*MU GANI A ƘASA...* _Hot Love_ ©FATIMA SUNUSI RABIU UMMU AFFAN _GAWURTATTU BIYAR._🔥 *Page 1-2* *Godiya ga Allah (S A T) da ya sake bani dama da iko da sake zaman rubuta muku wannan labarin, dubun tsira da aminci su ƙara tabbata ga manzonmu Annabi Muhammad (S A W). Da fatan zaku bini sannu a hankali domin jin inda wannan karon labarina ya nufa.* _Haƙƙin mallaka na Ummu Affan ne, ban yadda a juya mini labari ta ko wacce siga ba, ko ɗaurawa a wata kafa ba tare da izini na ba, yin hakan kuskure ne. Sannan ƙirƙirarren labari ne, ban yi shi domin kowa ba idan yazo daidai da rayuwarki/ka a rashi ne._ *_Ɗungurungun littafin nan sadaukarwa ne ga Auntyna Ƴar'uwata Ta gaban goshina ta ƙasan zuciyata MARYAM MODIBBO wato ADDA Maman Hamdana da Hamd. Ke ɗin ta daban ce Zinariya kike a zuciyar Abbansu Humaid._*🙈💃😍 *Masu san na musu talla a pages na littafina zasu iya magana cikin farashi me sauƙi mai tallah shi ke da riba.* _Bismillahir rahmanir rahim._ *ABUJA NIGERIA* Sanyayyiyar iskar damina ce ke kaɗawa a daidai lokacin, gari ya yi luf da ni'ima ya yin da sararin samaniya ya yi fayau dashi gwanin burgewa da ban sha'awa. Tuƙi yake cike da ƙwarewa yana sharara gudu saman lafiyayyar kwaltar da ke birnin tarayya Abuja. Yayi tafiya me nisa kafin ya iso babbar unguwar tasu ta Asokoro. Wani katafaren gate ya dosa inda ya buga hurn, da sauri Maigadi yazo tare da wangale mishi ƙaton gate ɗin ya kutsa hancin motar shi ciki. Sannu da zuwa Officer ke masa hannun shi kawai ya iya ɗaga mishi. A cikin babban harabar gidan ne ya samu guri ya yi parking, kusan minti biyu kafin ya iya zuro ƙafarshi daga motar, ƙafar tashi mai sanye da ƙayatattun baƙaƙen takalmi sau ciki ce ya zuro a hankali kamar mai tsoran fitowa. A hankali kuma sassan jikin ya fito da shi, "Ma sha Allah" Ƙyaƙƙyawa ne ajin farko. A hankali yake tafiya kamar mai tsoran takawa hannun shi ɗauke da ƙatuwar wayar shi yana duba saƙon da yaji shugowar sa tun yana tuƙi. Dan tsaki yaja ganin mai saƙon kafin ya zura wayar cikin aljihu ya doshi hanyar da zata sada shi da parlourn gidan. Da gudu ta taso tare da nufarshi da niyyar faɗawa jikin shi "Oyoyo Yaya Aliyu!" Ta furta da tsantsar farin ciki. Saurin dakatar da ita ya yi ta hanyar ɗaga mata hannu, chak ta tsaya jiki a matuƙar sanyaye. Ƙarasawa Yayi gaban Amminsa dake tsaye tana kallon abin da ke faruwa. Zaunawa yayi saman Cushin yana me duban Ammin tashi. "Barka da hutawa Ammi!" Ya furta cikin sanyi bazaka taɓa cewa shine yayi maganar ba, sakamakon laɓɓansa ne kawai suka motsa idan ma ba kusa dashi kake ba, ba lallai ne kaji me ya furta ba. Wani kallo ta ma shi ba tare da ta amsa ba, ta mayar da kallonta ga yarinyar da ya nunawa ko in kula wacce ke tsaye kamar gunki har zuwa lokacin. "Sareenah tsayuwar ta isa haka, ko baki gaji da kallon nashi ba ne?" Cike da kunya tayi wani far! Sai ta juyo a sanyaye tare da zama gefen shi. "Abuturrab har yanzu halinka na nan ko? Ko ka mance wacece Sareenah a gareka ne?" Wuci ya fesar me zafi kafin ya ce"Ammi yunwa nake ji" Ya faɗa da nufin ɓangarar da wancen zan cen. Kallonsa take ko ƙittawa babu, wani murmushi ta saki wanda ita ce kawai tasan ma anarsa kafin ta kalli Sareenah "Ki kai mishi abinci part ɗin shi" "No Ammi!" Ya furta kamar zai yi kuka. "Ki kawo mishi anan" Girgiza kai yake amma ya kasa cewa komi sakamakon kallon da Ammi tayi mishi. Tashi tayi a gurin yabi bayanta da kallo har ta ƙarashe hawa saman benen, sanyayyar ajiyar zuciya ya saki ƙirjin shi na wani irin bugu. Bai san time ya ɗan ja yana gurin zaune ba sai da Sareenah ta ƙara so tare da ajiye tray ɗin dake hannunta. "Yaya Aliyu ga abincin!" Ta faɗa tana ƙoƙarin zama gefensa. Da sauri ya miƙe yana jifanta da wani mugun kallo, ƙala bai iya ce mata ba ya miƙe tare da nufar ƙofar parlour. "Abincin fa? Ko na biyoka da shi part ɗinka?" Ta jero mishi tambayoyin a lokaci guda, juyowa bai yi ba balle tasa ran zai amsa mata. Yana fita kai tsaye part ɗin sa ya dosa, komi fes-fes kamar yadda ya zata. Kai tsaye bedroom ya wuce yana zuwa komi na jikinsa ya cire tare da faɗawa toilet, wanka ya yi ya ɗauro alwala sannan ya fito ɗaure da towul ɗaya a hannunsa yana goge sumar kan shi. Mirror ya nufa inda ya shafa maya-mayansa tare da feshe jikinsa da turaren sa mai daɗin ƙamshi, Ƙananun kaya ya saka dogon wando tare da riga t-shirt sai ya ɗora wata me kauri ta sanyi me haɗe da hula, sakamakon yanayin garin na sanyi. Ya so ya huta amma kiran sallar ta Azahar da ake ƙwala kira a masallacin ƙofar gidansu ne ya sashi nufar hanyar fita daga badroom ɗin. Yana fita kai tsaye masallaci ya nufa. Sareenah bayan fitarsa da gudu ta hau sama bedroom ɗin Ammi, tana shiga ta sami Ammin na waya da gudu ta ƙarasa tare da faɗawa jikinta ta saki wani kuka. Ba shiri Ammi tayi sallama da wacce suke wayar tare da sanar da ita anjima zata kirata. "Sareenah lafiya kuwa?" Ammi ta tambayeta bayan ta ajiye wayarta saman ƙaramar durowar dake kusa da ita. Cikin kuka wanda zallarsa shagwaɓa ne da sangarta ta ce "Ammi Yaya Aliyu ne! Mene ne na masa ya tsane ni haka?" Da sauri Ammi ta katseta ta hanyar ɗaura ɗanuatsanta saman laɓɓan Sareenah "Kar in kuma ji" Ammi ta faɗa tare da kawar da ɗan yatsanta kafin tacigaba da cewa"Shi har ya isa? Bai kai matsayin tsanarki ba Sareenah kicigaba da shige masa kamar yadda na nuna miki a juri zuwa rafi dai, nasan dole wata rana tulu zai fashe." "Har zuwa yaushe ne tulun zai fashe Ammi? Kin san dai yarda Yaya Aliyu ke zuciyata!" "Ke dai Sareenah albasa ba ta yi halin ruwa ba, da tayi tabbas ba za ta yi yaji ba tun da har na ce miki haka to ki ɗauka mana, kin san bana san ɓacin ranki" Ammi ta faɗa tana sharewa Sareenah hawayen dake zuba a fuskarta. Numfashi ta sauke tare da lafewa jikin Ammin tana sakin ajiyar zuciya akai-akai, sannan tasan wacece Ammi bata faɗin ƙarya sai abin da ke ƙasan zuciyarta. Fitowarsa daga masallaci ba ɓata lokaci ya ɗauke key ɗin motarsa, cikin tafiyarsa ta alfarma ya doshi harabar gidan, tun daga nesa ya dannawa motar key ta buɗe yana zuwa ya faɗa ciki tare da kunnawa. A ɗari ya fita gate ɗin gidan daman tuni Maigadi ya buɗe masa tun lokacin da yaga ya doshi motar. Wani gidan abinci ya nufa na manya sai wanda ya amsa sunansa ke cin abinci a gurin. "Barka da zuwa ƴallaɓai" Wata murya siririya ce tayi maganar. Bai ɗago kan shi ba, tun bayan zamansa saman kujerar haka jin maganarta bai sa shi jin zai ɗago ba, duk kuwa da jin bugun zuciyarsa da ya tsananta. "Me kake buƙata?" Maganar ɗazu ta ƙara ratsa masarrafar sautin sa, bai ce ko ci kanki ba wata farar talarda ya ga an ajiye mishi, sai lokacin ya kai idanuwansa kan takardar, abinci ne da nasha da dangin na ƙwalama kala-kala rubuce a jikin takardar. Pen ya ciro gaban rigar shi tare da making abin da ke buƙata tare da ture takardar da baya jin zai iya magana miskili kenan kafi mahaukaci ban haushi. Ta ɓangarenta kuwa tun bayan parking ɗinsa Madam (Shugabar gurin abincin) Ta ce"Ke *Tataah* ga kostoma nan jeki gurinsa" Cikin sanyinta ta miƙe tana ta fiya sulow kamar yarda take, daidai zamansa ta ƙarasa tare da tambayarsa abin da yake buƙata. Jin shuru ta ɗago idanuwanta ta dubesa, gabanta taji ya bada dammm! Haka ta daure ta kuma tambayarsa cikin sanyi amma bai bata amsa ba sai ta saka mishi takardar tana mai jin haushi a zuciyarta sakamakon ko in kula da ya nuna mata. Ganin abin da yayi a ranta ta ce"Uhmm! Masu abu da abin su, tabbas a rashin kira karen bebe ya ɓata" Tana duba irin wannan izza da girman kai na wannan mutumin. Lokacin da Madam ta ce taje tsoro ne ya fara ɗarsar mata sakamakon yadda ƙadangarun bariki ke kai mata haushi a gurin, tana tsananin tsoron zuwa tambayar abin da masu sayen abinki ke buƙata saboda wasunsu maganar banza suke mata, a kallon farko ta ɗauka shima hakanne musamman da ta ganshi matashi sai ta fuskanci maganar nan ta kowa da halinsa amma wannan kuma girman kai ke damunsa, da wannan tunanin ta ɗauki takardar tare da nufar gurin Madam ta miƙa mata. Komi da ya buƙata aka haɗa masa tare da ba Tataah ta kai mishi, tsaye tayi a gurin tana kallon yarda yake danna wayarsa bai damu da kallon kowa dake gurin ba. Jin tsayuwar mutum kuma ba a ce komi ba ya sashi ɗagowa a hankali, idanuwansu ne suka gauraya da na juna, sauran kaɗan tiren hannun Tataah ya sun ɓule saboda tsorata da tayi da yarda da tsinci gabanta na dukan tara-tara. Da sauri ya saka hannun ya amshi Tray yana jan dogon tsaki duk da shima yaji shock a haɗa idanuwansu amma ba zaka taɓa gane hakan ba. Wani banzan kallo ya aika mata da faɗin "Noneses baki da hankali ne zaki ɓata ni?" Da sauri ta juya tare da barin gurin. Duk bayan saƙon ɗaya sai yaja tsaki jin zuciyarsa ya yi sam babu daɗi, yunwar da yake ji ne yasa shi buɗe abincin ya fara ci, amma da ya tuno fuskarta sai yaja tsaki da haka ya cika cikinsa, Drink ya ɗauka yana sha a hankali yana amsa wayar da ake ta kiransa tun ɗazu. "Aliyu ka shugo ne?" Abin da aka faɗa daga can ɓangaren kenan, sai da ya kurɓi lemunsa ya haɗiye sannan ya furta "I akwai wani abu ne?" "Ɗan renin wayau, mu muna nan muna jiranka kana shanya mu!" Robar lemun ya ajiye tare da cewa "Faruuk bacci zanyi" Ƙit! Ya katse kiran daidai miƙewarsa. Gurin biyan kuɗi ya dosa tare da barin gurin cikin sauri. Tataah dake leƙensa ganin yarda motarsa ta fita harabar gurin a sittin ta sauke numfashi nan take kuma idanuwanta suka kawo ruwa, kawar da abin da yazo mata tayi tare da dosar gurin zamanta. Ba ita ta bar gurin ba sai gabda magrib lokacin da ma'aikatan dare suka iso, gurin Madam taje inda ta bata sallamarta na ranar. Ƙarasawa tayi gurin kayanta tare da ɗaukar babban hijabinta da ke gurin wanda ya tsufa sosai, sakawa tayi ta ɗauki ƙaramar jakarta tare da kularta. Madam ta kai mawa ta zuba mata abincinta na rana da na dare wanda take basu, to ita bataci sai zata tafi take amsa. Kai tsaye bakin babban titin ta nufa domin samun Kekenapep da zai mayar da ita gida, ta tare kusan napep uku amma rashin daidaitawa yasa suke wucewa domin a kullum nera ɗari biyu ta ware domin zuwanta gurin a ɗari ta koma ɗari, idan bata samu wanda zai kaita a hakan ba to tana haƙura har ta samu. Tana tsaye gurin rungume da kularta da jakarta, yadda garin ya kaɗa hadari ne ya bata tsoro duk ta cure guri guda, tsoranta ɗaya karta ƙara hamsim ya zama ɗari da hamsim taci bugu gurin Gwoggonta domin duk wanda ta tsayar haka yake ce mata. Shada tayi akan ta sayar ta hau tasan dai bugu kam sai ta shashi haka ta fara ƙoƙarin tsayarwa amma duk wanda ta tsayar basu tsayawa sakamakon hadarin da ya ƙara turniƙe garin na Abuja har yayyafi aka fara, duk ta tsure sai kama hijabinta take daidai tsayuwar wata ƙatuwar mota. "Yan mata ina zaki?" Mai motar ya tambaya bayan yayi parking ya buɗe gilas ɗin gaban motar. Gabanta ne ya buga amma bata da zaɓi dole a wannan lokacin tana amsa mishi saboda tana buƙatar temakon nasa tabbas. Cikin rawar murya da sanyi ta ce"Maitama zani" "Hanyar za mubi zo mu rage miki hanya" Ma tuƙin motar ya faɗa domin sai yanzu na lura ashe su biyu ne cikin motar, matasa ne da baza su wuce 32 ba, ba yadda ta iya dan har ruwa ya fara sakkowa, ganin ya buɗe mata back sit da sauri ta shiga tare da furta "Na gode" Tun da suka hau titi ba wanda yayi magana har suka isa Maitama sai lokacin Matuƙin motar ya tambayeta inda zai ajiyeta domin an tsuge da ruwa sosai. Da sauri ta ta ɗago fuskarta domin ta cure guri guda sanyin gari da na Ac dake kunne a motar ya ƙara mata jin sanyi gashi daman basu shiri da sanyi har wata ƴar kyarma take. Kwatanta masa tayi har ƙofar gidan da suke zaune ya kaita. Tana niyyar fita ya ce"Sunana Faruuk ke baki faɗa mini naki sunan ba" Gabanta ya buga sosai "Faruuk!" Ta nanata cikin sanyi ta ce"Na gode sunana Tataah!" Daga haka ta fita da sauri, da gudu ta shiga cikin madaidaicin gidan. Tana motar Faruuk yayi abokinsa dake gefe mai suna Ma'aruf ya ce"Faruuk ka cika kwashe-kwashe daga temako mene ne kuma na faɗa mata sunanka da tambayar nata, bakaji rainin wayaun da ta maka ba wai Tataah wannan suna ne?" Murmushi ne ɗauke fuskar Faruuk ya ce"Tun da kaji ta ce haka to sunan nata kenan, ni fa ban faɗa mata sunana da wata manufa ba, kamar yarda ban tambayi nata da niyyar komi ba" Taɓe baki Ma'aruf yayi tare da lumshe idanuwanshi da haka suka ƙarasa gida. Tataah tana shiga kai tsaye ɗakin Ummanta ta nufa. Da sauri ta ƙarasa gabanta ganinta kwance kamar yarda ta barta tun safe, daman tasan hakan zata kasance, kular hannunta ta ajiye tare da cire hijabin dake jikinta, kama mahaifiyar tata tayi tare da saka fillow ta jinginar da ita jikin bango. "Sannu Umma!" Ta furta cikin tsananin jin tausayin mahaifiyar tata, kallonta kawai Ummar ke yi ko ƙittawa babu, tsumma ta ɗauko tare da share mata miyun dake zuba a gefen bakinta sannan ta ɗebo ruwa ta kafa mata kai, sosai Ummar tasha ruwan da alamar ba ƙaramin ƙishi take ji ba 'Dole taji ƙishi Tataah tun safe fa' Wani ɓangare na zuciyarta ya sanar da ita. Bata cika mata ciki da ruwa ba da sauri ta ɗauko abincin da tazo dashi tare da cokali ta fara ba Umman, ta ɗan ci ba laifi sannan ta ƙara mata ruwa tasha, duk bayan minti ɗaya tana jerowa Ummar sannu. Ganin Ummar ta ƙoshi sai lokacin hankalinta ya kwanta ta ci ragowar itan ma tun safe sai yanzu take ci, bayan ta gama sake tattare ƙaramin ɗakin nasu tayi tare da ɗaurawa Umma alwala jin ana kiran sallar Magriba ita ma fita tayi ta ɗauro. Salla ta gabatar ita ma Umma a yadda take zaune take tata a haka. "Tataah! Tataah!! Tataah!!!" Yarda taji muryar mahaifinta na ƙwala mata kira yasa ƴan hancin cikinta murɗawa. Tana ƙoƙarin miƙewa sai gasu sun shugo ɗakin shi da Gwoggonta, jiki na rawa ta duƙa ƙasa "Gwoggo sannu da gida..." Tsawa ta daka mata "Baƙar munafuka algumguma me baƙin hali baƙar fuska! Ashe kin dawo hakima mandiya shine kika barni ina ta jiranki" A sanyaye ta ce"Kiyi Haƙuri lokacin da na shugo ana ruwa ne shiya..." "Dakata mini haka!!" Ta katseta ta hanyar daka mata tsawa. Baba ya ce"Amma me na ce miki akan idan kin dawo gidan nan?" Tuni idanuwanta suka cika da hawaye "Kace na fara zuwa na gaisheta tare da bata duka kuɗin aikin" "To uwar waye ya ce yau ki karya dokar" "Kuyi haƙuri wallahi ruwa akeyi lokacin" "Karya ne ai kafin magariba kike dawowa kuma sai da aka kira sallah aka fara ruwa" Da sauri Baban ya kalli Gwoggo da ba hakan bane amma kallon da ta wurga mishi ne yasa yayi saurin cewa"Haka ne" Jawota Gwoggo tayi tare da fara kilarta tana cewa"Saboda kin raina maganar ubanki danni nafi ƙarfin ki rainani, kin zo gurin nakasasshiyar uwarki da bata da mamora to bani kuɗin da uwarki gantalalliya kawai, a haka zaki ƙare a gantale ke da uwarki!" Jiki na rawa tana kuka ta ta miƙa mata kuɗin duka, Allah yaso ta cire ɗari biyun motar gobe da kuma ɗarin ta ta yau da Allah yasota aka rage mata hanya, dan da tasan tana cirewa bazata bari ba.. Tana amsa ta turata ta faɗi tare da tasa Baba gaba suka bar ɗakin. Tataah ɗagowa tayi tare da sakin ƙara ganin hannunta da ta ɗora a goshi da jini, sake kama goshinta tayi tare da sakin kuka..... This book is not free. it's N300 via 0037219728 Fatima Rabiu Sunusi Stanbic bank. Then u show ur evidence of payment whatsApp number 08104335144 *MU GANI A ƘASA...* _Hot Love_ ©FATIMA SUNUSI RABIU UMMU AFFAN _GAWURTATTU BIYAR._🔥 *Page 3-4* Motsin da taji Ummanta nayi ne yasa ta saurin juyowa, da sauri ta ƙarasa kusa da ita. Hawayen da taga Umman nayi yasa ta mance da ciwon da ke goshinta, "Umma kuka? Mene ne ya faru? Dan Allah ki dena kuka Ummata!" Ta ƙarashe maganar ita ma tana hawayen tare da sharewa Umman nata hawayen. 'Ina ma ina iya magana, ina ma komi nawa yana motsi, ina ma ina da lafiyar da zan iya tsayar da zubar hawayenki, Tataah da bakiyi kuka ba har ƙarshen rayuwarki' Abin da Umma ke faɗa a zuciyarta kenan sai dai kamar yarda ta faɗa tabbas bata da damar hakan a yanzu. Tataah kuwa ganin tana goge mata hawayen amma wasu na zuba sai ita ta dena kukan nata cikin karyewar murya take faɗin "Umma na bari kema ki dena, zubar hawayenki tamkar ana ɗiga mini dalma ne a cikin jikina na bari" Ta faɗa da sakin dariya-dariya wacce take ta zallar yaƙe tana dariya amma hawaye na zuba. Jin ana kiran isha'i gabatarwa sukayi sannan Tataah ta jawo wani yaƙunannan zani ta shimfiɗa a inda zata kwanta ta gyarawa Umma kwanciyarta a saman tabarmar da ta gama fita hayyacinta sai zanin da ta shimfiɗa mata, wani tsohon bargo ta ɗauko ta lilliɓe Umman sakamakon ruwan saman da akayi ya sakar da sanyi me shiga jiki ita kuma ta rufe da hijabinta, haka bacci ya kwashe su daman suna sallahr isha'i take bacci saboda asubar fari take tashi. Ilai kuwa tun huɗu na asuba ta tashi alwala ta farayi tazo ta gabatar da nafila da yiwa Ummanta addu'ar samun lafiya kullum sai tayi wannan sallah dan roƙawa Ummanta samun sauƙi gurin sarki Allah. Bayan idarwarta fita tayi ta fara share tsakar gidan wanda hasken sola ya mamaye ta ɗayan gidan dake jikin nasu ne, mai gidan ya basu wannan ƙaramin suke zaune to har solar dake gidansa ya jona musu. Bayan kammalawarta ne ta shiga kitchen wanke-wanke tayi tare da gyara kitchen ɗin dake kaca-kaca kuma kullum sai ta gyara amma haka zata dawo ta iske shi kamar anyi yaƙi da kaya a cikin shi, fitowa tayi daidai kiran sallar asubahi wanka tayi da ruwan sanyi sai kyarma take saboda sanyin da ake sannan ta ɗaura alwala ta shiga da ruwa tayiwa Umma wacce ta iske ta tashi alamar gaisheta tayi sannan ta jinginar da ita domin tayi sallah. Ita ma ta gabatar da tata, ko man shafawa bata da zarrar shafa shi domin basu dashi, ta daɗe zaune tana lazumi ƙarfe shidda nayi ta miƙe ruwa ta bawa Umma tasha sannan ta gyara mata kwanciya tare da tofa mata addu'o'i cikin sanyinta ta ce"Kiyi haƙuri Umma yau ma haka zan fita ba tare da kinci komi ba, anan babu shago balle na sayo miki ko wani abu ne da nera ɗarin jiya, amma kiyi haƙuri har na dawo" Ɗan lumshe idanuwanta tayi wanda shine kawai ke aiki a jikinta alama ce ta mata da ba komi, jiki a matukar sanyaye ta fita tare da ja mata ƙofa. Kamar yadda Babanta ya sanar da ita ƙa'ida ne taje gaida Gwoggo kafin ta wuce haka ta shiga amma sai ta iske tana barci kamar kullum Baba ne zaune bakin ƙofa yana wankin Gwoggo da yaranta biyu mace da namiji ƙanne a gurin Tataah. Sudees da Tataah ta girma da shekaru biyu sai Ruhaima wacce ta girmi Tataah da shekara ɗaya amma sune BAba ke yiwa wanki, har ƙasa ta duƙa. "Baba ina kwana" Da sauri ya ɗago dan sam bai lura da zuwanta ba sai maganarta yaji, duba gefe da gefensa yayi dan ko gaisuwarta Gwoggo ta hana ya amsa a hankali ya ce"Lafiya ƙalau Tataah zaki wuce gurin aikin ne?" Gyaɗa kai tayi alamar "I" Ba tare da ta ce komi ba, shuru ya biyo baya na ɗan wani lokaci a hankali ya ce"Ki tashi kije kawai basu tashi bacci ba" Miƙewa tayi tana tafiya a hankali ba tare da ta ce ƙala ba, yabi bayanta da kallo yana girgiza kansa. Tayi tafiya mai nisa kafin ta iso bakin titi sannan ta daɗe tsaye kafin ta samu abin hawa, lokacin da ta isa gidan abincin bakwai saura minti goma, hamdala tayi domin ƙa'idar shiga gurin bakwai ne bata san latti kamar yadda aka gargaɗe su da hakan shiyasa take fitowa da wuri. "Baki latti har kin iso?" Ɗan murmushi tayi bata ce mishi komi ba, ciwon da ya gani a goshinta ne yasa shi salati tare da faɗin "Ciwo kikaji?" Sai lokacin ta tuna da ciwon ta ce"Faɗuwa nayi!' Tare da wucewa dan bata san wata magana kuma akan ciwon. Lawan abokin aikinta ne a gurin suna ɗan gaisawa da shi amma ita ba da kowa take magana ba saboda kamun kai da gudun shiga abin da bai dameta ba. Gurin masu girki ta ƙarasa tana temaka musu duk da ba aikinta bane amma tana sa hannu don sam bata da ƙiwwar aiki, suma duk suka tambayeta ciwon abin da ta cewa Lawan shi ta maimaita musu, wajen takwas duk an gama wasu yayin da kuma wasu aka barsu a wuta saboda karsu huce. Mutane ma banbanta ne ke ta shugowa gurin abincin saboda sunan da gurin ya yi ana son abincin gurin sosai ko ba komi akwai tsafta ga daɗin abinci. Tun bayan barin shi gurin abincin yake yawan tuno fuskar yarinyar, yaja tsaki yafi cikon masaki, kai tsaye gida ya wuce daret part ɗinsa ya shiga saman bed ya faɗa nan take kuwa barci me nauyi ya ɗauke shi. Ya daɗe yana barcin har zuwa lokacin da aka fara ruwan sama, sanyayyen sanyin da ake ne ya ƙarawa barcin nashi armashi ya shige cikin bargo ya naɗe yana kwasar baccinsa. Yaye bargon da akayi ne yasa shi buɗe idanuwa a hankali, idanuwansa suka sauka akan Faruuk dake riƙe da bargon, guntun tsaki yaja tare da gyara kwanciyarsa ba tare da yayi magana ba. "Aliyu magana fa nake" Ma'aruf da ya ƙarasa shugowa ne ya ce"Kai sai kace baka san wane ne Aliyu ba, ka barshi fa idan ba haushi ne kake so ya kar ka ba" Zaunawa Faruuk ya yi bakin bed ɗin yana faɗin "Tun jiya da yake ƙasar jajayen can nake kiransa yana wulakantani amma ba komi na shi auren zai zo ne?" Jin abin da Faruuk ya faɗa ne yasa shi tashi yana ɓata fuska "Auren wa?" Ya tambaya so silent, Ma'aruf ya ce "Aurenka! Ko bazakayi ba ne?" Ɗan smile ya saki na gefen baki kafin ya ce"Ku dai fitinannu Allah ya baku sa'a, ku dena lissafi da ni" Dariya suka saka su biyun har da tafawa "Ana maganar fitina har kai kayi magana Aliyu, wannan baccin ma da kake daga gani na wahala ne" Cewar Faruuk. Tsaki Abuturrab yaja tare da miƙewa ya nufi bathroom ba tare da ya ce musu komi ba, su kuwa dariyar shaƙiyanci sukaci gaba da yi mishi. Bayan ya fito dukansu sukayi alwala sannan suka wuce masallaci jin ana tada salla. Ko da suka dawo cikin gidan suka nufa Ammi tasa house girl ɗinta ta shirya musu komi. Aliyu ko kallon abincin bai yi ba, Faruuk daman yasan baci zai yi ba hakan yasa duka suka tashi kai tsaye motar Faruuk suka hau duka suka nufi Husse two gidansu Faruuk. Ammi da ta fito bin gurin tayi da kallo sosai ranta ya ɓaci da ganin abin da sukayi "Abuturrab!" Ta furta da huci kafin ta tuno Faruuk "Shege yaro da maƙar fuskarsa irin ta uwarsa wallahi duka sai nayi maganinku mtsuuuw!" Ta ƙarashe maganarta da jan tsaki. Sareenah wacce ta fito yanzu ita ma bin gurin tayi da kallo kafin ta ce"Ammi ina su Yaya Aliyun?" "Yadda kika ga gurin wayam haka nima na fito na gani, ai kin san wannan Faruuk ɗin idan har suna tare komi yayi shi Abuturrab ke yi" Sareenah da idanuwanta yayi ja saboda ɓacin rai ta ce"Wallahi ba tun yau ba na tsani Faruuk kina ganin ko gani na yayi sai ya dinga mini wani kallo a raine" "Barni da shi daga shi har uwarsa na tsane su kuma nice maganinsu, kwanaki akan uwar Faruuk sai da mukayi faɗa da Alhaji kin san ƙanwarsa ce kuma su biyu uwarsu ta haifa sonta yake kamar me, ni kuma bazan iya jura ba" Sareenah kasa cewa komi tayi sai numfashi da take saki cike da jin tsanar Faruuk a ranta. Sosai Mami ta cikawa su Abuturrab gaba da abinci, cikin farin ciki suka fara cin daddaɗan abinci Mami da ta kasance gwana gurin iya tsara girki. Faruuk ya kai lomar jellop rice bakin shi da taji haɗi na musamman ya ce"Mami gaskiya ko dai anan gidan zamu zauba da Rahina domin ta iya girki kamar naki?" Abuturrab ya ɓata rai kafin ya ce"Sai ana maganar mutane kana sako wannan ƙwailar yarinyar dan Allah ka din ga magana irin ta mutane" A yadda yayi maganar sai ka rantse da Allah ba shine ya yi ta ba domin laɓɓan sa ne kawai ke motsawa Faruuk ne kawai yaji mai ya ce yadda kuma ya mayar da hankalinsa wajen cin abincinsa sai ka rantse da Allah ba shine yayi maganar ba. Mami kam murmushi take ta ce"Wallahi ba dani ba wai gaɗa a hurumi, me zai jani zama da ku a gidan nan? To sai dai idan wata laluurar amma kaje da matarka can da rawar kanka" Tana faɗa ta miƙe ta basu guri, dan tasan halin Faruuk da shegen rawar kai yanzu sai ya ce zaiyi wata maganar. Faruuk ya mai da hankalinsa gurin Abuturrab bayan wucewar Mami "Limamin bayan fage me kake cewa ɗazun?" Banza Aliyu yayi masa yana ci gaba da cin abincin. "Da a maimaita mana da anji zazzafar amsa" "Mtsuw!" Abuturrab yaja tsaki ba tare da ya kuma cewa komi ba har suka ida. Ganin lokaci yaja ya ce"Malam zo ka mayar dani gida dare nayi" "Gida kuma? Wallahi baka isa ba zance zaku raka ni gurin Rahina" Ɗan zaro ido Abuturrab yayi alamar tsoro kafin ya ce"Zance? Mene ne hakan!" "Oho dai idan mun je ka san ko mene ne" Taɓe baki yayi tare da ɗaga kafaɗa cikin cool voice ɗin sa ya ce"Allah ya raka taki gona ba da Aliyu za a ganin shirme ba" Wata muguwar dariya Faruuk ya saki Ma'aruf ya ce"Ina rabaka da kiwo kana ƙyalla ta mutu Aliyu, kar nan gaba kaɗan ka afka ƙaton tafkin so kafi mu zaƙewa" "Allah sitiri buƙwi ba da ni ba" "Wai nikam ina kaji hausa ne?" Ɗan murmushi ya yi tunowa da wani abu kafin ya basar bai ce komi ba. Faruuk shi ya maida Aliyu gida kafin ya sauke Ma'aruf a nasu gidan sannan ya wuce gida dan sanyin da ruwan saman da akayi ya sakar yasa shi jin bazai iya zuwa gurin Rahina a yau ba. Ammi da ta kasa ta tsare tana jiran dawowar Abuturrab anan bacci ya yi gaba da ita, duk a tunaninta da mota ya fita idan ya dawo dole zataji ƙarar motarsa, shi kuwa a bakin gate yasa Faruuk ya ajiye shi sannan ya shugo ta ƙaramar ƙofa, daret part ɗin sa ya nufa bai ma yi tunanin shiga part ɗin Ammin ba. Coppe ya haɗa yana sha a hankali daidai ringing ɗin wayarsa, jawo wayar yayi ganin mai kiran yaja tsaki kafin ya ɗauka. "Lafiya cikin tsohon daren nan?" Sanyayyar ajiyar zuciya ta saki wanda shi kansa da yaji ta, cikin kwantar da murya ta ce"Tun ɗazu nake turo maka saƙo ba amsa, daman so nake naji ko ka sauka lafiya?" Huci ya fesar me zafi kafin ya ce"Baheerah please ki bar ni, wai ana so dole ne?" Tun kan ya sauke numfashi ya fara jin ƙarar kukanta Ƙit! ya yanke kiran cike da fusatuwa ji yayi coppe ɗin ma ya fita ranshi kitchen ya mayar tare da shigewa bedroom sai da ya watsa ruwa sannan ya kwanta bayan ya kunna na'ura me ɗumama ɗaki. Sareenah ce ta fito cikin sanɗa ta niyyarta na barin gidan domin saurayinta ya kirata yana wuce zasu wuce club, ganin Ammi a parlour taji ranta ya ɓaci, gurinta ta ƙarasa sai ta tarad da bacci take mai nauyi ajiyar zuciya ta saki tare da ficewa daga parlourn cikin sauri. Officer na ganinta ya sara mata "Ranki ya daɗe barka da fitowa" Murmushi ta saki tare da zage zagarta ta ciro dubu biyar ta bashi. Godiya ya fara mata da wasata ta ce''Kamar kullum kar wanda yasan da fitar nan, har Ammi" "An gama ranki ya daɗe" Har takai gate kuma ta juyo "Officer Yaya Aliyu ya dawo kuwa?" "I Ya shugo tun ɗazu kuwa" Gyaɗa kai tayi tare da fita daga gidan, nesa kaɗan da gidan ta hango shi cikin baƙar motarsa da sauri ta ƙarasa, tun kafin ta iso ya buɗe mata gaban motar, murmushi suka sakarwa juna "Ma'aruf!!!" Ta ambaci sunansa cike da ƙwarewa. Tada motar yayi sai da ya hau titi ya ce"Sareenah ta Aliyu" Gabaɗaya suka saka dariya ta ce"Har kasa naji wani sanyi, amma nazu raina ya ɓaci da Faruuk ya jaku wallahi ban taɓa tsanar wani irin Faruuk ba" Numfashi ya fesar da cewa"Faruuk bai da matsala jininku ne kawai bai zo daidai ba, shi ya mayar dani gida yana wucewa kuma na samɓo nan" Dariya tayi ta ce"Shi ya sa fa nake ƙaunarka kai ma kasan kan bariki" Ya ce"Hahahaha Sareenah kenan" Da wannan hirar suka ƙarasa shahararren gidan rawar dake garin na Abuja. Guri suka samu sukayi ciye-ciyensu da shaye-shayensu abin da Aliyu ko Faruuk basu san Ma'aruf nayi ba kenan. Daga ƙarshe ma ɗaki suka kama suka gama sheɗancinsu. Sareenah bata dawo gidan ba sai wajen biyar na asubahi, har lokacin Ammi na gurin tana sharara bacci, kasancewar Sareenah ba cikin hayyacinta ta ke ba yasa bata lura da ita ba bedroom ɗinta ta wuce tana zuwa ta faɗa saman bed wani fitinannan bacci ya yi awon gaba da ita.... This book is not free. it's N300 via 0037219728 Fatima Rabiu Sunusi Stanbic bank. Then u show ur evidence of payment whatsApp number 08104335144 *MU GANI A ƘASA...* _Hot Love_ © FATIMA SUNUSI RABIU UMMU AFFAN _GAWURTATTU BIYAR._🔥 https://arewabooks.com/u/ummuaffan Kubi link ɗin nan domin yin following ɗina arewabooks please. Sannan acan nake fara posting kafin nan.👎 *Page 5-6* Tataah Pov. "Tataah lafiyarki kuwa?" Da sauri ta juyo don har yaso ya tsorata ta. Numfashi ta sauke tare da sakin murmushin yaƙe. Farhan ne ɗa a gurin Madam ɗin su saurayi ne sosai bai daɗe da dawowa karatunsa ba a ƙasar waje. "Babu komi Yaya Farhan!" Girgiza kai yayi tare da zama gefenta "Ban yadda ba, ko dai kina jin yunwa ne?" Tayi mamakin tambayar da ya mata, tabbas yunwa take ji amma bazata iya cin komi ba saboda tunanin halin da ta baro Ummanta, ganin tayi ƙasa da kai tashi ya yi sai gashi da abinci ya miƙa mata, da sauri ta girgiza kai alamar a'a. Zaunawa yayi yana dubanta sosai "Tataah baki yadda da ni bane" Sadda kai ƙasa tayi cikin sanyinta ta ce"Ba haka bane" "To mene ne?" Kasa cewa komi tayi ta amshi abincin dan bata san tana cika gaddama da mutum, cokali ɗaya taci ta tino da Umma 'Yanzu a wanne hali take? Ita taci abincin ma kuwa? A'a ita ce amsar dan tasan idan suman mutuwa take Gwoggonta ba zata bata abinci ba. Hawaye ne suka gangaro idanuwanta da sauri ta goge dan bata san Farhan ya gane amma ta makaro "Tataah zan so naji tarihinki, ina jin tausayinki sosai a zuciyata" Kauda kai tayi ba tare da ta ce komi ba. "Dan Allah ki sanar da ni" "Jin sa bashi da wani amfani a tare da kai balle ni da na bayar" Zaiyi magana yaji Madam na kiransa. Ganin ya tashi da sauri ta sami leda ta juyo abincin taje cikin jakarta ta tura domin bata san ci ba tare da Ummanta ba balle har da nama yanka biyu ina zata iya ci ta bar Umma. Farhan ta hanga yana ɗaga mata hannu da alama tafiya zaiyi, gurin wanke-wanke ta ƙarasa ta wanke plate ɗin taje ta ajiye, wasu suka zo sayen abinci taje tambayarsu abin da za a kawo musu, ɗaya cikinsu ya dinga kallonta yana lasar baki, sam bata lura dashi ba sai da ta kai abincin sai ji tayi mutum ya riƙe mata hannu, da sauri ta fincike jikinta na rawa sosai. Ya ce"Dalla can na gani na yaba da yarintarki dare ɗaya zaki bani biya na musamman" Zaro ido tayi tsoro mai tsanani ya shigeta baya ta fara tana girgiza kanta ganin haka ya taso tare da riƙeta, nan fa suka fara kokawa ga mutane a gurin amma kowa harkar gabansa yake ba wanda ya damu dasu (Matsalar bariki kenan) girgiza kai take hawaye masu zafi suna zuba a idanuwanta gashi ta kasa magana, janta yake tare da nufar gurin motarshi da ita "Madamm!!!" Ta kira sunan da karfi, da sauri ta fito jin muryar Tataah. Ƙarasawa tayi gurin da sauri tana cewa"Alhaji dan Allah kayi haƙuri wannan ba irin waɗanda kake tunani ba ce, dan Allah ka rabu da ita!" Wani banzan kallo ya mata ya ce"Bana haƙuri da duk abin da naji ya mini" Girgiza kai Madam keyi cike da jin tausayin Tataah dan har cikin zuciyarta yarinyar ke bata tausayi. Tataah ganin ba wanda zai ceceta kuma wannan mugun da yayi jika da ita ba imani a kamanninsa yasa ta saka haƙoranta tare da gantsara mashi wani mugun cizo. Ai kuwa ba shiri ya saki hannun tare da riƙe hannun nasa, ita kuwa tuni ta arta a saba'in tana ihuw da kuka. Gudu take saman babban titin sam ta fita a hayyacinta, gani take kamar yana bin ta saboda tsoratar da tayi, ƙarar motar da taji bai sata tsayawa ba ta ci gaba da gudu. Ai batayi aune ba taga mota a gabanta ƙara ta saki tare da ɗaura hannu aka ta zube a gurin... Aliyu pov. Asubar fari ya tashi tare da shiga bathroom ya ɗauro alwala ya nufi masallaci, ko da aka idar da sallah bai shugo gida ba sai wajen shidda na safe, yasan Ammi bata tashi ba dan idan tayi salah tana komawa baccin safe hakanne yasa ya koma part ɗinsa, niyyar kwanciya yake yaji ƙarar wayarsa, ɗan tsaki yaja tare da kai idanuwansa saman wayar. 'My Dad' abin da ya gani saman screen ɗin wayar da sauri ya ɗauka dan yayi tunanin Baheerah ce. "Assalamu alaikum" Yayi masa sallama, amsawa yayi Aliyu ya gaishesa ya ce"Daddy da safe haka, Allah yasa lafiya?" Murmushi Daddy ya yi mai sauti har Aliyu yana ji kafin ya ce"Abuturrab ya ka dawo gida?" "AlhamduLillah Daddy!" "Ka koma aikin ne" Tura baki ya yi kamar Daddyn na gabansa ya ce"No Dad ai na ɗauki hutu, sai nan da sati ɗaya" "Ok yayi Alhaji Tasiu ke sanar da ni an kwantar da Baheerah asibiti kaji kuwa" Dam gabansa ya buga amma ba yadda za ayi ka fahimci hakan ya ce"Ban ji ba zan kirata in sha Allahu" "Ya kamata kam, nima cikin satin nan zan dawo" "Tom Dad Allah ya dawo da kai lafiya" Da "Amin" Ya amsa tare da katse kiran. Bin wayar yayi da kallo yana tunanin me zai sa Daddy sanar da shi ciwon Baheerah? Tabbas ɗiyar amininsa ce amma bai taɓa kawo hakan a zuciyarsa ba 'Allah yasa ba sanar da su tayi abin da ta sanar masa ba" Mtsuww! Yaja tsaki idan ma sanar dasu tayi can dasu gada shi ba ruwan shi. Gado ya faɗa domin yana san ya more hutunsa na satin da ya ɗauka kafin a koma fagen daga, kusan sha ɗaya ya farko wanka yayi tare da brush ya nufi part ɗin Ammi dan ya gaisheta. Ba kowa parlour yasan da wuya ma idan ta tashi fita yayi tare da wucewa gidansu Faruuk can ya karya Mami ta ce"Wallahi gara kuyi-kuyi aure ko ma huta da ciyar daku" Ƙasa yayi da kai bai ce komi ba daman tasan da wuya ta tanka miskili kenan kafi mahaukaci ban haushi, bayan ya gama office ɗin Faruuk ya wuce can ya kusan awa uku sallar Azhar ta fito dasu bayan su idar yayi mishi sallama ya nufi hanyar gidan saboda miscalls ɗin Ammi da ya gani kusan biyar lokacin suna sallah ta kira shi. Yana hanya tun daga nesa ya hango kamar mutum na gudu a titi haka dai yaci gaba da rahowa hr zuwa lokacin da ya ƙaraso gab da ita a tunaninsa mahaukaciyace saboda yadda take gudu tana waugen bayanta, duk ƙoƙarin kauce mata da yake amma haka ta tunkarosa wani wawan burgi yaja daidai ƙafafuwanta ganin yadda ta zube masa a gaban mota ne yasa shi fitowa da sauri. Ya daɗe yana kallonta ba tare da ya ce komi ba kusan na minti biyu, kafin ya koma motarsa baya yaja ya kauce mata tare da fusgar motar a sittin. Nannauyiyar ajiyar zuciya ta saki tare da bin bayan motar shi da kallo, ta daɗe a gurin kafin ta tashi jiki a sanyaye ta fara tafiya a hankali domin ƙafafuwanta ba kaɗan suke mata zafi ba, tunani ta fara ta nufi guda ko ta koma gurin Madam? Tasan muddin ta koma gida Gwoggo sai ta kusan kasheta da bugu, gurin Madam kuma tana tsoro karta koma Alhajin nan ya kuma kamata, wannan shi ake kira da gaba giwa baya siyaki, haka tana sharar ƙwalla ta nufi hanyar da zata sadata da gurin Madam domin ba wai gudun Gwoggo kawai take tsoro ba har da irin hukuncin da zata ɗauka akan Ummanta a yadda take ji da ka taɓa Ummanta gara ita ka mata ko mene ne. Taci sa'a baya gurin cike da ƙwarin guiwa ta ƙarasa. Madam na ganinta ta kamota da sauri tare da turata wani ƙaramin ɗaki. "Tataah kin san abin da kika yi, kin san wane ne wannan mutumin a ƙasar nan?" Tuni hawaye ya fara ambaliya a fuskar Tataah. Madam ta dubeta cike da tausayawa ta ce"Ya tafi amma ya ce ba zai barki ba sai ya hukuntaki, wallahi Tataah ina jin tausayinki a zuciyata a shawarce ki ajiye aikin nan" A hankali ta ɗago "Allah yasa haka shine mafi alkhairi, da mutumcina ya zube gara na bar aikin" Kularta ta ɗauko Madam ta zuba mata abinci kamar na kullum sannan ta biyata kuɗinta har da ƙari tare da mata fatan alkhairi, jakarta da babban hijabinta ta ɗauko sukayi sallama, tana tafe tana hawaye da tunanin makomar rayuwarta a gaba, shin ya gobenta zai kasance? Ta bar aikin da take samu suke ɗancin abinci a wani sau ɗaya ita da Ummanta yanzu ta bar aikin ya zasu kasance? Ga babban tashin hankalinta Gwoggo wanne irin mataki zata ɗauka idan taji ta bar aikin? Da wannan tunanin ta tare ɗan napep yau ko tayin bata da zarrar yi saboda hankalinta ba a kwance yake ba. Ko da ta sauka ta biyashi tafi minti biyar tsaye ƙofar gidan kafin ta shiga jiki sanyaye. Ba kowa tsakar gidan hakanne yasa cikin sauri ta shiga ɗakin Ummanta, tana nan kwance kamar yadda ta barta da sauri ta ƙarasa tare da jinginar da ita jikin bango dan tasan ta gaji da kwancin "Sannu Umma!" Ta furta hawaye na zubo mata, ƙura mata idon da tayi ne ta gane tambayarta take yi me ya faru? Kukan da take dannewa ne yaƙi dannuwa ta fashe da shi amma a hankali domin bata san Gwoggo ta gane ta dawo gidan. Nan take ta fara ba Umma labarin abin da yw faru domin Ummar na jin komi amsawa ne kawai bata iyawa, sai gani tayi Umman na hawaye da sauri ta fara share mata "Umma bana so kina kuka, wannan yana ɗaya daga cikin tarin jarabawata kar ki damu" Sai ita ta dena hawayen domin Umma ma ta bari, hakan yasa ta jawo kular tare da buɗe abincin tasa cokali tare da kaiwa bakin Umma amma sai taƙi buɗe bakin daman daƙar take buɗesa kaɗan-kaɗan take ci, ganin hakan yasa Tataah cewa"Dan Allah karki sa wannan damuwar a ranki komi zai zo cikin sauƙi" Da ƙyar ta samu Umman taci sai ta rufe musu sauran da dare ta ɗauko na ledar da ta zuba da Farhan ya bata taci. A ɗaki tayi akwalar sallar azahar tayiwa Umma sukayi tare basu daɗe da idarwa ba aka kira la"asar duk suka gabatar. Kwanciya tayi domin wani zazzafi ne ke damunta duk da yamma ce kasa ƙin kwanciyar tayi, baccin wahala yayi gaba da ita Umma nata kallonta har ta farka wajen shidda na yamma. Miƙa tayi tare da hamma fitsari take ji sosai hakan yasa ta ciro kuɗin da Madam ta bata ta ciro ta irga daidai wanda take bata kullum sauran ta ɓoye domin kuɗi sosai ta bata. Fita tayi ba kowa kamar ɗazun daman Gwoggo ko yaranta basu fiya zaman tsakar gidan ba, sun fi son rayuwar jin daɗi a rayuwarsu. Hakan yasa buta ta ɗauka tare da shiga banɗaki ta rage mararta, tana fitowa Ruhaima na shugowa cikin wata banzar shiga da bata dace da ita ba a matsayinta na musulma tana wani taunar cingam ji kake "Ƙas! Ƙass!! Ƙasss!!!" Tana gaba Tataah na bin ta a baya har suka shiga madaidaicin parlourn na Gwoggo. Ruhaima ta saki ɗan mayafinta wanda dashi gara babu a saman matsagaitan kujerun parlourn tana furta "Wash! Yau na gaji" "Sannu Ruhaima bari in kawo miki ruwa da abinci kici ki kwanta ki huta" Shugowar Tataah ne yasa Gwoggo ɗaure fuska tana bin ta da wani mugun kallo, da sauri ta zube "Sannu da gida Gwoggo!" Hannu ta miƙa mata "Ba sannu na tambayeki ba danƙa min" A sanyaye ta miƙa mata kuɗin, irgawa tayi daidai na kullum tare da cewa "Tashi ki fitar mini a parlour" Ruhaima ta ce"Gwaggo ki basu abinci na yau dan Allah" Da sauri ta juyo da cewa "Karki haɗani da Allah Baby bazan iya basu ba" "Tashi ki fita!" Ta daka mata tsawa, da sauri ta miƙe ta fita. Jiri take gani sosai tasan ciwon goshinta ne ya sakar mata da zazzaɓi ga gudun da tasha ɗazu, tana shiga ɗaki kuɗi ta cira tare da fita, tana tafe tana layi, gashi duk inda ta duba bata sami chemis ba, hankalinta ya tashi sosai ta nufo hanyar gida. Titi ta hau ba tare da ta sani ba, tun daga nesa yake danna mata hurn amma bata sani ba saboda yadda taji zazzaɓin ya fara hawar mata kai tafiyar kawai take ba tare da tasan inda take cilla ƙafafuwanta ba. Daidai ƙarasowar motar daidai zubewarta a gurin a sume, a furgice ya fito daga motar duk da yaga ba wai bugeta yayi ba amma yanayin da ya ganta da alamar tana neman temako shi kuwa Faruuk Allah yasa masa zuciyar tausayi ga fara'a dawowarsa daga wajen aiki kenan yau yayi yamma sakamakon wani aiki da yayi. Birkito da ita yayi nan take idanuwansa ya sauka akan fuskarta 'Tataah!' Ya ambaci sunan da ta faɗa musu ranar shi da Ma'aruf. Da sauri ya kinkimeta sai cikin mota inda ya tada ya nufi wani private hospital dake kusa da gurin, yana zuwa ƙara surarta yayi cikin asibitin nan take aka fara bata temakon gaggawa. Faruuk sai safa da marwa yake a harabar gurin ya kasa zama ji yake tamkar ƙanwarsa Nanaah da suke ciki ɗaya ce babu lafiya, kusan awa guda kafin Likitan ya fito da sauri ya nufe shi, tun kafin yayi magana Doctor ya ce"Kwantar da hankalinka ta farfaɗo, zazzaɓi ne me zafi na maleria sannan ciwon goshinta ma ya ƙara assasa mata zazzaɓin sannan tana da ulcer" Numfashi ya sauke a hankali tare da furta "Na gode Doctor zan iya ganinta?" "I Zaka iya amma ta samu bacci saboda mun mata allurar bacci tana buƙatar hutu sosai" Gyaɗa kai yayi tare da nufar ɗakin da aka kwantar da ita, tun da ya shugo idanuwansa ke kan fuskarta da tayi fayau sai ciwon goshinta da aka wanke mata shi ga allurar ƙarin ruwa liƙe a hannunta. Kujera ya jawo ta zaman masu jinya ya zauna har lokacin idanuwansa na kanta, kusan minti ashirin yana zaune gurin kafin ya miƙe da sauri jin wayarsa na ringing Mami ce ya ɗauka da sauri "Faruuk lafiya har yanzu baka shugo gida ba?" Yana ɗauka yaji muryar Mami na tambayarsa. Numfashi ya fesar ya kalli gadon da Tataah ke kwance "Lafiya ƙalau Mami wata yarinya na kaɗe da mota shine na kawota asibiti yanzu haka ina can" Kawai ya tsinci bakinsa da furta wannan kalmar. "Asibiti ya jikin yarinyar?" Mami ta tambaya a kiɗime "Ki kwantar da hankalinki ba wani ciwo taji me yawa ba yanzu haka an sa mata ƙarin ruwa ta samu bacci" "To Allah ya ƙyauta gaba, wanne asibiti ne?" Sunan asibitin ya faɗa mata tare da yanke kiran. Kusan minti talatin sai ga Mami tare da Nanaah sunzo hannunta riƙe da kwando da kulolin abinci. Kasancewar asibitin bai da wani girma sosai yasa tana shugowa basu sha wahalar gane ɗakin da suke ba. Bakin gadon ta ƙarasa bayan Faruuk ya amshi kwandon hannunta yana mata sannu, gabanta ya buga da ƙarfi ta ƙure Tataah da kallo kafin taja numfashi "Allah ya bata lafiya" Suka amsa da amin ya ce"Mami bare naje nayi sallah banyi magrib ba" Ta ce"Sai ka dawo" Fita yayi ya bar Mami da Nanaah ya nufi masallacin dake asibitin... This book is not free. it's N300 via 0037219728 Fatima Rabiu Sunusi Stanbic bank. Then u show ur evidence of payment whatsApp number 08104335144 *MU GANI A ƘASA...* _Hot Love_ ©FATIMA SUNUSI RABIU UMMU AFFAN _GAWURTATTU BIYAR._🔥 https://arewabooks.com/u/ummuaffan Follow me fans.😍 *Page 7-8* "Umma! Umma!!" Tataah ta furta da ƙarfi tare da ƙoƙarin miƙewa. Da sauri Mami ta ƙarasa tare da riƙeta ganin tana niyyar cire ƙarin ruwan da ake mata, "Ki natsu kina asibiti ne!" Komawa tayi ta kwanta tana sauke numfashi tare da kafe Mami da bata san ko wacece ba da ido. Tea Mami ta fara ƙoƙarin haɗa mata kafin ta tasota zaune ta ce"Sannu ga tea bari na baki" Ƙasa tayi da kai bata ce komi ba, Nanaah ta kawo ruwa aka ɗauraye mata baki kafin Mami ta fara bata tea ɗin daidai shugowar Faruuk. Ƙure shi da kallo Tataah tayi a ƙoƙarin gano inda ta taɓa ganin fuskar, can ta tuno da shine ya taɓa taimakonta ana ruwa ranar. Sosai tasha tea ɗin saboda yunwar da take ji kawai ta isa ta sa mata ciwo, farfesun kaza Mami ta zuba mata ai kuwa ta lashe tas! Ganin irin kallon da Faruuk ke mata yasata jin kunya sosai tayi ƙasa da kanta. Ummanta ta tuna da sauri ta ɗago "Ina so na koma gida" Kafin Faruuk ya ce wani abu Mami ta maganantu "Baki lafiya fa, ki bada addres sai Faruuk ya faɗo musu kina asibiti" Da sauri ta fara girgiza kai idanuwanta suka cika tab da hawaye ta ce"A'a ba sai yaje ba, dan Allah a sallame ni na wuce wallahi naji sauƙi" Suna maganar likita ya shugo "Ah me jinyata taji sauƙi irin wannan zance" Ya faɗa da alamar yana da barkwanci. Tataah ta ce"I Na warke dan Allah likita ka sallame ni gida zani" "Ai ƙya bari zuwa gobe ko? Bai kamata a sallame ki yanzu ba" Cewar likitan. Mami ta ce"Nima abin da nake faɗa mata kenan!" "Wayyo Allah! Ummata" Ta furta hawaye na zuba "Umma!" Faruuk da bai san kalmar ta fito ba sai jin sautin ya yi "I Umma, dan Allah ka mayar dani gurin Ummata" Ta faɗa tana hawaye domin bata jin zata iya kwana wani guri ba tare da Ummanta ba. "Likita kawai ka sallamemu, ka haɗa mana duk maganin da kasan ya dace" Faruuk ya faɗa idanuwansa na kan Tataah wacce tayi saurin ƙasa da kanta tana wasa da yatsun hannunta. Likitqn kwance mata robar ƙarin ruwan yayi saboda tuni daman ta ƙare amma cire allurar, bayan fitarsa Mami ta ce Nanaah ta gyara musu kayan basket ɗin. Minti goma bayan fitar likitan Faruuk yabi bayanshi kuɗi ya biyashi na komi ya bashi magungunan sannan ya koma ya ce su fito su wuce. Gida ya fara kai su Mami ta tun da kallonsa da mamaki shi ɗinma kasa ce mata komi ya yi bayan isarsa bakin gate ɗin, ganin ba zai ce komi ba ta ce"Ai sanake gidansu yarinyar nan zamu fara zuwa muba iyayenta haƙuri ko?" Sosai yake jin kunyar Mami a bisa ƙaryar da ya mata cewa bige Tataah yayi amma ya daure tare da cewa "Ku shiga gida naga dare yayi ne Mami bari ni naje kawai" Ko da yayi maganar ya kasa ɗago kai ya dubeta, ba musu ta cewa Nanaah ta sauka suje, kallon Tataah Mami tayi tare da dafa kafaɗarta "Ƴata Allah ya ƙara lafiya kiyi haƙuri da abin da ya faru sannan ki gai da mini Ummanki" Gyaɗa kai kawai tayi kanta a ƙasa, bayan fitarsu yaja motar ya doshi unguwarsu Tataah. Tun da ya hau titi bai ce mata komi ba ita ma kanta na ƙasa burinta kawai sanin halin da Ummanta take, Faruuk bai mance layin ba domin daidai ƙofar gidansu ya tsaya, sai lokacin ya juyo ya kalleta. A sanyaye ta ce"Na gode Yaya Faruuk Allah yasaka da alkhairi" Daga haka ta fara kiciniyar buɗe motar, magungunanta ya ɗauko tare da miƙa mata "Ga magungunanki ki daure kina sha kamar yadda likita ya rubuta miki zaki gani sannan ki dinga cin abinci akan lokaci" Da sauri ta ɗago suna haɗa ido ta mayar da kai ƙasa tare da amsa "Na gode" Ta fita cikin natsuwa, sai da yaga shigarta kafin ya sauke numfashi ya tada motarsa zuwa gida. Dare ne dan kusan tara da rabi hakan yasa ba kowa tsakar gidan ko da yake ko da rana ba cika zama sukayi ba, direct ta nufi ɗakinsu, hannu ta sa ta kunna gulop ɗin ɗakin da a kashe ta iske shi kuma akwai nepa. Tar! Idanuwanta ya faɗa ana Umma don ba bacci take ba, da sauri ta ƙarasa tare da ajiye ledar maganin ta nufi Umma "Kiyi haƙuri Umma wallahi ina can ina tunaninki" Ɗagota tayi tare da ɗibar ruwa ta bata sosai tasha ruwan, hawaye taji ya zubo mata ina da ta kwana ƙila da sai dai ta dawo ta taradda gawarta. Abincin ɗazun ta ɗauko tare da bata, ƙin amsa tayi tana ƙifta ido, ta gane abin da take nufi tana tambayarta inda taje ne "Umma na fita sayen magani kaina na ciwo ban samo ba, na faɗi a hanya wani ne ya temaka mini" Ta sanar da ita komi tare da jawo ledar maganin, kuɗi ta gani a ciki bandir guda gabanta ya faɗi ta ciro kuɗin tana juyawa tana zazzaro ido, Umma ma kallonta take ta ce"Shine ya saka min cikin maganin wallahi ko sanar dani baiyi ba" Ciro magungunan tayi tare da mayar da kuɗin leda ta ƙulle zuwa tayi ta ɓoye dan tafi tunanin ko bai sani ba kuɗin shiga shiga dan shi magani ne kawai ya ce ta amsa hakan yasa ta ɓoye da ƙudirin duk ranar da suka kuma gamuwa zata mayar masa da kuɗinsa. Abinci ta ɗauko taba Umma sai da ta tabbatar ta ƙoshi sannan ta ajiye ɗan ragowar dan ita kam a ƙoshe take, magungunanta tasha tare da gyarawa Ummanta kwanciya ita ma ta kwanta a ranta tana mai ƙara jin tausayin Umman nata wacce daga ƙwanciya sai zama shima zaman sai an jinginata da bango. Tunani ta faɗa akan temakon da Faruuk ya mata Maminsa da ƙanwarsa ta tuno abin su gwanin ban sha'awa sai ta tsinci kanta da sakin murmushi. Da haka barci ya kwasheta.. Aliyu pov. Cike da ɗacin zuciya yake tuƙin bayan barin shi gurin, yaja tsaki kam yafi cikin masaki "Mummuna me baƙar fuska!" Ya faɗa tare da fesar da wani huci me zafi, shi dai yarinyar bata mishi ba bai san dalili ba, ranar ya ganta a gidan abinci yau kuma a titi tana gudu anya ma kanta ɗaya? Ya tambayi zuciyarsa kafin ya ɗaga kafaɗa alamar bai dameshi ba. Yarinya ƙarama sai shegen gantalin tsiya daman matsalar ƴan ƙauye su shugo gari kenan. Da wannan tunanin ya ƙarasa gida, bayan ya shiga yayi parking kai tsaye part ɗin Ammi ya wuce. Sareenah zaune a parlour taci kwalliya kamar wacce zata gidan biki "Sannu da zuwa Yay..." Katseta yayi ta hanyar ɗaga mata hannu kafin ya ce"Ina Ammi?" Fuskarsa sam ba alamun wasa. Muryarta har rawa take wajen furta "Tana sama" Domin Aliyu va dai kwarjini ba. Cikin takunsa na isa ya fara taka saman ta bishi da kallo cike da so da sha'awa namiji har namiji irin mijin da take mafarkin samu, a fili ta furta "Wallahi tun da ina sonka duk yadda zanyi sai nayi ka zama mallaki, bari ka zama nawa sai ka gane kurenka" Zama tayi tare da ci gaba da kallon da take gefe guda kuma tana chart a waya. A hankaki ya tura ƙofar bedroom ɗin Ammi bakinsa ɗauke da sallama, zaune take bakin bed tana waya, saman kujerar dake ɗakin ya zauna jin da Daddy take wayar "Allah ya dawo da kai lafiya" Ta faɗa tana katse kiran, kafin ta ɗago ta kalle shi "Abuturrab" Ƙyawawan idanuwansa ya ɗago tare da sauke mata su. Ƙwarjininsa yasa abin da tayi niyyar faɗa masa ya kasa fitowa "Ammi kin kirani lokacin ina masallaci ne" Ya faɗa cikin sanyin murya. Ta ce"Abin da kake baka ƙyautawa Amma tun da jibi Daddynku zai dawo ai ya gani da idanuwansa" Ƙara zuba mata ido yayi ta gane nufinshi ƙarin bayani yake so yafi ƙarfin ya mata maganar ne, ƙarin tsaki taja tare da faɗin "Yau baka kwana gidan nan ba, ina ka kwana?" Kasa dena kallonta yayi yana mamakin Ammi yo shi ƙaramin yaro ne da za a masa wannan tambayar ko bai kwana gidan ba balle ya kwana. Ya ce"Gida na kwana" Wani kallo ta masa na ka rainani kafin ta ce"Ƙarya kake Abuturrab jiya nice parlour har wajen biyu na dare amma banji shugowarka ba" Bata san sanar dashi parlourn ta kwana saboda taji dawowarsa domin kar ya zargi wani abu. Ɗan smile ya saki dan da wuya kaga yana dariya yafi murmushi, "Na dawo, da yake Faruuk ne ya sauke ni a waje na shugo" Ƙura masa ido tayi kafin ta taɓe baki. Bai ƙara cewa komi ba, ganin shurun yayi yawa ne ta ce"Kayi mini zugun dan Allah tashi ka fita idan baka da maganar yi min" Da mugun mamaki yake dubanta sai kace ba ita ce tayi kiransa ba, to daman me zai ce yana jiran ji daga gareta akan kiran da take ta masa. Miƙewa yayi ba tare da ya ce komi ba ya doshi hanyar fita "Kaji Alhaji zai dawo jibi?" Ta wurga masa tambayar yana gab da fita "A'a!" Ya amsa mata tare da ficewa. Cije leɓe tayi wani abu na taso mata a zuciya, ta fesar da huci me zafi tana gyaɗa kai kamar wata ƙadangaruwa. Da sauri Sareenah ta miƙe ganin fitowarsa, kai tsaye ƙofa ya nufa "Am Yaya Ali...." Kallon da ya mata ne yasata kasa iya ƙarasa abin da zata faɗa fuww! Ya fita daga parlourn, jagab ta zauna zuciyarta na mata zafi kamar wuta. Wayarta da ta fara ringing alamar ana kiranta ta duba ganin ƙawarta Layla ce yasa tayi saurin ɗauka"Layla kina ina ne?" "Gani a hanyar gidanku" Layla ta bata amsa. Ajiyar zuciya ta saki tare da furta "Sai kin ƙaraso" Ta ajiye wayar direct bedroom ɗinta ta wuce ta huci, kusan minti goma Layla ta ƙara so, "Reenah lafiya kike ta faman kai kawo?" Kasancewar ƙawayenta Reenah suke kiranta, zaunawa tayi bikin bed bayan ta dubi Layla ta ce"Hmmm! Ke dai bari, wallahi yadda Aliyu ke wulaƙanta ni abin na damuna" Ƙarasawa Layla tayi tare da zama kusa da ƙawar tata ta dafata da faɗin "Wai kina nufin har yanzu Aliyu bai shugo hannunki ko bakiyi aikin da aka saki bane?" "Wallahi nayi sai dai my Aliy yana da wata kafaffiyar zuciya gani nake kamar magani baya cin sa" "Ƙarya ne!" Layla ta katse Sareenah ta ɗaura da cewa"Tun da asiri yaci Annabin Allah uban waye zai ce yafi karfin asiri? Tun da na wannan Malamin bai yi ba ki haɗa kuɗi akwai wani sai mu sake zuwa" Numfashi ta sauke "Ni wallahi har na fara gajiya da kashe kuɗi ba biyan buƙata" "Idan kin dena son sa shi kenan amma ai dole sai da kashe kuɗi idan ba a ci nasara a wannan ba ai a gaba idan da haƙuri juriya da jajircewa za a samu" "Haka ne kuma" Sareenah ta faɗa tana ƙoƙarin miƙewa "Tun da kikazo sai zuba muke bari in kawo miki ruwa" Tana faɗa ta fice. Washe gari Tataah bata tashi da wuri ba, tun bayan sallar asuba da tayi ta koma, sanin cewa ba zata fita wajen aiki ba, kuma daman ba lafiya gareta ba ƙarfin hali ne kurum. Kwance take wajen misalin ƙarfe tara na safe, sai juyi take tana tunanin yadda zata iya wuni a gidan tare da Gwoggo da kuma tunanin abin da zata ce idan ta tambayeta dalilin barinta aiki, tasan wuya kam sai tasha, amma wuya bata kisa, cikin mutuwar jiki ta nufi hanyar kitchen bayan fitowarta daga ɗakin, har lokacin su Gwoggin basu tashi ba, hakanne yasa ta fara aiyukanta cikin kwanciyar hankali. Ta kusan idawa Ruhaima ta shugo, kallon sama da ƙasa tayiwa Tataah kafin ta kau da ka tare jawo ƙaramar tukunya ta kunna ƙarimin rishonsu ta ɗaura, Tataah na gurin tana aiki har ta gama tafa indomie ɗinta biyu da ƙwai biyu, ta zuba a plate tare da barin wata a ciki ta miƙawa Tataah, kallonta tayi sannan tabi rahowar Indomie ɗin da kallo, gyaɗa mata kai Ruhaima tayi alamar ta amsa, hannu tasa ta ƙarɓa tare da furta "Na gode." A hankali. Juye indomie tayi cikin ƙaramin plate ta ida komi da sauri ta shige ɗaki Ummanta ta ɗaya tare da bata taci kuwa sosai ɗan murmushi tayi da cewa"Umma kina san infomie naga kinci" Lumshe ido kawai tayi tana bin Tataah da kallo wacce taci ragowar indomie ɗin. Wuni tayi a ɗaki alwala kawai ke fitar da ita, haka Tataah ta ɗauki tsawon kwana uku tana huda ba tare da Gwoggo ta sani ba. Kwatsam yau ta fita alwalar sallar azahar Gwoggon ta fito sukayi kiciɓis, bin ta da kollo tayi a wulaƙance kafin ta ce"Ballaga gantalalliya yau kuma zaman me kike a gida" Gaban Tataah na faɗuwa ganinta bata yi tsammani ba, ƙasa tayi da kai kafin ta ce"Uhm...Uhmm...da...ma....daman ai...!" Duk cikin inda-inda take ta kasa ma furta abin da ya kamata duk ta ruɗe. Baba ne shima ya fito binsu yayi da kallo Gwoggo ta dube shi "Baban Sudees kana ganin gantalalliyar nan yau bata fita ba ko? Wallahi kuwa zata ga yadda ake gantalewa a gidan" Kafe Gwoggo yayi ta kallo wata tsawa tadaka mishi "Kallona na kiraka kayi ne Malam? Wallahi yau idan banji hujja me girma ba akan ƙin zuwanki aiki, sai na lahira ya fiki jin daɗi, da ni kike zancen!" "Kiyi haƙuri bana lafiya ne, shine Madam ta ce na dawo gida sai gobe naje!" Tataah ta tsinci bakinta da furta hakan domin mafita take nema..... This book is not free. it's N300 via 0037219728 Fatima Rabiu Sunusi Stanbic bank. Then u show ur evidence of payment whatsApp number 08104335144 *MU GANI A ƘASA...* _Hot Love_ © FATIMA SUNUSI RABIU UMMU AFFAN _GAWURTATTU BIYAR._🔥 https://arewabooks.com/u/ummuaffan *Page 9-10* Wani kukan kura da Gwoggo tayi sai gata ta shaƙe wuyan Tataah. Ƙarar azaba Tataah ta saki daidai ƙarasowar Baba yana ƙoƙarin ƙwatarta "Dan Allah Zainabu ki rabu da yarinyar nan" Wata bangaza ta tayiwa Baba sai gashi a gefe, ya yin da tacigaba da kaiwa Tataah duka ta ko ina, "Kiyi haƙuri Gwoggo!" Abin da Tataah ta iya furtawa kenan cikin tsananin wahala, dama gashi ba ta lafiya ga ƙarin dukan Gwoggo. Bata ƙyaleta ba sai da ta mata ligib kafin ta ce"Mu zuba ni dake, shege ka fasa ɗan halak kuma sai yanka, dan ubanki yanzu wake da isasshiyar lafiya wallahi duk wanda kikawa sannu zai amsa da kowa takanshi yake sai dai ta wani tafi ta wani amma kowa ba lafiyar nan gare shi ba. Har ni zaki faɗawa baki da lafiya shi ya sa kika ƙi fita aiki saboda ke ga isasshiya to nima bana lafiyar ubanki ma ba lafiyar gare shi ba kuma haka yake fita nima in fita ai daurewa kowa keyi dan yanzu a ƙasar nan dai kowa bashi da lafiya." Sosai Tataah ke kuka kanta a ƙasa ta kasa ɗagowa sai zubar hawaye da take, hakan kuwa ya ƙara ƙufular da Gwoggo ta kai mata wani mari wanda tsabar zafinsa yasa mata sakin fitsari bata san lokacin da ya fito ba. Duƙewa tayi a gurin tana kuka kamar ranta zai fita, tafin hannunta ɗaure akan kuncinta da ƙarfi kuwa ta runtse idanuwanta sakamakon wasu fararen taurari da ta gani "Shegiya me baƙar fuska da baƙin hali, wallahi gobe idan kika kuma zama baki fita aiki ba sai na illataki, wallahi sai na miki abin da ya taka wannan algunguma ƴar kaza-kazan uban can." Kan Baba ta nufa tana huci "Kai kuma munafiki zamu haɗu da kai, wai har ina mata hukunci kazo wai zaka tare ta?" Ummm tayi wani murmushin takaici kana ta ce"Kai game ƴa! Ƴar ma da kake ƙila wa ƙala akanta" Da sauri ya ɗago ido yana kallonta tare da girgiza mata kai bai iya cewa komi ba, dan mugun tsoranta yake ji. Fuuu! Ta wuce ciki tana huci kamar kumurci. A sanyaye ya dubi ƴar tashi "Komi yayi farko yana da ƙarshe da izinin Allah!" Abin da ya furta kenan yabi bayan Gwoggo. Wani kuka Tataah ta saki, sai da tayi mai isarta kafin ta wuce ciki, tana shiga Umma ta kura mata ido, saddar da kanta ƙasa tayi sam bata so Umma ta gane tana cikin wani hali dan kar ta sawa Umma damuwa a rai, gashi ba lafiya gareta ba... A yau Daddy ya dawo sosai Ammi tasa aka gyara ko ina ga abinci kala-kala da ake ta shiryawa na tarbarsa.. Abuturrab tun safe yana part ɗinsa yana bacci, wajajen ƙarfe sha ɗaya yaji wayarshi na ringing kamar ba zai ɗauka ba sai ya jawo wayar ganin Faruuk ne ya ɗanyi murmushi tare da amsa kiran "Anaci kenan lafiya zaka kirani da sanyin safiyar nan?" Girgiza kai Faruuk yayi daga ɓangaranshi kafin ya ce"Dalla Malam fito ina bakin gate" Gyara kwanciya Abuturrab yayi tare da cewa"Bacci nake kuma bana san takura please!" Ƙit ya katse kiran yana jan tsaki tare da ajiye wayar ya gyara kwanciyarshi yana sake naɗewa cikin bargo. Gabaɗaya yaci an yaye bargon da fushi ya juyo idanuwansa suka sauka a fuskar Faruuk "Lafiya Malam!" Ya tambaya a fusace fuskarshi ɗaure. Faruuk gyara tsayuwarsa ya yi tare da rungume hannayensa a ƙirji ya ce, "Tambaya kake ko neman sani? Abey Malam tashi muje, mutum ya duƙa bacci kamar wata mace saboda lalaci" Saurin yaye bargon da ya rufa ya yi ya tashi da sauri ya duro gadon yana jan tsuka "Mtsuw! Kai kasan kallo ɗaya aka mini an san jarumi ne ni" Yana faɗa direct ya yi toilet. Zaunawa Faruuk yayi gefen gadon yana dariya, daman yasan za a rina Aliyu bai san a kirashi rago ko kalmar dake kace-ceniya da hakan. Kusan mintina sha biyar Abuturrab ya fito ɗaure da towel a ƙugunsa, ɗayan kuma yana goge sumar kansa, gaban mirror ya ƙarasa ya shafe jikinsa da lotion tare da buɗe durowa ya ɗauko doguwar riga ta jallabiya me matuƙar ƙyau da tsada. Taje sumar kansa yayi yana kallon Faruuk wanda shima idanuwansa yana kanshi "Haufa Guy!" Faruuk ya furta yana miƙewa, ɗan tsaki yaja yayi gaba yana furta "Ko kuturu ne kai akan naci haka ka barni haka" Faruuk na biye dashi har suka isa parlour, guri suka samu tare da zaunawa saman sofa. Faruuk ya ce"Kana ɓata mana lokaci fa Ma'aruf ya ce idan mun fito a kirasa ba zai iya zuwa zaman jira ba" Ya ƙarashe maganar da tsokana, kau da fuska Abuturrab yayi ba tare da ya ce komi ba. Ganin haka yasa Faruuk saurin tashi daga inda yake ya dawo kusa da Abuturrab cikin taushin murya ya ce"Please Aliyu idan zaka ka taso, idan kuma mu wuce ne shi kenan" Ɓata fuska yayi kafin ya ce"Da wucewar ku kayi da yanzu kunyi abin da ya dace, Faruuk kasan halina bazan iya zuwa gurin kuchakan yaran nan ba har na iya abin da kake tunani" A fusace ya miƙe cike da jin ɗacin kalmar da ya kira "Matar da zan aura ne kuchakar? Na gode Aliyu!" Faruuk ya fita da sauri. Taɓe baki yayi tare da ɗaga kafaɗa irin ko ajikin shin nan. Faruuk na fita Ma'aruf ya kira suka wuce duk abin da ya dace sai da sukayi sannan kowa ya wuce gida, tun da bikin ya ƙarato hankalin Faruuk duk ya koma can yana san zuwa duba cikin Tataah amma hidimar bikin kanshi sosai ya ɗauki zafi da komi kusan shi yake yi sai Ma'aruf dake temaka mashi amma sam Aliyu ya zare hannunsa kami da sha'anin auren. Faruuk ko ta kanshi ba yabi, har zuwa yau juma'a da ta kama bikin, shagali sosai ake babu masaka tsinke a gidansu Faruuk duk kuwa da girmansa, don shi ɗin ɗan dangi ne sosai. Ko yau da ake ɗaura auren Faruuk bai bi takan Aliyu ba harkar gabanshi kawai yake don yaji zafin kalmar da ya yaɓawa matar da zai aura Hibbah ta kuchaka shikam a haka yake ƙaunar abarsa. Baiyi tunanin ma zai zo ɗaurin auren ba abin mamaki sai gashi cikin wata ɗanyar shadda tamkar shine angon. Duk inda ya yi kallonsa ake tamkar wani tauraro, saboda ƙyawon da yayi cikin wata ɗanyar shadda marun tamkar shine angon har da malin-malin, masallacin sosai ya cika da al'ummar Annabi, bayan idar da sallar juma'a ne aka ɗaura auren Umar Faruuk Hassan da amaryarsa Muhibbat Kabir akan sadaki dubu ɗari biyar. Ana cikin ɗaurin auren kafin a tashi akaji muryar wani mutum na furta "Assalamu alaikum jama'a ga duk wanda ke buƙatar auren ƴata *Jameelah* ni mahaifinta zan bashi aurenta akan sadaki ƙalilan kai idan ma baka da kuɗin a yanzu? To zan baka aurenta a sadaka!" Gabaɗaya gurin ya ɗauki shuru baka jin motsin mutane ballantana kuma maganarsu, jin kowa yayi shuru ne wasu hawaye masu zafi suka sakko akan fuskar mutumin. Idanuwan sa ne suka faɗa akan fuskar Abuturrab shima kallonsa yake cike da mamakin uba irinsa. Gani yayi mutumin ya ƙaraso gabansa tare da ɗago shi, wani ikon Allah sai yaji ya miki mutumin ya buɗe baki da ƙarfi ya ce"AlhamduLillah wannan bawan Allah ya amince zai auri ƴata Jameelah!" Gaban Aliyu ya wani bada sauti me ƙara kamar yadda Faruuk da Ma'aruf suke dubanshi cike da mamaki, a tunaninsu shi ɗinne ya furta haka dan basa tunanin mutumin haka kawai zai ce ya amince, gaban limamin mutumin ya kai Aliyu wanda ya koma tamkar mutum mutumi yana duban uban wannan ƴa tamkar me taɓin hankali. Sai lokacin masallacin ya kachame da surutu na irin yadda Aliyu yayi shahadar wannan aure, su kansu limaman cike da mamaki suke, nan dai aka sa kowa yayi shuru kafin me ɗaura auren ya ce"Kana da sadaki a hannunka?" Mahaifin Faruuk ne wanda yaji tamkar an ɗaure mishi baki sai lokacinne ya iya cewa akwai kuɗi amma basu fi dubu ɗari biyu ba, Mutumi mahaifin ƴa ya ce dubu hamcin sun isa sadakin ƴarsa, haka Faruuk ya amsa gurin mahaifinsa aka bada inda nan take kuwa aka ɗaura auren Aliyu Muhammad Aliyu A.M.A da JAMEELAH Mahmud Abdullahi akan sadaki dubu hamsim. Abuturrab kallon mutane kawai yake tamkar wanda akawa asiri ko aka rufewa baki, ƙala ya kasa cewa har aka ɗaura auren inda mahaifin Faruuk ne ya wakilce shi. Faruuk ne ke masa wani kallo cike da al'ajabi "Angon Jameelah!" Yaji bakinsa ya furta daidai lokacin da Aliyu ya ƙaroso kusa da shi "Jameelah!" Ya furta ƙirjinsa na mugun bugawa da sauri da sauri, Mutumin nan kuwa na liƙe da Aliyu duk inda yaga yayi sai ya bisa, bayan angama komi aka fara watsewa mutumin nan ne ya kira Aliyu gefe, wata magana ya faɗa mashi da ni kaina ban jiyo ba sai wata ƙatuwar takarda wacce ko mene ne a ciki? Oho! Da ganan kuma sai ya nemi mutumin ya rasa, haka suka koma gida cike da al'ajabi. Anci gaba da gudanar da bikin Faruuk cikin farinciki ba wanda yasan da auren Aliyu sai wanda yaje gurin. Shi kuwa Aliyu tun da ya dawo gida bai kuma bi takan zancan ba, don duk a tunaninsa mafarki ne yayi ko kuma hasashe hakan yasa sam sai yaji ya manta da batun. Ƙatuwar takardar nan kuwa tun da ya buɗe durowa ya ajiyeta ya manta da batun ta. Washe garin kammala bikin Faruuk ne, Daddy ya dawo sosai aka mishi tarba ta kece raini Ammi kuwa an ɗauki wanka na alfarma an shirya mishi abinci da nasha kala-kala. Misalin ƙarfe sha ɗaya na safe jirginsu ya sauka a filin jirgi na birnin tarayya Abuja direba ne yaje ya ɗaukosa, lokacin Aliyu na ciki yana bacci kamar kasa, har mamakin yawan baccinsa Faruuk yake yanzu domin ada ba haka yake ba. Daddy sai da yayi wanka sannan yazo yaci abinci Ammi sai nan-nan take dashi haka Sareenah cike da girmamawa take komi. Wajajen sha biyu na rana Aliyu ya shugo part ɗin cikin ƙananun kaya, tun da ya shugo Sareenah ke bin shi da kallo har ya sami guri ya zauna kusa da Daddynsa "Abuturrab!" Daddy ya kira sunansa. A hankali ya ɗago kai fuskarsa ɗauke da ɗan murmuahi ya ce"Welcome Dad!" Shafa sumar kansa Daddy yayi ya ce"Thank you Son! Fatan na sameku lafiya?" "AlhamduLillah Dad" Gyaɗa kai Daddyn yayi ya ce"Wai ya batun gurin aikinka? Ko kuwa sallamarka sukayi kazo zaman gida tsawon sati biyu?" "No Dad na amshi hutu ne saboda ina san na huta kuma ga bikin Faruuk amma AlhamduLillah jiya angama komi" "Ma sha Allah" Cewar Daddy ya ɗaura da cewa"Ummaru yayi aure saura kai kuma" Wani irin sauti ƙirjinsa ya bada tunowa da jiya an ɗaurawa Faruuk haka an ɗaura mishi" Girgiza kai ya fara a ranshi yana cewa"Ba haka bane, mafarki nayi" Daddy ya ce"Me yafaru ne kake girgiza kai kamar wani kaɗangare" Chak! Ya tsaya da girgiza kan tare da tuno abin da mutumin nan ya ce da shi... This book is not free. it's N300 via 0037219728 Fatima Rabiu Sunusi Stanbic bank. Then u show ur evidence of payment whatsApp number 08104335144 *MU GANI A ƘASA...* _Hot Love_ ©FATIMA SUNUSI RABIU UMMU AFFAN *Wannan page ɗin sadaukarwa ne ga AMINATU SANI da kuma MAMAN YASEER da MINATU da HAJIYAR ALLAH, Comments ɗinku na sani nishaɗi Allah ya bar zuminci. Masoya littafin nan duk kuna raina ina ƙaunarku tamkar yadda kuke ƙaunar MU GANI A ƘASA... Tabbas kuna nunawa labarin ƙauna na gode.* _YA KUSA FITA KASUWA, MAI BUƘATAR BUGAGGENSA 1K NE KACAL YA MIN MAGANA TA 08104335144_ *Page 11-12* Numfashi ya sauke tare da fesar da wani huci me zafi idanuwansa akan Daddy. Shima zuba mishi ido yayi kafin ya furta, "Kana da wata maganar ne Son?" A hankali ya girgiza kai alamar "A'a" Daddy ya ce"To ya kamata dai ayi maganar auren naka, domin zama a haka bai kamace ka ba" Ammi da ta zauna yanzu ta ɗaura da ce wa"Ƙwarai kuwa Alhaji kullum maganar da nake mishi kenan amma yaƙi ya gane, to Faruuk dai yayi kai ma sai ka bada azama" Zaiyi magana ya fasa sakamakon sallamar Alhaji Hassan mahaifin su Faruuk. Sosai ƙirjinsa ya tsananta bugawa, tun da ya shufo parlourn ya kafeshi da idanu tamkar a ranar ne ya fara ganinsa. Daddy ya miƙe ya tarbi surukin nasa cikin fara'a da girmamawa, hannu suka ba juna bayan sun gaisa duka suka zauna a tare, Ammi ta gaishesa Aliyu kam ya kasa cewa komi sai gabansa da ke yawan faɗuwa. Alhaji Hassan ya ce"Aliyu baka koma bakin aiki ba kenan?" Sai lokacin ya iya sauke kan shi daga duban da yake mishi cikin mury me sanyi ya ce"Jibi nake saka ran komawa Abba, ina wuni?" "Lafiya ƙalau, to ma sha Allahu. Allah ya temaka!" "Amin Abba na gode." Sannan suka gaisa da Ammi ma. Gyara zama yayi yana duban Daddyn Aliyu ya ce"Aliyu ya faɗa maka abin da ya faru a masallaci kuwa?" Damm! Ƙirjin Aliyu ya bada wani sauti, kafe Abba yayi da ido ba tare da ya iya furta ko da kalma ɗaya ba ce. Daddy ya ɗan muskuta ya ce"Bai faɗa mini komi ba, mene ne ya faru Alhaji? Kasan Aliyu da zurfin ciki ga miskilanci na tsiya!" Abba ya ce"Duk zurfin cikinsa bai kamata ya ɓoye irin wannan magana va, domin ba abar ɓoyewa bace" Nan take ya basu labarin kaf abin da ya faru da auren da aka ɗaurawa Abuturrab. Daddy kafe Aliyu yayi da ido wanda yayi saurin sadda kan shi ƙasa. Ammi ta miƙe da sauri "Haba Alhaji Hassan ya za a haɗa baki da kai a aikata wannan babban kuskuren? Wallahi wannan auren bai auru ba." Kallonta Abba yayi ya ce"Tabbas aure kam ya auru, idan ba me shi ne ya warware kayanshi ba, amma tabbas Aliyu yana da aure" "To ba zai yuwu ba!" Ammi ta furta da ƙarfi harta miƙewa ta ɗaura da cewa"Idan ban da an mayar da Alhajin shashasha sai ayiwa ɗansa irin wannan gantalallan auren? To ba zai yuwu ba yadda aka haɗa baki da kai aka ɗaura shi haka zaka nemo gantalallun iyayenta a kwance shi domin ba zai taɓa saɓuwa ba wai allura a cikin ruwa." Daddy da tun ɗazu baiyi magana ba sai yanzu ya kauda idanuwansa akan Aliyu ya ɗaurasu kan Abba kafin ya ce"Amma Alhaji kana gani Aliyu zaiyi irin wannan wulaƙantaccen auren ka kasa dakatar da shi?" "Alhaji Muhammad bai kamata ka furta irin wannan kalma ba" Cewar Abba yana duban Daddyn Aliyu kafin ya ɗaura da cewa"Ko wanne aure ba wulaƙantacce ba ne, baka sani ba ko wannan da kake ganin wulaƙancewarsa shine me tarin albarkar akan wannan yaro, ba zato ba tsammani har mutum ya ɗauki auren ƴarsa bai san waye kai ba ya baka, idan baka gode mishi ba ai baka tsine mishi ba." "Waye shi, me ya mallaka a garin nan ƙasar nan da wajen ƙasar nan da har zai ba ɗa kamar Abuturrab?" Cewar Ammi a ƙufule ta ɗaura da cewa"Wallahi Aliyu yafi ƙarfin ƴar sadaka, Allah sitiri biƙu, yo *Mu gani a ƙasa...* Wannan ma zancen banza zancen wofi ne, daman can an haɗa baki da kai ne domin a cuci Aliyu domin wannan auren ba na Allah da Annabi ba ne" Daddy zaiyi magana Aliyu yayi saurin cewa"Daddy and Ammi ku kwantar da hankalinku, sannan ku dena cewa da haɗin bakin Abba akan auren nan nawa, domin babu ruwansa hasalima shi sadaki ya miyamin da me zan iya biyansa?" "Sadakin banza da wofi, Aliyu bana so ka tafka uban kuren da zakazo kana danasani, dubu hamsim ko albashin me gadin gidanka ya wuce wannan ballantana kuma ace ga matar da zaka aura? Shin kai kuwa kasan irin matar da ta dace da kai?" Ammi ta furta cikin tsantasar ɓacin rai. Numfashi ya sauke domin magana me yawa wahala dake bashi abin baiyi tunanin duk zasu ɗaurawa Abba laifi ba. Daddy ya ce"Aliyu da sa hannunka akayi wannan gantalewar ta aurenka?" Da sauri ya gyaɗa kai alamar "I" Ya ɗaura da cewa"Abba yana zaune ne a gurin amma ni ne nacewa uban yarinyar ina son aurenta." Dam ƙirjinsa ya buga jin maganar da ya faɗa tare da ƙasa da idanuwansa domin baya son haɗa ido da Daddy. Shi kuwa Daddy murmushi ya yi ya ce"Babbar damuwata yi maka abin da baka so, tun da har kai ka aminta da auren to Allah yasa alkhairi yasa abokiyar alkhairinka ce uwar zuri'arka" Abba ne ya amsa da "Ameen!" Ammi ta ce, "Yanzu Alhaji ka bada goyan bayan wannan gantalallan auren wanda baka san da shi ba? To ba zai yuwu ba." Da sauri Aliyu ya miƙe tare da cewa Abba "Taso muje Abba" Babu musu yabi bayansa. Ammi kamar jira take su fita ta fara surfa ruwan bala'i. Daddy dai bai kulata ba har dai da ya gaji shima ya fice, abin da ya ƙara fusata ta, ta dunga masifa ita ɗaya kamar mahaukaciya sabon kamu, wai har Aliyu ne zai aure ba tare da saninsu ba, babban tashin hankalinta ma irin halin da Sareenah zata shiga muddin taji wannan maganar..... A hankali ta fito sanye da dogon hijabinta har ƙasa, "Mtsuww!" Gwoggo taja tsaki kafin tayi gaba. Tataah ta bi bayanta jiki a sanyaye. Kekenapep Gwoggo ta tara suka shiga har lokacin Tataah kanta a ƙasa yake sam bata so ko ido su haɗa da Gwoggon, sun ɗanyi tafiya kusan ta minti goma kafin napep ɗin ya tsaya bakin wani ƙaton gate. Sauka Gwoggo tayi tana ciro kuɗi a jaka, hakan yasa Tataah saukowa don ta rura an kawo inda zasu kenan, Gwoggo na biyan kuɗin ta juya tare da nufar gate ɗin, da sauri tabi bayanta tana duba haɗuwa irin ta gidan. Ƙwanƙwasawa Gwoggo tayi mai gadi ne ya leƙo, ganin Gwoggo suka gaisa kafin ya basu hanya suka shiga ciki. Kai ma sha Allah ba a cewa komi gida ne da ya tara komi, ba shida girma sosai amma ba ƙarami can ba ne, sosai madaidaicin parlourn zai burgeka saboda yadda aka tsara komi a muhallinsa parlourn bai cika tarkace ba tamkar gidan turawa komi cikin tsari. Gwoggo ta zauna saman ɗaya daga cikin jerin kujerun dake parlourn, Tataah sami guri saman carpet ta zauna kanta a ƙasa gabanta na faɗuwa. Gwoggo ta ciro waya tare da yin kira "I Mun ƙaraso!" Abin da Tataah taji ta faɗa kenan ta katse kiran. Kusan minti biyar kafin wata dattijuwar mata da zata kai shekaru hamsin da biyar ta sakko daga benen dake parlourn. Gwoggo na ganinta ta fara washe baki kamar gonar auduga, "Hajiya barka da marece, fatan mun same ku ƙalau?" Sai da matar ta zauna kafin ta ce"AlhamduLillah!" A takaice Gwoggo har da duƙawa ƙasa kamar zatayiwa matar sujjada ta ce"Hajiya kiyi haƙuri fa, da ba wannan yarinyar naso miki ba a can ƙauye na aika ganin har yanzu ba a kawo su ba ita kuma wannan ta yiwa waccen aikin nata riƙon sakainar kashi nace bari na kawota nan kawai." Matar wacce da alamar zantukan Gwoggo sun fara isarta ta ce"Ya isa haka, zaki iya tafiya" Jiki a sanyaye Gwoggo ta miƙe tana hararata "Wallahi idan bakiyi abin da ya dace ba sai kinji a jikinki na dai faɗa miki" Kaina na sadda ƙasa cike da jin takaici a raina sai dai bani da yadda zanyi, har Gwoggon ta kusan fita Hajiyar nan ta kirata, wasu maƙudan kuɗi ta miƙa mata da bazan iya cewa ga yawansu ba, ai nan bakin gwoggo ya buɗe ta dunga ƙwararo godiya kamar ƙyautarsu aka bata! Kodayake a gurinta tamkar ƙyauta ne tun da ba ita zatayi aikin wahalar ba. Da haka ta fice a parlourn. Tataah tana zaune tamkar kayan wanki ba wanda yayi magana daga ita har Hajiyar kusan minti goma suna zaune kamar kurame "Halan a gidanku ba a koya miki yadda ake girmama na gaba ba ne?" Tambayar da Hajiyar ta banko mata ta sauka cikin masarrafar sautinta. Bata ɗago ba domin batayi tunanin da ita take ba ganin tun da ta shugo magana bata haɗasu ba. Hakan da tayi kuwa ya ƙara baƙanta zuciyar Hajiyar ta ce"Titaa kike ko Tataah ba magana nake miki ba?" Sai lokacin ta ɗago cikin sanyinta ta ce"Kiyi haƙuri banyi zaton da ni kike ba!" Mtsuwww taja tsaki tare da miƙewa. "Hajara! Hajara!!" Da sauri wata matashiyar mata da bazata wuce shekaru talatin da ɗoriya ba ta fito, kanta a ƙasa ta ce"Barka da fitowa Hajiya" Bata amsa mata ba ta ce"Ga sabuwar ƴar aiki nan, zata zauna ɓangaren Baheerah ne da zatw dawo gobe, dan haka ki nuna mata duka aikinta." "Angama Hajiya!" Matar ta faɗa Hajiyar ta koma sama ita kuma Hajara ta ce"Yarinya taso muje" Babu musu Tataah ta miƙe, wani part aka kaita wanda suke haɗe da wanda ta fito, sai dai shi bai kai girman na farkon ba yafi shi ƙanƙanta sosai dan ƙaramin parlour ne da ɗakin bacci guda ɗaya sai toilet da ƙaramin kitchen. Saman kujerar da duk tayi ƙura Hajara ta zauna, Tataah kuma tana tsaye domin ƙurar parlourn tayi yawa da bazata iya zama ba da alama an daɗe ba a shugo gurin ba. Hajara ta ce"Sunana Hajara a ɓangaren Hajiya nake aiki ke mene ne sunanki?" "Sunana Tataah!" "Tataah kuma? Ai Tataah ba suna bane" "Uhmmm!" Kawai ta iya cewa domin bata jin zata faɗi sunanta na gaskiya a yanzu. "Ok tun da baki san faɗa mini bazan takuraki ba" Duk abin da zatayi Hajara ta nuna mata kafin ta fita. Tataah kwaɓewa tayi ta fara da gyara parlourn sannan tayi moping tas parlourn, ta shiga ɗakin baccinta nan ma ta share da goge, duk wasu kayan wanki ta haɗasu guri ɗaya sannan ta koma kitchen nan ma ba ƙaramin aiki tayi ba. Duk kayan kitchen ɗin ta wanke ta goge komi su gas saman das ɗin kitchen ɗin da frigde sannan tayi mopping. Toilet ta wuce shima ba ƙaramin wanki tayi mishi ba, A wahale ta dawo parlour ga wata yunwa da take ji, Haraja ce da Hajiyar nan suka shugo, ko ina Hajiya ta fara duba. Hajara ta ce"Sannu da ƙoƙari Tataah duk kin gama aikin? Ina ta ƙoƙarin na ida girki nazo na kama miki" Ƙasa tayi da kai tare da cewa"Ba komi Aunty" Wace baki Hajara tayi cike da jin daɗin sunan da Tataah ta kirata. Hajiya ta ce"Kinyi ƙoƙari Tataah" "Na gode Hajiya!" Hanyar fita ta nufa tana cewa"Hajara idan ta huta taci abinci ki tayata wankin kayan Baheerah" Cike da girmamawa Hajara ta ce"Angama Hajiya" Sallah suka farayi tare da Hajara sannan ta kawo musu abinci mai rai da lafiya sukaci, tana ci tana tunanin Ummanta a hankali ta ce"Aunty har abincin dare za a dinga bamu?" Hajara ta washe baki ta ce"I Mana ai ya zama dole, nifa ke girkawa" Numfashi Tataah ta sauke ta ce"Toni bazan dinga cin na dare anan ba a dunga samin a leda ina tafiya gida da shi" Da sauri Hajara ta dubeta ta ce"Saboda me ƙanwata?" Sadda kai ƙasa Tataah tayi ba tare da ta ce komi ba. Hajara ta lura yarinyar ba mai buɗe ruwan cikinta bace tun da tayi shuru sai bata ƙara tambayarta ba, da haka suka kammala, wajajen ƙarfe bakwai bayan tayi sallar magrib tayi musu sallama Hajara ta zuba mata abinci a wata roba me kyau me murfi sannan sukayi sallama ta wuce gida.... This book is not free. it's N300 via 0037219728 Fatima Rabiu Sunusi Stanbic bank. Then u show ur evidence of payment whatsApp number 08104335144 *MU GANI A ƘASA....* © FATIMA SUNUSI RABIU UMMU AFFAN *Page 13-14* Napep ta tara ta hau, daman Hajiya ta bata kuɗin mota. Har ƙofar gidansu ya sauketa tana biyansa ta nufi ciki, sai da ta ɓoye robar abincinsu a tsakar gida sannan ta nufi ɗakin Gwoggo. Da sallama ta shugo idanuwan Babansu a kan ta yayin da Gwoggon najin sallamarta ta ɗaure fuska tamau, har ƙasa ta duƙa "Sannu da gida Gwoggo" Taɓe baki tayi memakon ta amsa gaisuwar sai cewa tayi"Wallahi Tataah ki ka yi sharmen da Hajiyar nan ta koroki sai kin gane kin tabka babban kuren da warwarensa zata baki kashi, kina ganin dai kuɗin da ta bani kuma nasan duk wata abin da yafi wannan ma badawa zatayi, su ba a ƙasar nan suke zaune ba, kina ganinta ma kin san ba ƴar ƙasar nan ce ba kamar yadda naji wani muhimmin abu ya dawo da ita nan, ƴar ta ma gobe zata zo, don haka kiyi taka tsam-tsam wallahi kinji na rantse ta koroki sai na gana miki azabar da zaki ce dama baki bari ta koro ki ba." Tataah kanta na ƙasa bata ce komi ba, Baba ya ce"Gobe zanje Ningi ko kina da wani saƙo?" Da mugun sauri ta ɗago tuni idanuwanta sukayi rau-rau "Dan Allah Baba kaje da Umma ka barta a can ni zan zauna anan nacigaba da aiki..." "Baza a je da itan ba" Gwoggo ta katseta da sauri ta ɗaura da cewa"Ba inda zataje zata zauna anan ne har ajalinta ya rusketa" Sosai kuka ya ƙwace mini da hanzari na ƙarasa gaban Gwoggo tare da riƙe ƙafafunta na ce"Gwoggon kiyi haƙuri, dan Allah ki amince Baba ya mayar da Ummata ga danginta hakan shine kwanciyar hankalina." Da sauri ta funcike ƙafarta daga roƙun da Tataah tayi mata ta ce"Ai hankalin naki ne bana so ya kwanta, kamar yadda bana son Uwani taje inda zataji daɗi har a mata maganin da zata warke, fatana ta iske kushewarta ba tare da kowa yasan halin da take ciki ba." Da sauri na miƙe saboda kalaman Gwoggo da suka fi komi ɗaci a zuciyata har na doshi ƙofa Gwoggo ta ce "Zo kiga tsarabar da Baban naki yayi" Chak na tsaya ba tare da na juyo ba. Ba tun yau ba na sani mahaifina ɗan ƙarya ne, idan har zaiyi tafiya tofa abin da bai dashi sai ya nemo ko da bashi ne kuwa. Ganin naƙi juyowa ta ce"Tafi dai kar baƙin ciki ya kashe ki tunda da kuɗin aikatau ɗinki aka yi rabin sayayyar" Da gudu ta fita, sai da ta tsaya bayan ɗakinsu tayi kukanta mai isarta sannan ta wanke fuska ta ɗauki abincinsu ta nufi ɗakin Ummanta.... "Wai Ammi da gaske kike ko wasa? Numfashi ta fesar mai zafi kana ta ce"Amma saninki ne bana maganar wasa a tsakaninmu" Wani uban ihuw Sareenah ta saki wanda ya bawa Ammi tsoro sosai har tana ƙoƙarin kamata ai kuwa tayi wulli da ita gefe "Aure fa kika ce yayi Ammi? Wayyo na shiga uku na lalace ni Sareenah, yo mene ne amfani na a duniyar nan idan Aliyu bai zama mallakina ba? Wallahi gara ace mini mutuwa Aliyu yayi da dai ya auri wata a duniya ba ni ba." Ammi dake can gefe zaune, tun bayan hanɓarar da Sareenah ta aika mata ta kasa ma cewa komi. Sareenah ta juyo ganin Ammin taƙi magana sai ta doshi hanyar ɗakinta da gudu tana kuka. Wayarta ta ɗauka ta kira lambar Ma'aruf, yana ɗauka ta sakar masa kuka "Ma'aruf da gaske Aliyu a ɗaura mashi aure ranar auren Faruuk?" Shuru yayi kamar ba zai ce komi ba sai kuma ya ce"Ƙwarai kuwa sunan matar tashi Jameelah abin fa kamar a film ko a mafarki" Kuka ta kuma saki tare da sakin wayar ta faɗa saman katifa, ita ma sulalewa tayi gurin tana rera kuka kamar wata ƙaramar yarinya. Sareenah wuni tayi a ɗaki tana kuka, gashi ba ci ba sha duk ta addabi kanta da tunani ranar wuni tayi ba lafiya zazzaɓi mai zafi ya rufeta, ko da Ammi tazo duba ta kuka ta dunga mata tayi-tayi da ita taci abinci ko kaɗanne taƙi, washe gari ma ko fitowa batayi ba, dabarar kiran aminiyarta Layla ya faɗo mata, kiranta tayi tana ɗauka ta sakar mata kuka. Daga can ɓangaren hankalin Layla ya tashi ta dunga tambayarta damuwarta amma taƙi magana hakan yasa ta ce mata tayi haƙuri ga tanan zuwa. Kusan mintuna ashirin Layla tayi sallama ta shugo bedroom ɗin Sareenah, ai kuwa tana ganinta ta ƙara fashewa da wani irin kuka "Layla ban ga wani amfanin da nake da shi a duniyar nan ba, dan Allah ki faɗa mini abin da zan sha da zan mutu na gaji wallahi na gaji da duniyar nan!" Ta ƙarashe cikin sakin wani rikitaccen kuka. Da sauri Layla ta ƙaraso tare da zama kusa da ita ta ɗagota "Sareenah me ke damunki haka? Kinga kuwa yadda kika lalace?" Cikin kuka Sareenah ta sanar da Layla duk kan abin da taji game da auren Abuturrab. Layla tayi wani murmushi ta ce"Amma Sareenah kin bani mamaki, yanzu saboda Allah akan wannan ƴar matsalar kika lalata rayuwarki kika koma haka?" Da sauri Sareenah ta tashi zaune ta ce"Ƴar matsala fa kika ce Layla, kin san kuwa yadda nake jin Aliyu a zuciyata? Wallahi zan iya kashe ko wacece ta ce zata raɓar mini shi. Aure fa Layla wata ce fa ta aure min mijin da nake burin muyi rayuwar aure tsakanin ni da shi wanda nake saka ran dagani sai shi zamu ƙare rayuwarmu, amma tun kafin ni na zama tashi har wata ta rigani" Ta rushe da wani kuka tana girgiza kai "Wallahi ba zai yuwu ba, sai na nemo ko wacece wannan Jameelahr na sabauta rayuwarta. Wallahi sai tayi da na sanin shiga rayuwar Aliyu" Ta sake sakin kuka me cin rai da gangar jiki. Layla hannu tasa tana share mata hawayenta, kafin ta ce"Sareenah ki natsu ki kwantar da hankalinki wannan fa ba wata babbar matsalar da za a ce har kin damu haka ba ne, kar ki manta kin ce a masallaci aka ɗaura auren ba tare da waliyan Aliyu ba, bugu da ƙari bai san matar ba kuma tun da ya dawo bai kuma maganar ba, wannan auren dashi da babu fa duk ɗaya ne, ba tarewa zatayi ba balle ki damu kanki, zamu iya abin da ma har abada bazai ganta ba yadda akayi auren a wulaƙance kuma ya saketa a hakan dama ba sanin juna sukayi ba" Sareenah ta saki wata ajiyar zuciya mai ƙarfi ta ce"Shiyasa nake ƙaunarki ƙawata kin san sirrin yadda zaki kawo mafita, na gode" Ta faɗa tana share hawayen idonta. "To ya yi ba komi kuma ai kin wuce hakan a gurina ki tashi kiyi wanka kici abinci ki kuma kwantar da hankalinki kamar kinyi baƙo ya mutu." Tana ɗan murmushi ta faɗa bathroom wanka tayi tazo ta shirya cikin doguwar riga ƴar kanti tare suka fito parlourn da Layla suka nufi dinning table Ammi ta ce"Layla sannu da ƙoƙari" Tana murmushi ta amsa da yawwa, Sareenah kuwa ko kallon Ammi batayi ba... AlhamduLillah ango Faruuk ya sami kwanciyar hankali tare da matarsa Hibbah suna gudanar da tsaftatacciyar soyayyar aure bisa koyarwar sunnar ma'aiki Annabi muhammad (S A W). Faruuk yayi wani ƙyau abin shi da ka kalle shi kasan ango ne, Hibbah tana kula dashi ko ince suna kula da junansu ainun. Mami tayi farin ciki da samuwar surika ta gari don Hibbah ta fito daga gidan tarbiyya. "Ai na ɗauka ba yanzu zaka koma ba!" Cewar Faruuk bayan Aliyu ya sanar dashi zai koma bakin aiki. "Hmmm!" Ya fesar da huci kafin ya ce"Daɗina da kai gwalishe mutum, to daman hutun sati ɗaya na ɗauka kuma na sanar da kai" Jinjina kai Faruuk yayi kafin ya ce"Me yasa ba zakayi transfer ka dawo aiki a ƙasarka ba ne? Kaje wata ƙasa da ba taka ba kana hidinta musu, ya kamata kayi tunani Aliyu" Kallon gefen baki ya mishi "Amma ai ƴan ƙasar ne suka koyar dani, shin mene ne laifina dan nayi aiki a ƙasar da su suka koya mini ilmin?" "Da laifi tunda kaima ƴan ƙasarka suna buƙatar jajirtaccen likita kamarka, musamman ma fannin da ka ƙware a kai" Miƙewa ya yi, "Kaga Malam sai anjima!" "Ya zaka tafi honey na kitchen kuma kasan dai kai ta shiga kawowa abinci" "Bana buƙata kuci kayanku, wannan ƴar yarinyar har wani girki ta iya, Faruuk kabi a hankali dai kar rawar kanka tasa ka illata musu yarinyar da bata isa komi ba" Mtsuww! Faruuk yaja tsaki "Wallahi Aliyu idan kana wani abin kamar ba likita ba, Allah ya shiryaka idan kai ka tashi aure ka auro sa'arka dan Allah" Aliyu na dariya ya ƙarasa harabar gidan ya shiga motarsa. Faruuk kuwa daman tun a ƙofa ya koma, kai tsaye gidan Mami Abuturrab ya wuce. Mami ta sa Naanah ta kawo mishi abinci, sosai yaci don dama yunwar yake ji abincin Hibbar ne baya tunanin zai iya ci. Sai da ya gama suka gaisa da Mami ya sanar da ita gobe zai koma bakin aiki, gyaran murya tayi da cewa"Aliyu naji komi game da auren da kayi bayan kammala na Faruuk, amma baka tunanin neman matarka!" "Matarka!!!" YA ƙara nanata kalmar. Murmushi yayi "Mami ki bar wannan maganar wallahi kallonta nake kamar wasan kwaikwayo" "Aliyu auren? Auren ne kake kallo kamar wasan kwaikwayo? To idan bacci kake ya kamata ka farka, maganar aure ba abin wasa bane. Mata dai ta zama taka tun ranar da aka ɗaura aure sannan tarin haƙƙoƙinta ya rataya a kanka tun daga ranar don haka ka farka kasan abin da ya kamata" Sosai jikinsa yayi sanyi ya ce"In sha Allahu Mami zanyi abin da ya kamata" "Hakan dai yafi" Yana barin gidan kai tsaye ya nufi gidansu. A Parlour ya iske Ammi da Sareenah sai ƙawarta Layla, ƙarasawa yayi gaban Ammi ya zauna gefenta "Barka da gida Amm..." Dakatar dashi tayi ta hanyar ɗaga mishi hannu "Wanne sannu zaka mini bayan ka gama watsa mini ƙasa a ido, wallahi ka bani mamaki Aliyu banyi tunanin zaka iya aikata wannan shirmen da ilminka ba!" Ƙasa yayi da kai "Kiyi haƙuri Ammi ban yi hakan domin baƙanta muku rai ba, mutumin ne ya bani tausayi yadda yazo cikin masallaci yana roƙon a auri ƴarsa" "Mtsuww!!!" Ammi taja tsaki mai ƙarfi "Aliyu baka da hankali, yanzu wannan dalilin zai sa ka amince da auren ƴarsa baka san wacece ba? Ba kasan halinta da nasabarta ba? Mata nawa ne ake maka tallarsu akan ka auresu su basu taɓa baka tausayi ba ka amince sai wacce baka san wacece ba, Hmmmm faɗa ma ɓata baki wallahi ƙarya kake Aliyu!!" Da sauri ya ɗago yana dubanta sai kuma ya miƙe, "Daman zan miki sallama ne, wataƙil gobe bazamu haɗu ba don da wuri zan wuce" "Zaka wuce ina?" Ta tambaye cikin ƙaraji, kauda fuska yayi gefe kamar ba zai ce komi ba sai ya ce"Wajen aiki" Yana faɗa ya kaɗai kai ya fice. Sareenah ta saki kukan baƙin ciki yayin da Ammi ta miƙe tsaye cike da ƙunar rai. "Ku kwantar da hankalinku!" Muryar Layla ta sauka masarrafan jinsu "Taya? Layla taya na tambayeki? Kina gani fa kina jifa nikam naga ta kaina, wallahi tawa ta sameni" Sareenah ta furta tare da sakin wani kukan. Ammi dake huci kamar wata kumurcin maji ta ce"Dani Aliyu yake zancen, lallai Aliyu raini ya shiga tsakaninmu, yaron da ko ido bai iya ɗagawa ya kalleni a baya shine yanzu na gaya mini magana, hmmm wallahi zamu gani kuma mu gani a ƙasa dani yake maganar Kuluwa ce fa ya tarowa kanshi faɗan da bazai iya rabawa ba!" Layla wani murmushin ne ɗauke a fuskarta ta ce"Tun da nace ku bari, to ku bari ɗin ni nasan abin da zanyi. Wallahi idan har kun bada haɗun kai sai Aliyu ya raina kanshi sai ya dawo yana binku kamar raƙumi da akala." Ammi na sakin ajiyar zuciya ta ce"Ko wanne irin goyan baya ne zamu bada, matuƙar Aliyu zai auri Sareenah babban burin da nake son cikawa kenan a rayuwata." "To kamar angama" Layla ta faɗa duka suka bita da kallo... This book is not free. it's N300 via 0037219728 Fatima Rabiu Sunusi Stanbic bank. Then u show ur evidence of payment whatsApp number 08104335144 [8/29, 5:21 PM] Sadfat: *MU GANI A ƘASA...* © FATIMA SUNUSI RABIU UMMU AFFAN *Page 15-16* Murmushi ta kuma saki tare da zama gefen coshin, suma suka bita tare da zaunawa. Ƙafa ɗaya ta ɗaura saman ɗaya ta ce"Hakan ba zai samu ba har sai Sareenah ta fara kwantar da hankalinta, sannan muje gurin mai gayya mai aiki da cikawa." Numfashi Sareenah ta sauke idanuwanta na kan Layla kamar yadda Ammi idanuwanta ke kan Laylar. Ammi ta ce"To Sareenah kina ji dai, ki kwantar da hankalinki maganar kuɗi kuma ko nawa ne zan iya kashewa akanki da samun cikar muradinki da kuma cika burina akan Aliyu." Numfashi me zafi Sareenah ta saki ba tare da ta ce komi ba... "Sannu Ummana" Tataah ta faɗa cikin tsantsar nuna kulawa. ''Kin wahala ko? Kiyi haƙuri idan na girma nayi aure zan kai ki ƙasar waje a duba mini lafiyarki ki sami sauƙi. Idan kuma mijina ba mai halin fitar da ke waje bane to zan kai ki babban asibiti a ƙasar nan domin samun babban likitan da yasan matsalar ciwonki Ummana." Shuru tayi na wani lokaci kamar mai tunani sai ga hawaye "Wallahi Umma har na fara hangoki cikin lafiyarki fiye da ta baya, kina magana kina tafiya kuma komi na jikinki yana aikinsa sannan kina gudanar da dukkan ibadunki ba a kwance ba" Hawaye ne ta gani a idon Umman da sauri ta ƙarasa kusa da ita tare dasa hannu ta goge mata "Kuka kuma? Umma kin san abin da nafi tsana shine ganin hawaye na zuba a idaniyarki. Nan ta fara share mata tare da bata abinci taci, tana ta mata hira iri-iri domin zuciyarta ta kwanta. Washe gari da wuri ta wuce gurin aikinta saboda Hajiyar ta ce ƴar ta dake ƙasar waje zatazo suzo da wuri, hakan yasa tun huɗu na dare ta farko bayan ta ɗaura alwala tayi sallah raka'a biyu tayiwa Ummanta addu'a sai taje ta gabatar da duk aiyukanta na gidan kafin a kira sallar asuba tanayi wajajen shidda ta wuce gidan aikinta. Ta taradda Hajara tana ta aiyukanta sakamakon ita a gidan take kwana da sauri taje ta tamata bayan ta gaisheta ta amsa cike da fara'a da jin ƙaunar yarinyar a zuciyarta. Wajajen ƙarfe goma na safe suka gama komi sai da suka karya Tataah ta nufi ɗakin Hajara kwanciya tayi saman katifarta nan take kuwa baccin wahala yayi gaba da ita. Ƙarfe sha ɗaya na safiya jirginsu Baheerah zai sauka hakan yasa tun ƙarfe goma da rabi Hajiya da direba suke Airport. Lokaci na cika kuwa jirginsu ya sauka fasinja suka fara sakkowa, a hankali take sakkowa daga matattakalar benen jirgin, ƙyaƙƙyawa ce sosai fara tas! Kamar a tsaga jini ya fito, kana kallonta zaka gane tana da tsatso da larabawa ko turawa domin fuska kalarta da jikinta da ya nuna hakan, idan kuwa kaji muryarta zaka ƙara gazgatawa. Hajiya na hangota ta fara washe baki cike da farin cikin ganin tilon ƴar ta ta, ita ma da sauri ta ƙara so tare da faɗawa jikinta, sosai ta rungumeta duka suna cikin tsantsar farin ciki. "Mom barka ya kike?" Ta faɗa cikin harshen turanci "Lafiya ƙalau ƴata fatan kema haka?" "Ina lafiya Mom" Cikin mota suka shiga tare da ɗunguma Unguwar da suke. Har suka iso Tataah na bacci Hajara ce ta tarbesu cike da fara'a. Wanka Baheerah ta fara kafin tazo dinning inda taci abincinta cikin kwanciyar hankali sai yaba girkin Nigeria take yi Hajara sarkin barkwanci da zance sai biye mata take suna kwasar dariya, da alama Baheerah tana da sauƙin kai sosai. Sai misalin ƙarfe sha biyu saura Tataah ta farko, toilet ɗin dake ɗakin ta faɗa bayan ta kama ruwa ta wanke baki da fuskarta sannan ta fito direct ta nufi parlourn gidan. Zazzaune ta taddasu suna hira ƙarasawa tayi cike da natsuwa kafin ta zauna saman carpet tana musu sannu da gida, Baheerah ta ce"Wow black beauty, Mom wacece ita?" Ta furta idanuwanta akan Tataah. Hajiya ta ce"Ita ce mai kula da part ɗinki" Har lokacin idanuwanta akan Tataah ta ce"Okey gaskiya tana da ƙyau Mom kalar da ba a saya a kanti" Duka suka saka dariya. Hajara ta ce"Gaskiya ne shalelen Hajiya baƙi fantin Allah" Ita dai Tataah kanta yana ƙasa bata taɓa jin wanda ya yabi kalarta ba sai yau, duk wanda zasu haɗu kusheta yake da ƙyamar kalar tata amma sai gashi yau farar mace ƙyaƙƙyawa tana yabon kalarta. Baheerah ta ce"Wai ke bakiyin magana ne? Mene ne sunanki?" Har lokacin kanta a ƙasa cikin sanyinta ta ce"Tataah!" Baheerah dariya tayi sosai har da tafa hannu ta ce"Tataah kuma? Wannan ai ba suna bane, wallahi sunan ma dariya ya bani" A hankali Tataah ta ɗago kallon Baheerah take wacce ke dariya duka dimple ɗinta sun lotsa kumatunta biyun, dariyar kanta ƙyau ta mana 'Lallai wannan ba ƙarin ƙyau ne da ita ba' Tataah ta faɗa a zuciyarta kafin ta ce"Yaya Baheerah da gaske Tataah ne sunana shi na sani" "Amma dai ba shine sunanki na asali ba" Ɗan shuru tayi sai kuma ta ce"Nima dai ban sani ba" Hajara ta ce"Tataah ƙuruciya na damunki" Ranar Baheerah ta sami farin ciki sosai haka kawai taji Tataah ta shiga zuciyarta jin ta take tamkar ƴar uwarta ta ciki ɗaya.... "Aliyu naji ance gobe zaka koma aikinka?" "I Daddy gobe zan koma" Ƙarasa shugowa Daddy yayi cikin parlourn ya ce"To tabbas ka shirya Baheerah ta iso kaje ku gaisa" Kauda fuska gefe yayi cikin biyayya ya ce"To Daddy" Juyawa Daddy yayi ya bar part ɗin gabaɗaya. Aliyu ya kalli jikinsa ta cikin mirror yaja tsaki a fili ya furta "Wai kamar ni ake son zaɓawa abokiyar zama, ai nayi girma da hankalin sanin komi na rayuwata amma ace har yanzu ban sami wannan ƴancin ba. Duk juyawa sai ya saki tsaki, da wannan tunanin ya gama shiryawa, wayarsa ya ɗauko tare da kiran lambar Faruuk. Har ta ƙarace ɓurarinta ba a ɗauka ba, tsaki yaja jin zuciyarsa yake tazo ƙirji saboda takaici ƙara kira yayi sai da ta kusan tsinkewa ya ɗaga. Cikin wata irin murya da bai san Faruuk da ita ba yaji ya ce"Malam lafiya? A dunga sanin lokacin da za a riƙa kiran mai iyali please." Ƙit Aliyu ya katse kiran yana faɗin "Ɗan iska kawai, ko me zai yaga a jikin wannan yarinyar oho" Car key ya ɗauka saman mirror ya fita a sittin ko part ɗin Ammi bai leƙa ba. Saboda yasan gidan su Baheerah kai tsaye can ya wuce, Maigadi na ganinsa yayi saurin wangale gate domin duk wanda ya tashi a gidan yasan matsayin Aliyu a gidan tamkar ɗan gida yake in dai jama'ar gidan na ƙasar. Guri ya samu yayi parking a ɗan madaidaicin harabar gidan, Iyayen Baheerah masu dukiya ne sosai, mahaifiyarta baturiya ce hakan yasa mahaifinta komi irin na turawa yake babu tsarin fankaɗeɗan gida a matsirinsu komi na turawa suke. Cikin takun ƙasaitarshi ya fara takawa zuwa cikin gidan knowking yayi. Tataah dake kishingiɗe parlourn ita kaɗai ta miƙe, domin sosai take jin daɗin aikinta a gidan ba qasu aiyukan wahala masu yawa idan ka gama komi gar bacci zaka iya idan kana ra'ayi kafin lokacin tafiyarka, Hajiya ce kawai me ɗan matsala ita ma ba sosai ba yanayinta ne haka amma musulma ce sai dai bata da fara'a idan ka kalleta kai tsaye zaka iya kiranta mai zafi amma bata da faɗa sai ka shiga sabgarta. Da sassarfa ta isa ƙofar domin Hajiya na sama Baheerah tana part ɗinta Hajara kuwa tana kitchen. Cikin natsuwarta ta kai hannu ƙofar tare da buɗewa, mutuwar tsaye tayi gabanta na mugun faɗuwa lokacin da suka haɗa ido, da sauri ta janye hannunta a ƙofar, bai ce mata komi ba ya raɓa ta gefenta ya wuce ciki, har ya ƙarasa ya zauna Tataah ta kasa barin ƙofor, ba ƙarin shock ta shiga ba a hankali ta juyo daidai ɗago idanuwansa suka ƙara haɗa ido, sai duk ta daburbu ce"Hmm...hmmm.Hajiya tana sama bari na kirata" Tana gaya tayi saurin barin gurin. Taɓe baki yayi da ɗaga kafaɗa a ransa ya ce"Useless girl kamar na tambayeta!" Ta daɗe tsaye a sama tana mai da numfashi sosai take a tsora ce tun ranar da ta fara ganinsa mugun tsoransa ya shiga zuciyarta, sai da ta dawo daidai sannan ta fara ƙwanƙasa ƙofar Hajiyar Bayan ta bata izinin shiga ne ta shaida mata tayi baƙo a waje sannan ta fito, sim-sim ta wuce parlourn kamar munafuka. Hajiya na sakkowa taga Aliyu ne ta saki fara'a, "Abuturrab yau an tuno dani kenan?" Ta faɗa cikin harshen turanci. Yana murmushi kansa a ƙasa ya ce"Sorry Mom aiyuka ne sukayi yawa" "Maganarka kullum kenan! To Allah yasa mudace" Gaisheta yayi ta amsa ba yabo ba fallasa, daman kuma haka yanayinta yake. "Tataah! Tataah!!" Ta ƙwala mata kira har sau biyu, da sauri ta fito daga ɗakin Hajara duƙawa tayi gabanta "Hajiya gani' "Ki kawowa baƙu abu ya motsa baki" Ƙanta a ƙasa ta amsa da "To'' Cikin sanyinta ta nufi kitchen. "Sannu da aiki Aunty" Tataah ta ce da Hajara "Yawwa Tataah" Ta amsa mata. Donut cake da chifs sai dambun naman kaza da drinks ta haɗa a saman triy tare da cup ta nufi parlour ƙirjinta na bugawa, center table ta jawo saitinsa tare da ajiyewa a sama, har ta juya Hajiya ta ce"Dawo ki zuba mishi idan kin gama ki kira Baby kice tayi baƙo" Da yake Baby Hajiyar ke kiran Baheerah. Ƙirjinta na bugun tara-tara ta dawo Hajiyar kuma ta haura sama, cup ta jawo tare da cika shi da juice zata buɗe dambun naman kazan ya ɗaga mata hannu, a rikice ta ɗago tayi tsaye jikinta na rawa gashi ta kafeshi da ido, shi kuwa fuskarsa na gefe. "Idan mayya ce ke sai dai kici kanki" Ya faɗa cikin wata siririyar murya da sauri tayi ƙasa da kanta dan har ga Allah bata san kallonsa take ba."Wai tsayuwar me kike? Ki ɗan bani guri ko naga haske mana, baƙa mummuna!" Da gudu ta far gurin hawaye na kwaranya a idaniyarta, ta daɗe tsaye bakin ƙofar Baheerah sai da ta goge fuskarta sannan ta shiga. Kwance take hannunta da waya da alama chating take, sallama Tataah tayi bata ɗago ba ta amsa mata sai dai fuskarta a sake take, kusa da ita taje ta zauna "Aunty Hajiya ta ce kije parlour kinyi baƙo" Da sauri ta ɗago "Baƙo!" ta maimaita sai kuma ta miƙe "Okey muje" Kallon shigar dake jikinta tayi, riga ce doguwa amma iyakarta gwiwa, yawancin irin shigarta kenan bata saka riga siket ko wando har ƙasa. Gyaran murya Tataah tayi "Amma Aunty baƙon namiji ne bai kamata ki fita haka ba" Murmushi tayi "No kar ki damu na saba da rayuwata a haka, zo muje" Ta doshi ƙofa, girgiza kai Tataah tayi "A'a ba sai naje ba Aunty" Dawowa tayi tare da kama hannunta suka fita. Tataah dai gabanta sai faɗuwa yake da haka suka ƙarasa parlourn. Shi kaɗai ne zaune, babu abin da yaci wanda Tataah ta kawo mishi, Baheerah na ganin Aliyu ne ta saki hannun Tataah tare da ƙarasawa da sauri kamar zata faɗa jikinsa sai kuma ta fasa tunowa da gargaɗinsa "Sannu da zuwa My Aliy!" Fuskarsa na kallon wani gefen ya ce "Yawwa" Zaunawa tayi gefensa "Kun gaisa da Mom?" "Eh" Ya bata amsa a takaice. Ƙara jawo center table ɗin tayi gabansa tare da fara ƙoƙarin buɗe masa "No karku buɗe na ƙoshi" "Haba dai Aliyu, bai kamata ba ace baka taɓa komi ba" Kallon kayan yayi, baiyi niyyar ci ba amma Baheerah sai da ta buɗe mishi komi ya ɗan taɓa kaɗan suna hira jefi-jefi. Juyowa tayi da niyyar kiran Tataah taga wayam, domin tun lokacin da ta saki hannunta ta ruga itama tayi baya da sauri ta bar parlourn. Kusan minti talatin yana gidan sannan yayi musu sallama kuɗi ya ajiyewa Baheerah ya fita, har wajen motarsa ta raka shi sannan ta koma ciki, ganin har an fara yayyafi gari na ruwa. Hurn yayi maigadi ya buɗe masa yana tafe yana tunanin wai a hakan Daddynsa yake so ya auri Baheerah tana da natsuwa da sauƙin kai amma shi yana mata kallo rashin tarbiyya sam baya jin Baheerah ta dace da tsarinsa. Ganin yadda take gudu a saman hanya ya sashi dallareta da fitilar motarsa, duk ruwa ya jiƙata har rawar ɗari take ganin yadda aka hasketa ta cure jikinta tare da ƙamƙamewa guri guda nan take ta fara hawaye, ƙura mata ido yayi kafin ya kashe hasken, har ya yi gaba sai kuma ya dawo ganin yadda ta tsugunna tana kuka ruwan nacigaba da dukanta. Tataah Ganin me motar ya dawo duk da bata san waye ba ta taso da sauri ta nufi motar, bata jira cewarsa ba ta shige ciki ta zauna kujerar gaba........ This book is not free. it's N300 via 0037219728 Fatima Rabiu Sunusi Stanbic bank. Then u show ur evidence of payment whatsApp number 08104335144 [8/29, 5:23 PM] Sadfat: *MU GANI A ƘASA...* _Hot Love._ ©FATIMA SUNUSI RABIU UMMU AFFAN *Page 17-18* Ƙoƙarin cire hijabin jikinta take saboda jiƙewar da yayi sosai ya haifar mata da jin sanyi, ga shi ita ba shiri suke da sanyi ba yanzu ta fara ciwo, rigar sanyin dake jikinta ma ta jiƙe, hawaye kawai tacigaba da zubarwa kafin ta ɗago ta ce"Mu tafi ma...." Ai ganin wane ne bata san lokacin da maganar tata ta maƙale ba, tayi saurin yin ƙasa da kanta jikinta na rawa kamar ana kaɗa mata mazari. "Idan kin gama shirmen naki zaki iya fitar mini a mota" Gabanta ya kuma faɗuwa lokacin da ta waiga waje ta ga yadda ake ruwa kamar da bakin ƙwarya. "Ki fita nace!" Ya faɗa da ɗan ƙara, a gaskiya sai dai ya kasheta amma bata jin zata iya fita cikin ruwan nan, juyowa tayi cikin rau-rau da fuska ta ce"Kayi haƙuri" Kau da fuska yayi daga kallonta, ganin yaƙi tafiya a hankali ta buɗe murfin motar, sai dai ruwan da taji ya feso mata ne yasa ta rufewa da sauri. Kuka ta saki, bin ta yake da kallo cike da mamaki, "Ke lafiya?" Ya tambayeta fuskarsa a ɗaure "Kayi haƙuri ruwa ake yi" Ta faɗa cikin kuka, bai sake kulata ba yaja motar, nannauyiyar ajiyar zuciya ta saki ganin ya fara tafiya cikin sauri ta sanar dashi unguwar da zata, bai kulata ba har suka isa, "Ga layin nan" Ta nuna masa da hannunta, kallon da ya jefeta da shine yasa ta saurin yin ƙasa da kai ta buɗe murfin motar don zuwa lokacin ruwan yayi sauƙi sosai sai yayyafi da ake, sai da ta fita a hankali ta ce"Na gode" Tare da rufe mishi murfin da mugun gudu ya bar gurin. Girgiza kanta tayi tare da gangarawa layinsu. Sosai ta shiga halin damuwa ganin yanayin da ta taradda Ummanta, duƙawa tayi saitinta tana girgizata "Umma! Umma!! Dan Allah Umma ki tashi" Idanuwan da Umman ke buɗewa yau a kafe ta gansu sai girgizata take amma bata motsi, da gudu ta fita tana kiran "Baba! Baba!!" Gwoggo ce ta fito tana jefa mata wani kallo ta ce"Lafiya?" Tana kuka sosai ta ce"Ummana ce bata lafiya ko motsi bata yi!" Taɓe baki Gwoggon tayi da cewa"Yoni ina ruwa na, ta mutu mana, shi kuma tsohon kin manta yayi tafiya ne?" Sosai kukanta ya tsananta, ta koma baya da gudu, faɗawa tayi jikin Umman bayan shigarta ɗakin, "Ki tashi Umma" Abin da take iya gaya kenan. Amma sam ko motsi Umman batayi, a ranar haka ta kwana jikin Umma tana kuka ko runtsawa bata iyayi ba, garin Allah na wayewa ta fita a rikice gidan moƙocinsu Alhaji Barau ta shiga, bakinta ɗauke da sallamar suna zaune parlourn suka amsa mata zubewa tayi a gurin nan take hawaye suka fara zubar mata "Me sunan wannan yarinyar me ya faru?" Matar Alhaji Barau Hajiya Sabuwa ta tambayeta kasancewar sunan ɗiyarta ta fari gareta shiyasa bata kiran sunanta. Cikin kuka ta ce"Tun jiya da dare da na dawo Ummata bata motsi" "Innalillahi wa'inna ilaihir raju'un muje gidan naku" Ta ɗauki mayafinta dake gefen kujera ta saka ɗanta na biyu Fahat yafi bayansu. Sosai Hajiya Sabuwa ta shiga tashin hankali ganin halin da Ummar Tataah take ciki. "Fahat maza gida ka kira me gadi kazo mu kamata asa a mota mu kaita asibiti" Ta faɗa cike da damuwa, har Fahat ya juya sai ya tsaya sakamakon maganar Gwoggo, "Ba zai yuwu ba, ai mijinta yana sane da halin da take ciki bai kaita asibitin ba dan cutarta ba ta asibiti bace, idan an kaita asibiti ma asarar banza za ayi don ba warkewa zatayi ba" Hajiya Sabuwa ta ɗago cike da tsananin mamakin jin furucin Gwoggon "Haba Zainabu wannan wacce irin magana kike? Baki ganin halin da take ciki ne?" "Ko wanne irin hali take ciki wai ina ruwanku? Shisshigi da ƙwalata da ƙwala kai a faranti kawai, to Malam ya ce kar in sake nabar wani ya fitar mashi da mata daga gida saboda haka kome zai sameta ba ruwan wasu aha" Gwoggo ta faɗa cikin zallar son zuciya. Numfashi Hajiyar ta fesar masu zafi cike da jin baƙin cikin kalaman Gwoggo, Fahat ne ya figi hannun Mahaifiyarsa cike da ɓacin rai suka bar gidan. Tataah ta kuma sakin sabon kuka sakamakon dangwashin da Gwoggo ta aika mata "Munafuka ƴar banza kawai, ke har kinsan ki kira maƙota saboda tsabar wulaƙanci da shegen kinibibi, ai na faɗa miki uwarki Balki a haka zata ƙare rayuwarta" Zubewa Tataah tayi gurin tare da ɗaura hannu a ka tana kuka, bayan fitar Gwoggo rarrafawa tayi gurin Umma tana sake sakin wani kukan cike da tausayin rayuwarsu, ganin kuka ba zai yiwa Ummanta maganin komi ba tashi tayi ta ɗauro alwala tazo ta dunga gabatar da sallar nafila da roƙawa Ummanta samin sauƙi gurin sarki Allah gagara misali. Ƙarfe tara na safe Gwoggo ta leƙo ɗakin "Wai algunguma ba ki tafi wajen aikin ba ne?" Kasa ɗago kanta tayi 'Wanne irin aiki kuma Ummana tana cikin wannan halin' Ta faɗa a zuciyarta, Gwoggo ta sake katse mata hanzari "Tataah magana fa nake miki, ko so kike kwana ɗayan nan da bakije ba ya jawo mana wata matsalar?" Tuni hawaye suka wanke fuskarta "Gwoggo kiyi haƙuri bazan iya barin Ummata cikin wannan halin na tafi aiki ba" "What? Ni nake magana kema kikeyi? Har wuyanki yayi kaurin ina magana kina yi? To maza ki shirya ki tafi aiki kafin na kassara rayuwarki, ƴar banza mai mugun hali na gado" "To!" Ta faɗa a sanyaye cike da tashin hankali, haka tanaji tana gani tabar Ummanta a cikin wannan mawuyacin halin, sai dai ko a gidan aikin ba ta samu wani natsuwa ba haka take duk a furgice Hajara da Baheerah ne suka tambayeta me ke damunta, sai kawai ta ce musu bata da lafiya ne... Abuturrab yana tafe a motarsa yana jan tsaki da haka ya ƙarasa gida, kai tsaye parlourn Daddynsa ya wuce can ya same su tare da Ammi bayan ya gaishe sune yake sanar da Daddy yaje gidan su Baheerah ne, Ammi wacce ko da ya gaisheta amsawa tayi a daƙile jin abin da ya ce ta juyo a rikice. "Baheerah kuma! To me ya kai ka gidan?" Ta tambaya cikin sauri, bai ɗago ba Daddy ne ya ce"Aliyu jeka zamuyi magana" "To Daddy na gode!" Bayan fitarsa Ammi ta ce"Alhaji ya ina tambayarsa kuma ka ce ya tafi?" Gyara zama yayi "Dan Allah Saratu ki kwantar da hankalinki, Baheerah ɗiyar aminina ce kuma kin san da alƙawarin aure tsakaninsu da Aliyu" A fusace Ammi ta ce"Wannan ai zancen banza zancen yofi ne! Alhaji me kake son bayar da ni ne? Bayan waccen maganar ta auren gantali ta aka masa yanzu ma wata kake so ya aura bayan kasan son da Sareenah take mishi?" Girgiza kai yayi "Amma dai kin san bazai yuwu nayi watsi da maganar da mukayi da aminina ba domin yarjejeniya ce tsakaninmu tuni, ke kin san abin da ya faru a lokacin" "Ba wannan magana, don kowa nasa ya sani Sareenah har suma ta dunga yi da taji an ɗaura auren Aliyu waccen koron yanzu me kake so taji? Ko kashe mini ƴa kuke son yi ne?" Miƙewa Daddy yayi ya wuce bedroom yana cewa"Ni dai na gama maganata, bazaki raba mini hankali guri buyu ba" Ganin zai shige ciki da sauri ta ce"To mu gani a ƙasa...'' Shima juyowa yayi da cewa"Zaku gani kuwa!" Ɓam ya rufo ƙofar, zuciyar Ammi ta soyi miƙewa tayi tana zagaye parlourn Layla ce ta tuno da sauri ta koma parlournta ta wuce sama, wayarta ta ɗauka tare da kiran lambarta bigu biyu ta ɗauka. "Layla wai ya maganarmu ne?" "Ammi ki kwantar da hankalinki, yanzu haka aikinku ne akeyi, Aliyun ne yana da taurin kai shiyasa har yanzu ba a sami yadda ake so ba" Numfashi ta fesar ta ce"Layla yanzu haka maganar da Alhaji yake wai Aliyun ma wani auren zaiyi! Shiyasa hankalina ya tashi" "Wani auren kuma Ammi?'' "Eh wallahi shiyasa na kiraki ba shiri, hankalina a tashe yake bana son Sareenah taji wannan maganar mu kammala komi dan Allah sannan har Alhajin a ɗaure mini bakinsa dan na lura shima kamar baya son Aliyu da Sareenah" Ajiyar numfashi Layla tayi ta ce"To Ammi dole yau na koma gurin shi tun da wata sabuwar kuma ta ɓullo" "Shiyasa na kiraki da wuri kafin abin yayi nisa" "To ki kwantar da hankalinki shi da aikinsa yake tamkar yankan wuƙa kafin ayi ne dai" "To Layla na gode zan miki transfer ta account ɗinki" "Badamuwa Ammi" Sauke wayar tayi a kunne, sai da ta turawa Layla dubu hamsim sannan ta ajiye wayar tana saukar da numfashi, a fili ta ce"Wallahi Alhaji daga kai har Aliyun sai kun dawo tafin hannu na, daman a nan kuke aikina ne yayi sanyi yanzu kuwa na dawo da zafina na.... "Hajara lafiya Tataah yau ba ta zo aiki ba?" Baheerah ta tambayi Hajara yanayinta da ɗan damuwa. "Wallahi uwar ɗakina ban san dalili ba, sai dai kin san ance jiki da jini halan ko bataji daɗi ba ne, kin san yau da gobe sai Allah nima tun ɗazu nake maganarta a zuciyata, yawwa kuma jiya da tazo kin san ta ce mana bata lafiya" Numfashi Baheerah ta saki hmmm tare da cewa" Haka ne kuma, Allah ya ƙare mu da lafiya" "Amin" Hajara ta amsa taci gaba da aiyukanta, Baheerah kuma zame jikinta tayi tare da ƙwantawa saman kujerar da take kai, sosai take jin ba daɗi na rashin zuwan Tataah yau. Ta shaƙu da yarinyar jinta take tamkar jini da tsokar jikinta. Tana nan kwance har aka kira sallar azahar Allah sarki Tataah ce ta faɗo mata domin idan har an kira sallah taga tana kwance tana chating zata ce"Aunty Baby an kira sallah ki taso muje muyi!" Ɗan runtse idanuwanta tayi ji tayi kamar ita ce ke gaya mata a yau ma, kitchen ta shiga inda taji motsin Hajara ta ce"Waini Hajara baki san gidansu Tataah ba ne?" Barin abin da take tayi tare da dawowa jikin ƙofar ta ce"Uwar ɗakina ban sani ba, kin san yarinyar da sanyin hali ba komi nata take buɗewa ba." Wucewa Baheerah tayi domin jikin ta taji yana bata wani iri, ranar haka ta kwana babu sukuni. Washe gari ma har ƙarfe sha biyu Tataah bata zo aiki ba, hankalin Baheerah ya tashi sosai, sama ta hau gurin Mom ɗinta. Bayan ta shiga Mom ta kalleta "Baby lafiyarki ƙalau kuwa, naga duk kinyi wani sanyi" Shafa gefen fuskarta tayi "Lafiya nake Mom, dan Allah kin san gidansu Tataah ne?" "A'a me ya faru?" Tagumi tayi, "Mom yanzu baki san gidansu ba kika ɗauketa aiki?" "To taya zan san gidansu ni kuwa Baby? Sai dai ina da number ɗin wacce ta kawota aikin" "Yawwa Sweet Mom ɗan bani ko kira mini ita ma zata fi saurin ɗauka" Ba musu Mom ta kira lambar Gwoggo bugu biyu kuwa ta ɗauka "Hajiya Ina wuni!" Tun kafin Mom tayi magana ta gaisheta cike da ladabi. Baheerah ta ce"Mom ki tambayeta me yasa Tataah bata zuwa jiya da yau?" Tambayar Mom tayi mata bayan ta amsa gaisuwar, rawar baki Gwoggo ta fara "Eh....am...Hajiya kiyi haƙuri bata da lafiya ne" Da yake cikin ƙarar murya ta saka Baheerah tana ji, sai ta ce"Ki ce ta faɗi addireshin zamu zo ni da Hajara" Baki na rawa Gwoggo ta faɗa musu addireshin kafin suyi sallama, da sauri Baheerah ta sauka ɗakin Hajara ta shiga ta faɗa mata zasuje gidansu Tataah ta shirya sannan ta faɗa mata addireshin "Kin san wajen?" "Uwar ɗakina nasan dai unguwar amma layin idan munje sai mu tambaya" ''To badamuwa ki shirya nima bari naje na shirya" Wata riga iya guiwa ta saka tare da gyara gashin kanta me tsawo ta ɗaura ribon, har ta kai ƙofa sai ta tsaya tunowa da maganar da Tataah ta taɓa yi mata wata rana. "Aunty Baby ba dai a haka zaki fita ba?" "To mene ne don na fita haka? Kin san ban saba da rayuwar nan ba" Girgiza kai Tataah tayi ta ce"Ya kamata kam ki saba Aunty domin rayuwar nan da ta can tana da tarin banbanci, ke musulma ce ya kamata ki suturta jikinki idan zaki fita, mutumci mace shine tarbiyyarta kamalarta kuma shigarta, wani ko yaso yiwa mace maganar banza ya duba shigarta zai gane ita ba ƴar banza bace shiga na ƙarawa mutum kamala da mutumci a idanuwan mutane kuma shigarka ita ce mutumcinka" A wannan ranar sai da Baheerah ta canza kaya yanzu ma drowwer ta koma tare da janyo wata doguwar riga har ƙasa ta saka ta yane kanta da ɗan kwalin rigar, ita kanta sai tajita cikin mutumci ba kamar ɗazun ba. Ɗakin Hajara ta shiga ita ma ta gama shiryawa hijab ta saka suka fito harabar gidan, motarta ta shiga Hajara ma ta shiga tayi mata key tare da barin gidan a sittin...... 🤔 *Me ya faru da Tataah kwana biyu bata zuwa gidan aiki???????* _Duk wacce bata biya ma ta hanzarta domin shine na kusa da ƙarshe a free pages, …... Ake jira to, amma dai Hajiyata harkar girma kawai kar ki tsaya jiran a sato ki karanta wannan ƙaranta ce, kuɗin littafin nan daidai aljuhun kowa ne. Don haka ku biya ku karanta ba tsada Mommys Auntys and Sisters domin magana da marubuciyar kai tsaye 08104335144 nasan ba zaku bani kunya ba, ƴan facebook ma zaku iya magana kira ko whatsAp idan ma baki yin whatsAp zamu san yadda za ayi gi dinga samu Ummu Affan taku ce masoyana a ko ina kuke domin labarin yanzu muka fara._ This book is not free. it's N300 via 0037219728 Fatima Rabiu Sunusi Stanbic bank. Then u show ur evidence of payment whatsApp number 08104335144 [8/29, 5:24 PM] Sadfat: *MU GANI A ƘASA...* _Hot Love._ ©FATIMA SUNUSI RABIU UMMU AFFAN *Last free page 19-20* "Ki tashi nace kiyi wanka!" Kuka take kamar ranta zai fita. "Ki tashi nace idan kuma irin bugun jiya kike buƙata, wallahi akan ki tozarta ni sai na miki wanda ya fi shi!" Ta ƙarashe maganar a fusace. Tataah tana jinta amma ko motsawa daga inda take ta ƙasa kuma batajin ko kasheta zatayi zata tashin, riƙe baki Gwoggo tayi cike da mamakin abin da Tataahr ta mata a yau, Ta ce"Wai ba da ke nake magana ba" A hankali ta iya ɗago rikitattun idanuwanta da suka daɗe da rinewa kimanin kwana uku da suka wuce ba wani haske a cikinsu sai ja da tarin damuwa "Gwoggo bazan iya tashi a nan ba, idan kika ga na tashi to nima ajalina ne ya riske ni" Zaro ido tayi "Ni kike gayarwa magana haka? Lallai kuwa yau idan bakiyi abin da nace ba za azo kam a kwashi gayar taki, dan wallahi kinji na rantse idan ban sabauta ki ba sai an kwashi gayar taki" A fusace ta fita ɗakin. Gaban Tataah ya buga da ƙarfi ƙirjinta ya dinga dukan tara-tara 'Tataah mene ne amfanin zamanki a gidan nan tun da Ummanki bata ciki?' Ta faɗa a zuciyarta, hawayenta ya tsananta zuba tunowa da tayi tun ranar da taga Ummanta kamar gawa Gwoggo ta tilasta mata zuwa gidan aiki ranar ana yin la'asar ta taho don ce musu tayi bata da lafiya, amma abin mamaki ko da ta dawo gida sai ta iske ɗakinsu wayau ba Umma babu dalilinta, abin da ya tada hankalinta matuƙa ta dunga kuka da kurma ihuw har Gwoggo sai da ta shugo,ita ma yanayinta ya nuna alamar kaɗuwa rashin ganin Bilkisun wato Umman. Sai ficewa tayi tun daga ranar Tataah ke cikin tashin hankalin kwana da wuni take tana kuka, washe gari bata je gidan aiki ba Gwoggo bata takura mata ba, sai ɗayan washe garin ta ce taje gidan aiki ita kuma ta nuna babu inda zata, shine ta duketa duka sosai duk da farfasa mata jiki, yanzu haka duk jikinta ciwo yake mata ga rashin barci. Tunowa da wannan kuma tasan Gwoggo zata iya fiye da hakan a hankali ta miƙe tana bin bango ta fice daga gidan, tayi nisa sosai taji jiri na ɗaukarta nan take ta zube a gurin a sume...Da muciya Gwoggo ta fito tamkar wata mahaukaci, ka rantse da Allah wani ƙasurgumin ɓarawon ne ta biyu amma sama ko ƙasa babu Tataah babu alamarta, ƙofar gida ta nufa tana cewa"Algunguma waje kika nufa? To wallahi yau ko uwarki Bilkisu ce zata dawo da lafiyarta ta bar hanani lakaɗa miki ɗan banzan duka da muciyar nan yau ko ni ko ke a gidan nan!" Bakinta tsukewa yayi sa'ilinta ta fita ƙofar gida taga babu me kama da ko Tataah a gurin, shuru tayi ta fara dube-dube amma bata, daidai lokacin aka sauke Ruhaima a wata ƙatuwar mota, kuɗi sosai taga an miƙa mata godiya tayi tana ɗagawa na motar hannu wanda da alamar zaiyi sa'an Kakanta. Bayan wucewarsa Ruhaima ta ƙaraso riƙe da jaka tana taunar jingam. "Gwoggo Lafiyarki da farar ranar nan a waje da muciya, ɓarawo kika ji anawa ihu halan?" Wani kallo ta aikawa Ruhaima na kin raina min hankali, irin kallon da kuwa bata taɓa yi mata irinsa ba, taɓe baki Ruhaima tayi tana niyyar shigewa ciki kamar zata bangajeta. Da sauri ta dakatar da ita "Kin ga tsaya ƴar nan, da kika fito baki ga gilmawar Tataah ba?" Baya Ruhaima ta dawo tare da zaro ido kafin ta ɗaure fuska "Gwoggo ba dai kin yiwa yarinyar nan abin da yasa ta gudu daga gidan nan ba? Wallahi idan har haka ne bazan ƙyaleki ba" Kallon mamaki Gwoggo ke bin Ruhaima da shi "Ke kina da hankali kuwa? Kin san da wa kike magana?" "Ƙwarai ina sane Gwoggo ba eh Gwoggo! Gwoggo Zainabu!!" Ta ƙarashe da tsiwa da chono baki gaba. "Ok na gane na ɗauka ko kina tunanin da Bilkisu kike magana ne" Wani kallo ta mata har ta juya zata shiga ciki ta dakata jin uban hurn ɗin da aka bugo musu. Sai da gaban Gwoggo ya bada wani rass! Ganin Baheerah da Hajara sun fito, nan take ta fara sunsunne kai, ganin haka yasa Ruhaima tukare bakin ƙofar dan taga alamar Gwoggon bata da gaskiya. Ai kuwa ta kalleta magana can ƙasa ta ce"Ruhaima me yasa ke ba ƴar rufin asiri bace, dan Allah ki matsa kar su ganni idan sun shugo kice musu bana nan" Jin haka Ruhaima ta ɗaga murya "Sannunku da zuwa bayin Allah, ai nan ne gidansu Gwoggon ga ta nan!" Hmmm ji Gwoggo tayi ina wuta ta jefa Ruhaima tabbas tayi da nasanin kwatanta musu gidan da yanzu hankalinta a ƙwance ba a zo takura mata ba. Dole ta juyo ta tare su da fara'a jagora tayi musu har zuwa cikin ɗakinta, duk suka zazzauna, ruwa leda ta kawo musu guda biyu ta sake zama "Ina wuninku Hajiya ya kuka baro Hajiya babbar?" "Lafiya ƙalau" Baheerah ta amsa a takaice ta ƙisa taga Tataah. Ganin bata da niyyar nuna musu ita ta ce"Gwoggo ina Tataahr ne?" Shuru tayi minti biyu sai kuma ta ce"Halan kuma ta ɗirka muku tsiyar ne? Wannan yarinya hali sak na uwarta babu inda ta barta komi nata na gado me, babu gidan aikin da za a kaita bata baro abin faɗa ba, mu kanmu a gida haƙuri muke da mugun halinta, dan Allah Hajiya kuyi haƙuri babu abin da muka mallaka a garin Habuja duk ƙarya ce, gidan nan ma aronsa aka bamu mu zauna ko sisi bama biya uwarta ta daman baƙin halinta ya hanata zama lafiya kowa baya faɗin alkhairi akanta sai mugun halinta shiyasa take kwance ciwo shekara da shekaru ko kare bai taɓe zuwa ce mata sannu ba, shi kuma uban ya tafi ƙauye ganin kaka tayi ya ɗan samo mana hatsi ita kuwa Tataah sai dai Allah ya shirya wallahi ko kwana gida bata so yin, yanzu haka batun da nake muku kwana biyun nan bata kwana gida ba" Sai ta fashe da kukan munafurci har da shassheƙa ta ɗaura da cewa"Haka ake gayar mini irin manyan motocin da ake sauketa da dare idan tayi niyyar kwanan gidan kenan, to nayi faɗan har na gaji taƙi bari to ƴar kishiya kar ace dan ba ƴata bace na barta sakaka amma wallahi ƴar nan bata jin magana yanzu dai tayi mai kankat kwana biyu bata dawo ba daman ta saba hakan, fara aikinta gidanku ne kawai ta ɗan rage to yanzu abu ya dawo sabo, sai tayi sati bata dawo gida ba" Gwoggo tacigaba da kuka kamar gaske. Tuni ran Baheerah ya ɓaci zuciyarta kuma ta harzuƙa ta jin irin wannan munanan kalaman akan Tataah domin bata yadda ba har abada kuma bazata iya yadda ba. Miƙewa tayi idanuwanta har sun fara ja, da sauri Hajara ta miƙe tana riƙe hannayenta, ko kallon Gwoggo basu kuma yi ba suka bar gidan. Ruhaima ta ce"An dai ji kunya Gwoggo yanzu da girmanki kike ƙarya? Girma dai ya faɗi?" "Ruhaima waini sa'arki ce ko tsararki? Ni na aife ki ko ke kika aife ni?" "Kece Gwoggo amma kin shurgo ƙaryar ne da yawa, gashi har sun gane sun barki nan kile kamar kayan wanki" Mafecin dake gefenta ta wullawa Ruhaimar ta rufeta da ashar "A'a Gwoggo bani nakar zomon ba, rataya aka bani, kuma ɓatan Tataah bakiji nanin ba yacin nima sai na bi mata haƙƙi, haba dan Allah ƴar uwarmu ce fa" A harzuƙe Gwoggo ta tashi "Ki kamani ki kaini ga hukuma dan kaza-kazan ubanki, inda zan gane tabbas ƴar uwarki ce kenan tun da Bilkisu ta haife ki" Zatayi magana Gwoggo ta bita da muciyar hannunta da gudu tayi ciki... A ƙofar gidan Baheerah taci burki tana mayar da numfashi cikin ɓacin rai ta kalli Hajara ta ce"Hajara anya matar nan ba wata manufa a zuciyarta? Ni sam maganganunta basu da wani tasiri a zuciyata!" "Tabbas uwar ɗakina ai maganar gizo bata wuce ta ƙoƙi, kana jin wannan zancen kasan ƙanzon kurege ne" Numfashi ta sauke tare da cewa"Zanyi bincike dole, Tataah zata dawo gidan in sha Allahu, da nasan irin baƙin halin da take ƙunsa kenan gurin matar uba da bata zauna a gidan ba" Hajara ta ce"Bari kawai ai yarinyar zurfin cikinta yayi yawa" Kai tsaye mota ta dosa suna shiga ta bata wuta suka wuce..... "Wai yaushe zaka dawo da aiki anan?" Faruuk dake tuƙa motar ya tambayi Aliyu dake kujerar mai zaman banza idanuwanshi a lumshe. Girgiza kai Faruuk yayi ganin bashi da niyyar amsa mishi, "Amma tambayarka nake ko?" Bai buɗe idon ba ya ce"Ka bari idan ƙwailar matarka tayi ciki, idan zata haihu nazo amsar haihuwar na dawo aiki nan kenan!" Ɗan ɓata rai Faruuk yayi Aliyu ya raina Hibbah da yawa shi kam a rayuwa zai ga matar da Aliyu zai aura. "Kace nan da wata tara kenan?" Da sauri ya baɗe ido ya tashi zaune "What? Wannan yarinyar ce zata haihu nan da wata tara? Kana da hankali kuwa Faruuk?" "A'a ina tunanin da ni da kai duk bamu da hankalin, mu ƙulla alƙawari dai idan har nan da wata tara Hibbah ta haihu zaka dawo aiki a ƙasarka kuma jaharka" Ɗan dariya yayi baya son yin ta amma sosai ta ƙara mishi ƙyau har siririyar wushiryarsa ta fito, "Eh na yarda" Faruuk ma murmushi yayi nan take kuwa suka ɗauki alƙawari tare da tsayar da date. Filin jirgi ya kaishi, suna mota kafin lokaci yayi Aliyu ya ce"Daddy ya matsa min da ina dawowa aure na da Baheerah ni kuma kasan ba wani kwanta mini tayi ba, ko da can abota ce tsakaninmu ba soyayya ba, amma Daddyna da Daddynta sunƙi fuskanta" Ɗan dafashi Faruuk yayi "Kayi haƙuri kayi biyayya zance, Baheerah bata da matsala kai kanka kasan tana da sauƙin kai kuma tana da shekaru irin na macen da kake buri me ilmi sosai komi yayi yadda kake fata kawai ka bada kai bori ya hau musha biki" Dukan wasa ya kai mishi "Daga neman shawara sai abin ya zama zolaya?" "Gaskiya na faɗa, buradinka tun muna yara. Sai dai Aliyu abu guda ɗaya har abada kar ka manta da nauyin wata a kanka *Jameelah* matarka ta sunna da aka ɗaura aurenmu rana guda" Gabansa yayi mugun bugawa sam mantawa yake da wannan auren sai idan an tuna masa, abin da mutumin nan ya bashi ya tuna tun da ya jefa drowwer bai ƙara bi ta kansu ba. Numfashi ya fesar mai zafi jin an fara kiran suna ya sauka yana ɗagawa Faruuk hannu. Faruuk bai tafi ba har sai da yaga tashin jirgindu sannan ya dawo hanyar gida. Ƙira'ar ƙur'ani ya kunna suratul rahman muryar Abdulrahaman Sudees, a hankali yake bin ƙira'ar ya gangalo unguwarsu Tataah ya hango hannu ana ɗaga mishi daga cikin ƙwalta. Gabanshi ya faɗi har ya wuce sai kuma ya dawo, baya hango komi Faruuk da shegen tausayi haka ya sakko a motar ya doshi gurin, sosai ƙirjinsa ya buga ganinta "Tataah!" Ya furta amma ina sam bata motsi, matar da ta ɗaga mishi hannu ta ce"Nima wucewa zanyi na ganta yashe a gurin kamar matacciya" Bai tsaya jin ƙarashen maganar ba ya sungimeta yasa a mota yaja da gudu ya bar gurin ko takan matar da ta tsayar dashi bai bi ba. Kai tsaye asibitin Aliyu ya kaita wannan karon, wanda ya zuba ma'aikata suke aiki. Ana ganin Faruuk da sauri aka amshe su hannu biyu aka nufi emagency room da ita, a gurin ya zauna tare da dafe kan sa. Tunani ya faɗa akan Tataah, tabbas daga ganinta kasan tana cikin wani hali, girgiza kai yayi ya rasa mene ne dalilinta a wancen karon naƙin sanar da shi ainihin wacece ita, tabbas yana jin tausayinta a zuciyarsa kuma yasa a ransa idan har ta faɗa masa to zai temaketa iya kar iyawarsa, karo uku kenan Allah na haɗasu. Yana zaune nan kusan awa guda sannan likitan ya tabbatar da mashi da sun samu nasarar dawowar numfashinta, ajiyar zuciya ya saki tare da hamdala a fili. Miƙewa yayi ya leƙa ɗakin tana kwance na abin zuƙar numfashi ga ƙarin ruwa da ake mata, fuskarta ya kalla tayi fayau duk da bata da haske sai ramar da tayi sosai fiye da ta baya a yadda ya santa, girgiza kai yayi ya cewa likitan dan Allah a kula da ita sosai yana dawowa, ya ce"Haba oga, aka kula da wasu can bare ma balle na gida kuma" Murmushi kawai ya yi ya fice daga asibitin. Kai tsaye gidansa ya dosa, wannan karon bai san sanar da Mami domin bai san ta wacce fuska zata ɗauki maganar ba, so yake sai yarinyar ta farka ta sanar da shi komi yadda zaijewa Mamin da ƙwarin guiwarsa. Hibbah ta amshe sa sosai cike da farin ciki da tareraya irin ta masoya, sai dai ta lura yanayinsa ba yadda ta saba ganinsa ba, bata ce komi ba ta haɗa mishi ruwa yayi wanka sannan suka fita dinning, a baki take bashi abincin tare da daɗaɗan kalamai na kwantar da hankali. "My luv lafiya kuwa? Naga yanayinka ba yadda na saba ganinka ba" Sai da ta tabbatar ya ƙoshi kafin ta jefo mishi wannan tambayar. Numfashi ya fesar tare da kama hannayenta ya ce"Hibbah wata yarinya ce da alamu tana cikin matsin rayuwa!" Ƙura mishi ido tayi gabanta na faɗuwa nan take kuma yanayinta ya sauya, kumallon matan ya motsa. Da sauri ya sake damke hannayenta "Kar ki saka komi a zuciyarki Hibbah Allah ya gani temakon yarinyar nan nake son yi" Nan ya bata labarin komi farkon haɗuwarsu ana ruwa da rashin lafiyarta ya kaita asibiti har zuwansu Mami tare da halin da ya ganta a yau. Da sauri Hibbah ta juyo dan ita ma akwai tausayi kamar mijin nata ta ce"Wallahi har naji ina son ganinta da jin tarihin rayuwarta" Murmushi yayi cike da jin daɗin goyan bayan da Hibbah ta bashi ya rungumeta tare da cewa "Na gode honeyna!" Duka sukasaka dariya, nan kuma zancen ya sauya kala, kinkimarta yayi suka koma bedroom aka lula duniyar ma'aurata. Hibbarsa tana saka shi farin ciki da iya ɗaukar ɗawainiyarsa, a kullum ya tuna da maganar Aliyu sai dai ya girgiza kai Gadanga kenan kusar yaƙi. Bayan sunyi wanka sun shirya, sallar la'asar ya fita yi ita kuma tayi tata a gida sannan ta haɗa abubuwa su abinci tea plate cup, faro da juice a babban basket yana shugowa ya ɗauka tare suka wuce asibitin... Tataah tun bayan da ta dawo hayyacinta ta fuskanci a inda take da sauri ta tashi zaune, duk da jirin da take ji haka ta tsige abin da ke hancinta ta tsige ruwan da ake ƙara mata ta sakko daga gadon asibitin. hijabinta dake gefe ta raruma ta saka, a hankali take takawa har ta fito daga ɗakin. Asibitin bai cika hayaniya ba da alama sai ɗan wane da wance, haka ta fara takawa har ta isa harabar asibitin, juyawa tayi gabas da yamma kudu da arewa, kafin ta fita gate ta ƙaramar ƙofa a hankali, domin me gadi yana gefe suna hira da wani mutumi sam bai lura da ita ba, shi kuma ɗayan mutumin ya ɗauka tazo an dubata ne ta koma, haka ta samu ta fice daga asibitin ta duƙa tafiya ba tare da tasan ina zata ba....... *Mu tara a paid group, ɗungurungun, tarin amsoshinku mu tara acan ni bazan ce komi ba yanzu, magana guda ko gundarin labarin ba mu shiga ba tukun. Labarin rayuwar Tataah mai cike da tarin sarkaƙiya😥 Fesa muku abu kaɗan afkawarta cikin wata al-umma da ba tata ba, koya makomarta zata koma a cikin al-ummar da ta kasance addininsu ba guda ba? Amsar na gurin Ummu Affan, sannan wacece Jameelah sai kun biyoni tsantsar tausayi abin al'ajabi soyayya kulawa sai a rayuwar Tataah, ku biyoni muje zuwa kuɗin ba mai tsada ba ne.* _Alƙalamin ƴar mutan Funtua Katsinawan dikko ɗakin kara Fatima Sunusi Rabi'u Uwar Affan._ This book is not free. it's N300 via 0037219728 Fatima Rabiu Sunusi Stanbic bank. Then u show ur evidence of payment whatsApp number 08104335144