani saboda muma ɗaya ne daga cikin ahalin gidan. Ɗaga ido tayi ta sauƙe akaina,dan tasan abinda zata fada zaifi tabani fiyeda khairiyyah. "Sabrah inaso ku kwantar da hankalinku idan kukaji abinda zance,banaso kusaka damuwa aranku tundaga yanzu da ƙuruciyarku. Nasan kunsan wasu sunzo sun tafi da maryam daga garin katsina koh akan zasu riƙeta?........ Dokar gidannan ne dole idan wanda basuda yara ko kuma suna buƙatar riƙe marayu indai sun cika sharuɗai to dole mu miƙa musu ɗan da suka buƙaci ɗauka,wani hankalinmu yana kwanciya da yaayinsa,wanin kuma saidai muyi tayiwa yaron addu'a a sallolinmu kan cewar allah yabashi ikon zama dasu cikin sauƙi. Yanda ta faru da maryam yana ɗaya daga cikin wanda muka yarda dasu sanann hankalinmu ya kwanta damu basu amanar ta. Saidai kash!,abinda kake gani a zahiri bashine yake faruwa a gaske ba. Ashe wanda suka ɗauki maryam ba ma'aurata bane wanda basuda yara,hasalima basu san juna ba aikine ya haɗasu,wanda aka biyasu domin su yishi. Ba ɗaukarta sukayi domin su riƙeta ba,ɗaukarta sukayi domin su sayar da itah ga wasu mutane daban,saidai har yanzu ba'a gano wanda suka sayarwa itaba" Tashi nayi zumbur na miƙe ina kallon inno tareda tariyo abinda ta faɗamin ɗin yanzu,mai take son cewa,sayarwa ƴar uwarmu suka sayar kaman wata akuyah,mai mukayiwa mutane muke ganin wannan ƙalubalen,yanzu rashin iyaye da mukayi laifi ne kenan? Shin mune muka kashe iyayen na mu da kanmu ko kuma muka gudu muna jinjirai?. Yanzu da a gaban iyayenta take shin zasu samu kwarin gwiwar zuwa kawai su ɗauketa dan kawai su sayar ta?.........wannan abin dame zan fasaltashi a cikin raina tukunna,wayema ya siyeta sannan tana ina mai ya sameta,ashema bangama jin labarin ba daga wajen inno. "Inno ya akayi aka gano hakan toh,sannan ina take" Yanayin fuskarta ne ya ƙara sauyawa dataji tambayar danayi mata. "Hmmm ƴar nan ina kuwa take banda gidan ta na gaskiyah inda kowa dolensa sai yaje,tsawon shekara uku da ƙarbarta a wajensu take,tana shika shekara sha biyar suka sayar da itah,bamusan ina bane,saidai jikinta ya nuna tasha azaba sosai kafin a kasheta,sanann da aka duba gawar babu ƙodah ko guda ɗayah a jikinta,wanda hakan yake nuna inaga masu tsafi ne suka kasheta. Antynku ce wata biyu da suka wuce ta gano gawar da'akayi da ɗorawa a facebook ko akwai wanda yasanta?,da gudu tazo ta nuna mana hoton,hajja kam hadda sumanta data gani . A nan ne muka nunawa baba shehu,a ranar suka tafi birnin katsinnan itada shi. Office ɗin ƴan sandan da suka tsinceta suka je,tareda bada labarin yanda suke da itah da kuma yanda aka taho da itah nan. Bincike akayi tayi ganin wanda suka santa sunzo,har aka samu makarantar da take zuwa da kuma gidan mariƙannata. Saidai babu kowa a gidan sun gudu ba'a gansu ba. Duk binciken da'akayi ba'a samosu ba,saidai dayake munada hotonsu lokacin da suka zo nan to sai aka ɗorashi a media koda wanda yagansu,bayan an faɗi lbarin abinda suka aikata. Zancen danake muku an samu labarinsu a garin bauchi,nan da nan kuwa aka kamosu zuwa garin katsinnan bayan an baki da ƴan sandan can. Tun daga lokacin ake ta shari'ah ana bincike akan hakan,wancan satin sunyi zama aka ɗaga shi sai yau. Abinda yafi bada tashin hankali ma ashe ba iyah maryam kaɗai suka sayar ba harda wasu yara guda biyar,kuma dukkansu an samu gawar su babu ƙoda da wasu sassa a jikinsu,lokacin da mukaji labarinnan munyi kuka har mun gaji,musamman idan mutum yaga yanda aka wulaƙanta gawar,dan a binciken an tabbatar ansha kwanciyah da ita babu adadi...... Yanzu dai suna can wajen shari'ar kuma ance a yau za'a rufe case,ɗin muna fatan tunda shaidu sun fito to a hukuntasu hukunci mai tsanani,daidai da abinda suka aikata. Kallon inno nake wadda take shabar kuka tun sanda ta fara bada labarin,saidai ba iyha ita kaɗai take buƙatar rarrashi ba,dukkanmu kowa yanaso,musamamn ma ni da bana iyah yin kuka saidai abin yayi tacin zuciya ta. Wani yawu nasamu na haɗiyah wanda tun ɗazu ya riƙe a maƙwagarona yaƙi wucewa,sai yanzu nasamu ya tafi. Tafiyah nake a hankali ina ƙokartawa dan kada na faɗi har na samu damar zuwa bayan ɗakunan mu inda babu kowa. Zama nayi a wajen tareda tsurawa wani waje ido nagagara ɗaukewa,wanda yake kallona a lokacin zai ɗauka wajen nake kallo,saidai haƙiƙanin gaskiya hankalina yana wani waje daban ne. Na dulmiyah cikin kogin tunanin rayuwar da mukayi da maryam ɗin,da kuma abinda inno tafaɗamin ya faru da itah. Halayenta nake tunowa na shuru da kuma koyaushe cikin murmushi,amma duk da hakan dan rashin imani irin na ɗan adam aka keta mafarkanta,aka keta maraicinta,aka keta darajarta sanann kuma aka keta rayuwarta gaba ɗaya. Fyaɗe,kisan gillah,azabtarwa da kuma cire sassan jikinta,dukka akan ƙaramar yarinya marainiyar Allha?" Wani tafashashshen hawayene ya zubomin mai ɗumin gaske akan kuncina,dan na rasa mai zanyi ma naji sauƙi suyar da kirjina yakemin. Share hawayen nayi ganin hakan babu abinda zai ƙaramin,sai bata lokaci kawai,wanda ta mutu ta riga ta mutu,tana can insha'allah ta dace da gidan ƙarshe,tunda zaluntarta akayi tayi tsawon zamanta dasu. Tashi nayi na fito daga wajen,inda na hango anty juwairah ta shigo gidan itada baba shehu. Ƙarisawa wajensu nayi,duk da zuciyata tana tsoron abinda zanji daga garesu amma kuma inaso najin. Kallon yanayin fuskarta ya tabbatar babu alamar nasara a shari'ar,saidai duk da hakan ban gazaba wajen tambayarta mai yake faruwa. "Ant.....ty... Juwairah meya faru an zartar musu da hukunci" "Uhm sabrah yaushe kuka dawo? Ba haka bane bari muyi sallahr la'asar tukunna kinji" Daga mata kaina nayi tareda nata hanya ta wuce,shikuma baba shehu ya tafi gidansa. Sai a wajen cin abincin dare inno ta tambayi anty juwairah mai yake faruwa,ganin taƙi faɗamusu komai. Kallonmu take da alamar batason faɗa a gabanmu. "Anty juwairah muma muna son jin mai yake faruwa,maryam ƴar uwarmu ce dan allah ki faɗamana mai yake faruwa" "Inno bamu da yanda zamuyi,idna kanada kuɗi to kanada komai,zakayi abinda kaga dama babu wanda zai taka maka birki,marar kuɗi kuwa,ko kisan kai aka masa bashida ikon komai,to ina ga kuma wanda shi ko iyaye bashida bare kuma zancen kuɗi,muna gani ƙiriƙiri shaidu sun nuna Haƙiƙa tabbas gaskiyane ankama su sa sayarda yaran,amma kuma shari'ah ta murɗe aka sakesu tamkar basuyi komai ba........." Kuka ta rusa wanda hakan yasa ta kasa ƙarisa maganar datakeyi. Matsawa kusada itah nayi na riƙeta ina matse nima nawa idon. Jan numfashi tayi kafin ta cigaba da maganar. "Maryam ta tafi,sun kasheta sun tafi a banza,jininta ya zuba an kasa yimata adalci,saboda wanda sukayi sunada ɗaurin gindin manya." Haka tashigaba ta kukanta ta maganganu amma babu wanda yasamu ƙwarin gwiwar hanata a cikinmu. Zaman makoki mukayi iyah mu kaɗai,dan babu wanda ya santa ma bare ya yazo mana gaisuwa. Kowa idan ka ganshi yayi wani iri,anty juwairah kam ma ko magana sosai batayi,ko yaushe tana ɗaki,nasan ba komai yake damunta ba sai yanda tanaji tana gani duk koƙarinta amma aka kasa yimata adalci akan ƙanwarta,saboda batada galihu ita marsiniyace wacce batasan suwaye iyayen ta ba. Bayan wata ɗayah da case ɗin maryam mun fara komawa dadai,saidai addu'a da muke yi mata a kowacce sallah. Tareda fatan allah yasa hutunta kenan. Tiren dayake hannuna na jefar fass a ƙasa ganin wacce take tsaye a gabana. Abaya ce a jikinta baƙa ta yafa mayafin akanta,wanda hakan yaƙara fito da farar fatarta mai kalar golden. Murmushi take yimin da dan karamin bakinta,kana ganin murmushin zaka ɗauka ƴar shekara ashirin ce da wani abu takeyi ba ƴar shekara sha shida ba. Takawa na farayi a hankali zuwa gareta,yayinda zuciyata take jiyemini kar ko mafarki nakeyi zan farka. Faɗawa nayi jikinta da ƙarfi tareda sakin kukan farinciki. "Khamriyyah!!!!" Na fada hankali,itama rungumenj tayi ta baya tareda sakin dariyah mai ɗan ƙarfi "Sabriyyah menene kuma na kukan,na cika alƙawarin dana ɗauka miki na cewa zan dawo ,gashi kuwa na dawo gareku,bakiyi farinciki bane kike kuka?" Sakin ta nayi tareda kai mata dukan wasa ta tare hannuna. "Harma zakice bana farinciki,tambaya ma kike koh" "Meyasa bazan tambaya ba,naganki wani iri kaman bakyason dawowa tah" Ɗan gajeren murmushi nayi kafin nasake kallon ta. "Khamriyyah kinyi kyau kin sanja sosai kaman bakece wannan yarinyar ba" "Eh ke ɗin kece wanann mai shegen tsokanar wacce kullum in anyi faɗa toh da ita ake" "Hmmm to naji, yakamata mu shiga ciki,dan daga gani babu wanda yasan kin shigo gidan koh. "Eh babu wanda ya ganni kece ta farko,ina anty juwairah da kuma khairiyyah" "Suna ciki dukkansu muje ciki" Kallonta nayi tareda cewa "Yaushe zaki tafi toh,kwana nawa zakiyi" "Na tafi ina na dawo kenan ai" Zare ido nayi tareda baza kunnuwana dannajiyo dadai,kuma hakan tasake maimaitamin cewar ta zo kenan. "Ina iyayennaki toh da suka tafi dake,kin dawo kenan kaman yah?" Murmushi tayi tareda cewa "Haka zancen yake nadawo kenan,nagama zaman dasune shiyasa na taho,kiyi haƙuri karki tambayeni ya akayi na taho,kiyi tunanin kawai cewa nace musu zan tafi suka ce toh" ........tohfahhh.......... Taku _sadi-sakhna_ Ƴar mutan jama'are *(¯`*•.¸,¤°´✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿`°¤,¸.•*´¯)* *MABARACIYAH* (mai harshen damo) тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιε. _haƙƙin mallaka_ _*sadi-sakhna*_ (Yar mutan Jama'are) Paid book #400 3131951977 Auwal sadiya First bank Mai turo kati kuma ta wanann number MTN 09035784150 Mutanen niger su tuntubi wanann number +227 97 21 16 15 Naƙara shafin free har zuwa page 20,zuwa lokacin inka shiryah kazo a fara dakai ranar juma'a. _____________________ Assalamualaikum barkan mu da wannan lokaci *ABMAR COLLECTION* ina nan na kawo muku kayana masu kyau da sauki👌🏻 KAMAR SU:- Atamfa, Atamfa Mai golden,💁‍♀️ Lace ,Shadda lace Yadi, Shadda Abayas💥 Kids wear Takalmi, jaka, mayafai💥 Sleeping dress, kananan kaya na gayu🔥kayan kitchen, DA DAI SAURANSU ina Sokoto ina tura kaya ko ina da izinin ubangiji mai son kayana pc ina maraba daku siyan daya ko sari👏🏻domin neman karin bayani sai ku neme ni ta wannan number waya👉08101521252 nagode kwarai da gaske💃💃 17••18 Hmmm kawai nace daga nan muka shiga cikin gidan sashen inno,dan dama ba yau na farajin karna tambayeta ba,dan haka ba abin mamaki bane a wajena. Itama inno da ta kalleta yanda nayi tayi,dan abune kaman sabo a wajenmu a tafi da yaro kuma ya dawo. "Khamriyyah kece kuwa nake gani?" "Eh nice inno,na sameku lafiyah?" "Lafiyah ƙalau ƴar nan,yaya mariƙannaki toh?" "Uhmm ƙalau suke inaga,dan rabona dasu munyi kusan shekara" "To a wajen wa kike tsawon lokacin?" "Ina wani gidane daban,suna da mutunci sun riƙeni sosai" Tana maganar da alama bata son faɗa,wanda hakan yasa itama inno tayi shuru da tambayar tata. Leƙawa take tana neman anty juwairah inaga da khairiyyah. "Sabrah inasu khairiyyah ban gansu ba" Jan hannunta nayi mukayi ƙofar su anty juwairan,ɗakin muka shiga khairyyah tana zaune ita kuma anty juwairah tana kan kujera sunajin littafi na audio. Saurin sake wayar sukayi da ear piece ɗin lokacin da suka ga khamriyyah a bayana. Fitowa tayi suka rungume juna itada anty juwairah,kowa yana dariya tareda mararin sake ganin juna. "Ƴar kanwat dama zan sake ganinki,na ɗauka mun rabu kenan tunda aka tafi dake" "Ahah anty gani na dawo gareku babu sauran tafiyah kuma" Sakinta tayi tasake rungume khairiyyah ma wacce ita ma dariyar take. "Khairiyyah meyasa baki sake girma ba kin wuce sabrah sosai ba,kika barta ta fiki har haka" "Kijimin anty khamriyyah kema ai sabrah tafiki girma duk da kin fita" Kaimata duka khmariyya tayi tana haɗe fuska ita a dole an faɗi gaskiyah,dukkanmu dariyah muka saka,ta dawo za'a cigaba kenan. "Yanda kuke kallona da mamaki kaman idan mutum ya tafi bazai iya dawowa ba ya tafi kenan,ni banga abin mamaki ba,dama fah nace zan dawo. Kenan idan maryam ma ta dawo mamaki zakuyi irin nawa?" Fuskarmu ce tayi saurin sanjawa lokacin data sako sunan maryam a hirar,bayama anty juwairah wacce lokaci daya idonta ya kawo kwallah. Kallon mu take da alamar tambaya cike da son jin abinda yake faruwa,amma kuma bata furtaba da bakinta,dan ita mutum ce da bata son a dameta da tambayoyi,itama kuma tana ƙoƙarin ganin bata dameka sai taji mai yake ranka ba. Matsawa nayi inda take ina jan majina alamar zuciya ta so take na zubar da hawaye,dan ji nayi abin yadawomin ɗanye a cikin raina. "Khamriyyah maryam ta tafi baxata dawo ba,an cutar da itah mu kuma an yaudaremu an maida mu tamkar dabbobi wanda za'a ɗauka sanda ake so sanann kuma a kashe babu abinda za'ayi" Labarin abinda ya faru da maryam na bata tundaga farko har karshe,duk da inayi ina tsayawa saboda yanda abin yake cin raina,anty juwaira kam tuni ta zube a ƙasa tana kuka. "Khamriyyah sunyi abinda suka ga dama,sun kasheta sun jefar da gawarta,tamkar itaɗin batada daraja irin ta ƴan adam,sanann ga shaidu nan sun nuna wanda sukayi aikin amma kuma an sakesu suna yawonsu tamkar basuyi ba,saima aka ce ƙazafi mukayi musu,sai mun biyasu tara,da ƙyar aka ƙyalemu saboda daga gidan marayun gwamnati muke" Tunda nake bata labarin dukkanmu kuka muke,amma ita a tsaye take kaman kungi,ta dunƙuke hannunta tareda cije fatar bakinta,idonta kuwa tamkar garwashi yana ruruwa a cikinsa. Hannunta na kama wanda yake kusada ni amma na gagara buɗeshi ,kallonta nake da alama bata cikin hayyacinta,abinda muka fadane yasaka ta haka kokuma ta tuna wani abu a cikin rayuwarta wanda ya jefata cikin yanayin. Hannuna na saka ina kaɗawa a kan fuskarta amma da alama batasan inayi ba. Jijjigata na farayi dan ta fara bani tsoro, "Ke khamriyyah meya faru dake,kina jina kuwa" Suma anty juwairah ganin hakan yasa suka matso domin ganin mai yake faruwa. Dukkanmu haɗuwa mukayi muna jijjigata amma tamkar dutsi haka jikinta yayi. Sai can kaman wajen minti talatin kafin taja wani zazzafan numfashi mai sauti. Kallon cikin idona take da alama sanann ta dawo cikin hankalinta,ƙiƙƙifta idanuwanta tayi tareda ƙoƙarin mayar da hawayen dayake son fitowa a idonta. Mamakine da tausayinta ya kamani ganin yanda hawayen kuwa yake komawa har yazamo babu ko ɗison hawaye a idonta. A halittar mace da kuka aka santa idan wani abun ya sameta,shikansa na mijima idan abin yayi yawa yakan zama ya zubar da hawaye domin samun salama a zuciyarsa,to ita kuma mai yake damunta da take hukunta kanta ta hanyar hana kanta zubar hawaye. "Khamriyyah lafiyarki kuwa,,naga kaman kin shiga wani yanayi yanzu" Jijjiga kai tayi tareda ƙirƙiro murmushi kana tace "Ahah kawai abinda naji daga bakinkune yasaka ni,amma ita wanda akayiwa ta ƙaremata,ta huta tunda ta koma ga mahaliccinta,babban abinda ya ɗagamin hankalin shine ganin karayar zuciya da kuma ƙunci akan idanuwanku,wanda kuma babu yanda zakuyi ku ɗau fansa domin jin sauƙin hakan. Wanann shine abinda yafi bata min rai fiyeda mutuwar maryam ɗin,sannan kuma su wanda suka aikata suna nan lafiyarsu ƙalau babu abinda ya samesu bayan mu kuma muna nan da tabon abin a cikin ranmu." Hannuna na sakala na rungumota jikina,sai duk naji babu daɗi dana fadamata abinda ya faru. Gani nake kaman laifina ne dana faɗamata,gashi yanzu ta shiga wani yanayi a sanadiyyata. Inno ce ta aiko yarinyah a ƙiramu,hakan yasa muka bar ƙofar zuwa sashennamu. Wow inno ranar ta burgemu,a kajinta datake kiwo da ta yanka mana guda biyu,nasan ma banamu bane na dawowar khamriyyah ne. Da daddare muna zaune ana ci wayar anty juwairah tayi ƙara,kallonmu tayi ta kasa ƙasa kafin ta ɗauki wayar zuwa ɗakinmu. Sigina nayiwa khamriyyah wacce ta ɗagamin gira alamar ƙarin bayani. "Uhm uhm shine fah ,yayannamu ne a makaranta suka haɗu lokacin dayake kaiwa ƙanwarsa,ko kuma idan yaje visit,baki ganshi ba kyakykyawa dashi,mun kusa shan biki kawai" Dariyah khamriyyah tayimin tareda miƙa min hannu muka tafah saiga anty juwairah ta fito,hararar wasa takai mana,inda ganin hakan yasa muka fiske muna dariya ƙasa ƙasa. "Munafurcina kuke koh,to kuyi da gaske yace wani satin zaizo domin su gana da baba shehu,sai ku shiryah" Tsalle na tashi na daka tareda faɗawa kanta muka jube a ƙasa,dukkanmu kowa dariyah yasaka,ita kuwa khairyyah sarkin rawa,tashi tayi tafara takawa ana mata tafi. "Tabbb!! Ai da zazzafan biki a gidannan,dama na anty shamsiyyah bamuda wayo,wannan kuwa ba mai hanamu raƙashewa a bikinnan,koya kika ce khamiriyyah?" "Kika faɗa a hankali,bikin antyn mu ta kanmu,ai event ɗinmu daban zamuyi shi,sai kunkuminmu ya gurmuɗe dan rawa" Khairyyah ce ta faɗa,har sanann bata zauna ba sai tsalle tsalle take,khamriyyah ce ta kalleta tareda cewa "Ana ta zancen biki kina da event ɗin rawa,ke wanann na rasa a ina kika koyo rawa haka" "Hmm ita da su suhaila sukeyi a makaranta,terayen hostel kikeji" Harara tayi tareda tsayawa da rawar. "Kutt rashin mutunci!..nice ma teruwar,ai gwanda ni bana guduwa jeji idan za'ayi aiki,idan an kamani a yimin duka,ko kuma zuwa tsokanar seniour da daddare" Anty juwairah ce ta kalleni jin abinda khairiyyah ta faɗa,da alama buƙatar ƙarin bayani take Ganin haka yasa na tashi na shiga ɗakinmu ina ɗaga musu muryar "saida safe". Har na isa wajen katifata ina jiyo dariyarsu,kuma nasan dani suke ganin na gudu. Wani farincikine ya jiyarceni ganin dukkanin fuskokinsu sun dawo da annashuwarsu,sanann har cikin raina naji daɗi yanda anty juwairah ta samu mijin dazai aureta,mai sonta sanann mai ƙaunarta,koba komai zata bar wanann gidan bayan tsawon lokacin data ɗauka a ciki. Dan duk cikin yaran da'ake riƙewa tafi kowa daɗewa a wannan gidan,sannan bawai halinta ne ya hanata rashin miji da wuri ba ,saidai ƙaddara,shiyasa mukafi yin murna data ce mana zaizo yaga iyayenta. Cikin magagin bacci naji shigowar su khamriyyah suma suka kwanta,sannan kenan suka tashi a hirar. Idan aka ce kaddara to abune da yariga fata,duk yanda kakai ga son tsallakeshi to bazai taba tsallakuwa ba dole sai ya sameka,kuma dama hausawa suna cewa "kana naka allah ma yanasa" Mungama dariyah da hira mai daɗi mun kwanta,bamu san ƙarewar kwanciyar hankalinmu kenan,sanann kuma faruwar ƙaddarar shigarmu cikin aikin da bamuyi mafarkin shigarsa ba kenan,daren ranar shine farkon komai sannan darene da bazan taba manta shi ba a tarihin rayuwata,darene daya kafa tarihi a birinin zuƙatanmu wanda yazame mana tabo abin tunawa a koda yaushe. Cikin daren gari yayi tsitt kowane bawa yana kwance domin samun hutu,bakajin komai sai ƙarar halittun da sukuma sanann suka fito domin samun abinda allah ya horemusu,ƙarar bugowar ƙofar mu ta kuma muryar namiji ne ta sani firgit na tashi tareda jan hijabina a gefe na saka. Bakina ba abinda yake ambato sai innalillahi wa inna ilaihi raji'un,mai yafaru kuma barayi suka shigo mana gida,mudai bamuda abin duniyah bare suce shi suka zo suka ɗauka. Tsawa ya dakamana wanda hakan yada mukayi firgigit kowa ta tashi daga kan katifar tata. Waje suka tunkuɗomu muka fito,dayake akwai nepa tarau tsaƙar gidan yake da haske,kallon mutanen gidan mukayi sahu sahu kowa ya jikinsa rawa yakeyi,dan bai san mai zai faru ba. Muma sahun layin muka bi inda mukaga wani a tsakiyah yana zaune,gefensa kuma anty juwairah ce a tsugunne tana kakkarwa,to mai ya haɗasu da itah kuma da zai jata kusada shi? Sauran mutanen gidan aka fitar dukka,kowa sai kuka yake,du inno kam suna rungume da ƙananan yaran wanda suke ta kuka,an tasosu tsakar dare. Tsawa ya daga mana tareda nuna mana bindiga,wanda hakan yasa kowa yayi tsit kaman ruwa ya cinyeshi. Sanye suke dukkansu da baƙaƙen kaya sannan kuma da yasaka baƙar fuska. Kama gashin anty juwairah yayi ya ɗagata lokacin dazai miƙe,yanayi yana kallon duk mutanen dasuke kewaye a wajen. "Haha wato ke ga wata shegiya koh,da kikaga gawar ƙanwarki maimaikon ki ɗauketa kawai ki yi tafiyarki kaman sauran mutanen sai kika fara bin diddigi keda wanann tsohon koh,miye dan anyiwa yarinyar fyaɗe an cire kodarta,shikenan dan anyimata fyaɗe takasa jurewa ta mutu sai mubar ƙodar a banza bazamu siyar ba,mezakiyi akai dan an kasheta,kina marainiyah wacce aka ɗuri ciki aka haifeta aka jefar da itah,menene amfaninku banda aji daɗi ma daku a sayar daku ɗin. Dukkan ku ganinku nake kaman bayi a gaban sarki lokacin zamanin jahiliyyah,kuba komai bane,yanzu zamu nuna muku kuba komai ɗin bane ma. Cire hular kansa yayi bayan ya jefar da anty juwairah a ƙasa,sai kuka take kaman ranta zai fita,amma hakan bai sakashi ko kallonta da idon tausayi ba bare imani. "Ku kalleni sunana Saifuddeen El bashir,ɗan gidan minister El bashir na garin katsina,a tunanin ku nasaka fuska ne dan ina tsoron ku ganni,baku kai hakan ba,ko karnuka na baku kai ba. Tunda nake kasuwanci na masu kawomin kaya basu taba samun matsala ba bareni sai akanku,wato kowa anyi masa yayi shuru kuga tsagera koh harda kaiwa ƙara kotu. Duk faɗin ƙasar nan babu wani wanda ya isa ya ƙarbi kukanku,domin duk wanda zaku kaiwa kukan tare muke dashi,hmmm hadda ɗaukar lawyer,wai kuma hakanma barister bashir" Maida idona nayi kan khamriyyah jin yadda ta damƙe hannuna jin sunan daya ambata,dama yanayinta kam a lokacin ban ma yi tunanin dubawa ba. Komawa yayi inda anty juwairah take kwance kafin ya ɗora da cewar. "Kinyi kuskure yarinyah da kika shigamin hanci,babu wanda ya taba abinda kikayi,idan na barki wasu zasu sakeyi dan haka dole na hukuntaki,badan anyi mata fyaɗene kika tashi hankalinki ba kega mai kishi,to barinayi miki ke naga shin mutuwa zakiyi ko kuma duk ƙaryace abin" Ihu dukkanmu muka saka jin abinda ya faɗa,hajjah kam ganin yana ƙoƙarin cire rigar jikin anty juwairah tayi kukan kura tareda yin kansa ta riƙe rigarsa da ƙarfi. Jefarta yayi gefe ta faɗi tareda sake kama anty juwairan. Muma ƙoƙarin zuwa wajen muka farayi domin hanashi,amma sai yarannasa suka hanamu,sai ya zamo duk wanda yayi motsi a cikin saidai yaji duka ta ko ina. Rigarta yacire ya jefar tareda sake yaga wandon jikinta ma na bacci. Kuka take tana kaimasa duka da yaguni amma tamkar tana yiwa dutsi ko a jikinsa, Ganin da gaske ya saita shirin yimata fyaɗenne yasa dukkanmu muka juya bayan mu,yara ma aka kuyar dasu tareda rufe idonsu da kunnuwansu.. Wata ƙara anty juwairah tasaki mai ƙarfin gaske lokacin da mutumin ya keta darajarta da kuma martabarta na ƴa mace.Abinda tsawon shekaru ta ɗauka tana karewa shiya karbe a lokaci ɗayah batareda amincewarta,yayi mata abinda ko dabba bazata juraba. Duk abinda ya faru akan idon hajjah wacce ta faɗi lokacin datayi ƙoƙarin hanashi. Akan idonta ya ketawa ƴar tata darajarta,abinda tayi ta ƙoƙarin itama karemata tana yarinyah,har yazamo tayi hankali tana kulada abinda,shiyasa yasaka gabansa mai ƙazanta mai zunubi yaketa batareda imani ba. Tunda anty juwairah tasaki wanann ihun naji wani abu mai tsiini yasokeni a cikin raina,na tabbatar suma sauran wanda suke tareda ni sunji haka aransu. Dan abin ya wuce mutum yayi kuka ma. Tashi yayi daga inda anty juwairan take kwance ko motsi batayi,. Wani lashe baki yayi tareda zuge ziff ɗin wandonsa. "Kai amma fah kinada zaƙi sosai,gaskiyah dole na yaba miki,gaki kuwa budurwa zam zam,nagode fah da wanann kyautar" A juciye hajjah ta miƙe daga kwancen ta dake ta kalleshi,idonta babu komai a cikinsa sai tsagwaron bacin rai. Kai tsinannane la'annanan allah,ko kafiri sai ya fika ganin rahamar Allah,ka ketawa ƴata budurcinta a gaban idona,wuta ce inda zaka shiga tsinannane kawai" Hakan bai isheta ba taje ta kama wuyansa tareda jijjigashi,kai kana ganin haka kasan babu tsoro a ranta,abinda takeji ya wuce gaban tsoro. "Ka kasheni kasheni da da wannan aika aikar dakayi mana,kuma inshaallah sai kaga yanda rayuwarka zata ƙare" Kamata yayi tareda shaƙe wuyanta,kakarin rashin numfashi tafarayi abinka da tsufah amma bai saketa ba har jikinta yah shika kafin ya jefar da itah a wajen. Kallonsu yayi a kwance ƴa da uwar,da wacce yayiwa fyaɗe sanann kuma da wacce ya kashe,kowaccensu ya tsayar da mafarkinta da kuma bugun zuciyarta,gwanda wacce ta mutuma ta yanke rayuwar duniyah amma wacce akayiwa fyaɗe taya za'a tsammaci wani cigaba a rayuwarta. Tsallekesu yayi ya wuce bayan yayi musu kallon karshe,suma yarannasa bin bayan sa sukayi suna wani huhhura hanci. Abinda akayi mana abune nayin kuka da kuma alhini,saidai kaff cikinmu babu wanda ya samu damar yin kukan,saima zubewa da mukayi a wajen mun tsira musu idon kawai. Khamriyyah ce duk cikinmu ta tashi tareda ɗaukar rigar anty juwairah a inda mutumin ya jefar mata. Isa tayi gareta tareda rufemata kirjinta,hijabinta ta sake cirowa tasaka mata lokacin data miƙe daga kwancen datake. Duk abinda khamriyyan take mata bata lura ba,hankalinta yana kan hajja uwa a gareta wacce ta rasa ranta sanadiyyar ƙoƙarin karemata mutuncinta,amma batayi nasara ba saima rasa ranta,yayinda shikuma yayi abinda yai niyyah kuma ya tafi hankali kawance,kaman yanda ya faɗa kuwa duk inda zasu kai kukansu babu wanda zai jisu. "Anty juwairah tashi mushiga ciki,bazan iya rarrashinki ba amma kuma kina buƙatar barin wajennan yanxu" Yarda tayi da zancen khamriyyan ta tashi da ƙyar tana runtse ido,dan baƙaramin rauni yayi mata ba, da saninsa. Hanyar sashennasu suka nufah,mukuma muka tattara yaran domin shiga dasu,yayinda su inno kuma suka matsa domin kulada gawar hajjan. Wanann daren haka ya waye mana baƙiƙƙirin,duk da safiyah tayi rana da fito amma garemu baƙine siɗik tamkar ƙarfe shabiyu. Tun sassafe mutane aka fara shigowa gidan,wasu na kuka wasu kuma na ajjabi. Anan ne labari yazo ashe sunje gidan baba shehu ma sunyi masa aika aika,yanzu haka an tafi dashi asibitin garin katsina a daren,shida iyalansa gabaɗayah,zai rayu ko bazai rayu ba allah ne kaɗai masani. Tashin hankali goma da ishirin haka muka afka cikin sa a wanann lokacin,ga jana'iazar marigayiya hajja da akayi ga kuma abinda yafaru da antyn juwairah,tun lokacin da khamriyyah tajata suka shiga ɗakinta har yanzu yau kwana uku kenan amma bata fito ba,iyakacinta taje banɗaki ta dawo,ƙawayaenta ma har sukazo gaisuwa suka tafi basu ganta ba,saidai dole a samu wani abu a fada musu,wasu kuma sun ɗauka zafin mutuwane yasaka ta cikin halin data ke ciki. A ranar da'akayi sadakar uku kowa ya kama gabansa,aka bar iyamu da alhinin rashinta kawai. A zaune nake nifa khamriyya a bayan gidan munyi shuru babu wanda yakewa wani magana,dan rabonmu dayin magana a tsakanin mu tun lokacin da akayi hira gabannin wanann mummunan daren ya afku. Kallonta nayi ganin yanda ta tsirawa wani waje ido ko ƙiftawa da kyau batayi sosai,komai take tunani allan ne kaɗai masani,tsorona ɗaya karta sake faɗawa cikin halin data shiga lokacin da taji labarin maryam. Jijjigata nayi a hankali kaman mai tsoron daba jikinta,bata kalleni ba amma da alama taji tabatan danayi. "Kina tsoron ko bana jin kine sabrah,ina cikin hankalinna,kawai abinne hankalinnawa yakasa gasgatashi har yanzu,wai an kashe hajjah kuma .........kuma wai abin takaicin ma an ketawa antyn mu guda ɗayah damuke da itah ta rage mana,wacce zamu garera mukai kukanmu ta amsheshi hannu biyu,yau itace aka ketawa mafarki da komai nata a gabanmu amma muka kasa yin komai akai sabrah,wannan abin yafi komai tada min hankali,idan na zauna ban ɗau fansaba nima zan iya rasa raina sanadiyyar haka" Sharrr idona yake zubar da hawaye lokacin da maganganunnata suke dukan dodon kunnena,na rasa mai zance akan lamarin. "Babu yanda zamuyi khamriyyah haƙuri zamuyi sanann mu tuna jarabawa ce wacce tana kan kowa da kowa,yanzu dai muje wajenta muga wane hali take ciki,dan abu yakusa sati guda amma babu wanda ya take,taƙi yarda ta nuna fuskarta bare a ga yanayinta,ni ina tunanin tana buƙatar mu kusada itah yanda zamu ɗauke mata kewa sanann kuma muji matsalarta" Tashi khamriyyah tayi bata ce komai ba muka nufi sashen mu ,dam inno ta ɗaukota daga can tunda babu kowa,sannan dole sai ana saka mata ido kartayi ƙoƙarin yin wani abu dazai ta'ba lafiyarta. Shiga mukayi ɗakin datake a hankali kaman masu tsoron kada taji shigowarmu,a zaune take a tsakiyar gadon inno ta saka kanta a tsakanin cinyoyinta,dan fuskarta ma bata ɗagota saidai idan wani abu zatayi. Zama mukayi akan gadon tareda tsura mata,mun kasa cewa komai. Cikin raunanniyar muryah mukaji tana magana,da alama ta kulada shigowarmu wajen. "Khamriyyah......nasan kune kuka zo,badan komai ba saidan kun damu da wane hali nake ciki,kkk....karku damu kunji,bazanyi wani abun dazai ƙara tada hankalinku ba bayan wanda ya tashi a baya,ina lafiya ku kwantar da hankalinku ku cigaba da rayuwarku kaman yanda kuka saba,abinda ya sameni kada ya ta'ba rayuwarku," Kuka na fashe dashi mai ƙarfi,dan gaskiya nagama iya ƙoƙarina wajen riƙe kukan,rarrafawa nayi har inda take na rugumeta tareda ƙara sautin kukana,nikam bazan iya jurewa ba. "Anty........dan allah ki daina wanann zaman,wlh zai iya ta'ba lafiyarki,kisani abinda yafaru dake ba iyah ke kaɗai ya shafa ba harda mu,zamanki a nan wajen kuma ƙara saka damuwa zayyi a zuƙatanmu,dan allah badan muba saidan allah dayafikowa sonki kuma shine ya jarrabeki dan yaga ƙafin imaninki,ki taimakemu ki dawo yanda kike da,kinji antynah" Ɗago da fusakarta tayi wacce ta kumburah suntum,idanuwanta da ƙyar ake kallonsu,gashi sunyi jawur kaman gautah,kwata kwata da sanja kamanni kaman ba itaba. Zaburah nayi tareda matsawa baya ina ƙarewa fuskarta ta kallo,dama haka fuskarta ta koma shiyasa take 'boyewa bata son kowa yagani. Hannuna nakai kan kumatunta na lotsa shi,saikace ba fuskar mutum ba. "Anty....kkkki..kiga fuskarki kuma a hakan kice lafiyarki kalau babu komai,wanann ne ba komai ba da har zamu iya kwantar da hankalinmu mu cigaba da rayuwarmu kaman ko yaushe?" Wayar tace a gefe tayi ƙara,khamriyyah ce ta ɗauka dayake tana gefenta wayar,ganin sunan Ammar saurayin anty juwaira yasa ta miƙamata wayar. Idonta ta sauƙe akan sunan tareda jijjigawa alamar bazata ɗauka ba. Khamriyyah batayi wata wata ba ta dannan amsa ƙiran tareda karawa a kunnenta. Sallama tafara yimasa tareda cewa mai wayar bata kusa. Wani abu ya faɗamata,can sai tace toh,kana ta ajiye wayar tana kallonmu,muma kallonta muke da alamar ta faɗa mai yace. "Anty juwairah ki shiryah yace gobe yana hanyar zuwa garinnan,daga garinsu Ɗan-musa. Kafin zuwansa ya kamata ki bar kukannan ki tunkareshi tareda faɗa masa gaskiyah,inya amince dake ki zana rayuwarki dashi,idam bai amince ba ki fitar dashi daga rayuwarki kana ki cigaba daga inda kika tsayah,wannan zamannaki a nan wajen yana illata ki tareda mu gabaki ɗayah,bazamu juri hakan ba" Tana gama faɗar hakan ta kama hanya tabar ɗakin. Allah ya kaimu goben toh........ Taku _sadi-sakhna_ Ƴar mutan jama'are. *(¯`*•.¸,¤°´✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿`°¤,¸.•*´¯)* *MABARACIYAH* (mai harshen damo) тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιε. _haƙƙin mallaka_ _*sadi-sakhna*_ (Yar mutan Jama'are) Paid book #400 3131951977 Auwal sadiya First bank Mai turo kati kuma ta wanann number MTN 09035784150 Mutanen niger su tuntubi wanann number +227 97 21 16 15 Naƙara shafin free har zuwa page 20,zuwa lokacin inka shiryah kazo a fara dakai ranar juma'a. _____________________ Assalamualaikum barkan mu da wannan lokaci *ABMAR COLLECTION* ina nan na kawo muku kayana masu kyau da sauki👌🏻 KAMAR SU:- Atamfa, Atamfa Mai golden,💁‍♀️ Lace ,Shadda lace Yadi, Shadda Abayas💥 Kids wear Takalmi, jaka, mayafai💥 Sleeping dress, kananan kaya na gayu🔥kayan kitchen, DA DAI SAURANSU ina Sokoto ina tura kaya ko ina da izinin ubangiji mai son kayana pc ina maraba daku siyan daya ko sari👏🏻domin neman karin bayani sai ku neme ni ta wannan number waya👉08101521252 nagode kwarai da gaske💃💃 19••20 Tashi nayi na nufi kitchen inda inno take itada khairiyyah. "Inno yah ammar yace gobe yana kan hanyar zuwa garinnan,wajen anty juwairah shida yayansa,zasuzo gaisuwa sannan kuma da zancen aurenta" Shuru inno tayi tana tunanin,ni kaina nasan tunanin mai take,tana tsoron kar yaji abinda yafarune ya fasa aurenta,hakan yasake karya mata zuciya. "Khamriyyah har ta faɗamasa a wayah cewa yazo" Nan na faɗamata abinda khamriyyah tace na tunkararsa,idan hakan bai yiyu ba shikenan. Na'am tayi da zancen,gwanda taji daga bakinsa akan tayi ta wasiƙar jaki da zullumi. "To shikenan zanyi ƙoƙarin yi mata magana akan hakan,yakamata tadaina wanann saka damuwar kam a ranta,abinda ya faru ya riga ya faru,tunashi da sakashi a rai ba komai zai haifarba sai damuwa" "Yawwa mun gode inno,yanzu barina faɗawa khamriyyah to mu share office ɗin baba shehu" Saida na faɗa ma na tuna ashe baba shehu wanda yake tamkar uba a garemu,komai namu yakan ƙoƙarin tsayawa,ashe sun lahantashi yana asibiti,gashi iyalansa sunce bazasu dawo ba,garinsu zasu tafi,karsu dawo azo a kasheshi gabaɗayah. "Uhmm inno yanzu waye zai zama shugaban wajennamu toh?" "Allah zai kawo sabrah,nasan bazasu bar wajen haka na,ni inaga abinda yafi a tsaya da ƙarbar yara,duk wanda aka kawo a turashi babban gidan marayu dayake katsina,nan gun babu tsaro sosai,musamman muna riƙe da yara mata,ganin wani yazo yayi abinda yaga dama ba abinda aka masa,wani ma ina tsoron yazo yasake mana rashin mutunci" Duk maganar tanayine cikin damuwa sosai. Saida muka saka anty juwairah a gaba kafin ta yi wanka ta shiryah,gashi sai janta muke da hira domin ta saki jikinta,dui bata kulamu ba amma fusakarta ta ɗan saki bakaman jiyaba. Lace ta saka ruwan kwai da kuma hijabi coppea lokacin da akace sun zo suna zaure. Zama tayi akan kujera tayi tagumi tana jiran su gama cin abinci. Kallonta muke mu sakata a gaba, "Anty juwairah in bazaki iyah zuwa ke kaɗai ba khamriyyah ta rakaki mana,nasan zaki ɗan fijin ƙwarin gwiwa" "Uhm inaga ta rakanin,bazan iya cewa komai ba koda naje,abinda nake tunani kenan" Shuru khamriyyah tayi dana kallleta,da alama batason zuwan,amma kuma ba ƙi amincewa ba. Tashi tayi tabi bayan anty juwairan suka nufi zauren,har sunzo shiga na kama hannunta khamriyyah tareda ɗaga mata hannun,ita ta gane abinda muke nufi,dan haka ta ɗagamin kai tashiga wajen ni kuma na koma cikin gida. Cikin sanyin jiki suka shiga wajen,su biyune suna zaune kulolin abincin kuma na gefensu,da alama sanann suka gama cin abincin. Khamriyyah ce tafara gaishesu kafin ta koma can gefe ta zauna domin basu waje. Shikuwa yayannasa yana ganin mun shigo bayan mungaisheshi yabara cikin office ɗin. Kaɗan daga inda suke khamriyyah takejin maganarsu,duk da bazatace ga abinda suke faɗa ba,amma kuma daga gani bayani tafarayi masa ta kasa ƙarisawa,shikuma yana son jin ƙarshen labarin ya takura mata data bashi amsa. Kukan data saki ne yasa khamriyyah ƙarisawa inda suke,maganarsa ce ta harzuƙata dan dama a kusa take. "Mai naji kina cewa,kina nufin kicemin wani abu ya faru keba budurwa bace,tukunna ma yakike son na ƙarbi zancen,so kike na yarda dake......." "Ahah ba buƙatarta dole saika yarda ba,da saika yarda take buƙata da bazata fara faɗamaka ba,saboda batason gina rayuwarta da kai akan ƙaryah shiyasa ta buƙacin kasan abinda yake faruwa. Abinda ya faru da ita ba lafinta bane ba laifinmu bane ko kuma laifinka ,allah ne ya zana hakan cikin rayuwarta,bakuma dan baya sonta ba sai dan ya jarabata,kaikanka kasan anty juwairah ba ƴar iska bace,a.......a gabanmu aka yi mata abinda kowacce mace take ƙyamarsa a rayuwartah,taji labarinsa ma bare a ce a kanta ne abin ya faru. Dan haka karkayi amfani da abinda ta faɗamaka kaci mutuncinta bayan wanda aka ketamata,bazamu juri ganin hakan ba sam. Yanzu ta riga ta faɗamaka abinda ya faru zabi yana hannuka,tuwanka ka tallafi rayuwarta ka rufa mata asiri ka kuma taimaki maraicinta. Ko kuma ganin koda kun zauna bazaka juri tuna abinda ya faru da itaba,toh domin soyayyar dakake mata yakamata ka fita a rayuwarta taji da wanda take ciki ma yanzu" Ƙarisa maganar khamriyyah tayi tarefa ɗunƙule hannun ta tana roƙonsa. Leƙawa yayi suka haɗa ido da anty juwairah wacce khamriyyah tasha gabansu ta tareta. Kana ganin shima yanda sau ajiyar zuciyah kasan jikinsa yayi sanyi da abinda ya faru. "Naji duk abinda kika faɗa ƙanwata,kuma abinda kika ce gaskiyane,amma zaki ɗan iyah bani wasu mintuna nayi magana da itah" Janye jikinta tayi daga tsakanin su tareda fita bakin office ɗin,batajin abinda suke faɗa amma kuma tana kallonsu,dan yi tai kaman uwa mai kulada ɗanta lokacin dayake a cikin halin jinyah,bata ƙaunar wani abu ya sake raunanata bayan wanda aka mata koda kuwa masoyinnata ne. Basuyi minti biyar ba da basu lokacin saiga anty juwairan tafito,fuskarta babu yabo babu fallasa. Tunda suka tafi har dare yayi aka wanye lafiyah babu wanda yace ma anty ƙala a cikimu,ganin yanda jikinta yaɗan saki ta fara dawowa daidai ma ya ishemu,mai yiyuwa haɗuwar da sukayi da ya ammar ɗin ya rage mata wani abun daga raɗaɗin datake ciki. Watanni sunja kaman misali guda uku bayan afkuwar lamarin,abubuwa da dama sun dan sanja,ciki harda komawar mu makarantar day,wacce muka shiga ta gwamnati a kusada anguwar tamu. Wanda ya tsayamana baba shehu iyalansa sun dage akan bazai dawo garin ba,saidai inya zaba kowaje ko su. Ta wani wajen banga lafinsu sosai ba,saboda shine tamkar bongo a garesu,idan aka ce ana barazana da ransa to hankalinsu bazai kwanta ba. Shikuma mataimakinnsa shida lusari ɗayah suke,saboda sai yayi sati ma bai leƙo inda muke ba,dan haka saboda iyayenmu ga kuma anty juwairah da tana buƙatarmu kusada ita sai muka yanke shawarar shiga makaranta a gida kawai. A ss2 aka ɗaukemu a makarantar,wannan shawarar khamriyyah ce wanda bamusan dalilinta ba,sanann dukkan mu ta bamu zabi akan wasu abubuwa kowa ya zabi inda yafi ƙwarewa,lokacin da mukaji abinda tazo mana dashi munyi matuƙar mamaki. Saidai kuma hakan baisa ta sanja ra'ayinta ba, "Mai kike faɗane khamriyyah,kowa ya zabi abinda yakeso akan mai toh?" "Kinada gaggawa ƴar uwata,idan kika tsayah zakiji mai zan zayyana,abubuwan sunada yawa saidai kuma ga wasu daga cikinsu ,na farko akwai Likitanci,Badda kama,Kutsen na'urah, Ƙwarewa a soyayya,Salon kamanni kala kala,Training na juriyah akan komai,Salon faɗa na wayo,Sumame,Koyon taurin zuciyah,ƙwarewa wajen tuka abin hawa. Kaman yanda na faɗamuku sunada yawa,inason a cikin ku biyu kowa ta ɗau wanda takeso nagani" "Me kike faɗane khamriyyah kanki ɗayah kuwa" "Kaina ɗayah kawai wani wasa ne,karki damu zamuga wazai ƙwarene idan kuka ɗauka" Saurin ɗaga hannu khairyyah tayi tareda cewa "Na ɗau kutsen na'urah idan wasane,dan gaskiyah inason wajen sosai" Murmushi nayi ganin ashe wasane ta haɗa, "Uhm ni naɗau fannin sace zuciyar mutum,dan fannin wajen zai bada citta shida badda kama" "Da kyau toh ni kuma na ɗau sauran dukka,wasane amma kuma zai farane a yau ba kuma zai ƙare a yau ɗin ba,kowa zaije yayi iya ƙoƙarinsa wajen ƙwarewa a fannin daya ɗauka,lokacin da muka gama secondry idan da rai kowa sai a ga mai yasamu akan wajen,karku manta sirrine,kayi ƙoƙarin sanin naka domin ɗayah kada ya fika,na ɗauki sauran kafin a samu wanda zasu ɗauka" "Wow abin yayi amma inaga ki saka deen a ciki,dannasan zayyi" Na faɗa tareda yin dariyah,zanso idan ƙarshen wasan yayi naga mai game over,nikuwa duk yanda zanyi saina ƙware a jawo hankalin wani,sannan kuma da badda kama kaman yanda na ambata. Wasa wasa abu har yayi girma,dan kowa ta dage wajen ganin nan da lokacin da aka saka karawar wasan to ta ƙware sosai. Da zuciyar mu ɗayah cikin sigar wasa muka amshi abinda khamriyyah tazo mana dashi,sannan ko yaushe muna cikin yin training ɗin kare kai daga mai kawo farmaki,wanann bamu kawo komai ba,sai muka ɗaukeshi a matsayin dan abinda ya faru da mune a ranar da akayiwa anty juwairah fyaɗe,suma su inno basu hanamu neman yanda zamu kare kanmu ba. Idan muka dawo daga makarantar safe,khariyyah tana tafiyah wajen masu computer ne domin koyah,nikuwa ko yaushe inabin diddgin labaran jawo hankali da kuma na wasu abubuwan daban. Abinda yafi bani mamaki da khamriyyah shine,wani lokacin daga munje makaranta take ficewa,idan nabita na tambayeta saitace zata faɗamin,kuma abin mamaki tana riƙe duk wani abu da'akayi a aji koda kuwa bata nan akayi. Tun muna na marmari saikuma abin yadawo fara bani tsoro,anyah kuwa kalau. Dana yiwa khairiyyah magana akan lamarin saitace ni tsoro ne dani,ita ba gudu baja da bayah dama tanada sha'awar ƙwarewa a na'urah sosai,yanzu gashi tasamu dama kuma inno ta barta. Nima ganin hakan yasa na cigaba da karatuna sanann dayin bincike akan fannin dana ɗauka,shima deen dayake ya dawo hutu,sai ya ɗauki na tuƙi,so yake ya ƙware wajen wana mota da kuma samo bayanai akan duk abinda yasaka a gaba. Abinda na kulada shi da khamriyyah,takan bawa abin muhimmanci sosai,kaman rayuwarta ta ginu akai,amma idan nayi magana kuma sai tace kawai wasane,nima ganin hakan yasa nace wasane kawai. Karatu muke amma kuma har gaba da namu karatun,dan in bincike yazo maka har sama kake zuwa ka nemo,saboda kar wani ya wuceka. Duk abinnan da muke ba wanda yasani,dan khamriyyah tace yazama sirrine tsakanin mu,lokacin da khariyyah ta buƙaci inno ta barta zuwa koyon na'urah hanata tayi,ita kuwa ganin hakan yasa ta faɗamata gaskiyah. Yanda tayi mata bayani bata fahimci abinba,amma ganin sana'ace kuma tace kar a wuceta,sai kawai ta barta tayi. Wani lokacin idan na tuna yanda muka yarda da tsarin khamriyya kuma muka bashi muhimmanci sai abin yabani mamaki. Yanzu khamriyyah wani lokacin ko kowa bai sani ba saita fice daga gidan,wannan abin ya fara damuna,musamman da koyaushe sai tace na taimaka mata,nikuma nakan kasa ce mata a'a,gashi na tambayeta ina take zuwa tacemin kada na damu. Yau ma tsaye nake a bakin ƙofar gidan ina leƙa hanya ko zan ganta,nayi ƙaryah nace tana gidan wata amaryah maƙwabciyarmu,ita kuma inno tace lallai saina ƙirata . Gashi bata dawo ba har sannan ,bazan iya komawa nace ban ganta ba,dan haka na kwammaci nasha faɗan nima na zauna a wajen . Hangota nayi da babban hijabinta da kuma jakarta a lanƙaye,kanta a sunkuye tana tafiyah cikin nutsuwa,a raina nace kaman ba itace mai ficewa ba a saniba,duk da har cikin raina inada tabbacin kashi casa'in cikin ɗari ba wani abin tirrr take ba,kawai dai a rayuwarta tana son sirri,ba komai takeson a gane tanayi ba. Kama kunkumi nayi tareda murtuƙe fuska ina kallon ta da kuma tsimayin ƙarasowar ta,tamkar yanda uwa take idan ta aiki yaro ya daɗe. Dariyah tasaka tareda rungumeni tana cewa, "Ƴar uwata ta kaina,kiyi haƙuri kinji,nasan na sakaki a damuwa,amma bazan sake ba koda nasake ma kaɗan zanyi" Nima rungumeta nayi tareda cewa "Nidai kisan yadda zakiyi ki kareni a wajen inno,dan nasan sai ta kusan yin babbakena idan na shiga" "Karki damu wanann mai sauƙine,godiya nake buhu buhu da taimakonki sabrah tah" "Uhm nadaiji,muje toh" Dafa kafaɗarta nayi muka shiga cikin gidan,yaran gidan duk sun tafi makarantar isalmiyyah,tunda muka yi sauƙar farko bamu koma ba.tacan tacan sallamar ƴan garko. Muna shiga na haɗa ido da inno tana kallona,da alama dadewar danayine,jan hijabin khamriyyah nayi da ɗan ƙarfi alamar tayi magana,aikuwa cikin ƙarewa tayi wata ƴar dariyah tareda ƙarisawa wajen innon,iyah wayancewa kam ta yi degree a wajen. "Ah inno dama fah danaje gidanne ta roƙeni akan na rakata ƙarbo ɗinkinta a bakin kasuwa,to damuka je bai gamaba saida muka ɗan jirah,ita kuma sabrah data tambaya akace muna can sai tabimu shine muka daɗe" Shuru tayi alamar kaman bata yarda ba, "Inno hakane amma da nasan zata daɗe bazan rakata ba kinsan" "Naji amma ya zama na........." Katsewa tayi da maganar bata kai ga ƙarisawa ba,jin kakarin amai a gefenmu,idonmu muka zuba mata ganin yanda take zuba amai kaman mai shirin fitar da kayan cikinta. Nice na ɗauki kofi na ɗebo mata domin ta wanke bakinta,inno kuwa ƙiƙama tayi kaman kungi. Tsugunnawa nayi ina mata sannu tareda miƙamata kofin. "Sannu anty juwairah,bakida lafiyane?" "Uhm sabrah banajin daɗi kawanannan,tashin zuciya nakeji da kuma zazzabi" Kama hannuna tayi muka tashi domin komawa ɗakin,haɗa ido mukayi da inno wacce take jijjiga kai idonta yana zubar da hawaye. "Innalillah,ke kuma haka allah yake jarrabarki ƴar nan,allah yabaki ikon cin jarabobinnan,mu kuma allah yabamu ikon kulada ke da kuma ɗauke miki kewa" Mai inno kuma take faɗa,na ayyana a raina,tashi ɗayah yanzu take min faɗa nida khamriyya amma kuma yanzu ta koma matsar ƙwallah. Matsawa tayi kusada anty juwairah tareda duba hannayenta,sanann ta buɗe cikin idanunta. Jan ajiyar zuciya tayi kafin takama hannunta suka zauna. "Juwairah inaso ki saurareni da kunnen basirah kinji. Da farko kawamana ke akayi cikin gidannan a kan tsumma,kuka da ƙyar kikeyi saboda wahalar dakika sha a juji ba'a ganki ba. A lokacin ke ƙaramace bakisan komai ba sannan bazaki iya yiwa kanki komai ba,haka muka tallafeki muka raini raguwarki,da da rana ɗayah bamu taba tunanin ƙyamarki ba saboda koba ta hanyar aure aka haifeki ba ko kuma wasune suka saceki,kawai muna kallonkine a matsayin ƴar mu,farincikinmu sannam kuma mai buƙatar taimakonmu. Saboda mun riga mun san babu wani laifin ɗa dayake shafar yaro,saidai idan shima shine yayi nasa laifin,kowanne ɗa daidai yakeda kowanne yaro,bai hallata a matsayinka na musulmi ka cutar da ɗan adam ba kawai dan iyayensa sunyi laifi. So nake yanzu na tambayeki,idan aka baki yaron da iyayensa suka miki laifi,basu kasance masu aikata daidai ba,hasalima yaron bata hanyar aure yazo ba,kuma yana buƙatar taimakonki,shin zaki rungumeshi ki lullubeshi da ɗuminki,ki tallafi rayuwarsa? Ko kuma zaki yi biris dashi ki juya masa bayah,koda kuwa yana kukan neman ɗauki?" Tunda inno tafarayin magana ba iyan anty juwairah ba muma kallonta muke da mamakin tambayarta. "Zan tallafeshi inno,zan yi masa duk wani iya ƙoƙarina dazan iyah,badan nima anyi min ba,sannan bazan duba iyayensa ba zanyi masa abinda yadace,har lokacin dazai fara yin komai da kansa. Kuma bazanyi nadamar hakan ba har cikin zuciyata nake faɗa" "Mashaallah nagode da amsarki juwairah,dan dama nasan zanji hakan,kinsan mai yasa na tambayeki?" "Ahahh ban sani ba" Hannunta takai ta ɗora akan cikin juwairah tareda yin murmushin takaici. "Juwairah tun wancan nafara ganin alamun ciki a jikinki,ban tabbatar ba da farko shiyasa nayi shuru,amma yanzu alamunsa ya bayyana a jikinki sosai,tambayar danayi miki bada kowa nake ba saida uban cikin jikinki. Yah cutar dake ya wargaza mutunciki a gabanmu,sannan mai kasance mutum nagari ba,amma kuma gashi ɗan sa dake jikinki yana buƙatar taimakonki,ko tsoka babu a jikinsa sai gudan jini,kowanne abu zai iyah cutar dashi,dake aka haɗashi ki bashi kariyah,shin zaki cutar dashi ta hanyar zubarshi ko kuma hantararsa idam kin haifeshi,ko kuma zaki tausaya masa da kaddarar dashima ta zanu a rayuwarsa,ki bashi tarbiyyah kaman yanda aka miki?" Hannunta ta maye gurbi aka cikinnata lokacin da inno ta ɗauke nata hannun,kallon cikin take kaman wanda zataga ɗan a ciki kwance. Kuka ta fashe dashi tareda matse hannun akan cikinnata,daga gani jitake ina ma mafarki take data farka daga baccin. Cikin raunin muryah ta kalli inno tareda cewa "Tambayar yanzu tayi tsauri nabada amsarta yanzu ina buƙatar lokacin,saboda barin cikin harda alaƙata da ammar zai shafa,dam haka ina buƙatar yin tunani idan zan samu dama" Itama inno hawaye take kafin tace, "Kinada damar yin tunani tsawon yanda kikeso,ina fatan kiyi zabin dazakiyi nadama ba,amma duk wanda kika zaba ni mai baki goyon baya ce" Daga kai tayi da maganar innon kafin ta tashi tashige ɗakinta. Sai a lokacin na kulada hawayen dayake zubomin akan kumatuna lokacin da anty juwairah tabar wajen. Khmariyyah kuwa ko motsi batayi,da alama ta tafi duniyar tunani. Tundaga inda abin yafaru a cikinmu babu wanda yasake tada maganar tamkar ba'ayi shi ba. Saboda wannan ba kyakykyawan labari bane daza'a dunga watsashi ga mutane. Wata biyu sun shige,zuwa lokacin cikin anty juwairah ya tafi wata biyar,yayi wata fitowa tamkar cikin wata bakwai,mudai yanda muke ganinta bamuga wani abin tashin hankali a gareta ba,muma sai muka kwantar da hankalin mu muke ƙoƙarin nuna mata komai ba komai bane. Duk da bata samu inno ta faɗamata zabinta ba,amma kuma ganin an ɗebi lokaci batayi ƙoƙarin cutar da cikin ba ko kuma cutar da kanta hakan ya nuna ta zabi ta raini cikin akan ta zubar dashi. Wanda hakan yasa inno ta jinjina mata da juriyarta,sannan ta zage dantsen kulada ita har zuwa lokacin dazata haife cikin. A zaune nake a ƙasa kan tabarma,ita kuma anty juwairah tana zaune akan kujerar da kwanon ɗan sululu akan cinyarta wanda maman yara tayi mata. ƙafarta nake matsamata wacce tayi suntum kaman an hura baloo. Mu kaɗaine a wajen khariyyah ta tafi shagon computer ogansu ya ƙirata,ita kuma khamriyyah tayi ficewar tata,a cewarta ta tafi isalamiyyah,wanda nasan ba can ta tafiba,kawai dan inno tayi shurune. Magana nake tayi amma banji anty juwairah tace komai ba,ɗaga kai nayi naga ta tafi tunani,ga kwanon a cinyarta amma bata ciba. Ta bata nayi a cinyarta wanda hakan yasa ta zaburah kaɗan. "Anty juwairah wanann zurfin tunanin dakikeyi kinsan fa da matsala,dan allah ki daina. Kuma yakamata ma kifara zuwa awu yanzu" Ɗan murumushi tayi tareda saka ɗan sululun a bakinta. "Hmmm sabrah don na zabi cigaba da kulada cikinnan da kuma maida komai ba komai ba,wani abin bazan iya ba,taya zam iyah zuwa awu kaman yanda masu cikin sunnah suke zuwa,taya zan daina tunani na dunga murmushi kaman yanda masu miji da kuma cikin sunnah suke,kodah nace zanyi bazan iya ba,karki manta inafah da tabo a cikin zuciyata wanda har yau zubarda jini yakeyi bai warkeba,kodah na takura kaina wajen bashshi ya warke bazan iyaba sabrah" Kukane yake son kubcemata amma taƙi bashi damar hakan,kallon cikin tayi tareda shafashi sanann tacigaba da cewa. "Idan nace ban tsani uban cikinnan ba nayi ƙaryah,idan nace banasonsa kuma bana jin haushinsa a lokaci guda to kowa yasan ƙaryah nake. Ina sonsa sosai,sannan inda burin riƙesu har lokacin da allah zai rabamu,amma bazan daina tunanin abinda ya faru dani ba" Maikuma nake dashi dazan ce bayan naji abinda tafaɗa kuma,dole shuru nayi ina zullumin abun a raina. A raina na cigaba da yimata fatan sauƙa lafiyah,sannan kuma dafatan sauƙi a lamuranta. Tafiyah ta tafi,cikin anty juwairah yazama ƙato,duk wanda ya ganta sai ya sake waiwai yawa saboda girman cikin. Komai yanzu yimata ake,duk da tana ƙoƙarin motsa jiki sosai,zuwa awu kam taƙi yarda taje,tunda ga dawowarta daga katsina zuwa shari'ar maryam bata sake fita waje ba har zuwa yau. Dan haka inba mutum shigowa yake ba sosai bazai ganta ba ma. Daff da haihuwarta sai ta fara kumburah sosai ,abin har ya wuce na lafiyah,ga ciwon kai da jiki datake fama dashi,amma kuma taƙi zuwa asibiti,idan an ce ta fita duk hankalinta sai ya tashi. Haka muka zubamata ido babu yanda zamuyi. Wataran mun dawo daga makaranta itakuma ta fito a banɗaki,babu zato babu tsammani sai ganin zubewarta mukayi akasa,jikinta ya ɗebi rawa kar kar kar. Khariyyah ce ta ƙwalawa inno ƙira itada maman yarah,da gudu suka iso wajen suna dubawa. Nida khamriyyah kuma muka fita da gudu neman mota a waje. Kayan makarantar da bamu cireba kenan aka nufi asibitin tareda mu. Tana kan cinyar inno a gidan baya itada maman yara,ina gaba wajen direba khamriyyha kuma tana gefensu. Lokaci lokaci nakan leƙawa ina ganin yanda numfashin ta yake sama sama,ga ritsetsen ciki a jikinta kaman wanda zata haifo ƴaƴa biyar. Gado suka turo da gudu aka ɗauketa sai cikin asibitin. Sauri sauri suke ganin halin da take ciki,wata nurse ce naji tana cewa, Wai jininta ne yayi mungun hawa saboda yawan tunani datakeyi,ga kuma ciki wanda hakan ya haifar da matsala babba. Tambayar da nurse ɗin tayimin ita ta tsayar da fitar numfashi na cak,dan ban san mai zance da ita ba "Ina katin awunta kuje ku ɗauko,tana cikin mawuyacin hali,sannan idan babu shi to bazamu tabata ba saidai kuje asibitin kuɗi" Shin cewa zan ce batada shi,saboda bata ta'ba zuwa awu ba,ko kuma haƙuri zan bata. Taya zamu shawo kansu su dubata a halinda take ciki,ni bansan ma mai zanyi ba a lokacin,kai na yayi mungun yin murfi. Wannan ita ake ƙira da rayuwa. Idon khamriyyah nagani yanda ta zubawa nurse ɗin jan idonta,a raina sunan allah nake ƙira yayi mana tsarewarsa,dan kuwa da alama wani abu take shirin yiwa matar,wacce tazage sai magana take mana babu alamar imani a tareda itah. Anan kam free ɗinku ya ƙare,duk mai buƙatar sanin mai zai wakana a littafinnan toh ya kasance dani ranar juma'a,a PAID group domin cigaba. Karku manta naira 400 ne zai biyamuku buƙata. 3131951977 Auwal sadiya First bank. Taku _sadi-sakhna_ Ƴar mutan jama'are. *MABARACIYAH* _haƙƙin mallaka_ _*sadi-sakhna*_ (Yar mutan Jama'are) 21••22 Tun kafin nayi wani yunƙuri khamriiyyah ta zari a wuƙa a wani faranta ta yankawa matar hannu. Ihu ta fara ganin yanda jini yake bin hannunta,sanann kuma wajene da in ba'ayi da sauri ba zata iyah rasa jini dayawa. Sauran nurse tahowa sukayi da sauri domin taimaka mata,saidai khmariyyah ta riƙe hannunta ta hanata barin wajen,ga jinin yana ta zuba,sanann ta riƙe wuƙar idan da mai buƙatar sake matsowa. "Kusan allah in kunga na sauta kunyi mata magani to kun duba antynah dake halin mutuwa koh rayuwa,inkuma kuna ganin wasane to kucigaba da tsayuwa. Munsan mun yi kuskure wajen rashin zuwa awu,amma kuma tanada babban dalilinta nayin hakan,wacece a cikinku wani zai shiga gidanta ya kashe iyayenta yayi mata fyaɗe,ta wayi gari ta ganta da ciki kuma tayi farinciki har ta samu damar zuwa awu,waye nace a cikinku takeda wannan ƙwarin gwiwar,na tabbata kusan dukkanku kashe cikin zakuyi daga sanda kuka sani. Toh wallahi ban faɗi karya na indai rashin tabata yasake zawo wata matsalar,saina cinnawa wajennan wuta bayan na fatattaki duk marasa lafiyar wajen" Dukkansu jikinsu rawa yakeyi,da sukaji abinda tace,ga yanayin ta ma daya nuna ba a hayyacinta take ba. Magana mukaji a bayanmu ta wata mace,da alama ta ɗan manyanta a shekarunta. "Mai ya faru a nan wajen haka?" Zaro ido tayi ganin khmariyyah ta damƙe nurse ɗin ga kuma jini yana zuba a kasa. Magana tafarayiwa matar dan ta taimaketa. "Uhm.....mmetron ki taimaka wanann batada hankali" Sauranne suka tsara mata mai yake faruwa,wanda yakan yasa maida kanta wajen khamriyyah. "Saketa yarinyah,ni zan duba yayartaki yanzunnan,barta su gyaramata karki ɗorawa kanki laifi da yarintarki,naji abinda suka ce gameda ƴar uwarki,ina mai tabbatar miki zanyi iya ƙoƙarina,allah yakare gaba" Babu kunya kuwa khamriyyah tasaki matar tareda tunkuɗata kana ta bita da harara,itadai ana sakinta tabar wajen da sauri. Wacce aka ƙira da metron ɗinne ta nufi ɗakin da aka kwantar da anty juwairah,wanda hakan yasa nayi ajiyar zuciyah. "Ke khmariyyha meyasa kika yi haka,kinsan fah hakan zai iyah jawomana wani tashin hankalin" "Dama dan ayi tashin hankalin nayi ai,kuma wlh ba sakinta zanyi ba har sai ta suma,naga bakin ciwa mutane mutuncin" "Uhm"shine kawai abinda nace,tareda komawa bakin ɗakin da anty juwairah take,inda sabo yakamata na saba da taurin ran khamriyyah. Tun azahar muke asibitin har dare,ko abincin rana bamici ba bare yin wanka,gashi har yanzu tana ciki basu bamu damar shigaba,kawai dai sunce haihuwar bata zoba da saura,saidai a halin datake ciki mai hatsari bazasu barta ta tafi gidaba,dan har yanzu bata san inda kanta yake ba. Allurar bacci suke ta ɗuramata daga ta farfaɗo,saboda a bawa ƙwaƙwalwarta hutu daga tunanin datake yi. Nida khamriyya komawa gida mukayi aka bar iyah maman yara da inno a ca,khariyyah kuwa dama tana gida,saidai tayi mana ƙira a ƴar wayarta yafi sau a ƙirga. A can dole su inno suka kwana saboda yanayin jikinnata,saidai kuma sun faɗamana ta fara naƙuda a lokacin. Shiryah wa mukayi muka tafi asibitin,dan koda mune makarantar ma babu abinda zamuyi sai tunani. Lokacin da muka isa asibitin har sanann likitocin suna kanta,amma ansamu nasarar sauƙar da jinin nata ba kaman jiyaba. Muna nan zaune har wajen sha biyu kafin mukaji kukan jinjiri daga ɗakin,zumbur muka miƙe muna jiran muga wazai fito. Duk da baƙin fentin da ubansu ya shafamusu,amma hakan bazai hana muyi marmarin yaranba,wanann ne karo na farko da haihuwar yaro akayi ba kawoshi ba. Nurse ne guda buyi suka fito da jarirai a hannunsu,sororo muka tsayah muna kallonsu,dama ƴaƴa biyune,kuma hakane gasunan mace da namiji tufarkallah. Nice na karbi mace inno kuma da karbi namijin,khmariyyah bata ko kalli yaranba,hankalinta yana kan ɗakin sai leƙawa take,ganin nurse ɗin batada niyyar yimata ƙarin bayani yasa ya tambayeta "Uhm uwar yaranfah tana nan ƙalau?" "Eh toh da sauƙi dai za'ace,amma gaskiya abin babu daɗi,jikinta ya kumburah sosai,hatsarin kuma shine ba sacewa yake ba ƙaruwa yakeyi gaba,kucigaba da addu'a insha'alla komai zaizo da sauƙi." Jikinmu ne yayi sanyi jin abinda tace gameda anty juwairan,dukkan bakinmu kowa sai motsi yake yana addu'ar da zai iyah wacce yasan tana buƙata. A asibitin mukayi ta sintiri,wasu na komawa gida wasu na dawowa,tun nurse ɗin suna yawan dubamu akai akai har suka koma suna tsallake gadon anty juwairan,dan sunriga sun san matsalarta,kuma ba sauƙi yake ba bare suce an ga canji. Ƙarshe dai yaran a asibitin suka ƙarbi sunan su,har suka shafe wata kusan guda da rabi. Idan ta farfaɗo takan karbesu da basu nono,idan tana kwance kuma a basu madara. Dayake babu abinda ya damesu suna ci suna ƙoshi sai girma sukeyi,ƙyawawane kam farare tamkar ubansu,wanda mukayi babban bincike akan sa,mun gano shi kaɗaine a wajen ubansa kuma bashida aure,shashanci yasaka a gaba kawai,abin takaicin kuma gashi ya bar mana da jininsa batareda yasani ba. Kallom fadeelah nayi wacce take kan cinyata,yarinyar badai kuka ba kam,gata batada bacci sosai kaman fadeel ɗin. Dawowa ta kenan daga gida na dawo daga makaranta. Khmariyyah kuma dama bataje na yau,itace a wajen anty juwaira,inno kuma tana gida ciwom ciki yadameta,maman yara kuma ita ke kulada gidan. Abubuwa dai duk sun kwabemana amma haka muke ta garawa,mun zubawa sarautar allah kallo muga yanda zayyi damu. Tashi nayi daga corridon da fadeelah a hannuna na shiga cikin ɗakin da mahaifiyarsu take kwance,yanzu idonta biyu tana kallon silin,ƙarar kukanne yasakata juyowa ta kallemu muna shigowa,kasancewar bata magana sosai,sai dai binmu kawai take da ido. Hannu ta ɗaga wanda yake rawa zuwa saitin yarinyar,alamar na bata ita. Kwantarta nayi a gefenta tareda buɗe nonon,dayake shi take nema ba 'bata lokaci takama tafara sha. Khamriyyah ce tashigo hannunta duk ruwa da goyon fadeel a bayanta yana bacci,da alama wankin kayan da anty juwairah ta bata tayi. Hawayene yake gangorawa a idon anty juwairah lokacin data kallemu,nasan tunani take a ranta yanda muka tsaya a gefenta iya wuyah da tsanani. Sallama mukaji ta anty shamsiyyah,dukknmu kowa ya tamke fuska yayi,dan iskancinta da cin kashinta ya ishemu haka. Sai tazo tayi ta iyayi tana nuna ƙaryar kuɗi a gaban mai jinyah,ko kuma idan sunzo da wata saita nuna tamkar ba gida ɗayah muke da itaba,ta wuce sa'armu ashe tare muke. Yanzu ma sallama tayi tashigo,zuwanta na uku kenan tun sanda aka kwantar da anty juwairah. "Mai jinyah ya jikinnaki dai,naga jiki kam har yanzu jiya i yau,amma baza'a gwada kaiki asibitin katsina ba ko za'a dace" Munajin ta faɗi haka khamriyyah tayi caraf tace. "Gaskiyaa ke ta musamman ce anty shamsiyyah,da kin kyauta kuwa idan kika ɗauki nauyin kaita,barina karbo takardar izinin ina dawowa" Dakatar da khamriyyah tayi tareda cewa "Ahah bashshi zanyi masa maganar,ba yanxu ba tukunna" Dawowa khamriyyah tayi tana sake tamke fuskarta,dama da gangan tayi dan taga yanda zatayi. Cire fadeelah tayi a nono ta miƙamin ita ganin tayi bacci,kafin ta ɗaga anty juwairan domin cire mata rigar jikinta tayi datti da yawa. Anty shamsiyyha tana kallon ta bata tayata ba,har ta gama ta mayar da itah shimfiɗin. Daga cikinmu babu wanda yasake kulata kaman bata wajen,muryar khariyyah mukaji tashigo hannunta ɗauke da kular abinci inji maman yara. Bayan sati biyu da zuwan shamsiyyah sai jikin anty juwairah yafara sauƙi,dan yanzu tana magana sosai ba kaman da ba,har yaran take karba da basu nono daga kwance,wannna abin ba ƙaramin daɗi muka jiba. Itama idan daga jin daɗinmu sai tayi ta murmushi. Fadeelah ce a kan cinyarta ta gama bata nono,sai khamriyyah ta karbeta,dan har yanzu jikinnata bashida ƙarfi sosai. "Ƙanne na haƙiƙa banida abinda zance muku sai allah yasaka da alkhairi,kuma allah yabaku mai yimuku kaman yanda kuke min...," "Dan allah anty juwairah kibar wannan godiyar,dama naga idanuwanki lokacin dakike kwance,kina buƙatar faɗin kalmominnan,babu komai,ganin zamu iyah yi miki mu shine kwanciyar hankalinmu" "Khamriyyah ku karbomin takardar sallama inason komawa gida,idan wani abu ya faru inyaso saina dawo,nagaji da zaman wajennan,kuma nasan kun gaji sosai" "Karki ce haka,kowa dama dayake zaman asibiti to zaman haƙuri yakeyi,abin farincikin shine da kika samu sauƙi har kika buƙaci tafiya gidan da kanki,barina gama gyara kayannan zanyi mata magana toh" Suma da khamriyyah ta tambayesu basuyi musu ba,dan dama na kula sun gaji damu kaman. Washagarin ranar maman yara tazo tayamu tattare kaya muka koma gida,ana ta murnar samun nasara,duk da bamai yawa bace amma dai an samu. Ban taba sanin idan an ce ana samun sauƙin tafiyah da gaske bane sai a kan anty juwairah,lokacin da muke ta murnar samun sauƙinnata bamu saniba ashe na amsa ƙiran mahaliccinta ne,mutuwarta tafi ta duk sauran girgizamu,saboda bamu zata mata ba sai kawai ganin afkuwsrta mukayi. Ranar da aka gama murnar dawowarta da daddare ciwo ta dawo ɗanye sharaf,da farko mun so nemo mota amaidata,amma ganin alamun rashin rayuwa a cikim idonta yasa dole muka haƙura jinkinmu ya saki muna tsimayin mummunan labarin dazamuji kuma mugani. Mutuwa rigar kowa,idan tazo babu wanda bazai amsa kiranta ba,koda kuwa waye ya bari dole sai ya tafi. Jijjiga jikinta yafara tana kikkifta ido,inno na gefenta tana shafa mata ruwa a fuska tareda yin salati. Hannun khamriyya ta riƙo tana nuna mata yaran da suke gefenta da idonta,ko bata faɗaba tana rokon a kula mata da rayuwarsu ne,wanda batasan kobata fadaba mu masu riƙesune da basu kulawa. Can bayan kaman wasu daƙiƙu dukkan wani motsi na jikinta ya tsaya,numfashinta ya daina shiga da fita,yayinda bugun zuciyarta shima ya tsaya cak dayi,rai yayi halinnasa daya saba a koyaushe. Khamriyyah ce datake tsaye tafaɗi yaraff sai jin buguwarta mukai timm a ƙasa. Kanta hankalinmu ya koma,a iya kwankinnan mun ɗanɗani mutuwa ba ɗayah ba ,ba biyu ba,saidai muyi fatan allah yasa muma tamu ta ɗaukemu muna kan turbar gaskiya. Kafin wayewar asuba su inno sun gyarata a cikin kayanta na ƙarshe,kowa sai matsar hawaye yakeyi,dan anty juwairah mutum ce da bata cutar da kowa wajen zama da itah. A masallacin anguwarmu aka sallaceta inda akayi nasu maryam da hajjah. Har aka kaita safiyah tayi hantsi ya washe khamriyyah bata farkaba,har muna shirin kaita asibiti sai kuma mukaga alamar motsawarta,daga gani doguwar suma tayi amma ba mai tsayi ba . "Sabrah ina anty juwairah take,dan allah kicemin mafarki nake kinji,karkice abinda nagani na bacewar numfashinta na ƙarshe da gaskene" Shine abinda ta fara faɗa bayan tasowarta daga suman datayi. Jijjiga kaina kawai nake ina share hawayen dayake zubowa a kuncina,wanda shikaɗai nasan ya isa ya faɗamata gaskiyar lamarin da take biɗar sani,dan da bakina bazan so na gaskata mata wannan labari mai ɗaci ba. Hannunta ta dunƙule tareda mayar da hawayen dayake ƙoƙarin zuba akan fuskarta,kana ta cije baki tana kallon bangon ɗakin. Da alama irin wanann yanayinnata ta shiga,wanda narasa menene yasaka ta a cikin halinnan. "Khamriyyah meyasa idan abin kuka yasameki bazaki zubar da hawaye ba saidai ki mayar dashi hakan fah yanada illah" "Sabrah bashida dalilinsa na sauƙowa a cikin idanuwana,bayan wanda yasakani na zubar ɗin shi bayyi ba" "Kai khamriyyah,ki dunga yarda da kaddara mana,shi sanadi ne,amma maƙasudin faruwarsa yine na allah" "Nasan wannan,amma shi bai saniba idan ba sanar dashi akayi ba,dan haka da ɗaɗɗai zan sanar dasu kuwa inshaallah" Idanunta a soye suke,ga wani numfashi datake fitarwa kaman mai shirin yin kokuwa da 'bauna,nidai ɗaga kai nayi,dan komai zan je bazata saƙƙoba sai taga dama. Bayan kwana uku da mutuwar anty juwairah wato ranar sadakar uku kenan,sai inno ta ƙira anty shamsiyyha daga cikin mutane zuwa ɗakinta. Iya mu yamu ƴah gidan kenan. Ɗanta wanda ya kusa shekara sai kuka yakeyi. "Shamsiyya dama akwai maganar danake so nayi miki,kinga dai ƴar uwarki kuma ƙanwarki ta rigamu gidan gaskiya,gashi tabar ƴaƴa marayu masu shan nono,wanda ko bazasu sha nonon ba dole zasu buƙaci madara. A halin yanzu bamuda kuɗin madarar dazamu shayar dasu,koda munada shi ma ni kinga ba lafiyace dani ba fama nake da ciwon ciki mai tsanani,ita kuma maman yara itama ɗanta a cikin satinnan zai ɗauketa dayaji mai yake faruwa a nan ɗin,dama ba da son ransa take zaune ba,kawai dai abune daya zama jiki. Sukuma su khamriyyah makaranta suke,abin zai musu yawa ga rainon yara ga kuma na makarantarsu,inaga idan mijinki zai amince shamsiyyah ki ɗauki yaranann a wajenki,inaga hakan zai fi" Saurin miƙewa tayi jumbur tareda zaro ido, "Haba haba inno mai kike cewa haka,na riƙe ƴaƴa,babu jinin daya haɗani dasu na riƙesu hakan ma kuma shegun ƴaƴa,wlh bazan iyaba,nifah zuwan danake asibiti da kuma gidannan dan kar a zageni nake zuwa,abinda ya haɗamu daku dama ya raba,zamane nikuma yanzu nayi aure na samu rufin asirina,bazan iyah saka ƙazaman ƴaƴa akan nono na ba,ko kuma nakashe musu a kuɗi a banza na siyan madara,bazan iyah....." Tasss kafin ta gama maganar inno ta ɗauketa da mari,danni kaina danake kusada khamriyyah saida na tsorita,dan ban taba ganin 'bacin ran inno ba irin na ranar. "Kinada hankali kuwa shamsiyya,ni kike faɗawa wannan maganar,?" "To wai dolene saina riƙe ƴaƴan da kowa yasan shegune,kuma daza'a tilastamin nima da'aka riƙeni ai ba'a banza aka riƙeni na,saidai gwamnati tabada albashi" "Abashi!....albashi kike ƙiramin ruƙon danayi miki shamsiyyah?...karki manta fah kebada madara na raineki ba da nonona na shayar dake ,jinki nake tamkar ƴar dazan haifah a cikina,sannan lokacin dana shayar dake bana tuna ke ƴar sunnah ce ko kuma ƴar gabada fatiha,kawai ni ke yarinyah nake gani ƴata kuma mai neman taimakona,sannan wacce zan raina na bata tarbiyyah,to barikiji abinda baki saniba,tun lokacin dana karbeki nasan duk wacce ta haifeki ba musulma bace,sannan kuma bada aure ta haifeki ba ,hasalima ubanki dayake matsayin saurayinta ne ya gudu yabarta,itakuma da ajiyeki a gaban coci ta gudu. Baba shehu zaije aikin shinkafah kogi da asuba yaganki,ba wanda yagani ya lallaba ya ɗaukoki ya kawoki nan dan kwaɗayin ki tashi cikin musulmai. Lokacin daya faɗamin mai yafaru,ban taba farincikin rainon ƴa ba kaman yanda nayi akanki,saboda ina hango riba biyu zan samu,na rainonki da kuma na nabaki tarbiyyha irinta ƴaƴan musulmai,amma shine kika faɗin anbiyani albashi na rainonki koh?.......hmmm ki fice ki bani waje bana buƙatar sake ganinki a rayuwata har abada" Shuru tayi bata tafiba,da alama jikinta yayi sanyi da zancen inno, "Uhm ko ban riƙesuba zan tafi dasu na kaisu gidan marayu a katsina,saina dunga zuwa ina dubasu......" "Ni zan riƙesu na rainesu,kuma zan fara sana'a da neman aiki domin siyan madara da kuma abincin dazasu ci,inshaallah jinin anty juwairah bazai tagayyara ba indai ina raye" Dukkanmu kallon khamriyyha mukayi wacce tayi maganar cikin dakewa,kuma babu alamar zata canja maganar tata. "Ke kuma shamsiyyah kaman yanda inno ta faɗa ki tashi ki tafi gidan mijinki,daga rana mai kaman tayau bamason ganinki a cikin gidannan koda wani abune ya faru,muna so ki manta damu a rayuwarki,ki ɗauka tamkar daga sama kika faɗo,kokuma kishiga duniyan neman uwarki,nasan ita zatayi daraja a wajenki tunda ita ba'a bata kuɗi ba sanda ta haifeki ba" Cikin muzanta da kunyah shamsiyyah ta zari jakarta ta bar gidan ma gabaɗayah. Jinake kaman na shaƙeta saboda haushinta danakeji,dama ni bama shiri da itah tun muna yara. Bayan fitarta daga ɗakinne inno ta kalli khmariyyah wacce take jijjiga fadeelah ta tashi daga bacci. "Amma aikin dakika karba zakiyi da kamar wuyah khamriyyah,inaga zai iyah tana rayuwarki" "Bazai taba rayuwata ba,in ma yatana babu damuwa,inda nice a madubin rayuwar anty juwairah haka ta faru dani dole na riƙesu,dan haka yanzu da bata nan sun zama ƴaƴa na,zan riƙesu tamkar ƴayan da allah zai bani a cikina" "Bazai gagara ba ma khamriyyah ,kina damu,zamu zama tamkar tsintsiya guda ɗayah,yaran nan gidan ma zamu cigaba da kukadasu kafin muga ya allah zayyi" Ina gama faɗin hakan na rungume khamriyyan,ita ma khariyyah tabi bayanmu tana sha ƙawallar idonta. Daɗi naji a raina ganin murmushin inno ya dawo ba kaman ɗazuba da ranta ya 'baci. Idan akace kana rayuwa toh saidai fa kawai kace mashaallah,dan lallai kaga yanda ranka yakeso ba. Da daɗi da babu haka muka cigaba da rainon ƴan biyun anty juwairah,sun wayo sosai dan sun doshi wata biyar yanzu. Ba wanda suka fi sabawa da itah kamar khmariyyah,dan tafi kowa shaƙuwa dasu,a wajenta ma suke kwana,duk da ma bata fiye zama a gidanba. Tana zuwa aiki da yamma bayan mun dawo daga makaranta,a gidan wani chairman. Duk da haka idan zata tafi saita ɗauki ɗayah daga cikinsu ta goyeshi,nikuma naji da ɗayah. Nima ba zama nakeba nasamu koyarwa a islamiyar anguwarmu,ita kuma khariyyah tana shagon computer su,sai yamma take dawowa. Yanzu gidan shuru ba kaman da ba,dan ma maman yara tana nan bata tafiba tukunna,tace ya ɗanta yaƙara bata lokaci tukunna,to hakanne yasa muka ɗan samu dama daman abin. Muna zaune dani da deen muna hira,dayake anyi hutun ss3 kafin a zana paper ya dawo gida,wani satin zamu fara jarabawa. inata tsokanarsa yayi tsayi muryarsa kuma ta zama ƙatuwa,wata yarinya ce tazo wajen da fadeelah a gefenta tana biyeda itah,ta cune bakinnan kaman na kifi,yarinyar dariyah take bani sosai,kwata kwata bata iyo mahaifyarta ba mai sanyin rai. "Yah deen wai kazo inji maman yara zata aikeka" "Ohh yanzu fah nadawo,kice ganinna zuwa yanzunnan" Harara ya dokamin lokacin daya tashi zai tafi. Nasan ƙiran bazai wuce na abinda zata siyaba zata koma asibiti wajen inno,wacce safi ɗaya kenan da'akayi mata tiyatar appendix a katsina,wani asibiti suka fara yin ayyuka kyauta na tsawon wata shida saboda marasa lafiyah,inda ana haka da an huta. Kallon fadeelah nayi wacce tafiyar tayi ɗan kwari sosai,dan dama itace mai sanyin yin abu da wuri ba kaman fadeel ba,shekara biyu amma bata daɗe dayin tafiya ba. Kallonta nake tana wasan kasa,kaman ba itace maimin kukan dareba tana ƙiran khamriyyah,yau kwana huɗu amma jinake kaman shekara,allah allah nake sudawo daga asibitin,dan naji ance aikin yayi kyau har banɗaki takezuwa ta dawo da kanta. Gaskiya khamriyhah tana ƙoƙari sosai,mai riƙe fadeelah ai saiya shiryah,batada daɗi ko kaɗan. Tashi nayi daga wajen na ajiye novel ɗin dayake hannuna,ganin lokacin tafiya makarantar islamiyyah yayi. Wanka nayi suma su fadeel nayi musu,dan suna zaune a gidanne amma basa cikin yaran gidan,dan haka mu muke musu komai ba ƴan aikiba. Ɗan maman yarane da wasu wanda aka rainesu a wajen suka ɗauki masu aiki guda biyar wanda zasu dunga kulada wajen. Sannan su dunga taimakawa da aikin yaran. Nafi minti biyar ina zaunar ta amma taƙi zama nayi mata wankan,shi fadeel tun ɗazu nayi masa wankansa har ya bushe ban saka masa kaya ba. "Yanzu fadeelah dan butar ƙaniyarki bazaki tsayaba koh,zan kaiki wajen karen madugu ya cinyeki kuwa" Shuru tayi tana zare ido,ga tsoron tsiyah dama. Da haka na samu dama na gama mata wankan na shirya su,sashen maman yara suka nufah ni kuma nafice daga gidan. Kwana biyar su khariyyah suka sake sai gasu sun dawo gida,anata murna aiki yayi kyau,saidai ance ta samu hutu sosai da sosai. "Inno shikennan yanzu kam anyi aiki,muna fatan kisamu lafiyah sosai" "Ah jiki kam yayi kyau sosai,banda ciwon wajen tiyatar babu abinda yake damuna,sunce kada na dunga shan ruwa mai datti,sanann kuma idan wani abu kona matsala yafaru to kada na naje ko wane asibiti sai can. Dama appendix ɗin waje biyune yake?" Da alamar tambaya na kalleta,wajen biyu kuma Nuna gefen cikinta tayi bangaren dama sanann ta nuna kusan mararta ma,wai duk ciwo takeji a wajajen idan bata sha magani ba" Ware biyu kuma,sanann sunyi gargaɗin kar a sha ruwa marar kyau,idan kuma matsala tafaru kar a je asibitin ko ina sai nasu. Mai hakan yake nufi,anyah kuwa babu wami abu a ƙasa kuwa. Hmmmm. Dama fah ance araha bata ado. Allah dai yasa lafiya kawai shi ake fata. Taku _sadi-sakhna_ Ƴar mutan jama'are. *MABARACIYAH* _haƙƙin mallaka_ _*sadi-sakhna*_ (Yar mutan Jama'are) 23••24 Da farko naso nazarin wannan tiyata ta inno,amma kuma ganin an samu abinda ake nema wato sauƙi,saikawai na bar zancen. Uwa uba kuma naga khamriyyah tayi shuru da zancen. Mun fara zana jarabawa,karatu ya fara zafi,dan kowa burinsa da mafarkinsa ya ɗauka akan sai ya cimma burinsa akai. Koyaushe idan kaga ɗaya daga cikinmu to da littafi a hannunsa yana karatu,shima deen dayake makarantarsu nasan hakanne a wajensa,munsan iya karatunne muke dashi dazamu dogara dashi, shiyasa bazamuyi da wasa ba. Waec muka farayi a makarantar daga nan bamu komaba,dan bamuda wanda zai biyamana kuɗin neco mu zana,sai allah ya dafamana muka ci guda ɗayar da muke da damar yinta. Musamman khairiyyah da deen sun fimu cin paper. To hakan ma gwanda ni da khamriyyah kam,taci math kam sosai amma english kam sai a alhamdulillah. Kallonta nayi lokacin da mukaje cirowa paper,ina ƙunshe dariyar datake cina,duk da nasan ta ganni. "Anty khamriyyah" Harara ta watsamin wanda hakan yasakani sakin dariyata,dan dama tasani idan na ce mata anty to tsokana naso yi. "Wace makaranta yanzu zaki tafi,naga subject ɗin da kika zaba ma wasu kala daban" "Suna ga damar yi,shiyasa na saka,ko kinaso nasaka wanda banajin zasuyi min amfani?" "Ahah ban ce ba,wace makaranta zaki tafi toh" "Ba ruwanki,kiji da taki makarantar kawai,kowa yayi nasa bangaren dayaga yafi masa" "Uhm ni inason karantar physicology,amma bangaren behaviour nakeso,saboda abin yana burgeni ga dunga ganin mutum kana gane ɗabi'unsa,yakika ce abin khamriyyah" "Hmmm kike min dariyar math kema fah naki bawani ƙoƙari kikayi sosai ba,kuma kinsan ana buƙatarsa sosai" "Eh dai yafi naki,khairiyyah kam naga taci nata,kodayake tana buƙatar sanin computer dole ta dage,shikuwa wancan mai engineering ɗin yanada aiki a gabansa sosai" "Menene aiki a ciki,sa kaine fah abin,gani yayi zai iya shiyasa yayi" "Uhm hakane kam,amma ba'a nan gizo yake saƙarba,kuɗin yin karatun shine aikin" "Kin fiye hasashen nesa sabrah tun baki ga farko ba,ke kam ki zubawa sarautar allah ido mana" "Uhm muna ta surutu yamma fa tayi gwanda mu hanzarta komawa gida" Na faɗa ina ƙara saurin tafiyata,itama khamriyyah dana faɗa sai a sannan ta kula ashe ta bar inno da rainon su fadeela,gashi ba lafiyace da itaba,ciwo yaƙi ci yaƙi cinyewa,anyi tiyata amma har hanzu kukan ciwo take da daddare,musamman idan tasha wani ruwa ba na pure water ba. Ƴar tsokana muka cigaba dayi a hanya na yau da kullum har allah ya kaimu gida. Ɗakin inno muka shiga dan mun hango takalmin maman yara a wajen,da alama kenan tana ɗakin,gabana ne ya buga,wanda suma sauran daga ganin kan fuskarsu kasan hakanne a ransu,dan daga ganin yanayin bana lafiya bane. Shiga mukayi da sauri can uwar ɗakin inda muke jiyo nishin inno maman yara tanayi mata sannu. A kwance take akan katifar hannunta yana dafe a mararta,jijjiga kai takeyi da alama ciwon yana matuƙar cin jikinta. Nice na kalli khamriyyah ta sauri kana nace, "Khamriyyqh barinaje na nemo mota mu koma asivitin,dama sunce idan wani abu ya faru to a koma da wuri" "Ahah bazamu koma can ba,asibitin garinnnan zamu kaita,munada buƙatar musan mai yake damunta da farko" Kallon alamun tambaya nayi mata,sai kuma nayi shuru,dan wanann ba lokacin magana bane. Fita nayi daga gidan zuwa gidan maƙwantanmu,yanada motar dayake haya,watakil zai iyah taimaka mana. Ina zuwa kuwa nayi sa'a yana nan,saidai yana shirin fita,dawowarsa kenan daga aikin,uzurina na bashi wanda hakan yasa ya amince. Tare muka shigo gidan na wuce ɗakin domin nuna masa,lokacin khamriyya ta aza kanta a cinyarta tana shafa mata ruwa. General hospital muka nufah da farko,amma ganin sunan asibitin da sukayi mana aiki yasa furr suka ƙi karbarmu,a cewarsu dole saidai mukoma inda akayi mana aiki. Kallon khmariyyah nayi wacce ta cije bazamu tafi katsinnan ba,to ina take so muje. "Dan allah yaya Sale ta ɗan kaimu Ali Maibara hospital mana" Karkara motar yayi zuwa can ɗin,dayake suma 24h suke buɗewa. Da sauri aka turata zuwa ɗakin gaggawa,saboda ganin yanda ta galabaitah sosai. Katinmu suka baƙaci mu bayar,nice nake riƙe dashi dan haka na fitar zan nuna musu,saurin maida hannu khamriyyah tayi tareda ɗan ƙaryar dakai tace, "Uhm dama ranki ya daɗa bamuje wani asibitin ba,jiya ta fara ciwon to dayayi tsanani shine muka kawota nan" Da kaman bazata yarda ba saboda ganin ɗinikin dayake kan cikin inno,amma kuma saita basar saboda ciwon ya warke garau,zata ɗauka maybe ba ciwonsa bane. "Toh shikennan yanzu zaku jiramu anan za'a kaita ɗakin scanning,zanyi ƙoƙarin saka file ɗinta da wuri saboda ganin halin datake ciki,kuna iyah zama kafin a fito da sakamakon. "Mun gode sosai" Shine abinda muka faɗa dukkanmu a tare,waya ƴar nokia ɗinnan khamriyyah ta daga tareda faɗawa maman yara inda muke,dan itama girma yafara kamata ciwon ƙafa take fama dashi,bazatayi mana sauri ba shiyasa muka taho,inyaso tazo daga baya. Ƙiran sallahr magriba ne ya tashemu a wajen muka shiga ɗakin da inno take kwance. Anyi mata scan ɗin amma dole saidai mujira gobe da safe kafin muji sakamakon,sun yimata allurar kashe zafi dai ɗazu,wanda hakan yasa ta samu bacci takeyi. Muna idar da sallahr ne maman yara ta shigo itada khariyyah da kular abinci a hannusu,sai a lokacin ma na tuna ashe fah inajin yunwa. Khamriyyah da maman yarane suka koma gida,inya so gobe da safe saisu dawo. Dan su fadeelah sai kuka suke suna ƙiranta,gashi babu kowa a sashennamu sai yara. Bacci dai rabi da rabi mukayishi,ga yanayin ƙasar tamu na sauro,ga kuma tashin da inno takeyi,wasu sunaye take ta ambata in mukayi magana ma bata ganemu kwata kwata. Wajen misalin ƙarfe bakwai khamriyyah ta dawo asibitin,hannunta ɗauke da flask ɗin kunu,ita kaɗai ta dawo maman yara tana gida . Nan muka cigaba da zaman tagumi bayan mun karyah,har zuwa lokacin da likitar ta turo muje mu sameta. Shuru mukayi dukkanmu muna sauraren mai zata zo mana dashi, "Kuyi haƙuri jiya lokaci ya ƙure shiyasa muka barku a duhu,maganar gaskiyah tiyatar da akayi mata a baya ta ƙoda tayi kyau sosai,saidai kuma rashin bin ƙa'idoji kafin ta warke ne ya jawo hakan,kasancewar yanzu ƙoda ɗaya ce da ita,dole sai tana kula,to saba dokar yasaka dole sai an mayar da ita anyi mata wankin wajen,mu bamayi a nan,zan rubuta muku takarda ku tafi katsina" Me mai take cewa,jinayi gabana yayi dummm data ambaci ƙoda,amya kuwa result ɗinmu ta faɗa,duk da ina zargin akwai wani a tiyatar amma ba har haka nake zargaba gaskiya. "Likita anya kuwa result ɗinmu kika faɗa" "Kwarai ma kuwa,akwai wani abune dayafaru?" "Ahah babu komai ,inaga tana cikin halin ruɗewane" Khamriyya ta faɗa tareda jana waje,kallonta nake ita kanta da mamaki,da alama tasan wani abun daban wanda ban sani ba ni. "Ke sabrah ki nutsu mana,kinaso ta gano asibitin da sukayi mana aikine,idan ta gano duk wani abu zatayi domin riƙemu a nan wajen" "Me kike nufi khamriyyah" "Hmmm abubuwa da yawa,bakiyi mamaki ba da daga kallon takardar asibitin general suka ƙi karbarmu,saboda zasu fuskanci barazana mai kyau idan sukayi hakan. Suna amfani da sunan wani ciwo si dunga ciran sassan mutane batareda saninsu ba,wanann dalilinne yasa suke iya ƙoƙarinsu wajen boye bayanan su,sannan suna da ƙarfi shiyasa kowa yaja bakinsa yayi shuru da aikin da,sukeyi" "Inna lillahi,muma muna ɗaya daga cikin wanda sharrinsu ya faɗa kanmu kenan,gashi sunfi ƙarfin hukuma inaga mu kuma,yanzu ykk ganin zamuyi" "Yanda zamuyi a fili yake,zamu koma asibitinne a yau" "Kuttt suyi mana wannan zaluncin kice mu koma kuma?,tabbas abinda zafi sosai,yana cinmu a zuciya,amma bazamuje ba su sake kashemu" "Bazasu kashemu ba,hasalima zasuyi iya ƙoƙarinsu wajen yiwa inno magani,kin manta su suka sakata a cikin halin,kuma sannan abinda sukayi suna iya ƙoƙarinsu wajen binneshi,shiyasa ma basaso wani asibitin su shiga cikin zancen. Karki damu zasuyi manaagani,sannan kuma zamu kokarin bin diddigi a can,abu ɗaya zamuyi shine . Karmu sake mu nuna musu cewar munje wani asibitin,kuma munsan abinda yake damunta,idan suka san hakan kuma dagani har ke mun zama shaƙaƙƙu" Tashin hankali kenan! Hantata ce ta kaɗa saboda jin bayanan da khamriyya tayimin,wannan wace irin rayuwace,mutum yana fama da talauci,ga kuma wahalar rayuwa,amma hakan bai isheshiba sai an ciremasa wani abin da allah ne yayi masa,bashida kuɗin sayarsa,amma su dasuke da watada naka ma bazasu bar maka ba saisun ƙwace,zuciyata ce tafara tafasa da kwakwalwata ta fara tunomin abubuwan da akayi ta mana a shekarunnan,kana ganinsu kasan tsagwaron zaluncine kaɗai,mugunta da kuma son zuciya. Komawa mukayi ɗakin inno,idonta biyu tana kallon silin,saidai bata jijjigar da cije baki irinna jiya kafin mu kawota,tausayinta ne yakamani da irin zaluncin da akayi mata,wanda kuma nasan ba iya ita kaɗai akayiwa ba harda dubunnan mutane bil'adama,inshaallah zamuyi iya ƙoƙarinmu wajen ganin bata san abinda ya faru da ita ba,dan hawan jininta zai iya tashi murasata gaba ɗaya a kowanne irin lokaci idan taji labarin. Karkatowa tayi a hankali tana kallon mu,yayinda wani siririn hawaye yake bin gefen kuncinta,babu abinda yake kan fuskarta face tsoron tafiyah ta barmu a wannan duniyah babu kuladamu,karisawa nayi da sauri na gurfana gwiwoyina a gaban gadonnata,nima zuwa sannan karfina ya kare na riƙe kukan. Jijjaga kai nake tareda furta magana cikin dashashshiyar murya. "Ahah ki daina irin wanann kallon,babu inda zakije inno muna tare,zaki samu sauƙi kawannan da izinin ubangiji" Khamriyyah ce ta shigo da paper a hannunta tana jingine da jikin ƙofah. Kallonta nake ganin tayi shuru batayi magana ba,inaga so take nazo muyi magana a waje. Sanin hakanne yasa na muka fita waje. "Sabrah na ƙarbo mana takardar sallama,sign sukayi akan sun turamu DR BUKAR INTERNATIONAL HOSPITAL,na karba amma bazamu tafi da takardar ba saboda kada sugane mun san mai ya sameta,zamuje kaman yanda sukace muje idan wata matsala ta faru" Ɗaga mata kai nayi kawai,danna san zata iyah ji da lamarin fiyeda mu gabaki ɗayah. Komawa ɗakin mukayi domin shirye shiryen tafiyah garin katsina a gobe,duk da munsan wajen amma ba ƙaramin aiki bane,ɗan kuɗin da muka ajiye na aikin da khamriyyah tayi da kuma zuwa shagon khariyyah,yanzu ma dole muka lallameta ta tafi,ogansu sai kiranta yake saboda ƙwarewarta a shagon. *****______******_______****** Karfe shaɗayah a asibitin tayi mana,da wurwuri muka fita danma mun tsayah a kan hanya abinka da motar hayah. Cikin sauri babu bata lokaci akan shirya mana dubata,dayake sunsan abinda suka shuka,masu dubatan jikinsu har rawa yake wajen yi da sauri,idan baka saniba ma dole sai kayi mamaki,duk wannan rawar jikin a banza babu ko sisi a Nigeria kuma,hakan ma mutum yasan bazaiyiyuba sam. Duk inda sukayi binsu kawai muke da ido ganin yanda suke aiki babu tsayawa. Wata matace zatayi shekaru talatin dai ta fito daga wani office mai daraja a cikin asibitin,idanuwanta jajur sukayi tana share hawaye,duk da tana iyah ƙoƙarinta domin kar a gane halin data ke ciki. Khmariyyah na kallah wanda ashe itama hankalinta yana kanta,duk wanda suka kawo marasa lafiyah harma da wanda suka dawo kamarmu sai murna suka suna sakawa asibitin albarka,mu kaɗai idan mai hankali ya kallemu zai gano munsan wani abu,amma dayake bakinmu a rufe muke shuru kakejinmu,dan gano munsani tamkar zama matattune. Wata nurse ce ta nufomu bakinnan a washe kaman gonar auduga. Munafuka na faɗa araina. "Sannuku yan mata,aiki ya kammala yanda akeso,munyi nasarar gyara mata tiyatar,yanzu babu matsala,amma duk da haka a kiyaye ka'idojin shan ruwanta da kyau" Tunda tafara maganar shekeke muke kallonta,jinake kaman na doketa,a wajen khamriyyah kam ma yafi haka. "Amma tiyatar appendix akayi mata,shin mai haɗin appendix da abinda mutum zai sha ma'ikaciyar jinya?" Ɗan murmushi tayi,amma daga gani na shiga zullumine. "Ehh....toh dama hakane mana,tunda akwai ciwo a cikinta tana buƙatar kare lafiyarta wajen cin abu mai kyau" "Amma kuma da farko kince abinsha,yanzu kuma abin sha,munyi bincike babu abinda ya haɗa tiyatar appendix da kuma shan ruwa marar kyau malama" Waigawa gefenta tayi,ganin babu wanda yake kallonta yasa ta jamu da sauri zuwa wani corridor,har gumi ya fara tsatstsafowa a jikinta na razana. "Kunga...nnnasan kuna cikin ruɗani gameda ciwon mahaifiyarku,amma ina rokonku da allah ku tsayah daga binciken dakukeyi,dan bazai haifar muku da ɗa mai ido ba. Wani abin zaifi kyau ka barshi a duhu daka haska da fitila kaga menene" Tana gama faɗin hakan ta dafa kafaɗar khamriyyah tareda yin murmushin takaici ta bar wajen. Ɗakin innon mukaje domin ganin aikin da sukace mana yayi kyau ɗin. A kwance take akan gado mai kyau da laushi,kaman gaske. Cije le'ben bakina nayi na ƙasa kafin na isa inda take kwancen,ba laifi kam daga gani muna saka ran tashinta lafiyah. Mun kwana kana mun waye amma har yanzu inno bata tashi ba,hankalinmu ya ɗugunzuma ya tashi,saidai kuma masu zuwa dubata akai akai sunce babu matsala sosai,zata tashi inshaallah. Mu huɗune a zaune da deen khariyyah sai kuma mu dama muna nan,maman yara kam munce ta zauna saboda ƙafarta,kulada gidanma da takeyi ya ishemu komai. Khairiyyah ce ta shigo ɗakin tana haki tareda sauƙe ajiyar zuciya,yatsanta kuma yana nuna waje,saboda kiɗima har ta gagara cewa komai. Dukkanmu kallon ta mukayi harda khamriyyah wanda fitowarta kenan daga banɗaki. "Bbbbaaaban su fadeelah,wlh shi nagani ya shiga wani office a cikin asibitinnan yanzu nan" "Ke khairiyyah kalau kike kuwa,ai wanann tsinannan mutumin kika gani kuwa,dama yana duniyar" Na faɗa da alamar tambaya. "Kutt harna kasa ganeshi,taya kike zaton zan manta da wanann fuskar a yanzu,kaman su ɗayah dasu fadeelah idan kika ganshi,yafi kama dasu musamman idan kinganshi da rana,shida wani ne mai baƙin glass. Da alama kuma sunada matsayi a asibitin,dannaga kowa yana gaishesu" Tashi nayi da gudu zan fita khamriyyah tayi saurin riƙoni tareda cewa. "Bakida hankaline sabrah,me kike shirin yi haka,kinsan wane irin garaje kike ƙoƙarin aikatawa kuwa? Da manyan mutane kike ƙoƙarin haɗa sabga,wanda shari'ah ma ta kasa yi musu komai,(wani murmushi tayi bayan ta ɗauke hannunta daga kan kafaɗata). Kibar komai a hannuna sabrah,cikin sauƙi da dabara zamuji da komai,bilahillazi jinin maryam da kuma budurcin anty juwairah harma da ranta da kuma hakkin su fadeelah bazai tafi a banza ba,sannan kuma inna gama dashi na dawo fansar ƙodar inno,babu wanda zai sha a hannuna daga cikinsu,zamu nuna musu muma mun iyah dabanci da iya shegen" Dukkan mu shuru mukayi muna jinta har tafita daga ɗakin,komai zata iyo allah masani. Ganin wasi wasin ina zataje bazai kaini ba yasa na bita da sauri,amma ina fota babu ita babu alamarta,waige waige na fayi ko zan ganota,can na hangi wata mai shara da goga na ƙoƙarin shiga office ɗin MD ,har tazo shiga ta tsaya tareda juyowa inda nake ta ƙiftamin ido. Wani numfashi naja na razana ganin waye sanye da kayan,khamriyyah ce tasha wata ɗamara ga baƙi tashafa a fuskarta ya maida itah baƙar dole,yaushe har tayi wannan shigar na faɗa a raina. Dukkanmu sauke ido mukai akan khamriyyah wacce tashigo da kayan masu goge gogen a jikinta tana haki, "Maza maza ku shiryah munada aiki babba,nagano anguwar dayake zaune,a yau basai gobeba nakeso mu gama dashi,saboda akwai abinda muke buƙata daga wajensa" "Ke khamriyyah me kike faɗa,taya zamu gama dashi,tukunna ma ya akayi kika gano inda yake " "Na'urar da khairiyyah ta haɗa a shagonsu ta bin diddigi nasaka masa a motarsa,sannan kuma riba biyune,naji yanacewa zaije sirrinsa,kunga zamu san inda yake,abinda muke buƙata shine motah" Nuna deen tayi da yatsanta wanda yayi sororo yana kallonta, "Mekikace,ni zan jaku zuwa inda za'a hallaka mu,inaaa bazan fara ba" "Hmmm zakace haka mana,nasan zaka faɗi haka,shin kamanta abinda yayi mana ne,kuma har yanzu yake kan yiwa wasu,amma duk da haka mu barshi ya cibaga da yin abinda yake so,ku zaku iyah mantawa da abinda yayi ku cigaba da rayuwarku amma ni bazan iyaba,sannan bazan tirsasaku ku tayani ba,zanyi ni kaɗai a ƙashin raina" Yanda take maganar kanaji kasam daga ƙasan zuciyarta maganar take fitowa,idonta ya ciko da hawaye amma da sauri ta mayar dashi kaman yanda ta saba. "Ta wane bangare zan taimaka" Khariyyah ta faɗa tana kallon khamriyyan,kuma yanda tayi magana babu alamar ja da baya. "Ki taimaka mana da tracking ɗinsa,dama na saka masa na'urarki a motarsa" Nima ganin hakan yasa na ce "Toh bari mu gwada training ɗi aikinmu muga ko zaiyi aiki?" Kowa murmushi yayi a cikinmu,da alamar aiki zai soma. Inno kuwa tana kwance bata farfaɗoba,bamu da matsalar barinta,dan munsan zasu kulada itah tamkar muna nan. Farawa mukayi da aron mota wacce zamu bisu,amma saida muka cire lambar motar tukunna. Tafiyah muke muna bin danjar dake screen ɗin wayar khariyyah har muka fita daga gari. Nidai zancen gaskiya tsoro yafara ɗarsuwa a raina,idan suka kamamu kuma fah ya zamuyi kenan. Toh allah dai ya tsare shine addu'ar. A bakin wani baƙin gida suka tsaya a dokar daji,tsittt kakeji babu kowa a wajen sai ƙarar tsayawar motarsu a can baya cikin bishiyoyi. Wata riga naga khamriyyah ta ciro jaaa mai ɗan karamin hijab,dukkansu kallona sukayi ganin ta mikomin kayan,ni suke nufi wai zanje. "Kije bayan bishiyar can kisaka kayannnan,a maganar dasuke naji za'a kawomasa wata yarinyah daga club,dan haka zakije a matsayin itace,basai na faɗamiki ba kinsan yanda zakiyi,ga takardar nan ki ɗan duba bamuda lokaci" Ta ƙarisa maganar tana miƙomin wata ƴar kwalba,ko ban faɗaba nasan magani fitarda mutum a hayyacinsa ne. Jikina yana rawa cikin dauriyah na karbi rigar da niyyar sakawa,yanda nake tunanin zan gwada basirata anya kuwa zan iya?. Bayan na gama saka rigar mai shegen kyau,wanda itama a hanya muka ɗaukota a wani shago,ina mun gama saimu biyasu,kwalliyah tayimin sama sama,daga nan kuma na nufi hanyar gidan kirjina na dukan uku uku. Kaina tsaye na nufi hanyar shiga wajen,a zato zasu tsareni sai kuma naga sun matsamin na wuce. Yanda nake tunanin wajen ba haka yake ba ta ciki,wajen aljannar duniya,ga kuma lunguna kala kala kaman wani masana'anta,maganar da akayi min ne yasani zaburah na waiga bayana. "Kece miss Suhailah?" "Eh....eh nice" "Ranki ya daɗe to nan zaki bi,zuwa sashen ogah" Ɗaga kai nayi tareda binta ina rausayah kaman wata bishiyah lokacin damina. Tafiyah muke waje daban daban,har muka isa waje dayafi ko ina kyau a ginin. Murɗa kofar tayi nasaka kai a cikin falon,wowww aljannar duniyah kenan,wani turnuƙuƙin baƙin ciki naji yana cina,yayinda duk wani tsorona ya bace a cikin zuciyata,ya cutar da mutane ya kashe mutane yayinda wasu ya keta musu mutunci,shikuma yana nan a zaune babu abinda ya dameshi,harkar gabansa kawai yakeyi. Kallonsa nake yana tsaye da riga marar hannu a jikinsa,sai three quater wando,murmushi yakeyi har dimple ɗinsa yana motsawa. Mai kyan ɗan maciji kenan,dui yanda zanyi sai na bada gudunmawa wajen duomiyar da rayuwarsa shima,kaman yanda ya dulmiyar da ta wasu rayuwar shima. Koni ko kuma shi!!!!........ Taku _sadi-sakhna_ Ƴar mutan jama'are. *MABARACIYAH* _haƙƙin mallaka_ _*sadi-sakhna*_ (Yar mutan Jama'are) 25••26 Shu'umin murmushi nayi saurin yi tareda kashe ido ɗayah. Ga mamakina kuwa saina ga ya narke wa kallon nawa,duk da ba wata kwalliya nayi na azo a gani ba,sannan kayana basu wani nuna tsaraici ba,abu ɗaya nasani shine inada kyau sosai. "Barka da zuwa duniyar saifuddeeen ƴan mata,ki saki jikinki ko kawashi ɗaɗi da kuma daulah,allah ya kashe ya baki" Ya faɗa cikin dashashshiyar murya irin ta ƴan bariki,jinayi kaman nayi amai saboda amon maganarsa,amma haka dole na daure tareda ƙaƙalo murmushin dole. "Nagode da wannan damar daka bani,nima zanyi ƙolarin shayar dakai ruwan daɗi daga korama ta mai ɗanɗano" "Hhhhh inajiran wanann daɗi baby" Ya faɗa yana shafa gefen fuskata,juyawa yayi ya shiga wani ɗaki,babu yanda na iya haka na bishi,indai inason cimma burina to dole saina daure. Sakin baki nayi ina kallon katafaren gadon dayake girke a tsakiyar ɗakin,badan komai aka sakashi ba sai dan sabon allah,kai azubillah. Zama yayi a bakin gadon yana ƙaremin kallo. "Babby ke kyakykyawace sosai,barina shiga banɗaki na dawo,kafinnan na yi oder a kawomiki abin motsa bakii. Yana gama faɗa ya cire rigar saman tareda wurgata akan gadom yashige banɗaki dagashi sai ɗan wando. Wata ajiyar zuciyah na sake daya bacewa ganina,anya kuwa zan iyah,tabbb ban taba ganin zingimemen mutum haka ba rigaba,yau gashi na gani ƙiri da muzu. Wata matace ta shigo dauke da faranti da lemuka akai kala kala,ajiyewa tayi a gabana bayan ta gaisheni tareda ficewa da sauri,da alama tana tsoron kar ya shigo ya gantane,haka kawai naji ban yadda da zaman ta a wajen ba,daga gani dole akayi mata abubuwan datakeyi. Saurin tsiyanya lemon nayi a kofi danaji motsin fitowarsa,hannuna yana rawa na zuba maganin tareda kaɗawa dan karya gani. Tundaga fitowarsa da yanayin kallon dayake min ya nuna alamar akwai wani abu a ransa. Ina nan zaune ya saka wata ƴar karamar riga fara da kuma farin wando,ƙaryah nake ma idan nace bayyi kyau ba,da haka suke yaudarar mata,nima kuma saina fara yimasa kallon na folawa halittatar tasa,duk da ta ciki kaman zan fashe dan tsoro. Zuwa yayi gefena ya zauna,yayinda kamshin turarensa ya cika hancina.. Lemon dayake kan tiren na ɗauko tareda miƙamasa ina murmushi,yayin da nikuma na kai wanda yake hannuna baki. Saurin riƙe hannuna yayi tareda karbar lemon,wanda na miƙa masa kuma ya kaishi saitin bakina,ɗan zaro ido nayi ganin mai yake ƙoƙarin shirin yi. "Hmmm me kike zato,kina nufin bansan bake nayi booking ba,ina hankalinki ya shiga da kika kasa ganewa saida naga wacce na zaba kafin nayi booking,ke kuma saiki zo kawai kuma na yarda dake,hhhhh da haka nake da tuni an gama dani,saboda mutane bila adadin na barazanar ganin bayana. Yanzu in kina so ki fanshi kanki to ki shanye wanann lemon yanzunnan" Ya faɗa yana miƙamin na hannunsa,babu yanda na iyah haka na bashi nawa tareda karbar nasa mukayi musanye. Ɗagawa nayi na sha kusan rabi kafin na ajiye,yayinda shikuma ya shanye wanda nake ƙoƙarin sha. Shuru mukayi babu mai cewa komai can sai naga ya fara gyangyaɗi,aikin yayi kyau yanda ake so. Kallon idonsa nayi ina dariyah, "Mai kake nufi kaima,a zatonka dama sha zanyi,jira nake ka karbi nawa wanda shine mai sinadarin a ciki,wanda na baka da farko babu komai a ciki,dama na san kana zargina,sannan kuma nasan ka gane bani kayi booking ba,dayake ance rana dubu da barawo rana ɗaya ta mai kaya,shiyasa ka barni har nazo i yanzu a wasan,yanzun dai ka shirya ga baƙi nan shigowa" Layi yake tayi amma yana ta iya ƙoƙarinsa wajen ganin bai bari abin ya cinyeshi ba. Ɗaukar wayah nayi tareda bugawa su khamriyyah wayah. "Kun gama shiryawa,toh na bashi yasha,yanda kikace kuwa haka ya kasance,yanzu zan kurma ihu sai ku shigo bayan minti biyar" Inagama kashe wayar na kifta masa ido daidai lokacin dayake fadawa kan gadonnsa,nikuma nayi waje da gudu ina ihun ya faɗi. "Wayyo jama'a kuyi sauri ya faɗi yana fitowa daga banɗaki,nakira motar asibiti ma suna kan hanya" Muna cikin hakanne khamriyyya suka shigo itada khariyyah da kuma deen,sun sha uniform kaman ƴan asibitin,dan dama munyi shiri tun rana kafin muka zo wajen. Da sauri suka kinkimeshi muka nufi waje dashi tareda sakashi a motar. Securityn kuma suka nufi motarsu domin binmu a baya,danni ma ana sakashi na shiga da sauri ina kuka. Dukkansu key sukayiwa motocin amma suka ƙi tashi,wannan aikin deen ne,kafin suyi wani abu tuni mun bace a cikin duhun daren,sai kurar motar kawai. Tafiyah muke cikin gudu,duk da munsan bazasu iyah biyomu na amma saboda tsaro. Sai wajen goshin asuba kafin muka tsaya a wani ƙauye nesa da garin katsina kaɗan. Wata bukka muka shiga tareda daɗɗaureshi a ciki tamau.. A daren khairiyyah da deen suka koma cikin gari wajen inno,yayinda khamriyyah kuma dani muka zauna. Kasa jure tashinsa khamriyyah tayi,hakan yasa ta ɗebo ruwa a wani masaki a gefen rafi ta shaƙa masa akansa. Wata zabura yayi tareda jan numfashi yana ƙare mana kallo,tambaya ce cike fall a bakinsa amma ya gagara furtasu. "Kana mamakine malam saifu,shari'ah ta gagara ɗaureka mukuma mun ɗaureka koh,wanann ba wani abin damuwa bane,yanzu dai abu ɗaya zuwa biyu muke so. Na farko information akan dr bukar zaka bamu,na biyu kuma wannan akan ka ne,yanzu dai fara bamu na farkon. Kuma karkayi gigigin ƙin bayarwa,wlh kasheka zamuyi mukashe banza mu bar wajennan." Duk da yana ƙoƙarin dakewa amma daga gani warninng ɗin khamriyyah ya shiga kwanyarsa sosai."meyasa kuke buƙatar information akansa?" "Kana tambaya ne dan karmu cutar dashi kaman yanda mukayi maka,toh illatashi zamuyi da mun samu da bamu samuba. Mun riga munsan cewar yana amfani da jinyar talakawa yana cire musu ƙoda daya,sanann kaikuma idan ka ɗauko yara mata daga gidan marayu ta taimakon yaranka masu zuwa a matsayin ma'aurata marasa ƴaƴa,saika siyarmasa da tsada bayan ka gama lalatasu ta hanyar yimisu fyaɗe da sauransu,shikuma idan ya cire ƙododinsu saiya kashesu,ka faɗamin abinda nasani daya wuce wannan." Diridiri ya farayi,dan bayyi zaton munsan har wanann kason daga cikin aikinsu ba. Dariya khamriyyah ta sheƙe da ita wacce banyi zaton ta iyata ba, "Mungama da wanann zangon idan ka zayyano min yanzu da bakinka" Ganin da gaske ba imani a cikin ƙalbinta yasa ya fara koro bayanai harda wanda bamu sani ba har ƙarshe. "Yawwa to yanzu faɗamana lambobin asusun bankink" Ƴar dariyah yayi tareda cewa "Nidama nariga nasani kuɗine yasa kuke wanann wasan,tun farko nace muku ku faɗa,idan kidnapping ne da yanzu ankawo muku kudinku na tafi,neman ai harda saboda iriku muke tarawa" "Eh duk naji mai kace,yanzu dai faɗamana asusun banki" "Bazan faɗa muku lambobina ba,ku faɗi nawa kuke so na baku kawai,idan ba haka ba kuma ku rasa gabaɗaya,dannasan yanzu ana ta nemana,babu daɗewa za'a kamaku,zuwa sanann kuma ku ji tausayin kanku" Wani drill khamriyyah ta dauko tareda sokashi a kan cinyarsa,dan tsabar tsoro nima saida na juyah,ga ihun sa ya cika wajen,banda jinin dayake ambaliya a cikin bukkar. Fitar dashi tayi ta nufi maƙogaransa,da sauri ya riƙe hannunta yana jijjiga kai,har sannan ihu yake muryarsa har ta dushe. "Zan.........zanfaɗa wlh zan faɗa" "Yaron kirki,nayi zaton ai kaizaka fara rasa ranka kafin mu rasa namu muzama abin tausayin" Numbobin yafara faɗa,daga ɗaya bangaren kuma khairiyyah tana jinsa har ya gama. "Yawwa aiki na biyu ya kammala,saina ukun ka kashe kunnenka kaji mai zan faɗa,yanda harka mutu maganganun zasu dunga taroyowa a cikin kanka. Bazan kasheka ba duk da inada muradin hakan,kasan dalili?....saboda ƴaƴanka danake matuƙar so a rayuwata,taya zan fuskancesu nace musu na kashe ubansu,duk da a wajensu kai mataceccene dan haka nake faɗamusu. Saidai zanyi musu abu ɗayah,zan dakatar dakai daga yimusu ƴan uba,zan datse ƙarfinka na maza,sannan kuma da sake haihuwar wasu yaran,dan dama hakan shine hukuncinka a kotu wanda batayi maka ba" Ihu ya fara jin furucin abinda ta faɗa,nima kaina na razana dajin abinda ta faɗa,duk da a cikin raina naji daɗin hakan,koba komai zuciyata zatayi sanyi da abinda yayi mana. Gudumar da take gefenta ta ɗauka bai ankaraba ta sauƙe akan gabansa,dan azabar data jiyarceshi ko ihu kasawa yayi,sai tsayawa kawai yayi yana kallon yanda take murmushin daɗin ɗaukar fansa,kafin yayi yaraf akan kijerar sumamme. Ƙarar wayar khariyyah mukaji,datake hannuna, "Ke sabrah kuyi saurin barin wajennan dan angano motar nan ta taho,sanann kuma an sallami inno Ta tashi jiya da daddare,kuma babu matsala" "Ya zancen kuɗin kin cire" "Dukkama kuwa,na ciresu tass ban bar ko kwandala ba a ciki" "Dakyau gamunan zuwa yanxunna toh" Figar hannunta nayi muka fita da gudu karmuje su samemu a wajen. Muna fitah muka samu mota mai zuwa cikin gari muka ɗale,bamu tsaya ko ina ba sai bakin asibitin. A zaune muka samu inno khariyyah tana haɗa ɗan kayan da mukaxo dashi. Ita kuma tana zaune akan gadon,turus mukayi tareda inda inda bamusan mai zamuce mata ba idan tace daga ina muke. "Mukan muna shirin tafiya ai,da bakuyi sauri ba bazaku samemu ba,kunacan gidan ƙawarku" Ajiyar zuciya nayi tareda dariyah danaji ashe khariyyah ta boyemu ma. Mun fito zamu tafi gida,daidai lokacin kuma ake shigowa da saifuddeen a gadon asibitin,duk jikinsa jini ne babu inda kansa yake. Kallon khamriyyah nayi wacce ta ɗaga min gira tareda yin murmushin gefen baki,suma su deen murmushin sukayi,ma'ana aiki yayi yanda ake so. Bayan kwana biyu da dawowarmu jikin inno yayi sauƙi sosai,dan yanzu tunda babu yanda zamuyi munsan mai yasameta to munabin ƙa'idoji yanda ya kamata,har sanann bamuyi zancen kuɗin da muka kwaso a asusun saifuddeen ba,gashi sai neman wanda sukayi danyen aikin akeyi a gari. A zaune muke dukkanmu a bayan gidannamu,ganin kowa yana nan yasa na taso maganar kuɗin da khamriyyah tace na mu kwaso. "Khamriyyah bakice komai ba akan wanann kuɗaɗen har yanzu" "Aikinsune bai zo ba shiyasa,nawane kuɗin duka duka" "Miliyan Hamsin ne 50M" Khariyyah ta faɗa. "Iya kuɗinnasa kenan ma" "Ahah ina tunanin ba iya nan yake ajiyewa ba,wannan ƙaramin asusu ne" "Shege yana ganin taurarin mutuwa amma son kuɗin yana ransa,dama duk a nan suka hallaka ai. Inaso mu gina gida a garin katsina,sannan muyi karatun daya kamata yanda zamu iyah tunkarar sauran,domin rashin ilimin bazai kaimu ba,sanann zan kulada rayuwar su fadeelah a cikin kuɗin,harma da karatunsu,idan nasamu aiki kuMa saina cigaba da kuladasu da kaina,ta haka zan biyashi kuɗinsa,dama na ubansu ne ai,gadone basuda shi amma sunada hakkinsa " Ihu muka saka dan dama kowa yana son zuwa makarantar,maganinsu kenan adunga kwashe kuɗin Sai a sanann na tuna ashe ina som zuwa Alqalam,makarantar tanayiMin a rayuwa,ita kuma khariyyah wai makarantar computer technology takeso,shikuma deen atbu,yanason Mechatonic Engneering. Mai gayyar kuma karatun State security zatayi(SSS), saboda sajewa a cikin masu bincike. Tun daga lokacin muka fara shirin abinda mukace zamuyi,dan har mun riga munce daga wannan babu abinda zamu sake,bayan dr bukar,kowa zayyi karatu yakama abinda yafi. Wata rana muna tsaka da shirin tafiyah makaranta saiga wasu mutane daga katsina,sunzo nemanmu,babu bata lokaci aka saka ankwa a hannunmu nida khamriyyah,wai angano mune mukayi wa Asibitin dr bukar sharri,kallon kallon muke akan yaushe hakan ta faru,saidai babu wanda zai ji mu bare bamu amsa. Inno tana kuka muma munayi sai kurku a garin katsina,abinda bamu saniba ashe angano cewar munsan mai yake faruwa a asibitin nasa,daga bakin wanann nurse ɗin,kuma ctv camera ta ɗauki khamriyyah lokacin datake saka kayan masu aiki zata shiga office ɗin dr bukar,saboda jin mai saifudddeen zaice,kuskuren damukayi kenan wanda muna ganin mun gudu ashe bamu tsiraba. Sannan kuma shaidu sun nuna mun je asibitin Ali Maibara kan zancen. Kai mutane dai ba'a iya musu a rayuwa. Kwanan mu uku a kurku babu wanda ya waiwayemu,banda wuyah da ƙazanta babu abinda muke ciki. Sai a kwana na ukunne aka shiga kotu kan sai mun amsa laifinmu a gaban alƙali. Duk yanda aka kawo shaidun ƙaryah wai wani ne ya sakamu muke ƙoƙarin shafawa asibitin kashin kaji,dan haka dole mu amsa laifinmu. Barr shehu ne ya fito tsakiyar kotun idonsa kyam akanmu. "Malamai shin zaku iya faɗamana sunanku na gaskiyah?" Har zanyi magana khamriyyah ta dakatar dani tareda cewa "Sunana khadija ita kuma zainab,dukkan mu a gidan marayun daurah muka taso" "Shin menene yasakaku yiwa asibitin dr bukar sharri,akan cewar yana kashe mutane,sanann an ganku a asibitin kuna bin diddigin ma'aikaciyar lafiyah,sannan kuma ke khadija kinyi baɗda kama zuwa cikin office ɗin shugaban aaibitin. Bugu da ƙari kuma kun shiga ɗakuna da dama kuna yaɗa musu ƙaryar cewar kashe mutane ake a asibitin,bayan kuma ba iya jahar nan ba hatta nigeriyah kowa yasan karamci da kuma taimako irinna wanann asibitin" Cikin ɗaga muryah khamriyyah tace. "Wannan ƙaryane ba haka akayi ba,kawai sharri ake yimana" Yana jin ta faɗi haka yayi murmushi,dama abinda yake so kenan,wasu mutane ya ƙira maza uku mace daya sai kuma wanann ma'aikaciyar asibitin. Dukkansu tambayarsu akai ɗaya bayan dayah,amma amsa iri ɗaya suke bayarwa kan cewar dagaskene munje mun faɗamusu kashe mutane ake a asibitin. Wasu kanma hadda ƙarinsu,kanaji kasan ƙaryah sukeyi,dan ko ganinsu bamu taba yi ba sai yau,idan aka cire nurse ɗin Duk da bamuda hujjah ko guda ɗayah,amma mun ƙi karbar laifin da bamuyi ba,wanda hakan yasa aka ɗaga ƙara sai gobe da safe. Turamu aka sake yi zuwa wanann baƙin ramin,muna kallon idonsu inno,baya khariyyah da idonta yayi luhu luhu kaman garwashi. Bayan mun koma wani garin kwaki aka bamu babu ƙarago babu suga,haka muka cusashi a cikinmu. Can kaman misalin karfe shabiyu mukaji motsin mutum yashigo cikin cell ɗin. Saurin tashi nayi na ƙanƙame khamriyyah wacce itama ta buɗe ido. Mai aikin wajenne da fitila a hannunsa da kuma wayah. Bayyi magana ba sai haskamu dayayi tareda nuna mana gaban wayar,brr shehu ne a zaune akan kujera,gefens kuma dr bukar kana ganin wajen kasan aljannar duniyane. "Nasan kunyi mamaki koh,toh muna so gobe ku amshi laifin da'aka ɗoramuku a gaban kotu,idan ba haka ba kuma,sai mun halakar da duk wani rai dayake wanann gidan marayun,sannan kuma kubi bayansu,saiku zabi ɗayah,idan kunada wayo kuyi yanda mukace muku,abubuwan dakuka sani kuma ku zama makafi sannan kurame akai,idan ba haka ba kuma hmmm gargaɗine ƴan yara,ku tuna bakuda ikon yin komai akai" Suna gama faɗin hakan wayar ta mutu,mutumin ko magana bayyi mana ba yafita daga cell ɗin tareda maida wajen ya rufe. "Khamriyyah anya kuwa ba wani abu suke nema daban ba,ba iya wancan ba" "Sai yanzu kika sani sabrah,hmmm da iyah wancan ne da yanzu sun kashemu har lahira,yanzun ma inaji a jikina suna gama wannan abin zasu kashemu,saidai in dabara zamuyi. Gobe zamuyi musu abinda suke so,amma karmu yadda mu shiga motar dazasu kaimu gida a cikinta,idan ba hakaba kuma kinsan sauran" Zaro ido nayi ina kallonta sai kuma yanzu nakulada hakan. Washagari da'aka bamu laifin bamiyi taurin kai ba,ta inda mutum zai gane shari'ar ta son kaice ba'a tambayemu dalilin daya saka mukayi ba,ko suwaye suka aikomu,saima wani batu da mukaji alƙalin ya zayyano,wanda shiya bamu tabbbacin shima ɗan cikinsu ne. "A bisa shaidu da aka kawo da kuma yanda masu laifi suka amsa lafinsu,kotu ta yanke zasu biya tara naira miliyan 60,saboda abinda sukayi mai girma ne sosai. Amma kasancewar a ƙarƙashin gwamnati suke itace iyayensu,toh gwamnati keda alhakin biyan wanann kuɗin,lawyarn gwamnati ko kanada tacewa?" Wani ne ya tashi a jerin lawyoyin tareda matsowa gaba. "Eh wato ranka yadaɗe,madadin biyan kuɗin gwamnati da bawa dr bukar wanann gidan marayu a matsayin tarar daza'a bashi,saboda bisa la'akari da abubuwan dasuke faruwa a wajen dama,ministern kulada fili sai yasaka hannu" Tafi suka ɗauka manyan wajen tamkar suna ɗakin taron siyasa. Da saurinsa ministern yazo yasakaa hannu a takardar tareda miƙawa alƙali. Shikuma ya miƙawa dr bukar takardun filin,wanda ko mahaukaci yasan wanann shari'ar wasace kawai. Dukkanmu sakin baki mukayi muna kallon abinda yake faruwa,kaman an haɗa drama,su kuma ko kunya basaji a gaban mutane lallai sunyi nisa basajin kira.. Yanzu ina zamu shiga kenan,nidama nasan akwai abinda suke so shiyasa aka yi mana haka,tamkar tumaki gaskiya idan bakada galihu ka shiga uku a rayuwar nan. Dayake sun samu abinda suke so nan da nan aka sallamemu harda motar dazata mayarmu gida. Mutane sai kallon banza ake mana,wasu suna allah wadaran naka ya lalace,wasu kuma na laifin iyayenmu ne,kowa da abinda yake faɗa. Duk baƙin jinin dazasu jawo mana bai damesu ba,mu tamkar dolly muke a wajensu su wana yanda suka ga dama,saboda babu wanda zaibi bayanmu kowa nasa ɗan yasani ba marayu ba. Anzo fita a garin katsinan kuwa mukayiwa direban wayo akan cewar zamuje wani waje,duk yadda yayi damu mukaki komawa motar bayan fita,ƙarshe ma guduwa mukai cikin jeji,da alama bai san wani abu za'ayi mana ba dam haka bai takuraba yaja motar ya koma cikin gari. Mu kuma muka Hau motar garinnamu. Bamiyi garajen zuwa gidaba sai muka tafi wajen a anguwar tamu,saboda tsaro. Kafin dare kuwa labari hatsari direban ya haɗa gari,ashe dayar motar tasa a since take,hmmm kisa baya yimusu wuyah,gashi motar kamawa tayi da wutah saboda abinda aka saka a cikin man motar. Dan haka babu wanda yasan mun mutu ko kuma munyi rai. Ko sati ba'ayiba dr bukar yakori dukka yaran gidan da kumamu gabaɗayah,dayake nida khamriyyah bama son a gane muna raye ,iyah su deen ne suiayi ta ƙoƙarin maida yaran zuwa gidan wani marayun. Maman yara ma tafiya tayi,itama inno da mukace mata makaranta zamu tafi sai tace zata ɗauki su fadeelah su tafi kyauyensu, Khamriyyah ce ta hana ta akan itama fama take da kanta,tunda gidanmu na katsina da muyi an gama acan zamu zauna kawai sai a samo mai kulada su idan khamriyyah ta tafi makaranta,tunda acan zatayi karatun. Jin haka yasa inno tace zata zauna dasu wanda hakan yasa mu yin murna,dan dama abinda muke so tace kenan kada ta tafi. *****______*****______***** Haka muka cigaba da karatunmu cikin jajircewa saboda cika burinmu na ɗaukar fansa musamman yanda dr bukar yagina asibiti a filin gidanmu yana more rayuwarsa kaman bayyi komai ba. Bayan khamriyyah tashiga tawagarka ne nikuma nayi amfani na salona najawo soyayyarka gareni saboda aikin yayi mana sauƙi,amma bayan wannan zamana dakai da kuma soyyayata duka gaskiyace a gareka Sadeeq,ina sonka har raina,sanann banida nufin cutarwa a gareka ko kuma ɗan mu dayake cikina,ka yarda dani akan hakan. Wanann shine abinda zan iya sanar dakai daga cikin rayuwarmu,abinda ban gaya maka ba kuma toh wanann sirrinmu ne. Sauran masu yi mana aiki kuma duk yawanci mun haɗu dasune a cikin wanda suke gidan saifuddeen, irin yanda ya kama maryam.Dr nawwarah ce kawai muka haɗu da ita a asibitin dr bukar,dama tana neman fansa akansa na mutanen dayake kashewa,cikinsu harda ƙaninta. Kayi haƙuri da abinda nay imaka,bazan iya fuskantarka yanxu ba har sai ka gane gaskiyata,idan ka fahimceni to ka nemeni mijina,a shirye nake na karbi duk abinda zaka yimin matuƙar ba saki bane. Ina sonka sosai,daga matarka Sabriyyah (Amrah). To mutane back to business inda muka tsaya😀😀😀 Taku _sadi-sakhna_ Ƴar mutan jama'are. *MABARACIYAH* _haƙƙin mallaka_ _*sadi-sakhna*_ (Yar mutan Jama'are) 27••28 Lokacin da dec. Sadeeq ya gama karanta littafin rayuwar sabrah shuru yayi ko motsin kirki ya gagara yi,tamkar ba a duniyar ba haka yake jinsa. Taya ake tunanin kwakwalwarsa zata ɗauki abubuwan daya ke ganin tamkar a cikin film suke gudana,duk tsawon zaman dayayi da matarsa da soyayyar daya nuna mata shida danginsa ashe ita bai ma santa ba kwata kwata,ta aureshine badan allah ba saidan wani kuɗuri nata. Duk da ta fadamasa soyayyarta ta gaskiyace amma taya zai yarda da wanda yayi mada wanannan karyar,gashi ƙarin abinma cikinsa ne a jikinta. Sannan soyayyar sa gareta tasa yakasa ganin laifinta a cikin lamarin,duk koda daukar fansane to sunada laifinsu suma. Anya ma kuwa zai iya cigaba da wanann binciken,yace ya kama wa to,ƴan uwar matarsa,saboda nayi musu laifi sun ɗau fansa,kokuma yakama matartasa wacce take ɗauke da cikinsa ya kaita kotu,wacce yake mutuwar so,inaaaa bazai iyah hakan ba gaskiya. Inama zai saka kansa yaji daɗi da wannan lamarin mai cikeda hargitsi. Jefar da littafin yayi idanunsa yana zubar da hawaye,gabaɗaya duniyar da juya masa baya a ƴan wasu daƙiƙu. Murza gashin kansa yayi tareda zamewa ya kwanta akan gadon,bacci barawo ne ƙadai yasamu damar sanɗawa kusada shi ya ɗaukeshi. Saboda yasamu yasamu salamar tunanin da sukayi masa kwanya a cikin kansa,wanda kashi mafi tsoka na tunanin duk na sabriyyah ne. ****_____*****_____***** Khairiyyah ce a zaune inno sai faɗa takeyi,ta inda take shiga ba tanan take fitaba,dan dawowarta kenan daga garinsu bayan wata biyu da tafiyarta. Daren jiya ta dawo nan taji labarin wai ƴan bincike sun kama khariyyan a wajen didi,wacce take kulada su fadeelah. "Kai ɗiyannan kun iyah jawo magana,kuba maza ba ba komai ba kusaka burin daukar fansa a kanku,kowa yasan abinda akayi muku da ciwo,amma inaku ina faɗa da gwamnati,idan an kasheku akwai tsiyarsu ne a ciki," Daga ido tayi ta kalli sabriyyah wacce tashigo tana sunne kai,da alama itama tasan zata kwashi rabonta. "Ke kuma me kike a gida da tsakar rana haka,ina sadiqun?" "Hmmm dama inno ya gano cewar ni ƴar uwar khariyyahce lokacin daya kamata a wajen aikinsu,shiyasa na taho saboda karyaje ya sameni a gidan" "Tabb me na fadamuku tunda farko,amma kuka ɗauki aure a wasa kuka kitsa komai,idan na nuna bana so ma sai anyi a bayan idona,yanxu toh kike nufi,ya sakeki ko kuma kin taho shikenan ki zauna da aure a kanki,yanzu ya kuke tunanin zuciyarsa zatayi kenan,ita waccer ta yaudareshi suna aiki tare,ke kuma matarsa ya gano bakinku ɗayah,kya taho ai saiki zauna kiji mai zaice koh?" "Inno kiyi haƙiri banaso ya sakeni ne idan yaje gidan,ina sonsa sosai" "So? Mai so bazatayi abinda kukayi ba sam,yanzu tunda anyi haka sai ku sake yin wani abun kuma,gaki da ciki,mezaku faɗawa danku toh" Zugum zugum sukayi inno tayi ta surfah faɗa har tayi ta gaji tukunna ta shige ɗakinta,saida ta bar wajenne tukunna sabrah ta matsa kusan khairiyyah tana kallon fuskarta wacce tayi jaa saboda mari "Ke khairiyyah ya jikinki" "Kai sabrah sai kace wata khariyyan da,babu komai zai sabe,amma kaman yanda inno ta faɗa yakamata mu daina fansar nan haka,duk wanda yayi ma yake shida allah yanzu" Warwara ido sabrah tayi tareda cewa "Wlh dan sun ƙarene,da badan haka ba suma sai sunji a jikinsu tsabb,tunda babu wanda yayi saura a cikinsu bai ƙarbi hukunci ba shiyasa aiki ya ƙare,Sadeeq kuma karki damu zamu sasanta,duk inajin tsoro sosai,amma bakomai na bar masa littafin tarihina a ɗakinmu zai san komai da ake ciki,daga nan sai ya yanke hukuncin tsakaninmu dashi" Tashi sabrah tayi ta nufi ɗakin khairiyyah da ƴar jakarta ta kayah. Ita kuma khairah ta bita da kallo tareda jijjiga kai. Deen ne yashigo gidan hannunsa riƙeda nasu fadeelah ya ɗaukosu a makaranta,kallon juna sukayi shida khariyyah ya kashe mata ido. Ganin hakan yasa tayi masa hararar wasa tareda shigewa ɗakin da sabrah tashiga. Ƙwalla mata magana yayi daidai tana shigewa ɗakin. "Masoyiya ya zanyi da yaran kuma kika tafi" "Kasan yanda zakayi dasu,dan rainin hankali ai kasan nafi ƙarfinka" "So baruwansa da yaro khari tah,ko kinfini ma zan iya sonki bare koda watannine ai nafiki" Juyi tayi masa tareda shigewa ɗakin tana murmushi,shima ƴar dariyah yayi tareda fita waje can baya inda nasa part ɗin yake. Duk abinda suke akan idon fadeelah wacce ta cuno baki tana naɗewa a kwanyar kanta Hanyar dakin inno sukayi,tunda sunsan ta dawo kuma antynsu bata nan sai wajen inno. Da daddare su khairi ne da fareedah sukayi abincin dare,didi itakuma ta huta,dan itama dayake dun saba da wanda ba iyayensu ba sai sukejinta tamkar su maman yara. Shirya abincin sukayi amma inno bata fitoba tana ɗaki,da alama tayi fushi kenan. Sabrah ce itada khairi suka shigs ɗakin innon,dan baƙaramin damunsu fushinnata yayi ba. A zaune take akan sallaya tayi gama sallahr magriba,tsugunnawa sukayi a gabanta har ta gama addu'ar. Sabrah ce tafara magana kanta yana sukunye "Inno kiyi haƙuri,wlh bazamu sakeba daga yau,zamuyi yanda kikace,amma don allah kidaina wanann fushin" "Ni ba fushi nake dakuba,fushi nake da taurin kanku,amma tunda kunce bazaku ƙara ba na yarda wanann karon,ke ki shirya da mijinki kuyi zamanku lafiyah,kada ki ƙara tashin tashina ko kuma cutarsa,ki riƙe maraicinki da kuma tarbiyyar dana baki,harkema ki bawa ɗanki. Ke kuma autah,nasan kuna soyayya da deeni dan dazu ma fadeelah ta faɗamin mai kukace ɗazu,idan kema kinasonsa yakamata kuyi auren,zamannan ya isa haka,kun girma yanzu. Ita kuma wancar munyi wayah da itah tacemin ƙarin karatu ta tafi na wata shida,allah ya dawo da ita lafiyah,da alama kam aikinku ya ƙare tunda bata nan,nasan dama itace shugabar komai. Yanzu abinda yafi damuna shine shari'ah,kunsan bazaku kashe manyan gari ku tafi a banza ba koh?" "Hmmm inna karki damu da wannan,tunda kin huce shikenan,muje muci abinci kar yayi sanyi" Tashi tayi daga kan sallayar suka fita zuwa cin abincin. Khamriyyah kam tunda asirinta ya tonu tsakaninta da deen da daina cewa komai,sai hararar fadeelah take tana cewa munafuka kawai. _____________________ Dec. Saddeq ne a zaune a falon hajiyah Indo ( mahaifiyarsa kenan) Mata mai kawaici kana da tsoron allah.. Tunda dazu yasaka kwanon cin abincin a gabansa amma ya gagara yin loma ko guda ɗayah,kwana uku kenan dayin abin aamma har yanzu bai koma normal. Zabura yayi jin muryar ammin a kansa tana magana,bai luraba ashe tayi kusan minti talatin akan sa. "Sadeeq mai yake damunka ne kwanann,sannan ina ita amratun kace min tayi tafiyah yau kwana uku,anya kuwa ba faɗa kayi kaƙi faɗamin " "Bamuyi fadaba ammi,kawai.....kawai dai uhm ta tafi gidane" "Zancen banza,haka kawai zata tafi gida,saikace a wani gari take,ka faɗamin mai yafaru a tsakaninku,nasan fah zuciyarka,karka cutar da ƴar mutane ban sani ba " "Allah ammi babu abinda ya faru,zata dawo kwanannan,ba wani abin dakuwa bane,au na manta ban fadamiki ba,khaleel gobe zai dawo daga china,yace ki shirya masa abincin daya fiso" Dec. Sadeeq ya faɗa yana kawar da zancen sabrah da ammi takeyi. Aikuwa yayi nasara,dan tanajin dawowar ɗannata hankalinta ya koma kai,na mai zata yi masa dazai faranta masa rai. Kowa ya kalli idon ammi yasan tanaji dashi kodaga magana ma,jijjiga kai dec. Sadeeq yayi yana murmushi,danshi kansa yayi kewar abokinnasa sannan kuma dan uwansa guda sosai. Fakar idon ammi dec. Sadeeq yayi ya shige ɗaki,dan dama neman yanda zai ajiye abincin yake,kan gadon sa na gidan ya faɗa ya kwanta tareda riƙe cikinsa wanda yake barazanar fashewa. "Amrah why,you i love you more than you can imagine,meyasa zakiyimin haka,meyasa zaki barni ni kaɗai,bayan kinsan bansaba rashinki a kusada dani ba,bazan kamaki ba dan allah kidawo gareni,zanyi komai domin nunawa duniyah keba mai laifi bace mai ɗaukar fansa ce,ki taimakeni ki dawo gareni mu raini ɗanmu tare,rashinki zai iyah yimin illah amrah " Zuwa lokacin zuciyarsa ta karye matuƙa,wanda hakan yasa shi dole yasaki kukan kewar matar tasa har bacci ya ɗauke shi. Itama sabrah a bangarenta hakan ce take faruwa,zata nunawa su khairiyyah ko nace sauran gidan babu komai,amma da daddare har kukan tsoron rasa mijinnata takeyi. Koyaushe khairiyyah ce ke rarrashinta akan zai dawo gareta,amma kwana uku har ta sare da zuwannsa. "Please sabrah ki daina kukannan dan allah,dare hutun bawa amma ke yazama na kuka a wajenki,ki kwantar da hankalinki na tabbata shima yana kewarki kaman yanda kikeyin tasa,komai zaizo da sauƙi inshaallah." "Nikam khairi gobe zanje wajensa na bashi haƙuri,nace masa ya yafemin na koma ɗakina" "Kai sabrah,anya kuwa so bai kwashemiki hankaliba,yanzu fah kukayi waya da khamriyyah tace miki ki ɗan dakata,shine zakije ki ruguza komai,ta faɗamiki zata san yadda za'ayi,inta kama zuwane zataje akan gyara tsakaninku,idan kika dulmiya komai wlh kinsan halinta banza zatayi dake kiyita kukan rashin mijinnaki,muda bamu dashi ma ai mun haƙura muna zaune" "Ke khairi dan ina faɗamiki shine kika tsigeni kaman kin samu kaza,ya isheki to haka,tun farko kinsan daɗin mijinne dazaki san zafin rashinsa" Tana gama faɗar hakan ta juya ta kwanta,ta bar khairiyyah a zaune da baki buɗe,mai kuka tabar kukan ta mayar martanin faɗa,ashe dama na tsiya ne. Tun safe ammi take ta jirjirgan taryar ɗannata wanda take ji dashi sosai. Meenah sai cunbuna baki take ammi ta hanata zuwa makaranta,a dole sai ta tsayah tayata aikin abincin ranar,gashi suna shirin zana jarabawar fita. "Ke meenah yi sauri ki ɗauko min shinkafar nan dana jiƙa ki markaɗa ta,a fara ɗana masar" "Kai ammi yanzu harda wata masa za'ayi,mutumin da rabonsa da ƙasarnan tun muna ƴan ƙanana,ni ban ma sanshi ba ko a hoto,haka alaƙarmu dashi babu wanda ya faɗamana" "Ke meenah inabaki kiyayeni ba saina karya kashinki,dahaka zaki tarbi yayannaki karon farko a rayuwarki,sanann yanayin aikinsa ne haka shiyasa bai faye zuwaba" Tafiya tayi zuwa makarden,badan tana so ba sai dan anyimata dole. Wajen misalin ƙarfe shabiyu baƙar mota ta faka a ƙofar gidan su dec. Sadeeq ɗin,kana ganin motar kaga new mordern wacce ake ji da itah. Buɗe ƙofar yayi da sauri tareda bayyanowa daga cikin motar,lallausan murmushi yasakewa ammi wacce take bakin baranda tana jiran ƙarisowarsa. Hannu ta buɗe masa ya taho da gudu tareda shigewa jikinta yana ƙanƙameta . "I really miss you my beloved mother,nayi murna da ganinki farincikina" "Nima nayi kewarka ɗan ɗana,ya ƙasar wasu da zaman haƙuri da aka yi,dafatan an samu abinda akaje nema" "Inshaalllah ammi,ina bro nah ban ganshi ba" Ya faɗa yana waigawa hagun da dama. Sakin baki meenah tayi tana ƙaremasa kallo,yayinda kirjinta yake bugawa fat fat saboda tsagwaron kyau da kuma kwarjini datayi arba dashi a jikin wanann bawan allah. Shin wanann balarabene ko kuwa baturene mai kyau,dan bayyi mata kama da ƴan nigeria sosai ba sam. Manyan idanunsa ne suka sauƙa akanta wanda sai a lokacin ya kulada itah. Murmushi ya sake mata daya sakara ƙara narkewa cikin begennasa. "Little ɗin ammi kece kika girma haka,ya makaranta,banga big anty ba,shine kotazo taryata koh" "Uhm. Uhm. Yah khaleel ina wuni ya hanya" "Lafiyah kalau,barina je ɗaki na huta zan kawomiki tsarabarki,kayan kam inaga sunyi miki yawa,dan kinfi yanda nake hasashenki sosai" Itadai meenah rasa bakin magana tayi kwata kwata ta faɗa cikin kogon tunanin da ita kanta bata san na menene ba. Duk abinda suke ammi tana kallo,babu abinda tayi sai murmushin manya kawai. Duk yanda dec. Sadeeq ke ƙoƙarin boye damuwarsa na rashin sabrah a gaban ƴan uwan saida khaleel ya fahimceshi. Suna gama cin abincin kuwa yajashi lambu tareda nuna masa da yatsa alamar menene yake faruwa. Jijjiga kai shima Sadeeq ɗin yayi alamar ba komai. "Karka cemin haka ɗan uwa,ka faɗamin abinda yake faruwa,shin kun kama wanann matanne,sanann kuma miye yasakaka a damuwa haka" "Bamu kamasu ba yanzu ma sun subuce,saidai wannan karon ba guduwa tayi ba,nine narasa ƙwarin gwiwar killaceta khaleel" "Kamanya kenan ban fahimta ba" "Da kabar zancennan khaleel,bai kamata daga dawowarka ka saka wannnan acikin abubuwan rayuwarka ba" "Hmmm yaushe ka fara tunanin abinda ya shafeka bai shafeni ba sadeeq,tukunnama ina Amrah ban gantaba?" "Abubuwa dayawa sun faru a kwana uku kacal bayan wayar da mukayi. Abubuwan sun karyar min da gwiwa,sun sakani ruɗani kana da shiga cikin wasi wasi. Kaman yanda ka faɗa yakamata nasamu wani na faɗamasa kuma ba kowa bane kaine,yanxu kuwa zakaji. Khaleel matata ......wacce na yarda da itah,na amince mata na bata ragamar farincikina,itama tana ɗaya daga cikin su" "Mai kake faɗa sadeeq ban fahimta ba" "Bazaka fahimta ba kaman yanda na kasa fahimta,amma yanxu zakaji mai yake faruwa kuwa" Cikin ƙanƙanin lokaci dec. Sadeeq yafaɗawa khaleel halin da ake ciki na kama khairiyyah harma da gano kamarsu da Sabriyyah da kuma tarihin rayuwarsu kaff. Shuru khaleel yayi yana jinsa har yagama bashi labarin kaff,kana ganin fuskarsa kasan yana girmama girman al'amarin sosai. "Wannan shine abinda ya faru,khaleel mai zanyi akai,abin ya ɗauremin kai sosai sanann yabani mamaki,bansan ta yanda zan fuskanceshi ba. Dan haka na yanke shawarar ajiye wannan case ɗin na ɗauki wami daban,idan bincike yazowa mutum da alaƙa bashida daɗi ko kadan" "Nasan da haka,sanann koni ma idan ina a matsayinka iya abinda zanyi kenan shiga zullumi,amma batun ajiye case inaga ya kamata kuwa" "Kobai kamata ba dole zan aiwatar,inason zuwa gidansu amrah,duk da tana da laifi a cikin abinnan amma babu yanda zanyi,matata ce haƙƙinta yana kaina,musamman daya zamo ba ita kaɗai bace,amma kuma tunda fansa suka ɗauka nasan abin bazayyi muni ba sosai. Kuma sannan wane bincike zan cigaba dayi tunda nasan wanda suke aiwatarwar,sannan ita kanta shugabar tasu bata garin ma ta tafi ƙarin karatu. "Ƙarin karatu kuma,bayan anyi haka kuma ta tafi ƙarin karatu akan aikin,kuma tasan bazata cigaba da aikinba?.....mtsss akwai ayar tambaya a gameda karatun,kodai tasan za'a kamasu ta gudu ta barsu ko kuma wani abin take shiryawa. Domin ruwa baya tsami banza" "To mai zata shiryah" "Hmmm a yanda ka karanta labarin sabrah tace batada suna su suka bata,kuma a yanayin yanda take musu magana batayi kama da wanda hankalinta ya gusheba,yanayinta kuma yayi kama da na wanda tashiga wani hakin kunci na rayuwa. Har yanzu baka zargi wani abu ba gameda itah" Jijjiga kai sadeeq yayi cikin yanayin kiɗima,danshi bai gano komai ba,amma tunda khaleel ɗin yace akwai wani abu toh inaga tabbas akwai. Ƴar dariyah khaleel ɗin yayi irinta ƙwararrun masu bincike har dimple ɗin sa yana lotsawa. "Hmmm karka damu dan uwa,ka share hawayenka inaga zan karbi case dinnan nacigaba daga inda ka tsayah,yanda kake tunanin binciken ya tsaya ba haka bane,ni inada yaƙinin akwai wani abu kullalle kuma boyayye gameda makasan gudan biyu,wato MABARACIYAH da kuma KHAMRIYYAH,kaidai kabar komai a hannuna.. Daga ganin yanayinka nasan baka yarda dani ba,amma lokaci zai warware komai dakuma hujjoji" Dafa kafaɗar sadeeq yayi tareda mikewa yayi hanyar waje. Har yazo fita ya dawo tareda ɗaukar kundin tarihin sabriyyah. "Idan bazaka damuba inason sake duba wanann littafin " "Bakomai zaka iya tafiya dashi" Sadeeq ya faɗa cikin kasalalliyar murya. Washagari monday dec. Sadeeq ya shirya cikin kayansa ya fito daga ɗakinsa. Da meenah suka haɗu zata tafi makaranta,sun fara jarabawa ranar shiyasa bata tafi da wuri ba. A bakin dinning yaganta tana shan shayi da sauri sauri a tsaye,da alama mai kaita makarantane yake jiranta. "Yah sadeeq ina kwana" "Lafiyah,mai kike a gida har yanxu" "Uhm dama mun fara jarabawa ne,yau aiki zakaje" "Eh sarkin tambaya,ina ammi kuwa da khaleel" "Ammi tashiga ɗaki,yah khaleel kuma yafita tunda safe" Ina kuma yaje,ya faɗa aransa,amma ya basar tareda zama ya karyah sama sama shima ya fita zuwa headquater su. Office ɗin shugaban su ya wuce domin kaiwa takardar ajiye case ɗin su khamriyyah. Yana shiga office ɗin suka haɗa ido da khaleel wanda yake zaune suna magana da shugabannasu,har zayyi masa magana khaleel yayi saurin ɗauke kansa tamkar bai ganshi ba. Shima sai a lokacin ya tuna ashe aikin su khaleel yafi nasu hatsari,su SSS ne shikuma secret interlligent security(SIS). Ba'a son asan familynsu saboda hatsarin aikin. Shima sadeeq ɗin kafsewa yayi tarefa miƙamasa hannu,suna gaisawa ya ɗauke kansa tareda sarawa shugabannsu. "Dec. Sadeeq sai yau muka ga idonka a wajen aiki lafiya?" "Uhm na ɗauki karamin hutune kawai,ayi haƙuri ogah" "Okay ya wuce,ya batun mission ɗin dakake kanyi na wannan matan,inaso ka kawo min takardun case ɗin,Dec. Khaleel yace zai cigaba da binciken. Bamuyi zaton daga karba rokonmu nayin aiki a wajenmu zai fara aiki yanzu ba,hakanma kuma a wanann tsohon case ɗin. Duk da haka muneda da godiyah dec. Khaleel,inshaallah dec. Sadeeq zai baka dukkan bayanai akai,in kanaso ma zaka iya ɗaukarsa mataimakinka,don mataimakiyarsa ashe itace shugabar masu yin ta'asar" "Duk naji wannan labarin,amma yanzu ba wanann mission ɗin zam faraba,inaso na fara dana MABARACIYAH,tunda itace ba'a gano wacece ba,kafinnan kuma ayimin afuwa zanyi wani uzuri na sati biyu tukunna." "Ba komai muneda godiyah,idan kagama saika fara shikenan" Daga haka sukayi sallama da shugaban securityn. Yana fitowa daga office ɗin kira ya shigo wayarsa. Ɗagawa yayi tareda amsa sallamar da'akayi masa. "Naji mai kace,amma karka kuskura kace na dawo kasarnan,ban yadda naji labarin a wajen kowaba,ciki harda mahaifina,abinda na daɗe ina jira tsawon shekara goma sha biyar yau zan farashi,babu wanda zayyi idan ba ni ba,haƙƙine a kaina dole sai nine zanyi,dan haka zuciyata bazata taba yin sanyi ba idan ban biya abinda tayi ba. Ka shirya min komai ina zuwa gobe " Yana gama faɗan hakan ya jefa wayar a aljihu tareda furzar da isa mai zafi daga bakinsa ,kana ya nufi inda motarsa take,har sannan fuskarsa tamau take babu alamar fara'ah a kanta. Toh dec. Khaleel kenan,ko menene a cikin ransa dayake boyewa allah ne kaɗai masani wannan labari. ____________ Deejah ce itada yadiko lami a tashar katsina dake garin daurah zasu tafi katsinan cikin gidan sarauta inda take aiki. Basu dade da hawa motar ba tacika,dan dama sun samu mutane a ciki. Dan murmushin gefen baki deejah tayi lokacin da motar ta fara haurawa kan titi da niyyar daukan hanya. Kallon bishiyoyin da suke wucesu take tareda yimusu bye bye itama da hannunta. Ba yaune shigarta na farko garin ba amma kuma wannan yana ɗayah daga shigarta zuwa aiki nata na kanta. Dan haka dole tafiyar tasakata nishaɗi sosai. Yadiko lami ce ta kalleta bayan ta gutsiri goro ta saka a bakinta, "Yarinyah kekuwa akan kiyi aure shine zakije fara aiki a gidan sarauta,kinsan fah wanann wajen ba daidai yake da sauran waje ba. Wajene da ake zuba mulki da kuma taƙama da nuna isa,dole kai talaka sai kayi haƙuri,duk da mu a bangaren Hajiya Saratu muke,ita babu ruwan Duniya Allahu masauƙi ce a wajenta. Amma kinga Hajiya fulani ateeka,hmmm karki yadda ko kashinta ne wani abu ya haɗaki dashi,dan ba lallai ki kwana lafiya ba,dan haka ki kiyaye ko sashinta kada kije inkina son gamawa da arziƙi" "Nikuma yadiko lami a sashenta nakeson nayi aiki,domin kuɗi nazo samu ba zaman lafiya ba,naji ance tafi biya da tsoka" "Keeee ƴar nan,ranki ai yafi kuɗi koh,toh ki kiyayi kanki da wanann banzan tunanin" "Babu abinda zai faru,ki kwantar da hankalinki,amma a wajenta nakeson aiki,kodah kuwa namana zata dunga yanka tana zubarwa da kaɗan kaɗan................. Kunji fah,muje zuwa toh ... Taku _sadi-sakhna_ Ƴar mutan jama'are. *MABARACIYAH* _haƙƙin mallaka_ _*sadi-sakhna*_ (Yar mutan Jama'are) 29••30 Tundaga wannan maganar yadiko lami bata sake cewa deejah komai ba,dan taga abinnata azeemunne. A tasha aka sauƙesu suka hau adaidaita zuwa gidan sarautar garin katsinan. Tundaga bakin masarautar yanda ake zuba mulki kasan ba wajene na wasan yara ba. A bakin kofar shiga gidan mai adaidaitan ya samu damar yin burki,dan yasan ko giyar wake yasha,bai isa tsallaka layin shigaba. Kuɗinsa yadiko lami ta fitar ta bashi,tanayi yana gaisawa da fadawan da suke tsaye a bakin kofar,da alama akwai sanayya a tsakaninsu. Itakuwa deejah amfani tayi da wannann damar wajen ƙarewa farfajiyar ƙofar kallo,duk da ba yau tafara shigaba amma kuma wanann zuwan na dabanne,dole ta lura kana ta maida hankali akan rayuwarta. Yadiko lami ce ta jijjgata tareda yimata kallon alamar tambaya. "Anyah kuwa deejah kalau kike,naga sai kalle kalle kike da kuma shiga tunani,saikace yau kika fara kallon fada,naga akwai a garinku daurah ma mai ɗumbin tarihi dayafi na nan" ......Masarautar daurah,masarautace data rayu a ɗumbin shekaru fiyeda da Dubu da suka gabata. Garin ya ƙara samun suna ne da kuma kambun a tarihi a lokacin mulkin Sarauniya DAURAMA SHAWATA,ita ce sauraniyata tara a lokacin,wacce ta gaji mulkin daga wajen sauran matan dasuka gabaceta. Sannan garin yana ɗauke da tarihin Abu yazeed wanda aka fi sani da Bayajiddah. Shi mutum ne daya samu shiga hikayoyi da kuma tarihihi na ƙarasa hausa. Wanda labari yazo cewa shine jarumin daya samu kashe macijiya SARKI da take cikin rijiyar ƙusugu ta har yanzu tana nan a garin dauran. Uwa uba kuma riƙo da sarauta da kuma al'adu......sannan kuma ga..... "Ya isa haka lami wannnan bayanin,haƙiƙa kin cancanci yabo da wanann bayanin naki,amma ki sani hattara,a gaban wata masarautar kike" Wani bafadene ya amshe maganar yadiko lami ɗin,aikuwa ta kifta ido,da alama dama dashi take maganar "Habadai,duk da tafita dadewa amma banda tarihi da daukaka,ko barta tayi kallo taga waje tamkar a kasashen larabawa" Shima ɗayan dayake wajen ya fada. Sunkuyar dakai deejah tayi taƙi bari su haɗa ido da bafaden,kanagani zaka dauka dan kunyah take yi badan tsaroba. Jiransu tayi a gefe suka gama surutunsu kafin yasaka wasu yara ɗaukar musu kaya zuwa can bangaren hajiya saratun inda take aiki. Bayan sun kutsa kai cikin gidan sarautar nan ma wani sabon kallon deejah ta kafa tareda na nazartar duk wani lungu da saƙo na gidan. Sashen babu laifi yanada kyau sosai,amma bai kama na sarauniyar gidanba wato fulani ateekah,dan komai nata ma dabanne dana sauran gidan,shi kansa sarkin a wajene yake sarki,amma in ya shigo gareta shine sarkin ba itah ba. Babban falon dayake farkon sashen suka shiga wanda aka malaleshi a jan carpet mai laushi da alfarma. Ma'aikata zai zirga zirga suke wajen tsaftace wajen da bashi ado na musamman. Wata matashiyace ta matso inda su deejah suke tsaye,zatayi sa'ar deejan,ko kuma ma ta fita da shekara guda. "Lahh Yadiko lami sannu da dawowa,baba asaben kuwa ta fita dazu,amma tace ba nisa zatayi ba,taje karbo kayane. Wannan kuma fah ƴar kice" "Eh to ƴar tawace,nan take gidan maƙwantammu tace zata biyoni tayi aiki anan" "Babu komai sai tazo mu dunga wanke wanke muzama mu shida kenan,dama kayan sunada yawa sosai" "Amma kuma tace ba a nan zatayi aiki ba wai a sashen fulani ateekah zatayi" Zaro ido budurwar tayi kaman ance mata ga can mutuwa. "Sashen ........uhmmm kuma?..anan zatayi aiki,yadiko lami ki fada mata mana,da alama batasam mai yake faruwa" "Ah to Salaha ya zanyi,na faɗamata tace anan zatayi,sai muyi mata fatan allah yasa taji da sauƙi" "Dama bani zan kai kaina ba,itace zata nemi nayi aikin a wajenta,lokacin data nemi naje kuma bazan ƙi ba,kunga babu zancen cutarwa,idan bata nemeni ba kuma shikennan zan zauna daku a nan muyi aiki har zuwa lokacin daxan tara abinda na tara na tafi. Nagode yadiko lami dakikamin zirin zuwa nan wajen,kema salaha nagode da haɗuwa dake" Ɗan murmushi tayi tareda jin daɗin hankalin deejah,dan haka take,tana da baiwar siye mutum da kalaman bakinta,tamkar tanasaka asiri a ciki. "Kin burgeni sosai,muna miki fatan alkhairi,menene sunanki?" "Sunana deejah" "Khadeeja dai ko" "Ahah deejah ne" "Tamm shikennan duk yanda kike sonsa dai deejah,muje na kaimiki kayanki ɗakinmu,mu zauna tare kafin ki koma can" "Kiyi haƙuri na zauna da yadiko lami tukunna kafin saina komai gunku idan bazaki damuba" "Lahh ba komai,da alama baki da sabo,nizan sakaki mu saba" Salahan ta faɗa cikin sigar wasa,wanda hakan yasa deejah yin murmushi. Ɗakin babu laifi saidai rashin privacy kawai,amma akwai silin da fanka da kuma katifa. Samun waje deejah tayi a gefen katifar salaha ta ajiye kayanta,wani idan ya ga kayan zayyi zaton kwana biyu zatayi ta tafi,saboda baifi kaya biyarba tazo dasu. Fitowa tayi daga ɗakin domin zuwa ta ɗan jaga cikin gidan. Iska ce take kaɗawa da alama hadarine ya taso amma yasaki iska,gyalen dayake kan wuyanta take ta ƙoƙarin gyarawa,yayinda idonta kuma yana tsaye kyam akan sashen Fulani ateekah,iya katafaren sashen wajenba abin kallone,kuma yanda labari yake jagayawa itada kanta tasake gina wajen ba wanine ya gidan mata ba. "Hmmm ki gama duk wani farinciki da walwala da kuɗin da kike taƙama dashi,abinda nasani guda ɗayah shine kinyi kuskure dakika bari na shigo wannan gidan,bazakiyi danasani ba ma saikin gayyaceni cikin inuwarki,a lokacinne nikuma zan fito dake daga cikinta!!!!!" Wata mata ta gani tafito daga cikin sashen sai sunkuyar dakai take,da alama wani waje zataje. Jikin deeejah ne ya bata akawai lauje cikin naɗi,wanda hakan yasata tunkarar matar batareda tsoro ko fargaba ba. Da gangan lokacin da sukayi arba ta bugi kafaɗar matar,ji kake timm ta faɗi a ƙasa,dan batayi mamakin deejah zata bugeta ba. "Ke kinada hankali kuwa zaki bugeni,kinsan ni wacece?,duk filin gidannan bai isheki ba saikin bangajeni saboda rashin hankali" Ta ƙarisa maganar tana tashi daga ƙasan,tareda tafa hannunta tana kaɗe ƙurar data ɗiba. Basarwa deejah tayi na dan wani lokaci,kafin tashi ɗayah sanja zuwa salon nuna tausayi lokaci guda. Marairaicewa muryah tayi tareda lumshe ido irinna mutane masu sanyin rai. "Kiyi haƙuri baba,bansan zaki zo ta nan ba da bazan bugeki ba" "Ke dubeni nayi miki kama da babarki" Kallonnata deejah tayi kaman yanda ta buƙata,to mai zata ƙirata,banda figyagygyiyar siffarta babu abinda ya haɗata da yara,don tsohuwa ce kaman bishiyar tsamiyah. "Toh mai zance miki innah" "Ke ƴar rainin hankali,innah kuma kina ganina yarinya,kicemin zee zee" Ta faɗa tana kashe ido dayah irinnasu na ƴan bariki. Dukkansu a tare hankalinsu yakai kan wani ƙullin jan tsumma a ƙasa,wanda zee-zee ta jefar lokacin da deejah ta bugeta. Deejah ce tayi saurin isa zuwa ɗaukar abin,wanda yake maƙale da wata ƴar takarda anyi rubutu da tawada. Cikin ƙwarewa da harkar kafin ta miƙa mata har tagama gane mai yake dauke a jikin a takardar. Karba zee-zee tayi tareda fara tafiya tana karyar dakai,da alama tana cikin fargaba da aikan da akayi mata. "Maganin ya baci ai" Juyowa zee-zee tayi tareda buƙatar deejah ta maimaita mata abinda tace. Ita kuma ganin hakan yasa tayi murmushi tareda juyawa zata tafi. Da gudu zee-zee ta finciko rigarta tareda juyota tana fuskantar ta. "Mekikace baiwar allah,taya kikasan magani ne kuma har ya baci. Nida nakawo shi daren jiyah babu wanda yaganni bansan ya baci ba sai ke,da ban taba ganinki komai kamarki ba a cikin fadar nan" "Nima bansan lokacin dakika shigo dashi ba saida na gani yanzu,batun bacinsa kuma naga wanda ya 'bata maganin ne a shigowata gidannan" "Waye ya 'bata maganin,meyasa bamu ganshi ba sai ke" "Saboda bakuda ikon ganinnasa,sannan batun waye mezakiyi idan na faɗamiki waye" Fisgewa rigarta deejah tayi zata tafi,amma maganar zee-zee ta dakatar da ita da cigaba da tafiyar. "Duk abinda kike so ki faɗa zan miki,amma dan allah ki taimakeni ki fadamin mai kika sani,daga ganinki ke ƴar baiwace irin mutanen da muke nema" "Toh shikenan zan faɗamiki waye ya bata,amma saikin bani labarin maganin menene,sannan waye yake amfani da maganin. Idan kika yimin hakan,nikuma zan faɗamiki waye ya'bata maganin." Shuru zee-zee tayi kaman bazata ce komai ba,can kuma saita numfasa tareda cewa "Inaga ke baƙuwace bakisan jinyar da yarima Mubarak yake ba,wanda yanzu tsawon shekaru goma kenan yana fama dashi,duk wani magani da akayi har yanzu ankasa samun nasara akan ciwon,ko yaushe cigaba yakeyi" "Wane irin ciwone haka" "Hmm babu wanda yasani,domin baya magana bare ya faɗi abinda yake damunsa,kullum idanuwansa ne a buɗe yana kallon sama,shikaɗaine alamar datake nuna shi rayayyene ba matacce ba. Asibiti ba iyah na ƙasarnan ba harda nawaje anje,amma babu nasara,shiyasa aka zubawa sarautar allah ido kawai,domin na hausan ma anyi ta jarrabawa amma shuru kaman ana shuka dusa" "Uhm to amma ke mai hadinki da neman maganin ,ina mahaifiyarsa take" "Kee kiyi hattara,maganar Fulani ateeka kikeyi,ina ba so kike kiji harshenki a ƙasa ba" Ta'be baki deejah tayi,da alama gargadin bai je ko'inaba. "Shikenan bari na faɗamik,wanda ya 'bata maganin ba mutum bane aljanine wanda jinsinsu yawanci sukan siffanta da dabbobine,yazo a jinsin baƙar kuliyah dazu da rana,shine ya 'bata maganin da kuma kawo gidan. Sannan kuma da alama akwai wanda bayason tashin majinyacin naku,domin shi baya aiki sai an aikoshi bayan an yanka masa baƙar kaza" Tsuru tsuru zee-zee tayi lokacin da taji labarin abinda deejah ta faɗamata,kenan babban aikine a gabansu ɗanye. "Amma in bakazi damu ba in tambayeki?" Kallonta deejah tayi kaman bazata ce komai ba sai kuma tace "Eh faɗi inajinki mai ya faru" "Daga gani keba ƴar nan bace,amma ke wacece" "Ni makashiyace,mai taimako ce,azzaluma ce,mai jawo ciwoce,sannan kuma mai maganice,mai sanyi ce kuma zazzafa ce,maƙiyyace kuma masoyiyace. Sai ki zabi da wanda kike ganin zaki kalleni da siffarsa,kowanne kika ɗauka zai bayyana miki wacece ni dadai yanda kika ɗaukeshi" Ƙamewa zee-zee tayi a wajen,har deejah ta bacewa ganinta bata sani ba,saida ta ƙofta idanuwanta kafin daga bata wajen. *_______*______* Dec. Sadeeq ne a gaban madubi yana gyara zaman hularsa,lokaci zuwa lokaci yake furzar da iska. Kana ganinsa kasan fargaba ce a ransa. Agogonsa ya ɗauka da key ɗin motarsa tareda fitowa a cikin ɗakin. A falo yayi kicibis da khaleel wanda yake zaune yana shan lemon daya ɗauko a cikin fridge. "Bro yaushe kashigo banji motsinka" "Ban daɗe da dawowa ba,ina ɗaki tunsafe wajen duba case ɗin da kuka bani. Ajiyeshi zanyi ma dan da alama bayason gaggawa. Dama akwai wani waje danake son zuwa,toh inaga gobe zan wuce" "Inane haka daga dawowarka,ya kamata ka zauna ka ɗan huta tukunna" "Babu zancen hutu ɗan uwa,aikin da dalilinsa yasa nayi wannan karatun shi zanyi yanzu" "Aiki kuma wane iri?" Jimm khaleel yayi kaman mai tunani kafin yace miƙe daga kan kujerar. "Manta kawai Ɗan uwa,in lokaci yayi zakasan menene,amma yanzu bazan iya faɗamaka ba. Yanzun ina zakaje naga ka sha sabin kaya,a sanina dai banji wani biki kwanannan ba" "Uhm uhm dama zanje wajen sabriyyah ne,ko zaka rakani mu tafi tare,dan jinake kaman naje kaman karnaje" "Wacece kuma sabriyyah,ohh Amrah kake nufi. Gaskiya Sadeeq banyi maka alƙawari ba,a yanda nasake karanta abinda sukayi bazan iya haɗa ido da ita ba yanxu,kasan yanzu case ɗinsu na hannuna,to zan iyah kamata Sadeeq,dan saboda kaine kaji nayi shuru ban kawo maka zancenba. Babban abinda yasa ban kamasu ba kuma so nake na kamo babbar,sannan na haɗata da zargin danake da Mabaraciyah. Saboda nasan tunda tana matarka to bazasu gudu ba,amma hukunci dole saisun fuskanceshi,koda kuwa iyayena ne ko naka sadeeq" Yana maganar ne cikin dakewar muryah,tamkar ba khaleel ɗin da yasani ba a jiyah,wanda ya karbi kukansa tamkar zai taimaka masa,amma yasanja zuwa mai tsaurin ra'ayi. Jijjiga kai Sadeeq yayi tareda cewa. "Ammmm.....amma kai kace zaka taimakamin wajen fitar da ita daga wannan halin,babban matsalar ga ciki a jikinta,mai zancewa ɗan idan yaji mamarsa ta taba shiga kurkuku?" "Hmm bakai bane wannann sadeeq,yakamata ka dawo daga kogin giyar soyayyar daka shiga,bai dace mai bincike irinnamu da naku ya faɗa zurfin soyayya kaman haka ba,saboda za'ayi amfani da hakan a cutar dashi kaman yanda akayi maka. Karka manta tun farko fah ta aureka ne domin manufarsu badan tana sonka ba,sannan ƴan biyunta tasha zuwa gidanannan domin neman bayanai,amma duk da yanxu kasan hakan bakayi komai ba, burinka shine kayi amfani da aikinka wajen kubutar dasu,saboda matarka ko kuma ɗan cikinta karya ji labarin ka saka uwarsa a kurkuku" "Khaleel nasan abinda nake ban kyauta ba tun ranar da akan idona khariyyah tafita daga ɗakin bincike,badan komai ba danna nazama mai rauni saboda soyayya. Amma hakan badaga ni bane babu yanda zanyi ne,soyayyar data shayar dani ne tariga ta kama dukkan ilahirin jikina da kuma jijiyoyin jikina,har takai bazan jure rashinta ba,ka taimakeni......." "Karkasake min wanann roƙon sadeeq,lokaci yayi dazaka dawo hankalinka,Da Detective Khaleel Muhammad kake zance. Wanda akan aikinsa zai iyah harbe kowa nasa indai akan aikinsa ne,jiya aikin ba a hannuna yake ba,amma yanxu a hannuna yake,dan haka sai inda ƙarfina yaƙare wajen ganin sun kankari hukuncinsu kaman yanda suka manna laifinsu. Wannan alƙawari ne,shawara ɗayah zan baka shine kanada damar ganinta a yanxu kafin bincikena yafara akanta. Gargaɗina shine karka barsu su gudu,damin kasan hukuncin matar data gudu koh,kai zan kama a matsayinta" "An faɗamusu ɗaukar doka a hannu dan anyi maka abu shine daidai,inda hakane da na daɗe da aikata fansata shekara goma da suka wuce" Ya karisa magana yana cije baki tareda fasa kofin glass ɗin dayake hannunsa. Jinine ya fara ɗiga akan tiles ɗin,amma ko kaɗan bai kulada shiba,saboda hankalinsa baya kan wajen.. Takan glass ɗin ma yataka yabar wajen. Zare ido dec sadeeq yayi yana jin furucin Dec. Khaleel ɗin,duk da bayyi mamaki ba na halayyar tasa amma kuma yayi mamakin yanda ya ɗau zafi akan lamarin. Har ya juya zai koma ɗaki saikuma wata zuciyar tace masa gwara yaje. Saboda kobai je bama a cikin lokacin da khaleel ta ɗeba masa zasu ƙare,dan tunda yace zai tabbatar anyi musu hukunci to babu mai hanashi. _____________________ Ɗan wake tasaka a gaba tanaci wanda inno tayi mata,da badan ɗan wake bane,yanda take cikin jimamin rashin mijinta ko kallonsa bazatayi ba,amma tunda sunsan bazata iya jure ganinsa bataci ba shiyasa sukayi mata shi. Fadeelah ce tashigo da gudu dr nawwarah ta ɗaukosu daga makaranta,saboda kusan inda yanxu take aikine bayan tabar asibitin dr. Bukar. "Anty Sabrah mijinki yana waje wai fadamki" Zumbur sabriyyah ta miƙe tareda kallon dr. Nawwarah,da alama neman ta gasgata mata zancen take. Daga kanta tayi tareda murmushi,da alama kenan gaskiyane.. Yatsun hannunta masu maiƙon mai da yaji ta suɗe tareda ɗaura ɗan kwalin kayanta . "Har cikin zuciyata inaso yazo,amma fargabar zuwan tafi son zuwan yawa. Gani nake kamar zai sakeni Anty nawwarah,banason narasashi inasonshi sosai" Hawayene yafara zaryah akan fuskarta,wanda hakan yasa sauran jikinsu yayi sanyi,ji suke kaman su tariyo baya karsu yaudari Sadeeq ɗin. Khairiyyah ce tazo da wayah a hannunta suna video call da khamriyyah,a wajen wani ruwa take mai kamada lambu,da alama inaga hostel ɗinsu ne. "Sabrah gashi inji khamrah,tace ki nutsu karki saka damuwa a ranki,ki cigaba da addu'a sannan ki je kiji da mai yazo" Karbar wayar tayi a hankali suna kallon juna itada khamriyyan. "Sabrah nasan zaki iyah,ki dunga saka hakan aranki,kije karki bata masa lokaci,idan wani abu yafaru ki ƙirani zanyi magana dashi kinji" Ɗaga kai tayi,kaman wata kurmiyah,yau kam surrutu da kwainane sun kau babu su. Hijabinta ɗauka fuskarnan a kode tayi hanyar kofar gidan,kirjin ta sai dukan tara tara yakeyi Daga nesa ta hango motar tasa a ɗan gaba gidansu. Cikin sanyi take tunkararsa kanta a sunkuye har ta isa wajen motar. Murufin ƙofar takama ta buɗe,amma kuma jura ƙafar zuwa cikin motar shiya gagareta. "Ki shigo mana,ko anan zaki tsayah" Dec. Sadeeq ya faɗa cikin dakewa,wanda hakan yaƙara sakata cikin razana. Sakin murfin motar tayi tareda shigowa kana ta maida shi ta rufe. Sun ɗau kaman minti shida babu wanda yace komai,shine idonsa kyam yana kallonta,amma ita kam glass ɗin gefenta ta zubawa ido. "Yaushe kika zama kurmiyah ko gaisuwa babu" "Iyee na'am uhmmmm......ina wuni,ya hanya" "Lafiyah kalau,ya gida dasu khairiyyah" Shuru tayi naya amsa masa ba,dan tasan yayi ne dan tasan ya karanta littafin. "Mai yasa danazo gida a ranar na tarar bakya nan,shin nabaki izinin tafiyah gidanku ne?" Maganar ce tazo mata a bazata,wanda hakan yasa tarasa mai zatace masa. Kafin ta bashi amsa wayar dake kan cinyarta tayi ƙara,tana dauka taga sunan khamriyyah,da kaman bazata dauka ba saikuma ta ɗaga,bata bari tafara magana ba tafara magana ba tace. "Sabrah ki bashi wayar zamuyi magana!" "Naji amma kiɗan......" Kafin tagama magana khamriyyah takashe wayarta tareda ƙiran ta sadeeq ɗin. Ɗauka yayi domin yaji mai zatace masa. "Malam Sadeeq barka da rana,kana magana ne da Khamriyyah ƴar uwar matarka Sabriyyah. Batun abinda ya faru a tsaninmu nasan zakaji babu daɗi,amma kayi haƙuri bamuyi niyyar cutarwa a gareka ba,sannan ina mai tabbatar maka da gaskiyah sabriyyah take zaune dakai,duk da shi auren dawata manufah tayi. Duk wani laifi da mukayi maka harda na wanda ya fada kansu duk laifina ne,kuma nayi maka alƙawarin ina gama abinda nake zai miƙa kaina gareku,ammma dan allah karkace zaka saki sabriyyah kamaidata ƘARAMAR BAZAWARA,(littafin ƙawata Ummu najma) na roƙeka" "Naji to idan kingama magiyar,batun kamaki kuma yanzu case ɗin yabar hannuna,kiyi iyah ƙoƙarinki,domin ina mai tabbatar miki kin kusa zuwa hannu" "Wannan ba abin damuwa bane idan har bazaka yanke alaƙarka da sabriyyya ba,dama ni na shiryah ranar ƙin dillanci" Kashe wayarta tayi daga haka.(bazata sanja ba dai)ya faɗa aransa. Kallon sabriyyah yayi wacce tayi zuruzuru. "Shin waye yacemiki zan sake kine,kowa yake tamin magana akai,dama haka kika ɗauki alaƙarmu,ta warware a abu irin wannan?,bazan rabu dake ba Sabriyyah,saima nayi alƙawarin taimaka miki,amma bazan iyah sake yadda kimin irin wannan ba,kinyi na farko kinyi na ƙarshe,kin yarda?" Maimakon bashi amsa faɗawa tayi kansa tareda ƙanƙameshi tana shaƙar ƙamshin turarensa wanda tayi mungun kewa. "Kayi haƙuri mijina farincikina,hakiƙa yanxu nasan kayi nisa a zuciyata da bazan juri rashinka ba sam" "Sunanki yayi min daɗi SABRIYYAH,mai haƙuri yake nufi,amma tawa sabrar dai a hankali" Dariyah tasaka tareda haɗe bakinsu waje guda da sauri,dan dama tayi kewarsa ba kaɗanba. Sake rungumeta yayi bayan yaraba bakinsu,bayajin zai iya rabuwa da ita. "Duk da nasan bazan aikata daidai ba,amma zanyi iya ƙoƙarina wajen kubutar dake daga tarkon ɗan uwana. Inasonki sosai sabrahhh!!" Dec. Sadeeq ya faɗa a cikin zuciyarsa lokacin dayake shafa bayan ta. Taku _sadi-sakhna_ Ƴar mutan jama'are. *MABARACIYAH* _haƙƙin mallaka_ _*sadi-sakhna*_ (Yar mutan Jama'are) 31••32 Da safe da deejah ta tashi aiki suka hau na wanke wanken da salaha tace ta tayasu. ita dai har yanzu bataga Hajiyah saratu ba,saboda lokacin da suka zo ranar ta tafi gidansu masarautar Gombe,Babanta wanda shine wazirin garin ya rasu,yayanta ya hau,yau ake bikin naɗashi da kuma rabon gado. Yau zata dawo shiyasa su salaha ma da basa girki yau zasu taya su lami. Bayan sun gama wanke wanken ma wani aikin daban suka fara na gyara kayan miyah. Deejah ce ta kalli salaha tareda cewa. "Masarautar nan ta bani mamaki,banga ɗa ko guda ɗayaba wanda yake ɗan sarki a gidannan tunda na shigo,bayan an san gidan sarauta da yara" "Akwai yara duk da ba sosaiba,abubuwan daya faru shekaru goma da huɗu da suka wuce sune suka haddasa rashin wasu daga yaran gidan. Hajiya Fulani ƴaƴanta dama huɗune,babban shine Yarima Junaid,a ranar da abin yafaru aka nemeshi ƙasa da sama aka rasa,wasu suna cewa ma ya mutu,wasu kuma sunce mahaifinsa ne ya turashi karatu ƙasar waje,amma dai kowa yana zaton ya mutu ɗinne. Sai mai binsa Nana Khadija,itakuma tayi aure a masarautar zaria,da yayanta huɗu. Na uku shine yarima mubarak,wanda tun a ranar ya faɗi har yau bai sake motsawa ba, kuma da ransa. Ɗan autanta shine Jalal,hmmm faɗan nace miki halayyarsa,karki so ki tona ma,yarone mai ji da kyau sarauta sangarta da kuma ƙururciyah,duk abinda zai miki a gidannan babu wanda zai kallah bare ya ɗau mataki,ciki kuwa harda mai martaba. Zaman lafiyarki shine karki shiga harkarsa sam. Saikuma ƴaƴan Hajiya Saratu,ita ƴaƴanta guda ukune kuma dukka mata ne sai autanta shine namiji,daga Madeena sai kuma mai sunan mahaifiyar sarki wato Ruƙayya,ana cemata Amal. Ita madeena tana makaranta a Buk,aji biyu,ita kuma Amal tana secondry ss2. Saikuma ɗan autanta Abdussalam mai shekara goma sha biyar,yana jss 3. Dukkansu suna EMIRATE NURSERY,PRIMARY AND SECONDRY SCHOOL. Shida Amal tare suka tafi da hajiya saratu masarautar Gombe,garin kakanninsu kenan,yau idan suka dawo zaki gansu" "Uhm naji batunki,amma baki faɗamin ita Hajiya fulani daga wane gari takeba,ko kuma wace masarauta" "Ita ba jinin sarauta bace,saidai mahaifinta babban malamine kuma hamshaƙin mai kuɗi a garin maiduguri,suɗin ainihin ƴan shuwa ne masuji da kyau da kuma kuɗi. Naji ance a Dubai suka haɗu da sarki lokacin yana karatu a can,yana gabanta a makarantar,acan suka zauna bayan anyi aurensu har suka haifi Junaid a can. Jijjiga kai deejah tayi tana ajiye dukkan wani silin bayani dataji daga bakin salahan. Sai wajen ƙarfe ɗaya na rana tukunna suka gama shirya komai. Warwas deejah tayi a ɗakinnasu tana sauke ajiyar zuciya,dan daga gani bata saba irin aikin ba yau ya kamata. "Kai wlh dolema nagama abinda ya kawoni natafi,irin wannan wahala" Ita kaɗai take mitar,babu kowa a wajen bare ya tayata. Daga bayane salaha tazo musu da abinci sakuci ,kafi Sukayi sallah. Cikin ɗan bacci daya ɗauketa ta jiyo hayaniyar algaita da kuma ƙarar motoci. Tashi tayi kana ta leƙa window,wanda yayi dadai da shigowar motoci guda shida cikin farfajiyar gidan. "Inaga tawagar Hajiya saratu ne,ta dawo kenan" Deejah ta faɗa a ranta. Tashi tayi ta fito daga ɗakin tareda tsayawa a corridor ɗin shiga sashen hajiya saratun. Fitowa tayi daga mota zata shiga cikin gidan,Bakace ba sosai ba kuma katuwa,amma hakan bai hana mutum yaga kyan taba,murmushi take suna gaisawa dasu yadiko lami suna mata sannu. Tunda daga nan zakaga fahimtar juna da kyautatawar datayiwa ma'aikatan nata. Su amal ne ke binta a baya,ita tana sanye da wani yaɗi maroon doguwar riga,shikuma Abdussalam ƙananan kayane a jikinsa,dukkan yaran kuma fararene,saikuma suka ɗauko kamanninta,ubansu mai martaba suka iyo a farin fata. Wayace a hannunta tana dannawa tana yatsina fuska,irinnasu na ƴan masu iko,su yadiko lami sai gaisheta suke suna washe baki,amma ko kallonsu batayi ba,shima Abdul ɗin bai kulasu ba ya wuce,kaman wanda suke jin haushinsu. Takaicine ya shaƙi deejah datake gefe,batasan lokacin data ciji fatar bakinta ba. Dawakai aka shigo dasu uku da wani matashi mai kuladasu,yana ɗaya daga cikin gadonta da aka raba musu. Bayan komai ya lafane yadiko lami ta shigo ɗakin su deejan. "Ke deejah zo muje ki gaida Hajiya tadawo daga gidansu" Toh kawai tace tareda bin bayan ta. Koba komai dama tanda buƙatar ganin wajen sosai. Falo na biyu suka shiga bayan na daya wanda tun farkon zuwanta tasanshi. Waya take tana zaune akan kujera,kan amal kuma yana cinyartata tana wani turjewa,wai sai an bata mota tafita wajen ƙawayenta tacemusu ta dawo. Sauke wayar tayi bayan tayi sallama tareda kallon amal ɗin. "Ke banason sakarci fah Amal,babanku bayason wannan fitar akai akai,hakanma ki ɗauki mota,idan zakije driver ha kaiki toh,ina kuma bazaki je ba karki ƙara yimin maganar. Dirvern mu ya tafi garinsu,kije saleem da muka taho dashi drivern su ummah a can ya kaiki,tunda yace yasan garin" Tashi tayi tana turjewa ta fice a falon duk abinda suke deejah ta zuba musu ido tana kallon ikon allah. "Amm Lami mai kikace ma" "Eh dama hajiya yarinya ce nazo da itah,tanason aiki a nanne sai muka taho tare" "Ayyah ba laifi ai,yafi zaman banza,bata iya gaisuwa bane?" Sunkutarta lami tayi tana haɗe fuskaa,wanda hakan yasa deejah murmushi tareda cewa "Ranki ya daɗe baki bani damar gaisuwar bane,ina jiran ki bani izini ne,.....ina wuni ya hanya,an dawo kalau?". Ta fada tareda durƙusawa a kasan carpet ɗin. Mamaki abin yabawa su hajiya saratu,amsa gaisuwar tayi cikin sake murya kafin deejah ta koma ta zauna. "Sannunki da zuwa,dama Amal tana neman mai kulada sashenta,idan zaki iya sai ki dunga gyara mata,dan naganki kinada tsafta da kuma hankali,da alama zaku shiryah" Daga kai deejah tayi tareda cewa. "Ba matsala zan iya inshaallah" Kallon ta yadiko lami tayi da mamaki,ba itace tace bazata yi aiki anan wajen ba,mai kuma yakawo ta wajen. _______________ Wani ne zaune akan bakin mota ya naɗe hannu sai zuba surutu yake ga wanda yake sunkuye yana ɗaure dawaki a rumfarsu. Shina tsugunnen kaɗan kaɗan yake bawa nakan motar amsa,kana ganin fuskarsa kasan surutun ya isheshi,sannan kuma bai saba dashi ba,koƙari kawai yake. "Wai eemran bakajin mai nake cewa ne?" "Ina jinka mana mai kake so nace,nida yanxu nazo masarautar taya zansan mai kake faɗa,kaida kasha zuwa bayaune zuwanka na farko ba" "Hakane kam nasha zuwa wajennan sosai,amma nayi mamaki da aka cemaka ka dawo aiki daga gombe zuwa nan kuma ka yarda" "Aikin kuɗi nake a can ma ba garin mu bane,nan ma kuma ba garinmj bane aikin kuɗi zanyi,menene banbanci a ciki?" "Ahah babu kam,idan ka gama gyara musu muhallin zamu ɗan zaga gari?" "Ahah bazan je ba,inaso na ɗan huta kafin gobe na nemo musu abinci" Amal ce ta tunkaro inda suke tareda sauƙe idonta akan saleem ɗin,hakanne yasa yabada hankalinsa gareta,tareda barin zancen da suke da eemaran. "Ran gimbiya ya daɗe,ƴar sarauta jinin sarauta,gaba salama baya salama,tafatan gajiyar tafiya tabi jiki" Ya faɗa yana ɗaga hannu. Wani murmushin jin daɗin yabon tayi masa tareda kallon eemran wanda ko ɗagowa daga aikin dayake bayyi ba bare ya kalleta. "Wannnan kuma fah,shiba baya gaisuwa ne yayi banza da mutane" "Gimbiya kinsan sabone a gidan,shine mai kulada dawakan da aka taho dashi" "Kuma shine dan yana sabo yafi ƙarfin gaisuwa,koba komai ai a ƙasan mu yake" Miƙewa yayi daga wajen dawakan tareda kallon saleem wanda har yanzu yake kan motar. "Saleem ni zan shiga ciki,saina ganka" Da yazo wucewa ma ko kallon amal ɗin bayyi ba kaman an ajiye masa dutsi. Tsuke baki tayi tana binsa da kallo,kyakykyawane ajin ƙarshe,da badan wahalar duniya da kuma halin rashi ba,bayyi kama da wanda zai kulada dawakai ba. Saleem ne ya kaɗa mata makulli kafin ta dawo daga kallonsa. "Ɗan rainin hankaline,shib kowa ba amma yake nunamin taƙama" "Ki rabu dashi,nida nasanshi bada daɗewa bama haka nake zama dashi" "Aikuwa saina koyamasa hankali" "Bazaki iyaba,kibar zaka cikin gashinta gimbiyar garin katsina" "Okay manta kawai,dama anguwa zaka kaini,idi bayannan ya tafi gidansu,barina je na shirya nan da minti talatin" "An gama ranki ya daɗe" Juyawa tayi ta bar wajen tana jujjuya ɗan karamin kunkuminta,a dole sai an ganshi ko bayanan sosai. Duk abinda suke akan idon deejah,wacce tazo wucewa zata koma muhallinsu daga wajen hajiya saratu,murmushi tayi ganin abinda wanda aka ƙira da eemran yayi wa Amal. Haka kawai taji ya burgeta da halayyarsa ta ƙin ɗaukar raini,dan ta tsani ganin mutum yana ƙasƙanta kansa dan bashida komai,ya manta darajar da allah yayishi tayinsa mutum kuma iri ɗaya da wanda yake kwantar dakai garesu. __________________ "Ke zainabu kin tabbatar watace a cikin gidannan ta faɗamiki cewar maganin ya baci,ba malaminne ya faɗa miki ba" "Eh ranki ya daɗe na rantse da allah watace tafaɗamin,kuma a gidannan take,saboda na gasgata zargin hakan yasa na je ga malamin,shima kuma haka ya faɗamin. Hatta wanda ya bata maganin saida ta faɗamin,kuma bayanin dadai yayi ta wanda Malam Malafah ya faɗamin" Numfasawa Fulani Ateeka tayi tareda ƙara miƙe jajayen kafafunta wanda wasu mata guda uku suke matsa mata. "In hakane zanso naga wacece wanann yarinyar,indai a ranar data shigo gidannan zata iya faɗan wanda ya bata magani bayan ba mutum bane,to lallai tanada baiwa a jikinta wanda muke buƙatarta. Ki tabbatar kin kawomin ita nan naganta,sannan naji mai take takama dashi,duk da nasan itaɗin bakomai bace a kaina" "Angama saurauniyar Katsina" "Mtsww wani banza mulkin katsina mai za'ayi dashi,nida nake mulkar tsibiri nawa na kaina a ƙasar Australia mai zanyi da wani takurarrnen mulkinnan,duk da haka kuma matsayinna na sarauniya ko ban karba ba babu wata mahaluƙiyar da take doron duniyar nan dazata iyah karba,walau aljanace ko mutum,saidai idan bana numfashi" Ƙirari matan wajen suka fara mata,wanda hakan yaƙara kambama mata kai. "Ki ƙiramin ita da daddare,dan gobe nakeson barin kasar,zafinta ya isheni haka,akwai meeting danake dashi" Cikin sauri jiki na rawa zee-zee wacce sunanta zainabu ta tashi tana cewa. "Angama ranki ya daɗe,zan cika aiki yanda kike sonsa,da sannu Yarima mubarak zai tashi da kafafuwansa" Deejah a tafito daga banɗakin amal ta wanke mata,sa'arta ɗaya ma babu datti sosai,da batajin zata iyah. A falon hajiyah saratun ta haɗu da Ita amal ɗin ta dawo daga anguwar wajen magriba. "Ke makikeyi a dakina kuma batarda izini na ba" "Ki tambayi hajiya zata faɗamiki dalilin shigata ɗakin" Deejah tana gama magana Amal ta ɗauketa da mari. "Har ina miki magana mai kike a dakina kina cemin wai na tambayi hajiya,ni ban isa na tambayeki ba kenan" Jakadiya ce tashigo falon,da alama sarki ne ya aikota wajen hajiya saratu. "Uwa uwar sarakai mai yafaru naga kina fushi?" "Banni jakadiya,wanann yar rainin hankalince take gayamin magana mana" Kallon deejah jakadiya tayi tareda ta'be baki. "Ke kuma wane gangancinne ya ɗebeki da dayin hakan,hala ke sabuwa ce bakisan gidan sarauta ba" Daga haka ta shige turakar hajiha saratun bayan ta nemi iso. Kallon amal deejah take tareda dafe kuncinta,babban abin takaicin tasan tafi amal nesa ba kusaba,amma kuma ta daga hannu ta mareta dan rashin tarbiyyah. Hmm kawai tace tareda gocewa ta gefenta ta bar wajen. A hanyar komawa sashensu ne tana cikin duniyar tunani kawai ji tayi ta bugi mutum a gabanta. Saurin razana tayi tareda ɗagowa idonta dan ganin waye. Zee-zee ce take murza goshinta tareda cewa. "Ina kike gani haka,tun dazu nake gabanki amma baki ganni ba" "Yi hakuri,amma mai kike a sashennan hakanma dare ya fara" "Wajenki nazo,kin tuna maganar da mukayi jiya,har kike fadamin magani baci?" "Eh na tuna menene" "To dakika fadamin ban yadda dake ba,saina tafi wajen mai maganin daya bayar,abinda kika faɗamin shima haka ya faɗa,shine abin yaƙi barin raina har saida na faɗawa Hajiya fulani. Shine tace na faɗamiki tana nemanki da daddarennnan,tanaso taji wace irin baiwa kike ɗauke da ita" "Nikuma,ba wata baiwa,kawai naganshi ne,shiyasa na faɗamiki" "To idan ba baiwa bace nima na ganshi mana ko wani a cikin gidan?,dan allah ke wacece daga ina kika zo" Ɗaure fuska deejah tayi ganin yanda ta takura mata,dama kuma ga bakincikin abinda amal tayi maga,tunani take yanda zata koyawa yarinyar hankali ,sai ita kuma wannan ta bayyana da nata buƙatar,ga kuma wasu tambayoyi wanda batada da dalilin amsa mata su. "Shikenan kice ina zuwa idan nayi sallah" "Lallaima yarinyar nan,har mai girma sarauniyar katsina zakisa tana jiranki a turakarta?" "Eh idan bazata jiraba,shikuma allah daya haliccetane zai jirani kenan saina gama da ita kafin nazo nayi sallahr?" Daga haka tawuce tabar zee-zee a tsaye yauma da mamaki. Itakuwa deejah tasan dama dole zata nemeta idan zee-zee tabata labari,saboda zatayi zaton wani abin hajiya saratu take ƙullamata da ita,to duk yanda zatayi zatayi domin ganin ta maidata sashenta. Duk da deejah tasan hajiya fulani tana jiranta amma saida tagama abinda zatayi kafin taje shashennata. Wasu body guard ne bakin ƙofar sunsha baƙaƙen kaya,kana ganinsu kasan ba a nan ta samosu ba. Ƙiƙama sukayi babu wanda yakeda yunƙurin barta ta shiga wajen. Zee-zee ce tafito tazo shiga sashen taga deejah a tsaye. "Lahh ku kubarta tashiga baƙuwar hajiya ce,ita ta bata damar zuwa." Matsamasu sukayi itada deejah suka wuce,batareda sunce komai ba. Duk wanda yayi yunƙurin haɗa shashen Hajiya fulani dana hajiya saratu to yayi ƙarya,dan akalla sashen zai yi ɗarin na hajiya saratu a ƙyau da kuma alatun duniya. Dan mutum zai ɗauka ba a nigeria yakeba. Kalle kalle deejah take tayi har suka isa falo na uku a wajen. Komai na wajen kama daga kujeru da kuma su dinning da adon wajen da gold akayi musu ado,ga ƙamshin turarukan muski irinna zahirinnan. Mutum idan ba shiga yayi yagani ba zai ɗauka da gaske bane,sabida abin ya wuce tunanin mai hasashe. Wasu ma'aikatane mata masu kaya iri daya suka fara jera mata abin sha,dukkansu fararene basuyi kama da ƴan nigeria ba,basa fitowa a wajen,iyakacinsu yin hidimar abinci da kulada adon wajen. Ita dai deejah tana kallonsu har suka gama shirya komai a wajen,amma batayi yunƙurin taba komai a wajen ba har akayi minti biyar. Wata ƙoface tayi sliding ta buɗe da kanta,hajiya fulanice ta fito daga wajen jikinta sanye da wani jan yadi mai daraja,dan kodaga hada ido dashi mutum yasan in basshida shi nai isa sakawa ba. Tanada dan jiki amma batakai hajiya saratu ba. Saidai ita farace sol har jaja take,ga kyau kaman ita tazana kanta,musamman yanda jan yadin ya dauki fatarta. Zama tayi a kujerar tadake mazaunin mutum dayah,kuma take kallon inda muke zaune a ƙasa. "Naji abinda zainabu tacemin kin fada gameda maganin rashin lafiyar mubarak. Shin ke wacece kuma daga ina kike,sannan menene yakawoki wannan masarautar?" Shuru deejah tayi batace komai ba,da alama tambayoyin yawo suke mata akanta. "Ba roƙonki nake ko kuma neman jin uzurinki ba,umarni ne nabaki ki faɗamin,dan haka dolene yanzu ki fadamin ke wacece" Haɗiye wani yawu deejah tayi kafin tace. "Sunana deejah,ni yar gidan wani maharbine dayake ƙauyen garin Kurfi. Duk da shi maharbine to kuma yana bada magani,sanan kuma yanada sani akan ciwukan dasuka shafi sanyi,sammu,asiri,da kuma na aljanu. Nima nagaji abinda yakene saboda tun ina yarinya tare muke zuwa nemo magani a cikin jeji. Hakannne yasa na ƙware wajen gane ciwo da kuma nemo makarins. Muna zaune ne mu biyu,kasancewar mahaifiyata ta rasu. Wata rana sai aka kawomana harin,wanda mu taka sawun barawo mukayi. Wasu fulanine suka biyo barayin shanunsu,sukuma barayin sai suka iyo yankimmu,garin tsautsayi suna harbinsu suka harbe babana a wajen. Ina ƴar shekara goma sha biyu lokacin da aka kasheshi,hakanne yasa nashigo garin kurfi a daren na hau motar da bansan ta inace ba. A garin daura aka sauƙeni,bansan kowa ba hakan yasa na fara bara. A nan allah ya haɗani da wani bawan allah yarikeni bayan yaji labarina. Ina nan zaune a wajensa na fara karatu. Zuwa nan kuma wata makwanciyarsa ce taje gida,data faɗamin anan take aiki saina biyota domin nasamu abin kaina nima" Dahaka deejah ta karisa labarin muryarta tana rauni,da alamar batason tunoda abinda ya wuce. Jan numfashi hajiya fulani tayi,bayan taji abinda deejah tace,ganin babu wani abin zargi cikin labarin yasa tasaki ranta tareda sake jeho mata wata tambayar. "Naji mai kikace,har yanzu kim iyah haɗa magani ko kuma kin manta ,iya mai bata maganin kawai kika samu damar gani" "Eh bazanje ba,amma duk wani laƙani da babana ya koyamin yana cikin kaina,yine kawai banayi da ina gidan mariƙina" "Toh idan baki manta ba,inason na jarabaki zakiyimin wani aiki,idan kin ci jarabawar zaki zauna a sashennan kuma a cikin falonnan,sannan kuma aikin dazakiyimin zan biyaki da tsoka,kudin dazan baki sai ya gigita ki ma. idan kuma baki ciba akwai gagarumin hukuncin dazan baki wanda zai iya sanadiyyar tafiyarki barzahu,ma'ana a bakacin ranki na batamin lokaci da kikayi,idan kin shiryah ki fadamin" "Eh naji abinda kikace ranki ya daɗe,kuma na yarda na karbi aikin zanyi" Mamaki abin yabawa ba iya zainabu ba harda hajiya fulani,dan tayi zaton deejah zata fara karkarwa,saikuma taga babu abinda tayi,tana cikin nutsuwarta,kaman bata fahimci sharadin da aka bata ba. "Okay shikenan ki biyoni toh " Tashi hajiya fulani tayi tareda nufar wata ƙofah. Binta sukayi suma a baya itada zainabu. Deejah tayi zaton daki zata gani idan an buɗe ƙofar,saikuma taga ashe wani irin wajene da aka kewayeshi da glass,tsakiyar wajen kuma wani farin balarabene a kwance yana kallon sama,gefensa duk wasu wayoyine na wayarin ɗin abinci zuwa cikin jikinsa. Wasu mutane kuma mace da na miji sanye da fararen kaya suna ta bincike,da alama likitocine masu kulada shi. Ƙarisawa sukayi har gabansa,deejah tasamu damar ƙaremasa kallo,labarinsa taji amma batayi zaton ganinsa yanzu ba. Lallai duniya abin mamaki,tamkar za'a ƙirashi ya amsa,amma kuma babu damar hakan. "Ina so kiganomin abinda yake damunsa,wanda masu magani dayawa suka kasa ganowa. Gobe inada zuwa singapore,sati guda zanyi idan nadawo zanji amsarki. Kafinnan kizama cikin shiri,sannan karki kuskura naji zancen a wani ware,domin ina son sirri,wanda kuma bazai iya ajiyewa a ransa ba to zan karbi harshensa,ta yanda ko yaso faɗa baxai sami iko ba. Ki kula yarinya zansa masu dubamin ke kafin zuwa nanda satin. Kinada damar fita inda kike so,domin nemo amsar gwajinnaki" Hajiya fulani tana gama fadan hakan suka fito daga ɗakin da ɗannata yake ciki. Ita kuma deejah ta fita daga sashen jikinta sanyi ƙalau. Taku _sadi-sakhna_ Ƴar mutan jama'are. *MABARACIYAH* _haƙƙin mallaka_ _*sadi-sakhna*_ (Yar mutan Jama'are) 33••34 Tafiya take gaba ɗaya ta dulmiya cikin tunanin aikin da hajiya fulani ta bata,kwata kwata yanzu tsoron aikin takeyi,bayan kuma ta amsa zata iyah,tasan ko giyar wake tasha to babu damar ta zanye tace bazata iya ba,aikin gama ya riga da yagama. Mutum taji ta buga ta ƙarfi,da alama shima tahowa yayi da karfi bai kulada ita ba. Goshinta ta dafe tana murza wajen, tareda ɗaga ido dan ganin wanene. "Mai doki" shine abinda ta faɗa hankali kaman mai raɗa,hannunta kuma dafe da goshinta tana mulmulawa,wanda yake mata raɗaɗi" Shima gishinnasa ya dan riƙe,kafin yakalli bayanta inda ta fito,wato sashen hajiyah fulani,mamaki abin yabashi,dan shima ɗazu ya kula a can sashen ya ganta tana aiki,yanzu kuma da daddare ta fito anan. Share tantamarsa yayi saurin yi,dan a yanda yaketa saurin kar ya rasa sallahr isha ko cikekken lokacin tunani bashida shi. Bai ce mata komai ba ya juya da gudu yayi hanyar masallacin da suke shirin gama raka'ah ta farko. Har deejah tajuya zata tafi saikuma ta kalli carbinsa fari daya jefar a lokacin da sukayi gware. Tsugunnawa tayi ta dauka tareda hango bayansa yana daff da shigewa masallacin dayake gefenta. Nannaɗeshi tayi a hannunta kaman igiya tareda kaɗa kanta ta nufi sashensu danyin tata sallahr,da niyyar gobe insun haɗu ta bashi abinsa. Bayan ta gama sallahr salaha ta kawomusu abincin dare,sai mita take wai ina ta fita kalan saitayi gamo da aljani. Dariyah deejah tayi amma batace komai ba saicin abincin data fara,wace aljana zata gamuda ita bayan ita kanta itama aljanarce?. Haka suka gama cin abincin sai surutu salaha take mata,amma wani ta amsa wani kuma tace hm. Gabaɗaya tunaninta ya tafi yanda zata samo amsar ciwon yarima mubarak,domin samun shiga sashen hajiya fulani kaman yanda take fata. Dare mahutar bawa kowa yana bacci,amma deejah tana zaune ta saka wani waje ido a bakin barandar ɗakinsu,hannunta kuma wasu duwatsune guda biyu tana juyawa. Wani farin mutum ne shiba a sama ba bakuma a ƙasa ba yana kallonta da wasu fararen idanuwa,wamda ko kaɗan basuyi kamada na bil'adama ba. "Sumail yaushe ka dawo,kuma mai kake anan wajen?" "Uhm saboda kin manta dani saina manta dake?,jiya nadawo,saikuma na shinshinoki a inda ba'anan nasaba jinki ba" "Kuttt wai har yanzu baka cire ajiyarka a jikina na,tukunna ma a ina kasaka iyee?" Ta faɗa tana tashi tsaye tareda dudduba jikinta. Dariya yayi mai wata irin sauti irinnasu,saikuma yayi shuru tareda cewa. "Meyake damunki naga kin fada kogin tunani,tun dazu nake wajennan amma baki kulada ni ba,menene yafaru ki faɗamin yanzu,tunda abokinki yadawo ki share hawayenki,koma waye saina juyarda kamanninsa" Zare ido tayi tareda galla masa harara, "Har yanxu ka tuna wanann kalmomin,bai kamata yanzu ka dunga fadan haka ba?" "Ke da gangan nake,dazu ina tafiya sainaga jejin da muka zauna,abubuwa da yawa sun dawomin loka.........." "Dakata Sumail,ya isa haka dan allah,kafi kowa sanin yanda na tsani wannan lokacin" "Kiyi haƙuri nadaina,amma kuma ki fadamin yanzu mai ya faru" "Kasan mai nake a gidannan .....?" "Ahah sai kin faɗa naji" "Nan gidan Hajiya fulani ne,nasan ka tuna sunan koh" "Zaro ido yayi yana jijjaga kai tareda cewa. "Ai wannan dai wacce nasani,wato........." Saurin saka hannunta tayi bakinta tareda kallon gefenta,saida kuma tayi hakan ta tuna ashe babu mai jin maganarsa sai ita,ajiyar zuciya tayi tareda kwashe abinda tazoyi ta fadamasa,harma da aikin data bata,wanda idan batayishi a sati ɗaya ba sunanta gawa. Kuma tafi kowa sanin zata aikata hakan. "Ya kake ganin za'ayi Sumail,nima banyi tunanin zata bani aiki irin wanann ba,sumail idan har hajiya fulani takasheni kafin nasamo mata amsar abinda ta tambayeni,bazan iya yafewa kaina ba harna dudduge a cikin ƙasa. Duk da haka banso fadamaka ba sumail,saboda taimakon damukayiwa juna bamuyi danna roƙeka wani abuba" "Deeejah nasha faɗamiki duk lokacin dakike buƙatar taimakona ki faɗamin,bana ziyartarki dan ki nemi wani abu a wajena kibiyani ta wata hanya,alaƙarmu bata irin sauran masu ƙiran aljanu bace kaman yanda kike,kece sanadiyyar shiriyata,wanda a yanxune nakejin ni rayayyane sabanin da. Dan haka a shirye nake dana taimaka miki. "to naji,maika kake ganin za'ayi," "Eh to haƙiƙanin gaskiya bazan iya shiga wajen ba,dole saina koma shaiɗani yanda nake a da,inkuma ba haka ba musamu wani yaje mana,ko kuma ......" "Ko kuma me?" "Ko kuma ki dole saikin samo kunnen jaki na jikin tsamiyah(wani ɗan ƙaramin ganye ne dayake fitowa a ƙasan bishiyoyi),da kuma ruwan rijiyar data shekara ɗari,za'a saka ganyen a cikin ruwan sai a yayyafa masa,akwai abinda nake zargi,in shine zamu gane da wuri" "Bazan iya ganin ka koma gidan jiyaba,sannan bazan bi sa'bawa allah wajen ƙiran wani arne ba. Babu ta yanda za'a gane menene a jikinsa inba tanan ba,kona ɗauko maka hotonsa bazayyi ba?" "Ahah bazayyi ba deeejah,saboda akwai abinda zan duba ba iya na ganshi ba. Tunda bakyason wanann dole saidai a nemo kunnen jakin,shikuma gaskiya in ba'a samuba to zai ɗauki lokaci,dan kuwa abin yanada matuƙar wahalar samu" Komawa deejah tayi jagwabbb ta zauna jin abinda sumail yafaɗa,gabaɗaya tashiga damuwa. "Kinga ki kwantar da hankalinki,tunda wanann shine aikinki na ƙarshe,zanyi iya ƙoƙarina wajen nemomiki inshaallah,ki tsimayi dawowata a ranar na uku,in kuma bansamu ba har ranar ƙarshe to zanzo musan nayi. Kije ki kwanta ki huta,sanann kicire damuwa a ranki" Yana gama faɗan hakan ya 'bace 'batt tareda barta cikin tunanin daya sameta dama a ciki. Tashi tayi cikin sanyin jiki tashiga ɗakinnasu,gaskiyar sumail ɗinnne gwanda ta kwanta ta huta. Washagari ta da ƙarfe takwas tashiga sashen hajiya saratu domin gyara ɗakin amal,wanda yake cikin aikinta. Babu kowa a falon,dan haka kai tsaye da wuce ɗakinnata,saboda ranar monday ne tayi tunanin bazata sameta ba,saikuma ta ganta a cikin bargo sai juyi take. Yaye labulen window ta fara,domin bawa harske damar yalwata ɗakin. Wata tsuka amal taja kaman gaiwa,tareda dagowa dan ganin wanene ya aikata hakan. Haɗa ido sukayi da deejah waccce itama kallon idonnata takeyi,dan yarinyar tun a jiya taƙara bata haushi data mareta,musamman ma data tuno yanzu sanadiyyar haɗa idon da sukayi. "Waye ubanki da har kike da ƙarfin gwiwar shigowa ɗakina ki buɗe min window,ke kika rufesu da,wai me kikeji dashine dakike wa mutane wani jiji dakai,to kiyi hankali dani inba haka ba zan saitaki a gidannan kaman sauran. Idan kuma kinga bazaki bini ba kiyi yadda nace to ƙofa a buɗe take ki bar gidannan" Ta faɗa tana daga murya tareda gallawa deejah harara. Ita abin ma mamaki ya bada,dan haka tasaki baki tana kallonta,anyi kuwa yarinyar nan kanta daya kuwa?,wata zuciyar tace mata ,kanta ɗaya,kawai so take a ɗorata akan hanya. Wani ɗan murmushi deejah tayi tareda cewa,"aikuwa zan saka ta hanyar,dan gidan tazo wajen saka mutane a hanya" Wannan karon amal tabari da mamaki,ganin maimakon deejah ta bata haƙuri,saima dariya data yi" "Yarinya ki tashi kitafi makaranta ba faɗa zaki tsaya yiba,nikuma ki bani waje nayi aikina,in kuma kinaga bazaki jeba,ke tashafa,nidai ki bani waje toh" "Kuttt anya kuwa kinsan dawa kike magana,harni zakice na tashi na baki waje zakiyi aikinki,kuma a ɗakina?" "To wacece ke banda wacce nake gani a gabana,ko ƙafa uku ce dake tawa biyu,faɗamin naji,ko kuma kanki ne biyu nawa ɗayah,da banbanci ne nida ke a halitta da allah ya fifitani akanki. Inkuma batun muƙamin ubane,naga babankine sarkin bakeba,sannan uwarki ce sarauniyar bakeba,shikansa muƙamin Gimbiya yana hannun babbar yayarkkune wato Nana khadijah" Zaro ido amal tayi,jin a cikin jimla ɗaya deejah ta gama da ita,rasa abinda zatayi tayi,wanda hakan yasa tajefi deejah da filon dayake gefenta,tareda fita da gudu tana ƙwalawa mahaifiyarta ƙira. "Mommy! Mommy!!," "Miye kike zubamin ƙira haka,wai yaushe zaki girmane da,wannan sangartakar,koh abdul yayi abinda kike ne?" "Mommy,wanann mai aikin dakika ɗaukamin jiya na koreta bana sonta,banda raini babu abinda takemin,kiji abinda take faɗa waini ba gimbiyar gidannan bace?" "Karya take toh,yaushe kika zama gimbiyar bayan antynku tana raye,kedai kawai ƴar sarki ce,amma banda muƙamin gimbiyar katsina kam" Dafiyah abdul yasaka wanda yake sanye da uniform yana shan tea. Harara amal ta watsamasa tareda buga ƙafarta. "Kaikuma wayasaka dakai iyee" "Kekika saka dashi,tukunna ma tashinki kenan,baki shiryaba,kinyi sallahr asuba kuwa,na bugamiki ƙofah kuma banji motsinki ba" Shuru tayi tana soka kai tareda turo baki,kobata faɗana yanayinta ya nuna batayi ba kenan. "Wai nikam yaushe zaki girma na huta da wanann takaicin,sai son mulki kaman wata mai jiran gado,mainene a mulkin banda ni ƴasu,karatun danake ƙoƙarin sakaki kina ƙin yi shine dai gatanki bayan na allah,inkin maida hankali kanki,babu abinda kika sani kai kamar fanko,sai shegen girman kai. Deejah kuma dakika kawomin ƙara babu sanjatan da zanyi,inkuwa kika ƙara kawomim ƙararta,ko kuma tacemin kin mata wani abu,wlh keda mai aiki saidai kiga anayi,komai ke zakiyi dakanki. Zancen sallah kuwa allah yaga nayi iya yina,kabarin na daban naki daban,dan haka ke kika sani" Ganin ita da takawo ƙara karshe fadan ya koma kanta yasa takoma ɗakin,motsin deejah taji a banɗakin wanda hakan ya tabbatar mata wanke banɗakin take. Zama tayi a bakin gadon tareda shiga whatsapp tana jiranta ta fito. Har deejah kuwa ta fito daga banɗakin bata tashi ta shiga ba,ƙarfi da yaji bazata makarantar ba take nufi. Itadai data gama aikinta fitowa tayi suka gaisa da hajiya saratu,daga nan tafito domin yin nata harkar. Eemran ta hango a wajen dawakai,ya zage sai gyara jikin wani doki yake,wanda baya daga cikin wanda Hajiya saratu tazo dashi. Riga da wandone a jikinsa na yadi mai matsakaicin kuɗi,amma kuma babu wanda zai kallah yaga kazanta,bayan rashin kuɗin daya gani a jiki. Deejah batasan lokacin da murmushi ya subuce a bakinta ba ganin yanda ya ɗan zaburah yayi gefe,sa'adda dokin yayi wani haniniya alamar bai sanshi ba. Juyawa yayi gefe da gefe,ganin babu wanda yake kallonsa sai ya sau ajiyar zuciya,dan abin da kunya kana kulada doki,kace gadon gidankune kuma a kanga kana tsoronsa. "Uhm ka kwantar da hankalinka,babu wanda ya ganka,amma ni naganka ai" Dagowa yayi ya kalli deejah wacce ta tsayah a gabansa tareda riƙe ƙugu tana kallonsa tareda yin murmushi,wanda yafito da ainihin jinin fulanin dayake kan fuskarta. "Wayace miki tsoro nake toh" "Nima bance tsoro kake ba,kawai nace na ganka" "Meya kawoki nan wajen,bakida aikine da safennan?" "Daga wajen aikin nake nagama,zan wucene nace barina kawo maka carbin daka jefar a hanyar da muka yi gware" Mamakine ya kwanta akan fuskarsa tareda tunani. "Awwn nayi ta nemansa dana gama sallah ban jishiba,sai nayi tunanin ko a ɗaki na barshi,dana koma na duba kuma banganshi ba" "Uhm to jefarshi kayi jiyah,a hanya kana sauri" "Dama nima inaso na baki haƙuri akan bugekin danayi jiyah,ban kula bane sam,ina sauri karna rasa sallah" "Ayyah bakomai,nima kayi haƙuri toh" "Haƙurin mefah,nine na bugeki ai bake kika bugeni ba" "Bana wanann bane,nayi amfani da carbinka ne naja tasbih da asuba" Da faɗa tana miƙamasa,har ya miƙo hannu zai karba,jin abinda tace yasashi janye hannunsa tareda cewa. "Ahh to ki barshi a wajenki na baki,daama biyune dani,zan dunga amfani da wancan" "Ammma....." "Karki ce komai,har raina nabaki,banaso nayiwa mutum kyauta ya maryamin dashi,ko yaƙi amsa,zanyi zaton kin raina ne" "Ahah ban raina ba,nagode sosai da kyautar ka" Har a fuskarsa ta kula yanda yaji daɗin kyautar datayimasa. Suna cikin tsaye babu wanda yasake cewa komai sai sukaji hayaniya a bayansu. Dukkansu juyawa sukai suna kallom Yarima Jalal,ɗan gata majida kyau da kuma ƙuruciyah,kallo ɗaya mace take ta fola,wannan shine abubuwan da aka sanshi dashi. Cikin taƙama yake tunkarosu har yazo daff da inda suke,wasu maza guda biyu suna biyedashi,irin manannannun abokannan,masu mannewa ƴaƴan masu kuɗi. Ingarmar dokin yakama tareda ɗora hannunsa akan bayansa. "Wow ya wanku yayi kyau kuwa,daɗin jawo hankali,ko dokin sarki iyakaci,tunda nine mai hawa karagar garin kunga dolene nafara abinda za'a ƙara sanina a garin,ko ya kukace?" "Wannan haka yake,ko mutane basaso kaine zaka hau kujerar garinnan,babu wani yarima a yanzu bayan kai" Wani murmushi yayi tana kallon eemran tareda ciro kuɗi a wallet dinsa dollar. "Kayi ƙoƙari wajen gyarashi yanda nace,inaga zan ɗaukeka aiki ka daina yiwa waccar matar,ni zan ninka maka kuɗin data baka zuwa ɗari ma idan kanada buƙata" Yaƙarisa maganar tareda watsawa eemaran dalolin suna bin yadin jikinsa zuwa ƙasa. Kollonsu eemran yake a ƙasan,dan daman kansa a sunkuye yake. Duk abin mutum bazai fadi shin baƙincikine ko kuma takaici kwance akan fuskarsa ba. Juyawa yareema jalal yayi zai bar wajen,kaman ya tafi saikuma ya dawo tareda sauƙe idonsa akan deejah,wacce take tsaye kamar bata wajen tana kallon mai yake faruwa. "Ke kuma fah zazzafa,bansanki cikin masu aikin gidanann ba,yaushe kika zo" Jalal ya faɗa yana ƙarisa inda take,lallausan hannunsa yasaka tareda ɗago fuskarta,yana cizar jar fatar bakinsa ta ƙasa. Duk macen data kalleshi a lokacin sai allah ya kareta kafin tatsare kanta daga faɗawa tarkonsa. Fincike fuskarta tayi tareda komawa bayan Eemran wanda yake kallon jalal ɗin. "Kuttt kin san kuwa ni waye,har nace na yaba da surarki ki nuna min turjiyah,ki bani kanki nashayar dake daulah da kuma zuma,ki amince ko kuma ki amince dan dole" Ya faɗa da yaidararriyar muryarsa yana yarfar da hannunsa daya tabata dashi. "Kin batamin hannu da dattin talaucinki,dole saina jiƙaki da nairah tukunna da kuma gyara kafin kiyi daidai da wanda zanyi harka,zo nan wajen yanzunnan" Yafaɗa yana mata murmushin yaudara. Sake maƙalewa tayi a bayan eemran,duk da bata tabashi ba amma yana jin sautin numfashinta yana sauƙa akan bayansa,da alama tashiga cikin firgici" "Kayi haƙuri ranka ya dade,bazata samu amsa gayyatarka ba,saboda ita ɗin budurwata ce,an riga anyi mana baiko" Kallon ƙeyar eemran deejah tayi,jin abinda yafaɗa wanda yayi mungun bata mamaki. Shima yasan dole zatayi mamakin,dan yanajin yanda kallom da take masa yana shiga jikinsa. "Hmmm ina ruwana da baikonku,sati ɗaya kawai zanyi da itah ta dawo gareka,a tunaninka aurenta zanyi,ina kwanciya da matan aure ma idan sunyimin bare wata budurwarka. Nidai tunda na ƙyasa to saina kashe kishriwata da ita. Jameel ku miƙomin ita yanzunnan" Tahowa sukayi zasu riƙo deejah daga bayan eemran,shikuma ya riƙe hannun wanda aka ƙira da jameel ɗin,ƙarass ya karyashi kaman ya samu karas. Kallon idonsa suke wanda yayi jawur,yayinda jijiyoyin jikinsa sukayi 'baro 'baro a jikinsa. Duk wanda ya kalleshi a lokacin koda na mijine dole tsronsa ya ɗan ɗarsu a ransa,amma ko kaɗan deejah bataji ɗigon tsoronsa a ranta ba,saima wani jin protective da take ji a tareda shi,koga sumail dayake ba mutum ba batajin hakan kaman yanda take ji ga bawan allah eemran,wanda yaune ganinta na uku dashi a rayuwarta. Matsawa yarima jalal yayi yana kallon eemran ɗin,shikuwa wanda aka karyawa hannu hankalinsa yana kan ciwon dayake ziyartarsa,sai ihu yakeyi. Fadawa ne suka rugo da gudu damin ganin mai yake faruwa. Yarima jalal ne ya kalli ɗaya daga cikinsu tareda cewa. "Maza yi sauri ka ƙiramin sarkin dogarai da kuma shamaki,haram da Uwar bayi" __sarkin dogarai a sarautun gargajiyah shine mai kulada dukkan shige da ficen abinda yake faruwa a cikin fada. __Shamaki shine shugaban masu kulada duk wani doki a cikin fada,kama daga shigowarsu fitada su harma da kuma masu kuladasu da abincinsu. __Uwar bayi a da itace mai kulada duk wani bawa a cikin fada,kasancewar yanzu zamani yazo,bayin fada sune matsayin ma'aikata,sai yakansance wani wajen ana ƙiranta da uwar ma'aikata na mata,a sashen matan sarki da sauran iyalansa. __Jakadiyah kuma itace ƴar aike tsakanin sarki da kuma matansa a cikin gida. Da sauri cikin rawar jiki wanda aka aika ɗin ya furma gidan nemo wanda aka faɗamsa yana baza babbar riga. Can da kaman minti talatin dukka suna tsaye sai gashi ya dawo suna biyeda shi a bayansa. Kallonsu yarima jalal yayi shima ransa ya baci sosai. "Kai sarkin dogarai kaine mai kulada shige da ficen kowa a cikin gidannan,yaushe wanann mutanen suka shigo cikin gidannan. Sannan kaikuma shamaki waya baka izinin ɗaukar wannan aiki a cikin fada. Ke kuma shugabar ma'aikata inaso ki faɗamin menene aikin ita wanann a cikin gidannan" Dukkansu diri diri suka farayi,dan kowa a cikinsu yasan rashin mutuncin yarima jalal a cikin gidan. Sarkin dogarai ne yafara magana,wanda deejah tana kallonsa ta ganeshi,shine wanda sukayi ta magana shida yadiko lami farkon zuwanta. "Eh toh ni ban binciki ita wanccar daga inda tazo ba,saboda naga tare suka shigo da lami,wanda an santa sosai tsawon kusan shekara goma. Shikuma wannan saurayin Hajiya saratu ce tazo dashi daga gidansu,ka tambayi shamaki tunda a bangarensa yake" Sarkin dogarai yanayin shuru shikuma shamaki ya cigaba. "Eh hakane,shine ya taho da dawakan hakiya saratu,kuma shike kulada su daga lokacin,dayake nasan babu wani abin cutarwa shiyasa bancd komai ba,musamman da sukace dama a canɗin yake aiki,ba'a taba samun matsala dashi ba" Ke kumafah shugabar ma'aikata?" "Eh kaman yanda sarkin dogarai ya faɗa hakane ranka ya daɗe,tare sukazo da lami,tace mana ƴar maƙotansu ce,kuma babu matsala a tareda ita,dan itake kulada sashen hajiya amal ma" Numfasawa yarima jalal yayi cikin ƙunar rai kafin yace. "Duk naji abinda kukace,saidai ku sani wanann ƙananan mutanen sun saba dokata saboda basu sanni ba,saboda basusan ƙarfin ikona a gidannan ba. Kai shamaki inaso a yanzu basai an jimaba ka koroshi daga aiki a gidanann,sanann kaikuma sarkin dogarai ka miƙashi ga dogarai su masa bulala ashirin. Ita kuma itama ta daina aikin datake a gidannan,kuma zata koma sashena dayin aiki,kullum ita zatayi komai a wajen,harda sharar filin wajen. Na gama magana koda mai ja anan wajen" "Gani nan nice mai ja da maganar taka,sanann kuma hukuncinnaka na sokeshi bayyiba,saboda mutanen dakake ƙoƙarin kora nina ɗaukesu bakaiba,dan haka saika bari idan ka dauki naka ma'aikatan sai kayi yanda ranka yakeso,kaji jalal?" Hajiya saratu ta faɗa lokacin datake ƙarasowa wajen,idonta kyam akan nasa,kana ganin kallon da take masa kasan dama ta daɗe tana shaƙar tijararsa a gidan. Shima kallonnata yake cikin rashin kunya,idonsa a tsaye. "Eh ma'aikatankine,amma kuma ni nan mai jiran gadon sarautar garinnan inada ikon dazan zartarwa kowa hukunci a cikin gidannan,ciki kuwa hardake hajiya saratu" Mari ta watsamasa tassss a kumatunsa na dama,bakinta har rawa yake dan bacin rai. "Kai harka isa kayimin rashin kunya bayan ka shiga gonata,ga bana aka yankewa yayanka cibi ma ba kaiba,sanann yanda kake ɗan sarki kake taƙama,nima ƴaƴana ƴayansa ne,yanda uwarka take matarsa haka nima nake matarsa,ko kai baka kaini iko a cikin gidanna ba,ƙafa nake ɗagama saboda a zauna lafiya. In jinin sarauta ne na gajeshi tun kafin nazo gidannan. Inkuma kana ganin ka isa kaman yanda kake faɗa,kasa ubannaka ya koreni a yau basai gobeba,inkuma har yanxu baka kaiba,to ka jira saika hau mulkin da mafarkin banza kake kowa yana kallonka,kaida mulkin garinnnan saidai kaga anayi. Mai mulkin wajen yana nan yana zuwa idan lokaci yayi. Karka fasa muzuba nida kai a cikin gidannan,uwarka tayimin ta barni bare kai" Kana ganin yanda take magana kasan tashaƙa dayawa. Shima kanƙance ido yayi yana hararata,daga nan yabar wajen yana yimata kallon zasu haɗu. Taku _sadi-sakhna_ Ƴar mutan jama'are. *MABARACIYAH* _haƙƙin mallaka_ _*sadi-sakhna*_ (Yar mutan Jama'are) 35••36 Kowa watsewa yafarayi a wajen,ciki kuwa harda dogaran,ganin wanda ake faɗan dominsu ma sun bar wajen. Tafi eemran yake deejah tana binsa a baya nesa dashi kadan,babu wanda yake cewa komai a cikinsu,da alama abinda ya faru suke tunawa. "Kayi haƙuri" Shine abinda deejah ta faɗa cikin sanyin rai, "Da akayi me kenan kike bani haƙuri" "Kana ƙoƙarin rasa aikinka akan kareni daga gareshi,nagode sosai" "Badan nasanki nayi hakam ba,nayine saboda kina a matsayin ƴa mace,kowacce mace ma idan naga za'ayi mata haka musamman idan tashiga bayana to sai inda ƙarfina ya kare,dan haka ki daina yimin godiya" Zuciyarta ce ta sosu da maganganunsa,bata san dalilin hakan ba. Har yafara tafiya ta tafi da sauri tareda shan gabansa. "Kaine aine mutum na farko a rayuwata bayan mahaifiyata daya taba yunƙurin tsayamin saboda wani abu zai cutar dani. Koda zaka ganni a matsayin ƴa mace kawai,ko kuma zaka ganni a matsayin wacce kasani,wanann bai shafeni ba,abinda nasani shine ka ƙara daraja a cikin idonanuna fiyeda koyaushe,irinku cikin al'umma ƙalilanne. Dan haka inayimaka godiyah sosai,ita kaɗaice abinda zan iya baka wacce nake da,idan bazaka karba bama nasan ka jita a kunnuwanka,sannan sunana deejah,koda a ganni a wani wajen zaka ƙirani nikuma ban ganka ba. Nasan sunanka eemran,suna mai daɗi,indai na ganka koda bazaka amsa ba zan ƙira sunanka,kunnenka su saurari jin amon muryata a duk lokacin da idanuwana sukayi tozali dakai" Tana gama maganar tasake masa wani murmushi mai tsada tareda dagamasa hannu tabar wajen. Shikuma ta barshi a tsaye sororo yana binta da kallo. Wannan ranar haka ta wuce deejah basu sake haɗuwa da eemran ba,kowa yana nasa harkar. Yau kimanin kwana uku kenan haɗuwar deejah da sumail,gobene yayi mata alƙawarin zaizo idan har yasami abinda yaje nemo mata,idan kuma bai samuba sai ana gobe aikin zai ƙare kafin ya dawo. Duk wani zirga zirga da murmushi datakeyi na dolene dan babu yadda zatayi.amma cikin zuciyarta jitake tamkar tangaranne yafashe. A zaune take a wata baranda tana kallon eemran yana sakawa dawaki abinci,shida wani yaron shamaki. Dariyah ita kaɗai tayi,tun ranar da abin yafaru duk sanda ta ganshi saita ƙira sunansa,wani lokacin da waiwayo bai ce komai ba,wani lokacin kuma ya shareta. Yanzun ma ɗaga murya tayi yanda zaiji tace. "Eemraaaaan" Shuru bai amsa mata ba tasake cewa "Eeeemraaaaan,bazaka amsa ba ko,idan baka amsa bama,kunnuwanka nasan sunjini kuma sun amsa min,sannu da aiki,na saƙƙo na tayaka?" Har sanann bai kulata ba,duk da tadan yajita daga yanda yake dan ƙaramin murmushi. Tashi tayi daga wajen ta nufo inda yake,hannunta riƙe da ɗan karan ciyawa tana juyawa. Murzashi tayi a bayansa yayi saurin dafewa tareda zuyowa a razane. Dariyah tasaka harda tsalle,yanda yayi da idon kaman an kwacewa yaro feeda. "Iyeeee jarumi da tsoron tsinke,nayi zaton yanzun ma bazaka juyoba ai" "Ke miye haka wai,duk da nayi shuru na rabu dake amma saikinzo har wajennan kina mace,ki daina ƙirana irin haka,kina mace bai kamata kina wannan wasan ba da kuma ɗaga muryah" Ya faɗa cikin alamar faɗa,da alama ya ƙosa da abinda take masa. Sanyi jikinta yayi,idonta yayi raurau kaman zai kawo ruwa. "Kayi haƙuri,banyi tunanin zakaji babu daɗi haka har haka ba dan ina kulaka,dama har haka na takura maka?. Ba yanda kake zato nake ba,ina ganinka ne kaman wanda nasani kuma nakeda shi a wannan wajen,ina cikin damuwa ne da fargabar rasa rayuwata,ƙiran sunanka danake da tsokanarka shikaɗai ke fidda ni cikin tunanin halin danake ciki. Amma bazan sake kusantar inda kake ba daga yau eemran,nagode da kyautarka,da kuma cetona dakayi ranar" Juyawa tayi zata bar wajen,yayinda hawayen dasuke kwance a idonta suka samu damar zubowa. Har tafara tafiyah taji muryarsa takama haruffan sunanta a karon farko na zamanta dashi. "Deejah,deejah!!!" Duk da yanda tayi fushi dashi kuma take ƙoƙarin barin wajen kasawa tayi,ga wani bugu da kirjinta yake kaman ana doka guduma,hannunta tasaka ta riƙeshi domin kar bugun ya wuce makaɗi da rawa. Takowa yake a hankali zuwa inda take,yayinda itakuma takejin kaman ta zura da gudu,dauriya kawai take. "Deejah duk abinda kika fahimta akaina ba haka bane,na faɗane saboda ki daina ɗaga muryarki kowa yana ji,sannan kuma kina tsalle maza dayawa suna kallon jikinki,wannan abinne yake batamin rai,gani nake kaman kowa idonsa a kanki yake,kiyi haƙuri ni mutumne mai kishi sosai" Saurin ɗagowa tayi tana kallomsa da niyyar ya ƙara mata bayani akan abinda yake nufi. Ɗan murmushi yayi tareda kallon cikin fararen idanuwanta wanda suka ɗan surka ja ja ja a cikinsu. "Duk tambayar da kike buƙata zan amsamiki da yamma,a lambun da nake zama kina zuwa ƙiran sunana. Menene ya faru wanda yake ƙoƙarin ɗauke rayuwarki?" "Nima zan faɗamaka a wajen idan ka bani karin bayanin wannan maganar taka" "Toh shikenan ina jiranki da ƙarfe huɗu,allah yasa karki banni nayita jiranki" "Bazan ta'ba barinka kana jirana ba,zanzo,nagode da kulawarka" "Nima nagode da kulawarki" Dariya tayi tareda rufe gefen fuskarta tabar wajen,binta yayi ta kallo,jiyake kaman ya bita su zauna karsu rabe koda da daƙiƙa ɗayane.Hannunsa ya ɗauka ya ɗora akan saitin kirjinsa inda zuciyarsa take bugawa dominta. Da farinciki deejah ta isa ɗakinnasu,gaba daya ta manta da wani abu daya ke shirin tunkarota na dawowar hajiya fulani,burinta kawai yamma tayi,danji take kaman ta jawota. Kasancewar bawani kayane da itaba,dan haka bada damu kanta ba,dan tasan idan ƙaryar adone daga ita harshi ba wasu bane na azo a gani. A bakin swimming pool ɗin dayake can bayan gidan ta hangoshi yana saka kafarsa a cikin ruwan. Duk a wanda ya ganshi a lokacin bazai taba alaƙantashi da kulada dokiba,ga yanda sumar kansa ta kwanta lufff. A hankali take taka ƙafarta har taje daff da inda yake zaunen. "Kin ƙara minti biyar a yanda mukayi" "Kayi haƙuri" "Ya wuce,zauna ga waje nan" Ya faɗa yana nuna mata gefensa,zama tayi itama tareda tsoma ƙafar tata a ruwan. Shuru sukayi kaman kurame babu wanda yake cewa komai,ɗagowa yayi ya kalleta tareda cewa. "Meyasameki kika canja lokaci ɗaya,ɗinke miki baki akayi ko mai" "Ahah bakina ƙalau yake,kawai surutun yanzu na barmaka ne,ka manta kai kace kanada abinda zaka faɗamin?" "Babban abinda nake son sanar dake,bazan iya ba a yanxu koda inada buƙata,saboda wani muhimmin dalili. Tunda nazo gidannan ko abokina banji inason yin magana dashi ba kaman ke,ina jinki a cikin raina fiyeda yanda kike tunani,wani irin abu zuciyata takeyi idam naganki cikin ƙunci ko kuma naga wani yana kallonki,musamman yanda yarima jalal yayi ƙoƙarin yin.....,......" Tsayawa yayi da maganar na ɗan lokaci kafin yacigaba da cewa. "Ki amincemin ƙiran sunanki a duk lokacin dana ganki,sannan inaso yazama nine yanzu zan dunga ɗaga miki hannu a duk lokacin dana ganki. Shin zaki amincemin hakan?...." Ɗaga masa kai tayi da sauri tareda ƙoƙarin mayarda ƙwallar datake shirin zubowa a idonta. "Kema kincemin zaki faɗamin wani abu dayake barazana ga rayuwarki,menene wannan ɗin" "Uhm.....uhm emran daka bar wannan" "Bazan iyaba deejah,ke kika fara ƙoƙarin fara kulla alaƙa a tsakanin mu,a kisani a zahiri kika rigani,a baɗini na daɗe da son yimiki magana,tun ɗazu zuciyata cikin zullumi take da kuma fargabar shin menene yake damun rayuwarki,ki faɗamin deejah,nikuma nayi alƙawarin taimaka miki matuƙar zan iya. Sannan bayannna inason kiyi min alƙawarin zaki sanar dani duk wani abu dazai kawo miki barazana a rayuwarki kinji" Ɗaga kai deejah tayi kafin tafara bashi labarin yanda sukayi da hajiya fulani akan rashin lafiyar yarima mubarak. Harma da tarihin ƙanzon kuregen data bawa hajiya fulanin. "Jibine hajiya fulani zata dawo,har yanzu bincike nake akan maganin,amma inshallah nakusa ganowa,saidai kuma har yanzu ina fargabar idan nakasa fah" Wani zuzzurfan tunani emran ya tafi,wanda babu wanda yasan mai yake damunsa sai sarki allah. Kukan deejah daya ƙara saurine ya dawo dashi cikin halin dayake ciki. "Amma meyasa kika karbi wannan aikin bayan kinsan yanada matuƙara wahala" "Nima bansaniba....tace idan naƙi amincewa ma a bakin raina" "Hmmm" Shine abinda emran yace,kana ganin fuskarsa kasan akwai abubuwa kala kala a cikinsu. A haka zamannasu na wajen yaƙare, emran sai rarrashin deejah yake da bata baki. Fitowa sukayi daga wajen suna hira da dariyah,kaman basune sukayi jigum ɗazu ba saboda muguntar hajiya fulani. "Uhm na rakoki yau kam har bakin sashenku,ki shiga ina kallonki kafin na tafi sallah. Sannan karki manta,banda ɗaga hankali,allah yana tareda ke,nima ina tareda ke" Murmushi deejah tayi masa tareda ɗaga masa hannu. "Nagode emran da lokacinka a yau,haƙika kai na musammanne,kayi sauri karka rasa sallah,gobe idan nagama aiki zanzo tayaka hira" "Shikenan zanyi ta jiranki har sai na ganki,idan kika zo zan barki kibawa doki abinci a hannu" "Da gaske,wow karka basu abinci harsai nazo,nizan ciyardasu dukka,kaikuma ka koma gefe ka huta" Juyawa yayi yana kallonta tana kallonsa har ya ƙulewa ganinta. Da daddare kowa yana kwance,amma deejah sai kaikawo take a barandar ɗakinnasu yauma tana jiran zuwan sumail,agogon karamar wayarta ta duba,ƙarfe biyu da rabi. Magana ta farayi cikin takaici. "Hmmm dama nasan ai ba'ayin abu dakai ya tafi daidai,wani inya ganni yace tsafi nake da tsohon darennan,kai ni nagaji" Hanyar tafiya tayi zata shiga ɗaki,saikuma taji dariyarsa a bayanta. Tsayawa tayi tareda juyowa ta dire masa harara kaman yanda ta saba. "Keda waye kike sababi haka,ko saurayinnaki ne ya tabaki" "Ka ganmu ne ɗazu a zaune?" "Na ganku mana,lallai kin iya kafce ba kaɗan ba,ji yadda kikeyi kaman gaske" Kutt da kana nufin bada gaske nakeba?" "Haba,ki faɗawa wanda bai sanki ba,kece fah deejah kuma Mabaciya ko me?. Taya zan yadda kece zaki faɗa soyayya mai zurfi irin wannan kuma a kwana uku kacal,inaga ko mutuwa yayi sau ukun a lokaci guda,zuciyarki bazata kai kansa ba bare kuma. Na tabbata wani abu kike so a wajensa idan ba haka ba ko kallonsa bazakiyi ba" Ya mutsa fuska deejah tayi,da alama ko bataso to sumail ya ganota.. "Ya isa toh,nibada mungun nufi na rabeshi ba,kawai akwai zargin danake akansa ne,daga nagano gaskiya zan barshi yayi harkarsa." "Zargi wane iri kenan,kuma kike ƙoƙari zefa zuciyarsa cikin kogin sonki,duk da naga shima da alama baya nan yakeso a wajenki,dan hankalinsa yafi kaiwa kanki da kika bashi labarin abinda yafaru tsakaninki da waccar matar" "Oho shiya ji wajen,dama ina ɗan shakkarsa ne shiyasa nakeson sakashi cikin idanuwana,don jiya na ganshi yana kewaya sashen hajiya fulani da daddare,lokacin danake jiranka. Oh ni na manta,ina abinda zaka kawomin ɗin,an dace ko kuwa har yanzu dai" "Ba'a samoba har yanzu dai an......." "Dan allah dagaske baka samoba" Ta faɗa tana zare ido. Dariya yayi tareda miƙamata abin a cikin wata kwalba,da ruwa a cikinta sai kuma ɗan ganyen a ciki. Karba tayi tareda ajiyar zuciya tana ƙara kallon kwalbar. "Nagode nagode,yanzu yazamyi kenan?" "Uhm babu,kawai ruwan zaki fatsa a jikinsa da ganyen,ko yaya indai aljanu ne suka tabashi ko kuma wani ciwone zakiga yayi girgiza. Idan kuma yayi shuru,ki sake yi a karo na biyu,idan yasake yin shuru kisake a karo na uku. Idan har sannan shuru to abinda nake zargi ya tabbata,wato babu kuruwa a jikinsa an ɗaiketa,(rauhu). Rauhunsa baya nan an ɗaukeshi shiyasa bazai motsaba. Wannan kenna sauran yana aiki na gareki,ni zan koma wajen karatuna,hutun da'aka bani ya ƙare" "Nagode sosai sumail da taimkonka,allah ya bada sa'a,ya sauƙeka lafiya" Daga haka ya bace ya barta ita kaɗai da kwalbar a hannu tana kallonta. Komawa tayi ta kwanta bayan tabawa kwalbar ma'ajiyi mai kyau. Da safe kuwa gaba ɗaya ta manta da haɗuwa dazasuyi da emran,hanyar sashen hajiya fulani ta nufah,domin a yanzu tafara ganin nasararta ta ɗaukar fansa tana bayyana. Kallonta suke da mamakin ganinta da safe,amma basuce komai ba suka matsa mata ta wuce. Kallon falo tayi wanda aka sauƙeta,kaman ba yanzu safiya ta wayeba,ma'aikatan sai hidimarsu suke. Bata kulasu ba sai wawwara ido take,da alama zainabu take nema. Hangota tayi akan dinning tana ta wawurar cinyar kaza.. Ƙarisawa wajenta deejah,ita abinma har dariyah ya bata. "Barka da safiyah yaya zainabu,kin tashi lafiya" Harara ta watsawa deejah tare cune baki. "Wannan wane irin sunane haka,wai meyasa ake min kallon tsofine?" "Saboda ke tsohuwar ce,kuma naga hajiya da zainabu take ƙiranki " "Naji menene ya kawoki da safennan,kin samo amsar gwajinkine" "Shinazo na samo dai a yau inshaallah,yanzu izinin ki nake nema zan shiga wajen,tunda kece ta hannun damanta" "Ta hannun damanta kuma?....kinga nayi kama da wannan matsayin,rufamin asiri na mutu maza su kaini,ta hannun damanta yau zata dawo daga dubai,ta turata wani taro" Ta faɗa jikinta har rawa yake kaman wanda tayi wani zunubin. Yar dariyah deejah tayi tareda cewa. "Naji to,yanzu dai nunamin inda yake,dan na manta ganina dashi na farko." Tashi zainabu tayi daga wajen kwanon naman,daga gani bata ƙoshiba,dan sai kallon naman take. Hanyar da sukabi wancan lokacin suka nufah. Suna tafiyah deejah tana nazarin wajen a cikin kanta har suka zo bakin ɗakin. Zainabu ce ta buɗe ta shiga,kafin itama deejah tabi bayanta. Kaman koyaushe yana kwance kansa yana kallon sama kamar zai amsa duk abinda aka faɗamasa. Raɗawa zainabu tayi a kunne,akan za'a iya bata waje daga ita sai shi? Jugum zainabu tayi kafin ta kalleta. "Eh zasu fita kiyi aikinki tunda sakaki akayi,amma minti goma kacal,daganan zasu dawo" "Bandake za'a fitane ?" "Ahah kiyi haƙuri,idan inason raina to dole na tsaya a wajennnan,dan har yanxu hajiya bata yadda dake ba,ina baki saniba ma duk gidannan akwai camerar tsaro" "Okay shikennan,amma ki ɗan koma da baya,idan kina son rayuwar taki yanda kika ambata" Fitowa da kwalbar deejah tayi a aljihun rigar ta. Buɗewa tayi kaman mai tsoron karta fashe kafin ta fito da ganyen dayake ciki. Fatsamasa tayi a fuska na farko,amma shuru bataga alamar motsiba. Maimaitawa tayi har sau uku amma babu alamar komai,maida kwalbar tayi ta rufe kafin ta kalli zainabu. "Zamu iya tafiyah nagama abinda zanyi" Daga kai zainabu tayi kawai,mekenan tayi yanzu,itadai bataga wani canji a jikinsa ba,amma daga ganin fuskar deejah zaka san hankalinta ya kwanta,alamar tasamo abinda aka umarceta. Fita tayi daga sashen bayan tayiwa zainabu sallama,in ba doleba kwata kwata batason abinda zai kaita wannan wajen. Kowanne sakan dayake bugawa na lokaci a wajen,bugawa yake da ƙara tsanar hajiya fulani,da kuma ƙaramata ƙarfin gwiwa na ɗaukar fansa. Saida ta fitone wajen ƙarfe goma sannan kafin ta tuna da zancen da sukayi da emran. Yar tsuka ta ɗanyi har zata tafi sashensu sai kuma taga rashin dacewar hakan,yanzu haka yana cam yana jiranta,ta faɗa a ranta. A bangaren eemran kuwa a zaune yake akan wani dutsi yana juya wani abu kaman ƙwallo ƙarama a hannunsa. Tunda ɗazu yake zaune a wajen har rana tafara isoshi,sai yazo tashi yafara aikinsa,sai kuma yatuna da yayi mata alƙwarin zai jirata,duk da shima har ransa bawani jin zuwantan yake ba,amma yanajin babu daɗi ya saba mata alƙawarin daya ɗauka. Jiyayi a jikinsa kamar ana kallonsa,wanda hakan yasa ya juya gefensa na dama,a tsaye take da goduwar riga a jikinta,saikuma mayafin datayi rolling a kanta.. Bugun zuciyarsa ne yaji ya ƙaru katt kafin ya koma yanda yake. Yana mamakin irin wannan yanayin dayake ji a iya gareta baga kowaba,tunda yake yasan bai taba shiga wannan yanayin ba,tukunna ma bai shirya shigansa ba koda yanada buƙatar hakan. Zuwa yanzu yafara tsoron tarayyarsu da deejan,kar a garin neman gira shiya rasa idonsa gabaɗaya fah. Takowa take a hankali,idonta nakan fuskarsa wanda shima ya tsura mata ido.. Tausayinsa ne da kuma jin babu daɗi na tsayar dashi yana jira suka mamaye ranta. Maida idonta tayi kan bakinsa wanda ya jajur,da alama matseshi yayi a cikin bakinsa yabada wannan kalar. Ɗan runtse ido tayi tareda control ɗin zuciyarta dan karta kawo mata negetive thinking a wannan lokacin. "Eemran ina kwana,duk da ina wuni ma yayi kusa,dan allah kayi haƙuri na tsaida ka,wani muhimmin aikine ya taso wanda nakeson yinsa a lokacin" "Daga yanda kike bada labarin nasan yanada muhimmanci sosai a wajenki aikin" "eh to kusan hakan,aikin dana faɗamaka hajiya fulani ta banine,alhamdulillah nagano amsar abinda yake damunsa yanzu. Ta faɗa tana faɗaɗa murmushinta,ta wata fuskar kuma tana nazartar eemran ɗin,dan ganin wane yanayi zai nuna. Dan murmushi kawai yayi tareda maida kallon wajen dawakan da suke ɗaure. "Muna masa fatan allah ya bashi lafiya,ko domin wannan yaron ya daina ganin shine da mulkin garinnan,naji daɗi daya zamo yanzu kin fita a cikin barazanarta,yanzu dai tashi mu tafi bayin allah suna jiranki ki basu abinci" Tayi mamaki da bai tambayeta abinda yake damunsa ba,saikuma tafara tunanin inaga zairginsa take a da leƙen asirin kawai,yanzu haka ba abinda yake nema a wajen. Wasa da dariyah suka cigaba a wajen bawa dawakan abinci,deeejah ta ƙyar take kaiwa hannunta kusa da bakinsu,hakan ma sai anyi da gaske. Wani dogarine yazo inda suke tareda cewa "Ke deejah saƙo daga yariman masarauta wato mai girma jalal,yan ƙiranki zuwa sashensa akwai abinda zaku tattauna" Kallon eemran take wanda shima dogarin yake kallon,hannunsa kuma a dunƙule da alama ransa ya baci da wannan maganar. Har ya buɗe baki zayyi magana deejah ta rigashi tareda cewa. "Ina nan zuwa amsa ƙiransa yanxu nan" Bayan dogarin ya tafi ne ta juyar da kallonta wajen eemran ɗin,har sannan fuskarsa a haɗe,kaman bashine yake mata dariyah yanzu ba. "Karka emran babu abinda zai faru,zanje na dawo lafiya kaman yanda na tafi,yin maganar ka zai iya jawo maka matsala ko a koreka" Tafiyah tafarayi a hanyar dazata kaita sashen yarima jalal ɗin. Batayi tsammanin zayyi magana ba sai taji yace. "Idan kika wuce minti talatin baki dawo ba zaki ganni nazo ɗaukarki,ki kula dakanki,shine kaɗai zai kwantarmin da hankali" Ɗaga kai tayi alamar taji kafin tabar wajen. "Duk da cewa ina fargabar zuwanki wajen,amman na tabbatar daga yanayinki kin fi ƙarfin matan da yarima jalal zai iya juyawa,tundaga kallon mai hankali zai ga ƙarfin kwarjininki (aura),wanda zai tabbatar masa da cewa ke ɗin ba irin sauran mata bace. Bakida jinin mulki a jikinki na ji hakan,amma kuma akwai halayyar tafiyar da mulki a tattareda ke,ko ban gani ba dole kin taba zuba mulki da jagoranci koda a kuwa a tsakanin iya mutum biyune. Daga ni har ke dukkanmu munsan akwai dalilin dayasa kowa yake aikin dayake,saboda kowa a cikinmu yasan ɗan uwansa ya wuce matsayin aikin dayake. Kowa a cikinmu yanada boyayyen kuɗuri a ransa,kaman yanda nasan kin ganni da daddare ina duba sashen hajiya fulani,nima na ganki lokacin da kike magana ke kaɗai ba kowa a gefenki cikin dare,sannan naji tatttaunawar maganin da kukayi,duk da dama nasan abinda yake damun yarima mubarak tun shekara goma sha huɗu baya" .......toh fah..........waye eemran? Zasu shirya da mabaraciyah kuwa idan ta gano. Taku _sadi-sakhna_ Ƴar mutan jama'are. *MABARACIYAH* _haƙƙin mallaka_ _*sadi-sakhna*_ (Yar mutan Jama'are) 37••38 Tundaga bakin sashennasa take juyo hayaniyarsa shida muryoyin mata guda biyu.. Batayi kasa a gwiwa ba ta ƙarisa cikin falon. Komai na wajen ja ne,kama daga kujerun table harda labulaye da kuma carpet. Wata ƴar yarinya ce bazata wuce shekara sha takwas ba akan cinyarsa,ɗayar kuma tana gefensa yasaka hannunsa a cikin rigarta. Dukkansu magana suke cikin maye,amma kuma bai kai ya gusar musu da hankali ba. Kallon su deejah take idonta a tsaye,ɗaya bayan ɗaya kafin ta samu waje ta zauna a kujerar datake facing ɗinsu. "Keee dana aika a ƙiraki sai yanzu kika ga damar zuwa koh?,wato rowar daɗinki kikemin dan kinga ina kwaɗayinsa koh,to barikiji na faɗamiki,duk wayonki saina moreki na kwashi romo,jiyama kwana nayi ina begenki" Ɗayar ce da take kan cinyarsa ta bata fuska tareda hararar deejah,wacce tun ɗazu kallonsu take batace komai ba. "Wannan kucakar ce dama kayi ta mana kukanta da daddare?,amma lallai ka bada mu,ni nayi zaton zanga wata ceelah,ashe wannan ce?" "Ke diamond,ki kiyayayi zaginta fahhh,karki rainani dan kinga tauraruwarki ce take haskawa" Har deejah tayi niyyar tashi ta tafi saikuma tayi wani murmushi tareda dawowa. Idonta ta ƙanƙance tana kallon nasa tareda cije fatar bakinta ta kasa. Cikin kasalalliyar muryah tafara magana,wanda ko su daƙyar su iya wannan shu'umancin. "Mai girma yareema,bansan mai yasa ka ƙirani ba,amma koma menene kamata yayi mushiga daga ɗaki tukunna,ko anan kakeson ganinnawa?" "Ahah muje ciki na faɗamiki,dama nasan dan gaban wannan ƙazamin ne shiyasa kika ƙi nunamin nufinki a gameda tayina" Ture wacce take kan cinyarsa yayi gefe tareda miƙawa deejah hannunsa. Kawar da kanta tayi kaman bata ganshi ba,wanda hakan yasa dole ya miƙe da kansa. Tafiyah yake yana layi har yashiga ɗakinnasa,ita binsa tayi tareda juyowa ta kashewa matan da suke zaune ido. Zama yayi a bakin gado yana ƙaremata kallo,ita kuma ta riƙe bakin ƙofah tana kallonsa. "Mai kike jira a tsaye,zo nan nabaki labari mai daɗiiiii" "Zanyi farincikin zama a kusada kai na saurari labarinka,amma kafin sannan kaima saikayimin abinda nakeso,idan bakamin ba kaida........." Ta kalli jikinta daga sama har ƙasa. "Haramiyarka,dan haka yakace toh" Kana ganinsa kasan ya kwaɗaitun da jikinnata,musamman yanda take jijjiga da gangan a gabansa. "Adadin wane kuɗi kike buƙata a wajena" "Hhhhhhhh kuɗiiiii,nafi ƙarfin kuɗi jalal,bazaka iya sayen abinda kake so a wajena da kuɗi ba. Saidai amma abinda nakeso inka yi yanda nace bai kai kuɗin ba ma. "Ina buƙatar bayanai akan mahaifiyarka,kama daga na kuɗi da duk wani abinda kasani gameda ita. Ba wanann ne babban ba,inaso ka ɗaukomin wani jan akwati a ƙarƙashin gadonta,idan kayi nasarar ɗaukomin akwatinnan toh ka faɗamin duk abinda kakeso" Kallonta yake da mamaki kafin yace. "Babu wani abu a wajen mahaifiyata sai kuɗi,idan kina so zan baki,mai zakiyi da wani akwati kuma?. Akwaitinnan tamkar rayuwarta haka yake,kullum saita dubashi kafin ta kwanta,sannan idan har bata gidan toh shima baya nan,inaga dashi take tafiya ko ina" "Eh dama idan ka ɗaukoshi zan baka wani kasaka a wajen,wanda zatayi ta ganin wancan ɗin a matsayin shine. Karka min musun cewa bazakayi ba,dolene sai kayi jalal,saboda babu mai min idan bakai ba,idan kuma bazakayi ba toh,............saika zaba ko damar mulkinka a garinnan ko kuma ɗaukomin akwatinnan" "Me kike nufi da hakan? Ke har kin isa ki tsoratar dani" "Hahahahah namafi haka jalal,kasan wani abu.....duk matan daka kwanta dasu a satinnan na zuwana gidannan inada vedionku dasu,sannan nice mai kulada rashin lafiyar mubarak a yanzu,kuma kasan me? Nagano wace irin rashin lafiya yake ɗauke da itah,sannan zan iya nema masa magani da izinin Allah. Idan har ya warke wa kake tunanin zai riƙe mulkin garinnan tsakanin kai dashi.?" Zaro ido yayi tareda ɗauke ƙafafunsa ya maisu kan gadon. "Idan fahimceki kinaso kicemin idan nayi miki wannan abin bazaki yimasa magani ya tashi ba harsai na karbi mulkin garinnan?" "Kacanki amsar daidai abokina,idan kuma baka samomin ba,zan saki vedionka kuma bazaka moreni ba yanda kakeso . Faɗawa wani kuma wannan maganar,..hmmmm...... Kayi hasashen cewa kaima ga naka gadon a gefensa kana baccin rashin jiran tsammani. Dan kaima kwantar dakai zanyi kaman yanda yake kwance" Jikin yarima jalal ne yafara rawa jin kashedin datayi masa,kuma idonta kawai ya kalla yasan zata iya,shi yanzu bai yadda cewar ita mutum ce bama. "Yawwa yaron kirki,ka manta da mun haɗu anan wajen har sai ka kawomin abinda nakeda buƙata,gobe hajiya fulani zata dawo,dan haka gobe zaka ga akwaitin dazaka saka mata a ɗakinka da safe. Aikinka sannan zai fara,saika shiryah" Murmushin mugunta tayimasa bayan tagama faɗan hakan kafin tabar ɗakinnasa. Har deejah tafita daga ɗakin bai saki ransa ba,gumi ya rufeshi shirkiff,shikansa yasan ya jawowa kansa tsiyah yana zaman zamansa,sunan wani littafi na yaƙi waishi GABA TSINI BAYA TSIYAKI. ___________________ A bangaren su dec. Sadeeq kuwa,ko yaushe yana hanyar gidan su sabriyyah,wani lokacin ma anan yake cin abincin dare. Zuwa yanzu sun saba dasu kahriyyah sosai,musamman ma faɗansu da sabriyyah,gashi ɗakinsu ɗayah. Yauma khariyyah ce da fareeda a kitchen suna abinci,sai sauri suke karsuyi dare,dan sun san uncle Sadeeq yana hanyar zuwa daga anyi magriba. Dadduma aka shimfiɗa a tsakar madaidaicin falon,tareda jera abincin daren. Duk wanda yagani sai abin yabashi sha'awa. Bayan sunyi salla zama sukayi suna jiran zuwan Sadeeq ɗin. Khairiyyahce ta kalli sabrah wacce waya take hannunta,da alama basu daɗe dayin waya da shiba. "Ke dallah ki faɗawa wancan mijinnaki yayi yazo muna jiransa,duk ni ta wajensa ce amma yaufah babu sauki,dan yunwa nakeji sosai ,tunda na dawo daga wajen aiki banci komai ba(aiki take a wata center ta conputer,Dec. Sadeeq ne ya sama mata,satinta guda kenan da farawa,ita kuma sabrah so take ta cigaba da karatu idan komai ya lafa na aika aikar da sukayi. Fareeda kuma tunda mutane basu san da itah ba ta koma aikinta na bincike). "Kuttt ke khairi mijinnawa ne kike wannan maganar,bari yazo na fadamsa,daga yanzu ya daina kulaki,iya fadeelah zai dunga kulawa,koh fadunah?" Tsalle fadeelah tayi jin an ce itah,gwaliyo tayiwa khariyyah wanda hakan ya ƙara ƙularta. Dama ita ga shiriri ta,sai ta dunga abu kaman ƙaramar yarinya. Tashi tayi zata duka fedeelan datake yimata dariyah,inno tana uhm uhm amma sunayi. Dariyah sabrah takeci harda rike ciki,ƴar kara tayi daidai shigowar Dec. Sadeeq. Da sauri ya isa wajenta akan kujera yana tambayar mai ya faru.. Ɗan zame jikinta tayi tana kallon su inno,wanda suma suka kawar da idonsu,da alama kunya taji. "Babu komai hayatee,kawai dariya nakewa su fadeelah,sainaa ji cikina yaɗan kama." "Ayyah amma ki dungayi a hankali,kinsan yanzu kin fara nauyi,gobema inshaallah zamu tafi gida,na faɗawa ummah halin da ake ciki" Zaro ido sabrah tayi,tun kafin tayi magana umman su sadeeq ɗin tashigo falon da sallama,da alama kaman waya tatsaya yi. "Salamu alaikum" "Wa'alaikissalam" Suka amsa mata,inno ta tashi tareda nuna mata kujera. Kalon sadeeq tayi wanda yake manne ta sabrah,itakam kanta a ƙasa ta gaisheda umman,kunya duk ta isheta ta sadeeq ɗin,sai tureshi take amma ko a jikinsa. "Inno nikam sai yau yake faɗamin abinda ya faru,kullum baya dawowa gida sai bayan isha,idan ya koma yace ya ƙoshi da abinci,sai nake tambayarsa ina yake cin abinci. Ganin raina zai baci shine fah yake fadamin cewar,ashe nan yake zuwa kuke cin abincinku sai ya koma. Kuma dayake yaga dama shine yake fadamin abinda yasa ta dawo gida,da nayi zaton faɗa sukayi,ashe abin gagarumine,banda sha'anin yaro ai sai ya faɗa tunda farko. "Hakane kam hajiya abune gagarumi,ni kaina dakika ganni bansan da labarin ɗaukar wanann fansa tasu ba sai daga baya,su ganin wai shari'ah taƙi yimusu adalcine. Amma komai yafi ƙarfinka ai saika barwa allah" "Toh yanxu dai zanyiwa mahaifinsa magana akan lamarin,komai muka yanke zakuji daga garemu,amma uhmm abin akwai dubawa,tashi mutafi Abbakar zan je gidanmu zanyiwa hajiya saratu gaisuwa tunda ta dawo" Tashi sadeeq yayi tareda yiwa su inno sallama,dukkansu kowa yayi jugum,dan kowa ya kalli fuskar umman yasan da wata a ƙasa,bazuwa tayi sasanto ba,tazone domin tabbatar da rashin amincewarta akan Abinda su khariyyah sukayi. Shiga mota tayi ta hakimce tana jiran shigowar sadeeq,wanda kana ganinsa kasan baiji daɗin abinda tayiba. "Wai zaka shigo motar kaja mujene ko kuwa sai dare yayi mana kai. Banda sakarcinka duk da abinda sukayimaka harka samu damar zuwa wani gun ɗiyarsu,wacce tun farko danta cutar dakai ta aureka?. Hannunka mai sanda nayi musu ai idan sunada hankali,kuma aurene dole sai an tsinkeshi,babu yadda banyi dakai ba ka auri yar yayana mai martaba wato Madeena,ta gaji sarauta gaba da baya,ga gidan mutunci amma kayimin biris da zancen. Kaje ka auro wacce ko asalinta bata ma saniba bareta bawa naka ƴaƴan,ga abin karin ma sheɗaniya makashiya masu kashe manyan gari. Dan haka bakai babu ita daga yau,batun saki bazance saika saketa ba,idan ɗana yakama su ma aka zo zartar musu hukinci ai dole ka saketa idan kaga zata ƙare a gidan yari. Hmmm ɗan cikinnata ma daya zama jininmu takaicinsa nakeji,ai wani abin ma sai babanka yaji labarin,ba ita ba har kai saika fuskanci fushinsa. Kuma aure babu fashi yanzu,madeena tana gama karatunta a BUK za'a tsaida ranar aure,banason sakejin labarin wannan yarinyar a bakinka." Masifah ummannasa ya dungayi har suka shiga cikin gidan masarautar katsinan bata daina,ta inda take shiga ba tanan take fitaba,shikansa yasan yau babu mai kwatarsa a wajenta. Ta barshi yaji da abinda tayiwa dangin masoyiyar tasa mana,hmm dan basu san yanda yakeji akan sabrah bane shiyasa duke faɗan hakan. Kuma yanda suka ɗauki su khairiyyah shiba haka yagansu ba,mutanennan cutar dasu akayi,amma kowa yimusu kallo yake kaman sune suka fara zaluncin,bayan kowa idan shine ba daɗi zaijiba.. Shikuma dec. Khaleel yace masa ya tafi daurah fara bincike daga farko akan labarin su sabrah,da kuma ya akayi suka haɗu da khamriyyah. Shikamsa har yanxu bai gama yarda da itah ba,dan komai akayi itace ta shiryah,su aiwatarwa kawai sukayi,in hukunci ne ma ai ita yakamata a yiwa basu ba. (Toh kaima ashe ka iya son kai ɗin. Har ummah ya yi hanyar shiga sashen hakiya fulani sadeeq bayyi niyyar binta ba,yana jingine a jikin motarsa ya faɗa kogin tunani. Kallonsa take cikeda takaici,don tasan zancen gizo baya wuce na ƙoƙi. "Ni kaɗai zan shiga kai bazaka shigaba,kodan nayi maka faɗane matar yayannawa ma bazaka yimata gaisuwa ba" "Kai ummah ni ban faɗaba,dama da kunzo keda meena ita so take ki barta tazo tayi hutu ma anan" "Banga damar zuwa ta itaba dakai naga damar zuwa,a haka zata ganka a matsayin surukin da take tunani" Bin bayanta yayi suka shiga sashen hajiya saratun. A falo na biyu lami tayi musu iso suka shiga,dayake kowa yasan Hajiya Khadeejah,wacce ƴar hajiya fulani ta Nana khadija. Ita ɗayace ƙanwar Mai martaba,wanda suke uwa ɗaya uba ɗaya,. Sauran mata guda biyu dukkansu ba a garin suke aure ba,kuma su mahaifiyarsu daban,daboda halin hajiya fulani dakuma irin zaman da'akayi yasa basa zuwa garinma sosai. Kasancewar salaha batada lafiyah tana ciwon mara na baƙon wata,yasa deejah zuwa a madadinta domin kawomusu ruwan sha. Tsugunnawa tayi ta gaisheda Hajiya deejah wacce take mai sunanta,harma da saurayin data gani a gefenta,wanda ko kallonta bayyi ba hankalinsa yana kan waya. Bayan hajiya saratu tazone suka fara gaisawa,cikin raha da sanin juna. "Uhm ina kuwa Fulani ko yanzu ma bata nan kaman kullum" "Hmmm Addah bata nan,tayi tafiya wai Singapore,amma gobe zata dawo inaga,haka naji a wajen hamman naki" "Hmmm sai kuyita haƙuri,ya hakuri na rashin waziri da akayi kuma" "Alhamdulillah Hajiyan yara,yazama dole hakuri kam ai,Babana kuma yanaga yana haɗe rai kaman ya haɗiyi kunama,daga gaisawa yayi shuru,ni rabona dashi ma na manta,inaga kuma babangida,wanda shi tun yana yaro rabona dashi,bakwason zumunci sosai" "Hmm kema kya faɗa,dani yake wai na masa faɗa,mata yaje ya ɗakkota babu asali ba komai,sai jawo fitina a gari. Bazan iya da rike matar nan tasa a matsayin suruka ta ba,duk waccar ja'irar kamriyyahrce ummul aba'isin. Kizama cikin shiri hajiya saratu,domin madeena tana dawowa za'a saka ranar bikinsu,waccar matar kuwa ko yana yaso ko bayaso idan ya daina ganinta dole zai haƙura" Ita dai hajiya saratu shuru tayi tana sauraran hajiya deejah,gabaɗaya bata fahimci komai ba na maganar,dayake babu ruwanta sai kawai ta zuba musu ido,har zuwa lokacim da jakadiya tasanar mata cewar mai martaba yana jiranta a falonsa idan ta gama. Sallama tayiwa hajiya saratu kafin suka fice itada sadeeq. Duk abinda suke deejah da take rakabe a bakin ƙofah tana jinsu har suka gama. Lokacin da suka zo fitane ta koma can nesa kaman mai jiran wani. Bayan fitarsu da minti biyar itama lami ta fito,dan dama ita take jira Tafiya suke shuru babu mai cewa komai,sai deejah ce ta katse shurun ta hanyar cewa. "Ni yadiko lami waɗannan ɗin suwaye suka zo?" "Ohh ashe kefah baki dade anan ba,hajiya deejah sunanku ɗaya,ƙanwar mai martaba ce wacce take auren General muhammad Kareem. Shugaban masu harkar tsaro na garinnan. Wannan dakike gani kuma Abbakar Sadeeq babban danta ne,yanada ƙanwa ɗaya mace Ameena,ana ƙiranta da meena. Saikuma ɗan yayarta data mutu da take riƙo wato Ibrahim khaleel" "Uhm allah ya jikanta,barina je na kwanta" Daga haka deejah ta wuce sashensu tana jinina abin a ranta,dama dec. Sadeeq yanada alaƙa da gidannan,dolene ta zama cikin shiri kenan. _______________ Sai wajen yamma kafin hajiya fulani ta dawo daga ƙasar data tafi. Mutane sai shiga ake da fita kaman itace mai sarautar garin,dama ance yanzu kuɗine yake mulki bawai martaba ba. Saida magriba tayi kafin mutane suka dauke ƙafa daga gidan. Bayan deejah ta idar da sallah ne taji muryar zainabu a bakin sashennasu,shigowa tayi tareda zama a kasan ɗakin. "Deejah idan kin gama hajiya fulani tana nemanki akan maganarku,kiyi gaggawar zuwa yanzu nnan" Tana gama fadan hakan batace komai ba ta tashi tabar ɗakin Kallon alamar tambaya salaha tayiwa deejah,saidai kuma ganin babu razana a fuskarta yasa ta bar zancen. "Kinsamu aiki a sashennata ne,nayi mamaki sosai,dama tana ɗaukar hausawa ne a sashenta?" "Ahah ba aikin abinci bane,wani aikine da ban,bari naje ina dawowa" Daga haka ta fice ta nufi sashen hajiya fulanin. A hakimce ta ganta a falonnata tasha wasu kaya baƙaƙe sai walwali suke da stone,ga kamshi yana tashi,da alama turakar mai martaba zataje. "Uhm ina jiran amsarki,ance kinzo kin dubashi jiyah,mai kika fahimta gameda ciwonsa,idan kuma baki saniba ko kuma kika faɗamin abinda ba hakaba,keda sake ganin hasken rana sai a lahira idan ta fito" "Ɗanki yareema mubarak babu wani ciwo a jikinsa. Bashida kuruwa a jikinsa wato rauhunsa bayanan an kamashi a wani wajen,shiyasa yake kwance kaman mai bacci,tsawon wannan lokacin" Ɗan murmushi hajiya fulani tayi tareda rausayar dakai,da alama dama tasan mai yake damunsa tun da. "Kin samo amsar daidai,babu abinda yake damunsa face raahin kuruwa a jikinsa,nasan da hakan ,ina jiran mai maganin dayasan hakan,shiyasa na ajiyeshi domin ƙwato kuruwarsa. Zan nemeki gobe yanzu akwai abinda nake son yi. Na ɗaukeki a matsayin mai kuladashi,daga yanxu zaki iya shigowa ki fita lokacin da kike so" Gefenta deejah ta waiwaya bayan hajiya fulani tabar wajen suka haɗa ido da yareema jalal wanda yake zaune. Ƙifta masa ido tayi tareda barin falon tana murmushin samun nasara. Toh fah ku taho dai,deejah tayi nasarar shiga inuwar hajiya fulani..........saura kuma me?..... Taku _sadi-sakhna_ Ƴar mutan jama'are. *MABARACIYAH* _haƙƙin mallaka_ _*sadi-sakhna*_ (Yar mutan Jama'are) 39••40 Hankali kwance kaman tsumma a randa haka deejah tayi kwanciyarta,ko tunanin mai gobe zatazo da ita bata kawowa a ranta. Ɗakin amal da buɗe tana kwance akan gadon kaman kullum,damma yau ba makaranta weekend ne. Bata yaye labulen ɗakin ba saita fara ta gyara kayan data zubar a tsakar ɗakin jiya da daddare. Tattarasu tayi ta kaisu cikin kwandon wanki,sauran kuma wanda taga sunada wanki tafara nade mata.. Kwata kwata hankalinta baya kan abinda take,sai jin ruwa tayi a bayan mai sanyi . Ajiyar zuciya tasaka tareda zuyowa tana kallon amal wacce take riƙe da kofi a hannunta,yaushema ta ɗebo ruwan deejah bata sani ba. "Ko zaki ramane,tun ɗazu ina miki magana kinyimin banza kaman bakya jina,ki wanke min wannan kayan dakika kai wajen wanki,in kuma kin fi karfi ki sanar dani" Baki deejah tasake,takula rainin hankalin yarinyar karuwa yake,dolene ta koya mata hankali. Fita tayi tana ƙiran mommy tun daga ɗakinnata,ta kula halinta ne hakan kullum da safe. "Mommmy dagaskene abinda Anty mubeena ta faɗamin wai,tana zuwa gobe?" "To kuma tafada miki karin bayani kike nema" "Ahah,yanzu dai yunwa nakeji,oh..... Naji wai yah sadeeq yazo shida umma,hadda meena suka zo?" "Ahah su kaɗaine,meena tana gida" Har wajen ƙarfe takwasa kafin deejah tagama wanke kayan amal ta shanya,wannan bacin injin wankin ai su akayiwa masu aiki. Daga wajen inda take shanyar tana kallon eemran yana haɗa dusa a cikin darom kwanuka. Yazage sai aiki yake kaman dama haka yatashi yana yi. Dariya yabata wanda hakan yasata tuntsurewa da dariyah. Takawa take a hankali har ta isa wajensa ta tsugunna. Dagowa idonsa yayi yana kallonta tanayi masa dariya. "Menene kike min dariyah da safennan,mafarkina kikayi ina wasan musha dariyah?" "Ko ɗayah,kawai yanda kake aikinne ka dage yabani dariyah,gaskiya daga gani za'ayi jarumin namiji mai neman nakansa. Jiya da daddare dazan wuce naga kanata turanci kaman ba kaiba,dama ka iya turanci haka?" "Uhm nayi karatu,kaman kema na ganki kina magana ke kaɗai rannan,shin kina magana da aljanune?" "Yaushe ka ganni?" "Ranar da kika cemin kin gano rashin lafiyar yarima mubarak," Shuru deejah tayi da zancen tareda ƙoƙarin sanja akalar maganar. "Shin kanason shiga sashen hajiya fulani?" "Meyasa kika tambayeni?" "Kawai naga kanason shigane,saboda wani lokacin inaganin yanda kake kallon wajen shigar" "Eh inason shiga sosai,saboda akwai wani abu danake son ganowa,wanda ya shigemin duhu" "Zan taimaka maka ka gano koma menene ya shige maka duhun,nasan wani abu gameda kai kana boyewa ne,yayinda nima nasan ka fahimci akwai abinda ban fito na bayyana ba. Alaƙarmu tana birgeni yanda kowa ke mutunta sirrin kowa,duk da haka inaso kasani har cikin raina. Na yarda dakai emran,kuma a shirye nake na taimaka maka idan bukatar hakan tazo,kaman yanda kake ƙokarin kuladani nima" Dan lumshe idonsa yayi tareda ɗaga mata kai alamar yaji. "Uhm kasaitarce ta motsa kaƙi yimin magana,anya kuwa kai ba jinin sarauta bane?" "Ke ma wani lokacin idan ina kallonki a cikin gidannan,saina dunga kallonki kaman jinin shugabanci,kinada kwarjini da kuma cika a tattare dake,naga yanzu yarima jalal ma shakkar ku hada hanya yake,jiya ina kallonsa ya canja hanya yafi uku idan ya tunkareki" "Hhhhh yaushe hakan ta faru,ashe dama kana kallon duk abinda nake,da wanine yayimin haka saina ji tsoron kar ayimin wani abu,amma yanzu hankalina kwance tunda kaine kake kallona ba wani daban ba" "Hakane ki kwantar da hankalinki,fatana karkiyi abinda zai cutar dake ko kuma wani daban,ta hakanne idan kinyi zanyi koƙarin taka miki burki,amma bayan wannan idan wanine yake ƙokarin yimiki wani abun zan tsaidashi tun kafin ki sani" "Uhm yanzu ka dawo normal kana surutu,duk da nasan iyani akewa wannan dogon maganar,barina shiga sashen hajiya fulani,zan duba jikin yarima,idan kanada buƙatar bina saimu tsara yanda za'ayi," "Ba damuwa zakijini idan inada buƙatar hakan" Tashi tayi tabar wajen tana waiwayensa har tashige. Jijjiga kai yayi bayan ta ƙule tareda cewa. "Yah Allah ga bawanka,nasan kaine ka jarrabeni da wannan soyayyar mai matuƙar zurfi da kuma makanta,ALLAH kayimin mai kyau" Kai tsaye ɗakin yarima mubarak deejah ta wuce,bata nemi ganin hajiya fulani ba,dan tasan bazata iya ganinta a lokacin ba. Tsayawa tayi a gabansa tana kallon idanuwansa dasuka tsaya cakk a waje guda. "Inshaallah zanyi iya ƙoƙarina wajen ganin na taimakeka,ta kwantar da ɗaya,ta kashe ɗaya,ta lalata ɗaya,ta rabu da ɗaya. Wannan wace irin uwace haka,wanda zuwanta cikin al'aumma bai haifar komai ba illah masifah. Inta kama in nata kuruwar zan bayar subada naka zan bayar,kayi sa'a naji tausayinka a cikin raina,ganin yanda ka zauna a wajennan ba iya na kwana ɗaya,biyu,sati,shekara daya ba,har shekara goma sha huɗu. Hmmm hajiya fulani kin shiga uku da a zaluncinki kika tabi wacce bata yafiyah,yanda kikamin aradu kema sainamiki,sa'arki ɗaya inda mutunci,da saina wulaƙanta rayuwar ƴaƴanki,dan an ce laifin uwa baya shafar ɗan ta ne da sai na rabaki da kowa tukunna kafin na hukuntaki" Duk wannan maganar cikin ranta takeyinta tana kallon fuskar mubarak ɗin.. Duddubashi tayi tareda jaraba yan wasu magunguna wanda tasan bayi zasuyiba,kawai danta shigo wajenne ta taho dasu. ______________________________ Sabrah ce a zaune idonta yayi luhu kaman an zuba mata garin barkono,khairiyyah tayi aikin rarrashin harta gaji tayi shuru,. "Yanzu sabrah bazakiyi shuru ba,dan bai zoba amma ai ya ƙiraki ya faɗamiki halin da 'ake ciki,kenan haka zakiyi idan an miki kishiyar ma kisata a gaba kiyi ta kuka.. Ina kissarki da iyah kalallame miji suka tafi?" "Hmmm khairi kennan,wane kalallama yanzu zanyi,bayan aurennawa ma shirin gundulewa yake,nasan badam abinda ya faru ummah taƙiniba,sabida ni ba ƴar kowa bace,banida asali,ni shegiyace marar asali, banda uban dazan bugi ƙirji na nuna,kuma sannan ɗanta yana sona fiyeda ƴar yayanta. Shiyasa ta tsaneni,inba haka ita macece mai maraba da kowa,nikaɗai nake ganin wannan bangare na jikinta. Shima wani lokacin batayimin sai abin ya taso tukunna. Khairi ina zan saka kaina,yarinyar fah wai ƴar sarkice,taya kike tunanin zan haɗa kaina da ita a fannin komai?. Kodayake meyasa ma nake damun kai na,nida zanje kurku bayan ɗaurin auren,nasan ko mijina bai kamani ya kaini ba khaleel ɗan uwansa idan ya kamo khamriyyah da mabaraciyah muma zai kamamu,sai muyi zaman mu a can,bangani ba bare na damu,ko ƴar uwa?" Kallonta khairiyya take kaman wanda ta tabu haka take zubo magana,juyawa tayi zata ƙira inno,saikuma sukayi kibis da ita,ashe tana tsaye a wajen tun ɗazu. Hawayen fuskarta ta share tareda isa inda sabrah take zaune akan gadon. "Karkice haka kinji ƴata,kinada kowa kinada wanda baya bacci wato ALLAH,ga kuma ni da ƴan uwanki,iya wuyah bazamu barki ba muna tare. Ki fawwalawa Allah lamuranki kinji?,karki saka damuwa a ranki har yakaiki ga cutar da lafiyarki,mijinkine yana sonki,babu wanda ya isa ya canja hakan idan ba Allah ba" Rarrashinta inno ta cigaba dayi,tareda kwantar mata da hankalinta,tana ajiyar zuciya har bacci ya ɗauketa. Fitowa sukayi daga ɗakin bayan sun tabbatar ta samu bacci. "Khairi babu matsala da bakije aiki ba,kinga baki daɗe ta fara aikinba kar oganku ya miki magana" "Inno babu matsala,ko akwai ma bazan iya tafiyah na barta a wannna halin ba,abin yana damuna sosai,musamman daba ita kaɗai bace,sai tana tunamin da anty juwairah,shiyasa banasonta ganin halin karayar zuciya,kaman yanda nayi ta kallon anty a ciki harta koma ga mahaliccinta. Barina je ɗauko su fadeelah a makaranta,deen baya nan ya tafi neman aiki an ƙirasu" "To shikenan,ni ya zancen uban yarannan ne,yana rayene har yanzu" "Eh yana raye,kwanaki ma nagani a labarai wai an kaishi ƙasar india za'ayi masa aiki,iyayen dayayi biris dasu yanxu sune suke ta fama dashi,tunda kuɗinsa kam babu. Aikin yayi kyau aka ce ta tashi,amma shida haihuwa kam saidai yagani a wajen wasu" "Hmmm Allah ya kyauta,shima kam baiyi daidai ba abinda ya aikata mana" "Shiyasa shima aka nuna masa rashin daidai ɗin ai,saboda ya ɗanɗana yaji" Daga haka khairiyya tafita a gidan zuwa makarantar su fadeelan. _______________________ Wata matashiyar budurwace a gaban aji tana danna iphone12 ɗin da take hannunta. "Am madeena wai dagaske kike yau zaki shige gida,ko hutawa bazakiyi ba gobe ki wuce,sai kace ana korarki" "Hmmm kina ce ƙarya nake Summy,yau zan tafi akwai wata maganar ma da ummah takeson muyi,bansan na menene ba amma kuma naji tana ambatar yah Sadeeq" Zaro ido wacce aka kirada summy tayi kafin tace. "Awwn Yah sadeeq naki dai koh,uhmm allah yasa bikin za'ayi mufara shirye shiryen zuwa katsina" "Saiku shirya kam,abinda aka daɗe ana jira yazo inshaallah" "Amma kuma naji ance yanada mata,da kishiya zaki zauna kenan?" "Hmmm mai ruwana da itah,naji ance ummansa bata sonta ko kaɗan,kinga nikuma wannan ce damata,yanda ummah deejah take sona komai zata iyah don na samu soyayyar yah sadeeq" Wayarta ce tayi ringing,tana dubawa taga number drivern da aka turo mata ne. Da sauri sukayi sallama itada summy ta nufi inda yayi mata kwatancen yana can.. Dayake hutun sati biyune bata ɗauki komai nataba banda jakarta. A bakin motar ta ganshi ya riƙe mata murfin ƙofar,ita kuwa kai ya ƙara fasuwa,duk da batakai amal taƙama ba. Tana shiga motar yamaida murfin tareda shiga wajen driver "Ran gimbiyar katsina ya daɗe,shin zamu iya kama hanya?" "Eh mutafi,kaine saleem ko?" "Kwarai kuwa nine da wannan suna" "Amal tayimin zancenka ai,tace kanada kirki,Allah yasa naga hakan nima" "Inshaallah gimbiyah" Daga haka suka cigaba da tafiya babu wanda yasake cewa komai har suka shiga garin katsina. Tarya ta musamman akayi mata,dan hajiya saratu tana ji da ita ba kaɗan ba. Deejah ce itada salaha suka shigo sashen domin yiwa madeena barka da dawowa. Itada amal ne a ɗakinnata suna ta zancen makaranta. "Wlh anty madeena bakiji yanda nakeji ba da wannan shegiyar secondryn ,ALLAH ALLAH nake na gama nima na zo jami'a,haba asha chilling" "Oh chilling ma zakiyi kenan,barina faɗawa baba toh. Ke ya jikin yah mubarak kuwa,yah jalal na ganshi da muka shigo zai fita a mota,ko kalloba bayyi ba bare ya tsaya mu gaisa,narada yaushe zai daina wannan girman kan" "Hmmm ni dama ina ruwana dashi,girman kansa yayi yawa,shiga kyakykyawa,sai kace wani mummuna ne. Yah mubarak yana nan jiki irin na yanda kika sani,har yanzu babu wani canji,keee...... Nifah nafi zargar inaga da hannun Hajiya a rashin lafiyarsa,gashi taƙi yarda Baba ya fita dashi madeena" "Toh ina ruwanki,bazaki daina gulma ba koh amal" Shigowar su deejah ne ta katsemusu hirar,inda suka tsugunna a tsakar ɗakin suna mata sannu da dawowa. Amsawa tayi cikin sakin fuska,dan dama tafi amal daɗin sha'ani wani lokacin. Ɗago ido deejah tayi tana ƙaremata kallo,har saida amal ta kulada hakan,dama garinsu da tsakuwa ita da ita. "Ke miye kika wani zuba mata ido kaman zaki cinyeta,kuruwar ta kur haramiyarki,tasha li'ilafi da su falaƙi,saidai ki lashi kanki" Buge hannunta madeena tayi,yayinda deejah taja hannun salaha suka bar dakin. Suna fita salaha ta kalleta cikin tsoro tareda cewa "Deejah kinajin tana faɗa amma bazaki bata haƙuri ba" "Haƙuri akan me kenan,ba itace ma zata ban haƙurin ba,hmmm inaga yarinyar nan saina koya mata hankali tukunna,zata san matsayina" "Iyeeee deejah wane matsayi dake daya wuce nasu?" "Karkiso sanin matsayina,dan hakan bazai miki kyau ba,abar kaza da gashin ta kawai" Fizge hannunta deejah tayi tareda barin wajen,ta bar salaha a tsaye tana sakin baki,na mamakin deejan. Tana barin wajen data leƙa babu wanda yake kallonta ta ɗauko waya a kunkuminta. "Ke biggy kuna ina ne yanzu haka" "Eh ogah ni ina wajen abinci,iklima kuma ta tafi saro kayan gwanzonta" "Zeety fah tana ina?" "Eh ita .....uhm ta koma shaye shayenta fah" "Meee..........dagaske kike?" "Eh ogah ta gaske nake,amma fah tace dan allah karmu gaya miki" "Hmmm batta zamu jone,yanzudai wani aiki nakeson kuyimin,wata yarinya nakeso ku ɗauke a hanyar makaranta,zan turo muku hotonta,gobe zata tafi makaranta da safe,EMIRATE NUR.PRI.SEC.SCH.takeyi,itada ƙaninta suke zuwa,iya ita kaɗai zaku ɗauka. Bance ku daketa ba fah,kawai gidana zaku kaimin ita,zanzo da daddare gobe idan kun kaitan" Tana gama maganar ta kashe wayar tareda ɗaga gira tana murmushi. "Zakici butar ƙaniyarki gobe,na kula inba gyaraki nayi ba bazaki daina ƙonamin rai ba,marar kunya kawai" Tana kashe ƙirannsu ta ƙira yarima jalal. Da farko bai gane wayeba sai daga baya ya tashi ya zauna daga kan gadonnasa. "Hel.....hello kece?" "Nice mana da waye,ka dauko ko har yanzu baka ɗauko ba?" Zan ɗauko dai,ɗazu tashiga wanka nashiga ɗakin,tun kafin nayi wani motsi naji ta baci sunana daga banɗakin,inaga fah akwai wani waje da take ganin mai shiga ɗakin da akwatin yake. Saidai karki damu zan jaraba yau da daddare idan ta tafi meeting,amma fah ina tsoron ta ganeni,dan zata iya kasheni idan tasan na sauya akwatinnan da wani daban" "Mtswww to ina ruwana da abinda zatayi,ni kashekan zanyi idan baka kawomin ba,ina jiranka nan da dare,idan har baka kawomin ba gobe zan ɗau mataki akanka,nayi zaton zan daɗe a gidannan to abubuwa sun cakuɗe inason gamawa da sauri" "Aikin me kikeyi amma a gidannan,tunda ni zan zama sarki inada haƙƙin na sani" "Hhhhhhh karka min shashanci,in ba sokake nasaka aljanun dazasu dunga dubamin kai ba" Kashe wayarta tayi ƙitt,tana nazarin yanda abubuwanta zasu kasance. Ita kanta tasan ɗauko mata wannan akwati dole zai ɗau lokaci,barazan kawai take masa domin yayi akan lokaci. Har tazo shiga ɗakinsu saitaga wata paper a soke a jikin katangarsu,duba tayi babu kowa,bare taga wanda ya ajiye. Sunanta tagani a jikin takardar,wanda hakan yasa ta bude. _aminci ya tabbata a gareki Khadeejah,kinyi kyau a cikin jan kayan da kika saka yau. Kwanannan naga hankalinki baya waje daya,da alama wani abun kike,kullum ina faɗamiki ki kulada kanki,karki saka kanki cikin wani abu mai haɗari. Bana ɗanjin daɗi yau,bazamu fita yawon ba kaman yanda nayi miki alƙawari,saidai ko wani lokacin. Eemran_ Ninke paper tayi kirjinta yana bugawa. Hannunta takai saitin zuciyarta ta dafe,yanzu kam ba itace tasaka tsoron a ranta ba,zuciyarta ce ta saka dan kanta,ambaton bashida lafiya dayayi duk sai taji babu daɗi. Maganar sumail ce ta faɗo mata a ranta,dayace kar a garin nuna masa kulawa bana gaskiya ba,domin neman wani abu ita kuma zuciyarta ta faɗa soyayyarsa a gaske,yazatayi kenan. "Hasbunallahu a wani'imal wakil,Allah gani gareka" Hanyar sashensu ta nufah da sauri domin ganin mai yake faruwa dashi. A bakin ɗakinnasu ta tsayah tana shakkar ƙwanƙwasawa. Haka kawai taji bai kamata tazo wajen ba bayan bata sanar masa,ko wani yakamata tasamu namiji ya rakota wanda zai faɗamasa tazo. Har ta juya zata tafi sai kuma tajiyo muryar emran yana faɗar wani abun. "Nima kaina saleem a dole nake zaune a gidannan,tsawon lokaci na gudu na buya a duniya tamkar wani matsoraci,ni kadaine naga abinda ta aikata shekara goma sha huɗu bayah. A gabana ta nuna mubarak da wani abu ya faɗi,ni kuma ina aman abinda naci a ɗakinta mai kaman minti,nayi zaton ta ajiyene domin ta bamu,bansan abin cutarwane dazata bawa wani ba. Saleem nakasa manta wanann ranar a cikin idona,nakasa yafewa kaina dana kasa ɗaukar mataki,nakasa fitowa duniya na faɗawa mutane abinda ta aikata saleem. Mahaifiyata matsafiyace,amma bazan iya faɗawa mutaneba,saboda babu wanda zai yarda dani,ta toshe duk wata ƙofah dazata nuna ita wacece,su kansu manyan garin da kuma mai martabar dukkansu a ƙarkashin ikonta suke. Khadeejah batada uwar dazata nuna in an tambayeta,mubarak raine dashi amma bashida ikon amfanar rayuwarsa,shikuma jalal ta maidashi tamkar ɗan awaki,ta sangartashi. Nikuma nakasa zaman gidan ubana,wanda bashida uba ma yafi ni,ina gidan ubana saleem amma banida ikon bayyana nine,domin yin hakan tamkar tasoda fitina ce. Ga cutar dana kamu da ita a ranar,duk lokacin daya tashi min jinake tamkar zan mutu,jinin jikina kaɗanne yake saura. Saboda tasan gubar dake jikin abin shiyasa ta bayyanwa duniya na mutu,dan tasan bazan iya rayuwa da ita ba. Bazan iya fadawa mutane ainihij sunana ba,na YAREEMA JUNAID,saboda mahaifiyata" Karaff ƙofar ta bada ƙara lokacin da deejah tajingina a jikinta,bata ma sani ba. Dukkansu ɗagowa sukayi su na kallonta,harda emran wanda ya riƙe kirjinsa,bakinsa duk aman jinin dayayi a lokacin...... Taku _sadi-sakhna_ Ƴar mutan jama'are. *MABARACIYAH* _haƙƙin mallaka_ _*sadi-sakhna*_ (Yar mutan Jama'are) 41••42 Sun kai kusan minti goma kowa kaman gawa yadaina motsi. Su suna kallonta da tsoron ko taji abinda suka faɗa,yayinda ita kuma take musu kallon abinda suka faɗa gaskiyane. Wani tarine ya kwacewa eemran wanda hakan yasa suka mayarda kallonsu gareshi. Gudan jinine yake fitowa daga bakinsa,yayinda yake mayar da numfashin wahala. Tsugunnawa deejah tayi a gabansa,dukkan ilahirin jikinta rawa yakeyi,saboda ganin yanayin data ga masoyinnata a ciki.. Saleem ne yayi saurin cewa. "Ka daure junaid,na ɗan lokaci kawai,barina je na karbo maganin,inshaallah yanzu zan dawo bazan jimaba" Cikin damuwa yake maganar da tunanin halin da abokinnasa yake ciki. Tsallakeshi yayi har ya fita ya dawo ya kalli deejah. "Ki kuladashi barina je na dawo yanzunnan,karki bar wajensa har sai na dawo" Ɗaga kanta tayi hawaye yana zuba a idonta,don baƙaramin tsorita tayi da yanayinnasa ba. "Eemraaan mai yake damunka ka boyemin ban saniba" "Bakiso sanin mai yake damuna ba deejah,alaƙar dake tsakaninmu naso tafi yanda take a yanzu,kowa a cikinmu yaboye sirrinsa ga ɗayan,ko kaɗan bayaso yasani,duk da mun san akwai sirrin. Shiya......sa nasan bazaki so sanin mai yake damunabaaaa,mai yasa zan nemeki na faɗamiki wanene ni,bayan bansan ke wacece ba" "Dan allah karka ce haka,indai abin yakai haka,nayi alƙwarin faɗamaka abinda yake faruwa harma da wacece ni,karka sake boyemin irin wannan jinyar,zanzo nasani emrann" Kuka dake haƙƙun,yayinda shikuma yake riƙeda kirjinsa,zuwa yanzu saura kaɗam ya kwanta,hannunsa daya dafene suka yimasa katanga da ƙasan. "Shikennan,ki daina wannan kukan haka,inshaallah babu abinda zai faru,dama ba yau na fara ba, Nayi alƙawarin faɗamiki idan ina halin daya zai iya ɗaga miki hankali,ki share hawayen" Share hawayen tayi tareda matsowa domin taimaka masa ya zauna,gani yana buƙatar taimakon hakan. Saurin dagatar da ita yayi kafin hanunta ya taba jikinsa. "Ahah deejah karki kusanto gareni,keba muharrama ta bace,sannan bamu kasance jinsi ɗaya nida keba,ki bari zan iyah jurewa ba komai." Basar da zancensa tayi tareda riƙo kafaɗunsa ta gyara fillon daya jingina dashi ɗazu. Ruwa ta gani da tsumma a gefenta,da alama saleem ne ya ajiye a wajen. Ɗauka tayi ta matse tareda goge masa kirjinsa inda duk jini ya bata,har da bakinsa inda shima jinin ya zuba. Kallonta yake amma ko haɗa ido dashi taƙiyi,sai aikin gabanta takeyi,duk da cikin ranta kasan abubuwa ne cunkushe a cikinsu. A haka ta gyara masa jikinsa tareda ɗauko rigarsa wacce ta gani a akan katifa. Ɗaukowa tayi tareda matsowa tasaka ta bayansa tana jira yasaka hannayensa,ganin bayyi bane yasata ɗan harareshi tareda cewa "Alaramma eemran,nima nayi karatu nasan hukuncin dayake tsakaninmu,amma kasan ko ma'aikaciyar jinya tana duba namiji a asibiti,badan komai ba saboda lalurin jinya ne da kuma babu mai taimaka masa sai ita a wajen. Hakan take tsakanin mu dakai,kai marar lafiyane ni mai taimaka maka,saboda wani baya wajen,dan haka kasaki wannan ran daka haɗe. Yana abu kamar mace,sa'a kaci ma dan kaine,da wanine ko kallonsa bazanyi ba,bare yayimin iyayi" Ta ƙarisa kalmar ƙarshen ciki ciki tana cuna baki. Kallonta yayi tareda cewa "Me kikace?" "Ni ba abinda nace,cewa nayi sannu kawai" "Hmmm zaki faɗi gaskiya koba yanzu ba" Ya faɗa yana saka hannunsa a cikin rigar,idonta ne yakai kan tsokar jikinsa yanda take juyawa duk sanda ya motsa jikinsa,haka kawai daji wani irin abu ya jira mata cikin zuciyarta Saurin kawar da kanta tayi tareda yin gyaran muryah. Zuba mata ido yayi da kuma jikinnasa wanda yanzu ya rufeshi da rigar. Ganin ya gama saka hannun ne yasa ta juyo tareda balle masa maɗalllin rigar. "Nakawo maka wani abune kaci kafin ya dawo,daga gani babu abinda kaci tun jiya?" "Bazan iya cin wani abuba inba maganin nasha ba,ki bari kawai nagode" "Sannu eemran,haƙiƙa nake ganin tawa rayuwar cikin chakwakiya,taka har tafi tawa ma" "Meyasa kika faɗi haka" "Duk naji abinda kuka faɗa kaida saleem,lokacin da maganar take dukan dodon kunnena,ji nake kamar a mafarki nake saurarensu,amma sainaga kaman ba kaiba yanzun,yanzu kafi kyau da fari akan yanda nake kallonka" "Hhhh har kin ban dariyah,kinada surutu deejah wasa wasa,inbanda abinki da haka nake fita ai da yanzu an ganeni koh,ko bakya ganin ina kama da su jalal da mubarak har ma mahaifiyata a haka?" "Eh nagani kam,dan inba a nan ɗakin naganka ba bazan ganeka ba nima sosai,amma fah ni zan ganeka" "Ke ta dabance deejah,inaji a jikina,kema kinfi kyau yanzu akan sanda nake ganinki" "Kai ka kalli hakan,amma ni babu abinda na shafa,kaine dai ka shafa" Suna cikin hirarne saleem ya shigo ɗauke da ƙullin magani dakuma gwamgwamin madara a hannunsa. Zubawa yayi a kofi tareda juye madarar a ciki itama. Wani ruwan rubutu na tawada ya juye a ciki wanda ya taho dashi. Miƙawa deejah kofin yayi dayake tafi kusada shi. Kaman bazai shaba saikuma ya miƙa bakinsa tasaka masa kofin yashanye dukka.. A jiye kofin tayi tana yimasa sannu. Rintse ido yake da alama ciwon bai gama sauƙa ba har yanzu,sai daga baya kuma gumi ya feso masa,baccin wahala ya ɗaukeshi. Matsawa tayi gefe saleem ya gyara masa kwanciyarsa. Share hawayen idonta tayi tareda cewa. "Amma wane irin ciwone haka daga shan minti" "Ba minti bane ai,wani abun tsafinne ta ajiye shikuma ya ɗauka yasha,koma menene da alama gubace" "Amma bata sakeshi ba har na tsawon lokacinnnan" "Yace mindai rabonda abin ya tashi masa tun shekara biyar shida baya,sai yanzu daya shigo gidannan tukunna,da alama abin yanada alaƙa da kusancinsa da nan wajen" "Hmmm amma yakamata ayi wani abu,ba'a dunga kawai bashi maganin lafawarsa ba,idan kuma ya tashi babu maganin fah" "Idan babu magani saidai yayi ta aman jini har na tsawon kusan sati,idan abin ya lafa sai a ƙaramasa jini,haka ake a lokacin baya" Jinjina lamarin deejah tayi a ranta,tareda ƙara tsinewa hajiya fulani a ranta,ɗan ta ma kenan inaga wani kuma. Tashi tayi tareda yiwa saleem sallama,akan zata dawo an jima idan ya tashi. Da yamma wajen magriba deejah ta nufi sashen su eemran da kwanon abinci a hannunta, ranar da tunanin halin dayake ciki ta wuni,duk santa da cire hakan a ranta abu ya faskara. A bakin ƙofar ta haɗu da saleem yana gyara takalmansa,gaisawa sukayi sai kuma tayi shuru batace komai ba. "Lahh ki shiga mana ya tashi yanzu,sallah ma yakeyi" Dama abinda take jira kenan,babu 'bata lokaci kuwa tasa kai ɗakin. A zaune ta hangeshi ya bata baya yana kallon gabas,da fara jallabiya a jikinsa,da alama har wanka yayi. Samun waje tayi ta zauna har ya idar da sallahr,juyowa yayi yana kallonta yanda ta tanƙwashe kafa tana kallonsa. "Ya jikinnaka yanzu " "Da sauƙi,ya aiki?" "Ƙalau,yanzu kam zaka iya cin abinci koh?" "Eh zan iya ci yanxu,amma bamai nauyi ba" "Eh nasani" Bude kwanon tayi ta zuba jallof ɗin dankalen turawan da tayi da hanta a cikin pilate,sai kamshi yakeyi na kayan kamshi. "Deejah a ina kika samu abincinnan,nasan dai ba irin wanda ake bayarwa a gidannan bane" "Eh nice na girka yanzunnan,bana gidan bane,na gidan shinkafa ce,nasan bazaka iya cinta ba,shiyasa na yi maka wannan " "Amm...." "Da kuɗina nayi eemran,koba zaka kar'bi kyautatawa daga gareni ba" "Ahah bahaka bane deejah,naga yanayin rayuwarne" "Ko kuɗina kenan zan iya yimaka,mutunci yafi kuɗi a wajena" Matsawa tayi da pilate ɗin gabansa tareda sakamasa cokali a ciki. Bismillah yayi tareda ɗiba a cokalin yakai bakinsa. Hannunsa ya ɗaga tareda yimata alamar yayi daɗi,yanda yayinne yasaka ta murmushi tareda boye fuska. Suna nan zaune yanacin abincin bai san lokacin daya kusa tashi dana kularba. A sakawa na ukune yace mata ya ƙoshi. "Uhm yanzu kam na ƙoshi,nasan na ɗan ci dayawa koh?" Dariya tasaka masa tareda nuna masa kular,sauran kaɗan a ciki,shima zaro ido yayi cike da mamaki,yana ɗan majewa alama yaji kunya. "Abincinne yayi daɗi sosai,shiyasa bansan lokacin danaci dayawa ba,na baki lambar yabo da wannan fannin. Amma a ina kika koyi abinci haka. "Abin sirrine,kaidai kawai tunda kayi santi ya wadatar,barina tafi tunda na tabbatar kaci dayawa. Ina wayarka ko baka da itah,ɗan sarki guda mai jiran gado" Zaro ido yayi tareda haɗe fuska,"rufamin asiri kina ganin jalal ido rufe yake neman sarautar" "Wazai bashi kuma,yarintarsa kawai yake,inkai baka ra'ayi ma ga mubarak nan,duk da yana kwance amma inshaallah tunda an gano mai yake damunsa ,maganin ma bazai gagaraba" "Hmmm allah ya tashi kafaɗunsa" Wayar ya ɗauka ƴar ƙarama ya miƙamata,lambar wayarta tasaka tareda kira ya shigo cikin nata wayar. "Gashi zan ƙiraka naji ya jikin in anjima,ka kula da kanka eemran,mukwan lafiyah" Bata bari taji mai zaice ba ta bar ɗakin. Ɗakinsu tashiga tareda ɗauko wata jaka a cikin kayanta ta fita daga ɗakin,lambun gidan ta nufa can wajen inda babu kowa ta zauna. System ta jawo a cikin jakar ta kunna. Hotonta a screen din da kayan bara a jikinta wanda ta saka lokacin dazata ɗauke brr. Shehu. Password ɗin tasaka mai dauke da MABARACIYAH,kafin system ɗin ta buɗe. Shedule ɗin aikinta ne kala kala a ciki kowanne da ranar yinsa dakuma wanda tayiwa,hotunan su amal da nemo itada madeena,take ta turawa wata photunnan. Rubutu tayi a ƙasan photon kamar haka. "Karamar itace wacce zaku kama gobe da safe,babbar kuma ƙarin bayani nakeso gameda rayuwarta,ku tabbatar kun samo kafinnna da gobe da daddare idan nazo zan ƙarba. Sannna inaso ku samo min labarin babban dan sarkin garinnan junaid wanda ya bata" Tana gama turawa ta shiga wasu file ɗin,abubuwa ne birjik,aikinda ta aikata harma da wanda ba ita ta aikata ba,dan hatta abubuwan dasu khamriyya sukayi tana dashi,tundaga aikinsu na farko akan Saifuddeen har wanda sukayiwa dr. Bukar. "Ƙananan ƙwari" Ta faɗa a hankali. Magana taji an shigo ana yi a cikin lambun. Kashe system ɗin tayi a hankali tareda leƙawa taga waye.. Hajiya fulani ce ita da wata mata,wacce zainabu tace mata ta hannun damanta ce. "Kinsan menene silver,kwananann inajin jinin junaid yana kusa dani,sannan ran dodo yasake baci da rashin karisa aikin da banyiba a kan junaid ɗin,ni nayi zaton ya manta ashe bai manta ba,tsawon wannan lokacin yana ta ƙoƙarin shanye jininsa,jiya Damzuk yake faɗamin. Na basu ruhin mubarak a matsayin na junaid amma sunyi shuru,su basu lasheshi ba su kuma basu sakeshi ba,sannan shi junaid basu ƙyaleshi ba" "Toh shugaba yakike ganin abin zai kasance" "Ni yanzu danasanin sallama mubarak nake akan junaid,zanyi ƙoƙarin nemo junaid na ƙarisa aikin akansa su ɗaukeshi,dan dama sunfi son jinninsa,shiyasa basu ɗauki mubarak ba. Idan yaso saisu sakemin mubarak ,idan na kashe sarkin yanzu nasan bazasu yarda da jalal a matsayin sarki ba,amma kuma zasu yadda da mubarak,kinga na kawar da junaid da kuma ubansa,sainayi duk yanda zanyi shima mubarak ɗin na dunga juyashi akan mulkin. Abin takaicinma dodo ya daina magana dani yanxu,idan nasamu wani wanda zai iya ɗakkomin ruhin da karfin gaske tsabbb zan aikata hakan" "Hakan yaya amma hakan yanada matuƙar hatsari fah gashi......" Shuru tayi bata ƙarisa ba jin motsin da ake a bayanta. Waigawa tayi tareda ɗaga murya tace "Waye a nan,koma waye ya fito idan yana son ransa" Fitowa deejah tayi daga wajen bayan ta tabbatar tagama recording abinda sukace tasaka a jakarta,dama da gangan ta yi ƙara da domin su jita. Hannunta ta ɗaga tana karkarwa cikin salon alamar shiga tsoro da fargaba. "Ninnnnni.......bazan faɗawa kowaba kimin rai ranki ya daɗe" Kallon kallon suke a tsakaninsu,yama akayi basu kulada mutum a wajenba harsaida suka buɗe sirrinsu. "Zan taimaka miki wajen ƙwato ruhin mubarak idan kika min rai ranki ya daɗe" "Mai take faɗa haka shugaba,barina yanke mata kai kawai da wuƙah" "Ahah ƙyaleta silver yarinyar tana da ƙwarewa akan aiki,itace wacce na faɗamiki ta gano mai yake damun mubarak" "Amma duk da haka taji abubuwa dayawa fah" "Karki damu,batada ikon buɗe harshenta ga kowa,idan tayi hakan tasan sauran. "Me kike anan wajen ke kaɗai" "Amm nazo shan isaka ne kawai,bansan zakuzo wajen ba" "Uhm naji,yanzu tunda kinji abinda bai kamata kijishi ba,kisa a ranki kin shiga tarkon da bazaki iya fitaba,aikin dazan baki shine. Inason ki ganomin a cikin gidannan wanene kikega zayyi kama da yarima junaid ke a ganinki,sannan kinada damar fita kana ki shigo lokacin da kikd buƙata,saboda ko yana gefen masarautarne ba a cikinta ba. Abu nagaba kuma inaso ki cigaba da binciken yanda za'ayi a ƙwato kuruwar mubarak daga inda aka ajiyeta" "Naji ranki ya daɗe,amma da kin bani labarin a ina kuruwar take,dannan ji ƙarfin gwiwar yin binciken" Harara silver ta watsawa deejah tareda cewa. "Wannann ba huruminki bane jin inda take,dan an jawoki cikin aiki bashine ke nuna zakiyi abinda ranki yakeso ba" "Na fahimta ƙaramar shugaba,zanyi binciken sosai,amma babu yanda za'ayi a fitarda shi daga cikin gidannan?" "Fitar dashi zuwa ina " "Inda kika yarda dashi shugaba,amma yin aikin a wajennan bazai yiyuba" "Shikenan zan shiryah fita dashi ,lokacin da kike buƙatar hakan saiki faɗamin" "Nagode shugaba" Sunkuyar dakanta tayi har suka bar wajen. Ɗaga ido tayi tana kallon fitarsu tareda ɗaga gira tana ƴar iskar dariyah. "Saini deejah,natsinci damin sa'a a akala. Da kunsan mai nake shiryawa da bakuyi saurin yarda daniba,taku ta ƙare idan nayi nasarar mallakar akwatinnan da kuma ɗauke mubarak daga gareku, Banda su shashashu mutumin da zuciyata takeso zan faɗamuku inda yake domin ku kasheshi......!?" Saida ta tabbatar babu mai kulada ita duhu ya fara kafin ta ɗauki jakar system ɗinta tabar wajen. Da daddare wajen misalin karfe tara,har ta ɗaga wayarta zata ƙira eemran sai taga shigowar ƙiransa. Ɗagawa tayi tareda gaisheshi da jikin. "Wannan jikidai ya warke yanxu" "Eh duk da haka ni hankalina bai gama kwanciya ba,sainaga ka fito aiki tukunna" "Uhm gobe zan fito aiki ai,nima zaman basonsa nakeba" "Idan zaka fito kayi wannan baɗɗa kamar sosai da sosai,yanda babu wanda zai ganeka" "Meyasa kika ce haka?" "Ahah babu komai,kawai hankalina bai kwanta bane" "Uhm karki damu,gobe inason muyi wata magana idan kinda lokaci" "Amma saida daddare,yanzu bazan iya haɗuwa dakai da rana ba,saboda wani dalili" Jimm yayi kaman mai son faɗan wani abu,saikuma yayi shuru tarede cewa "Shikenan yanda kikace,allah ya kiyaye koma menene,ki kula sosai. Saida safe" Daga haka ya kashe wayar. Ta dan daɗe tana kallon wayar kafin ta ajiyeta ta kwanta,tasan da alama fushi yayi amma hakan yafi mata da hajiya fulani ta ganoshi. Washa gari ƙarfe bakwai deejah tashiga ɗakin amal tareda buga gefen gadonnata. Tashi tayi tana harare harare da kuma tsuka. Bata kulata ba dacigaba da cewa "Yakamata ki tashi yanxu ki shiryah,kar driver yazo yayi ta jiranku" "To in ya jirani mai tsiyarki a ciki,nifah banason shishshigi,dan maita nace ki daina yimin aiki amma kinƙi" "Saboda bake kika ɗaukeni ba shiyasa,wanda ta ɗaukeni intace na daina zan daina" "Mtsswww mayyah kawai" Buge deejah tayi da ƙarfi ta wuce banɗaki,kana ganin idonta cikeda bacci,da alama jiya tayi dare tana hira da yayarta. "Kiyi ki gama,iya nayaune,nagaji da shanye wulaƙancinki,gobe idan ance kiyi bazakiyi ba" A haka ta gama shiryawar tana zuba rashin mutunci.. Jakarta ma ƙin ɗauka tayi sai deejah ce ta riƙe mata. Saida tashi motar kafin ta bata ta ɗora akan cinyarta. Saida taga ƙulewarsu kafin ta koma gefe ta ƙira waya. "Ku shirya sun fito daga gida,karku manta fah iya ita kaɗai zaku ɗauke,banda yaron..........shikenan idan kun kammala ku ajiyeta ina zuwa da daddare" Tana sauƙe wayar suka haɗa ido da yarima jalal yazo wucewa,saurin juyawa yayi zai sanja hanya.. Fito ta fara da bakinta wanda hakan yasashi juyowa,da idonta ta nuna masa wani corridor. Binta yayi a baya har suka wuce babu wanda ya gansu. "Inason ka kawomin akwatinnna a yau,dan gobe aikinsa zai fara,idan baka kawomin ba ka tabbatar iyanxu kana sume irinna ɗan uwanka. Zata fita da yamma,bazata fita da akwarinba yau,dan haka ka ɗaukomin!!" "Tam zan ɗauko ranki ya daɗe" "Hhhhh ɗan sarki mai jiran gado yana faɗawa mai aiki ranta da yadaɗe" "Amma bazaki tashi mubarak ba ina yanda mukayi alƙawari koh" "Hmm kaita mubarak kake koh,ita kuma uwarka ta kuɗurin kasheku takeyi,yanda bazaku kawomata matsala,musamman ma kai da tasan fankone,kawo wa akwatinnan shine tserar da ranka dazakayi daga hannunta" Mazari jikinsa yafara,gumi yana tsatstsafo masa,saurin barin wajen yayi domin fara zartar da aikin. "Hmm ana son duniyah ana tsoron mutuwa,haka mutane muke" Taku _sadi-sakhna_ Ƴar mutan jama'are. *MABARACIYAH* Taku_ _*sadi-sakhna*_ (Yar mutan Jama'are) 43••44 Assigment ɗin ta batasamu damaryi a gida ba tafara a cikin motar kafin su isa. Jitayi motar ta tsayah yayinda suka shiga wani titi mai shuru babu alamar motsin mutane. "Kai saleem menene naga ka tsaya lafiya?" "Ina kuwa lafiyah gimbiya,wasu matane masu jajayen kaya a gabanmu su uku,kuma dukkan su riƙe suke da bindiga" "Me bindiga?,mai mukayi musu toh?" "Taya zan sani,alama suke mana dai karmu kuskura mucigab da tafiya" manyane matan sosai su biyun,sai kuma ɗayar bata ƙarisa girmansu ba. Gidan baya suka bude tareda zaro amal daga cikin motar,ta faɗi a ƙasa farin kayanta ya baci da jar ƙasa. "Kai driver ja motarka ka tafi,mun ɗauki abinda muke biɗa" "Amma dan allah ku rufamin asiri,makaranta zan kaisu,bansan mai zance ba idan aka tambayeni a gida,ku taimakeni" "Kai ka rufe mana baki komu ruguruguza kanka yanzu nan,ina ruwanmu da mai zaka ce,wannan kaita shafa ba mu ba" Babbar cikinnasu tana gama faɗar hakan suka ja amal kiiiiii zuwa cikin jejin wajen. Bayyi kasa a gwiwa ba shima ya fito daga motar tareda bin bayan su inda sukayi..saidai wayam babu su babu alamar su. Cije yatsa yayi tareda juya akalar motar zuwa gida,dan abdul sai ihu yake yana ƙiran sunan addar tasa da aka samfe da ita. Yana yin parcking motar a harabar gidan abdul yafito daga ciki, tareda runtumawa da gudu sashen mahaifiyar tasu. Kuka yake yana faɗin abinda yake faruwa kan gari ya gari,kafin ya isa gareta har labarin yazaga ko ina ƴan kidnapping sun ɗauke amal. Wasu na allah ya ƙara,wasu kuma suna alhinin abin. Salati da sallallami hajiya saratu tafara,tareda maganganun da ba kansu ba ƙasansu. "Ya ilahi,hikuma jarabawar ɗaukemin ƴaƴa haka ta ganni?,an ɗaukemin ƴaƴana biyu kwanan su biyu da haihuwa ,yamzu kuma ita wannan an ɗauketa,yanzu hakama wanda yarabani da ƴaƴana tun suna tsumman zani shine ya rabani da wannan ma,bazan taba yafewa mai kwashemin yaƴa ba. Sai zan ɗaga magana ace nayi shuru,gidan sarauta bayason a dunga buɗe irin wannan magana,to da mai zanji a rayuwar nan.wayyyoooo" Yadiko lami ce ta riƙeta ganin tana ƙoƙarin zarewa,yayinda ita kuma deejah ta tsayah tana kallonta,ganin a sanadiyyar koyawa yarimyar hankali,da alama ta tabo mata gyambon dayake mata kaikayi a cikin zuciyarta. "Kiyi haƙuri haka hajiya,inshaallah ba irin wancan bane,wannan za'a ganta,ninafi hasashen masu ɗauke mutanene suce a basu kuɗi,zakiji sunyi magana a yau inshaallah.." Itadai hajiya saratu batace komai ba,abinda ya isheta ya isheta. Madeenah ce ta take kukan ɗauke ƙanwartata ta dubi hajiyan tareda cewa. "Ummah wane ƴaƴa aka ɗauke kuma" Kallonta tayi da ido jawur kafin tace. "Yanzu ba lokacin magana irin wannan bane,nidai a fito min da ƴa ta nakeso kawai" Rabewa deejah tayi tabar falon,kana ganinta kasan tunani take saƙawa a ranta,kona menene oho. Shuru akayi ta jiran ƙiran wanda suka ɗauketa amma babu ƙira ba alamarsa. Kowa a gidan yayi jugum yana jiran abinda Allah zayyi,duk da wasu a cikinsu ganin idone yasa sukayi,dan a ransu murnar bacewarta suke,dan dama ta damesu. A bangaren yarima jalal kuwa cikin fargaba da bugawar zuciya ya nufi ɗakin mahaifiyartasa. Kowanne taku dayake zuwa ɗakin yasan yana kasada ne da rsyuwarsa,saidai ya zayyi ya jefa kansa cikin halin tsaka mai wuyah,rana zafi inuwa ƙuna. Abinda yake sakawa a ransa shine,gwanda ya kamu a hannun uwarsa daya kasa aiwatar da aikin da deejah tasaka shi,saboda koba komai hajiya fulani uwarsa ce,kuma yasan shu'umancinta. Amma ita deejah bashi da masniyar mai zata iyah aikatawa,kuma babu alaƙar data haɗashi da ita. Da wannan tunanin ya isa gaban gadonnata tareda tsugunnawa yana kallon cikin. Wani wajen ya danna gadon yayi sama,ya fidda akwati na zinare an yi masa ado. To anan gizo yake saƙar,taya zai fito da akwatin ya maye gurbinsa dana hannunsa. Bayan baisan password ɗin ba. Dannawa ya farayi yana saka sunan da kuma abinda yasan zai iya dadai,amma babu wanda yayi daidai. 'J' yasaka sai yaga yayi dadai,sunansa ya saka amma yaƙi buɗewa,sunan yayansa ne ya faɗo masa a rai,wato JUNAID ga mamakinsa sai wajen ya buɗe. Dama har yanzu bata manta dashi ba,yanda yasani itace ta cutar dashi,to kuma ya akayi sunansa ya zamo mabuɗin sirrinta,tunanin ya kawar a aransa tareda buɗe abinda yake gabansa. Fitar da akwatin yayi sak irinna na hannunsa,ya akayi deejah ta gane irinsa oho,Allah masani. Mayarda wanda deejah ta bashi yayi wajen,kafin ya fice daga sashen da sauri,kafin tazo ta sameshi tayi wainarsa. Ƙara wayar tayi,tana dubawa taga ƙiran jalal,da sauri ta ɗaga, "Hello ka ɗaukomin akwatin ?" "Eh na ɗakko,kizo sashena ki karba,sannan ki tunada alƙawarina" Tana kashe wayar ta nufi sashennasa,burinta shine tayi ido biyu da abinda ta daɗe tana burin mallaka.. Bata ganshi a falo ba,dam haka direct ta wuce ɗakinsa,dan taga ƙofar a buɗe,da alama yana ciki. A bakin gadonsa ta sameshi a zaune,gefensa kuma akwatinne yana shafa jikinsa,wani murmushi ya ɗago da wurga mata ma shu'umai,lokacin data shigo ɗakin "Na cika miki alƙawarinki na ɗakko akwati,saura abu ɗaya shine ki cikamin naki alƙawarin na bani kanki a yanzu,da fatan dama da shirinki kika zo" Itama dayake jar wuyace idonta tsar akan akwatin,da alama wani abun take saƙawa. "Sumail ka dauki akwatin ka tafi dashi ketare ƙasar nan,dan idan yana cikin ƙasar nan zata iya bin diddiginsa da shu'umancinta,ka lalata tsafinta dayake cikinsa,amma karka share sunan mubarak tukunna,dan idan ka share nemo rauhinsa a wajensu zayyi mana wuyah" Tana gama faɗan hakan akwatin ya 'bace 'batt a ɗakin tamkar bai taba wanzuwa ba. Waige waige jalal ya fara yana neman inda akwatin ya shiga,kenan aljanace ita duk tsawon lokacinnnan bai sani ba? Matsawa ya farayi yana girgiza kai ,ita kuma ganinsa cikin hakan sai ya sakata nishaɗi,koba komai tayi wani abun dazai ƙaramasa tsoronta. Takawa take a hankali shikuma yana da baya,har taje bakin gadon da niyyar hawa,shikuma har yakai karshen gadon. "Haba yarima mai kyau,kaifah kace min kanaso kaɗan danɗana,yanzu kuma bakaso ne,tsorona kake kake ja da baya,jarumin masarautar katsina?" "Dadddan ALLAHHHH kiyi haƙuri ki taimakeni,wayyo allah nah,bansan ke aljana bace da bazan yimiki haka ba" "Allah ko baka sani ba?.....in faɗama wani abu dazai rikita ka,yayanka junaid yana raye,kuma yana kusada kai,sannan shima ɗaya yayannka yana daff da farkawa daga dogon baccinsa,taya zan taimaka maka kayi sarauta toh,so kake na kashesu dukka kokuma me?. Ka daina wanann mafarkin,babu inda zai kaika sai halaka,kai a duhu kake baka san komai ba. Ka gyara rayuwarka ka tsaya iya haka,idan kuma nasake ganinka da wata macen a gidannan,ko kuma kayi shaye shaye,.........hmmm don't imagine." Daga haka ta sau masa tattausan murmushi tabar ɗakin. A bakin ƙofar fitowa daga sashen nasa ta haɗu ta sumail yana jiranta. "Oh harka tsoratani,yaushe ka dawo" "Minti biyu baya. Taya zan tsorita aljana kuma?" Yafaɗa ta sigar zolaya. Dariya tayi tareda cewa. "Kajini kenan dashi,hmmm yanada rawar kai ne.Yanzu tunda munyi nasarar ɗaukar akwatin,kana ganin zata iyah gane inda yake,nifah nasan sharrin matar nan" "Hhh karki damu,na kaishi ga shugabana wanda nake ɗaukar karatu a wajensa akan ya buɗeshi,lokacin dana tahodai yana ƙoƙarin budewa,zai iya ɗaukarsa wataƙil kwana biyu ya bude,amma idan ya buɗe dole zata san baya nan,duk da cewar bazata san inda yake ba" Jinjina lamarin deejah tayi,inba an haɗa da mutanen boyeba taya zata iya wanann abin ita kaɗai. Wajen la'asar sakaliyah hajiya fulani ta dawo daga meeting itada ta hannun damanta,surayyah wacce aka fi sani da silver. Koda ta shiga ɗakinnata razana tayi,domin a jikinta taji cewar am buɗe mata ma'ajiyar sirrinta,saurin ɗaga gadon tayi tareda duba akwatin. Ganin yana ciki yasa ta sau ajiyar zuciya tareda ɗagowa ta kalli silver. "Huh komai normal,duk cewar ko ɗaukarsa akayi ma mutum bazai iya buɗewa ba,idan ya buɗema da sakanni zan gano inda yake. Ki ƙiramin deejah naji mai ta bincika a yau" Waya silver ta ɗauka ta dannawa deejah ƙira,akan suna nemanta. Babu bata lokaci kuwa tazo,dan dama hakan yana cikin tsarinta,an kulle gidan babu shiga babu fita ana bincike. In bada ƙwaƙwƙwaran dalili ba mutum bazai fitaba. "Ranki ya daɗe gani" "Uhm mai kika samo gameda yarima junaid,ko har yanzu bakiga wani ba wanda kike zargi?" "Eh banga komai ba,amma akwai wasu baƙi da akace sunzo jiya cikin gidannan da yamma samari,kuma suna zaune a bayan gidan galadima. Naso naje na duba,to kuma an saka matakin rashin fita,shiyas........" "Shiyasa me,ina ruwana da wani rashin fita na batan yarinya,saratu ma ta bace mana ba ƴar ta ba,ki shiryah yanzu zan aika a barki ki fita injini,ina son ganoshi da gaggawa,nagaji da riƙe wancan mai kama da gawar,dole ɗayam biyunsu zai mutu,ɗayan kuma zan mallakeshi na ɗorashi akan mulki" "Toh ranki ya daɗe,barina je na shirya nazo" "Yanzu zan aika saƙo,in kinzo fita ki wuce kawai,babu wanda zai hanaki,sannan ki tunada gargaɗina,karnaji plan ɗina a bakin kowa,idam ba haka ba ki shirya ganin ki babu harshe" Jiki yana rawar ƙarya deejah ta bar sashen hajiya fulanin. Cikin rashin sani suna ta sauƙaƙa mata shirinta hmmmm. Tafiyah take tana ƴar waƙa,bata luraba taji tayi karoda mutum a gabanta. Ɗaga kai tayi suka haɗa ido da Junaid wanda ya sarƙe hannayensa a ƙirjinsa yana kallonta. "Dama kina waƙa,ya naga kin fito daga sashennan,har yanzu kina yi mata aikin duba shi ne" "Ɗaga kai tayi,dan tasan mubarak yake nufi,duk da tanaga a alamar tausayawa ɗan uwanna sa a idonsa,amma yana ƙoƙarin boyewa. "Kanaso ka ganshi ne" "Uhm,amma bazan iyaba koda na samu dama,bansan a yanda zan ganshi yanzu ba,rabona dashi tun shekara sha huɗu baya,da farko nayi zaton ya mutu,sai akace wai yana raye,doguwar suma ya shiga" "Amma daga yanda kake magana,kaman kun shaƙu dashi sosai" "Mun shaƙu sosai,a lokacin iya mu huɗune,khadija sai mubarak da kuma khaleel,sai kuma mubarak shine ƙarami lokacin. Tare muka taso da khaleel,saidai shiya fini da watanni,mahaifiyarsa itace Babba,wato Hajiya Fulani maryama. Bayan rasuwarta ne mahaifiyarmu ta karbi matsayinta na fulani. Sannan hajiya saratu tana amarya,da tsohon ciki,ita kuma mahaifiyarmu tanada cikin jalal. Kusan a tare suka haihu,hajiya saratu ta haifi yara biyu mata,ita kuma ta haifi jala,tsiransu kwana biyu. Ranar Sunan jalal,su kuma kwanan su biyu aka nemesu aka rasa. Hayaniya ce ta kaure a gidan,ga mutanen kowanne bangare sun zo domin taya su samun ƙaruwar haihuwa. Babu irin shiga yanayin tausayi da hajiya saratu bata tsinci kanta ba,saidai kaman maye yaci shirwa haka zance ya shiririce,tun ana nemansu har aka haƙura aka zubawa Allah ido akan sarautar sa. Da farko kasamcewar babu wanda yasan abinda mahaifiyata take,babu wanda yazargeta akan abinda ya wakana a wannan lokacin,saidai da ta aikata na shekara sha huɗu baya,sai komai ya fito fili na halayenta. Deejah nayi bakin cikin kasancewata ɗa a gareta,saidai koma menene babu yanda zanyi,ita ɗin uwata ce Allah ya zana hakan. Dan haka banajin zan iya saka kafata a wannan sashen dana fado duniya na buɗe idona a wajen,sannan shigata daidai yake da zuƙewar jinina,wanda inajin wani abu yanzu ma yana fizgar ƙirjina ta ciki" Ya faɗa yana dafe ƙirjinsa ta bangaren hagun. Saurin saka hannu deejah tayi taja shi zuwa can kusan sashensu nesa da inda suke. "Kuma kasan hakan meyasa kazo kusada wajen,duk da hakan zai iya cutar dakai" "Saboda naga shigarki sashen,haka kawai hankalina yaki kwanciya ganin baki fito ba" Numfasawa deejah tayi tana kallonsa,yanda yake ƙoƙarin saita numfashinsa. "Saboda me kake nunamin irin wannan kulawar Junaid,a ganina kaman yayi yawa,tunda har zaka iya saka lafiyarka a hatsari saboda ni" "Saboda ina sonki ne,ina ƙaunarki,ina miki so tsakani da Allah har can ƙasan zuciyata,ia yimiki son da ni kaina idan na tambayeni bansan iya adadin zurfinsa ba. Allah ya jarrabeni da azabtacciyar soyayya,sanann kuma makahuwa,da bana ganin komai idan bakeba a bangaren bege,kewa soyayya da kuma sahihiyar ƙauna" Runtse ido deejah tayi tanajin yanda maganganunsa suke huda dodon kunnenta har izuwa can ƙarƙashin zuciyarta,tunda take bata taba jin kalaman da suka girgizata irin wannan ba.. Inda a satin bayane kafin ta gane shiɗin ɗan makiyyartane,da tuni ta karbi soyyyarsa,amma a yanz duk da cewa tana masa kwatankwacin soyayyar dayake mata,batajin zata iyah karbar wannan tayin. Domin bakomai zai haifar mataba sai kawomata cikas a cikin Kuɗurinta. Sauke idanuwanta tayi akan sa wanda suka sanja kala zuwa na emotion zalllah. "Ina sonka emran,ina sonka junaid,koma A wanne suna ka bayyana ina sonka,saidai kayimin uzuri da lamuni akan wanann babban ragama dakake burin na karba daga wajenka. Bazan iya karbar soyayyarka ba saboda wani dalili,kayimin haƙurin hakan" "Babu komai,saidai kisani ko yanxu zuciyata ta samu nutsuwa dana san cewar na amayar da abinda yake cin zuciyata,koda baki amsa ba nidai ya fita daga gareni. Zan cigaba da yin soyayyar bangare ɗaya har zuwa ranar dazaki amshi soyayyata deejah" "Nagode daka fahimceni,saidai nayimaka alƙawarin bazaka ga sanji daga gareni ba,yakamata ka shiga cikin ka huta,domin har yanxu jikinka bayyi ƙarfi sosai ba" Jijjiga kai yayi tareda yunƙurin miƙewa,dan matsawa tayi ya tashi,tareda kallonsa har ya shige sashensu. Hawayen dayake zarya a idonta tasaka hannu ta share,ita wacece a cikin mutane dazata ce batason yin rayuwa irinta kowa da wanann bawan Allah. Saidai ita kaɗai tasan mai zai faru idan har ta amince masa,kuma ya tarar abinda tayiwa uwarsa daga baya. "Kayi hakuri Junaid,ina sonka amma bazan iya ganin fuskarka a matsayin masoyiba bayan ina koƙarin kashe uwarka" Daga haka tashiga ɗakinsu tasaka wasu kaya baƙaƙe,riga da wandone amma rigar har ƙasan gwiwarta,jagaye kanta tayi da gyale kafin ta kalli salaha wacce take cin tuwo. "Salaha hajiya fulani ta aikeni Waje,zan fita koda yadiko lami tazo nemana,kice bazan dade ba" "Saikin dawo" Shine kawai abinda tace,daga nan tai hanyar waje. Tana zuwa kama. Yanda ta faɗa mata suka buɗemata kofah ta wuce. Wani layi tashiga ta baya,saiga wata mota tana jiranta,shiga tayi aka ja sai bayan gari. _______________________________ Khariyyah ce a zaune da system a gabanta tana wani aiki,sallama takeji amma ta gagara tashi daga abinda take. Fadeelah ce tazo wucewa,zata shiga kitchen. "Yawwa ke zokije ana sallama a waje,kijiyo ko waye" "Wai anty khairi har yanzu anty khamriyyah bazata dawoba ne?" "Ke ni rufemin baki,tujarar da kikayiwa deen dazu bata isheki ba saikin karamin wata,akwai wata khamriyyanne bayan wacce kukayi waya da ita,tace muku wani watan zata dawo,me kuma kike so kiji. Watan gaba zasu gama training ta dawo ƙasar. Yanzu dai maza jeki kiga wanene yake zuba uwar Sallama tun ɗazu" "Uhm da ayita cemana masifaffu nida twincy nah(khmariyyah),ashe ke masifarki tana hanyar zuwa,gashinan kin ishi mutane da hayani" Itadai khairiyyah bata dago kanta ba bare ta kula sabrah,wacce take rike da kofin cornplacks. "Hmmm ni mai yasa ma na zauna a gida nake aikine,da ina can hankalina kwance" "Yanzu ma waya riƙeki,tafi mana" Fadeelah ce tashigo riƙeda wata wasiƙa a hannunta. Sabrah ta mikawa dayake tafi kusada ita. "Gashi inji wani,wai daga madeena amaryar Uncle Sadeeq" "Amarya kuma,an ɗaura auren ne,kajimin ƴar iskar yarinya" "Wace yarinya kike magana sabrah,wai tukunnama mai aka turo a saƙon?" "Hmmm wai madeena matar Sadeeq,bariki ji mai tace a ciki. _assalam antynah ta wucin gadi,ina mai sanar dake cewa kifara sakawa zuciyarki hakurin rashin mijinki daxakiyi,dan daga zarar na nashigo kisani fita zakiyi. Idan kuma kina ganin zaki iya zan baki wani abu,idan kin isa har kika aikata,nikuma ina mai tabbatar miki da cewar ba bar miki shi halak malak. A yau an saka ranar aurena dashi,wani watan a daidai wannan lokacin. Idan har kin isa kuma zaki iya soyayyarki har ta kai haka. To kizo cikin gidanmu na masarautar katsina ki bayyana cewa kece a ransa,shima kuma ya faɗamin da bakinsa cewa ke yake so bani ba,idan har hakan ta faru,nikuma na barmiki mijinki..........naji ance kina tsoron bayyana kanki ga dangin miji Saboda bakida uban dazaki nuna ko dangin uban,taya wanann zata zama MATAR SADEEQ?_ Ajiye system ɗin khairiyyah tayi,tareda sake karanta wasiƙar da kanta bayan ta fizgeta. "Kutt kan ubancan,kiji ƴar iskar yarinya,mai take nufi kenan,anya kuwa bata san ke wacece ba" "Inma tasani zan nuna mata cewar nima ƴace,meye laifina dan bansan iyaye naba khairiyyah,sai tayi dana sanin wannan maganar kuwa,Allah ya kaimu ranar auren" Cikin kuka ta ƙarisa maganar,tana gama faɗa kuwa ta juya tashige ɗakin data fito daga ciki. Hmmm zata koma gidan jiya na kuka kenan......... Taku _sadi-sakhna_ Ƴar mutan jama'are. *MABARACIYAH* _haƙƙin mallaka_ _*sadi-sakhna*_ (Yar mutan Jama'are) 45••46 Duk gari da nepa,amma inda suka nufa da motar babu alamar haske sai duhu ƙirin. Gidane kaman kango,amma kuma taciki madaidaicine sosai. Fita deejah tayi a motar,idonta a toshe da glass baƙi,alamar babu mutunci.. Zare glass ɗin idonta tayi tana kallon amal wacce ta jigina da bangon ɗakin tana bacci. Zama deejah tayi akan kujerar da take gabanta tareda shurarta ta ƙafarta. "Ke tashi dallah,nan ba gidan ubannaki bane da zaki yimin bacci anan wajen" Sautin numfashi tayi na alamar wanda yayi wahalallen bacci. Da sauri ta murtsike tareda ja da baya tana kallon deejah wacce take zaune a gabanta. "Ke kuma mai kike anan wajen,bakiyi kama da wanda aka ɗaukeba,in aikoki akayi ki ƙwatoni to ki sinceni mu tafi" Zabga mata mari deejah tayi guda biyu a kowanne gefen kumatunta,kafin ta nuna mata yatsa a baki,alamar tayi shuru da bakinta. "Yimin shuru,kinga nayi miki kama da wacce zaki dunga magana a haka?" "To ke wacece bayan yanda na sanki" "Hmmm banda nashiga gidanku domin neman wani abuba,ke kin isa ko ido ki ɗaga a gabana,bare harki ɗaga hannu ki mareni? Yanzu zan zartar miki da hukuncin rashin kunyarki kafin gobe nasakeki ki tafi gida. Idan kuma koda wasa naji zancen a bakinki kokuma kika nuna alama kafin na gama abinda nake,hmmmmm. Zanga tsakanin keda jalal waye zai iyah riƙe tsoronsa gareni bai bari wani ya ganiba. Dagake harshi,idan naga kun cigaba da abinda kuke saina murƙusaku." "Tttto amm.....amma meyasa kike haka ko ku........" "Shhsh inayine saboda ɗan tausayina daku na wani dalili,yayanku yanajin haushin yanda kuke,nikuma bazan juri ganin yana kallon ƙannensa a haka,shiyasa zan gyaraku ku koma saiti. Hukuncin dazaki ɗauka kuma yanzu nayimin rashin mutuncine" Dariyah ta sheƙe da ita tana kallon yanda jikin amal yake rawa. "Bigggy,zo ki mata bulala ashirin,gobema da safe kiyi mata goma,ki bata abinci taci,nima iyayenta basu barni da yunwa ba. Sannan wajen misalin ƙarfe goma ku rufe mata fuska ku kaita gefen gidansu. Nizan koma,idan aka kaiki gidan naje gyaramiki jikinki gobe,saiki sakemin rashin mutunci,zan sake nuna miki yanda akeyi wanda yafi naki" Daga haka deejah ta mayarda glass ɗinta ta bar ɗakin. Tun kafin ta fita tafara jiyo ihun deeja biggy tana dukanta. Sai wajen misalin karfe goma kafin ta koma gidan,bayan tagama wasu uzururrukanta. Har tashige taga kamar alamar inuwar mutum yana kallon,tsarguwa tayi wanda hakan yasa ta ta nufi wajen. A hankali take tunkarar wajen,har ta isa inda inuwar take. Haɗa ido sukayi da junaid wanda shima kallonnata yake. "Meyasa kika ƙi dawowa da wuri,bayan kinsan akwai wanda bazai iya bacci ba har sai yaga kin dawo gida cikin koshin lafiya?" "Kayi haƙuri,naje wani wajene amma bazan sake yin daren ba" Ta faɗa cikin ƙaramar murya,kaman mai son nuna rashin laifinta. "Amma da bai kamata ka fito yanzu ba,bayan kaima bajin daɗi kake ba" "Babu komai yanxu zan kwanta,mu ƙwana lafiyah" Juyawa yayi cikin sanyin jiki,deejah tana kallonsa har ya kule. Itama nasu bangaren ta nufi,tausayi da kuma soyayyar junaid sun ƙi barin zuciyarta sam. Washagari kaman misalin karfe goma yanda deejah ta faɗawa su biggy,suka saketa bayan sunyi mata bulalarta guda goma,kuka kam da azaba babu wanda bata shaba. Since mata hannu suka,sanann suka tafi,na fuskar kuma ita tasaka hannunta dasukayi tsami ta buɗe. A bakin ƙofar gidannasu ta tsinci kanta,amma tacan nesa da mutane,yanda mutane basu kulada su ba. Takawa take a hankali jikinta yana rawa har ta isa bakin ƙofar. Wani dogarine yakula da ita,da sauri ya nufi wajen tareda duddubawa. "Subhanallah gimbiya Amal ce a wani yanayi,maza ana buƙatar suturtawa domin kaita sashensu" Wasu dogarawane suka matso da sauri akan tareda da babbar riga,yayinda mata biyu kuma suka kinkimeta zuwa sashen hajiya saratu. Kan kaceme dawowar tata ya zaga ko ina,wasu na barka wasu na Allah yakyauta. Salaha ce tazo da gudu ta ƙira deejah akan taje ta taimakawa amal ɗin. Tun ɗazu suka fadamata sun ajiyeta,ƙiran dama take jira. Ajiye wayar tayi akan katifarta,tareda tashi ta nufi sashen hajiya saratun A zaune take madeena a gefenta ɗayan wajen kuma hajiya saratu,dukkansu sai duba jikinta suke suna tambayarta me akayi mata,wanene ya ɗauketa? Amma taƙi cewa komai,sai kuka take kawai kaɗan kaɗan. "Shikenan yi shuru,munji daɗi ma da babu abinda yasami darajarki,basuyi miki fyaɗeba,ki daina tunawa ya wuce kinji. Daga yanzu za'a ƙara tsaro idan zaki fita sosai,tunda abin yazama haka,banason sake rasa wani yaron a yanzu" Gyaran murya deejah tayi,tun ɗazu tana tsaye tana kallonsu. Suna haɗa ido da amal tayi saurin sunkuyar da kanta,jikinta yafara rawa,duk da tana ƙoƙarin saitawa karsu gane. Ita deejah ta kulada hakan,shiyasa tayi saurin gyara murya tareda cewa. "Sannu gimbiya amal ya jikinnaki,sai mukaji kyakykyawan labari na dawowarki,Allah ya ƙara tsarewa,muje in taimaka miki ki gyara jikin,,kafin mutane sufara zuwa" "Hakane kam,jeki deejah ta taimaka miki ki gyara jikin" Itadai amal tana son cewa kar a barsu da deejah su kaɗai,amma kuma batada ikon faɗan hakan,dan kamar mala'ika haka take ganinta a yanxu. Tashi tayi ta bita a baya har suka isa ɗakinnata. Saurin tsugunnawa amal tayi ganin sun bar kan idon mutane. "Dan Allah kiyi hakuri,wlh baxan ƙaraba na rantse da......." "Dakata! Nafi kowa sanin bazaki karaba ai,nima kuma banca zan sake yimiki wani abunba,tashi muje banɗaki na taimaka miki ki gyara jikinki. Kiyayyata badaku bane dukka,dan haka ki kiyaye shiga gonata daga yau,nagama abinda ya kawoni na tafi" Da sauri amal ta shiga banɗakin tayi wanka sosai bayan deejah ta haɗa mata ruwan wankan. Lokacin data fito deejah tana zaune a bakin gadonta tana kallonta. "Ɗauke nata idon tayi tareda sunkuyawa,in tace zata daina tsoron deejah to tayi ƙarya" "Ga kayana ɗauki ki saka,nasan dukan baikai yanaki yin komai ba,na saka miki magani a ruwan wankan,nan da nan zai warke" "Nnnagode" "Hhhh godiya kike min,daina wannna zancen,kin kusa daina ganina ma a gidannan,watan gobe iya yanzu nabar rayuwarku gabaɗaya" Daga haka deejah ta fita daga ɗakin bayan ta tabbatar komai ya daidaita. Kwana uku kenan da dawowar amal,yau kamma har makaranta taje,jikinta da sauƙi sosai. Ta ɗan rage tsoron deejah yanzu,data san ba komai zatayi mata ba,amma fah ko da ido ta bata umarni yi take babu tsayawa. Hankalin deejah kwance yanzu,dan yanzu batada matsala da yarima jalal da kuma amal,madeena kuwa ita bashiga shirgin mutane take ba sosai. Wani satin zata koma makaranta zasu fara jarabawa,tana dawowa kuma za'a yi aurensu da Dec. Sadeeq,dan dama an saka rana. Hajiya fulani ce ta kalli deejah tareda cewa, "Na jaki jikina a lokacin da bai wuce wata guda ba,kin samu damar da ba wanda ya samu,yanzu zan tambayeki na ƙarshe,kin gano shi kokuwa baki ganoshi ba" "Na ganoshi ranki ya dade" Tashi hajiya fulani tayi ta zauna daga kwance da take. "Me kika ce,kin ganoshi yaushe" "Eh naganoshi,zan faɗamiki amma da sharaɗin bazaki kasheshi ba,sannan kuma zakiyi amfani da damarki kicire masa gubar dakika saka a ƙirjinsa. Idan kikayi haka toh zan nuna miki shi" "Well well yarjejeniya kikeyi dani,ke wacece?" "Ba yarjejeniya bace,shiɗin saurayina ne,kuma zan iya komai domin kareshi,kiyi amfani a jikinki ki kareshi nikuma zan faɗamiki a ina yake" "Nikuma bazan yimasa maganin ba saikin dawomin da akwatina da kika ɗauka,jiya nagane an ɗaukeshi,sannan jalal ne ya ɗauka,kuma nasan ke kika Sakashi. Abinda yasa bandamu ba saboda nasan duk innda kika kaishi dole zaki dawo dashi,idan kuma kika ƙi toh zaki karni kanki a gabanki" "Hhh bana tsoron abinda zaki ce Hajiya Fulani,idan na kawo nasan zaki kasheni idan ban kawo bama zaki kasheni,dan haka idan kinaso na dawo miki dashi,to dole saikin yi abinda nace. "Ki cire aljanin dayake kan jalal wanda yake sakashi yin shaiɗanci,sannan ki cire aljanin dayake yiwa Nana khadeeja aiki akan kishiyoyinta. Ki ɗauke gubar da take kirjin Junaida,sannan kuma ki nemi a saki ruhin mubarak. Idan ba hakaba,to bazan taba faɗamiki inda akwatinnan yake ba,idan kika kasheni ma kin rasa har abada." Zaro ido hajiya fulani tayi tana kallon deejah,batayi zaton yarinyar har takai haka ba. "Ya akayi kika yi nasara tsallaka kasarnan da akwatin bayan kina nan? Dan inaji a jikina yana nesa sosai" "Hhhhh wani abokina nabawa dazashi wata ƙasa ya tafi dashi,yana shirin dawowa,zabi yana gareki,ko kiyi abinda nace ya dawo dashi,ko kuma nace ya jefashi a teku a hanyar sa ta dawowa" Gumine yafara tsatstsafowa hajiya fulani,dan tasan idan babu akwatinnan duk matsayinta da dukiyar data mallaka duk sai sun salwance. "Shikenan naji zan cire abinda kikace,kafinnan saiki faɗamin a inda yake koh?" "Uhm wannan ba matsala bace,tunda kin yarda da abinda nace. Wanda yazo a matsayin mai kulada dawakan Hajiya Saratu,shine ɗanki yarima junaid." "Yau juma'a bazaiyu aikin yayi yanda ake so ba,amma gobe zan sa a ɗebeku harke dasu zuwa gidana na sirri,inda nake duk wani aiki. Sannan zan wanke kaina a wajensu,na nuna nice nakeson yin hakan bake kika sakani ba,idan kin yarda muhaɗu gobe" "Eh na yarda,buƙata shine kiyi abinda nace,na warware wannan abinda kikayi" "Ke wacece,da kikeson bada rayuwarki domin wasu daban,ki dawomin da abinda kika ɗauka,nikuma zan maidake abinda bakya zato a nigeria" "Wannan kawai nake bukata,saboda soyayyar danake yiwa ɗanki" "Uhm Allah kuwa ya tsinewa soyayay in hakane,shiyasa banga komai a cikinta ba sai wahala" "Bazaki gani ba kam,tunda kika kasa jin son ƴaƴanki" Daga haka deejah ta juya tafita a sashen,babu abinda taji a ranta,dan tasan babu abinda zata mata indai har akwatinnan yana hannunta. "Hmmm zaki ɗanɗana kuɗarki,Allah ya kaimu goben,daga nan tarihinki ya ƙare a doron ƙasa,saina miki abinda zaki buƙaci mutuwa dashi" Tana fita silver ta kalleta tareda cewa. "Amma meyasa kika amince mata,bayan kinsan idan babu akwati saidai fah ki maida gubar dake jikin Junaid kanki,inba haka ba sai kinyi musu alƙawarin wani na jikinki dazasu ɗauka" "Nafiki sani silver,nasan dodo bashida yafiyah. Amma kisani na shiryah haɗa musu tuggu ne da bazasu iya tsallakewa ba daga ita har su Nasan bazata iya samun wanda zai buɗe mata akwatinnan ba a mutane,dan haka zan wanke kaina a gabansu tamkar na tuba da abinda nayi musu,daga baya kuma bayan nacire abinda yakd jikinsu,zata dawomin da akwatin. Nikuma saina kasheta itada sarkin garin,na bada jininsu ga dodo a matsayin yarjejeniyata batareda su junaid sun sani ba. Kinga na dawo da yarda ƴaƴana ita kuma na kawar da ita,zan jefi tsuntsu biyu da dutse guda kenan" "Amma kuma kaman suna soyayya da junaid fah" "Hhhhh kaman kin mantani kennan,daga lokacin da na ɗorashi a mulki zan maidashi mutum mutumi ne,bazai san komai ba sai abinda na sanar dashi,ba zai ganiba saina nuna masa,bazai jiba saina faɗamasa. Kede ki tsaya kiyi kallo gobe,deejah kuwa duk da ta taimakeni a plan ɗina tayi kuka da kanta,dan saina yi mata abinda ban taba yiwa wata halitta ba" Junaid ta zubawa ido daga inda take zaune,zefi zefi yake ɗagowa ya kalleta,tun yana basarwa har abin yafara bashi mamaki. "Deejah menene ya faru,idan naganki kinamin wannan kallon to da akwai abinda yake damunki,ko kin kwarewa soyayyatane kema amma kin rasa yanda zaki faɗamin?" "Batun soyayayr ka dama na daɗe a ciki ai" "To meyasa kika ƙi amincewa zuciyarki" "Saboda batada ikoyin hakan koda kuwa tanada buƙata,in tayi ma zata cutar da kanta ne sannan kuma ta cutar da wanda yake son ta. Idan hakane taya wannan zuciyar zatayi garajen wannan kasadar" "Wace irin kasada kuma?" "Kayi hakuri junaid da abinda na aikata maka a yau,na bayyanawa mahaifiyarka wanene kai" Zaro ido yayi yana kallonta,bayyi tunanin hakan daga wajenta ba "Hakan bazai haifar maka da kowacce matsala ba,hasalima nayi wata yarjejeniya ne da ita,in exchange zata cire gubar dake jikinka,daga nan komai zai daidai ta shikenan" "Me zaki bata,nasan koma menene akwai illa a cikinsa" "Kayimin uzuri bazan iya faɗaba,kona faɗamaka ma bazayyi amfani ba,tunda ta riga ta amince" Shuru junaid yayi yana kallon deejah,duk da cewa daga nan bai sake cewa komai ba "Allah yayi mana mai kyau,amma ban miki alƙawarin bazan bincika menene ba da kaina,tunda bazanji daga gareki ba" "Nikuma dan allah ka taimakeni karka shiga sashennata da kanka,idan kayi hakan shikenan" Kaman yanda ta faɗa kuwa,a ranar ta aika a ɗauko mata gimbiya khadija daga gidan aurenta,duk da cewar ita babu komai a jikinta,amma saidai tana son ta buga wasan a gabanta. Dukkansu bude ido sukayi suka kallesu a wani a gida wanda basu wayeshi ba. Junaid ne yafara juyawa ya kalli khadija,wacce itama kallonnasa take da mamaki. "Kai kuma waye daga ina kake?" "Kina nan da faɗanki da kuma taƙamarki kenan Kadidi" Fuskarta ce ta nuna alamar mamaki,domin tasan sunan tun suna yara su junaid suke faɗamata. "Ke addah khadija ina fah da hannunsa a ɗaukomu,banda haka mai mukayi,kuma kinga can yah mubarak ma a cikin akwatinsa,me yake faruwa" Yar dariyah Junaid yayi,dan shi yasan mai yake faruwa,a yanda sukayi magana da deejah jiya yasan yanada alaƙa da wannan yanayin. "Me kukeci na baka yana zuba,wanda ya kawomu wajen zai bayyana kansa ai,basai kunyi wahalar tambaya ba" Har khadija ta bude baki zatace wani abu kalmar ta makale,ganin mahaifiyarsu ta fito daga wani ɗaki. Zaro ido sukayi,dan inka ɗauke junaid da kuma deejah da take gefen ɗakin a zaune babu wanda yasan zai ganta a lokacin. "Ummmah mai muke anan wajen kuma,wani kikayi mana?" "Ko ɗaya ƴata babu abinda namiki,abinda nayi muku a bayane nayi nadama,shine nakeson gyara kura kuraina idan zaku bani dama" Ta ƙarisa maganar cikin sigar tausayi da nuna nadama. Itama khadijan cikin mamaki tace "Ummah kece kuwa? Amma naji daɗi da hakan ta faru,koba komai farincikinmu ne mu ƴaƴanki" Dan murmushi tayi tareda shafa fuskar khadijan, "Hakane kam, na saka wani aljani dayake ɗaga darajarki fiyeda ta sauran yan gidan mijinki,harma da kishiyarki,zan janye na barki ki zauna lafiya,nasan yin hakan zai sa mai martaba ya daina jin haushinki na yin zalunci a gidan miji. Kaima jalal na taka rawa wajen lalacewarka,domin in zaka gujemin kabi ra'ayin mahaifinka nina hanaka. Haka kaima junaid na ajiye Guba ka sha,duk da bakai na ajiyewa ba,amma kuma ina sane na barka a wajen ranar dan kar nawa asirin ya tonu. Saikuma mubarak,da kaina na bada rauhinsa saboda wata buƙata tawa,saidai zanyi iya koƙarina wajen gyara laifina. Dafatan zaku fahimceni" Fadawa jikinta khadija tayi tana kuka. Ƴar dariyah deejah tayi babu wanda ya jita sai junaid da tun ɗazu ya kulada ita a wajen,amma kuma bai nuna ya ganta ba,haka kawai yakeji a jikinsa akwai wata a ƙasa na halayyar da uwar tasa take nunawa a yanxu. Wajenda mubarak yake kwance ta nufah tareda ɗora hannunta akansa. Wani abu takeyi na kusan minti biyar kafin ta ja wani numfashi,da alama aikinnasa ya bugeta. "Zai iya tashi daga nan zuwa gobe,komai zai koma normal,saikai junaid " "Ahah bana buƙata,inda gaske tuba kike bai kamata najiki kina ambaton sunan wasu aljanu ba,indai da shirka zaki warkarni to na ƙwammaci ciwom ya kasheni" Wani kallo tayi masa kafin kuma gyara fusakrta zuwa abin tausayi,kafin yayi wani yunƙuri saiji yayi yana ƙoƙodon amai. Kaman ana fizgar ƙirjinsa haka yakeji. Deejah ce ta taho inda yake da gudu,saidai kafin takai ga isa inda yake ta tsayah tareda kallon su jalal. "Ku tallafa masa,bazai ji daɗi ba idan na taba shi" Riƙeshi sukayi yana ta kakarin amai,can wani baƙi abu kaman kwalta yafara fito wa daga bakinsa mai kauri. Saida ya zubar yafi cikin jug kafin jini ya biyo baya,sai kuma aman ya tsaya. "Hmmm nizakayiwa iyayin neman magani,kowanne magani da layinsa ake warkar dashi,duk maganin dakayi da kwantarshi kake,kuma koyaushe sake cin jikinka yake. A da yawansa kaman mintin daka shane,yanxu kuma ka kalli yawansa a jikinka,da haka sai duk jikinka ya koma haka,shin zaka iya jurewa?" Shuru yayi yana kallonta,shikaɗai yasan mai yakeji aransa. "Shikenan nagama cire abinda nayi muku,yanzu kowa a cikin ku zai iya tafiya." Wasu mutanene masu baƙaƙen kaya suka taimaka musu suka fita daga ɗakin,saura ita kaɗai da deejah kawai. "Nagama abinda kika buƙata,yamzu sauran naki cika maganar" "Hmmm wannan ai kanki nasaka kika yiwa,saboda kar abin yamiki yawa,amma ko kusa bazaki iya shafe laifin dakikayimin ba a raina. Wai tukunna ma kinsan Malam AUDU Mai BARA,na garin KANKIA?" Tafiya tunani hajiya fulani tayi sai daga baya ta kalli deejah da alamar razana. "Keceeee?" "Ƙwarai,kinyi zaton sun kasheni kenan,ahah shi zakaran da Alllah ya nufah da cara ko ana muzuru ana shaho ai sai yayi. Bammmm Sumail kacewa malaminka yanzu zai iya fasa akwatin,lokaci yayi" Wani gigitaccen ihu hajiya fulani tayi,amma kafin ta ƙarisa ihun Taji wata ƙara a cikim ƙoƙon kanta,da alama aikin gama yariga ya gama. Ita kuwa deejah wata gigitacciyar dariyah tasaka,na ganin burinta da ta daɗe tana so yazo daf da cika. ........ Taku _sadi-sakhna_ Ƴar mutan jama'are. *MABARACIYAH* _haƙƙin mallaka_ _*sadi-sakhna*_ (Yar mutan Jama'are) 47••48 "Me kika aikata min da akwatin,waya taimaka miki kika buɗeshi" "Hurumin sanin waya taimaka min,kawai ya faru a lokacin da bakiyi zato ba kuma bakiyi tsammani ba. Dama ance rana dubu ta barawo rana ɗaya ta mai kaya,sannan kuma dama akwai ranar ƙin dillanci,yau taki ranar tazo." Kakarin amai hajiya fulani tayi tareda riƙe kanta,saboda barazanar ihun mutanen data kashe suke mata a kan. "Da nasan ke wacece ta tuni bakizo wannan matakin ba,saboda yaron daya tashi da burin daukar fansa,yafi kowanne mutum hatsari" "Gwanda da kika gane hakan,yanzu kiyi manage da wannan kafin nazo ɗaukar fansa ta a kanki gobe,babu makawa kuma saikin amshi hukuncina daidai da yanda kikayiwa mahaifina,ruwanki ne idan nayi miki ki jure ki rayu,ruwanki ne ki mutu bai dameni ba" Kasa jura tsayawa hajiya fulani tayi,kafin wani lokaci tayi luuuuu ta faɗi Tsallaketa tayi babu alamar tausayi ta nufi bakin ƙofah,mutanen wajen ta kalla tareda cewa. "Ta faɗi me yiyuwa tana bukatar taimakonku a ciki" Suna shigewa ita kuma tabar gidan gabaɗaya,tana fitowa ta tari adaidaita sahu sai gidan masarautar. Saleem ta gani yana gode motah,kunnensa rufeda ear piece yana jin waƙar rara. "Am saleem Eemran ya shigo ne?" Shuru yayi bai jita ba saida ta maimaita tukunna ya zabura ya juyo. "Ehhhh mekikace ne?" "Nace eemran ya dawone?" "Eh ya dawo,naganshi ɗazu ya wuce kansa a sunkuye,danayi masa magana ma bai kulani ba" Bata bari ta gamajin abinda yake faɗaba ta wuce inda ɗakinnsu yake. Sallama tayi amma yaƙi amsawa,kuma tana da yaƙinin yana jinta. Dan haka tura ƙyuren ƙofar tayi ta shiga cikin ɗakin A kwance yake rabinsa ya rufu ta bargo,yana jan numfashi a hankali. "Amma bai kamata ka shigo nan kai kaɗai ka zauna ba,yakamata ka bari ƴan uwanka su taimaka maka yanzu,dan nasan suna nemanka,basu san ka taho nan ba" "Bana buƙatarsu a yanzu,gabaɗaya abinda ya fari yau ya kullemin kai,ina jin zafi a raina da har yanzu nakasa samun matsayi a wajenki dakazaki iya faɗamin mai yake faruwa" "Ba haka bane junaid,wani abun barinsa a duhu yafi fito dashi,saidai koma mene kayi haƙuri ,iya abinda zan iya kenan shiyasa. Yakamata kaje suna buƙatar ka,sannan mahaifiyarku itama tana cikin halin neman taimako" "Hmmm a tunaninki na yarda da wasan da kuka yi cewar ta tuba,nasan hakan yana daga cikin abinda ki buƙata a wajenta,duk da bansan wani abinba amma nasan fiyeda babu. Dalilin faduwarta kuma nasan akwaitin sihiirin ta wanda tasaka sirrinta na tsafi a ciki kika buɗe,kuma wanann aljanin dayake miki aikine yayi wannan abin. "Ba aiki yake min ba ,taimakona kawai yayi kaman yanda na taimakeshi a baya yakoma kan hanyar gaskiya" "Eh to naji,yanzun suna ina su" "Sun tafi asibiti inda take kwance,yakamata kaima muje a dubaka,dan Allah karka cemin a'a" Har zayyi magana ta haɗa hannunta a fuskarta alamar roƙonsa. Baice komai ba ya tashi daga kwancen tareda jawo bargon kan kirjinsa,kasancewar bashida riga. Tashi tayi zata fita a ɗakin domin bashi waje,sai taji yayi mata magana. "Ki faɗawa saleem ya ɗanzo idan kin fita" Ɗaga masa kai tayi,daga nan ta fita. Tana zuwa ɗakinsu ta tattara kayanta waje ɗaya. Babu kowa a ɗakin,shiyasa ta samu damar yin duk abinda takeso. Bayan ta gama tafito,sannan har sun shiga mota zasu nufi asibitin,a gidan baya junaid ya kwanta saboda ya mike,itakuma ta shiga gidan gaba itada saleem. GENERAL HOSPITAL KATSINA. suka nufa direct,inda aka kwantar da Hajiya fulani. A raception aka basu bayanan inda take,dayake sunada Family register basusha wahalar neman inda suke ba. A kwance take kaman matacciya har yanzu,Nana khadija a zaune a gabanta,shikuma jalal yana tsaye,gefensu kuma mubarak ne a kwance shima. Dukkansu kallon Junaid yuyi wanda yake layi kaman zai faɗi a bayan Deejah, "Doctor maza kuzo ga wani na buƙatar taimako" Da sauri nurse ɗin wajen suka kwantar dashi a katafaren gadon asibitin shima,tareda bashi taimakon gaggawa. Babu bata lokaci likitoci biyu suka rufu akansa domin bashi taimakon gaggawa (Hmmm idan bakada kowa kuwa babu wanda zai kulada kai,saima a fara neman wasu dalilai dazasu hana a dubaka. Nigeria kasarmu,Allah ya shirya mana ita) Ledar ruwa kusan biyar Junaid yasha kafin ya mike daga kan gadon,tsawon lokacin Gimbiya khadija bata bar asibitin ba. Ranar satinsu guda a asibitin mubarak yafara motsawa,ba iya yan uwansa ba hatta sauran mutane saida hakan ya girgizasu. Idonsa yafara buɗewa akan hasken silin ɗin asibitin,saurin mayarwa yayi ya rutsen idon,dan ji yayi tamkar an caka masa abu a ciki. Hannunsa yajawo domin jin ko suna aiki,ga mamakinsa sai yaji sun motsa,tsawon lokacinnna yau yayi abinda ya daina mafarkin samun damar yi. Sake bude idanuwan yayi domin adjusting din harken wajen,wanda duk da ya rufe idon ma yana jinsa a ciki. Dusu dusu yake gani,amma duk da haka bai hanashi gane cewar,macece a zaune sai kuma wata a kwance a kan gadon. Ɗan tarin daya bar bakinsa da niyyar yin magana ne yasa Gimbiya khadija juyowa inda yake. "Ƙanina ƙanina,ka bude idonka kaine kake kallona,Oh Allah nah" Kallonta yacigaba dayi,yayinda kunnuwansa suke ƙoƙarin karbar maganar datake aika masa,dan a kalmominnata kaɗanne yake mai take cewa. Fita tayi da gudu ta ƙira likitan kwalkwalwar dayake dubashi,shima kansa yayi mamaki dayaga tashinnasa a dawuri,saboda basusan abinda hajiya fulani tayi ba akansa. Kafin zuwa yamma mutane sun cika asibitin ana kallom mubarak,wanda yanzu a zaune yake an jinginashi da jikin bangon ɗakin. Awa biyu kenan da farfadowarsa amma har yanzu babu abinda yace,saidai duk wanda zayyi magana ya juya ya kalleshi,da alama yanajin abinda suke faɗa kenan. Sannan babu laifi yasha ruwan tea da hajiya saratu ta bashi,dan ita ma tazo asivitin tun jiya domin ta taimakawa Khadija kulada masu jijyar. Itama madeena ranar da suka zo asibitin tazo dubasu,amma dayake washagari zasu fara jarabawa dole ta tafi. Hajiya saratuce a zaune tana ƙoƙarin bawa mubarak abinci a cokali,kallonta yake da alama baya ganewa sosai,sai tayi tukunna shima ya kwaikwaya. "Khadija yakamata a tuntubi likitannan yaushe zai fara magana koh?" "Eh munyi maganar jiya,yace wai tsawon lokacin daya ɗauka a kwancene,dole sai a hankali ko zai tuna komai" "Uhm to Allah ya kawo sauƙi,yayah hajiya fulanin itama bata motsaba,Allah yasa dai ba ita kuma wannan bacci rashin tsammanin ta faɗa ba" "Ameen ummah,nima abinda nake tsoro kenan,kar ko nata rauhin ta bashi ita ta fadi" Amal ce ta shigo da abinci a hannunta,a bayan ta kuma deejah ceh,wacce itama take riƙeda kula. "Sannunku ya masu jiki" "Da sauƙi amal,kema ya jikinki,naji labarin tsautsayin daya faru dake,toh Allah ya kiyaye gaba" A hankali ta amsa tana kallon deejah wacce ta ɗauke kai tana gaisheda jikin mubarak ɗin. Sunan zaune basu daɗe ba Mahaifiyar Su sadeeq ta shigo,shima yana biye a bayan ta. Ta ƙasa deejah take ƙaremusu kallo har suka zauna a kujerun ɗakin. Bayan an gaisa suka fara labarin duniyah. "Ummah Deejah,ina yah khaleel ne har yanzu bai dawo ba?" "Uhm au yayannaki,eh ya dawo amma baya garin" "Kuma shine ko yazo a gaisa,yasan labarin mubarak ya tashi kuwa,ai yakamata yanzu kam ya shigo gidan koh?" Shuru hajiya Deejah tayi,da alama bata son yin zancen saboda wani dalili. Haka kawai daga yanda deejah take nazarinsu ta kula akwai wani abu a ƙasa. Masu zuwa dubiyah sun ɗan ragu ba kaman da ba,shima mubarak da sauƙi sosai,dan yanzu yakan kama sunayen jalal,idan yana son abu kuma sai ya nuna da hannunsa,ko kuma ya fada a cikin kalmomi ƙalilan. Yanzu zaman asibitin saboda hajiya fulani kawai suke zaune,ita yanzu takan buɗe ido,duk daga gani bata gane komai dayake faruwa. Ganin abin bana asibiti bane yasa suka fara tunanin tafiya gida,zaman asibiti dama ai sai dole. Tashi Hajiya fulani tayi daga bacci,suna haɗa ido da deejah tayi saurin mayar da idonta ta rufe. Ƴar dariyah tayi kasa kasa babu mai kulada ita,ita dama tasan babu abinda ya samu hajiyan na tabin hankali,fargaba ce a jikinta kawai na bata san yanda zasu ƙare da dodonsu ba,da kuma haɗuwarsu da deejan wacce ta barta ta warke. Tattara kayan deejah suka fara itada salaha,dan dama dalilin zuwansu kenan dan su tayasu tattare kaya. Kowa fita yayi aka bar su iya deejah da kuma hajiya fulani sai khadija. Kallon hajiya fulani deejah tayi ta ƙasan idonta,kafin tayi mata alamar zatayi magana da ita. Tana ganin hakan ita kuma ta nunawa khadija banɗaki,tana uhm uhm da bakinta. Matsawa tayi tareda fita komawa gefe,ita kuma saita shige banɗakin. Wayarta ce da take hannunta ake ta ƙira,wanda hakan yasa ta kalli deejah tareda cewa. "Am deejah kike koh? Ki tsaya anan wajen har ta fito daga banɗakin sai ku fito,barina amsa wannan wayar a waje" "Toh Ranki ya daɗe" Deejah ta faɗa da sauri,dan dama haka take so. Gaskiya allah yana taimakonta,ta faɗa a ranta. Matsawa tayi kusada ƙofar banɗakin ta ƙwankwasa da ƙarfi. "Zaki iya fitowa ƴarki ta tafi" Buɗewa hajiya fulani tayi tana kallon deejah wacce ta kama kunkumi tana kallonta. "Hmm bazaki taba tuba ba hajiya fulani,nasan bazaki taba canjawa,ina jinki da daddare jiya kina wayah data hannun damanki,akan yanda zakuyi plan ɗin kasheni. Da nayi niyyar barinki kodan ƴaƴan ki,amma yanzu kin bata rawarki da tsalle. Dama an ce mutum baya tsiya sai yayi wa kansa,a yanzu babu wanda yasan Bakida ƙarfin iko saini da dakum babban ɗanki,kinga kenan bana cikin masu tsoronki koh? Biggy ku shigo yanzu nan" Tana gama faɗan hakan ta fesa mata abu a fuska. Kaman jira suke kuwa suka shigo ɗakin ɗauke da kwandon shara babba suna turawa. Kinkimarta sukayi suka jefata a ciki tareda rufewa suka fita a ɗakin da sauri. Deejah tana ganin sun fita, ita ma ta fito daga ɗakin da gudu tana ihu kan gari ya gari. "Ranki ya daɗe ku kawo taimako ku taimaka,babu hajiya ta bace,wasu baƙaƙen halittu sun bace da ita yanxu nan" Ko zazzzaro ido yayi su hajiya saratu da kuma su jalal,babu wanda ya musa abinda deejan tace,saima tsoro daya shiga ransu,dan sun san hakan dama zata iya faruwa tunda ta tuba. Ita kuma hakan da tayi yabawa su biggy damar fita daga gidan cikin kwanciyar hankali,batareda kowa ya sani ba. Shuru dukkansu sukayi aka rasa mai cewa komai, basu ma sam ya zasuyi ba,tunda kowa tunda yaji ance bacewa tayi,taya zasuyi yunƙurin nemota. Mota suka shiga domin tafiyah gida,babu mai cewa komai a cikinsu. A hanya saleem ya bugawa Junaid waya yake faɗamasa mai yake faruwa,dan duk cikinsu yanda sukayi tagumi babu mai cewa komai,suma bangaren hajiya fulani a tasu motar gwanda ma kowa dasu. Kafin su iso labarin bacewar Hajiya fulanin yaje ko ina a cikin gidan,yan uwanta ma daga maiduguri wanda basuzo dubata ba suna hanyar tahowa. Wanda suka san tsafin da take kuwa sun san ruwa baya tsami banza,wataƙil ta daba wanda suka fi ƙarfinta. A bangaren junaid kuwa kafin su iso,yana ajiye wayar yaga mata a gabansa tana rarrraba ido. "Am junaid,dama uhm dama Tsafin Mahaifiyarka ya karye lokacin data tuba sannan......." "Ya karye saboda deejah ta buɗe akwatinta,uhm mai zakice faɗi ina jinki?" "Uhm ba bacewa tayi ba,inaga deejah ce ta ɗauketa kaman yanda ta ɗauke amal wancan ranar" Ɗan nazari ya tafi na wucin gadi kafin ya kalli wacce ake ƙira da Silver. "Taya kika san hakan ke" "Share baki tayi ta sanar dashi duk abinda tasani gameda tsakanin hajiya fulani da deejan,harma da irin rashin tsoro da kasadar deejan. Abin yabashi mamaki amma ba sosai ba,dan kowa yaganta yasan macece mai kamar maza a ta fuskar kasada,abinda bai sani ba shine yanda deejah tayi yarjejeniya akan ta warkar dasu ita kuma zata bata akwatinta,saidai kuma ta buɗeshi daga ƙarshe,hakan ma bai isheta ba ta saceta a asibiti bayan ta farka. Bata ɗauketa tana sumeba saida taga ta tashi tukunna. Tabbas akwai abinda yake faruwa a ƙasa wanda bai sani ba. "DAUKAR FANSA take,to kennan wacece itah,sunaye mutane biyu hatsabibai ne suka shigo cikin kunnensa. MABARACIYAH &V-LADY,su biyunnan yafi zaton inaga ɗaya daga cikinsu ce,shitttt gashi har sannan dawowarsa kenan bai san suwaye ba,duk da yanada bayanan su amma kuma mai ya haɗa ɗaya daga cikinsu da hajiya Fulani??????....... Yana tsaye yana cizon yatsa motocin su Jalal suka shigo gidan daga asibiti. Duk wanda ya fito daga motar sai ya kalleshi har suka ƙare baiga deejah ta fito daga motar ba. Salaha ya kalla har zata shige ya ɗanyi mata magana. "Am salaha ina deejah kuwa,banga kun dawo da ita ba" "Ahah gaskiya bansani ba,inaga ta tsaya wani wajenne a hanya,dan dama tacemin wai zata duba wata mata a asibitin" Daga haka salaha ta shige ta barshi a wajen batareda ta kawo komai a ranta ba. Ɗan gefe ya koma yana kare fuskarsa,amma saida khadija ta kulada shi. "Yah Eemran am nace bah......" Tun kafin ta gama ta nemeshi ta rasa,suma su hajiya saratu kallon wajen sukayi amma basu ganshi ba,itama komai ta tuna sai tayi shuru da zancen,ashe fah bayan mutanen gidan yaja kunnen kar wanda yayi maganar dawowarsa. Duk da bata faɗi sunansa ba amma kuma sai taji dai bai dace ba,tunda baya so. Shikuma kiran da tayi masa sannna yaja saleem da sauri zuwa ɗakinsu. Suna shiga ya maida ƙofar ya rufe yana haki. "Kai khaleel lafiya kuwa?" "Uhm kaman kasan zan koma kan sunan,lokacin fara aikin su mabaraciyah dana karba zanyi yazo ,saidai kuma tsoro da fargaba sun mamaye zuciyata a yanzun" "Mai kake nufine,munzo domin Kama mahaifiyarka mu miƙata ga hukuma,yanzu kuma abin ya juye,wai ta bace ba ganta ba" "Kai dec. Saleem ina hankalinka ya tafi,ba bacewa tayi ba,ɗauketa akayi,kuma deejah ce ta ɗauketa" "Whattt mai kake nufi da deejah ce ta ɗauketa,kana da shaidu akan hakan?" "Shaidu kake nema,ga babbar sheda nan,shin kun dawo tareds ita ne yanxu a mota. Ta hannun daman Ummee tazo yanxu take faɗamun yanda sukayi da deejah daren da zasu ɗaukemu,sannan kuma ita ta ɗauke akwatin tsafinta ta fasashi,kuma itace ta ɗauke amal ranar da aka nemeta aka rasa. Kuma inada tabbacin khaleel ma akwai gargaɗin da tayi masa,kaina ya kulle dec. Saleem sosai,reshe yana nema ya kuye dani,gabaɗaya zuciyata so take ta ƙaryata abinda nake ji a cikin raina." "Gaskiya abin zaiyi maka babu daɗi,yanzu dole mukoma headquater mu buƙaci bayanai daga amal da kuma jalal" "Karkayi yanda yan gidan zasu sani,har yanzu ban yi niyyar bayyana musu a matsayin khaleel ba tukunna,da sauran lokaci" "Karka damu ogah za'ayi yanda kace,amma ya kamata ka faɗawa dec. Sadeeq halin da ake ciki,koya kace?" "Eh zan sanar dashi amma ba yanxu ba saina gano inda deejah ta ajiye Mahaifiyata tukunna" Kayansu na ɗakin suka fara tattarawa ba tareda kowa ya gansu ba. Suna gamawa saleem ya ɗaika yakai mota a jiye,shima Khaleel babu wanda ya ganshi ya shige motar suka fita daga gidan. Saida sukaje bayan gari tukunna saleem ya kalli Dec. Khaleel. "Toh mun bar area palace yanzu," Dec. Khaleel bai ce komai ba sai ɗaye abinda yake fuskarsa da yayi,take ainihin fuskarsa ta bayyana,wanda deejah ta taba kallonsa da ita lokacin yana jinyah. Shima saleem fuskar wawayen daya saka ya cire tareda furzar da isakar bakinsa. "Finally back to the business,ammafah nayi missing ɗin wancan saleem ɗin ogah" "Hmmm ai kana ban dariyah sosai a wancan fuskar,sai kace drivern gasken,inna ganka bazance kaine wanda muke training tare a china ba" Ƴar dariyah Dec. Saleem yayi tareda cewa. "Kaima waye zaice kaine wannan mai kulada dawakin hhhhhjj" "Hmmmm aikin akwai wuyah amma akwai shiga rai,danna saba da dawakan sosai a iya wannan lokacin" "Ka ƙira shamakin gombe ma kayi masa godiya da taimakon da yayi mana" "Okay inshaallah,yanzu dai kaini gida nayi wanka na kwanta tukunna,su san nadawo daga tafiyar danayi,amma fa zanyi missing ƙanwar nan taka sosai(amal),dan gaskiya tashiga raina" "Karka fara wannan wasan,kana nufin tunkararta zakayi kace mata kaine driver,ko zuwa mata zakayi a matsayin sabon mutum?" "Huhh kumafah nima bansaniba,yazanyi dole na haƙura,duk da nayi kewarta" Shuru Dec. Khaleel yayi bai kulashi ba har ya ajiyeshi a gidansu shikuma yawuce nasu gidan. Meena ya gani a falo tasaka headphone tana ta jijjiga kai,ɗaga ido tayi ta kalleshi tareda washe baki, "Lahh yah Khaleel yaushe ka dawo,ko sanarwa saidai muganka" "Ina ummah take?" "Uhm ta tafi fada,wai mama fulani ce ta bata ba a ganta ba" Ɗaga kai kawai yayi daga nan ya wuce ɗakinsa.. Tunda ya shiga ɗakin tunanin deejah suke son kallame zuciyarsa,amma yaƙi basu dama,har yashiga banɗaki yasaki ruwan sanyi a jikinsa. Furzar ta iska yake shi kaɗai yana dukan bangon ɗakin,gaba ɗaya yarasa inda zai saka kansa. "Yah Salaaam" shine abinda ya faɗa a sanyaye. Toh fah Taku _sadi-sakhna_ Ƴar mutan jama'are. *MABARACIYAH* _haƙƙin mallaka_ _*sadi-sakhna*_ (Yar mutan Jama'are) 49••50 Kwara mata ruwa tayi a jikinta,hakan yasa taja ajiyar zuciya tareda ware idanuwanta akan deejah,wacce take tsaya tasha riga da wando. "Kalleni dakyau nice dai ba wataba,mabaraciyar datake aiki akan wasu yau yazo kanki,saiki jiyaryi hukuncinki a yau ba sai gobe ba" Ko bakin magana hajiya fulani takasa samun yi,tsoron dayake jikinta take ƙoƙarin rikewa ta hanashi ya fito daga jikinta. Tsugunnawa deejah tayi a gabanta,su biggy kuma suna tsaye kaman samudawa. Idonta yasha kwalli na rashin mutunci,kana ganinta kaga irin fuskar ƴan farauta. "Toh barinayi sauri nagama dake kafin masoyina kuma ɗanki yazo ya riskemu,dan yanzu shine keda Akalar ragamar bincikenmu nida Khamriyyah. Hmm harya fara bani tausayi yanda ɗan uwansa ya bani,da alama ɗanki zai sha wahala,kema kuma zaki sha. Saina bari yakusa wajennan kafin na yi miki hukunci,saboda karki mutu kafin ya iso saboda zubar jini. Biggy ku kariso aiki zai fara,ina kun bashi hint ɗin inda muke,ko har yanzu bai ganoba" "Eh mun nuna masa,idan ya gane to da alama yana shirye shiryen zuwa" "Okay let we start,hajiya fulani kafin ki suma idan muka fara aiki,barina baki saƙonki. Kisaka a ranki wannan abinda zan miki shi ake ƙira da Retribution,wato ramuwar gayya kenan,duk abinda kikaga zan miki kwatankwacin yanda kikayiwa ubana ne,babu yafiya kema saina zartar miki shi. Dan haka muhaɗu a kotu idan kina raye da ranki" Tana gama faɗan hakan kafin hajiya fulani taja wani numfashi tasheka mata wani abu a hancinta. Injin katako ta ɗauko,yana kara ta yanke mata ƙafafu dukka. Bayan hakan bai isheta ba ta saka wani Karfe ta cire mata idanuwa dukka biyu,jini ne yafara ambaliya,hakan yasa tayi baya sauri tareda gode hannunta tana ganin aika aikar da tayi. Daga fuskarta zaka gano aikin da tayi yana cin ranta,amma haka ta danne ta ajiye wata wasiƙa a kan tebur suka nufi hanyar barin wajen. Waiwayawa tayi tasake kallon Hajiya fulani wacce jini yake zuba a ƙafafunta da kuma idanuwanta. "Namiki da daɗi ma akan yanda kika min,kin ci albarkacin ɗanki" Suna barin wajen baifi da minti biyar ba saiga su Dec. Khaleel sun shigo wajen a motar yan sanda ta sauri. Dama tun ɗazu suke ta ƙoƙarin nemo wajen a massage ɗin da biggy ta tura musu. Sai yanxu Allah ya basu ikon gano wajen. Saidai kash duk yanda yaso dakatar da ita da aikata hakan ya makara,ta riga ta aiwatar da mummunan aikin da yake fargabar kada ya auku. Takardar da take gefen wajen ya ɗauka tareda sakata a aljihu,bayan ya an fitada Hajiya fulani cikin mummunan yanayi,bata san inda kanta yakeba dan azabar dayake ziyartarta. Magana dec. Saleem yake masa,amma kwata kwata bays jinsa,fargabar abinda zai gani a cikin takardar data bar masa yakeyi,duk da acikin ransa yana addu'ar Allah yasa bata ɗaya daga cikinsu,Amma kuma zicuyartasa ma tasan gaskiya ai. Su dec. Saleem ne suka wuce da hajiya fulani asibiti,shikuma yana tsaye a wajen da wasu ƙananan ma'aikata yana duddubawa. To meyake da tabbacin zai duba a wajen ma,shikansa yasan waye ta aikata hakan,amma kuma yagagara faɗawa kowa wacece. "Oh yah Allah,dama ashe haka Sadeeq yaji,shi matace ma harda ɗa,nida ko hakkinta ba'a kaina yake ba,jinake kaman zuciyata zata faso kirjina,taya zan iya sakawa wannan hanayen ankwa,bayan mungun son danake yiwa mai su. Har cikin zuciya ta inada muradin kareta,duk da nasan mai ta aikata,burina shine yazamo tana da wani dalili daya sakata yin wannan aikin. Mai yasa daga dawowata rayuwata ta juye daga kwanciyar hankali zuwa tashin hankali?" Takrdar dake aljihunsa ya fitar tareda wareta __Assalamu Alaikum Yarima Junaid,ko kuma nace Dec. Khaleel. Kayi hakuri da boye maka abubuwa da dama da nayi,babu yanda zanyi ne dole saina aikata hakan. Kaman yanda kake so na da kuma begena nima haka kake a cikin raina,saidai muradin ɗaukar fansa tasa Alaƙar dakake buƙatar sakawa a tsakaninmu bazata yiyu ba. Bazan iya furta maka kalmar soyayyata har ta kaimu ga matakin gaba ba,alhalin ina akwai baƙin cikin tabon da mahaifiyarka tayimin a raina. Da zan iya yafewa nabari ya wuce danayi,saidai ganin duk da soyayyarmu nakasa hakura saida na dau fansa,yasaka bazan iya rayuwa tareda kai ba. Ka yafemun abinda nayi maka a zaman mu,Sannan ka manta dani ka auri ƴar mutunci,mai halin sanyi da tausayi irinna mata,ba irina ba wacce take da taurarriyar zuciya,da kasa manta abinda akayi mata a baya. Zanyi kewarka sosai,ina jiran ranar dazaka saka ankwa a hannuna ka kaini ga alƙali masoyina. Domin dama wannan shine aiki na ƙarshe daya ragemin,samuna zayyi maka wuyah,saboda koda zan kawo maka kaina saina gyara wani abu tukunna,wanda niya kamata na gyarashi,kafin sannnan ka huta,ka kwantar da hankalinka,babu wani aiki dazanyi Bayan wannan. Nasan hakan zai yi maka wuyah,amma ta hakannne kaɗai zaka manta dani a shafin rayuwarka,ka cigaba daga inda ka tsaya.____ Daga mai sonka da kuma ƙaunarka...... Khadija Abdullahi kankia (DEEJAH MABARACIYAH) saurin zefar da takardar yayi tareda ja da baya ya faɗi akan kujerar dake bayansa. Abinda yake gudu shine ya faru,itace ɗaya daga cikin wanda yake zargi. Tun yana china yakejin ɗanyen aikin Mabaraciyah,yaji ya tsaneta,burinsa shine ya dawo gida ya fara aikinsa akan ta bayan yagama aikin mahaifiyarsa. Bai saniba ashe zayyi rayuwa tareda ita,kuma yafaɗa muguwar tarkon soyayyarta. Riƙe kirjinsa yayi tareda zayyano duk wata addu'a data shigo bakinsa. Sati guda da faruwar abin aka fita da hajiya fulani ƙasar waje domin yi mata aiki,na idanu da kuma ƙafafu. Gari kowa ya ɗauka banda tsinuwa akan mabaraciyah babu abinda kake ji. A tsawon wanann satin Khaleel a killace yayi su,dan ko media baya son leƙawa saboda zagin masoyiyarsa dayake shiga kunnesa. Ana cikin wannan ne kuma khamriyyah tasako ƙafarta kasar,bayan wani muhimmin aiki dataje koyowa a ƙasar ƙetare,bikin Dec. Sadeeq kuma da Madeena shima saura sati ɗayah. Khairiyyha ce taje tarota a filin jirgi itada su fadeelah,dan ranar kin zuwa makaranta sukayi. A hankali take takowa daga cikin jirgin cikin wani salon arnen dafiya mai tafiyar da duk wanda yaga ta burgeshi. Wandon plazo ne a jikinta na jeans sai kuma top karama data ɗora a rigar saman,sannann ta kawo gyale tayi rolling dashi. Ga kuma baƙin glass ta toshe fuska. Buɗe baki khairiyyah tayi daga nesa tana kallon yanda ƴar uwartasu tazama kaman ba itaba,da alama zaman wajen ya ƙarbeta sosai. "Wow Khamree kinganki kuwa" "Yane na sauya ne?" "Tambaya ma kike,yanzu dai muje gida kawai,inada aikinyi nabari nazo daukarki,saboda deen bayanan an turasu Abuja akan neman aikinsu" Taji abinda khairi tace,amma bata bashi muhimmanci ba sosai saima hankalinta data miƙa kan abin sonnata,wato yaƴan da uwarsu haifarsu kawai tayi,duk wata wahalarsu ita tasha da kanta. "Fadeen kin kara girma a ɗan wata huɗun danayi bana nan,mai su khari suke baki kikeci" Kukan shagwaba tasaka,tareda narkewa a jikin khamriyyah,kana tace. "Anty khairi dukana take kullum,dannace suna soyyyah da uncle deen,kuma ma dan anty sabrah tace,idan uncle Sadeeq yazo bazai kula kowaba saini kaɗai" "Tabbb dukanki take kenan,banni da ita,babu abinda zan bata a chocolate ɗin mu,fadeel fah,shine kaja ka tsaya kana kallona koh" "Kiyi haƙuri mommy,nayi murna da kika dawo sosai" "Toh naji kuzo mutafi kar wannan antynnnaku ta cinyeni ɗanya,tun ban gama shaƙar iskar ƙasar ba" Daga haka suka shiga motar sai gidannasu. Tun a bakin kofah maryam da Fareedah suka taryeta,da inno ,balkisu wacce itama tazo taryar khamriyyah daga gidanta,saikuma Dr Nawwarah itama bataje aikiba,sai uwar gidan a wajen Dec. Sadeeq wacce take zaune da tulelen ciki na wata bakwai ya shiga na takwas. Hararar wasa khamriyyah tayi mata tareda ware mata hannu Babu yadda ta iya bataso tashi ba haka ta yunƙura ta miƙe tareda nufar khamriyyan. Rungume juna sukayi tareda saka dariyah a tare. "Gaskiya na daɗe bana nan,ji yanda wannan matar ta zama ƴar lukuta,khairiyyah tacemim kin fi kowa ci a gidannan. Tukunna ma ya zancen tsakanim ki da mijinkine har yanxu. "Komai normal Khamree,yanzu dai zoki ci abinci kiyi wanka ki huta tukunna,saiki bamu labarin Turkey ɗin,da kuma abinda kikayi" "Hmmm gasane fah aka tura a makarantar danaje ƙarin karatu,banyi ma nasara ba yanda nake so,ta biyu nazo suka bani mota,wata ƴar india ce tayi na ɗaya,saidai yafi babu,dama kawai fitarce ta ja hankalina,bani akayi niyyar turawa ba ma,Abinga nayi naje a madadinta,bayan na kalallameta" "Kai khamriyyah,kefa indai a wajen kutsene ki zama akan gaba bakida sauƙi kwata kwata" "Innnnoooo banganki ba,shine ko kimin sannu da dawowa ko inno" "Saboda nina turaki kije,ko kin faɗamin kika tsallaka kika tafi?" "Haba inno har yanzu baki huce na,nima na huce bareke,kema fah Garinku kika tafi bansani ba ina makaranta,sai dawowa nayi banganki ba,haka na haƙura shine..... " "Naji toh,mai bakin tsiyah karki tona min asiri,yanzu ya hanya,amma karki ƙara irin haka nan gaba. Ku dunga tunawa ba zaman kanku kuke ba" "Naji inno bazan ƙaraba daga wannan,ina kin huce koh?" "Ya zanyi toh in ban huce ba,Allah ya kiyaye gaba" Yanda sabrah ta faɗa tayi,wato tayi wanka tayi kwanciyarta abinta hankalinta kwance,kaman ba itace ta tafi tabar bayada ƙuraba. Washagari da safe su sabrah suna jiranta ta fito su ci abinci,sai ganin ta sukayi ta fito da shirin fita wani waje. Sabrah ce takasa ajiye mamakinta tareda cewa, "Ke kuma ina zakije daga dawowa jiya,ko kinyi wata ƙawane bamu sani ba a can" "Babu wata kawa,Wajen aiki zanje mana,na dade ban gaisa da ogah Sadeeq ba,zanje nafaɗa masa zan koma aiki" Dukkkansu zaro ido sukayi da abinda tace,saidai ita ko a jikinta,saima zama da tayi a gaban abinci tafara ci. Harda duba agogo irin mutum ya makara a wajen aikinnan. Babu wanda yasake cemata ƙala,harta gama cin abinci ta nufi waje. "Inno ƴan uwa saina dawo" Toh kawai sukace,daga nan tafita daga gidan zuwa waje. Motar da aka kawomata a daren jiyan ta kalla tareda jagayata,saida ta tabbatar komai yaji kafin tashiga tayi mata key. Ko yan gidan basu san an kawo motar ba,dan bata faɗamusu yau za'a kawota ba. Jan iska tayi tareda figar motar zuwa cikin garin. Sai kalle kalle take a hanya kaman wanda tayi shekaru bata nan. Dec. Khaleel ne ya kalli Sadeeq tareda cewa. "Ni narasa ma yazanyi,yanda nake tunanin abin yafi gaban haka sosai,a yanda ta faɗa dai tace shine aikinta na ƙarshe" "Amma fah karka manta mahaifiyarka ta nakasa,dole abin da ciwo,duk inda take ma dole za'a kamata,dama ita duk tafisu tantiranci" Zagin deejah Sadeeq ya cigaba dayi,ta inda yake shiga ba ta nan yake fitaba,wanda hakan daidai yake da sukan da zuciyar khaleel ɗin takeyi gameda zagin "Ya isa haka Sadeeq,kaima fah matarka harda ita a cikin laifinnan,meyasa ka daina shogo da itane da ahalinta sai Deejah kaɗai" Mamakine ya kwanta akan fuskarsa sadeeq yana ƙarewa khaleel kallo. "Anya kuwa kaine ɗan uwa,duk wanda yake zagin yarinyar nan fah a bayanka yake,yaukuma kai ke cewa wani ya daina,kuma ma har wani suna naji ka faɗa,wacece haka,ko sunanta kenan?" "Ah.....ah ba da ita bane,kawai sunan watane ya shigo cikin maganar ba komai........" Katsewa yayi da maganar saboda turo ƙofar da khamriyyah tayi zuwa cikin office ɗin,tasha dogon hijabi irinna zamaninnan baƙi har ƙasa,farar fuskarta kewayayyiya ta fito a ciki. Ga kuma baƙin glass ɗin data saka shima. "Salamu Alaikum,ko tattaunawar sirri kuke na jira a waje?" Da mamaki suke kallonta,da alama shi khaleel bai ma fahimci wacece ba,amma kuma ganinta sai ya haifar masa da wata faɗuwar gaba,wacce bai san ta mecece ba. "Khamriyyah mai kike anan wajen kuma yanzu" Yafaɗa cikeda mamakin ganinta a garin,kuma ma a cikim office ɗinsa kuma a gabansa,babu alamar tsoro da kuma fargaba. "Lahh ogah ashe ka ganeni,shine koka ce nazo na zauna,aiki na dawo mana,dama ai ba'a koreni ba,akwai abinda zai kawoni nan har office ɗinnan ba inba Zancen aikiba. Kasan dai kai surukina ne bare kace soyayya ce ta kawoni koh harka koh?" Ta karisa magana tareda zama akan kujerar da take gefen khaleel. Tunda ta shigo wajen take magana harta zauna ta dora jakarta akan cinyarta khaleel yake kallonta. Ita kuwa ko kuladashi batayi ba,saima surutunta da take da sadeeq wanda ya haɗe fuska yana harararta. Marairaicewa tasake yi,kaman mai shirin kuka tace "Habaaa ogah dan allah kayi haƙuri,wlh yanzu ba cutarka na dawo yiba,aiki nazo mucigaba,kuma ma yanzu ai babu abinda baka saniba a kaina,Sannan daga wancan aikin ban ƙara wani ba,dama na gama. Nasan zaka kamani amma har yanzu bakada shaidar nina keyi,dan haka idan muna aiki nasan zaka nemo yanda zaka kamani,nikuma kafin sannan na ɗanyi aiki,zaman gida babu abinda nake ya isheni. Beside nasan bazaka kamani ba baka kama matarka ba koh?" Takaicine da haushi ya ishi sadeeq,ganin yanda ta raina masa hankali a baya,yanzu kuma ta dawo hankalinta kawance tana cewa ta dawo aiki. "Hmmm sha kuruminki,yanxu banine da alhakin kamaki ba,dec. Khaleel ne keda wannan ragamar,kuma har matar tawa za'a haɗa,kinga kuwa bakida mafita" Nuna inda dec. Sadeeq ya nuna tayi,wato inda Khaleel yake zaune,ganin tana kallonsa yasa ya turnuƙe fuska tareda juyawa gefe. "Uhm shima ko shiɗinne inada lokacin,naji ance mission ɗinsa akan mabaraciyah yake ina,sai yafara kamata tukunna kafin yazo ya kamani,kafinnan nidai ku barni na dawo aiki,inkuma ba tsorona bansani ba kuka faraji,bayan kuna shugabannina" Wani kallo khaleel yayimata,jin wai sai yakama mabaraciyah kafin zai kamata,kaiii kuma dai yasan batasan soyayyar dayake mata ba,tunda a yanda yaji jiya ta duro ƙasar. Wani ƙayataccen murmushi yayi tareda cewa. "Ba wanda yake tsoronki v-lady,akan rashin barinki aiki,karkiyi zaton dan ana tsoronkine,batun miƙaki ga hukuma kuma wannan dolene idan lokacin yazo. Ki dawo aiki gobe,sannan karshen tabbatarwa ma kina ƙarƙashin team ɗina nida dec. Saleem,dan haka ki shiryah ,tayamu kama mabaraciyah,idan kikayi hakan wataƙila kisamu rangwamen laifinki" Yar dariyah khamriyyah tayi tareda cewa. "Nagode sir,inshaallah zakaji daɗin aiki dani,kuma zan taimaka muku,badan kuyimin ramgwameba,sai dan idan nadawo aiki,aikina ne,wanann karon alƙawarina da ƙasata na gaskene babu ƙaryah cikinsa" Daga haka tayi musu sallama tafice daga office ɗin. Tana fita sadeeq ya zarowa khaleel ido tareda cewa. "Kasan mai kayi kuwa? Dawo da ita aiki fah kayi,bayan kasan maita aikata,ma kake tunani" "Hmmm karka damu ɗan uwa,babu abinda zatayi,tariga tasan munsan komai akanta,dan haka bazatayi wani gigin yin komai ba,kuma zata taimaka sosai wajen kama mabaraciyah,saboda ance mugu shiyasan makwancin mugu" "Eh kuma wannan hakane,Allah ya taimakemu toh" Washagari kuwa kaman yanda sukayi da dec. Khaleel,ba kunya Khamriyyah ta dawo aikin ta na bincike. Kusan sati guda ta ɗauka bata ga su dec. Sadeeq,kasancewar tana ta ƙoƙarin gyara abubuwan data tafi ta bari,gashi tasan wani lokacin da gangan Dec. Khaleel yake aikowa a kawomata takaddu,idna taga hakan murmushi kawai takeyi. Har dare wani lokacin take kaiwa tana aiki a ɗakinta. Bironta ne yauma da safe tana cike wasu takaddu kafin taje office,ɗakin su khairiyyah tashiga domin dubawa,dan tasan bazasu rasa takardu ba. Drawer ta farko ta jawo bata ganiba,tasake jawo ta biyu babu,har zata mayar kuma sai taga wata takarda. Ƴar dariyah tayi tareda buɗewa tana cewa. "Hmm yanxu haka khairiyyah ce tayi kasuwa,barinaga kalaman soyayyah,tunda mu babu wanda ya taba bamu sai....." Cak ta tsayah da maganar ganin abinda takardar ta ƙunsa. Maganganu aka caccakawa sabrah akan rashin fitowa duniya ta faɗi ita wacece. "Kan buhun ubancan,mai akayi akai madeena,yarinyar nan tasanni kuwa,ba ƴar gidan sarkim katsina ba,inma ƴar sarkin duniyace zata gane shayi ruwane. Sabrahhhhh khairiiiiiii inakuke kuzo nan?" Da gudu suka shigo cikin ɗakin dan ganin mai yake faruwa. Turuss sukayi ganin ta dunƙule hannunta tareda cize baki,jikinta yana vibrating,ta mutsitstsike paper a hannunta. "Kinsan me khamriyyah bawai......." "Yaushene ɗaurin auren?" "Yaune za'a ɗaura auren idan taso daga masallacin juma'a" "Meyasa toh banga kunje kun nuna kanku a gaban kowa a cikin gidanba,mai kuke a zaune a cikin gida,lokacin daya kamata ace kunacan kuna maida martani. Da bangani ba shikenan haka wannan cin mutuncin zai tafi a banza.?" "Am khamriyyah ......" "Shshshsh karkuce komai,ku saka kayanku mutafi yanxu nan,wlh sai anje,idan kuman bazakuje ba zanje ni kaɗai. Badan kina kunyar ubaba kika ƙi nuna kanki,batun in kinason mijinki kuma bai tasoba,dole saikin nuna mata ke macece,kuma indai zata shigo gidanki dole tazo a ƙasanki ba a shugabarki ba. Shiryawa sukayi cikin kaya iri ɗayah dukkansu su ukun,farida tana kallonsu ,taso binsu amma babu dama,saboda kar a gano tana tareda su a cibiyar bincike. Fatan nasara tayi musu lokacin da suka shiga motar khamriyyan takece raini sai gidan masarautar katsinan. ................see you next......... Taku _sadi-sakhna_ Ƴar mutan jama'are. *MABARACIYAH* _haƙƙin mallaka_ _*sadi-sakhna*_ (Yar mutan Jama'are) 51••52 Jan motar tayi bayan sun gama shiga sai gidan su madeena. A lokacin ƙarfe tarane na safe,tundaga bakin kofar mutane maƙil anata shirye shirye,dan madeena itace ƴa tabiyu daza'ayi aurenta a fadar. A bakin kofa sukayi parcking motar su,dan babu wajen shiga koda sunyi niyyah. Tafiyah suke a tare,ga kayansu ma masu uban daraja da khamriyyah tazo musu dashi,takalman da gyalen ma iri ɗayah,sai gwalagwalai da suka yi ado dasu,(ayar tambaya,a ina khamriyah ta samo kuɗi haka)kana ganin shigar kasan da gayyah sukayi. A hankali suke takawa saboda cikin sabrah daya tsufah har yah ɗago riga. Wata mai aikice zata wuce khamriyyah tayi saurin tareta. "Ke sashen hajiya Saratu muke nema" Kallonsu salaha tayi daga sama har ƙasa,dan ita a ranta tayi zaton saƙƙowarsu kenan a jirgi" Nuna musu wajen tayi,tai gaba abinta da kuloli,wanda hajiya saratu tace a kaiwa su khaleel da suke sashen Yarima jalal. Bin yatsanta sukayi da kallo zuwa sashen data nuna musun. Aikuwa khamriyyah ce a gaba ta zasu zuwa wajen.. Shiga sukayi suna rarraba ido,babu wanda suka kula,suma masu binsu da idon basu kulasu ba. Amal ce ta fito daga ɗakin da madeena take tana ta magana a wayah. Katsewa tayi tareda kallon su khmariyyah tace. "Ku ƙawayen anty madeena ne,ku shigo nan tana ciki" Binta sukayi a bayah,dan dama abinda khamriyyah takeso kenan. Ƙarewa wanda suka ɗakin sukayi da kallo,wato kawayen madeenan. Ɗaga ido khamriyyah tayi tareda mintsina baki tace. "Ina amaryar ne,kaman yanda ta bada takadda kan cewa uwargidan Sadeeq tazo ta bugi ƙirji tace itace matar sa wacce yafiso,tofah dama ance rana bata ƙaryah saidai uwar ɗiyah taji kunya. Ka sabrah tazo tabbatar miki kan cewar ba kunyar uban kowa takeba wajen fitowa duniyah ta amsa sunan matarsa,kuma rashin cika magana sai ƙaramin mutum,dan haka gata a gabank8 bataji tsoron fitowa ba tazo har gidan naki uban" Dukkan ƙawayen amaryar harda amaryar ma tsayawa sukayi baki sake suna kallon khamriyyah wacce take zazzga masifah kaman bakinta zai cire. Tun anayin hayaniyar a ɗaki har manya suka fara zuwa neman ko lafiyah. Kowa idan yaxo yaji matar sadeeq ce tazo tabbatarwa madeena magana sai ya juya yakai gaba. Kafin awa ɗayah da zuwannnasu har kaf gidan ya ɗauka da zuwan su khamriyyan. Har sannan madeena kuwa kanta ya kulle,tarasama bakin maganar mai zatace da lamarin. Hakiya Daada yayar hajiya saratu ce taƙirasu falon hajiya saratun domin jin mai yake faruwa. Daidai lokacin shima sadeeq ya shigo falon shida su ahmad,khaleel da kuma saleem. Sai sauran wasu abokan. Hakuri aka bawa wasu suka fita,abinka da gidan sarauta dama yayah. "Ke wannan da kike magana,kince zuwa kikayi tabbatarwa amaryah cewa Sadeeq yafi son Uwargida,menene ma'anar wanann magana,kinfi kowa sanin nan ba gidan ƙananan mutane bane inda kuka saba yin haka nan gidan sarsutane. In wani abu madeena tayi muku ma bai kamata kuzo har gida wajenta ba,saboda matsayin da ubanta yakeda shi. Batun matsayi kuma wannan kafin a ɗaura aurene,ana ɗaurawa dole itace zata jagoranci komai,sha'anin jagoranci ai sai wanda ya gada. Zakuce tazagi ubaku,shin kunada ubanne ƙaryah tayi,duk wajennan kowa shuru yayi,amma babu wanda zaice ga ubanta a garinnan sanda sadeeq ya aureta. Inba shiririta irinta yaroba,shima yanzu gashinnan abin ya dameshi yazo biɗar ƴar asali" Har khamriyyah ta buɗi baki zatayi magana inno tashigo wajen,da lullubin gyalen babba,kana ganinta kasan sauri tayi kafin ta iso. "Kiyi haƙuri hajiya kibar wannan tone tonen,abin yarane shiyasa suka tashi hankalinsu,amma hakan bazata sake faruwa ba,batun mahaifi kuma ance kam shine yake ado,amma fah bashine yake numa kimaba,ko ɗan sarki ko talaka,mai uba da marar uba,hakan baya shafar duka gaba ta rayuwarka,ita kanta kima kai kake siyawa kanka,haka kyautatawa da kuma samun soyayyar mutane. Duk da ƴa ta batada gata irinnaku,haka ɗanku yaji ya gani yace ita yake so,bamu sayeshi da boka ko malam ba Allah ne ya dubi maraicinta yabata zuciyar mijinta,sannan ko kusa bana bakincikin ya auri ƴar uwarsa Fatana shine Allah yabasu zaman lafiya. Abinda yafaru anan kuma dan Allah a tufeshi,karya shafi auren daza'ayi" Wata harara hajiya Daada ta zabgawa inno tareda cewa. "Aikin banza wace kima za'a samu a wajen ƴaƴan gidan marayu,ko talaka bakowane zai auresu ba bare jinin sarauta. Ƴaƴan shegu na titine fah,wanda matan banza sukeyin cikinsu su zubar,ku kuma akai muku su a baku kuɗi ku rainesu. Ke kanki nasan bazakiso ɗan ki ya auri wannan kazamar ba ,amma haka kuka laƙanawa ɗanmu domin zalunci,wannan karyar wann............." Fasss kakejin ƙarar mari inno ta ɗauke mata fuska cikin zuciyah. "Kada ki kuskura kisake ƙiramin ƴaƴa ƙazamai,saboda ban shayar dasu da haram ba ban ciyarda su da haram ba,da taribiyya da kuma hanyar daidai na rainesu. Babu ruwana da iyayensu,da kuma abinda sukayi suka haifesu,walau su musulmai ne ko kuma akasin haka,abinda nasani shine tuna ranar 7 ga watan mayu na shekarar 1999 na ɗora idanuwana akansu suna tsumman goyo. A ranar nayi register su a matsayin ƴaƴana ba riƙon gwamnati ba,sannan da gumina na rainesu bada ƙwandalar gwamnatiba,ba madarar kanti na basu ba,madarar jikina suka sha suka rayu. Ina musu son kwatankwacin yamda nake yiwa ɗan da na haifa,dan haka karki ƙara ƙazantamin yara a gaban idona,babu uwar dazata juri haka" Hannun su khamriyyah taja da niyyar fita dasu daga wajen,amma sabrah ta fizge hannunta. Hanyar inda sadeeq yake tsaye taje ta zuba gwiwoyinta,kana ta kama ƙafafunsa tareda sakin wani zurfaffan kuka mai dulmiyar da zuciyar duk wanda ya saurara cikin duniyar tausayi. "Duk da cewar haramunne kuma bai daceba mace ta nemi saki a hannun mijinta,saidai babu yanda zanyi ya zamemin dole saina tambaya Sadeeq,ka sawwaƙemin ka auri ƴar uwarka,niba sa'arka bace a rayuwa yanda ta faɗa,ko talaka saina ƙasa ne zai zauna dani,hakan ma zan rayu cikin tsoron ranar dazai min gori. Ka taimakeni ya fitar dani daga wannan ruɗi daga nan,abinda yake cikina ma kabarmin shi zan raineshi ni kaɗai,ta haka ne zai rayu cikin salama. Karka damu mun ƙware a rainar wanda bashida mai tallafarsa." Kuka take rusawa wiwiwi wanda hakan yasa khairiyyah durƙusawa itama a wajen tareda juyota zuwa gareta. Shikuwa dama sadeeq tunda yazo wajen yaji abinda ake faɗa ya sandare a wajen bai sake motsiba na kirki. "Rabinah,meyasa kike wannan kukanne haka,kullum yau daban na gobe daban,kisakawa ranki salama kodan lafiyarki,nikam kinsani bazan iya jure rashinki ba koh,ke kaɗaice wacce na haɗa alaƙa da ita a duniyarnan. "Inji wa ɗin,waye ya faɗamiki haka?" Dukkansu kallon hajiya saratu sukayi wacce take tsaye idonta yana zubar da ƙwallah tana ganin abinda yake faruwa. Takawa take a hankali har inda su khairiyyah suke zaune,kama hannayensu tayi na dama tareda dubawa Abinda take nemane Allah ya nuna mata a tsakiyar hannunsu. Tawadace iri ɗayah,saidai ta khariyyah a ɗan saman ta sabriyyah. "Hmmmm dama naji a jikina sune ,zoki gani daaaaadddda,wlh sune sune fahhhh,tun ɗazu nina kulada yanda suke kama da Innar mai martaba,dan dama ita suka iya fitik lokacin da aka haifesu,amma ke baki kulaba sai masifah kike marar amfani" Hannun su sabrah takama ta matse a kirjin ta sai surutai takeyi,wanda ba'a rabasu dana farinciki. Ba iya su sabrah ba,kowa ma nawajen kallon mamaki yake mata. Tashi tayi da sauri ta nufi turakar mai martaba da take sashenta. da saurinta sai gata ta dawo da hoton Halimatussa'adiyyah,wato mahaifiyar mai martaba,wanda ta ɗauka irin marar kalar nan na da. Miƙawa mutanen wajen tayi kowa yana gani,wanda suka santa sai a sannan suke tunowa kumafah hakane,saidai ance wanda ya mutu dole sai an matashi. Banbancinta dasu khairiyyah a hoton ɗayane. Ta ɗan fisu manyanta,kuma kanaganinta bazaka ga wayewa irintasu ba. Hajiya saratuce ta ƙara dacewa. "Kai abdul je kace ana naman mai martaba a cikin gida saboda wani muhimmin Al'amari" Har sannan babu wanda yasake cewa komai,har itama hajiya saratun,kowa yana jiran yaga shigowar mai martaba a ga yanda zayyi. Shida fadawa guda biyu suka shigo,yasha sabuwar alkyabba na ɗaurin auren ƴar sa daza'ayi yanxu. "Hajiya ƙarama lafiyah kika ƙirani,ga kuma mutane a gida haka an taru" Da hannunta ta nuna masa su sabrah batareda tace komai ba. Ɗan zare ido yayi tareda sakin baki, "Daga adamawa suke?,ƴaƴan waye a cikin su baffah modibbo?" "Ahah ko ɗayah,acikin ƴayan da aka taba haifah a gidannnan waye yayi kama da marigayiya inna?" "Hmm ke kuma menene na tuna wannan labarin,ƴaƴa biyu Allah ya azurtani dasu masu kaman innata a lokaci guda....." "Suma wannan ƴan biyune,sun rayune a gidan marayu dake garin daura,sannan an tsincesune a hannun wata mata zata sakasu a kogi,ranar da tayi daidai da rasa ƴaƴana danayi,wanda suke da kwana biyu a duniya....." Sakin kuka tayi tareda durƙusawa a ƙasa,dama tana maganar muryarta tana rawa,kana gani kasan abin yana cin zuciyarta matuƙa. Kama kafaɗunta mai martaba yayi tareda ɗagota. "Addu'a zakiyi da nuna mafarinciki da Allah ya nuna miki su,ba kuka irin haka ba" Ɗaga kai tayi alamar ta fahimta,kafin ta kalli inno wanda itama idonta yake kanta. Takawa take a hankali har inda take tsaye,hannyenta ta ɗaga tareda cewa. "Nagode nagode,duk da nasan dan kina sonsu dakuma kyakykyawar zuciya yasa kika rainesu,amma duk da haka na godemiki yake wannan jajirtacciyar uwa. Duk da cewar na gano su sabrah sune ƴaƴana dana rasa a shekara ashirin da huɗu bayah,hakan bashine zaisa na rabaki dasuba,ƴayanki ne halak malak,Alhamdulillah naji daɗi,zuciyata ta samu nutsuwa dana tabbatar cewar suna cikin koshin lafiyah kuma cikin ingantacciyar rayuwa" Kama hannunta inno tayi tareda cewa. "Nice da farinciki da Allah yabani ikon nayi tozali da iyayensu,masu daraja da kuma mutunci,ba irin wanda mutane suke tunani ba. Nagode da kyautar da kikamin,amma kuma bazan iya ɗauke ƴayanki na tafi dasuba,dole kina buƙatar fahimtarsu,dan haka zasu zauna a wajenki na ɗan lokaci kafin kowa idan Allah yayi mata miji ta tafi ɗakinta. Wani daɗine ya jiyarci hajiya saratu da taji batun da tayi. Tun kafin tayi magana khariyyah tace. "Inno me naji kina cewa,ai tafiya zakiyi mu zauna a gidannan,ahah nikam bazan zauna a nan ba,ƙafarki ƙafata" Harararta inno tayi,amma tayi ƙiƙam da kai alamar babu inda zataje. "Dukkanku ku dawo nan da zama,akwai sashen Hajiya Marigayiyah,wato mahaifiyar Khaleel,saiku zauna a wajen,tunda ba namiji a inda kuken zaman ma hatsarine kuna mata" Ɗaga kai inno tayi da alama taji mai yace,a ranta taso ta koma garinsu idan sun dawo nan,saidai kuma wacece ita dazata ce bataso,koba komai gata ga ƴaƴanta ma. "Shikenan ranka ya daɗe mungode sosai,Allah ya ƙara martaba" "Ameen ameen,ke kuma madeena gwanda dakikayi wannan maganar,da yanzu abin ya ƙazanta yanda ba'aso,matarsa ta farko yayarkice ta jini uwa ɗaya uba ɗaya,dayanzu ba a saniba sai yayi rayuwar aure da yaya da ƙanwa" "Nifah baba dama bani natura wata wasiƙa ba,bansan ma mai suke magana akai ba" "Toh in bake bace waye ya tura,ga wasiƙar ƙarya zamuyi miki" Khamriyyah ta faɗa tana miƙa wasiƙar wajenta. Karba tayi tareda warewa ta karanta. "Amal,wannann rubutun amal ne ba nawa ba,ita ta tura baniba" Kowa juyawa yayi ya kalleta,yayinda ta sunkuyar da kai tana murza hannu. Dungureta hajiya saratu tayi dama tana kusanta. "Ja'irar ƴah,da badan wannan sabon lamarin ya fitoba da shikenan kin jawo husuma da tashin hankali koh" Tsawa mai martaba ya daka mata tareda cewa. "Ai wannan bai ishetaba,gobema idan aka barta zata sake,dolene ta fuskanci hukunci" Baba nima wlh vanice nayi haka kawai ba,deejah ce tace na rubuta lokacin data saceni,kuma tace inna faɗawa wani itace tayimin wannan dukan saita yankani,wai kashe hajiyan su anty khadija tazoyi babu ruwanta da kowa. Da nace meyasa zata sa a rubuta wannan takardar kuma sai tace wai ina ruwana" "Wacece deejah kuma?,kowa shuru yayi wanda suka santa kuma suka fara kame kame" "Uhm Aiki tayi a gidannan na wata huɗu a sashena,ranar da aka sace hajiya har yau babu wanda yasake ganinta" Amal ta faɗa bakinta yana rawa dan tsoro. "Me masu tsaron gidannan suke har tazo tayi hakan,waye yake taimaka mata a gidan" "Eh tareda ake ganinsu da yaron shamaki mai kulada dawakan Ummah,kuma data tafi bayan ta gama shima ba'a sake ganinsa ba,harda drivern ma" Dunƙule hannu mai martaba yayi tareda ƙiran dogarawa sukayi waje,domin neman ƙarin bayani. Har yazo fita idonsa yakai kan khaleel wanda yayi saurin kawar da kai. "Wannan fah,kaman yayan gidannan,wanene shi" "Yah khaleel ne wanda yake wajen su hajiya Deejah,bai daɗe da dawowa daga ƙasar china ba" " Khaleel kuma,ba ance sun mutu ba shida junaid. Mai yake faruwane a gidannan a rufe tsawon shekaru,sannan ...... Wannan ba khaleel bane,kama yakemin da ƙaramin junaid,kudai faɗi gaskiya,kuma kunsan gaskiya" "Eh Abbah nine Junaid,amma nasake suna da khaleel nake amfani bayan abinda ya faru. Kuma inaso na cigaba a matsayin khaleel har sanda numfashina zai ƙare" Kallon mai martaba yake lokacin daya faɗi hakan,kana kallon tsagwaron bakin ciki a cikin idanuwannasa.. Hajiya deejah ce tashigo itada meena,dan yanzu labari yaje mata wai an soke ɗaurin auren Sadeeq da Madeena. "Me nakejine a gari marar daɗi,mayake faruwa?" Idonta ta ɗorah kan su inno da suke tsaye suna kallon abinda yake faruwa tsakanin mai martaba da kuma ɗannasa junaid. "Kukuma mai kuke a gidannan,ko kune kuka wargaxa auren kai?" "Hadeeza ba sune suka wargaje aureba,nina dakatar dashi,saboda matarsa ta farko ɗaya daga ƴan biyun da aka rasane shekarun baya,wato ƴayan Hajiya saratu. Kinga babu auren daza'a ɗaura da madeena kenan. Sannan ba wannan bama,ya akayi junaid yazama khaleel,kincemin kincemin dukka sun mutu,mayafaru iyeee?" "Habaa Yaya,yazaka dawo da abinda ya wuce,komai yafarune saboda laifinku kaida matarka Hajiya fulani,ta kallameka kazama sai abunda tace,wato hajiya Fulani. Sannan niba nice nace ya rayu a matsayin khaleel ba,shine yace bayason zamansa a junaid sai a khaleel.Nikuma idan nace maka khaleel yana raye dole zata sani ,gashi shima hatsarine tasan yana raye,hatta kusancinsa da inda yake hatsarine,shiyasa nida mijina muka raineshi shida Sadeeq a tare,a ƙasar china,da muka tashi dawowa kuma sai muka barshi a can saboda tsaro. Batareda kowa yasani ba ya cigaba da rayuwa,khaleel shiya rasu bayan sun sha mintin da junaid ya ɗaukomusu na tsafinta,shine kaɗai ya rayu,shima sai bayan shekara biyu yana jinya a cam kafin ya tashi. Da har mun fidda rai da rayuwarsa,daya tashi yaji ɗan uwansa dasuka shaƙu wato khaleel ya rasu sai yace da sunansa zai cigaba da amfani,anan muka sanja masa suna bisa shari'a,muka barshi a can yayi karatun bincike a can" "Toh amma meyasa kika boyemin tsawon wannan lokacin" "Dolene yasa nayi hakan,an sace yara jarirai a tsumman goyo,Hajiya fulani Ameena,matarka ta farko ta rasu,kowa yasan shanye jininta akayi,amma ba a yi komai ba. Yarannan sunsha guba a ɗakinta,wani yaron ha ilau yafaɗa doguwar suma ta tsawon shekaru mai akayi akai,bayan doguwar jinya,ɗaya ya mutu ɗaya ya rayu,sai na faɗamaka,tabishi ta kasheshi shima. Duk da ɗantane amma ransa take nema saboda buƙatar duniyarta,yanzu ma da badan alkadarinta ya karye ba bazan faɗamaka ba. Ni wannan deejah da akace tayi mata aika aika tayimin daidai,duk da hakan bai kamata a ɗau doka a hannun ba" Taku _sadi-sakhna_ Ƴar mutan jama'are. *MABARACIYAH* _haƙƙin mallaka_ _*sadi-sakhna*_ (Yar mutan Jama'are) 53••54 Babban falone na mai martaba an cika shi maƙil da mutane,kowa ka ganshi dangine ko kuma shaƙiƙin amini na masarautar,kaman irinsu inno da khamriyyah da saleem,wanda sun haɗu da wajen ta wani dalili. Dukkan dangi dana kusa harma dana nesa an hallara a wajen domin jin mai mai martaba zai sanar dasu. Hajiya fulanice kawai bata wajen,ita tana caliponia wajen magani.Saidai wasu ƴan uwanta kawai. Kowa a wajen a carpet yake zaune,iya babban gayyar ne kawai a hakimce akan kujera. Farawa yayi da addu'a,bayan an gama sannan yafara da cewa. "Toh wasu sunsan abinda ya taramu a wajennan,wasu kuma basu saniba,saidai kuma suna mamakin yanda jiya har an hallara za'a ɗaura auren ƴa ta da kuma ɗan kanwata hajiya deejah,amma kuma aka fasa saboda wani dalili. Tohh babban dalilin shine,bayyanar ƴaƴan yan biyu mata wanda suka bata shekara kusan ashirin da huɗu da suka wuce,yau Allah da ƙudurinsa da kuma hikimarsa ya bayyana mana su lokacin da bama tsammanin hakan. Sannan wani abin mamakin ashe ɗaya daga cikinsu itace matar shi wanda madeen zata aura,kunga kuwa a musulunce aure tsakanin su babu shi a addinance. Sannan dalili na biyu kuma dana taraku anan wajen shine,inaso dani daku da kowa aji labarin mai yafaru bayan barin su gida da kuma yanda sukayi rayuwa. Dan haka muna sauraranku" Kowa ido ya zubawa su inno,wanda suke gefe guda kusada mai martaba ,domin maƙasudin taron akansune. Gyaran muryah inno tayi,cikin nutsuwa ta zayyano masu duk abinda yafaru,daga tsintar su khairiyyah da tayi,da irin ƙalubalen datayi harma da abinda suka aikata bayan cin mutuncin da akayi musu na fansa akan manyan gari. (Labarin da sabriyyah da bawa Sadeeq a cikin kundin tarihinta). Wajenne ya kaure da hayaniya,wasu na tausayinsu khairi,wasu na cikin mamakin abinda ya faru,yayinda wasu ke ganin ƙaryahne mutanen bazasu yi haka ba. Gyaran murya mai martaba yayi,wanda hakan yasa kowa yayi shuru. "Toh duk munji abinda ya faru,haƙiƙa abinda aka yi muku a garin daura abune da kowa akayi masa abinda zayyi kenan idan ya samu dama. Saidai kuma da zai zamo mutane suna ɗaukar doka a hannunsu to dokar bazatayi amfaniba kenan. Za'ayi bincike,idan ya zamto gaskiya kuka faɗa,nida kaina zan tsayah muku a kotu,duk da hakan ba ƙaramin abu bane,dan su kansu wanda kuka aikatawa haka manyan mutanene. Zaku zauna a cikin gidannan a matsayin kowane ɗa a cikin gidannan,ke kuma Sabriyyah zaki koma gidan mijinki ki zauna kafin muga yanda Allah yayi,idan wani abune ya taso duk zakiji mai ake ciki. Ku kuma sauran za'a tura mota ta ɗebo muku kayanku zuwa nan gida. Toh idan da mai tambaya kowani abu ya faɗa za'a rufe waje da addu'a,mai buƙatar ganinsu ko magana dasu a matsayin ƴan uwanku saikuje sashensu,nizan tafi fada ana jirana" Taronne ya watse daga haka,kowa na faɗin albarkacin bakinsa. Hajiya saratuce taza inno zuwa sashenta,dan ko barinsu su koma gida taƙiyi,a cewarta basai sunje ɗaukowa kayan bama,za'a ɗakkomusu,idan an gama shirya musu inda zasu zauna sai suje yiwa kaƙwantansu bankwana. Abinci aka shirya musu nagani na faɗa,duk wanda yaga hajiya saratu a lokacin yasan tana cikin farinciki sosai da sosai. Mutanenta kuwa da abokan arziƙi kowa sai taya murna yakeyi da bayyanar ƴaƴanta. Su khairiyyah sunga gata kam sosai a wajen danginsu da basu sansu ba sai yanxu. Wajen misalin ƙarfe takwas na dare khaleel ya shigo gida daga wajen aiki,dan yanxu wani lokacin sai daren yake dawowa,gabaɗaya abubuwa sun masa zafi,ga kewar masoyiyarsa,ga fargabar kamata dayake koda ya ganta,sannan kuma aibantata da mutane sukeyi ko yaushe acikim kunnuwansa,tun yana ƙoƙarin boyewa har sadeeq yafara gane akwai abinda yake faruwa tsakaninsa da ita. Shikaɗaine yasan yanda mutane suke ɗaukarta ba haka takeba,saidai kuma taya zai fahimtar dasu hakan,bayan ko abinda yake tsakanin su babu wanda yasani,dagashi sai saleem ne kaɗai suka sani. Gashi yanemeta yarasa a wannan duniyar,ko numberta yasamu,yasan jin muryarta zao rage masa damuwa,tayi masa abubuwan da koda baya sonta bazai manta da itaba. Itace mace ta farko bayan hajiya deejah da tasan lalurarsa,kuma ta tsaya a wajensa lokacin dayake bukatar taimakonsa,karshe ta ajiye muradinta ta nema masa lafiyar da tun yana da ƙananan shekaru ya rasata,saidai ya gani a wajen wasu,amma yanzu shine yake rayuwa ba fargabar wani ciwo zai shigo rayuwarsa a kowanne irin lokacin. Maizaice da wannan halitta ta ubangiji,wacce ransa yake matuƙar muradin ya rayu da ita,ta gujeshi da kunyar bazata iyah zama a matsayin surukar mahaifiyarsa,bayan abinda tayi mata. Batasan cewar shi ko kasheshi takeyi tana dawomar da ransa baya tunanin ciwon sonta zai bar ruhinsa ya samu salama..... Hajiyah deejah ce ta ƙatseshi da tunanin daya zame masa ci kana da kuma sha a kullum. "Ibrahim khaleel" Saurin juyowa yayi da sauri,dan duk sanda tayi masa wannan ƙiran toh fa abin yanada muhimmanci. "Tun ɗazu nake ta kiranka baka jini ba sam,mai yake damunka ne haka,gashi kaƙi sanar da kowa abinda yake faruwa. Dama mahaifinka ne yake faɗimun cewar kaje yana son yin magana dakai yanzu" "Toh ummah,barina cire kayan aiki tukunna" Duk da ba uniform yake sawa kamar su Sadeeq ba,amma kuma akwai yanayin shigar dayake wanda ita ta aikice kawai. Shiryawa yayi lokacin ana ƙiran isha,dan haka kawai daya tafi masallaci tacan ya wuce gidannasu. Ko abinci bai tsaya ci ba,dan dama bashida ɗanɗanon cin abincin. Dayazo shiga sashen mai martaban,dogarawa ne suka tsayar dashi,wanda da alama basuda labarin shine yarima junaid ɗin,(dan duk gidan sarautar kowa cewa aka cemusu yarima junaid ya dawo,wajen aikinsa kuwa da kuma wanda suka sanshi a waje,kowa da Khaleel ya sanshi. Tsayawa yayi yana kallonsa,shifa abinda baya cikin ra'ayinsa kenan,wato sha'anin sarauta,abune da tun yana gidanma baya so,inaga kuma daya tashi badashi ba,bai saba ba kwata kwata,bashshi a rayuwarsa ta freedom da privacy. Har ya buɗe baki zayyi magana,saiga waziri ya fito daga wajen sarkin. Alhaji Musa Malam,yanada yawan yan shekaru,dan ko a fuska ma yafi sarkin ɗan manyanta.Shine yayan Mahaifiyar ainihin Khaleel ɗin daya rasu,wato Hajiya fulani Ameena. "Ahh junaidu kaine,mukan da aka saba koba shigo nan ba aikazo mu gaisa koh" "Eh dama kuma bana kasar ai,Abbah yana cikine?" Yafaɗa a hankali cikin ladabi. "Eh yana ciki ka shiga,naga kuwa kaman dama kai yake jira,dan da yanzu ya shiga cikin gida" Cikin sanyi da nutsuwa Khaleel yasaka kansa cikin turakar mai martabar,bakinsa ɗauke da sallama. "Assalamu alaikum" "Wa'alaikassalam Junaidu" "Abbah khaleel ne fah" Yafaɗa cikin dan ɗaure fuska. "Kai nikarka min sakarcin dakakewa uwar taka,yaka matso tanan kazauna,akwai abinda zamu tattauna,duk sunan daka ɗauka daga cikinsu ma ai ba bu damuwa,dukkansu jinina ne,kuma ko kaine kaɗai a raye ko kuma shine,dukka ina ganin kune a jiki guda ɗaya,koyaushe saina tuna lokacin dakuke shigowa gaisheni nan wajen ku biyu a kowacce safiyah" Daga yanda yayi maganar kasan abin yana sosa masa zuciya sosai,da alama yayi kewar ƴayannasa. Shima khaleel ɗin lokacinne yadawo masa tamkar sabo a cikin kansa,yanda mahaifinnassu yake matuƙar nuna musu soyayya. Karisawa wajen ubannsa yayi tareda rungumeshi a jikinsa,dan idan yatsaya kwatanta jin kewar mahaifinnsa bazai yiyu ba. "Abbahhhh kayi haƙuri da rashin sanar dakai ina raye,akwai dalilin hakanne shiyasa,ammafa nayi kewarka sosai,sannan nayi kukan rashin ɗan uwana" Dafa bayansa yayi tareda yin murshi irinna manya kafin yace. "Nima nayi kewar rashinku kusada ni,a cikin wannan satin gani nake kaman nafi kowa farinciki,ƴaƴana har guda uku sun bayyana gareni. Inaso ka dawo gida da zama kaima,ga nan sashenka nasa a gyaramaka,yakamata ka dawo gida da zama,ka fara sanin sha'anin mulki,domin ni lokaci gaba yake min,dama kuma sanda na karbi mulki nafara girma,inaga kuma yanzu. Sannan ga mata kai har yanzu naga babu" Shuru khaleel yayi yanajin abinda mahaifinsa yake faɗa,a tsarin dawowa gidan ya cigaba da rayuwa kaman da, kwata kwata baya cikin tsarinsa,saidai kuma bazai iya cewa mahaifinnsa ahah ba. Sannan idan yace bazai karbi mulkinba to wa za'a baiwa,mubarak bai daɗe da tasowa daga doguwar suma ba,yanayin magana ma har yanzu bai gama ganeta ba,sannan iya kacinsa secondry kawai abinda yafaru dashi,kwakwalwarsa irinta wancan shekarunce har yanzu. Shiri turashi saudiyyah akema yayi karun addini ko hakan zai ƙara taimaka masa,saikuma jalal,wanda yanzune aka samu yafara nutsuwa ma tukunna. Shikuma shiyafi cancanta ya karba,amma kuma bayada ra'ayin hakan,saidai babu yadda zayyi dole ya dawo gidan kaman yanda mai martaba yace,ko yaƙi ko yaso shine babba yanzu a gidan. "Shikenan Abbah zan dawo gida da zama,amma ba yanzu ba tukunna akwai case ɗin danake running,banason haɗashi da sha'anin gidannan tukunna,inaso a barni idan nagama tukunna" "Shikennan babu matsala,kanada damar dazaka gama tunani akai,bari ninashiga cikin gida,amma kafinnan kaje ka gaida Hajiya saratu tukunna,dan kunsan a wajenta kuke kafin wannan abin ya auku. Ga gaida mahaifinnaku,(mahaifin Sadeeq),yaki zuwa mu gaisa wato,nadaɗe rabona dashi" "To shikenan zaiji Abbah,naji ummah tana cewa wai bayada lokaci,sha'anin zabe ya matso" "To shikenan Allah ya taimaka,kazo gobe da yamma idan kanada lokaci,domin zan nunaka gasu manyan gari" "Amma abbah da an bari tukunna,a yanayin aikinmu ba'a fiye son bayyana Ahali ba sosai" "Ohh to na fahimta" Daga nan Khaleel yafito daga sashen mahaifinnasa ya nufi cikin gidan. Tafiya yake yana kallon wajajen dayafi zuwa lokacin yana matsayin Eemran,wani wajen yayi murmushi,wani wajen kuma saidai ya jijjga kai,musamman idan ya tuna rayuwar dasukayi da Deejah,idan wani ne yabashi labari bazai gasgata shiba. Sabuwar kewartace ta dawo masa cikin kansa,yanda take abubuwanta sakk yanda yake muradin mahaɗin rayuwarsa ta kasance,mace mai juriyah jajircewa da kuma tsayawa akan ra'ayinta. Wata mace yagano a zaune akan dutsen da suke zama shida Deejah idan yanason yin magana da ita. A yanda tayi zaman da kuma jikinta sak irinna deejah. Gabansane ya buga giff,sannan haka kawai jikinsa ya bashi kaman itace. A hankali yake takawa zuwa wajen har isa tabb da inda take. Khamriyyah ce a zaune da waya a hannunta tana game ɗin bubble,sai fash fash suke cewa. Jin kaman da mutum a bayan tane yasa ta saurin juyowa tareda zaburah. "Ohhh Subahanallah yallabai ashe kaine,wani abune yataso na case ɗin muke aiki?" "Uhm uhm ahah,kawai yanda kikayi zamanne na ɗauka ko wanda nake nemane a zaune,am sorry barina shiga ciki wajen Umman su Madeena" Daga haka cikin diri dirice da alamar rashin cikar buri ya bar wajen. Kallonsa khamriyyah take,da tunanin mai yake damunsa,amma kuma babu wanda zai bata amsar hakan,kallon wajen da take xaune tayi,tareda sake kallon inda yabi. "Wa kuma yake nema anan wajen,hmm you are in my target. Danasha cikin salaha kan abinda tasani gameda deejah,tace anan wajen suke zama itada eemran suna hira,yanzu kuma Ogah khaleel yazo yana neman wata a wajen,yayi zaton nice ita ,mai hakan yake nufi,shida ance bai daɗe da dawowa daga ƙasar ba,taya yasan da wata anan wajen yazo nemanta?" Kaɗa kanta tayi itama ta bar wajen,ganin babu wanda zai bata amsa koda ta tambaya. Tun dawowarsu fada su khamriyyah basu taba fitaba,saboda yawan mutane dasuke zuwa kallon su sabriyyah,sannan dakuma zagawa dasu gurin yan uwa. Dan jiyama suka dawo daga gombe gidan su Hajiya saratu. Khamriyyah ce a gaban tangamemen madubin ɗakinnasu tana shiryawa cikin kayan haka normal,kayan aikinnata kuma tasakasu a cikin jaka saboda gudun abin magana a gidan. Tare suka gama shiryawa itada khairiyyah wacce itama zata wajen nata aikin. Sabrah kuwa tana zaune da tulelen cikinta tana kallon,da yau zata koma ɗakinta,Hajiya saratuce ta dage akan a barta ta zauna a gida,don koda tana gidanma dole zata dawo gidan,tunda cikin farine. Bori kaɗai sadeeq bai tayarba dayaji zancen hakan,gani haka yasa hajiya saratu cewa zata koma toh,amma mahaifiyarsa tazo akan cewa ta zauna a gida kawai,tunda tashiga wata na tara,ana saka ran haihuwar ta nanda sati uku masu zuwa. "Uhm kunji ɗadinku zaku fice kusha iskar waje,ni duk zamannan ya isheni ga nauyin jiki,duk da har yanzu ban warware da gajiyar zuwa gombennan ba" "Ko aiki kike kinsam ai bamai barki kifita daga gidanann da wannan cikin,gwanda ki kwantar da hankalinki" Har sabrah zata sake magana madeena tashigo ɗakin,da fara'arta ganin yayunnata sun tashi. "Anties ina kwannan ku ya gajiyar tafiyah?" "Lafiya kalau sis kin tashi lafiya?" "Alhamdulillah,Anty sabrah wai kije inji Hajiya saratu kisha maganin sassafe" "Toh,nimaganinne banajin daɗinsa a baki,duk da inajin daɗin sa sosai" "Kinga tashi yanzu haka tana jiranki,inkuma so kike na ƙira ogah SAdeeq ya goyeki kuma toh,duk munsan jiyama a gidan ya kwana a sashen Jalal,aimu da turaki akayi muka huta da ma'auratan zamani" Khamriyyah ce mai zuba wannan surutun tana shafa mai a ƙaramin bakinta mai shegen surutu. Dukkansu dariyah suka sa harda madeena wacce itama tasamu waje ta zauna tana kallonsu,Alaƙarsu baƙaramin burgeta yake ba,haka ma faɗansu. A iya sati ɗaya da sukayi a tare tajita gurbin data rasa yau ya cike,a dajinta take kaman batada yaya mace,saboda Antyn tah Khadija sanda tayi wayo anyi aurenta,kuma bata jansu a jiki. Amma yanzu zamanta cikin ƴan uwannnata yanasakata nishaɗi. Ji take kamaar karta koma makaranta wani satin. Suna gama shiryawa dama driver yana jiransu a waje.. Bayan sun gaisheda inno,suka wuce sashen Hajiya saratu ma. Sabrah tana zaune da magani a kofi sai yamutsa fuska take. Basu daɗe ba a wajen suka fita,hajiya saratu musu fatan Alkhairi cikin fara'ah,a cikin idonta zaka hango kaunar datakewa ƴan matan. Khairiyyah aka fara a jiyewa a wajen aikinta,kafin aka wuce da khamriyyah headquatersu. Drivern yana ajiyeta ta wuce rest room na mata domin saka kayan aikinta,sai sauri take dan tasan halin shugabannata. Kwankwasa ƙofar tayi,amma shuru ba'a amasa ba,hakanne yasa ta tura kofar ta shiga,dan a tunaninta bayanan. Turus tayi jin abinda yashigo kunnenta. "Duk da nasan ke mai laifice,kuma nine keda alhakin miƙaki ga alƙali,na minti biyar kacal ki yarda na ganki deejah,batareda kowa yasami ba,akwai abinda nake son muyi magana akai,sann......." Da sauri ya juyo suka haɗa ido da khamriyyah,wacce itama shiɗin take kallo......... See you next......😊 Taku _sadi-sakhna_ Ƴar mutan jama'are. *MABARACIYAH* _haƙƙin mallaka_ _*sadi-sakhna*_ (Yar mutan Jama'are) 55••56 "Ahh ogah ba komai fah kacigaba da wayarka kawai,barina je wani waje na dawo,bansan kana cikiba dama,nayi ta magana ba'a amsaba" "Dakata,amma kinji mai nace,sannan kinsan dawa nake wayah?" Juyowa tayi ta kalleshi tareda ƴar yin dariyah tace. "Ahhh batun waya kam ai dole naji tunda inada kunne,yanayin wayarma ya tabbatar dawa ake yinta,abin mamakin kuma shine a ina kuka haɗu da har kuke wannan maganar da ita. Duk da dama na zargi hakan tun daren jiya" Fesar da numfashi khaleel yayi tareda cewa. "Okay okay naji kingane abinda yake faruwa,amma please karki faɗawa kowa mai yake faruwa" "Uhm hakan bai daceba,amma duba da yanda ka damu zam taimakawa ogana nayi ƙus da bakina,amma nima da sharaɗin zaka daina min wanan faɗannaka,dan ya isheni,idan kana buƙatar taimako ma ƙofah a buɗe take,koba komai zan ɗan ja lokacin ba'azo kaina ba kenan,tunda sai angama da ita kan azo kaina,itakuma mai kafcen soyayyarta ya kafeka" Da dariya taɗan karishe magana tareda barin office ɗin. Binta yayi da kallo tareda sauƙe ajiyar zuciya,haka kawai shakkarta yakeyi,domin itama wajennnata ba sauƙi,inaga kuma shugabar. "Oh ya Allah gani gareka,inama zan iya mantawa da wannan baiwar taka" Daga haka ya koma jiki a sabule ya cigaba da abinda yake. Can kusan misalin shabiyu na rana khamriyyah ta shigo ɗauke da tea cup a hannunta,yanxu tunda itace mataimakiyarsa duk wani abu itake kula dashi.. Da sallama tashigo office ɗin ta sameshi yana rubuce rubuce akan paper. Zama tayi a kujerar datake facing ɗinsa ta zuba masa ido. Tsarguwa yayi da halayyarta ta wanda yakan yasashi cewar. "Menene kika zuba min ido haka kaman wanda yau kika fara kallona" "Uhm tausayi kake banine sosai,tun zuwana wajennan koyaushe sai kowa ya tafi ya barka,bawai dan kana aikiba saidan kana tunani. Kowa yana kulada ramar dakake a kwannan ,duk da kowa bai san ciwon so ne yake ɗawainiya dakaiba. Soyayyar data ke abinda kunya a gareka,wacce bazaka iya fito duniyah ka bayyana ta ba. Hmm waye zai iya cewa ya kamu da soyyayar wacce aka bashi ragamar yakama ta da laifi,shin wane suna za'a ƙirashi?......i am sorry ogah for this burden life" "Ba kunyar soyayyartace tasakani hakaba,dana sani nake da nadamar meyasa bab nuna mata kulawa fiyeda yanda na bata ba,har ta kubuce ta buya a duniya tareda kunyar kanta kanta. Inaso na haɗu da itah na nuna mata a shirye nake naji uzurinta da dalilinta,sannan kuma na fahimceta akai,idan nema mata kariyahne a gaban Alƙali zan iya domin taimakonta. Ita ɗin ba yanda kowa ke tunaninta bace,tana da halin na juriya,tausayi da taimako wanda bakowa zai gane hakan ba,saboda idan tayi niyyar taimakon tana nuna shine kamar zalunci take. Alhali ba haka bane. Khamriyyah inaso na haɗu da itah yau batareda kowa yasani ba,zuciyata tayi kewarta sosai?" Wani irin tashi khamriyyah tayi daga kan kujerar da take tareda kallon Ogannta,anya kuwa ba zaucewa yayi ba yake wannan bayanin haka. "Ogah anyah kuwa ƙalau kake?" "Ina za'a samu ƙalau a gun wanda yake irin wannan soyyayar,ina za'a samu a kalau a gun wanda yake kwana yake tashi da fargabar shin masoyiyarsa ta samu wajen kwana mai kyau ko bata samuba,sannan wacce take kwana da zullumin cewar za'a kamata saboda ta kashe wanda sukayi mata laifi" Sadeeq ne ya banko ƙofar ya shigo,idonsa cike fal da hawaye har yana zuba. Zaro ido khamriyyah tayi itda khaleel suna kallonsa. "Duk tsawon wannan lokacin kana cikin irin wannan halin amma baka taba sanar dani ba Khaleel,Anyah kuwa ka ɗaukeni ɗan uwa yanda na ɗaukeka,babu wanda na fara faɗawa sirrina saikai,amma kai naka sirrin bansan dashi ba,kullum ina cikin wasiwasin mai ya sameka,yanzu da banji ba shikenan haka zakayi ta zama babu mai taimaka maka,koma wacece kake so yakamata kasanar dani" Juyawa sadeeq yayi zai bar office ɗin,saikuma ya tsayah saboda abinda yaji Khaleel yana faɗa, "Sadeeq Deejah nakeso,wacce kafi sani da mabaraciyah!!! Ita nake yiwa son da bazan iya misaltashi ba a cikin raina,taya zan iyah sanar dakai irin wannan labarin ɗan uwa,taya zan buɗi baki nacemaka ina son wacce yakamata na tsaneta,taya zan iya cemaka inason wacce takeda laifi a idon duniyah,bayan kowa ya sanni da dannne abinda nakeji indai yazo a bangaren aikinah?!!! Bazan iyaba Sadeeq,badam kajiba zanyi ta jurewa har ya kaini ƙasa,domin abune dana kasa jurewa irin wanda na saba a koyaushe. Inason sanar dakai amma kuma na banida ƙwarin gwiwar hakan" Rungumeshi Sadeeq yayi ƙam a jikinsa tareda shafa bayansa. "Hmm khaleel kenan,duk duniyar nan babu wanda zaka faɗawa wannan labarinnaka ya fahimceka kamanni,saboda karka manta nima ina cikin irin koman da kake ciki yanzu. Koda yakasance ita mai laifi ce,sannan kuma zaka kamata,to karka yi wasa da wannan lokacin wajen fuskantarta,da kuma fahimtarta,ta hakane abin zai zo maka da sauƙi. Bansan a inda kuka haɗu ba,amma hakan yasa naji da akwai wani abu a ƙasa itama daya sata aikata hakan,saboda nasan bazaka faɗa soyayyarta ba idan ta kasance yanda kowa ke zatonta,dan haka ka haɗu da ita tun kana da damar hakan,ka haɗu da ita a matsayin masoyinta,lokacin daka fito da shaidu kuma ka haɗu da ita a matsayin Dedective IBRAHIM KHALEEL na tabbatar zata fahimce ka" Sauƙe ajiyar zuciya khaleel yayi,duk da ya yarda da abinda sadeeq ya faɗa masa,amma har yanzu yana kunyar sa sosai akan abinda ya faru Lallai bai kamata mutum ya faɗi abu kokuma ya zartar ba,alhali bai san mai yake faruwa ba. Gyaran muryah khamriyyah tayi ganin sun manta da ita a wajen, "Allah yabaka sa'a a soyayyarka ogah,kaman yanda kake sonta ina mai tabbatar maka itama tana sonka da zuciya ɗayah,kawai dai akwai dalilin hakan" Tana fita daga office ɗin khaleel ɗin ta hangi royal driver yazo ɗaukarta,anan ta tuna ashefah yanzu a can suke zaune. Shiga tayi suka nufi gida,tunani da tausayin Khaleel fal a ranta. Da yamma yau khaleel ya tafi gida yau,kirjinsa sai bugawa yake da tunanin taya zai fuskanceta a yau ɗin. Tun a motarsa kafin ya isa gidan yake ƙiranta amma batayi picking ba,hakanne yasashi turamata massage,akan inda zasu haɗu. Bayan ya fito daga wanka ne yaga massage ɗinta na addess ɗin inda zai sameta. "Bakin ruwa?" Yafada a ransa,mai kuma zai kaisu har bakin ruwa na bayan gari. Zuciyarsa ce ta sosu daya tuna har yanzu bata yarda dashi ba inaga. Shiryawa yayi cikin kayansa normal irinna gida,babu kowa a farlo ummah tana ciki,dan haka babu bata lokaci ya fice daga gidan. Tafiyah yake a mota zuciyarsa tana hasaso masa yanda zai ganta,finally bayan kusan wata guda yau zai ganta. Kamar yanda ta faɗamasa kuwa tana zaune ta juya bayan ta daga inda yake tahowa,duk da yasan tana jin takun tahowarsa wajen.. "Deejah kunyar juyo da fuskarki kike gareni komai,dan nasan kinji zuwana" "Abinda nakeji gameda kai ma har yafi kunya Eemran. A duk abinda nake a rayuwata,nakan saje a wajene nayi abinda nakeso sannan na bar wajen tareda ajiye tunanina a cikin zuciyarsu,sannan bana waiwayarsu koda kuwa da kaɗanne. Saidai kai......zuciyata ta gagara fitar dakai daga cikin raina,a tunanina idan na sauƙe fansata akan mahaifiyarka na tafi zan manta dakai,amma kuma ba haka bane,musamman daya kasance ina kallon shige da ficenka a kullum,na gagara mantawa..." Samun waje yayi ya zauna a kusada ita yana kallon ruwan dayake gabansa. "Hmmm wannan zancen dama nasan hakane,tunin sa kawai kike a cikin kunnena deejah,nariga nasani kina sona kaman yanda nake sonki,abinda na kasa sani shine yanda kika boye cikin duniyah,inda idanuwana bazasu iyah tsinkayoki ba. Abubuwa kaɗan zafi sukemin tareda nauyi a zuciyata,saboda komai saina haɗa da tunaninki cikinsa deejah" "Nasan hakan Eemran,a hakane a NAWA BANGAREN nima,inason tsayawa a gefenka,saidai kuma matsalar dazan jawo maka nake tunani. Kaine babba a gidan sarauta,nan gaba kaɗan zaka zama sarkin garinnan idan da kwana,taya zaka nuni a matsayin matarka a haka Eemran?" "Wannan kike tunawa,shiyasa kika gujeni akan haka,sadeeq ya tsayawa matarsa,itama tatsaya a gefensa amma kuma ke ko sau ɗaya kinkasa yarda dani deejah" "Na yarda dakai,abinda nake gudu shine,saimun shaƙu da juna na tafi magarƙama na barka" "Baki yarda dani ba,tunda bazaki tsaya tareda ni ba har Allah yayi nasa hukuncin,ina sonki deejah,guduwarki bazai sanja komai ba,face ƙaramana wahala" "Shikenan idan hakan kakeso zan amshi soyayyarka Eemran,nima ganinka cikin wannan halin baso nake ba,saidai ina mai tabbatar maka dole mu shiryah mai zaizo ya tafi,duk da nasan ƴan uwanka dasu sadeeq baxasu ƙini sosai ba." "Mai kike nufi da hakan" Ƴar dariyah deejah tayi tareda kallon eemran ta jijjiga kai. "Har yanzu baka sanniba,baka gama sanina,abinda ka sani ma na rayuwartawa bamai daɗin bada labarinsa bane,amma duk da haka ka yarda na kasance abar sonka?" "Na yarda shi so halitta ne,sannan kuma daga Allah ne,mutum baya sanja kaɗɗararsa,sannan baya zabar wanda Allah zai jarabceshi da sonta. Koma mai zakice ina ji a jikina ke Alkhairice a gareni,Addu'ar da nadaɗe inayiwa Allah kan ya haɗani da mace tagari bazata tafi a banza ba. Nafaɗa nasake faɗa,yamda kike nunaw mutane suke aibataki,sannan kuma suke tsoronki ba haka kike ba,kinfi mata fiyeda dubu idan aka jerasu. Kuma bana miki shakka cewar ka zan zaba a cikinsu deejah,inasonki har cikin raina,kuma bana nadamar hakan." Rau rau da ido deejah tayi,tana maimaita abinda ya faɗa a cikin kanta,hakiƙa ita kanta tasan soyayyar dasuke ma junasu they deserve each other. "Zan nuna maka wanda babu wanda na taba nunawa shi a tsawon rayuwata,zan bayyan maka hakanne saboda na nuna maka cewar na yadda dakai.......amma har yanzu zuciyata kokwanto take da alaƙarmu,ina jin tsoron......." Katseta yayi ta hanyar cewa. "Deejah yanzu babu sauran abinda ban sanar dake ba,nagameda soyayyata gareki,bazan tilastaki dole saikin amince ba a yanzu,nafara jin babu daɗi saboda roƙonki danake,nizan tafi magriba tayi,kikulada kanki sosai,sannan .....idan na ƙiraki nayi kewarki ne,ki taimaka min ki ɗaga" Yana gama faɗin hakan ya juya zai bar wajen,har yafara yin nisa,yaji abinda ya zuƙe masa ruwan kai,mai zai ji muryar Khamriyyah. "Dec. Khaleeeeeellllll,karka kujeni,ina faɗane dan banida zabi badan dan banasonka ba,komawata wajen aiki ma dominka ne,saboda na dunga kallonka ina kulada kai a koyaushe,yimaka hidima abune da bazan taba gajiya wa ba. A da nakasance mai HARSHEN DAMO wajen kamanni,yanxu kam zuciyata takai maƙurah wajen boyewa." A tsaye yake kyammm komai na jikinsa ya tsayah da aiki,ya dade a haka kafin ƙafafunsa suka taimakeshi suka maidashi zuwa inda deejah take durƙushe tana kunjin kuka. Shima tsugunnawa yayi a gabanta tareda zuba mata ido,yarasa mai zaice,gabaɗaya harrufan bakinsa sun tafi yajin aiki. "Kayi haƙuri khaleel,eemaran,junaid,komai ya farune da dalili,sannan babu yanda zanyine sai haka. Wasu sunsha wuyah tareda deejah mabaraciyah,sai suke ɗaukar fansar su tareda ita. Wasu kuma sunsha wahalane tareda khamriyyah V-lady,suma sai suke ɗaukar fansarsu tareda ita. A tsawon rayuwata nayita yanda zan banbanta waɗannan mutane biyu,ta yanda wanda yasha wuyah da ɗaya kar abin ɗaya ya shefeshi. Kaine mutum na farko daka haɗa alaƙa da mabaraciyah,kuma khamriyyah ta bayyana kanta,badan komai ba sai dan. Abinda mutane basu ganeba su mutane biyun zuciyarsu guda ɗaya ce ba biyu ba,ciwon kowacce da ƙalubalenta kan jiki guda yake faɗawa,haka feeling ɗin ta,walau bakin ciki ko kuma farin ciki. Nima mutum ce,inada iyakata Khaleel,na daɗe da kaiwa iyakar amma bansan nakai ba,kaine ka taimakeni ka nunamin nakai wajen da bazan iya sake ɗaukaba,nima ina buƙatar na jingina a jikin wani,ba wai kullum na dunga jan wasu su jingina dani ba. Abu ɗaya nake so kasani dec. Khaleel,kaman yanda deejah take sonka hakama ga khamriyyah,itama tana matuƙar son ka,Am sorry I love you!!!""" Kuka tacigaba da rusawa khaleel yana saurarenta,gabaɗaya yarasa mai zayyi,tuno acting ɗin deejah yake da kuma khamriyyah,duk da ƙwarewasa a fannin bincike bai isa yace mutum ɗayace na,duk da yana ji a jikinsa yasan khamriyyan amma kuma bai tana kawo hakan a ransa ba. Bude idonsa yayi akan fuskarta data jiƙe da hawaye,wanda yakan yasa fatar data saka tafara tasowa. Hannunsa ya kai wanda yake rawa ya ɗaye ta daga kan fuskarta,take kuwa fuskar khmariyyah ta bayyana tamkar abin almara. "Kenan wannan itace fuskarki ta ainihi,wato khamriyyah?" Ɗaga masa kai kawai tayi,dan batasan ma mai zata ce ba. "Tashi na kaiki gida dare yayi,karki faɗawa kowa wannan maganar,kicigaba da yanda kike,gobe idan kinje aiki zamuyi magana,inason nasan komai dan gane mutane biyun,karki boyemin komai,dannima na kai maƙura wajen sakani a duhu da kikeyi,idan har kin yardani zamuyi rayuwa tare,to bana son ko baoyemin komai" "Inshaallah bazan boye maka ba,amma kar hakan yasaka ka cikin wani tunanin" Ƴar dariyah yayi tareda cewa. "Baccin da banyi ba mai yawa na tsawon wata guda yau zanyishi cikin walwala,hankalina ya kwanta yanzu fiyeda yanda kike tunani. Nagode dakika yarda dani,ina fatan nakasance nine taki majinginar dakema yanzu zaki jingina deejah,tashi mu tafi na kaiki gida,yau a can ma zan ci abincin dare,gobe kuma zan koma gida" Zaro ido khamriyyah tayi,amma bata ce komai ba sai ɗan murmushi da tayi kawai. Tashi tayi suka nufi motar tasa,babu wanda yake cewa komai,kowa da abinda yake saƙawa a ransa. Yana packing ɗin motar tayi nufi sashensu batareda ta kalleshi ba,shima murmushi yayi tareda bin bayan ta kawai. Sallama ta ƙwallah amma babu wanda ya amsa mata,leƙa ko ina tayi amma babu kowa a cikin gidan. Haka kawai jikinta ya bata babu lafiya. Fitowa tayi da gudu zata je sashen hajiya saratu. A hanya sukayi karo da khaleel wanda ya biyota zai bata wayarta data bari a mota. "Lafiya naganki haka mai yake faruwa?" "Uhm babu kowa a sashen,inaga ba lafiyaba gaskiya" Tare suka nufi sashen hajiya saratun,saidai nan ma babu kowa sai masu aiki kaɗai. Salaha ta kalla tazo wucewa,da gudu ta risketa tareda tambayrta mai yake faruwa. "Uhm anty khamriyyah bakisan mai ya faruba?,anty sabrah ce ta sule a tile ɗazu da yamma ta faɗi,shine aka ɗauketa zuwa asibiti a sume jini yana zuba." "Meeeeee kikacewa,faɗuwa kuma da wannan cikin ya Ilahi,Khaleel maza muwuce asiviti" Da sauri suka koma motar sukaja da gudu sai general hospital,inda aka tafi da ita. Khamriyyah sai kuka take a motar tana ƙiran sunan sabriyyan......!!! Taku _sadi-sakhna_ Ƴar mutan jama'are. *MABARACIYAH* _haƙƙin mallaka_ _*sadi-sakhna*_ (Yar mutan Jama'are) 57••58 Ko packing khamriyyah bata tsaya sun gama ba ta nufi cikin asibitin da gudu. A bakin ɗakinnata ta haɗu tasu khairiyyah da sauran ƴaƴan gidan,idon khairiyyah yayi jawur dashi saboda kukan data sha. "Khairi dagaskene ina take itaɗin" "Uhm tana ciki,har yanzu wai jini take zubarwa,saidai kuma sunce wai zai tsayah,yana tsayawa kuma za'a shiga da ita ɗakin tiyata,domin tserar da abin cikinta" "Huh alhamdulillah" Khamriyyah ta faɗa cikin ajiyar zuciya,saidai duk da haka har yanzu hankalinta bai dawo kanta ba sosai. Ganin magriba tayine yasa su amal da kuma sauran wanda suke wajen suka shiga motar jalal domin komawa gida. Aka bar iyah su inno da hajiya saratu sai khamriyyah da khairiyyah,saikuma khaleel wanda ya tafi sallah zuwa masallaci. Sai bayan isha tukunna khaleel ya dawo ɗakinda aka kwantar da sabran,hannunsa ɗauke da ledodin abinci da kuma wasu magungunan da ake nema. Hajiya saratu ya miƙawa bayan ya tambayi jikin sabrah,wanda take ɗaki daban a gefensu. "Da sauƙi junaid,ɗazu muka ganta,gobe inshaallah za'a mata aikin,ya za'ayi da tsautsayi yazo,hmm" "Allah ya taƙaita ,ni barina tafi gida,zan dawo da safe kafin na tafi wajen aiki" Duk abinda suke sadeeq yana zaune baice komaiba,ɗazu da hajiya deejah tazo babu yanda tayi su tafi amma ya kafe ba inda zaije Kallon khamriyyah Khaleel yayi ta kasan ido tareda yin hanyar fita,ganin khamree bata biyoshi bane yasa yace.. "Am khamriyyah kizo akwai wata magana da zamuyi" Tashi tayi tabi bayansa,suna tafe babu mai magana har suka iso bakin motarsa. Kallonta yake kaman bazai ce komai ba saikuma ya buɗe bakinsa. "Narasa mai ma zance,kawai so nake nasake ganinki,ki kulada kanki sosai,sannan ki rage damuwa,da ikon Allah zata samu lafiyah. Gobe ba sai kinzo aikiba,saboda nasan ko kinzo babu abinda zaki iya" "Nagode Yah khaleel" Mamakin sunan data ƙirashi dashi yayi,itama ganin hakan yasata cewa. "Zan dunga bin bakin sauran ƴan gidane,saboda gudun gane tsakanin mu,kaman yanda kace ya zama sirri..yakamata ka tafi gida yanzu,nasan ka gaji sosai" Sallama sukayiwa junansu kafin suka rabu,kowa yanajin kaman karya rabu da rabin ransa. Washagari misalin ƙarfe bakwai aka shiga tiyata da sabriyyah,dan dama tun dare aka gama shirye shirye. Haka suma ƴan uwannnata kwana sukayi suna kaiwa kukansu ga Allah,domin nemawa ƴar uwartasu neman sauƙi. Awa guda ta wuce,zuwa lokacin su khamriyyah sunyi cirko cirko a bakin ƙofar wajen. "Inno har yanzu basu fito da ita ba" "Ki haƙuri khairi,inashaallah babu abinda zai faru sai alkhairi" Wata matace ta fito daga cikin thearter room ɗin,da kaya blue,da alama nurse ce irin masu taimakawa a ɗakin tiyatar,hannuta ɗauke da Tiren abinda ake buƙata a aikin. Da dan gudu khamriyyah ta isa gareta tareda marairaice fuska. "Sister ki taimaka,dan Allah ki faɗamin mai yafaru da ita" Murmushi tayi tareda cewa "Komai yazo yanda ake so,ga can likitan ma yashigo ki tambayeshi kiji" Juyawa khamriyyah tayi tana kallon likitan wanda yake magana da su hajiya saratu. Abinda ya faɗane ya ɗan kwantar mata hankali sannan ya jiyartar da farinciki cikin ranta. "Congrat ma'am,munyi nasarar cire jariran dake cikinta mace da namiji,saidai kuma a yanayin wahalar da suka sha bazayyi yiyu ku gansu yanzu ba. Ita kuma zamu riƙeta na tsawon kusan wata guda,saboda akwai haɗari ta tafi gida a yanayin da mahaifarta take" Dukkanmu munji daɗi bayaninnasa,sannan a shirye muke mu zauna a asivitin domin tallafa mata. Shikansa sadeeq jin labarin sai. Yanzu yayi magana tun sanda sabrah ta gamu da tsautsayin. "Mashaallah,allah mun gode maka,Babu komai likita mun gode sosai" Kwanan su sabrah hudu a asibiti kafin aka fara nunawa mutane yaran,kowa sai saka Albarka yake... Ga zahiri nan kuwa ya fito,yaran kamar su ɗaya dasu amal,amal sai murna take idan aka ce da ita babyn take kama,namijin kuma yafi ɗauko babansa. Har sannan sabriyyah tana kwance,amma jiki da sauƙi sosai,kawai hutune datake buƙata shiyasa aka sakata bedrest. Khamriyyah ce ɗauke da file ta shiga cikin office din khaleel. Sallama kawai tayi batareda neman izini ba ta shiga kai tsaye,tun jiya ta dawo aiki amma batayi aiki ba sai yau. Idonta ne ya sauƙa akan wata budurwa tasha kaya matsatstsu masu tsada,ga wata karairaya datake kaman an zona mata battery.. Haɗe fuska khamriyyah tayi tamau,kana ganin fuskarta kasan matar batayi mata ba,saidai batace komai ba. "Am ogah ga file ɗin dakace na kawo maka" Matsawa wajen kujerar sa khamriyyah tayi tana nuna masa abinda tayi indicating a cikin file din. Ƙarar buga tebur ne yasa su khamriyyah kallon wacce take zaune. "Ke mekikeji dashi dazaki shigo wani kai tsaye ki wuce inda yake,bakya ganin magna muke,menene matsayin ki a wannan wajen. Kai kuma Honey kamata yayi kace ta tafi,narasa gane mai yasa ka sanja tunda ka bar china,nayi ta jiran zakazo gidanmu baka zo ba,yanzu kuma nazo nan kana basar dani why,you know i like to marry you" "Honey. Marry. Gidanku?" Kallon khamriyyah sukayi wanda tsagwaron bakin ciki da kishi suka turnuƙeta,kana ganinta kasan babu sauki an tabota. "Khamreeee ki bamu waje,idan nagama da ita zan kiraki muyi magana kinji" "Karkayi wannan kuskuren dec. Khaleel,inakaga na bar wajennna to wannan figeggiyar tabar nan wajen,idan kuwa ka tursasani saina bar wajennan kun cigaba da wannan wasan,toh ya nunamin ka zabeta ne sama dani,kuma bazan sake waiwayoka ba sai ankai ruwa rana" Tana gama maganar tayi hanyar barin office ɗin. Da sauri cikin zafin nama ya tari gabanta tareda hanata barin office ɗin. Cikin idanuwanta yake kallo tareda gane yanayin yawa bacin ran data shiga. "Je ki zauna akan kujera yanzu nan,ke kuma Humairah zo ki bar office ɗinnan yanzu ,kuma karna sake ganin kinzo wajena da wannan maganar" Cikin dakewa yayi maganar,wanda hakan yasasu yin abinda yace nan take,amma maganar bata hanasu aikawa junansu harara ba. Bayan Humairah tabar office ɗin ya ƙarisa inda ruwa yake ya zuba a kofi,miƙamata yayi ta karba tasha kafin yafara magana. "Badan gargaɗinki yasana na hanaki barin wajennan ba kokuma na sallameta. Saboda har yanzu bake bace,kina buƙatar a koyar dake yanda zaki iya shanye abu ba tareda kin nuna ba. Kin amince zaki jingina a rayuwata,kuma zaki kasance tareda ni,karki manta watarana zan iya karbar mulkin garinnan. Bai dace ga sarauniya ta dunga bayyana kishinta irin haka ba,dole ki koyi hakuri,juriyah da kuma danne abu irin wannan,ta hakane rayuwa zata zomiki da sauƙi deejah. Inaso ki dunga kwantar da hankalinki,nayi alƙwarin taimaka miki da kuma nunamiki hanyar dazata kaimu ga nasara,amma saikinyi min alkawarin zaki dunga yin duk abinda nace bstareda musuba. Jiya naji lavarinki deejah,hakan yasa na ƙara jin ƙarfin gwiwar tallafa miki,nariga na zabeki a matsayin abokiyar rayuwata,bai kamata ki dunga tada hankalinki akan wannan irin abubuwan ba" "Kayi haƙuri yah khaleel,ina sonka da yawa na kasa control ɗin kaina,musamman danaji tana zancen aure,jinayi kaman zuciyata zata faso ƙirjina" "Uhm naji dadin hakan,amma duk da haka kidunga ragewa My Queen" Blushing kumatunta yafara dataji sunan daya ambaceta dashi. "Jiya naji kasako maganar case ɗinmu dasu sabrah,gashi ita kuma batada lafiyah" "Karki damu mun tsara komai nida sadeeeq,sannan duk shaidun dakuka bamu na abinda sukayi yana wajenmu. Case ɗin mabaraciyah kuma sai na gama dana wannan,saboda akwai plan ɗin danake son shiryawa akai,thank god babu wanda yadan kece ita" "Na yarda dakai,duk abinda kace in ma zartarmin da hukuncin kisane daya dace dani zan karba da hannu biyu,saboda nasan bazaka yimin abinda bai daceba" "Bazata kai haka bama,kedai ki zuba ido kawai. Zamu miƙaku kotu da zarar sabrah ta warke an sallameta a asibiti,saboda kar hakan yashafi lafiyarta." "Mun gode da bayyanar ku cikin rayuwarmu lokacin da bama tsamanni. Ohh na manta ban fadamaka ba,zanje makarantar su fadeelah karfe shabiyu,akwai event da suka shiryawa yaran,to an gayyaci iyayen yara,zanje musu idan babu wani aikin" Tana maganar ne tana kallon agogon office din,yayinda shikuma yake kallonta yanda take burgeshi saboda resposibility ɗinta. "Kina burgeni sosai Jarumata,you are their savior khamriyyah,Allah ne kaɗai zai biyaki abinda kikayi,kuma ina mai tabbatar miki ubansu sai yayi nadamar abinda yayi. Domin yanzu nazama ubansu nima,kuma bazan bashi su ba koda yaso hakan. Barina shiryah muje tareda,abbansu ma zaije yaga bajintarsu,sunyi sa'ar samun cute little parent" Dariyah dukkansu sukayi cikeda jin dadin yanayin. Ranar da ƴaƴan Sabriyyah suka cika kwana bakwai a duniyah aka raɗa musu suna. Namijin MUHAMMAN BILYAMIN,sunan mai martaba,saikuma mace taci sunan inno wato ZAINAB,ana ƙiran su da SULTAN da kuma SULTANAH. Yanda aka so yin gagarmin biki hakan bai samu ba,domin uwar gayyar tana kwance a asiviti,saidai duk da haka bikin sunan yasamu mutane ƴan uwa da abokan arziƙi sosai. Bayan sati biyu da haihuwar sabrah tafara tashi tana yawonta ko ina,tsakaninta da yaran sai sunzo neman abincinsu tukunna. Ga kulawa ta musamman datake samu daga wajen ƴan uwanta. Duk ta dawo gida bayan sati biyu,amma su khaleel basu fara zancen shari'arsu ba saida sabrah tayi arba'in tukunna. Hakan ma badan sunso ba saidan babu yanda zasuyi. Domin idan abin yayi nisa daga baya akaji dole zasu fuskanci matsla. Bayan haka kuma aikin hukuma ba wasa ba,sunyi alƙawarin yin gaskiya da amana,taya soyayyya zata rufe musu ido su manta da hakan. Duk wani abu da zai kasance sun riga sun tsarashi tass. Tun jiya aka kai su khamriyyah dukkansu su kwana a can,saboda bin ka'idar shari'ah. Khaleel ne sanye da kayansa normal,shikuma sadeeq da kayan aikinsa. Hajiya saratu ce a gabansu sai matsar ƙwalla take akan su ceto mata ƴayanta,amal ce da sadeeq suke bata bakin kan ce babu abinda zai faru. "Ki kwantar da hankalinki babu abinda zai faru,domin mun haɗa dukkan shaidun dazasu fito da masu laifin a fili" "Toh nidai ku kula dasu,musamman sabrah,har yanzu fah bata dawo normal sosai ba" "Kai ummee,wai mijinta ake cewa ya kulada ita,ki kwantar da hankalinki komai zaizo da sauƙi,sannan dan allah karfah kifara kifara kuka idan kika ga abinda bai miki ba" Dukan wasa hajiya saratu ta kaiwa jalal wanda yake mata dariyah. "Kai wato har bakin dariya ma ka samu a wannan lokacin?" "Menene a ciki,nasan masoyansu zasu fiddasu ai,suda sukeda mai garin ma a gefensu,bakisan yah khaleel ya folawa ƴar ki bane?" Wani kallo khaleel yabishi dashi akan yayi shuru,amma hakan baisa yayi shuru ba saida ya ƙarisa faɗin abinda yayi niyyah. "Uhmm naji,mun riga mun sani ai tun a asibiti kawai munyi masa irinna iyayen gargajiyane,shikenan kuje muna zuwa Allah ya dafamuku" Amsawa sukayi da ameen tareda yin hanyar sashen mai martaba. "Wai dagaske ɗan uwa kayi zurfi a soyayyar khamriyyah,to amma deejah fah ya zakayi da ita kenan,koka daina sonta ne" "Ban daina sonta ba,dukkansu ina sonsu sosai,sabida abinda yayi ɗayar shine yayi ɗayar" "Mai kake nufi,kasakani a cikin duhu ban ganeba" "Bazaka gane ba yanxu,bari a gama wannan case ɗin,case ɗin gaba zan warware maka zare da abawa,saboda muna buƙatar taimakonka akai" Daga haka khaleel bai sake cewa komai ba har suka shiga wajen mahaifinnasu,dukkuwa da yanda sadeeq yake binsa da buƙatar ƙarin bayani. Addu'ar fatan nasara yayi musu,tareda basu gudunmawar lauyoyi guda biyu daga fadar,saboda sukare masa ƴaƴannasa,wanda a hannun hukuma yanzu. Lokacin da suka isa police station ɗin har ya gaji da jiransu, "Ina kuka shiga yallabai ina ta jiranku,kotu ta buƙaci jin wanda ake zargi,dan lokacin ku tun bayan minti biyar yayi" "Am sorry DOP,wani abune ya tsayar damu,amma yanzu zamu iya tafiyah inshaallah" Fitowa akayi dasu khamriyyha daga cikin police station ɗin,kana ganinsu kasan babu abinda ya samesu. Mutane da ƴan jarida sai bi suke,yau sunga wadanda suka kaɗa hantar gwamnati da manyan gari a shekarun baya. Tun kafin su isa kotu tayi maƙil da mutane,ana shiga ba bata lokaci lauyoyi suka fara gabatar da kansu. Iyayen Saifuddeen sun dau nasu lauyoyin,hakama iyalan dr. Bukar da kuma barr. Shehu. Kowa idonsa cike da muradin mai za'a yiwa waɗannan yara yakeyi.. Sukuwa su khairiyyah musamman khamriyyah,kallonsu take babu alamar firgita,dan dama tasan ranar zatazo,musamman daya zamo a kotun aka yankewa musu hukuncin sun yi kazafi ga Dr. Bukar,sannan kuma aka kasa samarwa mahaifinta hakiƙinsa lokacin da kawunta yazo wajen su.. Wani tafarfasa kirjinta ya fara,kana ganinta zaka hango tsagwaron bakin ciki a cikinsa. Duk ta ɗau fansa ta huce,amma kuma har yanzu zafin ranta bai gama washewa ba,dubawa tayi a cikin ranta amma bata gano mai tayi missing ba daga cikin abinda ta aikata. Ta gano mai tayi missing tabbas ta gano. Maganar alƙalince takatse mata tunani inda taji yana jawo labaran ƙarya daya saba a koda yaushe,hmmm su khaleel basu san komai ba,amma tana ganinsa ta tabbatar a siyeshi kaman ko yaushe.. Tabbas su khaleel sunada harkar tsaro a hannunsu,amma kuma basu da harkar shari'ah a hannunsu. Tasan burin khaleel shine a wanke ta a matsayin khamriyyah,daga baya kuma idan tazo a matsayin mabaraciyah saita yadda a yanke mata hukunci,shikuma sai ya fitar da ita ya ƙona fuskar datake sawa a matsayin mabaraciyah. Kenan deejah zata rayu a matsayin azzalumar datayi laifi ta gudu. Inaaaa batayi aikinnan dan tayi irin wannann sunan ba mai sunan matsoraciyah. Tayi wannan aikinne dan ta ɗaga martabarta,da kuma irin wanda akayiwa mutane kamar ta. Zuwa lokacin idonta yayi jawur saboda muryoyin da suke safara a cikin kunnenta,kuma dukkansu zugata suke ba bata hakuri ba. "Kayi haƙuri khaleel da alkawarin danayi maka,bazan iya ture sunan deejah ta irin wanan hanyar ba. Idan nayi haka ban cika burina ba,ban nuna musu kuskurensu ba. Wannan shine abinda nayi missing wanda yake cin zuciyata,idan har kuma nabari tsoro yahanani ɗaukaka sunan mabaraciyah a zukatan mutane,to zan rayu cikin danasani da takaici. Dan haka bazan taba bari hakan ta faruba. Bude idanunta tayi akan alƙalin dayake shari'ar tareda cewa. "Objection mu lord,babu wani ɗaga ƙara daza'ayi. Ayita ta ƙare anan wajen kowa ya huta. Zan faɗamaka duk abinda kake buƙatar ji,kafin sannan kasaki wannan na bayana ka wanke su na laifinsu. Saboda babu abinda suka aikata,dukkansu umarni na suke bi" Kallon ta kowa yake da mamaki,shima alƙalin dubanta yayi tareda cewa. "Amma kuma wannan mutane guda uku na gefenki su yaran mabaraciyane kina nufin harda su" "Ƙwarai kuwa kana shakka ne,to bari kaji abinda baka sani ba. Khamriyyah itace mabaraciyah sannan kuma mabaraciyah itace khamriyyah. Ba kaiba har kowa dayake wajennan ya tsaya yaji labarina,da kuma dalilina nayin abinda nayi" Kallon idon khaleel tayi,tana ganin tsantsar gargaɗin kada tayi,amma kuma inaaa ba maida hannun agogon baya,dole tayi yanda ya dace. See you next in deejah's history......... Taku _sadi-sakhna_ Ƴar mutan jama'are. *MABARACIYAH* _haƙƙin mallaka_ _*sadi-sakhna*_ (Yar mutan Jama'are) 59••60 Kowa dayake cikin kotun saida ya girgiza dajin abinda ta fada. Hatta su sabriyyah saida abin yabasu mamaki,inaga kuma sauran mutane. Ganin yanda fuskar kowa tacika da zullumine yasata fitowa daga akwatin dasuke tareda sauran.. Gaban alƙali tazo ta tsayah tareda kallon al'ummar mutanen wajen. Da ɗaɗɗai take ganin tsana da kuma tsangwamar da mutane sukeyi mata. Alƙalan da wanda suke ƙara ne suka tashi tareda cewa. "Yah shugaba mai adalci,wacce ake ƙara ta bayyana cewar ita ke aikata wannan abubuwan,bama ga iya ɗaya ba,gabaɗaya mata biyun ta bayyana cewar itace,kuma ga shaida nan na hoton fuskar wacce ake ƙirada mabaraciyah a hannunta. Yakamata Alƙali ya gaggauta yanke mata hukuncin mai girma,ta yanda zai zama izina ga sauran masu muradin aikata laifi irinna ta" Ihu ne ya kaure mutane suna cewa Eh hakane a kasheta. Shuru alƙali yayi yana rubuce rubuce,wanda hakan yasa lauyoyin da sarki ya ɗauka suka tashi domin cewa wani abu. Hannu khamriyyah ta nuna musu na su zauna tareda cewa. "Karku saka kanku akan abinda bakuda masaniyarsa,duk da nasan kunyi ƴa dani sannan kuma kunsan aikinku,amma ina mai baku haƙuri kan cewar ku hutasar da kanku akan wannan lamarin. Da inada damar barin nahiyar ma zan bari na tafi,amma kuma inaso mutane su san dalilina nayi abinda nayi,dan haka bana buƙatar wani ya matsi bakina kokuma ya tari numfashi na. Kowa a yau ya saurari labarina da kuma abinda mutanen suka min,ban kashe kowa ko na lahanta kowa ba sai su" Sauƙe idonta tayi akan iyalan su dr. Bukar da brr. Shehu,saikuma na DOCTOR ALAWIYYAH(wacce takashe ta rubuta mata sunan ta a duk jikinta da karfen wuta) Sannan kuma da hajiyah fulani da saifuddeen,wanda suke zaune akan keken marasa lafiyah sun tsiramata ido. Suda Allah ya ƙaddara basu shiga list ɗin mutuwar ba. _____________________________ _GARIN KANKIA wasu shekaru masu yawa baya_ Sunana Khadija Abdullahi kankia,nikaɗai ce a ƴa mace a wajen innata. Mahaifina malam Audu yanada mata guda biyu. Magajiyah,wacce muke ƙiranta da iyah Gaji,saikuma mahaifiyata wacce HAUWA muna ƙiranta da Innan deejah. Iyah gaji auren Saurayi aka yimusu itada mahaifina,ƴayanta guda biyu ne. Daga harira sai Murjah,kuma dukkansu anyi aurensu kafin a haifeni. Innata kuma ƴayanta guda biyarne,yayuna maza uku,Hamza,Yusuf da Yahuza,saikuma ɗan autanmu umar,wanda da shekara ɗaya na fishi saboda yanayin rashin tsarin iyali. Kuma daga kan wannan inna bata sake haihuwa ba,saboda wani matsanancin ciwo ta gamu dashi lokacin haihuwar umar,anyi anyi takasa haihuwa da kanta,dole sai asibiti aka kaita. Nan ma daƙyar aka fitar dashi daga cikinta. Tundaga wannan lokacin ta gamu da ciwo a mararta,kasancewar babu kuɗi sannan babu wayewa,haka ciwon yacigaba da cinta har mukayi wayo,idan ya tashi saidai mu karbo mata jiƙo a wajen malam musa. A haka tacigaba da rayuwa cikin wannan halin har mukayi wayo muka gane mai yake faruwa a gidannamu. Iyah gaji irin mutanenne da babi ɗigon tsoron Allah a ransu,basayin komai sai abinda malamin dubansu ya faɗamusu,dan da wayonmu munsan iyah gaji bata Sallah. Ga baƙar mugunta da take yiwa innarmu itada ƴaƴanta su Harira. Babu dama mahafinmu yayi magana,inaga kuma innah,dole haka kowa yake nuna kaman babu komai,bayan kowa yasan yana faruwar. Ina kowa yana jurewa nikam saina fara maida martani,iyah gaji bata isa tayimin na ƙyaleta ba,duk ranar da nayi mata rashin kunya ranar bazata bani abinci ba,dan dama inna jijyarta yanata iya yin komai,kullum tana ɗaki tana fama da ciwo.. Gashi ta saka Malam yamin dukan tsiyah,dan zugashi take ta kalallama zance,wanda nikaina ban sanshi ba. A lokacin danake karama babu wacce malam yafiso fiyeda ni,amma yauda gobe ta wuce wasa,saida yazamo babu wacce ya tsana kamanni. Gashi yanzu dagani sai umar a gidan,ankai su yaha yahuza Almajiranci. Duk wani aikin wuyah saiyah dawo kan umar,lokacin ma shekararsa bakwai nikuma takwas,wani abin idan tasaka mu saboda ƙankantar shekaru bazamu iyaba,amma babu uzuri sai duka. Wata rana ina wanke wanke,umar yashigo gidan sai tangal tangal yakeda robar ɗiban ruwa,yajiƙe jikinsa jarab da ruwa,ga uban sanyi da ake a garin. Dukkanmu sanyi ya hudamu dagani har shi,dan wani lokacin ko muryarsa bata fita saboda mura. Magana yake cikin shaƙyƙyƙyiyar muryarsa. "Iyahh gaji na debo ruwan a sauƙemin" Magana yaketayi amma tana jinsa bata fito ta kalleshi ba. Ganin hakanne yasa na nufeshi tareda karba robar ruwan. Iyayine irinnawa,amma nasan baxan iya sauke masa ba,wahalar dayake shane zuciyata bazata iyah juraba. Dagani harshi ruwan kwaremana yayi a jikinmu,kaman anyi mana wanka a garin saukewar. Masifah iya gaji ta fara kaman an aikota,amma haka nayi biris da ita nazashi cikin ɗakinmu wajen innah,wacce take kwance tanajin abinda yake faruwa,ko a lokacin baya ma batada abin cewa bare yanxu. Cire kayan jikina nayi nasaka wani bushashshe,yayinda shima umar ba cillah masa marar jiƙa ya saka. Muryar iyah gaji na jiyo tana cewa. "Shegiyar yarinyah,to wlh bari kiji,idan kika kuskura kika sanja kayan jikinki sai na miki lahani a gidannan,kuma ruwane kin jawo masa,saiya ɗebo sau ashirin yau" Dataji hakan bai isheta ba ɗakin ta nufah da sauri tareda foncikoni nida umar,shikam sai ihu yake,amma idona ni a bushe yake kaff da tsanar matar ubannawa. Tari innah tayi ganin ta dage sai ta fitar damu a cikin ɗakin. "Yaya gaji ki ɗan bari rana ta fito mana kafin su cigaba da aikin,naga garin da sanyi sosai" "Ihuuuu ina kake malam maza fito gaji mai akemin anan wajen. Wai nice kulu takemin gorin dan ban haifi namiji ba bazan aiki ɗantaba,zo kaji malam,to wlh koni ko ita saika zaba,dama ba uwar komai take ba a gidan banda ci dakuma kashi" Masifa take kan gari ya gari da sanyin safiyar,fitowa yayi jin abin yayi yawa yazo bakin ɗakin. "Menene gaji da safiyannan kuma?" "Oh bakaji mai nace ba,to wlh sai tabar gidannan,tunda ina kulada ita bata ganiba,saika yanke hukunci yanzu,ko kuma abinda yaxo bazai maka kyau ba" Duk abinda suke ido kawai muka zuba musu,har yagama lallashin iyah gaji suka fita daga ɗakin. Tundaga wannan kaman an zuga iyah gaji wajen gana mana azaba,kowace rana da abinda zatayi mana. Shiryen shiryen tafiya sarin kayah malam ya fara zuwa kano,dan dama aikinsa kenan koyaushe,idan yaje kuma yakan ɗauki watanni bai koma ba,ina murna da neman kuɗi zaije,saidai kuma ina bakinciki da zai tafi ya barmu da uƙubarmu. Bye mukayi masa nida umar bayan mun rakashi har bakin tasha,umar sai kuka yake akan yatafi dashi. Tsugunnawa yayi daidai tsayinmu tareda yin murmushin takaici. "Hmmm nafi kowa jin zafin rayuwar dakuke ƴayana,saidai babu yanda zanyi kuyimin uzuri,a duk lokacin dana yanke zan gyara komai,ina shigowa sai kasa yin komai,mahaifiyarku ina sonta sosai,ina tausayawa rayuwarta sosai,saidai bazan iyah ɗaukar mataki ba. Da nayi tunanin na sawwake mata aurena,saidai kuma hakan ma ba shawara bace,domin batada kowa iyayenta duk sun rasu,ƴan uwa kuwa a wannan lokacin sai addu'a kawai. Kece kaɗai mace,kuma mai ƙaramin shekaru akan yayunki,amma kuma Allah yabaki zuciyar jurewa da kuma taimako,ki kulada ƙaninki da mahaifiyarki kafin na dawo kinji uwata" Muryarsa tana rawa ya ƙarisa maganar tareda zuyawa dan kada naga hawayen daya zubo masa. Tausayin iyayennawa ne ya kamani,gashi banida abinda zan iya akai. "Malam zanyi iya ƙoƙarina,amma ka dawo da wuri kafin ta kashemu kaji malam" Saurin shigewa mota yayi bayan ya jefo mana jaka biyu (400). Muna kallon motar har ta ƙule kafin muka dawo gida,kowanne yaro murna yake idan ya doso gidansu,amma mu fargaba ce take ziyartar zuciyoyinmu a duk lokacin da muka doso gidan. A hankali muka raba zuwa ɗakinmu saboda kar iyah gaji da ganmu. Allah ya bamu sa'a kuwa har muka shiga batagani ba,dan tana ganin kuɗin zata ƙwace da dakemu. Bayan an gama abinci munata jira tace ga namu sai mukaji shuru,har wajen la'asar bata bamuba,umar kam tun dazu yayi kukansa ya ƙoshi yayi shuru. Nima dauriyah kawai nake,amma cikina yanaji a jikinsa,ga inna ma batada lafiyah,dole zata buƙaci abinci. Kallonsu nayi dukka biyun wanda babana yace na kulada su,tun ba'a je ko inaba har nakasa kulada dasu ɗin. Tashi nayi da sauri na nufi ɗakin iyah gaji tareda zubewa a gabanta ina kuka. "Iyah gaji dan Allah ki bamu abinci,kar inna da umar su mutu" "Toh mutu mana ina ruwa na,in kina tunanin hakan da kikayi zaisa na baku abinci to ki sanja tunanin yar yarinya,babu ku babu abincin gidannan har abada,in zaki iya ki ciyardasu,ba ana zugaki ke mai zuciya ba,da yarintarki,to zuciyar ta basu abinci" Bansake cewa komai ba nafito daga ɗakin iya gajin,dan nasan komai zana sake cewa bazata sanja hukuncinta ba. Kayan jikina na kalla,dama duƙu duƙu suke da datti,kama skirt ɗin nayi na yaga shi,hakama rigar na yage hannunta. Zancen karshe dai na koma tamkar MABARACIYAH. kwano na ɗauka a tsakar gidan na nufi bakin tashar garinmmu,inda masu bara suke zama harma da almajirai dayawa. Tafiya nake hawaye yana bin kuncina,ko gabana bana gani sosai. Zama nayi ina bin bakin abin almajiran suke faɗa a gaban Manyan dasuke zaunen. Bani nasamu wani yabani guntun abinci ba har sai wajen la'asar,amma kuma nayi sa'a,domin dayawa ya bani. Gida na nufo da sauri murna fal cikina,koba komai nayi nasara. Ɗakinnamu ba shige tareda ajiye kwanon a gaban umar,barin kukan yayi tareda saka hannunsa a cikin jallof ɗin wacce tasha manja sosai. Kallon alamar tambaya inna tayi min,wanda hakan yasa na faɗamata abinda yake faruwa. "Innalillah,duniya ina zaki damu,kunyar kallonku nake deejah,nakasa kulada ƴayan dana haifa har sai sunyi bara" "Karki ce haka inna,babu abinda zaisa ki barmu a cikin wannan halin inba uzurin jinya ba,ki daina fadin haka" Turamata abincin nayi gabanta muka fara ci,duk da bamu ƙoshiba amma kuma mun kashe yunwarmu sosai,ganin yanzu umar ya daina kuka,inna ma ta daina riƙe cikin yunwa,yasani ƙara samun ƙwarin gwiwar komawa wata barar gobe. Zanci gaba da zuwa har lokacin dazan iyah yin aikin ƙarfi sannan sai na daina. Ga mamakina iyah gaji zata hanani zuwa bara,amma kuma sainaga bata hanani ba,abinma dadi yamata sosai,ace ƴar kishiyarta tana bara,mai yafi haka yimata daɗi. Wasa wasa har nafara sabawa da almajiran da muke bara dasu,don kullum tare muke,har nafara iyah sana'arsu da shoe shiner,wani lokacin kuma har tsangayarsu nake zuwa muna karatu tare. Shikansa malamin har ya sanni,domin nima allo ya bani yake doramin karatu da kansa. Yanda babban ɗan sa malam shazali,shine mai biya mana karatun. Ganin na fara koyane yasa na fara zuwa da umar ma,saboda shima yayi karatu,idan mungama kuma kowa ya ɗai robarsa ya fita nema. Nima sai bi cikinsu mu tafi. Duk inda na wuce zakaji ana cewa ga mabaraciyah a cikin Almajirai ga mabaraciyahh. Tun inajin kunyar sunan har yazamo ina amsawa da dariyah,sanadin haka ma wasu ke bani sadaka ko basuyi niyyaba.. Malam shazaline yanuna min cewar nadaina binsu bara,amma naƙijin sa,saboda ni baxan iyah fitowa na fada masa mai yake faruwa a gidanmu ba,sannna kuma bazan iya dainawa ba. Ciwon innarmu ne yafara tsanani sosai,wanda hakan yasa naje gida wajen kawunmu wato ƙaninta wanda suke uba ɗaya na faɗamasa.. Da farko banza yayi dani,saida nayi ta magiya tareda zubewa ƙasa kafin ya jini. Yana zagina yana aibatani haka yabiyoni muka dawo gidan,yazanyi dole na jure ko mai zaice,abin takaicin bansan garinda su yahuza suke ba,inna sani ma da nisa sosai,dannaji ance a ƙauyen Bauchi suke. Baro irinna masu ruwa aka samo muka sakata a cikin zuwa asibiti,lokacin magriba ta kusa. Inna laraba ma maƙwanciyarmu ta taimaka mana sosai,dan ɗanta ne ma ya tura mana baron. Lokacin da mukaje asibitin da suka gwadata cewa sukayi abin ya fi ƙarfinsu,domin Cancer mahaiface taci ƙarfinta sosai. Tun sanda ta haihu yakamata ayi mata magani,amma kuma ba'ayi ba,abin yanzu bazayyiyu ba. Ya mutum zaiji ace masa iyayensa ciwo yaci ƙarfinsu bazasu warke ba,saidai ya tsaya yayi kallon mituwarsu,haka naji a cikin ƙoƙon rai na. Da farko sun barmu mun zauna a asibitin suna mata allurar kashe zafi,koba komai zata koma ga Allah bata sha wahala sosai ba.. Amma daga baya sai suka ce dole sai mun kawo kuɗin daza'a dunga siyan magani. Matsawa nayi wajen kawunnawa wanda zuwansa kenan dubamu. "Kawu ka faɗawa su yaya yahuza dasu yusuf su dawo gida,a siyar da gonar inna a kaita katsinan da sukace muje" "Hhh yarinya kenan,bakida labarin gonar innar taku harda ita gwamnati ta karba a garinnan,duk wanda kuka je siyarwa babu wanda zai siya,saboda suna ƙarƙashin gonakin da brrr. Shehu Babban chair man ya ƙarba" "Amma meyasa ya ƙwace wa inna ginarta toh" "Ance sun shiga kan hanya za'ayi titi a wajen,ana saka ran zasu bayar da wani kuɗi amma har yanzu babu abinda suka bayar,amma dai tashi muje muyi masa magana a gidansa,ƙila ya taimaka mana" Tashi nayi tareda sake kallon inna wacce take kwance na bi bayan kawu,dan ma muna sa ran dawowar babana daga sarinsa a satin gaba. Gidan babu nisa sosai da asibitin dan haka bamu dade ba muka isa. Ni tsayawa nayi a gefe,suna magana da kawu,saida ya gama tsaramasa kafin yayi murmushi. "Kai Babannan,gona fah ba iya takuce ta shiga hannu ba,harda ta sauran mutane,an ce kuyi haƙuri kuɗinku zasu fito bada daɗewa ba" Ƙarisawa nayi gabansa tareda zubewa a ƙasa ina kuka. "Dan Allah baba ka taimaka,innata tana buƙatar aiki,gashi bamuda abinda zamu siyar,ka ara mana kuɗi inyaso idan suka fito saika ɗauka" Jefar dani yayi daga jikinsa tareda kaɗe kafarsa. "Ke wace irin yarinya ce,da wannan dattin kike tabamin farar shadda,nabaki kuɗina saboda nina damu uwar taki ta tashi,ki cemata tayi ta jira idan suka fito ta samu maganin" Haushine yakama kawu wanda hakan yasa ya cakumi kwalar brr. Shehu. "Ya isheka haka azzalumin banza,kowa yanada labarin cewa akwai wata manaƙisa dakayi,akan kuɗin mutane" "Hhhhhh ashe kanada wayo ka gano gaskiyah,kuɗi na cinyesu sun zama nawa,kuma babu abinda za'a iya min,ni lauyane zan kare kaina,bazan bada kuɗi ba,idan ka isa ka ƙwacesu a wajena" "Haka kace,shikenan kazuba ido ka gani,nikuma zan tsaya tsayin daka na ƙwato musu haƙƙinsu,shari'ah daga nan har katsina a shiga" "Ka gwada ka gani,basai kakai goben ma bare kayi shari'ar ba" Ture kawu yayi tareda ƙare mana kallo ya bar wajen. Bayansa nake kallon yanda yake tafiyah hankalinsa kwance kaman babu abinda yayi. Kawune ya ɗagani muka koma asibitin,har sannan kuka nake. Mai zan gani a wannan duniyar da yanzu ma nake fahimtarta. Lokacin da muka koma likita ne ya aiko kan cewa kawu yaje ana nemansa,komai zaice dashi oho. Bayan kaman wasu mintuna ya dawo fuskarsa ɗauke da damuwa. "Deejah sunce zasu koreta a asibiti idan bamu bada wani kuɗi ba,nikuma banida wani kuɗi a yanzu,iya gona tace ɗaya tal danake nomawa iyalina,amma karki damu akwai lambuna na hayin kogi,zan je nabada shi jingina na wannan shekarar,inyaso sai a basu wani kuɗin. Godiyah nafara yimasa bansan adadinta ba,da nayi zaton bashida mitunci,sai daga baya na gane ashe fadane dashi kawai. Abinci yasiyomana nida umar,taliyah da manja kafin ya tafi. Washagari dai jiya i yau,saidai sabanin kowanne lolacin,yau abinda yafaru yafi kowanne girgizani. Taku _sadi-sakhna_ Ƴar mutan jama'are. *MABARACIYAH* _haƙƙin mallaka_ _*sadi-sakhna*_ (Yar mutan Jama'are) 61••62 Wani irin abu kunne na yake jiyomin a bakin mutane. Kawuna wai ya rasu,jiya da daddare wasu sun shiga sunyi masa yankan rago,ya mutu muss har lahira. Gari ya ɗauka da hayaniya,nidai ina zaune a gaban mahaifiyata wadda taketa murkukusun ciwo,na yau kamma yafi na kullum,gashi wanda na kwana da tunanin zaizo ya tallafemu shima wasu sun kasheshi. Nurse ce ta shigo ɗakin tana duba wata a gefenmu,duk abinda inna takeyi ko juyo kanmu batayi ba. Karisawa nayi gabanta tareda jan hannunta,amma ban samu komai ba sai harara. "Mayu kawai,kunzo kun damu mutane,banda wari keda uwartaki babu abinda kuke,na kyautarku ya ƙare tin jiyah,ba an faɗamuku ku kawo kuɗiba?" Kwallah ce ta zubo a idona na kalleta tareda cewa. "Amma kawunnawa ance an yankashi jiya" "Toni na yanka shi,bare kice ya rataya a wuyana,kowa yasam waya yankashi ai,mai takaishi yin musu da Brr. Shehu" Tunowa abinda yafaɗa yayi jiyah,wanda hakan yasa na fita da gudu zuwa gidan br. Shehun. Samunsa nayi a zauren sa inda mutanen garin suke kallon sa idan zai musu shari'ah,duk da a sannan ƙaramin lauyane,amma kowa yasanshi da yin nasara,koda kuwa kaikayi cutah,indai kabada kuɗi kaine mai nasara. Tsugunnawa nayi a gabansa tareda haɗe hannuna. "Dan Allah bawan Allah ka taimaka,kawuna yacemin zai biya kudin aikin,amma kuma ka kasheshi,kai ɗin ka taimaka ma inna ta" Zaro ido yayi a gaban mutane tareda wanka min mari,ta inda yake shiga ba tanan yake fitaba,ni sannan bansan hatsarine nace shiya kasheshi ba. Wani yaronsa ya kallah akan ya kulleni,saida mutanen wajen sukayi ta bashi haƙuri kafin ya barni na fito,lokacin da ƙyar nake ɗaga ƙafa,saboda mugun duka da yaron yayi min. A hankali nake tafiyah ina kuka na nufo asibitin,saidai kafinna shiga na tsayah cakk ina kallon yanda nurse ɗin suka turo gawar innata akan kekensu,duk wadda ya kalleta bazaiso sakewa ba,saboda haka takoma tamkar horror dan wahalar duniyah. Kuka na dungayi,a lokacin bansan hakan shiyafi mata ba,bansan tafiyarta yafi halin datake cikiba,ni sannan baƙinciki nake ta tafi ta barni ni ƙadai dani da umar. Wani abune mai matukar duhu da kauri ya ziyarci cikin raina,haushin abinda iyha gaji tayi mana,haushin rashin zuwan yayinmu dana malam lokacin da muke matuƙar buƙatarsu,sannnan kuma dana abinda brr shehu yayi mana.. Wani aka bawa kura ya turamana gawar har zuwa gida,sai a lokacin dan takaici mutane suka buga waya aka faɗawa yayinmu mai hake faruwa,tunda danayi ta binsu su faɗamusu babu wanda ya faɗa,saida ta mutu tukunna. Muna zaune nida umar munsakata a gaba,iyah gaji kuma tana ta waƙar gaɗarta tana tankaɗe,liman ɗin anguwarne yashigo yana jera salati da carbi a hannunsa. Bayan yaga ɗanyen aikin da iyah gaji takeyi,hmmm jinake kamar na soyata a mai mai zafi,dandai banida ikon yin hakannne. Ƴan anguwane suka shigo aka wanki innah aka yi mata siturah. Sai bayan an kaita wajen la'asar kafin su yahuza suka shigo gidan,kowa yana kukan rashin dalili. Ɗauke kaina nayi daga inda suke,in dutse ya kallesu na kallesu,ko tunanin ba laifinsu bane banayi. Shima malam a lokacin ya shigo gidan,saidai shi sabanin su,yana shigowa gidan ya saki ƙara tareda zubewa a wajen. Kansa dukka mukayi muna girgizashi,amma ina ya riga ya suma.. Masu karbar gaisuwane maza suka taimaka muka kaishi ɗakin iyah gaji. Abundai ya taru mana goma da ashirin. Malam bai tashi ba sai washagarin mutuwar inna tukunna,nan da ihu ya tashi wanda hakan yasa duk muka afka cikin ɗakin. Shashima gefe da gefe yake yana cewa baya gani. Mamaki abin ya bamu,amma kuma da gasken cewa yake baya gani. Karisawa wajensa mukayi muna kallon fuskarsa,amma shi baya kallonmu,duk idonnasa a buɗe suke tarau. Wata damuwarce tasake ɗoruwa akan wata damuwar,ga waccar ga kuma waccar. Haka akayi sadakar bakwai na inna,baban har sannnan baya ganin komai,ya koma makaho. Har sannan kuwa bana kula su yahuza,duk yadda sukayi naƙi fahimtarsu,umar ne dai shi ba ruwansa,amma kuma koba komai iyah gaji ta rage yimana tsiyah sosai,tunda tana bamu abinci. Da daddare bayan isha mukaji ance wai iya gaji tayi baƙuwa,kuma wai da mota tazo. Lokacin nikadai ce a gidan,naraka malam banɗaki na dawo dashi yana alwala. Har zan kwanta saikuma gulma ta hanani,wanda hakan yasa na leƙo.. Wani mutum nagani ya sungumi malam a kafaɗarsa,iyah gaji kuma tayi lullubi tabi bayansu. Dan kwalina na ɗaura nima nabi bayansu. A bakin kofah suka haɗu da su umar da kuka yahuza,dama sune manyan. Tun kafin suyi wata magana suka buge musu ƙeya da wani abu ta bayah. Tsoro ne ya shigeni,yayinda nake Allah Allah kar yusuf hamza suma su shigo. Motar dukka suka shiga,amma a hankali take tafiya saboda cikin garine,kuma ga dare. Binsu nake ina cin gudu har haki nake. A gidan gonar brr. Shehu naga sun tsaya,wanda yake bayan gari. Saida nabari dukka sun shige kafin na fito na nufi wajen a hankali. Da window nake leƙawa,inda naga matar a zaune itada brr. Shehu da kuma iyah gaji,sai kuma wannan nurse ɗin data harareni a asibiti,mamakin ganinta nayi a wajen. Kuɗi brr. Shehu ya ƙirga masu yawan gaske ya miƙamata. "Kai brr. Ɗan wannan kuɗin,wancan satin ma fah nayi maka aikin kashe waccar majinya ciyar,wacce itama tana ɗaya daga cikin masu filayennan" "Hmmm nida akaso a ganeni,ni manta da wannan matar a cikin wanda za'a kashe,saida wani yayanta ya tunamin. Kuma tazo gidan sauƙi ashe kishiyar gaji ce,wacce itama tashigo cikinmu yanzu" "Koma dai mennene,jarirai nawa na kawo maka a shekarar nan,amma kuɗin basuda wani kauri" "Wannan aikin madam Ateeka ne gata nan a zaune,ita zaki tambaya,domin ita ta bani aikin nemo mata su" Tsawa matar ta daka musu tareda kallon iya gaji. "Kumin shuru dalla,yawwa ke gaji,ya za'ayi,tun a kano yarona ya biyo mijinki saboda irin idonsa mukeso a aikinmu,Ƙwayar fara fara kaman ta turawa ita mukeso,sannan zamu ɗauki ziciyarsa ma,nawa kike ganin zamu baki? Miliyan ashirin ya isa?" Wata zabura iyah gaji tayi tareda cewa "miliyan ashirin,wayyo daɗi." Kallon inda babana yake nayi wanda ake cinikinsa,da kuma su umar wanda ko farfaɗowa basuyi ba.. Ciniki suka cigaba dayi,inda Hajiya Ateeka tace zata bata Milinyan Hamsin harda su Umar ma,nan take kuwa iyah gaji ta amince,har guɗarta. Wasu yarane sukayi kansa inda yake kwance,sai a sannan nagano ashe makantarsa sune sukayi,damim basaso idon yacigaba da aiki daga ranar. Wani abu suka sa suka fitar da idanuwansa,yana kwance kaman gawa,hakan bai ishesu ba suka ƙara ciro zuciyarsa ma. Jini ne yafara malala a wajen,nikam kasa cigaba nayi da kallah,idanuwansu dukka na kallah kafiran,amma babu wanda yayi ko gezau,kowa acikinsu lokacin duniyace a ransa. Barin bakin windown nayi jikina yana layi,har zan tafi sai kuma na tuna da su umar,idan suka tafi dasu ina zasu kaisu,buɗe bayan mota ɗaya nayi na shige ina cigaba da sheshshekar kuka na rashin iyayena a cikin sati guda. Baccine ya ɗaukeni a haka,ban buɗe idona na sai ji nayi an ɗagani sama. Waresu nayi a wani waje mai tsayin katangu sosai. Wajen bayyi kama da gidajen mutane ba. Mazane a wajen,wasu yara wasu kuma kaman yayuna,dukkansu basuda wando tsirara suke. Saurin rufe idona nayi tareda son farkawa daga mafarkin danakeyi,saidai kuma duk yanda nayi da kin amsar hakn abin ya faskara,muryoyinsu sun ƙi barin kunnena. Wani ƙaton mutumne dagashi sai gajeren wando ya nufo inda muke. "Mai kuma wannan jinsin yake a cikin wajennan,kunfi kowa sanin rashin sa'ane wannan ƙazamin naman ya shigo nan wajen koh?" "Kayi hakuri dumumu,bamusan tana wajen ba,a mota muka ganta a kwance. Mu fitar da ita ko kuw" "Ahah ku fara sanar da ateeka tukunna ko ita tazo da itah,kar a sake irin kuskuren baya,kunsan bata da daɗi" Nidai ina jinsu amma ban bude idona ba,dan banason sake ganin abinda na kallah. Wani ɗaki aka kaini mai duhu marar daɗin gani. Jefani sukayi a aciki tareda yimin barka da zuwa gidan jini. Bangane mai suke nufi ba,burina na fita a wajen na nemo su umar,dan dama dominsu nazo,nakasa ganin wautata takasa taimakonsu a wajen. Jijjiga bakin ƙofar nake ina ƙara,amma babu wanda ya kulani a masu wucewa ta wajen. Sai wajen yammane kafin wani yazo ya bude inda nake ciki,fincikata yayi da ƙarfi yafara jana a kan sumuntin wajen,na tabbatar fatar ɗuwawuna ta daye. Wani ɗaki muka shiga mai matuƙar kyau da gwalagwalai,tamkar mutum ba a duniyah yake ba. Wannan matar data siyah su babana idona yayi tozali da ita,tana zaune akan kujerar zinare,gefenta kuma wasu kwanuka ne a rufe. "Hhhhhh yarinya kenan,kema ganan idonki yana kamada na ubanki,rashin sa'ar ɗayah naki jikin mace yake,kashe mace a gidannan ya sabawa dokar mu,amma da tuni naki ma yana jin nan wajen kamanna ubanki" Ta ƙarisa maganar tana buɗe kwanon,idone guda biyu da zuciya an yi farfesunsu,kuma wai na ubana. Wani amai ne mai tashin zuciya yazo min,bansan lokacin dana fara kakarinsa ba. Ɗagowa idona nayi a karo na biyu,daidai lokacin data kai yankan zuciyar bakinta ta tauna. Juuuuu naji kaina yafara juyawa,sai duhu dayamin sallama. Buɗe idona nayi naganni a ɗakin da aka kwantar dani ɗazu,saidai kaman safiyah nasake ganin garin,kenan kwana na guda ina bacci a wajen. Ƙoƙartawa nayi na tashi,hannuna sai karkarwa yake saboda tsananin yunwa. Kwanon abinci nagani a rufe a gefena. Saidai ko marmarin budeshi banyi ba,saboda ganin nake idan na buɗe idanuwannan zan gani da zuciya wanda matar takeci. Maganar ta karshe na tuna kafin na suma wanda take cewa wai.....tayi nasara takai matakin ƙarshe,dasamu babbar dama akan akwatin sirrinta,yanzu itama kuɗadenta zasu fara hauwa ba adadi..... Kenan dan tayi kuɗin ta cinyemin ubana? Ga ƴan uwana ma har yanzu ban gansu ba. Kuka na fara tun ina marar sauti har na ɗaga muryah,tsawa masu wajen suke ta dakamin amma ko a jikina,na ma daina tsoronsu yanzu ni. Wani ne a cikinsu yashigo ya min duka kaman yasamu babbar mata,lokacin ban fi shekara sha ɗaya ba. Akwance nake ko motsin kirki banayi sai nishi,wani ne yazo yaƙara daukata zuwa wannan ɗakin na jiya.. Saidai yau ba ita kaɗai bace,akwai manyan mutane dayawa a wajen,masu muƙami da faɗa a ji a kasar nan. Dukkansu jajayen kayane a jikinsu,ita kuma uwar gayyar nata kayan baki itada wasu maza uku,da alama sune manya.suna tacin nama da wani jan abu a kofi,wanda na tabbatar jini ne naman kuma na mutane. Sunkuyar da kaina nayi bayan na kallesu sau ɗaya. Tsawa wani babban acikinsu ya dakawa masu kawonin "Bakuda hankali ne zaku ajiye mace a cikin gidannan,kuma ma ku kawota nan wajen,indai ba member ba rashin sa'a ne mace tazo nan wajen. Maza ku fita da ita gada gidannan,sannan ku kasheta,ku tabbatar batayi rai ba. Amsa wa sukayi da angama kafin suka figeni zuwa waje. Kallon karshe nayiwa yan wajen,idona ya sauka akan matar da banida buri daya wuce naga nata idanun itama akan hannuna,zuciyata ta taure,banajin tsoron kashenin da zasuyi,abinda nake takaici shine zan mutu itakuma tana duniyar hankalinta kwance. Rufemin ido sukayi da wani bakin ƙyalle kafin suka sakani a cikin wata mota. Inajin muna tafiya amma kuma gudun sai kace bana motaba,kaman muna jirgi,nasan bai wuce saboda tsafinsu ba. Fitodani sukayi daga motar tareda ciremin abinda yake idonnawa. Waresu nayi akan wani kungurmin jeji mai ban tsoro,ko inane wajen oho su suka sani,nidai jira kawai nake naji sun yankani,nima nabi iyayena da yan uwana. "Kai dallah yi sauri ka kawo igiyar,lanƙayeta zamuyi a jikin bishiyar nan muna kallonta harsai ta daina motsi tukunna" "Ahah yankata zamuyi yanda shugaba ya faɗa" Musu suka fara nidai ina zaune ina kallonsu,dan ko ɗaga ido ma da ƙyar nake,bare kuma nayi koƙarin yin wani abu Ji nayi sunyi shuru da musu kamar ruwa ya cinyesu,ina juyowa na gansu a kwance sun fara bacci,mama ki abin yabani,kafin nayi magana naga wani mutum a ya bullo daga gefena,bashida riga,daga shi sai wani jan wando na fata. Kallonsa nake da alamar shakku,da alama akwai wani abu tattare dashi. Rigar jikina ya kama zai cire na riƙe ina kallonsa,ba abinda na wasa kaman cin zarafi. Wata rigar ya miƙomin mai datti akan nasaka na bashi tawa. "Ki saka wannan kibani taki,san saka mata jini ne na ajiyemusu,suga kaman sun kasheki" Karbar ta hannunnasa nayi tareda yin yadda yace. Bayan yagama shamata jinin wani kurege daya kashe,sai ja hannuna muka fara tafiyah. Baicemin komai ba nima ban cemasa ba,abubuwan dayake a hanyar suna bani mamaki. Munyi tafiya mak nisa kafin naga yaja ya tsayah yana kallona. "Kibi tanan kiyi ta tafiyah zaikai ki jejin mutane,karki juyo idan kina tafiyah,kin sam meyasa na taimakeki?" Jijjaga masa kai nayi,dan har raina bansani ɗin ba. "Jiya da daddare naji kina karanta abin musulmannan,sai naga wani haske ya rufeki,yahana tsafin Doƙoji dabaki,da tuni jiyah ya juyarda ra'ayinki kinshiga ƙungiyarsu,saboda kalar idonki alamar nasarace a wajensu" "Uhhh Qur'ani kake nufi? Addu'ar bacci inaga nayi ,dan nayi mafarki malam ɗalha yana cemin banyi addu' a ba na kwanta" "Eh ita,hakan dana gani yasa naji kin burgeni,bai kamata ki mutu a haka ba,ni zan koma ,idan kin tsira kice wanda kuke bautawa inason addininsa" Har yajuya zai tafi na tsaidashi tareda cewa. "To amma meyasa bazaka taho mu tafi ba tare?" "Niba mutum bane yarinyah,ni ɗayane daga cikin yaran dasuke ƙira da dodo,mune muke ɗaukar jinin dasuke kawowa mu kaiwa sarkinmu dayake ƙasan teku,shikuma sai ya basu sa'a,bazan iya barin jejinnanba saboda ina ɗaure da sarƙa,konaso tafiyah bazayyiyiu ba" Tsorone yakamani jin abinda ya fada,saikuma natuna ya taimakeni,watakila bashida niyyar cutarwa. "Amm ba kace haske yazagayeni ba jiya,mai zai hana ka karbi addini kaima ka karanta,wataƙila sai sarƙar ta sunceka" Juyowa yayi ya kalleni tareda cewa "Zaki iya koyamin abin a nan wajen,tayaya ake koyawa" Murmushi nayi tareda karanta kalamr shahada shima yana karantawa,bayan mungama saina fara karanta ayatul kursiyyu yana bin bakina,jikinsa ne yafara karkarwa amma kuma bai daina faɗa ba,ganin abin yanacin ƙarfinsa ne yasa naja hannunsa da sauri muka fito daga inda yace baya ƙetarawa. Kamar abin tsafi kuwa sai jikinsa koma yanda yake,haki yafara yana kallon inda bai taba tunani a rayuwarsa zai bar wajen ba.. Zubewa yayi a gabana yace. "Daga yau naza ma bawanki,ki umarceni duk abinda kikeso" Saurin jada baya nayi tareda girgiza masa kai. "Kalmar daka faɗa ka zama musulmi,daga yau kada ka sake durkusawa kowa bayan Allah mahaliccinka,nikuma babu abinda nakeso daga gareka,nagode ma da taimakona dakayi" Tashi yayi ya tsayah yana mamakin abinda nace,wai bana buƙatar taimako. "Eh bana buƙatar taimakonka,kaine kake buƙatar taimako nasanin addininka,saidai ni bazan iya yikamaka ba,tunda nima ban sani ba,kashiga duniyah neman ilimi tunda kana da iko" Ɗagamin kai yayi,. "Naji abinda kikace,hakiƙa sai yanzu nasan wannan shine addinin gaskiya,ba shan jini da yanka mitane na,baki faɗamin sunanki ba" "Sunana khadija,zaka iyah cemin deejah" "Hmmm nikuma sunana Tuddoor,amma yanzu nazama sumail,sunan wani aboki danayi a wajen,aka yankashi a gabana,shine wanda yafara bani labarin addinai da kuma yanda suke" "Uhm ya kyauta,saikayi tayi masa addu'a" Tafiyah mukaci gaba dayi tareda shi a cikin jejin,dan yace bazai tafi yanzu ba,baisan kowaba. Taku _sadi-sakhna_ Ƴar mutan jama'are. *MABARACIYAH* _haƙƙin mallaka_ _*sadi-sakhna*_ (Yar mutan Jama'are) 63••64 Bansan kwana biyu, uku,sati,watanni mukayi muna rayuwa dagani sai sumail ba. Nidai kawai abinda na sani shine muna kwana mu tashi,munemi abinda zamuci na ƴaƴan itatuwa,na koya masa sallah muyi,in labari yazo na bashi,shima kuma yabani labarai wanda hankali baya ɗauka. Saidai yau da kullum na fara ganin abubuwan dayake faɗamin normal. Bayan tsawon lokacin da muka ɗauka a jejin ranar saina ga garin mutane,abin yabani mamaki,a raina ina ganin kaman bamu daɗe da barin wajennan ba,amma kuma jikina yana nuna mun daɗe a wajen. "Sumail satinmu nawa a cikin jejinnnan?" "Hhhhh me kikaga kike tambaya" "Uhm naga mutanenncan shuka sukeyi,kuma lokacin da aka ɗaukeni a gidan kuma an girbe amfanin gona,mai yake faruwa" "Watanmi goma sha ɗaya a cikin jejinnan,saboda wani lokacin idan mun zauna muna yin wata biyu,zama dani ne yasa ganin tafiyar lokacinki yazama kaman nawa. Kiyi haƙuri kaman yanda kika faɗa ni yanxu zan tafi,kije ga mutane ƴan uwanki kiyi rayuwa dasu,ta hakane zaki iyah ɗaukar fansar dakike so,idan na samu wanda zanyi karatu a wajensa watarana zan zo nemanki" Yana gama faɗin hakan ya bacewa ganina,duk da zaman mu dashi inajin wani iri,amma kuma nasaba dashi sosai,yanda yake samomin abinci da tsarona innayi bacci. Juyawa nayi nafara takawa zuwa inda masu gonar suke. Suna ɗagowa dasuka kalleni suka furma da gudu,banyi mamaki ba nasan bai wuce shigar jikina ba,ɗayane daga cikinsu ya yi jarumtar tsayawa,magana yayi min amma haka kawai na tsinci kaina da ƙin amsa masa Ganin yayi yayi naƙi amsawa yasa ya ce nabiyoshi. Tafiya muke har muka iso gidan marayun dana rayu a ciki. Banyi zaton zan samu mutane dazasu taimakeni ba saida na haɗu inno dakuma sauran ƴan uwana na wajen. Tun ranar da aka kawoni sabriyya ta shiga raina,saboda yanda tajani a jikinta sosai. Tambayata tayi sunana,saidai kafin na buɗe bakina na furta mata naji ta ambaceni da sunan KHAMRIYYAH,da farko naso cemata ba sunana haka ba,saidai yanda yaran wajen suke ta dariyah suna maimaita sunan akan bakinsu yasa nayanke hukuncin zama dasu a matsayin wacce suka sakawa suna. Na yi alƙawarin duk abinda yashafi deeja na baƙinciki bazan bari ya shafi rayuwarsu ba,zan zauna tareda su a matsayin khmariyyah ƴar uwarsu,wacce batasan kowo ba sai su,sannam mai burin sadaukar da komai nata domin ƴan uwanta. Haka nacigaba da rayuwa tareda mahaifiyar dana samu dakuma yan uwana danayi,har zuwa lokacin da masu ɗaukar yara suka zo na tafi a madadin sabriyyah. Mutanen da suka ɗaukeni irin wanda suka ɗauki maryam ne,wato masu niyyar kasheni,na zauna a wajensu tsawon wata shida a wani ɗaki tareda wasu yara,sune su biggy. A wannnan wata shidane Allah yabani iko na samo hanya muka gudu,kafin nan kuma na samu information dayawa a wajen. Anan na gano Dr. Bukar da brr. Shehu da kuma saifuddeen sunada Alaƙa da wajen. Saboda koyaushe a gidan suke meeting ɗin mugayen abubuwansu. A duk lokacin dana kalli brr. Shehu a gidan ji nake kaman na kasheshi,dan sannan bansan sauran mutanen ba,kawai dai nasan saifuddeeen shiyake tura iyayen bogi su ɗauko yara a gidan marayu,ya sayarwa dr. Bukar ya cire ƙodar su,shikuma brr. Shehu ya tsaya musu ta wajen masu son yin ƙara da wasu abubuwan. Mutane uku kawai nayi nasara guduwa dasu,sune su biggy,sauran kam muna gani suka maida su gidan,suna kuka ina kuka haka muka barsu a ciki muka tafi. Cikin garin katsina muka shiga bamu san kowa ba,sai muka fara neman hanyar abinci,wankau muke a gidaje dasauran abubuwa,wani lokacin musamu aiki,wani lokacin kuma bama samu. Ganin nima ga rayuwata yanda take,kuma ina ƙoƙarin jawo wasu cikin ta. Shawara na basu akan su je gidan marayu na garin,daga nan muka rabu dasu nikuma nacigaba da rayuwata,gefe kuma ina bin diddigin mutane da duk na gani a wannan baƙin gidan. Ina cikin hakane wata rana nashiga tsangayar Almajirai,babu tsammani saina haɗu da yah shazali,yazo shida iyalansa da kuma almajiransa. Mamakin ganina yayi,musamman yanda nayi daƙa daƙa ga datti ga kuma yagaggun kayah,wasu ma ko ban tambaye su neman taimako ba ɗauka suke su bani. Sakani yayi a gaba na bashi labarin abinda ya faru,nan yake bani labarin iyah gaji tayi kuɗi sosai a garin kankia kafin ya taho,shikuma brr. Shehu anyi masa transfer shida wannan nurse ɗin zuwa garinnan. Banyi mamakin abinda ya faɗa ba,dannasan bazai wuce aikin wannan matar ba,data ruguzamin rayuwa,saboda buƙatar duniyarta. Duk yanda naso ƙin ɗora masa nauyin rayuwata,kasa barina yayi na tafi. Karatu na cigaba dayi a wajensa na addini da kuma na boko,dan burina danake dashi bazayyi yiyu ba saida ilimi. Bayan wasu shekarune shazali ya koma garin daura da zama,a nan kam ban zauna a wajensa,saina tafi inda nake ƙira da gidanmu,wato wajen su sabriyyah. Sunyi murna sosai da ganina,anan kuma naji abinda ya faru da maryam,banyi mamaki ba dannasan bai wuce aikin saifuddeen ba,zai aikata sosai. Hakan bai isa ba ya biyo gida yaimana cin mutunci,tareda ketawa anty juwairah zarafi. A lokacin banso su sabriyyah susan wannan ɗaukar fansar ba,saidai daga yanayin halin dasuka shiga irinnawa,yasa naja ragamar ɗaukar fansa,domin su samu salama a ransu,wanda suka aikata hakan kuma suma su samu hukuncinsu daidai da abinda suka aikata. Bani na tashi komawa garin Kankia ba,sai lokacin danayi cuku cuku ogah sadeeq ya turani garin aiki,dan dama hakannne burina. Abinda na gani ne ya girgizani sosai,hajiyah Gaji tayi kuɗi sosai,yayuna kuma yahuza da yusuf ta maidasu tamkar karnuka,a cewar ta wai sonsu take bayan iyayenmu sun rasu,ta sake musu kuɗi suna yanda suka so,shaye shaye da kuma aikin tantiranci,kowa zai zaginsu yake a gari. Wannan abin yafimin komai ciwo daga cikin abinda akayi min,gwanda iyayen mu su kashesu akayi,ba ɗauke su daga hanyar gaskiya ba. Yayanta mata su ta ɗorasu akan harkar kasuwanci,sukuma yayuna kashewar kawai ta nuna musu,tareda bata musu gobensu. Amma dayake Allah ba Azzalumi bane,sai ya zamo jikokinta dukka yawanci hanyar dasuka bi kenan,abin yana damunta amma kuma takasa yin komai akai. Tsara kamen ƴan iskan garin na shiryah,batareda na faɗamusu nice ba na kawosu garin katsina wajen horon matasa shashashu,har yanzu suna ciki,ina zuwa musu ziyara lokaci zuwa lokaci,tun basu san wacece ba har na sanar dasu. A nan ne sukayi kukan nadama na abinda suka faɗa ciki,saidai har yanzu ban bada izinin a sakesuba,dan har yanzu ƙwayar bata gama sakinsu ba. Hmm Hajiya gaji kuwa ta bayan fage na biyo mata,malamminta dayake mata aiki,take yiwa mutane sharri,da kuma zalunci,na ɗauke dukka yayansa,sannan nasa akayi masa dukan kawo wuƙa. Zabi na bashi akan yayi mata hukuncin dadai yanda yake ganin yayi daidai da ita,na kashe mutane dayawa,bana ma buƙatar itama nata jinin ya hau kan hannuna,dan bata kai ma matsayin hakan ba. A daren ya ɗauki alkalumansa ya turamata baƙin sammu. Manyan ƙuraje suka cika jikinta ta ko ina,ga hauka tanayi.. Bayan zama a cikin wanann azabar kuma,a sati na gaba gabobin jikinta sukayi ta gundulewa suna faɗuwa. Mutuwar walaƙanci tayi da Allah wadai,sannan kuma babu wanda ya je kan gawarta,jikokinta ne ƴan iskan suka je suka binneta. (Labarin abinda tayiwa Hajiya fulani da kuma su dr. Bukar tayi,har zuwa lokacin da Tazo gaban Alƙalin)............. ____________________________ Numfasawa tayi bayan ta gama labarin kafin ta kalli idanuwan mutanen wajen,zuwa lokacin fuskarta tayi shabe shabe da hawaye,saboda fama tsohon gyambon daya warke. "Wannan shine abinda yafaru a cikin rayuwata,kama daga haihuwa ta ,kashe iyayena,haɗuwata da su sabriyyah,kashe wanda sukayi min haka,bayan najira kotu taƙi daukar mataki,haɗuwata da iyalan gidan sarautar katsina,harma da soyayyarmu da ɗan gidan. Sannan inaso mutane wajenanan su sani,ko kaɗan bana nadamar abinda na aikatawa wannan mutane,dan haka a shirye nake naji hukuncina daga wajen alƙali" Shuru wajen yayi kaman babu mutane,kowa jikinsa yayi sanyi jin labarin abinda khamriyyah ta faɗa. Masu kuka sunayi,masu tausayawa sunayi,haka masu mamaki da shiga ruɗu. Alƙaline yayi gyaran murya tareda cewa. "Uhm uhm munji abinda kika ce,to shin kinada shaidu akan abinda kika faɗa,idan bakida shi kotu zata yanke miki hukuncin rai da rai a gidan yari" "Hmmm shaidu kake buƙata daga labarina,dan kaji ban ambaci sunanka a masu laifi ba a ciki? Duk wajennan kafi kowa sanin abinda na faɗa gaskiyane. Sannan idan naga dama bazan tsayah a gabanka na buƙaci hukunci daga alƙali irinka ba,karka manta duk rashin adalcin da akayi kaine ka zartar dashi. Batun ɗaurin rai da rai kuma bana buƙata,wata shida kawai zanyi,badan komai ba saboda nasan an min hukunci,kuma mai shirin yi a gaba shima karya tafi haka batareda hukunci ba. Idan kuma kanaganin abinda kaga dama nima zakamin,to zan bankaɗa mummunan lafinka kaima,sannan duk manyan garinnan dana gani a wannan gidan tsafin saina faɗi sunansu ɗaya bayan ɗaya a wajennan,dan kar nake kallonsu,kuma ba tsoronsu nake ba. Na baka minti talatin kayi tunani" Shuru nan ma kowa yayi,saidai daga ganin idonta kasan ba tsoro take ba,kuma zata aikata abinda tayi niyyah. Ko minti talatin ɗin ba ayi ba,saiga ƙiran daga babbar gwamnati akan a saketa yanzu nan,inkuma hukuncin takeso,to a tabbatar babu abinda ya faru da ita har zuwa ta fito,sannna ranar fitowar a shiryah gagarumar tarbarta. Wani murmushi khamriyyah tayi tareda kallon alƙalin tace. "Hmmm ƙasarmu najeriyah da baci,Allah ne kaɗai zai mana gyara a cikinta,ka bugamin takardar laifina kawai,su kuma wanda suke bayana ka wanke sunan su tass,su koma gida cikin koshin lafiya. Sannan kaman yanda nace,ka shirya bada order a fitarni nan da ƙarshen shekara" Ihune ya kaure a cikin kotun,lokacin da alƙali ya zartarwa deejah kuma khamriyyah hukuncin data buƙata. Wasu suna baza'a ɗaureta ba wasu kuma sunata zagin manyan ƙasa da abinda suke a ƙasar. Kafin su khamriyyah su fito daga kotun labarinta har ya zaga ko ina,mutane sai cewa suke tayi daidai,musamman da suka gano gaskiya ta faɗa. Fitowa akayi da ita da ankwa a hannunta,mutane sun cika hanyar da ƙyar ake wuce wa da ita.. Dec. Sadeeq ta gani shida khaleel a tsaye,kana ganinsa kamar an yi masa mutuwa. Excuse ta karba a wajen ƴan sandan ta nufi inda suke. A gabansa ta tsayah,tana zuba masa ido shima yana zubamata,zubewa tayi akan gwiwoyinta tareda sakin kukan da ita kanta rabonta da irinsa ta manta.. "Kayi haƙuri ka yafemin khaleel,nayi hakane saboda shiyafi dacewa,idan banyi haka ba hankalina a ƙarshe bazai kwanta ba. Ka yafemin fatali danayi da taimkonka a gareni kayi........" Ɗagota yayi shima yana ƙoƙarin maida hawayen idonsa. "Sai yaushe zaki daina wannan bada haƙurin,bayan kinsan baki taba burgeni ba irinna yau,kinyi abinda maza ma ba lallai su iya ba,ke jajirtacciyah ce kuma majingina khamriyyyah,Allah yabaki sa'a rayuwarki ta gaba,yasa hankalinki ya kwanta kiyi rayuwar farinciki. Zan dunga zuwa koyaushe ina miki ziyara,har zuwa lokacin dazaki dawo gareni,kisa a ranki kowa yana tareda ke" Jijjiga kai take tana murmushi hawaye bai daina zuba a kan kumatunta ba. Su fadeelah ta hango a gefe tareda su sabriyyan wanda suma kukan suke. "Haba my family,menene kuma na kukan,babu abinda zai faru,ku ɗauka naje karatu kaman koyau she,kunji twin ɗina,mommy zata dawo gareku" Rungumesu tayi a jikinta tana sauraren ƙaramar muryarsu ta kuka. Miƙewa tayi tsaye tareda karbar su sultan suma a hannun amal. "Dukka zanyi missing ɗinku kuma,Amal kiyi haƙuri da abinda na miki kinji,banyi miki dan inajin haushinki ba,nayi mikine saboda ki gyara halinki,sannan wannan takardar nine nasa kawarki ta zugaki akan ki tura,saboda a dakatar da auren sadeeq da madeena. Abubuwa dayawa nayisu batareda saninku ba,duk ku yafemin. Ku kulada kanku sosai,ke sabrah ki kwantar da hankali a gidan mijinki,kuma ƴan matana kanna dawo naji kyakykyawan labari kunji" Dukkansu sakin kuka sukayi,danji suke kaman tana musu wasiyyah. "Khamriyyah meyasa?" "Saboda banason kusha wahalar danasha,kokum labarinna ya bata muku rai,kudaina wannan maganar ya wuce haka" Mahaifiyar saifuddeen ta nufo wajen itada wata yarinya mai kamada su fadeelah,da alama kanwarsa ce. Sunkuyar dakai matar tayi tana kallon su fadeela.. "Tabbas kowa ya gansu yaga jininmu yarannnan,zanceki babu ƙarya a ciki,kuma kaman yanda kika faɗa zayyi nadamar abinda yayi yaran mutane tabbas yayi. Dan yanxu mu shiya turoni nabaki haƙuri akan abinda yayi muku,dan bashida ikon fuskantarku a yanzu,yara kuma komin sonsa daganinsu dole zai haƙura,kuma zancenki haƙƙun saidai yagani a wajen wasu" Tana maganar muryarta tana rawa ,itama kana ganin danasanin sangarta yaron datayi. "Babu komai hajiya,dama wanda yayi ba kyau dole zaiga ba kyau,naji dadi daya gane gaskiyah,koba komai shiɗin ubansune ko an so ko an ƙi,sannan kice masa dukiyarsa nina ɗebe ta,diyyar hajja da kuma anty zuwairah,sannan kuma nayi amfani da sauran a rayuwar ƴaƴansa" "Zaiji wannan saƙon,inshallah zaki ganmu ranar da kika fito daga gidan yari" Iyalan sauran wanda abin yashefesune suma suka zo inda khamriyyah take,harda mrs. Shehu wacce ta mareta,kana ganinta yanzu kasan cikin kunya take dakuma tirrr da halin mijinnata,tana ta yaba halinsa,batasani ba ashe shiɗin makashine,kuma masifah a cikin al'ummah. Haka ma dr. Bukar,a ranar aka rufe asibitinsa da kuma wasu abubuwansa,domin kwakwkwaran bincike. Bayan an gama neman yafe yafenne khamriyyah ta juya zuwa motar daza'a tafi da ita,mutane kowa na faɗin albarkacin bakinsa. Suma su khaleel mota suka shiga zuwa gida,haƙika shari'ar tazo masa a bazata ba yanda ya tsammata,amma hakan ma yayi,koba komai yaji farinciki da kwanciyar hankali daya gano tsagwaron murna jinjina a idon mutanen wajen,hakan ya ƙara tabbatar masa da masoyiyar tasa ta musammance..... Muhaɗu a chapter ta gaba wanda kuma itace ta ƙarshe inshaallah....... Taku _sadi-sakhna_ Ƴar mutan jama'are. *MABARACIYAH* _haƙƙin mallaka_ _*sadi-sakhna*_ (Yar mutan Jama'are) 65••66 _Bayan wata shida_ Wani mutum ne ya nufi taron mata guda shida suna zaune da uniform ɗin prison a jikinsu.. Khamriyyah ce a tsakanin su tana ɗoramusu karatu,wasu acikinsu sun fita ma a haife. Gaisawa sukayi kafin yace. "Madam shugaba yana ƙiranki a office,yaune ranar tafiyarki,har na kawo takarda daga sama,da kuma mota da kaya na rakaki gida" Ɗaga masa kai kawai tayi batareda tajiyo ta kalleshi ba,tundaga yanayin fuskar matan zaka san cewa sun saba da ita sosai,basa son fitarta daga wajen,saidai hakan shine mafi alkhairi ga duk wanda yashiga irin wannnan gidan. Tashi tayi tareda yimusu murmushi. "Karku damu yan uwa,zan dunga kawo muku ziyara har ku fita,idan kun fita kuma ku taho gareni,zan taimaka muku idan inada dama" Ɗaga kai sukayi,daga haka ta bar wajen zuwa inda mutumin yabi.. Cike ciken takarda akayi a office ɗin,daga nan shugaban ya ɗago kansa ya kalleta. "Madam yau kin gama wa'adinki na zama a gidannan,an wanke sunanki daga dukkan wani laifi da kika aikata,yanzu kina da damar dazaki koma ga dankinki domin kafa sabuwar rayuwa tareda su" "Nagode sir" "Babu komai,yanxu ki shiga nan lubna zata baki kaya ki saka,daga nan familynki suna jiranki a waje" Ɗaga kai khamriyyah tayi tareda bin inda ya nuna mata da yatsa. Wanka tayi da sabulu mai kyau ba irin wanda suke amfani dashi ba a banɗakin,kafin ta fito ta saka kayan ta taimakon matar da ya ƙira da lubanan. Doguwar rigace baƙa sai gyalen shikuma ja,irin adon rigar. Kayan sunyi mata kyau sosai,dan ma tayi looosing farinta ba kaman da ba. Fitowa sukayi tareda matar zuwa bakin get ɗin,inda take hango motocin masarautar katsina a wajen. A hankali take takawa kirjinta yana bada sauti mai ƙarfi,rabonta da kasancewa a waje,tun wata shida baya,ko zuwa akayi mata saidai ta kallesu ta bayan labule.. Da ɗaɗdai da ɗaɗɗai mutanen cikin motocin suka fara fitowa. Sabriyyah,khairiyyah,khaleel,sadeeq,inno,jalal,amal,madeena,hajiyah saratu,hajiyah deejah,meena,yah yusuf da yah yahuza,maryam,farida,balki,doc nawwarah,twins ɗinta(fadeelah,fadeel,sultan,sultana),saifuddeen da ahalinsa dukka. Su biggy,da wasu dukka mutane daban. Kuka khamriyyah ta saka tareda zubewa a ƙasa,lokacin dataga ɗumbin mutanen da suka zo taryarta. Su khairi ne suka rugo da gudu tareda rungumeta,da a tsaye take da sai sun jefar da ita. Dariyah suka sa ganin suma abinda yabasu dariyah,hakika sunyi missing ɗin ta sosai,tareda jiran sauraran zuwan wannan ranar. Idonta ta ɗaga ta sauƙe akan khaleel,wanda ya ɗan rame yayi duhu,bayyi kama da wanda yayi jinya ba,tasan bazai wuce tunanin halin da take cikiba. Idonta tasake sauƙewa akan yayunnata gudan jininta,wanda suke tsaye cikin nutsuwa kaman basuba,murmushi suke yimata mai cikeda nuna alamar nasara a ceto hankalinsu. Wajen da khaleel yake ta nufah tana sake masa murmushi,amma sabanin haka ɗan turbune fuska yayi,bazata ce kai tsaye da ita yake ba,tasan bai wuce tace ita hankalinta kwance ba,bata missing ɗinsa,dan abinda yake faɗa kenann kullum idan ya ƙira wayah an bata. Wajen su yah yahuza ta nufa tareda rungumesu batareda tace komai ba. Suma sakata sukayi a jikinsu suna jinjina ƙoƙarint,a,da kuma tausayawa halinda tashiga,domin gani suke kaman komai laifinsu ne,da suka kasa kulada ita,har wahalar rayuwa tayi mata yawa.Saidai alhamdulillah yanzu komai yayi daidai. Dukkan su garzayawa akayi fadar,inda aka shiryah gagarumin biki na taryarta zuwa gida.. A ranar khamriyyha taga soyayyar dasuke mata ya wuce yanda take mamaki,a tunaninta da ƴayan hajiyah fulani ateeka zasu tsaneta idan suka gano abinda tayiwa mahaifiyarsu,ga mamakinta ma sai haƙuri suke bata tareda roƙar ta manta abinda ya faru. Tunda suka dawo bata samu kona mintin ɗaya ta zauna ba,mutanen datayi rayuwa dasu harda na makarantarsu sai zuwa ake mata barka da fitowa,harda iyalan wanda tayiwa tsiyah,sune yanzu a cikin kunya,dan wasu daƙyar suke haɗa ido da ita. Dare mahutar bawa,saida magriba tayi kafin aka fara raguwa da mutane,wasu sai cewa suke sai wani sati kuma,bata gane mai suke nufi ba,itama kuma bata samu lokacin tambayarba. Ɗakinsu ta shiga tana yada kai na gajiyah. Kayan jikinta ta cire,wani yadi mai tsadar gaske,wanda sukayi anko da dukkan matan gidan,walima akayi wacce ta kayatar sosai. Banɗaki ta wuce tasakewa kanta ruwa mai sanyi,saida ta tabbatar sanyin ya ratsata kafin tashiga bahon wanka ta gasa jikinta sosai. Lokacin data fito duk an idar da sallahr magriba,dan haka haɗawa tayi da isah tayi,wacce ta taddata tana addu'a. Amal ce tashigo hannunta ɗauke da kwanon abinci ta ajiyemata. "Anty ga abinci,nasan baki samu kinci dazu da yawa ba" "Hmm kaman kuwa kin sani,duk jikina a mace yake" "Tabbb gashi kuwa yah khaleel da ina shigowa yace yana jiranki a wajen dakuka saba haɗuwa" Wata kasalalliyar ajiyar zuwa khamriyyah tasake tareda ɗaga kanta kawai,yazatayi tasan bata isa kawo masa uzurin bazai samu ganinta ba,bayan tafi kowa sanin yanda ya ƙagu ta dawo gareshi. Riga marar nauyi tasaka ta murza humrah kaɗan,daga nan tasaka hijabi tafita inda suke zama lokacin yana eemran tana deejah. A zaune ta hangoshi yana daddana waya da alama ya ɗan dade yana jiranta. Sallama tayi masa ya amsa ba tareda ya ɗago idonsa ba. Itama bata sake cewa komai ba tasamu waje ta zauna. "Fushi kake dani yah khaleel,mai nayi haka?" "Hmm khamreee nayi kewarki sosai,bansan iya adadin lokacin dana zauna tunanin fitowarki ba,gani nayi kaman shekara shida nayi ina jiranki ba wata shida ba. Kiyi haƙuri ba fushi nake dake ba,kawai ganin yanda mutane suka tarene suka hanani ganinki ni kaɗai na more" Yar dariyah khamriyyah tayi,soyayyarsa tana ratsata tace. "Nima nayi kewarka sosai,saidai alhamdulillah,yanxu duk wani abu daya tsayamin a zuciya na tsawon shekaru ya tafi,na yiwa wanda suka aikata ba daidai ba hukuncinsu,sannan nima kuma na karbi nawa hukuncin na gama,sai nake jina kaman wata sabuwar mutum a duniyar" "Ina fatan kuma wannan sabuwar halittar ta fara sabuwar rayuwa tareda ni,ta zauna a gefena har zuwa lokacin da Allah ya zai rufe mana ido,ta kasance abokiyar rayuwata sannan kuma uwar iyalina. Shin wannna halitta zata amince nazama mijinta kuma sirrinta,sannan farincikinta?" "Wannan halitta ta amicewa masoyinta ɗari bisa dari,batareda na nadama ko dana sani ba" Murmushi khaleel yayi najin daɗi tareda cewa. "Mashaallah,alhamdulillah bi ni'imati hi,dama ke ake jiran dawowarki na nemi amincewarki,anriga an gama shirin bikin da kuma inda zamu zauna,saidai mu bazamu dade ba,zan koma ƙarin karatu china,inda nayi karatu,tare zamu tafi wani watan. Amarya saiki shiryah ɗaurin aurenki wani satin,wani watan kuma barin ƙasar ya kamaki,kafin sannan saiki samu ki huta gajiyah,bazamu zauna a kasarnan ba yanzu" " umm Amma kuma naji ana cewa mai martaba zai ɗoraka akan sarauta koh,yana buƙatar hutu" "Ahah bazan kama zaman basirr ɗinnan yanzu ba,bangama cin gashin rayuwata ba,shima saida ya shaƙata kafin ya hau mulki,beside ban tara yara ba nayi rayuwa dasu irinta ko wane uba,saina fara zaman fadanci,inaaa there is time babyy,before let we chill okay?" Ɗaga masa kai khamriyyah tayi tana dariyah,dan itama tana buƙatar adjust ɗin rayuwarta kam kafin ta fara cuɗanya da sha'anin mulki. Daga nan akalar hirarsu ta sauyah zuwa ta masoyah masu begen junansu. Tundaga ranar da labari ya jagaya khamriyyah ta amince a haɗa a aurensu dana su khairiyyah da deen,madeena kuma itada wani lecturer su da yake sonta,saleem ma yaso a haɗa nasu shida amal,amma firr taƙi,a cewarta saita shiga jami'a tukunna ta fara,kuma ma bata son a haɗa bikinta dana wasu,bazatayi shagali a bikinba inda ita aka haɗa. Biki aka fara ba kama hannun yaro,inno ta taka rawar gani wajen yi musu gyaran jiki ta kuma bangaren tasirin turare da sauransu. Ita kuma hajiyah saratu takanass tashiga jirgi ta nufi dubai itada hajiyah deejah sayo kayan ɗaki,iri ɗaya akayi musu,kala ce kawai ta bambamta. Rana bata ƙarya kuwa,sati yana zagayowa aka ɗaura auren ƴan matan gidan,abinka da hannu da shuni,nan da nan akayi shiri da kuma yin duk abinda ya dace. Dukkansu kowacce sarki yabata alƙyabbar daza'a kaita,khamriyyah surukarsa,su khairiyyah kuma yayansa na jini,dan haka dukkansu sun cancanci samun Al'adar sarauta kafin kaisu gidan miji,duk da kana gani kasan yafiji da matar Babban ɗannasa na jini,surukarsa ta farko wacce aka kawo basu suka kai ba. Bayan haka kuma aka haɗasu da kyaitukansu dasuka samu daga manyan gari. Dan har dangin Hajiyah Ateek ma sun ƙarbi khamriyyah hannu bibbiyu,tunda sunsan yar uwarsu ce take da laifi,sannan kuma mai ya faru ya zasuyi,soon zasu haɗa jini da khamriyyahn,dan haka babu abin wani boye boye. Bajinta suka zage suka nuna a nasu na matsayin shuwa,kakan Khaleel kam harda kyautar Dadduma da kuma Alqur'ani mai kyau ya aikowa amaryar tasa. Madeena kano aka kaita,khariyyah kuma ana cikin katsina,haka ita ma khamriyyah. Da farko mai martaba yaso khaleel ya zauna a cikin gidan,amma ya ƙi yadda sam,shiyafi son rayuwar privacy da kuma rashin hayaniya. Duk wanda ya kalli gidajen amaren dole zai sake gani ya jinina,domin kowa anyi bata barin dukiyah da kayan alfarma. Masu kaiwa khmariyyah harda sabrah a ciki,wacce yayanta suke ta mata kukan zazzabin haƙori sun rame kaman basu ba. Bayan kowa yayi hanyar falo sabrah ta kalli khamriyyah wacce take zaune tana game a wayarta,babu alamar damuwa ko kaɗan. "To da farko dai ƴar uwa kinsan aure shi ba abin wasa bane......." "Sai kuma nace abin wasane,kinga dan Allah karki dameni da surutu kacan danki yanata kuka a falo kije ki karbeshi,wannan abubuwan sau nawa za'amin bitarsu ne,batun yin biyyaya dama ni nace ina so,dan haka basai kowa yacemin nayi ba," Dariyah sabrah tasaka tareda dungure goshin khamriyyah wacce take ta zuba kaman yayan kanya. "Ke dallacan,daga yin magana harkin fara masifah,wato missing ɗina ma. Bakyayi koh" "Innayi missing ɗinki saina zauna nayi ta kuka koh,idan ina kewarki zaki ganni a gidanki,yanzu dai ki tattara mutanen falon can ku tafi,dare yayi gasu matane kusan dukkansu da goyo" Daga haka khamriyyah tazari kayan baccinta ta nufi banɗaki. Sakin baki sabrah tayi tana kallonta,daga nan ta jijjiga kai tana zaki ƙwala a ranta. Bayan khamriyyah tayi wanka,saida ta tsaya tayi na turare yanda Anty yagana ta faɗamata,ƴar autar su hajiya fulani ateeka. Ta daɗe kafin ta fito daga banɗakin tana gyara igiyar rigarta. Turus tayi ganin mutum akan gado sanye da pyjamas shima ya zuba mata ido. "Uhm miye na tsoron,kicigaba da tafiyarki mana" Ya faɗa yana ƙaremat kallo. Kafesewa tayi tareda zuwa kusada shi ta zauna bakin gadon. "Yaushe kashigo,kenan na daɗe sosai?" "Uhm ba sosai ba,ina kin iyo Alwala,yakamata muyi yanda ake a darennan,dan ya fi albarka,bamu tsayah sai wani lokacin ba" Daga kanta tayi alamar tayi alwalar,daga nan ta dauki hijabinta ta saka,yajasu sallah raka'ah biyu. Sun daɗe suna addu'oi,zuwa lokacin khamriyyah ta jera hamm sun fi a ƙirga. Ganin hakan yasa ya dakata suka hau gadon. Duk da baccin dayake cinta sosai,amma tanajinsa yana sarrafa jikinta ta kasa yunkurin hanashi,tausayinsane ya kamata,ganin ita kanta shaidace shi mutum ne mai gudun abinda yake haramun gareshi,ita wacece kuma dazata hanashi halal ɗinsa,bayan tsawon shekaru daya ɗauka yana jiran zuwan halal ɗin,yajure ɗauke kansa daga haram duk rintsi duk wuyah,irin wannan mutumin zata hana hakkinsa dan kawai bacci yana cinta,inaaa bata fatan takasance cikin wannan matan. Ita macece marar tsoro,amma kuma mai matuƙar bin matakin yanda ya dace koda kuwa zata danne muradin nata zuciyar. Sakin dukkan jikinta tayi,tareda miƙa masa dukka ragamar sirrinta da kuma akalar rayuwarta,har xuwa lokacin daya kai matakin maidasu abu ɗaya ita dashi. (Wanda sukeda aure Allah ka zaunar dasu lafiya a gidajensu,ka albarkaci rayuwarsu data yayansu. Wanda kuma har yanxu Allah baka basu damar yi ba,Allah yabasu miji nagari,wanda zaija ragamar rayuwarsu har zuwa ga matabbata mai kyau.) _____________________________ _Bayan shekara ɗaya a china_ Khamriyyah ce a tsaye a bakin kofar ɗakinsu sai bubbuga kafa take tana sangartar gangan. Tayi tuleliyah ta ita,tundaga kafatunta har zuwa fuskarta. Tayi fari kam sosai,saboda tsohon cikin dayake jikinta. Duk abinda takeyi Khaleel bai kulata ba,saima cigaba yayi ta ciro mata kayan ta daga cikin drawer ta. "Wai ni yah khaleel nace maka lafiyata kalau,kalli fah yau har breakfast nayi mana,nayi excersice ɗina ma nasafe" "Ban yarda dake ba,jiya kwana kike kina saƙƙowa kasa daga kan gado kina murƙususu,akwai abinda yake damun babyna kike boyemin,kima daina wannan gardamar kizo na shiryaki mutafi asibiti ehe. Duk nasan wayonki bai wuce kice kin kalau kike ba,gobe mukama hanyar komawa gida,ba inda zan tafi dake cikin jirgi a haka,so kike haihuwa tazo miki a jirgi murasa yanda zamuyi?" "Niba haihuwa zanyi ba,lokacin fab bai zoba tukunna,nina gaji da wannan kasar chanhu chanhu ɗin,mutafi gida kawai,khariyyah ma ta haihu banje ba nina gaji da wajennan. Yanxun ma cikin rigima ta karishe maganar ,inda sabo ya saba,kullum tana cikin kuka da gardama,abinda batayi da ba shi cikin yasaka mata sosai. Hannunta ya jawo suka nufi banɗaki,sai cuna baki take. Sun kusa awa kafin suka fito da towel a jikinta,kayan yake bata tana sakawa,inda bata kai ba kaman zuge ziff yayi mata,har sannan taƙi sakin ranta. Ɗaukar ta yayi ya kaita har mota ya ajiyeta,daganan yadawo ya kulle gidan suka tafi. Tun a hanya take riƙe bayan ta tana yarfe hannu,shidai yana kallonta bai ce komai ba,sai waya dayayiwa midwife dij datake dubasu,akan gasunan zuwa,sanan ya kara gudun motar. Suna zuwa aka wuce da ita labor room,shidama ya kula naƙuda takeyi da daddare,irin tsayawa tayi da safe,shiyasa tace masa kalau take,tayi zaton bai ganta ba. Jijjiga kai kawai yayi yana murmushin halinnata,abin mamaki kuma a tsawon lokacin bai taba jin ya gaja da sauraranta ba,saidai in yan miskilancin suna na yayi mata shuru. Yana cikin tunaninne yaji an tabashi ta baya.. Yana juyawa suka haɗa ido ta nurse ɗin da baby a hannunta cikin towel,zaro ido yayi yana tunanin karba,dan bai kawo a ransa nasa bane. "Congratulation,you have beautiful baby daughter,you see the mommy if you like,she is in good condition" Tun kafin tagama bayaninta ya nufi ɗakin da khamriyyah take ciki. A zaune ya babu kowa a ɗakin sai nurse masu gyara wajen. Zama yayi rungumeda babyn a hannunsa har khamriyyah ta fito daga banɗakin. Kallonta yake cikeda tsantsar ƙauna har ta isa inda yake ta zauna tareda ɗora kanta akan kafadarsa. "Nagode daka fini sanin kaina da kaina habeebty,ina kewar su inno sosai,nasan ka faɗamusu koh" "Uhm na fadamusu,muma jibi zamu tafi a private jet na binciken nigeria dasuka zo,ina kin tabbatar bakyajin matsalar komai koh?" Da sauri ta ɗaga masa kai tareda washe baki da murmushin jin daɗi. "Nagode sosai my king" "Ur welcome my queen,ummu zahrah" Dagowa khamriyyah tayi daga rungumar da tayi masa tareda cewa. "Sunan daka sama kenan? Sunan wa taci?" "Ba sunan kowa ba,sunanta a sakamata saboda darajarsa" "Allah ya rayata da imani,yabamu ikon rainon tarbiyyarta bisa turbar gaskiya" "Ameen ya Arhamar Rahimeen" Thammat bihamdullillah. Anan na kawo karshen littafin mabaraciya,muna fatan Allah ya yafemana kuskuren da mukayi,wanda mukayi daidai kuma Allah ya bamu ladansa. Ina fatan an fa'idantu sannan kuma an nishaɗantu da fasaha ta. Allah ya hadamu da alkhairinsa a wani littafin inda kwananmu. Masoya da ƴan uwa musulmai inayiwa kowa fatan Alkhairi,dan Allah a yafemin idan nayiwa wani laifi ko kuma na soki wani ta wani bangare na littafinnan,rashin sanine. ALHAMDULILLAH. Taku _sadi-sakhna_ Ƴar mutan jama'are.