LITTAFIN KUƊI NE ₦500 VIA 0009450228 AISHA ADAM JAIZ BANK SAI SHAIDAR BIYA TA 08081012143 YOUR RECEIPT VALIDATE YOUR PAYMENT. "Cikin cunkusa baki ta ce ""To kuma shi ne zaka tsorata ni? Ko gama wankan ban yi ba na fito""" "Ya ce ""To mu je na ƙarasa miki""" "Tsuke bakinta ta yi ta kasa magana, jin abun da yake yi, da ba ta yi zato ba." "Kasancewar bayanta, yana jikin ƙirjinsa, yana jin bugun zuciyarta yana fita da sauri-sauri." """Meyasa ki ke shareni? Kwana uku kin yi mini laifi, kuma kina gaba da ni ko?""" "Ba ta yi mamakin ƙarfin hali, da ƙwarewa a iya rainin hankali, irin na Al'amin ba, wato ma" zaman jiran ta bashi haƙuri yake yi. """Kin san zaki yi gaba da ni, meyasa ki ka bari muka saba? Ba ni da saurin sabo, ki ka yaudare ni ki ka sa na fara sabawa da ke, shi ne zaki wani din ga mazewa. A din ga manta abu a kwana ɗaya ya wuce kawai a cigaba da life. Ni kaina ban san dalilin da ya sanya nake matuƙar jin baƙin ciki" "idan na ga wani abu ya raɓe ki ba""" "Da ƙarfi ta ce ""Master"" tayi maganar tana ƙoƙarin miƙewa." "Hankali kwance ya ce ""Yes"" ba tare da daina abun da yake yi ba." "Cikin rauni ta ce ""Wai meye haka?""" """Aure"" ya bata amsa kai tsaye." "Shiru yayi, jin yadda zuciyarta ke cigaba da bugawa da sauri, tana nema ta fara haki, saboda tsoro." "A hankali ya ce ""Common, relax mana""" """Babyn roba"" tayi masa shiru, ""Kodayeke yanzu babyn ƙarfe ce, ki amsa mana"" still ta yi masa" "shiru, yana jin yadda ta saka ƙarfinta ta riƙe hannunsa." "Fito yake yi mata a kunne, hakan ya sanya ba shiri, ta saki hannunsa, ta toshe kunnenta." """Ki amsa mana, tambaya zan yi miki mai muhimmanci. Kin san bana mantuwa, kamar na'aura mai ƙwaƙwalwa nake, in dai ka ajiye zaka zo ka ɗauka. Idan ban manta ba kin ce kina so mu rayu tare. Ina ta tsoron taɓa abun da nake ganin ban dace da shi ba. Ba na son cutar da rayuwarki, in yi silar gurɓacewarta kamar yadda tawa ta gurɓata, duk da kin daɗe ki na nuna mini ina rintse ido," "Al'amin ba ya abu bisa zalunci""" """Na nuna maka me?""" """In faɗa kenan, ko shekaranjiya meya kawo zancen zuriya? Ke 'yar yarinya kallonki kawai nake yi, amma kar ki damu da hakan ai lafiya ce"" wato da wani ne yake ba wa jauhar labarin maganganun nan daga bakin Al'amin suke fitowa, sai ta ƙaryata, amma ƙiri-ƙiri, ya shige duhu yana sakin" "maganganu yadda yake so, alhalin ya ce ba ya jin komai." "Tana cikin tunanin ta ji ya ce ""Kin amince mu rayu tare, a matsayin abu guda? Ba na son cutar da ke, ke ma kin shiga ƙalubale da dama, bana son ki sake shiga matsalar rayuwa, rayuwarki ta tafi a haka kawai. Idan kin amince, zan yi iya ƙoƙarina wurin zama da ke da zuciya ɗaya, amma sai kin yi wa yanayin rayuwata uzuri, duk da a yanzu ma kin taka muhimmiyar rawa a rayuwata. Be" "mine""" "Haka kurum ta fara kuka, kukan da ba ta san na menene ba ma." """Talk babyn roba""." """To ka ƙyale ni, gobe da asuba sai na gaya maka""" "Cikin buɗɗiyar muryarsa, da take fitowa daga ƙirjinsa, ya ce ""Na ƙi wayon, yanzu zamu gama" "maganar""" """Master""" """Mmmm""" """To zaka daina saka ni kuka?""" "Ya ce ""In sha Allah""" "Ta ce ""Zaka daina shaye-shaye?""" """In sha Allah, ina iya ƙoƙarina, ba abu ne da zan daina lokaci ɗaya ba. Mu bar wannan maganar," "baki bani amsa ta ba, zaki cigaba da zama da ni, a yadda nake, ina talaka marayan da ya rasa kulawa, sai bayan shigowar ki rayuwata?""" "Tana kuka ta ce ""Dama ai kai ka ke cewa zaka sake ni, ka ke sakani kuka, ina son in zauna da kai""" "Yayi ajiyar zuciya ya ce ""Duk wani abu da ki ka yi mini na alkhairi, yana rubuce a ƙirjina, ba zai taɓa gogewa ba, ban taɓa mantawa da ko guda ɗaya ba, babu wata mace da ta taɓa playing role ɗ" "in uwa a rayuwata sai babyn roba, bashi ne a kaina kulawar da ki ka yi mini""." """Ni saboda Allah nake kula da kai""" """Ni na isa in biya ki ne dama?""" "Jauhar ido yayi tsilli-tsilli, bayan da Al'amin ya ƙaryata tunaninta na ko ba shi da lafiya ne." "Ya tabattar su a matsayin miji da mata. babu tsammani aka kawo wuta, haske ya gauraye ɗakin, Jauhar ta takure jikinta, sai rawa jikinta yake yi, yayi murmushi ya ja bargo ya rufeta." "Ya zuba wa gashin kanta ido, ba baƙi ne wuluk ba, amma mai laushi irin na fulani, ya hargitse, ta" cusa kanta cikin bargo sai gashin a waje. "Ya daɗe yana kallonta, kafin ya kai hannunsa yana shafa gashin ya ce ""Amm ya ma sunan angela" "ko?"" Tayi masa shiru, ta sake dunƙulewa wuri ɗaya." "Ya cire bargon daga fuskarta, amma ta rintse idanunta." """Kalleni mana, abu zan gaya miki fa""" "Ta cunkusa baki, tana ta jan majina a hancinta, fuskarta duk ta yi ja saboda kuka." "Wani nishaɗi yake ji, ya cigaba da kallonta yana ta murmushi, kamar wanda aka yi wa Albishir da" kujerar makka. "Wayarsa da ta faɗa ƙasan gado ce, ta fara vibrating, ya juya ya zura hannunsa ya ɗaukota, ya sake" "matsawa kusa da jauhar, ya ɗaga wayar." """Maza"" muryar liti tayi amsa kuwwa a wayar." """Mmm""" """Kana ina ne?""" "A taƙaice ya ce ""Gida"" yayi maganar yana cigaba da shafa gashin jauhar." """Wai me ka ke yi ne? Ko baka da lafiya ne?""" "Al'amin ya ce ""Meyafaru?""" """To ai ji nayi kana amsawa kamar ana yi maka dole""" """Ina jinka ya aka yi?""" "Liti ya ce ""Akwai matsala ne fa""" """Ta me?""" """Yaran madaki, duk sun cire pastocin indabo, ka san ɗazu Walid da su guduma suka gama sasskawa, mu na dawowa muka tarar duk sun cire, ya tambaya aka ce masa yaran madaki ne, gashi can ya tafi, nayi-nayi ya ƙyale su, ya ɗau wuƙa ya tafi, shikaɗai kar su yi masa wani abun," "ka san Walid da baƙin taurin kai, kamar jinjirin jaka, dan yafi jaki taurin kai""" "Al'amin ya ja guntun tsaki ya ce ""Gani nan, bari na tafi cikin garin, maza ka kira yaran nan, ka yi" "magana da su guduma ma, zan kira yaran unguwar mu, maza su bishi kar su yi masa wani abun, gani nan"" ya yinƙura zai tashi, jauhar ta ja jikinta ta riƙe shi ta ce ""Rigima zaka je ka yi ko?""" "Ya girgiza mata kai ya ce ""Ba rigima zan yi ba, amma idan har ba a kai masa ɗauki ba, za su iya" "kashe shi""" "Cikin takaici ta ce ""Kana ganin halin da ka sakani, a haka zaka tafi ka bar ni, a wannan yanayin" "da nake ciki?""" "Ya ɗagota ya ce ""Ki yi haƙuri, bana son a sake asarar rai saboda ni, wallahi suka ga Walid shikaɗ ai, za su iya kashe shi, am sorry yanzu zan dawo, ki kwanta kar ki tashi kina buƙatar hutu"" ya ƙ" arasa maganar yana kwantar da ita ya bar ɗakin. "Ta lumshe idonta, hawaye suka cigaba da zuba, sai da ta yi ta gaji, sannan ta saukko daga kan" "gadon da kyar, ta haɗa ruwa mai ɗumi sosai ta tsarkake jikinta, ta nemi wuri ta kwanta." "Da asuba da ƙyar ta tashi, ko alwala ba ta yi ba, ta tafi ɗakinsa ta duba, ko ya dawo cikin ƙoshin" lafiya. "Ƙarar buta ta jiyo a banɗakinsa, alamar yana alwala, wani ɗan sanyi ta ji a ranta, yau da kansa ya" "tashi sallar asuba, ko yaushe ya dawo ma oho." "Ta koma ta yi salla, ta sake fitowa ta leƙa, ta ga yana salla, ga kayan shaye-shaye a kan katifarsa," "ganin yana salla, ta shiga kanta tsaye, ta tattare kayan ta fice." "Bacci ya ƙara kwasheta, tana cikin baccin ta ji ta a takure, ta yi miƙa ta buɗe idonta, ta saka a" nasa. """Kalli agogo ƙarfe sha ɗaya, yunwa duk ta yi mini illa, na sayo ƙosai na kasa ci, ya ja mai, kuma" farin maggi ya yi yawa a ciki sosai. "'ikon Allah, shi ko ɗan rarrashin nan ma ba zai yi bs, zancensa kawai abinci." "A ƙule ta ce ""In da ka tafi ba su baka abincin ba?" """Me ki ka ce?""" "Ba tare da ta kalleshi ba ta ce ""Na ce in da ka tafi ba su baka abincin ba?""." "Ya ce ""Ba su bani ba, ke zaki tashi ki bani yanzu""" "Kawai ta juya masa baya, dan daren jiya ta ƙulu yadda ya tafi ya bar ta." "Ba ɗaga ƙafa, ba komai, ya ƙara huce baƙar maganar da ta gaya masa, ya gama ya tada kai da" "jikinta, ya lumshe ido ya hau bacci." "Ta gama koke-kokenta, duk iya ƙoƙarin da tayi, ta ture shi ta tashi, ta kasa sai ma ji da tayi tana" "haki, Al'amin ya gama raina mata hankali ta ko ina." A haka har baccin dole ya sake yin gaba da ita. Ƙarshe har azahar ko wanke-wanke ba ta yi ba. "Ta yi wanka, ta canza kaya, ta fito ya basar da ita, kamar babu abun da ya faru, ta tarar da shi da wayarta a hannunsa, yana game, ta share shi ta wuce, sai da ta fita ya bi bayanta da kallo yana" murmushi. "Ta tarar yayi wanke-wanke, ya share tsakar gidan tsaf, har markaɗen kayan miya ya kai." "Ta dawo ta koma ɗakinta, ta ɗaukko bedsheet, zata fita ya ce ""Me zaki yi ne?""" """Wanki""" """Me ya same shi, zaki wanke? Ko karyawa ba ki yi ba? Ki saka shi a baho, zan wanke, ki samu ki" "karya""" "Sai cika take tana batsewa, mazewa kawai yake yi, don dariya yake son yi, amma ya maze shi ma" ya sha kunu. "Tun da ya kai markaɗen nan, ya dawo bai sake fita ba, wuni guda yana gida, duk da babu wanda" "yake kula wani, amma zaman kula da ita yake yi." "Har isha'i, kowa ya koma ɗakinsa, har ta kwanta, ta ji ya shigo ɗakin, kan tayi magana ya ƙaraso" kan gadon ya hau. """Malam ya ne? Menene kuma?""" """Kamar yaya?"" Yayi maganar yana janyo bargonta, ya rufe ƙafarsa." "Kamar tayi ihu ta ce ""Menene kuma?""" "Ya ce ""Da na kawo miki kajin mutum goma sha biyu, ki ka cinye ki ka yi kyautar wasu, kin" "tambayi ta mecece?""" "Cikin rashin fahimta ta ce ""Ban gane ba, ka ce a gidan oganka ka karɓo""." """To gaba sai ki dinga tambaya, kwaɗayayyiya, ki ka din ga ci kina rabarwa, ni sai dai ki sammini," "yanzu kuma tambayata lafiya? Ba lafiya ba""" "Cikin rauni ta ce ""Master"" ya ce ""Yes""" """Dan Allah ka koma ɗakinka"" ya kwanta ya ɗora ƙafarsa ɗaya kan ɗaya ya ce ""Zuriya fa ki ke" "so, ki ke wani basarwa"" Jauhar ta yi danasanin faɗar maganar nan." "Kawai ta zauna a zaune tana kallonsa, sai kaɗa ƙafa yake yi." """Zo ki kwanta, na ga lokacin da baki da lafiya, har wani ƙara lafewa ki ke yi, bisimillah"" yayi" maganar yana nuna mata ƙirjinsa. "Pillow ta gyara ta kwanta a kai, ta ƙi kula shi, mutumin da suka wuni ba sa magana, saboda tsabar" "son tayar da tarzoma, ya lallaɓo yana tayar da wani tsohon zance." "Da asuba ta riga shi tashi, ta shiga ta yi wanka, tayi alwala ta zo tana tashinsa, ƙarshe sai kusan shida da rabi suka yi sallar, bayan ya saka ta canza wani wankan da alwala. A wurin da tayi salla," ta kwanta a kan sallaya ta cigaba da bacci. "Iya ƙoƙarin sa yake yi kar ya sha komai, ya kasa jurewa, kamar zai fita hayyacinsa, ya lallaɓa ya dawo ɗakinta, ya tarar tana kwance a ƙasa tana bacci, boti ma yayi lakur a kan sallayar yana" bacci. "Tankaɗe boti yayi can gaba, ya kwanta a kusa da ita, ya ƙura wa fuskarta ido, ya kai bakinsa ya" sumbaci goshinta. "A ranar aka saka wa jauhar fankar solar, da ƙwai, ta din ga murna tana yi masa godiya." "Sai dai Al'amin ya uzzura mata, duk dare, sai ya ce mata wai shan fanka ya zo, zafi yake ji, sai da" "ta gaji ta ce ""Dan Allah master ka ɗauke fankar nan taka ka mayar ɗakinka , ko na huta""" "Ya ce ""A'a ai dama ke na sayawa, dan haka gara na din ga zuwa nan kawai ina shan isakar, idan na" "mayar da fankar can, bayan iska kuma takura mini za ta yi din ga yi""." "Ta ce ""A taƙaice dai, ni ce fankar kenan?""" "Ya ce ""Eh mana, ke ga taki fankar, ni kuma ga tawa"" yayi maganar yana nuna ta." *** "Kwanaki suka cigaba da tafiya, sai dai tsakanin Alhaji mu'azzam da Hafsa sai dai kallo, ranar da uwargidansa ta bari ya zo ɗakin hafsa, kawai ta ga ya nemi wuri ya kwanta." "Duk da irin kunya da kawaici irin ta 'ya mace, sai da ta cire kunya ta ce ""Wai ni Alhaji, menene" "matsayina a wurinka ne? Na kasa gane kan wannan al'amarin""" "Ya kalli hafsa ya ce ""Jauhar, yakam..." "A fusace ta ce ""Wace irin jauhar kuma? Wulaƙancin naka da rashin mutunci har ya fi da, ga mari" "ga tsinka jaka? Tun ranar da jauhar suka zo, ka rasa sukuni, ka ke kirana da sunanta ba na so""" "Ya ce ""Am sorry mistake ne, ki ƙara haƙuri ki bani lokaci, na yi wa Safiyya Alƙawarin babu abun" "da zai shiga tsakanina da ke, har sai lokacin da ta samu nutsuwa hankalinta ya kwanta, tana cikin damuwa sosai da sosai, kin san tana da kishi ne sosai da sosai ""." "Kamar ta ɗura masa ashar ta ce ""Au har gaya mata ka ke ba abun da ya shiga tsakanina da kai, har sai ta yadda? Ita take aurena kenan? Bakomai na gode, ta ci lokacinta when it comes to my turn, zata gane shayi ruwa ne"" ya girgiza kai ya ce ""Kin ga ba na son rigima, ba zaki zo ki sameni, ina zaune lafiya da iyalina ki ɗaga mini hankali ba Please, ina respecting farincikin matata sosai da" "sosai """ "Hafsa ta ja tsaki, ta fice ta bar masa ɗakin." "Al'amin na zaune a falon Indabo, ana ta tattauna yadda al'amura za su tafi kafin lokacin zaɓe, dan" "wata ɗaya kawai ya rage babban zaɓe, wanda yake dai-dai da lokacin sallar layya." "Ya rage daga Al'amin sai P.A da Indabo yana ta sake jaddadawa Al'amin, idan aka ci kujerar nan za su ji daɗi, dan tun yanzu an ce masa idan ya samu senator ɗin nan, akwai vacancyn mutum uku za" a bashi a NNPC. "Al'amin ya ce ""A cikin yarana, ko Nura guduma ne, ina son a samo masa aiki ko direban manyan" "motoci ne, yana can na saka ana koya masa jan manyan motoci""" "Indabo ya ce ""Ba ka da matsala, kawai ku yi aikinku, duk akwatin da ku ka ga zata bayar da" "matsala, ku tayar da tarzoma. Maganar da nake yi maka, a yarjejeniyar da muka yi da uwar" "jami'iyya ta ƙasa, kan na dawo cikinta, nan da wasu shekaru, za a tsayar da Abdul takarar" "mataimakin gwamna""" "Al'amin ya ce ""Har masu shaye-shaye ake tsayarwa su yi jagorancin al'umma kenan?""" """Shaye-shaye kuma, yaron da yake karatu a waje, in sha Allah shi zai zama mutum mai ƙarancin" "shekaru da zai zama gwamna""" """Menene sadakin aikina?""" "Indabo ya ce ""Me ka ke so ayi?""" "Hajiya Bilki ce matar indabo ta shigo da laces, da atamfofi da lesuna sun kai talatin a hannunta, ta" shigo ta zube a gaban Indabo. "Ya kalleta ya ce ""Madam ya dai?""" "Ta ce ""Kala goma zan zaɓa ka saya""" """Ke dai kullum cikin ɗinka tsumma, ko gajiya ba kya yi""" """Kana shirin zama distinguish, ba dole na ɗinka sutura ina shiga ina fita, ina barazana ba""." "Indabo ya ce ""To ki ɗauka, ina ta jiran Kwamishinan ayyuka ne, rage kuɗin wata kwangila, mu ƙ" "ara rage na campaign, ya haɗa kayansa yana kan katanga, jami'iyyar da tayi nasara zai koma da an yi zaɓe." "Ala'amin ya tashi ya tafi gaban kayan, ya zaɓo zuƙa-zuƙan lesuna, guda uku, da atamfa uku." "Indabo ya ce ""Yaya saya zaka yi?""" """Kai dai zaka saya, daga cikin sadakin aikina""." "Hajiya Bilki ta ce ""Kai, lesunna hannunk fa dubu tamanin guda biyu, ɗaya dubu hamsin da" "takwas, atamfofin nan dubu arba'in da biyar, har nawa zai baka? Kuɗin da yawa ai""" "Ya kalleta ya ce ""Ke zaki biya? Kuɗin kwangilar mutane za a sata a biya miki ai, wannan ma ya biya, ai ba kyauta zai bani ba, jinina da rayuwata zan saka a hatsari dan samun nasararsa. Ya miƙe da kayan a hannunsa, ya kalli Indabo ya ce ""Sauran kuɗina za su zama ajalan a kanka, komai daren daɗewa zan waiwaye su, yadda ku ke ƙwamusar kuɗin mutane ta gajimare dole a din ga kasawa da mu, idan ana son a ga dai-dai, tun da damu ake wahalar waccan 'yar yarinyar ta gidana," "itama yakamata a din ga damawa da ita. Kuma rabon tallafin karatu ma, a saka mini ita a ciki""" "Indabo ya ce ""Aminu kenan, shikenan jeka Allah ya taimaka""" "Ya haɗa hannayensa biyu ya ce ""Sa'a dai"" ya fice daga falon." "Hajiya Bilki ta ce ""Gaskiya honorable, yaron nan yana wuce gona da iri, kamar tsoronsa ka ke ji""" "Ya ce ""Ba tsoronsa nake ji ba, aikin da yake yi mini yana da yawa, kasada duk girmanta yana ɗ" "auka. Akwai lokacin da tilas na yakice shi ai""." "Al'amin bai shiga da kayan gida ba, sai cefane da yayi na abincin dare." "Ya tarar ta yi dambu tayi wa dambun miyar jajjage, da salad da awara." """Ke dai Allah ya yi miki iyayi, dambun da ake sakawa mai, ki ke yi wa miya, har da wata" "munafukar awara""." "Jauhar ta ce ""Idan munafuka ce, bamu mu raba da ni da boti, shikenan ba canji, kullum sai dai" "dambu da mai? Ai gara a din ga upgrading""" """Sai dai ya mutu da yunwa kuwa, to ai awarar ce, 'yar kaɗan""" """Wai master ba ka iya abun 'yan gayu ba? Babu naman da zan saka a cikin miyar, sai na haɗa da" "awara, bai bada ma'ana ba? Ko sai an cika kwanon da awarar passion ce a kai""" "Ya taɓr baki ya ce ""Eh to, gashi nan dai, zoɓon ma kamar yayi tsami, amma kwantai ne na jiya ne" "ko?""" """Mmmm, na waccan shekarar ne"" ta bashi amsa tana cigaba da aikin gabanta, na shirya stone." "Tsoknarta yake yi, ya matsata tayi tsiwa, ita kuma taƙi." """Yaushe WAEC ɗin ku za ta fito ne?""" "Jiki a sanyaye ta ce ""Ta kusa, har ba na son tunawa da ita""" """Saboda ba ki yi abun arziki ba ko?""" """A'a lokacin kana tsare, bana iya karatun""" "Ya ɗan rausayar da kai ya ce ""Eyya, abun tausayi, Yallaɓai dan Allah ku sake shi, ba shi da laifi, laifina ne, wallahi ba shi da lafiya ma, master dan Allah ka gaya musu ba ka da laifi"" yayi maganar" cikin sigar kwaikwayon yadda ta yi waccan ranar. "Murmushi ta yi ta ce ""Kada Allah ya kawo abun da ba zai wuce ba, a lokacin nan ji nake a duniya" "kamar nikaɗai aka tsana wallahi. Da aka ce mini an kai ka prison, kawai na saddaƙar ciwon zuciya" "ya kama ni, kuma wai ka ce kar a kaini na ganka, ai na ji haushi, a duniya ba zan manta da su yaya" "walid ba, duk da suna taimakawa wurin ƙara ingizaka a shaye-shaye, amma sun tsaya tare da ni a lokacin da kow yake ganin idan ya taimaka mini zai kwana a ciki""" "Ya ce ""Allah sarki 'yar madara, ba na son in ga kina kukan nan ne, ko kina yi wa 'yan sanda" "magana, suna wani yanƙwana mini ke, raina ɓaci yake yi shiyasa na ce kar a sake kawo ki""." "Ta ce ""Gashi ya wuce, duk da lokacin gani nake kamar ba zai wuce ɗin ba""" "Ta tashi ta shiga ɗaki, ta dawo ta tarar da robar alawar madarar da take sayarwa, a gefensa bakinsa" "kuma yana ta tauna, ta ɗaga robar ta ce ""Alawata ka ke sha ko?""" """Eh, ta guda uku na sha sittin, a rage mini naira goma hamsin kenan""" "Sororo take kallonsa, ""To ai ba a jikina ake tatso madarar ba, da zan sayar da ita ashirin ashirin," "naira hamsin ce fa duk ɗaya """ "Ya waro ido ya ce ""Ki ji tsoron Allah, har na sha ta ɗari da hamsin, gaskiya saba'in zan bayar""." "Abun da yake so ya gani ɗin ta fara, shagwaɓa tana cewa sai ya biya ta." """Gaskiya bani da kuɗi yanzu, zo ki shanye abarki"" ya fito mata da harshen sa." "Ta harare shi ta ce ""Bana so, kuma idan na zo yi maka wanki na tsinci kuɗi, sun zama nawa""" """Eh ai dama kin saba kwashe mini 'yan canjina, da kayan cajina shiyasa ki ke yi mini wanki ba dan Allah ki ke yi ba"" ya tashi kamar zai tafi, amma ya riƙeta, yayi kissing ɗin ta, ya ce ""To kin ga tare muka shanye, yanzu talatin ma zan baki"" ya saka hannu a aljihunsa ya ciro dubu biyu ya ɗora" "mata a wuyanta ya ce ""Gashi nan, uwar son kuɗi""" """Ai talatin ka ce zaka bani, saura dubu ɗaya, dubu uku yakamata ka bani""" "Ya ce ""Biyoni ɗaki ki karɓa""" "Ta ce ""A'a na yafe maka sauran, amma kar ka sake""" "Sosai wani bond mai ƙarfin gaske ya shiga tsakaninta da shi, har mamakinsa take yi, duk da mai hali baya fasawa, idan miskilancinsa ya motsa, ko kuma ya cake, ba ya sarrafuwa ta daɗi, amma haka take jurewa. Ga babban abun da yake ci mata tuwo a ƙwarya yanzu, wasu lokutan idan ya dawo daga shaye-shayen sa, da ƙaurinsa da komai yake zuwar mata, gashi ba abu ne mai sauƙi ba," "ta nuna masa hakan ba, dole sai ta cikin hikima da dabara." "Haka zata zauna, komai daren da zai yi sai ta jira dawowarsa, ta saka shi yayi wanka, ya canza" kaya. "Yau bayan ya bar ɗakinta, bayan ta idar da salla ta je ta same shi, a zaune a kan katifa." "Ta ɗauki kwalin sigarin gabansa, ta ciro guda uku ta bashi ta ce ""Wannan ta isa, kar a sha sama da" "haka dan Allah""" """Bani in je ƙofar gida in sha""" "Ta ce ""A'a ai shan nake so ka rage sosai da sosai, wannan ta isa""" "Ya juya mata baya ya shanye, tana zaune tana jiransa, ta bubbuɗe window, saboda hayaƙin ya fita." "Jira yake ta fita ya kuma kunna wata, amma ta cire masa shirt ɗin jikinsa, ta ce ya kwanta, ya" "kwanta yana jiran ta fita, amma ta kwanta a jikinsa, a hankali ta din ga karanto azkar ɗin safiya." "Babbar salla na ta ƙaratowa, jauhar hada-hadar neman kuɗi, ta cigaba da kankama, Al'amin bai ta ɓa saka ido a kan abun da take samu ba, dan yanzu iya ƙoƙarin sa yake yi, ya yi cefanensa, duk da kuɗin da take ɗan samu, in dai ya ji kuɗi a jikinsa, a kaso ɗari tamanin, ita zai kashewa, bai fi ya" "ƙarar da kaso ashirin ba, goma ya rabar goma ya yi shaye-shaye." "Idan ta fuskanci da kuɗi a hannunsa, ta din ga lallaɓa shi kenan, ayi wani abu mai muhimmanci," "idan ba haka ba, ba zai sai abubuwan da suka fi buƙata ba." "Kuma babbar hanyar samun kuɗinsa, wurin Indabo, ya din ga tatsarsa kamar mai, duk da yana" "samun hanyoyin samun kuɗi yanzu, tun da kakar siyasa ce." "Ana jibi salla, ya ba wa jauhar kuɗi, wai tayi kitson salla ita ma, ta je ayi mata zane a hannunta." "Ta dawo ta tarar da kaya a kan gadonta, ta zazzage taga kaya na alfarma duk an ɗinka su, har da" takalmi da turare. "Mamaki ya cikata, yana dawowa ta fito falo ta ce ""Master kayan waye a kan gadona?""" """Na kishiyarki ne""" """Wace kishiyata?""" """Ban sani ba, ko ina da wata matar ne bayan ke""" "Gaba ɗaya ta rikice ta ce ""Master wai nawa ne Gaba ɗaya?""" "Ya ce ""Naki ne babyn roba""" "Har ƙasa jauhar ta durƙusa tana yi masa godiya, ta rasa ma wace kalar godiya za ta yi masa, har" da matse ƙwalla. """Ni ba irin wannan godiyar nake so ba, a sheƙa mini girki, a yi wa fankata caji, in sha iska sosai""" "sunkuyar da kai ta yi, cikin matsananciyar jin kunya." """Allah ya ƙarawa fankata gudu, tana ba da iska sassanya, ƙarfin gudunta, bai sanya tana bada" "iska mai cutarwa ba""" """Amm bari na je na yi jajjage"" ta juya ta nufi ɗaki." """Dama a ɗaki a jajjagen"" ko waiwayowa ba ta yi ba, ta shige." "Ranar idin babbar salla ma, tare suka tafi sallar idi." "Ta sha kwalliya, tayi kyau sosai da sosai, a abun da bai fi wata guda ba, ta yi ƙiba fatarta ta ƙara" fresh. "Ta sha ɗaurin ɗan kwali, hannunta yayi kyau da zanen lalle ja da baƙi. Su liti suka din ga kiransa a waya, suna jiransa, yaƙi fita, sai da suka zo har gida sannan suka fita da shi, bayan sun kwashi" wainar masa da sinasir da miyar agushi. "Bayan la'asar sosai, ya dawo gida da nama kaya guda, har da karfatar sa, ga kayan ciki da uban" nama. "Kamar tayi kuka ta ce ""Master, aiki daf da magariba ya zan yi?""" """Ke da aiki ba ya yi miki wahala, ɗan wannan aikin zaki yi raki?""." """To aikuwa sai ka tayani, kuma ba ka sayo itace ba""" "Ya kalleta ya ce ""Ba a yi a gas, an hanaki shiga hayaƙi""." """Gas ɗin dubu nawa za a zuba? Dole sai a itace""" "Ya kalli naman, ya ce ""Ki shiga ciki, bari na aika nura ya sayo itacen, su walid suna waje, sai su" "shigo mu yayyanka""" "Ƙarshe dai hayaƙin da ba ya so, sai da ta shiga, har sha biyun dare suna aiki ita da shi." "Duk da haka aikin bai ƙare ba, sai washegari, ta ce masa tana son zuwa gida, ya ce sai ta gama yi" masa kwalliyar salla kan ta fita. "Ya samu dambun nama da cin-cin, ya din ga tumurmusa, jauhar ta ce ""Ni ban gane wannan" "lamarin ba, gaskiya rabawa za ayi. Kana ta ci idan cikinka ya ɓaci babu ruwana""." """Ke ki ke da ruwa kuwa""." "Sai huɗu ga salla, sannan ya bari ta je gida, ya kaita da kansa." "Aka yi sa'a Hafsa ma ta je gidan, tun da ta jauhar ta je, suke kallonta da kayan jikinta." "Sai da mama ta magantu ta ce ""Jauhar wannan leshin fa?""" """Mama kayan salla ne""" """Kin san kuɗin leshin nan kuwa?""" "Ta girgiza kai ta ce ""A'a shi ne ya kawo mini""" "Ta kalleta ta ce ""Wai sana'ar me yake yi haka ne?""" "Tayi murmushi ta ce ""Yana sana'oin sa, kuma kin san yana tare da 'yan siyasa""." "Hafsa ta din ga kallon jauhar, yadda take komai nata cikin walwala, kamar ba ta da wata damuwa," duk da tana auren ɗan daba. "Bayan jauhar ta ba su nama, dambun nma da cincin, aka din ga gaya wa jauhar, ai mijin hafsa rago" ya kawo. "Ta ce ""Masha Allah, Allah ya saka da alkhairi"" Duk yadda Hafsa ta so mazewa, sai da yanayin ta" ya nuna akwai damuwa. "Sai yamma Al'amin ya dawo, ya ce ta fito su tafi, babu yadda ba ta yi da shi ba, amma ya ce ba zai" shiga ba. "Gidansu ma da ya kaita, a waje ya tsaya, a gurguje jauhar ta shiga ta gaisa da Rahila, ta bata" "naman sallar sai dai ita ma, kayan jauhar kawai take kallo." "Ana gama bikin salla, aka shiga hada-hadar zaɓe." "Hankalin jauhar ya kasa kwanciya, saboda yawan shige da ficen da yake yi yawa." "Yau ake zaɓen sanatoci, dan haka tun kan ta tashi daga bacci ya fice." "Har yamma shiru bai dawo ba, kuma wayarsa ba ta shiga." "Gaba ɗaya jikinta a sanyaye yake, jikinta ya din ga bata akwai matsala, har bayan magariba bai" dawo ba. "Jin ana knocking ɗin gate, gabanta ya faɗi, ta saka hijjabi ta fito, ta ga Nura guduma a tsaye ta ce" """Yaya wannan karon me kuma yayi?""" "Ya ce ""Ki sako hijjabinki mu tafi""" """Mu tafi ina?""" """Asibiti!""" """Innalillahi wa Innalillahi raji'un!""" Ayshercool 08081012143. ₦500 ne via 0009450228 Aisha Adam jaiz bank sai shaidar biya ta 08081012143 90009343 'Yan Nijar ku turo katin airtel na 300fcfa Arewabooks ayshercool7724 "Muryarta na rawa ta ce ""Meyafaru? Wani abun ne ya same shi, ko ya yi wa wani?""" "Ya ce ""Ni ma ban sani ba, oga walid ne ya ce ""In zo mu tafi tare """ "Jikinta a sanyaye, ta kulle gidan, ta bi Nura guduma suka tafi, suna tafe tana ta addu'a a ranta." "Wani private clinic suka je, emergency suka nufa, ana ta kai komo da matasa, da aka ji wa raunuka daga wurare daban-daban na harkar zaɓe, kasancewar an yi tarzoma sosai da sosai a wasu wuraren," kuma nan asibitin ne mafi kusa. "Da ƙyar take iya ɗaga ƙafarta, wani irin yammmm haka jikinta yake yi mata, saboda tsoro da" tashin hankali. "A ƙofar wani ɗaki, ta tarar da Walid hankalinsa a tashe, yana kaiwa yana komowa." """Yaya walid, meyasame shi? Ko mutuwa yayi?""" "Walid ya ce ""Ki nutsu ba mutuwa yayi ba, yana ta kiran sunanki ne kafin mu zo nan""." """To meya same shi, yana ina?""" "Ganin likita ya fito daga ɗakin da yake facing ɗin su, ya sanya ta saka kai ta shiga ita ma." "Gigicewa ta yi, ganin Wuƙa a kwiɓin Al'amin a tsaye tsororo, jini baya zuba, amma tana jikinsa, ga gefen kansa, an naɗe shi da bandeji. An saka masa oxygen, gefe ga oxymetre na reading vitals" ɗin sa. "Cikin kuka ta ce"" Innalillahi wa Innalillahi raji'un, meya same shi haka? Waye yayi masa haka, Master dan Allah ka tashi, kar ku ce mini mutuwa yayi"" tayi maganar tana rirriƙe hannunsa cikin" tsananin tashin hankali. "Kukan jauhar ya janyo hankalin likitoci, da m'aikatan jinya, suka ce meyasa aka bari ta shiga?" "Da ƙyar aka fito da jauhar ana rarrashinta, aka tabattar mata da yana da rai, tiyata za a shiga da shi" "a cire masa wuƙar, sai a duba kansa." "Cikin tashin hankali ta ce ""Dan Allah likita zai rayu?""" """In sha Allah, da kun biya kuɗin za a shiga da shi""" "Ta kalli Walid ta ce ""Yaya Walid, nawa ne kuɗin?""" "Walid ya ce ""Kuɗin da yawa, P.A ɗin Indabo muke kira, su biya kuɗin, hannunmu kuɗin ba za su" "kai ba ayi masa aikin""" """Ka gani ko? Sun ma ƙi ɗaga wayar, su suna can hankalinsu a kwance, suna jiran sakamakon zaɓ" "e, ni kuma an kassara shi, wannan tashinsa ai sai Allah""" "Liti ya ce ""Ki yi haƙuri, in sha Allah zai tashi""" """Nawa ne kuɗin?""" """Da ɗan yawa, ki bari kawai""" "Ta girgiza kai ta ce ""Ni ku gaya mini dan Allah, a nema tun da wuri, wuƙa ce fa a cikinsa"" tayi" maganar tana wata irin ajiyar zuciya mai ban tsoro. "Suka din ga rarrashinta, amma taƙi saurarsu, Liti ya ce ""Bari na yi gaggawa na je na samu wannan" "banzan mutumin P.A, ko dai a san yadda za ayi a biya, wallahi ko mu jiƙa musu aiki""" "Jauhar kamar za ta yi hauka, ƙarfin Addu'a ne kawai ya saka mata nutsuwa, ta din ga kaiwa tana" "komowa, gashi an ce ba zata sake shiga ta ganshi ba." "Jauhar ba ta san yadda aka yi ba, liti da Nura guduma suka dawo da kuɗi, suka biya." "Ake ce ana buƙatar jini, dan da yiwuwar ana cire wuƙar, jini ya ɓalle." "Haka suka din ga zirga-zirga, jauhar itakaɗai a cikin su, babu wani daga danginsa, babu daga nata." "Nura guduma ne ya bayar da jininsa, dan shi ne yayi dai-dai da na Al'amin, aka shiga da shi tiyata." "Hawaye suka kasa barin idanunta, zuciyarta ta din ga wani irin zafi, ba ta taɓa tsanar wani abu ba, tsana mai muni sai yau duk da ba ta taɓa ganin indabo ba, tsananin haushinsa take ji, dan shi ne" musababbin wannan tashin hankalin. "Ta kai ta kawo, ta tsuguna tayi kuka, aka shafe sama da awa guda, ba a fito da shi ba, tayi alwala ta shimfiɗa ɗan kwalinta, ta tayar da salla, sai dai tana cikin sallar sai ta hau wasi-wasi, da tunanin" me zai faru ta kasa nutsuwa. "Babu tsammani likitocin suka fara fitowa, dan team ɗin tiyatar sun kai su biyar, gaba ɗaya suka" "nufe su, suna tambayar yaya?." "Jagoran tiyatar ya ce ""Alhamdilillah, an cire wuƙar, kamar yadda muka yi tsammani ya zubar da jini sosai, amma an saka masa jini, zamu kai shi ɗakin hutu, amma ba ma son a din ga shiga ana fita da sunan dubiya, kafin a kai shi ɗakin hutun, za a yi masa hoton kai, duk da saran da aka yi" "masa a ka bai yi zurfi ba, amma akwai buƙatar a duba""." """Alhamdilillah ala kulli halin, Doctor mun gode Allah ya saka muku da alkhairi, ya jiƙan" "magabatanku, Allah ya sa ku gama da duniya lafiya ku bar aiki lafiya, ka da Allah ya wulakanta rayuwarku bayan ajiye aiki""." "Cikin farinciki suka din ga amsar addu'a jauhar, da Amin, tare da ba ta ƙwarin gwiwa a kan zai" tashi ya warware gaba ɗaya. "Bayan an yo hoton, suka tabattar da babu internal injury, jauhar ta zauna ta zuba masa ido, ga jini" yana shiga jikinsa a hankali. "Walid ya ce ""Ina ganin ki koma gida, ko ni sai na kwana da shi a nan, kin ga idan ya tashi ba abun" "da zaki iya yi masa""" """A'a idan na koma ba zan iya zama bama, hankalina ba zai kwanta ba, ni kawai ku bar ni""." """To ai dole sai da namiji, ko zaki iya ɗaga shi, idan yana buƙatar hakan?""" Cikin ƙwarin gwiwa ta jinjina kai alamar eh. "Duk da alhini da suke ciki, sai da suka yi murmushi." "Walid ya ce ""Bakomai, ki kwana da shi, sai na kwanta a waje ni, idan ana buƙatar wani abun sai ki" "kira ni, yanzu bari na sayo wani abun, ki ci""." """Bana jin yunwa""" "Haka suka kwana da Al'amin, amma bai farfaɗo ba." "Ta din ga kallon wayarta, tana tunanin wa za ta kira, kamata yayi ace tana da wanda za ta kira, a kawo mata abun da zata buƙata saboda zaman asibiti, amma ta san ko za ayi mata sai an yanƙ" wanata ko gaya mata maganar da zata ɓata mata rai. "Kwana suka yi likitoci na kaiwa da komowa a kansa, ƙarfe shida ta kira Abbu a waya, ya dawo" "daga masallaci kenan, ya ga kiran jauhar. Ya ɗaga a nitse suka gaisa." "Ta gaya masa abun da ya faru, dumm ƙirjinsa ya buga, duk da ba wannan ne karon farko da" Al'amin yake kai kansa in da ake cutar da shi ba. "Abbu ya ce ""Shikenan, ki yi haƙuri ki daina kuka, in sha Allah zan zo asibitin, daina kukan haka" "yarinyar kirki""." "Rahila da bacci take yi, sama-sama take jin sa ta ce ""Lafiya, kai da waye?""" """Matar Al'amin ce, wai suna asibiti an caka masa wuƙa a ciki jiya a wurin zaɓe""" """Kai amma ka tsorata ni, shi ne ka ke ta rafka wannan salatin haka? Yau ya fara zuwa ayi masa illa" "a yawonsa? Dan Allah ka kwantar da hankalinka""" "Ya kalleta ya ce ""Wuƙa a cikin sa fa aka ce mini, waya sani ma ko mutuwa yayi, Rahila Al'amin fa" "ɗa na ne, ba shi nake ƙi ba miyagun ɗabi'unsa ne ba na so""" """Lallai kam na ga Alama, Allah ya bar soyayya"" ta juya ta cigaba da bacci." "Ƙarfe shidan, Nura guduma ya zo Asibitin, Walid ya saka ya raka jauhar gida, ta ɗebo kaya." "Suka tafi, jikinta duk a sanyaye." """Dan Allah Nura kana ganin zai tashi?""" "Ya ce ""Eh mana, in sha Allah, shi fa master ɗan baiwa ne, bar ganin abun da yake yi, yana da sa'a" "sosai da sosai in sha Allah zai tashi """ """Amma ya aka yi aka yi masa haka?""" """Wallahi ban sani ba, wai dai husuma ce ta tashi a wurin tattar sakamakon ƙananan hukumomi," "amma ban san shi ya aka yi hakan ta faru ba""" "Jauhar ta ce ""Allah ya sa ya tashi ya warke""" "Ya amsa mata da ""Amin""" "Ko da taje gida, ta ɗebo kaya suka koma, Alluran da aka yi masa sun fara sakinsa, ya na 'yan" maganganu a hankali. "Ban da 'yar madara babu abun da yake kira, ta je ta zauna a kusa da shi, ta riƙe hannunsa, ta kifa" kai tana kuka mai ban tausayi. """Gaskiya ƙanwa idan baki daina kukan nan ba sai kin tafi gida, duk muna jin abun da ki ke ji," "daurewa muke yi, ba gashi yana magana ba ya kusa dawowa duka""" "Ta girgiza kai ""Yaya walid ba ka san me nake ji bane""" """Mun sani, amma ki yi haƙuri""" "Abbu ne yayi sallama, wanda jauhar ba ta taɓa tsammani ba, ta dai gaya masa ne kawai, kar ace ba" ta faɗa ba. "Da sauri ta tashi ta durƙusa ƙasa tana gaishe shi ya ce ""Jauhar sannu ya mai jikin?""" """Jiki da sauƙi Alhamdilillah""" Su Walid ma duk suka gaishe shi. "Ya ƙarasa gaban gadon, ya ƙura masa ido, ya ce ""Ya aka yi abun ya faru""" "Tayi sauri ta ce ""Zai dawo gida ne wasu suka yi masa haka da daddare""" "Kallon da su liti suka yi mata, ya sanya Abbu gane ƙarya take yi." """Yanzu ya ake ciki to?""" "Walid ya ce ""An yi aiki an cire wuƙar""" "Ya jinjina kai ya ce ""Alhamdilillah, Allah ya tashi kafaɗunsa""" "Suka amsa da ""Amin""" "'yar madara da yake ta maimaitawa ya sanya Abbu cewa ""Wace 'yar madara kuma?""." "Gaba ɗaya suka kalli Jauhar, ta sunkuyar da kai cikin jin kunya." "Abbu ya yi murmushi ya ce ""Ikon Allah""" "Nurse ta shigo, ta ba su takarda a sayo magani." "Abbu ya bayar da kuɗi aka sayo, ya din ga yi wa jauhar nasiha a kan ta nutsu ta kwantar da" "hankalinta, dan har a lokacin tana kuka." "Sai dai wata nustuwa ta saukar masa, ganin Al'amin yayu ƙalau da shi." "Har azahar suna tare da Abbu, daga bisani, ya ajiyewa jauhar kuɗi, ya ce ""Duk yadda ake ciki su" kira shi. "Liti ne ya fita waje, ya kira P.A da wayar Al'amin, aikuwa ya ɗaga." "Wata muguwar ashar ya narka wa P.A sannan ya ce ""Saboda kai ɗan haramun ne, nake kiran wayarka tun jiya, ka ƙi ɗagawa. Saboda baku da mutunci daga kai har ubangidan naka, saboda kare ƙuri'arku, da ƙoƙarin hana ƙona sakateriya, yara sun fi sha biyar suka rufar masa da sara, ban da Mu ma akwai yaranmu a wurin da sai sun kashe shi, ka san ba maganin tauri yake sha ba, bakomai ba. Ka tsaya ka saurareni ma jiyan ka ƙi, da ƙyar aka samo kuɗin yi masa aiki, to wallahi ku saurari abun da zamu yi mu ma, wallahi hukumar zaɓen zamu cinnawa wuta, uban" "kowa ma ya rasa. Zaka gane ba ka da wayo daga kai har shi""" """Ka ga tsaya, duk na san a cikin yaransa ne, ku yi haƙuri kun san yanayin halin da muke ciki ba a" nutse muke.... """Halin da ku ke ciki ya fi rayuwarsa kenan? Ku sauraremu nan da wani lokaci"" ya kashe wayar." "Ya koma ɗakin da Al'amin yake, ya tarar da ya farfaɗo, har an ɗaga shi zaune ma, jauhar ta haɗa" "tea tana bashi, sai dai idanunta sun gaza daina zubar da hawaye." "Al'amin ya zuba mata ido ya ce ""Abbu ya zo nan?"" Ta ɗaga masa kai alamar eh." """Dan ke ya zo ko bani ba? Ke ki ka yi masa magiyar ya zo?""" """A'a""" "Walid ya ce ""Liti mu ba su wuri, abun na baru ne""" """Master""" "Ya kalleta, idanunsa sun yi ja, alamar yana jin jiki." """Ba na ce ka daina yi wa kanka illa ba, ko dan saboda ni? Sai zuciyata ta fashe hankalinka zai" kwanta ko? In sha Allah kujerar nan ko ya sameta sai ta zame masa masifa. Ban taɓa yi wa wani "muguwar addu'a ba amma na yi masa. Nayi nayi ka rabu da mutumin nan, ba mutumin arziki bane" "ba, amma ka ƙi aishikenan gashi nan yanzu ka janyo mana wahala""." "Ya lumshe idanunsa, dan ba ya son ya ga tana zubar da hawaye." "Jauhar ba irin addu'a da ba ta ja wa indabo ba, dan shi ne kanwa uwar gamin ƙara ta'azzara rashin" jin Al'amin. "A washegari hukumar zaɓe, ta sanar da soke zaɓen ƙaramar hukuma uku, ciki har da ta su Al'amin" "wadda kuma take ta indabo, sakamakon tashe-tashen hankali da aka samu, da kuma ƙona wasu daga takardun da aka kaɗa ƙuri'a." "Tuni P.A ya sanar da Indabo saƙon su Walid, kuma kansile ƙanan hukumomin, babbar barazana ce" ga nasarar indabon. "Babu shiri, washegari da daddare suka shirya suka tafi wurin malamin su, da shi da P.A, malamin ya tabbatar musu da cewa, an samu tangarɗa a aikin da aka yi ne, yarinyar da yayi amfani da ita, ta haura shekarun da ake buƙatar, kuma a yanzu ba abun da zai iya yi musu, sai dai a bi wasu sabbin" "dabarun, a samu a haye." "Suna tafe a hanya P.A ya ce ""Honorable, wallahi yakamata ka duba mai zamani, da ƙyar idan ba yaransa ne, suka tayar da tarzoma ba, ka san dole zamu sake buƙatar su, mussaman yanzu da zaɓ" "en ya zama inconclusive""." "Indabo ya ce ""Matsalar yaron nan na ta ƙarewa wallahi""" """To ya zamu yi, haƙuri zamu yi tun da muna amfanarsa"". Indabo ya amince da hakan, P.A ya kira" liti ya tambaye shi in da suke kwance "Al'amin so yake Jauhar ta zauna a kusa da shi, ya ji ɗuminta su yi hira, amma alamu suka tabattar masa da fushi take yi, dan da tayi masa abun da za ta yi masa sai ta koma gefe, ta ɗauki wayarta" tana karanta Alqur'ani. "Ga kawo-kawo ɗin da ake yi, kuɗin hannunta duk sun ƙare, dan ma su liti suna tsaye suna" "tallafawa, kuma idan Abbu ya zo ya kan ba ta kuɗi, duk da zuwan nasa biyu ne kawai." "Wajen ƙarfe ɗaya na dare ne, Ranar Walid da liti duk suna nan, duk da da facemask, a fuskar" "Indabo sai da suka gane shi, suka tashi suka ni bayansu." "Jauhar ta ɗaga kai ta kallesu, Al'amin ya buɗe idonsa da yake a rufe a da." "Jami'an tsaron suka bashi kujera ya zauna, yana kallon Al'amin da satar kallon jauhar." "Ta tashi ta ce ""Lafiya?""" "P.A ya ce ""Baki gane ni bane, wanda ku ka zo wurina lokacin yana prison, honorable ne wannan," "ya zo da kansa ba saƙo duba shi"" ta haɗe rai sosai, kamar ya make shi ta huta haka take ji." "Ya sauke facemask ya ce ""Sannu kin ji, ya mai jikin?""" Shiru tayi tana cigaba da haɗe rai. "Ya kalli Al'amin ya ce ""Wannan ce 'yar madarar kenan?"" Al'amin ya ƙura masa ido, bai yi magana" ba. "Ya kalli Walid ya ce ""Ba ya iya magana ne?""" """Yana yi""" """Dama cewa na yi bari na zo na ga yanayin jikin naka, Allah ya ƙara sauƙi. Ban sani ba ko ka" "samu labarin an soke mana wasu ƙuri'un abun bai yi daɗi ba, muna nan dai muna ta addu'a """ "Ya karkace ya ciro kuɗi kaya guda, ya miƙawa jauhar ya ce ""Ga wannan a sai magani""" "Ta girgiza kai cikin takaici ta ce ""Ba ma so, ka riƙe kuɗinka ni babban burina da fatana, ka fita daga rayuwar mijina, nima ina burin na ga ya shiryu ya zama mutumin kirki, kai ne ka ke saka shi aikata duk wani abu na rashin kyautawa. Idan ya shiga matsala kuma ka zame ka bar shi. Yanzu an riga an cuce ni, an tsugunar da shi. 'ya'yanka su suka fi cancanta su yi maka irin aikin da yake yi maka, tun da sun fi morarka, idan abun na Allah ne ka karɓi takardunsa ka sama masa abun yi" "mana, amma babban burnku yaran wasu su sha su bugu su sayar da rayuwarsu a banza gare ku""." "Ɗaya daga cikin jami'an tsaron ya daka mata tsawa, ta ce ""Wallahi ko zaku kashe ni sai na faɗi gaskiya, nima 'ya ce, kuma na cancanci zama da nagartaccen miji, na san akwai iyaye da yawa da suke da burin ganin yaransu a hanya madaidaiciya amma duk hana hakan, ni dai dan Allah ka rabu" "da mijina, ka ƙyalemu""" "Maimakon ya ji haushi, sai yayi murmushin ya ce ""P.A wato duk isa da kwarjinin namiji ya je gaban mace, sai abun da Allah ya yi, kalli Mai zamani a gaban matarsa. Aishikenan yarinya haryanzu baki san rayuwa ba, wannan yanayin mafita kawai ake nema, ki daina yi wa manya rashin kunya. Kuma mijinki zaki gaya wa ya daina abun da yake yi ba ni ba. Tun da a haka na" "ganshi, ki karɓi kuɗin nan""." """Ba ma so, ba zamu karɓa ba"" tayi maganar tana kuka." "Ya miƙawa P.A kuɗin, ya karɓa ya miƙawa Viper, shi kuma ya karɓa." Indabo yayi murmushi ya fice da tawagarsa. """Master ni ka dizga ka kunyata a gaban mutane, gara ka cigaba da karɓar kuɗinsu kana shaye-shaye ana yi maka lahani, ni ko? Kai am tired na gaji, ba zan iya ba na sare. Na ɗauka abun mai sauƙi ne, amma ya wuce yadda nake tunani, you are not willing to change. Kana samun sauƙi" "gida zan koma, na gaji da auren""" "Liti ya ce ""Subhanallah, dan Allah kar ki yi mana haka anty ƴar madara, muna murna Allah ya" "saya mana shi, kuma ki tafi ki barmu, ba fa shikaɗai ba har mu zamanki tare da shi muna amfana""" """Eh, kuma har da ku ai, kullum ku kuke ƙara haɗuwa da shi, ku ke ƙara abun da bai kamata ba," "Allah ya sa na mutu na huta""." "Duk wannan abun, yayi burus yaƙi magana." """In sha Allah, ba zaki mutu ba, ana mugun tare ai""" """Ba wani tare, ku daina shaye-shaye mana, kuma kullum a kansa tsautsayi yake faɗawa, ni na gaji, yana warkewa tafiya zan yi na haƙura da zaman da shi"" tayi maganar tana kuka, har ta fara tari" mai haɗe da haki. """Mai laya""" """Allah ya ƙara maka lafiya""" """Ayi walƙiya, sai da safe""" "Walid ya ce ""Iya wuya, yadda ka ke so haka za ayi"" suka tashi suka fice, ya juya ya saukko daga" kan gadon. "Kamar ba ciwo ne a cikin sa ba, ya tunkaro in da take ya zauna, ya ƙura mata ido tayi shiru ta" "sunkuyar da kai, tana haki sama-sama." """Ki ka ce tafiya zaki yi?""" """Eh"" ta bashi amsa kai tsaye." """Yaushe?""" """Kana warkewa gida zan koma, tun da ba ka so na, kullum cikin sakani ka ke a tashin hankali, na ce maka ba na son ka din ga zuwa in da za a ji maka ciwo, amma ka ƙi, ka dizgani a gaban" "wannan mutumin. Wallahi ba zan taɓa yafe masa ba, duk shi yake ƙara ɓata ka""." """Yanzu abun da ki ka yi dai-dai ne? Ubangidana ne fa, ki ka tsaya kina yi masa rashin kunya""." "A ƙule ta ce ""Shi dai-dai ɗin yayi mini, ba dan Allah ya yi da sauran kwananka a gaba ba, da" "yanzu wani zancen ake ba wannan ba, ni na rasa in da zan saka raina, abun da nake ta tunanin zan" "iya ashe ya fi ƙarfina, shikenan""." "Gyara zamansa yayi, ya janyota jikinsa, yana kissing ɗin ta a hankali." "She's not in mood, ta so ta ƙwace, sai dai kuma raunin jikinsa ya hanata yin hakan, kar ta fama masa." "A hankali ya cire bakinsa daga nata yana kallon ta, amma ta haɗe rai tayi kicin-kicin." """Ki gaya wa likitocin nan su sallameni gobe, ko kuma na yi tafiyata""" "Da sauri ta kalleshi ta ce ""A hakan ba ka warke ba?""" """Eh na gaji da yadda ake zuwa ana magana da ke, haushi nake ji, shi kansa indabo shirun da nayi" "masa, shi ne mafi alkhairi da mummunan naushi zan yi masa""" """Dan Allah ni ka daina taɓa ni, asibiti ne fa, idan wani ya shigo fa?""" """To je ki rufe ƙofa ki dawo, zafi nake ji, ina buƙatar fankata, lamba uku kawai, ba sai an ƙure" "mata gudu ba""" """Ko mafici ba zaka samu ba, ni rabu da ni"" tayi maganar tana sake ture shi." "Ya ƙi tashi ya din ga takura mata, duk dan ta sake ta ɗan samu nutsuwa daga fushin da take yi." """P.A wane mahaukaciya ne ya aura wa yarinyar nan mai zamani?""" """Allah masani honorable""" """Ikon Allah, kalarta kalar muryarta, ai rannan na kira ta ɗaga, kai ka ga yarinya zuƙeƙiya kamar ita tayi kanta. Amma kamar ta dace da aikin da malamin nan fa ya bayar, ya aka yi ba ka yi mini" "zancenta ba, gashi wannan an samu matsala""" "P.A ya ce ""Honorable, kai ka san ba kowane kaya ne yake taɓuwa ba, idan aka taɓa wannan za a" "iya samun matsala, kuma na manta da ita ne gaba ɗaya wallahi""" "Indabo ya ce ""Wace irin matsala? Ai tsaf za ta taɓu, ba tare da ya sani ba, idan ma ya sani na san" "yadda zan yi da shi. Lallai 'yar madara tayi kalar madarar sosai. Wannan yarinyar ita ce rauninsa kenan?""" """Sosai kam, dan alamu sun nuna yana mugun sonta""" Indabo yayi wani irin murmushi yana shafa tumbinsa. "Maƙwabtan su Jauhar sun yi mata kara, na zuwa duba Al'amin, suka kakkai mata abinci, daga" "gidan su Baba ya je Saifu sai mama, sun je sun duba shi, duk da maman ta gaggaya mata baƙar magana a kansa." "Satinsa ɗaya da ƙyar, ya uzzura akan lallai, sai an sallame shi, haka aka sallame su suka koma" gida. "Cikin ikon Allah, Indabo yayi nasara, bayan faɗi tashi, da shige-shige yayi nasarar samun kujerar" ɗan majalisa. "Har gida Abbu ya sake zuwa duba Al'amin, sai dai kamar wurin jauhar ya zo, da ita suka ɗan yi" "hira, ya tashi ya tafi." "Hafsa kuwa abun duniya ya hanata sukuni, da ƙyar ta samu Alhaji mu'azzam ya fara saurararta, sai dai yadda yake bin matarsa sau da ƙafa, yake ƙona mata rai, sai abun da ta tsara yake yi a gidan, idan ba ta ga dama ba, sai ya shafe kwana goma bai taka wurin Hafsa ba, amma kuɗi akwai su, komai take buƙata akwai shi, sai dai fa tsakaninta da miji sai an ga dama a bata aro, wataran yana wurin nata ma, za ta kira shi, kuma haka zai tsallaketa ya tafi wurin matarsa, ga yaransa" "marasa kirki, sun rainata rashin kunya kala-kala." "Da ta matsa ma da ƙorafi, ya ce idan ta gaji ta tafi, shi fa duk lokacin da ya zo wurinta, baya gane" "komai, haƙuri kawai yake yi shi ma, ta ƙyale shi." "Ta gaji tayi yaji, Anty ta din ga yi mata masifa, a kan dan me zata dawo gida, sai asirinsu ya tonu," dole ta cigaba da zama har zuwa lokacin da za a samu mafita. "Al'amin ya warke sarai, ya cigbaa da harkokin sa, sai dai jauhar kusan kullum tana gargaɗinsa a" kan indabo. "Gashi ta riƙe masa wuta a kan yin salla a kan lokaci, da yin azkar, har zama tayi ta ciro masa" addu'oi na musamman ta rubuta masa su. "Ita kanta ta san ikon Allah ne, da ƙarfin addu'a da take yi, da kuma yadda take bin sa da kyautatawa da biyayya, ya sanya take iya sarrfaa Al'amin, har yake jin nauyin aikata wasu" abubuwan saboda ita. "Da asuba idan ya je salla ya dawo, da kanta take ajiye masa sigari, kara biyu ko uku, ta ce masa ya" sha banda shan ƙwaya kuma. "Ta jira ya gama sha, yana ƙaurin yana komai, ta naniƙe masa a jikinsa, dan mantar da shi damuwa," kewar kayan shaye-shayen sa. "Da daddare suna kwance, ta ce ""Master, ka san abun da matar nan tela tayi mini?""" "Ya ce ""A'a""" """Wai na cewa matar nan dan Allah, ta koya mini ɗinki, idan ta yarda zan tambaye ka, na din ga zuwa, ta ce mini za ta yi shawara, wai daga baya ta ce mini mijinta ya ce a'a bai yadda na din ga zuwar masa gida ba, ko kara ba ta yi mini ba, duk wahalar da nake yi mata, wani abun ta biyani" "wani sai dai na yafe kuɗin, na ji haushi dama kuma ba ta zo tayi mini jajen abun da ya same ka ba""" """Saboda ni me mijin ya ce bai yadda ki je gidansa ba?""" """Wallahi ban sani ba, na dai ji babu daɗi gaskiya, amma ban san dalilinta ba""" "Al'amin ya ce ""Manta da ita, Allah ya baki wani abun da ya fishi, uwar son kuɗi""" """To wa ya ƙi kuɗi master"" yayi murmushi yana shafa bayanta." "Da asuba, mutane sun fito daga masallaci, faruku tela ya ga Al'amin a ƙofar gidan sa." "Gabansa ya faɗi ya ce ""Lafiya kuwa?""" "Al'amin ya ce ""Saƙonka na ji, 'yar madara ta ce a koya mata ɗinki ka ce a'a, fine idan na kuma ganin 'ya'yanka sun tako mini gida, sai na daddatsa su, na zuba a leda na kawo maka." "Na kuma yi suspending ɗin shagonka, na wata guda, wallahi ka buɗe sai an sassara mini kai"" yayi" "tafiyar sa ya bar faruku a wurin, cikin tashin hankali." "Ƙarshe sai da aka haɗa da zuwa har gida, magidanta suka zo ban haƙuri, jauhar tayi mamakin abun da yayi, ita kawai hira tayi masa abun miji da mata, amma ya je yana yi wa mutumin barazana. Ta" "ce zata yi masa magana ba wani abu, malam faruku ya cigaba da buɗe shagonsa." "Ya dawo da daddare, ta sha kwalliya, kamar yadda ta kan caccanza tare da ƙirƙiro da sabbin abubuwa, domin sabunta abubuwa da yawa a rayuwar auren na su, saboda rage barazanar" gundurar juna. "Ya nemi wuri ya zauna a falo, yana ta sauke numfashi, ta fito ta na murmushi ta haye kan cinyarsa," ta zuba masa ido ya lumshe idonsa yana ta huci kamar kumurci. """Nawan"" tayi maganar tana shafa sajensa." """Yau kuma me aka sha haka? aka ƙi kulani"" yayi shiru bai ce mata komai ba." """Master""" """Mmm""" """Me ka sha yau?""" """Wiwi""" "Jauhar ta ce ""Da me?""" Ya girgiza mata kai alamar babu. """Ba ka saba ƙarya ba"" ta saka yatsanta a bakinsa, ta ciro guntuwar ƙwayar da take ƙasan" "harshensa, laɓɓansa sun yi fari." """Ƙwaya ko? Meyasa. Na ce fa idan an ɓata maka rai ne, ko kana cikin damuwa ka yi ta ambaton" "Allah, kana azkar, meyasa za aje a sha ƙwaya, ka ɓata mini shirina na yau gaba ɗaya""" "Babu tsammani, ya miƙe da ita a jikinsa, ya tafi da ita ɗakinsa, rabi a buge yake, rabi a cikin" "hayyacinsa, yayi ƙoƙarin kissing ɗin ta, ta ce ""Ba zaka sumbace ni, da sauran ƙwaya a bakinka ba master, me aka yi maka?""" """Mhmmm bakomai, i need you""" "Ta ce ""A hakan, a buge fa ka ke""" """Ina hayyacina, kin yi mini kyau ne sosai"" kasa hana shi tayi, ya gama ya cigaba da yi mata" surutai. "Ta rungume kansa a ƙirjinta tana shafawa ta ce ""Na san wataran zaka daina master, Allah ya" "shirya mini kai mijina""" """Madarata""" "Ta ce ""Idonka biyu""" """Mmm""" """Me zaka gaya mini?""" """In sha Allah zan daina, ki cigaba da yi mini addu'a"" yayi maganar cikin muryar maye sama-sama." """Addu'a kullum ina yi maka master, Allah ya nuna mini ka daina""" """Madarata""" """Master na""" "Ya ja jikinsa, ya kai bakinsa saitin kunnenta, ta yi shiru, tana jiran ya yi mata magana." "Kawai ya fara murmushi, yana yi mata numfashi a kunne." """Zaki koma makaranta""" """Allah ya ja zamaninka, godiya nake""" "Cikin mayen ya sake cewa ""Ki daina yawan kuka ba na so""" """To ka daina sakani""" """Allah ya bani kuɗi na kai ki makka""" """Amin Mijina, da alama ƙwayar nan nishaɗi take sawa""" """Ke ce nishaɗin nawa"" yayi maganar yana dariya." "Ita ma murmushin ta yi masa, ya kwanta a gefenta, bacci ya ɗauke shi." "Da Asuba ya rigata tashi, ya tasheta shi kuma yayi wanka yayi alwala ya fita." "Da wani irin tashin zuciya ta tashi, kamar za ta yi amai, ta danganta hakan da awarar da ta yi wa" cin ƙoshi jiya da daddare ulcer ta tayar mata. "A ɗakinsa ta yi sallar ta idar, idonta ya sauka a kan robar cocala da ke gefen katifarsa." "A take ta ji idan ba ta sha coke ɗin nan ba, akwai matsala." "Ta ɗaukko, ta buɗe ta kafa kai ta fara sha, sai da ta shanye tas, sannan ta ajiye jarkar, still ta din ga jin kamar za ta yi amai. Ta yinƙura ta tashi, ta tafi banɗaki, ta yanke jiki ta faɗi, jini ya fara" gangarowa daga hancinta. Ayshercool 08081012143 ₦500 ne via 0009450228 Aisha Adam jaiz bank sai shaidar biya ta 08081012143 90009343 'Yan Nijar ku turo katin airtel na 300fcfa Arewabooks ayshercool7724 "Al'amin a masallaci, magidanta suka tare shi suna ƙara bashi haƙuri, a kan abun da ya ce wa" faruku tela. "Ya koma gida ya shiga ɗakinsa, yanayin kwanciyar da ya ga jauhar ne ya sanya ya tsaya yana" kallonta. """Wace irin kwanciya ce ki ka yi haka, ko baki da lafiya ne?""" Ya ga shiru ba ta motsa ba. "Ya ƙarasa gabanta, ya ɗagota, gabansa ya faɗi, ganin hancinta na ta zubar da jini, bakinta ma" jinin ne yake fita haɗe da wata kumfa. """Innalillahi wa Innalillahi raji'un"" ya furta cikin tashin hankali yana jijjiga jauhar." "Amma shiru ba ta amsa ba, ya ɗaga hannunta ya ga ya saki, ya kai hannunsa hancinta amma babu" alamar numfashi a tare da ita. """Jauhar, meya same ki haka? Meya sameki ne?""" "Jijjigata yake iya ƙarfin sa, amma ba ta motsa ba, kawai idonsa ya sauka a kan robar cocala. Ya" kai hannu ya ɗauka ta shanye komai tas. "A wurin Nura guduma ya ƙwace, ganin yadda ya haɗa uban ƙwayoyi a ciki zai sha, ya ƙwace ya" "ƙare masa zagi, ya ce idan yana wannan haɗin kashe kansa zai yi. Ya taho da shi gida ya ajiye a bayan katifar, ya kai kwana uku a ɗakin, shi ya ma manta da ita a ɗakin." "Da sauri ya ɗaukota ya fito da ita falo, ya kwantar da ita, ya fita da gudu, ya rasa wani gidan ma" "zai dosa, saboda ba shiga harkar mutanen layin yake ba, amma kasancewar a kiɗime yake, ya saka ya nufi gidan wasila, dan maigidan ya sai mota." "Wani irin mahaukacin bugu ya din ga yi wa gate ɗin gidan, ba shiri mijin wasila ya fito daga shi" "sai gajeren wando, ya buɗe yana rarraba ido." """Ɗaukko mota matata babu lafiya"" ya ce ""To"" dan a yanayin fuskar Al'amin ko ba'asi ya tsaya" "tambaya, bai san me zai yi masa ba." "Jin bugun gate ɗin, ya sanya wasu daga maƙwabtan su fitowa, su ji ko lafiya." "Mijin Wasila ya fito da mota, yanayin halin da ya fito da jauhar, ya sa gaba ɗaya jikinsu yin sanyi," dan babu alamar rai a tare da ita. "Mijin wasila ya ce ""Bari ya taso matarsa a tafi da ita, asibitin""" "Cikin ikon Allah suka yi wa Al'amin kara, mussaman da jauhar tana girmama su da jan yaransu a" "jiki, maƙwabcin mijin wasila ma ya shiga motar ya ce su tafi tare." Asibitin da ya taɓa kaita aka buɗe mata file suka tafi. Suna tafe yana girgizata yana ta tashi. """Malam Al'amin ka yi haƙuri, ka daina jijjigata kar ka ƙara gajiyar da ita""" "Al'amin bai bi takansa ba, ya riƙe hannun jauhar, ""Dan Allah ko motsi ki yi Zahra, dan Allah ki tashi"" su dai duk suka yi shiru, yanayin tashin hankalin da yake ta tattare da Al'amin ya ƙara" bayyanar da tsantsar soyayyar da yake yi wa jauhar. "Suna zuwa Asibitin, Al'amin ya nufi emergency da ita, sai da aka bishi aka tambaye shi file" numbern ta. "Mijin wasila ne ya biya kuɗin ganin likita, dan ba ya cikin nutsuwar da za a tambaye shi kuɗi." "Likita ya ce ""Malam, meyasame ta?""" Al'amin ya rasa ta ina zai fara. """Guba ta sha""" """Guba kamar yaya? Wannan ma ai kamata yayi sai an zo da 'yan sanda, ya aka yi ta sha guba?""" """Ka fara ceto mini ranta, duk wani bayani na yi maka daga baya, ka ceto rayuwar ta tukuna""." "Likitan ya ce ""Ai sai ka fara gaya mini meyafaru?"" Ya juya kan jauhar, ya duba pulse ɗin ta, tana" bugawa a hankali. "Aka samo bandage, aka toshe hancinta, saboda jinin da yake fita, aka ɗagota ƙirjinta a sama a" kan gadon. "Likitan ya ce ""A cire mata hijjabin nan""" "Al'amin ya riƙe hijjabin, ya yi shiru." "Nurse ɗin ta ce ""Malam ranta za a ceto, ka yi haƙuri""" Mijin wasila ya cewa maƙwabcinsa su fita. "Suka fita daga emergency, kayan bacci ne kawai a jikinta, doguwar riga iya gwiwarta." "Halin da take ciki, bai hana shi jin matsanancin kishinta ba, likita kuwa aikinsa kawai yake yi, zuƙ" "e jinin da yake bakinta, da kumfar da take fita." "Sannan suka fara yi mata CPR, a hankali take ajiyar zuciya, zuciyarta na ƙoƙarin responding." "Wasila ta ce ""Likita wani jinin na bin ƙafarta""" "Wani likitan aka kuma kira, aka tafi da ita scanning room, nan suka ga akwai ciki, sai dai shi ma" ya fita. "Al'amin ya rasa in da zai saka ransa, Nurses suna aikinsu, likitoci na nasu, aka ce Al'amin ya fita" ya ce wallahi ba zai fita ba. "Haka aka din ga ɗaga jikinta, ana ƙoƙarin tsayar da jinin da yake fita ta ƙasanta, allurai kuwa" "tsira mata kawai ake yi, ban da wanda ake zuba mata a cannula." "Al'amin ya ji da ma shi tsautsayin nan ya faɗawa ba jauhar ba, ko a iya haka ta galabaita." "Sakamakon gwajin jini, ya fito jininta ya yi ƙasa matuƙa ana neman a ƙara mata wani." "Ya fita hankali a tashe, mijin wasila ya ce ""Al'amin ya ake ciki?""" "Idonsa jawur ya ce ""Jini za'a bayar, ku bani aron waya dan Allah, na kira a kawo mini kuɗi, da" "kuma wanda za su bayar da jinin""." "Ɗaya maƙwabcin na su hadi ya ce ""Ai sun ce sai an yi depositing dubu hamsin za su ganta, mun je" "reception mun biya, yanzu jinin a fara dubawa a namu, ko za a dace""." "Ya ce ""To, amma a bani aron wayar dai, na yi kira""." "Walid ya fara kira ya ɗaga da ƙyar ya ce ""Maza""" """Kana ina ka nemo kuɗi ka zo asibitin da nake kai Ƴar madara cikin hanzari ba ta da lafiya""" "Tuni Walid ya ware ya ce ""Meya same ta?""" """Ka zo kawai""." """Gani nan""" "Likitocin suka kira Al'amin, suka zauna da shi suna tambayar sa meyafaru da ita." """Ƙwaya na ajiye a cikin cocacola ta ɗauka ta sha ba ta sani ba""" """Kwanakin baya fa, haka nayi ta counselling ɗin ka, a kan ka daina yi mata abun da yake saka" "jininta ya hau. Yau kuma ka bari ta sha ƙwaya wannan sakaci ne baka kyauta ba, idan ka yi silar" "rasa yarinyar nan, Allah ba zai barka ba""" Al'amin jikinsa yayi sanyi matuƙa. """Ko ka san cewa tana ɗauke da juna biyu? Yanzu dai ciki ya zube babu shi, kuma a shawarce," "idan Allah ya bata lafiya, yakamata tayi tsarin iyali, mahaifarta ta sake hutawa, dan ƙwayoyin sun yi wa jininta ƙarfi fiye da kima""" """Innalillahi wa Innalillahi raji'un, ba zata sake ɗaukar ciki ba kenan?""" """A'a zata iya ɗauka, amma a shawarce, mahaifarta ta huta, dan ya yi affecting ɗin mahaifar," "akwai buƙatar ta huta kan ta sake wani cikin """ "Daga shi har jauhar babu wanda ya san da cikin, tsananin son da take yi wa yara, ya sanya ta" "mayar da boti kamar ɗan da ta haifa, dan ma kwanan nan ya hanata ɗaukko yaran mutane, tayi ta fama da su tana yi musu hidima." "Ya tashi jiki babu ƙwari ya fita, su Walid suka ƙaraso Asibitin, a kiɗime suka nufe shi ""Mai" "zamani ina take? Meyafaru?""" "Bai ɓoye musu komai ba, ya gaya musu." "Cikin tashin hankali Walid ya ce ""Amma wallahi ɗan kutm..... Ne kai, wane irin hauka ne zai" "sanya ka ajiye abu in da zata ɗauka ta sha, kuma ba ka gaya mata menene ba? Ka san jikinta ba zai iya ɗaukar abun da yake ciki ba wannan ai hauka ne""" """Mai laya"" yayi wa Walid tsawa." "Sai dai walid ya kuma narka masa ashariya ya ce ""Ba za a kiyayeka ɗin ba, idan ka ji haushi ka" "saka mini ƙarfe, idan ta mutu kai ka yi asara, wannan ai ganganci ne da wauta""" "Wata irin zuciya ta yinƙuro Al'amin, ya nemi ya huce takaicin sa a kan Walid, amma Walid ma ya" "hayyayaƙo masa, dan ba ƙaramin mutunta su Juahar take yi ba, yarinyar was very simple and innocent." "Security ne suka shigo, suna ƙoƙarin korar su Al'amin, suna nema su tayar da hayaniya a cikin" Asibitin. "Liti ya kalli security ya ce ""ko dai ka ƙyale su, ko abun ya ƙare a kanka""" "Walid a fusace shi ma yake yi wa Al'amin martani ""Saboda ka ga ba ta da baki, iyayenta ba" "tuhumarka za su yi ba, shi ne zaka yi musu ganganci da rayuwar 'ya, wallahi daga nan gidan su zan je na faɗa, idan ma kashe auren za su yi, su ɗauke 'yar su"" Al'amin kawai yayi shiru, dan da" makami a jikinsa sai ya yi wa Walid illa. """A ina za a duba jinin?"" Yayi maganar yana kallon Al'amin." Yayi masa banza yaƙi magana. """Wallahi sai dai ka fashe, gaskiya ce sai na gaya maka"" ya ce ""Liti zo mu duba ina ne za a ɗauki" "jinin""." "Mijin wasila da suka koma gefe suna kallon sarautar Allah, suka gaya musu in da lab yake." "Ba a samu irin jinin Jauhar ba, sai dai sun bayar da jinin su leda biyu, aka tafi da shi babban asibiti," za a canzo da kalar nata jinin. "Suka shiga dudduba in da Al'amin ya shiga, aka nuna musu ɗakin da jauhar take." "Suka yi sallama suka shiga, an lulluɓe ta da green ɗin bedsheet, idonta a rufe hannunta biyu duka" an saka mata ruwa. "Al'amin na durƙushe a gaban gadon, ya riƙe hannunta idonsa yayi ja, fuskar jauhar ta yi yellow" sosai alamar ƙarancin jini. "Walid ya ƙarasa ya dafa kafaɗar Al'amin ya ce ""Mai zamani, ka yi sakaci da wauta, amma ka" "kwantar da hankalinka in sha Allah za ta tashi, ka yi mata addu'a. Ba a samu irin jininta ba, amma mun bayar da jinin za a canzo, likita ya ce a kira ka""" "Ya miƙe a hankali, suka fito, Walid yana ta cigaba da rarrashin sa, ya ciro kuɗi a aljihunsa ya ce ""Wallahi ka ga dubu ɗari da hamsin aka samu, shi ma jarin kaya ne, na ɗebo su kawai, kuɗaɗ" "enmu na hannun mutane, kana ganin za su isa kuwa?""" "Al'amin ya haɗiye yawu ya ce ""Ban sani ba, maƙwabcinmu ya bayar da dubu ɗari, sai a cire a" "bashi, in gani idan sauran za su isa""." "Walid ya dafa kafaɗarsa ya ce ""Ka yi haƙuri za su isa in sha Allah, yanzu me ake buƙata kuma?""" "Ya ce ""Jinin dai muke jira a saka mata""" """To shikenan, zan je na sake lalubawa ko za a samu kuɗi, ka yi haƙuri ka nutsu. Amma dole a" "sanar da iyayenta""" "Al'amin ya ce ""Wallahi babu wanda ya isa ya rabani da matata, ka ma daina wannan tunanin""" """Nima ban ce a rabaku ba, haushi ka bani ne, Allah ya taimake ka, na kiyayi mai zamani"" yayi" maganar cikin sigar girmamawa ga Al'amin. "Al'amin ya daki kafaɗarsa ya ce ""Get out""" Yayi murmushi suka fita da liti. Mamaki sai da ya kama mutanen da suka gansu suna faɗa ɗazu. "Al'amin ya bawa mijin wasila kuɗinsa, amma ya ce kyauta ya biya ba sai an biya shi ba." "Babban burin Al'amin bai wuce ya ga ta farka ba, da ya tuna abun da aka ce na game da mahaifarta sai ya ji ya tsani kansa, sai kokowa yake da zuciyarsa yaƙi bari haushin Nura guduma" yayi tasiri a zuciyarsa. "Wasila ta koma gida, ta dafo musu abinci ta dawo asibitin." "Har la'asar Al'amin ya rasa nutsuwa, aka kawo jini aka saka mata." "A gigice Nura ya zo asibitin jin abun da ya faru, sai dai ko kallonsa Al'amin ya ƙi yi." "Ya rasa in da zai saka kansa, mussaman da ya ga juahar a kwance ana saka mata jini, duk da" "tsananin kishi irin na Al'amin, Nura yana good time da jauhar, mussaman yake zuwa idan tana da aike, ya karɓa yayi mata, har kasuwa yake zuwar mata, sayen kayan beads da stone work." "Ta dafa abinci ta bashi, duk da yaron mijinta ne, kuma tana aikensa, hakan bai hanata girmama shi" "ba, da yi masa nasiha wasu lokutan." "Ganin shi ne sila, a ƙoƙarin hana shi illata lafiyar sa da Al'amin yayi tsautsayi ya faɗa kanta, ya" "sanya ya koma gefe yana kuka, saboda ya firgita da yanayin da ya ganta kamar gawa." Al'amin cikin tsawa ya ce masa ya fita ya bashi wuri. Nura ya fita wajen ɗakin ya tsaya cikin damuwa. "Al'amin ya je gida, ya bar jauhar da wasila, ya je ya yi wanka, ya ɗaukko mata kayan da za a" canza mata. "Sai bayan sallar magariba ya dawo, ya tarar da Baba tare da mama Anty zakiyya da kuma saifu a" "ɗakin, wasi ta goge mata jikinta, da taimakon Nurses ta saka mata kaya." "Tsayawa yayi yana kallonsu, yana tunanin ma a ina ya san su." "Sai daga baya, ya tuna Baba, ya durƙusa ya gaishe shi, ya amsa masa tare da faɗin ya mai jiki." "Ya amsa da ""Da sauƙi"" yana tunanin me Walid ya je ya gaya musu." "Baba ya ce ""Meyafaru ne? Wani ya je ya ce mana abokinka ne shi, wai ka turo shi an kwantar da" "jauhar a asibiti, hankalinmu duk ya tashi""" "Al'amin ya ce ""Ɓari ta yi""" "Anty ta ce ""Amma shi ne aka je aka ɗaga mana hankali, ni wallahi na zata wani abun ne ya same" "ta ma""." "Mama ta ce ""Duk da haka, tun da aka kai ga ƙarin jini tana jin jiki, Allah ya sa ba wani abun ne ya" "faru ba tayi ɓarin""" "Al'amin bai ce komai ba, ya ajiye kayan hannun sa, dai-dai lokacin Jauhar tayi wani yinƙuri zata" "faɗo daga kan gadon tana kiran ""Master kana ina?""" "Cikin hanzari ya ƙarasa gaban gadon, suna rige-rige da shi da Saifu." "Yayi hanzarin riƙe ta ya ce ""Zahra""" """Master""" """Na'am sannu""" """Meyasame ni ne? Kaina fa zai tarwatse ciwo master""" "Babu kunya ya rungumeta ya ce ""Zai daina, ki daina ɗaga muryarki""" "Cikin kuka ta ce ""Master bana gani, duhu nake gani bana ganinka"" tayi maganar tana tittirza ƙ" afarta a kan gadon. "Ya ce ""Zaki ganni in sha Allah, ki daina magana""" "Al'amin ko a jikinsa, ya ttatara hankalinsa a kanta, Baba ya ce ""Waliyiyya, sannu kin ji""" "Ta ce ""Baba""" """Na'am jauhar""" """Baba kai ne ka zo bana ganinku, duhu nake gani, makancewa na yi?""" "Saifu ya ce ""Baki makance ba, bacci ki ke ji, ki yi shiru""" """Yaya saifu, bana gani fa""" "Saifu ya ce ""Bacci ki ke ji ne""" "Cikin fita hayyaci ta ƙanƙame Al'amin ta sake cewa ""Master""" """Na'am madarata""" """Kaina zai fashe, ka riƙe mini shi da ƙarfi, marata ma ciwo take yi mini sosai"" tayi maganar" numfashinta yana fita sama-sama. "Yayi ƙasa da muryarsa yana yi mata raɗa ya ce ""Kina jina"" ta ɗaga masa kai." """Ki daina magana, ki yi shiru baki da lafiya""" """To meyasame ni?""" """Zazzaɓi ki ke yi""" "Ta ce ""To, ka je sallar asubar ne?""" """Na je mana, har na yi mana addu'a""" """To ka riƙe kaina da ƙarfi ka yi mini addu'a, jikina ma kamar an jona mini shocking nake ji""" "Nurse ɗin da ta shigo ta ce ""Malam ya ka ɗagata ana ƙara mata jini, so ake ta kwanta""" "Mama ta ce ""Faɗowa zata yi daga kan gadon, fizge-fizge take yi""" "Nurse ɗin ta ce ""Kwantar da ita, sai ayi mata allurar bacci""" "Ta rirriƙe Al'amin ta ce ""Kar ka ajiyeni, idan na kwanta bana iya numfashi""." "Al'amin ya ce ""To shikenan, ba zan kwantar da ke ba""" "Anty Zakiyya ta ce ""Wannan wane irin ɓari ne, zai saka mutum yayi ta surutai kamar" "mahaukaci?""." "Nurse ɗin ta kalleta ta ce ""Jini ta zubar sosai da sosai, dan haka jikinta yayi weak, alluran da" "muke yi mata kuma, sune suke burkita ta, dan haka ba abun mamaki bane ba""." "Al'amin yayi ajiyar zuciya, jin yadda Nurse ɗin ta rufe musu ainihin abun da ya faru." "Ita kuwa tayi hakan ne, dan tausayin yadda tun da ya kawo jauhar yake ɗawainiya, ko da" ganganci a lamarin yayi nadama. "Sai wurin sha daya suka tashi za su tafi, dan bayan allaurai ƙarancin jini ya saka ta fara haki," "athma kuma ta tashi, sai da aka sakata a kan oxygen." "Sai dai daga baya ta zama stable, baba ya din ga yi mata addu'a kan su tafi ya ce tsakanin mama" ko Anty Zakiyya wani ya kwana da ita Al'amin ya je gida. "Al'amin ya ce ""A'a baba, zan kwana da ita ba wani abu"" dama yanayin fuskarsu ya nuna ba su yi" niyya ba. "Baba ya din ga yi masa addu'a, sannan suka tafi." "Har suka je gida, suna mamakin kulawa da tashin hankalin da suka gani a tatatare da Al'amin." "Su Walid ma a reception suka kwana, da an ce a nemo abu, za su fita su sayo, shi kuma yana tare" da ita yadda ya ga rana haka ya ga dare. "Lokaci -lokaci tayi ta surutu, duk a dalilin mugun ƙarfin da ƙwayoyin suka yi mata." "Daf da asuba ta sake farkawa, sai dai ba ta zaburar, wannan karon tana gani, sai dai daga kwance" ma jiri take yi. """Master"" ya ɗago daga kifa kan da yayi, ya ce ""Sannu zahra ya jikin?""" """Alhamdilillah, jiri nake ji""." """Ki yi haƙuri, kin ga jini ake ƙara miki. Zaki daina ji in sha Allah, sannu"" yayi maganar yana" "shafa kanta, yana yi wa Allah godiya da ta farfaɗo." "Da sassafe Nura ya sake dawowa, har da guzirin bredi da madara da suga, ya dawo sake duba" "Jauhar, amma al'amin ya kore shi." "Liti ne ya dawo da shi ya ce ""Haba maza, Nuranka ne fa, waye ba ya kuskure? Kar ka yi masa haka dan Allah, kuma sakacin naka ne ba na sa ba, daka karɓa kamata yayi ka zubar ai, dan Allah" "ka yi haƙuri""" "Nura har da kuka ya ce ""Dan Allah yaya Aminu ka yi haƙuri, dan Allah wallahi ban ji dadin abun" "da ya faru ba""" "Daga kwance ta ce ""Master, laifin me ya yi ka ke korar ƙaninka, ayi haƙuri dan Allah, kalli ka" "saka yana kuka""" "Al'amin ya ce ""Ki daina magana kar hakin ya dawo""" """To ka ce masa ka haƙura, ka ga kuka yake yi""" "A hankali ya furta""Ya wuce""" """Yauwwa mai zamani, Allah ya ja zamanin maza"" tayi maganar tana ɗaga hannunta da ƙyar ta ta" ɓa fuskarsa. "Cikin jin daɗi yadda take ƙarfin hali, yayi murmushi ya ce ""Ban hana ba?""" Murmushi ta yi masa ba ta ce komai ba. "Da nurse ta shigo ta tarar da ita, tana magana, ga su liti a gefe ta ce ""Zahra gawa taƙi rami, sannu" "kin ji""" """Yauwwa Anty na gode """ "Ta kalli Al'amin ta ce ""Congratulations, na tayaka muranr farfaɗowarta, dan wallahi mun sare" "bamu zaci zaki tashi ba""" "Walid ya ce ""Sannunku da ƙoƙari, Allah ya biya ku""" """Amin, bari mu gyara mata jikinta, a bata abinci "" su liti suka fita, ya taimakawa nurse ɗin, ta" "gyara jauhar, ta zaunar da ita, duk da tana ta kuka da jiri da ciwon kai da na mara." "Ya haɗa mata shayi, da buredi, sai dai ta kasa ci, sai lallaɓata yake yi." "Wasila tayi sallama, suka amsa." "Ta ce ""Alhamdilillah anty jauhar jiki yayi kyau, ikon Allah""" "Nan suka ƙara gaisawa, ta ajiye abincin da ta zo da shi, jauhar ta ce za ta sha kunun gyaɗar da ta" kawo. "Ana haka su Baba suka zo, suka tarar da Al'amin yana ba ta abinci an zaunar da ita." "Gab ɗaya zamansu a wurin, bai hana shi tattalin matarsa ba, dan gani yake yafi kowa sa'a farfaɗ" owar da ta yi. "Babban abun da ya yi wa jauhar daɗi, bai wuce ganin 'yan gidan su, sun zo dubata ba, ko ba komai" sun nuna damuwar su da ita. "Duk saifu na ta zuga Baba ya bi diddigin yadda aka yi tayi ɓarin, ko dukanta Al'amin yake yi, amma yanayin yadda suke mu'amala ita da Al'amin ya sanya kowa yin wani tunanin daban, dan sa" ɓanin abun da ake tunani ake gani. "Har Abbu sai da ya zo duba jauhar, su shahida ma duk sun zo, Baba sai da ya yi ta yi wa wasila" "godiya da Addu'a, tana ta ƙoƙari da jauhar, maƙwabtan su ma na ta zuwa dubata." "A kwana na uku, da daddare take tambayar Al'amin ""Master wai dan Allah meya same ni ne? Na san kawai na ga lemo a ɗakinka na sha, daga nan ban san meyafaru ba, kuma na ji ana cewa nayi ɓari, ya aka yi na yi ɓari ai bani da ciki, ko kuma ina da shi ban sani bane? To yaya aka yi ya" "zube?""" """Ki yi haƙuri, likita zai yi miki bayani in sha Allah""" """To kai ka yi mini mana, wai shikenan babyn yanzu babu a cikina"" tayi maganar tana shafa cikin" ɗauke da damuwa. """Ni likita ne?""" """A'a amma ka gaya mini, haryanzu ina da cikin?""" "Al'amin ya ce ""Wai abun da baki san da shi ba ma, zaki bi ki damu, ki yi haƙuri za su yi miki" "bayani""" "Ta ce ""To shikenan, yi mini addu'a na yi baccin""." "Ya ce ""To""" "Gari ya waye, su surayya ma suka zo dubata, saifu ya kawo su, take tambayar ina yaya hafsa, aka" ce mata ta tafi umara. "Jauhar ta ce ""Dan Allah ku ce ta yi mini addu'a sosai da ni da master""" "Suryaya ta ce ""Wai ke kowa na gaya wa miji sunan 'yan gayu ke kina master""" "Tayi murmushi ta ce ""Baki ga mastern ne ba? Kuma ai mu ba 'yan gayu bane""" "Kasancewar Al'amin ba ya ɗakin ya sanya saifu cewa ""Ke, ki faɗa mini gaskiya, wani abun yayi" "miki ko?""" "Ta ce ""A'a me ka gani?""" """Wallahi ki ka rufa masa asiri sai kin daku, har likita na saka baba ya tambaya, ko dukanki yayi ya" "ce babu alamar duka a jikinki da aka kawo ki""" "Jauhar ta ce ""Master ba ya duka, bai taɓa dukana ba""." """Na san halinki da shegiyar gwaninta ne, da kare mai laifi ki gaya mini gaskiya""" """Wallahi babu abun da ya yi mini""" "Dawowar Al'amin ya sanya su yin shiru, ya ƙarasa gaban gadonta ya ce ""Me zaki ci?""" """Bakomai, kawai a sallame ni""" "Ya zauna a gefen gadon ya ce ""Ba na son rigima, wace irin sallama kuma?""" """Kai ka koya mini ai, kai fa har guduwa ka ke daga asibiti""" "Yayi murmushi ya ce ""Zaki gudun kenan?""" "Ita ma murmushin ta yi ta ce ""Kashe kuɗin yayi yawa, ina iya tashi ai""" "Rarrashin ta ya din ga yi, dan shi kansa ya san zaman asibiti da gundura." "Sai da ta kwana shida, an saka mata jini ya kai leda biyar, sannn aka fara zancen sallamar ta ranar." "Daga likitan sai ita da Al'amin a ɗakin, yayi mata bayanin abun da ya faru, tare da gaya mata" akwai buƙatar ta huta kan ta sake ɗaukar ciki. "Ya yi wa Al'amin faɗa a kan ya kiyaye sosai da sosai, wannan karon sun rufa masa asiri idan ya ƙ" ara faruwa. "Jauhar ta sunkuyar da kai, sai kuka." "Likitan ya ce ""Menene? Meyafaru? Kuma?""" "Al'amin ya ce ""Bakomai, zamu yi magana da ita""" Likitan ya rubuta musu sallama ya fita. "Yana fita ya ce "" 'yar madara menene kuma?"" Shiru ta yi masa ta cigaba da kuka." "Duk yadda ya rarrasheta, tayi haƙuri ta ƙi yin magana." "Baba ya zo da mota, ya ɗauke su ya kai su gida, ya yi ta yi wa Al'amin godiyar ɗawainiyar da ya" "yi ta yi da jauhar a asibiti, yayi musu sallama ya tafi." "Al'amin ya zauna kusa da jauhar ya ce ""Dan Allah ki gaya mini menene?""" """Komai ma, kawai ka janyo na rasa babyna, kuma wai ba zan haihu yanzu ba, wataƙila ma ba zan" "sake haihuwa ba""." """Subhanallah kar ki yi mana wannan fatan, zaki kuma haihuwa cewa suka yi kawai ki bayar da" "tazara saboda yanayin jikinki""." "Cikin kuka ta ce ""Ai da ka daina shan Wannan abubuwan, duk da ba haka ba. Kawai ka ja na yi" "asara ga jinina ya ƙare, kuma wai ba zan haihu yanzu ba""" "Cikin tsananin nadama yake rarrashinta, sallamar mutane ya sanya ya tashi, 'yan dubiya suka din" ga zuwa duba jauhar. "Al'amin na ta hidima da ita, da sassafe yake tashi ya yi aikace-aikace, girki ne kawai sai maƙwabta" sun shigo suke yi mata. "Shahida ma ta yi ƙoƙari sosai, dan tana zuwa ta taya jauhar aiki, a haka suka saba." "Guduma ya sake zuwa har gida ya duba jauhar, tare da gaya mata abun da ya faru." Jauhar tayi masa nasiha sosai a kan shaye-shaye. "Al'amin ya fara bata tausayi, har rama yayi sosai, mussaman daina kula shi da tayi, sai yayi ta" kame-kame. "Yau da ya dawo, normal ta karɓi abun ta." "Har ya tafi ya kwanta, ta bishi ɗakinsa." "Ta hau gadon ta kwanta ta ce ""Master""" """Mmm""" """Ka yi haƙuri dan Allah, komai ya wuce na ji babu daɗi ne kawai shiyasa kawai""" "Ya ce ""To""" """Kayi magana mana, ba to ba""" """Ina jin babu daɗi, missing babynki da ki ka yi, ki yi haƙuri laifina ne""" """Ba fushi na yi dan cikina ya zube ba, fushi na yi saboda bani ba har kai kana yi mini ganganci da" "rayuwarka, ka daina dan Allah for our own good and safety""" "Ya ce ""To in sha Allah""" """Yaya za a sha fankar ne?""" "Ya girgiza kai ya ce ""Likita ya ce ki huta tukuna kar ki sake ɗaukar ciki""." """Sun yi mini allura ai, ko haryanzu ba ka jin komai""" "Ya ce ""Da ɗin ma ina ji, mazewa nake yi, a madadin hakan sai in sha in bugu in manta da ke""" """Master nawa nikaɗai, daga ni ba ƙari""" """A'a saura uku""" "Ta ce ""To ga fili ga mai doki nan ai""" "Ya ce ""Filin da dokin naki ne ai, ki yi yadda ki ke so madarata""" *** "Jauhar ba ta samu damar yin jamb ba, saboda rashin lafiya, dan haka Al'amin ya samu indabo ya ce A alƙawarurrukan da ya yi masa, yana son ya samawa jauhar admission, tare da samawa Nura" "guduma aiki ko na direba ne, a manyan ma'aikatu." "Al'amin ya daina shigo da duk wani abu na shaye-shaye gidan, ko zai yi a iya waje yake tsayawa" yayi abun sa. "Jarin su duk ya ƙare a asibiti, dan haka ya yanke wata shawara a ransa." Ayshercool 08081012143 ₦500 ne via 0009450228 Aisha Adam jaiz bank sai shaidar biya ta 08081012143 90009343 'Yan Nijar ku turo katin airtel na 300fcfa Arewabooks ayshercool7724 "Jauhar ya fara samu da maganar, da daddare suna tare ya ce ""Na ce ba""" """Ka ce me ranka ya daɗe?""" """Wani abu na yanke ne, ina son na samu Abbu, ya bani gadona na wurin ummi, in sayar da abun" da zan sayar na karɓi kuɗi a wurin indabo na haɗa na fara wata sana'ar ina son barin sayar da wiwi "gaba ɗaya""." "Tayi murmushi ta ce ""Alhamdilillah, tunani mai kyau, amma ba a yadda ka gaya mini haka zaka je" "ka gaya wa Abbun ba ko?""" """A yaya zan gaya masa?""" """Cikin kwantar da murya, zaka yi masa bayani, ka san iyaye sai ana lallaɓa su, ka sani ma ko ya" "kai ka kasuwa?""" "Ya ce ""Ko ya kai ni ba na so, ya je ya cigaba da riƙe 'ya'yan matar can. Dama alhkina ne ya sa" "yanzu ba shi da kuɗi kamar da""" "Jauhar ta ce ""Haba master, Abbun ka ke gaya wa haka, kai zaka ji daɗi ka haifi ɗa yayi maka" "haka?""." "Cikin ko in kula Al'amin ya ce ""Duk tsanani, ba zan yi wa ɗa na abun da yayi mini ba""" """Master ka san shiga tsakaninka aka yi da Abbu, dan Allah ka daina irin wannan maganar""." "Yayi mata shiru, ta sake cewa ""Master yaushe zaka kai ni mu gaida su Hajiya?""" """Ba rana? Tun bayan kawo ki sun kuma zuwa?""" """Hmm master, Allah ya baka damarmaki, duk da ka rasa ummi da yaya sadik, da kuma uban gidanka. Ko yaya dole nan gaba yaranka su so ganin 'yan uwanka, dan da dangin uba ake ado. Ni fa duk wannan abun da ake yi, bani da wayo sanin mahaifiyata ta rasu, ba 'yar gari bace, yar jalingo ce, ba a taɓa kai ni garinsu ba, ba a taɓa nuna mini ko mutum ɗaya a danginta ba, kuma ban taɓa ganin kowa ya zo daga garinsu ba. Da na fuskanci babu uwata a gidan, na nemi ba'asin in da take, baka ga dukan da mama tayi mini ba, ban haƙura ba na tambayi baba, amma ya ce idan na kuma yi masa zancen dangin mamana, sai ya zane ni. Yadda yake nunawa da yadda su mama ke fa ɗa yana son mamana, amma nayi mamakin yadda yaƙi yadda a kai ni garin su na ga ko 'yan uwanta, da naga ba ya so kawai na daina maganar. Kai kuwa da ka rasa uwa akwai makwafinta, yakamata mu je mu ga hajiya mu gaisheta, ni ba wanda zan kalla na ce daga wurin dangin" "mahaifiyata yake""." "Yayi ajiyar zuciya ya ce ""Kuma ba ki san a ina take a jalingon ba?""" "Ta girgiza kai ta ce ""Ban sani ba, kawai iya abun da na sani kenan""" """Shikenan, zamu je mu gaida hajiya, amma sai na tambayi Abbu in da take a tofan ba zan iya" "tunawa ba""" """Yauwwa maigidan Allah dai ya iya maka, ya goyi bayanka yayi maka jagora """ "Ya shafa fuskarta ya ce ""Amin madarata""" """Yauwwa milona""" "Ya ce ""Ga madara ga milo, sai Shan shayi"" suka yi dariya tare." "Washegari da safe bayan sun karya, ya bata magunguna ta sha, tana ta lallaɓa jikinta, za ta yi" "aikace-aikacenta, ya hanata ya fito ya yi mata share-share, har tsakar gida ya wanke mata." "Kayan da ta cire yake wankewa, aka buga ƙofa, ya je ya buɗe hafsa ya gani a tsaye, hannunta riƙe" da leda. "Ya bata hanya ta shigo, a tsorace ta kalli Al'amin fuskarsa a haɗe ta ce ""Ina kwana""" """Lafiya ƙalau""." """Dan Allah wurin jauhar na zo"" da hannu ya nuna mata falo." "Daga falon ta ce ""Muryar wa nake ji kamar Yaya hafsa""" "Ta ce ""Nice""" "Ta tashi ta taro hafsa ta ce ""Sannu da zuwa""." "Hafsa ta ce ""Yauwwa sannu ya jiki?""" """Jiki Alhamdilillah, ya aka yi ki ka gane gidan?""" """Yaya saifu ne ya gaya mini hanya, kuma direbana da yayi tambaya aka nuna masa gidan ba" "wuyar ganewa""." "Ta ce ""Allah sarki yaya hafsa tun ina Asibiti nake tambayar kina ina, aka ce mini kina umara, na" "ce baki gaya mini ba muna chat, ai da na jero addu'a ayi mana ni da mai gida""" "Tayi murmushi ta ce ""yanzun ma an yi miki, wai jauhar ɓarin da wahala ne, na ga kin rame haka" "kin yi fari?""" """Kai da wahala mana, jini na zubar sosai shiyasa na yi haka, amma kwanaki ai ƙiba na yi sosai," "ashe ciki ne ban sani ba""" """Allah sarki, Allah ya kawo mai amfani, sannu""" """Yauwwa ai na warware """ "Al'amin ya shigo falon, jauhar ta ce ""Master ba ka ganeta ba ne? Yayata ce da muka je gidanta fa," "ba ka ga muna kama ba?""" "Kai tsaye ya ce ""Na gani, kin fita kyau""" "Jauhar ta ce ""Kai fa ka fiye son kai ta ina?""" """Ta ko ina"" yayi maganar yana shigewa ɗakinsa." "Hafsa tayi murmushi ta ce ""Aikam kin fi mu kyau ai duk gidan nan""" "Jauhar ta ce ""Rabu da shi, shi ma faɗa kawai yayi"" suka cigaba da hira, ya sake fitowa ya shirya" tsaf zai fita. """To yau me ki ke so? Kayan cikin ko ganyen wanne ki ke so?""" "Ta shagwaɓe fuska ta ce ""Kai""" """Ni ki ke so?"" Ta ɗaga masa gira tana murmushi." """Aikuwa zaki kwana da yunwa, me ki ke so?""" """Komai ka samu na gode""" "Ya ce ""Abun da zai ƙara miki jini aka ce ai""" """Jininka zan sha"" ta yi maganar tana dariya." "Yayi murmushi ya ce ""You are not serious, ki yi addu'a Allah ya sa na samu kuɗi, na sayo miki" "kaza""." "Hafsa ta ce ""Ai ga miya ma na yi miki, da kazar a ciki""" "Jauhar ta ce ""Ashe zaku yi faɗa da master, tun da ki ka riga shi kawo mini kaza""" "Murmushi ya sake yi, wanda ya bawa hafsa mamaki, take bin su da kallo, gwanin burgewa." "Har zai fita ta ce ""Master""" "Ba tare da ya juyo ba ya ce ""Kar na yi shaye-shaye da yawa, kar na yi faɗa da kowa, banda rigima da mutane"" ta kwashe da dariya ta ce ""Au ka haddace ma kenan, addu'a zan yi maka ai, Allah ya" "iya maka, ya goyi bayanka yayi maka jagora ya wadatamu da halal ya nesanta mu da haram""" "Ya waiwayo ya ce ""Amin ya haiyyu ya ƙaiyyum, 'yar aljannata"" ya juya ya tafi." "Yana fita Hafsa ta ce ""Innalillahi, jauhar dan Allah ya aka yi ki ka canza mutumin nan, dariya fa yake yi miki, kalli yadda yake yi miki, dan Allah jauhara ya ki ka yi ki taimake ni"" tayi maganar" cikin tsananin damuwa. "Jauhar ta ce ""Ban fahimci in taimake ki ba yaya hafsa, meyafaru? Wannan ai normal ne tsakanin" "ma'aurata, kodayeke shi ya koya mini rashin kunya, da ko kallonsa bana iya yi a gaban mutane""" "Idon hafsa ya cika da hawaye ta ce ""Jauhar, wallahi tun da na auri Alhaji mu'azzam hankalina bai kwanta ba, bai taɓa bani awa biyar cikakkiya ba. Sai abun da matarsa take so yake yi, bai tare a ɗ akina ba sai da matarsa ta amince. Ga kuɗin yana da su, yana kashe mini ya sakar mini amm ba su" "nake so ba, kulawarsa nake so da lokacin sa""." "Juahar ta ce ""Yaya hafsa ba fa abun da ki ke kalla a film ne soyyaya ba a ƙasar hausa da wurin mijin bahaushiya, dole ki fara kallon wane irin mutum ne shi, kin ga mijinki mutum ne mai hidindimu da yawa, ba zai yiwu ace kullum yana da lokacinki ba yakamata ki din ga yi masa" "uzuri""" """Uzuri jauhar, yana da lokacin matarsa da yaransa, gaba ɗaya auren ya fita daga kaina, na je na gaya wa anty, wai wallahi na ɗaga maganar nan, sai ta yi mini Allah ya isa, wai zan saka ayi mata dariya, na zama kamar hoto a wurinsa, ko ɗan abun ɗokin nan na amarci, duk fa ban san su ba. Ke da ki ka auri wanda ake yi wa kallon sai a hankali, babu imani da tausyai a zuciyarsa kalli abun" "da yake yi miki fa. Ni dai dan Allah idna wani malamin ne da ke, ki haɗa ni da shi""" "Cikin damuwa jauhar ta ce ""Yaya hafsa ni wallahi ban san in da ake ganinsu ba ma, canza mutum daga wani abu da baka so zuwa wani, ba abu ne mai sauƙi ba. Kin san ni irin wahala da gwagwarmayar da na sha kafin mu zo wannan matakin kuwa?" "Da fari nima damun kaina na din ga yi, daga baya na kama addu'a babu dare babu rana, na haɗa da biyyaya da kuma haƙuri." "Master mutum ne, kallon da mutane suke yi masa daban, wanda nake yi masa daban, biyayya da addu'a ne suka canza mini shi. Alkhairin da yake yi mini nake kalla kullum, nake yi wa laifukansa uzuri, har gara ke kina da uwa a raye, ni daga ni sai Allah, da na san bani da wata mafita, na bi abun da ƙaddara ta zaɓa mini, na rungumi abuna hannu bibbiyu. Kuma Allah ya shiga lamarina Alhamdilillah, mijina talaka ne, amma ba kowace mace take da ikon da nake da shi a gidan aurena ba. A zahiri shi nake bawa girman, shi ne jagoran amma a baɗini ni ce sitiyarin rayuwarsa, ina" "fatan kasancewa da shi har aljanna. Ke ma ki nutsu ki gano menene kurakuranki, sai ki gyara""." """Ba wani kuskure, ina kyautata zaton asri aka yi mini wallahi """ """A'a yaya hafsa, ki daina faɗar haka, ki miƙa wa Allah lamuranki, wallahi zaki ga canji """ "Duk yadda jauhar ta so nusar da Hafsa muhimmancin haƙuri da juriya, da dagewa a kan addu'a" amma taƙi ganewa kuma taƙi yadda. "Zuwa azahar ta tafi, ta yi wa jauhar uban farfesun kaji, da abinci, ta kuma ajiye mata kuɗi ta tafi." Har a lokacin ba ta yadda har da hakkin jauhar a abun da yake faruwa da ita ba. "Al'amin ne zaune a gaban Abbu, tun da ya gaishe shi, yayi shiru." "Abbu ya ce ""Ya jikin 'ya ta?""" """Da sauƙi""" "Abbu ya ce ""To Alhamdilillah yarinyar kirki, 'yar aljanna Allah ya ƙara mata lafiya, matso ka haɗ" "a shayi ga kayan breakfast nan""" "Sai da Al'amin ya kalli Abbu, ya girgiza kai ya ce ""Na ƙoshi""" """Too, yau kai ne ka ƙoshi da abinci kuma?""" "Ya bashi amsa da ""Eh na ci a gida""" "Abbu ya yi murmushi ya ce ""Na manta ne, ashe fa magidanci ne, ya aka yi?""." """Sonake a sayar da gadona, zan ja jari, sana'oin da nake yi, ba sa iya riƙe mu sosai, gashi ina so ta koma makaranta, babu isasshen kuɗi a hannuna." "Sai kuma ina son ka bani full adress ɗin hajiya, zan kaita ta gaisheta ta matsa a kan haka""" "Abbu yayi shiru yana ƙarewa Al'amin kallo, duk ya ɗan yi sanyi daga wani rashin mutuncin, babu uwar sumar da yake tarawa da faratan da yake bari zaƙo-zaƙo, gashi yadi ne a jikin sa saɓ anin da, da idan bai ga dama ba da 3quater yake yawo da shirt damatsansa a waje, ya wani nutsu sosai." "Abunka da uba da ɗa, wani irin shauƙi ya ji yana kama shi, a yadda ya ga tarin sauye-sauye a" tattare da Al'amin. """Kai amma 'yar nan tawa ta kyauta, amma wace sana'ar zaka yi?""" "Al'amin ya ce ""Da wurin buga bulo nake so, ko wurin yin buredi, amma ban gaya mata ba tukuna," "ban sani ba ko tana da wata shawarar""" "Abbu ya numfasa ya ce ""Kana ji na Al'amin, tsawon shekarun nan, filayenka sun yi daraja sosai da sosai, idan ka bari suka ƙara kwana biyu sai sun fi haka sosai. Ka je ka rubuto business plan ɗin ka kawo mini, tare da list ɗin abun da za ayi mata na makarantar, sai na baka kuɗin, idan Allah ya dafa maka, aka samu cigaba, sai a sayar da ko gona ce a garinsu a ƙara, ka san kana da wasu" "kadarorin a tofa""" "Al'amin ya ce ""A'a ni ba na son ka yi mini abu, daga baya azo a saka ka din ga yi mini gori, kawai" "dai a bani wanda na san nawa ne, kuma ma ni na fi son registration nayi mata da kuɗina da kaina, sai na fi alfahari da haka""" "Abbu ya ce ""Gaskiya ne, kamar ba a nan ka zauna kana ce mini, ba ka son auren ba""" Al'amin yayi shiru yana basarwa. """Ka rubuto business plan ka kawo mini, zan san abun yi, ka je ku yi shawarar ina jiranka." "Gaba ɗaya haushi ya cika Al'amin, kawai ya ji ba shi ne ba zai yi ba, ya ce ""Ina ne gidan hajiya a" "tofa""" "Abbu ya kwatanta masa, ya tashi ya fita." "A waje suka yi karo da Rahila, bai ko kalli in da take ba ya fice." "Ta shiga gidan da sauri, ta samu Abbu ""Yanzu na ga Aminu ya fita, Allah ya sa ba wani abun ya" "aikata ba?""" "Abbu yayi murmushi ya ce ""Al'amin ai rigima ta ragu yanzu, duk da wata rigimar ya zo yayi mini ya tafi. Wai gadonsa yake son a bashi, saboda yayi sana'a ya kula da matarsa"" gabanta ya faɗi, ɗan kuwa ba ƙaramin harin filayen nan take yi ba, manyan filaye ne awon gwamanti ga gidaje guda" uku. Ko da Abbu ya samu karayar arziki bai taɓawa Al'amin su ba. """Wace irin sana'a kuma, wallahi kar a sayar, ba shi da shi a ina ya samu kuɗin sayen leshin dubu tamanin ya bata ta saka, kalli a asibitin da ta kwanta fa na kuɗi, kalli uban kaji da naman da aka kawo gidan nan da salla, duk ba shi da kuɗin yayi haka? Ni ban taɓa zaton zai iya zama soko har" "haka ba a kan mace wallahi, yanzu saboda kula da itan ne za a sayar da wannan wuraren?""" "Abbu ya ce ""Ba dai nasa bane ba, shi ya ga zai iya ai""" "Jauhar ta lallaɓa ta cigaba da sana'oin ta, yanzu tana iya aikace-aikacen ta, ta gama aikin, ta idar da" "sallar magariba, ta ji bugunsa." "Ta buɗe ta kalle shi, ta ce ""Malam lafiya ka ke yi wa mutane wannan bugun haka?""" """Zance na zo""" """A me ka zo""" "Ya ce ""Ƙafata""" "Ta ce ""Ko keke ba ka da shi ma?"" Ta fito ta zauna a kusa da shi, a kan barandar gidan malam" "lawan ta ce ""To me ka kawo mini """ "Ya ajiye baƙar leda ya ce ""Gata nan gyaɗa ce marau, suyar yau mai zafi""" """Ka rasa me zaka kawo mini sai gyaɗa, anya ka na so na din ga fitowa zancen nan"" ya saka hannu zai ɗauke ledar, ta riga shi ɗaukewa ta ce ""Allah ya shiryeka, Allah master da da kanka a ka bari" "ka samo matar aure, za a sha wahala kan ka samu""" """In ji wa? Farinjini fa zan yi """ """A hakan kana muzurai da zare idon? Kan na saba da kai fa na daɗe, tsoro ka ke bani da sosai """ "Ya ce ""To yanzu fa?""" """You are my best friend ever, sauƙin kai ne da kai fiye da yadda ka ke tunani, miskilanci ne kawai" "matsalarka wuyatta na dafa abinci mai daɗi shikenan an wuce wurin """ "Suka kwashe da dariya tare, a kan barandar gidan, suka cigaba da hira, suna cin gyaɗa," "kasancewar a cikin duhu ne, babu wuta, yake ba gaya mata yadda suka yi da Abbu." """To yanzu wanne zaka yi a ciki, wace sana'ar zaka yi?""" "Ya ce ""Rabu da shi, idan muka je ƙauye zan saka a nuna mini gonakin, a sayar da wata na karɓo" "kuɗina""" """A'a kar ka yi haka master """ """Haka fa za a yi, wallahi ba zai taimaka mini ba muddin shegiyar matar nan ta sani, ban da ina" "duba darajar amintar da suka yi da marigayiyya, wallahi da sai na tsinke mata laka""" """A'uzibillah, wannan wace irin magana ce?""" """Mu bar wannan maganar, ɗaukko key ki rufo gidan mu fita yawo "" ta ce to." "Ta rufe gida, ya goya ta a babur, suka tafi ya din ga zaga gari da ita, ya kaita gidan su, ya ce ta" "shiga ta gaisa da baba mintuna goma ta fito, saboda ya lura shi ne kullum yake kiranta a waya, yana tambayarta ya jiki." "Baba ya din ga murna, ganin ta warware, baba da kansa ya rakota, suka gaisa da Al'amin, ya yi ta yi musu fatan alkhairi, da fatan samun wani rabon mai amfani jauhar ta yi shiru, shi kuwa ya amsa" da Amin. "Ba su da wurin zuwa, ya cigaba da zagaye da ita, suna tafe suna shan iska, ya saya mata kayan" "ciye-ciye, su rake, awara, dafaffen ƙwai kasancewar dama ba iya cin abinci take yi ba." "Har wurin sha daya sannan suka koma gida, ya ci abinci." "Ganin yana ta kaiwa da komowa tsakanin falo da tsakar gida, bayan sun yi shirin kwanciya, ya" sanya ta gane shaye-shaye yake son yi. "Ta kalleshi ta ce ""Master ka je ka sha, amma kaɗan dan Allah, ba da yawa ba, kar ka bugu"" ya ce" """To""" "Ya fita tsakar gida yayi abun sa ya gama, tana jin sa ya shiga ɗakinsa yana wanka, ya fito ya saka turare ya nufo ɗakinta, duk da yana ɗan warin sama-sama amma ƙamshin turaren ya hana warin" yin tasiri. """Ba ki yi bacci ba?""" "Ta ce ""Ban yi ba jiranka nake, na san ko na yi sai ka tashe ni""" """Allah sarki madarata"" yayi maganar yana rungumeta, ya kwanta da ita a jikinsa." """Wace sana'ar ki ke ganin zan fara?""" """Ka yi tunanin ko kala uku ce, sai mu yi addu'a Allah ya zaɓa mana mafi alkhairi """ "Yayi ajiyar zuciya ya ce ""Babu laifi""" """Masterna, kai zaɓin Allah ne a gare ni, na gode Allah da bai sanya ni cikin masu yi masa butulci" "ba""." "Ya ce ""Ni ɗin?""" "Ta jinjina masa kai. Nan ta bashi labarin hafsa, ya ce ""Allah ya ƙara, alhakinki ne ai, daga har ke" "turin jeka ka mutu suka yi mana mussaman ke, Allah ya ƙara""" """Master yayata ce fa""" """Koma wacece, ai Allah ba ya barin zalunci""." """Duk da haka master""" """Ni yanzu dan Allah da gaske kina jin daɗi rayuwar da muke yi a haka?""" "Ta ce ""Gaya mini matar da aka taɓa goyawa a tarihi, aka yi tafiyar da aka yi da ita a baya, saboda" "ba ta da lafiya? Gaya mini matar talakan da ake ajiyewa masu kula da ita? abubuwa da dama da mata suka rasa a gidan aure ni na samu""." """To ai wannan duk ba wani abu bane ba a kan wanda ki ka din ga yi mini, dan Allah kina jin daɗin" "zamanmu a haka? Just recently kin kusa rasa ranki saboda ni?""" "Ta ce ""Ba laifinka bane ba ai"" ya yi murmushi cikin jin nishaɗi, yake ƙoƙarin canza hirar zuwa" "wani abu daban""." """Master""" """Mmm""" """Ban taɓa jin ka ce kana so na ba, ko dai kara kawai ka ke yi mini, saboda halaccin da kake iƙ" "irarin na yi maka?""" """Nima baki taɓa gaya mini ba, kuma ina yi a aikace ai, ba dan haka ba, babu wanda ya isa ya saka" "na zauna da ke ai""." "Tana dariya ta ce ""Sai abinci""" """Ki kiyayeni da abincin nan, kina takura mini fa""" "Ta shafa bayansa cikin shagwaɓa ta ce ""Ba ka ce ba""" """Me?""" """Ka na so na""" """Yanzu dai jirani tukuna, na gama caji, koma menene ya biyo baya""." """Ba zaka yi cajin ba, sai ka gaya mini""" """Yanzu na tashi na yi waje, zan je na yi wanda na saba, na manta komai, yanzu zaɓi ɗaya""" """Ni zaka yi wa wayo ko?""" """A'a ba wayo zan yi miki ba, zaɓi na baki""." "Da safe jauhar ta fito falo, ta tarar da Al'amin a kan kujera, ta ce ""Master da me ka yi wanka ne a" "banɗakina?""" """Sabulu""" """Wanne?""" """To ai abubuwan naki ne da yawa, kuma kina bacci kawai na ɗauki na wata roba, na zuba a soso""" """Master feminine wash ne fa""" "Ya kalleta ya ce ""Me ke nan?""" """Abun kama ruwa ne, dan Allah yayi kama da abun wanka?""" "Al'amin ya ce ""Kai, wallahi tsirfarki tayi yawa, kama ruwan ma, sai an yi masa wani abu, to sai ki" "din ga rubutawa a jikin robar""" "Cikin shagwaɓa ta ce ""Gaskiya sai ka saya mini wani, dubu uku fa na saya""." """Iyee dubu uku, ke fa wasu lokutan kin iya damfara, dubu uku, wannan abun ne dubu uku, car" "wash ne fa""" """Morning fresh ne, wai car wash kuma yasin sai ka biya ni, ina jin daɗin amfani da abuna fa, kai" "da ba a gyarawa ka din ga lallaɓowa""" """A daina gyarawar, a bar mini abuna a haka, ko kuma ki karɓi car wash""" """Sai fa ka biyani, wuyatta na soya maka wainar fulawa da zoɓo mai sanyi, sai ka zazzage mini" "komai na aljihunka""" """Ai dama kin saba cin zalina, ki kwashe mini kuɗi""" *** "Tun sassafe jauhar ta shirya, kasancewar yau za su tafi tofa, gidan Hajiya, duk da ya ce wuni kawai za su yi da yamma su dawo gida, ba ta damu da hakan ba, tun da dai ya amince za su je ɗ in." "Ta zata tafiyar mai nisa ce sosai ma, sai dai ba su daɗe ba suka isa garin, kwatancen babu wahala," suka isa har gidan Hajiya. "Da ta amsa sallamar su ba ta gane su ba, sai daga baya ta gane Al'amin." Cikin hanzari ta tashi tana yi musu sannu da zuwa. """Al'amin, dama zaka tako ka zo in da nake?""" """Tun da ke kin watsar da ni ko?""" "Ta ce ""Ba haka bane, ku shigo""" """Amarya, ki yi haƙuri ban sake zuwa ba, ina ta fama da ciwon ƙafa, kuma ina tsoron wulaƙancin" "matar mahaifinka, ko lokacin bikinka, ba ka ga abun da ta din ga yi mana ba, mahaifinka ma" "haushina yake ji, shiyasa na janye jikina daga gare ku""" "Jauhar ta ce ""A'a hajiya ki yi haƙuri, ai laifin wani ba ya shafar wani, mu dai zamu din ga zuwa" "muna neman albarka""" """Allah sarki, aure mai gyara mutum, yanzu a dalilin auren ya sanya ka zo in da nake""" "Al'amin ya ce ""Eh, ba dan ta matsa ba ba zan zo ba gaskiya, tun da kema ba ƙaunata ki ke yi ba""." "Jauhar ta ce ""Master ya haka kuma?""" """Ba ƙarya nayi ba, ki ke zare mini ido""" "Sai hajiya ta kama kuka, ta ce ""Wallahi da gayya ba zan yi haka ba, ina son 'ya ta ina son ku," "amma an yi mini iyaka da ku, kusan kullum sai na yi kukan abun da mahaifinku yayi mini a kanku""." "Jauhar ta ce ""Dan Allah hajiya ki yi haƙuri, ki yafe musu, ke ce makwafin uwa a wurinsa dan" "Allah ki daina kallon abun da suka yi miki""." "Al'amin ko a jikinsa, dan ita kanta tsohuwar haushinta yake ji, yadda laifin abbu ya shafe su a" wurinta. "Daga baya kuma cikin hikima, jauhar ta din ga jan su da hira, kasancewar ranar kasuwar garin take ci, har kasuwa suka je sayen ƙwan zabi, Hajiya ta haɗa wa jauhar sha tara ta arziki ta ce ita" "da jauhar take jikar, shi kuma ya je ya ƙarata." "Yayi mata zancen gonakin mahafiyarsa, ta ce masa ""Hayarsu ake bayarwa ana noma, duk shekara" "ana karɓar kuɗin, mahaifinka bai bani damar zama da shi mu yi magana a kan hakkinka ba, amma kuɗinka suna nan ana tara su, ƙanina ne yake ajiyewa, sai dai ya je Lagos yanzu""" """Idan ya dawo zan dawo nima""" """Allah ya kawo ka lafiya, kuɗi ne masu kauri sosai kam""." "Sai yamma sosai, sannan suka koma gida." Ana ta kiran sallar magariba sannan suka shiga gida. "Da daddare har sun yi shirin kwanciya, Anty zakiyya ta kira jauhar a waya, jauhar ta ɗaga ta ce" """Anty lafiya kuwa?""" """Ban sani ba, wallahi jauhar ba kya tsoron Allah, kina so ki gama da duniya lafiya kuwa?""" "Cikin tashin hankali ta ce ""Anty me na yi, lafiya?""" """Ban sani ba, yadda mugun abun uwarki ya koma kanta, kema da yardar Allah sai naki ya koma" "kanki""." """Anty haryanzu baki gaya mini me nayi ba?""" """Asirin da ki ka yi wa hafsa, gashi an dawo da ita gida, tana ta fizge-fizge tana kiran sunanki," "wallahi ki gaggauta karya abun da ki ka yi mata, kafin mu gauraya da ni da ke, baƙar annoba kawai"" ta kashe wayar." "Cikin tashin hankali ta fita falo tana kuka, ta ce ""Master""" """Yes yaya""" "Cikin kuka ta ce ""Ka tashi ka kaini gida""." """Meyafaru a gidan?""" """Ka kaini gida kawai, ba zan iya bacci ba, wai an ce ni na yi wa yaya hafsa asiri, wai sai ihu take" "yi, tana kiran sunana, wallahi ni ban yi mata asiri ba""." "Tashi yayi zaune ya ce ""In ji uban wa?""" """Anty ce ta kira ni, dan Allah tashi mu je, wallahi ban yi mata komai ba"" tayi maganar tana wani" irin kuka. """Na ga alamar sai na taka wa 'yan gidan nan naku burki a kan zaƙewar da suke yi, ba Zamu je" "yanzu ba, sai da safe, zan je ni su yi mini bayani""" Ayshercool 08081012143 ₦500 ne via 0009450228 Aisha Adam jaiz bank sai shaidar biya ta 08081012143 90009343 'Yan Nijar ku turo katin airtel na 300fcfa Arewabooks ayshercool7724 "Cikin kuka ta ce ""Ni dai dan Allah ka tashi mu je, kar ayi mini wani sharrin ina zaune ban sani ba," "dan Allah ka tashi mu je""" """No ba in da zamu je, sai da safe idan Allah ya kaimu""" "Kuka ta din ga yi masa, har sai da ta ƙular da shi, ya daka mata tsawa, ya korata ɗaki, daga kuka" "kuma numfashi ya nemi ya tafi gaba ɗaya, sai da ya ɗaukkota ya fito da ita tsakar gida, ta kwanta ya din ga yi mata fifita." Kusan dai ba su yi baccin kirki ba. "Washegari da safe shikaɗai ya karya, hankalinta gaba ɗaya a tashe yake, ta kasa cin abinci, sai" wajen goma sannan ya ɗauketa suka tafi gidan. "Ita ta fara shiga gidan da sallama, ba kowa a tsakar gidan, duk sun tafi makaranta yaran gidan." "A ƙofar falon baba tayi sallama, ya amsa mata ta shiga ta tarar da shi a zaune yana dudduba wasu" takardu. """Waliyiyya, lafiya na ganki a yanzu menene?""" "Kawai ta je gabansa ta zauna tana kuka, hankali a tashe ya dafa kanta ya ce ""Menene? Wani abun" "ne ya haɗa ki da mijin naki? Wani abun yayi miki?""" Ta girgiza kai alamar a'a. "Mama ta shigo falon, tayi turus, ganin jauhar a gaban baba tana kuka." """Ikon Allah, sakinki yayi ne ko wani abun ne ya faru, ki ke wannan uban kukan haka?""" """Yana waje ma""" """Yana waje meyafaru?"" Gaba ɗaya ta kasa magana." "Ya kalli mama ya ce ""Tashi tijjani ko saifu, su je su ce masa ya shigo"" mama na fita, ya kalleta ya" "ce ""Gaya mini kafin ta dawo""" "Kasa magana ta yi, da ta buɗe baki za ta yi, sai haki." "Mama ta dawo ta zauna, mintuna kaɗan Al'amin ya shigo da sallama, sanye da baƙar jallabiya." "Cikin girmamawa ya gaida baba, amma mama ko kallo ba ta ishe shi ba." """Malam Al'amin, meyafaru da iyalin naka ne? Ko wani abun ne ya haɗa ku?""" "Ya girgiza kai ya ce ""A'a, lafiya ƙalau nake zaune da ita, dama na rakota mu zo mu ji ba'asin kiran wayar da aka yi mata ne jiya da daddare, da har ya hanata bacci. Bana son ace na yi wani abu na rashin kyautawa, amma zan iya cewa wannan zai iya zama zuwanta gidan nan na ƙarshe kuma" "bana buƙatar kowa ya je in da take, in dai har za a cigaba da tafiya a haka""." "Baba ya ce ""Duk me ya yi zafi haka? Baka faɗi meyafaru ba""" """Baba kwanaki yayarta ta zo ta dubata, a gidan na fita na bar su ma tare, na manta sunanta, amma wadda ta auri wanda za ta aura da, kwatsam jiya da daddare an kirata a waya, wai waccan ɗin an dawo da ita gida babu lafiya, tana ihu tana kiran sunanta wai ta yi mata asiri, kwana tayi tana" "wannan koke-koken ba ta bari mun yi baccin kirki ba, wane irin asiri ana zaune ƙalau?""" "Cikin tsananin ɓacin rai ya ce ""Zakiyyan ce ta kira ki, ta ce kin yi wa hafsan asiri?"" Ta jinjina" masa kai alamar eh. "Ya tashi ya fita tsakar gida, yana ƙwalawa zakiyya kira." "Mama tayi wani irin mugun murmushi, sannan ta maze ta cigaba da sallalami." "Tana mutsutsuka ido ta fito ta ce ""Lafiya ka ke yi mini wanan kiran, ka san jiya ba mu yi baccin" "kirki ba, saboda jikin hafsa""." """Yanzu kin kyauta, abun da ki ka yi?""" """Na me fa?""" """Ɗaukar waya ki kira jauhar, wai ta yi wa hafsa asiri, wannan wace irin magana ce?""" """Amma ai ba ƙarya nayi ba, tun da aka kawo ta sunanta kawai take kira ai""" "Ihun da hafsa take yi ne ya sanya, suka nufi ɗakin gaba ɗaya, ciki har da jauhar." "Sai fizge-fizge take yi, tana kiran sunan jauhar." "Jauhar ta ce ""Yaya gani nan, kin ganni menene"" tana jin muryar jauhar ta hau miƙa mata hannu." "Ta ƙarasa ta ce ""Gani menene, me ya same ki?""" """Jauhar, ji nake kamar na fita da gudu, ai ke na gaya miki abun da yake damuna, dan Allah ki gaya musu ko zasu yadda, Anty taƙi fahimta ta, ni a kashe auren nan na huta, bana son kuɗin, bana son auren. Wallahi jauhar an kai wata guda bana iya bacci saboda ɓacin rai kullum sai na sha maganin tari rabin kwalba, nake iya bacci." "Bani da nustuwa, babu walwala da kwanciyar hankali yaya zan yi ne? Ta mallake komai, ban ishe" "shi kallo ba, yanzu kuma ji nake kamar in fita da gudu, kamar ana yagar naman jikina"" tayi" maganar tana wani irin kuka mai tare da gunji. """Yaya hafsa magnin tari ki ke sha dan ki yi bacci, ai ni ba ki gaya mini ba, shaye-shaye fa ki ka" "fara kenan""" """Ni ki gaya musu a kashe auren nan, ba zan koma ba na gaji"" tayi maganar tana buge-buge. Babu" "kunya Al'amin ya tsallako, ya janye jauhar gefe, saboda kar tayi mata illa." "Asirin da zakiyya take gudun tonuwarsa, ya tonu kowa ya gani." "Baba ya girgiza kai ya ce ""Kowa ya sai rariya, ya san za ta zubar da ruwa, ki tsaya a nema mata" "magani, wannan abun da take yi babu lalallai wani asiri ne, wataƙila shaye-shayen da take yi ne""." """Haba ya zaka ce haka? Wannan surutan da take yi ba fa a hayyacinta take ba, balle a tabattar da" "abun da ta faɗa gaskiya ne""" "Al'amin ya ce ""Amma ki ka yadda ita take yi mata asiri, count her of this please, kar a ƙar sakata" "a wannan maganar""" "Baba ya ce ""Al'amin kama hannun matarka ku tafi, in sha Allah hakan ba zata sake faruwa ba""" "Jauhar kuwa kuka ta din ga yi wiwi, har da roƙon Al'amin ya bari ta zauna, amma ya ƙi ya ce sai" dai su tafi gida. "Saifu kuwa ya ce ""ba dai kuna murna kun cuci marainiya kun aura mata ɗan wiwi ba, kun aurawa" "taku mai kuɗi, ai ga reshe nan ya juye da mujiya""." "Jauhar har sai da ta ji haushin Al'amin, na hanata zama a wurin 'yar uwatta." "Aka rasa ainihin abun da yake damun hafsa, shaye-shaye ne? Sihirin ne ko aljanu aka kasa gane kanta, wasu lokutan babu magana abinci ma taƙi ci sai kuka, da daddare ta kasa bacci tayi ta" koke-koke tana ihu kamar mahaukaciya. "Iyaka Alhaji mu'azzam ya zo dubata, ya zube musu uban kuɗi ya tafi." "Jauhar ta samu admission a legal, ta fara karanta shari'a law, indabo ne ya bata scholarship, sauran" hidimar makaranta kuwa shi yake yi mata. "Har keken ɗinki, ya samo mata a irin wanda Indabo yake cewa zai rabawa mata goma, amma ace" "an bawa mata ɗari, ya ce ba zai bashi ba, sai idan ya yadda za a ɗauki hoton jauhar da keken a saka a social media." "Ya ce babu wanda ya isa ya ɗauki hoton matar sa, ya saka a social media, a kan wani keken ɗinki" kuma sai an bata. "Indabo ya ce wa Al'amin, ya saka yaron da ya ce a samowa aiki a abuja, an samu gurbin direba a wata babbar ma'aikata top 10 na Nigeria, tare da albashi mai tsoka ya ce ya kai takardunsa na" sakandare da aka ce yayi. "Guduma bakinsa ya ƙi rufuwa, saboda tsantsar farinciki da murna ta gaske, jin zai tafi Abuja aiki," "alhalin idan da wanda ya kamata ya tafi, shi oga kwata-kwatan ne." "Mahaifiyar Nura, sai da ta zo tun daga garin da take aure, ta zo ta yi wa Al'amin godiya, tare da" "jauhar, dan Nura duk ya bata labarin irin zaman da suke yi da su." "Jauhar ta mayar da hankali a kan karatu sosai, duk da a gefe guda tana yi wa Al'amin magiyar shi" ma ya koma makaranta. A kaso ɗari yanzu babu kaso arba'in na shaye-shaye da neman rigima da Al'amin yake yi. "Ya shiga ya fita, aka bawa unguwar su sabuwar transformer daga wurin indabo, lokacin da ta su ta lalace, a cewarsa 'yar madara ba ta son zafi." "Har burji aka yi wa unguwar aka gyara musu kwatocin layukansu, aka zuba musu burji a manyan" hanyoyin su. "Abu kamar wasa, sai 'yan unguwar suka fara girmama Al'amin, ganin cigaban da suke samu a dalilin sa, duk da wani abun Indabo ba a son ransa yake yi wa Al'amin ba, dan dai kawai ba shi da" yadda zai yi da shi ne. "Aka bashi kuɗin sa na garin tofa, na gonakin mahaifiyar sa, kuɗi ne masu yawa, ya yi wa jauhar gyaran gida sosai da sosai, ya canza mata wasu abubuwan, ya saka mata talabijin, dan ma tana" "hana shi yi mata wasu abubuwan, saboda kar kuɗin su ƙare a banza." "Ya buɗe wurin sayar da shayi, a can unguwar su, liti zai din ga kula da wurin, ko Abbu bai san ya buɗe wurin ba. Ta saka shi sun yi addu'a sosai a kan buɗe wurin." "Al'amin ya cewa jauhar tafiyar ggagawa ta kama shi zuwa Lagos, juyin duniya ya gaya mata me zai je yi, ya ce mata bakomai, zai je ya duba ne, idan da wani abun da zai iya sayowa ya zo ya" sayar a kano. "Kafin ya tafi, wasu irin mahaukatan karnuka ya ajiye a layin, su uku masu faɗan tsiya, malam" lawan ya tambayi dalilin ajiye wannan karnuka da suke barazana ga rayuwar su. """Tafiya zan yi, gadin mata ta za su yi mini""" """Amma banda abun ka, ai Allah ne zai kareta ba karnuka ba""" """Meyasa ka gina gida ka saka matrka a ciki, duk da ka san cewa Allah ne zai kare maka ita, ba ka" "bar ta a titi ba?"" Yayi shiru." """Kar ka sake shiga harkat da abun da nake yi na gaya maka""" "Ita kanta jauhar da fari ba ta ma san saboda ita aka ajiye su ba, ita kanta tsoronsu take ji, gashi sun" "san lokacin da take dawowa daga makaranta, a bakin titi take tarar da su, da sun ganta, sai biyu su shige gaba, ɗaya kuma yana bin ta a baya." "Sai da yayi kwanaki takwas a lagos, sai dai kullum su yi waya amma still bai gaya mata me ya je" yi ba. "Wurin shayin su liti kuwa, jauhar ita ce yin meatpie, cin-cin, dafaffen ƙwai ne, duk abun da ya samu yi take yi, a lokacin ana processing tafiyar Nura guduma bai tafi ba tukuna, shi yake zuwa ya ɗauka ya kai." "Ko ta tsiri yin awara bayan magariba ko wainar fulawa, ya ɗauka ya kai can wurin shayin," "kasancewar matasa na taruwa a wurin, sai dai ya kawo mata kuɗinta an saye." "Ta ce ""Nura ina yi maka murnar tafiyar nan, amma ta wani fannin ni aka yi wa""" "Ya ce ""Wallahi ni kaina na fara kewar ku, na san a can babu abinci mai daɗin naki""" "Tayi dariya ta ce ""Halinka ɗaya da yayan naka ai""." "Ranar da Al'amin ya dawo kuwa, ta sha tsaraba, har maƙwabta sai da suka samu." Ga kyakykyawar tarba da ya samu daga wurin Uwargida sarautar mata. "Hafsa kuwa haka nan aka sasanta, bayan ta ɗan samu sauƙi aka mayar da ita gidan Alhaji mu'azzam, sai dai ba a wani samu sauyi ba, a kan abubuwan da suke faruwa, a baya damuwa da take yi mata yawa ya sanya take shiga tashin hankali, amma tun da ta samu maganin damuwarta ta hanyar shan magunguna masu sanya bacci, sai ta yi overdose yadda za ta bugu sosai ta manta duk" wani abu da yake damunta. "Dawowar Al'amin ya zo da kuɗaɗe, kuma ya ƙi gaya mata yadda aka yi ya same su. Ba ta zargin" "sa, dan ta san ba ya taɓa kayan wani, duk abun da zai kai shi ga taɓa abun da ba nasa ba, ba ya ci." "Cikin ikon Allah, tun zuwan da suka yi tofa, hajiya take zuwa kawo musu ziyara, da wasu daga" dangin mahaifiyar Al'amin. "Ana ta shirin tafiyar guduma babban birnin tarayya, ya ce ya fasa ba zai je ba, mahaifiyar sa ta zo har gida ta gaya wa Al'amin, dan bai gaya wa Al'amin cewar ya fasa zuwan ba, mamansa ya je ya gaya wa." Mai unguwa yana ta barbaɗa an yi wa nura hanya zai tafi Abuja aiki. "Al'amin ya sa aka nemo masa Nura guduma, ya tambaye shi, menene dalilin sa na fasa tafiya." "Ya girgiza kai ya ce ""Bakomai""" """Ban gane babu komai ba, idan ka zauna a nan ɗin uwar me zaka ci ko ka yi, iyayenka na murna" "ka samu wurin da zaka rufawa kanka asiri ka ce ba zaka je ba, saboda me?""" """Babu komai""." "A fusace Al'amin""Zan fasa maka kai, ka buɗe baki ka yi mini bayani, meye dalilin da ya sanya" "lokaci ɗaya ka ce ka fasa tafiya? Duk yaran da suke ƙarƙashina babu wanda na ɗauka na zaɓa sai Kai ka watsa mini ƙasa a ido?""" Yayi shiru. """Ba magana nake yi maka ba""" """Yaya bakomai""" "Jauhar ta ce ""Master, ka kira shi indabon a waya, ko cire sunansa suka yi? Ko wani abun ne ya" "faru, tun da ai da murna yake yi zai tafi""." "Yana huci ya kira wayar indabo, yana ɗagawa ya ce ""Yaya aka yi Nura ya ce ya fasa tafiyar nan," "ko akwai matsala ne?""" "Indabo ya ce ""Shi zaka tambaya, su kusan bakwai ne, ranar juma'a za su tafi, a kai su wuraren da" "za su yi aiki, ni ban ma san ya fasa ɗin ba, P.A ne yake kula da shirin tafiyar su""." "Al'amin ya kashe wayarsa, ya ce ""Ba ka da wani dalili ko hujja, dan haka tafiya ranar juma'a """ Nura yayi shiru. """Ba magana nake yi maka ba?""" "Ya ce ""To in sha Allah """ "Bayan tafiyar sa, Jauhar ta ce ""Master da ka ƙara matsawa ka bincika, babu yadda za ayi ace da" "farko yana ɗokin tafiyar nan, lokaci ɗaya kuma ya ce ya fasa, anya babu lauje cikin naɗi?""" "Ya girgiza kai ya ce ""Iskanci ne kawai, maybe abokai suke ziga shi, idan ya tafi can zai zama busy" "sosai, ba zai samu isasshen lokacin yin rashin ji ba""." "Ta ce ""Eh to, zai iya yiwuwa Allah Ubangiji ya tsare shi, ya sa sanadin shiriyar kenan. To kai ma" "master a samo maka mana""" "Ya kalleta ya ce ""Wa?""" """Kai mana""" """Kema kin san ba zan yi ba""" "Ta ce ""Amma ai na ga ba ka raina sana'a komai ƙanƙantarta""" """Ba sana'ar na raina ba, ba zan ɗauki duk wani nau'i na rashin mutunci bane, kema kin sani""" """Haka ne kam, shiyasa nake mamakin yadda ka ke yi wa indabon nan, yake ƙyaleka, yadda suke" "wulaƙanta mutane wasu lokutan""" "Yayi murmushi ya ce ""Ni da shi wannan kar ta san kar ne ai""" """To ayi amfani da takardunka mana, a samo maka aikin""" "Ya ce ""Ni fa aikin ne ba na so, da zan yi da tun kan maigida dodo ya ware, da na yi, kuma uwa uba" "yanzu na ajiyeki, yaushe zan iya nesa da ke?""" "Ta kwantar da murya ta ce ""Master nema babu in da ba ya kai mutum, ka taimaka mana""" """Ba in da zani, ina maƙale da ke, ga wurin shayi Allah ya dafa mana, wurin bulo ma zamu buɗe," "indabo nake jira, shi zai sai injin bugawar""" """Ubangiji Allah ya taimaka ya dafa, idan Nura ya tafi, kai zaka din ga kai mini kayan sayarwa ta" "wurin shayin""" "Yayi dariya ya ce ""Ai idan ma cewa ki ka yi na sayar miki zan sayar madarata, balle kuma kaiwa" kawai. """Sannu mijin ta ce""" """Bakomai, normal ne"" suka cigaba da hira cikin nishaɗi." "Al'amin ya tattara Nura sai da ya tafi, Jauhar kuma haki ya addaba mata, wasu lokutan tana" "makaranta, za a kira Al'amin ace masa an kai ta Asibiti babu lafiya." "Sati ba ya zuwa ya shafe, asma ba ta tayar mata ba, kusan kullum suna hanyar asibiti, har ta fara" "tsoron kar ya fara gajiya. Sai dai sam ba ta ganin alamar gajiyawa, ko ƙosawa a tattare da shi." "Ga jiri ga haki, abinci ma gagararta ci yake yi, ga ciwon mara da ya sakata a gaba, period ɗin ya" ƙi zuwa sai kaɗan ta gani a phant. "S uka sake komawa Asibiti, aka tabattar da ƙarancin jini a tare da ita." "Likitan ya ce ""Zahra, kina cin abinci ki ƙoshi kuwa?""" "Ta ce ""Sosai ma, master yana ƙoƙari a wannan ɓangaren""" "Ya ce ""To ai ba kowane irin abinci ne ya dace da ke ba, kin manta rashin lafiyar da ki ka yi, da irin" "abincin da muka ce ki din ga ci""." "Juahar ta ce ""Wallahi Alhamdilillah, dai-dai gwargwado yana bani, duk abun da nake so, ko ba na" "so ma yana sayo mini""" "Al'amin ya ce ""Ka ga likita, da dai idan na sayo tana ci, amma yan, kwanakin nan, zaɓe-zaɓen" "abinci take yi, ba komai take ci ba""." "Likita ya ce ""Ayi gwajin ciki gaskiya""" "Jauhar ta ce ""Ai ka ce ayi mini allurar tsarin iyali, an yi mini kuma """ "Ya ce ""Guda nawa?""" """Ɗaya aka yi mini, an ce in dawo ta biyun, amma na ji an ce idan baka period ba ta sake ka ba, to" "period ɗin ma so yake ya zo, amma yaƙi zuwa sai wahalar da ni yake""" "Ya ce ""A nan asibitin aka gaya miki?""" "Ta ce ""A'a""" Yayi rubutu ya ce su je ayi scanning. "Suka je suka yi, suka dawo, ya karɓa ya duba, ya ce ""Ikon Allah, to akwai ciki, kuma jinin da" "yake zuba alamu ne na akwai tangarɗa da yiwuwar ya zube idan ba a ɗauki mataki ba""" "Al'amin ya rasa me zai yi, murna ko kuwa." """To amma likita kana ganin babu matsala, tun da kun ce kar ta ɗauki ciki, a nan kusa bai fi" "watanni biyar ba yanzu""" """Eh, zamu bar ta a ƙarƙashin kulawar mu, in Allah ya yarda babu matsala, yanzu haka ya fara" "alamun zai fita, tun da ta fara zubar da jini, dan haka muna buƙatar ta samu bedrest, na sati guda daga ci sai bacci, ban da aikin wahala""." "Cikin damuwa ta ce ""Ko a hankali ba zan yi ba""" """A'a ba zaki yi ba""" """Amma master ka san ba wanda zai zo ya zauna da ni yayi mini fa""" "Al'amin ya ce ""Ni zaman me nake yi?""" "Doctor Khalid ya ce ""Allah dai ya bar wannan ƙauna, sannan kai master kana ji na""" """A'a fa, wannan sunan ba kowa yake faɗa ba, kira ni da Al'amin ɗina""" "Yayi murmushi ya ce ""Bedrest ɗin da muka ba ta har da kai a ciki""" "Ya ce ""Kamar yaya kenan?""." "Doctor ya ce ""Ba zuwa turaka""" """Meye turaka?""" "Cikin jin kunya jauhar ta ce ""Idan mun je gida zan gaya maka""" """A'a ai ba sai kun je gida ba, bayani zan yi masa yana sane ai, babu kai ba ita zuwa mu ga abun da" "Allah zai yi, ba cikakken hutu ake so ta samu""" Al'amin yayi shiru yana kaɗa ƙafa. """Ina magana ka yi banza, idan ka na son babyn ya rayu lafiya kenan, ba tare da an samu matsala" "ba, idan kuma ka ƙi ba ruwana""" """Ai ni sai abun da Allah ya yi ne ban gane ba, nan da yaushe ka ke nufi ne?""" """Zuwa cikin yayi ƙwari mana""" """To"" ya amsa a taƙaice." "Doctor ya ce ""Ba ka yadda ba kenan?""" """Na yadda mana, sallame mu na mayar da ita gida, rana tana yi""" "Doctor Khalid yayi counseling ɗin su sosai, sannan suka tafi gida, Allah ya taimaketa a cikin hutu" suke a makaranta. "Sai dai ba a rufa sati da zuwan su Asibiti ba, laulayi ya saka jauhar a gaba, komai ta ci sai ta yi" "amansa, duk ta rame, har abun ya fara damun Al'amin, yake ganin kamar ɗaukar cikin da tayi da wuri ne, ya sanya take shan wahala har haka." "Babu tsammani Abbu ya zo gidansu da daddare, sun yi mamaki sosai da sosai." "Bayan sun karɓe shi ya ce ""Al'amin ina can ina jiranka, ka kai mini business plan, in ga abun da yakamata na taimaka maka, ashe ka zagaye ka je wurin kakarka ka karɓi kuɗi har ka buɗe wurin" "sayar da shayi""." """Eh, na san ko na rubuta, matarka ba zata bari ka bani ba""" "Jauhar ta ce ""Abbu dan Allah ka yi haƙuri, bai kamata a ƙi gaya maka ba, dan Allah ka yi haƙuri" "mun yi kuskure""" "Al'amin ya ce ""A'a ni ne ban gaya maka ba, ta ce a gaya maka na ce a'a, saboda ba na son matar" "nan ta din ga saka mini baki, a abun da ya shafe ni""" "Abbu ya girgiza kai ya ce ""Jauhar ba ki yi laifin komai ba, ni yabo da godiya na zo takanas na yi miki, rayuwar Al'amin ta canza sosai da sosai, fiye da yadda nake tsammani, da na san aure zai katange shi daga wasu laifuffukan da tuni na yi masa an wuce wurin. Allah ya saka miki da alkhairi. Duk da daga baya na samu labarin yadda aka yi, aka zo ga gaɓar aurenki da shi, amma ki ka yi haƙuri ki ka zauna da shi a yadda yake, ki ka din ga gwagwarmaya, a gaskiya ina ƙara yaba" "miki, Allah ya yi miki albarka ya sa ki gama da duniya lafiya""" "Jauhar ta ce ""Babu komai Abbu, da na yi watsi da shi nima, kamar yadda sauran al'umma suka yi," "da ba a samu Wannan nasarar ba""" """Haka ne, kai kuma"" yayi maganar yana kallon Al'amin." """Ka ji tsoron Allah, a zaman da ka ke yi da yarinyar nan, kana ganin duk wata masifa da kake ɗ aukkowa babu mai tsayuwa a kanka, sai ita sai abokan shashancin ka, kai kanka ka san yanzu rayuwarka ta canza ba kamar da ba. Duk rintsi duk wuya, ka rayu da yarinyar nan da mutuntawa da girmamawa, idan ka sake ka cutar da ita, ko wani abu mara daɗi ya faru da ita a dalilinka, to ni" "da kai sai dai kowa ya kama gabansa""." """A'a Abbu ba za ayi haka ba, yana iya ƙoƙarin sa, babu wani abu da yake yi mini ma na rashin kyautawa, ni yanzu roƙo ɗaya nake da shi Abbu, dan Allah ka janye maganar a dalilinsa a ka kashe ɗan uwansa, kuma ka saka baki a kan yayi haƙuri da batun ɗaukar fansar da zai yi a kan" "madakin nan, tun da ya fita sabgarsa ya zauna lafiya kwana biyu, hankalinmu a kwance""" "Aikuwa Al'amin ya haɗe rai, Abbu ya ce ""Ka ji abun da matarka ta ce, ka yi mata wannan alfarmar" "da ta nema, kuma nima na nema""" """Tom"" kawai ya faɗa a taƙaice." Abbu ya din ga saka musu albarka ya tashi ya fita. """Ban yi miki alƙawarin kawo ƙarshen gaba ta da madaki ba, har sai ranar da na tabattar na daina" "jin ɗanɗanon baƙin cikin, abun da ya yi mini""" "Cikin kwantar da murya ta ce ""To ka bi ta hanyar da ta dace ta shari'a, ba ta makami da illata" "junanku ba dan Allah""" """Ta in da aka hau, ta nan ake sauka"" ya bata amsa." "Ta fuskanci muddin tana son ganin ɓacin ransa, to tayi masa maganar madaki." "Washegari hafsa ta kirta a waya, ta ce ""Kwana biyu bana ganinki a online, ko ba data ne matar" "master?""" "Jauhar ta yi dariya ta ce ""Wallahi akwai data, kawai bana jin daɗi ne, wayar ma ba iya taɓa ta nake" "yi ba, ya jikinki kuwa?""" "Ta ce 'Hmmm jiki gani nan dai, ko dai ciki ne kin ce ba kya jin daɗi?""" "Tayi murmushi ta ce ""Ba wani ciki, jikin ne dai kawai""." """Bari zan wuce ta unguwar taku, sai na tsaya mu gaisa, me zan taho miki da shi?""" """Babu komai, ke dai Allah ya kawo ki lafiya""." "Bai fi awa biyu ba, sai ga hafsa, sai dai yanayin da jauhar ta ganta bai yi mata daɗi ba." """Yaya, wannan shigar fa kamar ba matar aure ba?" "Hafsa ta ce ""Taɓ, matar aure ai na ajiye aure a gefe, mafita nake nemawa kaina""" """Ban gane ba""" """Wanda yakamata na yi wa ya gani, bai damu da ni ba, ya haɗa kan matarsa da yaransa sun tafi dubai, sun bar ni ga kuɗi ga gida, nayi-nayi anty ta fahimce ni a raba auren nan, taƙi har tana nema" "tayi mini baki, zan cigaba da ba ta kuɗi, nima kuma zan nemawa kaina mafita""" """A'a yaya, wallahi gara ki kai ƙara hisba a kashe auren, da ki yi zina da aure, ko a sasanta ku ayi" "masa nasiha""." "Ta girgiza kai ta ce ""Mama tayi mini asiri, banda wanda matarsa take yi mini. Gaba ɗaya ba na gabansa, duk sai na yi maganinsu, daga nan har chadd ko zan tafi tsirara, su surayya ba zasu auru ba, kuma sai na kashe auren nan, ba zan iya ba. Kar ki damu da sai kin yi mini nasiha, dan ba zan ji ba wallahi. Kin ga bari na hanzarta zan je na karɓo kayan cajina a wurin wanda nake karɓa. Ke" "ni ko da mastern naki zaki haɗa ni ne, ya din ga bani kayan """ "Jauhar ta girgiza kai cikin matsananciyar damuwa ta ce ""Ki dai canza tunani yaya hafsa, ni master na yi nasara a kansa, da addu'a da haƙura, abun da yake yi ya kusa zama tarihi, ke ma da zaki yi ha" ƙu...... """Kin ga tafiyata jauhar, ga farfesun kifi nan da doya, ki samu ki ci, sai anjima""." "Abun duniya ya ishi jauhar, dan sai da ta zubar da hawaye, ta ɗauki waya ta kira Baba, suka gaisa ya tambayeta ya makaranta ya mijin naki, ta ce ""Lafiya ƙalau Baba, dama wani abu ne ya saka na" "kiraka""." """To waliyiyya, Allah ya sa lafiya""" """Baba dan Allah ka shiga lamarin auren yaya hafsa ka saka baki, kar abun da ba a so ya afku," "yanzu ta bar gidan nan ni dai ina jin tsoro, dan Allah baba ka saka baki""" """Waliyiyya kina ji na?""" """Eh baba""" """Duk Wanda ya ce ;zai haɗiyi gatari, sai ka sakar masa ƙota. Babu yadda ban yi ba, idan auren nan ba zai yiwu ba, a raba uwatta taƙi, na zauna da shi mijin, ya ce shi ba ta da cikakkiyar lafiya, kuma ba ta da kunya, uwatta ta tsaya a fuskanci menene matsalar, tun da ta saka son abun duniya a gabanta, amma taƙi. Ta ce wai asiri babar tijjani tayi mata, suna nan suka ta faɗace-faɗace, kuma" "na san duk hakkinki ne, ni na zubawa sarautar Allah ido""." """A'a baba, dan Allah kar ka ce haka, kada laifinsu ya shafeta, su matanka ne, ita kuma 'yar ka ce," "hafsa fa ta cigaba da ta'amalli da miyagun ƙwayoyi baba ka yi wani abu a kai""." "Ya girgiza kai ya ce ""Jauhar kenan, zan yi ki yi mata addu'a Allah ya shiryeta""" Suka yi sallama ta ajiye wayar cikin matsananciyar damuwa. "Al'amin ya dawo gidan yana mitar kwana biyu lambar guduma ba ta shiga sam, yana ta kiransa a" "kan idan an yi musu albashi, ya gaya turo da kuɗi a yi wa iyayensa sayayya, ya basu na neman albarka." "Amma shiru lambar ba ta shiga, ya kira P.A ya tambaye shi ya kasa samun sa. P.A ya ce masa suna" "nan ƙalau yana can yana aikinsa, yana zaton ko wayar ce ta samu matsala. Haka kawai Al'amin ya ji bai amince ba." Ayshercool 08081012143 ₦500 ne via 0009450228 Aisha Adam jaiz bank sai shaidar biya ta 08081012143 Wanda za su jira document 1K ne. 90009343 'Yan Nijar ku turo katin airtel na 300fcfa Arewabooks ayshercool7724 "Gaba ɗaya ya kasa samun nutsuwa sai da jauhar ta farga ta ce ""Master ya ne?""" """Na kasa samun Nura a waya""" "Ta ce ""Allah sarki, ɗan uwa nagari in sha Allah zaka same shi, maybe ko babu caji ne a wayar""" "Ya ce ""No, kusan sati fa kenan, na kira P.A ya ce mini suna nan lafiya, wataƙila wayarsa ce ta" "samu matsala, idan ma haka ne, ai ko wayar wani ya ara ya kira ni, tun da kusan kullum sai na yi waya da shi, na ja masa kunne""" "Jauhar ta ce ""Haka ne, amma ƙara masa kwana biyu mu gani""" "Jiki a sanyaye ya ce ""To shikenan""" "Al'amin ya hana jauhar duk wani aikin wahala, su halimatu ne ke zuwa ta yi guiding ɗin su, su yi" "mata snacks ɗin da ake kai wa wurin shayi, sai bead work da take yi tana daga zaune, shi ma faɗa yake yi yana mita." "Iya haƙuri da ɗaga ƙafa ta san yayi mata, dan yau sakata yayi a gaba yana mita, ba dan yana son" "cikin nan ba, da tuni ya daɗe da bin rariya shi ma." """Master"" ya ɗaga kai ya kalleta, ya haɗe rai." """Wai laifin me na yi ne?""" """Ni gaskiya na gaji, sai yaushe cikin zai gama ƙwari ne? Nima ai yakamata a duba lamarina""" "Murmushi ta yi, yadda yayi kicin-kicin, kamar wani ƙaramin yaro." """Lamba nawa ake so?"" Tayi maganar tana kashe masa ido." """Na gaji da lamba uku huɗu, lamba ɗaya nake so""" "Jauhar ta ce ""Baka damu da babyn nan ba ko?""" "Ya girgiza kai ya ce ""Wallahi na damu da shi, ina son abuna, amma ba shikaɗai yake buƙatar ya" "rayu ba, kuma ba shikaɗai yake buƙatar ki ba"" yayi maganar a marairaice." "Ta ɗan yi shiru tana nazarinsa, da gaskiyar sa, kusan kullum ba ta da lafiya, tana kallo wasu lokutan sai dai yayi zamansa a ɗakinsa, ya busa hayaƙi, dan kar ya takura mata, ko ya karya dokar" da aka saka saboda cikin. """Kin yi shiru fa""" "Dariya ta yi ta ce ""Subhanallah, master da shagwaɓa, lamari ya ɓaci, to lallaɓani""." """Ai lallaɓakin nake yi""" """Inyee dama ka iya shagwaɓa baka taɓa yi mini ba, yanzu da da safe zan ce ka yi mini mazewa" "zaka yi kana hararata. To daga yau mayar maka da fankarka zan yi, dama ta fara tsufa""." "Al'amin ya ce ""Zan yi zuciya fa""" "Ta ce ""To yi mana idan zaka iya, huta roro waken gizo yaƙi 'ya'ya"" tayi maganar tana jan dogon" hancinsa. """A'a ba zan yi ba ma""" Tayi murmushi tare da rungume shi. "Har suka kwanta tana lafiya, sai cikin dare ya farka ya ganta a zaune, ta takure wuri guda." """Madarata, ya aka yi ne?""" "Jauhar ta ce ""Bakomai, zafi ne ya dame ni""" """Zafi kuma? Ga fanka na yi?. Ko numfashin ne?""" "Ta ce ""A'a, lafiya ƙalau nake numfashina""" "Ya ce ""To ya aka yi na ganki a zaune?""" "Tausayinsa ya kamata, har istigfari take yi, ta gaji da ce masa ba ta da lafiya ba yau ba gobe." """Master ka kwanta dan Allah, na kasa baccin ne""" "Cikin damuwa ya ce ""Ka kwanta ka yi baccinka""" """A'a ban yadda ba, akwai matsala ne, gaya mini?""" """Marata ce take ciwo""" "Cikin tashin hankali ya ce ""Innalillahi wa Innalillahi raji'un, Allah ya sa ba zubewa zai yi ba, ya" "salam""" "Ta jingina da jikinsa ta ce ""Ciwon fa ba mai damu bane ba, ƙullewa tayi, na ji kwanciyar babu da" "ɗi, shiyasa na tashi zaune""" """Ko asibiti zamu je? Wallahi ina son cikin nan zahra, na kwaɗaitu da son ganin abun da zaki haifa" "mini, tun da muka rasa na farko, nake tunanin ko yaushe zamu kuma samu? Kuma mun samu wannan karon ma, zan yi dalilinsa, mu je asibiti kawai""." "Cikin sigar rarrashi ta ce ""Master, dan Allah kar ka ɗaga hankalinka, ba ciwo take yi mini ba, ƙ ullewa tayi ne sosai kuma na duba babu abun da yake fita. Ɗawainiyar da ka ke yi da ni ka da Allah ya gajiyar da kai, Ubangiji Allah ya nuna mini ka daina komai kan Allah ya kawo mana" "babynmu""" "Yayi ajiyar zuciya ya ɗora hannunsa a mararta ya ce ""Ba zan taɓa gajiya da duk wani abu da ya ji ɓance ki ba, ba alfahari nake yi miki ba, ɗan halak ne ni, kar ki taɓa sakawa ranki zan gaji, da ƙ arfin ikon Allah ba zan gaji ba, in sha Allah, ni dai duk abun da ki ka ji na ciwo ki gaya mini dan Allah, ina son kasancewa da ke da iya adadin abun da zaki haifa mini, mu yi rayuwa mai tsayi da daɗi. In sha Allah zan yi iya ƙoƙarina na zama uban kirki ga 'ya'yana, kuma miji abun alfahari" "gareki""" "Haka kurum ta ji jikinta yayi sanyi, da maganganun sa, ji take kamar akwai wani abu mai girma da" "zai faru da su, sai dai ba ta sani ba, na daɗi ne ko akasin haka." "Ta sake lafewa a jikinsa, tana jin tsananin buƙatuwar son cigaba da kasancewa da shi a cikin rayuwarta, ita wannan kulawar da yake yi mata, tana shafe dukkan sauran abubuwan da yake" aikatawa. "Zuwa da safe ta ji ƙwarin jikinta, har ta ce masa zata makaranta, da ƙyar ya amince, saboda tana" da test. "Har ta fito ya karɓi jakarta, ya ce shi zai kai ta, kar ta hau ɗan sahu, ayi ta gargada da ita." "Ya duba jakar ya ce ""Ina inhaler ki?""" "Ta ce ""Tana aljihun wandona""" """Meyasa ba zaki saka a jaka ba""" """Zai iya yiwuwa ciwon ya tayar mini, jakar tana nesa da ni, amma a wandona da na laluba zan ji" "ta""" """Allah ya baki ingantacciyar lafiya, ya rabaki da ciwon nan gaba ɗaya""" "Ta ce ""Amin bugun zuciyata""" "Ya ce ""Iyeeee?""" "Ta jinjina kai ta ce ""Eh mana""" """To bani da kuɗi dai, kayan abinci zan sayo mana, idan kuma na ɗauka na baki shikenan""" "Ta tsuke fuska ta ce ""Kai ba ayi maka abun arziki, da na yi maka kalamai, sai ka hau ce mini ba ka" "da kuɗi, me ka ke nufi""" "Al'amin ya ce ""Ai ke ɗin ce, wasu lokutan haka ki ke yi mini, bana sanin lokacin da ki ke sakawa" "na zazzage miki aljihuna""" "Jauhar ta tura baki ta ce ""Wannan kalaman wataran da kuɗi ba zaka ji su daga bakina ba""" "Take jikinsa yayi shock ya ce ""Ban da irin wannan wasan"" idonsa ya nuna ƙarara tsananin" fargabar rasata. "Ta basar da zancen, ya kaita makaranta." "Abu kamar wasa, sama da kwanaki biyar, Al'amin bai ji ɗuriyar Nura ba, bai kuma same shi a waya ba, dan haka ya wanke ƙafa ya tafi gidan indabo, kasancewar ba shi da shamaki da gidan," "babu mai tambayarsa wurin wa ya zo, ina za shi, kai tsaye ya shige." "Ofishin indabo na gidan ya tafi, kasancewar imdabon yana Abuja, cikin sa'a ya tarar da P.A." """Mai zamani, ya aka yi ne?""" """Na kasa samun Nura a waya""" """To ai ina zaton wayarsa ta samu matsala ne kamar yadda na gaya maka""" "Ya girgiza kai ya ce ""Ba zai yiwu ba, shirun yayi yawa. Ba zai yiwu na baku amanar yaro, garin da" "ba uwar sa babu ubansa na kasa samunsa a waya, kusan sati biyu, na zauna na yi shiru ba, ba zai yiwu ba, dole ka san duk yadda zaka yi ka haɗa ni da shi""" """Amma mai zamani ina nan yana Abuja, a ina zan iya haɗaka da shi?""" "Cikin ɗaga murya ya ce ""Ka kira indabon, duk yadda zai yi ya haɗani da shi""" P.A ya tsaya yana kallon sa. """Zaka yi abun da na ce, ko sai na saka maka ƙarfe?""" "Ya janyo waya ya kira Indabo, suka gama magana. Ya kalli Al'amin ya ce ""mun yi magana da" "honorable, ya ce in anjima zai aika a duba shi, yanzu suna meeting da shugaban ƙasa""." "Yayi ƙwafa ya juya zai fita, Abdul ya kawo kai shi ma ya shigo. Sai dai Abdul ya tsaya yana jiran Al'amin ya bashi hanya, wannan ce haɗuwar su ta biyu, kasancewar ba a ƙasar yake zaune ba, ya" fi sanin ɗayan wato Ja'afar. "Ala'amin bai tsaya jira ba, ya yi wa Abdul wata muguwar bangaza da kafaɗarsa, sai da ya dangana" da faɗuwa ƙasa. "A fusace ya miƙe zai bi bayansa, P.A da sauri ya tsare shi ya ce ""Kul, sai ya yi maka illa, ba" "mutunci ya cika ba wasu lokutan""" "A fusace Abdul ya ce ""Mahaukaci ne shi, baka ba ka ga irin bangazar da ya yi mini bane?""" """Yi haƙuri, ai duk abun da ka ga honorable yana bi a sannu, ka san ba ƙarami bane ba, yi haƙuri""." "Ya kalli P.A ya ce ""Babu ruwana za abun da yake bi a sannu, wallahi muka sake haɗuwa sai na" "koya masa hankali"" ya juya ya fasa yin abun da zai yi." "Har la'asar Al'amin yana kallon wayarsa, yana jiran kiran indabo, ya je wurin shayi, komai yana" "tafiya dai-dai, ya tafi gida." "Yayi jajjage ya feraye doya, ya dafa ruwa ya zuzzuba a flask, duk ya rage wa jauhar aiki." "Wayarsa ta fara ringing, ya ɗaga ya kara a kunnensa." "Muryar Nura yaji ƙasa-ƙasa ya ce ""Yaya""" """Kai Nura wani irin shirme ne zaka kashe waya, ko ta wani ba zaka ara ba ka kirani, ina ta tunanin" "meyafaru da kai?""" "Nura ya ce ""Ka yi haƙuri dan Allah""" """Ya ake ciki? Na ji muryarka wani iri?""" "Nura ya ja numfashi ya ce ""Zazzaɓi ne yake damuna, sun bani hutu ma, an kai ni asibiti an bani" "magunguna ma""" """Yasalam, kai daga zuwa garin mutane sai rashin lafiya, ko aikin ne da wahala?""" "Ya ce ""A'a""" """To Allah ya sauwwaƙe, zan cigaba da kiranka, idan ka ga babu hali, kawai ka dawo gida""" "Nura ya ce ""Godiya nake, Allah ya kiyaye ka ya ƙara tsawon zamaninka""" """Ka huta, ka kula sosai duk yadda ake ciki, ka sanar mini, ina fatan sun sallameka, dan na ga wata" "ya ƙare""" """Eh an bani kuɗi masu yawa ma, ka bani account number ɗinka, na sako maka abun da na samu," "amma a ciki a sayawa Antynmu turimin atamfa dan Allah, da ita da babata a sai musu iri ɗaya""" "Al'amin ya ce ""A'a, ta gode sosai, amma ba haka za ayi ba, ka ba wa maman abun da zaka bata, ka" "tallafawa babanka da wani abun ya sai kayan abinci""" "Nura ya ce ""Shikenan, tun da ka ce haka, amma dan Allah ka saya musu atamfa iri ɗaya da" "mamanmu, tana sonta sosai """ "Al'amin ya ce ""Zan duba na ga abun yi, ka kula da shan magani ka ji ko?""" """In sha Allah""" """Good boy, sai anjima"" ya kashe wayar, sai ya ji wata irin sa'aida a zuciyarsa jin muryar nura, dan" babu irin saƙe-saƙen da bai yi a kansa ba. "Da jauhar ta dawo, aikin gida ƙarashe ne, duk yayi, sai godiya take yi masa tana yi masa addu'a." "Jauhar tun da cikinta ya fara tasawa, da an buga gate, sai ta saka hijjabi tana ɓoyewa, wai kunya take ji." "Yayi ta yi mata dariya, ya ce ""Da ki ɓoye, da ki bar shi, ƙarewa haifarsa zaki yi ƙarshen kunya," "gara ma ki bar shi kowa ya gani""." "Cikin shagwaɓa ta ce ""Ni dai ka bari na ɓoye abuna""" "Ya ce ""Ai sai ki yi ta yi""" "Al'amin ya sha mamaki kuɗin da guduma ya turo masa, dubu ɗari da hamsin, wai a bawa babansa" "dubu ashirin kawai, sauran har da su oga liti da oga walid ya ce duk rarraba musu." "Al'amin ya ce ""Wai aikin direban ne aka baka wannan kuɗaɗen har haka?""." """Eh Oga, ka san birnin tarayya ne nan, kuɗi ba wahala suke yi musu ba, ka cigaba da yi mini" "addu'a, jikina ne babu daɗi""" "Al'amin bai matsa da bincike ba, ya ƙyale shi." "Jauhar ta yi mamaki da ya kawo mata atamfa, sai Nura ne ya turo da kuɗi a saya mata iri ɗaya da" mamansa. "A lokacin ta ƙara yadda da ƙani ya ɗauki Nura, da wani ne daban ya bata, cewa zai yi ba zata" saka ba. "Al'amin da kansa tare da rakiyar su Walid, suka je suka kaiwa mahaifiyar Nura, abun da ya aiko a" "bata, ta din ga murna tana yi wa Al'amin godiya tare da yi masa addu'ar gamawa da duniya lafiya." "Mai unguwa kuwa raina dubu ashirin ɗin nan yayi, a ganinsa tun da Nura ya tafi Abuja, dubunan" "ɗaruruwa zai aiko masa, ya fara zargin ko Al'amin ne ya rage kuɗin." "Ɓangaren Abbu kuwa, Abba ɗan wurin rahila, ya haɗa kai da abokai, suka fara yi wa Abbu sata," "da ƙaramar sata suke yi masa, wani ya gani ya kawar da kai, wani kuma ma bai san sun yi ba." "Sai dai a wannan karon, satar da suka yi masa ba ƙarama bace ba, dan har ya kai ga reporting wurin Jami'an tsaro, da fari rahila ta ɗauka abun mai sauƙi ne, dan ta na ta yi wa Abbu masifar a kan me zai tayi mata terere da ɗa dan ya ɗauki kuɗi, ai shi mai rufa masa asiri ne yayi masa" "nasiha, sai dai ta girgiza da ta ji ya saka 'yan sanda sun kama shi." "Tamkar za ta yi hauka, da ƙyar ya saka aka sake shi, ya ce sai dai ya bar masa gida ya koma gidan" "ubansa, nan ma ta ce sai dai ya zaɓa ko dai ya zauna da ita da yaranta ko kuma idan ya matsa su tafi gaba ɗaya, ya ce ta kwashe yaranta su tafi." "Sai da ta ga ba ta da sauran mafita, sannan ta koma lallaɓa shi, da ƙyar ya saukko." "Juahar tuni ta fara zuwa awo, dan yau shi ya rakata awon ma, a wurin scanning aka nuna masa yadda zuciyar jaririn take bugawa." "Gaba ɗaya ya rikice, bakinsa ya ƙi rufuwa, ya zubawa screen ɗin ido, yana ta washe baki yana" murmushin. "Jauhar ta ce ""Ni fa na gaji zan tashi""" "Ya ce ""Ɗan yi haƙuri, bari na ƙara ganinsa mana""" """Ka ga me? Me ake ganewa a nan, ni banda duhu ba na ganin komai""" "Al'amin ya kalleta ya ce ""Sautin bugun zuciyar ta sa ne nake ji har cikin raina""" "Sai da mai scanning ɗin ya yi dariya, aikuwa ta tashi zaune ta ce ""Ni na gaji, haka kurum, na" "fuskantar tun yanzu kafi son ɗan tayin nan, to ka matso ka saukko da ni""" "Ya miƙe ya saukko da ita daga kan gadon, ya ce ""Ki din ga motsawa a hankali, kar ki takura shi""." "Tayi murmushi ta ce ""Idan ban tafi da gudu ba, ka ce ba ni ba ce""" "Ya ce ""Yi haƙuri, ai dole na lallaɓaki"" suka je aka gama yi mata awo, suka tafi wani shago na kayan jarirai, suka fara sayayya, kasancewar an ce musu tun a wata shida, kan ciki yayi bakwai ake haɗa kayan haihuwa, saboda haihuwa za ta iya zuwar mata a wata bakwai, sannan ya tanadi" "kuɗi, dan ba a san ya haihuwar zata zo ba, ko ta haihu da kanta, ko kuma ayi mata tiyata." "Ta zo ta shirya kayan da suka sayo a wani ɓangare na wardrobe ɗin ta, kallon kayan kawai nishaɗ" i yake sakata. "Washegari da safe, yana falo yana kallon wrestling, ta fito daga ita sai wata rigarsa da ta saka shirt ce, tayi mata yawa nesa ba kusa ba, iya cinyarta ta tsaya, sai kanta tayi kalba guda biyar, ta sake su" ta fito tana miƙa tare da hamma. "Ya buɗe mata hannayen sa, yana murmushi, ta ƙarasa ta zauna a kan cinyarsa, ya rungumeta ya ce" """Sannu""" """Yauwwa. Ina kwana?""" """Lafiya ƙalau, ya jiki ya babyna?"" Yayi maganar yana shafa bayanta." "Ta ce ""Ni babyn ko wa?""" """Ƙatuwa da ke ke ce babyn, unborn dai""" "Boti ya hawo saman kujera, ya hawo jikin Jauhar, Al'amin ya kai hannu zai cillar da shi, ta riƙe shi" "tana dariya ta ce ""Master dan Allah ka bari magen nan ya huta, duk ya tsaneka saboda cin zalinsa da ka ke yi, akwai buƙatar na yi muku sulhu""" """Babu sulhu tsakanina da wannan abun""" "Ta ɗauki boti tana shafawa ta ce ""Boti ku daina faɗa da master dan Allah"" muzurun ya kawar da" "kansa gefe, Al'amin ya ƙwace shi ya ajiye shi a ƙasa, ya koma da baya yana kartar carfet ɗin yana yi masa kuka." "Jauhar ta din ga dariya, ta ce ""Wallahi daga kai har shi dariya ku ke bani""" "Al'amin ya lumshe ido ya buɗe, yana shafa cikinta ya ce ""Duk kin zama ƙazama, kalli kin daina kitso, ga wata uwar riga kin saka, wadda sai an saka irinki goma a ciki, ni ɗaga rigar na din ga" "kallon jaririna""" """Master kenan, ba zaka gane ba, ni kaina ba na son zama da kan nan a haka, amma da an fara yi" "mini kitso zafi yake yi mini, kayana kuma duk sun yi mini kaɗan, amma idan na saka rigar nan taka, balance nake yi a ciki""" "Ya kashingiɗa a jikin kujera, yana cigaba da kallonta, yana jin wani irin kusanci da shauƙin kasancewar sa da ita wuri ɗaya. Kullum yana ƙara girmama lamarin Ubangiji yadda ya ƙaddara kasancewar su tare, wanda idan ba ƙarfin ikon Allah ba, babu abun da zai haɗa shi da ita, har ya" nemi aurenta. To wa ma zai bashi auren yarinya irin jauhar a yadda yake. """Master ka san menene?""" Ya girgiza mata kai. """Na ji an ce akwai lokacin da ma'aurata kan gaji da juna, ko miji ya ji matarsa ta gundure shi, dan Allah idan Allah ya raya mu ka fara jin irin haka a kaina, dan Allah ka yi haƙuri kar ka canza mini, na saba da kai sosai da sosai. Ina jin daɗin yadda na samu mai tausayina wanda ya mayar da ni mutum, yake zama ya saurari damuwata. Dan Allah ko nan gaba ka samu wadda ta fini, ko na fara" "gundurarka kar ka yi mini wulaƙanci ko ka manta da ni dan Allah"" tayi maganar very serious." "Ya ƙura mata ido, yana mamakin maganganunta." """To ai ni ko yanzu kin gundureni, duk kin hana ni rashin ji na, na saba da rayuwata ta ɓalla ƙ" "arafa da hawa network duk kin hanani, zaman haƙuri kawai nake yi da ke, kin isheni""" "Wasa yake yi mata, kawai ya ga tana kuka." "A ɗan rikice ya ce ""Haba Madarata, ke yanzu idan aka ce miki zan yi miki abu makamancin haka zaki yadda? Ina sake maimaita miki ni ɗan halak ne bana manta alkhairi. A lokacin da kowa ya yasar da ni, yake yi mini kallon mara amfani a lokacin ki ka rungumeni a yadda nake, ki ka yi ya ɗawainiya da ni, ba tare da kin gaza kin ƙosa ba, bana fatan Allah ya nuna mini ranar da zance kin" "gundureni""" "Ta share hawayenta ta ce ""Ka san wani abu, kai diamond ne da mutane ba su farga da shi ba, suke" "maka kallon mara amfani. Sai yanzu da ƙyallinka da haskenka ya fito""" "Ya kwantar da kanta a ƙirjinsa yana murmushi ya ce ""Ke dai ki ke kallon hakan, ga al'umma na" "zama mara amfani, saboda ɗan daba ne ni""" """To ni dai kana da amfani a wurina""" "Yayi murmushi ya ce ""A ɓoye fa rigima kawai ki ke so ki yi na rarrasheki, to na ji sannu yi haƙ" "uri""" """Yauwwa mata da yawa ba ayi mus irin yadda ka ke yi mini ɗin nan, zuciyar zinare ce da kai" "master, kana da tausayi sosai da sosai"" ta kara kunnenta a ƙirjinsa ta ce ""Zuciyarka sai kiran" "sunana take""" "Al'amin ya ce ""Ni dai yi magana a hankali, na ji babyna yana motsi, kar kwanciyar da ki ka yi ce" "kika takura masa, tashi zaune""" "Ta ɗaga kai ta kalleshi ta ce ""Master, zaka dawo ka tarar da ni, ina 'yar gala-gala da cikin nan, duk" "sai nuna banbanci ka ke yi""" "Shi ma kallon fararen idanunta yake yi yana dariya, ya ce ""To breakfast fa, me zamu ci?"" Ta tashi zaune ta ce ""zan dafa maka wani abun, amma ni anty wasila nake jira, za ta kawo mini wainar" "gero""" "Ya tsuke fuska ya ce ""Roƙo ko?"" Ta ce ""A'a geron da ka kawo na ɗiba na bata tayi mini, idan ni" "na yi ba zan iya ci ba""" "Ya ce ""Ok""" "Har azahar yana gida, jauhar ta hana shi fita, sai azahar yayi shiri ya fita, saboda sallar azahar, yanzu jauhar ta daina fama da shi a kan yin salla a kan lokaci." "Sai ga anty lubabatu, ta zo maƙwabciyar su mai ba ta aikin bead a gida." """Oyoyo anty lubabatu, yau ke ce a gidan""." """Yau gani na lallaɓo, an ce mini kin kusa juyewa, na ce bari na zo ga ya kike""" "Jauhar ta ce ""Ohh ni zahra'au in ji wa? Ba a gaya miki daidai ba""" """Eh ba a gaya mini ba, ni na gani yanzu ai""" "Da sauri jauhar ta kalli cikinta ta ce ""Haba dai dan Allah a na gani"" Anty lubabatu ta kwashe da dariya ta ce ""Lallai yarinya, wannan uwar ƙibar da ki ka yi ma da haka ki ke? Kin zama uwar" "mata""" "Juahar ta yamutsa fuska ta ce ""Na yi muni ko?""" """A'a babu wani muni, wallahi kin yi kyau, kallo ɗaya mutum zai yi miki ya san a kwanciyar hankali ki ke. Jauhar gyaran gida aka yi miki haka, lokacin da na zo gidan nan kina amarya tsurar bulo ne fa, ikon Allah har da sola, wato a duniya idan Allah yana yinka ko wa ma yaƙi ka. Ga Alhaji mu'azzam can Allah ya bar su da shi, matarsa na ta gana wa hafsa azaba, abu har da 'yan sanda, ya ce idan ba zata zauna da matarsa lafiya ba tayi mata biyayya ta tafi gida. Gidanku kuma" "ana ta tashin hankali, Anty zakiyya ta ce mama ke yi mata asiri""" "Cikin damuwa jauhar ta girgiza kai ta ce ""Bari kawai Anty lubabatu, lamarin gidan nan namu sai" "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, kuma wasu lokutan har da laifin baba, kodayeke shi ma sun" "mayar da shi sai yadda suka yi da shi, ai da ni aka ce ina yi wa hafsan asiri. Ko gidan ya hanani zuwa, sai idan da daddare ya kaini na gaida baba na dawo gida""" """Allah ya taimake ki, ke da suka so su tozarta rayuwarki Allah ya rufa miki asiri, ɗan daban da" "suka aura miki dan ki wulaƙanta, hakan ba ta faru ba""" """Tababs babu abun da zan ce wa Allah sai godiya, Anty lubabatu mijina a maza ɗari irnsa ɗaya ne tak. Daba da shaye-shaye su ne ƙaddararsa amma, ya ci sunansa amintacce rauninsa mutane" "suke kallo, basa kallon nagartarsa"" sun daɗe suna hira sosai kafin ta tafi." "Kusan duk bayan kwana biyu zuwa uku, sai hajiya kakar Al'amin ta kira Jauhar ta yi mata ya jiki," dan tun wani zuwa da tayi ta fuskanci hakan. "Tun da ya fita da azahar har bayan magariba bai dawo ba, sai da ta kira shi a waya, ya ce mata" gashi nan. "Hnakali a tashe ya dawo mata, dan sai da gabanta ya faɗi ya ce ""Master lafiya?""" """Nura aka kawo daga Abuja, wai ba shi da lafiya, tun lokacin nan da ya ce mini ba shi da lafiya," "yake kwance""" "Ta ce ""Innalillahi wa Innalillahi raji'un, meya same shi haka?""" "Ya ce ""Ban sani ba, an dai kai shi asibiti, na je na ganshi a galabaice, yayi magana ya faɗi meyake damunsa ya ƙi, na ga a galabaice yake sosai, an saka masa ruwa da sauran abun da yakamata gobe" "in Allah ya kaimu dai zan koma""." "Jiki a sanyaye ta ce ""Allah sarki Nura, sai da ka ce idan ba zai iya ba ya dawo, wataƙila dan kar ka" "yi masa faɗa ne ya zauna bai dawo ba. Allah ya bashi lafiya""" Ya amsa da Amin. Ya ciro mata envelope ya ajiye mata. "Ta ce ""Menene wannan?""" "Ya ce ""Duba ki gani mana""" "Hotunasu ne shi da ita, wanda galibi a wayarta suka yi, ya kai aka ciro su, sai kuma ƙatuwar viva," "da aka yi frame ɗin hoton da suka yi na sallar eid ɗaya an rubuta musu happy marriage life, ɗaya kuma an rubuta first eid with habibi." "Tayi murmushi ta ce ""Kamat yayi a rubuta Master weds madara"" duk da a cikin damuwa yake sai" "da yayi murmushi, ya ce da safe zai kafe a falo." "Ta kalleshi tana murmushi, bai taɓa ce mata yana son ta ba, sai dai actions ɗin sa, yana tabattar mata da hakan. Da fari kai ba ka ce ya iya duk wani abu da yake da alaƙa da kulawa ba, saboda" "he's always serious, sai dai a hankali ainihin halayensa suke fitowa." "Jikin Nura yayi tsananta, kullum Al'amin cikin sintiri yake, jauhar ce mai lallaɓawa tayi musu girki, mahaifiyarsa ce take zaune da shi a asibiti tana kula da shi, gashi an rasa gane abun da yake damunsa, Al'amin har gona ya saka aka sayar masa a ƙauye, saboda kula da Nura, dan asibitin ku" ɗi ya saka aka mayar da shi. "Da daddare babar Nura ta fita, Al'amin ya zo, cikin ƙarfin hali ya ce wa Al'amin ""Yau ina Antyna" "ba ta zo ba?""" "Ya ce ""Eh, ni na hanata zuwa, tayi nauyi. Nura yakamata zuwa yanzu ka gaya mini menene yake" "damunka, ana ta kashe kuɗi an rasa gane abun da yake damunkaa yayi maganar cikin damuwa""" "Nura ya ce ""Idan na gaya maka ba zaka yi fushi da ni ba?""" """Ya za ayi na yi fushi da kai? Ka gaya mini in san ta in da zan kamo bakin zaren""." "Ya riƙe hannun Al'amin ya ce ""Na san ba lallai na rayu, amma ba ka da laifi ka taimaki rayuwata ne. Na gayawa mama na ce kar ta gaya maka. Lokacin da na ce maka na fasa tafiyar nan, Honorable ne ya ce sai ya yi ɗabi'ar mutanen annabi luɗ da ni, na ƙi yarda, ni kuma na kasa gaya maka, dan ya ce idan na gaya maka, kashe mai unguwa zai yi, amma idan na amince shikenan, ba wanda zai san an yi kuma zai bani aikin." "Na ɗauka daga haka shikenan, sai dai tun da ya tafi da mu, a wani gida aka ajiye mu, abun da suke yi mana kenan, yana da masu kula da mu, babu ta in da mutum zai gudu, kuma ba shikaɗai ne yake yi mana hakan ba, akwai wasu manyan mutane a ƙasar nan, da duk zan gaya maka sunayensu." "Kuma kamar tsafi suke yi ta hanyar amfani da mu, bana iya riƙe bayan gida, mama ce take gyara mini kafin mutane su zo dubiya, Indabo ya lalata mini rayuwa amma ka rufa mini asiri dan Allah," kuma kar ka zargi kanka! Ina da hujja mai ƙarfi da zan baka a kan haka! Ayshercool. 08081012143 ₦500 ne via 0009450228 Aisha Adam jaiz bank sai shaidar biya ta 08081012143 Wanda za su jira document 1K ne. 90009343 'Yan Nijar ku turo katin airtel na 300fcfa Arewabooks ayshercool7724 "Gaba ɗaya fuskar Al'amin ta sauya takmar ta horo, ta koma Al'amin ɗin sa na ainihi, tamkar bai taɓa sanin wani abu wai shi dariya ba. Wani irin gumi ya shiga tsatstsafo masa, jijiyoyin goshinsa zuwa kansa suka miƙe suka kukkumbura, idonsa yayi wani irin ja mai ban tsoro, bugun zuciyarsa ya ƙaru da saurin gaske, jikinsa ya fara ɗaukar wani irin zafi saboda tashin hankali da tsananin ɓ" acin rai. "Ba tare da tunanin halin da Nura yake ciki ba, yayi wa hannun guduma wani irin mugun riƙo, da" sai da ƙasusuwansa suka yi ƙara. "Nura ya ɗora ɗaya hannun a kan na Al'amin ya ce ""Yaya, kai ɗan uwa ne da Allah ya bani rana tsaka a titi, duk wannan abun ka yi ne dan inganta rayuwata, ba ka taɓa yin wani abu da zaka cuceni ba, na san da ka san abun da zai faru da ni kenan, ba zaka bari na je ba, dan Allah ka kwantar da hankalinka, ni na san ba zan rayu ba, abun da suka yi mini ya fi na kowa muni da tashin hankali, ban san yaya zan misalta maka ba, amma dan Allah kar ka yi yinƙurin yin wani abu, idan ba haka ba za su yi maka illa. Na bar su da Allah ka tayani Addu'a Allah ya yafe mini laifukana, idan na mutu dan Allah ka yi mini wanka kar asiri na ya tonu, ba na son a zargeka da abun da mutane ba su san menene ainihin abun da ya faru ba." "Wurin bayan gidana ya riga ya ɓaci, kowa ya gani zai gane meyafaru dan Allah kar wani ya je kan" "gawata idan ba kai ko mama ba""" "Al'amin ya riƙe hannun Nura gam, amma ya kasa magana sai wani irin numfashi mai haɗe da huci," ya sunkuyar da kai yana sauke numfashi. "Yanayin yadda mahaifiyar Nura ta tarar da Al'amin, ya sanya ta gane ya gaya masa." "Ta ƙarasa gaban gadon, jiki a sanyaye ta ce ""Al'amin, ka kwantar da hankalinka dan Allah, zan iya dafa Alqur'ani na rantse, ba zaka kai mini nura in da za a cutar da shi ba, na san da ka san me zai faru kenan ba zaka yadda ya je ba, a irin yadda yake bani labarin zamanka da shi. Iya ɗ awainiyar da ku ka din ga yi da mu kai da matarka ya ƙara tabattar mini da haka. Cuta ce an riga" "an cuce mu, amma mun bar wa Allah, ni ba zan zargeka ba""" "Ya saki hannun Nura a hankali, ya tashi ya juya ya fice." "Nura yayi ajiyar zuciya ya ce ""Allah ya sa kar ya ce zai ɗauki wani mataki, dan mutanen nan sun" "wuce duk yadda yake tunani, ni dai ku cigaba da yi mini addu'a da fatan cikawa da imani""" "Duk da juriya da mahaifiyar Nura take yi, sai da ta kasa ta zubar da hawaye, cike da karaya, dan magana kawai Nura yake yi, amma komai sai an yi masa, gashi buni-buni jininsa ya ƙone, sai an saka masa wani, dan bayan bayan gidan, har da jini ne yake zuba daga wurin, jini sosai ba kaɗan" "ba, a tunaninsa da na mahaifiyarsa ɓoye wa likitocin ainihin abun da ya faru shi ne rufin asirin su," "dan babu wanda zai fahimce su, cewa za a yi shi ya kai kansa, saboda kwaɗayi da son abun duniya," dan Nura ya yi girman da ya fi ƙarfin ace dole aka yi masa. "Ikon Allah ne kawai ya kai Al'amin gida, dan ko me za ayi masa bai san ya aka yi ya isa gidan ba." "Jauhar har ta yi bacci, dan 'yan kwanakin nan bacci take yi sosai da sosai, duk in da ta ji kwanciya" ta yi mata daɗi sai bacci. "Ba ta farka ba, sai bayan sha biyun dare, shi ma dan taji ta gaji da kwanciyar ne, a hankali ta tashi" "jikinta duk yayi tsami, ta kalli ƙofar ɗakin Al'amin, ta tashi ta nufi ɗakin, ta ɗaga labule ta shiga." "Yanayin kwanciyar da ya yi, ya tabattar mata da yayi shaye-shaye ya bugu, dan wata irin kwanciya" yayi. "Jiki a sanyaye ta ƙarasa gaban katifarsa ta zauna a hankali ta ce ""Haba master yau kuma?"" Dan bai fiye shan abun da zai gusar masa da hankali gaba ɗaya har haka ba, yana yi amma ba sosai ba, ya fi ganewa busa hayaƙi. Kuma kwanakin nan da Allah ya taimaketa tayi galaba a kansa, bai fiye shan abun buguwa ba sai shan sigari, wiwin ma ya rage shan ta sosai, amma ta zo ta tarar da shi a" wannan yanayin. "Da ƙyar tana haki, haka ta gyara masa ƙafarsa da hannunsa, ta shafi sumar kansa, sai wani irin gumi yake yi, naman fuskarsa yana ɗan yi rawa lokaci zuwa lokaci ga ajiyar zuciya da yake ta yi" a kai kai. "Ganin ba ya hayyacinsa, balle su yi magana, ya sanya ta tashi ta tafi ɗakinta, cikin zullumi da" tunanin me aka yi masa?. "Kiran sallar farko ya farka, sai dai zuciyarsa cike da tsananin baƙin ciki da ɓacin rai, ya san ko ya je gida ba zai samu indabo ba yana Abuja, kuma ba zai iya tafiya Abuja ba, cikin fargaba zai tafi" kar yana matsawa wani abun ya samu Nura. "Alwala yayi ya fice, a hanya yayi sallar asuba, ya ƙarasa Asibitin, maman nura na ta kokowar" "yadda zata ɗaga shi, ta saka masa pampers, yayi mata girma." "Al'amin ya bubbuga ƙofar, ta ce ""Waye?""" "Da ƙyar ya iya magana ya ce ""Al'amin ne""" "Nura ya ce ""Mama buɗe masa""" "Ta buɗe masa ya shigo, Nura ya gaida Al'amin, jinjina kai kawai yayi, suka gaisa da maman Nura," "da ƙyar yake iya magana, saboda tsananin ɓacin rai da tashin hankali." "Ya taimaka mata, suka canzawa Nura pampers, jinin da Al'amin ya gani a pampers ɗin ya ɗaga" "masa hankali, gaba ɗaya halittar duburar Nura ta fito waje, babu ƙyanƙyami babu komai, ya taimaka mata suka gyara shi, suka saka masa pampers uku, kamar yadda take saka masa, sai kuma ta kawo zannuwa ta tuttura masa ta toshe ko ina, ta fesa masa turare, ta kunna turaren wuta, ta" shiga banɗaki ta wanke kayan da aka cire mas. "Al'amin ya rasa me ma zai cewa Nura, abun duniya ya ishe shi, ya ji ya tsani kansa, komai baya yi" masa daɗi. "A hankali ya kalli Nura ya ce ""Zan gaya wa likitoci, su duba idan da abun da za a iya yi, ayi maka" "babu dabara a ɓoyewa likitoci wannan lamarin""" "Da sauri Nura ya ce ""Dan Allah kar ka yi mini haka, ka rufa mini asiri, wallahi babu wanda zai" "yadda dole aka yi mini, na san ba zan rayu ba, lokaci kawai nake jira, dan Allah yayana wannan ce alfarmar ƙarshe da zan nema a wurinka, dan Allah kar ka gaya wa kowa""" "Cikin matsananciyar damuwa Al'amin ya ce ""Nura ka yafe mini, wallahi ban san abun da zai faru" "ba kenan, na zata hakan zai taimaki rayuwarka ne... Sai ya kasa ƙarasawa muryarsa ta fara rawa." "Guduma ya ce ""Wallahi na sani, kai mutumin kirki ne yayana, dan Allah idan na mutu ku din ga yi mini addu'a, na san sauran jama'ar gari babu lallai su yi mini, saboda ban shuka alheri ba, amma na san kai zaka yi mini kai da mama, da Antynmu. Dan Allah idan ta haihu, idan namiji ne, ka" "saka masa Nuraddenni ka din ga tunawa da ni"" yayi maganar yana murmushi." "Al'amin ya haɗiye wani abu mai tsananin ɗaci, ya kalli Nura, amma ya kasa magana." "Nura ya sunkuyar da kai, yana share hawayen karaya." "Maman Nura ta fito ta gama wanke kayan Nura, muryar sa na fita a hankali, ya kalli maman Nura" "ya ce ""Me za a sayo muku ne? Da me zaku karya ba ta tashi ba na taho""" "Mama ta ce ""Kar ka damu Al'amin, ƙanwata suna nan tafe, da wuri za su zo, ai da ƙannensa ma su duba shi, baiwar Allah ai tana ƙoƙari Allah dai ya raba ta da cikin nan lafiya, ta sauka lafiya ƙ alau. Ai ta ce tuwon dawa zan yi mata, da miyar ɗanyar kuka da man shanu idan ta haihu, in sha" "Allah kuma ana ce mini ta sauka, zan dafo na taho kano, yajin daddawa ma ni zan yi mata""." "Nura ya ce ""Mama ni dai ki tayani roƙo, na ce a saka sunana idan an samu ɗan saurayi""" "Suna yin hirar ne, dan Al'amin ya kwantar da hankalinsa, sai dai fuskar nan tamau ya kasa yin" fara'ar. "Ƙarfe takwas da mintuna, wata yarinya ta shigo ɗakin, 'yar baƙa mai kyau, da siririn billenta, a" gefen fuskarta. "Babu ko sallama ta faɗo ɗakin ta ce ""Mama mun zo""" """Baki iya sallama ba ne?""" "Ta ce ""Assalamu alaikum, yaya wai da gaske ka je Abuja?"" Tayi maganar tana ƙarasawa gaban" gadonsa. "Nura ya ce ""Eh ramma, ya gida ya makaranta?""" "Ramma ta ce ""Lafiya ƙalau, yaya wai to ka ga shugaban ƙasa?"" Ya girgiza mata kai alamar a'a." """To idan ka koma zaka ganshi? Ka ce masa dan Allah a gina mana burtsatse, wurin ɗebo ruwa da" "nisa sosai""" "Ya shafa kanta ya ce ""To zan gaya masa, ina Sani?""" """Babanmu ya ce ba za a zo da shi ba, ya tafi makarantar Allo, nima da ƙyar ya bar na biyo innar" "su jafarun muka taho""." "Mama ta ce ""Ke baki iya gaisuwa ba, balle ki yi wa yayan naki yaya jiki ba?""" "Ta kalli Al'amin ta durƙusa ƙasa ta ce ""Ina wuni?""" "Ya jinjina mata kai kawai, ta ce ""Yaya sannu ya jiki?""" """Jiki da sauƙi Alhamdilillah""" """To Allah ya baka lafiya""" "Wata mace ce tayi sallama, tana faɗin ""Ke kuwa ramma an yi ƴar bantan uba, ina can ina bulayin" "in da aka kwantar da ku, kawai na nemeta na rasa shashasha ba zaki yi hankali ba""" "Ta zauna suka gaggaisa, Mama ta nuna mata Al'amin ta ce ""Atine ga uban gidan Nura, shi ya samo" "masa aikin nan, yake ta ɗawainiya da mu""" "Atine ta ce ""Allah sarki, ni wallahi kama yake yi mini da mai gyaɗa, yana kama da 'yar nan ta ta" "da ta rasu wadda tayi aure a birni, zahra'u"" da sauri Al'amin ya kalleta Mama ta ce ""Wallahi kuwa, mun yi waya da ita ma, ta ce zata zo duba Nura""." "Taɓ yana da alaƙa da Nura ne, ko kuwa kawai dai hasashe ne, ko abun su na mutanen ƙauye, da" "kowa ma ɗan uwan su ne? saboda tsabar miskilanci bai yi musu magana ba, ya tashi ya tafi." "Ya je gidansa ma, ya kasa kawai ya tafi ya samu wani kango, yayi zamansa, abun duniya ya ishe" "shi, bai ma san ta ina zai fara ba." "Bai koma gida ba sai can bayan la'asar sannan ya koma gida, ba ta ce masa uffan ba, tayi masa" "sannu da zuwa, ita babbar godiyarta ga Allah, dawowarsa lafiya, ba tare da wani abu ya faru da ita shi ba." "Sai dai ta haɗa abinci ta bashi, amma ta ga ya daɗe bai motsa ba, daga baya ya ɗauki cokali ya din ga tura abincin da ƙyar, kamar mai tura magani, ya gama ya nemi wuri ya kwanta bai ce mata" uffan ba. "Duk da yanayin hakan bai yi mata daɗi ba sam, amma ta daure ta ɗan bashi lokaci, amma taga a jere, kusan kwana uku, ba ya ce mata uffan, kuma kullum sai ta yi bacci zai dawo, da asubar fari kuma yake ficewa. Idam ya fitan nan, asibiti yake tafiya ya taimakawa babar Nura ta gyara masa" "jikinsa, sai dai kullum jikin nasa babu sauƙi." "Ranar na haɗu, da ya fito zai fita ta tare shi ta ce ""Master, wai dan Allah laifin me na yi maka har" "haka ne? Meyake faruwa yakamata ka sanar da ni""" "Ya ce ""Zan gaya miki idan na dawo"" daga haka ya fice ya bar ta." "Abun duniya ya ishi jauhar, ta kasa gane meyake faruwa haka yake ɓoye mata." "Yana zuwa asibiti ya tarar da mahaifiyar Nura a gefen gadon Nura, ta rufe shi, idanunta sun yi" jawur. "Cikin matsanancin tashin hankali ya ƙarasa gaban gadon, ya yaye zanin, ya tarar Nura ya cika." """Innalillahi wa Innalillahi raji'un"" ya furta cikin matsanancin tashin hankali, ya zauna yayi shiru shiru, ya kasa zubar da hawaye sai wani abu da yake yi masa zillo, tsakanin maƙogwaronsa da ƙ" irjinsa. "Ya saka gwiwoyinsa a ƙasa a gaban mahaifiyar Nura ya ce ""Ki yafe mini saboda girman Allah, ban taɓa tunanin abun da zai faru da Nura kenan ba, da na san haka zata kasance wallahi ba zan" "tura shi ba""" "Ta share hawayenta ta ce ""Wallahi na sani, kuma ni ban zargeka ba, Yanzu fatana Allah ya sa mutuwa hutu ce a gare shi, Allah ya yafe masa kai ma ɗawainiyar da ka yi da mu, Allah ya baka" "lada""." "Ya ɗauki waya ya sanar da su liti su samo mota, a asubar su zo a tafi da gawar Nura Allah ya yi" masa cikawa. "Sun girgiza sun kaɗu matuƙa da mutuwar Nura, da asubar aka tafi da gawarsa gidan mai unguwa, ta ce ita za ta yi wa Nura wanka, Al'amin ya tayata ya ce ban da su biyu, kar wanda ya je kan" gawarsa. "Mai unguwa ya din ga bala'i, yana yayi asara kuwa, ya rasa wanda zai gayyato kan gawarsa sai ɗ" an daba. "Maman Nura ta ce ""Ɗa na bai yi asara ba wallahi, kai ka yi asara, dan da ka kula da shi ka riƙe shi" "da mutunci da amana, ba zai faɗi haka ba. Kuma ba in da aka ce ɗan daba ɗan wuta ne, ko an haramta masa zuwa kan gawa""." "Haka suka yi wa Nura sutura, aka sanar da rasuwar sa." "Duk da ana ganin Nura baya ji, amma ya tara mutane, saboda daga baya duk wani aikin gayya na" cigaban unguwa da shi ake yi. "Sai ƙarfe goma na safe, Al'amin ya dawo gida, yana zullumin yadda zai gaya wa Jauhar mutuwar" "Nura, ga zuciyarsa da take wata irin tafasa take raya masa kashe Indabo ya huta da baƙin cikin da ya jefa shi a ciki." "Cikin matsananciyar damuwa ta ce ""Master wai meyake faruwa dan Allah?""" """Allah ya yi wa Nura rasuwa""" "Gaba ɗaya sai ta manta waye ma Nura, ta ce ""Waye kuma Nura?""" "Ya ce ""Guduma ɗan gidan mai unguwa"" kamar shashasha haka ta bishi da kallo, daga bisani wani irin jiri ya ɗebe ta, cikin azama ya riƙe ta, jikinta ya hau wata irin tsuma, ta saka hannu iya ƙarfin ta, ta toshe bakinta, dan hana kukan da yake ƙoƙarin taso mata fitowa amma ta kasa, iya ƙarfinta ta din ga maimaita ""Innalillahi wa Innalillahi raji'un, Innalillahi wa Innalillahi raji'un, Innalillahi" "wa Innalillahi raji'un. Allah ya sa ba Nuran da na sani ka ke faɗa ba""" "Jiki a sanyaye ya zauna da ita a jikinsa ya ce ""Ba kyau yi wa mamaci kuka fa kin sani, ki yi masa" "addu'a""" "Cikin kiɗimewa ta ce ""To me zan ce?""" """Ki ce Allah ya jiƙan Nura yayi masa rahama""" "Tari ta fara yi, ya ɗaga ta yana yi mata fifita, tare da yi mata sannu." "Sai da ya tabbatar ta ɗan samu nutsuwa, sannan ya riƙe hannunta, suka tafi gidan mai unguwa," "idanunta sun kumbura sun yi jawur, fuskarta ma tayi ja sosai da sosai." "Sai dai suna shiga ɗakin da mahaifiyar Nura take karɓar gaisuwa, suka tarar da hajiya a ciki a" "zaune, a kusa da Maman Nura." "Hajiya ta ce ""Al'amin, yanzu nake cewa zan kiraka na ga kamar unguwarku ce nan""" "Maman Nura ta ce ""Ai wannan ne ubn gidan nasa da ya ɗauke shi kamar ɗan uwa da nake gaya" "miki""" """To ai ɗan wurin Zahra'u ne, jikana ne""" """Iko sai Allah, Al'amin da kakarka da mahaifiyata uwar su ɗaya uban su ɗaya, Allah bai saka" "mun san juna ba""" "Ya zaunar da jauhar, ta zubawa mahaifiyar Nura ido, amma ta kasa magana sai sheshsheƙar kuka, maman Nura ta rungumeta tana ƙoƙarin rarrashinta, amma ta kasa sai suka cigaba da kukan tare gefe ga ramma da ƙaninta sani, da suke uwa ɗaya da Nura, suma su na ta kuka, hakan ya ƙara" karya zuciyar Al'amin. "Har aka gama zaman makoki, Al'amin yana cikin damuwa da tashin hankali, Hajiya da su ramma, a gidan Al'amin suke kwana, har zuwa kwana bakwai, sai dai kafin a gama zaman makoki, mai unguwa ya fara yada maganganu cewar Al'amin ne yayi silar mutuwar ɗan sa, Allah kaɗai ya san" "ina ya kai shi, idan abun gaskiya ne, meyasa shi bai je ba ya tura shi." "Kafin a ƙare zaman makokin, sai da maman Nura suka yi kaca-kaca da mai unguwa, ta ce Al'amin" "babu yadda za ayi ya kai shi in da za a cuce shi, idan ma haka ne, ai ɗan uwansa ne ba ruwansa." "Aka share zaman makoki, amma Al'amin ya kasa cigaba da walwala, tun jauhar na bin sa na" "tambayarsa ko lafiya? Ta yi rarrashin tayi ban bakin, har ta gaji ta zubawa sarautar Allah ido." "Zuciyar sa na ta azalzalarsa ya bi Indabo can Abujan, ya halaka shi kowa ma ya huta, amma ya" daure ya jira ya dawo. "Sai da Nura yayi sati uku, sannan aka gaya wa Al'amin Indabo ya dawo." "Gaba ɗaya baya cin abinci yadda yakamata, idan ya fita baya iya zuwa wurin sayar da shayi, sai ya samu wurin da babu wanda zai takura masa ya kwanta yayi ta tunani, ya din ga jin da ma bai san Nura ba a rayuwarsa gaba ɗaya da duk haka bata faru da shi ba, ashe duk abun nan ma suna" da alaƙa da juna. "Hatta jauhar yanzu ba ta iya samun kulawarsa yadda yakamata, dan ko in da take ya daina zuwa, ba ya dawo wa ma sai ta yi bacci." "Gashi ta shiga wata na bakwai, haki ya sakata a gaba, ga nauyin cikin ya fara damunta, da ƙyar" take iya tafiya. "Indabo yana zaune a falonsa, yana ganin mutane, ya ga Al'amin ya faɗo falon kamar daga sama." "Cikin sauri ya sallami waɗanda suke tare da shi, ya miƙe tsaye ya ce ""Mai zamani lafiya kuwa? Ya" "na ganka a haka?""" "Kafaɗar Indabo ya daka ya hantsila kan kujera, ""Me zamani distinguish senator kamar ni ka yi wa" "haka, dan na sakar maka na ba dama a kaina?""" """Zuwa na yi na gaya maka shukar da kayi tayi huda""." """Kamar yaya?""" "Al'amin ya kalle shi da jajayen idanunsa ya ce ""Ba na jin magana, amma wallahi ba na cin amana," "kuma duk wanda ya ci tawa sai ya biya. Nura guduma ya mutu, na karɓi saƙonka ka jira amsar da za ta biyo baya""." "Ras! Gaban indabo ya faɗi, dan ba haka suka tsara ba, ya aka yi ya san Nura ya mutu?." """Ban gane Nura ya mutu ba""" """Shut up! Ka sam komai, tsohon munafuki algungumi, na san komai, ka lalata rayuwar yaron da nayi niyyar ingantawa. An dawo da shi rai a hannun Allah, na san baka san ya aka yi aka dawo da shi gida ba, bayan ka shirya yayi hatsari idan ya tashi dawowa yadda zaka ɓatar da abun da ka aikata. Wallahi ka ci amanar Al'amin kuma sai ka biya." "Ba ka yi mamakin yadda nake yi maka biyayya ba na yi duk abun da ka ke so?, ka zata kawai saboda kana bani kuɗi ne? Bari na tuna maka ni yaron dodo ne, dodo babban sarki doodn da yake ɗauke da makamin tarwatsaka, ka zata ya mutu da sirrin nan a cikin sa ne? Wallahi ma'aruf na sanka fiye da yadda ka san kanka, a Nigeria ko wajen Nigeria wuraren da ka ke tafka tsiyatakunka." "Wallahi na buɗe bakina a kanka, ka gama kaɗewa bar ganin kana da rigar kariya, kuma ku ne ku ke juyar ƙasar, dodo ya mutu ya bar ni da babban kundun da zan iya rusa ku." "Niyyata idan na zo na kashe ka, sai dai hakan ba zai saka na huce ba, saboda yanzu ba irin da ba ne, na ajiye wanda suke buƙata ta. Akwai dabarun da masu kimiyyar lissafi suke bi, wurin yin solving wato BODMAS. Bracket Open, division, multiplication addition sannan subtraction. To ni upside down nake yi indabo, sai na fara division nake multiplication na yamutsa komai sannan na saka a bracket na rufe." "Ka rubuta ka ajiye daga yanzu, ni ne babbar barazanar rayuwarka" "Daga yanzu duk motsin da zaka yi, zaka yi shi a tsakanin tarkunan da zan saka maka, ka daina shan ruwa cikin kwanciyar hankali, ni ne magajin dodo kuma zaka biya cin amanar da ka yi mini""" ya juya ya fita yana huci. "Cikin tsananin tashin hankali, Indabo ya tashi, ya ɗauki wayarsa ya daddana, ya kara a kunnensa." "Cikin tashin hankali ya ce ""Ya aka yi Nura guduma ya bar gidan nan, garin yaya? Waye ya dawo" "da shi kano ban sani ba wane munafukin ne ya rusa mana plan?""" "Jifa yayi da wayar, ya hau safa da marwa, cikin tashin hankali ""Kenan kallon biri yake yi mini duk" "tsawon lokacin da muka yi tare? Amma Allah ya tsinkewa dodo albarka, ya ƙara tsine masa cin" "amanar da ya yi mana kenan?"" Ya kuma ɗaukko wata wayar ya kira P.A ya ce ""Maza ka ƙaraso" "gida ina nemanka""." Ya ajiye wayar ya cigaba da kaiwa yana komowa. "Afujajan P.A ya ƙaraso, ya ce ""Yallaɓai ya ake ciki ne, meyafaru na ganka cikin tashin hankali?""" """Dodo""" "P.A ya ce ""Me dodon yayi?""" """Dodo ya daɗe da kashe mu, kafin mu kawar da shi ashe ya gaya wa mai zamani komai? An dawo" "da yaron nan Nura kano, ya san komai, na yi waya wai an nemi obi an rasa, ya gudu yanzu ya san komai, na kaɗe idan yayi magana ya gama rusa ni, Allah ya tsinewa dodo albarka""" """Ka kwantar da hankalinka, honorable wai waye wani mai zamani, me aka yi aka yi shi ne? Mutum nawa ka kawar kan mu zo in da muke yanzu? Ba zai tayar mana da tarzoma ba, bayan" "mun yi nasara kawar da shi kawai zamu yi""" "Indabo ya ce ""Tayaya wannan yaron mai shegen taurin rai, da ƙarfin tsiya, ashe tsawon lokacin" "nan kallona kawai yake yi""" "P.A ya ce ""Kwantar da hankalinka akwai abun yi, zan yi maka bayani""." "Cikin dare jauhar na zaune tana lazumi, tayi sallar dare, ta ji shigowar Al'amin, ta ɗan jira wasu" "mintuna, sannan ta bi shi ɗakinsa." "Ƙwayoyi ta tarar da shi ya haɗa zai sha, cikin azama, ta durƙusa ta kwashe ƙwayoyin, ta dube shi ta ce ""Akwai abun da ka ke ɓoye mini master, ba iya mutuwar Nura ce take damunka ba, akwai" "wani abu a ƙasa ka gaya mini. Baka saba ta'amalli da ƙwayoyi haka ba""." Yayi shiru bai ce komai ba. """Master ka yi mini magana dan Allah ka gaya mini "" tayi maganar cikin matuƙar rauni." """Ki yi haƙuri ki je ki kwanta, dare yayi""" """Ka san kwana nawa nayi bana iya bacci, saboda damuwar da ka ke ciki? Kallonka kawai nake yi kar na takura maka ina jiran ka yi mini bayanin menene amma shiru, haba master ka gaya mini" "dan Allah""" "Ya juyo ya riƙe hannun jauhar, yana murzawa cikin matsananciyar damuwa, ya sunkuyar da kai ya" "ce ""Duk da abun a ɓoye ne, amma bai kamata na ɓoye miki ba, bai kamata na bar abun a raina nikaɗai ba""." Sai a lokacin ya gaya wa jauhar abun da ya faru. """Innalillahi wa Innalillahi raji'un"" tayi ta maimaitawa cikin matsanancin tashin hankali." """Master, ka ga irinta ko? Yana ɗaya daga abun da ya sa nake ta fatan ka nesanta kanka da mutumin nan, ya cucemu amma kansa ya yi wa. Baka yi da niyya ba, Allah ya jiƙan Nura ya saka" "masa""" "Al'amin ya kifa kansa a kan cinyar jauhar, sai a lokacin ya ji wasu irin hawaye suka zubo masa." """Sadik ya mutu a sanadina, Nura yayi wulaƙantacciyar mutuwa a dalilina, na zama annoba kenan? Mahaifiyar Nura har ta mutu ba zata manta, ni na kai yaron ta, in da ka yi dalilin gurɓata masa" "rayuwa ba""" "Jauhar ta girgiza kai ta ce ""Dan Allah ka daina faɗar haka master, kowa abun da Allah ya rubuta" "masa yake riska ba kaine sila ba"" tana kuka tana rarrashin sa." "Tun da Allah Nura ya mutu, Al'amin ya ƙara nutsuwa, babu abun da yake yi masa daɗi. Ita kanta jauhar ta kasa daina jin ɗacin rashin Nura, dan tun da Al'amin ya ce masa an samo masa aiki a Abuja yake murna, yake bata labarin shi wata yarinya ya gani yake so, kullum sai ya je ƙofar makarantar islamiyyar su idan an taso su ya ganta, yanzu yana fara aiki, idan ya ginawa mama" "gida a cikin kano, ta dawo sai ya nemi auren yarinyar, amma kar ta gaya wa master." "Take yi masa dariya ta ce masa ai mamansa aure take yi sai dai ya haɗo da mijinta, ya ce ya fasa" "zai yi aure ya ɗaukko ramma ta dawo cikin gari, ta baro ƙauye." "Ta ce ""Ban da abunku Nura haryanzu fa da sauran ƙuruciyarka, ɗawainiyar aure da yawa fa""." "Ya ce ""Ni dai kawai ki yi mini addu'a, da na dawo, zan fara zuwa wurin yarinyar nan zance""" "Da haka tayi ta tuna ire-iren hirarsu, da barkwancinsa, ta kasa mantawa da shi." "Al'amin har tofa ya sake zuwa, ya yi wa mahaifiyar Nura gaisuwa, ya kai mata abun alkhairi, ya" biya ya gaida Hajiya ya dawo gida. "Jauhar cikinta yayi girma sosai, kamar kana fita ka dawo zaka tarar ta haihu, ƙafafuwan ta duk suka kukkumbura, saboda girman cikin, aka ce yana shiga wata tara ayi inducing ɗin ta ta haihu ta" "huta, dan bayan nauyin cikin kullum cikin haki take, a haka kuma take lallaɓawa ta je makaranta." "Wurin shayin Al'amin kuwa, wasu irin kuɗi ne suke shiga suna fita, dan tun safe ake aikin ɗorawa" "da saukewa, ya zama chamber matasa sosai da sosai, duk da suna sayar da kayan shaye-shayen su a wurin, ba sa cutar Al'amin shi kuma ba ya yi musu mugunta." "Da safe su yi shayi, da rana indomie shayi, taliya haka suke wuni saye da sayarwar abinci." "Juahar sun gama haɗa kayan haihuwa, dan washegari ne ya kama ranar da za su je ayi mata" "inducing, tana ta jin tsoro yana kwantar mata da hankali." "Ta ce ""Master""" "Ya ce ""Mmm""" """Ka ji sai motsi yake yi, kamar ya san gobe in Allah ya kaimu za a fara inducing ɗin nan""" "Ya ce ""Ya ƙagu ya ga daddynsa, Nuradeenin daddy, in sha Allah sunan Nura zan saka, kamar" "yadda na yi masa alƙawari""." "Ta ce ""Allah ya jiƙan Yaya Nura ya sa ya huta""" "Ya ce ""Amin""." "Cikin shagwaɓa ta ce ""Amma a gabanka zan haihu master, tsoro nake ji, an ce haihuwa akwai" "wahala fa""" """Ba wata wahala in sha Allah, ina kusa da ke, ina yi miki addu'a zaki haihu, Ni zai fara gani kafin" "ya ganki "" yayi maganar yana sumbatar cikin nata." """Ni dai na fuskanci ba a so na, ta babynka kawai ka ke yi"" tayi maganar cikin shagwaɓa." """Ni na isa? Dukkanku ina sonku madarata""" """Ba wani, ni baka taɓa cewa kana so na ba""." "Yayi murmushi ya ce ""Amma kina gani a aikace ai""." """Baka taɓa faɗa ba""" "Yayi dariya ya ce ""Ai ke da ruwan zinari aka rubuta sunanki a zuciyata. Ina sonki madarata, ina ƙ" "aunarki ƙauna mai tsanani ya fi ubban shadidan""" "Ta ce ""Wayyo Allah daɗi. Wallahi har cikin tsakiyar zuciyata na ji kalaman nan, ba ka taɓa gaya" "mini ba, ka cigaba da gaya mini, da daɗi""" "Ya ƙara rungumeta ya ce ""I love you madarata""" """I love you too babyna, kuma baban babyna, masterna abun ƙaunata""" "Har mamakin irin kalaman soyayyar da suka din ga musaya take yi, da ba ta taɓa tsammanin jin su" daga bakin mastern ba. "Cikin matsanancin shauƙin so da ƙauna, suka kasance cikin farin ciki. Suka yi wanka, ya" rungumota daga toilet tana takawa a hankali da ƙaton cikinta a gaba. "Ya taimaka mata, ta saka rigar bacci, sannan suka kwanta, ta kwanta a jikinsa, tayi balance da ta" motsa sai yayi mata sannu. Wani irin nannauyan bacci ne yayi awon gaba da ita. "Ji tayi kamar ana kokowa a falo, ta laluba ba ta ga Al'amin ba, ga wani irin ƙaurin taba ya cika ko" ina. "Hasken fitila ta hango an kunna ƙwan falo, ta saukko ta fito falon tayi arba da wasu matasa" "hannunsu riƙe da miyagun makamai, madaki ta fara ganewa gabanta ya faɗi." "Sun rirriƙe Al'amin, suna shaƙa masa wani abu, jikinsa ya saki yana ta layi." "Madaki ya bushe da dariya ya ce ""Ka ce baka ji, dama ka ce da ni da kai sai wani ya kawo ƙ arshen wani, to ni zan kawo naka ƙarshen yau ina dodon da kake taƙama da shi? Duk da zuwan ba nawa bane ba, na uban gidanka ne Indabo, amma ya jaddada mini in tabattar ka tafi da wani" "mugun miki a zuciyarka""." "Cikin tashin hankali jauhar ta janyo jikinta ta nufi in da Al'amin yake tana kiran sunan sa ""Al'amin" "me ka yi musu ne? Dan Allah ku yi haƙuri mana""." "Al'amin ko harshensa ya kasa motsawa, balle wata gaɓa ta jikinsa." "Madaki ya riƙo gashin jauhar, ya kalleta ya ce ""Yanzu kin zama ragowa, ni kuma ba zan ɗana" "abun da yake ragowar maƙiyina ba, gashi kin zama cuus"" ta riƙe ƙasan gashinta da Madaki ya riƙ e." "Cike da mugunta, ya saka ƙafa ya kawashe na jauhar ta gaba ya saketa, ta faɗi a kan cikinta, ta ƙ wala wata irin razananiyar ƙara ta ce ""Ya Allah, Ya Allah, Ya Allah"" ta faɗa sau uku, take jini ya fara malala daga jikinta, harshen ta kawai take motsawa a hankali tana kiran sunan Allah, ta din ga ɗaga hannunta tana son kiran sunan Al'amin. Ya ƙura mata ido yana kallon ta, cikin buguwa da" "mutuwar jiki, tun tana ƙoƙarin magana a hankali har ta daina motsi." "Madaki ya samu wani ƙarfe ya bugawa Al'amin a ka, shi ma suka sake shi a wurin." Ayshercool 08081012143. ₦500 ne via 0009450228 Aisha Adam jaiz bank sai shaidar biya ta 08081012143 Wanda za su jira document 1K ne. 90009343 'Yan Nijar ku turo katin airtel na 300fcfa Arewabooks ayshercool7724 "Wayar Walid ce ta fara ringing, yayi shiru ya cirota daga aljihunsa ya kara a kunnensa ya ce ""Ya" "aka yi?""" """Oga walid ka yi sauri ka dawo dan Allah, ya fara dawowa hayyacinsa, kar ya dawo gaba ɗaya ka" "san ba zan iya da shi ba""." "Walid ya ce ""Gani nan, ka yi iya ƙoƙarinka, kar ka kuskura ya fita, idan ya fita akwai ƙura ka sani, gani nan zuwa"" ya katse wayar ya sakata aljihunsa, ya kalli matasan ya ce ""Ku mayar da ita kawai"" ya juya zai tafi." "Cikin azama Nabila da idanunta suka yi ja saboda kuka ta ce ""Dan girman Allah ka yi haƙuri, kar ka tafi, ka ƙarasa mini labarin nan, yaya aka yi Viper ya tafi prsion? Shi aka ɗorawa kisan matarsa? Ta mutu ne ma ko kuwa yaya aka yi, ya kuma aka yi ya fito yanzu? Ni abubuwa da yawa ban gama fahimtar su ba, sun cukurkuɗe mini sun shige mini duhu, dan Allah kar ka tafi baka ƙ" "arasa mini ba""" "Walid ya ce ""Ba zan ƙarasa ba ɗin, ba dai ke mara mutunci ba, na ɗauka haɗuwarki da shi, zai zama alkhairi amma ki ka yi mana halinku na mata, laifina ne da na kawo masa ke, Al'amin ya daɗ e da cire mata a rayuwarsa, sai zuwan jauhar cikin rayuwarsa daga kawo ki a tashin farko kin mayar mana da hannun agogo baya, Viper ba zai taɓa zama ya bar liti a tsare ba, saboda shi ɗan" "halak ne""" "Cikin matsananciyar damuwa ta ce ""Na ji, na yi kuskure amma dan Allah ka yi haƙuri ka ƙarasa" "mini""" """Ba zan ƙarasa ba, ki je shi ya ƙarasa miki""" "Cikin hanzari ta sake tarar Walid ta ce ""Dan Allah ka sake yi mini jagora, ka kai ni wurinsa na nemi afuwarsa, na yi kuskure kaina ne ya riga ya gama kullewa na faɗawa lamuran a gaggauce" "cikin duhun kai, amma a shirye nake na gayara kuskuren da nayi""" "Walid ya ƙare mata kallo ya ce ""Kin riga kin aikata abun da ba zai gyaru ba, kuma kar ki sake yin" "gangancin zuwa in da yake, idan ba haka ba, ko bai kashe ki ba ni zan kashe ki. Ku ɓatar da ita daga gabana""." "Suka saka Nabila a gaba, suka tasa ƙeyarta zuwa cikin napep ɗin da suka kawota, tana ta kallon" "walid tana yi masa magiya, amma suka ja babur ɗin suka tafi da ita." "Suka mayar da ita hanyar law firm ɗin su, suka bata wayarta suka tafi, wani abun hawan ta tare, ta nufi gida, zuciyarta sai bugawa dake da sauri da sauri, cikin matsananciyar damuwa da tashin hankali, ga matsanancin tausayin Al'amin da ya mamaye zuciyarta, lallai an yi wa rayuwarsa" yankan ƙauna mafi munin da har ya mutu ba zai manta da shi ba. "A falo magajiya take ce mata sumayya ta zo har gida tana nemanta, duk an kira layukanta ba sa" "shiga, ko akwai matsala ne, gashi yau ta daɗe sosai ba ta dawo ba." "Ai har baba magajiya ta gama maganarta, ba ta fuskanci komai ba, ta tafi ɗakinta ta rufe ƙofa, wayarta na ta ringing ta duba, missed calls ɗin sumayya sun fi ashirin, ga na Nasir, ban da barrister Habib, ta kashe wayar, ta cillata kan gado, ta shiga banɗaki tayi alwala ta fito ta yi sallar" azahar da la'asar. "A kan daddumar ma haɗa kai da gwiwa ta yi, ta din ga kuka, za ta iya cewa tun da ta buɗe ido a" "duniya, ba ta ji labari mai ban tausayi da tsayawa a zuciya ba kamar na Al'amin." """Why Nabila kin yi garaje, why would you judge the book, according to cover? Why?"" Ta tambayi" kanta cikin tsananin takaicin abun da ta aikata. "Ta kifa kanta a kan gadonta, wani abu tsananin ɗaci yana yi mata zafi a tsakanin ƙirjinta. Gaba ɗ" "aya ta ji ta tsani kanta, wani mugun haushin kanta ya isheta." """Ko yaya yake ji a zuciyarsa yanzu? Dole ya zama bugagge gaba ɗaya, amma idan aka bar shi ya cigaba a haka, to tabbas zai haukace, amma yanzu yaya za ayi na samu ƙarashen labarin nan? Ta haihun ko mutuwa tayi, kuma wa ya kashe aka kai shi prison? Wait, to yaya ma aka yi aka sake shi daga prison ɗin, yana yawonsa idan ya ga dama har ya je yayi ɓarna, kuma still a haka wai nansa ake yi. Wai wannan wane irin lamari ne mai sarƙaƙiya haka? Kar na je na haukace a banza mana""" tayi maganar kamar za ta haukace ɗin. "Ta cigaba da sintiri, tana ƙirga yatsunta, tana lissafi." """Kai dole na samo ƙarashen labarin nan, ko da kuwa me zai yi mini, ko dai wanda ya fara ya ƙ arasa mini, ko kuma shi Vipern ya ƙarasa mini, no matter how and what it takes sai na ji ƙarshen labarin nan, kuma sai na yi wani abu a kai. Haba dan Allah What a pitful life of his? Kai, to ita meye nata ma da za ayi mata haka? Me ta yi she don't deserve this at all"" tayi maganar tana" fashewa da kuka iya ƙarfinta. "Bugun ƙofar ɗakinta ake yi, amma ko gezau, da ta gaji da jin bugun ma, sai ta tashi ta tafi banɗ" "aki, ta rufe ƙofa ta kunna fanfo, ta cigaba da kuka da tunani." "Ƙarfe takwas na dare Abba ya dawo gida, Nabila ya fara tambaya tana ina, Mama ta yamutsa baki" "ta ce ""Ta dawo""" "Ya jinjina kai, ya tafi sashensa, har ya fara cin abincin dare, ya ajiye cokalin ya kalli mama ya ce" """Kirawo mini ita, ina ga ba ta san na dawo ba""" "Haushi ya ƙule mama, ta tashi ta fita, ta je ɗakin Nabila, ta tarar da ƙofarta a rufe, ta din ga" "jijjiga ƙofar tana bugawa, amma ba ta buɗe ba." "Magajiya ta ce ""Hajiya tun da ta dawo fa ta rufe kanta a ɗaki, taƙi buɗe wa, ba yadda ban yi ba ta" "ƙi buɗewa""" "Mama ta yi tsaki, ta koma ta ce wa Abba, ""To ka ji tun da ta dawo, ta rufe ƙofa taƙi buɗewa""" """Kuma lafiyarta ƙalau?""" """Ƙalau take, tsagwaron iskanci ne""" "Ya girgiza kai ya ce ""No, ko an ɓata mata rai ne, a wurin aiki ko a gida, ƙyaleta na ganta da safe na ji menene, ko kuma rigimar ce ta motsa"" yayi maganar yana murmushi. Wani malolon takaici," "ya ƙule mama, yadda yake lallaɓa Nabila, yana bin ta kamar wata uwarsa." *** "Abdul kuwa ganin ramma taƙi mayar da hankali ta ci abinci, hakan ba ƙaramin ƙular da shi yayi ba." "Ita kuwa jikinta ne babu daɗi, ga kewar gidansu, tana tunanin mama, ga baƙin cikin abun da yake" "aikata mata, gashi ya sakata a gaba duk sai ta kasa cin abincin." "Tana cikin zancen zuci, ta ji hannunsa a kan fusarta, ta tsorata ta ja da baya, ya tsuke fuska ya ce" """Meye haka ne?"" Ya buɗe idonta, ya ga she's still pale." """Solomon"" ya ƙwalawa kukunsa kira." "Solomon ya fito tare da cewa ""Yes sir""" """Kana da kayan miya ko?""" Solomon ya jinjina kai alamar eh. """Kawo mini tumaturi manya guda uku, da wuƙa ka haɗo mini da Apple ja guda biyu""" "Ya ce ""Ok sir"" ya cigaba da kallon ramma, da ta ajiye cokalin, ta hau jan rigarsa da take jikinta," tana rufe ƙafafuwanta. "Mintuna kaɗan solomon ya dawo, da plate biyu, ɗaya ɗauke da tumatir, ɗaya kuma Apple sai ƙ" aramar wuƙa guda ɗaya. "Ya karɓa, ya matsa kusa da ita, ya ɗora ƙafarsa ɗaya a kan cinyoyinta, ta ɗago cikin rauni" "idanunta sun tara hawayen takaici, ya yanka tumatirin ya miƙo mata. Ta tsaya tana kallonsa tana kallon tumaturin." "Miƙa mata yayi bakinta, ta kawar da kanta ta ce ""Ni ba zan iya cin tumatur a haka ba""" """Zaki karɓa ko sai na burma miki wuƙar nan a ciki?"" Yayi mata maganar cikin tsawa. A tsorace ta" "buɗe baki, ya din ga bata tumaturin nan, tana taunawa da kyar." "A zatonta zai bata tuffar, ta washe bakinta da ta ci tumatur, amma ya hau yanka tuffar yana ci," "yana yi mata tauna a fuska, yana kallonta ga ƙafarsa a kan cinyoyinta da tayi musu nauyi." "Ya gama cin Apple ɗin sa, ya taɓa wuyanta ya ji babu zazzaɓi, ya ce ""Haryanzu kina zubar da jinin ne sosai?"" Tayi masa banza kamar ba da ita yake ba, ya harzuƙa ya ɗaga hannu zai kwaɗa" "mata mari, ya ga ba ta motsa ba, sai hawaye da yake bin kuncinta." "Ya janye ƙafarsa daga kan cinyarta, ya ce ""Ki cigaba da ina yi miki magana kina kallona, ki yi" "mini banza kashe ki zan yi a banza"" tayi shiru ba ta tanka masa ba." "Jin ana knocking ɗin ƙofar falon, ya sanya ya tashi tsaye, ya ce ""Tashi ki tafi ɗaki, za a shigo""." "Ga mamakinsa ko gezau ba ta yi ba, ta cigaba da zama tana zubar da hawaye." "Zuba mata ido yayi, cike da tsananin mamakin shegen taurin kai a wurin kucakar 'yar ƙauyen" yarinyar. "Tashi tsaye yayi, ya fizgi hannunta, amma ta faɗi a wurin, saboda dama jikin babu ƙwari, ga jiri" tana ta fama. "Ya durƙusa ya ɗauke ta, ya nufi bedroom ɗin da ita, a bakin ƙofa ya dungurar da ita ta ciki, ya ja" "ƙofar ya rufe, ya koma ya buɗe ƙofar falon." "Wata matashiyar budurwa ce a tsaye, sanye cikin doguwar rigar material, sai hula a kanta," hannunta riƙe da Jakarta. """Ko wata ce a ciki ne? Ina ta bugu amma baka buɗe ba?"" Bai yi magana ba, ya bata hanya, ta shigo ta ajiye jakarta ta nemi wuri za ta zauna ta ce ""Abdul, staining ɗin jini nake gani a kan" "kujerar nan""" "Cikin ko in kula ya ce ""And so?""" """Mace ka kawo gidan nan?""" """Eh, akwai magana ne?""" "Cikin takaici ta ce ""Abdul don't try me, ka sanni ka san halina, ba zai yiwu nayi dumping guys ɗ" "ina just because of you ba, and ka din ga rough play da ni ba""" "Yayi murmushi ya ce ""Nina, ki na da matsala, saif ne ya yanke hannu da wuƙa, yana cin Apple, yayi bleeding sosai, amma ba abun da ki ke tunani bane ba"" tayi ajiyar zuciya ta ce ""Yauwwa ko" "kai fa, har hankalina ya tashi, i so much miss you"" tayi maganar tana rungume shi." "Gaba ɗaya sai ya ji banbarakwai, kamar ranar ya fara rungumeta, haka ya lallaɓata suka tafi ɗaya ɗakin sheƙe ayarsu, sai dai hankalinsa na kan ramma, kuma gaba ɗaya ya ji bai samu abun da ya" samu a tattare da 'yar ƙaramar baƙauyyiyar yarinyar ba. "Duk yadda ya so mazewa, sai sa Nina ta fuskanci hankalinsa a ba a kanta yake ba da tayi magana" sai ya ce mata ba shi da lafiya ne. *** "Har washegari, Nabila ba ta ci abinci ba, ta dai buɗe ƙofar cikin dare da zafi ya isheta, ta fara" numfashi da ƙyar. "Ta ɗaukko wayar Viper, ta din ga kallo, kamar shi ne a gabanta, ta rintse idanunta tana tuno" "kamanninsa, a zahiri suffarsa ta ban tsoro ce, amma a baɗini abun tausayi ne." "Ƙarfe takwas na safe, yaran gidan na ta zuwa gaida Abba, sai da sauda ta shigo ta gaishe shi, ya ce ""Sauda duba mini Arfa ko ta buɗe ƙofar, ki ce mata ina bata haƙuri idan laifi nayi mata, da ya sanya tun jiya ba ta neme ni ba, yau kuma ba ta zo ta gaishe ni ba"" Sauda ta tashi, ranta a ɓace ta tsani yadda Abba yake sakata a shirgin Nabila ta girmeta gashi ba shiri suke yi ba, amma ayi ta" zubar mata da girmanta. "Ta je ta tura ƙofar ɗakin taga ta buɗe, taga Nabila a kwance a kan gado, ta kwanta a kan hannunta," ta murɗe jikinta. """Ke! Malama ki taso Abba yana kiranki"" sai dai shiru Nabilan ba ta motsa ba." "Walida ce ta shigo ɗakin tana faɗin ta ga dama ta buɗe ɗakin kenan, sai dai tana ganin irin" kwanciyar da Nabila tayi ta ja ta tsaya. "A fusace sauda ta tafi ta ɗala mata duka Walida ta ce ""Yaya sauda kina ganin irin kwanciyar da tayi, da ƙyar idan ba iskokai za ta yi ba"" da sauri Sauda ta ja da baya ta ce ""Taɓ wallahi ba zata" "dake ni a banza ba"" Nabila ta saka hannayenta, ta toshe kunnuwanta dan ta daina jin maganar su." "Sauda ta koma ta gaya wa Abba, cewar Nabila iskokai ta tayar." "Abba ya taso yana yi wa sauda faɗa, a kan cewa ya hana cewa Nabila tana da da iskokai, takura ce" kawai ba ta so da ɓacin rai. Ya ƙarasa ɗakin yana kiran sunan Nabila. "Ya ɗagota daga kwanciyar da ta yi, jikinta yayi wani irin mahaukacin zafi, har wani huci take yi." "Idanunta sun kumbura sun yi suntum, ga wani irin ja da suka yi, ga wasu irin siraran jijiyoyi da" suka kwanta a saman goshinta. "Sai da Abba ya razana da yanayin da ya ganta, ""Arfa, meyasame ki haka? Meyake yi miki ciwo""" "Ta buɗe baki za ta yi magana, amma bakin ya din ga karkarwa ta kasa furta komai, hawaye ya din" ga bin gefen idonta. "Ya kalli walida ya ce ""Bani bedsheet a rufe mata jikinta"" ta duba ta ɗaukko masa, ya rufe wa arfa" "jikinta, ya din ga tofa mata addu'a." "Wani abu mai nauyi, ya tokare mata ƙirji, ya hana numfashinta fita yadda yakamata, a ƙalla Abba ya kai awanni biyu, yana yi mata addu'a yana tofa mata, sai bin sa take yi da ido, amma ta kasa" "magana, sai can wani irin nananuyan bacci ya ɗauke ta, dan ba ta yi bacci ba jiya gaba ɗaya." *** "Walid ne yake ta kokowa da Al'amin, a kan lallai sai ya fita ya kai kansa wurin 'yan sanda, a sakar" "masa liti, shi a kama shi, amma kafin nan sai ya fara kashe Nabila." """Ita wannan da tayi maka abun da bai taka kara ya karya ba zaka kashe, ko kuma zaka fuskanci" "indabo da madaki ne ka bar maganar wannan ƙaramar alhakin?""." "Viper ya ɗaga rinanun idanunsa jawur da su ya ce ""Zuwa yaushe? Zuwa yaushe mutane za su daina cutuwa a dalilina? Ba zan sake gangancin da na yi a baya ba, dole a saki liti, in dai kai kaina" "zai saka a sake shi""" """Is a minus case, dole zai fita, amma bama buƙatar a sake kama ka, ka gane mana, dole mu shirya" "ɗaukar fansar ka""" "Viper ya sake kallon Walid ya ce ""Sai na kashe yarinyar nan fa""" """Indabo yakamata ka kashe da Madaki, wani tunanin yakamata ka yi a kan wannan yarinyar ba" "wannan ba""" """Tarko aka yi mini da ita, ko ba ka gani?""" "Walid ya girgiza kai ya ce ""Haryanzu bamu da tababcin hakan, amma ba ka da wani sharhi ko" "tunani a kanta?""" """Babu, idan na sake ganinta kuma sai dai wata ba ita ba"" ya bashi amsa kai tsaye." """Shikenan, yanzu dai zan fita in ga me za ayi a sako mana liti""." "Viper yayi shiru bai ce masa komai ba, sai da ya yinƙura zai tashi, Al'amin ya riƙe shi. Walid ya" "juyo ya kalleshi ya ce ""Ina alƙawarin da ka yi mini?""" "Walid ya ce ""Ina sane, haryanzu kayan ba su sauka bane ba, ka san yanzu hanyar akwai tsaro sosai" "ba irin na da bane ba""" """Bani wanda ka kwashe ka fita""" "Cikin damuwa walid ya ce ""Wai dan mai zamani so ka ke yi sai ka haukace ne gaba ɗaya hankalinka zai kwanta, wannan uban ƙwayoyin da ka ke jibgaw kanka ba abun da suke yi maka," "jikinka duk ya riga ya bujire, ka yi haƙuri mu bi a sannu""" """Mai laya....." "Walid ya ce ""Mai zamani""" """Ka yi mini abun da nake so, ai na riga na daɗe da gama haukacewa, ka bani idan na cigaba da" "zubawa na san za su yi mini""" "Walid ya girgiza kai ya ce ""Da za su yi maka, da tuni sun yi, ka yi haƙuri ka bani lokaci""" "Al'amin ya waro masa idanunsa ya ce ""Ka fara kaini bango, baku san fa me nake ji ba, bana bacci," "ƙwaƙwalwata so take ta tarwatse, sonake komai ya shafe daga cikin kaina, ko da hakan yana nufin zan haukace""" """Fansar ta ka fa""" """Zan ɗauka""" "Walid ya yinƙura zai fice ya bar Al'amin, amma ya sake riƙe shi, Walid yana ƙoƙarin ƙwacewa," "hakan ya ƙara tunzura Al'amin, ya fara ƙoƙarin shaƙe Walid." "Babu yadda Walid ya iya, duk da yadda Al'amin yake zuba wa kansa kayan maye, amma yafi ƙ" "arfin sa, ya dunƙule hannu, ya daki jijiyar wuyan Al'amin, ya silale ya faɗi ƙasa." "Yayi sauri ya durƙusa a kansa, ya ga Al'amin yana ta ƙifta idanunsa, bai kai ga suman ba, jikinsa" ya saki gaba ɗaya. "Walid ya dafe kai yayi shiru, abubuwa na neman su ƙwace musu, gashi alamu sun fara nuna ƙwa" ƙwalwar Al'amin na nema ta fara taɓuwa. "Ya dafa kafaɗar Al'amin ya ce ""Ka ƙara bamu lokaci ɗan uwa, zamu kawo ƙarshen komai, da" "yardar Allah"" ya tashi ya fice." *** "Abba da magajiya sai anty, su ne suka yi ta ɗawainiya da Nabila, har ta ɗan samun nutsuwa, take ta uban bacci, tana tsaka da baccin sumayya ta zo, dan jiya hankali a tashe ta kwana, ta jirata har ta gaji, taje can wurin aikinta an ba ta je ba, ta zo gida an ce ba ta zo ba, ga lambobinta ba sa shiga, ta din ga fargabar Allah ya sa ba su indabo ne suka yi mata wani abun ba, gashi suka din ga kiranta suna tambayarta ta gaya musu me suka tattauna da Nabila." "Yanayin da ta ga Nabila, ya tsoratata, gaba ɗaya kamar ba ita ba, duk ta yi wani iri." "Cikin ikon Allah ta farka daga nannauyan baccin da ya kwasheta, da sumayya ta fara tozali, cikin" "kulawa sumayya ta ce ""Sannu"" ta jinjina mata kai kawai." "Duk shegen surutu irin na Nabila, sai bakin ya mutu, ta kasa cewa kowa uffan." "Sai da suka kaɗaice, sannan sumayya ta ce ""Nabila ki yi magana mana, meyafaru da ke? Kiran me" "ki ka yi mini kina so mu haɗu? Kuma na neme ki na rasa jiya, yau kuma na ganki a haka ko wani abun ne ya faru?""" "Nabila ta ƙura mata ido, yanzu ita ta ina za ta fara yi wa Sumayya bayani ma, wataƙila idan ta bata labarin abun da ya faru ma ƙaryata ta zata yi, ta ce mata ba ta da hankali, ta san babu lallai ta bata goyon baya, a kan abun da take niyyar yi. Ba wannan ba shi kansa Nasir idan ya dawo, ta ina za ta bi ta warware mugun ƙullin da tayi, muddin ta yarda aka kama Viper a sanadinta, ta zama azzaluma duk da ba ta ji ƙarashen labarin ba, amma yin hakan shiga hakkinsa ne." "Sumayya duk yadda ta kaɗa ta raya, fafur Nabila taƙi cewa komai, hasali ma zancen zuci ta din ga" yi taƙi kulata. "Abba ya din ga yi wa Nabila faɗan yawo ba ɗankwali, jin kaɗe-kaɗe da kuma yawan kwalliya." "Walida ta shigo da waya a hannunta, ta miƙawa Nabila ta ce ""Gashi Yaya ne zai yi magana da ke""" "Nabila ta girgiza mata kai, ba zata karɓa ba." """Me zan ce masa to?""" "Sumayya ta karɓi wayar suka gaisa da Nasir ta ce ""Yaya mutuniyar jikin ba daɗi, taƙi magana ma" "gaba ɗaya, ka yi haƙuri ko zuwa anjima mu gani idan zata yi""" "Ya ce ""Shikenan, hanklina ne a tashe, ban ji ɗuriyarta ba ai, na sake kira anjima"". Suka yi sallama" ta kashe wayar. *** "Kwanaki kusan uku ramma na fama da jikinta, kafin ta ɗan ji ƙwari, a kwanaki ukun nan, Abdul bai kulata ba, zai dai ba ta abinci ya bata magani, sai a kwana na uku da ya ga yi ƙwari, har tana salla." "Tun da rana ta fara ganin take-takensa dan haka hanklinta ya ƙi kwanciya, da daddare ta kasa bacci sam, aikuwa kamar yadda ta yi tsammani, sai gashi ya shigo ɗakin, yana miƙa yan kallonta." "Cikin hanzari ta tashi tsaye. Ya mayar da ƙofar ya rufe ya ce ""Ina zaki ne?""" "Ta hau ja da baya, ya nufota gadan-gadan kawai ta ciro wuƙar yanka fruit, ta ce ""Wallahi ka taɓani" "sai na caka maka, sai na kasheka azzalumi mara imani kawai""" "Ya ce ""Ohh wow, in ajiyeki ina ciyar da ke, ki ɗauki wuƙa ki ce zaki kashe ni, ni da ki ka samu ban kashe ki ba? Dole na canza taku." "Ya danƙota sai ga wuƙar a hannunta, amma ta kasa yi masa komai da ita, ba ta wuƙar yake yi ba, ya fara ƙoƙarin yi mata abun da ya saba, taƙi sakin wuƙar, garin kokowar ƙwatar kanta ya yanke shi da wuƙar hannunsa. Sakin wuƙar ta yi ta ce ""Na shiga uku"" ya tsaya yana kallonta, hannunsa" na zubar da jini. "Tayi sauri ta saka hannunta, ta danne wurin da yake ta zubar da jinin, ta ga hakan ba zai yi ba, ta" "kama rigar jikinta tana dannewa tana cewa ""Ka yi haƙuri"" ya ƙura mata ido, gaba ɗaya sai ta rikice." """Ni zaki kashe ko?""" """A'a ba kasheka zan yi ba, sonake kawai ka ji tsoro ka ƙyaleni, ka yi haƙuri"" ya fizge hannunsa ya fice, ta samu wuri ta zauna hankalinta rabi a tashe, rabi kuma tana gode wa Allah da ya saka ya ƙ" yaleta. "Nabila ta warware, sai dai gaba ɗaya walwalarta ta ragu sosai da sosai, ba ta iya bacci, tunaninta" da lissafinta kawai yaya zata ɓullowa lamarin. "Ta sake ɗaukko wayarsa tana jujjuyawa, ta tuna abun da Walid ya ce mata ""Sai dai ki je shi ya ƙ" "arasa miki""" "Tayi ajiyar zuciya ta ce ""Dole zan je, zan neme shi, sai na ji ƙarshen labarin, for now dole na" "tsayar da aikin DSP, na kamo bakin zaren nan, dan gudun kar a haihu a ragaya." "Ranar monday ta kunna wayarta, ta shirya ta ce wurin aiki zata tafi, ana ta zancen Nasir zai dawo," "sai dai ko a jikinta, dan ba ta shi take yi ba, ta shirya ta fice." "Da ƙafarta take ta tafiya, dan kar ta hau abun hawa tayi saurin zuwa wurin aiki, ba ta gama" "tunanin da take son yi ba, wataƙila ko za ta samu mafita a haka." "Kamar an ce ta waiwaya, ta ga wata baƙar mota, na ta bin ta sannu a hankali, tun da ta fito titi kuma ta ga motar, ta basar ta cigaba da tafiya, bayan wasu mintuna ta ƙara waiwayawa ta ga" motar still tana bin ta. "Tsayawa tayi ta juya ta nufi motar, sai aka tsaya aka yi parking aka daina bin ta, glasses ɗin motar" "tint ne, dan haka ba ta ganin na ciki. Ta ƙarasa ta hau ƙwanƙwasa glass ɗin, amma ba a sauke ba." "Ta gaji ta tari abun hawa, ta tafi." "Ta shiga reception kenan, ta tarar da wasu matasan mata su biyu, a cikin tashin hankali." "Ba ta damu ba ta wuce su, ta tafi office ɗin ta, ta ajiye kayanta ta sake fita harabar wurin, ta gansu" a tsaye suna kuka. "Har ta gota su ta dawo, ta kallesu ta ce ""Lafiya kuwa?""" "Ɗayar ta ce mata ""sannu""" "Nabila ta ce ""Yauwwa meyafaru ne?""" """Dama babanmu aka yi wa sharri, an kai shi wurin 'yan sanda ma, wai kotu za a kai shi, an ce mu" "ɗaukar masa lawya mai zaman kansa, mun ji ba zamu iya ba, abun da tsada sosai""" "Nabila ta ce ""Sharrin me?""" """Gadi yake yi a wani gida, sai ɗan wan matar gidan ya yi wa mai aikinta fyaɗe ya gudu, su suka" "fara kaita asibiti, da shi mai wankin gidan, shi ne daga baya aka kama su, wai su ne suka yi mata""" "Nabila ta yi shiru tana nazarin maganar ta kalli ɗayar ta ce ""Yayata kin tabatta, ba na shiga case ɗ" "in mutumin da ba shi da gaskiya, kar na yi bincike na tarar da saɓanin abun da ku ka gaya mini""" """Wallahi ba ƙarya muka yi miki ba""" "Ta ce ""Well, yanzu ina da tarin ayyuka a office ɗina, personally zan taimaka muku, ku zo gobe in" "Allah ya kaimu ƙarfe tara na safe, zamu je wurin mahaifin naku, na ga abun da zan iya yi a kai""" "Godiya suka din ga yi mata, tamkar za su durƙusa mata, yanayinsu kawai ya nuna suna fama da" matsin rayuwa. "Ta so haɗuwa da barrister Habib, amma bai shigo ba, ya tafi gudanar da wasu shari'oi dan haka ta" zauna ta gudanar da nata ayyukan. "Sha biyu na cika, ta ɗauki jakarta ta fita, kiran Nasir ya shigo wayarta, kamar ta share, sai ta ɗaga" tayi sallama. """Barrister, kina office ne na biyo?""" """Ka dawo kenan?""" "Ya ce ""Eh ina cikin kano""" "Nabila ta ce ""No, zan yi wata shri'a ne, ka je gida ka huta na kusa dawowa nima"" ba ta jira mai zai" "ce ba, ta saka wayar a Flight mode, ta tari abun hawa, ta nufi unguwar da Viper yake." Ayshercool 08081012143 ₦500 ne via 0009450228 Aisha Adam jaiz bank sai shaidar biya ta 08081012143 Wanda za su jira document 1K ne. 90009343 'Yan Nijar ku turo katin airtel na 300fcfa Arewabooks ayshercool7724 "Suna tafe a hanya, Nabila na ta saƙe-saƙe daban daban a cikin ranta, har suka iso dai-dai in da ta" "sauka wancan zuwan, ta sallami mai napep ɗin, ya din ga kallonta yana tunanin ita kuwa me za ta yi a irin wannan wurin haka ranar tsaka." """Malam lafiya, ka tafi mana"" ya ce ""To, tafiyar zan yi"" ya ja baburinsa ya tafi." "Sannu a hankali ta bi waccan hanyar da Walid ya bi da ita wancan karon, amma ta kasa gane" "hanyar da suka bi, balle ta gano gidan." "Ta din ga nausawa cikin wurin, tana bulayi, amma ko rabin gano hanyar ba ta yi ba, gashi ta fara" gajiya ga rana tana yi. "Sosai take bulayi, tana sake nausawa wani wurin, amma sai ta ga ta ɓulla wani wurin daban." """Ke baiwar Allah"" ta ji muryar wani a bayanta, ta waiwayo tana kallon mutumin, sanye da" uniform ka security. """Me ki ke yi a nan wurin rana tsaka haka?""" "Ta ce ""Dan Allah malam wani gida nake nema""" "Ya kalleta ya ce ""Gida a nan kuma?""" "Ta ce ""Eh""" """Gida fa ki ka ce?""" """Eh wani ƙaramin gida ne, rannan na zo ma amma hanya ta ɓace mini"" ya girgiza kai ya ce a'a" "babu wani gida a nan haka, duk kamfanunnunka ne, sai gonaki, can kuma idan ki ka bu dutse ne, daji zaki shiga dan haka babu wani gida a nan""" "Nabila ta ce 'Malam akwai gida a nan haka, na je gidan fa""" "Cikin tsawa ya ce ""Ke babu wani gida a nan, ki bar wurin nan tun ban sakar miki karnuka ba, ko" "na kama ki na haɗaki da jami'an tsaro""" "Ta ƙare masa kallo ta ce ""Ni zaka saka a kama, na yi maka kama da ɓarauniya ne?""" "Ya ce ""To wa ya sani, yanzu ai ɓarayi ne kawai ɓata gari ba, kuma ba a goshi ake ganin ɓata" "garin ba, ta cigaba da ƙarewa wurin kallo, ba ta ga hanyar gidan ba"" ta ja guntun tsaki ta juya ta fara tafiya, sai mamaki take yi, tabbas gidan a nan haka yake, amma ya aka yi haka ta faru?" Haka ta koma ba tare da ta gane wurin ba. "Tun daga haraba yake murmushi, kamar bakinsa zai yage, cikin ƙarfin hali ta ƙaƙalo murmushin" "ita ma, ta ƙarasa ta ce ""Welcome home DSP"" ya miƙa mata hannu, ta miƙa masa na ta suka gaisa ya ce ""I really miss you barrister""" """Me too, ya aiki?""" """Aiki Alhamdilillah, daga shekranjiya zuwa yau duk ina cikin damuwa, an ce ba ki da lafiya, ba" "kya ɗaga wayata""" "Ta ce ""Ka san ni ɗin ce a lallaɓa, auren zamani, yau da lafiya gobe babu, bari na je na yi wanka na" "ci abinci""" "Ya ce ""Take your time, ki huta sosai zuwa yamma, zan je office ne, zan ga mutumin da aka kama, aka ce ya san in da Viper yake, kan na dawo ki bani abun da ki ka ce"" dammm! Ƙirjinta ya buga," "amma ta maze ta ce ""Ok bye bye, sai ka dawo"" ya ɗaga mata hannu ta shiga cikin gidan." "Sai yanzu ta tuna tayi alƙawarin gaya masa wani abu idan ya dawo, wanda dama wayar Viper take" "son ba shi, wanda a yanzu ko me za'ayi mata ba zata miƙa wayar nan ba, sai ta ji ƙarshen labarin nan." "Tana wanka tana zancen zuci, idan ta ce za ta yi wa Nasir bayani, ba ta da wata cikakkiyar hujja," "da za ta sanya ya fuskanci in da ta dosa, kuma sai ta tonawa kanta asiri na cewa ta haɗu da Viper." *** "Ɓangaren ramma kuwa, tun da ta yanki Abdul da wuƙa, ba ta sake ganinsa ba, har gari ya waye, duk abun duniya ya ishe ta, wai ita ta yi wa mutum illa da wuƙa har ya zubar da jini." "'sai me, ke kin manta abubuwan da ya aikata miki?' wata zuciyar ta tambayeta." "'Duk da haka, da kuma na caka masa in da zai mutu fa?"" Ta tambayi kanta." "Ta buɗe falon, ta fito da rigarsa sai towel da ta ɗaura, ta rufe jikinta da ɗan kwalin kayanta, ta fito" falon ba kowa. "Solomon ya fito zai shirya abinci a kan dining, ta ce masa ""Ina kwana?""" "Cikin gurɓatacciyar hausarsa ya amsa mata, ta ce ""Yana ina?"" Yayi mata saroro ba ya jin hausa." """Kai ba ka jin hausa ne? No hausa?"" Ya jinjina mata kai tare da yin murmushi." "Hausa da turanci take haɗawa, tana tambayar sa ina wannan mutumin, mai gidan nan?""" "Turancin nata ya bashi dariya, da turanci ya ce mata bai kwana a gida ba." """Ina ya tafi?""" "Ya ce ""Ba a tambayarsa in da ya tafi"" tayi ajiyar zuciya ta kalli, kwanukan abincin ta ce ""Duk kai" "ka ke dafa wannan? A ina ka iya girki?""" "Ya ce ""Catering school na yi, tun ina ƙarami kuma, ina taimakawa mamana wurin yin girki, tana" "sayar da abinci""" "Ramma ta ce ""Ka san koko?""" "Ya yi shiru yana kallonta, kwatanta masa ta shiga yi, yayi dariya ya ce ""Pap"" ta ce ""Eh, shi ka din" "ga yi mini turancin ƙanana yadda zan gane""" "Yayi dariya ya ce ""Ai normal turanci ne, kawai dai pidging ne"" a dai-dai lokacin Abdul ya shigo" "falon, ya tarar da ramma a tsaye, tana magana da solomon tana murmushi." "Wani abu ne ya tokare masa wuya, suka ɗago suna kallonsa, tana ganinsa ta haɗa fuska, ta din ga" "satar kallon hannunsa, da ya naɗe da bandeji." """Solomon, yaushe na zama sa'anka da zan ajiye yarinya ka din ga hira da ita? Kai ka ajiyeta? So" "kuna shirya yadda za ta gudu kenan?"" Da sauri solomon ya girgiza kai ya ce ""Ba zan taɓa cin amanarka ba sir, abu ta tambayeni nake ba ta amsa""" """Babu ruwanka da ita, idan tambayar ce ta tambaye ni""" "Ya jinjina kai. ""Bar wurin nan"" da sauri ya bar wurin." "Ya ƙarasa dining ɗin, zai zauna ramma ta tashi. ""Zauna ina zaki je? Haɗa mini abinci in karya""" "Cikin tsananin takaici take bin sa da ido. ""Zaki haɗa mini, ko sai na turmusheki na yi breakfast ɗ" "in da ke, 'yar dabar ƙauye kawai, ki na 'ya mace kina ɗaukar wuƙa""." """Ni ba 'yar daba ba ce ba, kare kaina nayi yinƙurin yi daga mugu irinka mara imani""" "Ya ɗora ƙafarsa a kan dining ya ce ""Na ji, haɗa mini, ko kuma wallahi na yi abun da na ce""" "Tuni hawaye ya cika mata ido, ta haɗa masa tea, da doyar ta tura masa gabansa, ta tashi zata tafi ya riƙota, ya ɗaga mata hannunsa na dama, wanda a nan ta yanke shi, ya ce ""Da wani hannun zan" "ci?"" Ta tsaya tana kallonsa." """Oya feed me, tun da kin riga kin yi wa hannun illa, idan ba haka ba kin san condition ɗin"" babu" kalar tsinuwa da zagin da ba ta yi masa a zuciyarta ba. "Cike da ƙwarewa a fannin iya rashin mutunci da bariki, haka yake haɗawa da hannun ta idan ta bashi a bakin, yana wani ƙare mata kallo. Sai ƙanƙame jikinta take yi, gaba ɗaya wani iri take" jin ta. "Ya cinye doyar ya ce ta ƙara masa, a ranta ta ce ""Shege jaki""" "Lomar ƙarshe, ya riƙe hannunta, da yatsunta a bakinsa, kokowar ƙwacewa take yi, amma ya riƙe su a bakinsa yana yi mata kallon 'yan iska a cewarta. Ba ta san lokacin da ta dunƙule ɗaya hannun nata ta ɗirka masa duka a kafaɗarsa ba, ɗan dukan da babu in da ya je, ya saki yatsun yana murmushi, da ƙoƙarin tauna sauran doyar, wani irin mugun kallo take yi masa, tare da goge yatsunta a jikin rigar jikinta, ba ta fargaba ya sake tashi, ya haɗe bakinsa da nata, yana ɗura mata ragowar abincin bakinsa, cikin tsananin jarumta, take naushinsa ta ko ina, amma ya saka hannu, ya" "danna maƙogwaronta, babu shiri ta haɗiye, ya cikata ya nufi 3seater ya kwanta." "Iya ƙarfinta ta zage ta din ga zaginsa, har da kalar wanda ba ta taɓa tunanin ta iya ba, ya lumshe" "idanunsa ya yi mata banza ya ce ""Na san maganinki""" "Nasir ya ƙarewa liti kallo, sannan ya kalli sageant ɗin da suke tare ya ce ""Kana nufin bai yi" "magana ba gaba ɗaya?""" """Eh sir, ya ƙi yi""" "Ya mayar da idonsa kan liti ya ce ""Ka sauƙaƙawa kanka, ka sauƙaƙa mana aiki, ka gaya mana" "abun da muke tambayarka a kai. Ina Aminu Viper?""" """Ban san in da yake ba""" """Ƙarya ka ke yi, rahoto ya zo mana a kan ba shi da wasu makusanta bayan iyayensa sai ku, babu" "iyayensa a lissafi tun da dama sun riga sun sallama shi, ka fi kowa sanin in da Aminu viper yake""" "Liti ya ce ""Tun da ka samu wannan rahoton, kai ka san amanar da ke tsakaninmu ba wadda zan yadda ta rushe ba ce a kan ƙaramar bazarana ba ce. Kalleni da kyau, na yi gwagwarmaya na ga rayuwa, prison ceil, na shiga kala-kala. Kuma ban taɓa zuwa gaban ɗan sanda na yi magana biyu mabanbanta ba, idan zan yi zan yi kawai. Eh ko a'a. Ko kasheni zaku yi a yanzu, ban san in da" "yake ba""" "Nasir ya kaɗa kai ya ce ""Kar ka cika baki, wataƙila wannan karon, ka zo in da zaka yi magana" "biyu, ina Aminu Viper yake""" "Liti ya ziraro harshen sa, kamar yadda Al'amin ya ke yi ya ce ""Allah ya ja da ran mahadi mai dogon zamani. Ambaton sunansa kawai, girma muke bashi na musamman. Abun da ba ka gane ba shi ne, shi fa mai gida ya ci dubu sai ceto wallahi. Idan ba haka ba tayaya za a saki mutumin da" "yake tsare, kuma a dawo ana nemansa? Gangan ma kenan""ya yi maganar yana dariya." "Nasir ya ce ""Babu laifi, zaka yi magana dan dole""" """Magana biyu, abun da liti bai taɓa yi ba kenan, ko wace irin azaba kuwa zaka gana mini, ai ƙ arshen ƙwarewar taku kenan, ku yi ta ganawa mutum azaba, ya amsa laifi nasa da ba nasa ba. Idan har manyanka ba su saka na yi magana biyu ba, ba ka da wata izaya da zaka yi mini na yi" "magana biyu, idan kuwa na yi magana biyu ashe ba yaron Viper bane ni""." "Wata inkiya Nasir yayi, kamar yadda liti ya faɗa kuwa, aka saka wasu kurata, suka din ga jibgarsa da kulki, kamar sun samu tumu, suka yi iya yin su suka yi masa lilis, sannan suka kai shi wani ɗ" aki mai duhu suka kulle shu. "Gaba ɗaya Nabila tana ɗakinta, tana ta lissafin yadda za ta ɓullowa al'amuran nan da suka sakota" a gaba. "Ta idar da sallar isha'i, ta zauna a kan daddumar, sai tufka da warwara take yi, gashi ta rasa da wa" zata tattauna maganar ta ji daɗi. """Tunanin me ake yi haka ne?"" Ta ji muryar Nasir." "Tayi ajiyar zuciya ta ce ""Yaya sannu da zuwa""" "Ya zauna a gefen gadonta tare da cewa ""Yauwwa arfa, kin ga ban dawo da wuri ba ko? Na je na ga mutumin da ki ka yi mini bayani, na saka aka kama, ta tabbata yaron Aminu Viper ne, amma riƙaƙ ƙen mara mutunci ne, ya ƙi magana, duk wani nau'i na tuhuma an yi masa amma ya ƙeƙashe ƙ" "asa yaƙi magana""." "Nabila ta ce ""Ikon Allah, bai faɗi in za yaken ba kenan?""" "Ya girgiza kai ya ce ""Bai faɗa ba. Amma muna nan muna trying, alamu sun nuna ya sani, ɓoyewa" "yake yi. Yauwwa yanzu gaya mini me ki ke son ki gaya mini lokacin bana nan""" "Tayi ajiyar zuciya ta ce ""Nothing much, dama dai duk a kan case ɗin nan ne, na ce me zai hana ka" "bibiyi case ɗin daga tushe, misali daga gidansu, iyayensa mutanen kewayen da ya zauna da su""." """Me hakan zai amfana?"" Yayi maganar yana kallonta." "Ta ce ""Kawai ji nake kamar akwai lauje a cikin naɗi, a kan sha'anin Aminu Viper, kamar abun da" "aka baka a kansa is not complete, something is missing, yakamata a fara samo full details na abun da ya faru""." "Ya girgiza mata kai ya ce ""Duk bani da isashshen lokacin yin haka, na yi ƙoƙarin yin hakan, aka ce ba shi aka sakani ba, kuma duk maganar nan da ki ke yi is a very long way, gara shortcut, idan ya zo hannu muka gama da shi, kotu zamu tura shi, a can ne aikinki yake idan ma tssya masa zaki" "yi"" tayi murmushi ta ce ""Hakan fa zai iya sawa na yi suna ko?""" "Yayi dariya ya ce ""Ke dai kin damu da maganar yin sunan nan, gaba ɗaya kin canza, ko dai" "haryanzu jikin ne? Gaba ɗaya kin rage ɗokin case ɗin Vipern ma, ko akwai wani abu ne ki gaya mini "" ta girgiza kai ta ce ""Babu komai""" "Ya ce ""Are you sure?"" Ta jinjina masa kai, ya tashi tsaye ya ce ""Ban yarda iya abun da ki ke son" "gaya mini ba kenan, akwai abun da ki ke son gaya mini ki ka fasa, amma da sannu zan gano menene da kaina""" "Shiru kawai ta yi tana murmushi ya fita, yana ƙoƙarin fita daga falon, ya ci karo da mama, sai da" "ya ɗan tsorata ya ce ""Mama""" """Me ka ke yi a ɗakinta da daddaren nan?"" Tayi maganar rai a ɓace." "Ya ce ""Subhanallah, dan Allah mama kar ki kawo komai a ranki, muna magana ne a kan aiki..." """Rufe mini baki, aikin banza da na wofi, sai ubanka ya farga ya fara yi maka terere a cikin gidan nan ko, kana zuwa ɗakinta da daddare, ka dai san ita ba zai tagayyarata ya nuna laifinta ba sai kai." "Duk lokacin da na yi ƙoƙarin fahimtar da kai, irin wannan abun ba ka gani, daga dawowar ka," "zaka fara sakani magana saboda wannan sheɗaniyar yarinyar ko Nasir? Ka cigaba ban ce ka fasa ba"" ta nufi ɗakinta ta bar shi a tsaye a wurin saroro yana kallonta." *** "Ramma tana kwance ta sha kuka har ta gaji, tunanin halin da mamanta take ciki kawai take yi, ta san tana can hankalinta a tashe, tana faɗi tashin neman in da take." "Ta gaji da kwanciyar, ta ɗauki ruwan da yake ajiye, a kan side bed, ta sha fiye da rabi, saboda ma" "ƙogwaronta duk ya bushe, saboda kukan da ta sha." "Ta kwanta tana jiran bacci ya kwasheta, amma bacci ya gagara, sakamakon wani irin yanayi da ya din ga bijiro mata, har wani irin gumi take yi, ta tashi cikin matsananciyar damuwa, amma ta rasa takaimaimai meyakamata ta yi. Ta nemi wuri ta kwanta, ta takure, tana ta mamakin wannan wane" irin abu ne haka. "Abdul ne ya shigo yana fito, tayi shiru ba ta motsa ba, ya nemi wuri ya kwanta a bayanta." "Ba ta yi masa tashin hankali ba, ko ƙoƙarin yin gardama ba, babban abun da ya ɓata mata rai, ya sanya ta ji tamkar ta kashe kanta, bai wuce yadda ta iya biyewa Abdul ba, ta tabatta mazinaciya!. Kuka take yi iya ƙarfinta, har da sheshsheƙa ko a jikinsa, kaɗa ƙafa kawai yake yi, daga baya ya tashi zaune yana kallonta, yayi dariya ya ce ""Ba dai ke taurin kai ba, ai na san maganinki, you are very healthy and unique, zaki yi mana baƙin ciki. Ba kya buƙatar komai kan ki yi functioning lafiyayyiya ce ke, amma tsinanane taurin kai irin na ɗan ƙauye ba zai bari ki yi abun da ya dace ba"". Ya ɗago wata ƙwaya ya ce ""You force me to use it on you. Idan ki ka bari muka cigaba a haka ke zaki sha wahala, dan zata iya cutar da ke, aikin gama ya riga ya gama ba wani sauran amfani da zaki yi, ni ban ga abun ƙi ko damuwa ba. Na aika a gaya wa babarki ta daina nemanki" "na ajiye mata ke a in da ya dace""." "Cikin kuka ramma ta ce ""Ba zan taɓa yafe maka ba, Allah ya isa, mazinaci mugu""." "Ya ce ""Mazinata dai har ke""" """In sha Allah ba zaka gama da duniya lafiya ba""" "Ko a jikinsa ya ce ""Idan Allah ya nufa na gama da ita lafiyan, sai ki hana ai"" ta cigaba da kuka, shi" kuma ya juya ya hau bacci. "Ta bi shi da kallo, ba ta tunanin ko wankan janaba yana yi, sai da tayi mai isarta, ta tashi ta yi wanka, ta saka wata jallabiya, ta leƙa fuskarsa, ta ga bacci yake yi sosai." "Ta lallaɓa ta fita daga ɗakin, ta fara laluben ƙofar fita, sai dai ta nemi hanya ta rasa." "Ko ina a rufe ta girgiza manyan ƙofofin, amma ko motsi ba sa yi, ta zauna a falo, ta cigaba da" "kuka, ta din ga jin haushin karnuka, tsoro yakamata, ta tashi ta koma bedroom ɗin, ta tarar da shi a zaune yana danna wayarsa." Ta nemi wuri ta kwanta a ƙasa. """Idan ki ka kuma yinƙurin guduwa, sai na bar garin nan da ke, ba garin nan ba kawai, zan iya" "barin ƙasar nan da ke, babu wanda zai sake jin ɗuriyarki, gara ki shiga hankalinki""." """Ai ba zan tabattar da kai tabattacen azzalumi bane, sai ka rabani da duniyar"" ya kalleta, kamar ba" daga bakinta maganar ta fito ba. "Duk a yawon barikinsa, babu karuwar da ta isa ta ci masa mutunci ko ta zage shi, amma a garin kwashe-kwashensa, ya kwaso 'yar mitsitsiyar yarinya tana cin zarafin sa, yayi mata shiru, yana jin ta tana yi masa Allah ya isa ƙasa-ƙasa har da Allah ya tsine masa, amma ya shareta, tun da yau ya" samu abun da yake so. "Nabila tana office ɗin ta a zaune, tana ɗan danna system, sai dai hankalinta ba a kan system ɗin" yake ba. "Aka danna ƙarrarawar office ɗin, ta bada umarnin a shigo, matasan matan nan ne, wani masinja" "ya rako, ya ce ""Hajiya Nabila, ga baƙi kin yi""" "Ta ce ""To na gode sosai. Bisimillah ku zauna"" suka zauna tare da gaida Nabila." "A kallo ɗaya zaka ga Nabila ta yi kalar mata masu izza da jin kai, amma kuma kana zama da ita" zaka ga saɓanin hakan. "Suka gaisa ta ce ""Jiya ina sauri zan fita, mun fara magana bamu ƙarasa ba, duk da yau ɗin ma ina" "son fita ne""" "Ɗayar ta ce ""Ai mun gode ma saurarmu da ki ka yi. Lauyan gwamantin sai yawo yake yi mana da" "hankali, aka ce mu ɗaukar wa baban lauya mai zaman kansa kawai, mun zata abun mai sauƙi ne, ashe yafi ƙarfinmu""." "Nabila ta yi musu tambayoyi, ciki har da in da aka ajiye mahaifinsu, ta yi musu alƙawarin za ta je" "da kanta, ta tattauna da shi, za ta bibiyi komai, kafin a shiga zaman kotu." "Suka yi ta yi mata godiya, ta ce ""Kar ku damu, ku bani lamabar wayar da zan iya samunku""" "Suka bata, ɗayar ta ce ""To ƙanwata nawa ke zamu baki?""" "Nabila ta ce ""Karku damu, ku yi mini addu'a kawai, akwai abun da na saka a gaba, Allah ya sa na yi nasara baki ɗaya, da case ɗin ku da ɗaya abun da na saka a gaba"" da suka fara yi mata addu'a, sai da ta fara jin nauyinsu, dan tamkar ta yi musu bushara da mahaifinsu ya fito, suka hau yi mata hira da labarin yadda sunan mahaifin na su ya ɓaci, a cikin unguwa. Tayi ta basu ƙwarin gwiwa," da tabbacin da yardar Allah za su yi nasara. "Bayan tafiyarsu, kawai ta yi wani tunani, ta ɗauki jakarta ba ta zame ko ina ba, sai wurin aikin" "sumayya, ba ta tarar da ita ba sai Lawisa, sai zuba iko take tana hura hanci." "Nabila ta yi murmushi ta ce ""Anty lawisa, Sumy ta shigo kuwa?"" Ta ɗaga kai da ƙyar ta kalli" "Nabila ta ce ""Eh""" """Tana ina?""" """Recording take yi""." "Ta ce ""Ok, bari na jirata a nan"" tayi maganar tana ƙoƙarin zama." """No please, ba na son takura, ko zaki jirata a reception?""" "Nabila ta ce ""Ba zan iya zaman reception ba, kujerun ba su da daɗin zama a nan zan zauna"" tayi" maganar tana zama a kan kujerar office ɗin. "Baki buɗe lawisa take kallon Nabila, ta maze ko a jikinta, ta na danna wayarta." "Ta kalli lawisa ta ce ""A kan kujera kawai na zauna, ba hira na ce mu yi ba, 10-20 minutes, ai is not" "that much da zaki ce ba kya son takura"" ta cigaba da danna wayarta." "Bayan mintuna goma sha biyar, Nabila ta ji yo muryar sumayya, ta ɗauki jakarta ta fice, ba tare" da ta sake kula lawisa ba. "Sumayya na ganinta ta harareta, Nabila tayi murmushi ta ce ""Haba masoyiyya daina hararata" "mana""" """Matsa ko na make ki, ni ki ka yi wa wulaƙanci ki ka daina ɗaga wayata""" """Ba haka bane ba, ayyuka ne suka yi mini yawa, daga nan ma wani wuri zan je na ce bari na biyo" "mu yi magana""" "Suka shiga wani office da babu kowa suka zauna, Sumayya ta ce ""Wai ni me zaki gaya mini last" "week ne? Ki ka shanya ni da yake ba mutunci ne ya ishe ki ba, wayarki ma gaba ɗaya ta daina shiga, har gida na je ina nemanki""" "Nabila ta kaɗa kai ta ce ""Aiki ne ya zo mini unexpected, mun je court ne, ina da shari'a kuma zan ga wasu clients ɗina. Dama a tsakanin lokacin nayi tunanin zan iya squeezing time ɗina, mu haɗu," "kuma bai yiwu ba""." "Sumayya ta ƙare mata kallo tayi murmushi ta ce ""Ko dai kin sake komawa wurin Aminu Viper" "ba?""" "Nabila ta yi murmushi ta ce ""Kina zargin na koma ne?""" """Na san hali zaki aikata ai, ina gargaɗinki a kan kasada da rayuwarki Arfa""" "Tayi murmushi ta ce ""Ina ma zan iya jin maganarki""" "Sumayya ta ce ""Baki yadda ba kenan?""" "Nabila ta ce ""Mu bar maganar nan, ni wani taimako nake son ki yi mini """ "Sumayya ta ce ""Ina jinki""" """Ke ce uwar neman labari, bincike nake son yi a kan honorable ma'aruf Indabo""" "Sumayya ta kalleta ta ce ""Kamar yaya?""" """Kamar yadda na gaya miki, taimaka mini nake son ki yi, ki binciko mini duk wani labari da" "yakamata a kansa""" """Me ku ke so ku mayar da ni ne daga ke har shi?""" "Nabila ta ce ""Shi wa?""" Sai kuma sumayya ta farga da katoɓarar da ta kusa tafkawa. """Indabon yayi miki wani abu ne?""" "Sumayya ta ce ""No kar ki damu, haushi ki ka bani ne, kin ce Naja'atu Bunkure, kin ce Aminu" "Viper yanzu kuma kin ce Indabo, Nabila me ki ke son ki zama ne?""" "Nabila ta tashi tsaye ta ce ""Zan je wani wuri yanzu, Ina jiranki dan Allah sumayya, da tarihinsa da" "tarihin siyasarsa komai da komai da yakamata ina son sani a kansa""" "Sumayya ta ce ""Wai me zaki yi da shi to?""" """Amfani mai muhimmancin gaske, sai anjima, ki gaida umma zan zo har gida na gaisheta, kwana" "biyu ba mu gaisa ba. Ina jiranki dan Allah"" ta ɗauki jakarta ta yi waje." "Kamar ta tafi gida, sai ta fasa ta ɗaukar mai napep, ta tafi police station ɗin da aka ce mata" "dattijon nan yana tsare, da ta je ta tarar an canza masa wuri, an mayar da shi sashen kula da manyan laifuffuka." "ID card ɗin ta kawai ta nuna, aka bata damar ganinsa, aka fito da shi, dattijo ne amma ba tsoho" cancan ba. "Suka gaisa ta ce ""Baba ni ce, wadda 'ya'yanka suka same ni, a kan maganarka, yaya meyafaru?""." "Nan ya ba ta labarin duk abun da ya faru, ta ce ""To baba yaya sunan shi ɗan yayar matar?""" "Yayi shiru ya ce ""Wallahi ban sani ba, yana dai zuwa gidan da yake ban daɗe da fara aiki a wurin" "ba""" "Ta ce ""Yanzu ina ne gidan da ka ke aikin, sannan ina yarinyar take, dole zan ganta """ "Ya share hawayensa ya ce ""Wallahi ban sani ba"" Nabila ta tambayi 'yan sandan suka ce sai dai ta" "koma can in da aka fara binciken case ɗin""" "Ta ɗauki bayanan da zata ɗauka, ta yi musu sallama ta tafi." *** "Kasancewar Abdul da wuri ya fita, solomon ma baya nan, Ramma ta din ga yawo tana neman hanyar fita tana kuka, amma ta rasa, tayi-tayi ta samu hanya ta rasa, ƙarshe ta koma falo ta zauna tana kallon Tv." "Wata magazine da tarin takardu ta gani, ta ɗauka tana kallo, signing ɗin sa mai kyau, Abdul" yassar ma'aruf Indabo. "Shiru ta yi tana tunanin, kamar ta san sunan nan." "Ƙofar falon ya saka key ya buɗe ya shigo, yayi sallama ta amsa a hankali, sai dai yayi kissing ɗin" "kumatunta sannan ya zauna, ta tsuke fuska tana matsawa." "Ya kuma matsawa kusa da ita ya ce ""Kin ci abinci kuwa?"" Ta yi masa shiru." "Ya ɗago mata jakar hannunsa ya ce ""Yakamata ki san menene a jakar nan"" taƙi kula shi." "Ya buɗe jakar, ya zazzage mata, kayanta ne a ciki, da kuma wasu sababbin kayan ya sayo mata." """Babarki tana gaishe ki""" "Ta kalleshi idonta fal hawaye ta ce ""Me ka ke nufi?""" """Na ce ta sallama mini ke, ba sai ta cigaba da nemanki ba""" "Ta sake kallonsa ta ce ""Waye indabo?""" Ayshercool 08081012143 ₦500 ne via 0009450228 Aisha Adam jaiz bank sai shaidar biya ta 08081012143 Wanda za su jira document 1K ne. 90009343 'Yan Nijar ku turo katin airtel na 300fcfa Arewabooks ayshercool7724 "Queen collection, dealers of all kind of textiles, bedsheet, Adashi stock fish and others. Follow this link to join my what's app group https://chat.whatsapp.com/Hp4ZLNtrNXvJQkAV8UWZcv" "Ya kalleta ya ce ""Meye alaƙarki da sunan? Kin san shi ne?"" Ta girgiza masa kai alamar a'a." """To a ina ki ka ga sunan?"" Ta ɗago masa takardar ta ga signing ɗin sa, da full name ɗin sa." "Ya ce ""Well babana ne, ba abun mamaki bane dan kin san shi, ɗan siyasa ne""" "Cikin rauni ta ce ""Me ka ce wa mamana da ka je?""" """Ba na gaya miki ba, na ce kar ta sake nemanki, kin zama mallakina""" """Saboda ba ka da tausayi da imani ko? Wallahi idan baƙinciki ya kashe mahaifiyata ba zan yafe" "maka ba""" """Ikon Allah, me zai sa baƙin ciki ya kasheta, na kai mata kayan buƙata a matsayin ina tare da 'yar ta. Ku ne haryanzu ku ke wannan kidahumancin, kun ƙi ku waye, turawa duk in da mace ta kai 18yrs tana da ikon zuwa in da take so tayi rayuwa, amma ku da an yi magana sai ku ce aure aure," "in anjima kuma ku yi ta surutun wahala ku ke sha a auren""" "Ramma ta ce ""Saboda yahudanci ko? Mu ai ba turawa bane, musulmai ne baƙar fata, hausawa masu riƙo da addini da al'ada. Ni ban shekara sha takwas ɗin ba, idan ma na yi ai sai da yadda ta da amincewa ta. Kawai saboda bamu da kuɗi ka yi mini fyaɗe ka je har gidanmu gaban uwata ka ɗaukko ni, ka rabani da ita, kuma ka koma ka karɓo kayana ka ce mata ta daina nemana kai ba aurena ka yi ba, kai ba wani abu ka yi da zaka taimaki rayuwata ba, ka ɗauki hakkinmu ba ka yi" "mana adalci ba""" "Ya ce ""Ke kin isheni, sai ka ce ke kaɗai ce 'ya? Ni fa ban taɓa ɗaukar wata mace na ajiye ina lalla" "ɓata ba sai ke, kuma ma ku da ake haihuwar ku barkatai babu tsari, har wani damuwa za a shiga" "dan an ɗauki ɗaya? Kashe ki fa na yi niyyar yi na ƙyale ki""." """Mu ba ai haife mu barkatai ba, mu uku ne, yayanmu ya rasu, ƙanina ba shi da cikakkiyar lafiya, ni kuma ka ɗauke mata ni, ban da dalilin maraici babu abun da zai saka ka ganni a birni aikatau, har ka keta mini haddi, bayan ka turo mana wata azzaluma, da fari ta ce zata taimaka mini, ta koma gaya mana yahudanci, ka ɗauke ni a gaban uwata, ka zo ka mayar da ni karuwa ka yi wa" "kanka adalci dan Allah kuma nima ka yi mini?""" """Naja'atu Bunkure ba ƙarya ta gaya miki ba, tun a lokacin da ba ku nuna taurin kai ba, da ba a zo" "nan ba, ku ku ka janyo koma menene ai""" "Ramma ta haɗa hannayenta biyu, ta rufe fuskarta tana kuka ta ce ""Ka cuce ni, ka lalata mini rayuwa, dama kasheni ka yi na huta, ka wulaƙanta rayuwata a matsayina na 'ya mace musulma da addinina ya suturta. Da ƙanwarka ce ni ko 'yar ka, ba zaka zuba mini ido ka ce na je na yi tarayya da wani ba aure ba, kayi amfani da kuɗi, ka wulaƙanta ni dan ni 'yar talaka ce ba ka kyautawa" "rayuwata ba"" ga ta yarinya ƙarama, sai iya tsara magana." "Abun da bai taɓa ji ba sai a wannan karon, kukan ramma a cikin zuciyarsa, maganganun ta suka" "tsaya a zuciyarsa, amma a zahiri ya nuna ko a jikinsa, ya tashi ya bar ta a falon ya tafi ɗaki." *** "Ɗan mama yana ta kaiwa yana komowa, tsakanin ɗakin Viper da tsakar gida, yana jiran Walid ya" "fita, amma ya ƙi fita ya zauna ba shi da niyyar fita." Viper kuma sai bin ɗan mama yake yi da ido. "Walid ya ce ""Kai ɗan mama, kamar ba ka da gaskiya""" "Ɗan mama ya ce ""Haba Oga walid me ka gani?""" """Ba sai na gani ba, alamun hakan na gani, wallahi na ga abun da bai yi mini ba, sai ranka yayi" "mugun ɓaci""" "Ɗan mama ya ce ""Kar ka damu Oga walid, babu wani abu da zaka gani wanda zai ɓata maka rai""" "Walid ya jinjina kai, ya cigaba da shan sigari." "Al'amin ya yinƙura ya tashi, Walid ma ya tashi ya ce ""Ina zaka?""" Al'amin ƙura masa idanunsa da suka yi wani irin mugun jaa. """Ba wai tuhumarka nake yi ba, ko wani abu ba, kawai dai ba na son ka yi wani abu da zai wargaza" "mana shiri ne""" """Iska zan je sha, ko yau ma yinƙurin kashenin zaka yi?""" "Walid ya girgiza kai ya ce ""Last time ɗin ma, ni ba niyyar kasheka na yi ba, ƙoƙarin hanaka abun da ka yi niyya na yi, a dawo lafiya"" Al'amin ya nufi ƙofar fita, ɗan mama ya ce ""Oga Viper, bari" "na zo mu je na taka maka"" Walid ya riƙe rigarsa, ya tsare shi da ido." "Ya sosa kai ya ce ""Dama raka shi zan yi""" "Al'amin bai waiwayo ba, kawai ya fita, Walid ya fara saka hannu a aljihun ɗan mama yana caje" "shi, Ɗan mama ya riƙe hannunsa ya ce ""Dan Allah ka yi haƙuri zan yi maka bayani""." """Sakar mini hannu, ko na kwaɗa maka mari""" "Ɗan mama ya sakar masa hannu ya ce ""Amma dai da ka tsaya na yi naka bayani""" "Walid ya ciro baƙar leda a aljihunsa, ya buɗe, ampoules ɗin allura ne da sirinji, sai baƙin capsule." "Walid ya kalleshi, ɗan mama ya ce ""Wallahi cewa yayi sai na nemo masa su, idan ba haka ba, ba" "ya iya bacci, kansa zai fashe ni kuma sai ya bani tausayi, daga ƙarshe kuma ya ce wallahi idan ban samo masa ba sai ya kashe ni""" """Sai ya kashe ka, kai ka taɓa ganin ya kashe wanin?"" Ɗan mama ya girgiza kai." """Wallahi idan ka kuma sayo wannan hard drugs ɗin ka kawo masa, sai na saka maka ƙarfe ka ji na rantse"" ɗan mama ya ce ""To, amma dan Allah shi ma ka gaya masa, ka san idan na ce masa a'a" "ba zai yi mini da daɗi ba""." "Walid ya ce ""Idan ya ce ka kawo masan, ka ce masa to, ka gaya mini"" ya jinjina masa kai." "Viper yana zaune a kan dutsen, ya zubawa wuri ɗaya ido, kansa kamar ya tarwatse haka yake ji, ga ƙirjinsa kamar an ɗora masa dutse, da ƙyar yake iya numfashi, ga jikinsa sam babu ƙwari, banda kashe masa jiki babu abun da ƙwayoyin nan suke yi, soyake yayi bacci mai sunan bacci, ko" ya manta komai da yake cikin ƙwaƙwalwarsa amma abu ya gagara. """Madaki! Indabo!"" Ya faɗa a hankali yana sunkuyar da kai, ya ɗaga kai kamar a mafarki ya" "hangota, ta sauka daga adaidaita sahu, sai waige-waige take yi, yana saman dutsen sosai, dan haka yana hangota. Ta tsaya tana kallon hanya, in da yake take facing, amma ita ba ta ganinsa." "Dogon hijjabi ne a jikinta yau, a hankali take tafiya tana cigaba da waige-waige, mamaki ne ya kama shi, me kuma ya dawo da ita wurin nan yau? Zuciya ce ta tinziro shi, ya ji kamar ya sauka ya je ya naɗa mata shegen duka. Mata halin su ɗaya, cin amana 'yar madarar sa ce kawai ta fita" "daban sai umminsa, ta sace masa waya ta gudu, ta saka an kama liti, saboda tsagwaron rashin" "kunya ta sake dawowa, ko uban me ta dawo yi oho?." "Hakan ya ƙara tabattar masa he's not safe, za ta iya kawo jami'an tsaro su kama shi, sai dai kash," "shi ba ya fargabar a kama shi, a kama shi ko a ƙyale shi, shi ba wannan ne a gaban shi ba yanzu." "A yau ma ba ta iya gane hanya ba, bulayi take ta yi, tana nema, amma ta kasa ganewa." "Babu tsammani suka yi kiciɓis da ɗan mama, ya kalleta ta kalle shi, ya ce ""Ke! Me ki ke yi a nan" "wurin?""" "Ta ce ""Yauwwa, kai ne wanda na gani a gidan Viper ranar ko?""" """Ke, ki ka kuma kama sunansa, sai na ƙara wa ƙofar bakinki faɗi wallahi, kar ki sake ambatar" "sunansa ko ki kama sunansa""." "Nabila ta ce ""Tom, ba zan sake ba, dan Allah taimakona nake son ka yi, ganinsa nake son yi dan" "Allah""" "Ɗan mama ya ce ""Ka ga wata mayyar kuma, baki ji kashedin da yayi miki ba kenan? Kin ɗauka" "da wasa yake yi da ya ce ""Ya sake ganinki zai kashe ki, kin san waye Viper kuwa?""" """Ba zai kashe ni ba, muhimmiyar magana nake son mu yi da shi, na san na yi muku laifi, ku yi haƙ" "uri dan Allah, ka taimaka mini ka haɗani da shi dan Allah""" "Ɗan mama yayi mata wani irin mugun kallo ya ce ""Ya aka yi ki ka san ba zai kashe ki ba?""" """Viper ba ya kashe mutane, mussaman mata da ƙanan yara, dan Allah ka haɗa ni da shi na kasa" "gane gidan""." """Ke bar nan wurin, na haɗaku ki saka a kama shi ko, to ta Allah ba taki ba, wuce ki bar wurin nan""" Ta sake marairaicewa za ta yi magana. "Ya zaro wuƙa ya ce ""Idan shi ba ya kisa ni ina yi, ware ko na zaro hanjinki yanzun nan"" wuƙar sai" "ƙyalli take yi, ya fara tunkarota, yana wulwula wuƙar, ba shiri ta juya, gwiwa a sanyaye ta bar wurin." "Har ta miƙe ta ɓacewa ganin Al'amin yana hangota, ya miƙe ya kwanta a kan dutsen, ya lumshe idanunsa rana tana dukansa, yana jin yadda zafin ranar ke ratsa shi, yana ƙara masa ciwon kai," amma ba shi da niyyar tashi. *** """P.A""" """Na'am honorable""" """Ka tabattar binciken da ka yi a kan yarinyar nan daidai ne, babu kuskure a cikin sa?""." "P.A ya jinjina kai ya ce ""Babu fa, ka san ba na yadda a samu kuskure a irin wannan lamarin," "mussaman a irin wannan ƙadamin, ba a samu kuskure ba, yadda na gaya maka hakan ne""" "Ya jinjina kai ya ce ""Shikenan, ina ita ƙawar ta ta, ana cigaba da bibiyarta?""" """Eh, a wurinta muka samu wasu abubuwan ma""" "Indabo ya ce ""Haryanzu ina mamakin yadda aka yi ta ce ayi mata bincike a kaina ne, shiyasa nake" "ta tantama anya ka yi binciken a kanta dai-dai?""" "P.A ya ce ""Haba honorable, ya ma za ayi wannan ƙaramar alhakin ta yi wani bincike a kanka," "wataƙila hakan yana da alaƙa da harkar siyasa ne kawai, ko kuma sakata aka yi""." """Ba ita ce a gabana ba, Viper mai zamani, shi ne babbar barazanata, shi ne damuwata, ku cigaba" "da aikinku kawai, duk abun da ake ciki, ka din ga sanar da ni """ "P.A ya ce ""In sha Allah, ai yaronsa ɗaya yana hannu, sai dai na bincika an ce Haryanzu bai yi" "magana ya faɗi in da yake ba""" "Indabo ya ce ""Ƙyale 'yan sandan nan, sonake na riga su samunsa, idan na riga su kawai kashe shi" "za ayi salin alin, duk madaki ne yayi mini shirme wallahi, amma yanzun ma komai zai daidaita""" """Kar ka damu honorable, ai kai maganin kowane shege ne a ƙasar nan, ba ma ɗan daba ba, zamu" "yi maganinsa, amma da alama kamar kana da maguatan ɓoye, da suke tallafa masa""" """Na sani, amma yanzu duk ba wannan ba, a cigaba da abun da yakamata""" "P.A ya ce ""To shikenan, na barka lafiya """ "Bayan fitarsa Indabo ya shiga cikin gidansa, ya tarar da Abdul a falo, tare da mahaifiyarsa." "Ya kalli indabo ya ce ""Welcome""" """Thank you"" ya zauna ya kalli Abdul ya ce ""Dama nemanka nake yi""." "Abdul ya ce ""To gani""" """Ya maganarmu ta rannan?""" """Daddy maganganun namu ai da yawa, wacce daga ciki?""." """A'a, ka san wanda suka fi muhimmanci ai, mun daddale da jam'iyya, kai za a tsayar mataimakin gwamna, tun yanzu yakamata ka fara harkar campaign, da buga pastoci. Amma ka san dole ka daina duk wani shashanci da kake aikatawa. Sannan maganar da nake yi, maganar aure, shekara talatin da biyar, uban me ka ke jira? Muddin lokaci ya cigaba da gabatowa, abokan adawa suka san baka da aure, sai ku samu matsala a harkar takarar nan, amma da na yi maganar auren sai ka" "din ga gocewa""" "Ya ɗan tsuke fuska ya ce ""Wai constitution ne ya ce dole sai mutum yayi aure zai yi shugabanci" "meye amfanin auren mutum a cikin siyasa to?""" "Indabo ya ce ""Ban sani ba, idan ba zaka yi ba, ni ina da wadda zan haɗaka aure da ita, ga 'ya'yan" "abokai da yan uwa nan sai dai ka ji an yi""." "Hajiya Bilki da tun ɗazu ba ta yi magana ba sai yanzu ta ce ""Haba distinguish, ka bi shi a hankali" "mana, zai yi, ba sai an yi masa dole ba""." """Ba zan bishi a hankalin ba, na gaji da wannan shirmen nasa, rayuwarku nake ƙoƙarin ingantawa," "wataƙila idan ya zama mataimakin gwamna, shi ya fi ni samun dama, ya kuɓutar da ɗan uwansa""." "Hajiya Bilki ta ce ""Distinguish, kai da ka fishi daɗewa a harkar, ba ka samu yin hakan ba sai shi," "ni na karaya da lamarin jafar""" """No, kar ki yi mamaki ya fi ni samun authority, da damar fitar da shi, da dai a nan Nigeria ne, da" "tuni an daɗe da wuce wurin""" "Ta ce ""Haka ne, Abdul dole ka yi haƙuri ayi maganar auren nan, tun yanzu za a fara share fagen" "samun damar yin nasarar ka, dan idan ku ka gama tenure ku, kai zaka yi gwaman nan gaba""" "Cikin sangarta ya ce ""Mummy ba ƙi na yi ba, auren ne ba na so""" """Aikuwa haka zaka yi haƙuri"" suka cigaba da tattaunawa a kan yadda tsare-tsaren za su kasance." *** "DSP Nasir na tsaka da aiki, aka sanar da shi yayi baƙuwa, ya ce ace ta shiga, tana shiga ya ga Nabila." "Yayi murmushi ya ce ""Ke ce baƙuwar dama?""." """Eh mana, ko na koma ba ka san ganina?""" """A'a ni na isa na na ce haka. Zauna bari na kawo miki lemo, daga wurin aiki ko daga ina?""" "Nabila ta kashingiɗa ta ce ""Na je wani trial ne""" "Ya ɗaukko mata ruwa a fridge ya ce ""Sannu""" "Ta ce ""Yauwwa"" ta karɓi ruwan ta sha, ya ce ""Amma kin bawa kanki wahala da yawa, wace" "court ɗin ki ka je, har ki ka iya biyowa nan?""" "Ta ajiye robar ruwan ta ce ""Wani wuri na je, na ga wani client, DSP""" """Na'am barrister Nabila maitama """ "Tayi murmushi ta ce ""Wai ina mutumin nan?""" "Ya ce ""Wanne?""" """Wanda ku ka kama, haryanzu bai faɗi in da Vipern yake ba?""" """Ina fa zai faɗa, yana ta wahalar da mu""." """Dan Allah ka nuna mini shi""" """Ki yi masa me?""" """Babu komai, ganinsa kawai zan yi""" "Nasir ya ce ""To bari na gama aikina, sai mu je ki ganshi""" "Nabila ta zauna ta jira Nasir ya gama abun da yake yi, ta ɗauki jarkar ruwanta suka fito, yana ta nuna wa abokan aikinsa ita, yana gaya musu ita yana gaya musu ƙanwarsa ce, lawyer ce. Suka" "gaggaisa da abokan aikinsa, sannan suka ƙarasa in da liti yake." "Laɓensa duk ya bushe, saboda yunwa da ƙishirwa, yana ganin Nabila ya ganeta ya ƙura mata ido," "ta kawar da kanta ta ce ""DSP tun da ya ce bai san in da yake ba, haka zaku cigaba da ajiye shi?""" """Eh har sai ya yi magana tukuna""" "Ta girgiza kai ta ce ""Amma a doka, ai kotu za a kaishi ko a sake shi, ina ga fa tun da ya ce bai sani" "ba, bai sani ɗin ba""" "Nasir ya ce ""Ya sani ba zai yi magana ba ne"" ta miƙa wa liti ruwan hannunta, ta ce ""Ga ruwa""" "banza yayi mata, Nasir ya juya ya fita yana amsa waya daga wurin ogansa." "Tayi ƙasa da murya ta ce ""Na san na yi muku laifi, amma dan Allah ka yi haƙuri, zan san yadda" "zan yi ka bar wurin nan""." "Ta ciro wani ruwan a jakarta ta bashi, ta ce ""Dan Allah ka yi haƙuri, na fahimci kuskuren da na yi," "ban kyauta ba amma zan gyara komai""" "Nasir ya dawo ya ce ""Mu tafi?""" """Eh, amma gaskiya, yakamata a san abun yi, kar a taka doka da yawa""" "Ya ce ""To masu doka, mu je gida""" """Da gaske fa nake, ko mu shigar da hukumarku ƙara""." "Ya mayar da abun wasa, suka tafi gida." *** "Ƙarfe huɗu na yamma, Nabila ta shirya ta fita, ta tafi gidan matar da aka ce an yi laifin fyaɗen nan a gidanta." "Ganin Nabila cikin shiga mai kyau, ya sanya masu gadin ba su tsaya tuhumar wacece ba, suka" bata damar shiga gidan. "Sai da haushi ya fara kamata, saboda jiran da aka bar ta tana yi, daga baya matar gidan ta fito," suka gaisa da Nabila. "Nabila ta ce ""Na san baki sanni ba, sunana barrister Nabila Yusuf maitama, lawyer ce ni mai zaman kaina. Akwai mai gadin gidan nan malam isyaku, da ake accusing da laifin fyaɗe, ni ce" "lawyer sa. Na zo ne dan Allah in ji details ɗin abun da ya faru""." "Matar ta tsuke fuska ta ce ""Ke, ni ki ka zo ki yi wa wannan tambayar? Wurin 'yan sandan na je na fara karɓar report, an ce na dawo station ɗin da aka fara case ɗin, amma na ga dacewar fara zuwa gidan nan, tun da an ce yarinyar 'yar aikinki ce, kuma ainihin wanda ya yi laifin kina da alaƙa da shi, ku ka yi framing ɗin sa aka ce shi ne. Yanzu duk ba wannan ba a matsayinki na uwa kuma 'ya mace nake so mu fara magana. Ina yarinyar take? Ina ne gidan iyayenta? Ban damu da sanin koma" "waye yayi laifin ba, fatana kawai a wanke mai gadi, tun da kun san wanda yayi laifin """ "Matar ta miƙe ta ce ""Ki koma wurin jami'an tsaro, su zaki yi wa wannan tambayar, kuma ba ki da" "wata hujja, da take tabattar da ba shi yayi ba, idan kin gama kina iya tafiya""" "Nabila ta miƙe tsaye ta yi murmushi ta ce ""Na gode sosai antyna da bani lokacinki"" ta juya ta fice." "Station ta sake nufa, wanda a nan aka fara case ɗin, aka nemo statement ɗin da aka rubuta, da sunan Asibitin da aka kai ramma, na cikin gari, tana tsaka da dubawa, wanda yake evening duty, shugaba a wurin, ya fito afujajan, ya ƙwace file ɗin wai ba a ba su damar su bata file ɗin tayi" bincike ba. "Cikin mamaki da takaici Nabila ta ce ""Waye zai bayar da damar, bayan wadda ƙasa ta bayar, lawyer ce fa ni, dan me za a hana ni damar dubawa, doka ta bani damar neman hujjojin da zan" "gabatarwa kotu, na wanda zan kare, yaya za ayi a hana ni""" "Fafur suka hanata, suka ce ta tafi, ta kira Nasir a waya, amma wayarsa ta ƙi shiga, ranta yayi" mummunan ɓaci. "A gajiye ta koma gida, ana ta kiraye-kirayen sallar magariba, ta yi wanka tayi salla, ta ɗaukko" wayarta ta kira sumayya. """Ke ya ki ke aikin?""" """Sumy raina a ɓace yake, kin san menene?"" Sumayya ta yi sauri ta katse wayarta, ta saka a Flight" "mode, ta ɗauki wayar ummanta, ta kira Nabila ta ce ""Sorry wayar ce caji ya ƙare""" Nan ta labartawa Sumayya abun da yake faruwa. "Sumayya ta ce ""In dai ƙasar nan ce, ai kaɗan ki ka gani d....." "Cikin sauri Nabila ta katseta ta ce ""Sumayya few months back, ina wannan case ɗin da yaya" "murtala ya saka, har aka kusa korarsa? The case are similar""." "Sumayya ta ce ""How?""" """In so many ways, dan Allah ki sake binciko mini labarin, ko ma ki haɗani da yaya murtalan, ke zan ma zo na same shi, the same yadda matar ta ce an yi wa yarinyar fyaɗe, ɗan yayan matar gidan, shi ma dattijon nan haka ya ce mini, ɗan yar matar gidan ne yayi abun ba shi ba ne ba, shi asibiti kawai suka kaita, da shi da ɗaya mai aikin da wani mai yi musu hidima a gidan, definitely" "duk case ɗin ne but i want to confirm""" "Sumayya ta numfasa ta ce ""Ban ƙi ta taki ba, amma ki bi a hankali, kin ga a kan case ɗin, sai da" "Murtala ya kusa rasa aikinsa, ke daga ji kin san case ɗin babba ne""" """Sumayya tsoron da muke ji, da ja da baya shi ke saka wasu ma suke Fuskantar irin matsalolin," "idan na gama bincike na, i will raise the case, hatta 'yan sandan nan da abun da suka yi mini, duk sai na yaɗa, just support me sumy, Allah zai taimekemu, ke 'yar jarida ce, zaki iya kema""." "Sumayya ta ce ""Haka ne, amma kar ki kira ni a wayata, zan ki ra ki da wani layin, sai mu haɗu da yaya murtalan"" ta yi wa sumayya godiya, tana sake bawa kanta ƙwarin gwiwar lallai za ta tsaya" wa wannan dattijon kuma za ta yi nasara. *** "Abdul ne yake kallon ramma, yadda duk take a takure, tana kallon tv, amma hankalinta ba a kan tv" yake ba. """Rahama""" """Na'am"" ta amsa tana kallonsa." """Meyake damunki ne?"" Tayi shiru ta sunkuyar da kai." "Ya kwanta a kan cinyarta, ya ɗora ƙafarsa ɗaya kan ɗaya yana danna remote." "Ya tashi ya ce canzo hijjabinki ki zo, ta yinƙura jikinta na rawa, ta sako hijjabi, ta fito." Ta tarar da shi a tsaye da mukulli a hannunsa yana waya. "Ta ƙaraso jikinta yana tsuma, tunaninta ko gida zai mayar da ita, ya riƙe hannunta, ya buɗe ƙofar" falon suka fito. "Da kansa ya sakata a mota, ya rufe sannan ya zagaya ya kunna motar ya fita da ita." "Sai kallon gari take yi, duk da dare ne ko ina da hasken fitila, tun da ya kawota a sume, ba ta sake" "fita ba, kuma ba ta san a ina take ba." """Gida zaka mayar da ni?""" "Ba tare da ya kalleta ba ya ce ""Ai na ce ki daina wannan tunanin ma""" "Cinema ya kaita, wai kallon film, bayan tv suka baro a gida, ta din ga waige-waigen yadda za ta yi ta gudu, amma a in da suke zaune, yana rungume da ita, ga wurin duk ƙabilu ne, abun da ta" "fuskanta, ba iya cinema ne wurin ba, dan daga can wani wuri, kaɗe-kaɗe na tashi." """Naga ki na ta waige-waige, ba mahaukaci bane ni, da zan kawo ki inda zaki iya guduwa, ko ki yi" "wa wani magana ba, kowa sabgar gabansa kawai yake yi a wurin nan, gara ma ki nutsu""" "Tayi ajiyar zuciya ta ce ""Ko bangon duniya zaka kai ni, idan Allah ya yi niyyar fitar da ni ba ka da" "dabara""." "Yayi murmushi kawai, sai da ya gama abun da yake yi, ya ɗauke ta, suka tafi ya kulleta a mota, ya" "sayo mata abinci, ya mayar da ita in da suke." *** "Nabila kuwa tana ta bin kwatancen da dattijon nan yayi mata, na gidan zulai ɗaya mai aikin da" "suke aiki tare da ramma, amma ta kasa gane kwatancen, ganin ta gaji, kuma ta hanyar ake bi, a je in da Viper yake, ya sanya ta tare abun hawa, ta sake tafiya." "A wannan karon da ta sauka, google map ɗin ta buɗe, tana duba abubuwan da suke wurin, ba tare da gazawa ba, ta cigaba da yawon bulayin neman gidan, cikin sa'a bayan shafe mintuna talatin" "tana bulayi, ta hango gidan." "Wata irin ajiyar zuciya ta yi, sannan ta nufi gidan." "Ƙofar gidan a rufe, ta saka hannu ta tura ƙofar, tayi sallama." "Ƙofar ta buɗe, sai dai ba ta ji motsi ko alamar mutum a gidan ba." "Duk da gabanta faɗuwa yake yi, amma haka ta ke ta addu'a ta shiga. Tsakar gidan ko ina shirgi," "can bokiti, ga tukunya can kaya sauran sigari tsakar gidan kaca-kaca." "Ta ƙarasa ta leƙa ɗakin, ta hango Viper durƙushe a kan gwiwarsa, yana ƙoƙarin yi wa kansa" "allura, sai dai hannunsa sai rawa yake yi, gashi ya huda jijiyar, jini ya fara zuba." "Da sauri ta ƙarasa, ta durƙusa, ta gyara masa sirinjin, ta cigaba da zuba masa ruwan allurar." "Rintse idanunsa yayi, jin yadda allurar take ratsa jikinsa." "Babu tsammani, ta zare sirinjin ta ce ""Wannan abun da ka ke yi, zai iya shafar ƙwaƙwalwarka fa"" ba ta gama maganar ba, ta ji ya faɗo a jikinta, ta faɗi a wurin saboda nauyinsa, ƙoƙarin ture shi" "take yi, dan ji ta yi tamkar wani ƙaton dutse ne ya faɗo mata." "Ya ɗago idanunsa ya kalleta, ya saka hannu ya shaƙe wuyanta." "Numfashinta ya fara fita sama-sama, ta rirriƙe hannunsa idanunta suka yo waje." "Walid ne ya faɗo ɗakin da gudu, ya fara ƙoƙarin janye Viper daga kanta." "A tunaninsa jikin Viper yayi sakin da zai ture shi kawai, amma ya ji da ƙwarinsa." "A wahale ta ce ""Zaka kashe ni fa"" a hankali ya saki wuyanta, Walid ya ɗago shi da ƙyar, ya kalli" "walid, ya kalleta ya sake mayar da idonsa kan Walid da ƙarfin gaske ya ce ""Walid""" """Na'am Al'amin""" """Walid matata, matata walid! Ɗa na Walid mata ta"" yayi maganar yana wani irin ƙaraji, tare da" jan rigar walid da ƙarfin da sai da ta yage. """Easy maza, easy yi haƙuri""" """Walid zan haukace, walid kaina zai tarwatse, me zan yi ne wai, ka fitar mini da yarinyar nan, ba" "na son ganinta matata walid"" yayi maganar yana girgiza kansa." "Nabila ta tashi da kyar, tana ta haki, ta ce ""Zaunar da shi zan yi masa magana dan Allah""" "Walid ya ce ""Ɗauki jakarki ki tafi, yi sauri""" "Kawai Viper ya shammaci Walid, ya buga kansa da ƙarfi a jikin bango, take jini ya fara biyo" "hancinsa, ya faɗi ya suma a wurin." "Nabila ta ƙwala ihu, saboda sautin da kansa ya bayar, da ya buga kan, Walid ma a rikice ya ɗago" "shi, amma ko motsi baya yi." Ayshercool. 08081012143 ₦500 ne via 0009450228 Aisha Adam jaiz bank sai shaidar biya ta 08081012143 Wanda za su jira document 1K ne. 90009343 'Yan Nijar ku turo katin airtel na 300fcfa Arewabooks ayshercool7724 "Cikin matsanancin tashin hankali Nabila ta nufe su, Walid ya rikice, ya rasa me ma yakamata ya yi" ya taimakawa Viper. "Cikin azama Nabila, ta ɗaga kan Viper yana kallon sama, ta ciro hular kanta, ta toshe hancinsa da yake zubar da jini, ya zamana ta gefen bakinsa yake numfashi." "Cikin kuka ta kalli walid ta ce ""A kai shi asibiti mana, ya bugu da yawa, tun da abun ya kai ga" "zubar da jini ta hancinsa""" "Walid ya ce ""Ba za a kai shin ba, uban waye ya ce ki kuma zuwa ai duk ke ki ka ja?""" "Cikin rashin fahimta ta ce ""Ni kuma? Ni me na yi? Zuwa na yi na bashi haƙuri a kan abun da na yi bisa kuskure, wallahi ban yi masa komai ba, tarar da shi na yi yana yi wa kansa allura jikinsa yana rawa, na karɓa amma wallahi ban yi masa komai ba. Ko duk haushin abun da na yi wa ɗan uwanku ne? Na je station ɗin ai, kuma na yi magana da shi, dan Allah ku yi haƙuri rashin sani ne ya sanya na aikata abun da na yi masa, abun da ake faɗa a gari a kansa daban, ni kuma ban san" "gaibu ba, amma dan Allah ku yi haƙuri"" tayi maganar hawaye wani na bin wani a fuskarta." "Walid ya ce ""ya isa haka, tashi ki tafi""" """A haka za a bar shi, ba zaka kai shi asibiti ba?""" """Ta yaya zamu kaishi asibiti ana nemansa a kama shi?""" "Fizge-fizge Viper ya fara yi, yana ƙoƙarin tashi, Walid ya daddane shi, cikin ɗaga murya ya ce" """Walid""" "Ya ce ""Na'am Al'amin""" """Liti"" walid ya ce ""Ya shiga banɗaki""." "Viper ya sake cewa ""Mai laya""" """Na kiyayi mai zamani, Allah ya ƙara maka lafiya""" """Gobe zamu je asibiti da ƙanwarka 'yar madara, sun ce inducing za su yi mata 'yar madara za ta" "haihu, ragonta yana ƙauye wurin Hajiya""" "Walid ya ce ""Masha Allah, Allah raba su lafiya""" """Walid""" """Na'am mai zamani""" """Cikin nan yana ba ta wahala, nima na ƙagu ta haihu, na ga yarona, sunan ƙanina nura zan mayar," "idan ta kuma haihuwa na saka sunan Sadik""." "Walid ya ce ""To Allah ya kawo mana su lafiya da albarka""" "Wani irin ihu ya hau yi, yana ƙoƙarin ture Walid, cikin ƙaraji ya ce ""Walid matata ɗa na, ba zan" "iya komai ba, ka riƙe madaki, kar ya illata mini mata, ka riƙe shi walid wai me ka ke yi ne?""" "Sosai suke kokowa da Walid, ga hancinsa na cigaba da zubar da jini, ga damuwa da fita hayyaci a" dalilin allurar nan. "Walid ya ce ""Sai na ci uban ɗan mama idan ya dawo, bai ji me na gaya masa a kan kawo maka" "kayan maye ba, sai ya saka mun yi babu ka rasa ƙwaƙwalwarka tukuna""." "Nabila kuwa iya ƙarfinta take kuka, tsananin tausayinsa ya mamaye zuciyarta, da ƙyar walid ya danne shi, a hankali jikinsa ya saki, ya daina motsi, amma yana motsa idanunsa, a buge yake ya fita hayyacinsa amma ba bacci yake yi ba, abubuwan da suka wuce ne suke dawo masa cikin" mayen. "Nabila ta ce ""Dan girman Allah ka gaya mini ƙarashen labarin nan, ina jauhar ina abun da yake" "cikinta?""." "Walid ya ce ""Kin ga ni ba wannan ne a gabana ba, lafiyar ɗan uwana da taya shi ɗaukar fansa ita na saka a gaba, dan haka ki tashi ki tafi kawai""" "Nabila ba ta sake magana ba, ta tashi jiki a sanyaye, ta ɗauki jakarta, har ta kai bakin ƙofa, ta waiwayo ta sake kallonsa, hakan yayi dai-dai da buɗe idanunsa, sun yi jawur gwanin ban tsoro, ya" "tsura mata ido, a hankali ta juya ta fice." "Cikin maye ya ce ""Mai laya""" """Allah ya taimaki mai zamani""" """Ba na son ganin yarinyar nan, zan iya fara kisan kai a kanta""." "Walid ya girgiza kai ya ce ""Ba ka taɓa yi ba, kuma ba zaka fara a kanta ba"" surutan da Viper ya" "cigaba da yi ne, ya tabattar wa da Walid ba ya cikin hayyacinsa." *** "Ramma ta na zaune, ta na cin farcenta, tana zancen zuci, ta ji Abdul ya kama hannunta. Sai da ta firgita, kasancewar tayi zurfi a zancen zuci." "Hannunsa riƙe da nail cutter, ya fara cire mata faratan ya ce ""Ƙazama kawai, da baki ki ke cin" "farce"" janye hannunta ta yi ta ce ""Ni kar ka shafa mini cuta"" tayi maganar tana haɗe rai." """To cuta ta nawa kuma, in dai ina da ita da tuni kin ɗauka ta can wurin. Duk rashin ji na, ina using" "protection, a kanki ne kawai nake gaba gaɗi, shi ma dan na san am safe na killace ki"" tsaki ta yi ta kawar da kanta gefe." "Ya kama hannunta, ya cigaba da yanke mata farcen ta ce ""A banza, wallhi ko haɗiyeni zaka yi, ka" "fito da ni, ba zan yafe maka zaluncin da ka yi mini ba""" "Bai kalleta ba ya ce ""Dama ban ce ki yafe mini ba ai"" ya na cikin yanke mata, ta ga yana ɗan yamutsa fuska, ya gama ya tashi ya koma ɗaki, ta kalli falon komai tsaf solomon yake gyarawa, a ranta ta ce ""Dama aure ne da ni, ace nan gidana ne ba wannan ƙazantar ba. Tunanin hakan kawai" ya saka idanunta cika da hawaye. "Ta ɗaukko magazines ɗin da ke falon, tana ta kalla, har ta manta da shi a gidan, ta shiga bedroom" "ɗin, ta tarar shi a kan gado yana murƙususu." "Ta kalleshi ta ce ""Menene?""" "A wahale ya ce ""Kira mini solomon"" ta juya ta fita, ta kiro shi." Ya ɗaga kai ya ce masa ya kawo masa biro da takarda. "Ya kawo masa, yayi rubutu a jiki, ya ce yaje ya sayo masa." "Solomon ya fita cikin sauri, ta kalleshi ta ce ""Wai menene?""" "Ya ce ""Epigastric pain ne""" """Me kenan"" ya nuna mata cikin sa." "Ramma ta ce ""Sannu Allah ya sa mutuwa zaka yi na huta""" "Yayi mata shiru, ya cigaba da juyi, ya dunƙule hannunsa yana dukan gadon a hankali, yana yi yana" miƙa alamar yana jin jiki sosai. "Ta tsaya tana kallonsa, gumin da yake yi, ya sake tabattar mata ya fara galabaita." "Yayi mata nuni da hannunsa ta je, ta ce ""In zo in yi maka me?""" "Girgiza kai ya hau yi, yana kiran ""Mummy, rahama cikina am in pain""" """To sannu""" "Ta samo jarka da ruwa, ta tofa masa bisimillah ƙafa 19, da suratul fatiha ƙafa 7, ta hau kan gadon ta ce ""To tashi ka sha ruwa"" ya tashi da ƙyar ya karɓa, ya shanye, yayi jifa da jarkar, ya kwanta a" "kan cinyarta ya ce ""Rahama cikina""" """Allah ne yayi maganinka, a cikin sakans idan ya ga dama, zai rabaka da rayuwarka, ka ga idan" "mutuwa zaka yi, ga saɓo kana yi, ga zaluncin da ka yi mini, Allah ya sa ka mutu""." "Abdul ya ce ""Da na mutu shahidi, ciwon ciki ne ya kashe ni, kuma ƙarshe ace ke ki ka kashe ni""." """Ko shahidi ka mutu kan ka shiga aljanna, sai ka shiga .... Sai kuma ta yi shiru. ""Allah dai sai ya ƙ" "watar mini hakkina a wurinka na zalunta ta da ka yi""" "Solomon yayi knocking, Abdul ya ce ya shigo, ya shigo da leda a hannunsa, Abdul ya karɓa, ya sakawa kansa butterfly needle, ya saka ramma ta haɗa allurar da aka kawo, ya ce tai masa." """Ni ba zan iya ba, tsoro nake ji""" """Tsoron me malama, ciwo zai kashe ni""" """To ni taɓa yi na yi?""" "Cikin tsawa ya ce sai ta yi, hannunta na rawa, ta zuba allurar a cikin butterfly needle ɗin." "A haka ya nuna mata yadda za ta saƙala masa ruwa, yana yi suna faɗa, ta saka masa ya sa hannu ɗ" "aya ya janyota, ya sake kwanciya a kan cinyarta." "Yadda yake wash wash da kiran sunanta, sai ya ƙular da ita kamar ba namiji ba." """Ni ka daina kiran sunana tun da ba ni na ɗora maka ba""" """Wash rahama cikina"" tsaki ta yi ta ce ""Wai shekarunka nawa?""" """36yrs"" yayi maganar yana kallonta." """Amma an yi asarar ƙuruciya, idan ba ka yi wasa ba kana cikin wanda annabi ya ce kun yi asara, ka tafiyar da ƙuruciyarka a shirme da shashanci, a mintuna ashirin ɗin nan da Allah ya ga dama, da yanzu babu kai, me zaka ce wa Allah, ka sha giya ka kwana kana zina da 'yar da ka raba da" "uwatta, ka canza tunani da halaye, ko Allah ya yi maka rahama""." "Ya lumshe idanunsa ya yi shiru, bai ce mata komai ba." *** "Nabila kanta tamkar zai tarwatse ita ma haka take ji, so take ta kamo bakin zaren tallafawa Viper. Babban abun da yake buƙata yanzu rehabilitation ne, a fara nesanta shi da shaye-shaye, sannan a kwantar masa da hankali da ƙoƙarin tirsasa masa karɓar ƙaddararsa ta hanyar da ya dace. Sannan a fuskanci kamo zaren tsaya masa, ya ɗauki fansar abun da aka yi masa ta hanyar doka, ba ta hanyar da yake tunanin ɗauka ba, sai dai alamu sun nuna mata ba zai sarrafu cikin sauƙi ba, balle a samu fahimtar juna da shi, sai dai ta ƙudurce a ranta, duk tsanani da wahalar lamarin, za ta tsaya" "a kan sa, ko da kuwa sanya rayuwarta cikin hatsari ne, za ta yi domin taimakon Viper." "Sai dai hakan ba zata yiwu ba, sai ta ji ƙarshen labarinsa, amma ta yaya?. Da ta tuna yadda yake" "kururwa yana kiran matarsa, ɗansa sai ta ji ta karaya, tausayinsa ya ƙara kamata." "Ringing ɗin wayarta ne ya katseta daga tunanin da take yi, ta ga lambar sumayya, ta ɗauki wayar" ta kara a kunnenta. "Sumayya ta ce ""Na yi wa Uncle murtala kwatancen gidanku, zai zo ya same ki, sai ku yi magana""." "Nabila ta ce ""Kai sumy, ban da ni ki bari na je na same shi, ni da nake nema?""" "Sumayya ta ce ""Ya zo ya same ki is more safe, ba wanda zai kawo wani abu, kin san yanzu" "rayuwa babu tabbas mussman irin aikinmu""." "Nabila ta yi murmushi ta ce ""Hakane masoyiyya, na gode sosai, saura ɗaya aikin""" """Wanne kenan?""" """Waye indabo?""" """Kin ga ki raba kanki da indabon nan, wai me ki ke nema a kansa ne? Ba dai kin yi masa wulaƙ" "anci kin ƙi gaishe shi ba, menene na bibiyarsa""" "Nabila ta yi murmushi ta ce ""Ba zaki gane ba, ki taimaka kawai""" """Nabila kamar kina ɓoye mini wani abu fa""." """Ba abun da nake ɓoye miki, mamakinki kawai nake yi, duk kin canza kina abu kamar mara" "gaskiya kwanan nan sumayya""" "Dummm gaban Sumayya ya faɗi ta ce ""Ban gane ba""" "Nabila ta yi dariya ta ce ""Kar ki manta fa ni lawyer ce, idan na so zan gane idan ma baki da" "gaskiya, don't mind me kawai dai na ga kina ƙoƙarin kawar da maganar indabon nan ne, shiyasa nake tsokanarki, am about to do something big, zan gaya miki menene daga baya""" """Nabila Please, kar ki je ki yi abun da ba shikenan ba, ki raba kanki da duk wani abu da zai sake" "haɗa ki da Aminu Vipern nan, kar ma a cetare ku ke. Ki bar DSP yayi aikinsa dan Allah""" """Ni ba maganar Viper nake yi miki ba, case ɗin dattijon nan nake magana a kai, amma ki binciko" "mini maganar indabon nan, ko na binciko da kaina""." "Sumayya ta ce ""To shikenan na ji zan yi, amma ki san in da zaki din ga zuwa da abun da zaki din" "ga yi kin ji arfan Abba""" "Nabila ta yi murmushi ta ce ""Ji sai ka ce wata uwata, to na ji sai anjima"" ta kashe wayar tana murmushi, a duniya bayan Abba ba ta tunanin akwai wanda ya kai Sumayya damuwa da ita, da" "tsoron ta aikata wani abu, da zai janyo mata matsala." "Bayan sallar magariba, Murtala ya kirata a waya, ya sanar mata da ya zo, yana ƙofar gidan su." "Ta saka hijjabi ta fita, suka gaisa ya ce ""Sumayya ta ce ""Ki na nemana""" """Au ba ta yi maka bayani ba?""" "Murtala ya ce ""Tayi mini, daga bakinki nake son ji""." """Haka ne, ka ga wani case na samu, na wani dattijo, an yi framing ɗin sa, wai yayi wa wata yarinya 'yar aikin da yake gadi fyaɗe, na je na yi magana da shi, yayi mini bayani, ya ce ba shi bane ba, ɗan yayan matar gidan ne, so abubuwa da yawa are similar to rahoton da ka bayar" "kwanakin baya, shiyasa na ce bari na neme ka, ka ƙara yi mini bayanin yadda abun yake""." "Murtala ya numfasa ya ce ""Kin san duk abun da aka ce, harka ta manya ce, sai dai a lallaɓa a yi" "komai a ɓoye ko ba haka ba, an ce yaron nan ɗan manya ne, kar mu je ki yi wani abun da zaki" "sakamu a matsala fa""" "Nabila ta ce ""Uncle murtala, ba zan saka kowa a matsala ba, dattijon nan nake son na taimakawa," "kunna mini recording ɗin matar, na sake ji""." "Ya kunna mata recording, ta saurara tiryan-tiryan, Nabila ta ce ""Uncle murtala, case ɗin dai ai" "wannan, ba shi ne aka ce Naja'atu Bunkure ta shiga case ɗin ba, ai da na ce zan shiga case ɗin yarinyar""." "Ya ce ""Shikenan, faɗuwa ta zo dai-dai da zama, amma dan zatin Allah don't mention my name""." "Ta jinjina kai ta ce ""Kar ka damu in sha Allah ba zan yi mentioning ɗin ka ba. Naja'atu Bunkure" "ko da me take yawo a kanta, sai ta gaya mini in da case ɗin ya tsaya, ka san ina station ɗin da aka fara case ɗin, aka ƙwace file ɗin daga hannuna, wai ba zan duba ba""." "Haske su aka yi da fitilar mota, Nabila ta tura baki, tana kare fuskarta, Nasir ya gyara parking ɗin" "sa, ya fito ya nufo su." "Ta ce ""Yaya sannu da zuwa"" bai amsa mata ba, ya kalli murtala ya ce ""Malam ya dai, ya aka yi?""" """Yaya idan saurayina ne, haka zaka yarfa ni dan Allah? Abokin aikin sumayya ne, muna" "tattaunawa ne a kan wani case""." "Nasir ya sake tsuke fuska ya ce ""Kuma da daddaren nan?""" """Eh, saboda shi ɓoyayyiyar shaida ne, da ba zan bayyana shi ba, ba na kuma son a samu trace, na" "wani ya ganshi, shikenan uncle murtala ka gaida gida""" Yayi wa Nabila sallama ya tafi. "Ta cigaba da yi wa Nasir mita, ""Gaskiya yaya na fuskanci saboda kai wasu samarin namu suke" "tafiya, da haka za a aure mu, kana zare musu ido, kamar wasu 'yan ta'adda""." """Eh, gara a zare musu idon, su san nan ba wurin da za su zo su kawo wargi bane ba"" kawar da" "zancen ta yi, ta hanyar bashi labarin case ɗin dattijon nan, da yadda aka ƙwace file ɗin." "Sosai ya din ga mita, har yayi alwashin rakata sake komawa station ɗin, a bashi tun da tana" "lawyer, dole a bata dukkan haɗin kan da take buƙata." "Bayan ta koma ɗakinta, ta din ga murmushi itakaɗai, abu zai case zai haɗa ta da Naja'atu Bunkure, ""Sai na ga abun da ya ture wa buzu naɗi kuwa"" sai dai walwalarta ta ɗauke, bayan tuno wa da Viper, kar ta shagala da ramuwar gayya a kan Bunkure ta sakankance ta gaza samo mafita a kan" nasa case ɗin. "Tana buƙatar wanda zata tattauna case ɗin da shi matuƙa, amma ba ta ga wanda ya dace tayi maganar da shi ba. Dan ko da wasa ba zata tunkari DSP ba, balle sumayya tsfa zata ce za ta gaya wa Abba, dama ban da su biyun nan, ba ta wanda ya dace, ta sanarwa wannan gangancin da take" shirin yi ba. "Sai dai kwana ta yi, tana tunanin ko yaya Viper, ya farfaɗo gaba ɗaya ya warware ko kuma yaya?" "Washegari da safe, da DSP suka tafi station ɗin nan, a hanya yake sanar mata da an yi belin Liti, ta tambaye shi waye ya yi belin Litin, ya ce mata bai sani ba, waya kawai aka yi masa aka ba shi" umarnin ya sake shi. "Nabila ta ce ""Nigeria ƙasata""" "Suka isa police station, Nasir ya nuna musu id card ɗin sa, sannan ya nemi su bashi file ɗin da Nabila ta nema, amma suka tabattar masa da an zo an karɓi file ɗin an mayar da shi babbar" headquarter. "Nabila ta ce ""No wonder, hakan ya sake tabattar mini da lallai wanda ya aikata laifin, ɗan manya ne, kuma ba dattijon nan ne yayi ba"" ta cewa Nasir kawai su tafi dama ta san a zaman farko sai an" "aike da baba prison, kafin ta gama tattara hujjojinta." "Sai dai duk da haka, Nasir ya nemi a ba su in details, statement ɗin, da Asibitin da aka kai" "yarinyar, amma suka ce ba a ba su wannan umarnin ba, komai da komai yana babbar headquarter." "Suna tafe take ce masa ""Kar ka damu yaya, zan baka mamaki ƙoƙarin da zan yi a kan lamarin nan, zan tattara hujjojina na shiga kotu"" yayi murmushi tare da ccigaba da ba ta ƙwarin gwiwa, ya biya" ya ajiyeta a wurin aiki sannan ya tafi. "Cak ta tsaya a harabar wurin, tana ƙarewa motocin kallo, ta tsayar da idonta a kan baƙin motocin" "da ta gani guda uku, sai dai ɗayar ita ce motar da ta din ga bin ta, har ta tsaya tayi knocking ɗin glass. Ta ƙarasa ta zagaye motar, ta sake tabattar da ita ce, ta jinjina kai ta shiga." "Ta je office ɗin ta, ta ajiye jakarta, ta fita ta tafi office ɗin Barrister Habib, a hanya ta ci karo da" "MD barrister Kabir da wani babban mutum, da ta taɓa haɗuwa da shi a office ɗin sa." "Cikin girmamawa ta risuna, ta gaishe su, suka amsa, Barrister kabir ya ce ""'yar ƙwalisa in ji habib," "an shigo kenan?""" """Eh sir, na biya neman wata shaida ne, ban samu ba ma, na taho""" "Ya ce ""Sai haƙuri, haka lamarin aikin dama yake, wataran nasara wataran sai haƙuri, na ji daɗi da" "na ga kina mayar da hankali yanzu kin rage kwalliya""." "Mutumin ya zuba mata ido, yana ta murmushi kamar an yi masa kyautar kujerar makka, dan sai da" "ta faki idon Barrister kabir, ta galla masa harara, sannan ta yi gaba." """Yaya Habib""" "Ya ce ""Yau kuma?""" "Ta ce ""Eh mana, yau baƙi muka yi ne?" "Ya gyaɗa kai ya ce ""Dama wurin nan ai kullum cikin baƙi yake""" """Wasu motoci na gani, wata farar mota ta waye?""" "Ya ƙura mata ido sannan ya ce ""Hala na samu demotion ne zuwa mai gadi?""" "Tayi dariya ta ce ""Am very sorry, ka san wani abu?""" """Sai kin faɗa""" """Ka san shi Allah, mai son bawansa ne, da kuma jin ƙan sa""" "Barrister Habib ya ce ""Wannan haka yake""." """A wannan karon, ba tare da na yi tsammani ba, akwai yiwuwar case ya haɗani da Najar bunkure," "to kuma ka san ni yanzu kai ne mentor ɗina, na zo mu yi magana """ "Yayi dariya yana mayar da wasu files, drower gabansa ya ce ""Nabila 'yar ƙwalisa, haryanzu ba ki" "san wacece Bunkure ba ko?""" """And ba na buƙatar na sani, kawai i need your support, i want expose her hidden face to the world" """" """How?""" "Nan ta bashi labarin duk abun da yake faruwa, da case ɗin da yake hannunta." "Ya ce ""Nabila""" """Na'am barrister yaya Habib""" "Yayi murmushi ya ce ""Zaki ga yaya, aradu ki ke shirin tara da ka fa""" """Na shirya mata""." """Tana da wanda suka tsaya mata matar nan """ """Ni ma Allah ya tsaya mini""" "Ya jinjina kai ya ce ""Kin gama magana""" "Nabila ta ce ""Yauwwa barrister, and i want you to support me, dan Allah ka taimaka mini""" """Ba ƙi nayi ba Nabila, matar nan manyan mutane da manyan ma'aikata sun kasa ja da ita, ke kin" "san ba haka nan take ba""" "Nabila ta sake gyara zamanta ta ce ""Support me, you will be proud of me""" "Ya sauke numfashi ya ce ""Duk abun da ki ke buƙata na taimako, ki yi mini magana kamar yadda na taimaka miki ki ga file ɗin Viper, zan cigaba da taimaka ki, amma ya zama sirri tsakanina da ke"" tayi shiru tana kallonsa, ji tayi kamar ta yi masa zancen Vipern, sai dai a zuciyarta ta ji, ba ta gama amincewa da shi ba, kuma ba kowa za ta yi wa magana a kan case ɗin sa ba, dan haka ta yi murmushi ta ce ""Na gode Allah ya saka da alkhairi ya raya maka zuriya. Amma yanzu ya kake" "ganin za ayi? Office ɗin ta zan je, a kan ina son bayanai daga gare ta, da bakin yarinyar?""" """Eh mana, go as a barrister, ke ma lawyer ce, go with your full confidence""" "Tayi murmushi ta ce ""Na gode sosai ranka ya daɗe"" ta juya ta fita cikin farinciki." "Sai dai kuma tunanin Viper ya cika mata zuciya, ko yaya jikinsa? Ya warware gaba ɗaya ko" kuwa? "Ba tare da dogon tunani ba, ta ɗau jaka ta fita, ta samu mai sayar da fruit, ta sai uban kayan" marmari ta tari abun hawa ta tafi. "Sai dai ta sha wahala, tana ta bulayi, ga uban kaya a hannunta, ta kunna Google map, yau sai ya" "fara yi mata hauka ta ce ""Wai shi wannan ma anya ba aljani bane ba?""" "Har ta fitar da rai, kawai ta hango roofing gidan, haka ta cigaba da tafiya, har ta isa ƙofar gidan." "Duk da tsoro da fargabar waccan shaƙar da ta sha, na neman kashe mata gwiwa, ta tsananta addu'a" tare da neman kariyar Ubangiji. "Jin sallamar mace ya sanya gaba ɗaya suka ɗago suna kallonta, liti ya zabga ashar ya ce ""Ke" "uban me ya kawo ki nan, munafuka macuciya?""" "Ta ce ""Ashe kuma ka fito""" """Ban sani ba, uban me ya kawo ki?""" """Wurin Viper na zo"" ta bashi amsa kai tsaye. Ya tashi tsaye zai zare wuƙa, Walid ya hana shi, ya ce" "mata ""Me zaki yi masa, kin manta abun da yayi miki ne? Ki bar taƙama da baya kisan kai, zai iya farawa a kanki, dan yanzu ƙwaƙwalwarsa sai a hankali """ "Nabila ta ce ""Shi ne dalilin sake zuwana, in ji ya jikinsa kuma na ji ƙarshen labarin nan""" "Walid ya ce ""Jiki yayi sauƙi mun gode, amma ki tafi kar ki sake zuwar mana, saboda zuwan da ki" "ke yi zamu canza wuri""" "Liti ya fusata ya ce ""Ke dalla fita""" """Ka daina hantarata, ba wurinka na zo ba. Ni dai ku taimaka ku haɗani da shi, yakamata na ji da" "bakinsa ya yafe mink""" """Ke! Ni ki ke gaya wa haka?""" "Walid ya ƙara dakatar da Liti ya ce ""Ya riga ya yafe mikin ai""" "Ta girgiza kai ta ce ""Ban ga alama ba, akwai buƙatar sama masa nutsuwar ƙwaƙwalwa kafin tunkarar duk wani abu, a ɗan zuwan da na yi, na fuskanci kuna amfani da ƙarfi wurin tursasa masa karɓar abun da ya zo masa a yadda yake." "Baku da raunin, da zaku tausasa masa yadda yake buƙata""" "Walid ya ce ""Kamar yaya?""" """Kamar yadda nake faɗa yanzu, a fara samo ƙwaƙwalwarsa, ta hanyar daidaita gangar jikinsa, da hana shi ta'amalli da miyagun ƙwayoyi, a saita tunaninsa da tunatar da shi shi wanene, ko ba duka ba, ayi ƙoƙarin samar masa da wani abu na farinciki ko yaya, a gwada canza masa tunani ba ta ƙ" "arfin tsiya ba, kuma a sama masa likitan da zai din ga duba ƙwaƙwalwarsa""" "Walid ya ce ""Taɓ, ke zaki iya duk wannan ɗin?""" "Cikin ƙwarin gwiwa Nabila ta ce ""Ku bani dama, na san kuma a ba a karon farko ya karɓe ku ya" "saba da ku ba""." "Kafin wani ya kuma magana, ya turo ƙofa ya shigo." "Walid ya ƙure shi da ido, dan kar yayi wa Nabila wani abu, ko nuna ya ga mutum a wurin bai yi" "ba, balle ya yi wani abu, ya shige ɗakinsa ya nemi wuri ya zauna a kan katifa." "Babu fargabar komai, ta bi bayansa, tare da yin sallama a ɗakin, bai amsa ba kuma bai ɗago ba." "Ta je gabansa, ta durƙusa da gwiwoyinta a ƙasa, ta ce ""Ranka ya daɗe, wurinka na zo fa"" ya" cigaba da 'yan dube-dube. """Duk da na san, ba zaka amsa mini ba, amma na san kana ji na, wannan zuwan da na cigaba da yi, ina yi ne don neman afuwar kuskuren da na tafka bisa duhun kai, da rashin sani, amma dan Allah" "ka yafe mini ka yi haƙuri dan Allah"" tayi maganar muryarta na rawa." """Dan Allah ka yi magana, wallahi na kasa sukuni, a dalilin jahiltal abun da ya sameka, ban san" "haka abun yake ba, ka yi magana ka ce ka yafe mini please""" "Still bai yi magana ba, sai dai ya ɗago ya kalleta, hakan ya sanya ta saurin cire idonta daga nasa." "Ya miƙa mata hannunsa ya ce ""Bani""" "Jakarta ta ɗaukko ta buɗe, ta ɗaukko wayarsa, ta miƙa masa, ya saka hannu ya karɓa, sannan ya" "ce ""Sai da nayi kaffara a dalilin rantsuwa da na yi zan kashe ki, ban kashe ki ba, ki ka sake na sake rantsewa sai na aiwatar""" """Da kuwa ka ci amanar 'yar madara""" Ayshercool 08081012143 ₦500 ne via 0009450228 Aisha Adam jaiz bank sai shaidar biya ta 08081012143 Wanda za su jira document 1K ne. 90009343 'Yan Nijar ku turo katin airtel na 300fcfa Arewabooks ayshercool7724 "Cikin hanzari ya kalli Nabila, yana mamakin a ina ta san wannan sunan, dan sam bai san Walid ya" gaya mata labarin sa ba. "Ya ƙureta da ido, ta kawar da kanta gefe, ta ce ""Eh, idan ka kashe ni, ka ci amanarta, ta barka ka kusa dawowa hanya, amma ka koma ruwa fiye da baya. Zan so na ji ƙarshen labarinta, amma kafin nan bari na tafi yanzu, ga kayan dubiya nan na kawo maka, Allah ya ƙara sauƙi"" sai da ta" "gama maganar sannan ta ɗago ta kalleshi, still ita yake kallo." "Ta sake cewa ""Ina fatan zaka yafe mini laifin da nayi, rashin sani ne"" ta tashi a hankali ta ɗauki jakarta ta fita, tana yi wa Allah godiya da wannan karon, ba ta sha shaƙa ba, hakan ya sa ta ƙara" kin ƙwarin gwiwar cigaba da gwagwarmayar da ƙuduri aniya. "Bayan fitar Nabila, Viper ya ɗaga kai yana kallonsu ɗaya bayan ɗaya, Walid ya ce ""Ko ba ka yi" "magana ba, na san menene a ranka, ba kowa bane ba, ni ne nan na gaya mata labarinka""." "Ya tsayar da idonsa a kan Walid ya ce ""Saboda me?""" """Saboda dalili mai ƙarfi, cigaba da cusa kanta a lamuranka cikin duhun kai, tamkar ƙara yawan matsalolinka ne, zuciyar mace ta na da rauni, fiye da dukkaninmu, ina ganin hakan zai iya yi mana am..... Bai ƙarasa ba, viper ya katse shi ya ce ""Ta yaya? Na ce ta yaya? Meye amfanin gaya matan, na gaya maka bana buƙatar cigaba da ganin yarinyar nan, sai an haɗa baki da ita an ƙara rusa ni" "kenan? Da raunin na su ake amfani a sarafasu a cuci mutum, halittu ne su marasa imani...." """Raunin 'ya mace, da tausayinta irin na halitta, kar ka manta shi ya jefa ka a cikin halin da ka ke ciki, idan mace ɗaya zuwa goma sun cutar da kai, ɗaya zuwa biyu sun yi maka abun da ba zaka taɓa iya biyansu ba, wanda tausayi da soyayyar da mace ta nuna maka, giɓin da ta bar maka ne, ya ƙara assasa tunzura zuciyarka ka ke fama da jinyar da muka rasa bakin zaren yi maka maganinta. Idan zaka yi adalci, ka yi musu hukunci da halin ƙanwata, Jauhar ko ba dukkansu ba. Yarinyar nan gaskiya ta gaya maka, idan ka yi kisan kai ka ci amanarta, wannan miyagun ƙwayoyin da ka" "ke ƙara ɗurawa kanka, su ma ba ka yi mata adalci ba""." "Al'amin da ya ji maganganun Walid sun ishe shi, sai ya miƙe tsam ya sake ficewa." Walid ya yi wa Ɗan mama inkiya ya bi bayan sa ya ga ina zai yi. *** "Ramma ce take dukan gefen fion da Abdul yake ""Abdulyasar Abdul yasar"" ya buɗe idonsa da kyar ya kalleta." """Ka tashi ka yi sallar asuba, gari yayi haske, sallar ma baka yi"" ya ja tsaki ya sake juyawa." "Ta sake cewa ""Ka tashi gari fa yayi haske""" """Kin san jiya da daddare fa ban yi bacci ba, ki ƙyaleni""" "Ramma ta ce ""Haka ne kam, dama ba ka da lafiya, wataƙila a cikin baccin za a zare maka rai, ban sani ba ko kana da abun da zaka gaya wa Allah a kan rashin salla"" kan ta rufe baki ya tashi zaune" yana ƙifta ido. "Ta girgiza kai ta ce ""Kai yanzu baka shirya wa mutuwa ba, ka ke rashin mutunci? Allah sarki ɗan" "Adam abun tausayi"" ji yayi jikinsa yayi mugun sanyi, kamar mutuwar ce ke tunkaro shi, ya je ya yi alwala, ya fito ya tarar tana gyara gadon da ya tashi." "Wayarsa ce ta fara ringing, ya tashi da sauri, ya ɗauka, ya saka a kunnensa ""Hello mummy""" """Kana ina ne?""" "Ya ce ""Ina gidana""" """To zuwa anjima ka zo gida, zaka yi magana da babanka, shugaban jam'iyya ya ce ka je ka ga 'yar" "sa, ku daidaita kanku, ayi magana dan ba za su yadda a baka takara ba, baka da aure""." """Haba mummy, aure kuma? Ni wai dole ne auren nan, a haƙura mana""" """Ban gane a haƙura ba, waye zai yadda ka yi deputy governor ba ka da aure, lallai ka zo anjima ku" "yi magana dama yana cewa ni nake hure maka kunne""" "Abdul ya ce ""Ba ni da lafiya fa""" """Ka sha magani ka zo, ulcer ce?""" "Ya ce ""Eh, kuma wallahi ina jin jiki, dan Allah ki bashi haƙuri zan zo ne""" "Cikin damuwa ta ce ""Ko na turo a ɗaukko mini kai, ba na son ciwon cikin nan naka fa""" "Ya kashingiɗa ya ce ""A'a, zan warware, idan na ji sauƙi zan zo, sai anjima zan ɗan kwanta"" ya" "ajiye wayar. Tun da ya fara wayar, ramma ta ƙura masa ido har ya gama." "Ta ce ""Ka ga banbancin rayuwar mace da ta namiji ko? Kaga duk abun nan da ka ke yi, kai an" "samo maka mata ni mecece makomata?""" "Ya kalleta ya ce ""Kishi ki ke yi ne?""" """Allah ya rufa mini asiri, na rasa a kan wa zan yi kishi sai kai, ka wulaƙanta mini rayuwa ka cuce ni, kai ka yi aure ka tara iyali, ni kuma babu wanda zai kalleni, ka yi mini fyaɗe ka mayar da ni ƙ" "aramar karuwa, har ciki na ɗauka duk ta ƙazamar hanya ka wulaƙanta rayuwata""" "Abdul ya zauna sosai ya ce ""Ke ki ka fara wulaƙanta rayuwarki, da ku ka yi yinƙurin cewa zaku" "nemi hakkinku a kotu, alhalin ba zaku iya ja da ni ba""" """Sannu tsohon azzalumi, dama mai kuɗi shikaɗai Allah ya ce ya ji daɗi a duniya? Yanzu duk wannan abun taƙamarka kana da kuɗi ni 'yar talakawa ce? In sha Allah sai Allah ya ƙasƙantaka da kai da masu goya maka baya, suka tsaya maka kake rashin mutunci. Na san akwai ire-irena da yawa yaran talakawa da kuka zalunta, Allah ya na kallonku. In sha Allah sai Allah ya nuna maka" "iyakarka tun a duniya Abdul yasar""" "Duk da ya ji zafin maganganunta amma sai cewa yayi ""Ko wanda ya raɗa mini sunan nan, bai kai" "ki iya faɗar sunan ba Rahama, Abdul yassar""" "Kallonsa tayi tana kuka, haushin kanta yakamata da lokacin da yake waya, ba ta yi ihu a wayar ta ce a taimaka mata ba sace ta yayi. Yanzu ko wayarsa ta ɗauka ba zata iya operating ɗin ta ba," kuma ba ta da lambar wanda ta haddace balle ta kira. *** "Abba yana zaune yana kallon labarai a Aljazeera, Nabila ta shiga da sallama, yana kashingiɗe, ya tashi zaune yana murmushi ya ce ""Barrister, kin yi mini wuyar gani da yawa fa, kullum na dawo kina aiki, baki dawo ba aiki ya hana mini arfana sukuni""" "Tayi murmushi ta ce ""Abba ni kaina ina kewarka, bana samun zama, yanzu na shiryu ai, ina aiki" "sosai da sosai, na san addu'a ka ke yi mini""" "Ya ce ""Kullum Addu'ata a kanku take, mussaman ke arfana, Allah ya yi miki jagora a dukkan" "lamuranki""." """Eh mu ma Allah ba zai tagayyara namu ba"" Umma tayi maganar tana harar Nabila." "Nabila ko a jikinta ta ce ""Abba dan Allah abu na zo roƙonka""" "Ya ce ""Ina jinki ƴar albarka""" """Abba dan Allah mota nake so, wallahi wahala nake sha samun napep, ayi ta haɗani da maza, ga zirga-zirga na yi ta kashe kuɗin mota, kuma haryanzu ni ba na yi wa client ɗina charges mai" "yawa""" "Yayi dariya ya ce ""Nawa ki ka tara?""" "Tayi shiru sannan ta ce ""Ina da 400k""" "Ya kwashe da dariya ya ce ""400k, sai dai a gyara miki tsohuwar honda ta""" "Cikin shagwaɓa ta ce ""Haba Abba, big girl kamar ni, da tsohuwar mota, ka taimaka Please""" """Babu komai, za a sai mota in sha Allah, amma da sharaɗi ba na son yawon babu gaira babu dalili," "kuma ke zaki din ga zuba manki, ba zan sai mota na din ga cacar mai ba""" "Cikin takaici Umma ta ce ""Major mu fa? Muna zaune zaka saya wa Arfa mota, wannan wane irin" "rashin adalci ne?""" "Ya kalleta ya ce ""Da walida zan saya wa mota, ba zaki faɗi haka ba, ku fa da me? Ga mota nan ana kai ku unguwa a ciki, meye na kishi da 'yar cikinku? Ku daina haɗa kanku da ita, kun san abun da" "nake nufi""." "Arfa ta tashi ta ce ""Abba sai da safe"" ta juya zata fita, ta yi wa Umma gwalo, a ranta ta ce ""Saura" "ma babar su DSP idan ta ji, sai dai ku mutu""." "Ta koma bedroom ɗin ta tana murna, ta ɗauki wayarta, Viper ya faɗo mata a rai." "Lambarsa da ta saka a wayarta, ta lalubo, ta zubawa ido, murmushi ta yi, ta kira lambar ta saka a" kunnenta. "Yana zaune a kan katifa, yana ta shan sigari, zubawa lambar ido yayi, ya gaji ya ajiye wayar, ya" "cigaba da abun da yake gabansa. Ba ta gaji ba ta din ga kiransa babu ƙaƙƙautawa, har sai da ya hasala, ya ɗaga wayar, amma bai yi magana ba." """Har na kusa fushi sannan ka ɗaga, na san da 'yar madara ce, ko ba ta san mai lambar ba, zata ɗ aga kuma za ta saurareni, haka zalika zata yafe mini laifin da na yi mata. Akwai abubuwan koyi sosai da sosai a rayuwar ta, da ya ci ace ko ba duka ba, ka yi koyi da wasu, ba ta wulaƙanta ɗan Adam da tana yi, da ba ta riƙe ka da amana da tausayawa ba. Ina sake roƙonka yafiya, da kuma fatan samun haɗin kanka, ka ƙarasa mini labarinka da kanka, ina sha'awar kasancewa wani ɓ angare na labarin nan, mai ban tausayi da ratsa zuciya Viper, sai da safe"" tun da ta fara maganar, ya sunkuyar da kai, ya saki sigarin da take hannunsa, ya sunkuyar da kai hannunsa yana rawa. Ta" "gama maganar ta katse wayar, amma ya kasa ajiye wayar." "Sai da liti ya dafa shi ya ce ""Maza yane?"" Ya ɗago idanunsa ya kalli liti." """Kamar Muryar wannan shegiyar yarinyar na jiyo a wayar, duk Walid ne da wannan sheɗancin""" "Ya cigaba da ƙurawa Liti ido, babu abun da yake fata, banda ya zubar da hawaye ko na mintuna" "biyar ne, amma ko na sakan ɗaya ya kasa tsawon shekarun nan." "Murya a sanyaye ya ce ""Liti""" """Na'am mai zamani""." """Ina kewar jauhar sosai""" "Walid da da yayi musu shiru, dan ya lura daga Viper har liti haushin sa suke ji, amma maganar da" "Viper yayi yanzu ta sanya jikinsa ya yi sanyi, tausayin Viper ya ƙara kama shi." """Da yanzu yarona ya isa shiga makaranta, wataƙila ma ta kuma haifa mini wasu""" "Walid ya taso, ya dawo gaban Al'amin, ya riƙe hannunsa ya ce ""Ka ƙara haƙuri mai zamani""." """Zuwa yaushe? Ko na ɗauki fansa kamar yadda nake buri da fata, kashe kaina zan yi saboda ba ni" "da wata makoma, idan kuwa hakan ba zai samu ba, zan koma in da na fito na ƙarasa rayuwata""." """Dan Allah maza ka daina irin wannan maganganun, kana karya mana zuciya wallahi "" liti yayi" maganar cikin damuwa. "Viper ya girgiza kai ya ce ""Ba zaka gane ba""" "Kawai ya gyara ya kwanta, gaba ɗaya suka kewaye shi suna kallonsa." "Nabila kuwa kallon wayar ta cigaba da yi, ta ce ""Allah ya bani nasara a kanka, ya bani ikon" "taimaka maka""." "Kira ne ya shigo wayarta, ta ɗaga ta saka a kunnenta, ta yi sallama." """Wa'alaikum Salam da 'yar ƙwalisa""." """Wa ke magana?""" "Yayi murmushi ya ce ""Bawan Allah ne""" """To, ai kowa ma bawan Allah ne, wanne daga ciki?""" "Yayi gyaran murya ya ce ""Wani case ne da ni, nake so a taimaka mini""" "Nabila ta yi hamma ta ce ""Office zaka zo, ba ta waya ba"" ta katse kiran, dan a zatonta irin samarin" "nan, ne masu kiran wayar mata anyhow, duk da Muryar wannan ba ta yaro ba ce." "Wani nannauyan bacci, yayi awon gaba da ita wanda babu abun da take yi ban da mafarkin Viper," dan sai da ta kusa makara yau. "Kwanaki uku da zuwanta wurin su Viper, ba ta sake zuwa ba, she's very busy, tana ta off and down" "na tattara hujjoji, duk da ana ta taɗiyeta, duk in da za ta bi ta samo shaida, sai a rufe, sai da aka aike da dattijon nan gidan kaso." Gashi sai tayi ta sintiri a hanata ganinsa. "Kamar uba da ɗa haka Walid yake ta lallaɓa Viper ya ci abinci, sai dai ya cakala ya bari, ba ya cin" abinci. "Private numbrn nan da ake kiransa da ita ce, ta kira shi, wayar tana ta ringing liti ya ce ""Maza ka" "ɗaga mana""" """Me zan ce?""" "Walid ya ce ""Ko ba ka da abun cewa, ka ɗaga kawai""" "Ganin ba shi da niyyar ɗagawar, ya sanya Walid ya ɗaga ya sakata a hansfree." """Aminu Viper, kwana biyu. Ashe ta dawo maka da wayar. Alamu sun nuna kwana biyu ka yi sanyi," "Kodayake kai sai an sakankance ka ke ɓarna. Gargaɗi nake sake yi maka, ka nesanta yarinyar nan da ga gareka, za a iya cutar da kai ta hanyarta""." """Ni nake da ikon yanke hukuncin abun da yake daidai da rayuwata, babu wanda ya isa ya juya mini rayuwa yadda nake so, ka cigaba da ɓuya ko ka bayyana kanka, zan yi abun da nake ganin" shi ne dai-dai da rayuwata. "Mutumin yayi murmushi ya ce ""Aminu Viper, shikenan idan ka ƙi ji, ba zaka ƙi gani ba ai""" """Babu abun da ban gani ba, dan haka na shirya ganin koma menene"" ya katse wayar." "Liti ya ce ""Duk walid ne ya janyo komai, ni na san a rina, wannan yarinyar idonta kawai zaka" "kalla ka gane munafuka ce""" "Kallon da Viper yayi masa ne, ya sanya shi yin shiru, Walid yayi dariya ya ce ""Ayi dai mu gani, za" "a gane waye mai gaskiya tsakanina da ku""." "Liti ya ce ""Ba wata gaskiya da ka ke da ita, ka dakatar da mu daga making moves, wallahi mun" "kusa fita operation kwanan nan""" """Ku fita yaƙi ma ba operation ba""" Haka liti da Walid suka kusa yin faɗa. "Tun ana gobe Nabila zata je wurin Naja'atu Bunkure, suke waya da sumayya, take bata ƙwarin" "gwiwa, a kan za ta iya, kar ta ji tsoro." "Da safe sai da ta fara zuwa wurin aikinsu, ta samu barrister Habib, shi ma ya ƙara mata ƙwarin" "gwiwa, da yi mata fatan alkhairi." "Cikin ƙasaita take fiya a farfajiyar office ɗin, har ta ƙarasa, mutane ta tarar jingim. Wanda" "galibin su mata ne, suna jiran shiga wurin Barrister Naja'atu Bunkure." "Kai tsaye Nabila ta shiga wurin sakatariyarta, ta nuna mata ID card ɗin ta, nan da nan ta bawa" "Nabila wurin zama, na ciki na fitowa ta yi mata iso zuwa wurin Barrister Naja'atu." "Tun a hanya take maimaita ""la hula wala ƙuwwata illa billa"". Har ta shiga wurin Bunkure." "Tayi sallama, ba tare da ta ɗago ta kalli Nabila ba ta amsa mata, ta ƙarasa ta zauna ba tare da an" yi mata umarnin hakan ba. "Kayan jikin Nabila kawai ta kalla, ta fuskanci ba kalar gajiyayyun da suke zuwa wurinta bane ba." Ta gyara zaman gilashin fuskarta ta na kallon Nabila. """Sannu da aiki ma"" Nabila tayi maganar tana murmushi." """Yauwwa sannu""" "Nabila ta ɗaga mata id card ɗin ta ta ce ""I am barrister Nabila Yusuf maitama""" "Bunkure ta jinjina kai ta ce ""You look familiar to me""" "Nabila ta jinjina kai ta ce ""Na yi mamaki ma, da ki ka iya tuna kamar kin sanni, saboda na san" "jama'ar ne da yawa. Ni abun da ki ka yi mini ba zan taɓa mantawa ba har abada""" "Bunkure ta ce ""Ohh really""" """Yeah and i have a promise to fulfil, a dalilin abun da ki ka yi mini""" "Ta kashingiɗa da jikin kujerarta ta ce ""That's very good, ina son mutane masu yarda da kansu, ba" "na buƙatar sanin me nayi miki, ko kuma wani alwashi ki ka yi ba, ga ki ga bunkure Allah ya ida nufi """ "Nabila ta ce ""Na ji daɗi da ki ka ce Allah, dan kuwa shi ne gaba da komai, na gode sosai barrister""" """Mentioned not""" "Nabila ta gyara zamanta ta ce ""Yauwwa, ba komai ne ya kawo ni ba, na zo ne a kan wani case, duk" "da ba mu haɗu a court ba, an kai wanda nake depending prison, amma ban ganki a court ba sai wakilanki""" "Bunkure ta ƙarewa Nabila kallo, sannan ta ce ""Wane case ki ke magana a kai?""" """Yarinya da aka yi wa fyaɗe, ki ka ce kin tsaya mata, ni ce lawyer wanda ake ƙara, na je wurin" "'yan sanda ana ta yi mini yawo da hankali, ina son doctors report, kuma ina son zan ga yarinyar zan yi magana da ita""." "Naja ta yi wa Nabila kallon baki da hankali sannan ta ce ""Kin san a gaban wa ki ke?""" """I am barrister Nabila, ba ruwana da a gaban wa nake, ina neman hujja ne da zan kare client ɗina""" """Nawa suka baki, ki ka samu ƙwarin gwiwar yin wannan kasadar? Zan ninka miki, ki ajiye case" "ɗin, kafin ki kunyata a idon duniya """ """Watch your words, it can be use against you a kotu, kin san me nake nufi, you are also a lawyer""" """Who the hell are you?"" Bunkure ta yi maganar tana tashi tsaye, Nabila ma ta tashi tana sake ɗaga mata id card ɗin ta ""Sai da na fara gabatar miki da kaina, sannan na gaya miki meya kawo ni." "Ko dai ki bani abun da nake buƙata kawai, ko kuma na fasawa duniya wacece ke?""" """Ni ɗin? Yaushe ki ka yi grduating, da me ki ke taƙama ki ke jin karanki ya kai tsaikon da zaki" "tunkare ni kina gaya mini maganar da ki ka ga dama?""" "Nabila ta girgiza kai ta ce ""Cikin dukkanin girmamawa ta seniority a aiki, nake faɗar duk abin da nake magana a kai. You were my mentor before, abun da ki ka yi mini ya tabattar mini you are green snake under green grass. Keep your eyes open, Barrister bunkure, zan iya baki mamaki a lokacin da baki zata ba. Zan cigaba da bibiyar case ɗin ramma, da ƙoƙarin wanke wanda nake karewa har sai na yi exposing ainihin gaskiya ko da kuwa ita ce ajalina"" tun da ta yi face to face da" "ita, ta ji duk wata fargaba da tsoron da take ji sun kau." "Ta ɗauki jakarta, ta fita daga office ɗin." "Tsaki Bunkure ta yi ta daki tebur, ta ɗauki wayarta, ta danna ta kara a kunnenta." """Yauwwa barrister Kabir ya kake?""" """Lafiya ƙalau manyan ƙasa ya aikin?""" """Normal ne, wacece Nabila a ma'aikatanka?""" "Ya ce ""Lafiya kuwa? Ya aka yi ki ka santa?" """Wacece ita, a id card ɗin ta na ga a wurinka take aiki""" "Ya ce ""Barrister Nabila, a law firm ɗina take""." """Ta zubawa kanta fetur a jiki, tana kuri, idan na ƙyatta ashana, ba ita ba har kai, zaka ƙone ƙ" "urmus ka ja mata kunne, ɓera ba ya taka rawa a gaban mage, ko da kuwa tana kan gargara ne""" "Kabir ya ce ""Subhanallah, me ta yi?""" """Ka bincike ta, ba na bari ayi mini kuskure biyu, ko yinƙurin yi aka yi, ina daƙile duk wani abu da" "zai kawo mini cikas""." "Kabir ya ce ""Na fahimta, ki yi haƙuri dan Allah zan yi magana da ita, zan kuma ja mata kunne"" ta" ajiye wayar tana tsaki. "Cike da annashuwa ta fito daga wurin, tare da jin kanta tamkar ta yi facing ɗin babban abun" tsoronta. "Ta tsaya a gefen hanya, ta ciro wayarta, ta kira Viper, ya ɗaga sai dai bai yi magana ba." """Hello, ya jiki? Na san ba zaka yi magana ba, dama so nake na ji ya jikinka, na so zuwa na ganka" "amma rana tayi sosai, zan je wani wuri ne, ka kula da kanka sosai"" ta katse wayar, ji yayi tamkar" "ya aikata wani uban zunubi, ya din ga bin wayar da kallo, yana tunanin yarinyar nan tana da hankali kuwa?." "Gida ta tafi cikin matsanancin farinciki, duk da ba su kwasheta da daɗi ba ita da." "Gida ta tafi ta yi wanka, ta ɗauki wayarta ta kira sumayya, amma line busy." Ta ajiye wayar ta kwanta tana bacci. *** "Shiru shiru Abdul bai je kiran iyayensa ba, yana nan yana fama da kansa, kuma ya hana duk abokansa zuwar masa gida." "Duk da Allah ya isa, da fatan mutuwa da ramma take yi masa, hakan ba ya hanata tausaya masa," "idan ciwon ciki ya murɗe shi, har mamaki take yi da ya ce mata ulcer ce, dan ita ta ɗauka yunwa ce take kawo ulcer, yaran masu kuɗi ba sa yi." "Da daddare yana kwance a kan gado, tana zaune a ƙasa tana karanta wani novel na turanci, da ta" "ɗauka a falonsa, duk da ba wani ganewa take yi ba, amma yana ɗebe mata kewa." "Tana ji aka kira shi a waya, ya ce yana zuwa, ya tashi ya fita." "Bayan ya fita, ta ɗaukko pillow, ta ajiye a ƙasa ta cigaba da karatunta." "Hamma da take ta yi ba ƙaƙƙautawa ne ya sanya ta gane bacci take ji sosai, ta tashi za ta rufe ƙ" "ofar ɗakin, kasancewar ya bar key ɗin ta ciki, dan ciwon cikin nan da yake yi, ta samu sassauci daga akuyancinsa." "Sai dai ta buɗe ƙofar falon ba ya nan, ta fito ta wuce kitchen, ta daɗe a kitchen, ta zubawa fridge ido, komai akwai na morewa rayuw a gidan, amma gaba ɗaya ba ta jin daɗinsu, saboda ƙ" azantacciyar rayuwar da take ciki. "Ta sha ruwa mai sanyi, ta cika cikinta, ta fito falo, sai dai abun da ta tarar ya sanya gabanta" mummunan faɗuwa. "Cikin hanzari ya ture Nina daga jikinsa, ya yi tsilli-tsilli da ido, yana kallon ramma." """Abdul wacece wannan?""" """Amm maid ɗina ce, mai aikina ce""." """Kamar yaya, ina solomon ɗin, shi zaman me yake yi? Me ka ke yi da mace a zaune a gidanka?" "Abdul kar ka raina mini hankali mana, karuwa ka ajiye Abdul?""" """Kar ki sake ce mini karuwa, ni ba karuwa ba ce, ke ce karuwa amma shi ki tambaye shi yadda" "aka yi na zo gidan nan?"" Ta yi tsaki za ta tafi." """Abdul ka yi mini magana wace banzar ce wannan?""" "Abdul ya miƙe ya ce ""ya isa haka, ki je gida za mu yi magana """ """Ban gane ba, ka gaya mini wacece wannan?""" "Bayan ramma ya bi da sauri, Nina ta biyo shi, amma yana shiga ɗakin, ya mayar da ƙofa ya rufe" da key ta ciki. Ramma tuni ta kwanta wani abu mai zafi ya tsaya mata a rai. """Rahma, ki tashi mu yi magana dan Allah, zan yi miki bayani"" tayi masa shiru ta ƙi motsawa." """Dan Allah ki tashi ki ji, zan yi miki bayani""" "Ramma ta waiwayo sosai ta kalleshi ta ce ""Ba ni zaka yi wa bayani ba, Allah zaka yi wa bayanin abun da kake aikatawa ba tare da tsoronsa ba. Ni baƙincikina, muzanta rayuwata da ka yi ne da wulaƙanta ni." "Ka yi zina da wasu, ko wankan janaba baka yi, ka zo ka kuma afka mini, wannan wace irin rayuwa ce, Abdul yasar ka gama da rayuwata, wallahi ko baka kashe ni, ina son kashe kaina na huta, dan dai kawai ina tunanin makomata ne, amma ka cuceni wallahi"" tayi maganar hawaye na" ta gangarowa ta gefen idonta. "Hannu ya sa yana share mata hawayen, amma ya kasa ce mata komai." "Ya numfasa ya ce ""Kina ji na?""" """Dalla ƙyale ni, ba abun da zan ji, ni ƙyanƙyamika ma nake ji, mazinaci ƙazami mara tsoron" "Allah""" "Duk da yadda maganganunta suka yi masa zafi, amma ya daure ya ce ""Dan Allah Rahma ki daina" "kirana da mazinaci, kalmar nan na yi mini ciwo sosai. Wallahi tun a kanki ban sake zina ba, yanzu ba abun da ki ke tunani ba""" "Aikuwa kamar ya tunzura ta, ta tashi zaune ta ce ""Ni abun da ka ke yi mini menene? Na faɗa na" "kuma"" ta sauka daga kan gadon tana huci, cikin ɓacin rai." *** "Naja'atu kuwa tana zaune a bakin gado, tana ta haɗa ƙwayoyi a cikin roba, ta na zuba ruwa a ciki, shiru ta yi tana tunanin maganganun da Nabila ta gaya mata, mamakin ƙarfin halin yarinyar take" "yi, yadda ake shakkarta da shakkar yin gaba da gaba da ita, ita wannan yarinyar zata yi wa cin" "mutunci haka. Me take nufi da za tayi exposing ɗin ta. Ta daki teburin gabanta ta ce ""Wai ma wacece ita?"" Ta yi wata ajiyar zuciya ta ɗaga kai, ta shanye ƙwayoyin cikin robar nan da ta narka." "Nabila ce zaune tare da Nasir, tana bashi labarin yadda suka yi da Naja'atu Bunkure, yake ƙara ja" "mata kunne, a kan ta bi sha'anin matar nan a hankali, kar ta yi mata illa." "Tayi murmushi ta ce ""In sha Allah ni zan karya alkadarin matar nan""" "Ya ce ""To, Allah ya sa""" "Ya amsa da ""Amin, na ji an ce kin ce mota ki ke so?""" "Ta jinjina masa kai ta ce ""Abba ya saya mini mota,kai kuma ka din ga zuba mini mai"" tayi" "maganar cikin shagwaɓa. Kasa amsa mata yayi, sai bin ta da kallo da yake yi, yana murmushi." "Ta ce ""DSP ya ake ciki ne, da zancen binciken viper?""" "Ya numfasa ya ce ""Ina ta cigaba da bincike, gashi ana cigaba da matsa mini a kan kama shi, abubuwan ma na rasa yadda zan yi, duk shaidar da na kama sai ta zille, ace in sake shi, na rasa wannan wane irin abu ne. Amma dai an kwatanta mini wani yaro, dealer ne na wiwi, wai shi ɗan mama, idan na kama shi, ba zan bari a san na kama shi ba, sai na dangana da kama Viper in sha" "Allah"" gabanta yayi mummunan faɗuwa ta ce ""To wai suwaye suke sakawa a saki shaidun naka?""" "Ya ce ""Ban sani ba, daga sama kawai ake cewa na sake su""." "Ta jinjina kai ta ce ""Kuma anya ba su san in da yake ba, raina maka hankali kawai suke yi ba?""" "DSP ya ce ""To ko ma dai menene, zan ɓoye bincikena, sai na dangana da kama shi, na danƙa" "musu shi, su san yadda za su yi da shi. Ina nan mun samu bayanan lokutan da yake zuwa an tabattar mana da idan muka kama shi, zamu iya kama Viper """ "Kamar an mintsine ta ta miƙe, ta ce ""Bari na koma ɗaki, zan yi wani uzuri"" har da gudu ta haɗa, ta tafi ɗakinta, ta ɗauki wayarta ta din ga kiran Viper, amma yaƙi ɗagawa, tayi masa missed calls sun fi goma, amma ko ɗaya ya ƙi ɗagawa, ga yamma ta yi sosai, idan ta fita kan ta dawo" magariba zata iya yi. Ayshercool 08081012143 ₦500 ne via 0009450228 Aisha Adam jaiz bank sai shaidar biya ta 08081012143 Wanda za su jira document 1K ne. 90009343 'Yan Nijar ku turo katin airtel na 300fcfa Arewabooks ayshercool7724 "Kamar Nabila za ta yi hauka, tana kallon kiran Barrister Kabir yana shigowa wayarta, amma ta share, taƙi ɗagawa, ƙarshe ma rejecting kiran na sa ta din ga yi, taƙi ɗagawa babban burinta" "kawai Viper ya ɗaga wayarta, amma yaƙi ɗagawa." "Kwana tayi cikin zullumi, da addu'a kar Allah ya bawa Nasir nasarar kama Ɗan mama, dan a labarin Viper ba ta ji yadda aka same shi ba, balle ta san ingancin kasancewar sa tare da shi, tare da tabbacin ba zai faɗi in da Viper yake ba, kodayeke ta san ba zasu taɓa janyo wanda zai cutar da" su ba. *** "Abdul ne zaune a gaban Indabo, sai zazzaga masa faɗa yake yi, ya haɗe rai yana ta muzurai." """Ina magana kana shan kunu, Abdul ko ka ƙi, ko ka so dole ka yi aure, idan ba haka ba, babu yadda za ayi a ɗauki takara a baka, na gaya maka dan ba zaka yi mini asarar wahalar da na yi shekaru ina yi ba, dole ka je ka gano yarinyar party chairman ku daidaita, ko baka santa ayi, idan" "ya so daga baya sai ka auro wadda ka ke so""" "Cikin damuwa ya ce ""Daddy, ya za ayi ace na auri wadda ba na so, ni tun ban ganta ba, ba na" "sonta wallahi, a bar ni zan kawo wadda nake so ɗin""" "Indabo ya ce ""Inaa lokaci kuma ya ƙure maka, arranged marriage ɗin nan, duk cikin manufa ce" "irin ta siyasa, dan haka dole ka yi haƙuri, ka je ku daidaita"" Abdul ya yi shiru bai ce komai ba." "Indabo ya ɗora da cewa ""Sannan za'a fara haɗa structures a kowacce mazaɓa, tun yanzu za ku fara campaign kafin ƙaddamar da takararku"" Indabo har ya gama maganganun sa, Abdul bai saki" "fuska ba, yayi ya gama ya tashi ya bar office ɗin." "Yana fita P.A ya shigo, ya ce ""Distinguish yaya dai nake jiyo muryarka tun daga waje?""" "Indabo yayi tsaki ya ce ""Abdul mana, gaba ɗaya yaron nan ba shi da hankali, wai shi ba zai yi aure yanzu ba, so yake yayi mini asarar wannan uwar wahalar da na sha muka kawo wannan" "matakin""" "P.A yayi murmushi ya ce ""Rabu da shi, mu cigaba da dukkan shirye-shirye da suka dace, kuma a cigaba da bin malamai, dan Abdul akwai taurin kai, a kan auren nan zai iya fasa takarar amma a" "cigaba da matsawa""." "Imdabo yayi tsaki ya ce ""Yaya ake ciki? Ya batun yarinyar nan?""" """Mu na nan muna bibiyarta, sai dai bakin zaren gano in da Viper yake ne aiki, balle ayi masa" "tarkon da ita. A binciken da nake yi, shi wannan ɗan sandan ya kama liti, kwanansa kusan huɗu a" "hannunsa, aka ce lallai ya sake shi""" "Indabo cikin damuwa ya ce ""Waye ya ce a sake shi ɗin?""" "P.A ya girgiza kai ya ce ""Ban sani ba, haryanzu babu trace na wanda yake taimaka masa, kuma" "Viper yana nan a cikin garin nan yana yawonsa, sai dai gaskiya ƙarƙashin kulawar wani yake duk abin da yake yi """ """Kaii wai wannan wane irin abu ne? Hankalina kullum a tashe yake, ban san ta ina zai ɓullo mini ya ce zai ɗauki fansa ba, ka san ba zai taɓa barina ba, shi ma wancan banzan da duk laifinsa ne, ya kasa komai ya kasa kamo shi ya kasa gano in da yake, duk shi ya ɓata lamarin, da bai tabattar" "da Viper ya mutu ba tun a wancan lokacin, ina cikin tashin hankali""." """Ka kwantar da hankalinka distinguish, Viper fa zai zo hannu, ko da me yake yawo, ka yi haƙuri" "in Allah ya yarda babu abun da zai faru sai alkhairi"" yayi ajiyar zuciya ba dan ya gamsu da maganganun P.A ba." *** "Daga wurin Indabo Abdul gidansa ya wuce, ya tarar da Ramma na ta uban bacci, motsinsa a ɗakin ne ya saka ta farka, ya kalleta ya ce ""Baccin nan ba ya isarki ne?"" Ta ɗaga masa gira alamar eh." """Ko ki na da ciki ne?""" """Allah ya kiyaye, ya tsari mahaifata da ƙara ɗaukar ƙazantarka""" "Ya ce ""Hmm, ki bari cika baki, ki bari ayi gwaji tukuna""" "Ramma ta ce ""Ba abun da za a gwada""" "Lambar saif ya kira, ya ɗaga ya ce ""Yeah""" """Saif daddy ya ɓallo ruwa fa""" "Saif ya ce ""Zancen auren dai?""" """Shi fa, wai wata 'yar party chairman, ni tun ban ganta ba, ba na sonta wallahi dan kawai zan yi" "takara, sai na auri wata wadda ba na so, ya dage ya dage, kamar na gudu wallahi""." """Kai fa ka fiye gaggawa, ka bi su a sannu tukuna, ka je ka ga yarinyar """ "Abdul ya ce ""Ba ma wannan ba, Nina ta ga yarinyar nan a gidan nan, tana ta yi mini hauka, ga" "maganar auren nan idan ta ji, ban san haukan da za ta yi ba, ni gaba ɗaya na rasa abun yi ma""." "Saif ya ce ""Lallai ma Abdul, ba ka mayar musu da yarinya ba, kai baka kasheta ba, ka bar ta to" "yaya zaka yi da ita?""." """Mu haɗu in anjima a joint kawai""" "Saif ya ce ""Shikenan, Allah ya kaimu anjiman"" yana kashe wayar ramma ta kalleshi ta ce ""Bariki babu riba, dama duk wata hanya idan ba ta Allah, ai ba mai ɓullewa ba ce ba your excellency, na ga ku duniyar kawai ku ka saka a gaba, lahira kuma kun bar mana mu talakawa mu nema. Allah ya bamu a can." "Ni dai in an tashi, a taimakawa 'yan garinmu da hanya, a gyara mana babban asibitin garinmu, sai" "kuma makarantunmu, dan Allah kar a manta da mu""" "Yayi murmushi ya ce ""Ki na yi mini rashin kunyar za ayi abun da ki ke so?""" """To ba ma so, dama kuɗin haram bana halal ba"" bai ji haushi ba, ya kwanta a jikinta, yana kashe" "mata murya, yana kiran sunanta." """Rahmaaaa"" ture shi tayi a fusace ta ce ""Ni ka daina yi mini wannan abun 'yan iskan ba na so""" """Her excellency rahammaaa"" yayi maganar kamar mai shirin yin shagwaɓa." "Wani uban takaici ya cika mata zuciya, ta kasa ture shi, sai ma cakulkuli da ya fara yi mata, ta dun" "ƙule hannunta tana kai masa duka, amma ko a jikinsa, dariya ma yake yi, abun nata gwanin ban dariya." *** "Tun da aka idar da sallar asuba, Nabila ba ta koma bacci ba, ta shirya, gari na yin haske, ta ɗauki jakarta ta fice daga gidan, fuskarta sanye da niƙabi." "A hanya gari ya ƙarasa waye mata, ta tafi gidan su Viper." "Duk da akwai tafiyar ƙafa sosai, daga titi zuwa gidan, amma yanzu idan tayi bulayin, tana iya" "gano gidan. Kasancewar wurin da nisa, gari yayi haske sosai ta isa gidan." Ta tarar da su suna ta shirin ɗora karin kumallo. "Walid ya kalleta da mamaki ya ce ""Lafiya?""" "Ɗan mama ya ce ""Mun shiga uku, wannan akwai mayya wallahi, idan ba kama mu aka yi ba," "hankalinta ba zai kwanta ba""." "Liti ya miƙe a fusace, ya ɗauki wuƙa a kan taga, ya ce ""Ke ware dan kazakazanki, ko shi bai" "kashe ki ba sai na kashe ki ni, jarababbiya kai, uban me ki ke nema a wurinmu? Ke bayan haushinki da nake ji, har da wannan banzan saurayin naki ɗan sanda da ya din ga azabtar da ni," "sai na yi masa ido ɗaya, ba zai bar aikin ɗan sanda ba sai da tabona""." "Walid ya ce ""Meya dawo da ke kuma? Me ki ke nema?""" "Ta ce ""Viper""" """Me zai yi miki?""" """Ina son ganinsa ne""" """Yana cikin yanayi mara daɗi, ki yi haƙuri ki tafi kawai, ba zaki ji daɗin abun da zaki gani ba""" "Nabila ta ce ""Komai munin abun zan gani, zan jure""" """Kin ga, ba mutuncinki bane ba, kina 'ya mace, ki dinga sintiri a gidan nan, wurin mutane irinmu" "ma, yakamata ki daina zuwa""" """Zan daina, idan na samu abun da nake so, ka ƙarasa mini labarin jauhar, ni lawyer ce, ina son ya" "ɗauki fansa ta hanyar da ta dace ne, kuma niyyar da nake da ita ta alkhairi ce, dan haka na san ba zaku cutar da ni ba"" tayi maganar tana nuna wa Walid id card ɗin ta." "Walid ya ce ""Na san ke lawyer ce""" "Cikin mamaki ta ce ""Ta yaya?""" """A ina na saka aka ɗaukko mini ke?"" Sai kuma tayi shiru tana kallonsa." """Baki isa na bari ki raɓi Viper ba, muddin ban san wacce ke ba. Hatta gidanku na sani""." "Tayi ajiyar zuciya ta ce ""Nayi mamaki, dama jiya na kira Viper ya ƙi ɗagawa, wanda ya kama ka, ba saurayina bane ba, yayana ne. Kuma da shi nake taimakawa a kan neman Viper, yanzu haka ya tabbatar mini da yi wa wani ɗan mama tarko, ya ce idan ya kama shi, an ce zai samu Viper, sai dai" "ban san waye ɗan maman a cikinku ba""" "Walid ya ce ""Wani tabbaci muke da shi, ba zaki cutar da mu ba, ko ki ci amanar mu ba, duba da" "yadda ki ke zambatar ɗan uwanki cikin aminci""" "Nabila ta jinjina kai ta ce ""Haka ne, ni zan tsaya a tsakiya ne, na bi ɓangaren gaskiya, and no matter what, ina da ikon tsayawa duk wanda nake ra'ayin tsayawa. Amma dan Allah ku bari na" ganshi na yi magana da shi. "Walid ya ce ""To""" "Liti ya ce ""Ni fa ban yadda da yarinyar nan ba mai laya, ya ya za ayi ta ci amanar ɗan uwanta" "kuma, ta ce tana tare da mu?""" "Walid bai kula shi ba, ya buɗe mata ɗakin da Viper yake ciki, yana zaune daga shi sai gajeren" "wando, ko riga babu a jikinsa." "Jiki a sanyaye ya ce ""Maganar da ki ka faɗa gaskiya ce, ƙwaƙwalwar viper ta fara samun matsala," "a dalilin damuwa da ta'amalli da miyagun ƙwayoyi, yana buƙatar ganin likita, amma tayaya? Ina tsoron mu fita da shi a samu matsala""." "Duk ganin ƙirarsa ta razanata, yana zaune, daga zaunen ma maye kawai yake yi, ga uban karan" taba guntu-guntu a wurin. Kawai ta shiga ɗakin ta nufe shi kai tsaye. "Walid ya ce ""Ki daina gangancin tunkararsa yadda ki ka ga dama, ba ya cikin hayyacinsa fa""" "Nabila ba ta saurare shi ba, ta je gaban Viper ta durƙusa, ya ɗago ya kalleta ya ce ""Ban ce ki daina" "zuwa ba?""" """Ba zan iya ba ne, na fara jin abun da 'yar madara take ji, idan ta ganka a yanayi mara daɗi, yaya" "za ta ji idan ta tsinceka a yanayin da ya fi na baya muni?"" Ya zuba wa Nabila ido, wanda hakan ya tilasta mata kawar da kanta daga kallonsa." "Ta cigaba da cewa ""Yakamata ka ƙarasa mini labarin jauhar, kar na je na sakankance, ta dawo ta ƙwace mijinta, dan a labarinta na ga daga tausayi soyayya ta ƙullu, kuma nima dai gashi ba na son shaye-shayen nan, kar na je sai na yi nisa ta ƙwace mini kai, tana ina ne yanzu?"" Tayi" maganar tana jiran amsar da zai ba ta. "Ya ƙura mata ido, har sai da gabanta ya faɗi, ta fara tunanin ko shaƙetan zai yi." Amma ya jingina da bango yana lumshe ido. """Talk mana"" tayi maganar da sigar rarrashi." "Su liti duk suna window suna ganin ikon Allah, su ihu yake ta yi musu, yana kiran matarsa, amma" "yanzu ya nutsu, ko hargowar bai yi mata ba." """Na ga haryanzu baka gama dawowa dai-dai ba, bari na je zan dawo, sai mu yi magana ka din ga ɗaga wayata amma, sunana Nabila Yusuf maitama. Amma babanmu arfa yake ce mini, ranar arfa aka haife ni, shiyasa nake da sa'a sosai kuma yana son mamana sosai da sosai, kamar dai yadda ka ke son 'yar madara. Amma dan Allah ka gaya mini da wuri tana ina, kar in zo daga baya, ka ce baka san zance ba baka sanni ba"". Tayi masa maganar cikin sigar shagwaɓa." "Yayi shiru, ko tari bai yi ba." "Har ta gama surutanta, bai yi magana ba, ta tashi a hankali ta fito, ta kalli Walid ta ce ""Zan je" "gidan masu rangwamen hankali, na yi magana sa likitocin ƙwaƙwalwa, idan ta kama dole ayi arranging yadda zai ga likita, ina matuƙar buƙatar hankalinsa, kafin komai ya yiwu, sannan ku rage zirga-zirga an matsawa yayana lamba a kan kama shi, kuma ya dage by any means sai ya" "kama shi""." "Walid ya ce ""Shikenan, mun gode da gudunmawarki, sai anjima"" ya jinjina kai ta fice ta tafi." "Suka sake leƙa Al'amin, ya kwanta a wurin, yayi ruf da ciki, wanda tun bayan sallar asuba suke fama da shi, sai ya fita ya kashe madaki da Indabo, da ƙyar suka rufe shi a ɗaki, da kokowa, dan kuwa sun sha wahala, duk da su uku ne, shikaɗai neman gagararsu yayi, amma da Nabila ta zo" tana yi masa magana bai yi wannan hargagin ba. "Sai kusan sha biyu saura ta isa wurin aikinsu, mai yi musu goge-goge ne ya sanar da ita, Barrister" "kabir yana ta nemanta, ta ce masa to, sai da ta shiga office ɗin ta, ta dafa tea a dispenser tana da biscuit a office ɗin ta, ta haɗa ta karya." "Sai da ta kammala, sannan ta tafi office ɗin Barrister kabir, yana ta shiri zai fita yana da wani" "meeting, duk yadda yake yi mata wasa, idan suka haɗu yau sai ya sha kunu ya ɗaure fuska tamau." """Sir an ce kana nemana?""" "A ƙule ya ce ""Au an ce nema? Tun jiya nake kiran wayarki, baki ɗaga ba, baki biyo ba ki ji" "dalilin kiran""" "Cikin ko in kula ta ce ""Sir ban taɓa yin hakan ba, yakamata ayi mini afuwa ayi mini uzuri""" """Shut up, ba zaki janyo mana magana ba, kin san wacece matar nan kuwa?""" """But sir, this is my personal trial, ba under law firm ɗin nan zan yi shari'ar nan ba""." """Ina magana kina magana? Amma da ID card ɗinmu ki ke amfani ko? You better watch what you" "are doing, faɗa da matar nan tamkar faɗa da manyan mutanen nan ne, dan su take yi wa aiki""" "Barrister Habib ne ya ƙaraso, yana faɗin ""Subhanallah, lafiya kuwa meyake faruwa?""" "Barrister kabir ya ce ""Ka san yarinyar nan office ɗin Naja'atu Bunkure ta je neman magana, wai tayi mata bayanin wani case da yake hannunta, ina ruwan Nabila da Bunkure?"" Idanun Nabila ya cika da hawaye, tamkar ta fashe da kuka, kowa ya santa da barrister Kabir, suna good time sosai," amma yau yayi mata ihu a gaban mutane. "Barrister Habib ya ce ""Barrister Nabila, garin yaya, meyasa ba kya shawara waye ya aike ki? Kin san wacece Bunkure kuwa? Gaskiya kin yi wauta, mu je in ji ya aka yi, barrister yau da kai da daughter taka mu ganku a rana, amma ayi mana afuwa, ka san yanzu nine abun koyinta, mun" "shirya tana son aiki tana ƙoƙari. Ayi mata afuwa""." "Kabir ya girgiza kabir ya ce ""Rigimarta tayi yawa""" """Ayi haƙuri ke kuma wuce mu je"" Barrister Habib ya sakata a gaba, suna zuwa Office ɗin sa, ta" fashe da kuka. "Ya ce ""Ahhh ya haka? Kuka kuma karaya tun yanzu?""" "Cikin kuka ta ce ""Kana ganin abun da yayi mini, ita wacece Naja'atun ba mutum ba ce ba? She's" "just my senior kuma ni ba rashin kunya na yi mata ba, ajiye masa aikinsa zan yi nayi zaman kaina""" "Barrister Habib ya yi dariya ya ce ""Kin bani kunya, waye ya ce miki ana gwagwarmaya babu ƙ" "alubale ne? Dole ki shiryawa ƙalubale, and ki bar maganar resigning ɗin nan ba mafita ba ce ba. Yanzu yaya ku ka yi da ita?""" "Cikin tura baki ta ce ""Ni sai na bar wurin nan""" """Kar ki ga laifinsa, maybe kiransa aka yi, aka ja masa kunne, dan haka ki yi masa uzuri ai bai taɓa" "yi miki haka ba ai, haba 'yar ƙwalisa""." "Ta zumɓura baki, tana goge hawayenta." """Yanzu yaya ku ka yi da ita?""" "Nabila ta yi ajiyar zuciya ta ce ""Nothing much, alamu sun nuna babu gaskiya a lamarin nata, dan idan tana da gaskiya, zata gaya mini aka tsaya a lamarin yarinyar, amma ta kore ni, ta ɓuge da kiran sa." "Sai dai an hana ni ganin shi wanda nake karewar ma, amma dai ya kwatanta mini gidan ɗaya mai aikin, na je an ce ta tashi ta koma garinsu. Amma ya tabattar mini da yarinyar 'yar tofa ce, wai wani gari yaloko, amma bai san ina ba a tofa. Ni ban san ina ne ma tofan ba, balle na nemi gidan" "su yarinyar""." "Barrister Habib ya yi shiru sannan ya ce ""Kin tabattar a tofan ya ce miki take? A yalokon?""" Ta jinjina masa kai alamar eh. """To shikenan, ki bani kwanaki i will get back to you. Amma ki daina garaje, ki din ga bin komai a" "hankali""" "Ta ce ""To"" ya din ga rarrashinta, har ta huce, ta tashi ta koma office ɗin ta""." *** "Tun da Abdul ya dawo, yake cika yana batsewa, ramma ko kallo bai isheta ba, ta cigaba da" "sabgoginta, ko abinci bai ci ba, ya nemi wuri ya kwanta." "Haushi ya ishe shi, gaba ɗaya ba ta tasa take yi ba, karatun littafinta ne kawai a gabanta, babu" tsammani ta ji ya fizge littafin hannunta. "Ta kalleshi ta ce ""Lafiya?""" """Wai ke wace iri ce ne?""" "Ta kalleshi ta ce ""Kamar yaya?""" """Ke baki damu da ki ga mutum cikin damuwa ba, ki tambayi meyafaru ba?""" "Ramma ta ce ""To ina ruwana da abun da ya dameka? Ni banda damuwar da ka saka ni a ciki? Bani" "littafina malam""." "Abdul ya ƙura mata ido, ta tashi zaune ta miƙa masa hannu ta ce ""Bani dan Allah""." """Me ki ke ganewa a ciki ne?""" "Ramma ta ce ""Ko ba na ganewa, ai gara na karanta littafin, da kallon fuskarka ma, bani littafina" "malam"" ta yi maganar tana haɗe rai." "Wayarsa da take vibrating ya ciro, ya saka a kunnensa." """Yau Yakamata ka shigo Asibiti, yau zaka yi wa patient ɗin ka tiyata fa""" "Ya ɓata fuska ya ce ""Yau ne amma baku tuna mini ba, ni na manta gaba ɗaya""." """An yi booking ɗin su, da wanda za su ganka, kusan wata biyu suna jira, ba su samu ganinka ba""" """Zan kira Doctor Anas,ya je yayi am sick, ba zan iya tiyata ba""" """Amma doctor... Cikin hargowa ya ce ""Shut up, abun da na ce za ayi""" """To shikenan"" ya ajiye wayar, ramma ta ce ""Dama kai likita ne?""" """Ban sani ba, sai yanzu ki ga damar kula ni, saboda baki da imani, ki na kallo ko abinci na kasa" "ci""." """Kar Allah ya sa ka ci mana, kai har ka na bakin cewa wani bashi da imani Abdul yasar? Hala" "tsabar imanin ne ya sa kazo ka yi mini kurkuku a nan?""" """Ke fa taimakonki nayi, haka ki ka zo kalli yadda ki ka yi ƙiba, ki ka yi kyau, sai ma mun ci" "gwamnati, zaki fi haka ƙiba"" yayi maganar yana taɓa damtsenta." """Ni meye nawa idan ma kun ci gwamantin, in sha Allah ma ba zaku ci ba, ace a rasa wanda za su jagoranci al'umma, sai mutanen banza masu lalata yaran mutane "" ya ce ""Ok, Ai ba a wurinki" "muke nema ba""" """In sha Allah ba zaka ci ba, ko ƙuri'a ɗaya ba zaka samu ba""" "Abdul ya ce ""Ke ki ka sani, na je na ga yarinyar da aka ce zan aura, kyakykyawa nutsatiyya," "tabbatar Allah ba ya karɓar addu'arki""" "Da sauri ramma ta kalleshi ta ce ""Nutsatiyya, ai ba zaka taɓa auren macen kirki ba, sai wadda wani ya lalata kamar yadda ka yi. Ai ko ka ganta a nutse ma, in sha Allah irinka ce zaka aura. Ba zan yi fatan Allah ya baka lalatacciyar 'ya ba, dan ba ita tayi mini ba, amma in sha Allah sai ka" "auri lalatacciya"" tayi maganar tana hawaye." "Abdul ya ce ""A'a gaskiya ba lalatacciya kamar ke ba, Nutsatiyya ce sosai, idan na aureta kar ki" "damu, ba zamu rabu ba, ai ana mugun tare tun da kin zama 'yar hannu kema." "Ta ce ""Kai da Allah, kuma in sha Allah sauran wani zaka aura""" "Abdul ya ce ""Nima saurana wani zai aura, balle ba zamu iya rabuwa da juna ba, mun riga mun" "saba, ni zan iya aure, amma ke ba zaki iya ba, kawai mu cigaba da rayuwarmu a haka rahma""." "Hawaye wani na bin wani ta ce ""In sha Allah, sai Allah ya kuɓutar da ni daga hannunka azzalumi kawai"" Abdul tamkar jin daɗin tsinuwar da ramma take yi masa yake ji, ta zage shi tayi masa Allah ya isa, amma hakan ko a jikinsa, sai ma cigaba da tunzurata da yake yi ya ce ""Ohhh kishi a" "fili, ki dai yi a hankali, kar ki yi zurfi a soyayyata, 'yan mata ne da ni burjik""" """Eh tun da ga ka bunsuru ba"" ta tashi tsaye tana kuka." "Ya ƙyaƙyace da dariya ya ce ""Bunsuru ya ajiye akuya ta mussaman a gidansa ba"" kalmar akuyar" "tayi mata ciwo, kawai ta fita daga ɗakin ta bar shi, yana ƙyaƙyata dariya." *** "Indabo yana ta shiri zai koma Abuja, hutunsu na majalissa ya ƙare, ga shirye-shiryen da ake yi na" "fara zaɓen fidda gwani, wanda yake ta fafutuka a tabattar da yarjejeniyar da suka yi na ba wa Abdul takarar mataimakin gwamna. Sai dai sai fama yake da shi, idan yayi nan sai yayi can." "Naja'atu Bunkure ce ta kira shi a waya, ta ce masa tana office ɗin sa na gidansa, tana son ganinsa." "Ya san muddin ta yi masa zuwan gaggawa ba bu sanarwa, akwai damuwa ne, dan haka ya ajiye" "abun da yake yi, ya fita." "Ya shiga ya zauna yana faɗin ""Naja'atu masu ƙasa ya ake ciki ne?""" "Ta kalleshi ta ce ""Ina Abdul?""" """Oho masa, yana can tasa shiririta ya tattara ya koma gidansa da zama""" """Akwai ƙura fa""" "Indabo ya ce ""Wace irin ƙura kuma?""" """Yaya yayi da yarinyar da ya yi wa fyaɗe?""" "Indabo ya ce ""Mun yi magana da shi, ya ce mini ya kasheta""" """Ka tabattar da hakan kuma? Akwai matsala fa. Wata shegiyar yarinya ta zo office ɗina, wai na bata bayanan in da aka tsaya da maganar yarinyar, wai zata tsayawa mai gadin nan, hankalina ya kasa kwanciya jikina yana bani, ba itakaɗai take wannan abun ba, akwai abun da ta taka, duk da na kira law firm ɗin su na yi musu warning, amma jikina yana bani akwai wata a ƙasa, kar ta" "zurafafa ta gano wani abu, dan yarinyar a tsaye take babu alamar kunya a tare da ita""." "Indabo ya ce ""Kin daɗe kina magance matsaloli da rigingimun da Abdul yake ɗaukkowa, amma" "ya aka yi na ga karaya a tare da ke yau?""" """Ba karaya nayi ba, ka san hausawa sun ce, rana dubu ta ɓarawo, ɗaya tak ta mai kaya, na so ƙ arasa aikin da kaina, amma ka ce na bari zai yi maganin abun, ka nemo ɗanka ka tabattar da bai bar wani trace ba, gobe in Allah ya kaimu zan tafi conference ɗin da shugaban ƙasa ya tura mu," "dan haka ba zan samu damar zuwa gidan su yarinyar ba, dan haka ka nemo shi""" "Indabo ya ce ""Naja'atu, idan aka samu matsala the blame will be on you, sakacinki ne""" "Naja ta girgiza kai ta ce ""Sakacinku dai, na yi iya yi na ni, yadda ku ka yi da shi, ka sanar da ni""" "Indabo cikin hanzari, ya ɗauki wayarsa yana kiran Abdul, sai dai wayar taƙi shiga gaba ɗaya." "Nabila har wata ramar dole tayi, saboda zirga-zirga, gashi kwana biyu ba ta je wurin Viper ba," gashi tana cikin damuwa da tsananin son ganinsa. "Gaba ɗaya yanzu ba ta doguwar shawara, kafin ta tafi gidan Viper, yau ma haka babu tsammani" sai ganinta suka yi rana tsaka. "Duk suka bi ta da kallo, ta kalli Walid ta ce ""Ina wuni""" """Lafiya ƙalau""" """Ya mutumina, ina fatan yana lafiya?""" "Walid ya ce ""To da sauƙi dai, yana ciki""" "Liti ya ce ""Wallahi ba zata shiga ba, ke ware, ni fa ban yarda da yarinyar nan ba""." "Nabila ta kalli liti ta ce ""Ka kiyaye ni fa, ba ruwanka da ni, ba wurinka na zo ba, wurin Viper na zo," "zan duba lafiyar sa kuma mu yi magana""" "Walid ya ce ""Dan Allah liti ka daina haka, mana wai me ta yi maka ne, ta bayar da haƙurin abun" "da tayi ai""" "Liti ya ce ""Ni fa ba a iya yaudarata cikin sauƙi, fita malama, ba zaki ganshi ba""" """Ba zan tafi ba sai na ganshi, ba ruwanka da ni""." "Ya zazzaro mata ido zai yi magana, ya ji an hankaɗe shi daga bakin ƙofa, Viper ya fito yana ƙanƙ" ance idanunsa. "Suna haɗa ido, ta sakar masa murmushi, mai cike da nuna farincikin ganinsa, duk kallon na sa" tsoro yake bata. "Liti ya ce ""Mai zamani mai hakan yake nufi? Kai ma ka yarda da wannan munafukar, ita fa ta saka" "aka kama maka ni, aka rufe ni so take sai an kama ka fa""." "Walid ya ce ""Kai ɗin uwar me ka ke tsinana masa?""" "Duk bai kula su ba, ya taka ya fito ya ɗauki brush da toothpaste, ya matsa." """Ina kwana"" tayi maganar tana bin bayansa. Bai amsa ba, ya durƙusa yana wanke bakinsa." "Wayarta da take ta vibrating ta ciro, ta saka a kunnenta ta ce ""Hello""" """Ke Sumayya ce""" """Ohh sumy, kullum cikin sauya lamba kamar 'yar yahoo?""" """Malama kwana nawa ina nemanki a waya ban same ki ba, kuma baki neme ni ba""" "Nabila ta ce ""Sorry na yi laifi""" "Sumayya ta ce ""Yaya ku ka yi da Naja'atu baki gaya mini ba""" "Nabila ta ce ""Ke zan zo gida na baki labari, ina wani abun ne yanzu, dan na kusa rubuta resigning na ajiye musu tsiyar su, na fuskanci Naja'atu Bunkure gaba da gaba, naga gani take ita wata jan wuya ce, ko ban kaita ƙasa ba sai na razanata"" gaba ɗaya suka zuba wa Nabila ido, cikin hanzari" "Viper ya ɗago ya zubawa Nabila ido, ta katse wayar ta ce" """Meyafaru ku ke kallona ne?""" """Naja'atu Bunkure"" ya maimaita yana kallon idon Nabila." "Cikin rawar baki, saboda tsorata da kallon da yake yi mata ta ce ""Ka santa ne?""" """Mu je waje mu yi magana""" Ayshercool 08081012143 ₦500 ne via 0009450228 Aisha Adam jaiz bank sai shaidar biya ta 08081012143 Wanda za su jira document 1K ne. 90009343 'Yan Nijar ku turo katin airtel na 300fcfa Arewabooks ayshercool7724 "Jikinta ne ya hau tsuma, saboda irin kallon da yake yi mata, yayi gaba da nufin ta bi bayan shi," "amma ta ƙi, ya tsaya ya waiwayo yana kallonta, ta kalli Walid, ya gyaɗa mata kai alamar ta bi shi." "Kamar mara gaskiya haka ta bi bayansa, sai da suka ɗan yi nesa da gidan kaɗan, sannan ya" "waiwayo ya kalleta ya ce ""Me ki ke nema a wurina?""" "Ta kalleshi ta sunkuyar da kai. ""Ki yi mini magana, me ki ke nema a wurina? Meyasa ki ke sintirin zuwa in da nake? Idan so ki ke a kama ni, ki kawo su su kama ni mana, wace irin yarinya ce ke" "ne?""" "Yadda yake maganar cikin hargowa, sai da ta ja da baya, saboda tsoro." """Talk! Me ki ke so, waye ya turo ki?""" """Ni ba wanda ya turo ni"" ta yi maganar cike da tsoro." """Me ki ke nema?""" "A sangarce ta ce ""Ni ka daina yi mini magana a haka, tsorata ni ka ke yi, ni ban san me zan ce" "maka ba""ta yi maganar tana kawar da kanta gefe." "Ya tsareta da idanunsa, ita kuma taƙi ɗagowa, ta sunkuyar da kanta ƙasa tana haɗe fuska cikin" tsoro. "Ya sunkuyo dai-dai tsawon ta ya ce ""Ki bani amsa"" tayi shiru ta ƙi magana." "Hakan ya ƙara hasala shi, ya buga ƙafarsa ya ce ""Ki yi magana kan na saka ki yi ta ƙarfin tsiya""" "Cikin rauni ta ce ""Na gaya maka, ni babu wanda ya turo ni, ni na turo kaina, kuma ni tsoro ka ke" "bani ban san ta ina zan fara ba, tsorata ni ka ke yi""" "Ba ta ƙarasa maganar cikin nutsuwa ba, ta ji hannunsa a wuyanta. ""Naja'atu Bunkure, meye alaƙ arki da ita? Ita ki ke yi wa aiki a kaina, da ita da Indabo ko?"" Ba ta yi masa magana ba, sai idanuwanta da suka yo waje, ga hawaye na bin fuskarta, sai dai kallon da ta yi masa, ya sanya ƙ" "irjinsa bugawa da ƙarfi, ya saketa ya ja da baya, yana dafe saitin zuciyarsa." "Dai-dai lokacin Walid ya ƙaraso ya ce ""Viper meyasa ka ke haka ne? Ban sanka da cin zarafin mata ba, meyasa ka ke ƙoƙarin farawa yanzu?"" Ya nuna Nabila da yatsansa, amma ya kasa" "magana sai haki yake yi, saboda zuciyarsa ta ƙi nutsuwa. Ta ƙura masa ido, tana kuka." "Kawai ya juya ya bar wurin, Walid ya ce ""Sannu, kin ga abun da nake guje miki a kansa ko? Shiyasa na ce ki daina zuwa anyhow. Mun gode da gudunmawarki ga ɗan uwanmu, amma ki" "daina zuwan nan, ina tsoron yayi miki illa wataran""." "Ta girgiza kai ta share hawayenta ta ce ""Ina da kafiya wasu lokutan, haryanzu ban ji cewar zan karaya ba, da ya bi ni a sannu, da zan yi masa bayanin abun da ya haɗa ni da Naja'atu Bunkure. Kawai ji nake ya zame mini wajibi na taimake shi, ina son sanin ƙarshen labarinsa, har cikin zuciyata nake son ba shi gudunmawa, na yi masa uzuri, wataran ba zai yi mini haka ba, bari na tafi. Ayyuka sun yi mini yawa ne sosai, amma ina nan zan je wurin likitan ƙwaƙwalwar, zan kuma" "dawowa""" "Walid ya girgiza mata kai ya ce ""Rayuwarki fa, ke kanki zaki jefa kanki cikin hatsari""" "Nabila ta share hawayenta ta ce ""Kar ka damu da ni, shi ɗin a ceto rayuwar sa da hankalinsa, a ƙ" "wato masa hakkinsa, ba a san amfanin da zai yi wa al'umma nan gaba ba, ina son kamo bakin zaren lamarin ne, bari na tafi"" ta juya ta tafi." "Walid ya girgiza kai, duk haryanzu bai tabattar da manufar Nabila a kan Al'amin ba, amma a" jikinsa yake jin ba zata cutar da shi ba. "Ya koma gidan su, ya tarar da Al'amin ya cika yayi fam, ya kalle shi ya ce ""Mai zamani ba ka" "kyautawa gaskiya, shi yaƙi ɗan zamba ne, ko da turotan aka yi, sai ka bari mu bi komai a hankali, haka Ƙanwata tayi ta fama da kai, da wannan zafin zuciyar ta ka, ƙarshe ta zame maka sanyin" "idaniyarka. Ka din ga bin komai a hankali, bamu san mai gobe za ta haifar ba, kar ka daki kwano." "Ina son mu ƙara zurafafa bincike a kanta, wanda na yi bai gamsar da ni ba""" """Mai laya""" """Viper""" """Ka ƙyale ni da maganar yarinyar nan""" "Walid ya ce ""Ba zan ƙyaleka ba, sai ka fuskanci gaskiya Viper""." "Nabila tana tafe, tana mamakin dalilin da ya sanya Viper yake son kasheta wasu lokutan, amma" meyasa ya rikice haka da ya ji ta ambaci Naja'atu Bunkure?. "Gaba ɗaya al'amuran case ɗin Viper sarƙaƙiyarsu ta yi yawa, a labarin da Walid ya bata, ba ta ji" "in da Najar tayi masa wani abu ba, kodayeke haryanzu labarin bai kammala ba." "Gida ta yi niyyar tafiya, dan kanta ciwo yake yi mata, amma kwana biyu ba ta haɗu da sumayya ba, kuma gashi ba ta bata labarin karonta da Naja'atu ba, dan haka ta kira nufi gidan radiyon su" Sumayya. *** "Ramma na zaune na karyawa take kallon Abdul, yadda ya sha kunu, yana video call da wani likita, yana yi masa bayani, a kan wani result na patient da ya turo masa, yanayin yadda yake bayanin ya tabattar mata da ya san abun da yake yi. Sai da ya gama sannan ya rufe tab ɗin, ya kalleta ya ce" """Kalli gabanki kar ki lashe ni""" "Ta kwaɓe baki ta ce ""Ban ga abun lasa a jikinka ba, jiki duk najasa""." "Cikin ko in kula ya ce ""Haka dai ki ke zaune da ni"" tayi guntun tsaki, ta cigaba da tauna a hankali." "Can ta sake kallonsa ta ce ""Abdul yasar""" "Ya ce ""Your excellency""" "Ta ɓata fuska ta ce ""Ba na son wata your excellency""." """Ke ba abun alfaharinki bane ba, ace ke yarinyar deputy governor ce ba""" """Malam ka daina zaƙewa ba zaka taɓa ci ba, ai shugaba nagari ake fata, kai idan ka zama shugaba" "ai ina ga sai ka halatta zina, tun da gaka bature, yahudawa ne abun koyinka""" "Ya girgiza kai ya ce ""A'a iskancin nawa bai kai nan ba""" "Ramma ta ce ""Ga wanda bai sanka ba ba, ni tambayarka zan yi, wai dan Allah da gaske kai likita" "ne? Mamaki nake yi"" yayi mata banza yana shan tea." """Taɓ, kura da fatar akuya, ba su san har giya ka ke sha ba, ashe wataran zaka yi kisan kai, ko ma in ce kana yi. Saboda irinka wasu mazan suke raka mata asibiti, dan tsaf zaka yi wa matan mutane ɓ" "arna tun da ka saba"" yadda ya dire kofin yana kallonta ne ya sanya ta sha jinin jikinta." """Meyasa ba ki da ɗa'a?""" """Saboda ɗa'a muhalli ne da ita, nan kuma ba wurin da ya dace na nuna ta bane""" "Ya jinjina kai ya ce ""Haka ne, duk matar da na yi lalata da ita, ita ta kawo mini kanta, kar ki ƙara" "yi mini irin haka""" """Nima ni na kawo maka kaina kenan ko? Baka da kunya ko kaɗan, sai dai idan ka gama kumburin ka fashe, har abada mutumin banza ka ke a idona, 'ya mace ba ta taɓa mantawa da wanda ya kawar mata da mutunci, ko da kuwa ta hanyar aure ne, balle ta mummunar hanya, irin wadda ka yi mini, wallahi ban da zuciyar musulunci da tuni na kashe kaina na huta, kaf danginmu babu mazinaci," "amma ni kalle ni yanzu. Tsaki yayi, ya tashi ya zai fice." """Wallahi duk in da zaka je, Allah ya isata, na nan na bibiyarka har kabarinka"" Dummm ƙirjinsa ya" "buga, ya waiwayo yana kallon ramma da ke ta uban kuka." "Bai taɓa dana sanin aikata duk wani laifi da yake yi ba, sai a kan fyaɗen da ya yi wa ramma. Galibin saɓon da yake yi, tsakaninsa da Ubangiji ne, ba a taɓa tsayawa gaba da gaba, ana tsine masa da yi masa Allah ya isa ba, ya sha attempting ya mayar da ita, amma sai ya ji ba zai iya rabuwa da ita ba, kuma kamar yadda take yawan faɗa, ya riga ya gama lalata mata rayuwa, ba za" ta yi daraja a idon jama'a ba. "Motarsa ya shiga, ya tarar da wayoyinsa a ciki suka kwana, a buge ya dawo jiya tab ɗin sa ce kawai a cikin gidan, missed calls ɗin mahaifinsa babu adadi, ga na Naja'atu Bunkure, banda na mahaifiyarsa. Tunani yake yi ko lafiya ake yi masa wannan uban kiran hakan, shi ya san bai yi" wani laifin ba balle ace. "Haka ya ja mota, ya nufi gidan su, yana jin yadda Allah ya isan ramma, ke ƙara yi masa amsa" kuwwa. "Falon indabo ya nufa, ya na zuwa ya hau shi da faɗa, ""Wane irin rashin mutunci ne zai sanya ka ƙ i ɗaga waya tun jiya? Har na fara tunanin wani abun ne ya same ka? Kana can mashaya kana iskancin naka daka saba ko? Wallahi ka nutsu ba za ka lalata mini siyasa da shirina a banza a wofi ba, saboda shashancinka da rashin sanin ciwon kai ba, dole ka san abun da ka ke ciki ka shiga" "hankalinka""" "Zama yayi ya haɗe rai, yaƙi magana, har Indabo yayi masifarsa ya gama, sai da ya gama haki," "sannan ya ce ""Jiya Naja'atu ta zo mini hankali a tashe, yarinyar da ka yi wa fyaɗe, mutumin da aka ce shi yayi, wata lawyer za ta tsaya masa, ta je har office ɗin Naja'atu neman in da aka tsaya a case ɗin. Ina tsoron ranar da abokan adawa za su ɗagomu, ko su bankaɗo miyagun laifukan da ka" "ke aikatawa. Yanzu ina ka kai yarinyar yaya aka yi da ita?""" """Ban sani ba, wace yarinyar nake magana a kai? Yarinyar da ka yi wa lalatar nake yi maka" "magana""." """Amm...m...wai ita rahama?""" """Kai ka sani, ina tambayar ka kana tambayata?""" "Abdul ya ce ""Ba Naja ce ta je ba, zata ba su kuɗi a rufe zancen ba?""" """Zan kife ka da mari wallahi, uban najar, ba ta je ba suka ƙi karɓar kuɗin, suka ce sai an karɓar musu hakkinsu ba? Ka ce mini zaka kashe yarinyar yaya ka yi da ita? Sannna yaya ka yi da uwar yarinyar, muddin case ɗin ya cigaba aka samu sani leakage mun kaɗe, zan iya asarar wannan" "wahalar ta wa, takarar ma ba zaka samu ba""." "Abdul ya dubi Indabo ya ce ""Amma daddy ka riƙe muƙamai da dama a garin nan da ƙasar nan," "kai yakamata ace ka zama governor nan ba ma deputy governor ba da ka ke ƙoƙarin ɗora ni a kai ba, ni da ka bar ni da sabgar siyasar nan takura mini za ayi na kasa sukuni yadda nake so""." "Indabo ya jinjina kai ya ce ""Taɓɗijan, bilki anya ni na haifi yaron nan kuwa? Kina jin abun da" "yake faɗa?""" "Ta sha kunu ta ce ""Wace irin magana ce wannan ka ke yi?""" """Ki na jin abun da yake gaya mini, Abdul siyasa lissafi ce, idan ya ƙwace maka, babu wata fomular da zata yi maka solving duk wani hardship da zaka shiga. Na gama da jihar nan, sonake ka riƙa mini, sama nake tunani tawagarmu mu ƙarasa mamaye ƙasar nan, komai a lissafe nake" "yin sa""." "Abdul ya yi ajiyar zuciya ya ce ""Yarinyar ta mutu ai, babarta ce take nan""" """Ka tabattar?""" "Abdul ya jinjina kai. Indabo ya ce ""Dole aje a nemo babarta, ita ma a kawar da ita, kar su ɓata" "mana aiki""" "Cikin tashin hankali ya ce ""Ita ma wai kashetan za ayi?""" "Indabo ya ce ""To me za ayi idan ba a kasheta ba? Sai asirinmu ya tonu kuma, sannan azo a fara" neman mafita?. "And na ɗaga komawata Abuja, sai Allah ya kaimu weekends, kai kuma zaka tafi jibi in Allah ya" "kaimu, akwai meeting da shugabannin jam'iyya na ƙasa da na jiha, sannan akwai meeting na musamman da deligates, dan dai a samu ayi nasara. Sai ka je ka yi shiri ka bar ni da sauran""" "Gaba ɗaya jikin Abdul ya yi sanyi, ya tsare mahaifinsa da ido." """Menene kuma ka tsaya kana kallona? Kafin ƙarshen watan nan kuma za a kai kuɗin aurenka," "gidan party chairman kai da 'yar sa""." "Abdul ya murza goshinsa, saboda yadda kansa yake sara masa, gaba ɗaya ya rasa abun yi." *** "A nutse sumayya take kallon Nabila ta ce ""Arfa, idanunki sun nuna akwai damuwa, meyake damunki ne kamar ma fa kuka ki ka yi"" kamar Sumayya ta soso mata wurin da yake yi mata ƙaiƙ ayi, kawai ta saka mata kuka." "Sumayya ta ce ""Matsalata da ke kenan, shagwaɓa arfa"" ta share hawayenta tana zumɓura baki." "Sumayya ta yi murmushi ta ce ""Ƙila fa ba wani abin kirki ne ya saki kukan ba, ina jinki ko duk" "Najar ce, yaya ku ka yi da ita?""" "Nabila ta ce ""Wannan ai azzalumar mace ce"" nan ta gaya wa Sumayya yadda suka yi." "Sumayya ta jinjina kai ta ce ""To hakan ne ya saki kuka?"" Nabila ta girgiza kai ta ce ""Ke na gaji ne," "kaina ya ɗauki caji, kin ga rashin mutuncin da barrister Kabir ma yayi mini duk saboda ita, ni kamar na karaya ma, amma wallahi ba zan janye ba""" "Sumayya ta yi dariya ta ce ""Manya gatan wasa, karaya ba taki ba ce ba, akwai ƙalubale sosai a duk wata nasara da ake son cimma, dan haka ki yi haƙuri ki cigaba da addu'a, In sha Allah sai kin" "cika burinki a kan Naja'atu""." """Wallahi sumy da kamar na karaya, amma ba zan karayan ba in sha Allah, sai na cika burina""" """Yauwwa mutuniyar Viper"" da sauri Nabila ta kalleta ta ce ""Me ki ka ce?""" """Mutuniyar Viper mana, ko shi yanzu kin ɗaga masa ƙafa, kin haƙura da nemansa kin koma kan" "fansarki ta naja'atu bunkure?""" "Nabila ta ƙurawa fuskar Sumayya ido ta ce ""Al'amin mai dogon zamani"" tayi maganar tana" murmushi. "Sumayya ta ce ""Ban gane ba""" """Kawai shaƙar da yayi mini nake tunawa ne, na kusa sheƙawa""." """Amma haryanzu ba ki sanarwa DSP ba, yakamata ki tamakawa aikinsa fa""" "Nabila ta ce ""Taɓ haka kurum ya gaya wa Abba, ya saka Abba ya harbe ni da bindiga har lahira," "na je wurin ɗan daba, ba dani ba bari na tafi gida, marata ma ciwo take""" "Nabila ta tashi, sumayya ma ta tashi za ta rakata, a reception suka haɗu da P.A, gaban sumayya ya" "faɗi, ya din ga bin su da kallo, ita da Nabila." """Malam ka kalli gabanka mana, ji jaraba zai saka na faɗi"" Nabila ta yi maganar cikin ɗaga murya" tana kallon P.A "Sumayya ta ce ""Na shiga uku, haba Arfa, babba ki ke yi wa haka?""" """To waye ya ce ya kalle ni?""" "P.A ya ce ""Yi haƙuri, wallahi kallon sani nake yi miki ne, kina yi mini kama da wata da na sani""" "Nabila ta kwaɓe baki, yayin da jikin sumayya ya hau rawa." "Ya ce ""Sumayya wurinki na zo fa"" gaba ɗaya sumayya ta rikice, dan kar P.A yayi wani abun da" "zai sanya Nabila gane wani abun, dan sharp brain ce da ita sosai." "Nabila ta ce ""Bar rakiyar kawai, ni na tafi sai mun yi waya, kuma ki daina ccacanza lambobi kina" "kirana, kamar wata mara gaskiya ko 'yar 419, idan na kira layinki ba zaki ɗaga ba, sai ki yi ta canza lamba"" gaban sumayya ya faɗi, mussaman kallon da P.A yayi mata." "Cikin yaƙe Sumayya ta ce ""Layina ne yake bani matslaa, sai mun yi waya""." "P.A ya tasa ta a gaba, zuwa news room, in da take aiki, ya rufe ƙofa ya kalleta ya ce ""Wato canza" "lamba ki ke yi ki yi waya da ita ko?""." "Sumayya ta ce ""Ban san me zaku iya yi mata ba, dole sai na tantance abun zan din ga gaya muku a" "kanta""." """Haka muka yi da ke? Kin zaɓi ki salwantar da rayuwarta kenan?""" """Ba zan salwantar da rayuwarta ba, kuma babu abun da zai same ta sai wanda Allah ya ƙaddara mata, ku bani a hankali ai ina sanar muku da duk wani abu da take aikatawa kamar yadda ku ka bu" "ƙata. Menene na biyo ni nan kuma, ka yi mini magana a gabanta sai ta gane""." "P.A ya ce ""Ta gane me? Muddin ki ka bari ta gane, sai ta zama gawa, an sanar mini ta zo ne, kuma" "na san muddin ta zo, wani muhimmin abun ne ya kawo ta. Me yake faruwa? Dan kar ki yi zaton ke kaɗai ki ke yi mana aiki, duk motsinki kema ana saka mana ido a kai""." "Sumayya ta yi ajiyar zuciya ta ce ""Zauna mu yi magana""." "Nabila kuwa bayan ta fito harabar radiyon, still motar nan ta sake gani, wadda aka taɓa bin ta da" "ita, ta ganta a law firm ɗin su, yanzu ma gata a gidan rediyon su Sumayya, kuma lambar motar ce ta sake tabattar mata da motar ce dai." "Wani guntun murmushi ta yi ta ce ""Bari dai na ga ƙwal uwar daka""." *** "Ramma ba ta sake ganin Abdul ba sai can dare, ba ta yi zaton zai kulata ba ma, ta ɗauka fushin" "da yayi ne ya hana shi dawowa, dan har ta fara bacci, ta ji motsinsa a bedroom ɗin. Ta buɗe ido ta kalleshi, ta ga bai kulata ba. ""Kayi dare da yawa yau"" ya waiwaya ya kalleta ya ce ""Idonki biyu?""" """A'a motsinka ne ya tashe ni""" """Barin gidan nan zamu yi, gobe in Allah ya kaimu"" cikin rashin fahimta ta ce ""Saboda me?""" """Wani dalili kawai, zan yi tafiya ne na sati ɗaya""" """Kuma ka tafi ka bar ni nikaɗai?""" "Ya ce ""Eh babu abun da zai same ki, can zamu koma gaba ɗaya, bana son a gano ki a nan""." "Ta taɓe baki ta ce ""Kana nufin dai haka zan cigaba da zama kenan?""" """A'a ina tunani a kan zaman mu""" "Tayi shiru, ta gyara kwanciyar ta, ta cigaba da baccinta." "Juya tayi, ta ganshi a zaune, yana hana haɗa ƙwayoyi, ya ɓalle wannan ya ɓalli waccan. Matsawa ta yi ta ƙwace ta ce ""Ba zaka sha wannan ƙwayoyin ka mayar da ni jakarka ba, ba zai yiwu ba, wallahi ko na bar maka ɗakin"" a sanyaye ya ce ""Ba wanda ki ke tunani bane ba, damuwace ta ɗan yi mini yawa, bacci nake son na yi"" ta saka hannu ta kwashe packets ɗin ta ce ""Kai kamar ba likita ba, anya ma ba likitan bogi bane ba, haryanzu ina tantama babu likitan kirki" "da zai yi abun da ka ke yi""." """Ke ba zaki gane ba ne, ki bani kawai idan ba haka ba, baccin ba zai yiwu ba""." """Aikuwa sai dai kar ka yi"" ta watsa su bayan gadon, ta gyara kwanciyar ta." *** "Nabila tana zaune, tana kaɗa ƙafa tana cin gugguru, ta na zancen zuci, ta kalli wayarta da take" "silent, sai haske take yi, ta saka hannu ta ɗauka, ta saka a kunnenta." """Hello barka da dare""" "A hankali ta ce ""Yauwwa""" """Ya gida aiki?""" """Alhamdilillah""" """Na ce ina da ƙorafi, a taimaka mini an ce na je office, na je sau biyu ba kya nan""" "Ta yamutsa fuska ta ce ""Wake magana ne?""" "Ya ce ""Ni ne""" """To kai wa?""" """Bawan Allah, ni ne na kira ki rannan. Wataƙila ina da magana mai muhimmanci da ke""." "Nabila ta yi guntun tsaki ta ce ""Da maganar mai muhimmanci har haka, da ba a waya zaka tsaya" "kana zagaye-zagaye ba"". Ta katsewayar, tana cigaba da ɓata fuska." "Lambar Viper ta kira, ta na jiran ya ɗaga, har ta sare da zai ɗaga, ta ji ya ɗaga wayar." "Tayi gyaran murya ta ce ""Ka na ji na? Na san ma kana ji, ba magana zaka yi ba. An ce baka taɓa mata, amma ni kullum burinka ka kashe ni, ka yi ta shaƙe ni, ko cikakkiyar lafiya ba ni da ita, idan ka yi haƙuri ka ba a hankali zan yi maka bayanin komai, amma ka fiye zafin zuciya haryanzu maƙ" "ogwarona kamar an shaƙeni da ƙarfe nake ji"" ta yi maganar har da kukan kissa." Yayi shiru yana sauraren ta. """Ba zan yi zuciya na daina zuwa ba, har sai ka gaya mini sauran labarin nan, na ji ina 'yar madara take, ina son saninta, akwai abubuwan koyi da yawa a rayuwar ta. Zan sake dawowa in sha Allah," "amma ka rage zafin rai dan Allah, mu yi magana ta fahimta""" "Nasir ne ya shigo ɗakin unexpected, ta ɗaga kai ta kalleshi, ya ƙura mata ido." "Ba ta canza daga yadda take ba, ta ce ""Sai anjima, zamu yi magana"" ta katse kiran ta kalli Nasir ta" "ce ""Yaya shigowa ba excuse?""" """Da wa ki ke waya?"" Ta gyaɗa kai ta ce ""Wani ne""" """Wani wa?""" """Is confidential""" "Ya ƙura mata ido ya ce ""Confidential as how?""" """Haba Yaya, client ɗina ne fa""" """Amma ki ke wannan kashe muryar?""" "Ta ce ""Ikon Allah, to ai he's not just a client, ammm"" ba ta ƙarasa ba ya juya ya fice, ta yi ajiyar ta" "ce ""Ohh ni Nabila, yaya ai sai dai ka yi haƙuri""" "Walid ne ya shigo ɗakin, dawowarsa kenan, ya tarar da Viper, a ɗakinsa, yana goge wuƙarsa" sweazland. Ɗan mama kuma na zaune a gefensa. "Zaro ido ya yi ya ce ""Me zan gani haka? Viper waye ya ɗaukko wannan wuƙar, ya kawo maka?""" Al'amin yayi shiru yana jujjuyata a hannunsa. "Ya kalli ɗan mama da yake sunkuyar da kai, aikuwa a fusace ya saka ƙafa ya daki ɗan mama ya" "ce ""Amma an yi shegen yaro, wallahi baka da mutunci ɗan mama, uban wa ye ya ce ka ɗaukko masa wuƙar nan?""" "Ɗan mama ya ce ""To wai ya zan yi dan Allah? Cewa yayi sai na ɗaukko masa, kuma Oga liti ne" "ya ɗaukko ya bani, wai operation za su fita gobe, Madaki yana cikin gari""" "Walid ya din ga ɗurawa Ɗan mama ashariya, ya juya ya nufi Viper, Amma Viper ya miƙe tsaye," ya fito da harshen sa waje ya mayar. "Walid ya nuna kansa ya ce ""Ni zaka sakawa ƙarfe?""" """Ƙwarai, muddin ka yi ƙoƙarin dakatar da ni, wallahi jininka za ta sha, ai na gaya maka ka nesanta yarinyar da ni, muddin ina ganinta ba ni da wata nutsuwa, dan haka ba ka da ikon, dakatar" "da ni""." "Walid cikin ɓacin rai ya ce ""Hanyar da muke ƙoƙarin bi, ba mai ɓullewa ba ce, ka yi haƙuri""" """Shhhh"" ya yi maganar tsare Walid da ido." """Dalla matsa, ni zaka yi wa barazana, ka je ka yi duk abun da ka ga dama, na daina shiga harka," "tafiya zan yi ku ƙarata da kai da su litin, mu gani idan hanyar za ta fishshe ku""" "Suna cikin faɗa liti ya shigo, suka ya tarar da su, liti ya ce ""Kai walid, ba zaka hanamu abun da" "muke so ba, ka hanamu motsawa, wancan banzan madakin, yana ta rashin mutunci a gari, wallahi" "sai mun ɗauki fansa"" Walid ya fice ya bar musu gidan cikin matsanancin ɓacin rai." *** "Abdul ne da ramma suke tafe a mota, tana ta kallon hanya, ya yi locking ɗin motar, ga glass ɗin ta tint ne." """Wai tafiyar nan ba zata ƙare ba, ni fa na gaji""." """Eh, cinikinki zan je na yi na sayar"" ta harare shi, ta cigaba da kallon titi." "Wata unguwa suka yi, babu gidaje da yawa a wurin, sai tsilla-tsilla, kuma manya manyan gidaje ne," na alfarma a rukunin. "A ƙofar wani ƙaton gida ya tsaya, aka buɗe masa gate, ya shiga, wasu irin manyan karnuka na ta" "kai komo a harabar gidan, ya zagaya yayi parking, ya cire lock ɗin motar, ta buɗe ta fita." "Shi ma ya fito, ya buɗe boot, ya ciro akwatuna, ya ce ""Mu je""" """Yanzu da ka mayar da ni gida, gara ka sake kawo ni nan?""" "Yayi gaba ya ce ""Idan karnuka suka cinyeki, kya taho"" ta bi bayansa tana rarraba ido, gida mai" kyau na alfarma. "Saman bene suka hau, ya kaita wani katafaren bedroom, ya ce ""A nan zaki zauna, zuwa lokacin da zan dawo, kafin nan na samo mafita, zaki iya shiga ko ina, an ajiye duk abun da ki ke buƙata, sai dai ko haraba ba zaki fita ba. Zan ajiye miki waya duk abun da ake ciki, ki kirani ko idan kina" "buƙatar wani abu, wayar lambata kawai zaki iya kira""." """Wai dan Allah nikaɗai zaka bari a gidan nan, ni tsoro nake ji wallahi""" """Ki yi haƙuri mana, ba zan daɗe ba, na ɗan lokaci ne, zaki yi missing ɗi na ko?"" Yayi maganar" "yana kissing ɗin goshinta. Kuka take yi sosai, ya rungumeta yana rarrashin ta." *** "Yau ma kaca-kaca Walid ya yi da su Viper, Liti yana supporting ɗin Viper a kan iya wuya, kawai su afka su ɗauki fansa." "Duk yadda walid ya so fahimtar da su, suka ƙi fahimta." "Nabila ta fara gane kan hanyar zuwa gidan su Viper, kanta baya kullewa kamar da." "Babu tsammani ta yi karo da Walid, ta ja ta tsaya, ta zata zai yi mata masifa, ta ce ""Ina wuni?""" """Lafiya ƙalau""" """Amm yana ina?""" "Ya nuna mata dutsen da yake can gaba, ya ce ""Yana can, amma ki daina wahalar da kanki, taurin" "Al'amin yayi yawa, an ɗaukko masa wuƙarsa, zai je ya yi gaba da gaba da madaki yau, ki ƙyale shi kawai""" "Ta girgiza kai ta ce ""A'a, zan jarraba sa'ata"" tayi gaba ta nufi in da dutsen yake, ba ta ƙarasa ba ta" "hango shi, a zaune a gefen bishiya, cikin inuwa yana ɗan kaɗa ƙafa, ya na shan sigari." "Ta ƙarasa ta zauna a kusa da shi ta ce ""Barka da rana"" bai amsa ba, ta saka hannunta, ta zare sauran karan tabar hannunsa ta ce ""Ayi mini uzuri, ba na son hayaƙi, mara zuciya na sake dawowa." "Dan Allah kar ka shaƙe ni, magana zamu yi ta fahimtar juna""" "Ya ɗaga kai ya kalleta, ya yinƙura ya miƙe, ita ma ta tashi ta tsaya a gaban sa, ka saurare ni ko sau" "ɗaya ne, zafin zuciya da gaggawa shi ya sanya ka rasa da yawan mutane masu muhimmanci a rayuwarka""." "Sweazland ya saka mata a wuyanta, ya ce ""Gargaɗi na ƙarshe, ki rabu da ni, ki fita daga" "rayuwata""." "Ta kalli yadda wuƙar ke ƙyalli a saitin wuyanta ta ce ""Sai na ji ƙarshen labarinka, na ji wa ka" "kashe? Kuma ina jauhar da abun da yake cikinta?""" "Ya kalleta ita ma cikin ƙwarin gwiwa ta cigaba da kallonsa, duk da ƙasan zuciyarta a tsorace" take. """Ki daina kallona a haka, meyasa ki ke son ki zama raunina ne?"" yayi maganar muryarsa na rawa." Ayshercool 08081012143 ₦500 ne via 0009450228 Aisha Adam jaiz bank sai shaidar biya ta 08081012143 Wanda za su jira document 1K ne. 90009343 'Yan Nijar ku turo katin airtel na 300fcfa Arewabooks ayshercool7724 """Meyasa zan zama rauninka ne? Wallahi ba cutar da kai zan yi ba, ba na nufin yin hakan. Idan" "niyyata kenan a baya yanzu na canza tunani, dan Allah ka fahimce ni""." "Ya sauke numfashi ya ce ""Me ki ke buƙata?""" "Ta ce ""To dan girman Allah mu zauna, sai mu yi magana, ba dan ni ba""" "Ya koma ya nemi wuri ya zauna, ta yi ajiyar zuciya, tare da ƙara jinjinawa Jauhar." "Ita ma ta zauna, ya ce ""Ina jinki""" """Kamar yadda na gaya maka da farko, na yi nadamar abun da nayi, wallahi ba ni da niyyar cutar da kai ko kaɗan." "Dan Allah ka yi haƙuri, a shirye nake na taimaka maka, na ƙwato maka hakkinka, da na matarka kai har ma da na yaronka Nura, ko hakan zai sanya na baya su kuɓuta daga irin abun da ya faru da" "ku, amma hakan ba zai yiwu ba, sai ka ƙarasa mini labarin abun da ya faru""" """Bana buƙatar taimakonki, zan yi abun da nake ganin ya dace""" "Ta girgiza kai ta ce ""Bari, ɗan hakin da ka raina, shi ka iya tsole maka ido, ni ko ba dan kowa ba, dan 'yar uwa jauhar, wallahi labarinta kawai da na ji ta tsaye mini a rai, ina sonta saboda girman Allah, rayuwarta abun tausayi ce kuma abar koyi, har cikin zuciyata nake jin raɗaɗin abun da ya faru, ban rayu da ita ba, amma halayenta sun yi mini, sun burgeni kuma duk in da na zauna, zan" "buga misali da su. Dan Allah ka yarda da ni, ka bani haɗin kai""" "Kallon hawayen da take yi yayi, ya ji ina ma shi ne ya samu wannan damar, yake zubar da hawaye ya ji sanyi a ransa. Duk da yadda take ƙular da shi, amma hawayenta ya sanya zuciyarsa motsawa, da jin kamar ya amince mata, ko da cutar da shi za ta yi, tun da ta nuna tausayi da ƙauna ga" "matarsa, haƙiƙa ta samu wani mutunci a idonsa." "Ta share hawayenta ta ce ""Na bibiyi file ɗinka na shari'a, an rubuta kisan kai ake tuhumar ka da shi, wa ka kashe? Garin yaya ka yi kisan kai? An kama ka an sake ka, kuma an dawo ana" "nemanka""." "Ya kaɗa kai ya ce ""An bar jaki ana dukan taiki ba, sun fuskanci ƙarfen cikin wuta ne ni, na fi ƙ" "arfin hannu. Shekara ɗaya, biyu, uku, huɗu, biyar, Naja'atu Bunkure"" yayi maganar yana kallon yatsunsa." "Cikin zaƙuwa ta ce ""Me ta yi maka?" "nima da ka ji ina waya, na yi zancenta, wata yarinya aka yi wa fyaɗe ta shiga case ɗin ta karɓa, kuma an yi wa wani dattijo sharri wai shi yayi mata, alhalin ainihin case ɗin wani ɗan babba ne yayi, wallahi abun da ya sanya na ambaceta kenan a maganata, ba wai aiki nake yi musu ba. Ka yi mini magana dan Allah. Bana fatan ka ɗauki fansa ta hanyar da ba ta dace ba, ba zaka taɓa hucewa ba, ka bari rayuwarsu ta tagyayara tukuna." "One of the biggest fear na masu mulki, shi ne rasa ƙwarin gwiwar su daga mutane, yayin da" "asirinsu ya bankaɗu mutane suka daina yarda da su. Indabo yayi ƙarfin da ka tunkare shi kai tsaye, ba zai yiwu ba." "Kisan mummuƙe yakamata ka yi masa, dan Allah ka gaya mini me Bunkure tayi maka, hakan zai" "taimaka mini a wurin Shari'a""." "Viper ya ce ""Ba na buƙatar wata shari'a, ko wani ya ƙwato mini hakkina, shari'a ita ta fara cin" "zarafina, babu komai a harkar nan ta ku, sai zalunci da son zuciya, taimakon wanda ku ke so, da tozarta wanda ya gaza baku kuɗi duk gaskiyar sa""." "Taji daɗin yadda yake yi mata magana, dan bata taɓa zaton yana magana haka ba." """A'a kar ka ce haka dan Allah, Dan Allah da gaske kisan kai kayi?""" "Ya ce kalleta ido cikin ido ya ce ""Eh, kisan kai nayi, Naja'atu Bunkure made me confess it""" "Ta haɗiye wani abu, ta girgiza kai ta ce ""Ba zan taɓa yadda da hakan ba, labarin Viper da na ji, bai" "taɓa kisan kai ba, wa ka kashe?""" "Tashi yayi, ya ɗauki wuƙarsa yayi gaba, kamar mayya ta tashi ta bishi cikin sauri, amma saurinsa" "ya ninka nata, dan haka ya rigata isa cikin gidan, kafin ta ƙarasa har ya shiga ɗaki ya rufe kansa." "Ta taga ta tsaya tana leƙawa ""Dan Allah ka daina bani bayani guntu-guntu ka ƙarasa mini, hakan" "zai taimaka mini wurin sanin ina zan kama, wa ka kashe dan Allah?""" "Ya tsaya ƙyam ya juya mata baya, ya dafa jikin bango, zuciyarsa tamkar ruwa na tafasa a ƙasan" "gagarumar wuta, haka wani Irin zafi ya din ga taso masa daga ƙirjinsa zuwa ƙwaƙwalwarsa." "Nabila ta din ga bubbuga ƙofar, tana yi masa magiya ya buɗe, amma yaƙi, ta koma ta window, ta" ga tuni ya fara ɗurawa kansa allura. """Dan girman Allah ka bari, lafiyarka da ta ƙwaƙwalwarka, wannan ba mafita ba ce ba, dan Allah" "kar ka illata kanka""." "Liti ya ce ""Zo ki fita, koma uban menene ba ke ce sila ba, uban waye ya ce ki zo, yau ya tashi da" "'yar walwala kawai kin zo kin kuma tunzura shi""." "Cike da tsananin damuwa, da tashin hankali ta baro gidan, tana tunanin to ita menene laifinta, da" suke cewa ita ce sila idan ya ganta yake burkicewa. *** "Ramma ta zubawa Abdul ido, ya haɗa akwatin sa tsaf, ya kalleta ya ce ""Ƙarfe huɗu jirgina zai tashi, dole na shirya da wuri, akwai in da nake son zuwa kafin na tafi""" "Ta turɓune fuska, tayi masa shiru." "Ya zauna kusa da ita, ya ɗago haɓarta yana kallon fuskarta ya ce ""Ya dai?""" """Ni dai kar ka tafi dan Allah, tsoro nake ji wallahi, nikaɗai zan zauna a nan dan Allah""" "Ya kwantar da murya ya ce ""You start missing me?"" Ta girgiza masa kai alamar a'a." """Your excellency, ba iya tsoro ne a idonki ba, missing ɗina zaki yi""" "Ta ture hannunsa ta ce ""Allah ya kiyaye, ni gaskiya tsoro nake ji""" "Abdul ya ce ""Tafiyar nan dole ce, sannan ina son na je garinku yau, zan ce wa mamanki kina" "gaisheta""" "Ta marairaice ta ce ""Dan Allah ka mayar da ni mana""" "Ya girgiza kai ya ce ""Ba yanzu ba""" """Nan gaba zaka mayar da ni?""" """Eh to, sai ƙura ta lafa"" tayi shiru tana wasa da yatsunta." """Ki yi haƙuri, zan dinga kiranki kullum muna magana, idan da wani abun ma sai ki gaya mini, na" "ajiye miki komai na amfani a kitchen, ai kin iya girki ko?"" Ta jinjina masa kai alamar eh." "Ya ce ""Yauwwa your excellency"" ya tashi ya shiga wanka, yana ta shiri, ya zauna a gefen gado" "yana shafa mai, ta riƙe shirt ɗin sa tana kuka." "Nan ya lalace a wurin rarrashin ramma, ""Wai wannan kukan duk dan kar na tafi ne?""" """Ni ina ruwana da tafiyarka, tsoro nake ji ne""" """Ƙarya ki ke yi rahama, faɗi gaskiya dai""" """Ni ba na ƙarya"" tayi maganar tana murguɗa masa baki sannan ta ce ""Kuma wallahi ka bi mata" "Allah ya isa"" bai san lokacin da ya ƙyaƙyace da dariya ba, har sai da ya bata haushi." "Har ƙofar falon ta rako shi, tana kallonsa, ya kasa gane kallon me take yi masa har haka, yayi" "mata sallama, ya sanya mukulli ya kulleta, ya ja akwatinsa." *** "Kan Nabila tamkar zai yi bindiga, ta rasa abun da yake yi mata daɗi, haka ta koma jiki babu daɗi, kanta fal tunani daban daban." "Har ta shirya, zata ci abinci, kawai ta tuna kwana biyu ba ta haɗu da Nasir ba, kuma ba ya shiga" "sabgarta, gashi tana son sanin a ina ya tsaya a binciken Viper, saboda duk yadda za ayi ba ta son" "ya gano Viper ba ta gama na ta binciken ba, idan ya so ko kotu za a shiga, ta shiga da ƙwarin" gwiwar ta. "Gaba ɗaya mayar da hankali a kan aikinta ya sanya, ba ta shiga sabgar yan gidan, hakan ya rage" yawan faɗace-faɗace da suke yi da 'yan gidan. "Ta fito falo, dan ta gaji da zaman ɗaki, abubuwa duk sun dameta, sai ga Nasir yayi sallama a falo," "ta amsa sallamar tana kallon sa, amma ya basar da ita ya nemi wuri ya zauna." "Ta ƙarasa ta zauna a kusa da shi ta ce ""Sannu da zuwa""" """Yauwwa"" ya amsa mata a ciki." """Wai me na yi maka ne ka ke wani share ni?"" Tayi maganar a shagwaɓe." "Rasa me zai ce mata yayi, yai shiru, ya kawar da kansa gefe." "Ta zagaya in da ya kawar da kan ta ce ""Me na yi ne?""" """Bakomai"". ""To ka kula ni mana""." "Nasir ya ce ""Na gaji, kar ki dame ni dan Allah""" """Sai na gaya wa Abba kana hantarata""" "Ya ce ""Sai kin dawo"" ta rausayar da kai ta ce ""To ni dai ka yi haƙuri, dan Allah"" ya kalleta ya ce" """Ya wuce""" """Yauwwa DSP, to ya ake ciki ya aikin?"" Ya gyara zamansa ya ce ""Alhamdilillah, mu na ta fama ya" "naki?""" "Ta kwaɓe baki ta ce ""Babu daɗi, duk na gaji, da fa ajiye aikin zan yi, aka bani haƙuri"" Nan ta bashi" labarin abun da barrister Kabir yayi mata. "Nasir ya ce ""Ke baki da haƙuri ne, shiyasa wasu lokutan ba kya cin ribar abubuwa, ki daina" "gaggawa""" """Ai abun ne ya bani mamaki, daga zuwana wurinta, har an kira barrister Kabir an gaya masa, baka" "ga abun da ya yi mini ba, da cewa na yi sai na gaya wa Abba ma""." "Nasir ya ce ""No, ba za ayi haka ba, duk abun alkhairin da yake yi miki, sai a kan laifi ɗaya ki yi" "fushi""" """To meyasa zai yi mini tijara a kan wata Naja""." "Ya ce ""Hakan yana alamta miki cewa, kin ɗaukko gagarumin abin da sai kin yi kyakywan shiri na" "gaske""." "Tayi ajiyar zuciya ta ce ""Haka ne, ya ake ciki da naka aikin, yaya batun case ɗin Viper, akwai" "cigaba kuwa?""" """Wallahi ba wani cigaban kirki, ina da ta fafutuka, gashi sai hura mini wuta ake yi""" """Kai abun babu daɗi, but you can do it, na yarda da kai ai""." "Mama ce ta fito fuska a haɗe ta ce ""Nasir menene haka?""" "Ya ce ""Mama a ina?""" """Ban sani ba, uban me ka ke zaune a nan ka ke yi? Ka dawo gida tun ɗazu, amma ka gagara shiga" "inda nake?""" "Nasir ya ce ""Wallahi nayi tunanin bacci ki ke yi, shiyasa na yada zango a nan muke magana da" "Arfa, yi haƙuri""" "Nabila ko a jikinta, ta sake gyara zamanta ta kwanta sosai a kan kujerar tana danna waya." "Mama tayi mata wani mugun kallo, ko a jikinta, sai ma wani irin murmushi da tayi." "Messages aka din ga turowa Viper, da private numbrn nan, da ake kiransa da ita." """Muddin ka cigaba da biyewa yarinyar nan, asirinka zai tonu, kuma zata iya rasa rayuwarta a dalilinka, ba ka da sa'a wasu lokutan, kar ka bari ta zama raunin da maƙiyanka za su yi amfani da ita, wurin cimmaka har maɓoyarka"" Ya din ga jujjuya wayar, yana sake tunanin waye wannan, kowaye ya sanshi, ya kuma san in da yake, kuma yana ankare da duk abun da yake yi, amma" meyasa yaƙi bayyana kansa?. "Kiran Nabila ne ya shigo wayarsa," "tana zaune hannunta riƙe da waya a kunnenta tana kiran lambarsa, babu tsammani ta ji ya ɗaga." "Ta kalli agogon ɗakinta, ƙarfe goma daidai na dare." """Barka da dare, duk da ba amsawa zaka yi wa ba. Amma ina fatan kana lafiya?" "Na kasa jurewa ba zan ɓoye maka ba, ban ji daɗin yadda na baro ka ba, muna cikin magana ka tashi ka tafi, kuma ka je ka na yi wa kanka allura, gaba ɗaya ban ji daɗi ba, dan girman Allah ka rufa mini asiri kar ka yi wa kanka illa, ka bari mu yi nasara mu kamo bakin zaren. Na san maybe ka raina gogewa ta, kuma kamar ba zan iya ƙwato maka hakkinka ba, amma na san Allah yana tare da mu, dan Allah ka daina shan abun da zai yi maka illa, ba na jin daɗi, na san yayata ma 'yar" "madara ba zata ji daɗin hakan ba, dan gaskiya sai ta matsa mini na shigo, daga ni sai a rufe. Saboda son da nake yi mata make son mu kasance tare, idan na shiga gidanta, kaga gani ga ta, in ƙara koyon halayenta, in ƙara sonta, amma gaskiya ayi mana adalci, saboda kishi ne da ni sosai da sosai fa, kuma alamu sun nuna mini kana sonta da yawa""" "Kamar mai sauraren karatu, haka ya nutsu yana jin ta, ɗan mama da yake kusa da shi, har kuma le" "ƙa idonsa yake yi, ya ga reaction ɗin da zai yi, tare da jinjina rawar kan Nabila, a gaban Viper ko" "ƙwaƙwaran motsi ba ta iya yi, amma ta sameshi a waya, sai karairaya take yi tana shagwaɓa." "Ta sauke numfashi ta ce ""Bari na ƙyaleka, amma yakamata na san ƙarshen labarin nan, saboda na san yanayin shirin da zan yi, kuma kar sai na gama zaƙewa 'yar madara duk kirkinta ta ce ba zan shigo mata gida ba, dan ni gaskiya idan ba gidanta ba sai rijiya. Sai da safe take care"" tayi maganar tana ajiye wayar, cikinta na kaɗawa saboda ita kanta ta san ba ƙaramar kasada take yi ba, abun da take yi. Amma hanyar da matarsa ta bi ta iya samun kansa da farko, dole ita ma ta bi," "domin cimma nasara, saboda gaba ɗayansa hukuma ne, sai da rarrashi." *** "Sanye yake da face mask, yana tuƙi a hankali, saboda yadda hanyar ta ƙara lalacewa, a ƙofar gidan su ramma yayi parking, ya fito ya tsaya a waje yayi sallama, amma shiru, ya shiga cikin gidan sai dai tsakar gidan babu kowa, ƙofofin ɗakin duk a buɗe." "Ya ɗan jira ko za a shigo, ko fita tayi, amma shiru, ba ta dawo ba." "Ya fita ya tambayi maƙwabta, suka sanar masa kwanaki huɗu kenan, su ma ba su san in da ta tafi" "ba, ba ta yi wa kowa sallama ba." "Yanayin gidan ya tabattar masa da ba fitar nutsuwa tayi ba, ya lissafa shi yanzu kwanaki uku kenan, da mahaifinsa ya kira shi yai masa magana a kan batun ramma balle ya ce ko mahaifinsa" ne. "Yayi shiru yana tunanin to garin yaya haka, ya za ayi ta fita ta bar gida a buɗe haka babu kowa, tsawon kwanaki huɗu, ba ta yi wa kowa sallama ba, lallai akwai wani abu a ƙasa, yanzu me zai" cewa ramma? Ya tambayi kansa. "Lallai akwai wani abu a ƙasa, gashi lokaci na nema ya ƙure masa, ƙarfe huɗu zai tafi." "Saif ya kira a waya, ya sanar masa halin da ake ciki, saif ya ce ""Kuma baka tunanin ko guduwa" "tayi, ko kuma daddy ne yayi mata wani abun?""" "Abdul ya ce ""Bana tunanin haka, shekaranjiya yayi mini zancenta, da shi ya saka aka ɗauke ta zai" "gaya mini, na rasa wani lissafin ma yakamata na yi""" "Saifu ya ce ""Ka tafi kawai, zan tsaya na sake bincikawa, in Allah ya yadda ba wani abu""." "Ya ce ""To shikenan, ina saurarenka dan Allah"" ya ajiye wayar yana cigaba da tunanin lamarin." *** "Abdul yana sauka a Abuja, sai da ya kira Ramma, ya ce mata ya sauka, sai dai ba ta amsa masa ba sai cewa tayi ""Yaya ka baro mini mama? Tana nan lafiya? Ta tambaye ka yaya nake?""" """Ni ba zaki tambayi ya na sauka ba, sai mama kawai?""" """Dan Allah ka gaya mini, ko na ji daɗi""" "Abdul ya ce ""Zan gaya miki da daddare idan na huta"" ya katse wayar yana fargabar ranar da" "ramma ta san halin da ake ciki, bai san ya zai yi ba. Ya san duk laifin shi zata ɗorawa." *** "Katafaren falo ne, ya sha ado da kayan alatu na zamani, manyan mutane ne su uku, zaune a falon wanda kaf ɗin su sanannun fuskoki ne da su a ƙasa." "Kayan shaye-shaye ne a gaban su, suna sha suna hira, gefe ga kayan marmari." """Distinguish ma'aruf Indabo, ya ake ciki ne gaba ɗaya baka walwala?""" """Komai ma ya dame ni ne, Abdul sai so yake yi sai ya watsa mini lissafi, da ƙyar na yaƙo shi, ya" "tafi Abuja, zaman taron nan, nima gobe in Allah ya kaimu zan tafi birnin tarayyar""" """Ya salam, wai meyasa Abdul yake haka ne? Ya san wahalar da muka yi kuwa kafin mu zo nan," "shi me yake damunsa ne?""" "Indabo ya kora ruwan lemon da yake cikin kofin hannunsa, ya ce ""Oho masa, gaba ɗaya na kasa gane kansa, ina tsoron Allah ina tsoron ya aikata wani abun da zai yi dalilin takarar nan, amma ina" "nan na kafa na tsre ina monitoring activities ɗin sa""." """Ohh Allah ya kyauta, ya batun wannan yaron ne da ake nema?""" "Indabo ya girgiza kai ya ce ""Hmm honorable kenan, wallahi kullum da shi nake kwana nake tashi, kamar wani iblishi, ya gagara kamuwa, na rasa uban da yake tsaya masa, sai dai na samo wata yarinya da nake son ayi masa tarko da ita, to ita kanta yarinyar ba ta da cikakken saiti, wata barrister ce, 'yar wani tsohon soja, idan na matsa zata iya tona mana asiri, na saka ana yi mini monitoring ɗin ta, ta hanyar ƙawarta. Saboda wani furuci da tayi. Duk dai na ga hanyoyin ba sa yi mini sauri, na san dole yaron nan bakam yayi mini, at any cost sai na canza dabara, wadda za ta" "ɓulle mini da wuri, na kashe Aminu na huta""" "Haka suka cigaba da jimantawa, tare da tattaunawa da neman mafita, suna yi suna shaye-shaye." "Ramma tana duƙunƙune a cikin bargo, karnukan estate ɗin, da na gidan sai haushi suke yi." "Video call suke yi da Abdul, ta ce ""Ba ka ce mini komai a kan mama ba""" """Mama tana lafiya, ta ce a gaishe ki""" "Ta ce ""Hmm, to ya take, tana cikin damuwa ko? Tayi kuka?""" "Ya ce ""A'a, na bata tabbacin kina nan lafiya, har hotonki na nuna mata""" "Ramma ta ce ""A'a hankalinta ba zai taɓa kwanciya ba, ka manta rashin ɗa'ar da ka yi mata, ranar da ka je ka tabattar mata da kai ka keta mini haddi, kuma ka tafi da ni, ai a yanzu idan akwai" "wanda ta tsana bai wuce ka ba, kodayeke akwai wanda suka yi mata wasu laifuffukan""" "Yayi shiru jiki a sanyaye ya ce ""Laifin da suka yi mata irin nawa ne? Ai na nemi afuwarta""" """Ta ina ka nemi afuwarta? Hmm ta ce ta yafe maka ne? Kai baka ganin girman laifin da ka aikata fa saboda mu talakawa ne kana da kuɗi." "Mama ta sha wahala sosai, gashi duk mun ɗaiɗaice, kaga ƙanina sani daka je?""" "Ya girgiza mata kai ya ce ""Ina ga yana makaranta""" """Shikenan, sai da safe, bari na rintse idona ko zan yi bacci, haushin karnukan nan ya isheni""" "Ya ce ""Ni kuma sanyi ne nan ya dame ni, da muna tare da kin bani ɗumin jikinki""" "Cikin tsiwa ta ce ""Saboda gani heater ko?""" "Ya ce ""No, jikinki akwai ɗumi sosai, da duk ba zan ji wannan sanyin ba""" """Sai da safe""" """Dan Allah ki tsaya ban gama ganinki ba""" "ta ce ""Sai kuma ka yi ai""" """Miƙo bakinki na yi miki kiss""" """Ba na so"" tayi maganar bacci yana kwasarta, tana lumshe ido." "Ya ce ""Rahama""" """Na'am"" ta amsa tana buɗe ido da kyar. Sai kuma yayi shiru yana cigaba da kallon fuskarta, har" "bacci ya kwasheta, yana kallonta, tausayinta ya din ga ratsa zuciyarsa." *** "Yau weekends, Nabila tana gida, tana kai komonta, ta bayar da wankinta ayi mata, ta fito harabar" "gidan tana zagawa, Nasir ya fito da shirin fita." """DSP sai ina? Ko zance za a tafi rana tsaka""" """Wurinki zan zo zancen"" tayi dariya ta ƙarasa gabansa ta ce ""Ina zuwa yanzu?, La'asar ta kusa?""" "Ya kalli agogon hannunsa ya ce ""A kan Viper ne""" "Cikinta yayi ƙuuu, amma ta maze ta ce ""Ya ake ciki?""" "Ya ce ""Eh to, na canza dabara ne, a yanayin neman nasa, mun riga duk mun yi connecting da mutanen unguwar su, an ce yana zuwa gidansa da ya zauna, to kwana biyu bai je ba. Abokin faɗ ansa da na kama kwanaki madaki, an ce ya dawo yana cikin gari, akwai ƙishin-ƙishin na zai iya zuwa unguwar, neman rigima da shi madakin, duk mun baza komar mu, akwai wurin shayin yaransa, an ce ma wurin nasa ne, zuwana biyu wurin cikin fararen kaya, an kwatanta mini wani yaronsa Walid, na haɗu da shi a wurin, amma ko kaɗan ba sa zancensa a wurin. Da na so na zunguro zancen daba ma, na kama sunansa, cewa suka yi na tashi na fita. Ina kyautata zaton wannan Walid ɗin ya san in da yake, motsinsa zan sakawa ido sosai, ana ta yi mini binciken ina yake da zama, da a unguwar suke zaune, amma tun da Viper ya bar prison, sun daina kwana a unguwar sai idan za su yi aikin rabawa ƙanan dealolinsu wiwi. Ba zan motsa da wuri na kama shi Walid ɗin ba ba, kar shi ma ya zille mini, kuma an tabattar mini da ɗan amanrsa ne, ina dai ta bibiyar su ta hanyar mai unguwa, da wasu daga mutanen unguwa. Wanda nake baki labarin nan ma ɗan mama, ya daina zuwa arear da aka gaya mini kai kayan shaye-shayen na su, abun ne dai" "duk sai a hankali""." "Tayi ajiyar zuciya ta ce ""Wani aiki sai mai shi, Allah dai ya ba da sa'a, sannu da ƙoƙari DSP""" """Yauwwa arfan Abba, bari na tafi""" """To yanzu can ɗin zaka tafi?""" """Eh, zan je in sake zaɓar yarana su shiga unguwar su madakin a farin kaya""" "Ta ce ""Shikenan, a sauka lafiya, Allah ya tsare"" ya amsa da Amin, ya nufi motarsa." "Cikin sassarfa, ta nufi ɗakinta, Wayar Viper taƙi shiga, ta din ga kira amma a kashe." "Hankalinta ya ƙara mummunan tashi, har la'asar wayar viper ba ta shiga." "Shiryawa tayi ta saka niƙab, ta lallaɓa ta fice, ba tare da yi wa kowa sallama ba. Sauri take yi tamkar za ta tashi sama haka take fafaka sauri." "A hanya aka fara kiraye-kirayen sallar la'asar, har ta ƙarasa kiran lambarsa take yi, amma shiru" bai ɗaga ba. "Ɗan mama ta tarar a tsakar gida, shikaɗai, yana ta shafawa wuƙaƙe wani abu, da ba ta san ko" "mene ne b. Ya miƙe yana kallonta ya ce ""Dan Allah suna ina?""" """Su wa?""" """Su viper, da sauran""." "Ɗan mama ya ce ""Oga Viper ya fita, ya tafi cikin gari wurin madaki, da shi da Oga liti, Oga walid" "sun yi faɗa ya fita""" "Jikinta na rawa ta ce ""Innalillahi wa Innalillahi raji'un, shi Walid ɗin ina ya tafi? Wai ma meyasa" "Vipern ne yake da taurin kan tsiya, akwai hatsari a hakan fa """ """Ke, Oga Vipern ki ke faɗar baƙar magana a kan shi?""" "Ta juya zata fita ya ce ""Ina zaki?""" """Bin sa zan yi""" "Ya waro ido ya ce ""Ina?""" "Ta tsaya ta kalleshi ta ce ""Dabar madakin, ai na san wurin"" zai yi magana, ta fita da sauri sosai." "Shida saura na yamma, ta isa unguwar su madaki, saboda azalzalar da ta din ga yi wa mai" adaidaita sahun da ta hau. "Ta cikin niƙabinta, take kallon unguwar, ba zata taɓa manta, yadda aka sakar mata karnuka ba," suka kusa cinyeta. "Ta nufi cikin unguwar, sai dai kamar babu mutane, sai ɗaiɗaikun mutane da suke guje-guje." "Ta tsaya tana neman wand zata tambaya meyake faruwa, amma kusan kowa ta kansa yake yi." """Kai ku tafi gida, wannan ɗan tijarar ne ya shigo neman masifa, mai zamani ne da yaransa, suke faɗa da yaran madaki"" taji muryar wani matashi, yana yi wa wasu yara magana"" maimakon ta tsorata sai ta kutsa kai ta cigaba da tafiya tana fatan Ubangiji Allah ya sa kar wani abu ya same shi," Allah ya sa ta ganshi. "Tana saka kai wani layi, ta ga an yanki wani a cinyarsa, jini ya yi tsartuwa, ta gigice cikin tashin" "hankali ta fara ihu, ji tayi an ja hannunta da ƙarfi, an shiga da ita wani layi daban." Ayshercool 0808012143 "Cikin matsanancin tsoro, ta rintse idanunta, zuciyarta na bugawa da sauri sosai." "Da kyar ta iya buɗe ido ta ga wanda ya ja ta, kallo ɗaya ta yi wa idanunsa ta cire nata, saboda" mugun kallon da yake yi mata. """Uban me ya kawo ki nan?"" Mamaki take yi, yaya aka yi ya ganeta da niƙab." """Ba magana nake yi miki ba?""" "Ta ɗaga kai ta kalleshi ta ce ""Haka muka yi da kai? Meyasa zaka fito, kana da tabbacin idan suka kamaka a wannan karon zasu barka da rai ne, ba fa za su yadda su sake wannan kuskuren ba, dan Allah kar ka ɓata mini aiki, dan Allah ka daina fitowa"" mayafin da ya rufe fuskarsa da shi, ya" "sake gyarawa, ya sake damƙar hannunta, ya din ga ratsa hanya da ita, kowa ya gudu gida ya ɓuya." "A haka suka ƙaraso titi ya ɗaga wa wani mai baburin adaidaita sahu hannu, ya yi mata nuni ta" "shiga, shi ma ya shiga." "Ta kalli yadda duhun magariba yayi, sai a lokacin hankalinta ya kai kan me za ta ce a gida." "Ya ciro wayarsa, ya danna wata lamba, ya saka a kunnensa, a hankali yake magana ba ta iya jin me yake cewa a wayar, ya zirawa mai napep ɗin dubu ɗaya ya kama ƙarfen adaidaita sahun, ya" dire ba tare da mai napep ɗin ya tsaya ba. "Cikin sauri ta leƙa, ta ga wani ya tsaya a babur sanye da face mask, Viper ya hau suka yi wani" wurin. "Tana jin yadda wayarta take ta ringing, amma taƙi ko ɗaukkota, balle ta ga waye." "Ta gaya wa mai napep in da zai kaita, tuni aka fara kiraye-kirayen sallar isha'ai, motar Abba ta" "tarar da ta Nasir, alamar duk suna gida, gabanta ya faɗi." "Sannu a hankali ta ƙarasa falon, ta tarar da Abba a tsaye, hannunsa riƙe da waya, take wayarta ta" hau vibrating alamar ita yake kira a waya. "Yayi mta wani irin kallo, da sai da hantar cikinta ta kaɗa." """Daga ina ki ke?""" "Tayi tsuru-tsuru da ido, tana kallonsa." "Nasir ya ce ""Magana fa ake yi miki""" """Amm, Abba dama wallahi wata shaida nake so na haɗu da ita, wani case ne a hannuna shiyasa na" "fita""." "Abba ya ce ""Wa ki ka gaya wa zaki fita?""" "Mama ta ce ""Yaushe za ta gaya mana, tun da bamu isa ba""" """Wato arfa kullum rashin jinki ƙara gaba yake yi ko? Idan baki yi wasa ba, hatta aikin sai na hana" "ki zuwa, an ce tun safe ba kya gidan nan, wace irin shaida ce haka?""" "Nasir ya ce ""A'a har azahar tana nan ina ga da la'asar ta fita""" """Koma menene yanzu yakamata ta shigo gida, ƙarfe takwas da wani abu tun la'asar?""" "Ta sunkuyar da kai ta ce ""Dan Allah Abba ka yi haƙuri, in sha Allah ba zan sake ba""" """Daga yau, ki ka sake fita babu wanda ya sani, zamu gauraya da ke"" ta jinjina masa kai, ta wuce" "tana yi wa Allah godiya, da bai yi mata faɗa sosai ba." "Addu'a ta din ga yi, Allah ya sa kar Viper ya aikata wani abu da za a kama shi, ko kuma ya yi wa" kansa illa. "Gashi ba ta samu sun yi magana a kan abun da ya kaita ba, na shirin da Nasir yake yi na son kama" shi ta hanyar Walid ba. "Madaki ne a tsaye yana kallon Al'amin da yake tsaye a gabansa, duk da duhun dare ne, amma" manyan fitilun solar sun haske ko ina da ina. "Idon Al'amin kamar ana hura wuta, Madaki yayi dariya ya ce ""Mahadi mai dogon zamani, ka ci na wasu gaka kana cin naka. Viper ka ke maciji mai hatsarin gaske, dodon cinnaku masu ƙaryar kaki. Barka da sake haɗuwa da kai a dai-dai wannan lokaci, bayan dogon lokaci bamu yi ido da ido." "Tabbas labarin Mai zamani ba zai taɓa cika ba, sai an ambaci madaki." "Maza gumbar dutse ya ake ciki ne?""" "Yana rufe bakinsa, Al'amin ya soka masa russia a cinyarsa, a take jini ya fara kwarara a jikin" "madaki. Madaki ya kalli cinyarsa, ya kalli Al'amin." "Al'amin ya kalli madaki ya ce ""Na san zaka yi mamakin, yaushe na samu makarin tsafinka, amma na ƙyaleka a raye kana cin karenka babu babbaka." "Yadda daba ta bar mini mugun tabo a zuciyata, ka rubuta ka ajiye, kamar yadda ka ce labarin Viper ba zai cika ba, sai an ambaci sunanka. Ina mai tabbatar maka Viper zai yi maka saran da bai taɓa yi wa wani irinsa ba." "Kamar yadda ka canje ni, ka ke yi wa Indabo aiki, a madadina, ina da saƙon da zan baka ka bashi. Ka gaya masa ya toshe dukkanin ramukan da ke gidansa, ofishin sa da duk wani wuri da yake zuwa, saboda maciji ba ya raina ƙofa komai ƙanƙantarta, kuma ya tsammace ni, ta in da bai taɓa" "zata ba, kuma lokacin da bai taɓa zato ba." "Al'amin na rufe bakinsa, madaki ya saka masa ƙarfe a damtsensa, a take kokawa ta kaure a tsakanin su, sai dai madaki ya kasa sarrafa ƙafar da Viper ya soka masa wuƙa, rabon da a zubar masa da jini har ya manta, saboda laƙanin taurin da yake amfani da shi, fitar masa da jinin da Al'amin yayi, yana nufin laƙanin ya karye, kuma a kowane lokaci, ana iya yi masa rauni da ƙarfe" koma a kashe shi. "Sosai suka din ga yi wa junansu illa da makami, sai dai Madaki ya fara galabaita, dan haka ya fara" "ƙoƙarin guduwa, dan ba ya son wasu su farga cewar ƙarfe ya fara tasiri a jikinsa." "Amma Viper ya hana shi yin hakan, zuciyarsa ta din ga wata irin tafasa, ya din ga saran madaki, madaki ya saka hannu ya shaƙe Viper, take Viper ya ji abun da ya taɓa ji idan madaki ya shaƙe shi," "tamkar an yi masa sarƙa da dutse, ya kasa motsi." "Viper ya ji an saka masa wani abu a gefen wuyansa, a take ya silale ya ya faɗi ƙasa." "Madaki ya ja da baya yana kallon yadd mutumin ya saita shi da bingida, dan bai ga ta in da ya ɓ" ullo ba. """Zaka iya tafiya"" mutumin yayi magana yana nuna masa hanya." "Madaki ya ja jiki da kyar, yana ɗingisa ƙafa ya bar wurin." Wasu mutane manya manya majiya ƙarfi suka ɓullo wurin """Yaya kun tarwatsa yaran?""" """Eh sir, amma fa har an sanar da 'yan sanda zancen rikicin sun taho""" """Maza maza ku ɗauke shi ku tafi da shi, ayi masa treatment, ayi sedating ɗin sa, har a gama yi masa komai, kar ku mayar da shi maɓoyarsa yanzu, a bari zuwa da safe, idan yaransa sun fita nemansa sai ku mayar da shi. Su kuma su musa su tabattar sun goge duk wani trace da zai sanya a" "gane yazo unguwar nan""" """Ok sir""" "Suka cicciɓi Al'amin, suka saka shi a mota, suka ɗauki wuƙarsa da wayarsa, suka tafi." "Har wajen goma na dare, Nabila tana kiran wayar Viper, amma ba ya ɗagawa, hankalinta ya fara tashi, ko wani abu ne ya same shi, amma sai ta tuna, kaɗan da aikinsa ya ƙi ɗagawa mussaman" ma da tayi masa laifi yau. "Liti kuwa bayan ƙura ta lafa, ya koma gida, sai dai bai tarar da Viper ba, sai Walid." """Wai Viper bai dawo ba?"" Yayi maganar yana kallon Walid." Walid yayi masa banza. """Malam magana nake yi maka fa""" """Ban sani ba, da ni kuka fita?""" "Liti yayi tsaki ya ce ""Bari na san yana hanya shi da ɗan mama""" "Walid ya ce ""Ina fatan kun kashe madaki, kun wuce kun kashe Indabo""" """Ban sani ba""" "Walid ya girgiza kai, ya cigaba da abun da yake yi." "Ɗan mama ya shigo shi ma, jikinsa duk jini da alama yayi ɓarna sosai, ya ce ""Oga liti ina Vipern," "ina fatan yana lafiya, ni fa tun da muka afkawa su lakwari, ban sake ganinsa ba""" "Liti ya tashi tsaye ya ce ""Kamar yaya? Ya haɗu da madakin ne?""" """Ai ban sani ba, da muka rabu da ku, wani wurin yayi ai""" """Bari mu jira nan da awa ɗaya mu gani""" "Walid ya ce ""Hmm""" """To yana nan lafiya, ai ba wani abun ne ya same shi ba""" "Walid ya ce ""Na yi maka magana ne?""" """To kama yi mana""" "Walid ya ce ""Wallahi wani abun ya same shi, sai ranka ya ɓaci liti, daga kai har ɗan mama muguwar kasada cw da ganganci abun da ku ka biye masa ku ka yi. Kuma tun da ya kai i yanzu, akwai abun da yake faruwa gara kawai"" yayi maganar yana miƙewa tsaye, ya ɗauki wuƙa ya soke" "a jikinsa, ya fice." """Ɗan mama, Walid fa gaskiya ya faɗa anya ba wani abun ne ya faru ba?""" """Tashi mu koma, akwai matsala mun yi wauta da muka bar shi ya yi mana wayo, da ƙyar idan bai" "haɗu da madaki ba"" haka suma suka tashi, suka fita." "DSP Nasir da kansa ya jagoranci tafiya unguwar su madaki, bayan kiran da suka samu daga mai" "unguwa, sai dai da suka je ba su tarar da kowa ba." "Duk ga alamu nan na faɗan dabar an yi, dan 'yan unguwar sun tabattar da hakan." "Da safe Nabila har ta gama shirinta, baya ɗaga wayarta, tana zaune tana karyawa, ta shiga what's" "app tana duba messages, sai ga wani saƙo, an turo mata wani voice message, amma bayan an turo lambar tayi blocking ɗin ta." """Dan Allah ku taimaka mini, a ƙwato mini hakkina, an yi wa ɗiyata fyaɗe, na nemi a bini hakkinmu a kotu, amma wata Naja'atu Bunkure ta ce mana ita lawyer ce, ta ce zata taimake mu, amma wai sai mun janye ƙorafinmu, ko mu haƙura wanda yayi laifin yafi ƙarfinmu." "Tayi mana tayin kuɗi bamu karɓa ba, yaron ya zo har gida, ya ci mini mutunci, ya ɗauke mini ramma ya tafi da ita ta ƙarfin tsiya, ban san ina ya kai mini 'ya ba, ya dawo ya karɓi kayanta, wai nayi haƙuri ta zama tasa. Ban san meyake nufi ba, dan girman Allah a bi mini hakkina, a nemo mini 'ya ta bani da ƙarfin ja da su, ni talaka ce, amma dan Allah a dawo mini da 'ya ta mu ji da ciwo ɗaya na keta mata haddi da yayi, ku taimaka mini dan Allah"" matar ta ƙarasa maganar tana kuka. Da sauri Nabila ta tashi tsaye, ta din ga kunna voice ɗin tana saurare, wani irin gumi ya fara tsatstsafo mata, ba ta raba ɗaya biyu, wannan Muryar babar ramma ce, ita ce Muryar da aka saka" a radion su Sumayya. """To amma waye ya turo mata voice ɗin?"" Ta tambayi kanta." "Buɗe ƙofar office ɗin da aka yi ne, ya sanya ta ɗan nutsu." "Mutumin nan ne da yake zuwa wurin Barrister kabir, babban mutum ne sosai." """Na shigo ko na koma a nema mini iso?""" "Ta ƙaƙalo murmushi ta ce ""Bisimillah""" "Ya shigo ya zauna, ta ɗan risuna ta ce ""Sannu da zuwa sir""." """Yauwwa barrister Nabila, ya kike ya aiki?""" """Alhamdilillah""" "Ya ce ""Masha Allah, ai na yi wa Kabir magana, shi ya bani numbernki, kuma na kira kin ce sai na zo office"" ta waro ido ta ce ""Dama kai ne? Yi haƙuri dan Allah, ban sani ba na zata kawai masu ha" "ɗa lamba ne""" "Yayi murmushi ya ce ""Kar ki damu, hakan yana da kyau ai, ai mace da aji aka santa." "Sunana Wada M karofi, maybe kina ɗan jin sunana""" "Tayi murmushi ta ce ""Oh yes, dama kai ne M karofi?"" Ya jinjina mata kai ya ce ""Eh barrister, ina son ki zama ɗaya daga cikin lawyoyina, masu kula mini da dukiyata da kadarorina, ina biya sosai, na yaba da nutsuwarki, na ce da ganinki zaki yi amana, na yi magana da barrister Kabir ya ƙara" "bani tabbacin hakan""." "Nabila ta gyaɗa kai ta ce ""Haka ne, amma am very sorry sir, ni bana son irin wannan, a bar ni a" "hakana kawai""" "Yayi murmushi ya ce ""A bar ki a hakanki anya kuwa? To shikenan idan ba za a kula da dukiyata" "ba, to ni a kula da ni mana"" yayi maganar yana kallon ta." "Murmushi ta yi tana girgiza kai ta ce ""Haba sir, manya ba sa haka fa""" """Subhanallah, na yi miki tsufa kenan?""" """A'a ban ce ba, namiji ai baya tsufa""" """To shikenan, zamu yi waya, bari na barki ki yi aikinki, idan ta kama ma sai na zo gida""" """To Allah ya kawo ka lafiya ya tsare""" """Amin Barrister na, ga wannan ki sha ruwan roba, ba na leda ba"" yayi maganar yana ajiye mata ku" "ɗi a kan tebur""" """Ina fatan ba cin hanci ka bani ba, hakan ba zai hana in ta kama na saka alƙali ya ɗaure mini kai ba""ta yi maganar tana kallonsa." "Ya yi dariya ya ce ""Funny you, ni na isa, ayi aiki lafiya"" ya fita yana murmushi." "Yana fita ta ɗauki kuɗin ta ce ""Alhamdilillah, tsuntsu daga sama gasashe, Allah ya kawo amanar baban wasu hannuna, na samu mai zuba mini mai idan mota ta iso"" da sauri ta zube kuɗin, ta sake ɗaukar wayarta, ta sake jin voice message ɗin nan, tayi sauri tayi saving ɗin sa a gmail ɗin ta," dan kar ya ɓata. "Kamar ta turawa Sumayya, sai kuma ta fasa." *** "Ramma na kan dining tana karyawa, ta jingine waya tana kallon Abdul da shi ma karyawa yake yi." """Rahama kin taɓa gaishe ni kuwa?""" """Waye ɗi na kai da zan gaisheka?""" """Your life saver mana, yadda na ceci rayuwarki, da ki ka kusa mutuwa""" """A'a da ka sha giya dai ka kusa kashe ni""" "Ya sosa kansa ya ce ""Ke abu ba ya wucewa ne, sorry mana""" "Ta harare shi ta ce ""An ƙi ayi sorryn""" "Ya kashingiɗa ya ce ""Ɗan cire hannunki, na din ga gani sosai""" "Cikin rashin fahimta ta ce ""Ka ga me?""" Ya ɗaga girarsa yana nuna mata ƙirjinta. """Wallahi Abdul ka ɗuma asara, kai a duniya abu ɗaya Allah ya saka maka a cikin kanka ne? Haba" "mana""" """Future governor ki ke gaya wa haka? Zan fa hanaki first lady, kodayeke wadda zan aura ce zata" "zama first lady, ke kuma maid ɗin ta"" tayi shiru, tana tauna cornflakes." """Ki lallaɓa ni na dawo da wuri""" "A fusace ta ce ""Kar Allah ya sa ka dawo ɗin, in sha Allah ka tafi kenan, ko jirgin ya faɗi, kai kaɗai" "ka mutu""" "Yayi dariya ya ce ""Kin ga sai ki mutu kekaɗai a gidan nan ba, dan babu wanda ya san na ajiye ki a" "ciki. Gara ki yi sauri ki janye addu'ar ki, idan kina son ki fita""" "Ajiye kofin tayi, ta fashe da kuka, har da sheshsheƙa." "Ya ce ""Is ok, ke ce ba ayi miki abu, sai ki yi ta tsine mini, ina jin pain fa, am sorry ya isa haka, haba your excellency"" maimakon ta yi shiru, sai ma ta ƙara sautin kukan, nan da nan ya rikice, ya hau bata haƙuri, amma tayi disconnecting kiran, ta cigaba da kuka." "Ta ɗauki wayar, tun da ya tafi, take gwada kiran lambobi daban-daban, amma ba ta tafiya sai ta sa" "kawai. Ta dudduba ko ina, ko da hanyar da za ta iya guduwa, amma babu ga wata irin kewar mama da sani ƙaninta da take yi." "Su liti tamkar za su yi hauka, gaba ɗaya suka rikice, da Viper bai kwana a gida ba, duk in da suke tunanin za su ganshi ba su same shi ba. Har gidansa Walid ya je, ya haura ta katanga, ya shiga amma ba su same shi ba, gashi madakin da aka ce ya zo yana unguwar, shi ma yayi ɓatan dabo," an neme shi an rasa. "Gaba ɗaya hankalinsu ya tashi, mussaman liti, amma saboda tsananin ƙi faɗi, yaƙi yarda ya karɓi" "laifin, Walid ya din ga yi musu luguden ashariya daga shi har ɗan mama, suka yi masa shiru suka" ƙi kula shi. "A sukwane Nabila ta tashi daga wurin aiki, bayan cin karo da batun faɗan daba a tsakanin yaran" "madaki da na Viper, sai dai babu ɗaya daga cikin su da ya zo hannu, tsakanin Viper da madaki, al'ummar unguwar na cigaba da zaman ɗar-ɗar, sakamon rashin tsaro." "Ofishin Nasir ta tafi, babu sanarwa sai ganinta yayi, sai da hankalinsa ya tashi ya ce ""Arfa lafiya" "kuwa?""" Ta ciro wayarta ta nuna masa posting ɗin. "Ya ce ""To wannan ne ya saka ki ka taho har nan?""" "Ta ce ""Eh, na yi zaton baka sani bane""" "Ya girgiza kai ya ce 'No, na sani""" """To yaya ake ciki?"" Ya ɗan tsareta da idanunsa sannan ya ce ""Ni duk kin ruɗa ni, ko kece ke" "binciken nan, sai haka Arfa. Na je, sun yi faɗan daba, amma babu tabbacin yazo""." """Baka kama shi ba kenan?"" Ya jinjina mata kai alamar eh." """To ko yaran nasa ba ka kama ba?""" """Lokacin da muka je, sun yi sun watse"" wata irin ɓoyayyiyar ajiyar zuciya ta yi, sannan ta ce ""To" "shikenan, ai ban zaci ka gani ba, shiyasa na zo da kaina, bari na tafi""" "Nasir ya ce ""Yanzu mussman ki ka baro aikinki ki ka zo kawo mini rahoto, arfa mai abun mamaki," "zauna na gama abun da nake yi, na rage miki hanya""" "Ta ce ""A'a yi aikinka, ina da wurin zuwa"" ta lallaɓa shi ta fice." "Sai dai hankalinta ya rarrabu kashi-kashi, voice ɗin nan da aka turo mata, babbar shaida ce da zata" shiga kotu da ita da ƙwarin gwiwar ta. "Abdul ya kira saif a waya, ya tambaye shi yaya ake ciki ya ce masa ""Wallahi Abdul babu labarin" "matar nan, duk wani bincike da yakamata na yi na yi, amma shiru babu labari""." """Lahaula wala ƙuwwata illa billa, Saif akwai matsala me zan ce wa yarinyar nan idan ta gano" "mahaifiyarta tayi ɓatan dabo, bayan babu irin magiyar da ba ta yi mini ba, a kan na mayar da ita""" """To wannan kuma kai ta matsewa, tuntuni da ka san abun yi a kanta da duk ba a kawo nan ba""" "Abdul ya ce ""Dole na gano in da mahaifiyar rayya take, idan ba haka ban san kalar tsinuwar da za" "ta yi mini ba""" "Saif ya ce ""Ban gane tsinuwa ba, tsine maka take yi?""" """Manta kawai"" ya kashe wayar, ya din ga kiran wayar ramma, saboda tun jiya da safe da tayi kukan nan, ba ta sake ɗaga wayarsa ba, hankalinsa yayi mummunan tashi, ya fara tunanin ko wani abun ne ya sameta, kar ya je ta yi wa kanta illa, dan da wuƙaƙe a kitchen, kuma tana yawan iƙ" irarin cewa zata kashe kanta. "Kusan awanni ashirin da huɗu suka shuɗe, Nabila ba ta samu Viper a waya ba, can ɓangaren su" "Walid ma, hankalinsu ya kasa kwanciya, saboda yawon neman Viper." "Har ta je wurin aiki, ta kasa sukuni, kawai ta yanke shawarar zuwa gidan da yake." "Tana sauka daga abun hawa, wata mota ƙirar helux baƙa, ta fito daga hanyar, duk da wurin mota ba ta iya bi, tayi ta tunanin yaya aka yi mota ta bi ta wurin, ta ƙarasa gidan, tun a tsakar gida take sallama, amma shiru babu wanda ya amsa, ta nufi ɗakinsa, ta ganshi a kwance a kan katifa, gefensa ga wuƙarsa da wayarsa da ledar magunguna, yana sanye da riga baƙa armless, da dogon" "wando shi ma baƙi, ga damtsensa an yi masa ɗinkin rauni, da sauran wurare a jikinsa." "Cikin hanzari ta ƙarasa tana faɗin ""Subhanallah""" """Viper meyasameka?"" Sai dai kamar gawa, ta ƙare masa kallo, an yi masa askin uwar sumar da take kansa, an yi masa gyaran fuska tare da rage masa gashin da ya taru a fuskar sa. Yayi wani irin ƙayataccen kyau, hatta kayan jikinsa ba ƙaramin kyau suka yi masa ba. Wayarta ta ciro ta din ga" ɗaukarsa a hoto. "Ta daddaki gefen katifarsa ta ce ""Viper, bacci kake yi ne? Garin yaya ka ji raunuka haka?"" Sai dai" shiru ko motsi baya yi. """Me ka sha har haka ne? Ko sai na ce Master zaka tashi?"" Babu tsammani ta ga yana motsawa a" hankali. """Madarata"" Nabila ta ce ""Too yau kuma?""" "Yayi murmushi idanunsa a lumshe ya ce ""Ai a duniya babu wanda ya raina ni, daga ke sai Walid, kin daina jin tsorona gaba ɗaya zan kama ki ne"" murmushi yake yi sosai, wanda hakan ya" bayyanar da tsantsar shauƙi da soyayyar da yake yi mata. "Surutansa ya cigaba da yi ya ce ""Yakamata na gaya miki wani abu, da yakamata ace kin sani," "amma sai kin haihu tukuna, saura kuma ki isheni da tambaya na san halinki"" ya buɗe idonsa a" "hankali, ya kalli Nabila da ta zuba masa ido, ya miƙa hannunsa ya riƙo nata ya ce ""Zan gaya miki" "me na je yi Lagos ne"" sai kuma ya saki hannunta yana girgiza kai." """Laaa, ke ya aka yi ki ka dawo da shi, Walid ƙaraso ka ga"" liti yayi maganar yana shigowa ɗakin." "Gaba ɗaya su ukun suka shigo, suka kewaye ta." """Da gidan uban wa ki ka kai shi?""" "Ta kalli Liti ta ce ""Kamar yaya?""" """Gidan uban wa ki ka kai shi?""" "A ƙule ta ce ""Gidan ubana, tayaya zan iya ɗaga wannan shirgegen ƙaton""" """Ƙarya ki ke yi haɗa baki aka yi da ke aka ɗauke shi, wannan kayan na jikinsa ma ba nasa bane ba" "macuciya""" "Walid ya ce ""Ya isa dan Allah, Barrister nemansa muke ko sama ko ƙasa bamu ganshi ba, a ina ki" "ka gano shi?""" "Ta ce ""Wallahi yanzu na zo, bana samunsa a waya, yanzu na zo kawai na tarar da shi a kwance, wallahi ban san ma neman sa ku ke yi ba, duba wayarsa zaka missed calls ɗina da yawa. Amma dai naga wata baƙar helux ta fita daga hanyar nan, ban san ta ina suka biyo ba, na riƙe lambar" "motar a kaina""" "Walid ya ce ""Karki damu, na yadda da ke""" """Wallahi mai laya, ka cigaba da sakankancewa da yarinyar nan, sai tayi dalilin an kashe ku" "tukuna""" "Liti ya ƙarasa gaban Viper ya durƙusa a kansa, cikin zafin nama, viper ya danƙi wuƙarsa ya saita" ta a cikin liti yana wani irin huci. "Liti ya buɗe baki ya ce ""Ni zaka sa wa russia Viper?""" "A hankali ya ƙara buɗe idonsa, ya hankaɗe liti gefe ya ce ""Na zata madaki ne"" sai kuma ya kalli" "jikinsa, ya kalli kayansa, ya kalli damtsensa ya ga ɗinki, ya kalli Nabila ya kalli ɗakin ya ce ""Ke a ina muka rabu da ke?""" "Ta ce ""A titi, bayan ka dire daga adaidaita sahu""." """Me ki ka yi mini?""" "Nabila ta ce ""Au kaima ni ka ke zargin na sace ka kenan?""" "Walid ne ya yi masa bayanin abun da ya faru, ya lalubi wayarsa da sauri yana duddubawa." """Don't endanger your life again, madaki is still not your mate, da sauran lokaci"" ya ajiye wayar ya" "sunkuyar da kansa, da yayi masa nauyi yana tuno abun da ya faru a ranar." "Nabila ta kalli Walid ta ce ""Yay walid, yayana yana zuwa wurin sayar da shayinku, kuma akwai jami'ansa a farin kaya suna zuwa, kayi taka tsantsan, yanzu aikinsa a kanka yake. Kuma ka kula da" "wanda suke zuwa wurin sosai, kar wani information yayi leaking a wurin""" "Liti ya ce ""Munafuka, wadda take kwarewa ɗan uwanta baya ne, ku ke tunanin kuma ba zata bar" "ku ba wataran. Shegen yayan naki azzalumi, ƙugu kamar gatari""" "Nabila ta ce ""Allah ya isan sa, kuma ni ba munafuka ba ce, kuma wallahi idan baka kiyayeni ba," "zan kuma sakawa a kama mini kai, sai igiya tayi saura"" tayi maganar tana hararsa ta ɗauki jakarta." "Ta durƙusa a gefen Viper ta kai bakinta, kunnensa ta ce ""Viper, zan tafi zan je wani wuri, zamu yi waya, ka samu ka ci abinci, kar ka takurawa kanka da tunani da yawa, kar ka sha ƙwayoyin da za su yi maka illa. Saboda muna son ganinka cikin ƙoshin lafiya da ni da 'yar madara, na ji ka ce zaka gaya mata wani abu, to nima sai ka gaya mini, tun da nice amarya. Kayan nan sun yi maka kyau sosai da sosai, ka ci abinci kayi salla ka huta, ka bar wayarka a buɗe zamu yi magana dan Allah, ka yi mini addu'a zan cigaba da shari'a da su bunkure, take care dear"" ya ɗaga kai ya" "kalleta, taƙi kallonsa tayi waje." "Liti ya ce ""Makira, duk makircinki sai ya koma kanki"". Ta galla masa harara ta tafi." *** "Abdul yana ta kiran ramma, har ya fitar da ran zata ɗaga, yaji ta ɗaga muryarta ƙasa-ƙasa." """Bacci ki ke yi ne?""" "Ta ce ""Eh""" """Eyya sorry na tashe ki, nake ta kiranki a waya amma ba kya ɗagawa, lafiya dai ko?""" """Haushinka nake ji ne, zan iya ɗuɗɗura maka ashar, shiyasa bana ɗagawa""" "Yayi dariya ya ce ""Yanzu kin huce?""" """Eh""" """To masha Allah, kin tashi lafiya?""" """Eh""" """Duk muryarki wani iri, anya lafiya kuwa?""" "Ramma ta ce ""Ba wani lafiya, ni na gaji da zaman gidan, nikaɗai kamar mayya sai tv da haushin" "karnuka, ni ba prisoner ba""." "Abdul ya ce ""To yanzu ya ki ke so ayi?""" """Ni koma yane ayi""" "Ya ce ""To shikenan, zan dawo gobe in Allah ya kaimu""" """Ba sati ka ce zaka yi ba?""" "Ya ce ""A'a hankalina yaƙi kwanciya ne, zan dawo gobe in Allah ya kaimu """ "Ramma ta ce ""To Allah ya tsare""" """Kin fasa in faɗi a jirgin, kar in dawo?""" """A'a jirgin ya faɗi kai kaɗai ka mutu""" """Muguwa ba Amin ba""" """Ban kai ka mugunta ba ai""" "Yayi dariya ya ce ""Sai anjima""." *** "Washegari ya kama ranar da Nabila zasu cigaba da shari'ar mai gadi, ta shiga office ɗin ta, ta tarar da wani file a ajiye a kan teburinta, har ta fara masifar na meye wannan aka ajiye mata a kan tebur. Ta nemi wuri ta zauna, ta ɗauki wayarta, ta shiga social media ta rubuta, kuraye masu fatar akuya, an kusa walƙiyya mu ga kowa"" ta yi tagging ɗin Naja bunkure.Washegari ya kama ranar da Nabila zasu cigaba da shari'ar mai gadi, ta shiga office ɗin ta, ta tarar da wani file a ajiye a kan" "teburinta, har ta fara masifar na meye wannan aka ajiye mata a kan tebur." "Ta nemi wuri ta zauna, ta ɗauki wayarta, ta shiga social media ta rubuta, kuraye masu fatar akuya," "an kusa walƙiyya mu ga kowa"" ta yi tagging ɗin Naja bunkure." "M karofi ya kirata, ya din ga yi mata surutu, da neman ta bashi damar zuwa gidansu, ta ce masa" "yanzu aiki take yi, bayan sun yi sallama, ta ja file ɗin tana dubawa." "Sunan Naja'atu Bunkure ne a sama, sannan aka fara bayanin tarihin rayuwarta tiryan-tiryan, har zuwa fara aikinta, yadda ta taso cikin rayuwar ƙunci da wahala, yadda ta zama lawyer, bayan fyaɗ e da aka yi mata da ƙanan shekaru, gaɓar da Nabila ke son ganin meyafaru, a nan aka tsaya. Ta daki tebur, ta din ga jujjuya file ɗin tana tunanin waye wannan ya kawo mata file ɗin nan, da kyar" idan ba shi da alaƙa da wanda ya tura mata voice message ɗin nan. *** "DSP Nasir yana zaune yana rarraba ido a ƙaton falon, da ko ina sanyin A.C ne ke ratsa shi." "Babu tsammani mutumin ya fito, ya samu wuri ya zauna, cikin girmamawa Nasir ya ce ""Barka da" "wannan lokaci sir""" """Yauwwa barka, DSP Nasir Yusuf maitama, ɗan uwan barrister Nabila Yusuf maitama"" ya ɗago" ya kalle shi. """Na san zaka yi mamakin kiran da nayi maka ko?""" "Nasir ""Ƙwarai sir, na san ni dai babu wani abu da ya taɓa haɗa ni da kai, amma ka saka a nemo ni," "kuma ga sunana ka kama, da na ƙanwata""" "Indabo ya gyara zamansa ya kalli Nasir ya ce ""Nabila!""" "Cikin rashin fahimta ya ce ""Me tayi?""" Ayshercool 0808101243 ₦500 ne via 0009450228 Aisha Adam jaiz bank sai shaidar biya ta 08081012143 Wanda za su jira document 1K ne. 90009343 'Yan Nijar ku turo katin airtel na 300fcfa Arewabooks ayshercool7724 "Cikin rashin fahimta, Nasir ya ce ""Amma Yallaɓai me tayi ne?""" "Indabo yayi murmushi ya ce ""Bari mu ɗan ajiye batun ta a gefe. Aminu Viper, wanda aka fi sani" "da mai zamani a baya, kai ne incharge of bincike da ƙoƙarin kama shi haka ne?""" "Ya jinjina kai ya ce ""Eh sir""" """Na san kana fuskantar matsin lamba, daga wurin na sama da kai, a kan lallai ka kama Viper. Duk da abun mamaki ne, a baya yana tsare a prison lokaci guda yayi ɓatan dabo sama da shekara guda" "ana nemansa""." "Nasir ya ce ""Haka ne sir""" "Indabo ya sassauta muryarsa ya ce ""Akwai jiƙaƙƙiya tsakanina da Viper, wanda barazana ne ga siyasata da mutuncina. Saboda haka na yanke shawarar yin gaba da gaba da kai mu tattauna wataƙ ila kafi bawa aikin muhimmanci, tun da na samanka kawai nake gani, kai bamu taɓa haɗuwa ba," "kuma Alhamdilillah sai na yi sara a kan gaɓa""" "ya ajiye masa wata jaka ya ce ""Ga wannan ka sha mai, sannan akwai fuloti mai rai da lafiya a unguwar tudun yola da takardunsa a ciki, wannan zai zama wani ɗan hasafi, ko in ce ihsani domin ƙara maka ƙwarin gwiwa, idan aiki ya kammala, ina da kyakykyawan Albishir gareka, muddin Viper ya zo hannu, ko ma ya bar duniyar baki ɗaya ina da ƙarin Albishir gareka. Ɗana na shirin zama deputy governor a garin nan, zaɓe mai zuwa. Kuma ka san kujerar da nake kai, ka san ma'anarta. Zan iya yi maka alƙawarin zama CP na jihar nan, kai koma na yi maka babban muƙami a ƙasa. Akwai kyautar mota irin ta sanatoci, da gwamanti kan yi gwanjon su, gida ko fili sai wanda ka zaɓa. Kar ka yi dogon tunani, ba wai cin amanar ƙasa zaka yi ba, taimakon kai da kai ne, kai ma ka taimaki gobenka, idan ba haka ba, a haka zaka ƙare kana yi wa ƙasar da ba ta san muhimmancin ka ba bauta, ka gama babu wani allowance ɗin kirki ka ƙare rayuwarka a" "tagayyare"" Nasir yayi shiru yana ajiyar zuciya." """Sai magana ta biyu, Nabila ƙanwarka, akwai wasu abubuwa muhummai a tattare da ita. Abu na farko na sanya rayuwarta a matsayin tarkon da zan kama Viper ba tare da ta sani ba, duk da hanyar tana tangarɗa, amma tabbas ina ƙoƙarin kama Viper ta hanyar ta, ko da kuwa hakan yana nufin" "salwantar da rayuwarta ne""" "Cikin mamaki da rashin fahimta ya ce ""Kamar yaya?""" """Kamar yadda nake gaya maka, ai ba ta hannunku kawai nake nemansa ba, dan haƙa ƙwazonka, da nemo Viper shi ne zai kuɓutar da rayuwarta, haka zalika ka taka mata burki a kan shari'ar da take yi, na son yin gaba da gaba da Naja'atu Bunkure, saboda yin hakan tamkar yin fito na fito da ni ne, idan ba haka ba, wallahi rayuwarta zata salwanta a banza, ba zan taɓa bari sunana ya ɓaci a" "banza ko asirina ya tonu ba""" "Nasir ya ce ""Amma sir, dole sai an shigar da Nabila cikin wannan lamarin?""" """Dole ne, muddin kana son rayuwarta, make her withdraw the case, ta fita daga shari'ar nan""" "Nasir yayi sassanyar ajiyar zuciya ya ce ""Zan duba naga menene abun yi""" "Indabo ya ce ""Yauwwa, a ƙoƙarta, zaku tafi da P.A ɗina, za ayi wa motarka full tank, ka sanya" "ido sosai a kan yarinyar nan""" "Nasir ya tashi ya ce ""Thank you sir""" "Indabo yayi murmushi ya ce ""In dai muna tare, ka din ga samun damrmaki kenan, ai ba a zama" "haka DSP"" ya jinjina kai ya juya ya fita, kansa yana wani irin nauyi." *** "Cikin hanzari Nabila ta fito daga office ɗin ta, ta kalli mai goge-goge ta ce ""Baba, akwai wanda" "ya shiga office ɗina kafin na zo ne?""" "Ya ce ""A'a, shara kawai na yi na goge miki, na fito""" """Kai ka ajiye mini wani file a kan tebur?""" "Ya girgiza kai ya ce ""A'a, ban tarar da komai ba da na goge teburin"" ta jinjina masa kai ta koma," tana cigaba da mamakin waye haka?. "Ta window ta leƙa taga zuwan barrister Habib, tayi sauri ta fita, a ƙofar office ɗin sa ya tarar da" "ita ya ce ""Ya dai? Tara ko bashi, ki ka tsaya mini a ƙofar office"" tayi murmushi ta ce ""Babu ɗaya, nemanka nake yi ruwa a jallo ne""" "Ya saka mukulli ya buɗe, suka shiga, ya ce ""Allah ya sa ba wata shirirtar ba ce? Nima ina nemanki" "dama""" """Haba barrister, sai ka ce wata 'yar yarinya, is a very serious issue""" "Ya dubeta ya ce ""To yanzu dai, ki yi haƙuri, na fara karyawa tukuna""" "Noƙe masa kafaɗa tayi, tare da girgiza kai." "Ya ce ""Ke, kwanan nan fa nayi mata ta biyu, da na sani ma da ke nayi ta biyun nan, wannan" "shagwaɓar taki ai sai ki hanani karyawa""" """Taɓ matarka ta daka ni kenan, ni dai ka zauna Please muyi magana""" "Ya zauna ya ce ""Na zauna Nabila menene?""" "Wayarta ta ciro ta kunna masa voice message ɗin nan, cikin mamaki ya kalleta ya ce ""Waye ya" "turo miki?""" "Ta girgiza kai ta ce ""Ban sani ba, shiyasa na zo na nuna maka""" """To ai tun jiya naso na kira ki, na je garinsu yarinyar da kaina, har gidan su na je, amma ban tarar da kowa ba, maƙwabta sun tabattar mini da ta shafe kwanaki ba su san in da take ba, kuma ba ta yi wa kowa sallama ba"" Nabila tayi turus ta ce ""Ban gane ba, uwar ta ɓata kenan? Ko kuma guduwa" "tayi saboda gudun abun kunya?""" """Shi ne dai ban sani ba""" "Nabila ta ce ""Na kasa gane kan lamarin nan, to waye ya turo mini voice ɗin nan, an ce shi wanda" "yayi mata fyaɗen, ya zo ya ɗauke ta, to ya aka yi da uwar, waye ya naɗi wannan recording ɗin?""." "Barrister Habib ya ce ""Gaskiya dai abun tunani ne, lamarin akwai ɗaure kai, amma kar ki damu," "koma waye sauƙaƙa miki aiki yayi""" """Amma abun da mamaki fa, kuma wanda yayi hakan ba shi da wata manufa ta yin hakan, ya" "bayyana kansa mana idan yana da gaskiya koma waye""" "Barrister Habib ya jinjina kai ya ce ""Yauwwa, ya ku ka yi da Alhaji wada M karofi?""" "Ta yamutsa baki ta ce ""Soyaya muke yi """ """Soyayya kuma? Cewa yayi yana son ki shiga cikin lawyoyinsa, masu kula da dukiyarsa fa""" "Ta ce ""A'a gaskiya, ce masa nayi a'a, sai ya ce to shi na din ga kula da shi, shikenan""" "Habib ya ce ""Innalillahi, wallahi baki da lissafi Nabila, kin san waye mutumin nan kuwa? Kin san" "kuɗin da muke samu a wurinsa kuwa? Babban mutum ne fa a ƙasar nan""" "Ta tashi ta ce ""Oho, a hakan ma ai yana bani kuɗi, bana son dai ya zo gidanmu, naga he's very" "serious, kar ya zo suyi magana da Abba ace sai na aure shi, dan yasin bana son tsoho""." "Ya girgiza kai ya ce ""Ƙuruci dangin hauka, Allah ya shiryeki""" """Amin, ayi aiki lafiya"" ta fice daga office ɗin." *** "Ramma na zaune tana ta gyangyaɗi, ta ji ana murɗa ƙofar falon, Abdul ya shigo da akwatinsa." "Suna haɗa ido ya sakar mata murmushi ya ce ""I am back"" murmushin ita ma tayi masa." "Ya ƙarasa ya zauna tare da rungumeta, yayi kissing ɗin goshinta ya ce ""Kina zaune baki yi bacci" "ba kina jirana?""" """Ƙarfe tara fa ka ce, amma sai sha biyu, Club ka je ko?""" """Wallahi ban je club ba, abubuwan da na tarar da yawa a can, Shiyasa na kuma samu matsala ne" "da flight ɗin shiyasa, gudowa fa nayi saboda ke""" "Tayi ajiyar zuciya ta ce ""To sannu""" """Yauwwa sweetheart """ "Ta ce ""Taɓ babu daɗin ji""" "Ya ce ""Wallahi da daɗi, rantse baki ji daɗi ba da na ce sweetheart""" """Wallahi ban ji ba""" "Abdul ya ce ""Ƙarya ki ke yi, santaleln mutum kamar ni, na kira ki da sweetheart, ki ce ba ki ji" "komai ba""" """To waye kai ɗin? Sai ka ce wani mutum na musamman""" "Ya kaɗa ƙafa ya ce ""Ke kin san matan da suke crushing ɗina kuwa?""" """To ina ruwana?""" """Kina da ruwa mana, na gaji fa sosai Saboda na san maybe kina nan kina jirana, ko abinci ban tsaya na saya ba, yanzu zan yi wanka, sai ki rakani mu duba in da suke 24hrs, mu ci abinci""" "Ramma ta ce ""A'a, na yi girki ai tun magariba ma na gama, tun da nan gidan ba mak aiki, kayi" "wankan ka ci""" "Ya ce ""Iyee zan ci jagwalgwalo yau, bari nayi wankan"" ya ja akwatinsa, ya shiga bedroom ɗin da" take. A falo ya tarar ta ajiye fulasai. """Rahama kayan miyan cikin fridge ɗin ba su lalace ba kenan?""" "Ta ce ""Eh, har fruit ɗin, na iya reserving ɗin su ai""" "Yana cin abincin yana murmushi, ya ce ""Yanzu har sakwara ki ka yi, gaskiya kina ji da ni, ga" "shayin ma yayi daɗi sosai""" """Ba wani ji da kai da nake yi, tunani nake ina ma da guba a ciki, ka ci ka mutu""" "Yayi dariya ya ce ""Koma dai menene, idan ma da gubar na ci, ba mutuwa zan yanzu ba, sai kin haifa mana babies, kuma fa zama zaki yi kiyi kuka idan na mutu. Anyway abinci yayi daɗi sosai," "yaya aka yi ki ka iya girki haka?""" "Ramma ta ce ""Aikina kenan a gidan Anty maijidda, ta ce ba ta taɓa yar aiki kamata ba, sai gashi iftila'i ya faru da ni a gidanta, amma ta kware mini baya, saboda kai ɗan ɗan uwnta ne, ni kuma bata da alaƙa da ni, ko ganin idonta ban yi ba, wai sai ma umarnin idan mun zo kar a bari mu shiga da ta bayar, aka canza masu gadi.shikenan bakomai, shi talaka ai Allah yana son abun sa""" tayi maganar tana share hawayenta. "Sai jikin Abdul yayi sanyi, ya ce ""Rahama duk laifina ne, nayi kuskure, kuma duk sharrin giya ne da ruɗin shaiɗan, amma na rage shan giya ma, kuma wallahi rahama na daina bin mata, da ɗin ma sharrin giya ne da kuma abokai"" tashi ta yi ta bar masa wurin, saboda tuno hanyar da ya bi ya ci" mata zarafi da yayi. "Shi ma gaba ɗaya sai jikinsa yayi sanyi, duk da irin zaluncin da yayi mata, tana da matuƙar" "tausayi da imani, duk da yana shan zagi da tsinuwa, amma wasu lokutan sauƙin hali ne da ita." "A zaune ya tarar da ita a kan gado, tana ta uban kuka, bai ce mata uffan ba, ya rungumeta yana shafa bayanta, a hankali yake furta ""Am very sorry for what i did, ki yi haƙuri"" ya din ga rarrashinta, har suka kwanta, yana ta magana, amma tunani ne daban-daban a cikin kanta, babu" "tsammani ya ji ta ce ""Abdul yasar""" """Your excellency""" """Wai dan Allah da gaske ana yi wa maza fyaɗe?""" "Ya ce ""A'uzibillah, wannan wace irin magana ce?""" """Shekarun baya, kan yayanmu ya mutu, kamar haka na so naji an ce, wani ne ya ce zai samo masa aiki a Abuja, shi ne yayi masa fyaɗe yayi rashin lafiya ya mutu, kullum mama ta tuno da shi, sai ta kusa kwana tana kuka, sai ta daina cin abinci, kusan shekara shida fa, amma ta kasa mantawa. Kuma dama ba a hannunta yake ba, shi yana wurin babansa a birni. To ni haryanzu ban taɓa jin an ce an yi wa namiji fyaɗe ba sai mace, shi ne nake tunanin, ko wani abun suke nufi daban ban gane" "ba""." "Dummm haka Abdul ya ji kansa yayi, ita kanta kalmar ga mace ma babu daɗin ji, balle ga namiji, sai yanzu ya ƙara tabattar da in dai zancen ramma gaskiya ne, ya zalunce su. Hakan ya saka ya ji dolensa ya ƙara ƙaimi, ya nemo mahaifiyarta, ya nemi afuwarta, amma bai ji a ransa zai iya" mayar mata da ramma ba. """Abdul ka yi shiru, ka gaya mini mana""" """Ke kin ga alamar in da za a yi wa namiji fyaɗe ne? To ban sani ba ko ana yi, tun da nima yaro ne" "haryanzu, ban sani ba ko ana yi""" """Waye yaron?""" """Ni mana""" """Ka fiye abun haushi, da takaici, a'a mahaifa ne kai"" murmushi ya yi yana sumbatar ta." *** """Mai zamani"" Walid ya kira sunan Viper." Ya ɗaga ido yana kallon Walid. """Da gaske ka haɗu da madaki? Ko kuma yaransa ne suka yi maka wannan raunin na damtsenka? Na ji an ce an neme shi an rasa, kuma ban ji labarin yan sanda sun kama shi ba. Abun duk ya ɗ aure mini kai, daga majiyarmu ta dabarsa, hatta su yaransa ba su san a inda yake ba. Kuma na san abu ne mawuyaci ku haɗu ace iya illar da yayi maka kenan, bai kashe ka ba, tun da ya san nemansa ka ke yi, kuma kai ma da ka kashe shi da an ji labari, kuma bana tunanin zaka iya kashe" "shi a yanzu""." "Viper ya gyaɗa kai, ya ɗaga russia da take hannunsa yake ta goge ta, yana shafa mata mai." "Ya miƙawa Walid ita, ya karɓa. Ya ce ""Meyafaru?""" "Al'amin ya ce ""Duba da me aka ƙerata?""" "Mamaki ne ya kama Walid, tun da suke bai taɓa yi masa wannan tambayar ba, ya karɓa ya" "dudduba ta, ya ce ""Ƙarfe ne""" "Viper ya ce ""Duba dai""" "Ya sake dubawa ya ce ""Ƙarfe ce Viper""" "Viper ya haɗa tafukan hannayensa biyu ya ɗaga ya ce ""Allah ya jiƙan maza""" "Walid ma ya haɗa ya ɗaga ya ce ""Amin, dodo babban sarki""" "Viper ya ce ""Shi ya saka aka ƙera mini russia. An yi amfani da ƙashin ƙwaurin zaki ne, a samanta, ƙasanta kuma azurfa ce haɗe da ƙarfe, sai kuma aka yi amfani da magunguna wurin ƙ arasa haɗa aikinta. Shiyasa ba ko yaushe nake amfani da ita ba. Ya saka an ƙera mini ita, ita ce" makarin taurin da madaki yake amfani da shi. "Sai dai a lokacin ban ji cewar ya dace na kawar da madaki farat ɗaya, na kashe shi ba, na cigaba" da ajiyeta. "A wannan karon naga yakamata na nu na wa madaki, talala kawai nayi masa. Saboda shi aka ƙera russia, na gwada aikinta ne a kansa, kuma tayi tasiri, dan kuwa ta huda shi, ya kuma zubar da jini. Ƙafar da na soka masa, ta tashi daga aiki har abada, ba zan kashe shi farat ɗaya ba, sai na gama sabauta rayuwarsa, Indabo ya watsar da shi a dalilin Rashin amfanin da ba zai yi masa ba. A lokacin da sauran waɗanda yake cuta, za su farga asirinsa ha karye ya daina tasiri, su ma su fara far masa da kai masa hari. A haka zan cigaba da yi wa gaɓoɓinsa yankan ƙauna, har sai na fara jin" "sanyi a zuciyata""." "Walid ya ce ""Kan uba, yanzu duk tsawon lokacin nan, kana da makarin tsafin madaki, ka zauna" "muke bulayi? Har yayi maka illa ta biyu?""" "Ya sunkuyar da kai sannan ya ɗago ya ce ""Tun a baya, nayi niyyar ɗaukar fansa, amma daga cikin alfarmar da matata ta nema a wurina, ya haɗa da na bar madaki da Allah, kar na kashe shi, ba ta son nayi kisan kai, sunana ya ƙara ɓaci, hatta gabarmu sai da ta roƙi na kawo ƙarshenta, idan ban manta ba, har Abbu ta sako a al'amrin." "Kukanta ne ya tsaye mini a rai, tare da magiyarta, har na ji a raina na yadda, na haƙura zan kawo" "ƙarshen gabata da shi, domin in faranta mata amma. Sai kuma yayi shiru, ya fara huci, jijiyoyin sa suka fara kumbura, gumi yana tsatstsafo masa a goshinsa." "Walid cikin damuwa, ya daddaki kafaɗar Viper ya ce ""Am sorry mai zamani, ka yi haƙuri, kayi ha" "ƙuri""" *** "Nabila na ta rubuce-rubuce a cikin system, ta jiyo muryar Abba yana ""Ina Arfan Abban ne, ko ba ta dawo ba ne?""" "Daga ɗakin ta amsa ta ce ""Ina nan Abba, gani nan"" ta fito tana murmushi." "Ya ɗago mata key, ya ce ""To, ga 206 ɗin ki can an kawo, duk da na san ba kya son kalar motar""" "Wani irin tsalle tayi, ta rungume Abba, ta na ""Subhanallah, wayyo daɗi ina zan saka kaina, Abba dama zaka sai mini motar? Na zata da wasa fa ka ke yi mini"" murmushi ya yi, ya kama hannun ta, suka fita harabar gidan, wanda suka kawo motar ma ba su tafi ba, Vibe ce blue black sai sheƙi take" yi. "Kawai ta fashe da kuka, Abba ya ce ""Ya kuka kuma?""" """Abba na gode, na ma rasa me zan ce ne"" 'yan gidan duk suka fito suna kallon motar, masu tayata" "murna nayi, masu tsaki suna yi." "Ana haka Nasir ya shigo, ta nufe shi da sauri, tana nuna masa key ɗin motarta." """Congratulations, amma tawa zaki ɗauka ni bani sabuwar""" "Tayi dariya ta ce ""Ai ba aro ba ɗani, balle kyauta"" dama a karambani, Nabila ta iya mota, a kan ta Nasir, ya karɓi mukullin, walida ta ce bari ta zo a ɗana su, amma Nasir ya ce mata a'a, su biyu" kawai za su fita. "Suna tafe yana driving, bakinta yaƙi rufuwa." """Wow na zama big girl, idan zan je trial, sai dai a ganni a motata, a din ga cewa hajiya, shikenan na huta da hawa ɗan sahu, da masu warin hammata da zarnin fitsari"" ya ƙare mata kallo, sai nisha" ɗi take yi tana murmushi. """Arfa""" """Yes sir""" """Ina son mu yi magana ne""" "Ta kalleshi ta ce ""To yaya""" """Shari'ar da ki ke yi, da kuma adawa da Naja'atu Bunkure""" """Ok ina jinka""" """You have to withdraw the trial""" """What?""" "Nasir ya ce ""For your own good and safety, mace ce mai hatsarin gaske, kar wani abu ya same ki," "Abba ba zai iya jurewa ba, nima kuma haka ki rabu da matar nan""" "Nabila ta ce ""Yaya, ni fa dama masu ƙaunata ba su da yawa a duniya, dan haka ka ƙyaleni, why" "would that innocent old man suffer just to cover someone's evil did, ita kuma ta din ga zaluntar mutane, kuma ayi mata shiri, i can't nima Allah ya tsaya mini""." """Shut up, ina magana kina mayar mini, babu wanda ya shiga cikin maganar sai ke, tun da ki ga kowa baya tsoma baki a lamarinta, dan me ke zaki yi? Ki janye shri'ar nan tun ban saɓa miki ba, tun da baki san ciwon kanki ba. Ya zama dole ki janye, idan ba ƙafar wando ɗaya ki ke so mu saka da ke ba"" ya haƙiƙance yana yi mata masifa. Tayi masa shiru, gaba ɗaya ta nemi farincikin" "da take ciki ta rasa, saboda maganar da Nasir yayi, ya gama zagayawa suka koma gida." "Matan Abba kuwa mussaman mama, ta din ga mita a kan saya wa Nabila mota, itakaɗai a gidan, amma ya ce gidansa ne, abun da ya tsara shi za ayi, ba wanda aka tsara masa ba. Lokaci ne yayi da" zasu girbi abun da suka shuka masa a kanta. "Gaba ɗaya sai ta rasa karsashi, ta na ta zumuɗin kiran sumayya, amma yanzu ta kasa, saboda" haushi da mamakin abun da Nasir yayi mata yanzu. "Kawai sai ta kira Viper, ya ɗaga ya saka a kunnensa." """Ina wuni, ya jikinka kuwa?""" """Alhamdilillah"" sai da ta tashi tsaye jin ya amsa ta ce ""Kai, yau ka amsa mini, masha Allah, Allah ya ƙara maka lafiya da nisan kwana, ya kare mana kai. Dama na kira ne in ji ya jikinka, kuma"" sai" "tayi shiru, shima shirun yayi bai yi magana ba." """To ka tambayeni menene mana? Shikenan ma na san ba kulani zaka yi ba, sai anjima"" ta kashe" "wayar ta ajiye, ta kwanta tayi shiru, zuciyarta a cunkushe babu daɗi, ga abun farinciki, amma Nasir ya ɓata mata. Kawai ta fashe da kuka, ta yi ta gama, ta kwanta ta hau bacci." *** "Yau a kotu, hujjojin da Nabila ta bayar masu kyau ne sosai da sosai, sai dai lauyan gwamantin da yake kare ɓangaren ramma, sun fita gogewa suka din ga dankwafar da ita, kuma alƙalin ya din ga ɗaukar side, tare da soke wasu daga cikin hujjojin Nabila. Ya sake ɗaga shari'ar zuwa wata guda." "Ta kalli dattijon, gaba ɗaya sai ta ji ta fara karaya." "Jiki a sanyaye ta fito, tana fitowa murtala yana tsaye a harabar kotun yana jiranta." "Kamar ta fashe da kuka ta ce ""Yaya murtala kaga yadda shari'ar nan ke tafiya ko?""" "Murtala ya ce ""Kar ki damu, ai idan sun san wata, ba su san wata ba, kamar yadda muka tsara zan" "tattauna da ke a kan shari'ar yanzu, ki faɗi hints mai muhimmanci, zamu saka a live program yau" "da ni da Sumayya, sai dai duk mai faruwa ta faru." "Cikin damuwa ta ce ""Kar fa ku samu matsala a wurin aiki""" """Manta da su, duk da su ake haɗa baki ai, dattijon ne ma abun tausayi""" "Nabila ta ce ""Wallahi ko kallonsa nayi, sai tausayinsa ya kama ni, bana son na kasa sakawa a" "wanke shi""" "Murtala ya ciro recorder ɗin sa, ya tattauna da Nabila, na mintuna biyar, a kan shari'ar sannan ya" tafi. *** "Indabo tamkar zai kwaɗawa Abdul mari, saboda takaici ""Abdul wai me kake nufi da ni ne? Sai ka yi mini asarar wahalata, uwar me ka dawo kanon ka yi? Uban wa ka ajiye da ka taho, mutane sun zauna suna jiranka, kawai a nemeka a rasa, wane irin rashin mutunci ne, da iskanci har haka? Wato tona mini asiri zaka yi, ka nuna wa duniya ban isa da kai ba ko?""" """Daddy, uzurin gaggawa ne ya taso mini, wata tiyat....." """Ubanka da kai da tiyatar, ko tunanin ɗan uwanka da yake mexixo a tsare baka yi, dole sai ka" "nuna mini ban isa da kai ba, ka cigaba kar ka fasa ka kuma kyauta""" "Wayar Abdul ta fara ringing, ya cirota ya ga lambar ramma, ya ɗaga a saka a kunnensa, yayi ƙasa" "da murya ya ce ""Beb""" """Abdul kana ina?""" """Ina gida meyafaru?""" """Tun jiya fa zazzaɓi nake yi, cikina sai ciwo yake ina amai""" "A rikice ya ce ""Subhanallah, kina ji na, ki duba side bed drower, akwai pcm, ki ɗauka ki sha, daga" "shi kar ki sha komai, gani nan zuwa kin ji, ki samu ki kwanta"" sai da ya kashe wayar, ya tashi tsaye, ya ankare da katoɓarar da yayi, gaba ɗaya ya manta a gaban wa yake." """Abdul karuwa ka ajiye gidanka, har take rashin lafiya, saboda iskanci a gabana kuma kake waya" "da ita?""" "Ya girgiza kai ya ce ""A'a ba karuwa ba ce Daddy..ammm...." """Abdul, yanzu ba zaka daina sakarcin nan ba, sai abokan adawa sun farga, sun fitowa da duniya" "waye kai? Uban wa zai yadda ya zaɓeka, idan mutane suka san you are womanizer? Kuma har ka ajiye mace a gida, bama ka yi shahshashancin ta tafi ba. Na haramta maka kwana a waje, duk in da" "kake ka dawo gida ka kwana, kuma a cikin watan nan za ayi bikinka, ko ka yarda ko baka yadda" "ba""." "Abdul ya kalli Indabo ya ce ""Dan Allah Daddy ka bari na kawo wadda nake so na aura, ni wallahi" "bana son waccan yarinyar, ni ka bari zan yi maka bayani""" """Babu wani bayani da zan saurara daga gareka, dan nawa bayanin ne gaba da naka, kuma kaje ko sallami koma wace karuwar ce daga gidanka, tun kan na biyoka na ci maka mutunci"" cikin sauri ya fice, yana sake kiran rahama, a ransa yake jin sai dai ayi wadda za ayi, ko da kuwa hakan yana" nufin bayyanawa duniya ramma ne. *** "Yana tsaye a jikin bishiya, ya juya wa hanyar da take tahowa baya, yayi crossing ƙafarsa, hannunsa ɗaya riƙe da taba, ɗaya kuma yana danna wayarsa. Daga bayansa kawai, sai mutum ya so ya juyo ya ga fuskar sa, suffarsa ta ƙaƙƙarfan namiji duk a bayyane, saboda yadda damtsensa yake a murɗe, ya cika hannun shirt ɗin sa, hannunsa ɗaya kuma ya sha ɗinki. Rigar ja sai dogon wandonsa baƙi." """You are under arrest, officer ku kama shi"" ko motsi bai yi ba, balle ya waiwayo, ta zagaya ta gefen bishiyar, tana leƙa fuskarsa, ya ɗaga kai ya kalleta ta ce ""Kai baka jin tsoro ne?, ba ka ji" "tsoro ba da na ce you are under arrest"" ya ɗaga kai ya kalleta ya ce ""Tsoro?""" "Ta ce ""Eh mana""" """Hmm"" kawai ya ce, ya zuƙi sigarinsa, ya kawar da kansa gefe, ya din ga sakin hayaƙin, in a" "passionate way""" "Ta zuba masa ido, komai nasa na daban ne, kuma na musamman." """Wurinka na zo""" "Ya ɗaga mata idonsa da girarsa ɗaya alamar yana jinta, hakan ya sanya ta ɗan diririce." "Ya samu wuri ya zauna, ita ma ta zauna, ta kalleshi ta ce ""Sannu ya hannunka? Na ga da sauƙi ma" "baka da ƙan jiki"" ya kalli ciwon, ya basar, ya sake zuƙar sigarinsa." "Yana sakin hayaƙin, ta fara tari, ya kashe sigarin a jikin bishiyar, ya ce ""Ina jinki""." "Tayi gyaran murya ta ce ""Raina ma fa babu daɗi, shari'ar nan da nake yi, so suke su yi mink fin ƙ" "arfi, na fara sarewa kuma hope ɗin iyalin mutumin duk a kaina yake, ni da na gansu ma sai in ji zan yi kuka"" tayi maganar tana goge hawayenta." """Ohh, a haka za a tsaya mini? Idan bamu yi nasara ba, sai mu zauna mu yi kuka?"" Ta girgiza kai ta" "ce ""A'a zamu yi nasara in sha Allah, shaidar fa da na gabatar babbar shaida ce, wani ya turo mini" "voice na maman Yarinyar, tana kuka ta ce a taimaka mata, amma wanda ya turo ɗin yayi blocking" "ɗina, sai kuma aka ajiye mini wannan a office ɗin"" tayi maganar tana ciro file ɗin tarihin Naja bunkure ta miƙa masa daga cikin jakarta ta goyo." "Ya karɓi file ɗin ya fara dubawa, ya miƙa mata hannunsa, ya ce ""Bani wayarki"" ta ce ""Wayata?""" "Yayi shiru yana kallont, dan ba zai maimaita ba." "Ta ciro ta cire password ta miƙa masa, ya karɓa yana dannawa." "Ta zura kai tana leƙa wayar, ta ce ""Me kake nema a wayar?"" Ya janye wayar ya cigaba da" dannawa. "Kiran Nasir ne ya shigo, ya miƙe mata dan ta ɗaga, ta girgiza masa kai ta ce ""Rabu da shi""" """Ki ɗaga ki gaya masa muna tare, ba nemana yake yi ba?""" "Ta kalleshi ta ce ""Ga wayar nan a hannunka, ka ɗaga ka gaya masa"" kafin ta rufe bakinta, ya yi" "accepting call ɗin, ya kai wayar kunnensa." Ayshercool 08081012143 ₦500 ne via 0009450228 Aisha Adam jaiz bank sai shaidar biya ta 08081012143 Wanda za su jira document 1K ne. 90009343 'Yan Nijar ku turo katin airtel na 300fcfa Arewabooks ayshercool7724 "Wata irin zabura Nabila tayi, ta kai hannunta zata karɓe wayar, amma ya riƙe hannunta yana" "kallonta, girgiza masa kai tayi da sigar magiya tana kallonsa." """Hello. Hello, Arfa"" muryar Nasir ta fito rangaɗau a wayar." "Viper ya ɗaga idonsa yana kallon ƙwayar idonta, ga mugun riƙon da ya yi wa hannunta da take" jin tamkar zai ɓalle. """Arfa kina ina ne? Hello kina ji na?""" "Kallon da Viper yake yi mata, gaba ɗaya sai ta rikice, ga kusancin da suke da shi, ta ƙara" "rikicewa. Kasa daurewa tayi ta ce ""Wayyo hannuna""" """Nabila, menene? Kina ina ne?""" "Al'amin ya sakar mata hannunta, ya katse kiran, ta ja da baya tana murza hannunta tana ƙifta ido." """Amm meye ma sunan naki?""" "Ta kalleshi tana turɓuna fuska ta ce "" 'yar madara""" "Cikin sauri ya kalleta ya ce ""Iyee?""" """To idan ban kai 'yar madara ba, ka din ga ce mini 'yar suga, ko mazarƙwaila"" tayi maganar tana" cigaba da murza hannunta. """Baki shiryawa wannan ranar ba, ki ka yi gammon ɗaukar abun da baki san a ina zaki sauke ba?""" "Ta gyara zamanta ta ce ""Nayi mana, ai shi ramin ƙarya ƙurarre ne. Amma yau da ka gaya wa DSP muna tare, da ka gama kashe ni da raina, ban gama da aikin gabana ba, ka sake ɓallo mini ruwa." "Zaman kotun nan na yau ya bani haushi, Alƙalin alamu sun nuna side zai ɗauka, gashi dattijon nan ya musa ya ce ba shi bane ba, sun kafa hujja da shi ne, wai lokacin da abun ya faru daga shi sai ita, kuma ita da shi da wata mai aiki ne, amma har gidan ɗayar naje ban same ta ba." "Su kawo ita rammar kotu, ba su kawota ba, ba su da wata tabbatacciyar shaida, recording ɗin da" "na gabatar, an soke an ce sai dai uwar taje da kanta, ni na rasa me ma zan yi wallahi"" tayi maganar cikin matsananciyar damuwa." "Ya nuna mata file ɗin hannunsa ya ce ""Waye ya baki wannan?""" """Ban san waye ba, a kan teburina kawai na ganshi da safe"" ya cigaba da daddana wayarta, ba tare" "da ya kalleta ba ya ce ""Kin ɗauki hotona, dan ki nuna wa yayanki ya kama ni?""" "Ta kalli wayar hannunsa, ta ce ""Ai nayi hiding ɗin hoton, ya aka yi ka buɗe?""" "Ya sake kallonta ya ce ""Me kike da hotona?""" "Nabila ta ce ""Saboda in din ga kallonka, ina jin daɗi, askin nan da aka yi maka kayi mini kyau" "sosai da sosai ne"" tayi maganar tana murmushi." """Amm, amma dan Allah ina ka tafi, naji su Oga walid sun ce, ɓata kayi, wai ranar da muka rabu ina ka tafi? Can ka koma ko? A can aka ji maka ciwon nan. Na tsorata da naga an yanki cinyar" "wani, da sun ganni nima kasheni za su yi ko?""" "Gyaɗa kai yayi, ya ce ""Kina da system?""" """Eh tana gida amma"" ya cigaba da danna wayarta." """Wai dama kana magana haka? Baka taɓa yi mini doguwar magana ba sai yau. Hmmm da tabon wuƙarka da ka yi mini zan koma ga Allah, ka kusa fa kashe ni ranar farko da muka haɗu, ban san laifin da nayi maka ba ka kusa kashe ni. Amma dai yau ba ka sha komai ba ko? Naga yau ka yi mini kirki"" jefa mata wayarta yayi ya tashi tsaye, ya ce ""Ki kula da kanki, ana bibiyar ki, ana bibiyar wayar da ki ke yi da wata sumayya, akwai alamar tana bin diddigin abubuwan da ki ke yi," "ko kuma ana bibiya bata sani ba"". Ta tashi tana zare ido ta ce ""Sumayyan?""" """Wanda yake bibiyarki, shi ya turo miki wannan voice ɗin, ya baki tarihin bunkure, duk da bai baki complete ba. Yana bibiyar ki ko dan ya taimake ki, ko kuma yana da manufar da yake son" "cimma, dan haka ki kula""" "Ta dafe ƙirji ta ce ""Amma meyasa za a din ga bibiyata da sumayya? To wa ka ke tunanin yana bibiyata? Ka yi mini bayani sosai da sosai to me ma nayi za a bibiye ni?. Ya cigaba da tafiya bai" "bata amsa ba, tabi bayansa tana cigaba da magana." "Ya tsaya cak, ya waiwayo ya kalleta, tsayawa tayi ita ma, tana kallonsa tana jiran taji mai zai ce?." """Kin haɗu da Indabo?""" "Shiru ta yi, sai kuma ta waro ido ta ja da baya, ta ce ""Wai indabo ɗan siyasar nan, shi ne dai na cikin labarinka? Na ganshi a wurin aikin su sumayya, subhanallah shiyasa tun a ganin farko da" "nayi masa naji na tsane shi""." """Ya ganki?"" ""Eh, sai dai ban kula shi ba. Ai ni bai sanni ba, nima kuma ranar na fara ganinsa," "sunansa kawai nake ji, amma menene?""" "Ya girgiza kai ya ce ""Shikenan"" ya cigaba da tafiya." "Ta sake bin sa tana ɗan haɗawa da gudu, saboda saurinsa ya fi nata sosai, ""To ka yi mini bayani," "ni menene haɗina da shi to?""" """Babu, ki je ki mayar da hankali a kan wannan case ɗin, idan kin yi wining sai ki dawo, kar na" "sake ganinki a wurin nan""" "Cikin rashin fahimta ta ce ""To amma""" """Take your way, ki tafi na ce"" yayi maganar yana nuna mata hanya, ƙyam ta tsaya tana kallonsa, mamaki ne ya cika shi, tsawar da yayi mata ko a jikinta, ta tsare shi da idanunta masu matuƙar" "haske, yanayin yadda take abubuwan ta, ya sake tabattar masa da akwai sangarta a tare da Nabila." "Ya juya ya tafi, ita kuma ta tsaya cak, tabi bayansa da kallo, tafiyarsa kawai gwanin burgewa," "tafiya yake yi cike da ƙasaita, da bayyanar da ƙarfin da yake da shi, sai dai shi bai san yana" "hakan ba, har ya ƙulewa ganinta, sannan ta juya ta fara tafiya." "Sai yanzu take wasu lissafe-lissafe, tabbas sumayya ta canza, sun rage yin waya sosai yanzu, kuma ba ta kiranta da layinta sosai yanzu, kenan da gaske haɗa baki aka yi Sumayya a bibiyeta? To" waye yake bibiyar ta ta? Farar motar nan ce ya faɗo mata a rai. """To idan kuma an san ina zuwa nan fa, aka tona mini asiri, ina zuwa wurin mai laifi da ake nema" ruwa a jallo. Wace amsar zan bayar na kare kaina?. """Wai me ma ya aike ni tun farko? Ina zaman zamana"" tana tafe a hanya, wani irin ciwon kai ya" "saukar mata, da kyar ta ƙarasa gida." *** "A kwance Abdul ya tarar da ramma, cikin damuwa ya ce ""Rahama ya aka yi baki da lafiya, har na fita baki gaya mini ba?""" "Ta yamutsa fuska ta ce ""Na zata zan warke ne, ba sai na sha magani ba""" """Wannan ai ganganci ne, ko dai ciki ne?""" "Da sauri ta ce ""A'uzibillah, Allah ya yi mini tsari, ai kai ma ka san ba shi bane ba""" """Duk da haka, sai na gwada"" first aid drower ɗin sa ya buɗe, yayi mata gwaje-gwaje, babu ciki sai" malaria. """Rahama, wurin nan babu sauro a ina ki ka samo malaria kuma?""" "Ta kalleshi ta ce ""A jikinka""" "Yayi murmushi, ya haɗa allurai, zai saka mata cannula, ta hau kuka wai ba ta so." """Rahama kina wahalar da ni, yanzu alluran baki zan yi ki shanye ko kuwa?""" """Ni hannunka da zafi gaskiya, ka samo wani yayi mini"" ya harareta ya ce ""Wani wa? Babu wani" "mahaluki da zai ganar mini jikinki a doron duniyar nan, ina kallon shi""" """Eh amma ai kai ka iya kallon na wasu""" """Duk cikin aiki ne, kuma ki yi mini shiru nayi aikina, ko na caccaka miki allurar har a baki""" "Ya saka mata cannula, yayi mata allurai, ya saka mata ruwa, da duk ya ajiye su a gidan, saboda" ramma. "Ya rungumeta a jikinsa, yana shafa saman cannulan, ɗaya hannun kuma yana matsa jikinta a" hankali. "Ya zubawa hannunta ido, daga lokacin da ya ɗaukkota zuwa yanzu, ta canza sosai da sosai, fatarta tayi kyau, tayi haske. Ramma ba wani shahararren kyau ne da ita ba, amma yana jinta a kusa da" "zuciyar sa, duk da ba wani shiri suke yi ba, duk in da ya tafi tana ransa." "Bai taɓa raping ɗin mace ba, sai a kan ramma, hakazalika bai taɓa tarayya da virgin ba sai ita. Bai taɓa jin kunya da dana sanin wani rashin mutunci da ya yi ba, sai a kan abun da yayi musu, yanzu kuma uwa uba, ɓatan mahaifiyarta, bai san me zai ce mata ba, duk da yana ta ƙoƙarin ganin ya" gano in da take. "Yayi ƙasa da muryarsa ya ce ""Sannu, kan ya daina ciwo?""" """A'a, amma Alhamdilillah ya rage""" """Masha Allah, ki bani labarin ƙauyenku mana, zan cika alƙawari, na yi magana da ɗan majalisar ku, lokacin da naje Abuja, zai shigar da ƙudurin hanyar ku, burtsatse ma da ki ka ce, ina jiran injiniyoyi su gama lissafi su turo mini, za ayi muku guda uku"" ta tashi zaune ta kalleshi ta ce ""Da" "gaske dan Allah?""" "Ya jinjina mata kai yana murmushi, itama murmushin ta yi, ta ce ""Yan garinmu za su ji daɗi, mun gode Allah ya saka da alkhairi, mun gode sosai, yan garinmu mun daɗe muna koken rashin hanyar" "nan, amma ba ayi mana ba, mun gode""" """Yau ba Allah ya isan?""" """Ai wancan abun da ka yi mini daban, wannan ma daban, amma Allah ya isa tana nan""" "Abdul ya yi ajiyar zuciya ya ce ""Ki yafe mini mana sweetheart """ "Ramma ta ce ""Ka mayar da ni wurin mahaifiyata, ka nemi afuwarta, amma haryanzu a zuciyata" "ban ji zan iya yafe maka ba, daga kai har anty maijidda, da wannan bayahudiyar matar""" "Yayi shiru ya sunkuyar da kai, zuciyarsa babu daɗi, ta ɗaga kai ta kalli fuskar sa, ta ce ""Oho, ba zaka bani tausayi ba, ka tuba ga Allah ka gyara halayenka, dan ka samu kyakkyawar makoma. Ka" "cigaba hannun ya fara zafi"" bai ce mata uffan ba, ya cigaba da shafa mata hannun." "Ta saka ɗaya hannun ta juyo da fuskarsa, taga idanunsa sun yi ja, sun bayyanar da tsantsar" damuwa. """To meye kuma?"" Ya girgiza kai alamar babu komai." """Ka tabattar?"" Ya jinjina mata kai alamar eh." """Shikenan, to kayi haƙuri dai, ni gaskiyata na gaya maka, baka san zafin abun da ka yi mini bane," "amma naga kamar ka ji haushi""" """Meyasa zan ji haushi, carbi zan sayo ki zauna ki yi ta jan Allah ya isan son ranki"" ta murguɗa" "masa baki, ta kawar da kanta gefe." *** "Madaki ya zuba wa cinyarsa ido, yadda ciwon da Viper ya ji masa yayi wani irin mugun rami, maimakon ya yi ja ma, sai ya koma yayi kore, wasu irin jijiyoyi duk suka ɗaɗɗaga a gefen ciwon, ƙafar ta ƙara riƙewa, ba ya iya takata sai dai ya dinga jirgata." "Ya kalli babban amintaccen yaronsa ya ce ""Lakwari, ciwon nan fa cigaba yake yi, kenan ta tabatta" "alkadarina ya karye?""" """Nima na gani maigida, kaga ana ta saka maganin, amma sai cigaba yake yi. Ba zamu yi saurin yanke hukunci ba, mu bi dare kawai, muyi makabeli mu ɓace mu yanka gabas, mu koma in da aka fara, ya duba mana, idan da wani abu da za a yi a kai, idan ba haka ba, mai zamani ya yi maka" "muguwar illa, kuma yana sane yayi hakan""." "Madaki ya jinjina kai ya ce ""Haka ne, babban abun da ya bani mamaki, bai wuce wanda suka zo" "suka ɗauke shi ba, ban san suwaye ba. Ta tabbata yana da waɗanda suke goge laifukan da yake aikatawa, yakamata na sanar da indabo""" "Lakwari ya ce ""Haka ne, amma mu fara neman mafita, a karya dafin nan da ya saka maka, kafin" "duk wata magana ta biyo baya""." "Ya jinjina kai ya ce ""Shikenan""." *** "Sumayya da murtala ne a zaune a gaban MD sun yi fiƙi-fiƙi da idanu, gefe ga lawisa a zaune." """Abun da ku ke yi, da kai da sumayya ya fara yawa a wurin nan, ko dai ku bi tsarikanmu, da abun da muka ce dan cigaban tashar nan, ko kuma ku ajiye mana aikinmu. Duk jajircewarku akwai waɗ anda suka fiku. Gashi kun saka hankalin mutane gaba ɗaya ya yo kanmu, saboda recording ɗin da ku ka saki a duniya da yake bayyanar da zargi ga Naja'atu Bunkure, wands duniya kowa ya" "shida mutuniyar kirki ce, mai yi wa mutane hidima""." "Murtala ya ce ""Tuba muke, muna neman afuwa in sha Allah ba zamu sake ba""" """Daga kai har ita, wannan ne karo na biyu da kuka aikata mana laifuka, muna ƙyaleku, na uku" "kora ce. Yanzu dole mu san yadda zamu yi mu gyara wannan shirmen da kuka yi"" Murtala yayi ta bayar da haƙuri, sumayya kuwa fafur ta yi shiru, taƙi cewa komai." "Sun fito daga ofishin MD, tana hura hanci, ta tarar da Nabila." "Sumayya ta ƙarasa ta zauna a kusa da ita, ta ce ""Ke kuma daga ina? Kin je kin haɗa kai da Uncle murtala, mun saka recording ɗin da yayi miki, a kan shari'ar nan, yanzu aka gama sauke mana" kwandon jaraba a ka. "Nabila ta ƙurawa sumayya ido, ta ce ""Sumy why?""" "Cikin rashin fahimta ta ce ""Kamar yaya?""" "Nabila ta yi murmushi ta ce ""Don't mind me, mota fa ta iso, na zo na sanar miki""" "Ihun farinciki sumayya tayi ta ce ""Are you serious, ko kuma jirgani ki ke yi?""" """Da gaske nake, amma Abba ya ce ba zan hau ba, sai driving licence ɗina ya zama ready, kin san" "shi da ƙa'ida""" "Cikin farinciki ta ce ""Alhamdilillah, summa Alhamdilillah yawo ba kama ƙafar yaro, Allah ya saka wa Abba da alkhairi, uban marayu mai uban ma goyawa yake yi. Amma dan Allah arfat ki kula, ki san in da zaki din ga zuwa, banda rigima da faɗa da mutane a titi"" ta din ga kallon sumayya, da son tabattar da abun da Viper ya gaya mata, yanzu sai ayi amfani da ita, a cutar da ita," sam ta kasa yarda gaba ɗaya. "Wada M karofi ne ya kira Nabila a waya, ta ɗaga ta ce ""Hello sir""" """My beautiful angel, ya kike yau bamu gaisa ba gaba ɗaya, kin ƙi bari mu haɗu, gashi na koma" "wurin aiki""" "Ta ɗan kashe murya ta ce ""Ba haka bane ranka ya daɗe, ka san aikin namu ne babu zama, amma very soon zaka zo har gida mu gaisa"" yayi murmushi ya ce ""To shikenan, na san maybe kina wurin" "aiki, da daddare zamu yi waya in sha Allah""" """Ok Allah ya kaimu, ka kula da kanka sosai, kar ka yi aiki ka gaji da yawa""" "Yayi dariya ya ce ""Thank you my dear""" "Sumayya ta ce ""Ohh wa kuma ake yaudara, wa aka kwaso mana?"" Nabila ta bata labarin wada M" karofi. "Sumayya ta ce ""Allah ya sa shi ne mijin, kakarmu ta yanke saƙa, kin san waye mutumin nan kuwa" "Arfa? Allah ya tsaga miki farinjinin manyan mutane, kar ki yi mana buƙulu dan Allah""." "Nabila ta tashi ta ce ""Taɓ gaskiya ba na son shi, ki zo gida kiga motarmu""" "Sumayya ta ce ""Dolena"" Nabila tayi mata sallama ta fito, zuciyarta na cigaba da wasi-wasi a kan" "Sumayya, har ga Allah tana ƙaunar sumayya har cikin zuciyarta, ta kasa yadda da abun da Viper" ya gaya mata. "Nabila na tafiya aka kira Sumayya a waya, ta ɗaga tayi shiru." """Sumayya meyasa ki ke wasa da rayuwar ki, da ta ƙawar taki ne? Bayan ɗan waken zagaye da ki" "ke yi, Ki ke kiranta da wasu layukan daban, shi ne ki ka yi disconnecting ɗin bibiyar kiranki da ita da muke yi ko?""" """Ni kuma, ban gane nayi disconnecting ba? Wallahi ban yi disconnecting ba""" """Ƙarya ki ke yi, some hours back, aka yi disconnecting, zaki ga matakin da zamu ɗauka a kanki" "da ita, sannan zuwan da tayi me kuka tattauna?""" "Sumayya ta dafe kanta ta zauna, sannan ta ce ""Mota aka saya mata, sai labarin sabon saurayinta da" "tayi, Alhaji Wada M karofi, sai ƙorafin rashin nasara da take hangowa a kan shari'ar da suke yi""." "P.A ya maimaita ""Ki ka ce Alhaji wada M karofi?""" """Eh, shi""" """Ki cigaba da sanya ido a kanta, kina kawo mana rahoto, akasin haka zaki ga abun da ba kya so """ ta kashe wayar ta dafe kanta. *** """Indabo ya ga yarinyar nan""" "Gaba ɗaya suka kalli Al'amin, liti ya ce ""Shikenan, ai na san a rina""" "Walid ya ce ""Ya aka yi ka gane haka?""" """Mun yi magana da ita sosai yau, ana bibiyar ta, ana bibiyar kiranta da wata ƙawarta, na yi disconnecting duk wata hanya da za a cigaba da bibiyar kiranta. Amma rayuwarta na cikin hatsari," "kuma idan ta cigaba da zuwa za a gane inda muke""." "Liti ya ce ""Shiyasa tuntuni na ce, a sallameta ta daina zuwar mana nan, amma walid ya nace""." """I think i will sealed a deal with her""" "Suka haɗa baki suka ce ""Kamar yaya?"" Yayi shiru yana lissafa yatsun hannunsa." "Liti ya ce ""Ka yarda da ita ne? Ni haryanzu tantama nake yi a kanta ne""" "Walid ya jinjina kai ya ce ""Lallai a tafawa mata"" Viper bai sake ce musu komai ba daga haka, ya" tashi ya fita. *** "M karofi yana zaune yana shan shayi, wani jami'in tsaro, ya shigo da Indabo cikin falon." "Karofi ya kalli Jami'in tsaron ya ce ""Zaka iya tafiya"" ya mayar da idonsa kan Indabo ya ce ""Barka" "da zuwa sirikina, kwana da yawa, muna haɗuwa a Abuja, amma da ni da kai, babu wanda yake ziyarar wani. Duk ni yakamata ace ina kawo gaisuwa. Bisimillah zauna mana." "Indabo ya zauna, ya kalli M karofi ya ce ""M karofi""" """Ma'aruf Indabo""" """Sabo da kaza fa, baya taɓa hana a yanka ta""" "Karofi ya ce ""Wannan haka yake, ko a siyasance, ko ma a normal life""" """Auren 'yar uwata maijidda da kake yi, ba zai hana idan kayi mini kan kara nayi maka na itace ba," "hawainiyarka ta kiyayi ramata""" "Yayi murmushi ya ce ""Yakamata kayi mini fashin baƙi, akan wannan kurman baƙin da kake ta" "karanta mini""" "Indabo ya yi wata ƙwafa ya ce ""Soyayya da ka je ka fara da 'yar cikinka, saboda abun kunya," "kuma yarinyar da take ta gwagwarmayar sai ta tona mana asiri, wadda ka tsayawa, wallahi muddin asirin Abdul ya tonu kaine ba wani ba, kuma sai nayi maganinka a siyasance da duniyance""" "M karofi ya ce ""Iko sai Allah, kana nufin Nabila wai? Taɓ ai ni ban taɓa sani ba, banda yanzu da kake gaya mini. Ina da lawyer a law firm ɗin su, shi naje gani, na ganta naji ina sonta, kai idan nayi niyyar tonawa ɗanka asiri, da wani zancen ake yi ba wannan ba." "Kuma ni ban yi abun kunya ba, sonta nake yi da aure. Tun da ƙanwarka ba yar gwal bace, da zata hanani zama da mata ba." "Naji daɗin wannan gargaɗi da kayi mini sosai da sosai, amma ka kwantar da hankalinka, babu" "ruwana da shari'arku, nima aikina nake yi. Zaka iya tafiya idan baka da abun cewa""." "Indabo ya tashi, ya kalli idon kankarofi ya ce ""Kifi yana ganinka mai jar koma""" "Karofi ya ce ""A juri zuwa rafi dai "" Indabo ya fice yana baza babbar riga." *** "Nabila ta sake komawa gidan abokiyar aikin ramma, amma still bata same ta ba, aka sake gaya mata ta koma garinsu, sai dai samun sunan garin ma ya gagareta, ta kasa samu." "Tana kwance a kan gadonta, ta buɗe videos da hotunan da ta yi wa Viper, ta zuba masa ido, tana" "jin daɗin tsokanarsa da take yi, na cewa tana son shi, tana son zama kishiyar 'yar madara, mugun" "kallon da yake yi mata, ba ƙaramin dariya yake bata ba." "Mussaman da ta samu ya kulata, a haɗuwar su ta ƙarshe, duk da a ƙarshe, korarta yayi." "Tana kallon hotunan tana murmushi, ta ɗauki ƙaramar wayarta, ta saka lambarsa ta kira." "Sai da ta kira da ainihin lambarta, sannan ya ɗaga." """Ohh Allah, kayi saving lambata ne?, Ina ta kiranka da ɗaya layin amma baka ɗaga ba. Ina ta kallon hotunanka, ina son in yi bacci ." "Ka san ranar da nayi maka hotunan nan, har murmushi fa kayi, ka din ga fara'a murmushi yana yi maka kyau sosai dear. Yaushe zaka ƙarasa bani labarinka ne? Yakamata ka gabatarwa jauhar ni, a matsayin amarya, zan yi mata biyayya sosai da sosai, in tayata sonka. Ba zan yi kishi da ita ba, ina sonta sosai da sosai, dan Allah ko sau ɗaya ka haɗani da ita mana"" kamar da iska take, haka yayi" shiru ya ƙi magana. "Ba ta gaji ba, ta sake cewa ""Ina ƙaunar yar madara saboda Allah, dan Allah ka ƙarasa mini" "labarin ta""." """Meyasa ki ka shigo rayuwata?""" "Tayi ajiyar zuciya ta ce ""Labarin dogo ne, ba zan ɓoye maka ba, da dai ina taya Yayana nemanka" "ne, saboda nayi suna, na rama abun da Bunkure ta yi mini, na wulaƙanta ni a gaban jama'a. Shi ne na din ga up and down, har na haɗu da wannan litin, mara kirki""." """Saboda ki yi suna ki ke son taimakona?""" "Nabila ta ce ""Eh, a da ba, amma jin labarinka gaba ɗaya ya canza mini tunani, nake jin zan iya yin komai, dan na ga na ƙwato maka hakkinka, da kai da yar madara, duk da ban san ƙarashen labarin ba. Amma gwiwata ta fara sanyi, na fuskanci Naja'atu Bunkure nan, tana da goyon baya daga sama, kuma indabo babban mutum ne shahararre sosai, ina buƙatar support sosai, kai kuma" "sai korata kake yi kana hantarata""." """Idan na ƙarasa miki labarin, that means duk tsanani babu gudu babu ja da baya, zaki tsaya a" "shari'ata komai wahala da sarƙaƙiyarta?""" """In sha Allah, i promise it""" "Ya sake cewa ""Kin tabattar zuciyarki zata iya ɗauka komai muni, komai daɗin abun da zaki ji?""" "Cikin ƙwarin gwiwa ta sake cewa ""Eh zan iya""" "Viper ya ce ""Take your time to think, ki yi comparing da ƙalubalen da ka iya biyo bayan hakan""" "Ta lumshe idonta, hatta muryarsa, mai daɗi ce, duk a buɗe take saboda bayan naturally yadda take," wiwi da shaye-shaye sun ƙara making ɗin ta deep. "Ba ta bashi amsa ba, ya kashe wayar." "Walid ya ce ""Mai zamani, ka yadda da maganarta kenan? Zaka ɗauki fansa ta hanyar shari'a""" "Mai zamani ya girgiza kai ya ce ""Ta riga ta shiga tarkonsu, kuma na fuskanci ba ta ji ko kaɗan," "zata iya salwantar da rayuwarta"". Walid ya yi murmushi mai cike da jin daɗi ya ce ""To ɗaya maganar fa? Zaka gaya mata?""" "Al'amin ya kalli walid, yayi shiru bai ce komai ba." *** "Jikin ramma da sauƙi sosai, tana zaune a gefen gado, Abdul yana bata abinci, gefe ga magungunan ta. Wayarsa da take ringing ya ɗaga ya saka a hansfree ya ajiye ya ce "" 'yar mutanen bunkure, ya ake ciki ne?""" """Abdul""" """Na'am""" """Ya ka yi da yarinyar nan ne da ka yi wa fyaɗe? Wata yarinya ta tsaya kai da fata, sai ta wanke dattijon nan, mun yi duk abun da yakamata, ta koma tana amfani da social media against me, hankali na ƙoƙarin dawowa kaina, sai sintiri take yi wai lallai sai an kai yarinyar gaban shari'a, ga wani voice message da yake yawo na uwar yarinyar Abdul ya cire wayar daga hansfree, ya" "saka a kunnensa, yana kallon ramma." """Ka gaya mini yaya ka yi da ita? Tana raye ko ta mutu? Mu san abun da zamu shirya a kan shari'ar," "an je gidansu babarta bata nan an nemeta an rasa""" """Kina ji? Zan zo in anjima yanzu ina wani uzurin ne"" ya kashe wayar, ya kalli Ramma zai yi" "magana, amma ya kasa saboda mugun kallon da tayi masa." """Rahama ki tsaya ki saurare ni ki ji""" """Kayi mini shiru tun ba shaƙeka ka mutu na huta ba, azzalumin banza da na wofi, in sha Allah sai" "Allah ya tarwatsa ka da kak kai da duk masu goya maka baya kuna cutar mutane""" "Fafur ta ƙi saurarsa, tayi watsi da kayan karin kumallon, ta tashi ta bar masa ɗakin." *** "Nabila ta daina shiga harkar Nasir, dan sosai ya sakata a gaba, da masifar lallai sai ta daina case ɗ" "in bunkure, saboda lafiyar ta da rayuwarta, ita kuma ta ce babu wanda ya isa." "Sumayya ce ta kirata da wata lamba, ta ɗaga ta ce ""Waye?""." """Ke ni ce""" "Nabila ta ce ""Yar 419, yau kuma da lambar wa ki ka kirani, ko aiki ki ke yi a kaina ne?""" """Nabila, bar wannan maganar kin san menene?""" """No""" """Maganarki da muka saka a radio, a kan bunkure, wata mata ta zo mini, ta ce lallai ke take son" "gani, akwai information da zata baki a kan bunkure, ta ce macuciya ce, abun babu daɗin ji, bama itakaɗai ba, akwai gwarama, mutane sun fara magantuwa fa""" "Nabila ta ce ""Abubuwa sun fara yi wa kaina yawa, zan zo har gida na same ki""" "Ta ajiye wayar ta dafe kai tana tura baki. Duk da tayi farinciki da haka, dan kuwa gagarumin cigaba ne, amma gaba ɗaya ba ta yadda da sumayya ba yanzu, dole tana buƙatar ganin Viper kafin" tayi wani yinƙuri. "Babu tsammani ta ga Nasir ya shigo office ɗin ta, ta tashi tsaye ta ce ""Yaya lafiya?""" """Nabila wai ke meyasa a duniya ba kya nemawa kanki zaman lafiya ne? Gaba ɗaya na kasa gane" "kanki a 'yan kwanakin nan, menene yake damunki ne?""" "Cikin rashin fahimta ta ce ""Me kuma nayi?""" """Comment ɗin da ki ka yi da safe nake magana a kai"" yayi maganar yana ciro wayarsa ya" "daddana, ya buɗe facebook ɗin sa, ya tura mata wayar." "Ta kalli wayar, posting ne da hukumar yan sanda tayi, na cigaba da neman Aminu Viper ruwa a" "jallo, saboda ayyukan ɓarna da yake cigaba da yi." "Tayi comment da ""Wannan abun kunya ne ga rundunar tsaron Nigeriya, ace kuna tsare da mutum a prison, a sake shi kuma a dawo ana nemansa, ba shi ne abun bincike ba, hukumar 'yan sanda, da prison, da ta shari'a su ne abun tuhuma da zargi"" aikuwa mutane suka yi caa a kan comment ɗin ta," suna reply. """Yanzu yaya fisabilillahi menene laifina a cikin wannan comment ɗin nawa, ita hukumar 'yan sandan, dan ayi comment ai suka yi posting ɗin, kuma gaskiya na faɗa. Akwai ayar tambaya a kan ma'aikatar Shari'a, hukumar yan sanda da ta gidan yari a kan case ɗin nan, kar ka yi wani tunani" "daban, ina goyon bayan gaskiya ne kawai""" """Nabila ba kowane lokaci gaskiya take tasiri a ƙasar nan ba, yanzu ki ka shigo cikin system ɗin" "nan, ƙasar nan ta wuce duk yadda kike tunani""." """Na sani, amma rashin yin wani yunƙuri na kawo gyara, shi ne ke kawo mana koma baya yaya, ba" "wai ina goyon bayan Aminu Viper ba ne ba, menene gaskiyar abun da yake faruwa nake son sani""" "Cikin takaici ya girgiza kai ya ce ""Idan kin ƙi ji, ba zaki ƙi gani ba arfa""." "Ya ɗauki wayarsa ya juya ya nufi hanyar fita, ya kama handle ɗin ƙofar office ɗin ya murɗa ya buɗe. Sai dai wanda suka yi ido huɗu da shi a tsaye ya sanya gabansa wani irin mummunar faɗ uwa. Ya raɓa jikin Nasir ya shiga cikin office ɗin, Nabila ta waro ido tana kallonsa tana kallon" Nasir. Ayshercool 08081012143 ₦500 ne via 0009450228 Aisha Adam jaiz bank sai shaidar biya ta 08081012143 Wanda za su jira document 1K ne. 90009343 'Yan Nijar ku turo katin airtel na 300fcfa Arewabooks ayshercool7724 "Kallonta yake yi ta cikin baƙin glass ɗin idonsa, duk da ya saka facemask, babu yadda za ayi" Nabila ta kasa gane shi. "Nasir ya tsaya ya waiwayo, yana son sake ganin waye, duk da fuskarsa a rufe take da face mask," "amma ya tsaya ƙyam a tsakiya, ya juya wa Nasira baya, yana fuskantar Nabila." "A hankali ya ƙarasa takawa, yaje ya samu wuri ya zauna a kan kujera, ba tare da yayi magana ba." Nabila kuma ta kalleshi ta kalli Nasir. "Nasir ya juya ya tafi, yana fita da saurin gaske ta ƙarasa, ta rufe ƙofar office ɗin ta saka mata" key. "Ta dawo ta kalleshi, ya cire facemask ɗin sa da glass ya ajiye a kan teburinta." """Su maciji an fito daga rami, kuma kai tsaye aka yo wurina, dan Allah meyasa ka ke son lallai" "sai ka haɗu da yaya Nasir ne? Da ya gano ka da ni da kai zai haɗa duk ya kama, dan ban san me" "zan ce masa ba""" "Ta dafe ƙirjinta ta ce ""Wayyo Allana, haryanzu zuciyata racing take yi, ranka ya daɗe irin haka sai ka kirani a waya, ka ce in zo kana son ganina, amma wannan dirar mikiyar da ka yi mini ohh my God me ma zan ce ne? Allah ya sa babu wanda ya sanka"" ta zagaya ta buɗe fridge ɗin office ɗin" "ta, ta ɗauki plate ta ɗoro masa apple, ayaba da lemo ta zo ta ajiye masa." "Ta tsiyayo ruwan zafi a dispenser ta haɗa masa tea mai zafi, ta buɗe jakarta ta ɗaukko ɗan ƙara min flask, ta juye masa dankali a kan plate da ƙwai, ta ce ""Bisimillah, fara cin abincin sai mu yi" "magana naga yanzu safiya ce"" yayi shiru yana danna wayarsa." """Ka ci abinci, wanne zaka fara ci?""" "Still bai yi magana ba, har ta fara jin haushi." """Sweetheart, magana nake fa, 'yar suga na magana"" ya ɗago ya kalleta." "Ta saka hannu ta karɓi wayarsa ta ajiye, ta ɗauki kofin shayin ta miƙa masa ta ce ""Ba dan ni ba, dan Allah ka sha, a gabanka na haɗa, ban kuma son da zuwanka ba, balle ka ce na zuba wani abu a" "ciki dan Allah"" tayi maganar cikin kwantar da murya." "Ya saka hannu ya karɓa, sai dai kamar ƙaramin yaro, ya zubawa kofin ido." "Ta ɗaukko plate ɗin dankalin, ta riƙe a hannunta, ta kalle shi ta ce ""Sha mana"" ya tsareta da" idanunsa masu ban tsoro. "Ta sauke nata idanun, saboda yadda nasa suka yi mata nauyi." "Ta saka hannu ta kai kofin bakinsa, ya buɗe bakinsa a hankali, ya fara sha." "Tayi ɓoyayyiyar ajiyar zuciya, ya sauke kofin, ta miƙa masa dankalin, kamar mai koyon cin" "abinci, haka yake ɗauka yana ci." """Yauwwa My dear"" yana ci, Adam apple ɗin maƙogwaronsa, na kaiwa na komowa, sai yayi kamar zai yi magana, sai ya fasa ya haɗiye maganar tare da abincin, da ƙyar yake haɗiye abincin, a duk lokacin da ya saka abinci a gaba zai ci, haka yake ji, sai ya cakala ya bar shi, tun su liti suna" "lallaɓa shi ya ci abinci, har sun haƙura sun ƙyale shi, sun zuba masa ido." """Master, ciwonka ya gama warkewa, Alhamdilillah Allah ya ƙara tsarewa, ka daina zuwa in da za" "a cutar mana da kai dan Allah""" "Yayi mata shiru, yana cigaba da cin abinci." """Ko in ƙara gudun AC naga kana gumi"" ya girgiza mata kai alamar a'a." "Tana tayi masa hira, har ya cinye abincin tas." "Ta ce ""Alhamdilillah"" ta miƙa masa tissue ya goge hannu." """Wai dan Allah meyasa kake ta kallona ne? Ko wani abun nayi?"" Nan ma ya girgiza mata kai." """Kamar bacci ka ke ji fa, ko an sha ne?""" """Me fa?"" Yayi maganar yana kallon ta." "Ta ce ""Bakomai""" """Aiki na zo yi"" ya faɗa a taƙaice." "Ta ce ""Aikin me?""" """Computer zaki bani""" "Ta ce ""Ok, desktop ta aiki ce, bari na baka laptop ɗina"" ta ɗaukki laptop ɗin ta ta bashi, ya buɗe" ya fara dannawa. "Ta zauna a kusa da shi, tana kallon mai zai yi, sai dai ta kasa gane me yake yi ɗin, wasu irin" lambobi da alphabets kawai take gani a screen ɗin system ɗin. "Sunan Yaya Nasir ne ya fito a kan wayarta, ta ɗaga ta kai kunnneta, tayi shiru." """Arfa""" """Na'am""" """Waye mutumin da ya zo office ɗin ki?""" "Ta kalli Viper sannan ta ce ""Baƙona ne""" """Wane irin baƙo?""" "Nabila ta ce ""Client ɗina ne, ya zo muyi magana ne a kan wata shari'a meyafaru?""" "Nasir ya ce ""Gaba ɗaya ban yadda da shi ba""" """Daga fara ganin mutum yau ka ce baka yadda da shi ba yaya? Ka san shi ne?""." """A'a kawai jikina ya bani wani abu ne, amma akan case ɗin menene?""" """Is confidential, and against my professional ethics, ba zai yiwu na gaya maka ba, idan na dawo" "mayi magana"" ta katse wayar." """Meyasa ki ke tsoron gaya masa ne? Shi ne DSP Nasir ɗin? Shi a yadda yaken nan matsoraci" "yake son kama ni, ai karo da karo sai rago, na raina jarumtarsa""" "Ta tsuke fuska ta ce ""Ya haka? Yayana ne fa, banda cin fuska""" "Ya ɗaga kai ya kalleta ya ce ""Da lokacin da nake mai zamanina ne, aka bashi aikin kama ni, sai na yi masa karayar da zai shafe shekara yana zaune yana jinya. A yanzun nan da muka haɗu, ba zamu rabu lafiya ba." "Tarbiyyar Jauhar ce da girma ya sanya wasu abubuwan nake kawar musu da kai""." "Ta ce ""A hakan? Yanzun ma fa kana zuwa ka sari mutane, ka yi faɗa da neman magana""" "Ya matso da fuskarsa saitin ta ta, ta ja da baya. ""Lokacin da nake mai zamanina, bana bin ƙofa komai girmanta, sai dai na kama katanga kamar ɓarawo, bana biyo hanya ayi gaba da gaba da ni. Bana tsoron kowane irin nau'i na fitina ko tashin hankali, idan aka kwana biyu ban ji ni cikin rigima ba, sai na ji ni kamar mara lafiya." "Aiki tuƙuru da jajircewa tayi a kaina, ba dan ƙaddara ta rusa tanadi da burikan rayuwata ba, ta ci" "kaso mafi yawa na tarbiyantar da rayuwata a kan tafarki madaidaici. Ki daina haɗa kanki da ita""" "Ta lumshe idonta ta buɗe ta ce ""Shiyasa na ce tun da ita 'yar madara ce, ni kuma sai na zama 'yar suganka, amma ka ƙarasa mini labarin ta dan Allah"" ya zauna sosai ya cigaba da danna system sannan ya ce ""Idan na ƙarasa miki labarin ta, hakan na nufin we sealed a deal, da babu gudu babu" "ja da baya kenan, komai rintsi komai wahalarsa?""" Ta jinjina masa kai alamar eh. """A'a ki sake tunani, mussman ranar da zata fasu kina ɓoye shahararren ɗan ta'adda kamata""" """Kai ba ɗan ta'adda bane ba, ta'addancin da aka yi wa rayuwarka, shari'a ta kasa tsaya maka ya sanya ka zama haka. A labarinka da oga walid ya bani, da tun a lokacin da aka kashe yayanka, hukuma tayi abun da ta dace, da duk ba a zo wannan gaɓar ba." "Muna iya jure rashin makusantanmu ne, saboda ƙarfin imani, da tuna wanda ya bamu ne ya karɓi abunsa, amma idan wani ya zama sila, na rasa mutane masu muhimmanci a rayuwarmu, wannan imani na yarda da ƙaddara ya kan yi rawa a zukatanmu, mu kasa yadda da wanda ya bamu ne ya karɓa. Kai ba ɗan ta'adda bane ba mai babban suna, cin hanci a doka da shari'a su ne suka mayar da kai duk abun da ka zama a yau. Ba kowace zuciya ce zata jure tana kallon wanda ya cutar da ita yana rayuwa cikin kwanciyar hankali, alhalin ita an bar mata tabo mara warkewa ta jure ba." "Ban ce zan kai 'yar madara ba, amma na fuskanci giɓin da ka rasa nima akwai makamancin sa a" "rayuwata, da yake ci mini tuwo a ƙwarya yake damuna, ina ɓuya in yi kuka wasu lokutan na ji na" "tsani komai, kamar na kashe kaina na huta." "Jin labarinka ya sanya, na fuskanci me ka ke ji a zuciyarka. Har abada duk tsanani ba zan sake kuskuren kallonka a matsayin ɗan ta'adda ba, kuma zan tabattar wa da duniya haka, da izinin Allah. Sai an gyara fannin shari'a an murƙushe rashawa da bambancin hukunci tsakanin ɗan talaka da mai kuɗi, mai ƙarami da babban uban gida, idan ana son rage yawan 'yan ta'adda"" tun da ta fara magana, yake kallonta, duk da tana yi tana zubar da hawaye, hakan ya tabattar masa da akwai wani pain a zuciyarta ita ma." "Ya juya ya cigaba da danna computer, ta kifa kanta tana goge hawaye. Ta kwantar da kanta a kan" "teburin, tana danna wayarta." "Ta ɗaga idonta ta kalli, yadda yake ta sarrafa computer, bata san me yake yi ba." "Yanzun ma hotonsa take ɗauka tana murmushi, kamar ba yanzu ta gama kuka ba." """Master"" yayi mata shiru." "Ta sake cewa ""Maciji"" tai maganar tana dariya." """Viper, maciji mai hatsarin gaske, yau ka fito daga raminka, ka zo wurina, sarana ka zo yi ne?""" Still bai kulata ba. "Ta tashi sosai ta ce ""Da ni 'yar sugar da yar madara, wacce ta fi kyau ne? Kodayake na san ma ita zaka zaɓa, kafi sonta, amma dai kyakykyawa ce? Sannan fara ce ko baƙa? Doguwa ce ko gajeriya, ina son in ganta ka nuna mini hotonta, ko ba zaka bani haɗa ni da ita ba?"". Sai da ya dafe goshinsa, Nabila bata gajiya da surutu, Jauhar akwai lokutan da ba ta kula shi da hira, idan ba ya cikin mood," shi wannan surutun nata ba zai bari su daidaita ba. "Ya fizge wayar hannunta, yana dubawa yana danna computer." """Wai hacking ɗin wani zaka yi ne? Ni baka yi mini bayanin me ka ke yi ba, sonake ma mu yi" "magana, amma ka ƙi kulani, sai aiki kake yi kai kaɗai""." "Ya tashi tsaye ya ce ""Zan yi salla""" "Ta nuna masa toilet, ya shiga yayi alwala, ya fito yayi sallar azahar, sanann ya kalleta ya ce ""Tashi" "mu tafi""" "Ta tashi tsaye ta ce ""Ina?""" """In ƙarasa miki labarina, amma bisa sharaɗin da na gindaya miki da farko, babu gudu babu ja da" "baya, duk tsanani da wahala"" ta jinjina masa kai." "Ya ɗauki facemask ɗin sa ya saka, ya sanya baƙin glass ɗin sa ya yi gaba." "Dama yau hijjabi mai niƙab ta sako, dan haka ta saka niƙabin, ta bishi." "Cikin ikon Allah, chamber babu kowa, duk lawyoyin sun tafi kotuna, sai massenger da mai gadi." "Suka fito, ta ce ""To ina zamu je? Ba zai yiwu ka ƙarasa mini a nan ba?""" """I have to test you more, before i completely trust you"" daga haka ya tarar musu napep, ya gaya" masa in da za su je. "Suna tafe tana ta addu'a, Ubangiji Allah ya kare su, ya tsare duk in da za su je, Allah kar ya sanya" "ya cutar da ita, ko wani ya kama su." "Kasancewar rana ce sosai, layin shiru babu kowa, suka tsaya a ƙofar wani gate, ya ciro mukulli a" "aljihunsa ya saka ya buɗe, ya ce ta shiga. Ta shiga sannan shi ma ya shiga ya rufe ƙofa." "Ta tsaya tana kallon gidan, ya jingina da gate ɗin ya tafi tunani." """Waye yake mini kokowa da ƙofa zai karya mini gate?""" """Ɓarawo ne ya zo sace matar gidan"" tayi dariya ta ce ""Da alama ɓarawon nan, bai san gidan wa ya zo ba ko? Ka bari mijina ya zo ya same ka"" tayi maganar tana fitowa daga falon, fuskarta ɗ" auke da murmushi da tsohon cikinta. """Wai da ke muka haɗa kuɗi muka sai rigar nan ne? Ki din ga ɗaukar mini kaya kina sawa""" "Ta tura baki ta ce ""Kai da kaya mallakar wuya ne, da kayan da mai kayan duk mallakin 'yar" "madara ne"" tai maganar tana sakar masa murmushi." "Nabila ta ce ""Ya naga ka tsaya, ina ne nan?""." Yayi firgita ya dawo daga tunanin da ya tafi. "Ya tunkari ƙofar falon, zuciyarsa na bugawa da sauri da sauri, ya saka mukulli ya buɗe." "Falo ne sosai, komai neat sai dai yayi ƙura sosai." "Ta tsaya tana ƙarewa falon kallo, taji wani abu ya kama zuciyarta." """Viper, nan ne gidanka da 'yar madara tana ina? Kuma baka tsoron azo a kama mu?""" "Bai ce mata komai ba yama wuce ya shiga bedroom ɗin, ya tsaya yana ƙarewa ɗakin kallo," "komai ya din ga dawo masa, tamkar mai mafarki." "Tana tsaye, ya fito da wani riyo a hannunsa ya zo gabanta ya ajiye, yayi kneel down a gaban riyon," "ya buɗe ya shiga fesawa kayan turaren florie. Ya din ga ɗago kayan, na jarirai ne, komai na haihuwa yana ciki intact, hatta zannuwa zamzam, bagaruwa, pad pampers komai akwai a ciki." "Duk wanda ya ɗago sai ya fesa masa turaren ya ajiye, muryarsa na rawa ya ce ""Ɗaya daga cikin" "ƙamshi mafi soyuwa a wurin jauhar kenan""." "Gaba ɗaya zuciyar Nabila ta tsinke, gabanta ya tsananta faɗuwa, ta ɗauki kayan, ita ma ta kai" hancinta. """Yanzu tana ina? Ina kuma jaririn naga kayansa na jariranta haryanzu?""" "Ya ɗaga kai, yana kallon in da Nabila take zaune, ya ga jauhar kwance a wurin, cikin jini, tana ɗ" "ago masa hannun tana la'ila ha illa la, ya Allah." "Daga nan bai sake sanin in da kansa yake ba, sai ji yayi an watsa masa ruwa mai tsananin zafi, da" ratsa fata a jikinsa. "Ya yinƙura zai tashi a gigice, amma yaji shi a ɗaɗɗaure, tamkar huhun goro." "Ya buɗe idanunsa da ƙyar cikin matsananciyar galabaita, amma ya kasa magana, haka zalika" wuyansa ya kasa tsayawa. """Idan ya watstsake, ku cigaba da tuhumarsa, har sai ya amsa laifin da bakinsa""" """Ok sir""" "Suka cigaba da kwara masa ruwa mai zafi, amma sai dai ya zabura ya ƙanƙame jikinsa, amma" babu baki. "Suka kwance shi daga mugun ɗaurin da suka yi masa, sai dai ana gama kwance shi, ya faɗo ƙasa" jikinsa a sake. "Ɗaya daga cikin su ya ce ""Haryanzu bai gama dawowa hayyacinsa ba, ku ƙyale shi tukuna""" "Indabo sai kaiwa yake yi, yana komowa a falonsa,ya rasa me ma yakamata yayi, gefensa ga P.A ga" kuma madaki a zaune. """Wallahi kayi mini hauka madaki, ni ban san zaka yi mini sakarcin ba. Bambancinka da Aminu kenan, abun da aka saka shi yake yi, idan ka ga ya canza, to ya hango abun da ya fi naka ne, yanzu" "idan ya farka ya tona mana asiri ya kenan?""" "P.A ya ce ""Honorable, ka kwantar da hankalinka C.P yana hanyar zuwa nan, zamu ji mai zai ce" "mana""" "Madaki ya ce ""Honorable, da ka san hatsarin da yake tattare da yaron nan, da baka ce haka ba, mugun shu'umi ne. Hodar nan da guba na haɗata, kisa take yi har lahira, nayi mamaki da aka ce" "bai mutu ba, ba laifina bane ba, nayi iya ƙoƙarina""." "CP ne yayi sallama, ya shigo falon, suka amsa tare da mayar da hankalinsu kansa, ya miƙa wa" "Indabo hannu suka gaisa. Cikin zaƙuwa indabo ya ce ""Yaya ake ciki C.P?""" """Eh to, maganar gaskiya fa ya farfaɗo, kuma yana daf da watstsakewa a ko wane lokaci. Abun da" "muka yi guda ɗaya ne, a report ɗinmu, mun shigar da cewa ya sha kayan maye ne, ya bugu ya halakka matarsa""." "Indabo yayi shiru sannan ya ce ""Kai naji daɗi, amma kamar hanyar ba tayi ba sosai, idan ya buɗe" "bakinsa, zai iya faɗar gaskiya fa""" "C.P ya ce ba zamu bari haka ta faru ba, lokacin da muka je gidan, mun goge duk wani abu da zai nuna hujjar wani ne ya shiga ya aikata laifin ba shi ba. Sannan mun ajiye miyagun ƙwayoyi har da hodar iblis, da sunan mun kama su a gidan. Idan za a fara sharia dole a samo ƙwararrun lauyoyi, kuma a yi wa alƙalin kyakykyawan gani, ni dai daga ɓangarena komai zai tafi dai-dai da" "yardar Allah. Tun da dama ya riga ya shahara kowa ya san ɗan daba ne""" "Indabo ya yi ajiyar zuciya ya ce ""Haka ne, na gode sosai da sosai C.P, zaka ga saƙo da yardar Allah, kuma zan cika alkawarin da nayi, muddin komai ya tafi cikin nasara, amma C.P ba zai yiwu" "ku yi masa wani abu, ku kashe shi ba kawai?""" "Ya ce ""No, muddin wani abu ya same shi, mu kuma zamu zama abun arziki, saboda sanarwar da" "kakinmu ya fitar mun tabattar da yana hannunmu cikin ƙoshin lafiya""" """Shikenan babu laifi, na gode sosai da sosai"" ya sallami C.P ya tafi, ya ce ""Aikin Naja'atu ya zo," "P.A kira wo mini ita""." *** """Ka yi magana ka amsa laifinka, ka sauƙaƙa mana kai ma ka sauƙaƙawa kanka, idan ba haka ba mu zamu bi hanyoyin da zasu sama mana sauƙi""" "Al'amin ya ɗago da kyar, saboda a cikin mayen da yake, suka yi dukan tsiya, tamkar sun samu" "jaki, jikinsa ya ƙara mutuwa, kowace gaɓa ta jikinsa ban da ciwo, babu abun da take yi." """Ka amsa, ka ce ka sha kayan maye ka kashe matarka""" "Gefen bakinsa duk jini, sun tuɓe shi, daga shi sai vest da gajeren wando, ya sake ɗaga idonsa," "karo na farko yayi magana ya ce ""Ina jauhar?""" """Ban sani ba, ni kake tambaya ina juahar? Bayan ka kasheta?"" Tsaki yayi, ya taƙarƙare ya yinƙura" "ya tashi tsaye, suka saka kokara suka daki ƙafafuwansa, ya hantsila ya faɗi a wurin." "Duk abun nan da ake yi, da jibgar da yake ci, shi kawai mafarki yake yi, jira yake yi ya farka, dan" "ba ya son baccinsa ya cigaba da nisa, zai kai Jauhar asibiti da wuri." "A haka aka shafe kwanaki bakwai, amma Al'amin, yaƙi sakawa ransa cewa gaske ne ba mafarki" ba. "Kwanaki bakwan nan, babu wanda ya zo in da yake, ba wai dan ba a samu masu zuwan ba, an" hana kowa ganinsa. "Liti da walid, da sauran jama'arsa babu irin sintirin da ba su yi ba, amma aka hana su ganin sa." "Mutuwar jauhar, ta karaɗe kowane gidan jarida, unguwanni zuwa gidaje." "Abbu yayi kuka tamkar zai yi hauka, yayi dana sanin kasancewar sa mahaifin Al'amin." "Gidansu jauhar kuwa, ba su san sun yi rashi ba, sai da aka tabbatar da mutuwar jauhar, kowa kuka" da zubar da hawaye. "Abbu yana kuka, ya sanya gwiwoyinsa a ƙasa, yana roƙon Baba ya yafe masa, da ya san Al'amin" "zai kashe masa 'ya, ba zai yarda a aura masa ita ba." "Baba ya girgiza kai ya ce ""Alhaji Ibrahim, ni wallahi haryanzu ban ji na yadda Al'amin zai kashe" "mini 'ya. Akwai abun da ya faru ni ban yadda shi ya kashe mini jauhar ba""" "Abbu ya ce ""Wace hujja kake nema ko shaida bayan wannan? Ni na haifi Al'amin, kuma kowa ya" "san yana ta'amalli da miyagun ƙwayoyi""" "Cikin kuka mama ta ce ""Yaron nan ya cuce mu, bai yi mana adalci ba, haihuwar ɗa irin jauhar a" "gidan nan, daga kanta an gama, ba ayi ba, kuma ba za ayi ba""" "Hafsa ta girgiza kai ta ce ""Baba nima ina bayan maganarka, ƴan kwanakin nan, ina zuwa gidanta sosai da sosai, ina haɗuwa da shi, ita take bani labarin galabar da ta ci a kansa, da bani misalai daban-daban da aurenta. Son da yake nuna mata a gabana ba ya jin kunyata ko nauyina, suna matu ƙar ƙaunar junansu. Har take gaya mini na tayata da addu'a, yanzu sigari ce kawai damuwarta da shi, har sai da na ji raina ya biya, da irin kalar soyayyar da suke yi wa junansu, dan haka gaskiya ban yadda mai zamani zai kashe jauhar ba, mutumin da idan zata fita baya nan, yake sawa ana bibiyarta dan kar wani ya kawo mata farmaki, mugwayen karnuka ya ajiye a layinsu, suna gadinta" "lokacin da yayi tafiya, duk dan kar a taɓa ta, gaskiya ban yadda ba""." "Anty ma tana kuka ta ce ""Babu abun da mai shaye-shaye ba zai iya aikatawa ba, dan haka ba abun" "mamaki bane dan an ce ya kasheta, Allah sarki jauhar wannan wane irin mummunan ƙarshe ki ka yi?""" "A fusace Saifu yana kuka ya ce ""Kar ki sake aibata mana gawar jauhar, wallahi ba ta yi mummunan ƙarshe ba, ta bi Allah, ta yi wa iyaye biyayya, ta yi biyayyar aure, idan ana nuna ɗan aljanna a duniya to jauhar ce, koma wane irin mutum ne shi, ai ku kuka yi bita da ƙullin da ta aure shi, kuma wallahi Allah ba zai bar kowane azzalumi ba, ita ta mutu ta huta"". Haka aka din ga" "musayar yawu, har sai da Baba ya tsawatar tukuna." "Da taimakon Naja'atu Bunkure, suka haɗa kai da lawyoyin gwamnati, Indabo ya cika su da kuɗi," har da alƙalin kansa. Domin tsayawa tsayin daka wurin tattara shaidu da hujjoji. "Haka zalika ta fito ta bayyanawa duniya cewa, zata tsaya tsayin daka, har sai ta ga abun da ya ture wa buzu naɗi, sai an bi wa jauhar hakkinta, na kisan gilla da viper ya yi wa jauhar, mussaman" dama ya riga yayi suna a harkar sha da fataucin miyagun ƙwayoyi da kuma harkar daba. "Ranar fara shari'a, haka aka zo da mai zamani a cikin sarƙa, yana ɗingisa ƙafa, saboda azabar da" "ya sha a hannun 'yan sanda, a kan ya amsa cewa shi ya kashe jauhar." "Aka fara gabatar da shari'a, wani lawyer ya gabatar da kansa a matsayin wanda zai kare Al'amin," "bai taɓa ganinsa ba, sai ranar a cikin kotun." Aka gabatar da charges ɗin da ake yi wa Al'amin. "Ɓangaren tawagar lauyoyin gwamanti, da su Naja bunkure, suka din ga gabatar da shaidun bogi," "suka kawo ƙwayoyin da suka samu a gidan Al'amin, tare da kawo bayanan likita, na cewa dukanta aka yi har ta kai ga rasa ranta, da abun da yake cikinta." "Abun bai tsaya a nan ba, sai da aka kawo malam lawan, bayan shaƙa masa wasu muhimman kuɗa" "ɗe, ya zo ya bayar da shaidar Al'amin ya saba dukan jauhar, idan ya je ya sha ya bugu, haka za su yi ta jiyo ihunta yana dukanta, a ranar ma sun ji kukanta, sai dai ba su yi zaton zai kasheta ba." "Muryar Liti ce ta dawo da Al'amin hayyacinsa, dan duk surutan da ake yi, bai san me ake cewa ba." """Ƙarya kake yi dan ubanka, Viper ba ya dukan yar madara, ba ita ba kowace mace ma baya duka, a matsayin ku na maƙota idan yana dukanta, meyasa baku kai wa yan sanda ba, ƙarya kake maƙiyin Allah la'ananne, Viper ba zai taɓa cutar da matarsa ba, ba shi ya kasheta ba"" jami'an tsaro suka yi" waje da liti. "Sai dai wani irin ihu da Viper yayi, sai da wasu suka fara gudu, ya daki katakon gabansa da ƙ" "afarsa ya ce ""Ƙarya ne, jauhar tana nan a raye, gobe zata haihu, matata bata mutu ba""" "Da ƙyar aka danne shi, Alƙali ya aika shi gidan prison, tare da ɗage shari'ar." "Haka ya cigaba da buge-buge, tamkar zai jefar da motar gidan yarin, sai da suka sumar da shi," sannan suka samu nutsuwa. "Tun daga wannan ihun, bai sake magana ba, ba cin abinci, sai dai zai yi salla kawai." "Har aka yi zama na biyu a kotu, bai ce uffan ba, duk wasu hujjoji Bunkure ce ta samar da su," lawyern gwamanti gabatarwa kawai yake yi. "Sai dai juyin duniya, ya yi magana, yaƙi yi." "Bunkure ta je gaban Al'amin ta tsaya ta ce ""Amsa ɗaya kawai kotu take buƙata daga bakinka, kai" "ka kashe matarka jauhar?""" "Ya ƙura mata rinannun idanunsa, ta din ga yi masa wani irin kallo, mai cike da rainin wayo." Ya jinjina mata kai alamar eh. "A nan suka buƙaci a ƙarƙare shari'ar, ba tare da wata huɓɓasa ba, lawyern Al'amin, ya ce ya yarda da duk abubuwan da masu gabatar da ƙara suka gabatar. Daga haka aka sake ɗaga shari'ar zuwa" wata guda. "Wata gudan da sai da ya shafe shekaru biyar a prison, ba a cigaba da shari'ar ba, ba kuma a" sallame shi ba. "Kullum burinsa shi ne ya farka daga mafarkin nan da yake yi, shi dai ya san matarsa na raye, ba ya" "cin abinci baya iya bacci, ya koma tamkar mahaukaci." "Sai dai lokaci zuwa lokaci yana yi musu ihu, da kiran matarsa, ya kan kira sunan madaki da" Indabo. "Lokaci lokaci, ya kan ga aiken abinci, hakan ya sanya ya ƙara sakankancewa jauhar ce ke yi masa" "aike, bai sake ganin wani yazo wurinsa ba, tsawon shekaru biyar ɗin nan." Rana tsaka aka ce masa ya fita ya tafi gida an sallame shi. "A ƙofar prison ɗin ya tsaya, yana tuna lokacin da ta zo tafiya da shi, lokacin da aka rufe shi, aka" ce an kama shi da cocaine. "Bai tsaya ko ina ba, sai unguwarsu, da ƙafa ya taka ya tafi, amma ya tarar da gate ɗin a rufe." "Sai yayi tunanin ta koma gida ne, dan haka sai ya fara tafiya gidansu, dan tabattar wa." "Gidansu ya fara zuwa, rahila da yaranta, gaba ɗaya suka dare, suka gudu ɗaki tana ihu ta ce ""Ka fita ka kore shi, gashi can an sako shi, Allah wadaran yan siyasa, sun sako masifa da annoba," "wanda bai san halacci ba""." "Abbu ya fito ya kalli Al'amin, ya koma kamar wani mahaukaci, a gigice ya nufo Abbu ya ce" """Abbu, ina jauhar? Ta haihu ne? Ina abun da ta haifa?""" "Abbu ya ja da baya ya ce ""Kar ka matso kusa da ni, Jauhar tana gidan uwarka da ubanka, dama ka gaya mini zaka kasheta, kuma ka cika alƙawarin ka Al'amin, na gode da muguwar sakayyar da ka yi mini, da ɓata mana sunan zuriya. Ka fita babu ni babu kai, ka nemi wani uban bani ba, na sallamawa duniya kai, ba zan cigaba da rasa makusantana, mutanen da nake ƙauna ba saboda kai," "ka je na yafeka a duniya""" """Na ji na yadda, amma ina jauhar? Sun ce idan na ba su abun da suke so, zasu kai ni in da take""" """Sai dai ka bita kabari ka ɗauki ɗan naka, mara mutunci, ka fita ka bar mini gida, bana ƙaunarka" "bana ƙaunar ganinka""" """Ba zai yiwu ba, wallahi sai kun fito mini da matata"" ya juya ya fita da gudu, ya tafi dabar su," incomplete building ɗin da suke zaman shaye-shaye. "Su Walid suna ganinsa, suka rirriƙe shi suna kuka, ya watsar da su ƙasa, ya ce ""Walid, ina jauhar?" "Na san ta haihu ko?""" "Walid ya tashi tsaye ya ce ""Viper ka nutsu mana, ya aka sako ka ne? Ba yadda bamu yi ba, a ƙ" "arasa shari'arka mu ɗaukaka ƙara aka ƙi""" """Dalla ina tambayar ku, ina jauhar, ko ta koma gidansu, ku bani kaya na canza na je wurinta, na" "san hanata ganina aka yi""" "Hawaye na zuba a idon liti ya ce ""Viper, Ƴar madara fa ba ta raye, ta rasu""" "Al'amin yana zuwa nan a maganar, yayi shiru, yayi fatali da kayan gabansa, ya fara wani irin haki," yana nema ya kurma ihu. "Nabila tana kuka, ta toshe masa baki tana girgiza masa kai." "Ya saka hannu, ya cire hannunta daga bakinsa ya ce ""Ban cancanci na haukace ba? Ban cancanci" "na nemi fansa ko ta wane hali ba kenan?""" "Nabila ta girgiza masa kai, kuka ya hanata magana." """Na kashe matata, ni na kashe jauhar ɗina, halittar da ta nuna mini tsantsar so da ƙauna""" """Ba kai ka kasheta ba""" "Cikin tsawa ya ce ""Ni ne, ni na kasheta. Meyasa da Abbu ya ce mini zai yi mini aure, na ce zan" "kasheta, ya ce mini Allah ya taimaka? Meyasa na kasa tuba na daina bangar siyasa da daba, a" "lokacin da zabra take ta ankarar da ni illarta, mai yasa sakamakon laifina ya faɗa kan matata?""" """Astagfirullah, Viper kar ka yi saɓo""" """Meyasa ban karɓi ƙaddarata ba tun da farko, na furta idan aka yi mini aure zan kasheta? Meyasa na jinkirta barin aikata laifi, sai da na rasa mutane masu muhimmanci a sanadin daba da shaye-shaye. Daba da bangar siyasa ta yi mini mummunan tabo, na kasa zubar da hawaye ko sau ɗaya tsawon shekarun nan, meyasa ba zan haukace na huta ba." "Ina son matata, laifina ya shafe ta, ba ta ji ba bata gani ba, na kasa yadda ta mutu, haryanzu ina ganinta ina ganin ɗana a jikinta. Ko ban ɗauki fansa ba, ina fatan na haukace, ko na bita na huta. Ina ma jauhar ba ta sanni ba, da yanzu tana nan tana rayuwa cikin farin ciki, bani da sa'a ko kaɗan" "a rayuwata, duk wanda na saka sonsa a raina, sai Daba da bangar siyasa tayi masa illa""" "Huci yake yi, idanunsa suka rine zuwa ja mai ban tsoro." "Ta sake mayar da hannunta bakinsa, ta rufe masa, tana kuka ta fara furta ""Innalillahi wa Innalillahi raji'un, Innalillahi wa Innalillahi raji'un, Innalillahi wa Innalillahi raji'un. Astagfirullah wa" "atubuilaihi""" "A hankali ya fara maimaitawa shi ma, jikinsa na kyarma, kamar wanda ake kaɗawa gangi." "Nabila ta ce ""Ka yi i ajiyar zuciyan da kake dannewa"" ya kama ɗaya hannun nata, ya ɗora saitin" "zuciyarsa, yana wani irin haki, wani irin bugu zuciyarsa take yi mai ban tsoro." "A take ya saki wata irin nannauyar ajiyar zuciya, tare da hawayen da suka maƙale a tsakiyar" zuciyarsa tsawon shekaru shida! Ayshercool 08081012143 ₦500 ne via 0009450228 Aisha Adam jaiz bank sai shaidar biya ta 08081012143 Wanda za su jira document 1K ne. 90009343 'Yan Nijar ku turo katin airtel na 300fcfa Arewabooks ayshercool7724 "Cikin matsanancin tashin hankali, Nabila tana kuka ta ce ""Viper zuciyarka fa, dan Allah ka nutsu zata daina aiki, idan ta cigaba da bugawa a haka, ka cigaba da istigfari da maimaita Innalillahi wa Innalillahi raji'un"" tayi maganar cikin damuwa, ƙara danna hannunta yayi a kan ƙirjinsa, yana" "wata irin shaƙuwa mai haɗe da haki, numfashin sa na fita sama-sama." A jejjere zuciyarsa take bugawa da ƙarfin gaske. "Cikin tausayawa take kallon sa, Al'amin yana buƙatar kafaɗar da zai kwanta yayi kuka, babu wanda ya fuskanci ainihin matsalar sa, kowa ɗora masa laifi kawai yake yi, iftila'in da ya faɗa masa, kowa ya dare ya bar shi, sai abokansa duk da suna iya ƙoƙarin su a kansa, amma ba abun" da yake buƙata suke yi masa ba. "Ji tayi ina ma tana da damar, da zata rungume shi, ta bashi dama yayi kuka yadda yake so, ko zai" "samu afuwa a zuciyarsa, tsawon shekaru shida, yana dakon baƙin ciki da damuwa, kuma ya kasa zubar da hawaye sai a wannan lokacin." "Haka yayi shiru ya sunkuyar da kai, sai dai bai saki hannunta ba, hawaye ne kawai yake zuba daga" "idonsa, taya shi take yi, sai dai ta rasa me ma zata kuma ce masa, a tsorace take da kar zuciyarsa ta buga." "A hankali ya saki hannunta, ya goge hawayen sa, ya tashi zumbur, ya tattare kayan ya mayar ɗ" "akin, hatta kayan jauhar suna nan, lokaci lokaci, su Walid ne ke zuwa su karkaɗe gidan su share, dan idan ya bushi iska yana zuwa cikin dare, yayi ta tuna irin rayuwar da suka yi." "Yanzun ma yana shiga ɗakin, ƙwaƙwalwarsa ta nuna masa ita zaune a kan gado, tana shirin dutse," "gefe ga boti a kusa da ita a kwance, ya mimmiƙe yana ta goge jikinsa." "Ta ɗago ta kalleshi tana murmushi ta ce ""Manya gatan wasa, me ake so ne ake ta kallona? Ko" "fankar ce?"" Tayi maganar tana kashe masa ido." "Gadon ya nufa da hanzari ya kai hannu ya riƙe ta, amma ya ga pillow ne kawai a wurin." "Ya dafe hannunsa a wurin, daga baya ya fito jiki a sanyaye ya ce ""Mu tafi"" Nabila ta saki niƙ" "abinta tana ta kuka, suka nufi hanyar fita, ya gyara facemask ɗin sa suka fita." "Yana fita yaga wasu daga magidantan layin, a ɗan tsaitsaye, suka yi ido huɗu da malam lawan, ya" "zura da gudu ya shige gidansa, ya rufe ƙofa." "Ya danƙi hannun Nabila ya din ga sauri da ita, maimakon su bi titi, lunguna suka din ga bi, suna" "tafe yana haki, yana dafe ƙirjinsa." "A dai-dai wata kan kwana, ya saki hannunta, ya danƙo wani mutum da yake zaune yana jin radiyo," "yana cin karas, zuwa wani lungu." "Nabila ta ce ""Me yayi maka shi kuma?""" "Ya zaro iraƙi a ƙugunsa, ya saita masa a maƙoshinsa, ya ce ""Bani wayarka""" "Jiki na rawa, ya ciro wayar, ya miƙa wa Viper." """Ka janye mini mutanenka, zan yi walƙiyya, idan ba haka ba, zan yi maka rami a maƙoshinka""" "Mutumin ya diririce, ya ce ""Ban gane me ka ke nufi ba""" "Ya ɗaga mutumin ya haɗa shi da bango da ƙarfi, ya ce ""Ka janye mini mutanenku zan tafi, idan" "na kuma magana, hanjinka zan naɗo da wuƙar nan""" "Mutumin ya ce ""Ya aka yi ka gane ni, ka san identity ɗina?""" """Saboda tsohon mai laifi ne ni, ba yau na fara aikata laifi ba"" yana ƙoƙarin zira hannu a aljihu" "Viper ya riga shi, ya ciro bindigar da take aljihun mutumin ya ce ""Ka yi abun da na ce, ko na harbe ka""" "A razane Nabila ta ce ""Viper bindiga ce fa, dan Allah kar ka yi wani laifin mu shiga uku"" bai" "kulata ba, ya sake saita mutumin da bindiga." "Ya saka wayar a kunnensa ya ce ""Zaku iya tafiya, we missed the target"" ya katse wayar ya ce ""Sai" "ka bani bindigata na tafi""" "Viper ya ce ""Ɗaga hannunka, ka wuce mu je"" ya tasa mutumin a gaba, tamkar ya kamo mai laifi, yana gana suna bin sa a baya, da ya motsa sai ya ji Viper ya ce ""Idan ka waiwayo zan fasa kanka" "da bindigar nan"" haka suka yi doguwar tafiya a haka, sai kuma ya ji shiru." "Ya waiwaya, ya neme su ya rasa, a rikice ya bi hanya, saboda bindigar sa da take hannun Viper." "Yana shan wata kwana, ya ga abokin aikins a tsaye da bindigar a hannunsa." """Gata, tun da ya ritsaka nake biye da ku, a hanya ya yar da ita, suka yi wani wurin, nayi ƙoƙarin" "bin su, amma ban cim musu ba""." """Ohh shit, meyasa ba ka yi making wani move ba, wannan ai shirme ne kayi""" """No, kar ka gargaɗe mu a kan haka, ka ce sai abun da ka ce, kai ka ke son ka kama shi da kanka""" "Ya fesar da iska ya ce ""Kuma haka ne, amma gayen nan ya bani mamaki, na rasa ya aka yi ya gane ni a cikin fararen kaya." "Kaga fuskarsa?""" """A'a sir, fuskarsa a rufe take ai, ban ganshi ba, ni bayansa ma kawai na gani""." """Na so naga kammaninsa, ko wataran zamu sake haɗuwa, suma informer's ɗin banzaye, da ba su" "sanar da wuri ba. Yi shiru ga oga Nasir yana kiran waya""" "Ya saka wayar a kunnensa ya ce ""Hello sir""" """Ya ake ciki ne?""" """We miss the target sir""" "Nasir ya ce ""Kamar yaya?""" """Kafin mu je, ya bar unguwar, bamu tarar da shi ba""" "Nasir ya numfasa ya ce ""Shikenan, ku dawo mu haɗu a office, sai mu sake shiri""" """Ok sir"" ya kalli abokin aikinsa ya ce ""Mu je,ya ce mu koma office""" "Viper kuwa wata hanyar ya bi, suka ɓulla can wata unguwar daban." "Sai dai suna tafe yana ta haki, yana haɗa hanya." """Viper mu tsaya ka huta, kalli halin da kake ciki, ko mu samu wani asibiti a duba ka, kar" "numfashinka ya ɗauke"" bai ko nuna ya san da shi take ba, sai da suka fita titi ya saki hannunta ya ce ""Ki koma gida""" "Cikin damuwa ta ce ""To kai kuma fa?""" """Ki tafi nace"" yayi maganar da kyar, kawai ya tare wani mai napep ya shige ya tafi." "Jiki a matuƙar sanyaye, ta koma chamber ta ɗauki motarta, ita kanta ta san ikon Allah ne ya kaita" "gida, amma kusan gaba ɗaya ba ta hayyacinta, tarin damuwa ce kawai cunkushe a ranta." "Ba ta san yar madara ba, ba ta taɓa ganinta ba, amma ƙarshen labarin ya tsaye mata a rai, da wayonta ba a taɓa yi mata mutuwar da ta gigita ta ta ji ta ba, sai dai jin wannan mutuwar ta gigita" "ta, ta ɗaga mata hankali. A cikin zuciyarta take jin ƙaunar matar da ba taɓa gani." "A wannan karon ma tayi kuka mai isarta, ga uwa uba, tausayin mai gayya mai aikn wato Al'amin, dan ita yar madara ta mutu ta huta, amma shi da blame ɗin ya dawo kansa, shi ne babban abun a tausayawa. Wayoyinta suka isheta da ringing, ta kashe su gaba ɗaya ta ajiye." "Ta din ga fatan Allah ya mayar da Viper maɓoyarsa lafiya, dan ta tsorata da mummunan yanayin" da ya shiga. "Sannan haryanzu labarinsa da saura, ba duka bane ba, amma tana fargabar sake matsa masa son jin" "ƙarashen labarin, dan gudun kar ya sake shiga mawuyacin hali kamar yau." "Tana ta saƙe-saƙe, sumayya ta yi sallama, ƙasa-ƙasa ta amsa, sumayya ta shiga ɗakin tana mita." """Malama kin ce mini zaki zo, amma kin shanya ni, bayanai ne suke ta fitowa a kan mutuniyar ki," "ina son ki gana da mutanen direct, na haɗa ku, amma ki ka ƙi zuwa""" "Ji tayi Nabila tayi mata shiru, ta ce ""Arfa meyafaru ne? Kamar kuka ki ka yi fa""" """Kuka nayi sumayya""" "Cikin rashin fahimta ta ce ""Kukan me kuma? Ko duk a kan shari'ar ne?""" """Sumayya komai ma, yakamata nayi kukan ne kawai""" """Arfa yakamata fa ace kin san kin girma, haba abu kaɗan sai kuka, ki din ga miƙa wa Allah" "lamuranki mana haba Arfa""." """Arfa, Arfa"" suka jiyo muryar Nasir yana ƙwala mata kira." "Tayi shiru bata amsa ba, ya shigo ɗakin, ya tarar da ita a zaune, ta jingina da gado." """Ina magana ki ka yi mini shiru?""" "Ta ce ""Kaina ne yake yi mini ciwo""" "Sumayya ta ce ""Yaya ina wuni?""" "Ya amsa da ""Lafiya ƙalau sumayya, ya aiki?""" """Alhamdilillah""" "Ya sake mayar da idonsa kan Nabila ya ce ""Waye mutumin da ya zo wurinki ɗazu a Office ɗin" "ki?""" "Ta ɓata fuska ta ce ""Na gaya maka client ɗina ne ai""" """A'a arfa, na tambayeki wani irin case ne zaki tsaya masa, kin ce is confidential ban san lokacin da muka fara ɓoyewa juna abun da ya shafe mu ya shafi aiki ba. Mutumin nan yayi kama da masu" "aikata miyagun laifuka, duk da ban ga fuskarsa ba""" "Ta girgiza kai ta ce ""Allah ya kiyashe ni hulɗa da masu aikata laifuka, sai dai ko da mai laifin ne, a matsayina na lawyer babu ruwana da laifin sa, zan bashi kariya ne kawai. A wurinku ne ku ke kama mai laifi, a wurin lawyer babu ruwansa da mai laifi ko akasin haka, client ɗinmu ne a" "gabanmu ba laifinsa ba""." "Ya tsaya yayi shiru yana kallonta ""Ban gane me ki ke nufi ba""" "Tayi murmushi ta ce ""Ba wani abu da nake nufi yaya, aikinku kamo mai laifi, mu kuma namu" "aikin binciko gaskiya komai ɗacinta""" "Ya jinjina kai ya ce ""I see, ɗazu informer's ɗin mu sun sanar da mu Viper ya je gidansa, da shi da wata da ba a san ko wacece ba, sai dai kan jami'anmu su je, ya bar unguwar"" duk da ƙirjinta yayi dumm. Amma cikin iya siyasa ta ce ""Ikon Allah, lallai wannan Viper akwai shu'umi, ya cika macijin gaske, wato lokacin da ya ga dama, sai ya baro raminsa ya fito shan iska, to Allah ya" "shirye shi. Amma ya batun abokinsa da kake bibiya?""" "Nasir ya ce ""Nothing much, ya daina zuwa unguwar ma kwata-kwata, abun har mamaki yake bani, da mun hari wani abu da muke son mu kama shi, sai abun ya kuɓuce mana, amma muna nan muna" "ƙoƙari""" "Nabila ta ce ""Gaskiya abun da mamaki, Allah ya yi jagora""" "Ya amsa da ""Amin, Sumayya ki din ga yi wa yar uwar nan taki faɗa, bata ji ko kaɗan tana neman" "zunguro mana sama da kara, kasadarta tayi yawa sosai""" "Sumayya ta ce ""Ana yi mata fa yaya, ka san halinta da kafiyar tsiya ne, amma zata daina in sha" "Allah""" "Ya jinjina kai ya ce ""Allah ya sa"" bayan ya fita Sumayya ta ce ""Arfa, waye yaya yake magana a" "kai, ina fatan dai ba wani mai laifin bane ba, ko kuma wani abun ki ke shirin ɗaukkowa ba""" "Nabila ta kalleta ido cikin ido ta ce ""Kina son na ce miki viper ne, ki je ki ji daɗin gaya wa waɗ" "anda ki ke ba wa information a kaina?""" "Gaban sumayya ya faɗi ta ce ""Information a kan ki kuma?""" """Eh mana sumayya, ana bibiyata ta hanyarki, kina bibiyar duk activities ɗina kina sanar musu. To ki gaya wa ko suwaye suka saki, wallahi babu yadda suka iya da ni, gaba da gaba za su yi da ni, su" "karɓi abun da suke so daga wurina, ba wai su fake da ke ba kina ba su information a kaina ba""" """Nabila waye ya gaya miki haka?""" "Nabila ta ce ""Jira ki ke yi a gaya mini? Ni na ganoki, sai dai na kasa yadda saboda ƙauna ba ƙ arya ce ba, kuma wanda ya gaya mini ba zai yi mini ƙarya ba, dan bai sanki ba, balle ya san alaƙ armu da ke. Please sumayya You can leave, ko ganinki ba na son yi wallahi"" Sumayya ta ce" """Nabila, ki tsaya mu fuskanci juna dan girman Allah""" """Babu wata fahimtar juna da ta rage tsakanina da mai fuska biyu, ni da gaske na yarda da ke, ba zan bari a cutar da ke ba, mussaman ayi amfani da ni a cutar da ke ba, amma ke gashi ana ƙoƙarin cutar da ni ta hanyar ki. Koma waye yake bibiyar tawa, ki ce masa ya fuskance ni ya gaya mini" "abun da nayi masa. Idan kuma a kan ayyukan da na saka a gaba ne, babu wani mahaluki da ya isa" "ya hana ni abun da nayi niyya, ki tashi ki tafi""" "Sumayya ta miƙe tsaye, kawai ta ɗauki jakarta ta fita, tana tafe a hanya tana kuka, sam ba ta san da wasu kalamai za ta yi amfani ba, wurin fahimtar da Nabila ba, sai dai tayi mamakin gaske, a kan wanda ya gaya wa Nabila cewa ana bibiyar ta, da Nasir ne ya gaya mata, to da tabbas sai yayi" "zancen yanzu a gabanta, kuma sai ya tuhume ta, amma sai dai bai yi hakan ba." "Bayan tafiyar sumayya kuwa, Nabila ƙanƙame pillownta tayi, tamkar ta samu viper, ta cigaba da" zubar da hawaye. "Viper kuwa a galabaice ya ƙarasa gidan da suke, gaba ɗaya nema yake ya fita hayyacinsa, haki" "kawai yake yi, zuciyarsa na cigaba da wannan matsanancin bugun." "Ɗan mama ne kawai a gidan, ya tashi ya riƙo Viper cikin tashin hankali, ya shiga da shi ɗaki, ya kwanta a kan katifarsa, ya cigaba da ajiyar zuciya, yana haki, ga wani abu da yaƙi gaba yaƙi baya" a tsakiyar ƙirjinsa. """Oga Viper, meyafaru ne? Baka da lafiya ne? Meyake damunka?"" Ya jejjerawa Viper tambayoyin," "amma babu guda ɗaya da ya iya amsa masa, ya lumshe idanunsa ya na ta sauke numfashi." "Cikin sauri, ɗan mama ya kira Walid a waya, ya sanar masa halin da Viper yake ciki." "Walid ya ce ""Ka kula da shi, kar ka bari ya sake fita, gani nan zuwa""" *** "Madaki ne zaune a cikin dokar daji, a gaban wani mutum da shi da yaronsa lakwari." "Ya miƙe ƙafarsa da ciwon jikinta yayi rami, mai zurfi, sai wani irin kore ruwa ne yake fitowa, wurin ciwon ya kumbura suntum babu kyawun gani ko kaɗan." "Mutumin ya ƙare wa ƙafar kallo sannan ya ce ""Ya riga ya yi maka illa, tabbas yana da makarin asirinka, dan kuwa ya karya shi ɓara, wuƙa da kaifi, za su din ga tasiri a jikinka. Cikin tashin hankali da damuwa madaki ya ce ""Yanzu babu wani abu da za ayi a kai, idan ya so a kuma bani" "wani asirin?""." """Gaskiya babu, yanzu dai magani zan baka, aje a haɗa shi da diddigar maƙera, ka yi kwana arba'in" "ana sakawa ciwon, sai ya warke sai kuma mu ga da abun da zamu ɗora""." "Madaki ya yi shiru, saboda baƙin ciki, lokacin da aka bashi asirin, an tabattar masa da babu wani wanda yake da laƙanin karyewar asirin, sai shi wanda ya bashin, wanda yanzu ya mutu sai ɗan sa yanzu dan kuwa shi kansa ɗan ma bai san makarin asirin ba, dan haka sun yi mamakin yadda aka" yi Viper ya samu. "Sun kamo hanyar dawowa kano, madaki ko iya magana baya yi, babu tunanin da yake yi, da ya" "wuce wani mataki zai ɗauka a kan Viper, dan kuwa karya asirin nan, dai-dai yake da karya" alkadarinsa baki ɗaya. "Kiran P.A ne ya din ga shigowa wayar Madaki, sai da yayi da gaske sannan ya ɗaga, domin kuwa gaba ɗaya ransa a jagule yake saboda tashin hankali, da fargabar halin da zai shiga, idan aka" fuskanci Alkadarinsa ya karye. """Madaki, ina ka shiga ne, yau kwanaki kusan huɗu wayarka ba ta shiga, distinguish ya bayar da" "muhimmin aiki da kai kaɗai ne zaka iya yin sa""" "Madaki ya yi ajiyar zuciya ya ce ""Aikin menene?""" """Idan kana gari ka shigo""" "Madaki ya ce ""A'a, na ɗan yi wani balaguro ne""" """Duk in da ka ke ka dawo, honorable ya matsa a kan lallai a kama viper, yarinyar nan yake so a ɗ" "aukko masa""" "Madaki ya ce ""Wace yarinyar kenan?""" """Wata lawyer ce, wadda na fara yi maka zancen nan""" "Madaki yayi wani huci, ya ce ""Bari na shigo garin, zan yi maka magana""" "P.A ya ce ""Wai madaki lafiya kuwa? Kamar ba ka da karsashi, meyake faruwa ne?""" """Basar ka ɗauke tunaninka a kan hakan, zan faso idan na shigo gari"" ya katse kiran yayi shiru yana tunani, tabbas ta bakin Al'amin daga lokacin da suka ga ya daina yi musu amfani zasu watsar" da shi. *** "Nabila ta kira layin Viper ya kai sau biyar, dan ta ji halin da yake ciki, amma ba a ɗagawa, har ta fitar da ran zai ɗaga ta ji an ɗaga wayar." """Haba master, ka barni cikin zullumi da tunanin halin da kake ciki, ka ƙi ɗaga wayata""." """Walid ne""" """Oga walid, yana ina dan Allah?""" """Gashi muna ta fama, jiki ya rikice gaba ɗaya""." "Cikin tashin hankali ta ce ""Innalillahi wa Innalillahi raji'un, wani abun ne ya same shi ne?""" """Ke zamu yi wa wannan tambayar, dan babu yadda bamu yi da shi ba, ya ce sai ya fita, wurinki zai" "zo, zai yi wani aiki, mun yi iya ƙoƙarin mu mu hana shi, amma ya ƙi saurarenmu, ko kin yi masa wani abu ne ki gaya mana dan Allah""" """Wallahi Allah kenan, ban yi masa komai ba, office ɗina ya zo ɗazu...." "Walid ya katseta ya ce ""Office kuma? Ya ce kiranki zai yi a waya ku haɗu""" """A'a zuwa yayi, yayi amfani da wayata da computer ta ta, daga nan ya ce zai ƙarasa mini labarin" "da ka fara bani, har gidansa muka je"" ta yi wa walid bayanin yadda aka yi." "Walid ya ce ""To ki tayamu addu'a, jiki ya rikice, ɗan sakewar da yayi kwana biyu, ta gushe ya" "koma yadda yake a da. Salla kawai yake yi a kwance tun da ya dawo, sai dafe ƙirjinsa yake yi yana haki""." """Innalillahi wa Innalillahi raji'un, Oga walid da ka ƙarasa mini labarin nan, duk da haka bata faru ba, da na san halin da zai shiga kenan, da ba zan takura masa ya gaya mini ba. Ubangiji Allah ya kawo masa mafita, Allah ya bashi lafiya, ba zai yiwu na fito yanzu ba, dan Allah ku kula da shi" "sosai. Zan zo in ga jikin nasa in sha Allah""" """Shikenan, Allah ya kawo ki"" ya kaste wayar, yana kallon in da Viper yake kwance, hannunsa ɗ" "aya a kan ƙirjinsa, yana ta sauke numfashi." *** "Duk wasu kalamai da Abdul yake tunanin idan yayi amfani da su, zai shawo kan ramma, yayi amma fafur taƙi saurarsa, ya kaɗa ya raya, amma taƙi saurarsa. Da ya addaba mata cikin tsawa ta ce ""Wai me kake so ne Abdul, ai ban yi zaton mugun zaluncinka ya kai haka ba, ka yi mini fyaɗe an ɗora wa mutanen da suka taimaka mini sharri, wannan wace irin rayuwa ce?""" "Ya sake kwantar murya ya ce ""Ki fahimce ni dan Allah, zan yi duk iya ƙoƙarina a kan mutumin" "nan ya fita a sake shi, dan Allah ki daina ɗaga hankalinki""" """Dama dole ka ce haka mana, tun da kana ganin ko ta halin ƙaƙa, kuɗi zasu ƙwatar maka komai," "baka tunanin mawuyacin halin da zaka jefa zukata, baka yi dacen hali ba ko kaɗan"" taƙi sauraronsa, sai uban miyagun maganganu da ta din ga yaɓa masa." *** "Bacci ya gagari idanun Nabila, ta ga tamkar an ƙara wa daren tsawo, gashi ta kasa bacci, ƙarshe ta tashi tayi alwala ta tayar da nafila." "A gaggauce ta hana baba magajiya aikinta, ana idar da sallar asuba, ta shiga kitchen ta dafa abun" "da take buƙata, da duku-duku, ta ɗauki motarta ta fita." "Jin ƙarar mota ya sanya Nasir ɗaga labulensa ya duba, ya ga babu motarta, ya kalli agogo, hari" "sam bai gama waye ba, ya fara tambayar kansa ina tafi da wannan duku-dukun?." "Gudu ta din ga yi a titi, gani take yi tamkar kafin taje, wani abun ya same shi." "Gari yayi haske sosai tana hanya, ta ajiye motarta a wani wuri, ta fito ta tsaya ko zata samu abun hawa, amma bata samu ba, dan haka ta cigaba da tafiya da ƙafa, gabanta na ta tsananta faɗuwa sai" addu'a take yi. "Ta sha tafiya sosai, sannan ta samu abun hawa ta hau, ya ƙarasa da ita." "Kasancewar da tafiya daga titi zuwa gidan da yake, haka ta din ga haɗawa har da gudu, har ta ƙ" "arasa tana ta haki, ta shiga da sallama, ta ƙarasa ƙofar ɗakin, ɗan mama ta hango zaune a gaban Viper, yana ta rarraba ido, daga shi sai shi a gidan." "Ƙwayoyi ne a hannun Al'amin, gefe ga allura a cikin sirinji, amma sai haki yake yi mai ban tsoro." "Da sauri ta ƙarasa ɗakin, tana cewa ""Wannan ƙwayoyin na menene?""" "Kafin ta ƙarasa ya watsa su a bakinsa, babu ruwa yake ƙoƙarin haɗiyewa, ba ta san lokacin da" "cikin tsawa ta ce ""Viper meye haka? Ƙwayoyin meye wannan kashe kanka ka ke son ka yi?""" "Bai kulata ba, ya cigaba da ƙoƙarin haɗiyewa, sai dai ya kasa saboda abun da yake ji ya tokare" masa a wuyansa zuwa ƙirjinsa. "Matse bakinsa tayi iya ƙarfinta, tana girgiza masa kai ""Kar ka haɗiye, wallahi hakan ba mafita ba" "ce ba, dan girman Allah ka zubo su daga bakinka"" hankaɗeta yayi yana ta huci." "Ɗan mama ya ce ""Ki daina zuwa in da yake, zai yi miki illa, wallahi aiken su Walid yayi, ni kuma yayi mini barazana da wuƙa, na samo masa kuma wanda ya watsa a bakinsa sun yi yawa, sun yi" "masa ƙarfi""" """To waye ce ka kawo masa, ba sai ka gaya wa Oga walid ba, ai ka san ba zai taɓa iya kisan kai ba""" "Ta sake tunkarar Viper, sai haki yake yi mai haɗe da huci, tamkar kumurcin, yana motsa bakinsa a" "hankali, yana son haɗiye ƙwayoyin." "Bakinsa ta sake matsewa, idanunsa sai buɗewa suke yi suna lumshewa, wanda suka fara narkewa" "a bakinsa, sun fara rikita masa lissafi." """Kalleni nan, ka fito da su na ce"" tayi maganar tana zare masa ido." "Ya ɗago a hankali ya kalleta, ta ce ""Ka zubo da su, kar ka haɗiye. So kake ka kashe kanka, idan" "ka kashe kanka, ɗan wuta zaka mutu, kuma ko ka je lahira ka mutu ɗan wuta, yar madara kuwa muna saka mata ran tana aljanna, kaga ba zaka ganta ba""" "A galabice, ya buɗe bakinsa, yana zubo da ƙwayoyin da suka rage a bakinsa, yana ta haki." "Shammatarta yayi, ya ɗauki sirinjin da yake gefensa, ya caka mata a hannunta, wata irin ƙara tayi," "cikin razani, dan ba ta yi tsammanin hakan ba." "Ɗan mama ya rikice, ya nufo su da sauri, Viper ya kalli in da ya caka mata sirinjin, ya kalli" "fuskarta yadda ta fara kuka, sai kuma ya ankare da abun da yayi." "Sai ya rikice, ya zare sirinjin ya jefar ya riƙeta ya ce ""Zahra, me nayi miki? Yi haƙuri, na daina shan komai, ai nayi miki alƙawari"" yayi maganar yana ƙoƙarin kai hannunsa fuskarta, ya share" mata hawaye. "Walid ne suka shigo tare da liti, suka nufo su, liti ce wa yake ""Me ki ka yi masa?""" "Viper ya yinƙura ya tashi, amma ya yanke jiki ya faɗi." "Suka rufu a kansa, suka ɗaga shi da kyar, Nabila ta gaya wa Walid a halin da ta zo ta same shi." "Walid ya kalli ɗan mama, cikin tsananin ɓacin rai, ɗan mama ya ce ""Nifa bani na kawo masa ba," "wallahi ɗaukko masa kawai ya saka nayi, ban san a ina ya samo abun sa ba""" "Suka mayar da hankali a kan Viper, sai dai ba maye kawai yake yi ba, suma yayi, ga numfashinsa" iya ƙirjinsa yake. "Nabila ta ce ""Dole fa a kai shi asibiti, ko da hakan yana nufin a kama mu ne baki ɗaya, lafiyar sa" "ita ce mafi muhimmanci a wannan lokacin""" "Walid ya ce ""Haka ne, amma wani asibiti zamu kai shi?""" "Liti ya ce ""Akwai wani asibiti a can bayan gari sosai, sai dai na kuɗi ne, ina ga kamar can zai fi" "zama safe""" "Nabila ta basu mukullin motarta, ta gaya musu a in da take." Liti ya karɓa ya tashi ya fita. "Nabila kallonsa take cike da tausayawa, namijin gaske ne, sai dai ta wata fuskar yana da raunin" zuciya sosai. "Da liti ya kawo motar, suka yi kama kama, suka ɗauke shi, suka shafo tafiyar nan da shi, suka fito" titi. "Liti ne yake jan su a motar, ɗan mama da Viper da walid suna baya." "Asibiti ne mai kyau, sai dai ya yi nisa da gari sosai da sosai." "Ganin halin da yake ciki yasa suka karɓe shi da gaggawa, Nabila ta tambayi ya tsarin Asibitin yake, da payment ɗin, aka ce su bari, a fara ceto ransa tukuna." "Da aka tambayi sunan Al'amin, sai Walid ya ce ""A saka masa Muhammad Nura""" "Liti ya ce ""Meyasa baka bayar da normal sunansa ba""" "Ya bashi amsa da ""Saboda tsaro""" "A kan oxygen aka fara ɗora shi, saboda numfashinsa, sannan aka fara sauran ƙoƙari a kansa." "Walid kallonta kawai yake yi, yadda take a rikice cike da tashin hankali, babu ma alamar tana" "fargabar a kamata ko wani ya ganshi, ta uzzurawa likita da tambayoyi." "Likitan yayi mata bayanin yadda Jinin Al'amin ya hau, ga bugun da zuciyar sa take yi, fiye da" "kima kamar yadda ECG ɗin sa ya nuna, he's at very risk of having heart attack." """Subhanallah, dan Allah doctor kayi ƙoƙarin ka, na san Allah ne mai komai, amma dan Allah ka" "taimaka""" """In sha Allah zamu yi iya a ƙoƙarin mu a kai""" "Tayi masa godiya, ta tafi reception ita da litu, suka gaisa da cashier ta tambayi, me za su yi" "depositing, na patient ɗin su da aka yi admitting?." "Ya tambayi sunan mara lafiyan, liti ya gaya masa, ya duba cikin system ɗin gabansa ya kalle su ya" "ce ""Ai an biya""" "Suka kalli juna da ita da liti, liti ya ce ""Malam ka duba sosai, ɗazu muka shigo fa, aka ce mu bari" "a fara bashi taimakon gaggawa, ka duba ko masu irin sunan biyu ne""." """Shikaɗai ne me irin sunan da aka yi admitting yau, Al'amin Ibrahim""" "Suka kalli juna da Nabila, liti ya ce ""Mu sunan mara lafiyanmu Muhammad Nura""" """Wanda ya biya kuɗin, sunan da ya bamu kenan, ba shi ne na ɗaki mai lamba 2 ba? Al'amin" "Ibrahim ya ce mana, ya turo kuɗi ya ce ayi masa duk abun da yakamata""." Ayshercool 08081012143 ₦500 ne via 0009450228 Aisha Adam jaiz bank sai shaidar biya ta 08081012143 Wanda za su jira document 1K ne. 90009343 'Yan Nijar ku turo katin airtel na 300fcfa Arewabooks ayshercool7724 "Nabila ta ce ""Malam ya za ayi mu kawo mara lafiya, mu zo kuma ace mana wani ya biya kuɗ" "inmu, dama haka ake yi, wannan wane irin abu ne, ka gaya mana bills ɗinmu mu biya, mu bamu san kowa ba""" "Ya girgiza mata kai ya ce ""No ma, ba zan karɓi kuɗinku ba, na gaya miki an riga an biya""" """Waye ya biya?""" "Liti ya ce ""Kai bana son nuƙu-nuƙu, wanene ya biya kuɗin?""" """Nima ban sani ba, management ne suka turo mini receipt, aka ce kar mu karɓi kuɗinku, an yi" "settling bills ɗin""" "Nabila ta ce ""Suwaye management ɗin?"" Yayi shiru yana kallonta." """Malam kayi mini magana, ka tsare ni da ido, suwaye management ɗin? Suwaye suka biya kuɗ" "in?""" "Liti ya ce ""Ki yi magana a hankali, kar ki janyo hankalin mutane kanmu""" "Tayi ajiyar zuciya ta ce ""Ana bibiyarmu, wanda yake wannan abubuwan ya san duk wani motsi da" "muke yi""" "Liti ya jinjina kai ya ce ""Nima nayi wannan tunanin""" "Nabila ta ce ""Mu koma wurinsa, kafin mu san abun yi"" suka koma in da suka baro Al'amin da" walid da ɗan mama. "Walid na ganin su ya ce ""Yaya? Nawa ne kuɗin?""" "Nabila ta ce ""Kar ka damu, an biya""" "Tayi maganar tana zama a gefen Viper, ta tsurawa fuskarsa ido, kawai tuno yadda ya din ga kuka" "ta din ga yi, gaba ɗaya jikinta ya ƙara sanyi." "Walid ya ce ""Ba zaki ga likita ba, wurin da ya caka miki allura?""" "Ta girgiza kai ta ce ""Bakomai, ni yanzu ta lafiyarsa nake yi""" """Amma yakamata ki koma wurin aiki fa, ai muna tare muna kula da shi""" """No, ko na tafi hankalina ba zai kwanta ba, ba zan iya aikin ba, bari na jira naga abun da hali zai" "yi""" "Likita ya sake shigowa, yana duba Al'amin." "Ya ce ""Alhamdilillah, ina ga ya samu bacci, dan ya farfaɗo daga suman""" "Nabila ta ce ""Masha Allah"" ji tayi ya taɓa hannunta, ta kalli hannunsa, ya yi mata alama ta matso." "Ta matsa ta kai kunnenta saitin bakinsa, a hankali ya ce ""Ki gaya masa a cire mini wannan abun na" "hancina bana so""." """Haba master, baka ga yadda kake numfashi da kyar bane ba? Dan ya taimaka maka aka saka" "maka shi, dan Allah ka yi haƙuri ka ji, Allah ya baka lafiya""" "Ya sake cewa ""Ki ce musu bana iya bacci, yayi mini abun da zan yi bacci, kaina zai tarwatse""ta ɗ" "ago ta kalli likitan ta ce ""Doctor, ya ce dan Allah ayi masa allurar bacci, so yake yayi bacci baya iya bacci""" "Likitan ya ce ""Ai mun yi masa, kuma da jinin ya sauka zak yi bacci mai yawa mai daɗi in sha" "Allah""" "Ta sake sunkuyawa, zata yi masa magana ya ce ""Bana son baccin, ba na son jinin ya sauka, bani" "da rabon sake yin su, Allah ya nuna mini ranar da zan bi matata""" "Babu wanda yake iya jin abun da yake faɗa, sai ita, muryarta na rawa take yi masa magana a" hankali cikin nutsuwa. """Haba Al'amin, mai babban suna, shikenan bawa ba zai yi imani da ƙaddara ba, tun da ka fuskanci kurakuran da ka yi a baya, ba sai mu nutsu mu nemi mafita ba, yanzu idan ka mutu maƙ iyanka sun ci galaba a kanka kenan fa." "Dan Allah ina roƙonka ka janye wannan fatan da ka ke yi, kuma in dai muna tare in sha Allah zaka yi bacci mai daɗi mai cike da nutsuwa da kwanciyar hankali trust me." "Wallahi i feel your pain, bani na tsinci kaina a halin da ka ke ciki ba, but ina jin zafi a zuciyata, in sha Allah you won't cry alone, an cutar da kai, in sha Allah kuma sai in da ƙarfina ya ƙare a kan ƙwato maka hakkinka, in sha Allah sai nayi sanadin dawo da farincikin ka." "Amma sai ka yi haƙuri, ka yi haƙuri, kayi haƙuri na san da wahala, da ciwo, an yi maka illa, amma" "ina roƙonka a wannan karon kar ka jinkirta tuba, mu yi ta addu'a, Allah ya taimake mu, ka kwantar da hankalinka ka yi haƙuri, Allah da kansa ya rarrashi masu haƙuri a cikin Alqur'ani""" "Yayi shiru yana sauraren Nabila, hawaye yana bin gefen fuskarsa." """Madam ya kuma kike kuka, mu da muke son hankalinsa ya kwanta, jininsa ya sauka?""" "Liti ya ce ""Rabu da shi doctor, kukan shi ne samun afuwarsa, mun gode sosai da ƙoƙarin ku." "Cikin kalaman hikima, da tausasawa, ta cigaba da yi wa Viper nasiha, tare da bashi ƙwarin gwiwa," "a kan cigaba da haƙuri, da kuma Addu'a." "Har bayan azahar, Viper bai gama frafaɗowa ba, haka Nabila ta haƙura ta tafi gida, bayan ta ajiye" musu abincin da ta zo da shi. "Sai magariba ta isa gida, Allah ya sa Abba baya nan, balle ta sha tuhuma." "Message ne ya shigo wayarta, ta ɗauka ta duba." """Arfa dan Allah kar ki yi mini mummunar fassara, ki tsaya ki saurare ni mu yi magana, kin ƙi ɗ" "aga wayata, hankalina a tashe yake, amma ki bani dama nayi miki bayani, dan girman Allah""" "Har jikin Nabila yayi sanyi, kamar ta yarda da maganar Sumayya, sai kuma ta fasa, tayi mata reply da ""No peace for wicked person, kar ki sake tunanin zan yarda da maganarki"" ta saka lambar a" "busy, ta cigaba da sabgar gabanta." "Ta idar da sallar isha'i, tana zaune tana cin abinci, kawai Nasir ya faɗo ɗakin, babu ko sallama. Ta" "ɗaga kai ta kalle shi, amma bata ce masa uffan ba." """Arfa""" """Na'am yaya""" """Ina ki ka je yau?"" Ta ɗaga ido ta kalleshi ta ce ""Meyasa kake tambayata?""" """Ki bani amsa kawai""" "Cikin ko in kula ta ce ""Wurin aiki""" """Ƙarya ki ke yi, me ya kai motarki hanyar ungoggo?""" "Ta ajiye cokalin ta ce ""Haba DSP, mutum nawa ne suke da vibe a birnin kano?""" """Ya ina magana kina nema ki raina mini hankali, wurin aikinki an ce baki je ba""" """Amma yaya ka san aikina ba na zama wuri ɗaya bane ba, yaya ka ke yi mini tmbaya kamar ka" "ritsa ƴar ta'adda ne? Wataƙila harkar aiki ne ta kaini wurin, bibiyata kake yi kenan? Ko kuwa" "meyafaru ko rashin yadda ya shiga tsakaninmu ne?""" "Ya sauke numfashi ya ce ""Gaba ɗaya kwanan nan kin canza Arfa, na je Division ɗin ungoggo kan" "wani case, a hanya na ga motarki, dan lambar motarki ce""" """Abokin aikina ne ya ari motar, suka fita, ta sa ta samu matsala. Sannan kuma ni ban canza ba, kai ne dai ka canza mini kwanan nan, ni ban san me nayi maka ba, duk ka tsane ni, ka daina goyon bayan gaskiya, ni na fara tsoron ko kaima ka fara karɓar cin hanci"" tayi maganar tana ƙaƙalo" kukan kissa. "Sai kuma ya kwantar da murya ya ce ""No ki fahimce ni, ke ɗin ce yanzu dole sai ana saka miki" "ido, kar wani abun cutarwa ya samar mini ke, ki yi haƙuri ki daina kuka"" a haka ya ɓuge da rarrashin ta, ta nuna masa komai ya wuce, yana fita tayi masa gwalo, tare da ajiyar zuciya." "Ta ɗaukko wayarta ta ce ""Bari na kira na ji ya jikin ɗan marayan zakina"" sai dai wayarsa a kashe," haka ta haƙura. *** "Gaba ɗaya ramma ta fita daga harkar Abdul, abun duniya ya addabe shi, gashi ya kasa gano in da mahaifiyar ta take, babban tashin hankalinsa kar ta gano cewar mahafiyarta ta ɓata. Dan bai san wane irin kalar bori zata yi masa ba." "Ga Indabo ya uzzura masa, dan har an kai masa kuɗin aure, ga shirye shiryen takararsa na ta ƙara yin nisa, amma gaba ɗaya hankalinsa baya kan takarar. Abokansa sai mita suke yi masa a kan duk ya canza, ga aurensa an saka su fara shiri, amma ya kasa mayar da hankali a kai, sun kasa gane kansa gaba ɗaya." Babu wanda ya tsaya saurara da bashi amsa a kan surutun da yake yi. "Yana zaune yana kallo, amma hankalinsa ba a kan kallon yake ba, tunani kawai yake yi." "Ramma ta ƙaraso kansa ta tsaya, ya ɗaga kai ya kalleta, ya tashi zaune sosai ya ce ""Rahama, ya" "aka yi ne?""" "Ta ƙaraso ta durƙusa a kan gwiwoyinta, hawaye na bin fuskarta ta ce ""Abdul yasar, dan son da kake yi wa Allah da annabinsa, ka mayar da ni gaban mahaifiyata, naga message a notification ɗ in ka, wai aure zaka yi, dan girman Allah ka mayar da ni wurin uwata da ɗan uwana, na yadda zan ƙarasa rayuwata, a rushen zan tattara ta na rayu, ba ma na saka ran zan zan yi aure, na yarda na" "rayu a haka""" "Ya kalli ramma ya ce ""Daga ganin message sai ki ce aure zan yi? Bincike ki ke yi mini kenan? To" "ni ba wani aure da zan yi ""." "Cikin kuka ta ce ""Ka daina yaudarata Abdul, ka rabu da ni, idan kana son iyayenka, na gaji, na gaji" "na gaji da haƙuri, da fatan zaka mayar da ni gida, ka ƙyaleni dan girman Allah, ai ka gama morar" "abun da kake so zuwa yanzu, kowace irin ƙishirwa ce ka kasheta zuwa yanzu ka rabu da ni dan" "Allah "" tayi maganar cikin ɗaga murya." "Abdul ya kalleta a tsanake ya ce ""Kin manta alƙawarin da ki ka yi mini ne?""" """Babu wani alƙawari da nayi maka, ni ban san wani alƙawari ba, ka mayar da ni gida""" """Wallahi ƙarya ki ke yi ki rusa maganar da muka yi da ke, da alƙawarin da ki ka yi mini""" """Ka yi mini duk abun da ka ga dama, amma ni dai ka sakeni na koma gida, idan duk matan duniya ne ka je ka aura, ban damu ba, amma a yanzu tun da dai ka gama da rayuwata dan Allah ka rabu" "da ni""" "Abdul ya tsura mata ido, yadda take kuka wiwi har da majina." "Ya saukko daga kan kujerar, ya zauna a gabanta ya ce ""Rahama kishina fa ki ke yi""" "Kamar zata kai masa mari ta ce ""Ƙarya ne, Allah ya kiyayeni ya tsare ni da kishin ƙazamar halitta" "mara tsoron Allah kamar ka, ni kishin rayuwata nake yi""" "Ya sauke numfashi ya ce ""Zan mayar da ke, amma sai kin cika mini alƙawarina, sannan kin haifa mini ɗa sannan zaki koma gida, kin ga idan kika haihu duk duniya babu wanda ya isa ya raba ni" "da ke"" yayi maganar yana share mata hawaye." """Abdul ba zan taɓa yafe maka ba, na bar ka da Allah""" """Duk cikin kishina ne, matsayin matar da zan aura daban, naki ma daban, you are like my guest" "house, wurin hutawa ta da nishaɗina""" "Jiki a sanyaye ta ce ""Ka cuce ni Abdul, duk saboda ina 'yar talakan ƙauye, mara gata mara galihu""" "Ya girgiza mata kai, ya haɗe bakinsa sa nata, wata irin ajiyar zuciya take yi, a hankali ya cire bakinsa daga nata, ya kalli idanunta ya ce ""Iya wuya rahama, ina tare da ke, ban ga wanda ya isa ya raba ni da ke ba. A lokacin da maza da yawa suke gudun matan da suka lalata, ni a dai-dai" "lokacin soyayyar yarinyar da na lalatawa rayuwa ta yi mini kamun kazar kuku""." "Jiki babu ƙwari ta cw ""A hakan? Wace irin soyyaya ce zaka yanke mini farincikina ba tare da" "wani dalili ba, bana sonka Abdul ko kaɗan""" """Ki saurari zuciyarki, kina jin zafin abun da nayi miki ne kawai, amma kina so na rahama, nima" "kuma ina matuƙar sonki""" """Da ban yi wa kaina, da mahaifiyata adalci ba, idan na fara sonka Abdul yasar""" """Zuciyar ki, cike da ƙuruciya, kina ƙoƙarin sakawa kanki ƙiyayyata ne ta ƙarfin tsiya ne""." """Wallahi wannan ba so bane, ka gama lalata ni, ka samu abun da kake so, kuma ka ce sona kake," "me yayi saura?""" """Kin san abun da na ɗauko ki ki yi mini, kuma na daina kamar yadda ki ka buƙata. Wuri ɗaya nake kwana da ke nake tashi, amma na daure, ban sake yi miki ba, kuma na lazumci istigfari kamar yadda ki ka gaya mini. Kar ki saɓa alƙawarinmu mana. Wa ki ka taɓa ganin ya lalata yarinya ya bita kuma yana so? Ke kin san waye ni a garin nan da ƙasar nan. Na fiki shekaru, da ilimi da tarin dukiya, amma gaba ɗaya na bar abun da yake gabana na tattara hankalina a kanki, ki yafe mini mana sweetheart, ki yarda ki so ni, zan goge laifukana zan kuma mayar da ke wurin" "mama in sha Allah""" """To yaushe?""" """Very soon, da zarar kin yafe mini, kuma kin cika mini alƙawari""" "Ramma ta share hawayenta ta ce ""Abdul ta yaya zan haihu da kai, in kalli duniya in ce musu me?" "Baga mata nan zaka aura ba, ba sai ku haihu ba?""" """Naki nake so please"" yayi maganar yana sumbatar goshinta, cikin tsananin so da shauƙinta." *** "Yau ma uban sammako Nabila ta yi, ta tafi asibitin da Viper yake, sai dai ba ta ɗauki motarta ba." "Yanzu ma ɗan mama ta tarar, yana ta sharar uban bacci, babu liti babu Walid." "Viper kuma yana zaune, ya jingina da bango idanunsa a lumshe." "Murmushi tayi, tare da farin cikin ganinsa a zaune." "Ta ƙarasa ta zauna ta ce ""Yallaɓai, good morning, ya jiki? Alhamdilillah na ji daɗin ganinka a" "zaune"" sai dai kamar mai bacci, bai buɗe idonsa ba." "Hannunsa ta kalla, ɗaya da drip, ɗaya kuma kamar lazumi yake yi. Wani irin farinciki ya kama" Nabila. "Wani baƙin abu ta hanga, a gefen pillown sa, ta saka hannu ta janyo, ta ce ""Menene wannan, ko" "kayan da zaka canza ne?"" Tayi maganar tana buɗewa." """Wannan rigarka ce?"" Buɗe idonsa yayi ya kalleta, cikin wani irin zafin nama ya fizge rigar daga" "hannunta, ya hau waige-waige." "Ta ce ""Menene? Meyafaru?""" "Ya kalli in da ɗan mama ya saki baki yana bacci, ya kalli taga babu hanyar shiga ko fita ta tagar," ya sake ɗaga rigar. "Baƙar riga ce shirt, mai ɗauke da hoton tambarin dragon a gefen rigar, bayanta kuma an rubuta" "wasu alphabets, da bai bar Nabila ta karanta ba. Duk da jikinsa babu ƙwari haka ya saka ƙarfin sa, ya yayyaga rigar, yana cigaba da waige-waige." "Cikin rashin fahimta ta ce ""Wai me yake faruwa ne?"" Ya girgiza mata kai, ya sake jingina." "Nabila ta kalle shi ta ce ""Akwai damuwa fa, jiya an yi settling bills ɗin ka, sai dai bamu san waye" "ba, an ƙi gaya mana ko wanene"" ya ƙura mata ido, ta jinjina masa kai, alamar da gaske take." """Dan Allah ka gaya mini, menene yake faruwa ne, bai kamata ka ɓoye mini komai ba, tare fa" "zamu yi gwagwarmayar nan"" Sai ya lumshe idanunsa ma, yaƙi kulata." """Haba master, yar suganka ce fa, talk mana"" a hankali ya fara kaɗa ƙafa, amma bai yi magana ba." """Sweetheart"" ta faɗa tana dariya ƙasa-ƙasa." """Sweetheart magana nake fa"" sai ya kwanta ya juya mata baya baki ɗaya." """Am sorry wasa fa nake yi maka, ya ƙarfin jikinka to, ina fatan akwai progress, kana samun sauƙ" "i?""" "Ya girgiza kansa alamar ""A'a""" "Ta ce ""Ohh ni Nabila ina ganin mulki yau, Allah dai ya jaddada rahama da Fatima jauhar, ta yi ƙo" "ƙari sosai""" "Ya ce ""Amin"" tausayin sa ne ya sake kama ta, ta ce ""To tashi ka karya, na san yanzu za a zo yi" "maka allurai, kuma na san kana jin yunwa""" "Bai yi magana ba liti ya shigo da leda a hannunsa, ya kalli ɗan mama da yake ta bacci, ya dake shi" "da ƙafarsa ya ce ""Tashi, ɗan asara, idan ma sace shi za ayi, kana kwance ka shanya baki kamar fatarin mata kana bacci"" ɗan mama ya tashi yana mutsutsuka ido." "Jauhar ta kalleshi ta ce ""Ina kwana?""" "Ciki ciki ya amsa, ya dafa Viper ya ce ""Maza ya ne, ya jikin?""" """Alhamdilillah""" """To masha Allah, ga brush ɗin da toothpaste, ka wanke bakin, yanzu Walid zai kawo abinci, sai ka" "yi wanka ka canza kaya""" "Ya yinƙura ya tashi zaune, ya ƙurawa ɗan mama ido, sannan ya ce ""Kai waye ya shigo ɗakin nan" "jiya da daddare?""" """Likita ne, sai mai bada magani Nurse, sukenan""" """Ƙarya kake yi""" "Ɗan mama ya ce ""Wallahi sukaɗai na gani""" "Liti ya ce ""Dama ya kwanta yana ta uban bacci, ya za ayi ya san me ake yi? Ina fatan ba wani" "abun ne ya faru ba?""" """Babu komai""" "Da Al'amin ya shiga banɗaki, sai Nabila ta fita tana waya da barrister Habib, ya ce lallai yana son" "ganinta, Sumayya T ladan ta turo wasu mata, kuma zasu taimakawa aikinta a kan bunkure." "Nabila ta yamutsa fuska ta ce ""Ka sallame su kawai, babu buƙatar na gansu""" """Kamar yaya, abu mai muhimmanci da ki ke nema, ki ce a sallame su""" """To ai nayi nisa ne, yaushe na bar abun da nake yi na zo""" """Ki bari koma menene ki taho yanzun nan"" to kawai ta ce masa, ta ajiye wayar." "Ta cikin niƙabinta, take ƙarewa asibitin kallo, wurin cashier ta sake zuwa, sai dai yau wata mace" "ce. Suka gaisa Nabila tayi mata bayanin abun da ya faru jiya, ta buƙaci ta dubo receipt ɗin da aka turo musu na biyan kuɗin, ta ciro ta bata." "Ta shiga computer ta duba, ta kalli Nabila ta ce ""Ban ga receipt ba, kawai an saka bill settled""" """Ina ne ofishin MD, ko admin na asibitin nan, dole fa a nemo wanda ya biya kuɗin nan""" "Ta ce ""Ba sa shigowa da wuri, amma maybe zuwa anjima""" Nabila ta juya ta koma ɗakin Viper. Ya canza kaya ya zauna a kan gadonsa. "Har walid ma ya zo, ya buɗe masa wainar shinkafa ta sha ƙuli-ƙuli, yana lallaɓa shi ya ci." """Barrister har kin zo ashe?""" "Ta ce ""Eh oga Walid, na zo tun ɗazu, naje likita ya duba ni, allurar da master ya caka mini jiya," "hannuna ya sage"" da sauri Viper ya kalleta." "Walid ya ce ""Subhanallah, Allah ya sauwwaƙe ya ƙara afuwa""" "Ta kalli wainar gaban Viper, ta ce ""Oga walid ɗauke wainarka, na dafo masa abinci." "Ta janyo ledar viva daga ƙarƙashin gadonsa, ta buɗe food plask, ta ɗaukko mini tea flask ɗin ta," ta haɗa masa tea. "Faten dankalin turawa ne, ya sha ganye sosai da nama, sai ƙamshi yake yi duk ya cika ɗakin da" ƙamshi. "Ta miƙa masa shayin ta ce ""Bisimillah ranka ya daɗe, kaga tea ne, da ɗuminsa sai ka samu cikinka ya warware, kaga tun jiya baka ci komai ba, ina fatan Allah ya baka lafiya da wuri, mu" "cigaba da aiki muna addu'a, in sha Allah sai mun dangana da nasara""" "Ya ɗaga kai yayi mata wani irin kallo, ta ce ""Ba danni ba, dan Allah idan baka ci ba ba zan ji daɗi" "ba, dan kai na girko na kawo maka. Lafiyarka na da matuƙar muhimmanci a wurina please mana, ka karɓa"" ya miƙo mata hannu, ta saka masa kofin tana kallonsa tana murmushi." """To yi bisimillah ka fara sha""." "Ɗan mama ne yake ta ƙoƙarin yin dariya, amma yana jin tsoro, ganin yadda aka bar Walid da busashshiyar wainarsa. Liti kuwa ƙyaƙyatawa ya din ga yi ya ce ""Walid, miƙo mana wainar nan," "mu ƙaddamar mata""" """Sannu maye, aikuwa ba zaku ci ba, ku ci kanku""" "Nabila murmushi ta yi, ta cigaba da yi wa Viper hira, cike da tausayawa, da bashi ƙwarin gwiwa a" kan haƙuri da ƙaddara. "Sannu a hankali yake cin abincin, har ya cinye tas, ya shanye shayinsa." "Wani murmushin ta sake yi masa, ta ce ""Alhamdilillah ala kulli halin. Allah ya ƙara maka sutura da ingantacciyar lafiya, ya baka tsawon rai ya bamu nasarar ɗaukar fansar abun da aka yi mana. Har cikin raina nake jin zafin abun da ya faru da kai, but before then. Please promise me ka daina z1y ³y2ubar da hawayenka, wanda ka yi ya isa. Kuma kayi mini alƙawarin ba zaka sake shan ƙ" "wayoyin da za su illata mini kai ba""" "Liti ya tashi ya ce ""Nikam nayi waje, wannan wace irin fitsara ce?""" """Ka kalleni mana dan Allah"" ya ɗaga kansa ya kalleta." "Duk da idanunsa sun yi mata nauyi, amma ta ce ""Ka ce Nabila, nayi miki alƙawari ba zan sake shan miyagun ƙwayoyi ba, ba zan sake yi wa kaina allura ba, zan baki cikakken goyon baya in ɗ" "auki fansata ta hanyar da ta dace""" """Tashi zan kwanta"" ya faɗa a taƙaice." "Duk wannan zubar da ta gama yi, ba su ne a gabansa ba, kawai ta tashi zai kwanta." "Ta fuskanci aiki ne jawur a gabanta, ba ta sare ba taƙi tashi, ta kuma ƙi magana." "Ya ture ta, ya raɓa ya kwanta ya juya mata baya." """Allah ya baka lafiya ya jaddada rahamarsa ga marigayyiya jauhar""." """Amin ya Allah, na gode"" yayi maganar idanunsa a lumshe." "Tayi murmushi jin ya amsa, ba ya wasa da duk abun da ya shafi Jauhar." "Walid ne ya rakota, take ce masa ""Ku yi haƙuri da wasu abubuwan da zaku ga ina yi, ina yi ne" "saboda sama wa ƙwaƙwalwarsa nutsuwa, idan ba haka ba zai iya rasa hankalinsa baki ɗaya""" "Walid ya ce ""Karki damu na fahimce ki, ki rabu da liti, ba kan gado ya cika ba dama""." *** "Ramma na kwance a jikin Abdul, yana waya da mahaifiyarsa, tana yi masa magana a kan haɗa lefensa, ya ce su yi duk abun da yakamata, yau zai je asibiti ne, zai yi tiyata cikin dare, dan haka yayi busy. Ya kashe wayar, ramma ta motsa tana ƙoƙarin tashi ya riƙe ta ya ce ""Beb, ina zaki kuma?""" "Rai a haɗe ta ce ""Na gaji da kwanciyar tashi zan yi""" "Ya tashi zaune ya ce ""Haba rahama, nifa duk wani motsinki ina gane me kike nufi, ai na baki haƙ" "uri, kin san dalilin auren nan....." """Ni cewa nayi na damu da aurenka? Ina ruwana ne ni damuwata na koma gaban iyayena""" "Abdul ya ce ""Zaki koma, amma sai Allah ya sa kin samu ciki kin haihu, am doing this for your" "own benefits, saboda ke duk nake haka""." """To bana so, ka daina""" """Haba sayyada, ba fa zina zan yi ba aure zan yi, kin ce in yawaita istigfari Allah zai yafe mini, to" "ke kuma kin ƙi ki yafe mini, ki yi amfani da iliminki mana haba sayyada rahama""" """Ba wata sayyada, sayaddar da ka kafawa ƙahon zuƙa sai ta haifi ɗan shege ko?""" "Kawai ya kama dariya, ya ce ""Ke dai ba a iya miki, idan an yi nan sai ki yi can, anjima zan kai ki" "shan ice cream mu ɗan fita mu zagaya""." """Ba zan je ba""" "Ya ce ""Shikenan huta roro, na ɗauki amaryata mu je""" "Tayi tsaki, ta sauka daga kan gadon, ta nufi toilet." "***Bunkure ta fito daga shari'a kenan, ta nufi motarta, ta tarar da Nabila a tsaye tana jiran" isowarta. "Ta tsaya ta kalli Nabila, Nabila ta kalleta ta ce ""Na je office ɗin ki sau biyu, an ce ba kya nan, kin yi balaguro, da ki ka dawo kuma, bani da isashshen lokaci." "Ina son sanin in da ramma take, ita wadda aka yi wa fyaɗen, da shi kansa likitan da yayi" "documenting ya tabattar da an yi mata rape, ba wai takarda kawai ba." """Ke, kin fara wuce gona da iri fa, kar ki bari na waiwayeki, nayi yinƙurin ɗaukar mataki a kanki""" """Wane matakin kenan? Harka ce ta aiki fa, idan kina da gaskiya menene na ɓoye-ɓoye. Nayi mamakin yadda kina mace, once a rape victim, amma ki zama tsanin kare masu laifi. Na san kin ga shaidar da na gabatar a kotu, ta sautin muryar mahaifiyar ramma, kuma ko sama ko ƙasa an nemeta an rasata yanzu. Shikenan idan kina taƙama da kun saye lawyoyi da alƙalai, ki shirya motsi na gaba da zan yi." "Sai na bankaɗo duk wani shu'umanci, da zalunci da ki ke yi, kuma ko a ina kuka ɓoye ramma, sai na tona muku asiri, na tonawa wanda yayi mata fyaɗe asiri. Kar ki manta ɗan hakin da ka" raina. Bata sake cewa komai ba ta tafi ta bata wuri. "Wayarta ta ɗaukko ta tura wa Indabo message. ""Yakamata ka motsa a kan yarinyar nan, ta fara" "wuce gona da iri""" "Kasancewar ta sha zirga-zirga, a gajiye ta ƙarasa office ɗin su." "Wurin Barrister Habib ta fara nufa, tana zuwa ta tarar da Sumayya da wasu mata su biyu, a Office" ɗin Barrister Habib suna jiranta. "Suka gaisa da Habib, ta juya ta fice, zai yi magana, Sumayya ta ce ""Bari na je na same ta." "Ta iske Nabila a office ɗin ta, ta ce ""Arfa, tun safe fa bayin Allah nan suna jiranki, har na zo nima," "baki zo ba ina ki ka je ne haka?""." """Sumayya wai baki da zuciya ne, alaƙa da ke ce bana so, na menene zaki din ga bibiyata kuma?""" """Nabila, dan Allah ki tsaya mu yi magana, mu fuskanci juna dan Allah""" """Babu wani abu da zan fuskanta, ni kin riga kin sire mini, ki fita ki bani wuri, ko ni baki wuri""" Sumayya ta tsaya tana kallon Nabila. "Nabila ta zo zata fice, Sumayya ta riƙe ta, ta ce ""Ni yakamata na fice na baki wuri, na san nayi kuskure amma yakamata ace ko sau ɗaya kin saurare ni." "Tabbas ina bayar da duk wasu bayanai, da aka nema a kanki, amma ni baki san a wani hatsarin rayuwata take ciki ba, domin kare taki. Ni 'yar halak ce, zan daina binki dan ki saurare ni, amma zan cigaba da aikin da aka bani a kanki. Idan kin ga dama, ki saurari matan can, idan kuma kin ga" "dama, ki kore su, matsalarki ce ba tawa ba"" ta ja da baya, ta buɗe ƙofa ta fita." "Ta so bin bayan sumayya, amma sai ta fasa, Sumayya ta faɗi maganganu masu muhimmanci, da" "yakamata ta tsaya ta ji menene, amma sumayya ba ta fushi, idan kuma tayi tana da wahalar sha'ani, dan haka bata bi bayanta ba ta koma wurin barrister Habib da wannan matan." *** "Ƙarfe biyar Al'amin ya koma maɓoyarsu, bayan su Walid suna ta fama da shi, ya ce a sallame shi, sun ce sai ya gama warwarewa, shi kuma ya san akwai hatsari zamansa a asibitin, suna fita salla ya fice daga ɗakin, ya bar Asibitin." "Sai dai yana shiga ɗakinsa, ya tarar da wata baƙar rigar, irin wadda aka ajiye masa da safe a" "asibiti, ya ɗaga ta ya juya, irin waccan ce sak." "Ita ma a take ya yayyagata, ya watsar, ringing ɗin waya ya ji a ɗakin, ya duba ya ga wata ƙ" "aramar waya keypad, wata lamba ce ke kiran wayar." Ya ɗaga ya saka a kunnensa. """Al'amin Viper, ka daina jayayya da ƙaddararka, bin wannan ƙaddarar itakaɗaice mafitar da ta rage maka, ka karɓi kayan da muka baka, ka dawo gida Viper"" aka katse kiran, ya bi lambar," amma aka ce lambar dose not exist. Yayi jifa da wayar ya ja da baya ya tsaya yana huci. Ayshercool 08081012143 ₦500 ne via 0009450228 Aisha Adam jaiz bank sai shaidar biya ta 08081012143 Wanda za su jira document 1K ne. 90009343 'Yan Nijar ku turo katin airtel na 300fcfa Arewabooks ayshercool7724 "Ya cigaba da zazzare ido, yana kallon ɗakin, ya ɗauki wayar da ya watsar, ya sake haɗata, ya" "kuma kiran lambar, amma a sai ace masa lambar dose not exist." "Ya fita waje, ya zagaye gidan yana dube-dube amma bai ga kowa ba, ya koma cikin gidan ya ɗ" "auki wayar da rigar da ya yayyaga, ya shiga banɗaki, ya watsa su a masai ya fito." *** "Nabila kuwa bayan tafiyar sumayya, ofishin Barrister Habib ta koma, suka sake gaisawa da matan nan, ya ce ""Ina sumayyan?""" """Ta tafi gida ne, na ce gani me yake tafe da su ne?""" "Ya kalle su sannan ya kalli Nabila ya ce, maganarki da ki ka yi, su sumayya T ladan suka saka a" "radio, a kan Barrister Naja'atu Bunkure, shi ne ya sanya suka zo, su sanar miki da wasu abubuwa da zai taimaka miki""." "Nabila ta ce ""Masha Allah, bari na aika baba masinja, ya sayo musu ruwa da lemo, naga azahar ta" "wuce, kafin nan nima nayi salla""" "Ya ce ""To babu laifi""" "Tayi salla ta dawo, suka zauna da matan, ɗayat ta fara bata labarin abun da ya faru ""Ni 'ya ce da ni, mun rabu da mahaifinta, tana wurin babanta, yayi mata auren dole, take ta guje-guje saboda ba ta san mijin. Ake ta fama har tayi yinƙurin kashe kanta, magana har gidajen rediyo, ta turo wakilanta, suka tafi da mu can office ɗin ta, ta ce aure ba dole bane ba, dan haka dole a kashe auren nan. Da fari na so ayi sulhu yarinya ta koma ɗakinta, tun da bama tare da ubanta." "Na din ga yi mata nasiha, a kan tayi haƙuri, tun da babanta yana ta tsine-tsine a kan ta bujire masa, ta haƙura ta yarda, amma matar nan ta ce sai an kashe auren, zata kai ni ƙara hukumar kare hakkin ɗan Adam, ta ɗauke mini 'ya, ta tafi da ita, sai da aka yi sati biyu sannan ta dawo mini da ita ga babanta da mijinta suka ƙara matsa mini lamba, bayan ta dawo da ita, yarinya ta ƙara tuburewa ba ta san zancen aure ba." "Tamkar an canza mini ita, idonta ya buɗe, har mijin 'yar tawa ta saka aka kama aka rufe, aka kashe auren nan. Yanzu maganar da nake yi miki, shekru uku kenan, yarinyar nan ta ce aure wani abu ne al'ada da muke takurawa kanmu a kai, addini bai wajabta mana ba, haka take rayuwarta, sai ta shafe kwanaki ba ta gida, tana yawonta. Babanta ya sallama mini ita, bayan ya gama tsine mana daga ni har ita. Har a cikin unguwa ta cigaba da yi wa sauran ƙasayenta mummunar huɗubar adawa da aure, wai ana tauye musu hakki, kuma wallahi Naja bunkure ce ta mayar mini da 'ya" "haka,tana fakewa ne kawai da taimako, tana zaluntar mutane""." "Ɗayar ta ce ""Nima kusan hakan ne, wani yaro ɗan masu kuɗi, ya lalata mini yarinya daga aikenta" "gidan, jami'an tsaro suka ƙi kama yaron, uban ɗan ya ce in dai arziki yana rana, zai kare ɗan sa, ba wanda ya isa ya kama shi ya hukunta. ni kuma jin shirye-shirye da ake yi a kanta, na taimakon" "marasa galihu, ya sanya nima na je neman ta taimaka mini. Da farko abu kamar gaske zata taimaka mini, ƙarshe abun ya juye, aka nemi a mayar da case ɗin wai sharri muka yi wa yaron." "Wallahi ƙarshe yarinyata fiya-fiya ta sha ban sani ba, yar shekara goma sha huɗu ta mutu. Wallahi matar nan azzaluma ce, bamu da wurin da zamu je, mu nemi hakkinmu sai wurin Allah, haryanzu idan zance yayi zance a kan tayar da maganar abun da ya faru da yarinyata, wanda hakan ba ƙ" "aramin tsaye mini yake yi ba"" tayi maganar tana kuka mai ban tausayi." "Nabila ta tashi ta rungume matar, tana rarrashinta ta ce ""Ki yi haƙuri dan Allah, ki kwantar da hankalinki, Allah ya jiƙanta, kuma in sha Allah da ikon Allah sai mun kai matar nan ƙasa, zan yi iya yi na, in bankaɗo duk wani mugun abu da ta aikata muku, kuma sai ta girbi abun da ta shuka, ku yi haƙuri. Yanzu duk zaku bani adress ɗin ku, zan bi cases ɗin ɗaya bayan ɗaya, na tabattar" "da abun da ya faru kafin na san abun yi""" "Jikin Nabila yayi sanyi sosai da sosai, da jin abubuwan da Bunkure take aikatawa, tamkar ba 'ya" "mace musulma ba, da matan ke iƙrarin ciwon ƴa mace, na 'ya mace ne." "Har kuɗin mota ta basu, bayan tafiyarsu ta kalli barrister Habib ta ce ""Yaya habib, ka ji wani" "yahudanci? Ina laifin ta tsaya a kan iya kashe auren an yi wa 'yar auren dole?""" """Ke ce baki san wacece ita ba sai yanzu, wannan wata ɓoyayyiyar aƙidarta ce, na bawa mata" "damar ƙin zaman aure da lasisin karuwanci. Tana saye yaran da kuɗi, da abun duniya wurin cusa musu wannan mummunan ra'ayin, da koyar da su daidaiton jinsi tsakanin su da maza""." """Innalillahi wa Innalillahi raji'un, amma duk da haka Alhamdilillah, na samu hints a kan yadda zan" "bankaɗo asirin matar nan, and one more thing kuma"" ya kalleta ya na jiran me zata ce." """Maganar da muka yi da kai kwanakin baya, a kan case ɗin Aminu Viper""" """Ina jinki""" """Naja'atu Bunkure tana cikin tawagar lauyoyin da suka tsaya kai da fata a kan shari'ar da aka yi masa. Kuma ka san ita ungulu ce ba ta jewar banza, dan haka akwai manufa a cikin shiga shari'ar da tayi. Viper ba ɗan siyasa bane ba, kuma ba shahararren mai kuɗi bane ba, balle ace tsaya masa tayi a shari'ar. Dan haka akwai ayar tambaya a kan charges ɗin da aka yi masa na kisan kai." "Take a look at it barrister, an tsare mutum shekara biyar, an yi masa shari'a sau biyar kawai, an kai" "shi prison an ajiye babu conclusion na shari'ar, is je guilty or innocent? Kwatsam an ce ba a ganshi a prison ba, kuma an cigaba da nemansa, ruwa a jallo, anya akwai gaskiya a lamarin nan kuwa?""" "Ya tsura mata har ta gama, yayi murmushi ya ce ""Haka kwanyar nan take cike da basira, amma aka ƙarar da ita a wurin iyayi da kwalliya?." "Maganarki gaskiya ce Nabila, amma ina rabaki da case ɗin Vipern nan, akwai badaƙala sosai a" "kan case ɗin""." "Nabila ta ce ""Me da me ka sani a kai?""" """Nothing much, kawai na san dai akwai bita da ƙulli ne a ciki sosai""" "Ta jinjina kai ta ce ""Haka ne, bari na tafi gida, yau a matuƙar gajiye nake"" tayi masa sallama, ta" "tafi office ta ƙarasa shirinta, ta tafi gida. Ta sake karo da file a office ɗin." "Cikin mamaki ta ɗauka, ta fara buɗewa." Aka rubuta continuation a ciki. "Cigaban tarihin Naja bunkure ne, bayan rape da aka yi mata, cousin brother ɗin ta, aka rufe case aka ce abu ne na dangi, bayan ta ƙara girma tayi aure, ta sha wahala sosai a hannun mijinta na farko, ya azabtar da ita tamkar baiwarsa, ko haihuwa ba ta yi ba auren ya mutu." "Yayanta ne ya taimaka mata, ya mayar da ita makaranta, tayi candy, ta shiga jami'a, sai dai bayan rasuwar yayanta, aka rasa mai sponsiring ɗin ta, ta cigaba. Mahaifiyata na can wani garin tana aure, babanta kuma ya ce ba ruwansa da ita, tun da taƙi zaman aure." "A lokacin har wurin ɗan majalisar su, ta je neman kuɗin makaranta, lokacin yana tare da Indabo, indabo ya ce zai bata, amma sai dai ayi bani gishiri na baka manda. Ta amince tun daga nan, ta" "zama tamkar matarsa su watse ya biya mata kuɗin makaranta, babu wani sirri nasa da bata sani ba." "Ta nemi ya aureta, bayan tayi graduation, amma yaƙi, ganin haka ya sanya, ta samu wani suka" "daidaita ya aureta, sai dai Indabo ya cigaba da bibiyarta." "Ta fara aiki a matsayin lawyer mai zaman kanta, Naja tana da burin yin luxry life sosai, sai dai mijinta yana da rufin asiri amma ba irin wanda take hange ba, Indabo yayi mata alƙawarin haɗa ta da manyan mutane, lokacin ya zama ɗan majalisa, wanda zata din ga samun alkhairi da damarmaki." "Kwaɗayi da buri, ya sanya suka koma ruwa da aurenta, ya din ga kashe mata kuɗi, yana kuma haɗ ata da manya. A wurinsa ta koyi shaye-shaye. Tsakanin ta da mijinta babu ragayya ko kyautatawa," duk son da yake nuna mata da kulawar da yake bata sam baya gabanta. "Ta fara tashe sosai tana shahara, ana programs da ita a kafafen watsa labarai, ta buɗe ƙungiyar ta ta kanta, bayan joining ɗin ƙungiyoyin yahudawa, masu da'awar daidata jinsi, reshen Nigeria, ta" cigaba da yi musu aiki ta ƙarƙashin ƙungiyar ta. "Sai dai a haka take miyagun harƙallarta, na yi wa manyan mutane safarar mata a birnin tarayya," "musamman ƙananan yara, da akan yi amfani da su saboda asiri." "Red handed mijinta ya kamata, chats ɗin ta da wani minista, na ƙazanta, yayi kuka, amma ko a" "jikinta, ta ce idan ba zai iya ba ya rabu da ita. Haka ya saketa, ta samu cikakken gashin kanta." "Ba ta taɓuwa, ko da kuwa tayi laifi, yanzun nan ƙungiyoyin kare hakkin ɗan Adam zasu shiga" "lamarinta. Ta din ga binne mutane ta hanyar bayyana musu kyawawan ayyukanta, da ɓoye na laifin." "Bayan mutuwar aurenta labari ya bazu, mutane suka din ga tsinewa mijinta, wai ya saki macen" "kirki, aka yi hira da ita, ta din ga kuka tana yi tsohon mijinta sharri kala-kala." End the story.... Aka rubuta a ƙarshen page ɗin. "Wani irin gumi, ya din ga tsatstsafowa Nabila, ta ma rasa abun yi, da tunanin da yakamata tayi, ba ta bari ta takura ƙwaƙwalwarta wurin hasaso waye ya kawo mata file ɗin a karo na biyu ba," kawai ta ɗauki jakarta ta fita. *** "Sumayya ce a tsaye tana kuka wiwi, shi kuma ya zuba mata ido, ko ƙiftawa baya yi, sai da tayi mai isarta sannan ya ce ""Kukan ya isa haka, meyafaru?""" "Ta share hawayenta ta ce ""A gaskiya sir, ni na gaji da aikin nan, na samu matsala da ni da Nabila, ni Nabila ba ƙawata ce kawai ba, ƴar uwata ce, ta riga ta yi fushi, ba zata saurare ni ba, ni ban san wanda ya gaya mata ina bibiyarta ba, ga wancan honorable ɗin ya addaba mini, duk motsina sun sani, sai kuma sun tambaye ni, me tayi me take ciki, banda barazana da suke yi mini ba yau ba gobe, ni dai dan girman Allah ka yi wani abu a kai, kar ni ko ita ayi wa wani illa, indabon nan fa" "ba imani ne da shi ba"" ta ƙarasa maganar tana sake fashewa da kuka." "Yayi murmushi ya ce ""Haba ƴar jarida, ya da kuka wiwi haka da karaya nan da nan? Da kin sanni, kin san zan taimake ki? Baki san ya aka yi na gane Indabo yana yi miki barazana ba. Har na shigo lamarin ba, dan haka ba zan bari a cutar da ku ba, dukkaninku a kan gaskiya ku ke, sai dai ita naga buyaginta yayi yawa." "Ki yi haƙuri ku daidaita, da haka zan cigaba da yi mata supplying abubuwan da take buƙata a" "harkar shari'ar nan""" """Sir yanzu fa ka gama cewa buyaginta yayi yawa, sai ce mini munafuka take yi, babu yadda" "tsakanunmu yanzu""" "Ya ce ""No, tayi fushi ne kawai, and ki ƙara kiyayewa sosai da sosai, ki daina bari tana gane kina" "bibiyarta""." "Sumayya ta ce ""Yanzun ma, wallahi ina kiyayewa, ban san yadda aka yi ba""" "Ya din ga rarrashinta, sannan ya saka aka ɗauke ta a mota, aka mayar da ita gida." *** "Nabila da ƙyar ta isa gida, ta watsar da kayan a kan gadonta, ta fara kiran wayar Viper, amma a kashe, ta kira ta Walid amma baya ɗagawa, haka ta haƙura ta shiga banɗaki tayi wanka ta yi alwala ta fito." "Har washegari da safe, Nabila tana neman layin Walid, hankalinta ya ƙara tashi, tayi tunanin ko" wani abun ne ya same shi. "Tana saka kayan abinci a motarta, Nasir ya fito." "Ta ce ""Yaya ina kwana?""" "Ya amsa da ""Lafiya ƙalau, wai ina ki ke zuwa da kwanukan abinci kwana biyun nan ne?""" "Ta ɗago ta kalleshi ta ce ""Ci nake yi mana, wataran ai wuni nake yi bana gida""" "Ya ɗage kafaɗa ya ce ""Ban sanki da dakon flask ba, saboda haka kin gwammace ki ci biscuit da" "sauran kayan ciye-ciye""" """Haba yaya, yanzu ba mota ce da ni ba? Kuma zan je in ta cin abinci nikaɗai duk ga mutane ne a" "wuri?""" "Ya girgiza kai ya ce ""A'a, amma yanzu ƙarfe bakwai saura kwata, har shida da rabi kin fita, saɓ" "anin da har goma saura sai ki kai a gida""" "Ta tsaya sosai ta dube shi ta ce ""Yaya me kake nufi ne? Ka daina ɓoye-ɓoye ka fito fili ka sanar" "mini cewar, tuhumata kake yi, da aikata rashin gaskiya mana""" "Yayi murmushi ya ce ""Ai ba a tuhuma sai an tabattar da zargi my dear""" """Da ka daina zargin, dan wahalar da kanka kawai zaka yi, ko kuma irin abun naku zaka yi mini na" "masu kaki"" tayi maganar tana murmushi." "Shi ma murmushin ya yi, ya ce ""A sauka lafiya""" Ta amsa da Amin ta tafi. "Tana tafe a hanya sai ga kiran wayar Walid, ta ɗaga wayar ta ce ""Oga Walid, sai kiranka nake yi a" "waya, shi wayarsa ba ta shiga, wayarka kuma baka ɗagawa""" "Walid ya ce ""Bari kawai, kin san halin mutumin naki sai a hankali ai, jiya bayan tafiyarki, ya kafa mitar sai an sallame shi daga Asibiti, da mu da likita muka din ga rarrashin sa, yayi mana banza, mun fita salla ya gudu, baki ga yadda hankalinmu ya tashi ba, na ce musu kawai mu koma gida, dama ya saba irin haka, ko lokacin da ƙanwata take raye, haka take fama da shi, idan aka kwantar" "da shi, da ɗanyen ciwo haka zai bar asibiti sai dai ta ƙarasa masa dressing a gida ya warke""." "Nabila ta ce ""Allah sarki, Allah ya yi mata rahama, shi kuma ya bashi juriya. Kana ji na, zan shigo dan ga abinci ma nayi, yayana ya fara saka mini ido ne, dole na canza takuna, zuwa azahar zan bar" "motata a chamber, zan zo in sha Allah""" "Ya ce ""To Allah ya kawo ki, dan zuwan naki yana da amfani, yaƙi cin abinci ya ƙi shan magani," "yana kwance kawai tun jiya""" """In sha Allah zan zo, ayi masa sannu"" ta ajiye wayar tana murmushi, rigimar Viper tana da yawa," idan ba ka da haƙuri ba zaka iya da shi ba. "Har ta fara neman lambar sumayya, sai kuma ta fasa kiranta, dan har ta manta sun yi faɗa. Kawai ta din ga jin ta wani iri, akwai abubuwa da dama da take son gaya wa sumayya, saboda kusancinsu da shaƙuwarsu, ta musamman ce. Sai dai haryanzu tana mamakin dalilin da zai sanya a din ga" "bibiyarta ta hanyar sumayya, kuma waye yake bibiyar ta ta." "Sai dai ta fara zuwa courts ɗin da take da trials, ta gabatar da shari'oi, sannan ta koma asibitin da" "aka kai ramma, lokacin da aka yi mata fyaɗe." "Ta nemi a bata copyn report ɗin da aka yi confirming rape case ɗin, aka ce an bawa ƴan sanda." "Ta nemi ganin likitan da ya kula da ita, aka ce ya tafi ƙaro karatu, a bata lambarsa nan ma aka cigaba da yi mata yawo da hankali." "Sai da ta gama zagayenta, sannan ta ajiye motar a wani wurin parking, ta karɓi pass, ta tafi wurin" su Viper. "Yau a tsakar gida ta tarar da shi, sun shimfiɗa masa tabarma, yana zaune yana ya danna wayarsa," "sai dai idanunsa sun ɗan yi wuri wuri ya faɗa, gabansa kuma kwalin sigari ne da lighter." "Tayi sallama duk suka amsa, ya ɗaga kai ya kalleta ya mayar ya sunkuya." """Ohhh masha Allah, the most handsome man ever saw, kaga yadda ka yi kyau sosai da sosai"" ta nemi wuri ta zauna a gabansa ta ce ""Manya gatan wasa, fisabilillahi mutum sai ya gudu daga" "Asibiti ba a sallame shi ba? Idan kuma bai warke ba fa, ni gaskiya ban ji daɗi ba""" "Ba ta saka ran zai kulata ba, ta ce ""Ina wuninku, ya mai jiki kuma?""" Suka amsa da sauƙi. "Walid ya ce ""Ba yadda bamu yi da shi ba, amma sai nemansa muka yi muka rasa""" "Tayi dariya ta ce ""My, ya kake haka ne, duk muna ta taka, amma kai ko a jikinka. Wannan sigarin ina fatan ba sha aka yi ba, kaga an ce jininka ya hau, kuma kana smoking ba zai sauka da wuri ba, an ce mini baka cin abinci, duk ka rame ai ba zan ji daɗi ba"" ta janyo ledar abinci ta ce ""Ka yi haƙ uri ban kawo abinci da wuri ba, Yaya Nasir ya fara saka mini ido"" ta ƙarasa maganar tana miƙa" "masa plate, da cup ɗin da ta zuba masa kunun alkama." "Ya saka hannu ya karɓa, ya fara ci." "Liti ya ce ""Wato mai zamani mune dai ba ma yi maka gwaninta ko?""" "Nabila ta yi murmushi ta ce ""Ka san wani abu?"" Ya girgiza mata kai alamar a'a." """Ni fa na gaya wa Sumayya, na san tana bibiyata, duk da jiya ta kawo mini wasu mata, da suka yi mini complain a kan Bunkure, amma mun yi faɗa da sumayya." "Sannan an sake ajiye mini file a office ɗina, na ƙarashen labarin Naja'atu Bunkure." """Ku ka yi faɗa ba ƙawarki ba ce ba?""" """Eh, amma meyasa zata ci amanata?""" "Ya kalleta ya ce ""Ya aka yi ki ka tabattar da cin amana ne ya sanya take bibiyarki?""" """Saboda kai ka gaya mini""" """Ban ce tana bibiyarki dan ta ci amanarki ba, kuma baki da tabbacin da gaske nake ko akasin" "haka""" "Ta gyara zamanta ta ce ""A labarinka da na ji, baka ƙarya dan ka ci amana, kuma bana tunanin" "zaka fara a kaina""" "Ya jinjina kai ya ce ""Bani wayarki"" ta ɗaukko wayarta ta bashi, ya nutsu sosai yana ta daddanawa." """Yayanki ma na ƙoƙarin yi wa layinki kutse, sai dai na rufe damar hakan. Yana zarginki a kan da shi kansa bai san menene ba. Yayanki ya ga Indabo yana yi masa aiki a kaina, yana kuma gargaɗin sa a kan abun da ki ke yi a kan bunkure, na san zuwa yanzu ya matsa miki lamba a kan ki rabu da" "ita""" "Ta waro ido ta ce ""Ya aka yi ka sani? Anya yayan kuwa?""" "Ina bibiyar kiran wayarsa ta hanyar amfani da wayarki, hakazalika duk wasu maganganu da yake yi, recording ɗin suna kan computer ki. Wayarsa da Indabo kawai nake bibiya, ba ruwana da" sauran harkokin sa. "Ta ce ""Subhanallah, amma yaya ya bani kunya, shiyasa yake ta uzzura mini? Amma nima ka yi" "hacking ɗin wayata kenan? Kana jin duk wayar da nake yi da samarina?""" "Tsaki yayi, ya jefa mata wayarta. Ya ce ""Ina magana serious kina yi mini shirme?""" "Ta ce ""To ai kar ka ji ina kalamai ne, ka zo kana kishi, nifa duk ba son su nake yi ba, kai kawai" "nake so"" tayi maganar da niyyar sake kunna shi." "Ƙoƙarin tashi yayi, tana dariya ta ce ""Yi haƙuri, dan Allah ka duba mini ƙarashen labarin nan, na" "Najar bunkure ka gaya mini menene opinion ɗinka""." """Mu yi aiki kawai, ki daina yi mini wannan shirmen""" """Ba shirme bane ba fa, ni da gaske nake"" ya karɓi file ɗin, ya cigaba da duddubawa." "Ya ɗaga kai ya kalli walid ya ce ""Mai laya""" """Mai zamani""." """Yakamata ku je ku daba mini mahaifiyar Nura, tun da na fito yakamata ace na je na ganta, amma ba zan iya ba, ban san wace irin karɓa zata yi mini ba, maybe ita ma irin kallon da ake yi mini," "take min""" "Liti ya ce ""Haba maza, babu lallai gaskiya""" "Nabila ta ce ""Ina kakarka to? Wadda oga walid ya bani labarinta?""" """Ta mutu ina prison""" "Walid ya ce ""Har tare da ita mun je prison, sau biyu ba a bari mu ganshi. Baiwar Allah nan tashin" "hankali da damuwa ne, suka haɗu suka kasheta""" "Jiki a sanyaye ta ce ""Allah sarki, Allah ya yi mata rahama, ya sanya sun huta baki ɗaya, da yar" "madara, da Hajiya, da mamana da sauran al'ummar musulmi baki ɗaya"" suka amsa da Amin." "Walid ya ce ""Mamanki ta rasu?""" "Ta jinjina masa kai ta ce ""Eh, ban ma santa ba, sai dai hotunanta na gani a wurin Abba""" """Allah sarki, Allah ya jiƙanta""" "Liti ya ce ""Shiyasa ba kya ji, ina tausayawa mariƙanki, sun sha wahala da ma ba kowane maraya" "ne yake ji ba""" """Oganku shi ne na farko a marasa jin, in dai maraya baya ji"" ta yi maganar tana satar kallon Viper." """Amma Viper, ka sake komawa wurin Abbanka kuwa? Na san zuwa yanzu ya huce, zai kuma" "fuskance ka, ka yi masa bayani, shi fa tsakanin ɗa da iyaye sai Allah"" yayi mata shiru." """Ni ka bani dama naje na same shi, na san zai fahimce ni""" "Ya ajiye file ɗin ya ce""Kar ki kuskura ki fara wannan gangancin, kar ki kusanci unguwarmu, ko ki" "ce zaki je unguwar da gidana yake, idan ki ka yi ɗaya daga ciki, zan yanke aikin da zan yi da ke," "kuma hakan zai iya sanya wa na kashe ki""" """Au ba zaka daina zancen kisan kan nan ba ko? To maza nima ka kashe ni, na ga wanda zai din ga" rarrashinka. "Ta tashi ta ɗauki jakarta, ta tattara kwanukanta, ta ce ""Bari na tafi, kar nayi yamma da yawa, zamu" "yi magana"" tashi ya yi ya ce ""Muje""" """Rakani zaka yi? To muje"" suka fita kamar gaske. ""Ina sake gargaɗinki, kar ki sake ki ce zaki nemi" "gidanmu ki je, ko gidan su 'yar madara, zaki ɓata mini aiki, duk da na samu labarin sun bar unguwar, idan kuma ki ka ɓata mini aiki, ba na jin zan iya yafe miki""" "Ta ce ""Subhanallah, in sha Allah ba zan je ba, amma yakamata ku daidaita da mahaifinka." """Ba wannan ne a gabana ba""" """To menene a gabanka? Iyaye fa ba a fushi da su""" """Ki rabu da ni""" "Ta ce ""To, Allah ya baka haƙuri""" """Ki cigaba da kula sosai da sosai a kan zuwanki wurin nan, za a iya biyoki har nan, bana tunanin" "iya wayarki ake bibiya""" "Ta kalleshi ta ce ""Akwai wata mota da na lura da tana bina kwanakin baya, amma ba wannan ba. Na faa tunanin anya a cikin yaranka babu wanda suke sanar da wasu abubuwan da muke yi? Ko kuma wani yana binka ko kuma ni da ake bi, an san ina zuwa wurinka ba? Suwaye suka ɗaukeka" "kwana biyu? Sannan ya aka yi aka san kana asibitin nan, har aka biya maka kuɗin asibiti""" "Ya sauke numfashi ya ce ""Kar ki shagala da tunani da yawa, ki manta da abubuwa masu" "muhimmanci, ki je zamu yi magana""" "Ta kalleshi ta ce ""To, amma dan Allah ka ɗaga wayata da daddare in ji muryarka, ka ji Oga"" wani" "irin mugun kallo yayi mata, ya nausa ya bi wata hanyar, ita kuma tayi gaba tana murmushi." *** "Ramma na zaune a kusa da Abdul, yana kallon ball, ita kuma ta kunna radio a wayarta, tana ji." "Ya kalleta ya ce ""Dan Allah ki rage radion nan""" """Ina ruwanka da ni ne, ka yi kallonka mana""" """Kin cika mini kunne da radio ne""" """To ita ball ɗin magana ake yi? Ba ihu bane ba kawai?""" "Abdul ya ƙure volume, ita ma ta ƙure volume, ta kara masa radion a kunnensa." "Yayi mata shiru ya ce ""Kya yi kya gama""" "Sumayya ce tare da murtala a studio, suka gabatar da program, kasancewar an samu akasi masu" gabatar da program a dai-dai lokacin ba su samu zuwa ba. "Program suke yi akan abubuwan da suka shafi rayuwa, suna yi suna karanto saƙonnin masu" sauraro. "Murtala ya ce ""T ladan, ga wata tambaya daga masu sauraro, wai an ce a tambayeki, wace irin ala" "ƙa ce tsakanin ki da Nabila Yusuf maitama, da kullum ba kya taɓa aiki ki tashi, baki ambace ta ba, baki tsokane ta, ko saka waƙoƙi domin jin daɗinta ba?""" "Sumayya ta yi murmushi ta ce ""Barrister Nabila, voice of voiceless a lady of her words, a hardworking, strong minded young barrister, she's exceptional, lovely and simple sister of me""" tayi maganar tana jin zafin saɓanin da suka samu a tsakanin su. "Murtala ya ce ""Tirƙashi, duk wannan kirarin itakaɗai?""" """Sosai, Nabila mutum ce ta mussaman a rayuwata, ina yi mata son fisabilillahi""" """To yanzu da saurayinki, da Nabila wa ki ka fi so?"" Ta kwashe da dariya ta ce ""Uncle murtala" "wannan ai haɗa faɗa ne""" """To yanzu kafin muyi sallama da masu sauraro, gaya mana kalma ɗaya tak a kan Barrister" "Nabila""" """Mai gaskiya ce, ina yi mata fatan nasara, ya ɗaukaka mini ita, ya kuma kare mini ita a duk in da" "take, ya dauwwamar da ita a kan gaskiya""" "Murtala ya ce ""Amin ya haiyyu ya ƙaiyyum, Allah ya bar wannan ƙauna, kafin mu ƙarƙare shirin, mun karɓi takardar wata baiwar Allah da za a yi wa ɗanta aikin ƙaba, amma ba ta da hali, tana neman taimakon bayin Allah. Akwai kuma wadda take neman kuɗin sayawa mahaifiyarsu" "magani mai fama da hawan jini, muna fatan zaku taimaka""" "Nabila kuwa tana driving, ba ma'abociyar jin radiyo bace ba, amma saboda sumayya take sauraren" "radio. Hawaye ta din ga sharewa, tare da tuna abun da ta yi wa sumayyan." "Ramma kuwa cewa ta yi ""Allah ya ƙarfafi wannan baiwar Allah, ya tabattar da ita a gaskiya, kar" "ya kauce hanya, kamar waccan munafukar mara imani"" Abdul yana jin ta, yayi mata shiru. Ganin" "bai kulata ba ya sa ta ce ""Ba zaka ce amin ba""" """Ni fa ball nake kallo""" """Allah ya sa a cinye club ɗin da kake yi""" """Ba amin ba"" ya ɗauki wayarsa, ya kira admin ɗin asibitin sa, ya ce a je gidan radion su sumayya," "a kai yaron nan ayi masa aiki kyauta, mai hawan jinin ma a kai ta a bata magani." "Ramma ta ce ""Kalle shi kamar na Allah"" duk yaƙi kulata, ta tashi ta nufi ɗaki, ta saka hannu ta" "kashe tv ta riga ɗaki da gudu, kawai yayi dariya." *** "Kwanaki biyu, Nabila ta daina samun Viper a waya, sai dai da ta kira walid, ya tabattar mata da lafiyarsa ƙalau." "Nabila ta fara gazgata zancen Viper, duba da yadda Nasir yake kashe-kashen kuɗi, ya canza mota" "ya cigaba da gininsa, kuma salarynsa gaba ɗaya ba wani shahararre bane ba." "Nabila tana kwance tana waya da Alhaji Wada M karofi, yadda yake lallaɓata yake yi mata magana, har kunya yake bata." "Fuskar viper kawai take hangowa, yanzu da shi take yi wa kalaman nan, da tuni ya haɗe rai yana hararta. Bayan sun yi sallama ta ajiye wayar, Walid ta shigo ɗakin ta ce ""Arfa, isa ne ya shigo" "yanzu, wai ana sallama da ke a waje""" """Kai, wane ɗan baƙin cikin ne zai hana mini jin daɗi a magaribar nan? Ni fa ban yi da kowa za a zo wurina ba""" "Walida ta ce ""Ace ya tafi kenan?""" """A'a gani nan zuwa""" "Ta yafa mayafin abayarta, ta fita, a ƙa'idar Abba a cikin gida suke zance, ganin bai shigo ba, ya" sanya ta gane lallai wanda ya zo ɗin baƙo ne. "Ta zira kai ta leƙa ƙofar gida, dan duba waye." A opposite ɗin gidan ta ga Viper a tsaye yana kallon ta. Ayshercool 08081012143 ₦500 ne via 0009450228 Aisha Adam jaiz bank sai shaidar biya ta 08081012143 Wanda za su jira document 1K ne. 90009343 'Yan Nijar ku turo katin airtel na 300fcfa Arewabooks ayshercool7724 "Gaban Nabila ya faɗi, cikin matsanancin tsoro da tashin hankali, ta din ga waige-waige tare da" "dubawa, idan akwai wanda ya ganshi, amma layin babu kowa, sai manyan security light da suka haska ko ina." "Ta sake kallonshi, ta tabattar shi ne, ta ƙarasa in da yake da sauri ta ce ""Viper, waye ya nuna maka" "gidanmu? Yau kuma ba office ba har gida?""" """Akwai matsala ne?"" Yayi maganar yana ƙara ƙureta da ido." """Au tambayata ma ka ke yi? Amma dai ka san yayana nemanka yake yi ko meyasa zaka zo" "gidanmu, lallai sai ka tona mini asiri ne? Waye ma ya nuna maka gidanmu?""" """Shi yayan naki, ki shiga ki gaya masa gani ya zo ya kamani mana, shikenan ki daina wahalar da" "kanki da fargaba mana. Kina tunanin zan yi aiki da wadda ban san wacece ba?""" "Ta ce ""Yanzu dai duk ba wannan ba, dan Allah mu je daga wancan lungun, mu yi magana""" "Ya sha kunu ya ce ""Ban gane muje lungu ba""" """Eh mana, mu je can mu yi magana kar a ganka""" """A'a ni ba zan shiga lungu a daren nan ba""" """Innalillahi wa Innalillahi raji'un, to ai ba wani abun na ce ayi a lungun ba, magana kawai zamu yi" "kar a ganka nake tsoro""" """Kuma sai ki ce in shiga lungu""" """Na shiga uku, sai ka ce wata 'yar iska, kar ka yi mini wata mummunar fassara mana""" "Viper ya ce ""Ke da duk baki yi wannan tunanin ba, ki ka amince da aiki tare da ni, ki ke iƙrarin zaki taimake ni? Ki tsaya ki saurare ni"" ya yi maganar fuskarsa ɗauke da matsananciyar damuwa." "Duk da bai kasance mai fara'a ba, amma yau akwai damuwa sosai a tare da shi." """Amma dan Allah waye ya nuna maka gidanmu""" """Ba wannan ne ya kawo ni ba""" """To Allah ya baka haƙuri sir, me yake tafe da kai?""" """Nura"" ya faɗa a taƙaice." """Waye hakan?""" """Ƙanina Nura guduma, bayan mutuwarsa ina duba mahaifiyarsa, sai dai bayan an tsare ni ban samu damar yin haka ba, amma su Walid sukan je amma ba ko yaushe ba, bayan fitowa ta kuma, bani da cikakkiyar nutsuwa, kuma ina matuƙar jin nauyinta ban je ba, ban kuma saka su walid sun" "je ba""" "Nabila ta nutsu tana sauraronsa, duk a tsorace take, kar wani ya ganshi, duk da akwai facemask a" fuskar sa. """Mijin da ta aura bayan baban Nura ya rasu, shekaru biyu da suka wuce, tana ta fama da rayuwa, ga yaranta guda biyu, a taƙaice dai jiya da su Walid suka dawo daga garin, sun tabbatar mini da" "'yar ta aka yi wa fyaɗe ita kuma ba a san in da take ba"" Nabila ta zabura ta ce ""Kuma?""" """Yarinyar da ki ke bincike a kan case ɗin ta, Naja bunkure ta shiga case ɗin""" "Nabila ta ce ""Innalillahi wa Innalillahi raji'un, kalmar nan ko daɗin ji ba ta da shi, dama ita ce? To" "ba su gano in da maman take ba?""" """Ina gaya miki kina tambayata, na baki nan da sati biyu rak, tun da kin ce wanda ake zargi ba shi" "bane ba, ki fito da mai laifin, ko kuma ni na fito da shi ta ƙarfin tsiya""." "Cikin rashin fahimta ta ce ""In fito da mai laifi kuma ta ina? Nima bulayin nemansa nake ai saboda" "in wanke client ɗina""" """Sai fa kin nemo shi, ko kuma ki tabattar an yankewa mutumin nan hukunci dai-dai da abun da ya" "aikata""" """Amma dai ka san ni lawyer ce ba 'yar sanda ba ko? Jami'an tsaro sune za su yi maka wannan" "aikin, ni kuma na tsaya na tabattar kotu ta yi adalci""" "Ya tsare ta da idanunsa ya nuna ta da yatsansa ya ce ""Ke zaki yi, ba wanda zai yi sai ke, ki nemo" "ainihin mai laifin, ko kuma ki bari a hukunta wannan mutumin""" """But he's not guilty, he's innocent, ka bari na bi komai a hankali""" "Ya ɗan yi shiru sannan ya ce ""No matter what it takes, ki binciko ainihin mai laifin nan, an cutar" "da matar nan fiye da yadda ki ke tunani""" "Nan ya warware mata ɓangaren labarin sa na Nura, da ba ta sani ba." "Rawa ƙafafuwanta suka fara yi, jikinta yayi wani irin sanyi, ta kasa magana." """Ki din ga yi mini uzuri wasu lokutan, ni mutum ne mai tarin laifuka ga mutane, bana son in ga wani a cikin damuwa, ina tsoron ace matar nan guduwa tayi saboda baƙin ciki, ba haka ba ma, voice message ɗin da ki ka kunna mini, sai a yanzu na sake tabattar da muryarta ce, ta tabattar da har gida wanda yayi rape ɗin yaje ya ɗauke 'yar, dan haka ramma tana tare da wanda ya yi mata fyaɗe, kuma Naja'atu Bunkure ta sanshi, ba dan ta tsayawa yarinyar ta shiga case ɗin ba, dan ta" "bawa mai laifin kariya ne""." """Yanzu ka yadda wanda nake karewa ba shi da laifi?""" """Na sani, amma dole ki yi wani abu, a nemo yarinyar nan da mahaifiyarta""" "Nabila zata yi magana, aka haske su da fitilar mota, ta saka hannu ta kare saboda hasken fitilar, shi" kuwa yayi ƙuri yana kallon fitilar. "Viper ya ce ""Ko dai ki gaya masa ya kashe fitilar nan, ko na haɗa idonsa da na motar na ɗauke" "musu wuta gaba ɗaya""" "Fitowa yayi daga motar ya ƙaraso in da suke, ya kalli Viper, sai dai a wannan karon ma ya ji" "wannan faɗuwar gaban. Kallo ɗaya ya yi wa Viper, ya tuna a in da ya ganshi." "Ya kalli Nabila ya ce ""Arfa waye wannan? Irin wannan samarin kuma ki ka koma kulawa?""" "Ta kalli Viper sannan ta kalli Nasir ta ce ""Yaya me yayi maka ne? Na gaya maka tun waccan ranar" "he's my client""" """Client like how? Shi ne zai din ga biyoki har gida? Get inside kafin na kwaɗeki a wurin nan""" Addu'a take Allah ya sa kar Viper ya hasala. "Viper ya ciro wata fitila daga aljihunsa, ya haske idon Nasir, ya matsa daf da shi, Viper ya fishi" "tsawo sosai ya ce ""Talk to me, like a man, baka din ga yi mata shouting ba""" Ya ja da baya ya kalli Nabila ya yi mata alama da hannunsa na i will call you. "Ta jinjina masa kai, shi kuma ya juya zai tafi." """Waye kai?"" Nasir yayi maganar cikin dakewa, dan muryar Viper kawai a bar tsoro ce." "Viper ya juyo, ya kalli Nabila, da ta bashi tausayi, ban da tana wurin, kuma bai san me abun da zai" "aikata ka iya haifarwa ba, da sai ya sakawa Nasir iraƙi sannan ya gaya masa waye shi, kamar yadda ya yi wa tijjani yayan yar madara." "Ya kalli Nasir ya ce ""A man"" ya faɗa a taƙaice." "Nasir ya waiwaya, ya kalli Nabila zai fara masifa, amma ta zura da gudu ta shige gida." "Rufa mata baya yayi, yana masifa har ɗakinta ya bita, yana yi mata bala'i, ganin yana neman ya" tozarta ta a gabam mutanen gidan ya sanya ta fara kiran sunam Abba da ƙarfi. "Aikuwa Abba ya saukko daga kam benensa yana faɗin ""Wai waye yake taɓa mini yarinyar nan, kai Nasir menene haka? Dukanta zaka yi? Shekara Ashirin da biyar sai ka kamata kana duka dan" "rashin mutunci?""" """Abba ba dukanta zan yi ba""" """To me ka yi mata take wannan kururwar haka?""" """Abba gaba ɗaya Arfa ta canza, ta tsiri wasu irin ɗabi'u na rashin gaskiya, rannan na je ofishin ta, na tarar da ita da wani mutum, gaba ɗaya bai yi kama da mutanen kirki ba, yauma still ta tsaya da wani a waje, maimakon cikin gida tana zance, kamar dai wancan mutumin ne, gaba ɗaya bai yi" "kama da mutanen ƙwarai ba""" "Abba ya kalli Nabila ya ce ""Arfa, yayanki a kan gaskiya yake, ni kaina shige da ficen samarin nan" "naki, ya fara isata""." """Abba, wallahi ba mutumin banza bane ba, kuma ko mutumin banza ne, ba wata muguwar alaƙa" "ya gani tsakani na da shi ba, na gaya masa client ɗina ne kawai, amma yaƙi yadda kwanan nan komai nayi sai ya din ga zargina na rasa me nayi masa gaba ɗaya""" """A'a Arfa, Nasir yana cikin masu goyon bayanki a gidan nan, tun da har ya magantu, to ya fiki gaskiya, ki san irin mutanen da zaki din ga tsayawa, kuma ki din ga mu'amala da su, yanzu a cikin samarin nan naki, lallai ki duba mai nutsuwa ya zo in ganshi, nima zan fi samun kwanciyar hankali ace kina ɗakinki"" Nabila ta yi shiru, Abba yayi ta yi mata nasiha, bayan ya gama ya fita," Nasir ya bi bayansa. "Nasir ne ya bi bayan Abba, suka shiga ɗakinsa ya ce ""Abba, yakamata ka ja wa arfa kunne, wasu" "abubuwan take yi kwanan nan, shishishigi a kan wasu abubuwa. Ta sako wannan barrister Naja'atu Bunkure a gaba, kar ta je ta janyo wa kanta wata matsalar""" "Abba ya ce ""To ai ni kaga ban sani ba, ban san me take aikatawa ba wasu lokutan, amma babu" "komai, zan yi mata nasiha, ka san ba kowane lokaci faɗa yake tasiri ba""." "Nasir ya ce ""Haka na, sannan kuma Abba""" """Sannan kuma me, ina jinka""" "Ya ɗan muskuta ya ce ""Abba dan Allah ka bani auren Arfa""" "Take annurin fuskar Abba ya ɗauke, ya ce ""Auren arfa kuma?""" Ya ɗan yi shiru yana wasa da yatsunsa. "Abba ya numfasa ya ce ""Kenan kishi ne ya saka ka shigo kana yi mata faɗa?"" Ya girgiza kai ya ce" """A'a Abba, ba haka bane ba""" """To, Nasir kai ɗa na ne, hakazalia arfa, babu wani banbanci a tsakaninku, dan haka ba zan so abun da zai cutar da ɗayanku ba. Ba zan manta abun da mahaifiyarka tayi mini a kan yarinyar nan ba, kuma haryanzu ina kallon irin ƙiyayyar da take nuna mata, na daɗe da gane kana sonta, amma ina fatan ta samu wanda hankalinta zai kwanta da shi. Muddin ka aureta mahaifiyarka ba zata taɓa barinta ta zauna lafiya ba." "Ni bani da matsala da son da kake yi mata, amma ka nemi yardarta, da ta mahaifiyarka tukuna""" "Nasir ya ce ""To Abba, na gode sosai"" ya tashi ya bar ɗakin." "Nabila banɗaki ta shige, ta rufe ƙofa ta kira Viper." """Yanzu fisabilillahi ka kyauta mini kenan? Ka saka an yi mini faɗa, Allah ne ya rufa mini asiri," "dan Allah ka daina zuwa in da nake, gara ka kirani na zo da kaina""" """Ki je ki yi tunani a kan abun da na saka ki, ki san abun yi sati biyu kawai ki ke da shi""" """Ya kake bani umarni ne a haka, ka din ga lallaɓani mana, why are you always bossy ne? Sai da safe zan duba na ƙara effort, ina iya ƙoƙarina a kai, tauye ni ake yi, ka san ba ni da kowa sai" "Allah ni, amma ka yi mini addu'a in sha Allah ni zan kawo ƙarshen bunkure""" """Allah ya sa"" ya kashe wayar." *** "Ramma ce ta ƙurawa wayar Abdul ido, ta kalli ƙofar banɗaki, yana ciki yana wanka, ta miƙa hannu ta ɗauka ta bar ɗakin." "Bai jima ba ya fito daga banɗakin, sai dai ya nemeta ya rasa a ɗakin, ya fita nemanta, ya tafi" "kitchen, ya tarar da ita a tsaye a kitchen, da wayarsa a kunnenta cike da rashin gaskiya." "Babu tsammanni ta ji ya fizgota, ya kwaɗa mata mari, har sai da ta faɗi ƙasa." "Ya duba call logs ɗin sa, ya ga ba a ɗaga kiran da ta yi ba, ya kalleta a matuƙar fusace ya ce" """Saboda kin ga ina ɗaga miki ƙafa shi ne zaki tsallake gona da iri, zaki wuce makaɗi da rawa? Bari na koma miki ainihin Abdul ɗina, kuma wannan huakan da ki ka yi, dai-dai yake da sake" "nesanta kanki da iskar 'yanci. Kuma bari na sake gaya miki, babu wani mahaluki da ya isa ya rabani da ke a duniyar nan ko waye shi, idan kin ga dama ki cigaba da ƙoƙarin lallai sai kin bar gidan nan, zaki ga yadda zan yi da ke""ya fice daga kitchen ɗin ya bar a zaune, hannunta riƙe da" "kuncinta, hancinta har ya fara zubar da jini, saboda azaba." "Ta rasa me ma yakamata tayi, saboda zuwa yanzu zuciyarta ta ƙeƙashe, kukan ma ba iya yin sa" take yi ba. Ta ja wuri ta zauna sosai saboda jirin da take ji. *** "Sallama take yi a tsakar gida, ta ce ""Na shigo ko na koma?""" "Umma da take ƙofar kitchen ta ce ""Idonki kenan arfa? Yaushe rabonki da gidan nan?""" """Tuba nake umma, ayyuka ne sun yi mini yawa sosai, amma ayi mini afuwa dan Allah""" "Umma ta ce ""To Allah ya yi jagora""" """Amin umma, ina sumayya?""" """Tana ɗakinta""" "Nabila ta nufi ɗakin sumayya, ta sameta tana ta aiki a cikin computer, sallamarta kawai ta amsa," ta mayar da hankali ta cigaba da abun da take yi. """Sumy, dan Allah ki kalleni mana""" "Sumayya ta ɗago ta kalleta ta ce ""Idan na kalleki mai zai amfana miki, ni da nake munafuka?""" "Jiki a sanyaye ta ce ""Dan Allah ki yi haƙuri, nayi kuskure abun ne ya bani mamaki ya ɗaure mini" "kai""" "Tuni hawaye ya cika idon sumayya ta ce ""A yadda muke da ke, ban taɓa tunanin wani zai kawo" "miki aibuna ki yadda ba, ba tare da kin yi bincike ba, amma kai tsaye ki ka danganta ni da kalmar munafunci, baki san wahalar da nake ta yi dan kare rayuwarki ba""" "Nabila ma sai ta saka kuka ta ce ""Dan Allah masoyiyya kiyi haƙuri ki yafe mini, ɓacin rai ne, kin ga sam baki yi mini bayanin komai ba, na samu labarin an saka ki kina bibiyata, dole na shiga" "damuwa kuma ke baki gaya mini ba""" "Sumayya ta dubeta ta ce ""Waye ya gaya miki ana bibiyarki ta hanyata?""" """Ba shi da amfani faɗar, amma dan Allah waye ya saka ki bibiyeni, ki din ga kai masa rahotona?""" "Sumayya ta kalli Nabila da take ta share mata hawaye, Nabila cikin jin kunya da sanyin jiki, take" ta ƙara bawa Sumayya haƙuri. "Sumayya ta numfasa ta ce ""Honorable indabo ne""" "Nabila ta waro ido ta ce ""Indabo kuma? Meye alaƙata da shi? Me na yi masa?""" "Nan Sumayya ta warware wa Nabila yadda suka yi da Indabo, lokacin da ya ce taje gidansa su yi" program. "Hankali a tashe Nabila ta ce ""Amma meyasa baki gaya mini ba Sumayya?""" """Ya za ayi na gaya miki? Ya ce muddin ki ka sani, zaki iya rasa ranki, kuma na san dole zaki iya aikata wani abu, da zai sanya su yi miki illa, babban abun da ya bani mamaki bai wuce lokacin da muka yi waya da ke ba, ki ka ce kin haɗu da Viper, ya ƙara rikicewa gaba ɗaya, amma na tabattar masa da ƙarya ki ke yi, baki haɗu da shi ba, ina tunanin akwai wani abu a tsakanin sa da Viper," "dan cewa yayi, zai yi wa Viper tarko da ke, ya kama shi""" "Gaban Nabila ya faɗi, gaba ɗaya sai kanta ya kulle." """To tayaya zan zama tarkon da za a kama Viper? Meye alaƙata da shi?""" "Sumayya ta ce ""Ban sani ba, amma dan Allah ki nutsu, kar ki aikata wani abu da zai saka ya cutar da ke, wallahi rashin imanin mutumin nan ya wuce tunaninki, ke hatta a wurin aikina akwai masu saka mana ido, da kin zo sai su kirani, su ce me muka tattauna, har wayar da nake yi da ke suke" "bibiya shiyasa nake kiranki da wasu lambobin""" """Na shiga uku, to ni uban me na yi masa? Sumayya da wace lambar suke kiranki?""" """Private number ce, ba sa kirana da lamba"" zumbur Nabila ta tashi." "Sumayya ta ce ""Ina zaki je?""" "Tayi waje da sauri ta ce ""Zamu yi qaya kawai"" a tsakar gida ta yi wa Umman Sumayya sallama ta" fice. "Ƙaramar wayarta ta ɗauko, ta kira Viper, ya ɗaga a rikice ta ce ""Kana nan ne, gani nan zuwa""" """Ke tsaya mana, ki zo ina?""" """In zo wurinka mana ina cikin ruɗani da rashin fahimta""" """Koma menene ki nutsu, ki yi mini bayani ina jinki""" """Ni ba wani bayani da zan yi maka, kawai zan zo gani nan""." "Ya ce ""Hanya babu kyau, na gaya miki kar ki zo fa""" """To a ina zamu haɗu? Rayuwata tana cikin hatsari, ni kawai kana ina, na shga uku""" "Viper da yake zaune ya tashi tsaye ya ce ""Malama ki nutusu ki yi mini magana, kina cikin hatsari" "kamar yaya?""" "A fusace ya ce ""Na gaya miki hanya babu kyau, ana bibiyarki ko kin manta? Za a fara tracking" wuraren da ki ke zuwa yanzu haka. Ki tsaya ki saurare ni. """To ina jinka""" """Zan tura miki adress ɗin da zaki same ni, idan kuma ni in zo shikenan""" "Ta ce ""A'a kar ka zo""" """Ki samu wuri ki ajiye motarki, zan turo miki adress ɗin in da zaki same ni""." """To ka yi sauri"" ta cigaba da tafiya a motar, tana waige-waige ko zata ga wani yana bin ta." "Ya turo mata adress ɗin da zata same shi, ta ajiye motarta, ta bi adress ɗin." "Wurin kamar garden haka yake, ba kowa a wurin, sai manyan bishiyu, ga wurin sanyi mai daɗi." "Tana tsaye tana waige-waige, ta ciro wayarta, tana ƙoƙarin kiransa, kawai ta ganshi unexpected a" "bayanta, sakin wayar tayi ta hau ihu." """Menene?""" """Ba tsorata ni ka yi ba, sai ka zo kana wani sanɗa da na zura da gudu fa, ka daina wannan sanɗar""." "Ya kalleta ya ce ""Idan ban yi sanɗa ba, ban amsa sunan Viper ba, sai da aji hucina, ko bayan nayi" "ɓarna a ankare da na zo wuri, gani menene?""" "Ta ƙare masa kallo ta ce ""Ɗan beauty""" "Ya tsuke fuska ya ce ""Neman me ki ke yi mini?""" "Cikin damuwa ta ce ""Mu zauna, na gaji da tsayuwa""" "Suka samu wuri suka zauna, ta ce ""Dan Allah Viper meye haɗina da Indabo? Shi ya saka sumayya" take bibiyata. Ta gaya masa yadda suka yi da sumayya. "Ya numfasa ya ce ""To me zan yi miki?""" """Ban gane ba, ka gaya mini meyasa Indabo yake bibiyata, me nayi masa?""" "Cikin ko in kula ya ce ""Ya za ayi in sani?""" """Dan Allah ka gaya mini, kai ma fa ka tambayeni ko na haɗu da shi, me kake ɓoye mini ne? Dan" "Allah ka gaya mini mana""" """Meyasa liti ya rikice ranar farko da ya ganki, ya amince ya kawo ki maɓoyata?""" "Ta ce ""To ya za ayi in sani, ina tambayarka kana tambayata? Ka gaya mini mana""" Ya ɗago ya tsura mata ido. """Ka yi magana mana, dan Allah meyasa yake bibiyata, ta ce ya rikice lokacin da ya ji na ce na haɗ" "u da kai"" still bai yi magana ba." """Talk please""" "Zuciyarsa ya ji tana harbawa da sauri, ya girgiza kai ya ce ""Kamar na ji kin ce mamanki ta rasu" "ko?""" "Turɓune fuska ta yi ta ce ""wai ina ta rayuwata, kana tambayata wani abun daban""." """Nan gaba zaki so jin dalilin da ya sa na tambaye ki, bana surutun banza ni""" "Kamar za ta yi kuka ta ce ""To ni yanzu ya zan yi da wannan indabon?""" "Viper ya ce ""Ba ruwanki da shi, ni ne dai-dai shi, ki ji da bunkure karki manta, sati biyu kawai na" "baki ki yi mini aikina""" "Ta narke murya ta ce ""Nawa zaka bani ne da ka sakani aikin, ka san dai ba lawyer gwamanti ce ni" "ba""" """Nawa ki ke so?""" """Kai nake so"" gabansa ya faɗi, da ya tuna Jauhar sararta ce faɗar haka." """Kina wuce gona da iri"" yayi maganar yana kallon in da yake facing." """Daga zuwanka, ka saka DSP ya haɗa ni da Abba, an ce sai na duba samarina na fito da miji, sai" "ka aureni, tun da duk kai ka janyo koma menene""" """Are you serious? Ɗan ta'addan zaki aura kina gidan masu kaki?""" "Ta ce ""Eh mana, ka bani dama na zama yar suganka""" "Ya ɗora hannunsa a kan ƙirjinsa, ya ce ""Ki daina wannan wasan ba na son sa ko kaɗan, haryanzu ina jin motsin jauhar a cikin zuciyata. Idan ki na irin wannan maganganun ji nake tamkar na aikata zunubi mai girman gaske, babu wani abu da zan iya haɗawa da soyayyar jauhar a zuciyata, ki" "kiyaye wannan ki daina wannan wasan, kar ya zama gaske""." """Ba ka son yar sugar kenan sai madara ko?""" """Ke ki ka san sugan, ni ba na ta'amalli da shi ma""" """To zuma fa ko mazarƙwaila"" ya yi mata shiru." "Ta tashi ta ce ""Kar ka so ni ɗin, amma to ni ya zan yi da wannan indabon bashi da imani, kar ya" "kashe maka ni""" "Viper ya ce 'Idan ya kashe ki ya hutar da ni""" "Murguɗa masa baki tayi, ta kama hanyar tafiya. Sai da tai nisa sannan ya waiwaya yana kallonta." "Ita kanta murmushi ta yi, saboda yau ya sake, babu wannan alamar ƙuncin da damuwa a tare da" shi. *** "Da daddare Nabila tana kan social media, taga wani dogon rubutu, da aka yi, na jinjinawa Naja bunkure, a kan ayyukan ta na jin ƙai. Sumayya na ganin posting ɗin, tayi tagging ɗin Nabila." "A take Nabila tayi reposting ɗin post ɗin, tare da caption kamar haka *Lokaci yayi da yakamata mu san haƙiƙanin ayyukan da Bunkure foundation ke gabatarwa, shin da gaske dan talaka take yi, ko kuwa dan rufe ɓarnar masu ido da kwalli kawai take yi?." "Mu duba case ɗin yarinya zulaiha, da ya faru shekarun baya, wadda ta fuskanci cin zarafi, daga wani ɗan mai kuɗi, bunkure foundation sun shiga case ɗin domin su tsaya mata, a hukunta shi, amma ƙarshe sai labarin mutuwar zulaiha muka ji, ta kashe kanta ta hanyar shan fiya-fiya, shi kuma wanda ya aikata, yana shekarar ƙarshe na kammala karatun degree a ƙasar Amurika." "Bana ƙwaina sai da zakara, akwai tarin hujjoji da nake da su a kan maganata." "Jikinta na tsuma, ta yi posting ɗin, ta rufe data." "Tayi addu'oin kwanciya bacci, ta kashe wayarta, har ta rufe ido maganganun ta da Viper suka faɗo" mata. "Lumshe idanunta ta yi, amma maganar sa ta din ga kai komo a zuciyarta." "*Ba zan iya haɗa soyayyar jauhar da komai ba, dan haka ki ma daina wannan wasan*" "Dafe ƙirjinta ta yi, ta ce ""Na shiga uku, tausayin sa kawai nake ji, da wasa nake yi, me nake ji a" raina ne?' ta tambayi kanta. "Wasi-wasi ne kawai, ta bawa kanta amsa tare da kwanciya." "Washegari da safe bayan sallar asuba, ta kwanta ta sha bacci, kasancewar lahadi ce, babu aiki." "Sai wajen ƙarfe goma ta tashi, ta yi wanka ta fito ta shirya ta ɗauki wayarta ta kunna." "Jerin saƙonni ne suka din ga rige-rigen shigowa wayarta, bayan ta kunna data." "Messages kuwa, ga na barrister Habib, ga na summaya." "Ƙarƙashin post ɗin ta kuwa, comment ya kusa dubu, da masu kare Bunkure da masu zagin Nabila," kasancewar alherin bunkure galibi mutane suka sani. "Ta ɗaga kiran wayar sumayya da yake shigowa, ta ce ""Ya ne?""" """Nabila daga tagging ɗin ki a post, kin rikita media""" "Nabila ta ce ""Ai makaho ba ya sanin ana kallonshi sai an taɓa shi, bar su su gama haukan da kare" "ta, ina nan zan saki maganar ramma bayan an kuma zaman kotu""." """Amma Arfa kar fa ta yi miki wani abu""" """Ba abun da ta isa ta yi, ai ina da hujjoji """ """Allah ya ƙara tsare ki, zan cigaba da nemo miki sahihan bayanai a kan ta""" "Naja ta kalli posting ɗin ta yi murmushi ta ce ""Bari na nuna wa yarinyar nan ainihin kalata da take" son gani. "Kira Nabila ta gani da private number, babu tsoro ko fargaba ta ɗaga." """Wane irin move ne haka, kin san mutanen nan ba za su barki ba ko?""" "Nabila ta ce ""Kai ka bani aiki ka ce nan da sati biyu, aka yi sara a kan gaɓa, sumayya ta yi tagging" "ɗina a kan post ɗin, na ga ya dace na tofa wani abu""." "Viper ya ce ""Shikenan, amma ki shirya matakin da za su ɗauka a kanki""" "Nabila ta ce ""Ina da kai ai, idan na je aiki zan kiraka""" "Nasir ne ya faɗo ɗakin ta ya ce ""Nabila, wai meyasa baki da hankali ne""" "Ta kalleshi ta ce ""Me nayi kuma?""" """Ban ja miki kunne a kan Naja'atu Bunkure ba? Kin je kin tsokanota, gashi an fitar da sanarwa" "hukumar DSS suna nemanki, an shigar da ƙararki for defomation of character""." Ayshercool 08081012143 *KARFE A WUTA* *63* ₦500 ne via 0009450228 Aisha Adam jaiz bank sai shaidar biya ta 08081012143 Wanda za su jira document 1K ne. 90009343 'Yan Nijar ku turo katin airtel na 300fcfa Arewabooks ayshercool7724 "Ta ce ""Ban gane ba, su DSS ɗin uban me na yi musu suke nema na, kamar wata 'yar ta'adda""." """Shut up, ina magana kina yi mini gatsali, abun da nake ta ankarar da ke kenan ai, matar nan tafi" "ƙarfin ki, ba sa'ar yinki ba ce ba, amma saboda zunzurutun taurin kai, da zigar da ki ke ɗauka, kin cigaba da abun da ki ka ga dama, da yake ba kya son zaman lafiya""" """Ina son zaman lafiya DSP, kuma duk abun da nake yi da hujja nake yin sa, dan haka a gaban kotu" "yakamata ta ƙalubalance ni, ba wurin DSS ba, uban me nayi mata?""" """Look arfa, matar nan ba zata bi abun da doka ta tanada ba, dan tana tsoronki, koma menene za ta yi shi ne, dan kawai ta tozarta ki, ta nuna miki ke ɗin ba kowa ba ce ba, kuma babu abun da wani ya isa yayi. Ko hurumin DSS ne su kama ki, ko ba hurumin su ba ne, za su yi abun da ta ce ne," "kuma babu mai ƙwatarki""" "Kawai Nabila ta saki murmushi ta ce ""Ai DSP duk wanda ya ce ayi wasan jifa, ya san me ya taka ne? Dss ai ba lahira bane ba, a yadda nake ji na yanzu, hukuncin Allah shi ne abu mai razanarwa da firgitarwa a gare ni. Ban fara wasan ba, sai da na tabattar da ingancin ƴan wasa na. Ita taƙ amarta tana da manya a sama, da zasu tsaya mata, abun da ta manta da ita da manyan banzan nata shi ne, ƙanan na ƙasa su suka zama tsaninsu wurin zuwa ƙololuwar in da suke tafka tsiyar, daga zarar na ƙasan sun yi bore, na saman dolennsu su shiga hankalinsu, ita ta iya Black market ni ta" "hanyar shari'a zan nuna mata kuskurenta legally""" """Shut up a beg, uban me ki ka taka, mara hankali kawai, zaki tayar wa da mutane zaune tsaye"" tayi" masa shiru ya fice yana sababi. "Nan fa yan gidan, suka samu topic of discussion, ko a jikinta, ta gama shirinta tsaf, Baba magajiya" "ta iske a falo, ta ce ""Yauwwa arfa, dama ke zan zo na kira, babanki na nemanki yanzu da gaggawa""." "Duk da sauri take yi, amma ta nufi ɗakin Abba, ta iske shi da shi da Nasir, hankalinsa a tashe." """Arfa, me ki ka je ki ka aikata? Yayanki ya ce kin yi posting a social media kin tayar da tarzoma" "jami'an tsaro suna nemanki""" "Nabila ta ce ""Wallahi Abba ban tayar da tarzoma ba, gaskiya kawai na faɗa, kuma haryanzu a" "hukumance ni ban ga cewar DSS su kama ni ba""" """Ƙaniyarki da ke da hukumar, amma dai kin san ni yanzu ba da bane ba da zaki je ki tsokano mutane ko, tsokanar taki ma, ki ka kasa yin dai-dai da ke, sai in da zaki sha wahala, haka kurum ki tayar mana da zaune tsaye, muna zaman lafiya a ga DSs sun yi mana dirar mikiya a gida, kamar" "wasu yan ta'adda""." """Abba ba su da hurumin kama ni, ban ɓata wa kowa suna ba, gaskiya kawai na faɗa""" """Rufe mini baki, ko na saka ki tsallen kwaɗo yanzun nan, mara kunya fitsararirriya""." "Wayarta ce take ringing, ta ce ""Bari na ɗaga waya""" """Hello yaya Habib""" """Nabila kina ina ne?""" """Ina gida, yanzu zan fito wurin aiki""" """Maza ki hanzarta ki ƙaraso, na ga wani rumors yana yawo, a kan posting ɗin da ki ka yi jiya," "wai Dss suna nemanki, duk da ba officially na ga sanarwar ba, magoya bayanta ne suke ta zuzuta maganar, maza ki ƙaraso mu riga su ɗaukar mataki""" """To Barrister, gani nan in sha Allah"" ta sauke wayar ta ce ""Abba daga law firm ɗinmu ne, bari na" "tafi""" """Ki tafi ina, an ce ana nemanki?""" """Eh zan je in ji me za su ce ne""" "Abba ya kalli Nasir ya ce ""Ka kai ta law firm ɗin na su, duk yadda ake ciki, ka kirani, zan je na ga" "likita sai na biyo""" "Sam Nasir ba haka ya so Abba ya yi wa Nabila ba, ya so ya ja mata kunne sosai, ya taka mata" "burki a kan abun da take yi, amma bai yi hakan ba." "Suna tafe a mota, ba ta kula shi ba, sai waya take yi da sumayya da murtala, sumayya ta ce zata ƙ" arasa law firm ɗin su Nabila. "Tana sauke wayar sumayya, kira ya shigo, an rubuta Confidential a kan lambar." "Ya kalli Nabila, ya kalli wayar, kasancewar Bluetooth ne a kunnenta, ya sanya ta amsa dan" kaucewa zargin sa. """Hello boss""" "Viper ya ce ""Ya ake ciki? Sun kama kin ne?""" """So ka ke su kamanin kenan?""" """Am asking? Ya ake ciki?""" """Eh, ba su da hurumin kama ni, yanzu ina hanyar law firm ɗin mu ne, Oga na a wurin aiki ya ce" "maza naje, a riga su ɗaukar mataki""." """Ok, amma you over react, na so ace a sannu ki ka bi abun, amma yanzu zamu raba hankalinsu" "biyu, zan yi wa Indabo aike, hakan zai sanya su kasa tsayar da hankalinsu wuri guda""" "Ta kashingiɗa da jikin seat ɗin mota ta ce ""Aiken me?""" """Ke da waye a motar nan?""" """Meyasa ka tambaya?""" """Akwai rashin sukuni da tsoro a cikin maganarki, ke da wayar""" "Nabila ta waro ido ta ce ""Kai ya aka yi ka gane, vi Saurin katse maganar tayi, da tuna katoɓarar" da kusa tafkawa. "Tayi gyaran murya ta ce ""Zamu yi magana anjima, yanzu ina cikin zullumi jami'an tsaro za su" "kama ni, ka bari na yi salati na nemi agajin Allah""" "Viper ya ce ""Ok"" ya kaste kiran." """Da wa ki ka yi waya?""" "Ba tare da ta kalli Nasir ba, ta bashi amsa da abokin aikina ne." *** "Ramma ta takure kanta sosai da sosai, tun da Abdul ya dake ta, ya fice daga gidan ba ta sake ganinsa ba, itakaɗai take kwana take tashi, kuma ya ɗauke wayar da ya bata, da take kiransa a ita, hatta system ɗin sa guda ɗaya da yake ajiye mata, yana koya mata computer ko tayi kallo, dan har fina-finai na hausa, yake yi mata downloading dan su din ga ɗebe mata kewa, gaba ɗaya ya haɗa ya kwashe, ƙofar da zata fito da ita, ta sauka daga kan bene ma zuwa falon ƙasa, duk ya haɗ" a ya rufe. "Sam ba ta ko iya cin abinci, damuwa ta dawo mata sabuwa fil, ta rasa abun da yake yi mata daɗi" baki ɗaya. "Tana zaune bayan sallar isha'i a bedroom, ta ji ya buɗe ƙofa ya shigo, a razane ta waiwaya ta ɗan" ja da baya. "Ya ɗan tsura mata ido, sannan ya mayar da ƙofar ya rufe, ya nufi in da take hannunsa da leda." "Ya ajiye ledar, sannan ya zauna a kusa da ita, amma ta sake ja da baya." """Guduna kuma ki ke yi yau?"" Da ya motsa sai ta zabura, dan gani take dukanta zai kuma yi." "Shammatarta yayi, ya janyota jikinsa, ya rungumeta a ƙirjinsa ya ce ""Am sorry please, ki yi haƙ" "uri dan Allah"" ta yi shiru ba ta ce masa komai ba." """Ki yi haƙuri, tsantsar tashin hankali da na shiga ne, ya sanya na aikata miki abun da nayi, bana son gardama da taurin kai, tun da ki ka ga na ajiyeki, duk da irin son da nake yi miki, da magiyar da ki ke yi mini, ban mayar da ke gida ba, akwai matsala ne, mamanki ina zuwa wurinta, na tabattar mata da kina cikin ƙoshin lafiya, abin da ki ka yi shirin yi, barazana ne ga rayuwarki. Wallahi regret ne ya hanani dawowa tun da na fita na nutsu, gaba ɗaya nake cikin damuwa, amma" "ki yi haƙuri dan Allah""" "Tayi lamo a jikinsa, amma taƙi magana." """Rahama talk dan Allah, ki yi mini magana mana ko na ji daɗi dan Allah ki yi haƙuri ki yafe mini, son da nake yi miki ne ya sanya na ga abun da ki ka aikata barazana ne ga cigaba da" "kasancewarmu tare, ki yafe mini"" ai kamar gunki, taƙi cewa uffan." "Ya ɗago fuskarta, yana kallonta, amma ta sunkuyar da kanta ƙasa." "Ya janyo ledar gabansa, ya buɗe tsire ne fal a ciki, ya ce ""Ki ci abinci, duk kin faɗa kwana biyu," "dan Allah ki yafewa Abdul ɗinki, ba zan ƙara dukanki ba""" "Ta saka hannu ta share hawayenta ya ce ""Yauwwa babyna, ai na zaki yafe mini, kina da yafiya shiyasa nake ƙara ƙaunarki Rahama, Allah ya yi miki albarka ya shirya miki ni"" da ƙyar ya din" "ga bata abincin a baki, ta ci kaɗan ta tashi, sam taƙi sakar masa fuska." *** "Nabila suna zuwa law firm ɗin su, Barrister Kabir ya balbaleta da faɗa, Nasir ma ya taya shi, akan kasadar da ta yi." "Duk da Nabila ba ta son faɗa a rayuwarta, amma ko a jikinta, ta maze tana cunkusa baki." "Barrister Habib ya ce ""Dan Allah ku yi haƙuri haka, aikin gama fa ya riga ya gama, ta riga ta aikata, sai a san abun yi, kuma wannan duk ba abu ne na tayar da hankali ba, in dai mutum yana da gaskiya, ai faɗa ba nasa bane ba." Nabila shigo office mu yi magana. "Barrister Kabir ya ce ""Naga kamar goya mata baya kake yi Habib, idan kuka janyo abun da ba" "zaku iya ba, to ku tsaya can, kar ku raɓa ni a ciki""" """To barrister idan ba a goya mata baya ba, kware mata baya zamu yi, ma'aikaciyarmu ce, tayi abun da wani bai yi yinƙurin yi ba, ai kamata yayi a duba, idan akan gaskiya take, a ƙarfafeta, shigo mu" "yi magana""" "Nabila ta shiga cikin office ɗin sa, ya ce ""Good girl, i like your confident, a lady of her words, kin" "dage sai kin cimma burinki a kan matar nan""" "Ta ce ""Yanzu dai ba wannan ba, meye abun yi, kafin a zo a kamani, nima su saka a kaini prison a" "ajiyeni babu Shari'a kamar yadda suka yi wa Viper""" """Suka yi wa Viper ita da wa?""" "Nabila ta ce ""Oho mata, shi ma wannan case ɗin ina nan zuwa kansa, zata gane bata da wayo ai""" "Yayi murmushi ya ce ""Ba wannan ba, na yi wa Bashir ma magana, yana hanya, zamu yi maza mu" "shigar da ƙara, a kan lallai kotu ta dakatar da kamun da aka ce Dss su yi miki idan ma da gaske zasu kamakin, ba su da wannan hurumin, sannan su daina yi miki barazana dan kin faɗi albarkacin" "bakinki""" """To ayi sauri ayi, dan wani update ɗin zan saki, da ni take zancen""" "Duk da hantarar da Barrister Kabir ya yi wa Nabila, tare da shi, da sauran lawyoyin law firm ɗin," "suka haɗu suka tattara bayanai, da hujjoji da za su kai kotu, dan hana kama Nabila." "Suna can suna ta ƙoƙari, Nabila suka keɓe da Sumayya, ta tura mata videon yaron da ya ketawa" "zulaiha haddi, a cikin abokansa a ƙasar amurka." "*Wannan shi ne Najib, wanda ya keta wa yarinya zulaiha haddi, har ta kaita ga rasa ranta, a shekarun baya, shin ina shari'ar ta tsaya? Ko ya fi ƙarfin doka ne, dokar a kan talaka kawai take aiki?" "Kwana kwanan nan, mun ga yadda labarin wani matashi ya cika dandalin sada zumunta, a kan yadda aka tsare wani matashi shekara goma sha biyu, a gidan gyaran hali, bisa zargin sa da aikata fyaɗe, sai bayan shekaru goman nan, a ziyarar da wani bawan Allah ya kai gidan, ya tausaya masa, ya tsaya masa aka cigaba da yi masa shari'a har aka gano ba shi da laifi, saboda shi talaka ne ya sanya Bunkure foundation ba ta shiga ire-iren cases ɗin nan, sai dai na mata kawai? Me zai saka ace mata kawai foundation ɗin take tsayawa ban da maza? Anya babu wata maganar a ƙasa?." "Wannan ra'ayina ne a matsayina na ƴar ƙasa, wanda yake da ja, a gaban Alƙali zai ƙalubalance" "ni, ba wai a din ga yi mini barazana ba* tayi posting ɗin tana murmushi, ta ce ""Sumy na zama celeb fa""" """Zaki ci ƙaniyarki ke da celeb ɗin, kina kan sirɗin duniya kina rashin mutunci, akwai buƙatar mu" "nutsa sosai, mu cigaba da samo hujjoji, dan mutane su yadda da abubuwan da ki ke tonawa, dan na san haryanzu akwai masu tantama a kai""" """Haka ne, wannan kuma sai idan muka sake tsayawa a gaban kotu a kan case ɗin ramma""" """Allah ya ƙarfafeki, ya baki sa'a""" """Amin godiya nake masoyiyya""" "Sumayya ta ce ""Amma Nabila ya za ayi da Indabo ne? Ina tsoron mutumin nan, kin ga kuma shi babba ne, tun a lokacin na so na kai report, amma yayi mini kashedi a kan haka, babu ma wanda" "zai yadda da ni, saboda muƙaminsa""" "Nabila ta ce ""Rabani da zancen wannan mutumin, ni yanzu wannan matar ce a gabana, shi kuma" "akwai dai-dai shi""" """Wa kenan?""" Nabila ta basar da zancen ta shiga wani. *** """Indabo ka yi wani abu a kan lamarin nan, lallai a kama yarinyar nan a koya mata hankali, ban san da me take taƙama ba, ba a taɓa samun tsageran da yayi mini abun da take yi mini ba, idan fa asirina ya tonu, kuma naku ya tonu wallahi""" """Kar ki damu, muke da ƙasar fa, babu abun da ta isa tayi, na riga na bayar da order da ta kamata""" "Ta kashe wayar, cikin fushi, tana mamakin ƙarfin halin Nabila, manyanta ma sun gaji sun ƙyaleta," "ba a iya ja da ita, amma yanzu yar ƙaramar alhaki ta sakota a gaba." "Indabo ya daddana wayarsa, ya saka a kunnensa, ""Barka da wannan lokaci distinguish senator""" """Barka dai, ya ake ciki ne maganar yarinyar? Na ji kun ce Dss su kamata ya ake ciki, dole fa a" "toshe duk wata hanya da za a tonawa bunkure asiri dole a tosheta""." """Sir yarinyar nan fa tana da wayo, kuma tana da wanda suka tsaya mata, ta tafi kotu, ta ce lallai a" "hana kamata kuma ba wanda ta ɓatawa suna, sai dai bunkure ta ƙalubalanceta a gaban shari'a""" "Ya numfasa ya ce ""Haka ta ce? Wane alƙalin ne? Wace kotun ce zan bayar da umarni a bi" "umarninta a ƙi bin nawa""" """Honorable ka gane wani abu, abun nan fa ya haɗa da social media, ba zai yiwu mu yi abu gabaga ɗi ba, su kansu ƙungiyar lawyoyin ba zasu bari ba, kuma madam tana da magauta a cikin su kansu lawyoyin, za su iya taimaka mata, idan aka yi over reacting, to asirin da ake gudun tonuwarsa zai" "tonu""" "Indabo ya ce ""Shikenan, na fahimta""." *** "Madaki ya kalli ƙafarsa, ya kurma wani irin uban ihu, tamkar mahaukaciya, Lakwari ya ce ""Dan Allah ka yi haƙuri ka daina wannan ihun, hakan ba mafita bane ba""." """Ka rabu da ni nayi ihun nan, sai na kashe yaron nan, abun kunya ne ace kamar ni, ƙasƙantaccen" "maƙiyina, ya ga bayana ya sabauta rayuwata, sai na kashe mai zamani na ƙarar da zuriyar su*." "Lakwari ya kalli ƙafar madaki, ta kumbura kamar mai dundumi, sai wani irin koren ruwa ne yake fita daga cikin ciwon ga wari da yake yi, ga maganin da aka bashi, aka ce ya din ga sakawa, ya" "sanya raunin ƙara jagwalgwalewa, ko iya taka ƙafar baya yi." """Madaki, ka yi haƙuri mu je asibiti a duba ƙafar nan, ni fa ban ga alamar ciwon nan yana" "warkewa ko zai warke da haka ba, ƙara jagwalewa yake yi""." """Idan na je asibiti asirina tonuwa zai yi, idan lakwayen nan suka san alkadarina ya karye na shiga" "uku, kai ka san ta'adin da na yi ai""" """Haka ne, amma duk da haka yakamata muje asibiti a duba ƙafar nan, tun da babu sauƙi a ciki"" ya" din ga lallaɓa madaki har ya samu ya amince. "Viper yana tsaye tare da su liti, ɗan mama ya shigo, Viper ya ce masa ya ake ciki?" """Komai normal, saƙonka ya isa cikin aminci da kwanciyar hankali. Na shiga area na yi bincike sosai, babu wanda ya san in da madaki yake, amma an tabbatar mini da yana jinya, kuma lakwari" "ne a tare da shi, sai dai ba a san in da yake ba""" "Viper ya zaro russia, ya jujjuyata a hannunsa, ya kalli ɗan mama ya ce ""Ka nemo duk in da suke, ina son ka samo target mai kyau, in da zan ritsa lakwari, na san ƙafarsa ɗaya ta mutu zuwa yanzu," "zan hari wani wurin na daban kuma""" """Sai da kai ubangidana, abun da ka ce shi za ayi""" """Bari mu ga respond ɗin da Indabo zai yi, idan ya ga saƙona""" *** """Hello, barka da wannan lokaci""" """Yauwwa barka sir""" """Ina magana da justice maijidda ɗan rimi ne""" """Eh nice""" """Good, ina fatan kin gane mai magana?""" "Tayi murmushi ta ce ""Ya za ayi na ce ban gane ba sir, na gane""" """Masha Allah, akwai ƙara da wata yarinya da sauran lawyoyi suka shigar gabanki, barrister Nabila Yusuf maitama, a kan ki hana Dss kamata, da kuma hana yi mata barazana, ki bi tsarin doka ki yi abun da ya dace, na san dole za a nemi ki yi wani abu ba dai-dai ba, idan ki ka yi akasin abun da doka ta tanada, zai iya janyo wa ayi seizing license ɗinki, nima umarni aka bani daga" "sama""" """In sha Allah sir, zan yi abun da ya dace ba tare da son rai ba, na gode sosai da sosai""" "Ya ce ""Yauwwa""" "A media kuwa aka cigaba da samun musayar ra'ayi, kowa da abun da yake faɗa, waɗanda bunkure" "foundation ta cutar, suma suka samu damar bayyana ra'ayoyin su, duk da mutanen da suke ganin hassada ta sanya ake yi wa bunkure hakan sun fi yawa." "Bayan Bunkure ta gama sakankancewa, ta gama da babin Nabila, sanarwa ta fita, kotu ta haramtawa Dss kama Nabila, ko yi mata barazana a kan abun da take aikatawa, a matsayin ta na" "ƴar ƙasa, tana da ƴancin faɗar albarkacin bakinta." "Indabo kuwa yana cikin majalisa, ya zauna, ya fara ƙoƙarin buɗe envelope ɗin da aka bashi, aka" ce an aiko masa da ita. Ya buɗe ta ya ƙara ciro wata ƙarama a ciki. "Hoton ciki ya kalla, Simon ne tare da Viper a cikin hoton. Simon yana daga cikin yaran da Indabo ya lalatawa rayuwa, kuma ya zama ɗaya daga cikin masu yi masa hidima, a wannan gidan da suke sheƙe aya da shi da ire-iren sa, da suka sanya neman duniya a gaba." "Wanda shi ne ya kuɓutar da Nura guduma daga gidan, ya saka shi a mota, ya haɗa shi da wani ya kai shi kano. Shi kuma ya gudu daga gidan, indabo ya bayar da cigiyar a nemo simon, ya bayar da kwangilar a kashe shi, aka tabattar masa da an kashe shi, amma hoton ya nuna masa kwanan nan" aka ɗauka. "Cikin tashin hankali yake sake kallon hoton, tabbas na kwanan ne hoton, saboda Viper ya ƙara" "girma, fuskar nan babu annuri a tattare da ita ko kaɗan." """Simon yana raye kenan?"" Ya tambayi kansa, ya juya bayan hoton ya ga an rubuta Viper da jan" abu. "Bai san ya tashi tsaye ba, sai da na kusa da shi ya ce ""Honorable, ya aka yi ne? Me kake gani?""" """A'a ba komai, ulcer ta ce ta tashi"" ko izini bai nema ba, yayi waje daga cikin majalisar kamar" babbar rigarsa zata harɗe shi ya faɗi. *** """Assalamu alaikum, Assalamu alaikum ba kowa a gidan ne?""" "Walid ya ce ""Wa'alaikum Salam, barrister yau ke ce?""" """Ina wuni Yaya walid""" "Yayi murmushi ya ce ""Lafiya ƙalau, yau kin tuna mini da ƙanwata jauhar""" "Ta ce ""Allah sarki, Allah ya sa tana aljanna""" "Ya amsa da ""Amin""" """Ina ogan yake?""" """Ya tafi caji""" "Ta ɗan yi turus ta ce ""Caji kuma, kamar wani power bank?""" "Yayi dariya ya ce ""Ya ce, ya fita shan iska yana wurin wancan dutsen""" "Ta ce ""Ok, bari na je""" """To Allah ya sa yana ƙasa, ba saman ya hau ba""" "Nabila ta ce ""Idan ma saman ya hau, zan bi shi""" "Da tazara daga gidan zuwa dutsen, duk da daga gidan sai ka zata taku kaɗan zaka yi ka ƙarasa." "Daga nesa ta hango shi, a zaune a ƙasa-ƙasa, ta hango tashin hayaƙi a wurin." "Ta ƙarasa da ƙyar, dan duk ta gaji, kwali guda ne a gabansa, ta ƙarasa ta kai hannu ta ɗauke, caraf ya riƙe hannunta. Tsorata tayi, dan cikin sanɗa ta ƙarasa wurin, amma har ya ankare da ita" ya hanata ɗauka. "Ta haɗe rai ta ce ""Sakar mini hannu, nan ka gama cewa zan saka a lungu, shi ne zaka wani riƙe" "mini hannu?""" """Ni na kawo ki? Ban ce ki daina zuwa ba ma?""" """To ko kirana ba ka sake yi a waya ba, idan ma an kama ni, ko ma menene ya same ni, ba ruwanka ko?"" Tari ta fara yi, saboda hayaƙi, sakar mata hannu ya yi, tayi sauri ta ɗauke kwalin sigarin da" "ashanar, ta tura a jakarta." "Satchet ɗin maganin da ya leƙo a gefen aljihunsa, shi ma ta ɗauke, tana mita ""Wallahi Allah ya hore maka taurin kai, wannan shaye-shayen ne ba zaka daina ba ko?"" Ya ƙura mata ido, saboda" jin tana ƙamshin turaren florie irin na 'yar madara. """Ina magana kana kallona, baka tausayin lafiyarka, yanzu duk ƙoƙarin jauhar a kanka ya tashi a" "banza, yawaita yi mata addu'a, istigfari da mayar da hankali a kan addu'a, shi zai rage maka damuwa, amma baka ji, kullum cikin hayaƙi, da shan miyagun ƙwayoyi""" """Faɗa fa ki ke yi mini""" """Au kar na yi maka? Ka daina mana da na yi maka mana, wannan abubuwan da kake yi ba shi yake nuna halaccinka a gareta ba, ka daina abun da ka ke yi, ka zama mutumin kirki, shi ne cikar" "halaccinka a gareta""" "Kawar da kansa gefe yayi a hankali ya ce ""Angry bird""" """Ni ce bird ɗin? Wallahi ni ba tsuntsuwa ba ce ba, da ba ka neme ni ba, ni gani ai na zo, ba a" "kama ni ba fa""" """Dama na san ba za a kama kin ba ai""" """Haba ya aka yi ka sani?""" """Bani wayarki"" ta ciro wayarta ta miƙa masa." "Ya ciro tasa ya danna, sannan ya saka a kunnensa." "Muryar P.A ta fito rangaɗau a waya ya ce ""Hello""" "Viper ya yi shiru, bai ce komai ba." "Ya sake cewa ""Hello"", still bai yi magana ba." """Waye ne ya ɓoye lamba yake kirana, idan ba za ayi magana ba, zan kashe, waye?""" """Mai zamani ne"" waro ido P.A yayi ya ce ""Wane mai zamanin?""" """Zuwa yanzu, na san saƙona ya iske shi, ya shirya, zan bayyana a lokacin da bai yi tsammanina ba," "kuma ya daina wahalar da kansa a kan lallai sai an kamani, ko da an kama ni, nafi ƙarfinsa, ya kuma jirani aikena na biyu"" ya katse wayar yana ajiyar zuciya." """Kai, Oga kana burgeni, ka din ga acting kamar a film ɗin indiya hausa, wai dan Allah, a ina ka" "ko yi wannan halin naka?""" Ya jefa mata wayarta jikinta. """Amma wait, wai ne ka ke yi a wayata ne baka gaya mini?""" """Yaushe zaki fara shari'ata?""" "Nabila ta ce ""Shari'arka akwai sarƙaƙiya boss, sonake na gama da ta ramma gobe in Allah ya" "kaimu zamu koma kotu."" Ya jinjina mata kai." """To zaka fara bani kuɗin aiki ai, ka ɗan ragen wani abu, na din ga zuba mai, tun da na je fa aka" "nuna mini file ɗin ka, nake ta up and down, ina tattara abun da zan tattara. In sha Allah zan zama sanadin daina zubar hawayenka""" """Dama kuka nake?""" """A'a murna ka ke yi""" "Ya girgiza kai ya ce ""Ko matata da muna tare, ta daɗe kafin ta iya kallona ta yi mini magana, balle" "ta yi mini baƙar magana, amma ke kin mayar da ni kamar wani sa'anki, har hantarata ki ke yi""" """Ni ɗin ce na rainaka? Ni na isa wacece ni? Amma dan Allah sweetheart meyasa ka kusa kashe ni" "ranar farko da na zo wurinka?""" Ya ɗago ya kalleta ya yi shiru. """Ka amsa mini dan Allah""" """A lokacin ai kamar mahaukaci nake shiyasa""" "Ta girgiza kai ta ce ""A'a, wani abu na din ga gani a idonka, da na rasa menene? Dan Allah" "meyasa?""" """Ke ban sani ba, tashi ki bar wurin nan""" "Ta noƙe masa kafaɗa tana kallon idonsa, abun da ya tsana. Yayi tsaki ya kawar da kansa gefe." "Turare ta ɗaukko a jakarta, ta toshe hancinta, ta fesa a wurin. Ba shiri ya waiwayo yana kallon" hannunta. """Gashi yanzu na saka ka waiwayo ai, gashi saya maka na yi"" ya karɓi turaren, ya din ga juya shi a" hannunsa yana kallo. "Ta na ƙoƙarin ɗaga wayar da ake yi mata, ta ga hawaye na ɗiga a hannunsa." "Sai jikinta yayi sanyi gaba ɗaya. ""Haba mai babban suna, a yanzu fa kuka ba naka bane ba, wanda ka yi ya isa, mu cigaba da addu'a da ƙoƙarin tattara shaidun da zamu shiga kotu da su, dan Allah" ka daina bana jin daɗi. """Da jauhar na raye, da yanzu na san ta kammala law school, maybe ta haifi yaronmu na biyu ko uku, ina da tarin burika a kanta, na kyautata rayuwar ta, ta ji daɗi ta huta, saboda wahalar da ta sha a rayuwarta, amma wauta ta da rashin hankali, ya sanya ta mutu ta bar ni a duniyar. Lokacin da duniya ta yi watsi da ni, ake yi mini kallon mara amfani, ta rungume ni, ta karɓi ƙaddararta, ta kula da ni, a lokacin da nake ƙoƙarin kyatata ratuwarta na fara bata kulawa, lokacin da na fara gano haske yana tunkaro rayuwarmu, ashe yayi daidai da lokacin da zan yi girbin ya mummunar hanyar da na zaɓawa rayuwata, na rasata"" yayi maganar yana ƙoƙarin mayar da hawayen sa," "amma suka cigaba da zuba, kamar an kunna famfo." """Viper, ka yi haƙuri, Allah ya ambaci masu haƙuri a wurare daban-daban a alƙur'ani, tare da yi" "musu bushara. Viper Allah ya fi kowa so da kishin bawansa, wataƙila mutuwar jauhar a wannan lokacin shi ne mafi alkhairin ta, a duk buɗe ido muka yi muka ganmu a duniya, dan haka ba zamu tsarawa Allah yadda muke son kasancewa ba a duniya." "Ba kowa Allah ya tsarawa jin daɗi a duniyar nan ba, ai dama ita duniyar kurkukun mumini ce, aljannar kafiri. Wani ga jin daɗin yana cikinsa a zahiri, amma a baɗini rayuwar kawai suke yi mara ma'ana." "Yanzu tsohon ubangidanka ga duniyar ya samu, yana jin daɗin amma nauyin zunubin da yake aikatawa ba zai taɓa barinsa ya rayu cikin kwanciyar hankali ba. Ba sai mutum ya samu wadata dan ya sha wuyar rayuwa, shi ne tabbacin Allah yana son sa ba, duk tsananin rayuwa da ka ke ciki, idan har ya barka da imaninka, kuma ka yi kyakywan ƙarshe, wallahi ya fiye wa ɗan Adam duk wani abun more rayuwa." "In dai ana samun aljanna a biyayyar iyaye, da biyayyar aure in sha Allah Jauhar ta samu"" ya" jinjina kai yana cigaba da zubar da hawaye. "Ta bashi handkerchief ɗin ta, ta ce ""Share hawayen haka, kaga ni ma ka saka ni kuka, bana iya jure in ga mutum a cikin damuwa ko yana kuka, alhalin ba zan iya yaye masa damuwar sa ba." "Yanzu ni kaina, duk abubuwan da nan da nake yi, ƙarfin hali nake yi, zuciyata akwai wani ciwo da yake addabata, ina kuka iya yi na wasu lokutan, sai dai babu yadda na iya, da abun da ƙaddara" "ta zana mini"" tayi maganar ita ma tana kuka." "Ya ɗago ya kalleta, ya motsa baki, yana son ya faɗi wani abu." Ayshercool 08081012143 "Ta share hawayenta, ta ɗaga kanta ta ga ita yake kallo ta ce ""Ka ce mini ka yi wa Indabo aike, me" "ka aika masa?""" """Hotona ne""" """Hotonka kuma?""" """Eh, hotona ne da ni da wani yaronsa da yake zaton ya saka an kashe masa shi""" "Ta zaro ido ta ce ""Wai shi mutane nawa ya kashe kenan a rayuwarsa?""" "Ya rausayar da kai ya ce ""Mutane sun ɗauki duniya fiye da yadda ki ke tunani. A baya bayan matsalar da nake fuskanta a gidanmu, fatan da nake yi kullum, Allah ya bani abun yi, ko iya abinci in din ga samu ina ci, sai da na haɗu da uban gidana dodo, ya haska mini duniya da in da mutane suka saka gaba. Da na so na yi kuɗi da yanzu ni hamshaƙin attajiri ne." "A lokacin da jauhar take ciyar da ni, da fari babu abun da yayi mini zafi, gani nake kawai auren dole aka yi mini, sam ba ta gabana, sai dai abun mamakina da ita, duk abun da zan yi mata bata jin haushi, naga yadda take sana'a tuƙuru iya yin ta, dan kar mu zauna da yunwa, daga baya nayi" "noticing idan abinci ba zai isa ba, sai ta bani ita tayi kame-kame ba ta ci ba, a lokacin ba wai dan" "tana so na bane take yi mini haka, ta rungumi ƙaddara ne, kuma tana tausayina." "Daga baya sai na fara jin kunyarta, lokacin da ta roƙi na sayo mata omo, naga responsibility ɗina, amma na zuba mata ido take yi, kuma bata taɓa nuna mini ta gaji ba. Sai dai a lokacin ba ni da wata sana'a sai sayar da wiwi da ƙwayoyi, yadda take yi mini addu'a Allah ya wadata ni da halal, ya nesanta ni da haram, ya sanya na ji ba zan iya ciyar da ita da kuɗin wiwi ba." "Sai a lokacin naga ashe, bayan mutuwar Sadik kukan daɗi nayi, da na ce na rasa sana'a, dan a lokacin na din ga faɗi tashi, saboda kar na ciyar da ita da kuɗin ƙwaya." "Da in ciyar da ita da wannan kuɗin, gara na dawo na maze na ce bani da kuɗi, na san ba ɗaga mini hankali za ta yi ba." "Gashi lokacin tana ta ƙoƙarin rabani da hulɗa da Indabo, wataran idan na ga wahalar tayi mata yawa, haka nan nake zuwa na tsitsiye Indabo ya bani kuɗi." "Zuciyata ta sha raya mini, na faɗa mummunar hanya, na samu kuɗi saboda jauhar ta huta, bana nuna mata hakan a zahiri, amma zuciyata kullum a takure babu daɗi. Duk da tsamin alaƙar da ke tsakanina da mahaifina, sai da na din ga jin tamkar na je na ce ya bani aron kuɗi nayi jari, amma na kasa, mussman tuna halin matarsa." "A lokacin da tausayinta ya fara zama tsananin so a cikin raina, da tana uzzura mini ko yi mini tashin hankali, da babu abun da zai hanani kauce hanya, dan yahoo zan fara, kuma kuɗi zan samu sosai da sosai, haka nan na san in da zan yi dillancin miyagun ƙwayoyi a tsakanin manyan mutane, har da ƙasashen ƙetare na samu kuɗi, amma ban taɓa burin tara kuɗi da mummunar hanya ba." "Ina ga lokacin da tayi ɓari ne, bani da wasu kuɗi sai na wiwi, shi ne aka yi mata magani da su," "amma banda haka, ban taɓa ciyar da ita da kuɗin ƙwaya ba""." """Viper, labarinku abun tausayi, kuma gwanin daɗi, Allah ya bani ikon zama kamar jauhar, ina" "sonta sosai""" """Sai dai ki kamanta, ba zaki iya ba, ke mafaɗaciya ce, matata kuwa kan tayi faɗa sau ɗaya ana da" "ɗewa, shiyasa nake kiyaye abun da zai ɓata mata rai ya sa tayi fushi, har ta yi faɗa. Na gode sosai da saka ni kuka da ki ka yi""" """Saka ka kuka kuma?""" """Eh, tun da na rasa jauhar, ban zubar da hawaye ba""" """Ai kai jarumi ne, bari na tashi na tafi gida, ka yi mini addu'a, gobe in Allah ya kaimu zamu zauna" "a kotu""" "Ya jinjina kai ya ce ""Allah ya bada sa'a, bani maganina""" """Dan Allah ka daina shan magungunan nan, lafiyarka fa""" "Ya ce ""Duba na na menene?""" "Ta ciro maganin ta duba, cikin magungunan sa ne na Asibiti, ta ajiye masa ta ce ""Allah ya baka" "lafiya mai amfani, ya bamu nasara a kotu, in sha Allah case ɗin ka ne next, ka yi mana addu'a"" ya" jinjina mata kai. Ta tashi ta ɗauki jakarta tana ɗaga masa hannu. *** "Daren yau Nabila tayi ta addu'a, suka yi waya da Barrister Habib, ya ce su haɗu a kotu." "Ya ƙara mata ƙarfin gwiwa, kafin shiga shari'a, suna tsaye a harabar kotu, tana dudduba abun da zata tsaya a gaban shari'a da shi." "Nabila ta tsaya a gaban kotu, ta ce my lord, kamar yadda na gabatar da hujjojina a wancan zaman da aka yi, akwai voice na muryar mahaifiyar ramma tana kokawa akan a nema mata hakkin 'yar ta." "Haryanzu ina da ja, a kan zargin da ake yi wa wanda nake karewa, a hirar da aka yi da mahaifiyar ramma, a gidan rediyo, wanda suka yi iƙirarin ya yi wa ramma fyaɗe, ya sha banban da wanda aka gabatarwa kotu." "Haka zalika, voice message ɗin da yake yawo, na mahaifiyar ramma, ta koka a kan wanda ya yi" "wa ƴar ta fyaɗe, ya dawo ya ɗauketa ta ƙarfin tsiya daga gabanta." "Lauyan gwamanti yayi suka, ya nemi da a gabatar da mahaifiyar ramma, ba wai kame-kame da" abun da babu wanda ya san tushen sa ba. "Nabila nan take ita ma ta buƙaci, a gabatar da ramma, tayi mata tambayoyi." "Lawyan gwamnati ya ce Ramma na ƙarƙashin kulawar, likitoci haryanzu, dan haka ba za a" gabatar da ita a gaban kotu ba. "Nabila ta sake cewa Wane irin illa aka yi mata, da har zuwa wannan lokacin za ace ba ta warke ba, a shekarun baya shekara sha uku sha huɗu ake yi wa mata aure, ba a samun matsala, suna zaune lafiya, a report ɗin da aka bayar na case ɗin ramma, abun bai zama complicated da za ace tsawon" wannan lokaci tana Asibiti ba. "Lauyan gwamanti ya soki maganar Nabila, tare da neman a bashi dama ya gabatar da shaidunsa na" gaba. "Wata mata ce ta fito, aka tambayi baba mai gadi, ko ya santa? Ya ce Eh, ita ma mai aiki ce a gidan." "Aka tambayi me ta sani, a game da abun da ake tuhumar mai gadi da shi, babu kunya babu tsoron Allah, ta bayar da shaidar zir, tare da tabattar da mai gadi ne yayi laifin, sai bayan da yayi aika-aikar, ta dawo daga sayen kayan miya, ta tarar da ramma, kuma daga shi sai ramma ta bari a" gidan. Baba mai gadi ya sunkuyar da kai cikin matsanancin ɓacin rai da mamaki. "Nabila ta ce ya za ayi ace gida kamar wannan babu cctv camera, akwai buƙatar idan da cctv" camera a duba abun da ya faru. "Daga nan Nabila ta nemi a bata damar ta gabatar da nata shaidar ma, aka bata dama, ta buƙaci wata mata ta fito." "Nabila ta buƙaci matar ta gabatar da kanta, ta gabatar da kanta a matsayin maƙwabciyar su ramma" a can garinsu. """Me ki ka sani game da abun da ya faru da ramma?""" """Eh to, bayan an dawo da ramma gida, ta cigaba da jinya, dan sallamo su aka yi daga Asibitin birni, saboda rashin isashshen kuɗi. Babar ramma ta gaya mini wata mata ta zo ta ce zata taimaka musu, amma sai sun yarda sun janye shari'ar." "Da suka ƙi, ta ce zasu gani, bayan wasu 'yan kwanaki, wani mutum ya zo da shi da wasu, ya gaya" "mata shi ne ya yi wa ramma fyaɗe, kuma ta ƙarfin tsiya, ya kama hannunta ya tafi da ita""" "Nabila ta ce ""Ko ta gaya miki sunan wanda ya keta wa yar ta haddi?""" """A'a, ba su san sunansa ba, ramma ba ta daɗe da fara aiki a gidan ba, amma ta tabbatar da ƙanin matar gidan ne. Bayan ya sace mata 'ya, ta je birni gidajen radiyo ba a saurareta ba, haka zalika" "wurin jami'an tsaro, kawai lokaci ɗaya muka nemeta muka rasa""." """My lord, shaida ta tabbatar da cewa wanda ya yi wa ramma fyaɗe, ya dawo ya saceta, wanda nake karewa da ake zargi yake tsare, tayaya zai je ya sace yarinyar. Kuma har zuwa wannan" "lokacin, ba mu ga ramma a zaman kotu ba, shin ina ramma take?""" "Lauyan gwamanti ya ce bai kamata a karɓi shaidar maƙwabciyar su ramma ba, tun da ba a kanta" "abun ya faru ba, dan haka ayi fatali da shaidarta." "Duk yadda Nabila ta so bayyanar da nagartar hujjojinta, amma kotu ta din ga soke su." "Nabila tana ji tana gani, aka yankewa dattijon shekara goma sha huɗu a gidan yari, wata irin bahaguwar shari'a, mara fasali balle ɗigon adalci, yanke hukunci cikin gaggawa ba tare da" "kammala tabattar da ingancin shaidun kowane ɓangare ba, sai dai an basu damar ɗaukaka ƙara." "Yanayin yadda ta fito a gigice kawai zai tabattar wa da mutum ba a hayyacinta take ba, sumayya" "da suka zo ɗaukan report ce ta nufeta da sauri, watsi ta yi da file ɗin hannunta, ta faɗa jikin sumayya tana kuka." "Barrister Habib ya ƙaraso, ya ce ""Haba Nabila, wannan ai sai ki saka ayi mana dariya, akwai" "appeal a gaba, dan Allah ki nutsu." "Cikin kuka ta ce ""Sumayya mu tafi gida, ba zan iya sake haɗa ido da mutumin nan ba, i try my" "best, ai kun ga yanayin shari'ar da aka yi, dama haka aka koyar da mu, an bi Principles na law a wannan shari'ar?""" "Sumayya ta din ga rarrashinta, suka sakata a mota, barrister Habib ya ce ""Bari mu kaita gida," "Bashir kai ka tafi da motata""" "Suna tafe a mota tana cigaba da kuka, Barrister Kabir ya kira Habib, ya ce ""Ya ake ciki ne?""" """Gamu zamu tafi, ba ta yi wining ba, sai kuka take yi""" "Kabir ya ce ""Ai dama na gaya mata, waye ya gaya mata jayayya da mutanen nan abu ne mai sauƙ" "i?""" """Dan Allah kar ka saka ta sare gaba ɗaya, za mu yi appeal, kuma saboda ita nima zan yi abun nan" "kyauta fisabilillahi i really appreciate what she did"" ya ajiye wayar yana cigaba da yi wa Nabila nasiha." "Bunkure ta ƙyaƙyace bayan kammala wayar da ta yi, ta kalli badi'a." "Badi'a ta ce ""An kammala komai kenan?""" """Eh, an ƙarƙare shari'ar a yau, uba ya yi abun da ya dace, wallahi da bai yi wani yinƙuri ba, sakar musu zan yi su ƙarata daga shi har ɗan nasa, su ta shafa, amma a wannan karon dole na ɗauki mataki a kan yarinyar nan, da gaske so take yi sai ta tona mini asiri, dole zan tattauna da indabo," "ya ɗauki mataki a kan ta""" """Amma kina ganin hakan zai yiwu, tun da abu ya shiga social media, kuma ta fara samun masu" "mara mata baya?""" """Iyayen gidanta ma, ba su kai ko ina ba, amma an ce mini an hangeta da barrister Habib, kuma ina kyautata zaton da saka hannunsa a wani abun da take yi, amma duk na san matakin da zan ɗauka" "akan dukkansu"" ta ƙarasa maganar tana haɗiye ƙwayoyin da suke hannun ta, ta bi su da ruwa." "Nabila bayan sun kaita gida kuwa, ba ƙaramin kuka tayi ba, gaba ɗaya sai ta ji ta karaya, komai" ya fita daga kanta. "A ɗakin Nasir, ya sameta bayan ya dawo daga aiki, ko da ya tarar da Nabila ta sha uban kuka, tuntsirwa yayi da dariya, ya ce ""Haba barrister, ina ƙwarin gwiwar ta ki? Har kin karaya haka?. Abun da na yi ta nuna miki kenan, nake gargaɗinki a kan ki fita daga sabgar nan, ba ke kaɗaice mai gaskiya a ƙasar nan ba, amma tun da ki ka ga kowa ya ja baki yayi shiru, to abun ya gagari kundila, amma ki ka ƙi ganewa ki ka cigaba da dagewa, ki gode Allah da ba su yi wani abu da za" "su taɓa lafiyarki ba ma"" ya gama surutansa ya fita, ba ta ko kalleshi ba." "Yana fita ta mayar da ƙofa ta rufe, tana ƙoƙarin kiran Viper, wayar Alhaji wada ta shigo. Ajiye" "wayar tayi, ta ɗauki ƙaramar ta ta, ta kira Viper." "Bugu ɗaya ya ɗaga, kawai ta saka masa kuka." """Meye ne?""" """Kana kallon wulaƙancin da aka yi mini a shari'ar nan, kaga wata irin shari'a da aka yi mai cike da wulaƙanci da zalunci, wallahi gaba ɗaya na karaya, na gaji da aikin nan, ina ji ina gani, mutumin" "da bai ji ba bai gani ba, zai tafi prison, zuciyata kamar ta fashe na gaji""." """To ni kuma wa zai tsaya wa tawa shari'ar?""" "Nabila ta ce ""I give up, na karaya"" tayi maganar tana kuka." """Ke kin isa? Ai tun da muka fara, sai mun kai ƙarshe, tied your belt against next trial""." """Ni ba zan iya ba, ina ga ma ciwon zuciya ya kama ni, duk na tsani komai, haka zamu cigaba da" "tafiya, mai kuɗi ne kawai ɗan gata? Ƙiri-ƙiri fa aka murɗe komai""." """Sai ki gyara, kar ki gaji, sai kin gama da ni tukuna, anyway an hukunta wanda ya aikata laifin," "saura kuma ki matsa ki gano in da ramma take da mahaifiyarta""" """Wai kai wane irin mutum ne? Na gaya maka dattijon nan ba shi yayi laifin nan ba, kuma ni ina" "zan ganta?""" "Ko a jikinsa ya ce ""Wannan matsalar ki ce ai, ki ƙarasa wannan ki zo ki yi nawa""" "Katse wayar ta yi, ta ajiye ta cigaba da kuka." ***** """Lakwari, ka je ka samu P.A ɗin Indabo, ka gaya masa ni na aikoka, ya uzzura mini da kiran waya, a kan lallai sai na je, wai mai zamani ya yi masa aike, dan haka dolena na nemo masa shi, haryanzu ban sanar masa da halin da nake ciki ba, amma ka je, idan ka je wurin P.A ɗin, ka kira ni" "zam yi masa bayani""." """Shikenan, amma kana ganin ba za a samu matsala ba?""" """Ba za a samu ba, daga nan ma sai ka samo mana kuɗin zuwa asibitin nan, dan na tattara kuɗin" "hannuna gaba ɗaya na aika a kawo mana ganye, shi ma kuma na ji shiru, idan ka dawo daga wurinsa ka biya ka duba mana""." """Shikenan an gama""" *** "Nabila kuwa ba a iya Nasir ba, hatta yan gidan suka sakata a gaba da tsokana, suna yi mata dariya," "bisa yadda ta shiga matsananciyar damuwar rashin nasarar da ta yi, a kotu. Ba ta taɓa yin shari'ar da ta shiga ranta ba kamar wannan, gashi dai kyauta take shari'ar babu ko sisi, amma duk ta bi ta damu, hatta hawa social media ya gagareta, saboda yadda ake yi mata dariya, ƴan koren Bunkure ke cigaba da nuna cewar Nabila hassada take yi wa bunkure, kuma kwangila ta karɓo a hannun wasu." "Sosai ta fusata, ta hau social media tayi posting, ja da baya ga zaki ba tsoro bane ba, shirin faɗa ne." "Kuma ko bayan shekara dubu, sunan gaskiya baya taɓa canzawa, a saurari fitowa ta gaba." "Ɓangaren Nasir ma, yana fuskantar matsin lamba sosai daga wurin Indabo, da kuma manyansa a wurin aiki, a kan kama Viper." "Gefe guda ga fargabar abin da Nabila za ta janyo musu, tun da ita ba ta so a zauna lafiya, yana" matuƙar fargabar Indabo ya yi mata wani abun. "Gaba ɗaya ta daina walwala, ko fitowa ta daina yi, sai idan fita zata yi, sai dai a kai mata abinci ɗ" aki a ajiye. "Ganin ta takura kanta da yawa, Nasir ya sameta yana rarrashinta, da bata baki a kan ta jure ta karɓi" ƙaddara. """Ba wata ƙaddara da zan karɓa"" tayi maganar tana hura hanci." """Ke saɓo zaki yi kenan?""" "Nabila ta ce ""DSP, abun da Allah ya hukunta shi ne ƙaddara, ba abun da mutum ya ga dama yayi" "da son rai ko son zuciya ba, ko da me matar nan take yawo, sai na tona mata asiri wallahi, gara ma ka ƙyale ni da wannan nasihar""" """Na ƙyale ki, amma idan kin ƙi ji, ai ba kya ƙi gani ba, tun gashi yanzu kin fara ganin ma, amma ba wannan ba, wai haryanzu babu wani news da ki ka samo a kan Viper ne? Na ga duk kin yi" "sanyi, kin daina taimaka mini""" "Ta kalleshi ta ce ""Ba dole na yi sanyi ba, ai dama ka ce na daina saka kaina a abun da babu ruwana," "dan haka wannan ma babu ruwana da shi""" "Yayi murmushi ya ce ""Haryanzu a fusace ki ke arfa, to ba ni ne dai Naja'atu Bunkure nan ba," "amma yakamata idan da wani hints a taimaka mini""" "Ta kalleshi ta ce ""Babu wani hints, ban san komai ba""" """To shikenan, idan kin huce sai mu cigaba da maganar"" ta harare bayansa har ya fice." "Kasa samun nutsuwa ta yi, ta sake ɗaukar wayarta ta yi posting, ""Idan har mahaifiyar ramma ba ɓ" "ata tayi ba, kuma da gaske Bunkure foundation na kula da ramma ne, to tana ina, al'umma yakamata su samu update a kan halin da take ciki, kuma shin suna da masaniya a kan ɓatan" "mahaifiyarta? Idan eh to ina tafi? Tana tare da 'yarta ne ko kuwa?"" Tayi posting ta nemi wuri ta" "zauna, lissafi da tunani daban-daban suka din ga kaiwa suna komowa a cikin ƙwaƙwalwar Nabila." *** """Indabo, yakamata fa ka sake matsa Abdul, ya gaya maka in da yarinyar nan take, hankali ya fara dawowa kanmu, yarinyar nan fa ta matsa, kuma ban ga alamar, zaka ɗauki wani muhimmin mataki a kan ta ba""" """Ya ce mini ya kasheta""" "Bunkure ta ce ""Ya kashe ta ta yaya? A binciken da na yi, an tabattar mini uwar yarinyar ba ta garin nan, tafiya ta yi babu shiri, kuma Abdul ya je gidan fiye da sau ɗaya, bayan ya ɗauke yarinyar," "me ya je yi, ni fa ba na son a din ga gaba ana baya, kar asirinmu ya tonu fa""" "Indabo ya numfasa ya ce ""Abubuwa sun fara caza mini kai Naja, ga takarar Abdul da nake ta fafutuka, ga auren nan da ake shirin yi na shi. Ga ɓangaren ki taki matsalar, duk is a minus case, bababr damuwata yanzu Viper, aiken da ya yi mini ya tayar mini da hankali, idan ba a kama shi an kashe ba, hankalina ba zai taɓa kwanciya ba, ga ƴan adawa sun sako mu a gaba, ga tunanin jafar" "da yake tsare na rasa wane tunanin ma yakamata na yi""" """Ai wanda ya fi muhimmanci shi zaka yi, wallahi idan aka cigaba da ƙyale yarinyar nan, muna" "raina abun da take yi zata bamu mamaki fa""" "Ya jinjina kai ya ce ""Na ga alama, kuma ba zan taɓa bari hakan ta faru ba""." "P.A ne ya kaste su, ta hanyar yin sallama, suka amsa duk suka ɗago suna kallonsa." "Ya kalli indabo ya ce ""Akwai matsala fa""" """Again?""" """Ƙwarai kuwa, madaki ne ya yi aike, wai ya samu rauni a ƙafarsa, yanzu haka ko iya tafiya ba ya yi, ɗazu ya turo yaronsa har ya buƙaci a bashi kuɗi ya je asibiti, amma wai duk wani abu da" "yakamata, yana da yaran da za su iya yi maka""" "Indabo ya buga tsaki ya ce ""Maganar banza kenan, zuwa yaushe zan cigaba da rarraba sirrina, wannan yayi mini aiki wancan yayi mini, kalli yadda haryanzu jarabar ɗan tahaliki ɗaya take ta" "ɗawainiya da rayuwata. Na gaji ya je Allah ya kyauta, na nemi wata mafutar""" """Amma kana ganin watsi da shi, ba zai zame mana wata ɓarakar ba ko barazanar ba?""" """Babu abun da zai zame mana sai wahala, tun da ba shi da wani amfani yanzu, Viper da na bari ya" "ci karensa babu babbaka, saboda yaron dodo ne, ina matuƙar jin tsoron abun da ya sani a kaina, kuma kamar yadda na yi tsammani, ya san abubuwan da idan yayi magana kashinmu ya bushe," "dole fa a nemo Viper akwai matsala wallahi"" yayi maganar yana zazzaro ido cikin tashin hankali." "Sai da aka kusa sati da yanke hukunci, sannan Nabila ta tafi wurin iyalan dattijon nan, tare da sake rarrashin su, a kan su yi haƙuri su ƙara mata lokaci, zata ƙara shiryawa sosai a appeal ɗin da za" "su yi, tana saka ran za su yi nasara in sha Allah." "Suka yi ta yi mata godiya, sai da zata tafi, ƙaninsa ya keɓe da ita, ya ƙara yi mata godiya, sannan ya ce ""Dan Allah ki ƙara bincikar ɗan uwana, kamar fa ya san wanda ya yi laifin, barazana aka yi" "masa Shiyasa ya kasa gaya miki komai""" """Barazana kuma, wace irin barazana?""" "Ya ce ""Eh, akwai ziyara da na kai masa, ya gaya mini amma ya nemi kar na gaya wa kowa, ya san" "sunan wanda yayi laifin, da alaƙarsa da matar gidan, amma bai san ɗan waye ba""" "Ta ce ""Ya salam, to amma meyasa ni bai gaya mini ba, babu yadda ban yi da shi ba a kan idan ya san wani abu, ya sanar mini, amma ya ce mini babu abun da ya sani, sunansa ma bai sani ba," "kawai dai ya san ɗan yayan matar gidan ne""." "Ta ce ""Subhanallah, shikenan zan san abun yi, a cigaba da yi mana addu'a""" "Ya ce ""In sha Allah, kullum cikin yi muku ake, Allah ya jiƙan magabata mun gode sosai da sosai""." "Tana kan hanya saƙon Viper ya shiga wayarta, a kan yana son su haɗu." "Ji tayi kamar ta maze taƙi zuwa, amma ina, ba ta ji alamar zuciyarta zata bari ta aikata hakan ba." "Garden ɗin da suke haɗuwa, a can ta same shi, ta tsaya tana kallonsa ya rage sumar kansa, yayi" kyau sosai. "Wata tab ta gani a hannunsa, cikin basarwa ta ce ""Ina wuni?""" """Wayarki zaki bani""" "Ta kalleshi ta ce ""Wai baka san meya same ni bane? Baka jajanta mini rashin nasara da nayi ba," "abu duk ya dame ni""" """Yanzu ki ka fara, idan har rashin nasara ba zai saka ki ƙara jajircewa ba, sai dai ki yi kuka""" "Nabila ta ce ""To idan ban yi kuka ba ya zan yi?""" "Ya kalleta ya ce ""Babu""" """Waye ya sai maka waya?"" Yayi mata shiru." "Ta sake cewa ""Haryanzu fa ina da tarin tambayoyin da baka amsa mini ba""" """Wanne daga ciki?""" """Meyasa Indabo ya ce zai yi maka tarko da ni ya kama ka? Ni meye haɗina da kai?""" "Ba tare da ya kalleta ba ya ce ""Wataƙila ya san kina zuwa wurina""" """To amma ya aka yi haryanzu bai kama ka ɗin ba? Kuma ni haryanzu kana ɓoye mini wasu" "abubuwa""" "Ya saka ƙaramar wayarsa a kunnensa, ya ce ""Ɗan mama ya ake ciki?""" """Oga Viper, mun ƙwamuso Lakwari fa, yanzu duk in da madaki yake, dole ya bayyana, tun da" "babu mai taimaka masa ko ya kula da shi""" "Viper ya ce ""Good job, zan gaya muku what next""" "Cikin zaro ido Nabila ta ce ""Viper kidnapping?""" """Eh ina son na sauƙaƙa miki aiki ne, shaidu na fara tattara miki, kafin a fara shari'ata, Madaki yayi" "jigatar da ba zai iya musa laifin da ya aikata ba""" """Amma ka gaya mini me ka ke yi da wayoyi? Ka daina yi mini ɓoye-ɓoye. Sai kin zo kan" "shari'ata zaki ji koma me ki ke buƙatar ji""" "Kamar shashasha haka take kallonsa, gaba ɗaya ta ma rasa me za ta ce masa." "Ya miƙa mata wayarta ya ce ""Angry bird""" """Am confused""" """Sorry""" "Kamar ta sake fashewa da kuka ta ce ""Zuciyata kamar a kurku, haka nake jin ta, mai laifi daban" "yana can yana rayuwarsa, mai karɓar hukunci daban, wane irin abu ne wannan?""" "Viper ya gyaɗa kai ya ce ""Kamar dai ni a kwanakin baya, idan aka kama mai laifi, sai ayi musanye" "a saki wancan saboda ɗan gata ne, ni kuma a tsare ni a matsayin mai laifin""" "Ta ce ""Kuma dai? Wani yayi laifi kai kuma a tsareka?""" """Mmm, a saka matata tayi ta yawo tana wahala ba, wata Shari'a sai a lahira, duk rintsi kar ki yadda" "ayi amfani da ke ki ci amana, ba kowa ne yake da zuciyar yafiya ba""" "Jiki a sanyaye ta jinjina kai, ya ce ""You can leave""." "Kusan a tsukin lokacin, Nabila ta zama topic of discussion a social media, sai dai ba ta karaya ba," wurin cigaba da posting a kan bunkure foundation. *** """Abdul tun muna shaida juna, ka gaya mini ina yarinyar nan take? Ka kashetan ko kuwa? Sannan uban me ya sake mayar da kai gidansu, bayan ka je ka ɗauki yarinyar, kuma saboda hauka maimakon ka saka ayi? Kawai sai ka wanke ƙafa ka tafi da kanka ka je ka ɗauki yarinyar, kamar baka san matsayinka ba? Idan ka san uwar yarinyar nan ma, tana tare da kai, ka gaya mini, na san" "matakin da zan ɗauka a kai""" "Ya girgiza kai ya ce ""Ni ban ɗauki uwar yarinyar ba, ban san in da take ba""" """Da ka kashe yarinyar yaya ka yi da gawarta?""" "Abdul ya ɗan yi jimm sannan ya ce ""Ruwa na jefa ta""" "Indabo ya ja guntun tsaki ya tashi, maganganun da bokansa ya gaya masa ne suke ta yi masa kai komo a zuciyarsa, wai dutsen da ya gaya masa zai ci karo da shi, lokaci yayi da shi bai san ya za ayi ba, dole ayi ɗayan biyu, ko dutsen yayi nasara a kansa, ko kuma su yi mutuwar kasko, amma" "babu yadda za ayi, ya iya maganin dutsen nan da kansa." "Nabila fa ta sake jajircewa, da cigaba da ƙoƙarin gano bakin zaren matsalolin da take tunkara." "Bayan shari'ar ramma, akwai shari'oi da dama a gabanta, amma wannan c ta fi ci mata tuwo a ƙ" "warya, sai kuma ta Viper da zata fuskanta." "Kasancewar da sassafe ta je wurin aikin, duk babu mutane, ta shiga office ɗin ta, ta ajiye jakarta," "ta yi addu'a ta zauna, ta buɗe computer ta fara aiki." "Ƙaurin wayar wutar lantarki ta fara ji, ta ɗaga kanta, ba ta ga komai ba, ta sunkuyar ta cigaba da" aikinta. "Wata irin ƙara wearing ɗin office ɗin ta yayi, ya fara ci da wuta, a razane ta tashi cikin tashin" "hankali, ta nufi ƙofa zata buɗe, ta ji an kulleta ta waje, ta jijjiga iya ƙarfin ta, amma a ƙofar a kulle gam, ga wuyar wuta sai cigaba da ƙara take yi wuta na kamawa tana tarwatsi." "Da ƙyar ta iya ɗaukko jakarta, ta ciro wayarta, tuni ta fara gani dishi-dishi, saboda hayaƙi, tari ya" turnuƙeta. "Hannunta na rawa, lambar Viper kawai ta iya gani, ta danna." "Ya ɗaga wayar sautin tarinta ya fara ji, tana ta yi haɗe da haki, da ƙyar ya iya fahimtar ta ce" """Wuta"" daga nan ya ji ɗif" Ayshercool 08081012143 ₦500 ne via 0009450228 Aisha Adam jaiz bank sai shaidar biya ta 08081012143 Wanda za su jira document 1K ne. 90009343 'Yan Nijar ku turo katin airtel na 300fcfa Arewabooks ayshercool7724 "Cikin hanzari Viper ya tashi ya tsaye, yana cewa ""Kina ina ne? Meyake faruwa?"" Sai dai still shiru" ba ta ce komai ba. "Su Walid ma duk suka miƙe tsaye, suna kallonsa." "Walid ya ce ""Yaya meyafaru Viper?""" """Ki yi mini magana, kina ina meyake faruwa ne?""" "Liti ya ce ""Mai zamani menene wai?""" """Yarinyar nan tana cikin matsala""" """Subhanallah, to tana ina ne yanzu?"" liti yayi maganar yana kallon sa." """Safiya ce yanzu, ko tana gida, ko hanya ko wurin aiki. Babu yadda za a yi ace a gida ne wani abu" "ya same ta ta kira ni, da hanya ne kuma da tuni an kai mata ɗauki, ko dai an ɗauketa ne ko kuma tana wurin aiki, wuta na ji ta ce""" "Hanyar fita Viper ya nufa, Walid ya riƙe shi ya ce ""Ina zaka fita ka je? Ba kai yakamata ka fita ba," "liti ko ɗan mama, ɗan maman ma dai, ka san wurin aikinta ai in da kuka ɗaukkota?""" "Ya ce ""Eh oga Walid""" """Je ka gano mana menene yake faruwa""" "Ya ce ""To bari na canza kaya""" "Viper ya cigaba da bin layin Nabila yana kira, amma shiru ba ta ɗagawa." "Nabila kuwa tuni ta fice daga hayyacinta, ba ta sake sanin in da kanta yake ba." "Masinja ne da shigowarsa kenan, ya ga wurin ya turnuƙe da hayaƙi, ya shiga dudduba daga ina hayaƙin yake fitowa." "Cikin tsananin tashin hankali, ya nufi ƙofar office ɗin Nabila, ya din ga bubbuga ƙofar, amma ya ji ta a rufe gam, ya girgiza ya girgiza amma a rufe, ya fito ya nufi wurin masu gadi, ya na sanar da" su wuta. "Suka tashi gaba ɗaya suka rankaya a guje, ɗaya daga cikin su ya ce ""Innalillahi wa Innalillahi" "raji'un, Nabila fa ta shigo aiki, tana ciki jama'a ku taimaka""." "Nan da nan wuri ya cika da mutane, ana ta ƙoƙarin a ɓalle ƙofar a cirota, a daidai lokacin" "barrister Habib ya ƙaraso cikin tashin hankali, kasancewar an kira shi a waya an sanar masa." "Da kyar aka ɓalle ƙofar, wani irin huci mai ɗauke da hayaƙi ya buso waje suka ja da baya, wani matashi ne ya kutsa kai, ya na nemanta, ya hangota a yashe a cikin office ɗin ga jakarta da system" "ɗin ta, da wayarta a wurin." "Wutar ta mutu ba ta cigaba da ci ba, iya wadda ta kama ce ta haddasa hayaƙi, da huci mai zafi." "A kafaɗarsa ya saɓo Nabila, yana fitowa barrister Habib ya karɓi wayar da system ɗin, yayi waje" "da ita. A motar barrister Habib aka saka ta, suka nufi asibiti." "Barrister Kabir ma hankalin sa yayi mummunan tashi, ya din ga kiran waya, Habib ya ce masa sun" tafi da ita Asibiti. "Gaba ɗaya hankalin ma'aikatan wurin ya tashi, dan duk jin kan Nabila da gayunta akwai girmama" "mutane, ga yawan kyauta da take yi musu." "Viper ya kasa zaune ya kasa tsaye, Liti da Walid ne suke ta rarrashin sa, amma ya kasa nutsuwa," "sai cewa yake tafiya zai yi ya gano halin da take ciki, suka din ga kiran wayar ɗan mama, amma bai ɗaga ba." "Viper ya ce ""Walid, ba zan lamunci a wannan karon wannan ita ma ta rasa ranta ba, dole fa na" "gano halin da take ciki""" "Walid ya ce ""Mun sani, amma ka fara bari mu ji daga bakin ɗan mama""" "Suna tsaka da maganar ya kira waya, Viper ya fizge wayar daga hannun liti, ya ɗaga ya ce ""Kai" "ana ta kiranka ka ƙi ɗagawa, yaya aka yi ka sameta?""" """Wuta ce ta kama fa a ofishin ta, lokacin da na je an buɗe ƙofar an fito da ita, za a tafi asibiti""" """Dalla ba wannan na tambayeka ba, tana ina yanzu a wane hali take ciki?""" """Eh, sun tafi kaita Asibiti, na bi bayansu a adaidaita sahu, an kaita wani ɗaki an hana kowa shiga," "haryanzu dai ina asibitin, likitocin dai ba su ce komai ba, amma dai kamar fa ba ta da rai""" "Ashar Viper yayi masa, ya ce ""Yaya aka yi ma wuta ta kama a iya ofishin ta kawai? Me hakan" "yake nufi? Likitoci sun ce ta mutun ne?""" "Ɗan mama ya ce ""A'a ni nake tunanin hakan, bata motsi ko numfashi a yadda naga an sakata a" "mota wallahi da ƙyar idan ba mutuwa za ta yi ba""" "Liti ya ce ""Ɗan mama ko ɗan shegiya, gaba ɗaya yaron nan gaɓo ne, ya za ayi ka gaya masa" "wannan maganar?""" "Walid ya karɓi wayar daga hannun Viper, ya saka a kunnensa ya ce ""Ɗan mama kana ji na?""" """Eh oga Walid""" """Duk abun da ka ke ciki, ka din ga sanar da mu""" """To oga walid in sha Allah""" """Jikinta wutar ta taɓa ta ne?""" """A'a, ba ta ƙone ba, hayaƙi ne ya yi mata illa, wutar ma ba ta kama sosai ba""" """To shikenan, muna saurarenka""" "Walid ya kalli idon Viper, yadda ya bayyanar da matsanancin tashin hankali." """Viper, ka kwantar da hankalinka dan Allah komai zai zo da sauƙi, in sha Allah ba zata mutu ba," "sai ta cika maka burinka""" "Jiki a sanyaye ya ce ""Walid yanzu shikenan duk wanda ya raɓe ni, rayuwarsa sai ta shiga hatsari," "idan ita ma ta rasa ranta fa, jikina yana bani set up ne abun nan""" "Liti ya ce ""Kar ka zargi kanka, dama can wannan ba ta ji, kuma haryanzu ai bata fara shari'ar ka ba," "balle ace saboda kai ne""" "Walid ya ce ""Ya isa haka liti, kai abu ba ya wucewa a wurinka""" """Yaushe zai wuce, tun da ta munafurce ni, ta saka aka kamani""" *** "Abba kuwa Allah ne ya tsare bai yanke jiki ya faɗi na, bayan sanar masa da cewar, gobara ta kama a ofishin Nabila tana Asibiti." "Haka Nasir ma, cikin gigita da tashin hankali, ya nufi Asibitin da aka ce an kai Nabila." "Likitoci sun hana kowa ya shiga, an cire mata kaya an saka mata wata gown, ana duba jikinta ko da in da ta ƙone, amma babu, sai dai ga zuciyarta na bugawa, amma babu numfashi, idan tayi" "kamar zata yi numfashi, sai tayi ta tari, hayaƙi na fita ta hancinta da bakinta, sai tayi ɗif." "Gaba ɗaya Abba a rikice ya ƙaraso asibitin, cikin matsanancin tashin hankali Abba ya ƙarasa" "asibitin, zuwansa babu daɗewa Nasir ma ya ƙaraso, Abba ya nemi a bar shi ya ganta, amma aka ce ba a shiga likitoci na aiki tukuna." "Abba ya ce "" 'ya ta ce, ko me za ayi mata ayi a gabana, idan ma ta mutu ne a bari na ganta, ai ni musulmi ne na kuma yadda da ƙaddara mai kyau ko mara kyau"" suna ƙoƙarin lallaɓa shi ya haƙ" "ura kar ya shiga, ya burkice musu, babu shiri aka bashi damar shiga wurinta." "A kwance ya tarar da ita, ana ta allurai, ya ƙarasa gaban gadon ta ya zuba mata ido, dama ya lafiyar kura balle ta yi hauka, an sha wahalar ciwonta na asma sosai da sosai, sai da ta girma ta ɗ" "an samu sassauci, tayi gado mai wahala, dan mahaifiyarta ce mai ɗauke da ciwon ta gada." "Ya kalleta a kan gado, sai ya ga ta koma masa kamannin mahaifiyarta sosai da sosai, lokacin da" take gadon asibiti ta riƙe hannunsa a halin rashin lafiya. "Ya riƙe hannun Nabila, ya ga alamar akwai rai a jikinta, amma a galabaice take, ya daɗe yana yi" "mata addu'a, sannan ya tashi ya fita waje." "Barrister Kabir kuwa tuni suka yi reporting wurin Jami'an tsaro, aka zo aka fara bincike a kan musababbin tashin wutar, abun bai tsaya iya nan ba, sai da aka tattare masu gadin wurin, aka tafi" da su wurin 'yan sanda domin fuskantar tuhuma. "Sumayya ma tun kan ta ƙaraso asibitin take uban kuka, saboda yadda aka gaya mata faruwar abun," ta riga ta fitar da rai Nabila tana raye. "Sai da Nabila ta shafe awa biyu, likitoci na procedure daban-daban a kanta, aka samu numfashinta ya dawo, sai dai a wahale take yin sa, aka fito da ita daga emergency, aka mayar da ita wani ɗ" akin. **** "Bunkure ta daki tebur ta ce ""Tana raye kenan?""" "Mutumin gabanta ya ce ""Eh ranki ya daɗe, an samu nasarar fitar da ita daga wurin, amma na samu" "tabbacin tana raye, bata mutu ba sai dai tana cikin mawuyacin hali""" """Babu ruwana da mawuyacin hali, wannan wane irin aiki ne? Yaya za ayi ni ga yadda muka yi da" "ku, amma abun da ku ka yi daban?""" """Ba daga mu bane ba ranki ya daɗe, wallahi aiki an yi shi yadda yakamata, agajin gaggawa aka" "kai mata shiyasa""" "Ta numfasa ta ce ""Shikenan, zaka iya tafiya, a asibitin zan saka a ƙarasata""." *** "Hankalin Viper bai dawo jikinsa ba, sai da ɗan mama ya dawo, ya tabattar masa da a kan idonsa aka fito da ita, tana raye, kuma ba ta ƙone ba, ko ƙwarzane babu a jikinta." "Nannauyar ajiyar zuciya Viper ya sauke, yana fatan Allah ya sa hakan, ya kuma bata lafiya." "Hatta 'yan gidan su Nabila, sai da suka tausayawa halin da take ciki, duk da ba shiri suke yi da ita ba, baba magajiya kuwa kuka ta ɗora hannu a ka ta din ga yi, ba ta san iya tashin hankalin da zata" "shiga ba, idan aka ce ba Nabila." "Sumayya na gefen Nabilan, ta riƙe hannunta tana ta matsar hawaye, tari ne ya kuma turnuƙe ta," "kawai ta yinƙura zata tashi zaune, duk suka nufo kanta, Sumayya ta riƙeta tana kiran sunanta." """Viper wuta, wani ya kulle ni ta waje, ku taimaka mini, Viper wuta"" gaba ɗaya sai suka yi sak," suka zuba mata ido. "Abba ya ce ""Waye kuma Viper?""" "Cikin matsananciyar tuhuma Nasir yake bin ta da kallo, da yake ta surutai cikin fita hayyaci." "Barrister Habib ma sak yayi, Sumayya ta ce ""Abba sunan wani ɗan daba ne, da take bincike a kan" "sa, maybe tana ƙadamin aiki a kansa ne abun ya faru""" "Abba ya ce ""Na rasa irin Arfa, wataƙila ma a dalilin wannan kwashe-kwashen nata, aka yi yinƙ" urin cutar da ita. "Barrister Habib ya ce ""Bana tunanin haka sir, maybe ƙaddara ce kawai, ai tana yawan zancen ɗan" "daban nan ne, ta ce Yayanta shi ne incharge na nemansa tana fatan ta taimaka masa""" "Nasir duk da ido yake bin su da kallo, yanayin yadda take surutan, kamar akwai sabo da kuma sha" ƙuwa a tsakanin su. "A hankali sumayya ta ce ""Masoyiyya""" """Na'am sumy""" """Na'am""" """Wuta aka saka mini a office ɗina, da ta tashi, na tafi da gudu na buɗe ƙofa na ji an rufe ni ta" "waje""" "Abba ya ce ""A'a Arfa, Allah ne dai ya ƙaddara tashin wutar, kar ki zargi kowa""" "Nabila ta ce ""Abba, ni fa na buɗe office ɗin da kaina, na bar key a jiki ta waje na shiga, da wutar" "ta tashi na je na buɗe, na ji an murɗa key ɗin sau biyu""" "Abba ya ce ""Ki na cikin hayyacinki, kin farka gaba ɗaya?"" Ta jinjina masa kai." "Ya ce ""Alhamdilillah"" nan aka din ga jera mata sannu, duk da tana ta haki a hakan ma." *** "Ramma ce a tsaye, ta shirya cikin doguwar rigar abaya, ta ɗora mayafin a kanta, Abdul ya bata facemask ya ce ""Saka wannan"" ta karɓa ta saka, ya ce ""Wow, kin yi kyau sosai beb"" ta yi murmushi tare da gyara mayafinta." "Ya riƙe hannunta, har cikin motarsa, da hannu ɗaya yake tuƙi, hannunsa ɗaya kuma ya riƙe nata," "loka-lokaci sai ya sumbaci hannunta, yana jin wani irin so da shauƙinta yana ratsa ilahirin jikinsa." """Ni ka daina shafa mini yawu a hannu""" """Haba Rahama, yawun ƙauna ne fa"" yayi maganar yana satar kallonta." "Ta jingina da seat ɗin motar, ta numfasa ta ce ""Yaushe ne bikinka, ko an yi ne?""" "Ya ce ""A'a, ya za ai, ayi ba ki sani ba? Wai bata ƙarasa karatu ba, da an so ayi ne idan ta dawo" "shikenan ta tare, babanta ya ce a bari ta gama, saura 2months""" "Ramma ta ce ""Allah sarki, ni nawa karatun ko oho, na zama karuwa""" """Haba rahama, dan Allah ki daina wannan maganar, ina da kyakykyawan tanadi a kan rayuwar ki" "da iliminki, na san na cutar da ke, amma zan gyara laifina in sha Allah"" tayi masa shiru tana kallon titi." "Dare ne sosai, duk sahu ya ɗauke." "Ya zuba mata ido, a lokacin da take shan ice cream ɗin gabanta, ya tuna yadda yake ta fama da" "mahaifinsa, ya tsunduma tunanin ya zai yi ya sanar da shi batun ramma? Dan sai dai ayi wadda za" "ayi a kan ramma, amma bai ji duk iya bala'in da za ayi zai rabu da ita ba, ta kalleshi ta ce ""Ka sha" "mana"" yayi murmushi ya jinjina mata kai, mama ya cigaba da jujjuya cokalin." "Hakan ya sanya ta fuskanci a cikin damuwa yake, ta ɗebo icecream ɗin ta kai bakinsa, ya ɗaga" "ido ya kalleta, ya buɗe bakinsa ya karɓa." "Ya ce ""Kin yafe mini dukan da nayi miki, kin daina fushi da ni?"" Ta jinjina masa kai alamar eh." """To ɗaya laifin fa?""" """Ban yafe wannan ba"" ta bashi amsa kai tsaye." """Tun da ki ka yafe wannan, wancan ma zaki yafe mini in sha Allah"" ta yi shiru tana kallonsa." "Sai da ta gama ciye-ciyenta son ranta, sannan ya ce ta raka shi asibitin abokinsa, zai duba wasu" marasa lafiya. "A zuciyarsa yake zargin kamar wani cikin ne da ramma, amma bai tabattar ba, kuma bai ambata ba, balle ta tashi hankalinta, muddin kuma ya ce zai gwada za ta gane, kuma ta daina yarda da shi, dan" "ce mata yai, yayi mata allurar planing, ba zata sake ɗaukar ciki ba sai allurar ta sake ta." "Waɗanda ya yi wa tiyata a asibitin ya duba, sun fito take tambayarsa ""Nan ne asibitinka?""" "Ya ce ""A'a, Asibitina na can wajen gari, na kan je wasu asibitocin da aka buƙace ni, na gabatar da" "aiki, zan kai ki namun ma ki gani""" "Ramma ta ce ""Naka dai""" """A'a namu dai, idan komai ya daidaita, ai bikinmu za ayi, na nuna wa duniya ke, komai ya wuce""" "Ta ce ""Taɓ kwaɗo""" "Babu tsammani yayi karo da wata matashiyar budurwa, hannunta riƙe da ledar Pharmacy." """Ke ba kya gani ne?""" """Ban gane bana gani ba, kawai ka zo ka tsaya a hanya, kana rangwaɗa, da alama kai jin daɗi ne ya" "kawo ka asibitin ba mara lafiya ne da kai ba"" Ramma ji tayi kamar ta san muryar." "A fusace ya yinƙura zai yi masifa, ramma ta ce ""Dan Allah ki yi haƙuri, mun tsare hanya kam," "Allah ya ƙara afuwa ga mara lafiyan""" "Sumayya ta amsa da ""Amin"" ta harare shi ta wuce." """Dan Allah ka din ga rage faɗa, har marasa lafiyar ma, faɗa ka ke yi musu, haba kai kuwa"" ƙwafa" yayi suka tafi. *** "Sosai Viper yake son kiran wayar Nabila, amma babu hali, dan ɗan mama ya tabattar masa da ya ga an fito da wayarta, da jakarta da system ɗin ta, wani mutum ya karɓa, amma alamu sun nuna a wurin yake aiki shi ma." "Viper bai san waye ya karɓi wayar da system ɗin ba, akwai ayyukansa a cikin system ɗin ta, da" suke buƙatar sirri sosai da sosai. "Nasir ya karɓi system ɗin Nabila da wayoyinta a hannun barrister Habib, sai dai ya kasa buɗewa, dan bai san menene password ɗin ta ba, har su walida ya tambaya ko sun sani, suka ce ba su sani ba." "Ƙaramar wayarta kawai ya iya buɗewa, sunan confidential ya fara nema, yayi sa'a ya samo lambar, sai dai ya duba lambar da aka yi saving a kan sunan, ya tarar da suna babu lamba, ya duba ya duba, amma ya rasa samun lambar, ya din ga kwafar lambobin wayar, yana dubawa a Truecaller ɗin sa," amma babu wani suspicious abu da ya samu. "Yanzu tantamar da yake yi a kan Nabila, ya wuce zargi, akwai abun da take aikatawa na rashin gaskiya, ya ƙallafa ransa sai ya gano, waye wannan mutumin da ya gansu tare sau biyu." "A kunne ya bar wayoyin, sai dai yadda aka din ga kira babu ƙaƙƙautawa, tun yana ɗagawa yana" "saka ran, zai samu wani abu na information, harya haƙura ya daina ɗagawa." "Nabila ta farga da rashin wayoyinta, ta tambayi a bata wayoyinta, aka ce mata suna wurin Nasir, ta" jira ya zo Asibitin ta ce ya kawo mata wayoyinta ya ce ba zai bayar ba. "Cikin mamaki ta ce ""Amma meysa na san za a neme ni a wayar?""" "Ya ce ""Kina fama da kanki, uban me zaki yi da wata waya?""" "Sumayya ta ce ""Ke ma dai arfa, uban meye a wayar ne, ki hutawa kanki ki gama farfaɗowa"" kallon Nasir take yi, tana nazarin irin kallon da yake yi mata, ta fara fatan Allah ya sa ba wani" abun ya gano a wayar ba. "Abba ne ya shigo, suka gaggaisa, ya din ga tsokanar Sumayya tare da Nabila, ko wurin aiki Sumayya ba ta zuwa, tana liƙe a asibiti da Arfa, Sai da Nabila ta magantu a kan wurin aikin" sumayya amma ta basar da ita. "Ƙwanƙwasa ƙofar ɗakin aka yi, sannan aka buɗe." "Jmau'an tsaro ne da bindigogi suka fara shigowa, gaba ɗaya suka yi ƙuri da ido, suna kallonsu." "Alhaji wada m karofi ne ya shigo, suka gaisa da Abba, Nasir ma ya gaishe shi." "Nabila ta ce masa ""Lafiya, wannan kama ni za su yi?""" "Yayi murmushi ya ce ""Saboda ke ce Sarkin laifi ba, yaya jiki ashe haka wannan iftila'in ya faru?""" """To ai na ganka da yan sanda me na yi?""" "Yayi mata shiru, suka ƙarasa gaisawa da Abba suka gaisa, Sumayya ta ce ""Ina kwana?""" """Lafiya ƙalau T ladan, ya gidan radio?""" """Yana nan sir""" "Nabila ta ce ""Dama kin san shi?""" Sumayya ta girgiza kai. "Ya ce ""Eh ba lallai ta sanni, amma ita muryarta sananniya ce ai, kuma kina bani labarinta ai, ko ba" "sumayya T ladan ba ce?""" Sumayya ta jinjina kai tana murmushi. "Nan yake gaya wa Abba, ai a law firm ɗin Barrister Kabir yake ganin Nabila suke gaisawa, shi" yake sanar masa tsautsayin da ya faru. "Nasir dai ya din ga mamakin yadda karakainar Nabila, ta kai ga ta ga sanin manyan mutane har haka, bayan ya gama duba ta, yayi musu sallama ya tafi, Nasir ma da Abba tafiyar suka yi, aka bar sauda da Sumayya, suna tafiya Saudan ma ta shura takalmanta ta fice, dama ba son zaman take yi" ba. "Sumayya ta kalli Nabila ta ce ""Nabila na ajiye aikina fa""" "Nabila ta waro ido ta ce ""What? Saboda me?""" "Sumayya ta numfasa ta ce ""Hakan shi ne yafi dacewa ne""" """Sumayya wannan ai wauta ce, meyasa zaki ajiye aikin?""" """Na gaji da barazanar da ake yi mini, da tashin hankalin da ake yi mini, Allah ya taimake ni an shiga tsakanina da indabo, ya rabu da ni, amma support ɗin da muke baki, da ni da yaya murtala baki ga rashin mutuncin da ake yi mana ba, ga hantara da tsangwama. Da barazanar kora babu yau" "babu gobe, na ajiye musu bakin da Allah ya tsaga ba ya hana shi abun da zai ci""" "Cikin matsanancin damuwa Nabila ta ce ""Sumayya baki kyauta mini ba, da ki ka ɓoye mini" "wannan babban al'amari haka, ki rasa aikinki a dalilina, haba sumayya""." "Sumayya ta yi dariya ta ce ""Kar ki damu, umma ma ta sani, kuma ta bani ƙwarin gwiwa yaya murtala yana yi mana processing ɗin wani sabon gidan radio, za su bani aiki da ni da shi, shi ma" "baro can zai yi, su ci kansu""" "Cikin damuwa ta ce ""Sumayya duk da haka ban ji daɗi ba, idan kuma ba a samu aikin ba fa?""" """Zafa a samu in sha Allah, na bawa yaya murtala cv na, ya ce mini sun yi murna sosai da jin zan" "koma wurinsu, sabon gidan radio ne, za a buɗe dama lawisa a ƙule take da ni, ta ƙara takura mini, saboda mutane suna yi na, sai su kwaɗa gidan radion su cinye""" "Nabila ta numfasa ta ce ""Sai mu duƙufa addu'a masoyiyya, Allah ya sa ki samu ya tabattar da" "dukkanin alkhairansa""" """Amin, amma Nabila wannan wutar kuwa ba set up bane ba, ana sane aka sakata ba?""" "Nabila ta ce ""Set up ne mana, sai da na shiga na zauna sannan ta kama, na taho na fita kuma, aka" "sakawa ƙofar key""" """Wa ki ke zargi?""" "Ta girgiza kai ta ce ""Bana zargin kowa, abun da nake yi ne dai ba zan bari ba""" """Nabila""" """Na'am sumayya T ladan""" """Haryanzu kina zuwa in da Viper yake kuna haɗuwa?""" "Nabila ta kalleta ta ce ""Wace irin tambaya ce wannan?""" """Amsa zaki bani, ba ki tambaye ni ba""" """Ban ga gurbin yin tambayar a nan ba, ko dai haryanzu yaudarata ki ke yi, aiki ki ke yi wa Indabo" "a kaina?""" """Ko kaɗan, indabo ma Allah ya yi mini maganinsa, ya rabani da shi, amma alamu sun nuna kina" "haɗuwa da Viper, da sunansa ki ka farfaɗo a bakinki""" """Tuhumata ki ke ko zargi?""" """Babu ɗaya""" """To idan har ba aiki ki ke yi wa wani a kaina haryanzu ba, to ki bar maganar nan""" "Sumayya ta ce ""Shikenan, an bar ta""" "Likita ne ya shigo, ya kalli Nabila ya ce ""Barrister jiki yayi kyau, jiya doctor yasar ya shigo, ai da" "na sani nayi masa magana ya duba jikin naki, idan da wani abu da zai ƙara miki""" """Doctor ni dai dan Allah ka sallame ni, na gaji wallahi""" """Ki yi haƙuri, zai sake shigowa yanzu, mun yi waya da shi, zai ga masu hawan jini kan ya wuce," "kin san shi abun ne ya haɗar masa, ga siyasa ga kuma aikin likita""" """Ashe kuwa zaka neme ni ka rasa a asibitin nan, tafiya ta zan yi na gaji""" """No ba za ayi hakan ba, bari na rubuta miki sallama, Alhamdilillah ai jiki yayi kyau sosai""." "Sumayya ta ce ""Mun gode sosai doctor""" "Tashin hankalin da Indabo yake ciki a yan kwanakin nan, duk sai tsufansa ya fito, ko bacci baya" "iya yi sai ya sha ƙwayoyi, saboda damuwa da tashin hankali." "Cikin dare ya ga kiran Wada karofi, ransa ya ɓaci kamar kar ya ɗaga, sai kuma ya ɗaga ya ce" """Karofi wani irin wulaƙanci ne ya sanya kake kirana ƙarfe ɗaya na dare?""" """Kashedi, da kuma gargaɗi, Nabila ta tsallake wannan tarkon da kuka yi mata, kamar yadda na taka maka burki a kan ƙawarta, ina mai ja maka kunne a kanta, wallahi wani abu ya samu" "yarinyar nan, zan yi abun da baka so""" """Wacece hakan?""" """Ka fi ni sanin wa nake magana a kai indabo, mukiyaye abun da zai zubar mana da mutunci a idon duniya a matsayin mu na 'yan siyasa kuma sirikai da ni da kai, ba zan lamunci wani mummunan abu ya same ta ba, mu cigaba da yaƙar juna ta ƙarƙashin ƙasa kar duniya ta ji wannan labarin ka kiyaye""" *** "Madaki ne ya lallaɓo ya fito daga cikin ɗakin da yake, yana ta kiran wayar lakwari, amma taƙi shiga." "Walid ya gani a tsaye, yana kallonsa, ya tsaya cak, suna kallon kallo." "Walid ya yi murmushi ya ce ""Duk ƙoƙarin da ka yi, ka gaza ɓoye mamakinka na ganina madaki," "wannan da uban gayyar ka gani sai yaya kenan?""." """Meya kawo ka wurina?""" """Ahh ai ba abun faɗa bane ba, zuwa na yi na duba ya yanayin jikinka yake? Ni na hana mai zamani zuwa wurinka, da yazo nan da wani zancen ake yi ba wannan ba." "Zuwa yanzu na san kana mamakin ina lakwari, kuma ya aka yi muka san in da kake? Lakwari dai Macijin nan mai ban tsoro viper, ya saya shi a cikin raminsa, sannan indabo yanzu ba ta taka yake yi ba, dan haka yanzu zaɓi ya rage gareka kafin mai zamani ya waiwayo gareka, ko dai ka fita ka nemi madafa, waɗanda ka zalunta su ƙarasa ka, ko kuma yunwa da wannan ruɓaɓiyar ƙafar taka su ƙarasaka a wurin nan." "Ba zaka yi wa mai zamani wani amfani ba, saboda ya riga ya gama da kai, iya hakan nan da ya barka azaba ce mai zaman kanta, sannan ka sani, duk in da ka motsa ka tafi, yana sane da in da ka ke, ɗaukar fansa cikin ruwan sanyi"" ya ƙarasa maganar yana ciro wata zabgegiyar wuƙa daga ƙ" ugunsa. "Madaki ya zaro ido ya ce ""Kar ka matso in da nake, kar ka zo in da nake"" yayi maganar yana dakatar da walid, dan idan yayi kyakykyawan yinƙuri, ji yake kamar naman cinyarsa zai zaftare ya" faɗi. "Babu tausayi, Walida ya kwarfe shi, ya danne shi a ƙasa, ya zana masa V a gadon bayansa da wuƙ" ar hannunsa. "Ya ce ""Ka ce labarin Viper ba zai cika ba, sai an ambaceka, to kai kuma har ka ƙarƙare rayuwarka kana dakonsa da alhakinsa a kanka da gadon bayanka. Ka shirya a kowane lokaci zamu iya yi wa waɗanda ka zalunta cunenka. Kuma ina yi maka Albishir da hukuma ta kama tabar wiwinka da ƙ" "wayoyi, baka ga tsuntsu ba ka ga tarko madaki""" *** "Nabila ce tsaye a falo, tana yi wa Nasir magiya." """Dan Allah Dsp ka bani wayoyina, ina buƙatar cigaba da amfani da su, ga ayyukana a ciki, amma" "ka riƙe mini waya da system ka hana ni""" "Ya kalle ta ya ce ""Ba dai da wayoyin ki ke janyo wa kanki matsala ba, kin yi sallama da su, ba zaki sake riƙe waya a gidan nan ba, and beside gaba ɗaya ni ban yarda da ke ba, akwai abun da ki" "ke aikatawa wanda ki ke ɓoyewa""." """Dan Allah ni ka bani wayoyina, ya za ayi ka karɓe mini kayan aikina, yaya wai meyasa ka ke yi" "mini haka ne?""" """Ni ki ke ɗagawa murya haka?""" """To ka bani mana""" "Abba ne ya shigo falo ya ce ""Haba arfa, daga farfaɗowarki daga ciwon ki ke ta ɗaga murya har" "haka, sai numfashin ya sake samun matsala""" """Abba kayan aikina ya ɗauke mini, ka ce ya bani wayata da system ɗina""" "Mama a ƙule ta ce ""Dan ubanka ka bata kayanta, ƙannanka babu wanda ya isa yayi maka abun da" "take yi maka, da sun motsa sai hantara da zagi, amma kalli abun da take yi maka""" "Abba ya ce ""Tsaya, Nasir meyasa zaka kaeɓe mata kaya ka hanata?""" """Abba nayi seizing wayoyinta ne for a while, da su take amfani take janyo mana magana," "haryanzu ba a tabattar da musababbin tashin wutar nan ba, amma zai iya yiwuwa saboda abubuwan da take yi ake neman sabauta rayuwarta""." "Abba ya ce ""Haka ne, kana da gaskiya, amma ka yi haƙuri ka bata, ke kuma ki kiyaye da" "abubuwan da zaki din ga aikatawa da wayar nan, idan ba haka da kaina zan ƙwace su aikin ma ki daina yin sa. Bi shi ya baki kayanki""" "Nasir ya numfasa, yayi gaba ta bi bayansa, ya ɗaukko ya miƙa mata yana kallon idonta cike da" tuhuma. """Wuƙa garin tone-tone take tono wuƙar yanka kanta, yaya, ina martabaka da martaba zumuncin da yake tsakanina da kai. Bana son harkar aiki ta zama tangarɗa ga wannan alaƙa da na lissafa maka, bayani ne nake yi maka da manyan baƙaƙe a kan farar takarda, sai dai ba zaka gane nufina a yanzu ba, ko dai ka bari a haka, ko kuma lokaci ya zo da fassarar da ba ita kake buƙata ba, ina fatan idan" "lokacin ya zo, zaka tuna wannan bayanin nawa, kuma ba zaka ga abun a bazata ba""." Ayshercool 08081012143 ₦500 ne via 0009450228 Aisha Adam jaiz bank sai shaidar biya ta 08081012143 Wanda za su jira document 1K ne. 90009343 'Yan Nijar ku turo katin airtel na 300fcfa Arewabooks ayshercool7724 "Cikin rashin fahimta, yake bin ta da ido, sai dai tamkar soko, har tayi maganar ta gama, bai iya" "tofa mata uffan ba, har tayi ta gama ta karɓi wayoyinta da system tayi tafiyarta ɗaki." "Ɗakin ta rufe, ta shiga duba call logs ɗin ta, amma kaf ba ta ga kiran Viper ba, wani irin takaci ne" "ya turnuƙe ta, wato duk siraɗin nan da ta tsallake da kyar, bai kirata ba, balle ya ji a wane hali take ciki." 'To idan kuma bai san abun da ya faru ba fa?' ta tambayi kanta. Ta basar ta ce bari ta jira zuwa "gobe, taga ko zai kira wayar." "Ƙasan zuciyarta kuma ta din ga hamdala da Allah ya sa bai kira ɗin ba, dan da ya kira Nasir zai ɗ" "aga ne, kuma ba abun da yayi masa zafi, zai iya gaya masa waye, idan ya tambayi waye." *** """Naja wai ko ke ki ka saka aka yi wa yarinyar nan wani abu ne?""" """Wace yarinyar?""" """Barrister nan? Karofi ya kira ni yana yi mini kashedi, ina tsoron Allah ina tsoron shu'umancin" "mutumin nan""" "Naja ta ce ""Eh, ni na saka aka yi mata haka, dan so nayi ma ta mutu, na ga kai ka ƙi mayar da hankali ka yi abun da yakamata, ba zai yiwu ta tona mini asiri a banza ba, mutuncina ya zube a idon duniya ba. Ba a taɓa samun wanda ya yi yinƙurin kawo mini tangarɗa ba, ka ƙyale shi ka ke" "jan ƙafa a kansa ba, sai a kan wannan yarinyar""" "A fusace Indabo ya ce ""wai meyasa ki ke haka ne Naja? Duk iya ƙoƙarin da nake yi a kan lamarin nan? Na gaya miki zata iya zama tarkon da zan kama Viper, kuma ina amfani da ita wurin yi wa yayanta barazana yake yi wa umarnina biyyaya, lokaci ɗaya karofi ya bijiro, yake yi mini gargaɗi a kanta, wai sonta yake yi, wataƙila ma yi yake yi dan kawai ya muzanta ni. Amma gaba gaɗi" "babu shawara, kin je kin aikata abu, kin saka yana ta kiran wayata yana nema ya tozarta ni""" """Nifa ban yi danasanin abun da nayi ba, kuma zan cigaba da bibiyarta sai na ga bayanta, ban damu da abun da zai biyo baya ba muddin zan tsira, kar ka manta kai ka koyar da ni hakan"" ta kaste" wayar tana jan guntun tsaki. *** "A gurguje Abdul ya yi breakfast a wurin ramma, yayi mata sallama ya fice." "Bayan fitarsa ta daɗe tana kuka, kamar zuciyarta ta fashe haka take ji, saboda damuwa da tashin hankali, tun tana lissafin adadin kwanakinta a wurin Abdul, har ta karaya lissafi ya ƙwace mata, tana matuƙar son sanin halin da mahafiyarta ke ciki. Ta sha attempting ta saka wuƙa ta kashe Abdul, amma sai ta kasa, ita kanta ta sha yinƙurin kashe kanta, amma tuna makomarta sai ya" sanya ta fasa. "Gashi yanzu sam ba ta iya bujirewa buƙatar sa, rayuwa suke yi tamkar ma'aurata, ta yi kuka tayi istigfari amma da ya zo ya kalallameta da zance, sai ta bayar da kai bori ya hau, wasu lokutan idan ta kalli hidimar da take yi masa, ta gyaran gida, kula da abincin sa, yin wani abu da zai saka shi" farinciki sai ta yi sai ta ji haushin kanta ya isheta. "Abdul kuwa Asibitin su doctor AK ya wuce, ofishin sa ya je suka gaisa ya ce ""Kai ne zaka yi" "morning kenan?""" "Ak ya ce ""Eh ni ne your excellency kai fa zuwa yanzu ya ci ace ka ajiye Lab coat, tun da ana ta ƙ" "ishin-ƙishin kai ne zaka zama lamba biyun garin nan, zaka koma field ɗin dadynka""" "Abdul ya ce ""Nifa Ak ko lamba ɗayan ƙasar nan na zama, ba zan iya daina aikin likita ba, ina" "gudanar da office ina consultation"" suka tafa tare da kwashewa da dariya tare." "Ak ya ce ""Sannu doctor excellency, ina ƙanwar ka da kuka zo tare kuwa? Baka wani tsaya mun" "gaisa da ita ba, ko dan kar na ƙyasa ka bani ita, ai ban taɓa sanin kana da ƙanwa ba, na zata kai ne ƙarami""" "Abdul ya tsuke fuska ya ce ""A wane room patient ɗin take ne?""" """Ai ta uzzura sai da aka sallameta, amma Alhamdilillah jikinta yayi kyau sosai, sai dai ka yi mana ward round idan da abun da za a taimaka mana ayi mana"" ya jinjina kai ya juya ya fice daga office" ɗin. *** "Tun bayan da ɗan mama ya tabattarwa Viper an sallami Nabila daga asibiti, yake kallon wayarsa yake jiran kiran wayarta, amma shiru ba ta kira shi ba, har ya fara tunanin ko ƙarya ɗan maman ya yi masa da ya ce ta warke an sallame ta." "Shigowar Walid ce ta dawo da shi hayyacinsa, ya ɗaga kai ya kalle shi, Walid ya ciro wuƙarsa ya zareta daga cikin gidanta, ya kalli Viper ya ce ""Lakwari da gaske yake, na iske madaki, ƙafarsa ba ta takuwa, raunin da ka yi masa ya zama gyambo a ƙafarsa, ga shaida harafin sunanka na zana" "masa a gadon bayansa, yadda shi ma ba za a kammala na sa labarin ba, dole sai an ambaceka""" "Viper yayi kamar zai yi murmushi ya ce ""Mai laya""" "Walid ya ce ""Na kiyayi mai zamani, Allah ya kiyaye mini kai ɗan amanata""" "Viper ya ce ""Ina kewar wancan kwanakin, kwanakin da aka yi rashin ji da gaske, yanzu girma ya" "fara zuwa duk an daina wasu abubuwan""" "Walid ya yi murmushi ya ce ""Rashin jin ai duk ba na daɗi bane ɗan uwa, duk da kai ƴar madara ta fara saita mana kai, Allah ya karɓi kayarsa, amma duk da haka ba zan gushe ba ina jinjinawa Nabila, dan ita tayi abun da muka kasa, albarkacinta mun sake ganin walwala a tare da kai, duk da" "ba ta kai ta wancan lokacin ba""" """That angry bird, masifaffiya"" ya furta yana kallon liti ya ji me zai ce." "Aikuwa kamar mai jiran ƙiris hya e ""Ba wata tsiya da ta tsinana masa, sai shegen naci da taurin" "kan tsiya, mara kunya da ita sai kayan ƙaton kai kamar injin markaɗe da ƙwala-ƙwalan idanuwa" "kamar an soya aya, ai wallahi 'yar madara duniya ce, ga kunya da girmama mutane, wannan" "tsagerar kuwa, tana zazzarewa mutane ido, ni har mamakin mai zamani nake yi wallahi""." "Walid ya ce ""Ai ita ce daidai da ku, daga kai har mai zamanin, mu da muka kasa iya masa, ita ai" "gata nan yana saurarenta""" """Ba wani nan, ni haryanzu ba gama yarda nayi da ita ba, yar leƙen asiri ce""" "Walid ya ce ""To tayi leƙen asirin, ai ba asirinka ta leƙa ba ko?""" """Ware, ban da naga kuna ta tata, da sai na saka tsumagiya na jiƙa mata jikinta, sai na yi mata" "mazinacin dukan da ba zata iya tashi ba, na rama muguntar da yayanta yayi mini a station""" "Viper yana gefe yana jin su, wasu lokutan faɗan Walid da liti nishaɗi yake saka shi, kamar sako da" sako. "Nabila wuni tayi da waya a hannu, amma shiru babu kiran Viper, shi ma haka ne, wuni yayi yana" "kallon wayar ta sa yana sauraren kiran wayarta, amma ba ta kira ba." *** "Nasir ne zaune a ɗakinsa, yayi zurfi sosai a cikin tunani, yana ta tuna wasu abubuwan da suka faru a 'yan kwanakin nan sosai yake jin yana zargin Arfa tana aikata wani rashin gaskiya, da take ɓoyewa, mussman da ya ji ta ambaci viper lokacin da ta farfaɗo, ba zai yiwu a ce magagi ne kawai ba, kuma a yan kwanakin nan tayi watsi da lamarin cewa zata taimaka masa a kan nemansa balle ya ce tsananin saka abun a ranta ne ya sanya ta farko da sunansa, amma haryanzu yana son sanin" "dalilin da ya sanya Indabo ya ce zai yi tarko da Nabila ya kama Viper, menene haɗinta da shi?." "Nabila tana zaune a kan gado, tana waya da Alhaji Wada, sai kashe murya take yi, wai ita" "haryanzu ba ta warke ba, ya biye mata sai sangarta take yi, kamar ba babban mutum ba yana lallaɓ ata, tun da ya ce zai kuma zuwa gida dubiya ta ce masa ai ta warke ba sai ya zo ba." "Sallamar baba magajiya ce ta sanya tayi masa sallama, ta ɗago ta kalleta da murmushi." """Yauwwa yar gari, ai dama zuwa nayi na tashe ki, ki samu ki karya ki sanya wani abun a cikinki," "ashe ma kin tashi """ """Eh hajjaju, ina kwana""" """Lafiya lau, ya ƙarfin jiki kuma?""" "Nabila ta ce ""Alhamdilillah da sauƙi""" """To Allah ya ƙara kiyayewa, ki cigaba da addu'a Allah ya ƙara tsarewa, dama mu ma addu'a cikin" "yin ta muke babu dare babu rana, Hasbunallahu wa ni'imal wakil, ki yawata faɗarta babu adadi, da" "yardar Allah ba dai mutum ba sai dai Allah""" "Nabila ta yi murmushi ta ce ""Kin faɗa kin nanata mini, na daɗe da haddacewa ai""" """Kya ci ƙaniyarki da kin daɗe da haddacewa, zamanin nan na yanzu waya ce miki ana zama haka? Kana da ido ba na ganin gari ba, Addu'a kake tuƙuru iya yinka, baka san waye maƙiyin fili da na" "ɓoye ba""" "Sosai Nabila take dariya ta ce ""Aikuwa maƙiyina yana ruwa, dan ni kaina ba wani cikakken saiti" "ne da ni ba in ji Abba""" """Ke ki yi addu'a kawai yar nan, tashi ki je ki samu abun da zaki ci"" ta saukko daga kan gadon, ta" "fice falo tana miƙa, wayarta take kallo lokaci lokaci, duk kiran Viper take jira, amma shiru." "Sauda ta kalleta ta ce ""'yar asara an fito""" "Nabila ta ce ""Wallahi kuwa, Allah ya nufa barka da safiya, bazawara uwar son banza ga gadonki" "ga na asara""" """Arfa, me ki ka ce?""" """Sauda kin sani sarai bana shiru idan aka gaya mini babu daɗi, ni yanzu a kan tsini nake, magana ɗaya mara daɗi ki ka yaɓa mini, sai na yi miki goma mai zafi, ba girmata ba Allah ya sa haifata ki ka yi"" Sauda za ta yi magana, ta jiyo takun Abba yana saukkowa daga kan bene, dan haka ta haɗ" "iye maganar ta, tana kallon Nabila." *** "Abbu ne zaune a gefen gadonsa, fuskarsa sanye da farin glashi, ya zubawa hoton hannunsa ido. Shi da Zahra'u ne, da sadik, shi kuma hannunsa riƙe da Al'amin, bai fi shekaru biyu ba a lokacin, sai dai fuskar nan ta sa tamau, babu alamar fara'a." "Murmushi Abbu yayi, tun Al'amin yana yaro baya son wargi, ba shi da faa'a, ya tuna yanzu a jikin hoton ba kowa sai Al'amin, shi ma ga yadda ya zama, rabon da ya saka shi a idonsa, tun fitowarsa" "daga prsion da ya zo masa nan, kusan shekara guda kenan." """Wai meyafaru ne kamar kuka fa kake yi?""" "Ya ɗaga kai ya kalli rahila ya ce ""Kuka kuma?""" "Ta leƙa ta kalli hannunsa, ta kwaɓe baki ta ce ""Kai ta wani abu kamar ƙaramin yaro, ka ɗauki" "hoto ka saka a gaba kana kuka, haba kai kuwa?"" Yayi mata shiru bai ce komai ba." """Abbu, dan Allah magana nake so mu yi da kai""" """Ina jinki""" """Dan Allah ka yi haƙuri ka yafewa Abba, ya koma kasuwa, sai raragefe yake yi a gari da shi da" "Nazifi, ina tsoron kar su faɗa wani mummunan halin, rashin sana'a ga matashi babbar matsala ce""." "Ya ƙare mata kallo ya ce ""Rahila, nawa ɗan ma da ya kangare, sallama shi nayi, ba zai yiwu in" "cigaba da jan ɓarayi a jikina suna zalunta ta ba, su yi ta yawo babu sana'ar, ai uban su yana raye, ya nemi abun yi ya ba su""" """Ni kake kallon idona ka ke cewa yarana ɓarayi?""" """Na faɗa rahila, ba ɓarayin bane ba? Wane irin gata ne ban yi musu ba, ƙarshe rashin lafiya na kwanta aka rasa wanda zai zauna da ni a cikin su a asibiti, ƙarshe cewa ki ka yi kar na ga laifin su, ba hakkinsu bane ba, amma ni na riƙe su na ciyar da su, na kula da su, ni nawa hakkin ne? Yanzu nake ƙara danasanin biye miki, na wofantar da nawa ɗan, kuma ki tattatara su gaba ɗaya su bar" "mini gida, dan ba hakkina bane ba riƙon su""" "Cikin takaici ta ce ""Wallahi ba zan rabu da 'ya'yana ba, sai dai na tattara da ni da su mu bar maka" "gidan""" """Allah ya raka taki gona, ya tsare hanya""" "Cikin fargaba ta kalleshi ta ce ""Au babu ruwanka kenan in tafi baka damu ba?"" Tashi yayi, ya ja" tsaki ya mayar da takardun gabansa ya bar ɗakin. *** "Nabila ta kasa jurewa, hankalinta ya fara tashi, ko wani abun ne ya samu Viper, duk da bai fiye kiranta ba, sai da ƙwaƙwƙwaran dalili, amma shirun yayi yawa. Yau take shirye-shiryen komawa wurin aiki, Barrister Habib ya tabattar mata da an gyara office ɗin ta, an canza mata wani." "Har ta shirya ta tsaya, ta kira lambar Viper." "Yana kwance idanunsa a lumshe, yana ɗan kaɗa ƙafa, ya ji ringing ɗin wayarsa." "Ganin lambarta sai da ya yi ajiyar zuciya, amma ya zubawa wayar ido, sai da ta kusa katsewa," sannan ya ɗaga kuma yayi shiru. """Hello Viper""" """Salamu alaikum"" ya faɗa a nutse." """Wa'alaikum Salam, kana lafiya?""" """Ƙalau""" "Cikin marairaicewa ta ce ""Wai baka san abun ya same ni bane ba? Kwana nawa baka ga kiran wayata ba baka neme ni ba, wrong connection na wearing aka yi a office ɗina, wuta ta shi, aka" "rufe ni ta waje fa""" """Na sani""" """Ka sani?""" "Ya ce ""Eh""" "Cike da takaici ta ce ""Kuma ka kasa nemana a waya, da mutuwa na yi fa""" """Allah ya jiƙanki, zahra ma da mutu haƙuri nayi, balle ke. Sai ki ƙara taka tsantsan da abubuwan" "da ki ke yi""" "Wani ƙululun takaici, ya tokare mata wuya, sosai ta ji zafin abun da ya ce mata, kawai ta katse" wayar. "Walid ya ce ""Viper, kamar baka kyauta ba fa"" yayi masa shiru, hakan ya sa shi ma yayi shirun bai" kuma cewa komai ba. "Baƙin ciki da ɓacin rai ya sanya, babu wanda ta yi wa sallama a gidan ma, tayi tafiyarta." "Tana tafe a hanya ta din ga jin wani abu mai kama da kishi, da ɓacin rai yana taso mata, har ga Allah ba ta san jauhar ba, amma tana son ta saboda Allah, amma abun da yayi mata yau, ya sanya" ta ji ranta ya sosu. """Meyake damuna ne? Wai son bawan Allah nan nake yi? Na shiga uku me yake shirin faruwa da ni ne? Idan ta tabatta son shi nake yi, na yi wauta, to yaya ma za ayi hakan ya yiwu abu daga wasa?"" Har ta ƙarasa wurin aiki, tunani take a zuciyarta. Tayi shiru tana sauraren zuciyarta dan ta tabattar da abun da take tunani gaskiya ne ko akasin haka, amma bata kai ga hakan ba, aka ƙwanƙ" "wasa glashin motarta, masu gadi ne suke yi mata barka da dawowa, tare da yi mata sannu da jiki""." "Ta saukko daga motar, suka gaggaisa, sannan ta shiga ciki, a cikin ma murnar ganinta suka din ga" yi suna yi mata sannu. "Ko mintuna talatin ba ta yi a sabon office ɗin ba, barrister Habib ya ƙaraso." """Autar lauyoyi, ƙaramar su babbar su, aminiyar sumy, ƙaramar sauro ka da ƙatuwar giwa, ba" "giwar ba hatta toron ma kayarwa ki ke yi""" "Nabila ta yi murmushin yaƙe ta ce ""Ni har ka bani kunya ma""" """To yaya jikin naki?""" """Alhamdilillah yayi sauƙi sosai""" "Ya ce ""Masha Allah, yanzu ya ake ciki da batun shari'ar nan? Zamu je prison ɗin ne wurin" "mutumin?""" """Za a bari mu ganshi kuwa?""" "Habib ya ce ""Za'a bari mana ba dole ba, ai na je lokacin kina gadon asibiti, ba na son abun da zai" "kawo tsaiko a harkar shari'ar gaba ɗaya""" """Kai amma na gode sosai yaya habib """ """Kar ki damu Nabila, ba ke ba, hatta ni na ji haushin yadda shari'ar nan ta gudana, kuma cin" "mutuncin harkar shari'a ne, a wannan karon zamu yi nasara in sha Allah """ """Allah ya sa yaya Habib"" suka fito suka hau motar barrister Habib suka fita." "Nasir da yake bin Nabila a wata motar, ya ga fitar Barrister Habib da Nabila, ya sake rufa musu" "baya, sannu a hankali ba tare da sun san yana bin su ba, sai dai azabar kishi ya sanya ya ji har wani dishi-dishi yake gani." "A wannan karon Nabila tayi mamakin yadda aka basu damar ganin baba maigadi, ba tare da an" raina mata hankali kamar yadda aka saba ba. "Suka gaisa cikin mutuntawa, duk ya rame yayi wani iri." """Baba, ina mai sake baka haƙuri, amma ban karaya ba, in sha Allah zamu ɗaukaka ƙara ne""" "Jiki a sanyaye Baban ya ce ""Kina ta ɗawainiya, ni idan babu hali, kawai a bar maganar nan, na" "bar wa Allah""" "Barrister Habib ya ce ""No ba zai yiwu ba, ka manta yadda muka yi da kai wancan zuwan da nayi" "muka haɗu?""" Yayi shiru ya sunkuyar da kai. """Ka yi magana mana, mun yi magana da kai fa sosai baba, ka bata haɗin kai dan Allah, a wannan karon muna fatan ayi nasara, ka yi mata bayani, saboda ƙoƙarin kamanta gaskiya har nema aka yi a sabauta rayuwarta, ka yi magana baba, ka yi mata bayanin komai." "Nabila let's record it Incase""" "Ta jinjina kai ta ɗaukko wayarta, ta danna recording ta ajiye." "Cikin tsoro ya ce ""Dan Allah to kar ku gaya wa kowa, kun ga yarana duka mata ne, na aurar da wasu, ina da biyu ƴan mata, an ce muddin na yi magana abun da ya samu ramma zai same su, koma su rasa rayukansu gaba ɗaya tsoro nake ji"" mamaki ya cika Nabila, dan ita duk bai yi mata" wannan maganar ba. """Baba, ni na baka tabbacin nan, babu abun da zai samu iyalanka, ka ba ta cikakken haɗin kai, idan" "ka bari ta sake faɗuwa a shari'ar nan, kaga magauta sun yi galaba a kanta, kuma yayan da ka ke yi wa, ka ɓata musu suna""" "Ya jinjina kai ya ce ""Ana saura kwana biyu uwar ɗakin hajiya jidda, tayi waya ta ce aje garin su ramma, ta dawo su haɗu da ɗaya mai aikin, ayi mata gyaran gida, saboda tana ji da Ramma sosai, tana da biyayya, kuma bata yi mata sata." "Ranar an ɗaukko ramma, suna ta aiki, zulai ta tafi kasuwa, ɗan yayar matar gidan ya zo, sunansa Abdul, ban daɗe da fara aiki a gidan ba, dan babban mutum ne sosai mutumin, in da suka baro, jami'an tsaro ne suke yi masa gadi. Unguwar nan da suke ne, jami'an tsaro layuka suke gadi, ni kuma aka samo mini buɗe ƙofa da rufewa a gidan." "Bayan yayi mata, ya tafi zulai ta fito tana kururuwa, bayan ta dawo daga wurin sayen kayan miya. Bayan mun kai ta Asibiti, magana ta bazu, aka ce an sallame ni daga aiki, amma za a neme ni, daga baya yan sanda suka je gidana suka tafi da ni, wai zan ba da bayanin abun da na sani, muna zuwa aka rufe ni aka ce ni ake zargi, kuma aka yi mini barazana da muddin na ce bani bane ba" "yarana na cikin haɗari""" "Nabila ta ƙulu ta ce ""Amma meyasa baka yi mini wannan bayanin ba ni, na san ta ina zamu ɓ" "ullowa lamarin? Nayi ta wahalar neman shaida ka kuma ƙi bayani a kotu""" "Barrister Habib ya ce ""Kwantar da hankalinki, ki yi haƙuri kin san uba da 'ya'ya""" """Ki yi haƙuri na san nayi kuskure amma a tsorace nake ne nima""" "Ta kalleshi ta ce ""Ya sunan mai gidan?""" "Ya girgiza kai ya ce ""Ban sani ba""" """Ya za ayi ka yi aiki a gidan wanda ba ka san sunansa ba?"" Yayi shiru ya sunkuyar da kai." "Barrister Habib ya ce ""Tashi muje, ma ƙarasa sauran aikin"" haka suka fito Nabila tana mita," barrister Habib yana bata haƙuri. "Law firm ɗin suka koma, suka fara arranging ɗin yadda zasu yi appeal, sun gama ta fito suka haɗ u da barrister Kabir, yayi mata sannu, tare da yi mata kashedi, a kan ta raba kanta da aikata duk" "wani abu da zai sanya ta shiga matsala, ta bishi da to, ta fita ta shiga motarta ta nufi gida." "Nasir bai ga wani abu ba a bibiyar Nabila da ya yi yau ba, amma bai ji zuciyarsa ta gamsu ba, ya" sakawa ransa zai yi assigning wani wanda zai din ga bibiyar masa ita lokaci zuwa lokaci. *** "Su liti suna karyawa, Viper kuwa yana zaune yana yanke farcensa da nail cutter." "Wayar liti aka kira, ya karɓa ya ɗaga ya ce ""Ya ne?""" """Normal, kwana biyu ba ku shigo gada ba fa""" """Eh ka san yanayin ne, sai muna bayyana muna ɓacewa, meye labari?""" """Baban Viper ne ya zo rumfa, ya na neman ka, ko kai ko walid"" liti ya kalli walid ya kalli Viper." """Meyafaru yake nemanmu?""" "Ya ce ""Ban sani ba, ya dai tambaye mu, ko Viper yana zuwa wurin, muka sanar masa rabonmu da" "shi, tun kafin a kama shi, shekara shida kenan""" "Liti ya ce ""Normal ne, zan faso fatan rumfa komai lafiya?""" """Lafiya ƙalau tana ta garawa""" Ya jinjina kai ya ajjye wayar. "Liti ya cigaba da kallon Viper, Viper bai kalle shi ba ya ce ""Ko dai ka yi magana, ko kuma ka" "daina kallona""" """Allah ya baka haƙuri, na daina kallonka"" kamar ya gaya wa Viper, zuwan mahaifinsa rumfar" "shayinsu, sai kuma ya fasa ya haɗiye maganar." *** "Abdul ne yayi sallama a falon, ya shigo a gajiye, ta amsa sallamar tana tashi zaune daga kwancen" da take. "Ya ajiye jakarsa, ya kwanta a jikinta ya ce ""Wash""" "Ta ce ""Sannu""" """Yauwwa sweetheart"" ta kama hannunsa, ta cire masa agogon hannunsa." """Tashi a cire safar""" """Ki bari na huta na gaji""" "Ramma ta ce ""Ƙato da kai kana shagwaɓa, wataƙila ma ba wani aiki ka yi ba kake wani wash""" "Ya ce ""Kaii, baby kin san mutum nawa na yi wa tiyata kuwa? Ga kusan asibiti uku naje na ga" "marasa lafiya""" """To tashi ka yi wanka, ka ci abinci"" ya kalleta ya yi murmushi ya tashi zaune, ya shafa kanta ya ce" """Allah ya yi miki albarka babyna, i so much love you"" yayi maganar yana sumbatar goshinta." "Kallonsa take yi, tana son jin matsananciyar tsanarsa a zuciyarta, amma abu ya gagara, sai wani" ma kyau da ta ga yayi mata. "Ya tashi ya tafi bedroom, yayi wanka, Ramma ta goge hawayenta tana fatan Allah kar ya jarrabeta" da son Abdul. "Yayi salla ya fito, ta bashi abinci." """Beb, in sha Allah komai ya kusa zuwa ƙarshe, zan bayyanawa duniya ke, ina daf da gayawa babana maganarki, a san yadda za a gyara lamarin mu cigaba da rayuwarmu, am ready na ɗauki" "kowane risk mu zauna tare in sha Allah my rahama""" Tayi ajiyar zuciya tare da murmushi. """Dan Allah ko sau ɗaya ki ce kina so na mana""" """A'a ni ban iya ƙarya ba""" "Ya ce ""Zaki yi bayani ne""" *** """Hello masoyiyyata""" "Nabila ta ce ""Na'am sumy kalar kyau""" """Albishirinki?""" """Kuɗi dubu goma""" "Sumayya ta ce ""Mayyar kuɗi, ba za a bayar ba""" "Tayi dariya ta ce ""Fesa mini""" """Arfa ranar monday in Allah ya kaimu, zan fara aiki, ni da yaya murtala zamu buɗe gidan radion""" "Nabila ta miƙe ta ce ""Dan Allah masoyiyya""" """Wallahi da gaske, ke Allah ne ya kawo mana mafita, an bani damar ƙirƙirar programs, har na sami program ɗin da zamu din ga yi tare, mu ci karenmu babu babbaka, babu mai yi mana" "barazana da daka tsawa""." """Ke gani nan zuwa gidan naku ma, tare da ni za a buɗe gidan rediyon nan in sha Allah""" "Duk wannan abubuwan da Nabila take yi, ƙarfin hali ne kawai, zuciyarta na tare da Viper, tunaninsa kawai take yi, tama rasa wane irin tunani take yi a kansa, ga zuciyarta da take ta" azalzalarta da son ganinsa. "Tare da Nabila aka yi bikin buɗe sabon gidan radio, mutane suka din ga kiran wayar suna yi wa" "Sumayya fatan alkhairi, tare da tabattar mata da duk in da ta tafi suna tare da ita." "A program ɗin farko da suka fara yi da sumayya, suka sanya masa suna ƙeƙe da ƙeƙe." "Tun da sumayya ta gabatar da Nabila, kasancewar masu saurare sun santa a bakin sumayya, suke ta tura sa ƙ onnin gaisuwa, wasu kuma suna tambayarta dalilinta na ƙalubalantar bunkure" "foundation, duk da irin gudunmawar da take bawa al'umma." "Sumayya ta ce ""Masoyiyya, kin ji tambayoyin masu sauraro mai zaki ce?""" "Nabila ta yi murmushi ta ce ""Babu abun da zan ce, sai su kasance da mu a sabon shirinmu, na ƙeƙ e da ƙeƙe. Ba wai bunkure foundation ba, duk wani abu da ake kitimurmura a cikin sa, ko rashin adalci zamu yi bajekolinsa a wannan shiri, kuma program zai iya bi ta kan kowa, duk wanda ya ga kuma an yi masa ba dai-dai ba ya ƙalubalance ni a gaban shari'a." "Manyan shari'oi da aka yi bita da ƙulli a ciki, yadda ake danne hakkin mara galihu ake tsayawa yaran masu kuɗi, yadda ake wasa da hankalin talaka, da tauye masa hakki, shi fa wannan program ɗin, kai har da shari'ar wani gawurtaccen matashi da ya shahara, jami'an tsaro suna nemansa, sai dai abun mamaki shi ne sai da ya shafe shekaru biyar ba ayi masa shari'a, a shekara ta shida aka sake shi, kuma yanzu an ce ba bisa ƙa'ida aka sake shi ba wai nemansa ake yi." "Akwai tarin kwamacla a harkar shari'a a ƙasar nan, a shirin ƙeƙe da ƙeƙe zamu fayyace" "abubuwa da dama, na ban mamamki"" suka ƙarƙare program ɗin cikin wasa da barkwanci." *** "Alhaji wada hankali kwance yake zaune yana shan lemo a kofi, yana kallon indabo da yake ta haƙ ilo yana magana." """Karofi, ka shiga gonata da yawa, ka kiyayeni, muddin kana son yarinyar nan ta rayu, ya zama" "dole ka takawa shirin nan da zasu fara gabatarwa burki""" "Karofi ya ce ""Sabod me? Kai da kake ɗaukar nauyin gidan radion ka ake abun da ka ke so waye" "ya hana ka? Ni na ɗauki nauyin program ɗin dan haka babu ruwanka da abun da ake yi""" """Karofi, ka san na fi ƙarfin kafi ga bayana ko?""" """Ai ka san shi ƙarfen cikin wuta sai da ɗan uwansa ƙarfe, babban mutum mai kima a ƙasar nan, bai kyautu ace ka na ɓata lokacinka a kan wata ƙaramar alhaki kamar wannan yarinyar ba." "Auuu ashe fa ta sako wani zance a maganarta, mai kama da maganar Al'amin Viper, wato mai zamani. Kana tsoron ta tona maka asiri cewa kai ne ka saka aka kashe matar Viper ko? Ka kwantar da hankalinka ba ta san wannan labarin ba, idan har ba tana haɗuwa da Viper ba ya gaya mata da" "kansa""" "Wani irin shock indabo yayi, ya sandare a tsaye, jin yadda Alhaji mu'azzam wada kankarofi yake" farke sirrin da bai taɓa tunanin wani mahaluki ya sani ba. Ayshercool 08081012143 ₦500 ne via 0009450228 Aisha Adam jaiz bank sai shaidar biya ta 08081012143 Wanda za su jira document 1K ne. 90009343 'Yan Nijar ku turo katin airtel na 300fcfa Arewabooks ayshercool7724 "Indabo da ƙyar ya iya buɗe bakinsa ya ce ""Kankarofi""" """Indabo""" """Wace irin magana kake faɗa ne?""" """Irin wadda ka ji da kunnenka, ka zata daga kai sai waɗanda kuka aikata laifin ne ku ka sani? Kamar na so na fika iya playing cards ɗina ko?""" "Indabo zai yi magana, Jidda ta shigo wadda ita ce matar kankarofi, kuma ƙanwar indabo." """Yaya yana ganka a tsaye ne? Ba dai har tafiya zaka yi ba?""" "Kankarofi ya ce ""Eh, ya ce tafiya zai yi, dama ziyarar ta bazata ce, mu je na taka maka"" kamar" wawa haka indabo ya bi kankarofi suka fito. "Ya sake kallon indabo da yake ta rarraba ido, kamar shege a rabon gado ya ce ""Ka fa kwantar da" "hankalinka, kar ka yi zaton zan gaya wa wani wannan sirrin tsawon shekaru kenan, ina dakonsa ba wanda ya sani, ko ma na faɗa bani da wata ƙwaƙƙwarar hujja a kai, ina gargadinka ne kawai" "ka kiyayi yarinyar nan""." """Kankarofi""" """Indabo""" """Hawainiyarka ta kiyayi ramata, sanin wannan sirrin ba shi yake nufin kana da lago na ba""" "Kankarofi ya ce ""Na sani, na ankarar da kai ne kawai, na san abun da kake yi, dan haka kar ka" "tsallake gona da iri""." "Indabo kawai ya jinjina kai zai juya ya tafi, Kankarofi ya ce ""Na san zaka yi mamakin yadda aka" "yi na sani ko? Ba abun mamaki bane ba, kar ka je ka sakawa kanka damuwa da dogon tunani"" bai ce masa komai ba, ya yi gaba." *** "Abdul yana kwance yana bacci, saboda daren jiya bai yi bacci ba, ramma tayi bacci, aka kira shi asibiti, sai bayan sallar asuba ya dawo." "Ramma ce ta shiga ɗakin a gigice, tana dukansa a kafaɗarsa." "Ya buɗe idonsa ya ce ""Meye haka kuma?""" """Ka tashi""" """In tashi in yi miki me? Rahama ban yi bacci ba fa jiya, ina asibiti""." "A gigice ta ce ""Ina ruwana? Abdul ban ga al'ada wancan watan ba, wannan ma lokaci ya wuce""" """Kuma shi ne zaki tashe ni ina bacci?""" """Dole na tashe ka, me hakan yake nufi ka tashi ka duba ni, ba zan sake ɗaukar ciki ba, ni ka tashi" "ka duba ni""" "Tashi yayi daga kan gadon, bai ce mata komai ba, ta bi bayansa tana kiran sunansa, amma ya" "rigata fita ya kulleta a ɗakin, ya tafi wani ɗakin ya yi kwanciyarsa." *** "Sosai sumayya take jan jama'a a sabon gidan radion da kama aiki, da ita da murtala." "Saboda bayan kasancewar ta sananniya, tayi ƙoƙari wurin samar da sabbin shirye shirye masu ƙ ayatarwa, wanda za su tafi dai-dai da matasa da ma dattijai baki ɗaya. Wasu daga cikin abokan aikinta da ta baro a can, suka din ga yi mata magiyar suma ta samar musu gurbi a in da ta koma, suma su koma. Yanzu sumayya ba ta da fargabar ta samo rahoto, a kushe ace mata ba irinsa ake bu ƙata ba, saboda kawai bai yi dai-dai da abun da wasu suke son ji ba." "Ranar farko da suka gabatar da program ɗin ƙeƙe da ƙeƙe ita da Nabila, program ɗin ya yamutsa hazo, dan tayi sukuwa tayi zamiya, ta ƙarewa bunkure foundation ta tas da hukumar shari'a, tayi bayanin yadda shari'ar baba mai gadi ta kasance a kotu, tare da jaddada idan har da gaske dan al'umma suke ayyukansu, ya zama dole a bayyana ina ramma take, idan kuma da gaske tana asibiti, a bawa lauyoyi da ƴan jarida damar zuwa su ganota, kuma a kawo bayanin likita a kan abun da yake damunta zuwa lokacin da aka gaza ganinta a gaban kotu." "Hatta lauyan gwamanti ta din ga challenging ɗin sa, a yadda suka din ga taka doka yadda suke so." "Nan fa mutane suka din ga tururuwar kiran waya, wasu suna sharhi, ciki har da wani lauya mai zaman kansa, da ya kira waya, ya tofa albarkacin bakinsa tare da tabattar da akwai jabun lauyoyi da suke yi wa doka hawan ƙawara, a yi cuwa-cuwa a danne hakkin mai ƙaramin ƙarfi, a wanke yaran masu ido da kwalli, ire-iren foundations ɗin bunkure suna da yawa. Ya ƙara faɗaɗa" "bayanan da Nabila tayi, tare da fito da wasu abubuwa ma da ita hankalinta be kai, kai ba." "Nabila ta ji daɗin program ɗin sosai da sosai, dan kuwa ji tayi, zuciyarta ta rage raɗaɗi da baƙin" cikin abun da aka yi musu a kotu. "Bayan kammala program ɗin, still cigaba da kiran wayar a aka yi, ƙarshe sai kashewa suka yi." "Sumayya ta ce ""Mutuniyata kin yi bala'i fa""" "Nabila ta ce ""Ke ni ɗin ta wasa ce? Ai sai Najar bunkure ta zubar da hawaye, yanzu ta ƙarƙashin" "ƙasa zan yi analysis nawa ƙungiyar take samu na tallafi a wata, da kuma abun da ake spending wurin tallafwa mutanen da ake iƙirari. Ni ɗin fa ba ta wasa ce ba""" "Sumayya ta ce ""Ba wani ta wasa ko ba ta wasa ba, dole mu daga da Addu'a fa, Allah ya tsaremu" "Masoyiyya""" """Amin dai, amma yanzu meye abun yi?""" "Sumayya ta ce ""Eh to, kamar yadda ki ke tunanin kawo ƙarshen bunkure, ni kuma sonake na ci uban indabo, duk da ya fi ƙarfina, amma zai ga abun da 'yar matsiyata zata iya yi, dan wallahi sai" "na kusa girgizo shi daga kan kujerar nan""" "Nabila ta kwashe da dariya ta ce ""Me yayi miki ne, ki ke wannan alwashin?""" """Zagin cin zarafi yayi mini, lokacin da ya ce na din ga bibiyar masa ke, kin san na taɓa zuwa na bayar da wani rahoto, a kan cewa an ce an yi wani aiki a yankinsa, kuma da na je ban tarar an yi ba, kin ga abubuwan da aka yi mini a kan hakan? Program ɗin da zamu din ga yi da yaya murtala, irin su Indabo zamu din ga bankaɗawa asiri. Zamu faɗi abun da suke karɓa na consituency project duk wata, da kuma ayyukan da suka gabatar a watan, daga nan ya ragewa al'ummar yankin da ake" "wakilta, su yanke hukuncin da ya dace""" """Allah ya ƙara lafiya, ƴar gwagwarmaya amma shirin ya ƙayar da ni, Allah ya taimakemu ya ƙ" "arfafi gwiwarmu masoyiyya. Abun mamaki shekarun baya bamu taɓa tunanin samun wannan damarmakin ba, sai dai mu yi ta dama dama""" """Haka lamarin Allah yake, yanzu ya ara mana damar da muka roƙa, ya rage namu mu yi abun da" "ya dace da ita""" """Haka ne, Allah ya taimake mu ya bamu sa'a"" suka ce Amin." "Ko da ta koma gida, Walida ce ta fara tararta ta ce ""Arfa, yanzu muka gama jin program ɗin ku," "live ku ka yi shi, kina ta ɓarin maganganu ko tsoro ba kya ji""" "Nabila ta ce ""Walida, wanda bashi da gaskiya ai shi ne yake tsoron a faɗeta, bamu fara dan mu" "daina ba""" """Zaki ga baki fara dan ki daina ba, yaya ya shigo a ƙalla sau uku yana nemanki, ya kira wayarki" "ma, kin ƙi ki ɗaga""" """Duk a kan program ɗin da na yi""" "Walida zata bata amsa ya shigo, fuskarsa babu annur ko kaɗan." "Ta tsaya tana kallonsa, ya ƙaraso gabanta ya kalleta ya ce ""Arfa ba zaki taɓa yin hankali ba ko?" "Meyasa ki ke son yin wasa da rayuwar ki ne?""" """Dsp, rayuwa ta ka ce ai, nikaɗai nake abuna ai, shiyasa nake takatsantsan kar baya tawa rayuwar," "na saka ta wani a hatsari""" """Zaki rufe mini baki, ko sai na kwaɗa miki mari, ni kike gaya wa ba kya saka rayuwar wani a hatsari? Duk tayar mana da hankalin da ki ke yi ba kya gani, yadda ki ke tayarwa da Abba hankali a shekarunsa ba wasa da rayuwarsa ba ce ba? To wallahi ba zaki kashe mana uba ba, muna da" "burin ganinsa a raye""." "Aikuwa ta gyara tsayuwarta, ta haɗiye wani abu mai ɗacin gaske, ƙirjinta na yi mata zafi ta ce ""Good, an zo wurin, kar na kashe muku uba, tun da ni ba nawa uban bane ko? To ku mayar da ni wurin nawa uban mana, meye na zama ana yi mini gori, how many years for now? kuna yi mini gori, kai ɗin ma da baka yi yau gashi ka fara, alhalin kun fi kowa sanin bani na zaɓi hakan ba, da" "da yadda zan yi, da tuni na bar muku gidanku, ku nuna mini hanyar gidan nawa uban mana""" "Ta baya ya fizgota, ya ɗauketa da lafiyayyen mari." "Gigicewa tayi, jikinta ya hau rawa ta kalli Abba, da ransa yake a ɓace, fuskarsa babu annuri." "Ya riƙe hannunta, ya zazzaro mata ido ya ce ""Me ki ka nema kika rasa? Me kike buƙata a rayuwar" "nan da ban yi miki ba da ki ke zancen mahaifinki, menene shi Nabila?""" "Ta sunkuyar da kai tana kuka, ta dafe kuncinta." """Ki gaya mini, kafin na kasheki, me uban naki ya tsinanawa babarki ma, balle ke? Uban me ki ke" "nema a wurinsa?""" """Abba ka yi haƙuri, ba zan sake ba""" """Ba zan yi haƙurin ba, ki gaya mini ta ina na gaza, menene ba na yi miki""" "Mama da jin hargowar su ya sanya ta fito ta tarar da su, ta ce ""Mhmm, ai tsintacciyar mage ba ta ta" "ɓa yin mage major, kuma gurbin ido ba ido bane ba, muna nan da kai wataran sai ta saka ka zubar da hawaye""" "Nasir ya ƙarasa ya ce ""Abba dan Allah ka yi haƙuri, ba zata sake ba in sha Allah, kar ka kuma" "dukanta""" """Shut up! Kai ma har da kai, ina yi maka kallon mai hankali ashe ba haka ba ne, ku kuke tunzurata" "take wannan zancen""." "Ya ce ""Ka yi haƙuri dai Abba, in sha Allah ba za a sake ba""" Ya saki hannunta ya fice daga gidan baki ɗaya. Nabila kuwa da gudu ta ƙarasa ɗakinta tana kuka mai cin rai. *** "Ƙarfe sha ɗayan dare, liti yana ƙofar gidan su Al'amin, yana rarraba ido, babu yaron da zai aika cikin gidan, kowa ya watse." "Ya bubbuga gate ɗin gidan, ya koma gefe." """Waye?""" """Nine""" "Ya buɗe gate ɗin ya kalli liti ya ce ""Ya aka yi?""" """Wurin Abbu nazo shi nake nema""" "Jin muryar liti, ya sanya Abba gane jama'ar Viper ne, dan haka ya ce ""Mai zamanin yana tsare ai," "ka sani kake nemansa""" """Dan uwarka wurin mai zamani na ce maka na zo? Wurin mai gidan na zo, baka gane ni bane liti" "ne"" yayi maganar yana cire facemask ɗin fuskarsa." """Na gane ka, amma a kan me zaka zo nemansa, ka gaya mini na je na gaya masa""" "Wata uwar shaƙa liti yayi masa, ya watso shi waje ya ce ""Shege, kai ka isa in zo wurin maigida ka ce na gaya maka menene sa'anka ne ni, wallahi idan baka kiyayeni da abun da ya shafi mai zamani ba, sai na sassaraka na bar wa uwarka tabon daba, makira yar wuta"" tamkar gidan ubansa, liti ya" kutsa kai ya shiga gidan. Ya tsaya a tsakar gidan yana kwaɗa sallama. "Rahila ce ta fito ta ce ""Wane mara mutuncin ne haka a tsakar gidanmu, malam balaggagen gardi" "ka shigo mana gida""." """Ɗanki ne ya so na shigo, eh sarkin gida nake nema, an ce ya je gada biɗata, mu kuma tsakainmu da maƙyanƙyasanmu akwai amana, mussaman maƙyanƙyashin mai zamani, ai dattijonmu ne iya" "wuya, ace masa gani na amsa kira""." """Wace irin magana ce kake yi wannan, ni ban gane ba""" """Gana ce, kuma kin gane mai nake nufi, ki yi mini magana da mai gidan, ko na shiga na neme shi" "da kaina""" "Abba ya shigo gidan yana zare ido, ya sake cewa liti ""Ka zo ka fitar mana daga gida""" """Gidan ubanka ne ko na mai zamani? Idan gidan ubanka ne sai na fita, idan kuma gidan uban mai" "zamani ne nima gidanmu ne""" "Rahila ta ce ""Wane mai zamanin, ka tafi can ka neme shi, ka fice ka bar mana gida""" """Ke yar wuta ban saka da ke ba, baƙar sheɗaniya, idan baki nemi yafiyar mai zamani ba, wuta ɗ" "aya zaki shiga da matar sheiɗan, kai ware ka yi mini magana da mai gidan"" yayi maganar yana zaro makami." "Abbu kuwa bacci yake yi sosai, a cikin baccin ya jiyo muryar liti, kawai zuciyarsa ta raya masa" "Al'amin ne, ya zo da mutanensa." "Da sauri ya fito tsakar gida, yana tambayar ko lafiya." "Liti na ganin sa ya mayar da makamin, ya durƙusa ƙasa ya ce ""Abbu barka da dare""" """Yauwwa barka, lafiya ka shigo mana gida a wannan daren?""" """Liti ne Abbu, an ce ka je namanmu, ko ni ko walid, shiyasa ban yi sanya ba, na ce bari na" "gangaro na amsa kira, duk da mu masu laifi ne, ya kyautu ace muna zuwa muna kawo gaisuwa""" "Abbu ya ce ""Ikon Allah, meye sunanka na gaskiya ne?""" "Liti yayi murmushi ya ce ""Bawan Allah nake ai sarkin gida, Abdallah ne""" """To ni Abdallahn zan ce, bisimillah shigo mu shiga daga ciki""" "Rahila ta ce ""Ya shiga ina? Makami ne fa a jikinsa, sai yayi maka illa, ya zaka shiga da shi" "makwancinka?""" "Abbu bai kulata ba ya ce ""Ƙaraso Abdallah""" "Ya bi bayan Abbu, yana baza babbar rigar daya saka a kan ƙanan kayansa ya kalleta ya ce" """Munafuka, haddsana mai raba ɗa da uba, idan baki yi wasa ba, tun a duniya sai kin tozarta""" "Duk tsagerancin Al'amin baya saurarta balle ya zageta, amma liti sai ƙare mata zagi yake yi." "Abbu ya kalli liti ya ce ""Abdallah, dan Allah ko ka san in da Al'amin yake? Tun da ya zo mini" "daga prison na kore shi, ban sake ganinsa ba, ina matuƙar kewarsa da son na ganshi, na san ku ne makusantan sa, ban sani ba ko kun san in da yake?""" "Liti ya ce ""Eh to, gaskiya ban san in da yake ba, amma dai muna haɗuwa""" "Abbu ya ce ""Ban gane ba""" "Liti ya ce ""A bar shi hakan da na faɗa, ban san in da yake ba, amma muna haɗuwa, kuma maganar gaskiya, yana fushi da kai, tun da aka ce yayi laifin nan baka bashi dama ko sau ɗaya ba, ka" "saurare shi""" """Wace damar zan bashi, na nema masa auren yarinya girma da arziki, amma ƙarshe yayi silar" "rayuwarta""" "Liti ya kalle shi ya ce ""Haryanzu ka yadda shi ne ya kashe yar madara?""" """Meyasa ba zan yadda ba, tun da ya furta mini, kuna gashi yana shaye-shaye""" "Liti ya jinjina kai ya ce ""Haka ne"" ya tashi tsaye ya ce ""Baka shirya ganin sa ba, maybe zuwa gaba kaɗan, amma wallahi mai zamani, Allah ne yayi da sauran kwanansa a gaba, dan ya kusa kashe kansa, ko mun lalace fa ku iyayenmu ne, bamu da sama da ku, duk son da mai zamani yake yi maka, ka fita daga zuciyar sa, ya daina maganarka ranar da na yi masa zancenka ce mini yayi shi yanzu ba shi da uba, kaga wannan ba dai-dai bane ba, alhalin ga wani ɗan kut Da yafi mai kora" "shafawa da shi da yan uwansa, suna zaune a gidan, mu kuma kun sallamawa duniya mu. Bari na ɓ" "ace, Allah ya ƙara maka lafiya da nisan kwana, ka cigaba da yi mana addu'a a duk in da muke," "mai zamani zai samu yanci ya cigaba da gudanar da rayuwarsa kamar kowa, ba tare da yana ɓuya ba""" "Abbu ya miƙe suka fito tsakar gida ya ce ""Kayi mini wani taimako Abdallah, ka tayani kwantar" "masa da hankali kafin ranar da Allah zai saka na ganshi dan Allah""" """To in sha Allah""" "Ya ɗaukko kuɗi ya bawa liti, liti ya ce ""Meyasa zaka bani kuɗi, ni ba zan karɓa ba, ayi mana" "addu'a kawai, in sha Allah mai zamani ya kusa samun ƴanci"" yana gama maganar ya fice." *** "Liti ne yake ta kallon Viper, ya numfasa ya ce ""Mai zamani""" """Farin jakada"" liti yayi dariya, ya ce ""Rabon da ka gaya mini sunan nan har na manta, kwanan nan" "kamar kana jin raha, menene sirrin ne?""" "Ya ce ""Abubuwa da yawa, ƙwaƙwalwa ta ta samu nutsuwa a 'yan kwanakin nan, sannan na fara" "jin daɗin yadda nake wasa da hankalin maƙiyana, ka san sanyawa mutum tsoro yafi kowane horo wahala""" "Walid ya ce ""Ai mun gode Allah, da bayan tafiyar jauhar, Allah ya kawo mana Nabila rayuwar ka," "haƙiƙa bayan ƴar madara ita ta ceto mana ƙwaƙwalwarka da tunaninka""" """Ba wani nan, da an yi magana ka fara sako maganar wannan makirar ba wani, ba uwar da ta" "tsinana masa""" """Wai anya liti idan aka bi salsala ba daga zuriyar fir'auna kake ba, kai wai baka yafiya ne""" """Ba zan yafe ba, kace ma nine fir'aunan kawai mana walid""" """A'a ni ban ce maka fir'auna ba, amma dai baka da zuciyar kirki""" """Ni rabu da ni, zan yi magana ka hana ni, zaka saka na manta""" "Ya kalli Viper ya ce ""Mai zamani, Abbu yaje rumfar sayar da shayi yana nemana ko ni ko walid"" a" take ɗan annurin fuskar Viper ya ɗauke. "Liti ya ɗora da cewa ""Na ɗan yi yawo na nemi bayanai, kar na je ko wani set up ne, amma na fuskanci lafiya ƙalau ne, dan sai na ci uwar agolan nan na gidanku, da ya kawo mini wargi, mun haɗu da Abbu, ya ce mini yana son ya ganka, amma na ce ban san in da kake ba, akwai tarin" "nadama a tare da shi, dan Allah mai zamani ka sassauta, naka mahaifin ne kawai ya rage mana, mu" "yi haƙuri mu yafe masa, na tabattar masa da ka kusa yin 'yanci da yardar Allah""" """Bani da uba, nawa uban ma mun rasa shi, dama can ba ya ta tamu, dukkanmu marayu ne, da muke zaune a matsayin ƴan uwan juna, ko na yi ƴanci, ba zan sake zuwa in da yake ba, na bar" "shi da waɗanda yake so""" """A'a Viper, su fa iyaye komai za su yi, ba a fushi da su"" harshensa ya zaro waje, ya ɗago sweazland ɗin da take gefensa, ba shiri liti ya tsuke bakinsa, yayi shiru ba dan ya rasa abun faɗa" "ba, sai dan sanin cewa yana sake magana sai ya saka masa ƙarfe." Message ne ya shigo wayar Viper. """An yi maka gargaɗi a kan yarinyar nan tun da farko, amma ka ƙi ji, yanzu ta zama rauninka, sai" "ka yi aiki tuƙuru, dan kare rayuwarta!." *** "Nabila ba ta san ya aka yi aka samu lambar wayarta ba, mutane suka din ga kiranta a waya, wasu na zaginta a kan program ɗin da ta gabatar, ta taɓa bunkure foundation, wasu na jinjina mata, tare da nuna mata goyon bayansu, da ta gaji kashe wayar ta yi gaba ɗaya." "Gaba ɗaya kewa da tunanin Viper, suka haɗu suka uzzurawa rayuwarta, tana ta ƙoƙarin basarwa" amma abu yaya gagara kamar yadda dariya ta gagari kare. "Ta tsaya a gaban mudubi tan ƙarewa kanta kallo, bayan ta fito daga wanka, ta shiga ƙarewa kanta" "kallo, kyakykyawar farar fatarta sai sheƙi take yi." "Idanunta jawur, saboda kuka, gaba ɗaya haushin Nasir take ji, gaba ɗaya komai yayi mata zafi," ba ta jin daɗin komai. "Message ne ya shigo ƙaramar wayarta, ""Mu haɗu a garden"" ta zubawa notification ɗin ido, tayi" "wata irin ajiyar zuciya, kamar sanyi ta ji a ranta, da ganin saƙon nasa." "'Wai me nake yi haka ne? Ta tabatta son shi nake yi kenan? Wace irin ƙaddara ce haka?""" "Ta lumshe idanunta, hawaye ya ziraro daga idaunta, abubuwa da yawa suna damunta, kuma babu" "wanda take burin ta gayawa sama da Al'amin, mutumin da bai damu da ita ba ko kaɗan." "Jiki a sanyaye ta shirya, ta saka kayanta, ta kawo facemask ta saka, ta fice." "Ko da ta je garden ɗin, ba ta tarar da shi ba, ta kira wayarsa amma ba ta shiga, haushi ya kamata," "ranta ya ɓaci, dan da niyyar ta ganshi ta zo, haka kurum tayi ta ɗokin ta zo su haɗu." "Ta nemi wuri ta zauna cikin takaici, haushin kanta take ji, yadda ta faɗa soyayya cike da wawanci." "Ta ɗan jima a wurin a zaune, sannan ta tashi, ta ɗauki mota zata koma gida, ya kirata a waya." "Bai jira tayi magana ba, ya fara ""Yayanki yana bin bayanki, nan da kilometer biyu, akwai wani" "gidan cin abinci, ki tsaya ki shiga"" ya gama maganar ya katse." "Babu tunanin komai ko musu, ta cigaba da tafiya, sai dai ta din ga kallon mirror, amma bata ga" alamar wani ita yake bi ba. "Ta tsaya a restaurant ɗin, ta shiga ta sake kiran wayarsa, bai ɗaga ba ya tura mata saƙo ""In the" "next 10 minutes, ki koma motarki, ki samu wuri ki zauna ki jira""" """Wai dan Allah meyasa. Katse wayar yayi, ba tare da ta gama maganar ba." "Ta nemi wuri ta zauna ranta a ɓace, mintuna goma na cika ta ga saƙonsa." "Ta tashi ta fita, ta ƙarewa harabar wurin kallo, amma ba ta ganshi ba, ta buɗe motar sai da ta zauna, kawai ta ganshi a cikin motar, da ihu zata kurma, amma tayi shiru, tana rarraba ido, ta rufe" "motar ta kalleshi ta ce ""Ta ina ka shigo?""" """Ta ƙofa"" ya bata amsa." """Amma to meyasa kayi ta wahalar da ni?""" """Fita ki zagayo, zan ja motar"" ta jinjina masa kai, ta fita ta zagaya, shi kuma ya koma mazaunin" "direba, ya bawa motar wuta, ya ja ta da uban gudu ya bar wurin." """Ka tuƙa a hankali, tsoro nake ji"" bai ce mata uffan ba, ya cigaba da fafara gudu, sai da ya cimma" "wani a kan babur, ya sanya hular kwano." """Kin san wannan?"" Ta girgiza kai alamar a'a." """Kin tabatta?""" """Eh, ɗazu dai ka na ƙaraso nan, na wuce shi a kan titi""" "Ya jinjina kai ya ce ""Ke yake bi, kin wuce ni a mota, na ga yana binki, ina kyautata zaton ko dai" "yayanki, ko wani ne ya sa ya din ga binki""" "Ta sauke numfashi ta jingina da jikin dai-dai lokacin da ya saka hannu a jikin seat ɗin, yana ƙoƙ" arin shiga wata kwana. "Tudun gashinta ta ɗor a kan hannunsa, ta lumshe ido, fuskarta ɗauke da matsananciyar damuwa, jikinsa ne yayi wani irin sanyi, yayi saurin cire hannunsa, ya ƙarasa in da yake son su je." "Shi ma lambu ne wurin, amma babu kowa, sai sanyin bishiyun wurin, ta fuskanci yana son yanayi" irin haka. """Yaya ake ciki da case ɗin rahama, a ina ki ka tsaya?""" "Kawai ta zuba masa ido, ya yi mata wani irin kyau, ma'abocin ƙanan kaya ne, shirt ce ajikinsa baƙ a da zanen damusa a jiki, sai dogon wandon jeans, mamaki ma take yi, a in da yake samun kuɗin" sayen kaya masu kyau. "Sai ƙamashin turaren florie yake yi, ya yi gyaran fuska, ya kuma yi saisaye, idanunsa sun rage" "wannan jan, alamu sun nuna ya ɗan tsagaita da shan miyagun ƙwayoyi." """Malama ina magana kin yi shiru kina kallona""" """Yanzu rashin muhimmancina har ya kai na shiga wannan tashin hankalin, ka sani amma ka kasa nema na ko a waya, ka ce mini sannu, i almost lose my life fa, a yaya ka ɗauke ni ne? Bani da muhimmanci har haka a wurinka, haba dear, ni ka san ba zan taɓa yi maka haka ba, ina son rayuwarka, ina son ganin walwalarka da farincikin ka, ina son na maye maka gurbin jauhar, da wasa na ɗauki abun, amma ya zame mini gaske. Ka daina nuna mini halin ko in kula, bana jin daɗ i ko kaɗan. Damuwa ce da ni a raina sosai, ina son wanda zan gaya wa ya saurare ni, wanda zai" "fahimci haƙiƙanin abun da nake ji""" """Ki shiga hankalinki, bana son wannan wasan da ki ke yi mini, da zarar aikina da ke ya kammala," "kowa zai kama gabansa, ki daina yi mini irin wannan wasan, na gaji da yi miki kawaici, ba na so""" "Cikin ƙarfin halin da rauninta ya hana ta aikata hakan, hawaye ya fara biyo kuncinta ta ce ""Ba wasa nake yi maka ba, ƙaddara ce da na roƙawa kaina da bakina, ba wasa nake yi maka ba, da fari wasa nake yi, amma yanzu ya zame mini gaske, ban taɓa tunanin zan iya cewa wani namiji ina son" "shi ba, amma kai naga kamar nutsuwar ka ta kai na gaya maka""" "Ya ce ""A'a karki yaudari kanki, wace nutsuwa nake da ita?""" """Rauninka mutane kawai ke iya gani, ni kuma nagartarka nake gani, kamar kai ne zaka zama" "dai-dai da ƙaddarata""" "Wani abu ya ji yana nema ya rinjayi zuciyarsa, mussman da ya fara ganin fuskar jauhar a cikin ta" Nabila tana kuka. "Cikin ƙarfin hali, yayi ta'awizi ya kaurara muryarsa cikin tsare gida ya ce ""Jauhar ɗaya ce, kuma na sameta ta suɓuce mini, babu wata mace da zata iya maye mini gurbinta, sanya wata macen a zuciyata tamkar cin amanar 'yar madara ne, a kanta na gama soyyaya, kuma na gama aure, dan haka kar ki ƙara yi mini wannan maganar, ki nemi wani ki aura, wanda iyayenki za su yi alfahari" "da ke da shi, jauhar ma ƙaddara ce ta saka aka bani ita""" "Ta share hawayenta ta ce ""Nabila mace ce mai aji, aji ma na gaske, ban taɓa mafarkin fara furtawa" "wani namiji ina son shi ba, raunin macen kenan, daga tausayi na faɗa sonka ban shirya ba, kai banda ƙaddara da haɗin Allah, me zai kai mace kamata yin kasada da rayuwata kamar wata wawuya ina nemanka ina zaman zamana?." "Sannan ka sani idan akwai macen da nagartarta zai hana a auri wata mace bayan wafatinta, to Sayyada Khadijah ce Allah ya ƙara mata yadda, kuma idan akwai macen da soyyayar da ake yi mata, zai hana ayi mata abokiyar zama, to sayyada Aisha ce radiyallahu anha." "Baka san wace damuwar ce a raina ba, ka zaɓi ka yi mini haka, ko baka so na, ba haka yakamata" "ka yi mini ba, bani mukullin motata na tafi"" tayi maganar tana kuka tare da miƙa masa hannu." "Kallonta kawai yake yi, babu in da ta bar 'yar madara a kamanni, hatta kukan nan da take yi," "jauhar kawai yake gani, sai dai Nabila ta fi jauhar murya, da kilewa kuma ita mafaɗaciya ce." "Loosing control ɗin sa ya kusa yi, da zuciyar sa take raya masa, ya rungumeta ya rarrasheta," "sannan ya ji menene damuwarta, fizge mukullin motar tayi, ta ƙara gaba tana kuka." Ayshercool 08081012143 ₦500 ne via 0009450228 Aisha Adam jaiz bank sai shaidar biya ta 08081012143 Wanda za su jira document 1K ne. 90009343 'Yan Nijar ku turo katin airtel na 300fcfa Arewabooks ayshercool7724 "Cikin zafin nama ta juya tana kuka, ta nufi hanyar barin wurin, har ya ɗaga ƙafa da niyyar ya bi ta, sai kuma ya fasa, dan idan ya bita bai san me zai ce mata ba, yana kallonta ta hau motarta ta bar" wurin. "Bashi da zaɓin da ya wuce shi ma ya bar wurin, sai dai ya tafi zuciyarsa cike da wasi-wasi, ko cikin duhu aka tara mata dubu, zai cire 'yar madararsa, amma haryanzu ya kasa gane dalilin da ya sanya Nabila take kama da jauhar, ba kuma wai kama sama-sama baz kamannin ne tamkar an raba" kara biyu. Ya cigaba da takawa a hankali ya bar wurin. *** """Indabo ina fatan ka saurari program ɗin da wannan sheɗanun yaran suka gabatar, ka shirya ɗ" "aukar mataki ne, ko kuma ni na ɗauka da kaina? Na gaya maka ba zan bari wahalata ta shekaru ta" "tafi a banza ba, in ƙare a lalace, ƙaramar yarinya ta rusa ni ba, ko dai ka saka a dakatar da" "program ɗin nan, ayi abun da ya dace a kanta, ko kuma ni zan ɗauki matakin abun da ya dace""" "Indabo ya kalleta ya ce ""Naja, wai yaushe ki ka zama haka ne? Duk wata matsala tare muke" "magance ta, amma wannan sai nema ki ke yi ki zame, ba fa wata babbar matsala bace ba""" """A wurinka ne ba babbar matsala ba, kuma ƙaramar matsala ita ce take zama babba. Kana jin manyan lauyoyin nan da basu samu dama a kaina ba da, yanzu sun samu suna ta bata goyon baya, mutane sun fara farga da abun da take yi, ni na rasa wai waye uban ɗakinta ne waye ya tsaya" "mata?""" "Ya numfasa ya ce ""Kankarofi ne""" """What? Kankarofi kuma? Meya kawo shi cikin wannan maganar?""" """So yake lallai sai ya ga bayana, ya rama abun da ya faru a baya, maimakon ya rama a siyasance," "ba ta haka yake son yi ba, so yake lallai sai na tozarta""" "Naja ta ce ""Ikon Allah, to menene ribarsa, alhalin kuna sirikai?""" """Aurenma da ya auri jidda, duk cikin plan ne na siyasa, kin san ita siyasa babu maƙiyi na dindindin, kuma babu masoyi na dindindin, mun zauna jam'iyya ɗaya da shi a baya kamar yadda na taɓa gaya miki. A lokacin nan mutane suna matuƙar sonsa, duk da ba wani babba bane ba, kuma naga take-taken ana kiransa ya fito takarar kujerar da nake hari. Na shiga na fita da wasu mutane, sai da suka fita suka bar mana jam'iyyar, duk da a lokacin ba wani mayar da hankali yake a kan siyasar sosai ba, gidansu yan kasuwa ne, shi ne yake taɓa siyasa." "Bayan sun bar jam'iyyar, aka bani takara, shi ma jam'iyyar da ya koma, suka bashi takara, nayi ta bita da ƙullin siyasa, da yi masa yarfe kala-kala." "Ni da yan jam'iyyar mu, kasancewar muke da mulki a sama, muka shiga muka fita, aka murɗe zaɓ en, ya ce shi ba zai kai ƙara ba, jam'iyyarsa suka kai ƙara, amma duk aka kori ƙarar, duk da haka mutane suka so yi mini bore, shi suke so. Na haɗa kai da shugabannin jam'iyyarmu, muka kunno masa wuta ta sama, EFCC suka zo har gida suka kama shi, aka yi seazing ɗin wasu kadarorinsa, da zimmar ya mallake su ba bisa ƙa'ida ba." "Kasancewar ba shi da manyan iyayen gida, bai iya shige-shige da neman wurin zama da biyayya a wurin manya na wannan lokacin ba, ya sanya sai da aka tsare shi a prison, ana binciken sa, bayan an sake shi duk da haka aka ƙwace masa kadarori." "A lokacin mahaifinsa ya ce, baya son sa da harkar siyasa, ko zai yi ya bari sai bayan ransa, sai ya cigaba da kasuwancinsa, kuma bai taɓa ce mini uffan ba, sai bayan rasuwar mahaifinsa ya dawo yake taɓa harkar siyasa, har aka yi masa muƙamin nan, ashe ya ƙwafe wannan abun a ransa, so" "yake sai ya ɗauki fansa ta ƙarfin tsiya yanzu""" "Naja ta ce ""Taɓ, gaskiya kana ruwa indabo""" """Ban gane ina ruwa ba?""" """Au muna ruwa zan ce? Wannan rigimar ai ban san lokacin da aka yi ta ba, balle ace da ni aka ƙ" "ulla a nemi mafita, a kanka yake neman fansarsa, dan haka ni kar a saka ni a ciki ba zai yiwu ba, haka kurum ana nema ayi mini tsirara a idon duniya""" """Naja""" """Na'am""" """Haka ki ka ce? Kin san bana tafiya da butulu?""" """Babu in da nayi maka butulci, na bauta maka da ƙarfina da gangar jikina, abun da nake yi ba" "butulci bane, iya ruwa ne fidda kai""" "Ya jinjina kai ya ce, ""Haka ne, na fahimta""" *** "Abdul ne a zaune, ya zubawa ramma ido, tamkar mahaukaciya, gaba ɗaya ta burkice masa, idanunta sun yi jawur saboda kuka, yana kallonta rabonta da abinci tun jiya, muryarta duk ta dashe" "saboda kuka, ya ma rasa ya zai yi mata, yayi tsawar ya zare idon, amma duk a banza." Ya kaɗa ya raya taƙi cin abinci. """Rahama"" ta ɗago ta kalleshi kamar wata dodanniya." """Me ki ke so?""" """Ka duba ni, wallahi ba zan zauna da cikin shege ba, idan shi ne ka cire mini, ka mayar da ni" "gaban uwata, na gaji da yi maka biyayya baka da niyyar cika alƙawarin da kayi mini, ban sani ba ko sai ka cika alƙawarin ka na kasheni sannan hankalinka zai kwanta""." """Yanzu da kanki ki ke cewa a zubar da ciki? Alhalin lokacin da tsautsayin nan ya faru, mun nemi a" "zubar a rufe maganar amma ku ka ƙi""" "Kamar ta ɗura masa ashar ta ce ""Wancan idan tsautsayi ne wannan fa? Wallahi Abdul zan kashe" "kaina in huta, na gaji""" "Ya ce ""Is ok, shikenan yanzu ko cikin ne babu lallai na gani, ki bari zan tafi da ke asibiti na yi miki" "gwaje-gwaje sosai, amma sai kin yadda kin yi wanka kin ci abinci""" "Cikin rashin wayo ta jinjina kai, ya lallaɓata da kyar, ta yi wanka, ya dafa tea da indomie ya bata," "sai dai tana gama ci, ta hau amai." "Ya ce ""Kin gani, ulcer ta kama ki, daga jiya zuwa yau da baki ci abinci ba, shiyasa kina cin abincin" "ki ka yi amai""" "Cikin kuka ramma ta ce ""Wallahi ciki ne da ni, ni bani da wata ulcer """ """In ji wa? Ulcer ai tana saka amai, baki ga nima yadda take yi mini ba ne? Ai rashin cin abincin ne" "ya janyo haka, kuma idan ki ka cigaba da ƙin cin abincin tumbinki ne zai ta rarakewa, komai ki ka ci sai kin yi amai""." """Dan Allah da gaske kake, ulcer ba ciki ba?""" """Zan yi miki ƙarya ne?"" Yayi maganar yana tsuke fuska." """To ka rantse da Allah""" """Ba zan rantse ba, ina likita zan yi miki ƙarya ne? Kuma kan nayi miki allura ban gaya miki" "allurar tsarin iyali na iya ɗauke miki al'ada ba, tun da artificial homones ne aka saka a jikinki ba?""" "Ta ɗan yi shiru sannan ta ce ""Eh ka gaya mini""" """Amma shi ne ki ke ta yi mini wannan borin ko rahama, ni ko?""" """Da ka san me nake ji a zuciyata da baka ce ina yi maka bori ba, na gaya maka mamana mu biyu" "ne da ita, yayanmu ma ya mutu, ya za ayi hankalinta ya kwanta ina nan? Kalli tsawon lokacin da na ɗauka ban ganta ba, ka tausaya mini mana""" "Ya saka hannu yana share mata hawaye ya ce ""Zan mayar da ke rahama, sonake sai na sanar da" "mahaifina komai tukuna, bana son sunanki ya ɓaci kamar yadda ki ke ta iƙrari""" """Ɓacin suna na nawa kuma? Ai ya riga ya ɓaci""" """Zan gyara shi da yardar Allah babyna""" "Sai da yayi ajiyar zuciya da yaga ta ɗan nutsu har ta ɗan saduda, sai da ta samu bacci, sannan ya" "tashi ya fita, ya kira saif a waya ya ce masa su haɗu." *** "A harabar gida Nabila ta tarar da Nasir, tana gama parking ya fito daga cikin tasa motar ya tareta ya ce ""Daga ina ki ke?""" "Kamar ta wanka masa mari, a hasale ta kalleshi ta yi shiru." """Ina magana kin tsare ni da ido""" """Iska na fita sha""" """Wa ki ka gaya wa, sai Abba ya dawo yayi ta faɗa ko? Kuma wace irin shan iska ne zaki fita ki yi" "nisa da gida, kukan me ki ke yi ma?""" """Dan girman Allah ka ƙyale ni"" tayi maganar cikin sauti mai ƙarfi, ta nufi cikin gida da sauri," kamar mahaukaciya sabon kamu. "Ta shiga ɗakinta, ta rufe ƙofa ta wulwula jakar hannunta tayi jifa da ita, ta samu wuri ta zauna ta" "dafe kanta, da take jin tamkar zai rabe biyu." """Ya haiyyu ya ƙaiyyum, ya zuljalalu wal ikram"" take ta maimaitawa, tunanin ma ta rasa wanne" yakamata ta yi. "Viper ya ƙular da ita, amma tafi jin haushin kanta, da ta iya buɗe baki, ta furta tana son shi, a da ko me za ayi mata, ko da wasa ba ta taɓa sakawa a ranta zata iya furtawa wani tana son shi ba. To saurayi ya ce yana sonta ma, wahalar da shi take yi, ko da tana sonsa, saboda ta ja ajinta, amma wai yau ita ta furtawa wani so, kuma yayi rejecting ɗin ta kai tsaye." "Viper yana da qualities ɗin da ya cancanci a so shi, ba ta taɓa zaton wasan da take yi zai zama gaskiya ba, dan ita da fari tsokanarsa kawai take yi, sai kuma matsanancin tausayin sa sa take ji, gashi tausayi ya juye ya koma mata soyayya shi kuma baya ta tata, ga wannan tsohon ciwon nata da ta fama. Zuwa yaushe Abba zai fuskanci gurbin ido ba ido bane ba, duk wani abu da ya faru a baya, bata san an yi shi ba, ba ta san maman nata ba dama wannan an tabattar mata da bata raye, to mahaifinta fa, komai lalacewarsa zata so ta ga abun ta, kuma komai ya yi wa mahaifiyarta, wani abu ne da ya wuce a baya, da ba ta nan ma aka yi shi, to na menene za a gadar mata da wani abu" da ba shi da tushe balle cikakkiyar makama. "Ta zabura ta tashi, ta watso drower littatafanta, ta ɗaukko hotunan mahaifiyarta, cikakkiyar bafulatanar yarinya ce ba wata babba ba, fara sol da ita mai dogon hanci, tayi ɗauri irin na mutanen da, ta zubo da dogon gashinta ta ƙarƙashin ɗan kwalinta, har ka kafaɗarta, dukkanin hotunan uku, fuskarta ɗauke da murmushi daga yanayin hotunan zaka fahimci ba ta da hayaniya, kuma mai yawan murmushi ce." "Ta daɗe tana kallon hotunan tana kuka, ta gaji ta kwanta a kan gado, sai ajiyar zuciya take yi." "Washegari da safe, ta shirya zata tafi wurin aiki, ta shiga wurin Abba ta gaishe shi, amma ya" "shareta yaƙi amsawa, sai gajiya tayi, ta tashi ta fita." "Ko da taje wurin aikin ma, kanta ta kifa a kan teburin office ɗin ta." "Barrister Habib har yayi knocking ya shigo, ba ta sani ba, sai da ya daki teburin, sannan ta ɗago." """Nabila ya dai? Na ji program ɗin ki ya ɗau hankalin mutane, ki zo a mayar da hankali wurin" "neman shaidu, kin shigo kuma kin zo nan kina bacci""" Tayi shiru ba ta ce Komai ba. """Wai meyafaru ne?""" """Ba na jin daɗi ne""" """Yasalam, sannu kuma kika fito? Kina da tiral ne yau?""" """A'a, na zo ne dama mu cigaba da aikin shari'ar nan, ai na sha magani, bari na biyoka office ɗin""" "Tare suke aikin, amma sam hankalinta baya kan aikin, ƙarshe ya ce, su bari sai ta samu sauƙi" tukuna. *** "A wani wurin cin abinci saifu suka haɗu da Abdul, suka zaune saifu ya ce ""Mutumina harkar siyasar nan duk ta ɓoye mana kai, wurin chilling ɗin ma duk ka daina zuwa. Hafsa ta ce tana son ta zo ta ganka, na ce ko ta je asibiti baka zama, ayyuka sun yi maka yawa, asibitin ma ba wani" "zama kake yi ba""" "Yayi murmushin ƙarfin hali ya ce ""Ya jikin nata?""" """Da sauƙi sosai Alhamdilillah, likitanta ma sun sallameta, sun ce ta warke, ina ga wani abun ne" "yake damunta, ta ce kafi dubata sosai, na rasa wani siddabarun kake yi wa patient suke liƙe maka""" """Saif, mu bar wannan maganar, akwai damuwa fa""" """Ta me?""" """Haryanzu babu labarin mahaifiyar yarinyar nan, gashi kuma ta matsa mini, kullum cikin kuka" "take""" "Saifu ya ce ""Ai fa Abdul ka yi mugun ganganci abun da ka aikata, ka mayar da ita wurin iyayenta," "tun kafin asirinka ya tonu, sunanka ya ɓaci""" """Saif, ni fa ba ta sunana ya ɓaci nake yi ko akasin haka ba, ni wallahi burina kawai na cigaba da" "ratuwata da ita, wani irin abu nake ji a kanta, da rabani da ita tamkar rabani da rayuwata ne""" """Kai Abdul, ba ka gama ɗibar abun da kake so ba, ko haryanzu bai isheka ba?""" """Ba wannan nake yi wa ba, ita nake so, tun bayan da na ɗaukota take bani tausayi, ka san ban taɓa" "raping ba, sai a kanta, wallahi son rahama nake yi, so mai tsanani""." "Cikin mamaki Abdul ya ce ""Taɓɗijan, aurenka ne fa yake gabatowa, yanzu yaya kenan, gashi ana" "ta fitina a kan ainihin wanda ya yi mata fyaɗen, wata lauya ta kafe, sai an fito da ita ta bayar da" "shaida a kotu. Ina ga fa dolenka ka gaya wa mahaifinka gaskiya, ya ɗauki matakin da yakamata a rufe abun nan""." """Ina son gaya masa, amma ina tsoron abun da zai iya yi, ba zai ɗauki maganar da sauƙi ba""" """To ai kuwa ko da yaya zai ɗauki maganar, haka ne kawai mafitar""" Abdul ya yi shiru yana zancen zuci. *** "Viper yana zaune, ya tsurawa hoton jauhar ido, yana hararo kamannin Nabila a cikin kansa." "Walid ya dafa shi, ya ɗaga kai ya kalle shi." """Ya ake ciki ne? Mutuniyar kwana biyu, yakamata ace fa shirye-shirye sun yi nisa a kan shari'ar ka," "ta ina za a fara?""" "Viper ya ce ""Fushi take yi """ "Walid ya ce ""Fushin me? Wani abun ya faru ne?""" "Ya girgiza kai ya ce ""Akwai magana a bakinta da yakamata na saurara, wataƙila zai haska mini" "abun da kake gaya mini, sai dai ta bijiro da abun da dole na taka mata burki""" """Wane abu ne?""" "Ya ɗan yi shiru sannan ya ce ""Bakomai""" """Mai zamani, yakamata ka din ga bin komai a sannu, mata fa dukkansu ba irin jauhar bane, jauhar one in million ce, ba kowace mace ce zata iya juriyar da ta yi ba, kar ka yi treating ɗin Nabila" "yadda kake treating ɗin Jauhar, suna da banbanci""" "Yayi shiru, ya cigaba da kallon hoton hannunsa." """Allah ya jaddada rahama a gareki, ya kyautata makwancinki my wife "" yayi maganar yana shafa" "haƙoranta na jikin hoton da yake da shi da ita ne, fuskarsa da ƙuruciya sosai lokacin." "Walid ya ce ""Amin"" ya karɓe hoton, ya ajiye shi a wani wurin." "Yayi shiru yana tunanin ko me Nabila take son ta gaya masa? Ko yanzu tana wani hali? Da gaske son shi take yi, ko kuwa dai still da wasa take yi? Kukan da tayi ya tabattar mata ba wasa take yi ba." To su mata babu wuya sun fara son mutum kenan? Ya ga damuwa sosai da sosai a cikin idanunta "da suka haɗu, ya so ya ji menene damuwarta, amma ta zo da lamari mai girman gaske, son da take" "yi masa wahalar da kanta kawai zata yi, yana cikin wannan halin na ɓoye-ɓoye, idan ta fara son shi yaya zata yi, tun da ba aurenta zai yi ba, kuma shi ba ma wannan ne a gabansa ba gaba ɗaya." *** "Kusan kwanaki huɗu, amma Abba baya saurar Nabila, fushi yake yi da ita sosai, gajiya tayi da" "fushin da yake yi da ita, ga habaici da yar da magana da ake yi mata a gidan." "Ta shirya tafiya aiki, ta shiga ɗakinsa, ya na karyawa." """Abba ina kwana"" yayi mata shiru ya cigaba da karyawa." "Ta tashi ta je gabansa ta zauna cikin kuka ta ce ""Dan Allah Abba ka yi haƙuri ka yafe mini, dan Allah ka yi haƙuri ka yafe mini, in sha Allah ba zan sake maganar babana ba, idan raina ne ya ɓ aci aka yi mini gori, duk sai na ji babu daɗi amma dan Allah ka yi haƙuri ka yafe mini ba zan sake ba"" da fari yayi mata shiru, amma daga baya ya numfasa ya shafa kanta ya ce ""Kukan ya isa haka, na ji na yafe miki, duk da kin sha yi mini wannan alƙawarin amma ba kya cikawa, yau da mahaifinki wani abun kirki ya tsinanawa mahaifiyarki, rabuwar arziki aka yi, babu yadda za ayi na nesanta ki da shi har haka, na yanke duk wata alaƙa tsakaninki da shi. Ki yi haƙuri na san kina haƙ uri da abun da ake yi miki, da zarar kin yi aure shikenan kin wuce wurin, ki yi haƙuri ki cire" "maganar mahaifinki a zuciyarki""" "Nabila ta jinjina kai, amma ƙasan zuciyarta ba ta ji zata iya daina maganar mahaifinta ba." "Ta tashi ta fita ta tafi aiki, ita ma ta fita daga harkar Nasir gaba ɗaya." "Yau ba ta da shari'ar da zata halatta, dan haka tana office tana ta nazarin shaidunta, da za su yi" appeal. "Wayarta ce tayi vibrating, ta ɗaga ta duba ""Mu haɗu a restaurant ɗin da ki ka je, zamu yi magana mai muhimmanci"" ta zubawa wayar ido tana kallonta, ta ajiye wayar. Har mamakin kanta take yi," yadda take abu babu tsoro take wannan kasadar haka. "Ta ajiye wayar ta kifa kanta, can ta miƙe, ta tattara system ɗin ta da kayanta, ta tashi ta fito, suka" yi karo da barrister Habib. "Ya ce ""Yauwwa wurinki zan zo dama, ina son mu je unguwar da abun nan ya faru ne, ko da wani" "abu da zamu kuma samu, da bamu haske a kan shari'ar""" "Ta ce ""Amm ganin likita zan je ne, ko mu bari sai gobe in Allah ya kaimu?""" "Ya ce ""Subhanallah, jikin ne dai?""" """A'a ba wani abun damuwa ne sosai ba, zan dai je na ga likita ne, yau yakamata na koma dama""" """Ok, to Allah ya ƙara afuwa""" Ta amsa da Amin. "Ta je wurin cin abincin, ta kira wayarsa ya ɗaga." """Gani na zo ina wurin""" """Ki miƙe sosai ciki, ki tambayi Vip 2"" ta ƙarasa ta tambaya, aka nuna mata, ta buɗe ta shiga." "Yana zaune, ya ɗora ƙafafuwansa a kan tebur, yana sanye da facemask da facing cap ya rufe" fuskarsa. "Fuskarta babu annuri, ta ƙarasa ta ja kujera ta zauna, ta ajiye jakarta da wayarta, da mukullin" "motarta, amma ba ta ce komai ba." "A yanayin yadda ta tafi wancan karon, bai zaci da ya ce ta zo zata kuma zuwa ba." "Tayi masa shiru, tana danna ƙaramar wayarta." "Ya ɗan daki teburin ya ce ""Attention, magana zamu yi""" "Ta ajiye wayar ta ce ""Ina ji""" "Ya ja babbar wayarta, ya buɗe ya ɗaukko tab ɗin sa, ya fara daddanawa." "Mai kawo abinci yayi knocking, ya kawo ruwa da lemo." "Ya sauke facemask ɗin sa ya ce ""Yaya ake ciki da maganar wancan case ɗin, zuwa yaushe zaku yi appeal ɗin? Sonake ki kammala da wancan shari'ar, sannan ki mayar da hankali a kan tawa, already ina da shaidu guda biyu a ƙasa"" har yayi maganar ya gama, bata ɗago ta kalleshi ba, wasa" kawai take yi da zobunan hannunta. """Magana fa nake yi""" """Ina ji ai""" """Ba jin nake buƙata ba, hankalinki zaki bani"" iya idanunta ta ɗaga ta kalleshi tana yi masa wani" irin kallo. """Ina magana a kan yaushe zaki yi appeal, ki zo ki fara processing tawa, ina da shaidu biyu a ƙasa""" still ba ta ce komai ba ta cigaba da kallonsa. "Zubawa sarautar Allah ido yayi, ya saka mata nasa idon shi ma, ta gyara zamanta, ta kwantar da" "hannunta a kan teburin, ta ɗora kanta ta kwanta ta yi masa shiru." "Ƙasa yayi da muryarsa ya ɗan matsa ya ce ""Meyake damunki ne?""" "Kawai ta fashe da kuka, yayi mata shiru, tayi iya yin ta, ta ɗago ta share hawayenta ta ɗauki" "jakarta, ta ɗauke wayarta daga gabansa, ta juya za ta fita." """Ina miki magana zaki tafi? Ina zaki je ina yi miki magana?"" Yayi maganar cikin tsawa da sai da ta" "firgita, ta ja da baya tana kuka." """Talk"" yana mata tsawa tana ƙara sautin kukan nata." """Meyake damunki? Kin san haka zaki yi mini, ki ka yi mini tayin dawowa normal rayuwata? Ki" "ka ce zaki taimaka mini""" """Ina amfanin tarayya da mutumin da kansa kawai ya sani kuma yake so? Ba cewa kai baka so na ba? Rashin amsa tayina bai yi mini ciwo ba, irin halin ko in kula da ka nu na wa rayuwata, hakan na nufin duk da risk ɗin da na saka rayuwata baka damu ba ko da zan rasa rayuwata. Saboda kana ganina a haka do you know what am going through ne? To an fasa taimakon naka, i destroy the" "deal and i am out of it, ka je kayi duk abun da ka ga dama""" "Murmushi ya yi, sai da haƙoransa suka fito, abun da ba ta taɓa gani ba." """Angry bird, always angry for no reason, duk saboda na ce bana sonki, ki ke wannan abun? Ba zan" "taɓa sonki ba, zuciyata ta jauhar ce itakaɗai""" """Ai baka burgeni ba, da aka zauna baka bi ta lahira ba""" "Viper ya ce ""Ai nayi niyyar bin nata, ki ka hanani, wannan deal ɗin sai an kai ƙarshensa da ke""" """Komai zaka yi, ba zan sake zuwa in da kake in dai ni yar halak ce, babu amfani tarayya da" "mutumin da kansa kawai ya sani"" ta raɓa shi ta wuce ta bar wurin." "Ajiyar zuciya yayi, ya koma ciki ya zauna." "Gida ta tafi, abun duniya duk ya dameta, tana ganin kiran sumayya, amma ta share ba ta ɗagawa," gaba ɗaya ta zama so silent. *** "Abdul ne yake kallon ramma, yadda take ya shiri, ya ce wai shirin me ki ke yi haka ne?" """Asibitin ka zaka tafi da ni, ni dai mu je ka duba ni na tabattar""" """Rahama haryanzu tunaniki ƙarya nake yi kenan?""" """To wa ya sani, tun da haryanzu ban ji na warke ba, amai yaƙi tsayawa, muje idan ma shi ne kawai" "ka zubar da shi""" "Ya girgiza kai ya ce ""A'a ni ba na zubar da ciki gaskiya""" "Ta kalleshi sheƙeƙe ta ce ""Yaushe ka fara tsoron Allah, har ka ke cewa ba ka zubar da ciki?""" """Ai lokacin da zan kama aiki, rantsuwa nayi, ba zan ci amanar aikina ba""" """Kai har wata darajar rantsuwa ka sani? Ni ka daina yi mini wasan kwaikwayon nan, kawai mu" "tafi""" """Rahama mutuwa fa aka yi a wurin zubar da cikin nan""" """Na ji, bakomai, Allah ya yi mini rahama""." "Ya sauke numfashi ya ce ""Na ji, zamu je, amma wallahi ki ka takura mini ba zamu je ba, kuma kar" "ki dame ni""" "Ta haɗe rai ta ce ""Zan baka nan da sati ɗaya, idan na ji shiru zan kuma magana"" ta cire mayafinta," ta bar ɗakin. *** "Unguwar gidan aikin ramma take son sake zuwa, kamar yadda barrister Habib ya buƙata, take ta yi masa yawo da hankali." "Tana daf da shiga mota, ta tsaya tana amsa kiran waya." """Salamu alaikum, Barrister, walid ne""" "Ta ce ""Oga walid, ya kake?""" """Lafiya ƙalau, mutumin ne babu lafiya fa, ko zamu haɗu a wani wurin mu kai shi asibiti a motarki," "saboda yanayin tsaro""" "Gabanta ya faɗi ta ce ""Subhanallah, wani abun ya je ya sha?""" """A'a, ai rabon da ya sha wani abu, an kwana biyu, ciwon ciki yake yi, tun yana yi sama-sama," "tsakanin jiya da yau har suma yake yi""" "A rikice ta ce ""Ya salam, a ina zamu haɗu to? Ina wurin aiki gani nan""" "Da gudu gudu, ta ƙarasa ta hau motar, ta ja, tana tafe tana waya da su, har suka haɗu, sun ɗaukko" shi a adaidaita sahu. "A sume suka saka shi a motarta, hankalinta yayi mummunan tashi ta ce ""Oga walid yana" "numfashi?""" """Eh yana yi, Suma dai yake ta yi""" """Yanzu wane asibitin zamu nufa? Ka ga wancan ga matsalar da aka samu""" Suka tattauna suka yanke shawarar kai shi wani asibitin daban. "Asibitin shi ma a wajen gari yake, amma yayi kyau ya tsaru, ko ina tsab da shi." "Nan da nan aka shiga da shi emergency, aka fara yi musu tambayoyi a kan meyasame shi." "Su walid suka yi musu bayani, aka tafi da shi wurin yin scanic." "Nabila ta fita da sauri, dan ta je ta ji ya tsarin Asibitin yake, da biyan kuɗin, taga ɗan mama yana" ƙoƙarin komawa in da ya baro su. "Ta ce ""Sannu ɗan mama""" "Ya ce ""Yauwwa, an gano meyake damun nasa?""" "Tayi murmushi ta ce ""Suna ƙoƙarin yin hakan dai, wannan karon ma ka je ka sanar da su ne su zo" "su biya bills ɗin asibitin nasa?""" "Yayi turus yana kallonta, ya ce ""Kamar yaya?""" """Kamar yadda wancan karon kayi, kai ka yi waya aka biya bill ɗin Viper, dan babu wanda ya san mun je asibiti, yanke muka din ga yi, mu ƙaddara ma wani ya sani yana bibiyarmu, ana tsaka da treating ɗin sa hankalinmu yana kansa, ka zame ka fice. Kana kawo masa miyagun ƙwayoyi a duk lokacin da ya buƙata, abubuwa da yawa idan ba na kusa da shi ba babu yadda za ayi a san su," "wa ka ke yi wa aiki?""" Ayshercool 08081012143 ₦500 ne via 0009450228 Aisha Adam jaiz bank sai shaidar biya ta 08081012143 Wanda za su jira document 1K ne. 90009343 'Yan Nijar ku turo katin airtel na 300fcfa Arewabooks ayshercool7724 "Ɗan mama yayi murmushi, ya ƙara taku biyu gabanta, ya kalleta ya ce ""You better count yourself out of this. Ba ni da niyyar cutar da Viper, da cutar da shi zan yi, da tuni na yi so bakinki ƙanin ƙ" "afarki"" daga haka ya miƙe ya nufi in da suka baro su walid." "Aka fito da Viper a kan gado, aka ce za a ba su ɗaki, za a turawa likita result ɗin." "Kamar yadda Nabila ta yi tsammani, an biya bills ɗin, ta din ga yi wa ɗan mama kallon tuhuma," "shi kuwa da sun haɗa ido, sai yayi mata murmushi, hakan ya ƙara jefata cikin tunani." "Likita ya shigo da file a hannunsa, suka sake gaisawa, ya tattaɓa cikin Viper, sai dai duk da an yi" "masa allurai ya samu bacci, da ya taɓa cikinsa ɓangaren dama, sai da ya zabura ya motsa." "Ya duba scanic ɗin hannunsa, ya ce ""Hantarsa ce ta kumbura gaskiya, amma ƙodojinsa da sauran" "abubuwa lafiya ƙalau, amma duk da haka zaku yi x-ray na cikin, mu sake tabattarwa ko da wani abun""" "A tsorace Nabila ta ce ""Likita hantarsa ta kumbura kuma?""" """Eh, amma karki damu babu wani abu in sha Allah, idan aka yi x-ray ɗin, akwai likitanmu da zai" "zo ya duba shi, ba wani abun tayar hankali bane ba, zai samu sauƙi in sha Allah""" "Walid ya ce ""Allah ya sa""" "Ɗan mama ya ƙurawa wayarsa ido, sannan ya kalli Nabila, yayi mata alama da su haɗu a waje." Ya tashi ya fara fita sannan ta bi bayansa. "Ya ce ""Ana bibiyarki, yanzu aka turo mini saƙo, zaki bani mukullin motarki, zan kawo miki ita" "gida a matsayin bakanike""" """Nifa ban fahimci duk wannan abun ba""" """Tsayawa dogon bayani, ba zai haifar da ɗa mai ido ba, ki ga gaggauta muje na raka ki, na ɓulla" "da ke wata hanyar ki hau napep ki tafi gida, zan kawo miki motar gida""." """Kamar wani abun kake shiryawa a kaina"" ya miƙa mata wayarsa, ta karɓa ta duba, message aka" "turo masa aka yi masa bayanin kar ta tafi a motarta, akwai yiwuwar a kamata, ko kuma ayi mata" wani abu. "Bai bari ta yi wa su liti sallama ba, ya fitar da ita daga asibitin, ya tare mata abun hawa ta hau ta" tafi tana mamaki. "Ta koma gida, duk a gajiye, abubuwa duk sun dame ta, tana ta tunanin ciwon Viper, tayi ta addu'a" "Allah ya bashi lafiya, sai ta ji ba ta kyauta ba maganganun da ta gaya masa, haɗuwarsu ta ƙarshe." """Allah ka bashi lafiya, ka bani ikon cika masa alƙawarin da nayi masa""" """Arfa""" """Na'am"" ta amsa tana daga zaune." """Ina motarki?"" Nasir yayi maganar yana shigowa cikin ɗakinta." """Lalacewa ta yi, na bawa bakanike""" """Wane bakaniken?""" """Bakanike dai mai gyara mota""" """An ce an ganki da wasu maza a motar, a can ring road, sai dai ba a san in da ku ka yi ba, na saka" "jami'ai a arear in da ake tunanin kin bi, aka kama wani da motar yanzu haka yana tsare a wurina""" "Ta miƙe tsaye ta ce ""Wai dan Allah yaya me kake nufi da ni ne? Motata ta lalace zan yi gammo na" "ɗauketa a kaina ne, na kira masu gyara su tafi da ita sai ya zama laifi, na menene zaka saka a din ga bibiyata ma?""" """Saboda baki da gaskiya arfa, gaba ɗaya kin canza, kuma ba kya tsoron salwantar da rayuwarki""" """Kalli, kamar da gaske ka damu da rayuwar tawa, ba ta rayuwata kake yi ba, mafitar ka kawai kake nema Yaya Nasir, amma ai ramin ƙarya ƙurarre ne ka cigaba da bibiyata. Na roƙe ka ka saki bawan Allah, gyaran mota kawai na bashi, abun arziki bai kamata ya zama na tsiya ba"" ta fita daga" ɗakin gaba ɗaya ta bar shi. "Da daddare ta kira walid, ta ji ya jikinsa, ya tabattar mata jiki da sauƙi sosai, ya farka ma." "Nabila ta ce ""Oga walid, shaye-shayen nan ne fa ya fara taɓa shi, ya janyo masa wannan matsalar""" """Ai bama sai kin faɗa ba, shi ne ba wani abun ba""" """Dan Allah oga walid ku daina wannan rayuwar, idan ba haka ba da ƙuruciyarku haka zaku rasa" "lafiyarku ku mutu, dan Allah"" yayi murmushi ya ce""Karki damu, za a daina in sha Allah""" """Allah ya sa, ayi masa sannu dan Allah""" "Ya ce ""Zai ji in sha Allah"" bayan ya kashe wayar, ya fita yana mitar ina ɗan mama ya tafi har" wannan lokacin bai dawo ba. "A harabar Asibitin ya haɗu da ɗan mama, kamar ya kwaɗe shi, dan haushin abun da yayi, shi" "kuma bai gaya masa ainihin abun da ya faru ba, ya ce masa wani wuri yaje." """Ka wuce ka je ka zauna da shi, liti ya je nemo wani magani, ni kuma zan je gida""." """Kar ka je gidan nan oga Walid, hanya babu kyau, cinnakun nan sun ɗana mana, akwai wani abu" "a ƙasa ka ɓad da sahu, ka lafe a wani wurin, akwaisu sosai a hanyar gidan nan""" "Walid ya ce ""Na fahimta, muddin kaga wani abu da baka yarda da shi ba, ka kira sanar mini"" ya" jinjina masa kai. "Nasir yana zaune ya gama cin abincin dare, aka kira shi a waya." "Ya ɗaga a take, ganin daga office ɗin su ne." """Yallaɓai yaron nan fa, wasu sun zo sun yi belinsa""" """Wane yaron?""" """Wanda muka kama, kuma sun ɗauki motar ma""" "Tashi tsaye yayi ya ce ""What? Meyasa ku ka bari suka ɗauka? Waye ma ya ce a sake shi?""" """Manyanmu ne yallaɓai"" mukullin motarsa ya ɗaukko ya fito da sauri, kawai ya tarar da motar" arfa a gareji. "Bin motar ya din ga yi da kallo, dan ya tabattar ita ce, ko ba ita ce ba. Bai haƙura ba sai da ya" dangana da zuwa ya dudduba ya tabattar dai ita ɗin ce. "Bai tsaya ba, ya shiga cikin gidan, ya tarar da ita a falo, suna kallo a falon ita da mutanen gidan." """Arfa waye ya kawo miki motarki?""" """Ina ga bakanike ne, yaro ne ya kawo mini key ya ce an kawo motar"" tayi maganar cikin ko in" kula. "Ganin da mutane a wurin, ya sanya bai ja maganar ta yi tsawo ba, ya bar falon." *** "Liti yana zaune yana game a wayarsa, likita ya shigo, ya kalli likitan, likitan ya ce ""Sannu ko, ya mai jikin?""" """Da sauƙi""" """Masha Allah, naga ya samu bacci ma, shi ne mai hepatitis ko? Yayi maganar yana duba file ɗin Al'amin. Kodayeke ma bacci yake yi, bari ba sai an tashe shi ba, idan aka yi x-ray ɗin na duba shi, idan ya farka gaba ɗaya"" yayi maganar yana taɓa cikin Al'amin. Sai dai yayi shiru yana kallon Viper, yana ƙoƙarin ganin fuskarsa sosai, dan kamar ya san shi, sai dai yanayin kwanciyar da ya" "yi, bai bashi damar yin hakan ba." "Ya kalli file ɗin Al'amin, an rubuta Muhammad Ibrahim. Ya juya zai fita, ya tsaya ya sake" waiwayowa ya kalli Al'amin ya ɗan yi shiru sannan ya fita. "Yayi iya ƙoƙarin sa wurin tuna a ina ya san shi, amma ya kasa dan haka dolensa ya haƙura." *** """Rahama""" """Na'am""" """Zan fita da ke, zamu je asibiti, wallahi idan ki ka yi misbehaving, ke da ganin mahaifiyarki har" "abada""" """Idan da zan yi misbehaving, da tuntuni da kake fita da ni da nayi, amma na fara gajiya da ƙaryar da kake yi mini, na cewa gwargwadon bin umarninka da nake yi, shi zai sanya ka sada ni da mahaifiyata. Ina tsoron tonuwar asirina na wulaƙanta a idon duniya, shiyasa bana yi maka ihu, da neman agaji, sonake ka mayar da ni cikin sirri da rufin asiri, yadda ba zan tozarta da yawa ba," "amma haryanzu na kasa gane in da ka dosa""" "Ya ce ""Zaki fahimta ne, muddin ki ka yi yekuwa, to ke zaki kunyata fiye da ni, kuma ni zan iya wanke kaina, ke kuwa zaki tozarta, dan sai kin samu masu ɗoraki a social media kowa ya ganki," "kin san duk abun da namiji yayi ado ne""" "Ta girgiza kai ta ce ""Wannan wani banzan tunani ne, na waɗanda ba su san girman Allah ba, babu al'ada a batun saɓon Allah. Allah bai ware wutar mace ba, kuma bai ware ta namiji ba, bai ce zai sassautawa wani ba dan yana wani jinsi idan ya saɓa masa ba, dan haka babu ado da zunubi, idan al'ada ta nuna maka duk abun da ka yi ado ne, addini kuma ya koyar da kai tsoron Allah da tsoron azabarsa""" "Wato ramma akwai baki, wasu lokutan duk abun da yake ji da shi, sai ta ƙure shi ta hanyar kafa" "mishi, hujjoji da addini, dan haka ya ja bakinsa yayi shiru, suka cigaba da shiri." "Tana sanye da niƙab, a kan dogon hijjabinta, yake nuna mata wurare a cikin asibitin, wai nan ma" "branch ne na Asibitin, ba shi ne main branch ɗin ba, sai dai yayi kyau ya tsaru sosai da sosai." "Washegari da safe Nabila ta je court ɗin da take da trial, tayi ta kammala, ta samu wurin parking," "ta bayar da ajiyar motar, ta hau napep ta fita asibiti." """Ki zauna a nan, zan je na fara zagaywa na duba marasa lafiya na, sai na zo na tafi da ke, in da zan" "duba ki""" "Ta kalleshi ta ce ""To ka tafi da ni mana, ni ba wani abun zan yi ba""" """So ki ke sai wani ya ganki wai?""" """Matsalar rashin gaskiya kenan""" """Eh na ji, ga kayan tea nan, fridge akwai lemuka, ga kayan kallo nan, ki yi duk abun da ki ke so," "ban da fitina, zan rufe ki a nan, zan je na ga marasa lafiya, sai na yi ward round na dawo""" "Ta ce ""Saura ka daɗe""" "Abdul ya ce ""No ba zan daɗe ba in sha Allah"" yayi kissing goshinta ya ce ""I love you, ki yi mini" "addu'a na yi komai cikin nasara""" """To jeka, kar su gaji da jiranka"" haka kurum ya din ga jin is no safe, ya bar ta nan, kamar wani abu" "zai faru, ya din ga waiwayawa yana kallonta, har ya fita ya rufeta a wurin." "Nabila ta shiga cikin Asibitin, tana saanye da hijjabin da ta ɗora a kan uniform ɗin ta da facemask, sai waya take yi, tun da ta taho, wata matashiya da ita ma tahowa take yi, suna facing ɗ in juna, take bin ta da kallo. Ji take yi, tamkar ta je ta ɗage facemask ɗin fuskar Nabila taga wacece, har ta wuce hanyar da yakamata ta tabi." "Wayarta ce ta fara vibrating, ta ɗaga ta ce ""Hello yaya""" """Dalla malama kina ina, gashi ya zo, zai fara ganin marasa lafiya, ki zo ya fara da ke na mayar da ke gida, amma kin tafi yawonki"" kasa bashi amsa tayi, ta ɗaga kai tana dube-dube, ta nemi Nabila" ta rasa. "Jiki a sanyaye ta shigo office ɗin, saifu kamar ya mareta ya ce ""Wai ina ki ka tafi, yazo ya zauna" "yana jiranki?"" Bata amsa ba, ta zauna jiki a sanyaye." "Abdul ya ce ""Dan Allah ka daina yi mata tsawa, ka san mara lafiya ce, ba na son naga ana kyarar" "mini patient, Hafsat ya aka yi ne?""" """Doctor Abdul, jauhar fa na gani ta saka niƙab ta wuce""" "Ya ce ""Wacece haka?""" "Saif ya ce ""Na fuskanci ba ta warke daga depression ɗin nan ba, likita ya sallameta, ƙanwarmu" "da ta mutu fa take magana a kai""" """Wallahi yaya, ka taso mu bi hanyar da ta bi, ka ganta kaima, ta saka niƙab""" """Kuma da niƙab ɗin ki ka ga jauhar ce?""" "Ta ce ""A'a, gani nayi kamar na santa, kuma wallahi irin idonsu ɗaya, ai naga idonta""" "Abdul ya yi murmushi, ya fara bin hanyoyin su na likitoci, wurin daidaita tunanin hafsa, da saka" mata nutsuwa. "Nabila tayi sallama. Al'amin yana zaune, ya jingina da jikin gadon, yana ɗan yamutsa fuska." "Suka gaisa da ɗan mama, shikaɗai ne a wurin, ta ƙarasa gabansa ta ce ""Sannu ya jiki?"" Ya jinjina" mata kai alamar da sauƙi. """Kaga ɗaya daga cikin illar shaye-shayen miyagun ƙwayoyi ko? Kodayeke zuwa yanzu ai ba illa ɗaya ka gani ba, illoli daga dabar shaye-shaye da bangar siyasa wanne yayi maka rana a cikinsu? Daba da bangar siyasar a dalilin su, ka rasa makusantanka, ka rasa soyayyar mahaifi da ta ƴan uwa, illar da aka yi maka, ka kasa karɓar ƙaddararka, ta'amalli da miyagun ƙwayoyi ya sanya, ka nemi ka rasa imaninka, ka halaka kanka, yanzu gashi lafiyar ka ta taɓu, gaba ɗaya abubuwan nan babu wanda zaka ɗaga na ce ga ribar da ka samu a dalilin su, dan Allah ka cikawa yar madara burinta, duk da bata duniya, ka zama mutumin kirki, ka zame mata sadaƙatul jariya, ya zamana bata raye, amma tana da kamashon ayyukan alkhairin da zaka yi idan ka zama mutumin kirki, tun da ita ta ɗaukko hanyar saita rayuwarka bisa hanya mai kyau"" kamar ba zai yi magana ba, sai ya" buɗe idonsa ya zuba mata ido. "Ita ma shi take kallo, amma ta yi ƙoƙarin janye nata idanun daga nasa." "Ya zuba mata ido kamar zai haɗiyeta, hatta maganarta wani abun idan tayi, kamar Jauhar." """It all depends on you"" ya furta yana cigaba da kallonta." "Ta ɗago ta kalleshi, ""Ke zaki ƙarasa abun da ta yi niyyar yi, ta hanyar cika mini alƙawarin da ki ka yi mini. Na gode da ki ka taimaka mini, ban rasa imanina gaba ɗaya ba, tabbas a duniya daba da shaye-shaye basu tsinana mini komai ba, sai asara kashi-kashi wata na bin wata. Abu ɗaya nake fata, ko da ba zan rayu ba, naga an hukunta wanda suka kashe mini mata ba tare da hakkinta" "ba, shi ne babban fatana, ke ki ka cusa mini aƙidar in ɗauki mataki ta hanyar shari'a ba hanyar" "da nake so nake ganin ita ce dai-dai ba. Ba wai ina roƙonki bane ba, kina da zaɓin yin abun da ki" "ke ganin shi ne dai-dai a gareki""" "A ƙasan zuciyarta ta ce 'Ai ba zaka canza ba""" "Kiran sumayya ta gani a waya, ta ajiye ledar kayan marmari da ta shigo da su, ta fita amsa waya." "Ba ta san dalilin kiran sumayyan ba, dan haka ta nemi hanyar da zata nesanta ta, da wurin shige da" ficen mutane. "Tabi wata hany, ta ɓulla wani wuri da babu kowa, ta tsaya a wurin ta ciro wayarta ta ɗaga ta ce" """Hello, Sumayya T ladan baki abun magana, maƙogwaron kakaki radio""." "Gaban ramma ya faɗi, jin muryar mace a wurin office ɗin, sunan wadda aka ambata ne ya daki zuciyarta, Sumayya T ladan, tana jin program ɗin ta, sai dai a rufe take a cikin office ɗin babu" hanyar fita. """Ba shakka Nabila Yusuf maitama, ni kike kira da ni da sunan ubana ko?""" """To ai kin rama, ya ne ya ake ciki, ya gidan radio?." "Abdul ya shiga ɗakin da Viper yake, da shi da wata Nurse da take on duty." "Ya kalli ɗan mama ya ce ""Ina mara lafiyan?""" "Ɗan mama ya ce ""yana banɗaki""" "Ya ce ""Ok, sister je ki room 4 ki duba mini temperature yaron nan, kafin na zo"" ta ce ""Ok sir""" "Ya tsaya yana dudduba medication ɗin da aka yi chatting, ya juya baya yana amsa waya Viper ya fito, ya nemi wuri ya zauna a kan gadonsa, ya gama amsa wayar ya juyo, idonsa suka shiga cikin" na Viper. "Ƙiris ne ya rage bai yar da wayar hannunsa ba, an kusa shekara bakwai rabonsa da Viper, tun wata haɗuwa da suka yi, ya zo hutu suka kusa faɗa P.A ya gargaɗe shi a kan hakan, Viper ya ƙara" "girma, kwarjini ya ƙara baibaiye shi." "Shi bai san abun da ya faru ba, shi dai ya daina ganinsa a wurin mahaifinsa, ya ji labarin kisan kai yayi, aka rufe shi, sai kuma yaji mahaifinsa yana nemansa, kasancewar shi ba mai shiga abun da" "babu ruwansa bane ba, sam bai damu da sai lallai ya ji meyake faruwa ba." "Da ido Viper ya yi wa Ɗan mama magana, ɗan mama ya taso, ya zo, Abdul bai gama tunanin ba," "Viper ya zare wuƙar da ke ƙugun ɗan mama, ya fuzgo labcourt ɗin Abdul, ya zauna a gabansa. Ya kalli ɗan mama ya ce ""Ka gindaya katanga, ba shiga babu fita"" ɗan mama ya jinjina kai ya" "fice, ya rufe su ta waje." """Ka yi mamakin ganina ko? Nima mamakin ganinka nake yi, haka mahaifinka ya adana rayuwarka, ni kuma ya tagayyara tawa, ya bar ni da yawon ramuka ina ɓoye kaina, tamkar maciji, kodayek macijin ne ni, ina nan zan yi fitar burtu daga ramin, zan yi masa sara mafi muni, da zai yi" "ajalinsa""" """Da mahaifina kake yi, ni meye nawa a cikin abun da ya haɗaku?""" "Viper ya saka masa kaifin wuƙarsa a jijiyar wuyansa ya ce ""Kai likita ne, na san ka san ma'anar wannan jijiyar, kuma ka san mai hudata yake nufi ga rayuwar ɗan adam, idan ka yi wani yinƙuri da bai gamshe ni ba, zan yi wa jininka magudana zuwa doron duniya. Ya saka hannu ya ciro wayar" "Abdul daga gaban labcourt ɗin sa, ya ce masa ""Buɗe ta""" "Ya karɓa ya buɗe masa, Viper ya karɓa yayi danne-danne a ciki, sannan ya miƙa masa ya ce ""Gashi nan, zan tura masa saƙo mai muhimmanci ta hanyarka, kafin nan ka gaya masa, zan cigaba da farautarsa babu dare babu rana, sai na ɗaiɗaita farincikin sa, ni ƙarfen cikin wuta ne, hannun da yake ƙoƙarin sakawa dan ya kamani, idan nayi masa illa, sai ya nakasa, nakasa kuma ta har abada. Ƙarfen da yayi yinƙurin yin amfani ya ɗaukko ni, wutar tayi masa zafin da na riga na narka shi, ba kowane irin ƙarfe ne zai ciro ni ba. yana gama maganar ya hankaɗa Abdul da hannu" "ɗaya, sai da ya faɗi ƙasa." "Nabila kuwa babu yadda ba ta yi ba, ta shiga, ɗan mama ya hanata, ya ce likita ne yake duba shi, ya ce su fito waje." "Ita kuma ga sumayya na jiranta, tana ta tuna mata lokacin program ɗin su ya kuss, ga barrister Habib yana ta kiranta shi ma, dan haka kawai tayi masa sallama, ta ce za suyi waya." "Ɗan mama ya ce ""Jiya bayan fita ta da motarki yayanki da kansa ya kama ni fa""" """Ina ta son na yi maka magana, ya aka yi kuma ya sake ka""." """Waɗanda nake yi wa aiki ne suka karɓo ni, na kawo miki motar ki gida, na bayar da mukullin aka" "kai miki ciki""" "Nabila ta ce ""Suwa ka ke yi wa aikin kenan?""" """Ai sauri ki ke yi, kuma ya saɓa dokar aikin da nake yi, ki kula sosai yayanki tarko yake yi miki" "ko ta ina, siled mistake zai iya kama ki"" ta ɗan yi shiru sannan ta jinjina masa kai ta ce ""Na gode""" "Cikin ɗakin kuwa da sauri Abdul ya tashi, ya shafo wuyansa da wuƙar Viper ta fara yankarsa, ya ga jini, ya ja da baya a hankali yana kallon Viper, ya nufi hanyar fita ya jijjiga ƙofar da ƙarfi, ɗan" "mama ya buɗe, ya fice cikin matsanancin hanzari, ɗan mama kuma ya shiga." "Wuyansa ya cigaba da tsatstsafar da jini, ya fita gate wurin security, ya ce su hanzarta, su shiga" "amenity 2, su kama wanda yake cikin ɗakin, babban ɗan ta'adda ne, da jami'an tsaro suke nema""" "nan da nan suka tashi da gudu, suka yi cikin Asibitin." "Ma'aikatan suka ce, ya tsaya ayi masa treatment ɗin wuyansa, ya ce musu a'a, ya je ya buɗe Office ɗin sa, ramma na ciki ta kwanta a kan couch ɗin ɗakin tana bacci, ya danƙota daga kan" "kujerar, sai da ta razana, ya fita da ita da sauri, ta ce ""Abdul lafiya kuwa? Menene wai?""" """Akwai matsala ne"" ya faɗa lokacin da ya sakata a mota ya rufe." "Suna tafe a hanya ta ce ""Meyasame ka a wuya ne? Wai me yake faruwa?""" """Wani patient ne mahaukaci, ya yanke ni a wuya""" "Cikin tausayawa ta ce ""Subhanallah, sannu Allah ya sauwwaƙe, kuma baka tsaya ka saka magani" "ba""" """Bakomai, idan muka je gida na saka""" "Security kuwa suna zuwa suka tarar da ƙofar ɗakin a buɗe hanhai, sai dai babu kowa a ciki." "Suka dudduba har cikin banɗaki, amma babu kowa." "Suka je suka rufe gate, aka hana kowa shiga da fita, tuni aka sanar da jami'an tsaro, Viper kuwa da" "ɗan mama tuni suka dire katanga, ya kira su walid ya ce kar su dawo, asibiti babu lafiya, Viper ya haɗu da ɗan gidan indabo." "Liti ya ce ""Maganar banza kenan, kuna daidai ina mu zo mu same ku?""" "Viper ya ce ""Ba sai kun zo ba, zamu zo mu same ku""" "Sai da ya kai ramma gida, ya zauna ya yi wa kansa dressing, aka kira shi a waya, aka ce ya je yan" sanda za su ɗauki report ɗin abun da ya faru. """Kai ba zan sake dawowa wurin nan a yau ba, sai an tabbatar da security wurin""" "Ɗan sanda ɗaya ya karɓi wayar, ya ce ""Doctor, to ko zaka gaya mana wani ɗan ta'addan ne?""" """Aminu Viper ne, wands ake cewa mai zamani da""." """Mai zamani kuma, yallaɓai Viper fa""" """Eh shi fa""" "Ɗan sandan ya ce ""Ok to"" Nan da nan suka kira DSP Nasir a waya suka sanar masa." "Nabila bata san abun da yake faruwa ba, ta ƙarasa gidan radion su sumayya, sai da suka yi faɗa da" "sumayya, saboda lokacin shirin ya ɗan ja sosai, sai itakaɗai ta fara program ɗin." "Sai da ta nutsu, suka gama faɗan dai-dai lokacin aka dawo daga talla, sumayya ta gabatar da ita" suka ɗora da program. "Yau ma dai program ɗin na su, a kan abun da ya shafi harkar shari'a ne, kanta tsaye take bayyana" ƙulle-ƙulle da rashawar da ta yi katutu a harkar shari'a. "Nan ta tabattar da cewa zasu yi appeal, a kan shari'ar ramma, kuma tana fatan hukumar shari'a zata" sanya ido sosai a kan yadda shari'ar zata gudana. "Sumayya ta ce ""Yanzu dai kina da hope kenan, a kan appeal ɗin da zaku yi?""" """Sosai kuwa sumayya, kuma ina nan a kan bakana, lauyoyin gwamnati da bunkure foundation su gabatar da victim a gaban kotu, kuma ina da kyakykyawan fata a kan wannan shari'ar, sannan" "bayan haka akwai tarin ƙulle-ƙulle da zan warware a wannan zaure, masu tarin ban mamaki""" """To shikenan, da ni da masu sauraro muna dako, duba da yanayin lokaci, baki samu shigowa da wuri ba, da haka da haka nake cewa muna nan muna saurarenki, domin jin wane irin ƙulli zaki warware mana." "The lady of her words, the young capacitated barrister, gugan ƙarfe sha kwaramniya iron lady," "kuma boss lady, voice of voiceless Barrister Nabila Yusuf maitama ayi sallama da masu sauraro""" "Dariya Nabila ta din ga yi ta ce ""Kirarin nan naki dariya yake bani Sumyya, ai ke ce voice of voiceless, baki abun magana, a sayar da a tsage gaskiya, the lady of the century Sumayya T ladan, Allah ya ƙara kiyaye mana ke, masu sauraro Assalamu alaikum"" suka ƙarƙare shirin cikin nishaɗ" i da dariya. "Tuni Nasir ya isa asibitin, ya fara investigation, aka ɗaukko masa file ɗin Viper da aka buɗe, sai" "dai babu lambar waya a jiki, ya ce meysa babu lambar wayar mai file, record suka ce, emergency aka buɗe file ɗin, kuma ba su ne a shift ɗin da aka buɗe file ɗin ba." "Ya saka security su kawo masa littafin da masu shiga da fice suke rubuta sunan su a ciki, aka kawo" "masa yana dubawa, babu wani sanannen suna a ciki, sai dai ya tsaya cak, ganin sunan Nabila a cikin book ɗin." "Nabila kuwa ta ɗauki hanyar titi, bayan ta ɗauki motarta, tana tafe yau jinta take sakayau," "kwanakin da ta yi cikin takaici, zuciyarta tamkar an wanke mata ita." "Ta kalli glass ɗin motarta, ta ga wata babbar mota ta taso ta a gaba, idan ta kauce, ta bar hannun ta bawa motar dama ta wuce, sai motar ta rage gudu, ganin ba zasu bata damar tafiya cikin kwanciyar hankali ba, ya sanya ta ɗauki titi sosai, ta wuce su, amma suka cigaba da binta by fire" by force ita suke hari!. "(Am sorry for delayed posting, am sick ayi mini addu'a please)" Ayshercool 08081012143 ₦500 ne via 0009450228 Aisha Adam jaiz bank sai shaidar biya ta 08081012143 Wanda za su jira document 1K ne. 90009343 'Yan Nijar ku turo katin airtel na 300fcfa Arewabooks ayshercool7724 "Al'amin da ɗan mama suna kwance a cikin ciyayi, in da suka ɓuya nesa da Asibitin sosai." "Suna ta jin kai komon motocin yan sanda, ɗan mama ya kalli Viper, ya ga yadda yake rintse idanunsa, yana damƙar ciyayin wurin, ya ce ""Sannu oga Viper, cikin ne? Ko wani asibitin zamu" "tafi?"" Ya girgiza masa kai alamar a'a." """To tun da da cannula a hannunka, kaga magungunanka da na kwaso, naga suna yi maka wannan" "allurar, ina ga ita ce ta ciwon cikin, bari na yi maka""" "Viper bai ce masa komai ba, ɗan mama ya haɗa allura ya hau zuba masa a cikin cannula, a" "hankali viper ya fara buɗe idanunsa, amma kansa ya fara juyawa, ya kasa magana." "Ɗan mama ya koma gefe, ya kunna sigari yana sha, mintuna goma Viper ya tafi gaba ɗaya, ya" "ciro wayarsa ya danna, sannan ya saka a kunnensa ya ce ""Hello sir, eh su yi sauri ya samu bacci, amma yana cikin ciwo sosai""" "Ya ajiye wayar ya cigaba da shan sigarinsa, mintuna arba'in sai ga wata helux baƙa ta iso wurin, wasu narka narkan ƙarti suka fito, suka saɓa Viper suka saka shi a cikin motar, ɗan mama ya" kama ya hau suka tafi. "Suna tafe a hanya su liti suna kiran ɗan mama a waya, ya gaya musu yana ina, da shi da Viper, ya" "din ga raina musu hankali yana yi musu kwana-kwana, suka din ga zaginsu amma ya ce ""Oga" "walid ka yi haƙuri, wayar zata mutu babu caji"" ya katse wayarz ya cire batirinta gaba ɗaya." "Wani Asibiti suka kai shi, likitoci suka rufu a kansa, suka dudduba shi, suka ce babu wata matsala zai warke, ba wata gagarumar matsala bace ba, sai dai dole ya nisanci shaye-shaye idan yana son" zama lafiya. "Nasir jiki na rawa ya ɗaukko wayarsa, yana kiran Nabila, sai dai yayi mata missed calls, sun fi biyar, ko ɗaya bata ɗaga ba, hakan ya ƙara fusata shi ainun, ficewa yayi ya ɗauki mota ya bar" "Asibitin, yana ƙoƙarin gazgata zargin da yake yi wa Nabilan." "Yana ƙoƙarin sake kiran wayarta, sai ga kiranta, ya ɗaga zai yi magana ya ji muryar da bata" "Nabila ba, ta wani daban." """Malam ina mai wayar?""" """Ta haɗu da hatsari, tana emergency na asibitin cikin gari"" wani wawan burki ya ci a tsakiyar titi," wanda sai da ya kusa haddasa hatsarin shi ma. """Ta mutu ne?""" """A'a, ana kula da ita, ni ɗan sanda ne, mu muka kaita asibitin""" """Nima ɗan sandan ne, ka gaya mini ta mutu ko?""" """A'a, muna dai jiran abun da likitoci zasu ce ne"" ana tayi masa horn, amma hankalinsa baya kai," ya fizgi motar ya canza hanya. *** "Ramma kuwa bayan Abdul ya gama wayar ta ce ""Ka ce mini mahaukaci ne ya yanke ka, kuma yanzu na ji yan sanda ne suka kiraka ana zancen ɗan ta'adda""" """Eh shi ne mahaukacin ai""" "Ta ɗan yi shiru sannan ta ce ""Kamar na san sunan da ka faɗa fa""" """Wanne?""" """Mai zamani, amma kuma kamar ba haka ake ce masa ba, mama ta san shi""" "Basar da zancen yayi ta hanyar cewa ""Wayyo wuyana""" "Cikin kulawa ta ce ""Sannu, ka kwanta to""" """To ki zauna sai na kwanta a kan cinyarki""" """Gaskiya ba zaka takura mini ba, wai kai jinyarka sai ka ce wani jariri, ka yi ta ragwanci, ɗan" "wannan ciwon sai wash kake, wannan idan kaga fuska kuka zaka yi kenan?""" """Haba baby, ki tausaya mini mana, da na mutu fa""" "Ramma ta ce ""Haka nake fata dama""" """Ƙarya ki ke yi "" yayi maganar yana janyota, yana ƙoƙarin kwanciya a jikinta, ta ture shi ta ce" """Baka isa ba, idan ka gama sangartar ka watstsake, mutum ba juriya""" "Shagwaɓe fuska yayi, yana kuma kwanciya a jikinta ya ce ""Zafi""" """To sannu""" """Yauwwa baby, i love You, ki kula da ni sosai""" """To samo zani sai na goyaka ƙarewar kula, ka rabu da ni dan Allah"" ƙarshe ta gama mitar ta rabu" da shi. *** "Nabila kuwa a emergency, aka gano gocewar ƙashi a hannunta, sai buguwa da tayi a ka, ta fasa" "goshi, ga jini na fita daga hancinta, in da Allah ya taƙaita abun, da seatbelt a jikinta take driving, dan Abba na yawan gargaɗinta a kan hakan." "Godiya Nasir ya din ga yi wa Allah, da ya tarar bata mutu ba, daga nan asibitin, ya ɗauketa ya" canza mata wani. "Da ƙyar ya iya kiran Abba ya gaya masa, saboda yadda baya ɗaukar lamuranta da sauƙi." *** "Lokacin da aka kai Viper da ɗan mama gida, su liti basa nan, sun bazama nemansu, duk da a hanya, sai da jami'an tsaro suka tare motar, da son bincikar motar, amma ganin masu motar, ya sanya aka basu dama suka wuce." "Suka kwantar da Viper suka tafi, ɗan mama ya gyara gidan, ya nemi wuri yayi zamansa hankali a" kwance. "Dare yayi sosai, su liti suka dawo, suka tarar da ɗan mama da Viper yana bacci." "Zabura liti yayi, zai kwaɗe shi, Walid ya hana shi, ya ce ""Ɗan mama, wane irin wulaƙanci ne ka yi" "mana haka?""" """Oga Walid, wayata ce ta mutu fa, ɗan gidan indabo ne likitan da ya shiga duba shi, tona mana asiri ya so yayi, a kama mu, muka yi layar zana, muka dirge, muka samu wuri muka ɓuya, ciwon cikin ya sake tayar masa, na yi masa wata allura da na ga suna yi masa a cikin kayan magungunan sa, kawai naga ya ware, shi ne na samu abun hawa, na kai shi wani asibitin, da kyar na kawo shi" "gidan nan, hannunsa na saƙalo a kafaɗata muna tafe muna faɗuwa har gida""." "Liti ya ce ""Ɗan azzaluma, duk sai da ka azabtar da shi, ga ciwo yana fama, shegen taurin kai" "kamar jinjirin jaki, ka gaya mana kuna ina, ka ƙi da yake ɗan kut....ne kai, ɗan wahala kawai""." "Walid ya ce ""Dan Allah liti kayi haƙuri, tun da Allah ya dawo da su gida lafiya""" """Ai yaron ne, wasu lokutan yadda ka san rainon garke, gaba ɗaya rayuwar sa, babu lissafi""" "Ɗan mama ya ce ""Ayi haƙuri""" """Kai ni fa ban ma yarda kai kaɗai, ka iya kawo Viper gida ba, Allah ya sa ba wani haukan kayi, ka" "kawo mana wani ya ga in da muke ba""" """A'a oga liti, nikaɗai na kawo shi gidan nan""" """Ware maƙaryaci kawai""" *** """Abdul""" """Na'am daddy""" """Saura wata guda bikinka, babu wani alamar shirye-shirye da kake yi, kawai dai gaka nan, ta ƙarfi" "da yaji ka ke son salwantar mana da wannan damar""" """No daddy ba haka bane ba, ina shiri, amma yau ka ji news kuwa?""" """A'a wasu lokutan news ɗin nan, hawan jini yake saka mini, amma meyake faruwa?""" """Na haɗu da Viper fa"" miƙewa tsaye Indabo ya yi ya ce ""Wane Vipern?""" "Abdul ya ce ""Ya naga ka tashi tsaye? Viper dai naka, ya je ƙaramin branch ɗina, an kwantar da" "shi har ya kwana""" "Indabo ya ce ""Innalillahi wa Innalillahi raji'un, wai da me yaron nan yake taƙama har haka, yawo ma yake yi a cikin gari har da zuwa asibiti? Anya ba harinka yake yi yayi maka wani abun ba, ya" "sanya ya je?""" "Abdul ya girgiza kai ya ce ""Bana tunanin hakan, unexpected muka haɗu, naje da daddare ban gane" "shi ba, yana bacci, sai yau da safe muka haɗu, amma dan Allah Daddy, meya haɗaka da Viper har haka, yake farautarka kai ma kake farautarsa?""" "Indabo yayi wuƙi-wuƙi da ido ya ce ""Ya gaya maka wani abun ne?""" """A'a, amma ya ce yana nan zai yi fitar burtu, yana nan tafe gareka, dan Allah mai ka yi masa ne?""" "Indabo ya ce ""Babu komai, kawai dai ka san yan daba, ba alƙawari ne da su ba, babu wani abu da nayi masa"" yanayin yadda yake maganar, ya sanya Abdul gane akwai wani abu a ƙasa, amma ya" "ɓoye masa, Abdul ya jinjina kai ya sake cewa ""Daddy""" """Na'am Abdul""" """Bayan na auri 'yar gidan party chairman, idan na kawo wadda nake so, zaka aura mini ita?""" """Wacece kuma a ina take?""" """A'a kafin in gaya maka, zaka yarda na zauna da ita, kuma ba zaka yi mini faɗa ba?""" "Indabo ya ce ""To ai haryanzu ba ka yi mini bayani ba""" """Amm yarinyar da nayi raping tana raye""" """What! Tana raye? Tana ina?""" "Cikin sanyin jiki Abdul ya ce ""Dan Allah Daddy kayi haƙuri ɓoye makan da nayi, tsawon lokaci," "dan Allah ka yi haƙuri""" """Na ji, na ji, tana ina yanzu?""" "Abdul ya girgiza kai ya ce ""To ai daddy baka ce komai ba, dan Allah ka yi haƙuri, na san nayi kuskure, sai da na ce zan kasheta, na ga ashe kisan kai ba abu ne mai sauƙi ba, dan Allah ka yi haƙ" "uri """ "Indabo ya yi shiru sannan ya ce ""Na ji, amma yanzu tana ina? An yi sara a kan gaɓa, hankalin mutane ya dawo kan appeal ɗin da waccan shegiyar yarinyar zata yi, dan haka dole zata bayyana" "a gaban kotu, amma da baka kasheta ba tana ina?""" """Daddy, abun da kawai zan iya gaya maka kenan ban kasheta ba, saboda ina tsoron matsala ta taso" "daga baya, amma ba zan iya barin rahama taje gaban kotu ba""" """Me kake nufi?""" "Cikin damuwa ya ce ""Ban san me zai iya biyo bayan hakan ba, rahama tana tare da ni a wuri" "daban, tsawon wannan lokacin"" wani lafiyayyen mari Indabo ya ɗauke Abdul da shi, ya dafe kuncinsa ya ja da baya." """Abdul yasar, yaushe ka yi girman da zaka yankewa kanka hukunci ba tare da sanina ba? Yanzu duk dambarwar da ake yi yarinyar nan na tare da kai? Audio da yake yawo aka ce muryar babarta ne, da gaske kenan zuwa ka yi ka ɗauke ta, saboda mahaukaci ne kai, sai ka je da kanka, ba ma turawa ka yi a ɗaukko maka ita ba, lallai ta tabbata baka da hankali dabba ne kai, wallahi ba zaka" "lalata mini siyasa ba duk wannan wahalar da nayi ta tashi a banza ba""" """Daddy, dan Allah ka fahimce ni""." """Shut up my friend, ubanka zan fahimta ka je ka kawo mini yarinyar duk in da ka kaita, kafin na" "casaka wallahi ba zan bari ka tona mini asiri ba, saboda hauka da wautarka ba, fice ka bani wuri kan na tattaka ka""" "Abdul ya tsuke fuska sai hura hanci yake yi, ya fice, sam bai ji cewa ko indabo zai jajjaga shi, zai" "kai masa Ramma ba, ko ya yarda ta tsaya a gaban kotu ba, sai dai ayi duk wadda za ayi." *** "Bayan farfaɗowar Viper daga baccin da allura nan ta saka shi, ya din ga mamaki, wace irin allura ce haka, bai takura da kansa da dogon tunani ba, sai dai yadda ya din ga jin ina ma, ya yi wa Abdul mummunar illa, kan ya baro asibitin, sai kuma wata zuciyar ta tuna masa, ba shi ne yayi" "masa laifi ba. Wata zuciyar kuma ta ce kai ma ba matarka ce tayi musu laifi ba, suka kasheta." "Ya tashi ciwon cikin da sauƙi, ya yi alwala ya rama sallolin sa, da daddare ya zauna yana jiran kiran wayar Nabila da daddare, dan ya san ba zata iya zuciya ba, sai ta kira shi ta ji ya jikinsa, amma shiru ba ta kira ba, har cikin dare idan ya juya, sai ya duba wayarsa ko ta kira bai sani ba," "amma babu kiranta, shi ma kuma ya kasa kiranta." "Abba kuwa godiya ya din ga yi wa Allah, da likitoci suka tabattar masa da ba wani abun tashin hankali ne ya samu Nabila ba, ta bugu ne a ka, kuma babu internal injury, sai hannunta da ta samu" gocewar ƙashi shi kawai za a gyara. "Mama ta hau masifa, ta ce ""Ba dai ita yar gata ba, an ɗauki mota an bata ba, Allah kaɗai ya san tu" "ƙin gangancin da take yi, ko dan ma tayi burga a titi, gashi ta tayar da mutane tsaye""" "Abba ya ce ""bata tayar da kowa tsaye ba, babu wanda na yi wa dole ya zo ya zauna mini da ita, a da ma baku yi ba sai yanzu? Kuma tuƙin da take yi, ai masaniyar doka ce ita ma, ba wani tuƙi da take yi na ganganci, jarabta ce kawai Allah ya kawo, kuma ya taƙaita, Magajiya zata yi mini jinyarta, zuwa a sallameta, ban ce dole ayi mini ba"" mama ta ja bakinta tayi shiru, jin abun da ya" ce. "Ya cigaba da kallon Nabila, cikin tsananin tausayawa, kwanan nan abubuwa sai samunta suke yi," daga wannan sai wannan. *** "Nasir ne zaune a gaban Indabo, fuska babu walwala Indabo ya ce ""Naga alamar aikin nan baka ɗ" "auke shi da muhimmanci ba, idan har ba zaka iya ba, zan saka a canza mini kai, nayi abun da nake ganin shi ya dace""." """Ina mai baka haƙuri, amma komai ya kusa zuwa ƙarshe""" """Idan ma baka kawo shi ba, ni zan kawo""." *** "Hafsa ce zaune a gaban baba ta ce ""Baba""" "Ya ce ""Na'am ƴar baba""" """Baba na san ai kai ba zaka ƙaryata ni ba ko?""" """Eh mana yaya zan yi na ƙaryata ki ma?""" "Hafsa ta gyara zamanta ta ce ""Ai dai ka san na warke yanzu, bana yawo, ba na shan komai, kuma" "na warke ai dai ko?""" "Ya ce ""Alhamdilillah kam, duk na sani hafsat""" """To yadda naga jauhar yau Allah ya nuna mini annabi haka, ta saka niƙab, da irin tafiyarta, da irin" "idonta, amma sai da na ganeta, na so na bi ta, yaya saifu ya kira ni, na nemeta na rasa""" "Baba ya ajiye cokalin sa, ya ce ""Anya kuwa warkewar nan hafsa? Yaya za ayi ki ga wanda ya riga" "ya mutu, kuma ta cikin niƙab ɗin ki ka iya gane ita ce?""" """Haba Baba, ka san dai yadda nake da jauhar, amma ko ina ga fatalwarta ce, amma dai da ko da ta zo mini a fatalwa, sai ta tsaya mu gaisa, bai kamata ta nuna kamar ba ta sanni ba, ina ga haryanzu haushina take ji, saboda na auri Alhaji mu'azzam yakamata ai ta yafe mini, ba ta ga irin wahalar da na sha ba, ai ko gaisawa sai ta tsaya mu yi. Ka ce na din ga yi mata addu'a, ina yi mata fa, amma duk ba ta ga wannan ba, ta share ni, ban san ya aka yi waliyiyyarka ta koyi wannan halin ba baba""" tayi maganar tana kuka iya ƙarfin ta. "Ya share hawayen da yake shirin gangaro masa, ya ce ""Bata kyauta miki ba, zan yi mata faɗa," "amma ina ga zamu koma Asibiti ganin likita""." "Hafsa ta ce ""Baba da hankalina fa, ba hauka nake yi ba, ina sane da duk abun da nake yi fa"" Mama" "ce ta shigo ɗakin ta ce ""Ke mahaukaciya, tashi ki fita ki bashi wuri, ya gama cin abinci dan Allah," "kin saka shi a gaba da sakarci""" "Hafsa ta ce ""Ni ba mahaukaciya ba ce ba, cutar damuwa nayi ba hauka ba""" "Baba ya ce ""Na sha gargaɗinki a kan kiranta da mahaukaciyar nan, wannan salon ki sake tunzurata" "ne ai""" """A'a dama ai a tunzuren take"" Hafsa ta tashi rai a ɓace, ta fita tsakar gida tana kiran Anty." """Hafsa wane irin kira ne wannan? Menene?""" """Kin ga maman su surayya tana ce mini mahaukaciya ko? Ni fa ba mahaukaciya ba ce ba""" "A fusace Anty ta nufi ɗakin Baba ta ce ""Wallahi kar ki sake kiran ya ta da mahaukaciya, idan ba" "haka ba duk abun da nayi miki ke ki ka saya""" """Mecece idan ba mahaukaciya ba, ba dai auren cin amana ba, da son abun duniya ba, ta haɗu da babarta a makirci a matsayin kishiya ai, ga hauka ga ba auren, sai an yi magana ace depression ne," "yarinya ta zama yar ƙwaya ta haukace""" """Eh bakomai, tun da har ta yi auren ai, ta shiga ta fito, da babbar budurwa ai gara ƙaramar bazawara, da kike maganar zama yar ƙwaya, naki ɗan uban menene ba ya sha? Ko kina tunanin" "bamu san komai ba""" "Hafsa ta koma gefe tana kuka, saboda ta tsani taji an kirata da mahaukaciya, kuma haryanzu idan ta tuna jauhar, da cin amanar da aka yi mata sai ta ƙara shiga damuwa, tayi ta kuka, ta san hakkin" jauhar ne ya sanya ta tsinci kanta a wannan mawuyacin halin da take ciki. "Baba yana jin su, ya fito a zuciyarsa yana Addu'ar, Allah ya sa jauhar da mahaifiyarta suna tare a" aljanna. Ya fice ya bar musu gidan. "Walid yana ta lallaɓa Viper, ya ci abinci ya sha magani, gaba ɗaya jin sa yake yi wani iri babu daɗ" "i, ya karɓi kofin shayi yana sha a hankali." "Ɗan mama ya kunna radion wayarsa, liti ya hau mitar ya cika musu kunne, ya ce ""Dan Allah oga" "liti kayi haƙuri, labarin wasanni zan ji""" """Ai sai ka yi""" "Tashar su Sumayya ya kai, a dai-dai lokacin da murtala yake sanar da hatsarin da Nabila ta samu a" "jiya, bayan kammala program da suka yi ta tafi, suna barar a sakata a cikin addu'a." "Buredin da viper ya haɗiya ne, ya tsaya masa a maƙogwaro, tamkar ya haɗiyi dutse." "Liti ya fizge wayar hannun ɗan mama ya ce ""Ban gane hatsari ba, ji ya ma fa taje Asibiti duba" "Viper, har yaushe ta yi hatsari kuma?""" "Walid ya ce ""Babu kusa babu nesa ga Allah, amma dai dole mu san halin da take ciki""" "Liti ya ce ""Taɓ yarinyar nan tana shan azaba, dudu yaushe ta kusa mutuwa a gobara, yanzu kuma" "hatsari?""" "Viper ya din ga murza kofin hannunsa, gumi yana tsatstsafo masa, amma bai tofa uffan ba." "Ɗan mama ya tashi ya ce ""Bari nayi maza nayi wanka, na je unguwar su na jiyo, wane asibitin" "take? Ko kuma na je asibitin da ta kwanta lokacin da tayi gobara, yadda ake ciki dai zan kira ku""" """Saura kuma ka kira mu ka yi mana wannan gaɓancin naka, kayi mana wauta, ka tsaya ka nutsu," "kuma saura ka ce baka da caji a waya""" "Ɗan mama yayi murmushi ya ce ""Ni na isa, in sha Allah ba za ayi haka ba""" "Walid ya ce ""Viper ka ƙarasa ci, in sha Allah babu wani abu, tun da ba su ce ta mutu ba, an ce dai" "ta ji raunuka ne kawai"" shi dai bai ce komai ba, ya ajiye kofin shayin." *** "Yanayin yadda Abdul ya shigo, sai da ramma ta ɗan tsorata, maye yake yi sosai." "Ta tashi ta nufi in da yake, ta ce ""Abdul giya ko? Baka ce mini ka daina shan giya ba?""" Yayi shiru yana ta numfarfashi. """Kai dai ba zaka taɓa gyara rayuwarka ba, idan ka yi kamar zaka nutsu, sai ka ƙara fanɗarewa," "kayi ta yi mini alƙawari baka cikawa""." "Ya kama hannunta ya rirriƙe, ya ɗaga jajayen idanunsa da ƙyar ya kalleta ya ce ""Rahama""" """Meye?""" """Dan Allah karki rabu da ni, ban san me zai iya faruwa a gaba ba, ina sonki, ina sonki Ai zaki" "yafe mini ko rahama"" yayi maganar cikin maye yana kallonta." "Ta kwantar da kansa a kan cinyarta, tana shafa sumarsa a hankali ta ce ""Kana so na amma ka je ka" "sha giya, kafi bawa soyayya muhimmanci a kan tsoron Allah ko?""" Ya girgiza kai alamar a'a. """Ga lokacin Sallah yayi, amma babu damar ka yi saboda kana maye, idan ka mutu a haka fa, zan" "yafe maka ne kawai, ranar da ka mayar da ni gaban mahaifiyata ka nemi afuwarta""" """Idan nayi hakan, zaki yafe mini, mu cigaba da zama tare?"" Tayi shiru ba ta ce komai ba." """Wallahi rahama, komai zai faru sai dai ya faru, idan aka yi ƙoƙarin raba ni da ke, zan ɗauke ki" "ne na yi gaba da ke, muje mu cigaba da rayuwarmu tare""" "Ta ce ""Mhmm Abdul yasar rigima, kayi shiru ka daina wannan surutun ka samu ta sake ka, kayi salla ba na son ka mutu kana rashin ji, wasu lokutan dai kayi ta abu kamar mutumin kirki, amma" "zunubanka da kake tafakawa ne, sun wuce misali""" """Rahama""" """Abdul yasar""" """Wallahi ba zan yadda a rabani da ke ba, ina sonki sosai""" """To likita, amma na ce kayi shiru ai""" "Ya ce ""To na yi"" da haka ya din ga sauke numfashi, yana bacci." **** "Ƙarfe biyu da rabi na dare, Viper yana cikin asibitin da Nabila take, sawu duk ya ɗauke, yan dubiya babu kowa, daga majinyata, sai marasa lafiya da ma'aikatan da za su kwana." "Ya jinjina ƙofar ɗakin da Nabila take, ya tura a hankali, bai ji an yi magana ba, ya sake turawa ya ga duhu, an kashe fitilar ɗakin, ya shiga ya rufe ƙofar, ya kunna fitilar wayarsa ya haska, baba magajiya na ƙasa kan carfet tana bacci." "Ya haske Nabila tana kan gado, ita ma baccin take yi, ana ƙara mata jini." "Ya taka a hankali, ya je gaban gadonta ya durƙusa, an naɗe mata hannu ɗaya da bandeji wanda ta" samu gocewar ƙashin. "Hular kanta ta zame, tun daga farkon goshinta, a cike yake da gashi mai santsi, kasancewar ba" "gwanar yin kitso bace, gashin nata a tsefe yake." "Ya kai hannunsa goshinta, in da aka rufe da plasta, da alama rauni ne a wurin, ya dawo ya riƙe" "hannunta ya ce ""Get well soon, Allah ya baki lafiya""" """Viper"" ta furta a hankali kamar mai raɗa." """Angry bird""" """Ya jikinka?""" "Ya ce ""Na ji sauƙi""" """Yanzu ma na san ba zaka kira ni a waya, ka yi mini sannu ba, ka tsane ni""" "Ya girgiza kai ya ce ""Ban tsane ki ba Abla, ina so ki rayu ne, in cigaba da ganin fuskar jauhar a" "cikin taki""" """Viper""" """Mmm""" """Zan cika maka alƙawarin ka in sha Allah, duk wuya duk rintsi, zan tsaya maka sai ka yi 'yanci," "duk girman barazanar da zasu yi mini, zan tabattar da an yi maka adalci da kai da matarka""" """Allah ya baki iko""" "Ta sake cewa ""Viper""" """Mmm Abla""" """Dan Allah kar ka tafi daga mafarkina yanzu, na san idan na tashi, ba zan iya zuwa asibiti na" "dubaka ba""" "Yayi shiru bai kuma ce mata komai ba, ta ƙara riƙe hannunsa, da yafi nata girma sosai." "Jikinta ne ya ƙara saki, ta cigaba da bacci, tana yi tana surutai, a hankali har ta yi shiru. Ya sake haskata da fitilar sa, irin innocent face ɗin jauhar ta bayyana a fuskar Nabila. A hankali ya zare hannunsa daga nata, ya yinƙura ya tashi ya fita daga ɗakin." "Washegari da safe, sai tunanin mafarkin da tayi jiya take yi, tana tunanin gaske ne, ko kuma kawai" mafarki ne?. "Da safe ana ta zuwa dubata, wajen ƙarfe sha ɗaya Nasir ya zo, lokacin babu kowa kasancewar" "ranar aiki ce, sai baba magajiya. Suka gaisa, ya aiki baba magajiya ya rage saura daga shi sai Nabila a ɗakin." "Ya zauna daf da ita a kan gadon, yana kallonta ya ce ""Sannu ya jikin?""" "Ta amsa da ""Jiki Alhamdilillah, da sauƙi, zuwa gobe in Allah ya kaimu nake so na tafi ma, i have a" "lot to do""" "Ya ce ""Well, tambayarki zan yi, kuma bana buƙatar ki yi mini ƙarya, saboda zargina ya tabatta" "gaskiya ne a kanki""" """Wane zargin?""" """Nabila kin san in da Viper yake, kina haɗuwa da shi!""" Ta kalleshi ta ƙura masa ido amma bata yi magana ba. """Ina magana kina kallona, na samu rahoton an ganshi a A.I hospital, naje bamu sameshi ba, amma" "naga signing ɗin ki, kin je asibitin me ki ka je yi?""" """Ni ganin likita naje, ka daina zargina tun da baka da wata hujja, mai asibitin aka tura ni wurinsa" "follow up, saboda lokacin da aka sallame ni, bai zo ba""" """Ƙarya ki ke yi Nabila""" """Ni ba ƙarya nake yi ba, ka fara samo tabattaciyar hujja, kafin ka ƙaryata ni""" "Ya jinjina kai ya ce ""Zamu gani ai, bayan duk wannan abubuwan hujja ki ke so na kawo miki? Shikenan zamu gani, amma ki sani aikinki ba zai baki kariya ba, muddin aka kama ki da laifi," "sunanki yar ta'adda kema, mai ɓoye mai laifi""" """Abun kunya ne ga hukumar yan sanda ace sun gagara kama mutum ɗaya, da yake iya yawonsa a cikin gari, sai ma a din ga bibiyar wanda bai ji ba, bai gani ba, ana yi masa baranaza"" tsananin" "fusatar da yayi, ya sanya kawai ya tashi ya bar ta a ɗakin." "Ta dafe ƙirjinta, saboda yadda yake tsananin bugawa, ta yanke a ranta dole tayi gaggawar fara" "shari'ar Viper, kafin ta kammala ta ramma." "Ya fita babu jimawa, baba magajiya ta dawo, ta karɓi aron wayarta, ta shiga banɗaki, ta kira wayar" "Walid, Allah ya taimaketa ya ɗaga." "Ya ce ""Barrister ashe tsausayi ne ya faru haka, ya jiki?""" """Jiki da sauƙi, meyake faruwa ne? Yayana ya ce mini ya samu labarin Viper ya je asibiti, ina yake" "ina fatan babu wata matsala?""" """Eh, Yana nan cikin ƙoshin lafiya mun koma gida ma, haɗuwa yayi da ɗan Indabo a matsayin" "likitan da ya duba shi, shi ne ya sanarwa security""" "Ta ce ""Haba dai? Likitan da ya duba shi kuma? Garin yaya dole mu ƙara taka tsantsan amma ba" "abun da ya faru?""" "Walid ya ce ""Babu abun da ya faru, mun bar Asibitin ma, muna gida""" """Dole na haɗu da shi, nan kusa Allah ya ƙara afuwa"" ta katse wayar ƙirjinta na cigaba da" bugawa. *** "Indabo yana ta sanya ran ya ga ta ina Abdul zai ɓullo, ya kasa zaune ya kasa tsaye, saboda matsalolin da suke kunno kai, ya rasa wanne yakamata ma ya fara ƙoƙarin kawarwa." "Kwanaki biyu kenan, ko ya nemi Abdul a waya, baya samunsa. Kuma bai sake zuwa gida ba," hakan ya ƙona wa Indabo rai fiye da kima. "Viper bai sake neman Nabila ba, ko a waya, dama bata saka rai ba, dan ta san bata gabansa, idan ta tashi, Walid take kira ta tambaye shi ya jikin Viper, tana ta neman hanyar da zata bi, ta samu ta ganshi, dan sosai Nasir yake sanya mata ido yanzu, ya hanata sakat duk motsinta a kan idonsa, kasancewar motarta tayi damage, an kaita garrage wurin gyara, hatta wurin aiki shi yake kaita, da farko ya so ya Abba ya hanata fitar ma, amma ta din ga kuka, taba nuna wa Abba cewa akwai" shari'oin da suke buƙatar ta yi attending. "Bayan ya ajiyeta a wurin aiki aƙalla yayi mintuna talatin a tsaye, ko da zata fito, sai da ya samu ɗ" "aya daga cikin security na wurin, ya lambar wayarsa, ya ce masa idan ya ga fitar Nabila ya kira shi ya gaya masa, ya kawo alheri yayi masa sannan ya tafi." "Nabila kuwa a office ta iske barrister Habib, ya shirya tsaf zai fita, ta shiga da sallama." "Ya amsa mata ya ce ""Sannu Nabila, ya hannun?""" """Hannu Alhamdilillah, fita zaka yi ne?""" "Ya ce ""Eh, zan je shari'a ne""" "Ta ce ""Mu fita tare, magana nake son mu yi da kai"" ya ce ""To shikenan babu laifi"" suka fita suka" shiga motarsa suka fice. "Kamar mai aljanu, suna tafe a hanya, ta ce ""Ya ajiyeta, tayi mantuwa, office zata koma, ya ce zai" "kaita ta ce masa a'a, ta fice ta hau napep." "Viper ya buɗe ƙofar gidan zai fita, ya ganta a tsaye tana shirin shiga, ta saka hannu ta ɗage niƙ" "abinta, suka yi ido huɗu ya ɗan tsura mata ido, ta faɗa sosai." "Ta ce ""Ya jiki, ka warware?""" """Mmm""" """Zuwa nayi mu ƙarasa tattaunawa, ka fara yi mini bayanin shaidun da kake da su a hannu, zan" "fara gudanar da shari'ar ka, zan cigaba da yi tare da ta ramma, kafin su halaka ni, accident ɗin nan, da nayi, takani aka so yi da mota, garin na kauce musu, nayi accident"" ya tsura mata ido, tare da" haɗiye wani abu a wuyansa. "(Alhamdilillah ala kulli halin, ina godiya sosai da sosai addu'oin da ku ka yi mini, bisa ga rashin" "lafiya da nayi, Ubangiji Allah ya bar zumunci na gode ƙwarai)" Ayshercool 08081012143 ₦500 ne via 0009450228 Aisha Adam jaiz bank sai shaidar biya ta 08081012143 Wanda za su jira document 1K ne. 90009343 'Yan Nijar ku turo katin airtel na 300fcfa Arewabooks ayshercool7724 "Cigaba yayi da kallonta, ita kuma ta kasa sake ɗaga idonta ta kalleshi." Yanayinta ya nuna sosai akwai damuwa a tare da ita. """Kin fasa cewar ba zaki tsaya mini ɗin ba kenan?""" "Ta jinjina masa kai ta ce ""Eh, idan ma na fasa, zuciyata ba zata nutsu ba, alƙawari ne da nayi, yakamata na cika, ko ba dan kowa ba, dan wadda aka kashe ba da hakkinta ba"" tayi maganar ba" tare da ta kalleshi ba. "Ya jinjina kai, a hankali ya furta ""Ina zuwa""" "Ya koma cikin gidan, tana tsaye ta bi ƙofar da kallo, ya fito ɗauke da jaka a hannunsa, ya ce ""Muje"" ba tare da ta san in da zasu ba, ta bishi. Sai da suka yi nesa kaɗan da gidan, sannan ya ja ya" tsaya ita ma ta tsaya. "Ya samu wuri ya zauna, yayi mata nuni, ita ma ta zauna, ta sauke tata jakar daga bayanta, hannunta ɗaya an naɗa mata bandeji, in da ta samu gocewar ƙashin, sai dai hannun rigarta ya rufe" wurin. "Ta ciro system ɗin ta, ta ajiye ta ajiye wayarta." "Ya zuba mata ido, bai yi magana ba, sai da ta ɗan ɗago ta ce ""Wace shaidar da wace shaidar ce da" "kai, and dan Allah kar ka ɓoye mini komai, saboda kar sai mun je kotu, wani abu da ban san da shi ba, ya taso daga baya""." """Me ki ke son sani?""" """Shaidunka, da ka ce kana da su""" "Ya ɗan lumshe idanunsa, sannan ya buɗe ya ce ""Madaki, duk na yi masa illa, sai kuma babban" "yaronsa lakwari, duk suna wurina""" """Garkuwa kayi da su kenan?""" """Kusan hakan""" """Laifi ne fa ka aikata yin hakan""" "Ya tari numfashinta ya ce ""In sake su kenan?""" "Ta ɗaga idonta, amma taga kallonta yake yi." "Jikinta ya ƙara sanyi, maimakon ta mayar da hankali a kan abun da take yi, sai hannunta ma ya" "hau rawa, wata irin ƙaunarsa ta din ga fizgarta, ji tayi tamkar ta ɗurawa kanta zagi." "Ya ɗan matsa kusa da ita, yana kallon fuskar system ɗin ta. Ta takure jikinta, ƙamshin turaren sa" da warin sigari suka cika mata hanci. "Murya na rawa ta ce ""Viper""" """Mmm""" """Ka sha sigari ko?"" Yayi shiru bai bata amsa ba." """Kar ka bari lafiyarka ta taɓu bamu gama shari'ar nan ba, kuma kaga ya fara taɓa maka internal" "organs, an ce hantarka ta kumbura""" "Yayi shiru bai yi magana ba, sai kallonta kawai da yake yi." """Akwai abubuwa da yakamata ka gaya mini, amma kamar kana ɓoye mini, yakamata idan kana ɓ" "oye mini ka gaya mini, kar wani abu ya bamu matsala daga baya""" "Har ta fitar da ran zai yi magana ya ce ""Kamar me?""" """Suwaye suke goge laifukan ka idan ka yi? Ranar da muka je gidanka, ya aka yi ka gane jami'an tsaro a fararen kaya, har muka tsere musu? Wannan rigar da ka yaga a asibiti ta mecece? Kuma me" "kake yi da wayata da kake connecting?""" "Viper ya yi gyaran murya ya ce ""Wasu tambayoyin ba su da alaƙa da abun da yake gabanmu, amma na gane jami'in tsaro a farin kaya, saboda ni tsohon mai laifi ne, ba lokacin na fara aikata laifi ba, dan haka duk wani nuƙu-nuƙun jami'in tsaro sai na gano shi. Rigar da ki ke magana a kai, bata da alaƙa da abun da zaki yi a court. Wayarki kuma ina connecting ina duba wasu location, da" "tura saƙonni. Mai goge laifukana kuma ban sani ba. Sai kuma me?""" "Nabila ta ce ""To shikenan, nan da kwanaki biyu zaka ji ni in Sha Allah, zan har haɗa abun da nake" "buƙata, saboda yayana ya sakani a gaba da yawa""" """Good luck"" ya faɗa a takaice, tamkar ta kurma ihu, ko sannu ya jiki bai iya yi mata ba, dan" "takaici ta tattare system ɗin ta, ta yinƙura ta tashi ta ce ""Sai anjima"" ya jinjina kai." "Jiki a sanyaye take takawa, kamar mara karsashi, ya waiwaya yana kallonta, yadda take ɗaga hannunta tana saukewa, ya tabbatar masa da kuka take yi. Sai da yaji zuciyarsa ta motsa, shi gaba" ɗaya tausayinta ma yake ji. "Tana tafe a titi, barrister Habib ya kirata, ta ɗaga ya ce ""Nabila kina ina ne?""" """Meyafaru?""" """Wai yayanki yaje ɗaukar ki, an ce masa mun fita, ya kira ni, wai muna ina?""" "Guntun tsaki ta ja, ta ce ""Rabu da shi dan Allah""" """A'a kamar yaya na rabu da shi? Kina ina ne, ni ya addabe ni""" """Wani wuri naje, ina kan hanyata ta komawa gida, ina son ma ganinka urgent, amma sai Allah ya" "kaimu gobe""" "Ya ce ""To Allah ya kaimu""" "Ta amsa da ""Amin""" *** "Naja'atu Bunkure ta dubi Indabo ta ce ""A haka ana wannan yanayin zaka koma Abuja?""" """To idan ban koma ba yaya zan yi, matsaloli sai kuma cakuɗewa suke yi""" """Dole fa a nemo Abdul, kuma ta wani fannin rashin kashe yarinyar nan yayi amfani, amma kuma ya tafka shirme da hauka, dan me zai ɗauketa ya je ya ɓoye, kuma saboda wulaƙanci yaje har" "gidansu da kansa, dole fa a nemo Abdul ya fito da yarinyar nan""" """Kin san ya kashe wayoyinsa gaba ɗaya, kin san a haukan yaron nan ce mini yayi, wai idan ya" "auri yar party chairman bayan aure zan bari ya auri wadda yake so, kawai ya yi mini wannan" "maganar, ban sani ba ita yake nufi zai aura ko wata oho""" """Taɓɗijan, lallai Abdul wannan karon ya ɗebo ta da zafin gaske, wallahi sai an yi taka tsantsan" "kafin a warware wannan shirmen da yayi""" "Indabo ya yakice gumi ya ce ""Na rasa makama gaba ɗaya, ga rayuwarsa na cikin hatsari, ya haɗu" "da mai zamani, wai yaron da ake ta nema ido rufe, shi ne yake yawon sa har da zuwa asibiti, tsoro ma nake ji, kar Vipern yayi masa wani abun""" "Naja ta ce ""Yanzu neman Abdul, shi ne abu mafi a'ala, ina tsoron yayi wani abun da zai tona mana" "asiri""" "Yayi ajiyar zuciya ya ce ""Ni ɗan da na haifa, nake ta fafutuka a kan rayuwarsa yake neman ya" "kware mini baya, saboda mace, aishikenan da ina da wata hanyar da zan fito da jafar, da ƙyale shi zan yi, idan abun da yake bi a jikin nata ya gundure shi, sai ya dawo hayyacinsa""" "Bunkure ta kwashe da dariya ta ce ""Barewa bata gudu..." "A fusace ya kalleta, ta haɗiye dariyar, tana mazewa." *** """Nabila ina ki ka je daga wurin aiki? An ce kun fita da barrister Habib, na kira shi ya ce ba kwa" tare. """Eh, uzuri ne ya kamani, na je prison ganin wanda nake karewa ne, ko yanzun ma kana zargin" "wurin Viper na je?"" Kawai ya gyaɗa kai ya fita." "Ta kwanta ruf da ciki, ta buɗe wurin da ta ɓoye videon da ta yi wa Viper, ta din ga kallon hotunan" "da video, tana ƙara jin yadda ƙaunarsa take mamaye zuciyarta." "Ta yi shiru, bata taɓa zaton zata tsinci kanta a irin wannan yanayin ba, duk yadda take kallon kanta," a matsayin mai class taga namijin da ya ƙure wa ajinta gudu. "Ta dinga shafa fuskarsa, ta kan screen ɗin wayarta, ta lumshe ido tana tuno muryar sa, da a zahiri" "mai ban tsoro ce, amma a baɗini daɗin sauraro take yi mata, da sanya mata nutsuwa." "Ƙarfe takwas da rabi, tana ofishinta, tana jiran barrister Habib." "Yana isowa, ta tashi ta tafi, ya ce ""Yar ƙwalisa, yaya aka yi ne? Ya hannu""" "Ta zauna ta ce ""Hannu Alhamdilillah, yaya Habib""" """Na'am ƙanwa Nabila""" """Kamar yadda baka gajiyawa da ni, na sake dawowa neman alfarma a wannan karon""" "Habib ya ce ""To Nabila, me ni ke so?""" """Wataƙila wannan ta zama alfarma ta ƙarshe zan neman a wurinka, duk da akwai haɗarin gaske," "amma yanzu burikana biyu ne, bayan ganin bayan Bunkure foundation, sai wanke Viper daga zargin da ake yi masa""" "Da sauri ya ce ""Kamar yaya?""" """Kamar yadda nake gaya maka, bana nufin na sanyaka a matsala, kamar yadda ka taimakeni" "kwanaki a kansa, yanzu ma ina neman taimakonka, dan Allah""" """Nabila, wannan wasa da rai ne fa, ke ya aka yi ki ka san ba shi da laifi? Tayaya zakinkare" "mutumin da hukuma take nema ruwa a jallo?""" "Nabila ta numfasa ta ce ""Zaka ga ta yadda zan yi, ni dai haɗin kanka nake buƙata da taimakonka""" "Ya girgiza kai ya ce ""Nabila matana biyu fa da yara uku, haka kurum ki saka su zama zawarawa da" "marayu, na gaya miki case ɗin sa yayi involving manya haka kurum ki ja mana fitina muna zaman lafiya""" "Cikin marairaice wa ta ce ""Dan Allah yaya habib, ba zan bari sunanka ya fito ba, dan Allah copyn" "file ɗin sa nake so, da aka yi masa shari'a shikaɗai nake buƙata""" "Ya ce ""Taɓɗijan, ke kin san uban process ɗin da na bi, aka baki ki ka gani wancan lokacin, balle" "yanzu kicw copy ki ke so""" """Dan Allah ka taimake ni barrister Habib""" "Yayi shiru sannan ya ce ""Gaskiya sai kin bani lokaci, dan wanan aiki ne da yake buƙatar ɓ" "oyayyiyar gwagwarmayar """ "Cikin farinciki ta ce ""Zaka nemo mini ɗin?" """Zan jarraba ne na gani idan zai yiwu, ba alƙawari nayi miki ba""" "Ta miƙe cikin farinciki ta ce ""Na gode sosai, Allah ya saka da alkhairi ya raya zuriya""" Ya amsa mata da Amin. *** "Ramma tana ta gogewa Abdul labcourt ɗin sa, ya daɗe a tsaye yana kallonta, wani irin" matsanancin tausayinta ne ya mamaye zuciyarsa. "Ya ƙarasa ya zauna ya ce ""Rahama"" ta ɗago ta kalleshi." """Ina da masu gugu fa, kaiwa nake yi ayi mini, ki ke wahalar da kanki""" """Ka ce zaka yi tiyata, shiyasa nake goge maka""" "Yayi murmushi ya ce ""Ai ba da labcourt muke shiga tiyata ba, kayan tiyata daban suke""" "Ta ce ""Ok, duk da haka ka saka wani lokacin""" "Ya jinjina kai ya ce ""Rahama menene babban burinki a rayuwa ne?""" "Ta sunkuyar da kai ta ce ""Ka mayar da ni wurin mamana""" """Na san da wannan, zan mayar da ke, burinki na rayuwa?""" "Ta ɗago idanu ta kalle shi ta ce ""Babu""" "Ya ce ""Kamar yaya? Kowane ɗan Adam yana da buri da yake son cimma a rayuwarsa""" "Rahama ta kashe socket, ta kalleshi ta ce ""Wace rayuwar? Rayuwar da ka gama kassarawa wane buri ne yayi mini saura? Ka mayar da ni wurin mahaifiyata na ƙarasa rayuwata shikaɗai ne roƙ ona a gareka, amma ba ni da wani sauran buri da nake da shi, gaba ɗaya rayuwar ta fita daga raina," "babu abun da yake burgeni yake bani sha'awa""." "Abdul ya koma kusa da ita ya zauna, ya ɗan tsura mata ido, ita kuma ta kawar da kanta gefe ɗ" aya. """Dukkanin mai rai baya fitar da rai, da cimma burikansa na rayuwa, na san ni ne musababbin rushewar naki, amma haryanzu ina dana sanin abun da na aikata, amma zan cika miki burinki Rahama, zaki koma makaranta kiyi karatu mai zurfi in dai muna tare in sha Allah, makaranta mai kyau zan mayar da ke, na gyara makarantun garinku, kuma an karɓi ƙudurin gyaran hanyarku, aiki yayi nisa na yi muku boreholes kamar yadda nayi miki alƙawari, idan aka kammala zan nuna" "miki""" "Maimakon ta yi magana, kawai sai ta fashe da kuka." "Cikin damuwa ya ce ""Rahama menene kuma?""" """Ni duk bana son wannan abubuwan, kawai na koma gidanmu na ƙarasa rayuwata, babu wani abu" "da zan zama a rayuwa da zai katange ni, daga tsangwamar da zan fuskanta a cikin al'umma," "wannan ɗabi'a ce ta hausawa""" """Ina tabattar miki da idan muna tare, babu wanda zai tsangwame ki, wasu shirye shirye nake yi ne, da sun tabatta in sha Allah zamu je ki ga mama, amma babu maganar rabuwa tsakaninmu, ba sai" "na bar ki a tsakanin hausawan ba ma zau yi miki, ki daina damuwa Please bana so""" "Wayarsa ce ta fara vibrating, ya ɗaga ya ce ""Yeah Salim ya ake ciki ne?""" """Wai ina ka shiga ne? Mummy ta kira saifu a waya, wai an nemeka a waya an rasa, ya ce mini shi" "ma baya samunka a waya, ni kaina kwanana biyu kenan ina nemanka yanzun ma ban zaci zan sameka ba, nace bari na jarraba kiran wannan layin naka""" "Abdul ya numfasa ya ce ""Akwai damuwa ne Salim, mu haɗu a gidana na by pass""" """To shikenan, ka san nina har ta gaji da nemanka ita ma, har clubs ka daina zuwa, gidanka da take" "samunka ma yanzu baka zama, kuma ta daina samun wayarka, na ce mata kayi busy ne da shirye shiryen siyasarka""" "Abdul ya ce ""Manta da ita, zan je asibiti zan yi tiyata da daddare, idan na kammala ko kafin na tafi," "sai mu yi magana sai mu haɗu""" """To shikenan, sai na ji ka""" *** "Walid ne ya ƙarasa in da Viper yake a zaune a kan dutsen nan, yayi shiru yana nazari." "Ya zauna a kusa da shi ya ce ""Sannu da hutawa""" """Yauwwa sannu da zuwa""" """Yauwwa, tunanin me ka ke yi ne?""" "Viper bai ba shi amsa ba ya ce ""Meye labari?""" """Labari, yan unguwar su madaki, sun addaba wa yan unguwarmu, naji ɗan mama ya ce zai shiga unguwar, sai kuma na je maɓoyar madaki, na tarar baya nan, ko dai ya tafi wani wurin bamu sani" "ba?""" "Viper ya ɗan kaɗa kai ya ce ""Kar ka damu na san in da yake""" "Cikin mamaki ya ce ""Ka san in da yake kamar yaya?""" """Kamar yadda na ce"" ya faɗa a taƙaice." "Shiru ya wanzu na wani ɗan lokaci, Viper ya ce ""Jibi yarinyar nan zata shiga kotu, ta kuma ce a kwankin nan zata fara shari'ata, i need to assist her, a haka ma rayuwarta na cikin hatsari, muddin" "ta shiga case ɗin nan matsaloli zasu ninku fiye da baya, akwai buƙatar na taimaka mata sosai""" "Walid ya ce ""Haka ne, Allah ya tabattar mana da alkhairi, ya bamu dukkanin nasara, ka yi yanci" "mai zamani, ka daina wannan zaman ɓuyan""" "Viper ya dafa kafaɗar Walid ya ce ""Mai laya""" """Na kiyayi mai zamani""" """Mu huta wannan zaman ɓuyan zaka ce, idan Allah ya bamu nasara, in ga kun tsaya da ƙ" "afafuwan ku, na aurar da kai, da wancan sarkin faɗan""" "Walid ya ce ""A'a, ka yi yanci, muga farincikinka da walwalarka sun dawo dai, mu dai mu cigaba" "da gurgura rayuwa""" "Viper ya girgiza kai ya ce ""Aure yana da daɗi mussaman idan ku ka yi dace kamar yadda na yi. Ni na taɓa yi na more shi, kuma yakamata ku yi, idan na bari ku ka ƙarar da rayuwarku a kan" "hidimata kawai ban yi wa kaina adalci ba muhsin""" "Walid ya ce ""Taɓ anya na taɓa jin ka kira ni da ainihin sunana kuwa?""" "Viper ya yi murmushi ya ce ""Ka tuna mini da watarana, da 'yar madara ta sakani a gaba, ta ce sai na gaya mata ainihin sunayenmu, na ce mata ni Muhammad Al'amin, kai Muhsin, liti Abdullahi. Ta rafka salati, ta ce kalli yadda duk kuka mayar da sunayenku wani iri, har ma ɗan gara yaya walid, duk da shi ma wataran mai laya kake ce masa, gaskiya ku canza hali, sunayenku masu daɗi, amma duk kun canzawa kanku suna. Na ce ;Sunan waye yafi daɗi, tayi murmushi ta ce na mijina, na ce yauwwa ke ma sunanki mai daɗi an saka miki wani iyayi daban. Muhsin ku yi aure akwai alfanu a cikin aure, haryanzu na kasa manta rayuwar cikin aure, na san abu ne da ba zai bar ƙwaƙ walwata ba. Ina son naga kun samu cigaba a rayuwar ku, ba zan yi alfahari da ku ƙarar da" "rayuwarku a kaina ba""" "Walid ya kalli Viper ya ce ""Al'amin, ko mai muka yi maka a rayuwa ka cancanta, ai duk ɗan halak" "baya manta alkhairi, idan kai ka manta ni ba zan manta ɗawainiyar da ka yi da ni da mahaifiyata ba, haka zalika mutuntawar da matarka tayi mana""" """Muhsin, mahaifiyar ka, mahaifiyata ce, ka daina saka wannan a lissafi""" "Walid ya ce ""Na daina, amma dai sai mun fara aurar da kai tukuna, farincikin ka da walwalarka su" "dawo, sannan mu san abun yi mu ma""" "Viper ya girgiza kai ya ce ""Bani da ra'ayin kuma yin aure a rayuwata, wancan ma tsautsayi da ƙ" "addara ne ya saka aka yi shi""" "Walid ya yi murmushi ya miƙe ya ce ""Wannan kuma, ƙaddarar tausayi da soyayya zai saka a ayi shi"" har Walid ya yi gaba, Viper ya miƙe da sauri ya ce ""Ina ba zai yiwu ba, jauhar ce kawai a" "zuciyata"" kawai walid ya ɗaga masa hannu ba tare da ya waiwaya ba ya yi gaba yana dariya." *** "Salim ya kalli Abdul da ya shigo a gajiye, ya zauna ya ajiye labcourt ɗin sa a gajiye." """Yaya ne mutumina, na ganka a wahale""" """Aiki na sha yau ɗin nan, na je asibiti ya kai huɗu, na duba wanda na yi wa tiyata, sannan na yi" "wa wasu aikin sai godiyar Allah""" "Salim ya yi murmushi ya ce ""Sannu, ko in ɗaukko maka abar ne, ina da ita a mota?""" "Abdul ya girgiza kai ya ce ""Rahama ta san warin giya, faɗa zamu yi da ita""" "Salim ya ce ""Wow, to ko abinci zamu je ka ci?""" "Nan ma ya girgiza kai ya ce ""Ina da special cook a gida, yarinyar nan dar ce"" yayi maganar yana" kashingiɗa. "Salim ya kwashe da dariya ya ce ""Allah mutumina, ta saduda kenan?""" Abdul ya yi murmushi. """Ina jinka, bani labari""" """Salim, kai ka san komai, tun da ka tafi fa babu labarin mahaifiyar yarinyar nan, gashi ta matsa mini na mayar da ita gida, ni ba mayar da itan ne ya dame ni ba, na fara yi wa daddy bayani ko zai fahimce ni, ya hau ni da faɗa da zagi, kuma wai lallai sai na kai masa ita, sai an kaita kotu ta bayar da shaida, ni fa na yanke shawarar zan ɗauke ta mu ƙara gaba, har takarar ma bana so. Wallahi Salim ban taɓa dana sanin aikata wani abu a rayuwata ba, irin yi wa rahama fyaɗe ba, kuma ban ta ɓa jin so da ƙaunar wani abu a raina ba, kamar yadda nake jin son ta, ya mamaye zuciyata ba, Salim wallahi ba zan iya rabuwa da rahama ba, ba wai ina sonta da jikinta ko wani abu ba, ita ɗin" "nake so""" "Salim ya ce ""Ƙarya ne malam, mun san komai fa""" "Abdul ya yi murmushi ya ce ""Ita ta sani ai, ba zan yi maka ƙarya ba""" "Salim ya ce ""Kar ka damu, na fahimta maganar ka ɗauketa kayi gaba bai taso ba fa, ka zauna ka" "yi wa daddy cikakken bayani""" """Salim na san waye mahaifina ciki da bai, muddin na fito da rahama, zai iya salwantar da rayuwarta, ita kanta mahaifiyarta ina tantama a kan bashi ne ya ɗauke ta ba, ni kuwa a kan" "rahama sai dai ayi duk wadda za ayi""" "Salim ya waro ido ya ce ""Da iyayen naka? Abdul yaushe ka koma haka ne? A cikinmu duk rashin" "nan da kai da Saif kun fi mu mutunta iyaye ma da jin maganar su mussaman kai, meyasa ka ke son canzawa saboda mace?""" """Kamar yadda take yawan faɗa, na riga na ɓata rayuwarta, dan haka ba zan bari a sake tagayyara rayuwarta ba, ina son rahama irin son da nake son na ƙarasa rayuwata da ita, idan Daddy ya" "cigaba da matsawa, ba zan yi wancan auren ba""" "Ya girgiza kai ya ce ""Ba za ayi haka ba, ka je ka fara maganar da mahaifiyar ka, ko zata" "fahimceka""" "Ya ce ""Taɓ ayi sha'ani kawai, zan je zanji kiran da yake yi mini amma in fito da rahama dai," "gaskiya ban ji zan iya ba""" """Amma fa Abdul mun tafka shirme a gaban uwar yarinyar nan, anya zata yafe maka kuwa? Ga" "tsiyar da ka je ka kuma yi daga baya""" "Abdul ya numfasa ya ce ""Sharrin giya ne, da gigin arziki da nake ji da shi, nake jin kamar zan iya" "taka na ƙasa da ni, ni komai zata yi, mini tayi mini amma ban da raba ni da yarinyar nan""." "Salim ya ce ""Lallai ka faɗa da yawa mutumina""" """Rahama, akwai haƙuri, duk da ina cin zagi a wurinta da tsinuwa, amma da ta ganni cikin rashin lafiya, ko damuwa hankalinta yake tashi, ita take dafa abincin da zan ci, yau har da yi mini guga. Nifa yarinyar da aka ce za a haɗa ni da ita, gaba ɗaya bata yi mini ba buɗaɗɗen ido ne da ita, gara" "a bar ni da rahaman dai, na san koma menene ni ne sila""" Salim ya jinjina kai. *** "Nabila ce a tsaye a gaban court, tana ƙoƙarin fara gabatarwa da mai shari'a appeal ɗin su, ta kalli" "barrister Habib, ya jinjina mata kai alamar bata ƙwarin gwiwa, ta tsaya ta gabatar da kanta cikin harshen turanci, tare da fara karantowa kotu koken su." "Na kotun ta yi duba da rubutaccen jawabin da suka gabatar, a kan hukuncin da kotun farko ta yi, bisa ga wasu kurakurai da suke ganin an tafka a wurin yin shari'ar, na rashin bayyanar wadda abun ya faru da ita a gaban kotu, da rashin gabatar da medical report ta hannun ɗan sandan da kuma" likitan da ya tabattar da yin laifin ba. "Hakazalika a hujjojin da suka gabatar a kotun farko, akwai sautin murya, na mahaifiyar ramma tana koken a kawo mata agaji, domin kuwa wanda ya yi mata fyaɗe ya dawo ya ɗauke ta, idan kuwa haka ne, wanda ake zargi ba shi ne ya aikata wannan laifin ba, sannan kuma wanda ake zargin ya amsa laifin ne, a sakamakon barazana da aka yi masa, da haka take roƙon kotun ta bibiyi" "shari'ar da kotun baya tayi, ta tabattar da adalci""" Ta miƙa file ɗin aka miƙa gaban mai shari'a. "Suna tafe a mota tare da barrister Habib ta ce ""Yaya, gaba ɗaya jikina a sanyaye yake, gani nake" "wannan karon ma, ba zan yi nasara ba""" """Bana son saurin karaya dan Allah, kin manta wadda ki ke ƙoƙarin tunkara ta fi wadda ki ke yi" "yanzu? Kuma yanzu hankalin mutane da yawa ya dawo kanki, ba common mutanen gari ba, har da ma'aikatan shari'a""" """Idan Allah ya sa na yi nasara, akwai gagarumin tonin silili fa"" tayi maganar tana murmushi." "Barrister Habib ya kalleta ya ce ""Na me fa?""" """Zaka gani kai dai, ya batun case ɗin Viper, samo mini copyn shari'ar da na ce?""" """Ai na gaya miki ba aiki ne mai sauƙi ba, ina nan ina ƙoƙartawa, yanzu idan aka san ina ƙoƙarin" "samo file ɗin ma, rayuwata na cikin hatsari""" "Ta jinjina kai ta ce ""Haka ne, Allah ya ba da sa'a""" *** """Inadabo, wallahi akwai matsala muddin Abdul bai kawo yarinyar nan ba, tun da ya ce maka tana wurin sa ya fito da ita mana""" """Naja duk wani ƙoƙari ina yi, bai taɓa bujirewa umarnina ba sai a wannan karon, yama daina" "zuwa in da nake gaba ɗaya, bana samun wayoyinsa""" """Ka san kuwa me nasararta a appeal ɗin nan yake nufi? Yarinyar nan fa ba zata zuba mana ido ba," "dole ka yi ƙoƙari fa a kai""" """Kar ki damu, zan ga alƙalin da kaina""" "Bunkure ta girgiza kai ta ce ""Ƙoƙarin ka ba a kan alƙali kawai zai tsaya ba, har da wannan" "yarinyar, dan ni na yi iya yi na""" "Inadabo ya katse kiran, ba tare da ya sake yin magana ba." **** "Babu tsammani, indabo ya shiga falon mai ɗakinsa, ya tarar da ita tana yi wa Abdul faɗa. Yayi" "turus, sannan cikin tsananin ƙuluwa ya ce ""Ai dama na sani, ke ki ke goya masa baya, yake rashin mutunci""" """A'a nima fa yanzu na ganshi, nake tambayarsa ba'asin ina ya shiga, kar ma ka ɗora mini wannan" "zargin""" """Wato Abdul ban isa da kai ba kenan ko? Nayi maka magana sai ka ɗauke ƙafarka gaba ɗaya" "daga gidan ka daina zuwa, ina yarinyar take?""" Abdul ya yi shiru ya ƙi magana. """Ka gaya mini in da take, tun ban tattaka ka ba, yau an yi appeal ɗin shari'ar yarinyar, kuma" "muddin aka wanke mutumin nan, babu lallai ka tsira ba tare da asirinka ya tonu ba""." "Abdul ya ce ""In dai hakan yana nufin na cigaba da rayuwa da ita, shikenan ni ba komai asirin nawa ya tonu, dan Allah Daddy ka yi haƙuri, wallahi ba zan iya fito da rahama gaban duniya ba, ban san iya abun da zaka yi mata ba, kuma bana fatan abun da zai ƙarasa zubar da mutuncinta," "dan kuwa fito da ita gaban kotu kamar cigaba da yayata abun da ya faru da ita ne""" "Tamkar shashasha indabo ya tsaya yana kallon Abdul, babu kunya babu tsoron Allah Abdul yake" gaya masa wannan maganganun. "Ya numfasa ya ce ""Babu laifi, ni na san matakin da yakamata na ɗauka""." *** "Nabila ta shiga office ɗin ta, ta zauna ta janyo drower zata ɗauki biro, ta ga file, ta ɗaukko file ɗ in ta buɗe, kawai taga copyn shari'ar Viper ne a ciki, sai da ta razana ta ja da baya, tana waige-waige." "A razane ta ɗauki waya, ta kira barrister Habib, ya ɗaga ya ce ""Hello Nabila""" """Barrister ka samo file ɗin nan ne?""" """A'a, ina ta ƙoƙari dai a kai, ki yi haƙuri""" """Barrister, file ɗin na gani a office ɗina""" "Ya ce ""Wane file ɗin?""" """Na shari'ar Viper""" """Iyee, waye ya baki?""" """Nima ban sani ba, a office ɗina na tarar kamar yadda aka ajiye mini na Bunkure""" """Kar ki gaya wa kowa, gani nan zuwa""" Ta ajiye wayar tana sake dudduba file ɗin. "Ji ta yi an buɗe ƙofar office ɗin ta razana da sauri tana ɓoye file ɗin, ya rufe ƙofar office ɗin," ya ƙaraso. "Ta ce ""Yau ma kai ne da kanka?""" "Ya ce ""Eh, ko in koma ne?""" """A'a, bisimillah zauna""" "Ya samu wuri ya zauna, kamar yadda a wancan karon, tayi masa hidima, haka ma a wannan karon, ta haɗa masa tea, ta bashi abincinta da ta zo da shi, ta bashi"" wannan karon babu gardama ya karɓa" ya ci. "Ta ciro file ɗin ta ajiye masa ta ce ""Yau da safe aka kawo mini shi, ban san kuma wanda ya kawo" "ba""" "Ya karɓa ya bubbuɗe, yana dubawa." """An fitar da sanarwar cigaba da nemanka jiya, wai yaranka sun je sun yi faɗan daba, jami'an tsaro" "na ta cigaba da yayata nemanka""" "Ya girgiza kai ya ce ""Ni ma na ji, sai dai ni bani da masaniyar hakan, na samu labarin faɗa" "tsakanin yan unguwarmu da yan unguwar su madaki, ban san ma me ake ciki ba""" """Zan je kotu, na nemi kotu ta hana kama ka, kafin na ɗauki mataki na gaba""" Viper ya jinjina kai yana kora shayin hannunsa. "Ya ce ""Bani system ɗin ki""" "Ta ɗaukko, ta bashi ya ciro tab ɗin sa, ya ɗan jima yana danne-danne, yayin da ita kuma take" satar kallonsa kamar yau ta fara ganinsa. "Kamar kar ya tafi ta daina ganinsa, wani irin shauƙi da farinciki ya din ga ratsa zuciyarta." """Ki shirya, zamu je ki ga shaidar da nake da shi, idan da abun da ki ke buƙatar sani""" "Ta ce ""To shikenan, ka sanya lokaci sai mu je, sai kuma mu yi ta addu'a""." "Ya ɗan daddana tab ɗin hannunsa ya ɗan yi shiru sannan ya ce ""Barka da wannan lokaci, kana magana da mai zamani ne." "Babu buƙatar yin doguwar magana, na san zuwa yanzu ka san labarin haɗuwata da ɗanka, zuwa yanzu na san duk wani motsinsa, duk in da yake zuwa na sani, amma ba wannan ba, akwai buƙatar ka bibiyi case ɗin ɗanka da ka ke musayar sa da ni, a lokacin da yake Nigeria yake aikata laifuka, ina da babban albishir gareka, Mexico na shirin miƙawa amurka shi, ya fuskanci shari'a, kuma ina mai sanar da kai kisan kai ne hukuncin abun da ya aikata." "Na san zaka yi mamakin yadda aka yi aka kama Jafar, akwai buƙatar mu haɗu fuska da fuska nayi" "maka bayani"" ya katse wayar, tare da tashi tsaye ya ce ""Ka zan bar wurin nan""" "Ita ma ta miƙe ta ce ""Amma...." """Amma me?""" "Sai ta tsaya tana kallonsa ""Ina son mu yi magana ne, ina da tambayoyi""" """Ba yanzu ba, am not safe here""" "Ta ce ""To muje, na raka ka gate nima fita zan yi"" ta tattaro file ɗin, da jakarta suka fito." "Tun kafin su ƙaraso, ya zuba masa ido, duk da fuskar Viper sanye yake da facemask, amma hakan" bai hana shi gane ko waye ba. "Suna ƙarasowa yayi murmushi ya ce ""Barrister, wurinki na zo, ina Abuja aka ce mini kin samu accident, sai dai na samu labarin da sauƙi jikin, duk da haka na ce bari na zo na ganki, kuma na" "ganki da baƙo. Assalamu alaikum"" yayi maganar yana miƙawa Viper hannu." "(Ayi mini afuwa ji na shiru, bani da lafiya ne)" Ayshercool 08081012143 ₦500 ne via 0009450228 Aisha Adam jaiz bank sai shaidar biya ta 08081012143 Wanda za su jira document 1K ne. 90009343 'Yan Nijar ku turo katin airtel na 300fcfa Arewabooks ayshercool7724 Viper ya tsaya ƙyam yana kallon Alhaji mu'azzam da ya miƙo masa hannu. "A rikice Nabila ta ce ""Amm eh, ai na ma warware na ji sauƙi, ka shiga, ka jira ni a office ɗina," "yanzu zan dawo""" "Viper ya kalli Nabila ya ce ""Koma ciki"" sai ta tsaya tana rarraba ido, tana kallonsa tana kallon" Alhaji mu'azzam wada. "Wani irin kallo Viper ya yi mata, da ya tilasta mata barin wurin, tana waiwayawa." "Viper ya saka hannunsa a hannun Alhaji mu'azzam, ya sauke facemask ɗin sa yana kallon cikin" idonsa. """Dama ana ganinka, ka yi wa hukuma wuyar kamawa? Ya aka yi na ganka tare da yarinyar da" "nake so, kuma nake fatan na aura?""" "Viper ya tsananta riƙon da ya yi wa hannun Alhaji mu'azzam ya ce ""Ka gaya mata wani abu ne?""" """Kamar me fa?""" """Ka san abun da nake nufi"" yayi maganar yana ƙara tsare shi da ido." "Alhaji mu'azzam ya ce ""Kana tsoron wani abu ne?""" """Ba maganar tsoro bane ne ko akasin haka, gargaɗi ne nake yi maka, idan baka furta ba kar ka fara," "nike da alhakin kai ƙarshen wannan lamarin, idan ka yi wani yinƙuri da zai kawo tangarɗa ga abun da nake tsarawa, ka san abun da zan iya aikatawa""." "Alhaji mu'azzam ya yi murmushi ya ce ""Da fari jauhar, na bar maka ita, a wannan karon kuma" "Nabila, kar ka zama mai......" """Jauhar ta wa ce, haka zalika Nabila, muddin zan cigaba da ganin fuskar jauhar a cikin ta Nabila ta haramta a gareka, ba kai ba kowane mahaluki ma"" ya fizge hannunsa daga na Alhaji mu'azzam ya" mayar da facemask ɗin sa ya bar wurin. "Nabila kuwa kai komo ga din ga yi a office ɗin ta, cike da fargaba da tsoro." "Kankarofi ya turo ƙofar office ɗin Nabila ya shigo, ta tsaya tana kallonsa yayi mata murmushi ya" "ƙarasa ya ce ""Madam ya na ganki a tsaye ne?""" "Murmushin ƙarfin hali ta yi ta ce ""Bisimillah zauna mana""" "Ya zauna ya ce ""Ashe tsautsayi ne ya kuma afkuwa haka, ya ƙarfin jikin?""" "Ta ce ""Jiki da sauƙi Alhamdilillah""" """Amma dai babu wani mummunan rauni ko?""" "Ta ce ""Eh, gocewar ƙashi na samu a hannuna, amma Alhamdilillah da sauƙi""" """To Alhamdilillah, na ji daɗi ƙwarai, ya shari'a kuma?""" "Tayi murmushi ta ce ""Mu na ta fama, sai fatan Ubangiji Allah ya iya mana""" """Allah ya yi jagora, kin ga kamata yayi ace har gida na je dubiya, daga nan na miƙa buƙata ta ga Abba, ayi komai a kan lokaci, kin ga babban mutum ne ni, amma soyayya ta saka sai wahalar da" "ni ki ke yi, kina sakani sintiri, sai dai na yi ta biyoki office""" "Ta ɗan shagwaɓe fuska ta ce ""Wahalar da kai kuma?""" "Ya kwantar da murya ya ce ""Eh mana, ko ba ayi na ne, ya sanya ake ta bani wahala""" """Matanka fa biyu, ni gaskiya..." """Ba kya son mai mata ko?"" Ta jinjina masa kai alamar eh." """To meyasa?""" """Wahala ake sha, kuma nan da nan ake sakin wadda ta zo daga baya, impact ni fa tashin hankali ne" "ba na so, gidanmu ma uku ne, ina ganin tashin hankalin da ake yi""" "Yayi dariya ya ce ""Barrister, dabarar mutum ba ta sanyawa ya kaucewa ƙaddararsa. Da dabara da wayon mutum na sanyawa ya kaucewa ƙaddara, da wataƙila haryanzu fatima tana raye da ni ta" "aura""" """Wacece hakan?""" """No kar ki damu, kawai dai misali nake yi miki, wata yarinya ce da na taɓa ƙallafa raina a kan" "aurenta, Allah bai yi ba""" """Baka aureta ba, sai ka auri mata biyu, yanzu da sai ka yi ta uku da ita ni ta huɗu?""" "Sosai ta bashi dariya, saboda yarinyata da kishinta da suka gaza ɓuya." """Karki damu, labarin ne akwai sarƙaƙiya, idan ya zo ƙarshe zan baki. Amma matana ba matsala bane. Uwargidana tana Abuja, amaryata kuma na kano, ke kuma sai in da ki ke so zaki zauna"" Noƙe kafaɗa tayi, tana ɗan tura baki, har ya gama yi mata hirar, bai yi mata magana akan Viper ba, duk da ta so ta tambaye shi ko ya san shi, amma ta ja bakinta tayi shiru, dan da Viper yakamata su" tattauna wannan maganar. **** "Naja'atu Bunkure ce zaune a office ɗin Abdul yasar, ya hakimce a kan kujera yana saurarenta." """Abdul, yarinyar nan fa dole ka fito da ita, even for your own safety, idan fa aka wanke mutumin" "nan, akwai cakwakiya, bamu san ya shari'ar nan zata kasance ba, taurin kan nan da kake yi, babbar barazana ce gareka da mahaifinka Shari'a saɓanin hankali ce""" "Abdul ya ce ""Ba wata barazana, ai ba yau ki ka saba goge laifi ba komai girmansa, wannan karon" "ma ki yi wani abu""" """Nayi iya yi na, da kai da mahaifinka ne kuka ɓata komai, Abdul idan lamarin nan ya kwaɓe fa," "zaku shiga matsala mussaman ma kai. Kuma an gaya maka shaida kawai zata bayar a kotu shikenan ba wani abu ba""" "Abdul ya yi murmushi ya ce ""Naja'atu Bunkure, na sanki fa, na kuma san waye mahaifina, na san abun da zaku iya na san wanda ba zaku iya ba. Idan aka kuma cutar da yarinyar nan a karo na biyu, ba zan yafewa kaina ba, ke da kanki kin san kura tayi lafiya, duk da a duk lokacin da zan shiga Asibiti ina ajiye duk wani iskanci a gefe, in shiga a nutse, amma ke kin san yanzu na nutsu sosai" "da sosai, albarkacin rayuwa tare da rahama""" "Naja ta tafa hannu ta ce ""Innalillahi wa Innalillahi raji'un, Abdul kidnapping fa kenan, bayan fyaɗe" "ka saceta kana rayuwa da ita, wani laifin fa kake aikatawa a kan wani""" """Babu wani laifi da nake aikatawa, da na barta to da tabbas kun yi mata wata illar, barinta a wurina" "shi ne zata zauna safe""" """Shikenan, zamu ɗauki duk wani mataki da hukuncin da muke ganin ya dace""" Ya ɗage kafaɗa alamar ko a jikinsa. *** "Indabo kuwa gaba ɗaya ya kasa zaune ya kasa tsaye, ya rasa abun da yake yi masa daɗi, tun yana" "ƙirga adadin shigarsa banɗaki, har ya sare lissafi ya ƙwace masa." "Gudawar tsoro da fargaba kawai yake yi, tun bayan da Viper ya kira shi a waya." "Embassy ɗin Nigeria na Mexico ya kira, domin a bincika masa da maganar da Viper ya kira shi ya gaya masa, idan gaske ce." "Ya ma rasa wa zai kira ya gaya wa maganar, ashe da gaske yana sane da cewa, da shi yake sakawa ayi exchange a duk lokacin da jafar ya aikata laifi, to ko da sanya hannunsa aka kama masa ɗa?" "Amma ya za ayi common ɗan daban gari, ya saka a kama masa ɗa a ƙasashen ƙetare?." "Waya ya ɗauka ya kira IG, ya din ga masifa, a kan jan ƙafar da ake yi, wurin kama Aminu Viper," "tare da jadadda idan har ba za su yi abun da yake so ba, zai shiga ya fita a ɗauke shi daga garin" "kano, a canza wani IG. Tun da suka kasa kama mutum ɗaya, alhalin yana yawonsa a gari, da" aikata abun da yake so. "Yayi ta bashi haƙuri, tare da bashi tabbacin suna iya ƙoƙarin su, amma komai ya kusa zuwa ƙ" "arshe. Ya ajiye wayar yana mamakin ya za ayi, ace senator guda ya tayar da hankalinsa haka a kan" "ɗan daba guda ɗaya tal har haka, ya din ga ɓata lokacinsa a kansa." "Yadda indabo ya kira shi, ya tayar masa da hankali, haka shima ya kira Nasir a waya, ya ce masa nan da kwanaki talatin, idan babu improvements a aikin nan, zasu karɓi aikin daga hannunsa su" "bawa wani, kuma hakan ka iya janyo masa demotion, da rasa wasu damarmaki." "Shi ma haƙurin ya din ga bayarwa, tare da bada tabaccin zai kama Aminu Viper." *** "Abdul da la'asar ya koma gidansa,ya tarar rahama na wanka, ya kwanta ya yi ɗai-ɗai a kan gado." "Ta buɗe ƙofa ta fito, ta tarar da shi ta ɓata fuska ta ce ""Abdul meye haka?""" Ya buɗe ido ya kalleta. """Na gyara gadon, kawai ka hau ka ajiye mini shirginka, wata uwar jaka kamar wanzami, kalli" takalmi har bedroom ba a wancan ɗakin nake ajiye maka ba? "Lumshe idanunsa ya yi, ta ƙarasa ta kwashe kayan, ta hau kan gadon ta kwance agogon hannunsa," "dan ta san ƙarshe ya cire, ya yar da shi a wani wurin, ya zo ya isheta da nema." "Ya kai hannu ya fara shafa bayanta, tayi masa banza, tana cikin ɓalle masa labcourt ya cigaba da shafa gashin kanta, sai da ya kai hannunsa kan towel ɗin ta, ta buge hannunsa da ƙarfi ta ce" """Tashi kayi sallar la'asar na san baka yi ba"" ya buɗe idonsa ya kalleta." """Eh kana wani manne ido, ka tashi kayi sallar la'asar""" """Zan yi in anjima, yanzu na gaji""" "Ramma ta buɗe baki ta ce ""Wace anjiman? Kai ke da anjiman? Waye ya baka guarantee kai wa anjiman? Abdul wallahi wutar duniya ma ba zaka iya da ita ba, balle ta lahira, kai a wuta kala nawa kake so a saka ka ne? Saƙara fa, wutar marasa yin salla, ita ka ke so ka shiga ko? bayan ta shan giya da neman mata. Ba shiri ya tashi ya ajiye labcourt ɗin ya ce ""To naji, ai dama ban ce ba zan yi ba, zan yi Astagfirullah in sha Allah ba zan shiga wuta ba, shan giya da neman mata ai kin" "san na daina"" yana maganar ya nufi banɗaki." "Sai da tayi dariya, Abdul ga tsoro ga iskanci, ta tabatta da ya samu kyakkyawar tarbiyya, da" "isashshen ilimin addini, da bai aikata wasu abubuwan ba." "Taje gaban mudubi ta zauna, mudubin fal da turaruka, da kayan gyaran gashi da na fata, wasu" "abubuwan duk shi ya koya mata amfani da su, har wasu supplement yake bata tana sha. Ita kanta ta san tayi ƙiba ta yi kyau. Tayi ajiyar zuciya ta fara shafa man." "Ya fito ya tayar da salla, ta ce ""A kyautata niyya da nustuwa idan ana salla, yadda ka yi ta haka zata zo maka a kabari"" ta shirya cikin doguwar riga, yana idar da sallar, ta ɗaukko masa azkar ta ce ""Ungo, ka san shi yawan ambaton Allah, yana hana mutum aikata alfasha, abu ne mawuyaci kaga wanda yake da kusanci da Allah, yana aikata ɓarna kala-kala"" haka ta saka shi a gaba, ya" idar suka je ya ci abinci. "Gaba ɗaya rayuwa da ramma ya sanya ya ji tamkar an canza shi, zuwa wani na daban, haka" kurum yake jin wata nutsuwa a tare da shi. "Mussaman saita shi da take yi a kan ibada, da yawan tsoratar da shi a kan yin ta, haka yana saka masa nustuwa da kwanciyar hankali, kuma ya rage aikata tsageranci da rashin ta ido. Hakan ya" "sanya yake ƙara jin raba shi da ramma, tamkar raba shi da rayuwar sa ne." "System ya kunna ya ce ""Your excellency zo ki ga wani abu""" """Wanke-wanke zan yi na ɗora abincin dare""" """Karki damu, zan yi mana takeaway""" """Sai dai idan zaka yi wanke-wanken""" "Abdul ya ce ""Na ji zan yi""" "Ta ƙaraso ta zauna, ya rungumeta a jikinsa, sannan ya buɗo wani form ya ce ""Kin san na menene" "wannan?""" """No""" """Form ɗinki ne na makaranta""" "Ta kalleshi ta ce ""Makarnta kuma?""" "Ya ce ""Eh mana, ko ba kya so?""" """Ina so, amma gida zaka mayar da ni?""" """Eh, zaki je ki ga gida, daga nan sai school, boarding ce, mai kyan gaske, saboda sonake ki nutsu ki yi karatu da kyau, yadda babu wanda ya ganki, balle yayi miki gori, da kin gama karatu kuma, ƙasar waje zaki tafi jami'a, shiyasa nake tambayar ki me ki ke son zama, na biya komai, na yi" "rubutu, yadda ko bayan raina ba zaki tozarta ba in sha Allah, ko bana raye karatunki ba zai tsaya" "ba sai kin kammala in sha Allah""" """Yar uban wace ni da zaka yi mini duk wannan hidimar haka?""" """Ba yar kowa ba ce, amma komai zan yi miki, ba zai kai nauyin laifin da nayi miki ba, ba zai biya budurcinki da na karɓa ta ƙarfin tsiya ba, da kuma rashin darajar da naje gidanku nayi ba, ba zan gaji da cigaba da neman afuwar ki ba rahama"" ta sunkuyar da kai ta yi shiru, hawaye na zubowa" daga idanunta. "Ya saka hannu yana share mata hawayenta ya ce ""Ki yi haƙuri, na san na cutar da ke, dan Allah ki yafe mini rahama, soyayyar nan kawai da Allah ya jarabbe ni da ita, ta isheni, baki san tarin ƙ alubalen da yake a gabana nake ta ƙoƙarin karewa a waje ba, amma dai ki yi haƙuri dan Allah"" a" "hankali ta zare hannunta daga nasa, ta tashi ta bar falon tana kuka." *** "Nabila kuwa da file ɗin Viper ta tafi gida, ta kai shi ɗakinta, ta cigaba da duba shi daki-daki, tana picking ɗin kurakuran da aka tafka a cikin shari'ar ta sa. Kai da ganin fasalin shari'ar ka san cewa cike take da mugunta da zunzurutun zalunci." "Zafi ne ya isheta, babu wuta, ga solar sai ƙara take yi, kasancewar ranar ba ayi rana sosai ba." "Ta ɗaukko system ɗin ta, da wayoyinta, ta fita gareji, ta shimfiɗa sallaya, da kayan ciye-ciyenta," ta zauna ta cigaba da aikinta. "Nasir ne ya fito yana waya, ba ta san da wa yake yin waya ba, sai dai yanayin yadda ya fito yana" "wayar, bai san tana wurin ba." """Eh dan Allah, duk yadda za ayi a samo mana hotunansa, ko guda ɗaya ne, nima na daɗe da wannan tunanin, ban aiwatar ba, amma a yanzu naga hakan ne kawai mafita, a samo hoton nasa, dan IG ya kira ni ɗazu, shi kansa distinguish sai da ya kira ni, ni duk na ruɗe, nayi mamakin yadda aka yi mutum ɗaya ya gagari hukuma. Duk wata hanya da na bi da zan sameshi, sai ta kuɓ" uce mini. "Shiru ya yi, lokacin da ya lura da ita a wurin a zaune, ya ƙarƙare wayar ya saka a aljihunsa." """Dama har zuwa yanzu baka taɓa ganinsa ba, baka san kamaninsa ba?""" """Eh"" ya bata amsa a taƙaice." """Hmm""" """Ko zaki bani hoton nasa ne?""" """Ni a su wa?""" """Ke a 'yar kankamba mana, samunki da hotonsa ai ba abun mamaki bane ba""" "Nabila ta yi murmushi, kawai ta cigaba da aikin da yake gabanta." **** "Mutumin da yake zaune a cikin ofishin sa, ya kalli P.A ɗin Indabo ya ce ""Ɗan sake duba na da kyau mana malam""" "P.A ya ce ""Na kalleka""" """Shekaru huɗu rak idan Allah ya bani aron rai, suka rage mini nayi retire, a tarihin aikina, ban taɓa karɓar cin hanci na aikata son zuciya ba, ban ƙi ba wasu lokutan ina karɓa in yi abun da ya dace, duk da hakan ma saɓa doka ne. Ba za a haɗa kai da ni ayi rashin albarka ba, a tozarta harkar shari'a ba, idan na ci amana na tsayawa ƙarya a duniya, wa zai tsaya ni a kotun Allah idan zai yi mini hisabi, a cikin kai da uban gidanka, waye zai ƙwace ni? Tambayarka nake yi, na ce waye zai ƙwace ni? Kotun Allah saɓanin tunanin ɗan Adam ce, kuma wallahi dukkanin mu, sai mun tsaya a wannan kotun, kotun da bata buƙatar lauya, ɗan sanda balle ka yi tunanin bayar da cin hanci." "Duk da na san badaƙalar da ake tafkawa a cikin harkar shari'a, na yi mamakin wasu abubuwan da yarinyar nan ta din ga faɗa, yar cikina ce amma ina sauraron programs ɗin ta, kuma ko kaɗan ban ji haushin yadda take tsigalewa aikinmu ba, yadda ake amfani da mu, ake aikata abun da ake so. Babu wani rashawa da zaku bani na karɓa, zan yi abun da ya dace ne kawai, idan kuma aka sake zan yi abun da rai zai ɓaci. Kai in taƙaice maka doguwar magana zuwa gajera, daga sama aka yi mini magana a kan lallai nayi abun da ya dace a kan shari'ar nan, ba a buƙatar kuskure a ciki," "kuma ko ba haka ba, ni sonake na gama aiki na ajiye shi lafiya""" "P.A ya jinjina kai ya miƙe tsaye, ya ce ""Hakan ma babu laifi, muna godiya sosai"" ya juya ya fita" daga office ɗin. *** "Missed call kusan uku Nabila ta yi wa Viper, amma bai ɗaga ba, sai da ranta ya sosu, ta rasa irin wannan murɗaɗɗen hali nasa, gashi ko zata yi fushi da shi, na ɗan lokaci ne, ana jimawa ta manta." "Viper kuma fitowar sa kenan daga wanka, ya kalli wayarsa ya ga missed calls ɗin ta, har guda" uku. "Bai kula ba, ya fara ƙoƙarin neman kayan da zai saka, wayar Walid ta far ringing." "Walid ya ɗaga yayi sallama, ta amsa ta ce ""Oga walid barka da wannan lokaci""" """Yauwwa barkanmu barrister, ya aiki ya jama'a""" """Alhamdilillah, ina ta kiran Viper ya ƙi ɗagawa, wai ni ko wani laifin nayi masa ya tsane har" "haka ne?"" Walid ya kalli Viper, sannan ya ce ""Wanka yake yi yanzu ya fito""" "Ta ce ""Ai dama kai kare shi zaka yi, baka taɓa yadda yayi laifi, ko yayi laifin sai ka kare shi, dama" "magana nake son mu yi da shi, kuma na ma fasa barshi kawai, sai anjima""" "Da sauri Walid ya ce ""A'a ba za a bari ba, ko na haɗa ki da shi?""" """Ba zai kulani ba ai na sani, shiru zai yi mini kamar kurma, in dai yana lafiya shikenan sai anjima""" """Kin ga Nabila, tsaya ki ji mana, gaba ɗaya ke ce baki fahimci Al'amin ba, ba wulaƙanta ki yake" "yi ba""" """Ba wulaƙanta ni yake yi ba kace? Idan ba wulaƙanci ba, mai zai sanya ya ce baya so na, wallahi ban taɓa cewa ina son wani ba, ina zaman zamana, ƙaddara da rashin ya ja ni ya kai ni har in da yake, yayi ta wulaƙanta ni bai damu da rayuwata ba, amma ko haushi bana ji naƙi zuciya, ko kwana biyu nayi ban ji ɗuriyarsa ba sai na damu"" ta ƙarasa maganar cikin damuwa, da alama" abun ya na damunta sosai da sosai. """No, Viper mutumin kirki ne, kuma abun so, in dai ka zauna da shi zaka so shi, saboda yana da halaye masu kyau sosai da sosai, kina kallon muma da muke tare da shi, wasu lokutan haka yake" "yi mana, amma muna duba halaccinsa a garemu ne, kema baki fahimce shi bane""" """Ba wani ban fahimce shi ba, kalli yadda na shiga siraɗin gobarar nan, na zo nayi hatsari, amma" "sannu kawai ba wani abu ba, ya kasa ce mini""" "Walid ya ce ""Ki yi haƙuri, halinsa ne a haka, amma zan iya ce miki, bayan iyayenki, akwai wanda" "ya kai shi shiga damuwar abun da ya faru da ke""" """A hakan? In kusa rasa raina har karo biyu?"" Babu tsammani Viper ya fizge wayar hannun Walid, ya kashe ya dire masa ita, ya fice. Walid ya bishi da kallo yana kallon ikon Allah, shi bai" "rarrasheta ba, kuma ya hana a rarrasheta." "Ko da ya fice daga gidan, wayarsa yake kallo, yana jin tamkar ya kirata, har ya ɗaga ya kalli lambarta, sai kuma ya tsaya ya cigaba da kallon lambar, fasawa yai kawai ya mayar da wayar" aljihunsa ya yi gaba. *** """Arfa, wai meyake damunki ne duk kin wani rame kin tsotse"" Sumayya ta yi maganar tana ƙare mata kallo." "Baba magajiya ta ce ""Gara dai ki yi mata, ko ta ji, taƙi gaya mini meyake damunta, sun samu saɓ ani da babanta, kuma sun shirya, amma kwanan nan sai ƙarewa take yi kamar kuɗin guzuri, ko abincin kirki ba ta ci, duk ta zube sai uban nono da take kayansa kamar ya rinjayeta"" Sumayya ta ƙyalƙyale da dariya ta ce ""Wallahi kuwa baba magajiya, da 'yar ƙibarta tafi kyau, haba jarumar" "mu, idan ki ka saka damuwa a ranki, mu wa zai bamu ƙwarin gwiwar? Muje mu zanta na ji" "menene ya faru""." "Suka tafi ɗakin Nabila, Nabila ta zauna a gefen gado, sumayya ma ta zauna ta ce ""Gaya mini" "menene? Naji baba magajiya ta ce kun yi faɗa da Abba, me ki ka yi?""" "Ta kalli sumayya ta ce ""Sumayya haka soyayya take dama?""" """Soyayya kuma, ita ta hana ki cin abincin ki ke ramewa?""" "Ta girgiza kai ta ce ""Ba ita ta hana ni cin abinci ba, damuwoyi ne kashi-kashi suka sha mini kai sumayya." "Da fari nifa zuciyata na azalzalata a kan son ganin mahaifina, ina son sanin waye shi, ko yaya" "yake a bani dama na san shi, ni zan fara bincike ta ƙarƙashin ƙasa da kaina""" """A'a Nabila, kar Abba ya sani ransa ya ɓaci""" """Sumayya ya zan yi, ni ba na son na mutu ban san babana ba, idan a gidan babana nake, wani" "abun ba za ayi mini shi ba""" """Naji, zamu dawo kan wannan batun, naji kina maganar soyayya""" "Ta numfasa ta ce ""Ƙaddara ta kaini ta baro sumayya""" "Sumayya ta waro ido ta ce ""Kamar yaya?""" """Son abun da ba zan samu ba nake yi""" """A'a kar ki ce haka, amma wa ki ke so ɗin tukuna ma dai""" "Nabila ta tashi, ta saka key, ta buɗe wardrobe ɗin ta, ta ɗaukko file ta zo ta ajiye a gaban" Sumayya. "Sumayya ta ɗauka ta fara bubbuɗewa, ta tsaya ta gama dubawa sannan ta kalli Nabila cikin" "matsananciyar kiɗima da tashin hankali ta ce ""Ban gane me ki ke nufi ba haryanzu Nabila""" "Nabila ta goge hawayen da ya gangaro mata, ta sunkuyar da kanta ƙasa." "Ta daki kafaɗar Nabila ta ce ""Kin san in da mutumin nan yake, da gaske haɗuwa ku ka cigaba da" "yi da shi, har ki fara son ɗan daba?""" """Ɗaga murya zaki yi, ki tona mini asiri Sumayya""" """Nabila wannan hauka ne, ga yaya Nasir a cikin gida, yana ta haƙilo yana fama, ko ɗazu an kawo" "mana sanarwa, yan sanda na cigaba da nemansa ruwa a jallo, duk wanda ya nuna in da yake, ko in" "da za a same shi, akwai kyauta, kawai ki ke zuwa in da yake, idan aka kama da ke fa? Menene" "sunanki bayan mun gama fitowa duniya muna ɓaɓatu da nuna mu masu goyon bayan gaskiya ne?""" """Ban damu da abun da duniya za ta ce ba, ko yadda za a kalleni ba, zan tsaya a bayan gaskiya ne duk rintsi duk wahala. Sumayya zan tsayawa Aminu Viper, kuma kamar yadda ki ka faɗa tabbas" "ina haɗuwa da Viper, kuma na san in da yake, amma ba zan taɓa bari hukuma ta kama shi ba""" "Sumayya ta ce ""Innalillahi wa Innalillahi raji'un, wace lalacewar ce ta same ki har haka Nabila?" "Kina ya mace, ki ke zuwa wurin ɗan daba mashayi, dan ta'adda?""" "Ta girgiza kai ta ce ""Sumayya ƙaddara ce, kamar yadda na gaya miki da farko, idan zaki rufa mini" "asiri ne shikenan, idan kuma tona mini asiri zaki yi, kina da zaɓin yin wanda ya dace"". Ta tashi ta nufi wardrobe ɗin ta, ta mayar da file ɗin." """Kai!! Nabila ki canza tunani, ni ba zan bari ki cutar da kanki, ina kallonki ba""" """Ai ba gaya miki na yi, dan ki bani shawara ba, na riga na yanke abun da nake ganin shi ne" "dai-dai""" "Sumayya ta ɗauki jakarta ta fice, tana zare idanunta, dan tabattar da ba mafarki take yi ba, dan" bata taɓa tsammanin wauta da haukan Nabila ya kai wannan limit ɗin ba. "Bayan tafiyarta, Nabila ta duba wayarta, ta ga announcement ɗin jami'an tsaro, ta ɗauki, jakarta" "ta saka kayanta, ta faki ido ta fice daga gidan." "Sumayya kamar za ta yi kuka, ta marairaice a waya ta ce ""Sir dan Allah ka yi wani abu a kai, rayuwarta zata shiga cikin hatsari da matsala, za ayi mata kallon mutuniyar banza, ɗan ta'adda" "take shirin kasadar karewa""" "Yayi murmushi ya ce ""Sumayya ƙawarki ba ta ji, bar ta ai ɗaukaka take nema, mu yi mata fatan" "nasara""" """A'a sir, dan Allah ba zata iya ba""" "Kankarofi ya ce ""Haka ta ce miki? She can do it, ni na bayar da file ɗin sa aka kai mata, ki ja da baya ki tayata da addu'a, in da ki ka ga ana buƙatar taimakona kuma, ki yi mini magana kar ki yi" "ƙoƙarin dakatar da ita, wannan gargaɗi nake yi miki"" ya kashe wayar." "Sumayya ta ce 'Naga ta ta kaina ni sumayya""" *** "Suna zazzaune a ɗakin, suna ta shan sigari, ya ɗaga kai kawai ya ganta a tsaye a ƙofar ɗakin, tana kallonsu, ko sallamarta bai ji ba." "Ta rame sosai da sosai, duk da fuskarta kawai ake iya gani, saboda facemask." "Ganin ya tsareta da nasa idanun, ya sanya ta sunkuyar da kai, waiwayawa su Walid suka yi, su ga" "me yake kallo, suka ga Nabila a tsaye." "Liti ya ce ""Su 'yar anace ce da yamaccin nan ashe""" "Walid ya ce ""Afuwan barrister, kin zo mun cika wurin da hayaƙi, gashi ke ba kya son hayaƙi""" "Viper ya yinƙura ya tashi, ya ce ""Ki tsaya karki shigo, ki zo kina sumewa mutane sai an ta jagwalgwala ki"" yayi maganar yana nufota, sai da ya tunkarota sosai, sannan ta lura rigar jikinsa" "sunansa ne a jiki, an rubuta Viper, da zanen kan macijiya a jiki ta fito da harshenta." "Ya fito ya tsaya, yayi crossing lega ɗin sa, irin ina saurarenki." "Banza tayi masa ita ma, suka cigaba da tsayuwa, sai dai tsayuwar bata damunsa, ita kuwa ta fara" "gajiya, yana zuƙar sigarinsa, yana fesarwa a gefe." "Hannunsa ta kalla ta zare sauran sigarin ta yar a ƙasa, ya kalleta amma ta haɗe rai." """Ina jinki ya aka yi?""" """Alhaji mu'azzam da ku ka haɗu, dama ka san shi ne?""" """Haka ya ce miki?""" """A'a, tambayarka kawai nake""" """Ki bar maganar sa kawai""" """Saboda me?""" "Ya ce ""Saboda haka na ce""" """Nifa ina tsoron sai na je gaban kotu, in tarar da wasu abubuwa da ban san da su ba, na rasa yadda" "zan ɓullowa lamarin, ka gaya mini shi menene alaƙarka da shi?""." "A hasale ya ce ""Na ce ki bar maganarsa ko? Na san shi, amma sanin waye shi ɗin ba shi da wani" "amfani""." """Shhhh ka daina yi mini shouting, ka yi shiru ka saurare ni, aikina nake yi malam"" tayi maganar" tana kallon ƙwayar idon Viper. Ayshercool 08081012143 ₦500 ne via 0009450228 Aisha Adam jaiz bank sai shaidar biya ta 08081012143 Wanda za su jira document 1K ne. 90009343 'Yan Nijar ku turo katin airtel na 300fcfa Arewabooks ayshercool7724 "Cigaba yayi da kallonta, ita kuma ta kasa sake ɗaga idonta ta kalleshi." Yanayinta ya nuna sosai akwai damuwa a tare da ita. """Kin fasa cewar ba zaki tsaya mini ɗin ba kenan?""" "Ta jinjina masa kai ta ce ""Eh, idan ma na fasa, zuciyata ba zata nutsu ba, alƙawari ne da nayi, yakamata na cika, ko ba dan kowa ba, dan wadda aka kashe ba da hakkinta ba"" tayi maganar ba" tare da ta kalleshi ba. "Ya jinjina kai, a hankali ya furta ""Ina zuwa""" "Ya koma cikin gidan, tana tsaye ta bi ƙofar da kallo, ya fito ɗauke da jaka a hannunsa, ya ce ""Muje"" ba tare da ta san in da zasu ba, ta bishi. Sai da suka yi nesa kaɗan da gidan, sannan ya ja ya" tsaya ita ma ta tsaya. "Ya samu wuri ya zauna, yayi mata nuni, ita ma ta zauna, ta sauke tata jakar daga bayanta," "hannunta ɗaya an naɗa mata bandeji, in da ta samu gocewar ƙashin, sai dai hannun rigarta ya rufe wurin." "Ta ciro system ɗin ta, ta ajiye ta ajiye wayarta." "Ya zuba mata ido, bai yi magana ba, sai da ta ɗan ɗago ta ce ""Wace shaidar da wace shaidar ce da" "kai, and dan Allah kar ka ɓoye mini komai, saboda kar sai mun je kotu, wani abu da ban san da shi ba, ya taso daga baya""." """Me ki ke son sani?""" """Shaidunka, da ka ce kana da su""" "Ya ɗan lumshe idanunsa, sannan ya buɗe ya ce ""Madaki, duk na yi masa illa, sai kuma babban" "yaronsa lakwari, duk suna wurina""" """Garkuwa kayi da su kenan?""" """Kusan hakan""" """Laifi ne fa ka aikata yin hakan""" "Ya tari numfashinta ya ce ""In sake su kenan?""" "Ta ɗaga idonta, amma taga kallonta yake yi." "Jikinta ya ƙara sanyi, maimakon ta mayar da hankali a kan abun da take yi, sai hannunta ma ya" "hau rawa, wata irin ƙaunarsa ta din ga fizgarta, ji tayi tamkar ta ɗurawa kanta zagi." "Ya ɗan matsa kusa da ita, yana kallon fuskar system ɗin ta. Ta takure jikinta, ƙamshin turaren sa" da warin sigari suka cika mata hanci. "Murya na rawa ta ce ""Viper""" """Mmm""" """Ka sha sigari ko?"" Yayi shiru bai bata amsa ba." """Kar ka bari lafiyarka ta taɓu bamu gama shari'ar nan ba, kuma kaga ya fara taɓa maka internal" "organs, an ce hantarka ta kumbura""" "Yayi shiru bai yi magana ba, sai kallonta kawai da yake yi." """Akwai abubuwa da yakamata ka gaya mini, amma kamar kana ɓoye mini, yakamata idan kana ɓ" "oye mini ka gaya mini, kar wani abu ya bamu matsala daga baya""" "Har ta fitar da ran zai yi magana ya ce ""Kamar me?""" """Suwaye suke goge laifukan ka idan ka yi? Ranar da muka je gidanka, ya aka yi ka gane jami'an tsaro a fararen kaya, har muka tsere musu? Wannan rigar da ka yaga a asibiti ta mecece? Kuma me" "kake yi da wayata da kake connecting?""" "Viper ya yi gyaran murya ya ce ""Wasu tambayoyin ba su da alaƙa da abun da yake gabanmu, amma na gane jami'in tsaro a farin kaya, saboda ni tsohon mai laifi ne, ba lokacin na fara aikata laifi ba, dan haka duk wani nuƙu-nuƙun jami'in tsaro sai na gano shi. Rigar da ki ke magana a kai, bata da alaƙa da abun da zaki yi a court. Wayarki kuma ina connecting ina duba wasu location, da" "tura saƙonni. Mai goge laifukana kuma ban sani ba. Sai kuma me?""" "Nabila ta ce ""To shikenan, nan da kwanaki biyu zaka ji ni in Sha Allah, zan har haɗa abun da nake" "buƙata, saboda yayana ya sakani a gaba da yawa""" """Good luck"" ya faɗa a takaice, tamkar ta kurma ihu, ko sannu ya jiki bai iya yi mata ba, dan" "takaici ta tattare system ɗin ta, ta yinƙura ta tashi ta ce ""Sai anjima"" ya jinjina kai." "Jiki a sanyaye take takawa, kamar mara karsashi, ya waiwaya yana kallonta, yadda take ɗaga hannunta tana saukewa, ya tabbatar masa da kuka take yi. Sai da yaji zuciyarsa ta motsa, shi gaba" ɗaya tausayinta ma yake ji. "Tana tafe a titi, barrister Habib ya kirata, ta ɗaga ya ce ""Nabila kina ina ne?""" """Meyafaru?""" """Wai yayanki yaje ɗaukar ki, an ce masa mun fita, ya kira ni, wai muna ina?""" "Guntun tsaki ta ja, ta ce ""Rabu da shi dan Allah""" """A'a kamar yaya na rabu da shi? Kina ina ne, ni ya addabe ni""" """Wani wuri naje, ina kan hanyata ta komawa gida, ina son ma ganinka urgent, amma sai Allah ya" "kaimu gobe""" "Ya ce ""To Allah ya kaimu""" "Ta amsa da ""Amin""" *** "Naja'atu Bunkure ta dubi Indabo ta ce ""A haka ana wannan yanayin zaka koma Abuja?""" """To idan ban koma ba yaya zan yi, matsaloli sai kuma cakuɗewa suke yi""" """Dole fa a nemo Abdul, kuma ta wani fannin rashin kashe yarinyar nan yayi amfani, amma kuma ya tafka shirme da hauka, dan me zai ɗauketa ya je ya ɓoye, kuma saboda wulaƙanci yaje har" "gidansu da kansa, dole fa a nemo Abdul ya fito da yarinyar nan""" """Kin san ya kashe wayoyinsa gaba ɗaya, kin san a haukan yaron nan ce mini yayi, wai idan ya auri yar party chairman bayan aure zan bari ya auri wadda yake so, kawai ya yi mini wannan" "maganar, ban sani ba ita yake nufi zai aura ko wata oho""" """Taɓɗijan, lallai Abdul wannan karon ya ɗebo ta da zafin gaske, wallahi sai an yi taka tsantsan" "kafin a warware wannan shirmen da yayi""" "Indabo ya yakice gumi ya ce ""Na rasa makama gaba ɗaya, ga rayuwarsa na cikin hatsari, ya haɗu" "da mai zamani, wai yaron da ake ta nema ido rufe, shi ne yake yawon sa har da zuwa asibiti, tsoro" "ma nake ji, kar Vipern yayi masa wani abun""" "Naja ta ce ""Yanzu neman Abdul, shi ne abu mafi a'ala, ina tsoron yayi wani abun da zai tona mana" "asiri""" "Yayi ajiyar zuciya ya ce ""Ni ɗan da na haifa, nake ta fafutuka a kan rayuwarsa yake neman ya" "kware mini baya, saboda mace, aishikenan da ina da wata hanyar da zan fito da jafar, da ƙyale shi zan yi, idan abun da yake bi a jikin nata ya gundure shi, sai ya dawo hayyacinsa""" "Bunkure ta kwashe da dariya ta ce ""Barewa bata gudu..." "A fusace ya kalleta, ta haɗiye dariyar, tana mazewa." *** """Nabila ina ki ka je daga wurin aiki? An ce kun fita da barrister Habib, na kira shi ya ce ba kwa" tare. """Eh, uzuri ne ya kamani, na je prison ganin wanda nake karewa ne, ko yanzun ma kana zargin" "wurin Viper na je?"" Kawai ya gyaɗa kai ya fita." "Ta kwanta ruf da ciki, ta buɗe wurin da ta ɓoye videon da ta yi wa Viper, ta din ga kallon hotunan" "da video, tana ƙara jin yadda ƙaunarsa take mamaye zuciyarta." "Ta yi shiru, bata taɓa zaton zata tsinci kanta a irin wannan yanayin ba, duk yadda take kallon kanta," a matsayin mai class taga namijin da ya ƙure wa ajinta gudu. "Ta dinga shafa fuskarsa, ta kan screen ɗin wayarta, ta lumshe ido tana tuno muryar sa, da a zahiri" "mai ban tsoro ce, amma a baɗini daɗin sauraro take yi mata, da sanya mata nutsuwa." "Ƙarfe takwas da rabi, tana ofishinta, tana jiran barrister Habib." "Yana isowa, ta tashi ta tafi, ya ce ""Yar ƙwalisa, yaya aka yi ne? Ya hannu""" "Ta zauna ta ce ""Hannu Alhamdilillah, yaya Habib""" """Na'am ƙanwa Nabila""" """Kamar yadda baka gajiyawa da ni, na sake dawowa neman alfarma a wannan karon""" "Habib ya ce ""To Nabila, me ni ke so?""" """Wataƙila wannan ta zama alfarma ta ƙarshe zan neman a wurinka, duk da akwai haɗarin gaske," "amma yanzu burikana biyu ne, bayan ganin bayan Bunkure foundation, sai wanke Viper daga" "zargin da ake yi masa""" "Da sauri ya ce ""Kamar yaya?""" """Kamar yadda nake gaya maka, bana nufin na sanyaka a matsala, kamar yadda ka taimakeni" "kwanaki a kansa, yanzu ma ina neman taimakonka, dan Allah""" """Nabila, wannan wasa da rai ne fa, ke ya aka yi ki ka san ba shi da laifi? Tayaya zakinkare" "mutumin da hukuma take nema ruwa a jallo?""" "Nabila ta numfasa ta ce ""Zaka ga ta yadda zan yi, ni dai haɗin kanka nake buƙata da taimakonka""" "Ya girgiza kai ya ce ""Nabila matana biyu fa da yara uku, haka kurum ki saka su zama zawarawa da" "marayu, na gaya miki case ɗin sa yayi involving manya haka kurum ki ja mana fitina muna zaman lafiya""" "Cikin marairaice wa ta ce ""Dan Allah yaya habib, ba zan bari sunanka ya fito ba, dan Allah copyn" "file ɗin sa nake so, da aka yi masa shari'a shikaɗai nake buƙata""" "Ya ce ""Taɓɗijan, ke kin san uban process ɗin da na bi, aka baki ki ka gani wancan lokacin, balle" "yanzu kicw copy ki ke so""" """Dan Allah ka taimake ni barrister Habib""" "Yayi shiru sannan ya ce ""Gaskiya sai kin bani lokaci, dan wanan aiki ne da yake buƙatar ɓ" "oyayyiyar gwagwarmayar """ "Cikin farinciki ta ce ""Zaka nemo mini ɗin?" """Zan jarraba ne na gani idan zai yiwu, ba alƙawari nayi miki ba""" "Ta miƙe cikin farinciki ta ce ""Na gode sosai, Allah ya saka da alkhairi ya raya zuriya""" Ya amsa mata da Amin. *** "Ramma tana ta gogewa Abdul labcourt ɗin sa, ya daɗe a tsaye yana kallonta, wani irin" matsanancin tausayinta ne ya mamaye zuciyarsa. "Ya ƙarasa ya zauna ya ce ""Rahama"" ta ɗago ta kalleshi." """Ina da masu gugu fa, kaiwa nake yi ayi mini, ki ke wahalar da kanki""" """Ka ce zaka yi tiyata, shiyasa nake goge maka""" "Yayi murmushi ya ce ""Ai ba da labcourt muke shiga tiyata ba, kayan tiyata daban suke""" "Ta ce ""Ok, duk da haka ka saka wani lokacin""" "Ya jinjina kai ya ce ""Rahama menene babban burinki a rayuwa ne?""" "Ta sunkuyar da kai ta ce ""Ka mayar da ni wurin mamana""" """Na san da wannan, zan mayar da ke, burinki na rayuwa?""" "Ta ɗago idanu ta kalle shi ta ce ""Babu""" "Ya ce ""Kamar yaya? Kowane ɗan Adam yana da buri da yake son cimma a rayuwarsa""" "Rahama ta kashe socket, ta kalleshi ta ce ""Wace rayuwar? Rayuwar da ka gama kassarawa wane buri ne yayi mini saura? Ka mayar da ni wurin mahaifiyata na ƙarasa rayuwata shikaɗai ne roƙ ona a gareka, amma ba ni da wani sauran buri da nake da shi, gaba ɗaya rayuwar ta fita daga raina," "babu abun da yake burgeni yake bani sha'awa""." "Abdul ya koma kusa da ita ya zauna, ya ɗan tsura mata ido, ita kuma ta kawar da kanta gefe ɗ" aya. """Dukkanin mai rai baya fitar da rai, da cimma burikansa na rayuwa, na san ni ne musababbin rushewar naki, amma haryanzu ina dana sanin abun da na aikata, amma zan cika miki burinki Rahama, zaki koma makaranta kiyi karatu mai zurfi in dai muna tare in sha Allah, makaranta mai kyau zan mayar da ke, na gyara makarantun garinku, kuma an karɓi ƙudurin gyaran hanyarku, aiki yayi nisa na yi muku boreholes kamar yadda nayi miki alƙawari, idan aka kammala zan nuna" "miki""" "Maimakon ta yi magana, kawai sai ta fashe da kuka." "Cikin damuwa ya ce ""Rahama menene kuma?""" """Ni duk bana son wannan abubuwan, kawai na koma gidanmu na ƙarasa rayuwata, babu wani abu da zan zama a rayuwa da zai katange ni, daga tsangwamar da zan fuskanta a cikin al'umma," "wannan ɗabi'a ce ta hausawa""" """Ina tabattar miki da idan muna tare, babu wanda zai tsangwame ki, wasu shirye shirye nake yi ne," "da sun tabatta in sha Allah zamu je ki ga mama, amma babu maganar rabuwa tsakaninmu, ba sai na bar ki a tsakanin hausawan ba ma zau yi miki, ki daina damuwa Please bana so""" "Wayarsa ce ta fara vibrating, ya ɗaga ya ce ""Yeah Salim ya ake ciki ne?""" """Wai ina ka shiga ne? Mummy ta kira saifu a waya, wai an nemeka a waya an rasa, ya ce mini shi ma baya samunka a waya, ni kaina kwanana biyu kenan ina nemanka yanzun ma ban zaci zan" "sameka ba, nace bari na jarraba kiran wannan layin naka""" "Abdul ya numfasa ya ce ""Akwai damuwa ne Salim, mu haɗu a gidana na by pass""" """To shikenan, ka san nina har ta gaji da nemanka ita ma, har clubs ka daina zuwa, gidanka da take samunka ma yanzu baka zama, kuma ta daina samun wayarka, na ce mata kayi busy ne da shirye" "shiryen siyasarka""" "Abdul ya ce ""Manta da ita, zan je asibiti zan yi tiyata da daddare, idan na kammala ko kafin na tafi," "sai mu yi magana sai mu haɗu""" """To shikenan, sai na ji ka""" *** "Walid ne ya ƙarasa in da Viper yake a zaune a kan dutsen nan, yayi shiru yana nazari." "Ya zauna a kusa da shi ya ce ""Sannu da hutawa""" """Yauwwa sannu da zuwa""" """Yauwwa, tunanin me ka ke yi ne?""" "Viper bai ba shi amsa ba ya ce ""Meye labari?""" """Labari, yan unguwar su madaki, sun addaba wa yan unguwarmu, naji ɗan mama ya ce zai shiga" "unguwar, sai kuma na je maɓoyar madaki, na tarar baya nan, ko dai ya tafi wani wurin bamu sani ba?""" "Viper ya ɗan kaɗa kai ya ce ""Kar ka damu na san in da yake""" "Cikin mamaki ya ce ""Ka san in da yake kamar yaya?""" """Kamar yadda na ce"" ya faɗa a taƙaice." "Shiru ya wanzu na wani ɗan lokaci, Viper ya ce ""Jibi yarinyar nan zata shiga kotu, ta kuma ce a kwankin nan zata fara shari'ata, i need to assist her, a haka ma rayuwarta na cikin hatsari, muddin" "ta shiga case ɗin nan matsaloli zasu ninku fiye da baya, akwai buƙatar na taimaka mata sosai""" "Walid ya ce ""Haka ne, Allah ya tabattar mana da alkhairi, ya bamu dukkanin nasara, ka yi yanci" "mai zamani, ka daina wannan zaman ɓuyan""" "Viper ya dafa kafaɗar Walid ya ce ""Mai laya""" """Na kiyayi mai zamani""" """Mu huta wannan zaman ɓuyan zaka ce, idan Allah ya bamu nasara, in ga kun tsaya da ƙ" "afafuwan ku, na aurar da kai, da wancan sarkin faɗan""" "Walid ya ce ""A'a, ka yi yanci, muga farincikinka da walwalarka sun dawo dai, mu dai mu cigaba" "da gurgura rayuwa""" "Viper ya girgiza kai ya ce ""Aure yana da daɗi mussaman idan ku ka yi dace kamar yadda na yi. Ni" "na taɓa yi na more shi, kuma yakamata ku yi, idan na bari ku ka ƙarar da rayuwarku a kan hidimata kawai ban yi wa kaina adalci ba muhsin""" "Walid ya ce ""Taɓ anya na taɓa jin ka kira ni da ainihin sunana kuwa?""" "Viper ya yi murmushi ya ce ""Ka tuna mini da watarana, da 'yar madara ta sakani a gaba, ta ce sai na gaya mata ainihin sunayenmu, na ce mata ni Muhammad Al'amin, kai Muhsin, liti Abdullahi. Ta rafka salati, ta ce kalli yadda duk kuka mayar da sunayenku wani iri, har ma ɗan gara yaya walid, duk da shi ma wataran mai laya kake ce masa, gaskiya ku canza hali, sunayenku masu daɗi, amma duk kun canzawa kanku suna. Na ce ;Sunan waye yafi daɗi, tayi murmushi ta ce na mijina, na ce yauwwa ke ma sunanki mai daɗi an saka miki wani iyayi daban. Muhsin ku yi aure akwai alfanu a cikin aure, haryanzu na kasa manta rayuwar cikin aure, na san abu ne da ba zai bar ƙwaƙ walwata ba. Ina son naga kun samu cigaba a rayuwar ku, ba zan yi alfahari da ku ƙarar da" "rayuwarku a kaina ba""" "Walid ya kalli Viper ya ce ""Al'amin, ko mai muka yi maka a rayuwa ka cancanta, ai duk ɗan halak baya manta alkhairi, idan kai ka manta ni ba zan manta ɗawainiyar da ka yi da ni da mahaifiyata" "ba, haka zalika mutuntawar da matarka tayi mana""" """Muhsin, mahaifiyar ka, mahaifiyata ce, ka daina saka wannan a lissafi""" "Walid ya ce ""Na daina, amma dai sai mun fara aurar da kai tukuna, farincikin ka da walwalarka su" "dawo, sannan mu san abun yi mu ma""" "Viper ya girgiza kai ya ce ""Bani da ra'ayin kuma yin aure a rayuwata, wancan ma tsautsayi da ƙ" "addara ne ya saka aka yi shi""" "Walid ya yi murmushi ya miƙe ya ce ""Wannan kuma, ƙaddarar tausayi da soyayya zai saka a ayi" "shi"" har Walid ya yi gaba, Viper ya miƙe da sauri ya ce ""Ina ba zai yiwu ba, jauhar ce kawai a zuciyata"" kawai walid ya ɗaga masa hannu ba tare da ya waiwaya ba ya yi gaba yana dariya." *** "Salim ya kalli Abdul da ya shigo a gajiye, ya zauna ya ajiye labcourt ɗin sa a gajiye." """Yaya ne mutumina, na ganka a wahale""" """Aiki na sha yau ɗin nan, na je asibiti ya kai huɗu, na duba wanda na yi wa tiyata, sannan na yi" "wa wasu aikin sai godiyar Allah""" "Salim ya yi murmushi ya ce ""Sannu, ko in ɗaukko maka abar ne, ina da ita a mota?""" "Abdul ya girgiza kai ya ce ""Rahama ta san warin giya, faɗa zamu yi da ita""" "Salim ya ce ""Wow, to ko abinci zamu je ka ci?""" "Nan ma ya girgiza kai ya ce ""Ina da special cook a gida, yarinyar nan dar ce"" yayi maganar yana" kashingiɗa. "Salim ya kwashe da dariya ya ce ""Allah mutumina, ta saduda kenan?""" Abdul ya yi murmushi. """Ina jinka, bani labari""" """Salim, kai ka san komai, tun da ka tafi fa babu labarin mahaifiyar yarinyar nan, gashi ta matsa mini na mayar da ita gida, ni ba mayar da itan ne ya dame ni ba, na fara yi wa daddy bayani ko zai fahimce ni, ya hau ni da faɗa da zagi, kuma wai lallai sai na kai masa ita, sai an kaita kotu ta bayar da shaida, ni fa na yanke shawarar zan ɗauke ta mu ƙara gaba, har takarar ma bana so. Wallahi Salim ban taɓa dana sanin aikata wani abu a rayuwata ba, irin yi wa rahama fyaɗe ba, kuma ban ta ɓa jin so da ƙaunar wani abu a raina ba, kamar yadda nake jin son ta, ya mamaye zuciyata ba, Salim wallahi ba zan iya rabuwa da rahama ba, ba wai ina sonta da jikinta ko wani abu ba, ita ɗin" "nake so""" "Salim ya ce ""Ƙarya ne malam, mun san komai fa""" "Abdul ya yi murmushi ya ce ""Ita ta sani ai, ba zan yi maka ƙarya ba""" "Salim ya ce ""Kar ka damu, na fahimta maganar ka ɗauketa kayi gaba bai taso ba fa, ka zauna ka" "yi wa daddy cikakken bayani""" """Salim na san waye mahaifina ciki da bai, muddin na fito da rahama, zai iya salwantar da rayuwarta, ita kanta mahaifiyarta ina tantama a kan bashi ne ya ɗauke ta ba, ni kuwa a kan" "rahama sai dai ayi duk wadda za ayi""" "Salim ya waro ido ya ce ""Da iyayen naka? Abdul yaushe ka koma haka ne? A cikinmu duk rashin" "nan da kai da Saif kun fi mu mutunta iyaye ma da jin maganar su mussaman kai, meyasa ka ke son" "canzawa saboda mace?""" """Kamar yadda take yawan faɗa, na riga na ɓata rayuwarta, dan haka ba zan bari a sake tagayyara rayuwarta ba, ina son rahama irin son da nake son na ƙarasa rayuwata da ita, idan Daddy ya" "cigaba da matsawa, ba zan yi wancan auren ba""" "Ya girgiza kai ya ce ""Ba za ayi haka ba, ka je ka fara maganar da mahaifiyar ka, ko zata" "fahimceka""" "Ya ce ""Taɓ ayi sha'ani kawai, zan je zanji kiran da yake yi mini amma in fito da rahama dai," "gaskiya ban ji zan iya ba""" """Amma fa Abdul mun tafka shirme a gaban uwar yarinyar nan, anya zata yafe maka kuwa? Ga" "tsiyar da ka je ka kuma yi daga baya""" "Abdul ya numfasa ya ce ""Sharrin giya ne, da gigin arziki da nake ji da shi, nake jin kamar zan iya" "taka na ƙasa da ni, ni komai zata yi, mini tayi mini amma ban da raba ni da yarinyar nan""." "Salim ya ce ""Lallai ka faɗa da yawa mutumina""" """Rahama, akwai haƙuri, duk da ina cin zagi a wurinta da tsinuwa, amma da ta ganni cikin rashin lafiya, ko damuwa hankalinta yake tashi, ita take dafa abincin da zan ci, yau har da yi mini guga. Nifa yarinyar da aka ce za a haɗa ni da ita, gaba ɗaya bata yi mini ba buɗaɗɗen ido ne da ita, gara" "a bar ni da rahaman dai, na san koma menene ni ne sila""" Salim ya jinjina kai. *** "Nabila ce a tsaye a gaban court, tana ƙoƙarin fara gabatarwa da mai shari'a appeal ɗin su, ta kalli barrister Habib, ya jinjina mata kai alamar bata ƙwarin gwiwa, ta tsaya ta gabatar da kanta cikin" "harshen turanci, tare da fara karantowa kotu koken su." "Na kotun ta yi duba da rubutaccen jawabin da suka gabatar, a kan hukuncin da kotun farko ta yi, bisa ga wasu kurakurai da suke ganin an tafka a wurin yin shari'ar, na rashin bayyanar wadda abun ya faru da ita a gaban kotu, da rashin gabatar da medical report ta hannun ɗan sandan da kuma likitan da ya tabattar da yin laifin ba." "Hakazalika a hujjojin da suka gabatar a kotun farko, akwai sautin murya, na mahaifiyar ramma tana koken a kawo mata agaji, domin kuwa wanda ya yi mata fyaɗe ya dawo ya ɗauke ta, idan kuwa haka ne, wanda ake zargi ba shi ne ya aikata wannan laifin ba, sannan kuma wanda ake zargin ya amsa laifin ne, a sakamakon barazana da aka yi masa, da haka take roƙon kotun ta bibiyi" "shari'ar da kotun baya tayi, ta tabattar da adalci""" Ta miƙa file ɗin aka miƙa gaban mai shari'a. "Suna tafe a mota tare da barrister Habib ta ce ""Yaya, gaba ɗaya jikina a sanyaye yake, gani nake" "wannan karon ma, ba zan yi nasara ba""" """Bana son saurin karaya dan Allah, kin manta wadda ki ke ƙoƙarin tunkara ta fi wadda ki ke yi yanzu? Kuma yanzu hankalin mutane da yawa ya dawo kanki, ba common mutanen gari ba, har da" "ma'aikatan shari'a""" """Idan Allah ya sa na yi nasara, akwai gagarumin tonin silili fa"" tayi maganar tana murmushi." "Barrister Habib ya kalleta ya ce ""Na me fa?""" """Zaka gani kai dai, ya batun case ɗin Viper, samo mini copyn shari'ar da na ce?""" """Ai na gaya miki ba aiki ne mai sauƙi ba, ina nan ina ƙoƙartawa, yanzu idan aka san ina ƙoƙarin" "samo file ɗin ma, rayuwata na cikin hatsari""" "Ta jinjina kai ta ce ""Haka ne, Allah ya ba da sa'a""" *** """Inadabo, wallahi akwai matsala muddin Abdul bai kawo yarinyar nan ba, tun da ya ce maka tana wurin sa ya fito da ita mana""" """Naja duk wani ƙoƙari ina yi, bai taɓa bujirewa umarnina ba sai a wannan karon, yama daina" "zuwa in da nake gaba ɗaya, bana samun wayoyinsa""" """Ka san kuwa me nasararta a appeal ɗin nan yake nufi? Yarinyar nan fa ba zata zuba mana ido ba," "dole ka yi ƙoƙari fa a kai""" """Kar ki damu, zan ga alƙalin da kaina""" "Bunkure ta girgiza kai ta ce ""Ƙoƙarin ka ba a kan alƙali kawai zai tsaya ba, har da wannan" "yarinyar, dan ni na yi iya yi na""" "Inadabo ya katse kiran, ba tare da ya sake yin magana ba." **** "Babu tsammani, indabo ya shiga falon mai ɗakinsa, ya tarar da ita tana yi wa Abdul faɗa. Yayi turus, sannan cikin tsananin ƙuluwa ya ce ""Ai dama na sani, ke ki ke goya masa baya, yake rashin mutunci""" """A'a nima fa yanzu na ganshi, nake tambayarsa ba'asin ina ya shiga, kar ma ka ɗora mini wannan" "zargin""" """Wato Abdul ban isa da kai ba kenan ko? Nayi maka magana sai ka ɗauke ƙafarka gaba ɗaya" "daga gidan ka daina zuwa, ina yarinyar take?""" Abdul ya yi shiru ya ƙi magana. """Ka gaya mini in da take, tun ban tattaka ka ba, yau an yi appeal ɗin shari'ar yarinyar, kuma" "muddin aka wanke mutumin nan, babu lallai ka tsira ba tare da asirinka ya tonu ba""." "Abdul ya ce ""In dai hakan yana nufin na cigaba da rayuwa da ita, shikenan ni ba komai asirin nawa ya tonu, dan Allah Daddy ka yi haƙuri, wallahi ba zan iya fito da rahama gaban duniya ba, ban san iya abun da zaka yi mata ba, kuma bana fatan abun da zai ƙarasa zubar da mutuncinta," "dan kuwa fito da ita gaban kotu kamar cigaba da yayata abun da ya faru da ita ne""" "Tamkar shashasha indabo ya tsaya yana kallon Abdul, babu kunya babu tsoron Allah Abdul yake" gaya masa wannan maganganun. "Ya numfasa ya ce ""Babu laifi, ni na san matakin da yakamata na ɗauka""." *** "Nabila ta shiga office ɗin ta, ta zauna ta janyo drower zata ɗauki biro, ta ga file, ta ɗaukko file ɗ in ta buɗe, kawai taga copyn shari'ar Viper ne a ciki, sai da ta razana ta ja da baya, tana waige-waige." "A razane ta ɗauki waya, ta kira barrister Habib, ya ɗaga ya ce ""Hello Nabila""" """Barrister ka samo file ɗin nan ne?""" """A'a, ina ta ƙoƙari dai a kai, ki yi haƙuri""" """Barrister, file ɗin na gani a office ɗina""" "Ya ce ""Wane file ɗin?""" """Na shari'ar Viper""" """Iyee, waye ya baki?""" """Nima ban sani ba, a office ɗina na tarar kamar yadda aka ajiye mini na Bunkure""" """Kar ki gaya wa kowa, gani nan zuwa""" Ta ajiye wayar tana sake dudduba file ɗin. "Ji ta yi an buɗe ƙofar office ɗin ta razana da sauri tana ɓoye file ɗin, ya rufe ƙofar office ɗin," ya ƙaraso. "Ta ce ""Yau ma kai ne da kanka?""" "Ya ce ""Eh, ko in koma ne?""" """A'a, bisimillah zauna""" "Ya samu wuri ya zauna, kamar yadda a wancan karon, tayi masa hidima, haka ma a wannan karon, ta haɗa masa tea, ta bashi abincinta da ta zo da shi, ta bashi"" wannan karon babu gardama ya karɓa" ya ci. "Ta ciro file ɗin ta ajiye masa ta ce ""Yau da safe aka kawo mini shi, ban san kuma wanda ya kawo" "ba""" "Ya karɓa ya bubbuɗe, yana dubawa." """An fitar da sanarwar cigaba da nemanka jiya, wai yaranka sun je sun yi faɗan daba, jami'an tsaro" "na ta cigaba da yayata nemanka""" "Ya girgiza kai ya ce ""Ni ma na ji, sai dai ni bani da masaniyar hakan, na samu labarin faɗa" "tsakanin yan unguwarmu da yan unguwar su madaki, ban san ma me ake ciki ba""" """Zan je kotu, na nemi kotu ta hana kama ka, kafin na ɗauki mataki na gaba""" Viper ya jinjina kai yana kora shayin hannunsa. "Ya ce ""Bani system ɗin ki""" "Ta ɗaukko, ta bashi ya ciro tab ɗin sa, ya ɗan jima yana danne-danne, yayin da ita kuma take" satar kallonsa kamar yau ta fara ganinsa. "Kamar kar ya tafi ta daina ganinsa, wani irin shauƙi da farinciki ya din ga ratsa zuciyarta." """Ki shirya, zamu je ki ga shaidar da nake da shi, idan da abun da ki ke buƙatar sani""" "Ta ce ""To shikenan, ka sanya lokaci sai mu je, sai kuma mu yi ta addu'a""." "Ya ɗan daddana tab ɗin hannunsa ya ɗan yi shiru sannan ya ce ""Barka da wannan lokaci, kana magana da mai zamani ne." "Babu buƙatar yin doguwar magana, na san zuwa yanzu ka san labarin haɗuwata da ɗanka, zuwa" "yanzu na san duk wani motsinsa, duk in da yake zuwa na sani, amma ba wannan ba, akwai buƙatar ka bibiyi case ɗin ɗanka da ka ke musayar sa da ni, a lokacin da yake Nigeria yake aikata laifuka," "ina da babban albishir gareka, Mexico na shirin miƙawa amurka shi, ya fuskanci shari'a, kuma ina mai sanar da kai kisan kai ne hukuncin abun da ya aikata." "Na san zaka yi mamakin yadda aka yi aka kama Jafar, akwai buƙatar mu haɗu fuska da fuska nayi" "maka bayani"" ya katse wayar, tare da tashi tsaye ya ce ""Ka zan bar wurin nan""" "Ita ma ta miƙe ta ce ""Amma...." """Amma me?""" "Sai ta tsaya tana kallonsa ""Ina son mu yi magana ne, ina da tambayoyi""" """Ba yanzu ba, am not safe here""" "Ta ce ""To muje, na raka ka gate nima fita zan yi"" ta tattaro file ɗin, da jakarta suka fito." "Tun kafin su ƙaraso, ya zuba masa ido, duk da fuskar Viper sanye yake da facemask, amma hakan" bai hana shi gane ko waye ba. "Suna ƙarasowa yayi murmushi ya ce ""Barrister, wurinki na zo, ina Abuja aka ce mini kin samu accident, sai dai na samu labarin da sauƙi jikin, duk da haka na ce bari na zo na ganki, kuma na" "ganki da baƙo. Assalamu alaikum"" yayi maganar yana miƙawa Viper hannu." "(Ayi mini afuwa ji na shiru, bani da lafiya ne)" Ayshercool 08081012143 ₦500 ne via 0009450228 Aisha Adam jaiz bank sai shaidar biya ta 08081012143 Wanda za su jira document 1K ne. 90009343 'Yan Nijar ku turo katin airtel na 300fcfa Arewabooks ayshercool7724 Viper ya tsaya ƙyam yana kallon Alhaji mu'azzam da ya miƙo masa hannu. "A rikice Nabila ta ce ""Amm eh, ai na ma warware na ji sauƙi, ka shiga, ka jira ni a office ɗina," "yanzu zan dawo""" "Viper ya kalli Nabila ya ce ""Koma ciki"" sai ta tsaya tana rarraba ido, tana kallonsa tana kallon" Alhaji mu'azzam wada. "Wani irin kallo Viper ya yi mata, da ya tilasta mata barin wurin, tana waiwayawa." "Viper ya saka hannunsa a hannun Alhaji mu'azzam, ya sauke facemask ɗin sa yana kallon cikin" idonsa. """Dama ana ganinka, ka yi wa hukuma wuyar kamawa? Ya aka yi na ganka tare da yarinyar da" "nake so, kuma nake fatan na aura?""" "Viper ya tsananta riƙon da ya yi wa hannun Alhaji mu'azzam ya ce ""Ka gaya mata wani abu ne?""" """Kamar me fa?""" """Ka san abun da nake nufi"" yayi maganar yana ƙara tsare shi da ido." "Alhaji mu'azzam ya ce ""Kana tsoron wani abu ne?""" """Ba maganar tsoro bane ne ko akasin haka, gargaɗi ne nake yi maka, idan baka furta ba kar ka fara, nike da alhakin kai ƙarshen wannan lamarin, idan ka yi wani yinƙuri da zai kawo tangarɗa ga" "abun da nake tsarawa, ka san abun da zan iya aikatawa""." "Alhaji mu'azzam ya yi murmushi ya ce ""Da fari jauhar, na bar maka ita, a wannan karon kuma" "Nabila, kar ka zama mai......" """Jauhar ta wa ce, haka zalika Nabila, muddin zan cigaba da ganin fuskar jauhar a cikin ta Nabila ta" "haramta a gareka, ba kai ba kowane mahaluki ma"" ya fizge hannunsa daga na Alhaji mu'azzam ya mayar da facemask ɗin sa ya bar wurin." "Nabila kuwa kai komo ga din ga yi a office ɗin ta, cike da fargaba da tsoro." "Kankarofi ya turo ƙofar office ɗin Nabila ya shigo, ta tsaya tana kallonsa yayi mata murmushi ya" "ƙarasa ya ce ""Madam ya na ganki a tsaye ne?""" "Murmushin ƙarfin hali ta yi ta ce ""Bisimillah zauna mana""" "Ya zauna ya ce ""Ashe tsautsayi ne ya kuma afkuwa haka, ya ƙarfin jikin?""" "Ta ce ""Jiki da sauƙi Alhamdilillah""" """Amma dai babu wani mummunan rauni ko?""" "Ta ce ""Eh, gocewar ƙashi na samu a hannuna, amma Alhamdilillah da sauƙi""" """To Alhamdilillah, na ji daɗi ƙwarai, ya shari'a kuma?""" "Tayi murmushi ta ce ""Mu na ta fama, sai fatan Ubangiji Allah ya iya mana""" """Allah ya yi jagora, kin ga kamata yayi ace har gida na je dubiya, daga nan na miƙa buƙata ta ga Abba, ayi komai a kan lokaci, kin ga babban mutum ne ni, amma soyayya ta saka sai wahalar da" "ni ki ke yi, kina sakani sintiri, sai dai na yi ta biyoki office""" "Ta ɗan shagwaɓe fuska ta ce ""Wahalar da kai kuma?""" "Ya kwantar da murya ya ce ""Eh mana, ko ba ayi na ne, ya sanya ake ta bani wahala""" """Matanka fa biyu, ni gaskiya..." """Ba kya son mai mata ko?"" Ta jinjina masa kai alamar eh." """To meyasa?""" """Wahala ake sha, kuma nan da nan ake sakin wadda ta zo daga baya, impact ni fa tashin hankali ne" "ba na so, gidanmu ma uku ne, ina ganin tashin hankalin da ake yi""" "Yayi dariya ya ce ""Barrister, dabarar mutum ba ta sanyawa ya kaucewa ƙaddararsa. Da dabara da" "wayon mutum na sanyawa ya kaucewa ƙaddara, da wataƙila haryanzu fatima tana raye da ni ta aura""" """Wacece hakan?""" """No kar ki damu, kawai dai misali nake yi miki, wata yarinya ce da na taɓa ƙallafa raina a kan" "aurenta, Allah bai yi ba""" """Baka aureta ba, sai ka auri mata biyu, yanzu da sai ka yi ta uku da ita ni ta huɗu?""" "Sosai ta bashi dariya, saboda yarinyata da kishinta da suka gaza ɓuya." """Karki damu, labarin ne akwai sarƙaƙiya, idan ya zo ƙarshe zan baki. Amma matana ba matsala bane. Uwargidana tana Abuja, amaryata kuma na kano, ke kuma sai in da ki ke so zaki zauna"" Noƙe kafaɗa tayi, tana ɗan tura baki, har ya gama yi mata hirar, bai yi mata magana akan Viper ba, duk da ta so ta tambaye shi ko ya san shi, amma ta ja bakinta tayi shiru, dan da Viper yakamata su" tattauna wannan maganar. **** "Naja'atu Bunkure ce zaune a office ɗin Abdul yasar, ya hakimce a kan kujera yana saurarenta." """Abdul, yarinyar nan fa dole ka fito da ita, even for your own safety, idan fa aka wanke mutumin" "nan, akwai cakwakiya, bamu san ya shari'ar nan zata kasance ba, taurin kan nan da kake yi, babbar" "barazana ce gareka da mahaifinka Shari'a saɓanin hankali ce""" "Abdul ya ce ""Ba wata barazana, ai ba yau ki ka saba goge laifi ba komai girmansa, wannan karon" "ma ki yi wani abu""" """Nayi iya yi na, da kai da mahaifinka ne kuka ɓata komai, Abdul idan lamarin nan ya kwaɓe fa," "zaku shiga matsala mussaman ma kai. Kuma an gaya maka shaida kawai zata bayar a kotu shikenan ba wani abu ba""" "Abdul ya yi murmushi ya ce ""Naja'atu Bunkure, na sanki fa, na kuma san waye mahaifina, na san abun da zaku iya na san wanda ba zaku iya ba. Idan aka kuma cutar da yarinyar nan a karo na biyu, ba zan yafewa kaina ba, ke da kanki kin san kura tayi lafiya, duk da a duk lokacin da zan shiga Asibiti ina ajiye duk wani iskanci a gefe, in shiga a nutse, amma ke kin san yanzu na nutsu sosai" "da sosai, albarkacin rayuwa tare da rahama""" "Naja ta tafa hannu ta ce ""Innalillahi wa Innalillahi raji'un, Abdul kidnapping fa kenan, bayan fyaɗe" "ka saceta kana rayuwa da ita, wani laifin fa kake aikatawa a kan wani""" """Babu wani laifi da nake aikatawa, da na barta to da tabbas kun yi mata wata illar, barinta a wurina" "shi ne zata zauna safe""" """Shikenan, zamu ɗauki duk wani mataki da hukuncin da muke ganin ya dace""" Ya ɗage kafaɗa alamar ko a jikinsa. *** "Indabo kuwa gaba ɗaya ya kasa zaune ya kasa tsaye, ya rasa abun da yake yi masa daɗi, tun yana" "ƙirga adadin shigarsa banɗaki, har ya sare lissafi ya ƙwace masa." "Gudawar tsoro da fargaba kawai yake yi, tun bayan da Viper ya kira shi a waya." "Embassy ɗin Nigeria na Mexico ya kira, domin a bincika masa da maganar da Viper ya kira shi ya gaya masa, idan gaske ce." "Ya ma rasa wa zai kira ya gaya wa maganar, ashe da gaske yana sane da cewa, da shi yake sakawa ayi exchange a duk lokacin da jafar ya aikata laifi, to ko da sanya hannunsa aka kama masa ɗa?" "Amma ya za ayi common ɗan daban gari, ya saka a kama masa ɗa a ƙasashen ƙetare?." "Waya ya ɗauka ya kira IG, ya din ga masifa, a kan jan ƙafar da ake yi, wurin kama Aminu Viper, tare da jadadda idan har ba za su yi abun da yake so ba, zai shiga ya fita a ɗauke shi daga garin kano, a canza wani IG. Tun da suka kasa kama mutum ɗaya, alhalin yana yawonsa a gari, da" aikata abun da yake so. "Yayi ta bashi haƙuri, tare da bashi tabbacin suna iya ƙoƙarin su, amma komai ya kusa zuwa ƙ" "arshe. Ya ajiye wayar yana mamakin ya za ayi, ace senator guda ya tayar da hankalinsa haka a kan" "ɗan daba guda ɗaya tal har haka, ya din ga ɓata lokacinsa a kansa." "Yadda indabo ya kira shi, ya tayar masa da hankali, haka shima ya kira Nasir a waya, ya ce masa" "nan da kwanaki talatin, idan babu improvements a aikin nan, zasu karɓi aikin daga hannunsa su bawa wani, kuma hakan ka iya janyo masa demotion, da rasa wasu damarmaki." "Shi ma haƙurin ya din ga bayarwa, tare da bada tabaccin zai kama Aminu Viper." *** "Abdul da la'asar ya koma gidansa,ya tarar rahama na wanka, ya kwanta ya yi ɗai-ɗai a kan gado." "Ta buɗe ƙofa ta fito, ta tarar da shi ta ɓata fuska ta ce ""Abdul meye haka?""" Ya buɗe ido ya kalleta. """Na gyara gadon, kawai ka hau ka ajiye mini shirginka, wata uwar jaka kamar wanzami, kalli" takalmi har bedroom ba a wancan ɗakin nake ajiye maka ba? "Lumshe idanunsa ya yi, ta ƙarasa ta kwashe kayan, ta hau kan gadon ta kwance agogon hannunsa," "dan ta san ƙarshe ya cire, ya yar da shi a wani wurin, ya zo ya isheta da nema." "Ya kai hannu ya fara shafa bayanta, tayi masa banza, tana cikin ɓalle masa labcourt ya cigaba da" "shafa gashin kanta, sai da ya kai hannunsa kan towel ɗin ta, ta buge hannunsa da ƙarfi ta ce ""Tashi kayi sallar la'asar na san baka yi ba"" ya buɗe idonsa ya kalleta." """Eh kana wani manne ido, ka tashi kayi sallar la'asar""" """Zan yi in anjima, yanzu na gaji""" "Ramma ta buɗe baki ta ce ""Wace anjiman? Kai ke da anjiman? Waye ya baka guarantee kai wa anjiman? Abdul wallahi wutar duniya ma ba zaka iya da ita ba, balle ta lahira, kai a wuta kala nawa kake so a saka ka ne? Saƙara fa, wutar marasa yin salla, ita ka ke so ka shiga ko? bayan ta shan giya da neman mata. Ba shiri ya tashi ya ajiye labcourt ɗin ya ce ""To naji, ai dama ban ce ba zan yi ba, zan yi Astagfirullah in sha Allah ba zan shiga wuta ba, shan giya da neman mata ai kin" "san na daina"" yana maganar ya nufi banɗaki." "Sai da tayi dariya, Abdul ga tsoro ga iskanci, ta tabatta da ya samu kyakkyawar tarbiyya, da" "isashshen ilimin addini, da bai aikata wasu abubuwan ba." "Taje gaban mudubi ta zauna, mudubin fal da turaruka, da kayan gyaran gashi da na fata, wasu abubuwan duk shi ya koya mata amfani da su, har wasu supplement yake bata tana sha. Ita kanta" ta san tayi ƙiba ta yi kyau. Tayi ajiyar zuciya ta fara shafa man. "Ya fito ya tayar da salla, ta ce ""A kyautata niyya da nustuwa idan ana salla, yadda ka yi ta haka" "zata zo maka a kabari"" ta shirya cikin doguwar riga, yana idar da sallar, ta ɗaukko masa azkar ta ce ""Ungo, ka san shi yawan ambaton Allah, yana hana mutum aikata alfasha, abu ne mawuyaci" "kaga wanda yake da kusanci da Allah, yana aikata ɓarna kala-kala"" haka ta saka shi a gaba, ya" idar suka je ya ci abinci. "Gaba ɗaya rayuwa da ramma ya sanya ya ji tamkar an canza shi, zuwa wani na daban, haka" kurum yake jin wata nutsuwa a tare da shi. "Mussaman saita shi da take yi a kan ibada, da yawan tsoratar da shi a kan yin ta, haka yana saka masa nustuwa da kwanciyar hankali, kuma ya rage aikata tsageranci da rashin ta ido. Hakan ya" "sanya yake ƙara jin raba shi da ramma, tamkar raba shi da rayuwar sa ne." "System ya kunna ya ce ""Your excellency zo ki ga wani abu""" """Wanke-wanke zan yi na ɗora abincin dare""" """Karki damu, zan yi mana takeaway""" """Sai dai idan zaka yi wanke-wanken""" "Abdul ya ce ""Na ji zan yi""" "Ta ƙaraso ta zauna, ya rungumeta a jikinsa, sannan ya buɗo wani form ya ce ""Kin san na menene" "wannan?""" """No""" """Form ɗinki ne na makaranta""" "Ta kalleshi ta ce ""Makarnta kuma?""" "Ya ce ""Eh mana, ko ba kya so?""" """Ina so, amma gida zaka mayar da ni?""" """Eh, zaki je ki ga gida, daga nan sai school, boarding ce, mai kyan gaske, saboda sonake ki nutsu ki yi karatu da kyau, yadda babu wanda ya ganki, balle yayi miki gori, da kin gama karatu kuma, ƙasar waje zaki tafi jami'a, shiyasa nake tambayar ki me ki ke son zama, na biya komai, na yi rubutu, yadda ko bayan raina ba zaki tozarta ba in sha Allah, ko bana raye karatunki ba zai tsaya" "ba sai kin kammala in sha Allah""" """Yar uban wace ni da zaka yi mini duk wannan hidimar haka?""" """Ba yar kowa ba ce, amma komai zan yi miki, ba zai kai nauyin laifin da nayi miki ba, ba zai biya" "budurcinki da na karɓa ta ƙarfin tsiya ba, da kuma rashin darajar da naje gidanku nayi ba, ba zan gaji da cigaba da neman afuwar ki ba rahama"" ta sunkuyar da kai ta yi shiru, hawaye na zubowa" daga idanunta. "Ya saka hannu yana share mata hawayenta ya ce ""Ki yi haƙuri, na san na cutar da ke, dan Allah ki yafe mini rahama, soyayyar nan kawai da Allah ya jarabbe ni da ita, ta isheni, baki san tarin ƙ alubalen da yake a gabana nake ta ƙoƙarin karewa a waje ba, amma dai ki yi haƙuri dan Allah"" a" "hankali ta zare hannunta daga nasa, ta tashi ta bar falon tana kuka." *** "Nabila kuwa da file ɗin Viper ta tafi gida, ta kai shi ɗakinta, ta cigaba da duba shi daki-daki, tana picking ɗin kurakuran da aka tafka a cikin shari'ar ta sa. Kai da ganin fasalin shari'ar ka san cewa cike take da mugunta da zunzurutun zalunci." "Zafi ne ya isheta, babu wuta, ga solar sai ƙara take yi, kasancewar ranar ba ayi rana sosai ba." "Ta ɗaukko system ɗin ta, da wayoyinta, ta fita gareji, ta shimfiɗa sallaya, da kayan ciye-ciyenta," ta zauna ta cigaba da aikinta. "Nasir ne ya fito yana waya, ba ta san da wa yake yin waya ba, sai dai yanayin yadda ya fito yana" "wayar, bai san tana wurin ba." """Eh dan Allah, duk yadda za ayi a samo mana hotunansa, ko guda ɗaya ne, nima na daɗe da wannan tunanin, ban aiwatar ba, amma a yanzu naga hakan ne kawai mafita, a samo hoton nasa, dan IG ya kira ni ɗazu, shi kansa distinguish sai da ya kira ni, ni duk na ruɗe, nayi mamakin yadda aka yi mutum ɗaya ya gagari hukuma. Duk wata hanya da na bi da zan sameshi, sai ta kuɓ" uce mini. "Shiru ya yi, lokacin da ya lura da ita a wurin a zaune, ya ƙarƙare wayar ya saka a aljihunsa." """Dama har zuwa yanzu baka taɓa ganinsa ba, baka san kamaninsa ba?""" """Eh"" ya bata amsa a taƙaice." """Hmm""" """Ko zaki bani hoton nasa ne?""" """Ni a su wa?""" """Ke a 'yar kankamba mana, samunki da hotonsa ai ba abun mamaki bane ba""" "Nabila ta yi murmushi, kawai ta cigaba da aikin da yake gabanta." **** "Mutumin da yake zaune a cikin ofishin sa, ya kalli P.A ɗin Indabo ya ce ""Ɗan sake duba na da" "kyau mana malam""" "P.A ya ce ""Na kalleka""" """Shekaru huɗu rak idan Allah ya bani aron rai, suka rage mini nayi retire, a tarihin aikina, ban taɓa karɓar cin hanci na aikata son zuciya ba, ban ƙi ba wasu lokutan ina karɓa in yi abun da ya dace, duk da hakan ma saɓa doka ne. Ba za a haɗa kai da ni ayi rashin albarka ba, a tozarta harkar shari'a ba, idan na ci amana na tsayawa ƙarya a duniya, wa zai tsaya ni a kotun Allah idan zai yi mini hisabi, a cikin kai da uban gidanka, waye zai ƙwace ni? Tambayarka nake yi, na ce waye zai ƙwace ni? Kotun Allah saɓanin tunanin ɗan Adam ce, kuma wallahi dukkanin mu, sai mun tsaya a wannan kotun, kotun da bata buƙatar lauya, ɗan sanda balle ka yi tunanin bayar da cin hanci." "Duk da na san badaƙalar da ake tafkawa a cikin harkar shari'a, na yi mamakin wasu abubuwan da yarinyar nan ta din ga faɗa, yar cikina ce amma ina sauraron programs ɗin ta, kuma ko kaɗan ban ji haushin yadda take tsigalewa aikinmu ba, yadda ake amfani da mu, ake aikata abun da ake so. Babu wani rashawa da zaku bani na karɓa, zan yi abun da ya dace ne kawai, idan kuma aka sake zan yi abun da rai zai ɓaci. Kai in taƙaice maka doguwar magana zuwa gajera, daga sama aka yi mini magana a kan lallai nayi abun da ya dace a kan shari'ar nan, ba a buƙatar kuskure a ciki," "kuma ko ba haka ba, ni sonake na gama aiki na ajiye shi lafiya""" "P.A ya jinjina kai ya miƙe tsaye, ya ce ""Hakan ma babu laifi, muna godiya sosai"" ya juya ya fita" daga office ɗin. *** "Missed call kusan uku Nabila ta yi wa Viper, amma bai ɗaga ba, sai da ranta ya sosu, ta rasa irin wannan murɗaɗɗen hali nasa, gashi ko zata yi fushi da shi, na ɗan lokaci ne, ana jimawa ta manta." "Viper kuma fitowar sa kenan daga wanka, ya kalli wayarsa ya ga missed calls ɗin ta, har guda" uku. "Bai kula ba, ya fara ƙoƙarin neman kayan da zai saka, wayar Walid ta far ringing." "Walid ya ɗaga yayi sallama, ta amsa ta ce ""Oga walid barka da wannan lokaci""" """Yauwwa barkanmu barrister, ya aiki ya jama'a""" """Alhamdilillah, ina ta kiran Viper ya ƙi ɗagawa, wai ni ko wani laifin nayi masa ya tsane har" "haka ne?"" Walid ya kalli Viper, sannan ya ce ""Wanka yake yi yanzu ya fito""" "Ta ce ""Ai dama kai kare shi zaka yi, baka taɓa yadda yayi laifi, ko yayi laifin sai ka kare shi, dama" "magana nake son mu yi da shi, kuma na ma fasa barshi kawai, sai anjima""" "Da sauri Walid ya ce ""A'a ba za a bari ba, ko na haɗa ki da shi?""" """Ba zai kulani ba ai na sani, shiru zai yi mini kamar kurma, in dai yana lafiya shikenan sai anjima""" """Kin ga Nabila, tsaya ki ji mana, gaba ɗaya ke ce baki fahimci Al'amin ba, ba wulaƙanta ki yake" "yi ba""" """Ba wulaƙanta ni yake yi ba kace? Idan ba wulaƙanci ba, mai zai sanya ya ce baya so na, wallahi ban taɓa cewa ina son wani ba, ina zaman zamana, ƙaddara da rashin ya ja ni ya kai ni har in da yake, yayi ta wulaƙanta ni bai damu da rayuwata ba, amma ko haushi bana ji naƙi zuciya, ko kwana biyu nayi ban ji ɗuriyarsa ba sai na damu"" ta ƙarasa maganar cikin damuwa, da alama" abun ya na damunta sosai da sosai. """No, Viper mutumin kirki ne, kuma abun so, in dai ka zauna da shi zaka so shi, saboda yana da halaye masu kyau sosai da sosai, kina kallon muma da muke tare da shi, wasu lokutan haka yake" "yi mana, amma muna duba halaccinsa a garemu ne, kema baki fahimce shi bane""" """Ba wani ban fahimce shi ba, kalli yadda na shiga siraɗin gobarar nan, na zo nayi hatsari, amma" "sannu kawai ba wani abu ba, ya kasa ce mini""" "Walid ya ce ""Ki yi haƙuri, halinsa ne a haka, amma zan iya ce miki, bayan iyayenki, akwai wanda" "ya kai shi shiga damuwar abun da ya faru da ke""" """A hakan? In kusa rasa raina har karo biyu?"" Babu tsammani Viper ya fizge wayar hannun Walid, ya kashe ya dire masa ita, ya fice. Walid ya bishi da kallo yana kallon ikon Allah, shi bai" "rarrasheta ba, kuma ya hana a rarrasheta." "Ko da ya fice daga gidan, wayarsa yake kallo, yana jin tamkar ya kirata, har ya ɗaga ya kalli lambarta, sai kuma ya tsaya ya cigaba da kallon lambar, fasawa yai kawai ya mayar da wayar" aljihunsa ya yi gaba. *** """Arfa, wai meyake damunki ne duk kin wani rame kin tsotse"" Sumayya ta yi maganar tana ƙare mata kallo." "Baba magajiya ta ce ""Gara dai ki yi mata, ko ta ji, taƙi gaya mini meyake damunta, sun samu saɓ ani da babanta, kuma sun shirya, amma kwanan nan sai ƙarewa take yi kamar kuɗin guzuri, ko abincin kirki ba ta ci, duk ta zube sai uban nono da take kayansa kamar ya rinjayeta"" Sumayya ta ƙyalƙyale da dariya ta ce ""Wallahi kuwa baba magajiya, da 'yar ƙibarta tafi kyau, haba jarumar mu, idan ki ka saka damuwa a ranki, mu wa zai bamu ƙwarin gwiwar? Muje mu zanta na ji" "menene ya faru""." "Suka tafi ɗakin Nabila, Nabila ta zauna a gefen gado, sumayya ma ta zauna ta ce ""Gaya mini" "menene? Naji baba magajiya ta ce kun yi faɗa da Abba, me ki ka yi?""" "Ta kalli sumayya ta ce ""Sumayya haka soyayya take dama?""" """Soyayya kuma, ita ta hana ki cin abincin ki ke ramewa?""" "Ta girgiza kai ta ce ""Ba ita ta hana ni cin abinci ba, damuwoyi ne kashi-kashi suka sha mini kai sumayya." "Da fari nifa zuciyata na azalzalata a kan son ganin mahaifina, ina son sanin waye shi, ko yaya" "yake a bani dama na san shi, ni zan fara bincike ta ƙarƙashin ƙasa da kaina""" """A'a Nabila, kar Abba ya sani ransa ya ɓaci""" """Sumayya ya zan yi, ni ba na son na mutu ban san babana ba, idan a gidan babana nake, wani" "abun ba za ayi mini shi ba""" """Naji, zamu dawo kan wannan batun, naji kina maganar soyayya""" "Ta numfasa ta ce ""Ƙaddara ta kaini ta baro sumayya""" "Sumayya ta waro ido ta ce ""Kamar yaya?""" """Son abun da ba zan samu ba nake yi""" """A'a kar ki ce haka, amma wa ki ke so ɗin tukuna ma dai""" "Nabila ta tashi, ta saka key, ta buɗe wardrobe ɗin ta, ta ɗaukko file ta zo ta ajiye a gaban" Sumayya. "Sumayya ta ɗauka ta fara bubbuɗewa, ta tsaya ta gama dubawa sannan ta kalli Nabila cikin" "matsananciyar kiɗima da tashin hankali ta ce ""Ban gane me ki ke nufi ba haryanzu Nabila""" "Nabila ta goge hawayen da ya gangaro mata, ta sunkuyar da kanta ƙasa." "Ta daki kafaɗar Nabila ta ce ""Kin san in da mutumin nan yake, da gaske haɗuwa ku ka cigaba da" "yi da shi, har ki fara son ɗan daba?""" """Ɗaga murya zaki yi, ki tona mini asiri Sumayya""" """Nabila wannan hauka ne, ga yaya Nasir a cikin gida, yana ta haƙilo yana fama, ko ɗazu an kawo mana sanarwa, yan sanda na cigaba da nemansa ruwa a jallo, duk wanda ya nuna in da yake, ko in da za a same shi, akwai kyauta, kawai ki ke zuwa in da yake, idan aka kama da ke fa? Menene sunanki bayan mun gama fitowa duniya muna ɓaɓatu da nuna mu masu goyon bayan gaskiya" "ne?""" """Ban damu da abun da duniya za ta ce ba, ko yadda za a kalleni ba, zan tsaya a bayan gaskiya ne" "duk rintsi duk wahala. Sumayya zan tsayawa Aminu Viper, kuma kamar yadda ki ka faɗa tabbas ina haɗuwa da Viper, kuma na san in da yake, amma ba zan taɓa bari hukuma ta kama shi ba""" "Sumayya ta ce ""Innalillahi wa Innalillahi raji'un, wace lalacewar ce ta same ki har haka Nabila?" "Kina ya mace, ki ke zuwa wurin ɗan daba mashayi, dan ta'adda?""" "Ta girgiza kai ta ce ""Sumayya ƙaddara ce, kamar yadda na gaya miki da farko, idan zaki rufa mini asiri ne shikenan, idan kuma tona mini asiri zaki yi, kina da zaɓin yin wanda ya dace"". Ta tashi ta" "nufi wardrobe ɗin ta, ta mayar da file ɗin." """Kai!! Nabila ki canza tunani, ni ba zan bari ki cutar da kanki, ina kallonki ba""" """Ai ba gaya miki na yi, dan ki bani shawara ba, na riga na yanke abun da nake ganin shi ne" "dai-dai""" "Sumayya ta ɗauki jakarta ta fice, tana zare idanunta, dan tabattar da ba mafarki take yi ba, dan" bata taɓa tsammanin wauta da haukan Nabila ya kai wannan limit ɗin ba. "Bayan tafiyarta, Nabila ta duba wayarta, ta ga announcement ɗin jami'an tsaro, ta ɗauki, jakarta" "ta saka kayanta, ta faki ido ta fice daga gidan." "Sumayya kamar za ta yi kuka, ta marairaice a waya ta ce ""Sir dan Allah ka yi wani abu a kai," "rayuwarta zata shiga cikin hatsari da matsala, za ayi mata kallon mutuniyar banza, ɗan ta'adda take shirin kasadar karewa""" "Yayi murmushi ya ce ""Sumayya ƙawarki ba ta ji, bar ta ai ɗaukaka take nema, mu yi mata fatan" "nasara""" """A'a sir, dan Allah ba zata iya ba""" "Kankarofi ya ce ""Haka ta ce miki? She can do it, ni na bayar da file ɗin sa aka kai mata, ki ja da baya ki tayata da addu'a, in da ki ka ga ana buƙatar taimakona kuma, ki yi mini magana kar ki yi" "ƙoƙarin dakatar da ita, wannan gargaɗi nake yi miki"" ya kashe wayar." "Sumayya ta ce 'Naga ta ta kaina ni sumayya""" *** "Suna zazzaune a ɗakin, suna ta shan sigari, ya ɗaga kai kawai ya ganta a tsaye a ƙofar ɗakin, tana kallonsu, ko sallamarta bai ji ba." "Ta rame sosai da sosai, duk da fuskarta kawai ake iya gani, saboda facemask." "Ganin ya tsareta da nasa idanun, ya sanya ta sunkuyar da kai, waiwayawa su Walid suka yi, su ga" "me yake kallo, suka ga Nabila a tsaye." "Liti ya ce ""Su 'yar anace ce da yamaccin nan ashe""" "Walid ya ce ""Afuwan barrister, kin zo mun cika wurin da hayaƙi, gashi ke ba kya son hayaƙi""" "Viper ya yinƙura ya tashi, ya ce ""Ki tsaya karki shigo, ki zo kina sumewa mutane sai an ta" "jagwalgwala ki"" yayi maganar yana nufota, sai da ya tunkarota sosai, sannan ta lura rigar jikinsa sunansa ne a jiki, an rubuta Viper, da zanen kan macijiya a jiki ta fito da harshenta." "Ya fito ya tsaya, yayi crossing lega ɗin sa, irin ina saurarenki." "Banza tayi masa ita ma, suka cigaba da tsayuwa, sai dai tsayuwar bata damunsa, ita kuwa ta fara" "gajiya, yana zuƙar sigarinsa, yana fesarwa a gefe." "Hannunsa ta kalla ta zare sauran sigarin ta yar a ƙasa, ya kalleta amma ta haɗe rai." """Ina jinki ya aka yi?""" """Alhaji mu'azzam da ku ka haɗu, dama ka san shi ne?""" """Haka ya ce miki?""" """A'a, tambayarka kawai nake""" """Ki bar maganar sa kawai""" """Saboda me?""" "Ya ce ""Saboda haka na ce""" """Nifa ina tsoron sai na je gaban kotu, in tarar da wasu abubuwa da ban san da su ba, na rasa yadda" "zan ɓullowa lamarin, ka gaya mini shi menene alaƙarka da shi?""." "A hasale ya ce ""Na ce ki bar maganarsa ko? Na san shi, amma sanin waye shi ɗin ba shi da wani" "amfani""." """Shhhh ka daina yi mini shouting, ka yi shiru ka saurare ni, aikina nake yi malam"" tayi maganar" tana kallon ƙwayar idon Viper. Ayshercool 08081012143 ₦500 ne via 0009450228 Aisha Adam jaiz bank sai shaidar biya ta 08081012143 Wanda za su jira document 1K ne. 90009343 'Yan Nijar ku turo katin airtel na 300fcfa Arewabooks ayshercool7724 "*Ina ma'abota bibiyar litattafan bright pens, ƙarƙashin mikiya writers association, marubutan da suka kawo muku CUTARWA, MUNAFUKIN MIJI, YI WA KAI, A first batch ga second batch, Ƙ ARFE A WUTA, MUTALLAB ya fara zuwar muku da na sa saloz sai kuma ZAYTOON DA HADARIN GABAS NA NAN TAFE SUMA A CIKIN WANNAN WATAN, KAR KU BARI A" BAKU LABARI. "Waro ido suka yi waje, jin abun da Nabila ta yi wa Viper, liti ya doko tsalle yana faɗin ""Ke! Saken" "da ki ka samu har ya kai haka, mai zamanin ki ke yi wa tsawa?""" """Nayi ɗin, kai kuma a suwa?"" Tayi maganar cike da son huce takaicinta a kan liti." "Walid ya yinƙuro ya fito, amma Viper tuni ya danƙi ƙeyar Nabila, Walid ya yinƙuro, amma Viper" "ya ɗaga masa hannu, ya yi waje da Nabila." "Sai da ya yi nisa da ita, sannan ya saki ƙeyarta, ta ja da baya, tana ƙifta idanu." "Ya taka a hankali ya ƙarasa gabanta, ya tsaya ya kalleta ya ce ""Ni ki ke wa tsawa a gaban jama'a" "ko?""" "Ta sunkuyar da kai, tana yamutsa fuska tare da tura baki." """Karki yi ƙoƙarin tsallake iyaka, ki kaini bango, idan na yi magana bana son jayayya, ki ƙyale wannan maganar, ki tafi da id card ɗinki zan tura miki adress ɗin da zaki je, a asibiti ne kiga" "shaidan da nake da shi, wato madaki." "Ta ɗago ta kalleshi ta ce ""Kai ba zaka je ba?""" "Ya girgiza kai ya ce ""Tsoro nake ji, na samu labarin yayanki ya ƙara tsananta nemana kar ya" "kamani""" "Nabila ta ce ""Hotonka yake nema, ya ce a samo masa hotunanka, ina tunanin hotunanka za ayi" "sharing ace ana nemanka""" "Ya ce ""Duk neman da yake yi mini ma bai sanni ba, a confused blind man"" yayi maganar tare da" "yin murmushi. Sai da ta kuma kallonsa, ganin yana murmushi, murmushin ma a nutse yake yi." "Kallonta da ya yi, ya sanya ta daina kallonsa, ya ce ""Amm kwanaki, kamar akwai maganar da ki" "ke son ki yi mini, something like wani abu yana damunki""" """Baka tambaye ni a lokacin ba sai yanzu, ka manta ba wani abu bane, ya wuce"" tayi maganar cikin" "tsiwa, tana kawar da kanta gefe." "Kallonta yayi, bai ce uffan ba, ya zira hannu a aljihunsa, ya ciro wayarsa, ya danna ya saka a" "kunnensa, ya ce ""Kawo mini abun nan, na ƙasan katifata, ina wajen bishiyar kalgon nan""" "Shiru ya wanzu a tsakaninsu, sai ga ɗan mama ya ƙaraso, ya miƙawa Viper envelope, ya saka" "hannu ya karɓa ya ce ""Zaka iya tafiya""" "Ya kalli Nabila ya ce ""Gashi, wani abu ne daga aikinki ne na fara biyanki wani abu, idan komai ya" "kammala, in sha Allah zan yi miki kyakykyawan biya""" "Ta karɓi envelope ɗin ta jujjuyata, ta saƙala masa a hannunsa ta ce ""Da dan kuɗi zan yi maka aikin nan, da ba zan yi shi ba, bana buƙatar kuɗinka, a wurin Allah nake neman ladan abun da zan" "yi maka, ba wai dan halinka ba""" "Shi ma ya jujjuya envelope ɗin, ya ce ""Rashin sani, ya fi dare duhu, abun da yake ciki yafi kuɗi" "muhimmanci a wurinki, zaki dawo ki nema da kanki, shikenan a sauka lafiya""" "Ta shagwaɓe fuska tana kallonsa, shi ma ita yake kallo, ji yake kamar ya tambayeta me yake" "damunta, ta rame, amma ya kasa." """Kayi haƙuri""" """Da me?""" """Kayi haƙuri ka bani""" "Ya zira aljihunsa ya ce ""Ai kuma kin yi wa kanki, maganin mara kunya, wuce ki tafi gida, kan a" "fara nemanki""" "Ta sake marairaicewa ta ce ""Dan Allah""" "Viper ya ce ""Kar ki ɓata mini rai, wuce ki tafi""" """Korata ka ke yi ko? Dan Allah meyasa ka tsane ni ne? Me nayi maka?, Kalli duk rashin lafiyar" "nan da nayi, ko sannu fa Viper, sannu kawai baka iya yi mini ba, abun yayi mini zafi fa""" """Really?""" "Ta haɗiye wani abu mai ɗaci, ta gyaɗa kai ta ce ""Shikenan, bari na tafi, in sha Allah zan yi duk" "abun da ya dace"" ta juya zata tafi ya ce ""Amm meye ma sunan naki? Abla ko?"" Ta waiwayo ta kalleshi, ta fara tunanin a ina ma aka taɓa kiranta da wannan sunan?." "Ta girgiza kai ta ce ""A'a Nabila""" """Ohh, sunan yayi mini tsayi, just accept it Abla""" "Kamar ba yanzu ya gama yi mata wulaƙanci ba, ta ce ""Nice one, na gode sosai"" tayi maganar tana" ɗaga masa hannu. *** """Hello, Salim kana ina ne?""" """Bokan turai, ya aka yi ne?""" """Dan Allah gida nake son ka samo mini""" "Salim ya ce ""Gida kuma?""" """Eh salim, amma ba na son kowa ya sani, a wajen gari kuma, saboda na san daddy zai saka a fara" "bibiyata, sun dage lallai sai sun gano in da rahama take""." """To kai yanzu hakan da ka ke yi kana ganin shi ne dai-dai?""" "Abdul ya ce ""Shi ne, dole zan danƙata a wurin iyayenta, na kai ta makaranta kafin su san in da" "take""" """Abdul, ina tsoron abun da zai biyo bayan abun da kake yi ne?""" """Salim, rayuwar rahama nake ƙoƙarin karewa da ingantanwa, dan Allah ka taimaka mini, kar a" "kuma cutar da yarinyar nan a wannan karon""" """Shikenan, babu damuwa za a duba in sha Allah""" """And sirri ne Please, ko saif ba na son ya sani""" """Haba mutumina, ba sai ka jaddada mini ba, you are safe""" """Thank you""" *** "Kankarofi yana zaune a kan gadonsa, yana daddana wayarsa, ya ci karo da lambar Hafsat. Ya yi shiru yana kallon lambar ta ta, ya shafi saman lambar yana tuno ta, yarinyar ta nuna masa so," "kuma shi kansa ya san ba dan yana son ta ya aureta ba, amma beside his wealth, ta so shi, ta yi iya" "ƙoƙarin ta a kansa, amma ya kasa sakewa da ita, yayi mata adalci, har auren ya mutu." "Amma ita jidda bai ji haka a kanta ba, hasali ma sosai suke gogawa ita da Safiyya, duk da dama Jidda tsohuwar budurwarsa ce, lokacin tun suna jam'iyya ɗaya da Indabo, kuma za su yi sa'anni da Safiyya, ita kuwa hafsa yarinya ce dama. Ya ji ciwon rashin samun auren jauhar da bai yi ba, amma duk da haka yana yi wa Allah godiya, da ba jauhar ya aura ta wahala suka rabu ba." "Shiyasa ko zai ƙarar da duk abun da ya mallaka, sai ya tabattar da indabo ya girbi abun da ya shuka, ba ƙanwarsa yake aure ba, ko babarsa yake aure, bai ji zai iya ɗaga masa ƙafa ba, kisan" "mummuƙe zai yi masa, kamar yadda shima indabon yake yi." "Jidda ta ce ta shigo ɗakin, sanye cikin doguwar riga, ta ƙarasa ta zauna a kusa da shi, ya ce ""Ya" "dai?""" "Ta yi guntun tsaki ta ce ""Nifa gaskiya na gaji""" """Da me?""" """Haryanzu ana yi mini sintiri a kan rashin mutuncin da Abdul yayi, yau wannan ya zo, gobe wancan ya zo, duk security ɗin nan, gaskiya ni kawai ka canza mini gida, mu bar estate ɗin nan," "na gaji wallahi""" """Mu bar estate ɗin nan, amma ɗaya gidan kin san na sister ɗinki ne, a nan suke zama idan sun zo" "hutu""" """So find another one mana, am tired hell of all this, abu yaƙi ci yaƙi cinyewa, tun da abun ya faru ban sake ganin Abdul ba, ga babarsa ta kira ni tana nema ta gaggaya mini magana, wallahi rashin ramma a gidan nan, gaba ɗaya bana samun komai yadda nake so, khalifa da ansar haryanzu suna tambayata, yaushe yarinyar nan zata dawo, sun saba da ita, Abdul yayi mini hauka wallahi "" har ta" "gama surutanta, murmushi kawai Alhaji mu'azzam yake yi, bai ce mata uffan ba." *** """Hello Ambassador Tahir Arabi""" """Distinguish, ya aiki ya Nigeria?""" """Alhamdilillah""" """Masha Allah, dama maganar yaron nan ne""" "Indabo ya ce ""Na wurina? Jafar?""" "Amb Tahir ya ce ""Eh shi, wallahi distinguish sai haƙuri, sun bawa America shi, kuma yana daf da" "fara fuskantar shari'a, kuma na lura babu wani abu da embassy ɗin mu zasu iya yi a kai, duk da dai haryanzu muna cigaba da ƙoƙari""" "Indabo ya ce ""Innalillahi wa Innalillahi raji'un, Ambassador ba wani abu da za a iya fa ka ce?""" """Wallahi kuwa, ka san kisan kai yayi a amurka ya gudu Mexico ya cigaba da harkar ƙwayoyi da hodar iblis tsakanin Nigeria da mexico, yadda aka shirya kama shi, akwai ƙwarewa sosai da sosai, bisa ga wata yarjejeniya da haryanzu bamu san ta mecece ba tsakanin Amurka da mexico suka" "basu shi, wataƙila musayar fursunoni suka yi""" "Jiki a sanyaye Indabo ya ce ""Na gode sosai da sosai""" Ya katse wayar ya dafe goshinsa ya rasa abun da yake yi masa daɗi. ***** "Da daddare Nabila na kwance, tana ta tattara bayanai a kan shari'ar Viper, sai ƙarfe ɗaya na dare," sannan ta samu sukunin kwanciya. "Ta janyo wayarta, tana duddubawa, ta ga lambar Viper, kawai ta danna kira." Bisa ga mamakinta kawai ta ji ya ɗaga. "Ta ce ""Viper""" """Mmm""" """Ba ka yi bacci ba?""" """Mmm""" "Tayi murmushi ta ce ""Me ka ke yi ba ka yi bacci ba?""" "Muryarsa ƙasa-ƙasa kamar mai jin baccin ya ce ""Abun da ya hanaki bacci ne hana ni""" "Ta ce ""Wai ni? Ai ni soyayya ce ta hana bacci"" tayi maganar tana murmushi." "Viper ya ce ""Nima haka, tunani da kewar matata ne ya hana ni bacci""" """Ai addu'a zaka yi mata""" """Ina yi mata, zafi ya dame ni, ina missing fankata"" yayi maganar very serious yana lumshe" idanunsa. "Nabila ta ce ""Fanka? Wace irin fanka kuma?" "Ya ce ""Fankar solar ce, iskarta daidai ba mai cutarwa ba""" "Nabila ta ce ""To ko sayo fankar za ayi, ban zaci ana zafi a wurin nan ba ai""" """A'a nikaɗai nake jin zafin ai""" "Tayi dariya ta ce ""Ko ƙiba ka yi ne? Zan sayo maka fanka in sha Allah""" "Viper ya ce ""Ki ƙyale maganar fankar nan, ba ki da kuɗin sayenta, ba irin wadda nake buƙata zaki" "saya ba"" yayi maganar yana juyi tare da gyara kwanciyar sa." """Ka gaya mini, zan sai maka in sha Allah, wace iri ka ke so i promise""" "Ya ce ""Ba zaki iya sayenta ba""" """Ka gaya mini, zan nemota in sha Allah""" "Viper ya ce ""Ita fankar?""" """Eh mana""" "Kawai ta ji yana dariya, har da gyaran murya." """Kai, dama kana dariya?"" Tayi maganar tana tashi zaune." Yayi shiru bai ce komai ba. """Viper""" """Mmm""" """Dan Allah me ka bani a envelope ka ce zan dawo ina nema da kaina?""" """Ki manta, ya wuce kawai, zan baki address ɗin nan, ki je ki samu mutumin nan""" "Tayi ajiyar zuciya ta ce ""To, kayi bacci mai daɗi""" """Zafi ya dame ni, ba zan iya bacci ba""" "Ta ce ""Ka tashi liti yayi maka fifita""" """Na gaya miki fanka nake so ai, sai da safe""" """Ai ka ƙi gaya mini wace iri ce, dan dai fanka sai na saya maka, shikenan yau na ci pass an yi" "mini dariya""" """Hmm"" kawai ya ce." "Ta sake cewa ""Viper""" """Kar sunan ya ƙare""" "Tayi murmushi ta ce ""Sunan daɗin faɗa, Viper, in shot kuma V.Snake"" ta faɗa tana murmushi." "Ta sake cewa ""Wai a ina aka yi maka rigar nan, nima ina so""" """Wacce?""" """Wadda aka rubuta sunanka a jiki""" """Nawa zaki saya?"" Gyara zama tayi, jin yana kulata yau." """Ayi mata kuɗi, zan saya ko nawa ce, ka san wani abu, idan Allah ya sa muka yi wining a court," "rigar nan zan saka in yi ta yawo ina murna""" """To, Allah ya bamu sa'a""" """Amin V snake""" "Wasu lokutan simple da shi, wasu lokutan kuwa, sai ka rasa gane kansa gaba ɗaya." "Ta ce ""Sai da safe""" """Hmm"" kawai ya ce, ta katse kiran." *** "Sanarwa ko ta ina, a kan tsananta neman Al'amin Viper, tare da alƙawarin kyauta mai tsoka ga duk wanda ya nuna ko ya bayar da information a kan in da za a same shi." "Nabila ta damu sosai, ga Sumayya ta daina ɗaga wayarta, dan haka ta shirya tsaf, ta tafi wurin" aikin sumayya. "Sumayya na ganinta ta haɗe rai, Nabila ba ta yi fushi ba ta ƙarasa in da take ta ce ""Sumayya ba" "kya ɗaga wayata meyasa?""" """Ban sani ba, na gaji da wahalar da ki ke saka mu ne, babu dalili Nabila, daga wannan sai wancan?" "Gaba ɗaya kin hanamu nutsuwa da sukuni, ki jijjigo mana wannan masifa muna zaune, wane irin kallo ki ke so ayi miki, idan aka ga kin koma bawa ɗan ta'adda kariya, hukumar yan sanda na" "nemansa ruwa a jallo, ke kina tare da shi""" """Sumayya, baki yi mamakin yadda na sauya lokaci guda ba? Har kin manta huci da haƙilon da nake yi a kan a kama shi, kwatsam ki ji na koma na ce zan tsaya masa na bashi kariya, ayar" "tambaya yakamata ki fara saka mini, meyafaru?""" "Sumayya ta ce ""Ba wani in tambayi meyafaru, kawai ki cire kanki daga wannan sabgar""" "Nabila ta ce ""Wallahi ba zan ajiye ba, ko me za ayi mini"" kawai ta saki baki tana kallon Nabila." """Ko dai ki tayani a wannan karon ma, ko kuma ki ƙyale ni ki zuba mini ido, yanzu ya maganar" "program""" "Sumayya ta ce ""Mhmm yana nan, Nabila ni yanzu kin daina bani mamaki tsoro ki ke bani, yanzu" "duk bala'in nan, kin san in da Viper yake""" """Ƙwarai ki gaya wa uban kowa da ki ke so masoyiyya""" """To, Allah ya taimaka""" """Amin, gama mu tafi ki rakani wani wuri""" "Sumayya ta ce ""A'a ba zaki kai ni in da za a kashe ni ba""" "Nabila ta ce ""Wane irin kashe ki kuma, mu je dan Allah""" """To ki tsaya na kammala abun da nake yi, sai mu tafi""" "Ta kammala abun da take yi, suka fita, tare da sumayya." "Tiryan-tiryan suna tafe, har ƙofar ɗakin da Viper ya rubuto mata, wasu masu sanye da kaki, suka" "tarar a ƙofar ɗakin a tsaye, Nabila suka gaisa, ta ciro id card ta nuna musu." "Suka ce ta shiga, amma ban da sumayya, Nabila ta ce ""Ita ma ma'aikaciya ce, yar jarida ce""" "Suka ce ""A'a kekaɗai aka ce mu bari ki shiga""." "Sumayya ta ce ""Ba damuwa, zan jira ki a nan""" "Nabila ta shiga, ta yi sallama ta tarar da mutum a zaune a kan gado, hannunsa ɗaya an saka masa" "sarƙa, ƙafarsa kuma ɗaya an yanke ta." "Ta ƙarasa gaban gadon, ta ja kujera ta zauna, ta kalleshi ta ce ""Sannu malam""" "Ya ce ""Yauwwa""" "Ta ciro id card ta nuna masa ta ce ""Sunana barrister Nabila, na zo ne a kan case ɗinka da Al'amin" mai zamani. Ya ɗago ya kalli Nabila amma bai yi magana ba. """Ka yi magana, dan ka sauƙaƙa wa shari'a, me ka sani game da kisan da aka yi wa matar mai zamani?""ya yi shiru ya ƙi magana." "Tayi tayi, amma yaƙi cewa komai, ƙarshe haka ta fito bai yi magana ba." "Sumayya suna ta hira da security ɗin wurin, Nabila ta fito, tana ganin Nabila ta tashi ta ce ""Kin" "gama?""" "Nabila ta ce ""Eh mu tafi""" "Suna tafe ta kira Viper a waya, ta ce ""Hello V snake""" """Barrister""" """Naje wurin gayen nan, amma yaƙi magana, nayi nayi, yaƙi magana""" "Viper ya ce ""Rabu da shi, zai yi ta ƙarfin tsiya, ki tafi kawai""" """Ok, na ma taho, amma yakamata yayi magana gaskiya, bari na ƙarasa gida sai anjima"" ta kashe" wayar. "Sumayya ta ce ""Nabila wai wurin wa ki ka zo ne?""" """Zan yi miki bayani, amma ba yanzu ba""" "Ta ce ""Ok shikenan""" *** """Rahama kina ji na?""" """Ina jinka""" """Zamu sake barin gidan nan"" ""Zuwa ka mayar da ni gida?""" """Wai na mayar da ke gida ki yi me? Ai kin san iya wuya muna tare, nan zamu bari temporarily," "daga can kuma zan kai ki gida, sai kuma makaranta, a abuja zaki koma da karatu ai""" """Yar ƙauye a Abuja, to ai ban iya turanci ba, ni gaskiya na fi son makarantar garinmu""" "Abdul ya yi dariya ya ce ""Ai Shiyasa zaki je Abujan, zaki iya turanci, kan ki gama ki ƙara gogewa" "ki zama her excellency rahama""" """Taɓ abun ma ba tsari""" """Kamar ya babu tsari?""" """Wata zaka aura ai, kuma ni a lokacin mutane zasu ji daɗin nuna ni suna aibata ni""" "Abdul ya girgiza kai ya ce ""Muna tare, babu wanda zai aibata mini ke""" "Ramma ta yi murmushi ta ce ""Ba zaka iya canza komai ba, ɗabi'ace ta al'ummar hausawa""" "Ya ce ""Shikenan, mu bar maganar""" "Ta ce ""Ya dai fi""" "Wayarsa ya ɗaga, ya ɗan gyara zamansa ya ce ""Na'am Mummy""" """Wato Abdul kafi son ka yi ta sakani a tashin hankali da damuwa ko?""" """Mummy me nayi kuma?""" """Ban sani ba, ka saka babanka yana yi mini kallon ni nake goya maka baya ka ke yi masa rashin ɗ a'a, ka fito da yarinyar nan ka huta su huta ka ƙi, rashin mutuncinka har ya kai ka ajiye mace kana lalata da ita, bayan na keta mata haddi,, ga ɗan uwanka can an mayar da shi america, sai abun da Allah ya yi, shiyasa ake ta fafutukar ka zama gwamnan nan ko a samu ya fito, amma ka ƙi, ya ka" "ke so na yi Abdul, in bar muku duniyar ka huta ko?""" "Cikin damuwa ya ce ""Mummy ki yi haƙuri dan Allah, ki fahimce ni, ya za ayi na so ki mutu, ba haka bane ba. Wallahi Mumm tsoro nake ji na fito da yarinyar nan, ayi mata wani abu na daban, dan Allah ki yi haƙuri, zan zo gida nayi miki bayani, na san zaki fahimce ni in sha Allah. Kuma" "yaya jafar zai fito in sha Allah, ki yi haƙuri dan Allah""" """Ai shikenan, ka yi abun da ka ke so""" """A'a ba za ayi haka ba, zan zo har gida nayi miki bayani"" ta katse wayar, yayi ajiyar zuciya yana" "lumshe idanunsa ya buɗe yana kallon ramma, da ta yi kamar ba ta jin me yake faɗa a wayar." """Rahama""" """Na'am""" """An sakoni a gaba a kanki""" """An san ka sace ni kenan?""" "Abdul ya ce ""Ke fa ba a abun arziki da ke, ke da ban sace kin ba, da yanzu wani zancen ake ba" "wannan ba""" """Ai ba da kyakywar manufa ka sace ni ba, kashe ni ka ce zaka yi""" """Amma ai ban kashe kin ba ko?"" Tayi masa shiru ta cigaba da aikin ta." **** "Nabila ta fito daga banɗaki, kawai ta tarar da Nasir a tsaye a ɗakinta, ta kalleshi ta ce ""Lafiya?""" "Ya ɗago mata file ɗin Viper da yake hannunsa, ta bar shi a kan gadonta tana aiki, ya faɗo mata ɗ" aki. """Menene wannan?"" Ta ƙarasa gabansa ta saka hannu zata karɓa, ya janye yana sake tambayarta" """Menene wannan Nabila?""" """Babu ruwanka da ko menene, ka bani file ɗina kuma ka daina shigo mini ɗaki ba tare da iznina" "ba""" "Cikin tsawa ya ce ""Ki yi mini bayani kin tsaya kina wasu kame-kame da wasu maganganun banza" "da na wofi""" "Cikin dakewa ta ce ""DSP aikina nake yi, ka fita daga harkata ka bani file ɗina""" """Nabila, ta tabatta goyon bayan ɗan ta'adda ki ke yi?""" """Ni bayan gaskiya nake bi, kawai, ka bani file ɗina""" """Nabila kina haɗuwa da mutumin nan, kin san in da yake""" """Ni ban san in da yake ba, ka bani file ɗina tun ina ganin mutuncinka""" "Shammatarsa tayi, ta kafa masa haƙora a hannunsa, ba shiri ya sakar mata file ɗin, ta kwashe abun ta tayi waje, ya bi ta da kallo, ya kalli hannunsa yadda yake tsatstsafar da jini saboda iya ƙ" arfinta ta cije shi. "Cikin yarfe hannu, ya bi bayanta, sai dai ko sama ko ƙasa ya nemeta ya rasa a cikin gidan nan." "Zuciyar sa ta daɗe tana mamakin abun da ya gani, amma haryanzu ya kasa gazgata cewar Nabila" "tana haɗuwa da Viper, ta san in da yake, amma me zai haɗata da ƙasurgumin ɗan ta'adda haka" "tana ya mace, idan kuwa haka ne, duk hukuncin da doka tayi a kanta shi ba zai ce komai ba, amma ya yanke ya sake tuntuɓar Abba, ya kirata ya ja mata kunne, a lallaɓata a cikin gida idan da abun da ta sani, a sasanta abun, kar asiri ya tonu, dan shi kansa abun kunya ne a gare shi, ace yana can" "yana haƙilon neman ɗan daba, Nabila na zagewa ta haɗu da shi a ɓoye." "Da daddare Nabila na zaune a falon Abba, ga Nasir a gefe, sai kuma shi kansa Abban, tayi shiru ta" sunkuyar da kai fuskarta babu annuri. """Arfa"" Abba ya kira sunanta a kausashe." """Na'am Abba""" """Gaske ne abun da ɗan uwanki ya gaya mini?""" """Abba ai ban san me ya gaya makan ba""" "Abba ya gyara zama ya ce ""Gaske ne, kin san in da wanda yake ta haƙilon nema yake? Nabila" "meye haɗinki da ɗan daba ne? Kina 'ya mace?""" "Ta girgiza kai ta ce ""Abba ya za ayi na haɗu da wanda yan sanda ma suka kasa kamawa, file ɗin shari'arsa kawai ya gani a ɗakina, kuma ba nawa bane ba, na barrister Habib ne, nima karɓa nayi na duba, ina dudduba yadda aka gudanar da shari'ar sa a wancan lokacin ne, an ce yayi shekara biyar a prison ba ayi masa shari'a, kwatsam kuma aka ce an sake shi, aka dawo ana nemansa sai nake jin kamar akwai wani ɓoyayyen lamari, shi ne nake ta bibiya, ka san muna program da sumayya, so ina binciken cases makamantan nasa shi ne kawai, amma sai zargina yake yi, ni ban" "san meyasa ba""" "Abba ya yi ajiyar zuciya ya ce ""To kai ka ji abun da ta ce, me zaka ce?""" "Sam Nasir bai ji ya yarda da abun da Nabilan ta faɗa ba, amma ya ce ""Shikenan Abba, tun da haka" "ta ce""" """Dan Allah ku daina wannan rigingimun, da ba haka kuke ba, naga tare kuke sharing working experience ɗinku, amma yanzu kuna nema ku lalata tsakaninku, ni ban ji dama arfa zata iya bin wani ɗan daba ba, tana ƙyamar irin wannan laifukan, dan haka dan Allah duk ku yi haƙuri Allah" "ya yi muku jagora, ya rufa muku asiri""" "Nabila ce ta fara miƙewa ta amsa da Amin, ta fice tana hararar Nasir, shi kuma ya bi bayanta da" "kallo, sam bai yarda da ita ba." "Washegari aka dawo da motar Nabila, an gyarota fes har fenti an canza mata, ta ji daɗin dawowar" "motar nan, dama yawan zirga-zirgar nan ya isheta." "Ɓangaren sumayya ma, nata program ɗin da take gabatarwa a kan shirin siyasa, na an yi walƙiyya, yana ta jan dubban masu sauraro, sakamakon yadda take baje wa mutane komai, game da irin kuɗ aɗen da gwamantin tarayya take bayarwa domin ayyukan raya ƙasa, ta kan ɗauki ƙananan hukumomin shiyya ɗaya, ta kawo kuɗin da suka samu na wata, na tarayya, na jiha da na ƙanan hukumomin, da iya ayyukan da aka yi musu." "Sai dai tun da ta zo kan na Indabo, a ƙalla tafi sati uku, program ɗin a kansa yake, dan sai da ta faro tun daga farkon tenure sa, yadda take hawa da sauka a kansa, zai tabattar maka akwai wata a ƙasa tsakaninta da shi. Yan siyasa da dama, sun kawo wa program ɗin hari, da neman a dakatar da shi, amma hukumar gudanarwa ta tashar suka tabattar da cewa an riga an biya su ɗaukar nauyin program ɗin, dan haka ba zasu dakatar ba, wanda bai gamsu ba, ko ya ji an yi masa sharri ko cin" "zarafin sa, to ya kai kotu." "Da safe Nabila ta fito da motarta, sai ƙyalli take yi, ta batta a kunne, ta shiga gida ta haɗo kayan" "breakfast ɗin ta, ta koma cikin mota, Viper ya kirata a waya." "Ta ɗaga ta ce ""Hello V snake""" "Cikin dakakkiyar muryarsa ya ce ""Kin fita aiki ne?""" """Ina ƙofar gida ne, yanzu zan tafi ka tayani da addu'a, yau zan kai kokenmi kotu""" "Ya ɗan ja numfashi ya ce ""Ki bi ta farkon layinku, wurin incomplete building ɗin nan, ina nan ina" "jiran ki""" """Ok sir, gani nan""" "Ta ja motar ta ƙarasa in da ya ce mata, a wurin ta tarar da shi, ya tako a hankali, cikin nutsuwa. Ta" zura masa ido tana murmushi ba tare da ta san tana yi ba. "Ya shigo ya rufe ƙofar, ta kalleshi ta ce ""Good morning""" """Morning"" ya amsa ba tare da ya kalleta ba, ya ajiye mata baƙar leda." "Ta ɗauka ta ciro abun ciki, baƙar riga ce, da sunansa a jiki Viper, da hoton maciji." """Wow masha Allah, har an yi mini? Na gode sosai, wai waye yake yi maka rigunan nan?"" Yayi" shiru bai amsa mata ba. "Sai kuma ta ce ""Sanyin Ac yayi maka normal ko na rage?"" Kawai ya jingina da seat ɗin motar ya" zuba mata ido. "Sai ta ɗan rikice ta ce ""Menene? Ko wani abun ne?"" Still bai yi magana ba." "Ji tayi tsigar jikinta na tashi, ta ce ""Dan Allah ka gaya mini menene?""" """Ina jin ƙwarin gwiwa a kan shari'ar nan, wanda ke ki ka bani shi, and at the same time scared, idan rayuwarki ta salwanta saboda ni, ba zan yafe wa kaina ba, dan rayuwar ki kika saka a haɗari" "saboda ni, na zo ne in ce miki good luck""" "Duk da ta takura da kallon da yake yi mata, tamkar ta nutse, ga wata fargaba da bata san ta mecece" "ba, amma ta dake ta ce ""Allah yana tare da mu, in sha Allah zamu yi nasara""" """Allah ya sa, ko mun yi nasara ko bamu yi ba, ina da kyakykyawan tukuici gareki""" """Ni zuciyarka kawai nake so, shi ne tukuicin da nake so"" haɗe rai yayi ya ce ""You are not serious, ba zaki daina wannan shirmen ba ko? Wahala zaki yi ta sha kuwa, ba na kallon kowace mace mace idan ba jauhar ba, ki je ki samu wani ku daidaita"" yayi maganar ba tare da ya kalleta ba, yana ƙoƙ arin buɗe ƙofa ya fita, jikinta har yayi sanyi, idonta ya cika da hawaye"" yayi saurin ficewa, ba tare da ya sake kallonta ba. A guje ta fizgi motar, ta bar wurin, wanda hakan sai da ya bashi dariya, dan" ya san fushi ta yi. "Nabila tana tafe hawaye na zuba daga idanunta, duk ta ɓata kwalliyar ta, sai taga kamar zata yi" "nasara, kawai sai ya buntsure, gashi ita kullum ƙara son sa take yi so mai zafin gaske." "Da haka ta ƙarasa court, ta tsaya ta ƙara gyara fuskarta, sannan ta fita ta shiga cikin court ɗin." "Nabila ta nemi kotu, ta hana hukumar 'yan sanda kama Muhammad Al'amin Ibrahim, da aka fi sani da Viper, har sai an yi cikakken bincike a kan kisan kan da aka yi wa matarsa shekaru biyar da suka gabata, hakazalika yana neman hakkinsa, na tsare shi shekaru biyar ba tare da yi masa shari'a ba, a kan laifin da ba shi ya aikata ba. Ta gabatarwa kotu kwafin shari'ar da aka yi masa a" baya. "Duk da ba ma a fara shari'ar ba, amma haka nan ta din ga jin tamkar ta kama hanyar sauke" gingimemen nauyin da yake kanta. "Abun da Nabila bata sani ba shi ne, tuni aka kira Nasir, aka sanar masa da an ganta da wani, a" "wurin sabbin gine-gine da ake yi a unguwar, kamar yadda ya saka CID ta ko ina a kanta." "Ya shiga kitchen ɗaukar lemo a fridge ya tarar da wayar Nabila a kitchen tana ringing, ita kuma bata kitchen ɗin, ya ƙarasa in da wayar take, kiran ya yanke. Ya kalli wallpaper ɗin ta Hoton" "sunan Viper ne, da maciji a kan wallpaper da wani heart." "Ya saka hannu ya ɗauki wayar, wani kiran ya kuma shigowa." "Kawai ya ɗaga kiran ya saka a kunnensa ya ce ""Waye?""" """Viper ne, mai zamani""" Ayshercool 08081012143 "Albishirinku ma'abota bibiyar litattafan bright pens, kamar yadda ku ka ji daɗin littafin ƙarfe a wuta, to Mutallab ma free pages ya kammala." "*The story of a thug husband MUTALLAB, as a good parents za ku bada auren yarinyarki ga ɗan daba ɗan ta'adda? Ban ce ku fara kuka tun yanzu ba,ban ce ku ji soyayyar ciki kamar a ƙirjinku ake wanzar da ita ba.* *The story of TIGER and MOH The destiny of CAPTAIN and FIYYA." Finally the eternal love* *between..The love that separate them and back them together❤ * Page 15 last free episode For more updates follow Mutallab on Arewabooks in sha Allah ❤ "Page 15 shine last free pages na labarin, kar ka yi tunanin ganin wani page ɗin a waje ka yi payment a yi naka into paid group akan 500 kacal, love ɗin da kuke showing yanzu ne zai yi aiki฀MUTALLAB." "Book 1, 2 &3" 500 Naira 0116886423 Union Bank Na'ima Sulaiman S a tura shaidar biya ta nan 08164069385 'Yan Nijar tsarin biyan zai kasance ta *Stock na airtel*. Ku yi wa wannan layin 84506476 magana sai ta ba ku lambar da za ku turo mata stock ɗin. Kafin ɗorawa da inda muka tsaya zamu ɗauki hutun zango na sati ɗaya tal maybe har a yi albashi ko masu mining ta fashe musu. LAST FREE PAGES Waye Mutallab? Waye Scorpion? Wace Safiyyerh? Waye Daddy? Mene FS WORLD INVESTMENT COMPANY? Labarin Mutallab da tarihinsa ya fi wannan da muke ciki yanzu ai za ku zo jin wannan soyayyar ta ƙuruciya ba? Mene yake saka a fara daba da shaye-shaye? Wanne ganganci iyaye suke yi akan yara? Mece siyasa da cikakken tarihin dimokuraɗiyya? Za ku su sanin ya ake mulki a ƙasar nan? Har ku yi supporting yaran ku? Soyayya na saka shaye-shaye ne ko daba? Me ya sa Mata har uku suka mutu ta sadanadin MOH me ya sa ya kashe matarsa SAFIYYERH? YAUSHE SAFIYYERH TA HAIFI YARO? maza hanzarta yin payment chat with me on WhatsApp 08164069385 BRIGHT PENS... 2ND BATCH Ayshercool 08081012143 ₦500 ne via 0009450228 Aisha Adam jaiz bank sai shaidar biya ta 08081012143 Wanda za su jira document 1K ne. 90009343 'Yan Nijar ku turo katin airtel na 300fcfa Arewabooks ayshercool7724 "Ina ma'abota bibiyar litattafan bright pens, ƙarƙashin mikiya writers association, marubutan da suka kawo muku CUTARWA, MUNAFUKIN MIJI, YI WA KAI, A first batch ga second batch, Ƙ ARFE A WUTA, MUTALLAB ya fara zuwar muku da na sa saloz sai kuma ZAYTOON DA HADARIN GABAS NA NAN TAFE SUMA A CIKIN WANNAN WATAN, KAR KU BARI A" BAKU LABARI. "Cak Nasir ya ƙame, a daidai lokacin da Nabila ta dawo kitchen ɗin." """Wa ka ce?""" """Sarai ka ji abun da na ce, kar na sake kiran waya, ka ɗaga mini, ka bawa mai wayar, zan yi" "magana da lawyer ta""" "Hakan yayi daidai da shigowar Nabila da take tsaye a bayansa, ya waiwayo ya kalleta, ya miƙa" "mata wayar yana tsareta da idanunsa da ya zazzaro su, tamkar zasu faɗo ƙasa." "Ta saka hannu ta karɓi wayar, tayi ƙasa da murya, ta ce ""V ka kashe ni""" """Shhh ki tsaya ki saurare ni""" "Ta ce ""Tom""" """Yaya zaki yi da batun shaidun nan? kin ce gayen nan yaƙi magana, ina so zan je in da yake da" "kaina""" """To ai ka ga ni ban san me ma zan ce ba, ban san wace hukumar ta ce ta kama shi ba, dole yan" "sanda zamu shigarwa koken su kama shi""." """Na fahimta, na san abun da zan yi, dama na zata zai yi magana ne, ki samu wani abun as shaida, amma na san abun da zan yi masa, zai yi magana ta ƙarfin tsiya. And am sorry for what i did, na san zan saka ki a matsala, amma hakan ka iya zama maganin wasu matsalolin naki, dole za a zo wurin nan, cigaba da ɓoye-ɓoye ba zai haifar da ɗa mai ido ba, no matter what it takes, duk tsanani da ƙalubalen da zaki fuskanta ki jure, da Allah na dogara, amma kekaɗai ce ƙwarin" "gwiwa ta, Please don't give up""" """Kar ka damu, in sha Allah I won't, i promise you that""" """Thank you"" ya katse wayar, hankali kwance ta kammala wayar, Nasir ya zuba mata ido, yana jiran ta gama, ya ji wace ƙaryar za ta yi masa, kawai ya ga ta basar, ta cigaba da abun da yake" gabanta. "Da ƙarfin tsiya, ya janyo kafaɗarta ya tsayar da ita tana fuskantar sa, ya ɗaga hannu zai kwaɗa mata mari ya ji muryar Baba magajiya ""A'aaa lalalalaaaaa me zan gani haka, a kul ɗin ka, kar ka kuskura fara me yayi zafi zaka dakar mini 'ya Nasir"" tayi maganar tana nuna shi da yatsa, Nabila" "kuwa da gudu ta gudu ta ɓuya a bayanta, tana ƙifta idanuwa." """Ammm baba magajiya, ki fita daga cikin maganar nan""" """Ban gane in fita daga maganar nan ba, zaka kassara mini ƴa ka ɗaga hannu zaka daketa, ƙarfin" "ka da nata ɗaya ne?"" Ai tana rufe baki, ya ture baba magajiya ya danƙo Nabila ya fara janta." "Tirjewa ta din ga yi, tana zunduma ihu, tana a taimaketa zai kasheta." "Baba magajiya ta sake biyo su, tana yi masa masifar ya saki Nabila. Sai da ya kaita tsakiyar falo, sannan ya kalleta cikin ƙunar rai ya ce ""Nabila umarni nake baki, a yanzu yanzu cikin gaggawa ki sanar mini ina wannan ɗan iskan ɗan daban yake, kafin na tafi da ke na kulle ki, Nabila wace irin" "mahaukaciya ce, kina iƙirarin ke mai gaskiya ce, amma kina take doka kina ɓoye mai laifi?""." """Ni ban taka kowace irin doka ba, bisa doron doka nake gudanar da aikina""" """Shut up, ki gaya mini in da yake, kafin na saka ankwa ke na tafi da ke, na je na kulle ki""" "Nabila ta ce ""Ka kulleni a nayi maka laifin me?""" """Tambayata ki ke sake yi saboda kin raina mini hankali, ko bayan wannan hujjar wata ki ke nema? Am disappointed on you, kin bani kunya Nabila, ban taɓa tunanin duk wannan haƙilon da ki ke yi," "zaki iya cin amanar ƙasa ba, kuma ki ci amanata ba""" """Ban ci amanar kowa ba, ni ba maciyiya amana ba ce ba""" """Ba zaki yi mini shiru ba, sai na tattakaki tukuna? Ki na ɗiya mace daga gidan daraja da mutunci, amma ki zubar wa da kanki kima, dan ba zan ce mu ki ka zubar wa ba, ki gaya mini ina ce maɓ" "oyarsa, kafin ke nayi arresting ɗinki""" """Kayi arresting ɗina like how, DSP lawyer ce fa ni, lawyer ma mai zaman kanta, ina da ikon kare" "duk wanda ya zo gabana ya nemi hakan, duk girman laifin da ya aikata kuwa, balle wannan da makauniyar shari'a kawai ake yi. Ba ka da ikon kama ni, dan ban aikata laifin komai ba""" "Tuni yan gidan suka tattaru a falo, domin jin meyake faruwa, suke ta wannan uwar hayaniya da" yammacin Allah. "Sai dai jin turka-turkar da ake yi, ya sanya su mamaki ba kaɗan ba, jin abun da Nabila ta aikata," "gaba ɗaya sai suka haɗe mata kai, suka din ga jifanta da miyagun maganganu, na cin zarafi." "Mama ta kada baki ta ce ""Ai na san a rina, an saci zanin mahaukaciya, ba dai major ya ɗaukaketa ya nuna ita ce ya a gidan nan ba, an zo dai-dai in da nake son a zo, ɗan sa da ya haifa bai ja masa abun kunya ba, wata a banza gashi ta jawo masa, Allah ya sa ba yawon ta zubar take yi ba da sunan aiki, ban da haka, ya za ayi ta din ga hulɗa da ɗan iskan gari da ake nema ruwa a jallo, ta ce" "shi zata kare mutumin da yayi kisan kai ɗan ta'adda""." """Allah ba zai nuna mini yawon ta zubar a rayuwata ba, da ni da 'ya'yan gidan nan, in Allah ya" "yadda, babu wanda zai yi yawon ta zubar""" """Maman ki ke gaya wa haka Nabila?"" Yayi maganar yana nuna ta da yatsansa." "Ko a jikinta ta ce ""Zata iya kallon sauda, ko su siyama, ta ce suna yawon ta zubar? Ko yi suke na san ɓoyewa zata yi ba zata faɗa ba, sai ni 'yar Allah ba ni da ba ita ta haife ni ba, ai na daɗe ina yi mata kawaici kai ma ka sani"" Baba magaji sai haƙuri take bayarwa, Nabila kuwa bakinta yaƙi mutuwa, da sun faɗa take mayar musu, mama ta ce wa Nasir, ya rabu da ita ya jira major ya dawo, ya ɗauki duk matakin da yakamata a kanta, kar ya matsa tayi masa wani Sharrin amma duk abun" "da yakamata ayi mata na doka, a ɗauki mataki a kanta." *** """Abdul, so kake sai baƙin ciki ya kashe ni, ya kashe mahaifinka, mu bar maka duniyar ka rayu kai" "kaɗai ko? Tun da aka ce masa an mayar da jafar amurka, hankalinsa yaƙi kwanciya, wataƙila hukuncin kisa ne a kansa, jininsa yayi mummunan hawa, an bashi hutu ma zaman majalisar nema yake ya gagare shi, kai ana ta fama ka samu ka zama deputy governor ɗin nan, yanzu ko maganar bikinka ka daina yi, yau an ƙara watanni uku a kan lokacin bikin, amma ko ka bibiya meyafaru ya ake ciki? Babu ruwanka saboda ka ajiye yar mutane kana lalata da ita, so kake sai asirinka ya tonu mu shiga uku baki ɗaya, da wanne ka ke son mu ji? Wancan case ɗin ko kuma naka da ake ta" "bibiyarka ana lallaɓaka ka ke rashin mutunci?""" "Ya girgiza kai ya ce ""Mummy, ba haka bane ba, wallahi tsoro nake ji na fito da rahama, na san babu lallai abun ya tsaya a iya bayar da shaida a kotu, ina tsoron daddy ya yi mata wani abun, kin san halin sa, idan kuwa aka kuma cutar da ita, ba zan iya yafewa kaina ba, saboda nayi nadamar" "abun da na aikata""" """Ka yi nadama amma ka ajiye musu yarinya, ka ke lalata da ita? Wace irin nadama ce haka?""" "Ya ɓata fuska ya ce ""Ni ajiyeta kawai nayi, ba lalata nake da ita ba""" """To yanzu dai na ji, amma tana ina? Ni ka gaya mini, nayi maka alƙawarin babu wanda zai cutar" "da ita, har mahaifin naka ma, ba zan bari ya cutar da ita ba""" "Ya ce ""Gaskiya Mummy na san lallaɓa ni ki ke yi, kiyi mini wayo, amma na san tsaf zaki bayar da" "ita""" "Ta ce ""Laaa ƙarya nake yi maka kenan Abdul?""" "Ya girgiza kai ya ce 'To, zan dai dawo in gaya miki, amma ba yau ba, bari na tafi Asibiti zan je""ya" tashi ya ɗauki jakarsa. """Ba zaka je ka duba mahaifin naka ba?""" "Abdul ya ce ""Zan je, yanzu na kusa makara ne, kuma ina zuwa zai yi mini zancen yarinyar nan," "sai na dawo tukuna"" ya fice daga ɗakin." *** "Viper ya ƙurawa madaki ido, da duk yayi wani iri, babu wannan kwarjinin da ban tsoron da yake da shi, babu shaye-shayen ƙwayoyin da ya saba, gaba ɗaya sai tsufansa ya fito sosai da sosai." """Madaki, yanzu na tabatta har labarin madaki ya shafe, Viper ba zai bar zuciyarka ba, ko dan wannan ƙafar da aka yanke, kodayeke taimakonka nayi, ni na fika imani, ba dan haka ba, wannan ƙafar cin jikinka zata cigaba da yi." "Na turo lawyer ta, ku yi magana, amma ka ƙi, ni ba ta taka nake yi ba, kai ka san kasheka ba wahala zai bani ba, da kai da muƙarabbanka, amma ba ta kai nake yi ba, zan yi amfani da kai ne," "na dangana da Indabo, dan haka ka shirya yin magana ko baka shirya ba?""" """Ban shirya ba, kuma ba zan shirya ba, kayi kaɗan mai zamani, haryanzu ba ka kai in da zaka ga" "bayana ba, maƙiyina bai isa ya ga bayana ba""" "Viper ya ce ""Baya kuwa na riga na ganshi, tun da da hatimin sunana zaka mutu a gadon bayanka, na san duk abun da zan yi maka, ba zan huce ba madaki, ni zuciyata ka yi wa illa, amma zan iya kamantawa. Kar ka manta lakwari ma yana hannuna, sannan shi ya ji wuyar da ya shirya yin" "magana, dan haka ko ka yi magana, ko kar ka yi tare zata kwaɓe muku, idan yayi tamkar ka yi ne""" "Ya ciro wani jan gari, mai fatsi-fatsi a cikin yar leda, ya ɗago wa madaki shi, ya ce ""Da irin" "wannan, ku ka yi amfani wurin hanani kataɓus, ku ka yi mini illa ko?"" Madaki yayi shiru, yana bin hannun Viper da kallo." """Bari na yi maka amfani da ita, na ga wani irin hali na shiga kuma wane irin nishaɗi ka ji, lokacin" "da kake cin zarafina"" Viper ya miƙe tsaye, Madaki ya zazzaro ido, amma Viper haka ya sheƙawa madaki garin nan." "A take kansa ya fara juyawa, ya shiga girgiza kansa." "Viper ya ce ""Ina son ku ɗauke shi, ku kai shi kusa da tsohuwar dabata, in da yaran nan da yake cin zarafi yake yi wa kisan gilla, wanda ya sanya tsananin tsoronsa a zukatansu, idan dare yayi ku yasar da shi a can, gari ya waye su ganshi a wurin, da ƙafa ɗaya su tabattar da cewa alkadarin sa" "ya karye, ƙaryarsa ta ƙare." *** "Nabila na kwance, ƙirjinta na ta bugawa, jiran dawowar Abba kawai take yi, ba ta san me Nasir zai gaya masa ba, ba ta san a yaya zai karɓi maganar ba. Tana ta maimaita ""la haula wala ƙ uwwata illa billah"" bacci ne ya fara fizgarta, ta ji tsayuwar motar Abba, wajen ƙarfe goma na dare, zumbur ta tashi ta tsaya, ta tafi window tana leƙe-leƙe, har wurin goma na dare, shiru ba ta ji an kira ta ba." "Ta ɗauki wayarta, ta kira Viper, bugu ɗaya ya ɗaga, ya ce ""Ya ake ciki?""" """V am scared"" tayi maganar tana fitar da numfashi cike da tsoro." """Meye yake baki tsoron?""" """Ban san me Abba zai ce mini ba, tsoro nake ji, Abba bai iya fushi ba, bana tunanin zai fahimce ni" "cikin sauƙi, na shiga uku"" tayi maganar tana fashe masa da kuka." """Shhhhh, Abla"" ta ji kiran sunan har tsakiyar zuciyarta." """Mmm""" """Shi ramin ƙarya ƙurarrre ne, duk yadda ki ka kai ga ɓoyewa, dole sai ya fasu wataran, shiyasa" "na kawo ƙarshen zargin da yayanki yake yi miki. Haɗuwar da muka yi da ke, sai da aka gaya masa, yana bibiyarki ko ta ina tasa mafitar kawai yake nema. Ki nutsu ki cigaba da addu'a, babu abun da zai faru in sha Allah, you are my only hope as i told you before, idan ki ka karaya ni ya" "zan yi?"" Yayi maganar cikin rarrashin da bata taɓa tunanin ya iya ba." """Ba zaka gane ba, amma zan cigaba da addu'a, sai da safe"" ta kashe wayar tana dafe ƙirjinta," saboda yadda yake bugawa. *** "P.A ne ya shiga bedroom ɗin Indabo, bakinsa ɗake da sallama, ya amsa masa ya ƙarasa ya zauna, ya ce ""Barka da wannan lokaci""" """Barkanka dai P.A""" """Ya ƙarfin jiki kuma?""" """Jiki Alhamdilillah, da sauƙi sosai, maybe gobe in Allah ya kaimu zan shiga Abuja""" "P.A ya ce ""Yakamata ka ɗan dakata da shiga Abujan nan?""" "Ya kalli P.A ya ce ""Saboda me? Hutuna ya ƙare ai""" """Ƙishin-ƙishin na ji, maganar kuɗin scholarship ɗin da na harkar sadarwa, balli na daf da tashi," "EFCC zata bincike ku"" zumbur indabo ya tashi zaune ya ce ""Kai a ina ka ji?""" "P.A ya ce ""Majiya mai ƙarfi, amma ka kira shugaban marasa rinjaye, a wurin P.A ɗin sa na ji" "maganar, kuma ba jita-jita bane ba""" """Innalillahi wa Innalillahi raji'un, P.A wai ya aka yi abubuwa suke ta taɓarɓarewa ne haka?""" "P.A ya ce ""Nima abun ya fara bani tsoro, amma ka dudduba ka bincika mu ji""" """Ai ni har bana son kiran waya, duk wanda na kira akwai kalar masifar da zai gaya mini. Kuɗin nan fiye da rabi duk a kan ƙoƙarin ganin jafar ya fito ne, idan ba hali sai na lallaɓa na mayar, amma zan yi magana da ministan sadarwar da na ilimin, mu tattauna, koma dai na saka su bincika" "mana""." """Bayan nan, mutane fa suna ta surut a kan program ɗin da yarinyar nan take yi, na walƙiyya wallahi mutane sun fara dawowa daga rakiyarmu, na rasa uban da yake ba ta wasu information ɗ" "in da take faɗa a kanmu""" """Kaga P.A, dan Allah ka ƙyale ni haka, gaba ɗaya maganganunka ba alheri yau, tashi ka tafi dan" "Allah""" "P.A ya ɗan yi shiru, sannan ya tashi ya fita." *** "Yanayin da Abba ya fito falo, ya tabattar musu da ba lau ba, fuskar nan a murtuke babu annuri." "Ya kalli baba magajiya ya ce ""Kira wo mini Nabila"" sai da suka kalli Abba, jin ya ambaci Nabila," maimakon Arfa da ya saba kiranta. "Nabila na kwance baba magajiya ta shigo ta sameta, ta ce ""Arfa, babanki yana kiran ki"" sai da ƙ" "irjinta ya buga da ƙarfi, ta yi ajiyar zuciya ta ce ""To, gani nan zuwa"" baba magajiya ta fita daga ɗ" akin. "Da ƙyar Nabila ta tashi, ta nufi falon, ƙirjinta na ta bugawa da sauri." "Kusan kowa ya hallara a falon, ita kawai ake jira." "Ta ƙarasa ta durƙusa a gaban Abba, ta ce ""Abba gani""" "Mama ta ce ""Munafuka ga ladabin kura""" "Umma ta ce ""Ki yi shiru, karya haɗa da ke""." """Dama irin tarbiyyar da na baki kenan? Ki je ki dinga bibiyar 'yan iska a waje?""" "Gabanta ya faɗi, ta ɗaga kai ta kalli Nasir ta koma ta sunkuyar da kai." """Har muka yi zaman kudancin Najeriya, muka gama ki ka yi jami'a, duk baki lalace ba sai yanzu? Ina ke ina bibiyar ɗan daba, ɗan ta'adda kuma ɗan iska da hukuma take nema? Kin zama 'yar" "iska lalacewa ki ke so ki yi ko, ko ma in ce ki ka yi?""" "Falon yayi tsit, baka jin sautin komai, ƙarar gudun A.C, sun yi cirko-cirko suna kallon Nabila." "Tuni ta fashe da kuka, jin yadda maganganun Abba, ke dukanta." "Abba ya ce ""Nasir ya gaya mini komai, da duk bana yadda, yanzu sakamakona kenan a wurinki ko?" "Sakamakon tarbiyya da ilimin da na baki kenan, ki ƙare a ɓoye mai laifi, azo kama shi a haɗa da ke, ki tozarta ni ki zubar mini da mutunci""" "Cikin ƙulewa mama ta ce ""Wane sakamako ka ke saka ran samu daga tsintacciyar mage, ai ba zata taɓa mage ba, shiyasa nayi ta ƙoƙarin ankarar da kai tun a baya, uban wani ba ya zama na wani, yanzu duk da fifikon da ka nuna mata, bai hanata nuna maka, ita 'yar kunama ce ba, duk gidan nan babu wanda yake janyo maka magana sai ita, yayanka suna zaune lafiya amma ita" "kullum cikin ɗaga mana hankali take""" "Baba magajiya ta ce ""A'a fa, dan Allah ki sassauta maganganun nan, sun yi tsauri da yawa""" "Nabila kuwa da a zahiri ta nuna tashin hankali da nadama, cikin zuciyarta kuwa babu alamar hakan, ta yakice gumin fuskarta da yake ta tsatstsafo mata ta ce """"Abba ba mummunan sakamako bane ba, abin da ka tarbiyyantar da ni a kai ne, gaskiya ita ce nake tsaye a kai. Yakamata ayi mini adalci aji ta bakina, ba a goyi bayansa kawai ba ace ni ce bani da gaskiya ba. Wallahi Abba ni ba" "bibiyar yan iska nake ba, aikina kawai nake yi""." "Mama ta ce ""Har wata gaskiya ce da ke...." "Abba ya ɗaga mata hannu, ya dakatar da ita, ya ce ""Ya isa haka, ki tashi ki je, bana ko son ganinki," "ki je ki yi abun da ki ke ganin shi ne dai-dai, tun da a kan gaskiyar ki kike""" "Cikin tashin hankali ta ce ""Abba baka son ganina fa ka ce, me aka gaya maka har haka a kaina ya" "sanya ka yanke mini wannan hukuncin """ """Abun da ki ka aikata aka gaya mini, muddin kina neman zaman lafiya da gudun ɓacin raina, dole ki bawa ɗan uwanki cikakken haɗin kai, ya gudanar da aikinsa, ki fita daga wannan lamarin, kafin a saka ki cikin masu laifi a kama da ke." "Duk wahalar da yaron nan yake yi, kina ji kina gani, amma kika ja bakinki ki ka yi shiru, har barazana ake yi masa na kora, muddin bai kama mutumin nan ba, amma ki ka zagaye ki ka je ki ka" "ƙulla alaƙa da shi, kin fara bani tsoro Arfa""" "Cikin matsanancin tashin hankali ta ce ""Amma Abba ni kuma menene makomata? Yakamata ka ji" "ta bakina abba, na karɓi aikin nan ka fahimce ni Abba""" "Bai tsaya sauraronta ba ya ce ""Sai dai kin nuna mini ba ni na haife ki ba, na gode"" yayi gaba zai" bar falon. "Cikin tashin hankali, ta riƙe ƙafarsa ta ce ""Haba Abbana, idan har zan rayu kana fushi da ni, me yayi mini saura a duniya? Ka yi haƙuri zan yi abun da ka ce"" ta yi maganar tana kuka mai ratsa" "zuciya, tana sheshsheƙa kamar ta shiɗe, amma ya fizge ƙafarsa yayi gaba." "Yana bari falon, tamkar su cinyeta ɗanya, suka yi kanta da surutu, kowa na tofa albarkacin" bakinsa. "Tashi ta yi tsaye, ta goge hawayenta, cikin ko in kula, ita ma ta bi wata hanyar ta bar musu falon," cikin sigar kwa ci kanku. "Ɗakinta, ta shiga ta buɗe drower, ta fito da wasu takardu ta zube su a kan gado, ta kunna system ɗ" "in ta da take caji a gefen gadon, lokaci guda kuma ta ɗauki wayarta tana dannawa." "Jin motsin mutum a bayanta, ya sanya ta waiwaya da sauri." "A tsaye ta ganshi bakin ƙofa, fuskarsa babu walwala balle annuri." "Mayar da hankali ta yi, za ta cigaba da danna wayarta, Nasir ya tako zuwa gabanta, ya tsaya ya ƙ" "are mata kallo sannan ya ce ""Kin shirya aikata abun da Abba ya umarce ki ko kuwa? Ina zan kama Viper""" "Cikin hanzari ta tari numfashin sa ta ce ""Ban ce shirya ba, kuma ba zan shirya ba, daga nan har" "gaban abada,ka je can ka neme shi, yaya Nasir ka fita ka rabu da ni dan Allah""." "Cikin matuƙar mamaki yake bin ta da kallo, ""Yanzu duk kukan da ki ka yi a falo, ƙarya ki ke yi" "kenan?""" "A hasale ta ce ""Ina ruwanka, idan ma kukan ƙarya ne ko na gaske, ka yi aikinka in yi nawa. Ba dai ka je ka gaya masa ƙarya da gaskiya abun da ka ke so ba? Shikenan, amma kar ka sake yinƙ urin shigar mini aiki, idan ba haka ba komai yana iya faruwa, wallahi ba zan fasa abun da na yi niyya ba, idan kuma ka cigaba da takura mini, zan baka mamaki ka taka a hankali kar ka faɗo" "cikin aikina""" "Hannu ya saka, ya ɗagota daga kan gadon ya ce ""Menene zai faru, wani irin mamaki zaki bani? Me zai faru nake son ki gaya mini. Kina da hankali kuwa Nabila? Kin san doka amma kina taka ta yadda ki ke so? Da me ki ke taƙama ne haka? Sai da na zauna na nutsu, nake tunani, kenan duk hanyoyin da nake bi, dan na samu na kama mutumin nan, ke ce ki ke toshe su ko? Ki ke taka doka" "yadda ki ke so Nabila""" "Ta waro masa idanunta ta ce ""Doka ko? Ni iya takata na yi, kai kuma cin zarafinta ka ke ƙoƙ arin yi, ka ƙyale ni babu ruwanka da ni, ka yi naka aikin na yi nawa duk wanda yayi galaba shikenan. Idan ka ga dama ka je ka sake gayawa Abba abun da duk yayi maka a kaina, wallahi babu gudu babu ja da baya, ban fara dan ina saka ran dainawa ba, ba tare da na yi nasara ba. Ka rabu da ni muje a kan Sharrin da ka yi mini, ina bin ɗan daba a waje"" hankaɗata yayi kan gadon, yana wani irin huci, zuciyarsa na yi masa zafi, yayi wata irin ƙwafa yana bin ta da kallo. Cikin hanzari ya fice ya bar mata ɗakin, saboda idan ya cigaba da tsayuwa, zai iya yi mata abun da ba" "shikenan ba. Ta yinƙura ta tashi zaune tana haki, tana kallon ƙofar da ya fita." "Yana fita ta dafe kanta, saboda yadda yake wani irin sara mata, ta kira Sumayya a waya, sai da ta" kusa katsewa sannan ta ɗaga. """Salamu alaikum""" """Wa'alaikum Salam, sumayya dan Allah kina ina ne?""" """Gida, ban daɗe da dawowa ba ma""" """Dan Allah idan kin huta ki zo gida, ina son na ganki, ina cikin matsala ne, ba zama a bari na fito" "ba""" """Subhanallah, wace irin matsala kuma?""" """Ni dai ki zo dan Allah""" """Shikenan, bari na canza kaya na zo kawai""" *** "Tamkar an ɗora masa gingimemen dutse a kansa, haka ya buɗe idanunsa da ƙyar, ya na ƙoƙarin tashi, ya ce ""Masa oga kar ka tashi, ka huta tukuna""" "Madaki ya ɗaga kai da kyar, ya ganshi a dabarsa ya ce ""Ya aka yi na zo nan?""" """Yaran mai zamani ne, suka kawo ka, suka ce wai gaka nan ajiya, zai waiwayeka, amma oga ya na ganka da ƙafa ɗaya, sai nemanka muke yi da kai da lakwari babu wanda ya san in da kuka" "shiga?""" "Ya kalle shi ya ce ""Akwai wanda suka san na dawo?""" """Eh mana, su fidda na kogo, duk suna nan aka kawo ka, labari ma ya fara zagawa cewar an cire" "maka ƙafa ɗaya""" """Wani taimako nake so ka yi mini, amma bari sai na wartsake, kaina kamar an kunna wuta a" "cikinsa, kamar ana narka mini ƙwaƙwalwa, bari abun nan ya sake ni""" """To shikenan, sannu""" ***** "Sosai Nabila take yi wa sumayya kuka, tana gaya mata abubuwan da suka faru." """Nabila, shiyasa tun da fari na ja miki kunne, babu wanda zai tsaya ya saurareki balle ya fahimce ki, gaskiya ina bayan Nasir, ko dan rayuwarki, yakamata ace kin ajiye wannan shirmen da ki ke yi," "ni babban tashin hankalina haukan da ki ka yi wai son shi ma ki ke yi""." """Laifi ne dan ka tsayawa wanda aka zalunta?""" """Aka zalunce shi a gidan uban wa, mutumin da ya yi kisan kai? Kisan kai fa yayi. Kuma babban tashin hankalin son sa da ki ka fara yi. Ba zaki taɓa ganin laifinsa ba, mutuncinki ya zube a banza, a din ga yi miki kallon mutuniyar banza, wallahi hukuncin da Abba ya ɗauka a kan ki, yayi dai-dai duk wani abu na shaida ko hujja, ki tattara ki ba wa Yaya Nasir, a kama shi kowa ya wuce wurin, kan ki janyo wa mutane magana, ni ba a kyauta mini ba, da bai haɗa woyoyinki ya ƙwace ba, ya bar ki da su"" Ta ƙura wa Sumayya ido, yadda ta ɗauki zafin nan, babu alamar za ta tsaya ta" "fahimce ta, kawai ta yi mata shiru, ta gama masifarta, ta tashi ta fita." "Tayi shiru, gaba ɗaya ta rasa abun da yake yi mata daɗi, ta ji gaba ɗaya duniya tayi mata zafi," "rana zafi inuwa ƙuna, ta rasa ina zata kama, wurin wa za ta je taji sauƙi." "Gari ya waye, Nabila ta shirya tayi ficewarta wurin aiki, ba wanda ta kula, ta yi ficewarta ta tafi." "Ofishin barrister Habib taje, ta jira shi, ta samu wuri ta zauna, tana jiransa." "Kallo ɗaya yayi mata, ya buɗe ofishin sa, ya ce mata ""Taso""" "Ta tashi ta shiga, suka zauna, ya kalleta ya ce ""Ina jinki yau kuma menene?""" Nan ta kwashe komai ta zauna gaya masa. "Ya ce ""Ai dama na gaya miki, dole ki fuskanci ƙalubale, ki yi haƙuri, komai zai wuce, gobe in Allah ya kaimu kotu zata zauna a kan case ɗin su rahama, sannan zan cigaba da duk wani ƙoƙari" "na baki dukkanin goyon bayan da ki ke buƙata, amma mu cigaba da addu'a""" """To yaya Habib, kai kaɗai ne ka fahimce ni, kotu na yanke hukunci zamu shigar da ƙarar kotu ta" "tilasta wa bunkure foundation fito da ramma, tare da gurfanar da ainihin wanda ya aikata laifin""." """Ki yi haƙuri ƙanwata, nasara na tare da ƙalubale, ina yi miki fatan alkhairi da fatan nasara""." "A sanyaye ta ce ""Na gode""" """Amma Nabila, a ina zaki yi generating shaidun da zaki shiga kotu da su, a kan case ɗin Viper? A" "ina zaki ganshi?""" """Na ma ganshi, na riga na tanadi duk abun da nake buƙata, domin fuskantar shari'a""" """You can do it my dear, kuma in sha Allah za ki yi nasara, akwai yiwuwar zan je na samu major da" "kaina, nayi masa bayani""" "Ta girgiza kai ta ce ""No need, kar ka je, hakan ba zai sauya komai ba""" "Ta miƙe ta nufi hanyar fita, tana duba message ɗin da ya shigo wayarta." """Mu haɗu a garden, idan baki da aiki""" "Tayi masa reply da ""On my way""." "Yanayin yadda take tafe, tana jefa ƙafa, ya tabattar masa da a cikin damuwa take." "Tana zuwa gabansa kawai ta nemi wuri ta zauna, ba tare da ta ce masa uffan ba." "Ya samu wuri ya zauna a gefenta ya ce ""Ya aka yi ne?"" Ta girgiza masa kai alamar babu komai." """Akwai mana, fuskar ki ta nuna""" """Kowa yaƙi fahimta ta, Abba yayi zazzafan fushi da ni, wai sai na bawa yaya Nasir haɗin kai ya kama ka, ya je ya gaya wa Abba ƙarya da gaskiya, sam Abba yaƙi saurarara ta, sumayya taƙi fahimta ita ma, barrister Habib ne kawai ya fahimce ni, Vi na rasa ya zan yi, zuciyata zafi take yi" "mini, Nasir ya cuce ni, ya haɗa ni da Abba""" """Yanzu zaki ba shi haɗin kai ya kama ni kenan?""" "Ta girgiza kai ta ce ""Ba zan iya ba, ba zan iya bari a kama ka ba""." """Meyasa?"" Ta ɗaga kai ta kalleshi ta ce ""Ka sani ai""" """Ban san komai ba""" "Cikin basarwa ta ce""Kawai ina so ayi wa matarka adalci ne, kuma a hukunta wanda suka yi maka" "laifin""" "Ya ce ""Gwargwadon yaya ki ke son yar madara?""" """Gwargwadon yadda nake son ka""" """Ki ke son wa?"" Yayi maganar ƙasa-ƙasa." "Kasa jurewa tayi, duk jikinta yayi sanyi, ta kasa kallonsa, gashi ya matso daf da ita sosai." """To ungo share hawayen"" yayi maganar yana bata handkerchief ɗin sa." "Ta karɓa, amma ta kasa gogewar, ta cigaba da kuka." """Dan Allah kar ki karaya, ina ƙara jaddada miki, da Allah na dogara da ke na dogara, amma idan" "kin ga matsin yayi yawa, ki bayar da kai bori ya hau, ki bashi dama ya kama ni"" ta girgiza kai ta ce ""A'a, ba zan iya bari a kama ka ba"" tayi maganar tana sheshsheƙar kuka." """To ya isa haka kukan, ga wata 'yar ƙaramar kyauta zan baki"" yayi maganar yana sake bata" envelope ɗin da ya bata wancan karon. "Ta saka hannu ta karɓa, tana goge hawayen, tana buɗewa ƙananan hotuna ta ciro guda biyu," "wadda ta yi tozali da ita a jikin hoton ce, ta sakata razana, ta kalli hoton, ta kalli Viper ta shafa fuskarta ta ce ""Wace wannan?""" """Ni ma ban sani ba""" """Yaya zaka bani abu ka ce mini ka ce baka san wace ba? Wannan....wann... Kai wannan ba ni ba ce ba, bani ce a jiki ba, yaushe aka yi wannan hoton ban sani ba? Kai wallahi bani ba ce ba, wacece wannan meyasa take kama da ni"" ta yi maganar tana kallonsa, idanunta yake kalla, amma" bai yi magana ba. """Kayi mini bayani, ka yi magana wacece wannan"" tayi maganar kamar zata zare, tana riƙe rigarsa" tana zazzaro masa ido. Ayshercool 08081012143 ₦500 ne via 0009450228 Aisha Adam jaiz bank sai shaidar biya ta 08081012143 Wanda za su jira document 1K ne. 90009343 'Yan Nijar ku turo katin airtel na 300fcfa Arewabooks ayshercool7724 *BRIGHT PENS SECOND BATCH* "KU KASANCE DA LITATTAFAN BRIGHT PENS A SECOND BATCH, NA ƘARFE A WUTA (AYSHERCOOL)." MUTALLAB (NIMCYLUV) ZAYTOON (ZEE KUMURYA) DA HADARIN GABAS (NAZEEFA SABO NASHE) "Idanunta yake kallo, jikinsa a sanyaye amma yayi shiru bai yi magana ba." """Kayi magana, ka gaya mini wacece wannan? Bani ba ce a jiki, amma meyasa take kama da ni? A" "ina take?""" "Still bai yi magana ba, ƙara tsananta riƙon da tayi masa ta ƙara yi, cikin matsanancin kuka tashin hankali da ƙaraji, take jijjiga shi ta ce ""Ka yi magana, ka gaya mini wacece meyasa take kama da" "ni? Kuma a ina take?""" "Viper ya ce ""Ban santa ba, tsintar su nayi, naga ya dace kema ki gani, ban taɓa jin kin ce kina da" "yar uwa da ku ke ciki ɗaya ba, amma kamarku ta ɓaci da ita, shiyasa na ga ya dace na baki ki gani""" """Ka san wacece, ka saba yi mini wasa da hankali wasu lokutan, Please na roƙe ka, don't play with" "my emotions, ka gaya mini dan Allah"" tayi maganar tana kallon ƙwayar idonsa." "Ya ɗan jima yana kallonta, kan ya saka hannu ya cire hannunta daga riƙon da tayi masa, yana riƙe" "da hannunta ya ce ""'yan gidanku yakamata ki tambaya bani ba""" """Tayaya zan tambaya? Alhalin a duniya babu abun da Abba ya tsana sama da nayi masa zancen mahaifina, ban san dalilin wannan mummunar ƙiyayyar ba, sun yi abun su ya riga ya wuce, amma ya nesan ta duniyata da mahaifina, duk wata hanya da zata saka na san in da yake, Abba ya tosheta wai ba wani abu da zai tsinana mini. Wani abu ne mai ciwon gaske da yake addabar zuciyata, ka fama mini ciwon da yake zuciyata, kuma ka bar ni a duhu, ka taimaki rayuwata wallahi ko Wacece" "wannan tana da alaƙa ta kusa da ni""" "Viper ya ce ""How, an ce kowane mutum akwai irinsa guda uku a duniya..." """Ba wani guda uku, wannan kamar nice a jikin hoton, kamannin nan sun yi yawa, ka wayar mini" "da kai dan Allah""" """Me ki ke so na ce, duk abun da zan faɗa miki ƙarya zan yi miki, ki je gidan abun da suka ce miki" "shikenan""" "Ta fizge hannunta, ta yinƙura zata tashi, jiri ya kwasota ta hau tangaɗi, ya riƙe ta, ta ɗan yi shiru" "ta samu nutsuwa, ta juya ta bar wurin." *** "Ramma kuwa kwana suka yi, Abdul yana juye-juye, ciwon cikinsa ya tashi, ko baccin kirki ba su yi ba, sai bayan sallar asuba ya ɗan lafa masa, ya din ga tofa fatiha da bisimillah tana bashi yana sha." "Yana kwance a kan cinyarsa, tana ta shafa masa ruwan tofin a kan cikin, tana shafa masa, ya riƙe" hannunta yana mayar numfashi. """Sannu Abdul"" ya jinjina mata kai alamar yauwwa." """Wai wannan ciwon cikin, ka dudduba kanka sosai mana, kana likita amma ka din ga wasa da" "lafiyarka, kalli yadda ka ke shan wahala dan Allah""" """Tausaya mini ki ke yi?""" "Ramma ta ce ""Duk rashin imanina, idan ban tausaya maka wannan wahalar ba, ya zan yi, idonka" "har ja yayi saboda wahala""." """Rahama ina ga ciwon cikin nan ne zai yi ajalina, har ƙasashen waje na je, an kasa gano menene""" "Dummm ta ji ƙirjinta ya buga, jin abin da ya ce, amma ta ce ""Dan Allah ka daina wannan" "maganar, ka din ga addu'a ka cigaba da shan magani""" """Rahama baki san me nake ji ba ne, ina shan wahala fa"" yayi maganar yana miƙa, tare da lanƙ" "washe yatsun ƙafarsa, hawaye na bin gefen idonsa, saboda azabar ciwo""" """Dan Allah ni ka daina wannan maganar"" ya juya yayi ruf da ciki." """Idan na mutu zaki yafe mini?""" "Ta ce ""Wataƙila, ai ni dama bana fatan na je gaban Allah ina neman hakkina a wurin wani, ko wani yana nema a wurina, a duniya nake fatan Allah ya saka mini abun da ka yi mini, da kai da wannan jakar matar""ya yi murmushi ya ce ""Hakan ma na gode, alfarma ɗaya da zan nema, dan" "Allah rahama kar ki zubar mini da cikin nan, ina matuƙar son abun da yake cikinki""" """Wallahi sai na zubar tas, sai ya bi rariya, ni ka daina yi mini magana kamar wasiyya wasiyya, dan" "na tausaya maka""" "Sai da yayi dariya ya ce ""Abubuwa ne suke ta hargistewa Rahama, komai ya cukurkuɗe, ban san ya abubuwan za su kaya ba, ina ta ƙoƙarin baki kariya ne iya yi na, duk da ni mai laifi ne"" yayi" "hamma ya ce ""Idan ya lafa sai na ji daɗi, gashi bacci nake ji, ke ma na hana ki bacci""" "Yayi maganar yana shafo fuskarta, ta saka hannu ta sauke hannunsa, ta shafa kansa ta ce ""Kayi baccin, ko ka samu relief"" ya juyo yana fuskantar cikinta, da yake shafe a jikinta ya ce ""Bari na yi" "magana da yarona"" maganar ta sa tayi daidai da jin motsi a ƙasan mararta." "A haka bacci ya kwashe shi, ta zuba masa ido, tana jin tausayin sa, gaba ɗaya ya rikice saboda ita," ta ƙara lura da shaye-shaye da rashin tarbiyya ne kawai yake ingiza shi yake rashin mutunci. """Kayi haƙuri Abdul, amma komai ya kusa zuwa ƙarshe da yardar Allah""" ***** "Walid ne ya magantu, dan tun shigowar Viper ya lura kamar yana cikin damuwa, ya ce ""Mai" "zamani, ya ake ciki ne? Jikin ne ko wani abun ne ya faru?""" "Ya numfasa ya ce ""Na yi abun da ka ce, Nabila""" "Walid ya ce ""Masha Allah, ya ake ciki?""" """Ba ta da masaniya a kan hakan, things are complicated, ta shiga matsala daban daban, ta samu" "matsala da gidansu, an ce lallai ta bawa ɗan uwanta dama ya kama ni, she's almost alone, kamar ban kyauta ba, na ɗora mata abun da ya fi ƙarfinta""" "Walid ya girgiza kai ya ce ""Ƙaddara ce ta haɗa ku, kuma she's not alone, tana tare da kai, muna" "cigaba da addu'a in sha Allah, komai zai dai-dai ta, ba ta gaya maka komai game da labarinta ba?""" Viper ya girgiza masa kai. """Bata bani ba, amma na bata hoton, na ce taje ta tambayi yan gidansu""" """Ina jin alamun nasara, in sha Allah ka kwantar da hankalinka""" Viper ya amsa da Allah ya sa. **** "Nabila kamar mara laka, ta fito daga wanka, jikinta ɗaure da towel, ta jiƙo kanta da ruwa," "idanunta sun yi jawur, saboda ta yi kuka sosai da sosai." "Kawai ta ɗaga kai ta ga Nasir a tsaye a ƙofar ɗakin, ta ƙara haɗe rai, ta ƙarasa tsane jikinta." """Nabila, lokaci yana cigaba da ja, kuma ke nake jira, haryanzu baki ce mini komai ba, ki gaya mini in da zan samu mutumin nan, ina ɗaga miki ƙafa ne saboda Abba, kuma nima ina jin nauyin" "aikata miki hakan""" "Buɗe wardrobe tayi, ta ɗaukko phant da breziar ta jefo kan gado." """Magana fa nake yi miki""" "Tayi masa banza, ta ɗaga breziar tana ƙoƙarin fara sakawa." """Nabila wai baki da hankali ne? A gaban nawa zaki saka kaya?""" """Ni na kawo ka? Ko ka manta bin maza nake yi? Ba abun da zai hanani saka kayana, ai yanzu ba" "kunyar wani nake ji ba""" "Galala ya bi ta da kallo, jakar da ta fita da ita, ta janyo, ta ciro ƙaramar wayarta da take vibrating" "ta ciro ta ɗaga ta ce ""Hello V""" """Are you safe?""" """Yes Alhamdilillah""" """It seems you are bit disturbed""" """No at all""" "Yayi ajiyar zuciya ya ce ""Kin tambaya ɗin?""" """A'a, ai bai dawo ba, yayi tafiya ne, ni yanzu ina jiran abun da zai kasance a kotu ne gobe in Allah" "ya kaimu, and su oga Walid su shirya, zasu kasance cikin shaidun da zamu gabatar a kotu fa""" """Shikenan, zan gaya musu""" """Yauwwa, gobe in Allah ya kaimu daga kotu zan wuce wurin 'yan sanda, a kan case ɗin ka, Allah" ya sa...... """Nabila, wai me ki ka zama ne?"" Nasir yayi maganar yana tunkararta zai fizge mata waya, ta ja da baya ta ce ""Wallahi ka zo in da nake sai na saki towel ɗin nan, na saki ihu ai kai ka zo in da nake, get out from sight, wallahi Nasir ko me zaka yi ina kan bakana, ni, ko wani kaga zai yi mini ƙ azafin da ka yi mini, yakamata ka tare mini, amma ka ɓata ni a wurin mutumin da bani da tamkarsa, wallahi ka cigaba da matsa mini kai ma sai na ɓata maka suna a gidan nan, ka fita daga rayuwata ba ɗan daba ba, ko uban wa zan kare ni naga zan iya. Ka je ka yi aikinka nima na yi nawa, kai ma ai amfani ake yi da kai, ake son kama shi ba dan taimkon al'umma ka ke son kama shin ba, get out please"" yadda jikinta yake rawa take nema ta saki towel ɗin, muddin ta saki ba shi" da kalaman da zai kare kansa da su. **** "Indabo ya kalli Abdul da yake zane yana wasa da mukullin motarsa ya ce ""Wai meye ne, na ganka" "kamar wani mara lafiya?""" "Ya ce ""Bakomai, ka yi haƙuri na san maganar yarinyar....." """A'a, ai ba maganar yarinyar nan zan yi maka ba Abdul, ka yi abun da ka ga dama, yau saura sati biyu ɗaurin aure ko wurin yarinyar da zaka aura duk ka kyauta. Magana ce zan yi maka a kan kuɗ aɗen da nake sanya wa a account ɗin ka, balli na nema ya tashi, an naɗa kwamiti bincike a kan ku" "ɗaɗen nan, shi ne nake son ka dawo mini da shi, na mayar kan balli ya tashi asiri ya tonu""" Abdul ya yi sororo yana kallon Indabo . """Kake kallona kamar shashasha, ka dawo mini da kuɗi na ce, na mayar musu dama na ɗan jinkirta ne, idan komai ya tafi daidai ayi yaƙin neman zaɓenka da su, amma zan tanade su a kusa, da na ji" "ƙishin-ƙishin na mayar da su""" "Abdul ya ce ""To, zan dawo da su"" ya tashi ya fita." "Bayan fitar Indabo P.A ya shigo, ya samu wuri ya zauna, suka gaisa da Indabo." "Indabo ya ce ""Yaya me ka gano?""" """Eh, ana bibiyarsa gidan sa na lay out, ba kowa a ciki, duk gidajen shaƙatawarsa, baya nan" "abokansa duk na neme su, na bibiye su, amma babu alamar sun san zancen yarinyar ma, amma na" "in da yake kwana ne, haryanzu ba a gano ba, ka san wayo ne da shi, wasu lokutan a asibiti yake" "kwana, amma sannu a hankali ana cigaba da bibiyarsa""" """Abdul ban san ya aka yi ya zama haka ba, yanzu idan na matsa tsaf zai yi wani rashin hankalin, yanzu ka duba ka gani, saura sati biyu fa auren sa, amma gaba ɗaya hankalinsa baya jikinsa, idan na matsa masa a kan yarinyar nan hauka zai yi mini, shiyasa nake bin sa a sannu, zai zo hannuna" "sai ya ci ubansa""" "P.A ya ce ""Distinguish akwai matsala fa""" """Wace irin matsa kuma? Kullum cikin kiran matsala ka ke kwanakin nan""" "Ya gyara zamansa ya ce ""Distinguish, yarinyar nan sumayya T ladan, sai buɗa maka aiki take yi, kuma duk yan siyasar nan a kanka ta fi cin kashinka, yanzu wasu matasa daga yankinmu, sun kafa wata ƙungiya suna wayar da kan jama'a, wai za su rubuta takarda kiranye za su yi maka, ka dawo" "gida babu abun da kake tsinana musu sai kwashe musu kuɗi""" "Indabo ya kalleshi ya ce ""Kai ka taɓa ganin wanda aka yi wa kiranye a Nigeria? Rabu da su, ƙ" "aryar banza ce, yanzu muna da abubuwan da suka fi wannan muhimmanci""." "P.A ya ce ""A'a honorable, kar a fara a kanmu, matasan nan fa da gaske suke yi, ka san yanzu muna" "zamanin social media ne, har cikin ƙauyuka suke bi, da gaske kiranye zasu yi mana""" """Ka je ka haɗa sojojin bakan da muke da su, a basu kuɗi, su je su karemu, da daƙile abun, sannan" "a saya musu fili a kafafen watsa labarai, su shiga su karemu""" "P.A ya jinjina kai ya ce ""Shikenan, babu laifi za ayi hakan""" **** "Nabila kusan raba dare ta yi, tana kallon hotunan matashiyar da yake hannunta, ta takura ƙwaƙ walwarta, wurin yin tunani, ko ita ce a jikin hoton, amma ita dai ba ta san lokacin da aka ɗauki hotunan ba, tabbas ta san ta nuna hotunan nan, akwai sabon rikici, sai dai ta shirya karɓar duk" "abun da zai faru, amma sai ta san wacece a jikin hoton." "Gaba ɗaya ta ɗauki gaba da yan gidan, ba wanda take kulawa, ko abincinsu ba ta ci." "Ta shirya tsaf cikin uniform ɗin ta, ta shirya ta fice." "Nabila ce a tsaye a gaban kotu ta nemi kotu ta bata damar gabatar da shaidun da take da su, wanda" ba ta gabatar ba a kotun baya. "Kotu ta bawa Nabila dama, Nabila ta taso wata mata, matar ta zo ta tsaya a gaban kotu Nabila ta" "ce ""Hajiya ko zamu iya sanin sunanki?""" """Sunana hajara wali""" """Wacece ke a wurin rahama?""" """Ni mahaifiyarta ce, 'ya ta ce""" """Ko zaki iya yi wa kotu bayanin meyafaru""" "Mahaifiyar ramma, tayi bayani tiryan-tiryan." """Kin san wannan?"" Tayi maganar tana nuna mata dattijon." """Eh, tare da shi muka yi ta ɗawainiyar zuwa kai rahama Asibiti""" """Shi ne ya dawo ya ɗauke ta?""" "Ta girgiza kai ta ce ""Ba shi bane ba, wancan matashi ne""" "Nabila ta ce ""Yanzu ina rahama take?""" "Cikin kuka ta ce ""Ban sani ba, tun da ya ɗauke ta ban sake ganinta ba""." """Kafin ya zo ya ɗauketa meyafaru?""" "Ta goge hawayenta ta ce ""Wata mata ce ta zo ta ce mu karɓi kuɗi, a rufe maganar, na ce ban yadda ba, hakkin 'ya ta nake nema, shi ne bayan ta tafi ya zo ya ɗauke ta, bayan kwana biyu ya dawo ya" "ce mini na bashi kayanta, ta zama mallakinsa""" """Ko zaki iya gaya mana sunan matar?""" "lauyan gwamnati, ya nemi kotu ta dakatar da Nabila, tambayoyinta na ƙoƙarin ƙetare iyaka." "Ya taso zuwa gaban majaifiyar ramma ya ce ""Hajiya wanda ya zo ya tafi da itan, bayan ya tafi da" "ita, meyasa baki sanar da jami'an tsaro ba?""" """Na sanar da su, amma suka ce na je gida za su neme ni""" """Da basu nemeki ba kin koma?""" """Na koma har na gaji, amma babu wani cigaba""" """Sai aka neme ki aka rasa, ko sama ko ƙasa""" """Bibiyar abi mini hakkin 'ya ta da nake yi, ya sanya aka fara yi mini barazana, shiyasa na bar" "gidan"" ya yi wa kotu godiya ya koma ya zauna." "Nabila ta sake komawa gaban kotu ta kalli dattijon nan ta ce ""Baba a kotun baya, ka amsa kai ne" "ka yi wa rahama fyaɗe, shin da gaske kai ne ka yi mata fyaɗe?""" "Ya girgiza kai ya ce ""Cewa aka yi idan na ce bani bane ba, abun da ya samu rahama zai samu" "'ya'yana""." """Meyafaru ranar da abun ya faru?""" """A ranar aka ɗaukko ramma daga ƙauye, akwai ƙanin matar gidan ya zo a buge, ya tambayeni matar gidan sun dawo, na ce masa a'a, amma ya shiga, bayan wani lokaci ya fito ya ɗauki motarsa ya tafi. Sai bayan zulai ta dawo daga sayayya, ta fito tana ihu, ta ce na zo na gani, muka tarar da" "ramma a kwance a ɗakin girki, cikin jini""" "Nabila ta ce ta gama tambayoyin da zata yi, mai shari'a ya ɗaga shari'ar zuwa sati biyu domin" yanke hukunci. "Suka fito tare da barrister Habib da mahaifiyar ramma, da yaran dattijon, ta ce ""In sha Allah, mune" "ke da nasara, hukuncin da kotu zata yanke zata yi mana adalci""" "Barrister Habib ya ce ""In sha Allah, komai ya kusa zuwa ƙarshe""" "Nabila ta ce ""Zai dai zo, burina kawai a wanke baba, daga nan mu ɗora da cigaban shari'a"" iyalan" dattijon suka din ga yi mata godiya. FEW DAYS BACK "Cikin tsananin mamaki, kankarofi yake kallon Nabila. Ya ce ""Barrister, ke ce da kanki a office ɗ" "ina? Ya aka yi ki ka san wurin nan?""" "Tayi murmushi ta ce ""Ba abun mamaki bane ba, matambayi ai baya ɓata, yau gani a ofishin masu" "ƙasa""" "Ya ce ""Allah ya sa ba laifi nayi ba aka zo kama ni?""" "Ita ma murmushin ta yi masa ta ce ""Yan sanda ai su ne suke kama mutum"" ya bata izinin zama." "Ta samu wuri ta zauna ta ce ""Na yi sa'a, kana kano baka tafi Abuja ba kenan?""" """Eh, ina hutu ne, amma haryanzu mamaki nake yi, yadda aka yi ki ka tako da kanki, ki ka zo har" "in da nake""" "Ta numfasa ta ce ""Ka san komai dalili ne yake kawo shi""" """Haka ne, bari na saka a kawo miki abu mai sanyi""" "Ta ce ""A'a, Alhamdilillah tambayoyi ne nake da su a gareka Yallaɓai""" """To gimbiyata ina jinki""" """Case ɗin da nake yi, na yarinya da aka yi raping, ashe a gidanka aka yi. Na sake komawa na lura da sunan street ɗin sunanka ne, kuma na tambaya aka nuna mini gidan aka ce naka ne. Abun ya ɗ aure mini kai, sai dai na jajje amma ban samu abun da nake so ba, matar gidan ta koreni, kusan" "sau biyu ma, yaya aka yi haka yallaɓai?""" "Yayi murmushi ya ce ""Waye ya ce miki gidana ne?""" """Sir gidanka ne mana, Mu'azzam wada kankarofi street, kuma aka nuna mini gidan aka ce gidanka ne, sir ban yi tsammanin haka daga gareka ba, ɓoye mai laifi a ɗorawa wanda bai ji ba bai gani" "ba mai gadinka?""" """Nabila, ina iyakar ƙoƙarina, am even supporting you, baban yaron nan abokin adawata ne," "matata kuma akwai yara a tsakanin mu, bai kamata na tona mata asiri haka anyhow ba""" """Amma yarinyar mutane da aka zalunta fa? Maigadinka da aka rufe ba da laifinsa ba fa? Wannan" "ba hujja ba ce ba, what if ɗanka aka yi wa haka? Haba yallaɓai""" """Nabila, lamarin ƙasar nan ya wuce duk in da ki ke zato? Dole sai mutum yana lissafi, amma in tambaye ki mana? Waye ya ajiye miki tarihin Bunkure a Office ɗin ki? Waye ya tura miki message ɗin babar ramma? Duk kina tunanin wannan, ko kuwa kawai sabgarki ki ke yi?"" Waro" ido ta yi tana kallonsa. """Mayar da idanun madam""" "Cikin mamaki ta ce ""But how?""" """Through barrister Habib my dear. Ba zan tona wa yaron asiri kai tsaye ba, saboda ubansa ne tushen lalata shi, ba kuma nayi haka ne dan na ɓoye laifinsa ba, ina jan ƙafa a lamarin ne, saboda ki gano komai a sannu, yadda babu mai zargina, duk da akwai jiƙaƙƙiya tsakanina da ubansa." "Mahaifiyar ramma na tare da ni, ni na saka aka ɗauketa, tun kan a illata ta saboda case ɗin nan. Zan haɗa ki da ita, zata yi miki bayanin komai, amma ki daina zargina a kan ɓoye mai laifi, am supporting you, program ɗin ma da ki ke yi am supponsoring the program sweetheart, ki daina zargina please, tabbas a gidana aka aikata laifin, kuma ina iya ƙoƙarina a kai madam. Ki je ki" "cigaba da aikinki, zan cigaba da ƙoƙarina in taimaka miki""" Saroro tayi tana kallon kankarofi kamar sokuwa. """Akwai alamar gajiya a tare da ke, ki je zan saka Habib ya kai ki in da take""" """Amma duk tsawon wannan lokacin, kuka rufe ni ka ke yi mini yawo da hankali?""" """Akwai dalili ne, amma ki yi haƙuri dan Allah, a dalilin haka aka saka miki wuta a office, aka kusa taka ki da mota, duk dan ina tsayawa ina tsawatar wa ne, akwai hatsari a abun da ki ke yi nesa ba kusa ba, shiyasa nake taimaka miki ta ƙarƙashin ƙasa, amma kiyi haƙuri"" ba ta ce masa" "uffan ba, ta ɗauki jakarta za ta fita." """Ina baƙonki kuwa? Idan kun sake haɗuwa ki ce ina gaishe shi"" ta tsaya ta waiwayo ta ce ""Wane" "baƙon kuma?""" """Viper"" ya amsa mata kai tsaye." """Ka san Viper?""" "Kankarofi ya ce ""Na san shi, akwai labari mai sarƙaƙiya ne, amma kar ki matsa, ki bi a hankali, zai kawo ƙarshen labarin, kamar yadda ya faɗa, a sauka lafiya abar ƙaunata"" ba ta iya magana ba, ta murɗa ƙofar ta fice." "Tun a hanya ta kira barrister Habib, take yi masa masifa, a kan abun da ya yi mata, ya din ga yi" mata yawo da hankali da nuna bai san komai ba. "Sai da suka haɗu, yayi ta bata haƙuri, yana ƙara yi mata bayani, kankarofi yayi mata kwarjinin da" "bata tsigale masa ba, amma ta yi wa Habib ta tas." **** "Nabila tana tafe tana kallon hotunan hannunta, ta kira Viper ya ɗaga ta ce ""V ina wuni?""" """Lafiya ƙalau, ya ake ciki?""" """Ina hanya zuwa zan yi""" """To, Allah ya kawo ki lafiya""" **** "Ramma ta tsurawa Abdul ido, ya ce kunun gyaɗa yake so, yana sha yana waya, ya ajiye kofin kunun ya ce ""Daddy ni dai dan Allah ka yi haƙuri, wallahi ba zan iya fito maka da rahama ba""" "Ashariya Indabo ya din ga zabga masa, ya ce ""Wallahi zan saka jami'an tsaro su kama ka, su ci ubanka, uwar yarinyar nan ta bayyana a kotu, an ambaci sunanka, duk da ba a faɗi cikakke waye kai ba, ga maganar kuɗi na yi maka, duk ka yi kunnen uwar shegu da ni, Abdul kana son ka gama" "da duniya lafiya kuwa? Dole sai ka tozarta ni?""" """Daddy ba tozartaka zan yi ba, makomar rahama nake dubawa ita ma...." "Wata ashar ɗin indabo ya lailayo, kamar ba babba ba, ya gama masifar, Abdul ya ajiye wayar ya" dafe kai. """Kai ma da naci kamar me, ka fitar da ni mana, ko ma me za ayi mini ayi mini, sai ɓoye ni ka ke yi kamar ciwo, ni kaina tun ina masifa har na gaji, haba dan Allah"" tsaki ya ja, ya tashi ya bar mata" dining ɗin. *** """Abba ya yi tafiya, yau nake saka ran dawowarsa, zan nuna masa hoton nan, na ji mai zai ce, tun da kai kaƙi gaya mini wacece?""" """Yaya shari'ar ta kasance?""" """Alhamdilillah, babar ramma ta je kotu ta bayar da shaida, ina jin alamar nasara in sha Allah""" """Mhmm, a ina aka ganta?""" """Ta gudu ne wani wuri ta ɓuya, daga baya da taimakon barrister Habib, muka ganota""" "Viper ya jinjina kai ya ce ""ya nawa, ni ya ake ciki?""" """Shiyasa na zo ai""" """Ok""" """Kamar yadda na fara gaya maka jiya, dole ina buƙatar su oga walid, da wannan bugaggen a kotu" "su bayar da shaida""" """Wane bugaggen?""" """Oho ni na san sunansa ma? Amm sannan sai ka yi haƙuri, duk wasu rashin ji da ka yi, sai mun yi" "exposing ɗin su a kotu""" """Rashin ji kamar yaya?""" "Ta kalleshi ta ce ""Kamar yadda ka yi mana, sara suka, ƙulla wiwi black market duk da ka yi""" "Haɗe rai yayi ya ce ""Amma ba prison zan koma ba ko?""" """Idan ta kama ai dole ka koma""" "Ya ce ""What? Gaskiya ki yi yadda zaki yi, ba zan koma prison ba, wanda nayi 5yrs fa?""" "Ta zumɓura baki ta ce ""Ni na ɗaureka, sai abun da ya kama kawai, bari na je gidan, na ji wadda" "zamu yi da su, sai anjima""" ***** "Nabila ta tafi ɗakin Abba, domin amsa kiran da yayi mata, ta tafi bakinta ɗauke da addu'a, ta" "shiga ɗakin da sallama, suka amsa ban da Abba da yayi shiru ransa a ɓace." "Ta je ta durƙusa ta ce ""Abba gani""" """Nabila ban isa na gaya miki magana ki ji ba ko?"" Tayi shiru ta sunkuyar da kai." """Dole sai kin nuna wa duniya cewa ban haife ki ba ko Nabila? Kin nuna mini iyakata, ban isa na" "nemi alfarmarki ba kenan ko Nabila? Sai kin tozarta ahalin nan gaba ɗaya ko Nabila?""" "Ta girgiza kai ta ce ""Abba bani da wannan burin, kuma wallahi ba zan taɓa aikata wani abu da zan janyo maka zagi ba. Amma dan Allah Abba a yanzu, ka yi mini wani taimako, saboda zatin Allah" "kar abun da zan nema ya ɓata maka rai""" "Ta miƙa wa Abba hotunan, da Viper ya bata, ta ce ""Dan Allah Abba wacece wannan? Ni dai na san" "ba ni ba ce ba, dan Allah Abba ko kana da masaniya a kan ta jikin hoton nan." "Abba ya saka hannu, ya karɓi hotunan yana dubawa." "Ya gama ƙarewa hotunan kallo, ya ce ""A ina ki ka samu hotunan nan?""" Ayshercool 08081012143 ₦500 ne via 0009450228 Aisha Adam jaiz bank sai shaidar biya ta 08081012143 Wanda za su jira document 1K ne. 90009343 'Yan Nijar ku turo katin airtel na 300fcfa https://whatsapp.com/channel/0029Va9QtrY4dTnBYG1hST2VHADARIN *BRIGHT PENS SECOND BATCH* "Ku kasance da littatafan bright pens, second batch." *ƘARFE A WUTA (AYSHERCOOL)* *MUTALLAB (NIMCYLUV)* HADARIN GABAS (NAZEEFA NASHE)* *ZAYTOON (ZEE KUMURYA)* "Ta ɗan yi shiru sannan ta ce ""A office ɗina na gansu""" "A take Abba ya fara yayyaga hotunan, cikin kuka ta ce ""A'a Abba, dan girman Allah ka gaya mini idan ka san ta jikin hoton, Abba ba ka ga yadda kamaninmu suka ɓaci ba, dan Allah Abba ko sau ɗaya ka nuna mini wani a dangin mahaifina dan Allah Abba"" ƙarasa yayyaga hotunan yayi, ya watsa mata cikin matsanancin ɓacin rai ya ce ""Ki koma in da aka baki hotunan, su gaya miki koma wacece, ubanki kuma ga hanya nan, ki bar mini gida ki tafi yawon nemansa, yayi miki abun da ban yi miki ba, tashi ki bar gabana kan na tattaka ki, da uban naki ya damu da ke, da zuwa" "yanzu shi ya nemi in da ki ke""." "Anty ta ce ""Haba major, dan Allah ka yi haƙuri kar ka yanke wannan tsatstsauran hukuncin a kan" "ta, kayi haƙuri dan Allah "" gaba ɗaya jikin Nasir yayi sanyi, ganin yadda take ta uban kuka." "Cikin tsawa Abba ya ce ""Ki tashi daga gabana, ki tafi ki bar mini gida, ki je ki nemi ubanki, amma" "ki bar mini gida kar na sake ganinki a gidana""" "Wata irin ajiyar zuciya ta din ga yi, ta yinƙura ta tashi da kyar, ta bar ɗakin, ta koma ɗakinta ta kifa a kan gadonta, ta fara sabon kuka, shi kuwa Abba wace irin zuciya ce da shi haka? Ko menene a tsakanin sa da mahaifinta, yakamata ace ya wuce, ta san ya gama yi mata komai a rayuwa, yayi playing role ɗin uwa, yayi na uba a rayuwarta, amma duk da haka gurbin ido ba ido" bane ba. "Baba magajiya ce tayi sallama, ta ƙarasa kan gadon, ta dafa kafaɗarta ta ce ""Haba Arfa, ke a rayuwarki ba zaki iya haƙuri da tawakalli ba, tun da ya nuna miki baya son zancen nan ba sai ki ha" "ƙura ba, shekara nawa ana abu ɗaya kin ƙi ki gane ki haƙura""." "Nabila ta tashi zaune, idanunta sun yi jawur ta ce ""Baba magajiya""" """Na'am arfa""" """Kema laifina ki ke gani?""" Baba magajiya ta yi shiru tana kallonta. """Ki bani amsa mana, laifi nayi dan na nemi sanin in da mahaifina yake na ganshi ko sau ɗaya?" "Baba magajiya mahaifi fa, a duniya na san Abba ko baki yayi mini, sai ya kamani, bana nufin yi" "masa butulci ko tozarta shi, amma ina son sanin babana, baba magajiya dan Allah ina da wata yar uwa ne? Ke kin san komai, hoto aka bani da wata a jiki irina ɗaya da ita sak, ko yar uwata ce, dan Allah ki gaya mini. Ni idan kin san in da zan ga babana ki gaya mini, ko sau ɗaya na je na ganshi" "na dawo dan Allah""" "Baba magajiya ta girgiza kai ta ce ""Ni ban san komai ba, lokacin da na zo gidan nan, an gama" "dambarwar da za ayi, na zo, ni bani da wani labari a kan mahaifinki""" "Nabila tayi murmushi mai ciwo, hawaye na bin fuskarta ta ce ""Haryanzu kallon yarinyar da ki ka raina ki ke yi mini ko, shiyasa ki ke tunanin bani da wayo ko? Shekaru ashirin da biyar a doron duniya, ai na girmi ki yi mini wayo baba magajiya, amma shikenan, ai Abban ya ce na je ne nemi" "babana, zan neme shi kuwa in sha Allah """ "Baba magajiya ta waro ido ta ce ""Baki san gatse ba Arfa?""" "Nabila ta jinjina mata kai alamar eh, ta mayar da kai ta kwanta." "Baba magajiya ta ce ""Arfa na san har da damuwar matsi da takura da ake yi miki a gidan nan, ya sanya ki ke damuwa da son ganin mahaifinki, ni dai roƙona da ke, ki yi haƙuri idan da rabo zaki haɗu da mahaifinki ko danginsa, amma dan Allah dan Annabi, kar ki bari ku samu saɓani" "da maitama""" "Nabila ta yi mata shiru, dan gani take yi babu wanda zai fuskanci halin da take ciki." "Tamkar zuciyarta Abba ya yaga, haka take jin zuciyarta, idan ta tuna yadda ya yayyaga hotunan" "nan, sai dai har a lokacin tana ganin hotunan yarinyar mai kama da ita a cikin idanunta." **** "Duk da Nabila bata jin daɗin komai na duniyar, jin ta kawai take yi gata nan dai, haka ta cigaba da up and down a kan muhimman abubuwan da ta saka a gaba." "Ta sake shigar da koke gaban hukumar'yan sanda, ta nemi su kama madaki da wasu daga cikin" "yaransa, bisa zargin kisan matar Viper, shekaru shida da suka gabata." "Yau tana da program a gidan radio, kuma yanayinta ya nuna wa Sumayya tana cikin" "matsananciyar damuwa, sai dai ta shigo a ƙurarren lokaci, zasu fara gabatar da shirin, dan haka ba ta samu damar yi mata tambayar meyake damunta ba." "Nabila tayi iya ƙoƙarin ta, wurin ajiye damuwa a gefe, suka fara gabatar da program." "Sumayya ta kalli takardar hannunta sannan ta ce ""Jita-jita ta cika gari, cewa kin shigar da koke gaban kotu, a kan lallai kotu ta hana hukumar'yan sanda kamar shahararren ɗan ta'addan, da addabi wani yanki na garin nan, kuma akw zargi da kisan matarsa, duk da yadda hukumar ta 'yan" "sanda, take nemansa ruwa a jallo?""" "Nabila ta kalli sumayya da rinannun idanunta, tayi mamakin yadda sumayya tayi mata wannan tambayar, a tsakiyar program ɗin su haka, saboda ba magana ce da ta fita ba, balle ta ce an yi" "Jita-jita a kai. Sumayya ma ta tsare ta da ido, alamar tana jiran amsa." "Tayi wani irin murmushi ta ce ""Ba ɗan ta'adda bane ba, mutum ne kamar kowa, kuma ɗan ƙasa da ya dace ya samu duk wani 'yanci da kowane ɗan ƙasa ya dace ya samu. 'yan ta'adda na yawonsu a gari, an san in da suke, an san in da za a same su, hakkinsa muke nema a kotu, ba shi ya kashe matarsa ba. Na san mutane za su yi mamakin yaya aka yi mai dokar bacci ya ɓuge da" "gyangyaɗi, amma a bibiye ni a cikin shari'ar da zamu gudanar""." """Amma ba kya ganin hakan kamar taka doka ne, zaki yi amfani da damarki ta lauya ki taka doka," "ki kare mai laifi?""" """Sam, dokar da aka wulaƙanta, da ita nake son yin amfani wurin gyara kuskuren da aka yi. Tayaya mutum zai shafe shekaru babu Shari'a, daga baya alƙali da saka hannunsa da umarninsa da komai, a sake shi bisa doron doka da ƙa'ida, kuma daga baya a zo ana nemansa. Shin wanke shi aka yi daga laifin? Ko kuma akwai wani ɗaurin ɓoye da yakamata a warware? "" Tayi maganar tana ƙ" ure sumayya da ido. "Sumayya ta kalli agogo, lokaci ya cika, ta na tsaka da sallama da masu saurare, Nabila ta tashi ta" "fice, tana kammalawa, ta tashi ta bi Nabila, amma tuni ta ja motarta ta bar wurin." "Ta koma tana sauke numfashi, kiran kankarofi ta gani, ta ɗaga wayar suka gaisa, ya ce ""T ladan," "meyasa ki ka yi wa Nabila wannan tambayar a tsakiyar program?""" """Sir nayi ne, dan tun yanzu ta kare kanta a wurin mutane, kafin abu ya bayyana su yi mata kallon," "maciya amana mai fuska biyu """ """Sumayya waye ya gaya miki ana iya wa ɗan adam ne? Ba a taɓa iya wa mutum, dan haka ki kiyaye gaba, yayi wuri ki fallasa abun haka gaba ɗaya, amma babu laifi, baki yi kaifi ba, hakan" "zai ƙara mata ƙaimi""" "Sumayya ta ce ""Ok sir, na gode"" ta ajiye wayar ta yi shiru, ita a zahiri tayi hakan ne, ko Allah zai sanya Nabila ta ji nauyin dubban al'ummar da suke goyon bayanta, ta sassauta koma ta haƙura da" "batun Vipern nan, amma ba ta ga alamar hakan a tattare da ita ba." "Abbu kuwa a zabure ya miƙe tsaye, jin program ɗin da yayi, shi ba wani ma'abocin jin radio bane ba, yau kawai ya kunna yana saurare, ya ji shirin ya ƙayatar da shi, haka zalika muryar barrister, kamar sananniya ce a gare shi." "Sai dai jin sun yi maganar Viper, ya sanya ya tashi a kiɗime, tare da ɗaukar radion ya fito tsakar" gida. "Rahila ta ce ""Ya dai na ganka a firgice haka?""" """Wani shiri na gama saurara, wata lauya ta shigar da koken kotu ta hana kama Aminu, ko gidan" "radiyon zan je, wataƙila su sun san in da yake""" "Ta kwaɓe baki ta ce ""Ina rabaka da sabgar yaron nan, idan sun san in da yake me zaka yi masa? Salon ka sanya kanka a masifa, wanda ake nema ruwa a jallo da laifin kisan kai? Ka ganshi ka yi" "masa me? Guduwa fa yayi daga gidan yari""" "Ya ƙura mata ido, kawai ya girgiza kai, ya kashe radion ya fice." **** "Nabila tana driving, wani abu ya tsaye mata a maƙogwaronta, kukan ma gaba ɗaya ta kasa saboda" baƙin ciki da ɓacin rai. "Katafaren gate ɗin aka buɗe mata, ta shiga da motarta, tayi parking, ta sauka ta nufi cikin gidan." "A falo ta tarar da mahaifiyar ramma, tana ganin Nabila, ta tashi da fara'arta, tana yi mata sannu da" zuwa. "Nabila ta zauna cikin yaƙe, suka gaisa, kamar kullum yau ma mahaifiyar ramma, kallon Nabila take yi, kamar ta haɗiyeta, ita dai ban da an yi mata gargaɗi, da tuni ta faɗi abun da yake ranta, dan ta tantance abun da take tunani, sai dai an gargaɗeta a kan aikata hakan, dan haka ta ja bakinta ta" tsuke. """Mama ina fatan dai babu wata matsala ko? Ki cigaba da haƙuri, in sha Allah an kusa dawo miki da ramma, kuma hujjoji nake son kammala tattarawa, na gano ainihin mai laifin, za a gabatar da" "shi a gaban kotu, idan da wani abu ki gaya mini""" "Ta girgiza kai ta ce ""Ba wani abu, ina ta godiya Ubangiji Allah ya baki nasara, na gode sosai da sosai da ke da Alhajin da ya taimake ni, ina godiya Allah ya biya ku, ya ƙara miki zaman lafiya da" "mijinki""" "Nabila ta ce ""Ai ba mijina bane mama""" """A'a ba Alhajin ba, Aminu""" "Cikin mamaki Nabila ta ce ""Aminu kuma? Nifa ban taɓa aure ba, ba ni da aure"" tayi maganar tana" murmushi. "Babar ramma ta ɓoye mamakinta, kar kwaɓarta tayi ruwa ta ce ""Au, ai na zata kina da aure ne, Allah ya kawo miki nagari, ya baki mai sonki da gaskiya, Allah ya tsaya miki, kamar yadda ki ke" "ta ƙoƙari a kanmu""" "Nabila ta ce ""Amin mama, dan Allah a cigaba da yi mana addu'a, addu'aeku, ita ce ke tasiri a" "rayuwarmu""" "Maman ramma ta ce ""In sha Allah, addu'a yanzu aka fara""" "Nabila ta ce ""Na gode sosai"" ta tashi ta nufi hanyar fita, babar ramma ta bi ta da ido, dan ranar" "farko da ta fara ganin Nabila, ban da an gaya mata kafin ta zo, an yi mata bayani, da babu abun da zai hanata kurma ihu, ta ce taga gawa." "Tana driving sannu a hankali, ta tsaya ta sai abun da zata ci a gida, dan ba sabgar su take shiga ba." "A harabar gidan, ta wuce Nasir, ya zuba mata ido, duk ta bi ta rame, saboda ta saka jaraba a ranta," "ko kallonsa ba ta yi ba ta wuce. Duk sai ya damu da ramar da ya ga tayi, amma yana nan a kan bakansa sai ya kama Viper, ko zata mutu dan haushi." """Ga agolancin ga yawon ta zubar, ga ta'addanci, gashi an gandame an riƙa a gida babu aure, abun" "bai yi miki yawa ba kuwa Nabila"" Sauda tayi maganar tana dariya." "Ta sake cewa """ "An baki damar ki gusa ki bamu wuri, saboda baƙin naci, kin liƙe mana a gida, tun da ba zaki tafi ba, ki iya kanki, muna son ubanmu, ba zaki kashe mana da baƙin cikin ki a banza ba""" "Nabila ta tsaya cak, tare da murnar Sauda ta takale ta, ko banza ta rage zafi idan ta yaɓa mata" magana. """Ke da ki ke son uban naki, sai gashi kin gagara zaman aure, kin ƙi karatu balle hankalinsa ya kwanta. Ai sauda zaki yi mini gorin aure ne, a lokacin da ke ki ka iya zama a gidan naki mijin. Kuma karki manta da ni agola ce mai 'yanci, a dalilina igiya biyu aka sauke wa babarki ta aure, idan ku ka cigaba da matsa mini, ragowar ɗayan ma sai na tsinketa, sai ku ji daɗin zawarci tare ga uwa ga 'ya. Yawon ta zubar kuma, ina da abun bayar wa yayi mini rana, kema idan ki na so ki" "bayar nonsense""" "Sauda ta tashi a ƙufule, Nabila ta ce ""Kin san dai ba dakuwa zan yi ba, dama koma wa ki ka yi ki" "ka zauna""" "Sauran wanda suke wurin, suka tuntsure da dariya, dan yadda Sauda ke zuba mulki da rashin" "mutunci a gidan nan, Nabila ce kawai maganinta." **** "Cikin mamaki Abdul ya ɗago ya kalli indabo, saboda marin da ya kwaɗa masa." """Ina na kai mini kuɗi Abdul?""" Abdul ya yi shiru yaƙi magana. """Ka gaya mini in da ka kai mini kuɗi, kafin na tattaka ka a wurin nan? Yarinya da ka fito da ita, da kar ka fito da ita, matsalarka ce, ba zaka kashe ni da ɓacin rai ba, sai na samo wani wanda ba zai" "watsa mini ƙasa a ido ba, ina ka kai mini kuɗi?""" "Mahaifiyar Abdul ta ce ""Abdul wai ba magana ake yi maka ba? Ina kuɗin da ya zuba a account ɗ" "in ka, da sunan campaign kuma ya muka yi da kai a kan yarinyar nan?""" "Abdul ya numfasa ya ce ""Na yi wa 'yan garin su rahama gyaran makarantu da hanyoyi, na yi musu" "boreholes, sai kuma registration da nayi mata na karatu bar zuwa jami'a"" ya faɗa kai tsaye." "Salallami suka hau yi, da tafa hannu." "Indabo ya ce ""Abdul, kuɗin ka kwasa ka ƙarar a kan garin yar matsiyata da karuwa?""" "Ya girgiza kai ya ce ""Daddy ba karuwa ba ce ba, koma menene ni ne mai laifi, fyaɗe nayi mata," "nayi hakan ne, dan na goge laifina""" "A fusace Indabo ya rufe shi da duka, ga ƙiba ga hawan jini yana fama, a take ya hau haki, da kyar" P.A ya janye shi daga jikinsa. """Ƙarya ma kake yi, ka fito mini da kuɗina, sai na yi seazing ɗin asibitocinka, da duk wata kadara daka mallaka, da wadda na mallaka maka, ni zaka tonawa asiri, wallahi baka isa ba, kuma zan" "saka a nemo mini yarinyar ko ina ka kai ta, zan yi maganinka daga kai har ita""." """Dan Allah daddy kar ka cutar mini da ita, ba tayi laifin komai ba, ni zaka hukunta""" "Ashariya ya din ga zabgawa Abdul, yama rasa me zai yi, kuɗin da suka yi sama da faɗi da su, domin campaign bisa ga yarjejeniyar idan an yi nasara zasu mayar da kuɗin da uwar riba, ga balli na neman tashi, dama kuɗin mutane ne na wasu hukumomi a ƙasa, ga balli na neman tashi, kuma" Abdul ya yi masa hauka. "P. A ya ce ""Kayi haƙuri, kar ka je wani abun ya sameka, ka rabu da shi, zamu san abun yi, mu fara" "kashe case ɗin can na gaban kotu tukuna""." """Na fara tunanin anya Abdul ɗa na ne? Ƙiriƙiri ya zaɓi mace a kaina, ni zai tozarta?""" "P.A ya ce ""Jarabta ce da kuma ƙuruciya ke damunsa""" """A shekara talatin da shidan ne ƙuruciya?"" P.A ya din ga bashi haƙuri yana lalaɓa shi, Abdul kuwa" tunu yayi ficewarsa. ***** "Madaki na zaune a cikin ɗaki, ya din ga jin hayaniya, da iface-iface ana sara suka a ƙofar gidan" da yake. "Wani daga yaran sa ya shigo da kyar, ya ce ""Madaki, yan ƙofa ne fa suka zo gidan nan, muna ta" "fama da su, sai ƙoƙari suke lallai sai sun shigo gidan nan, su sareka""" "Madaki ya tashi ya ƙwalalo ido, sai dai kan yayi magana, sun faɗo gidan, sun kai su bakwai, suka" "zo ka hau shi da sara da suka, wasu na waje na faɗa da yaran madaki." "Duk da akwai ƙarfin zuciya, yana ta ƙoƙarin kare kansa, amma sai yaji jikinsa kamar an canza masa wani, duk yayi wani iri babu ƙwari, suka din ga saransa, ƙarshe suka janyo shi daga cikin gidan, suka din ga jan sa a ƙasa tamkar abun banza, duk da iya ƙoƙarin da yaransa suka yi, su ƙ wace shi, amma abu ya ci tura, tsofaffin yaran Viper, da yan unguwar su, da ya din ga shiga yana addabawa ya hana su sukuni, su suka yi gangankon ɗaukko shi, suka yi masa laga-laga, suka din ga yawo da shi, lungu da saƙo, daga ƙarshe da ƙyar jami'an tsaro suka kawo masa ɗauki, suka" "tarwatsa matasan, suka ɗauke shi a galabaice, dan ba su zaci yana raye ba, suka kai shi Asibiti." ***** """My Abdul"" ta yi maganar tana murmushi, cikin hanzari ya ɗago, dan bai zaci daga bakin ramma maganar ta fito ba." """Meyafaru ne? Gaba ɗaya na ganka a cikin tashin hankali?""" """Rahama abubuwa sun ƙara cakuɗe mini, barin ƙasar nan zamu yi""" "Cikin mamaki ta ce ""Mu bar ƙasar nan, mu je ina?""" """Rahama abubuwa ba zasu tafi yadda na tsara ba, zamu bar Nigeria""" """Ban gane ba, uwata fa?""" "Abdul ya ce ""Zan saka a kawo miki ita, yanzu visa za ayi miki, amma sai na fara barin garin nan" "da ke""" """Abdul, ni fa gani nake wannan guje-gujen, duk ba zasu kaimu ba, kayi haƙuri ka yi abun da" "mahaifinka ya buƙata mana""" "Ya kalleta ya ce ""Na kai ki kotu ki gaya wa duniya, ni ne nayi miki fyaɗe? Ba wannan ne ya dame" "ni ba, abun da zai biyo bayan shaidar da zaki bayar shi ne abun jin, dan haka ki nutsu kiyi abun da na ce kawai""" "Murmushi ta yi masa da ita kaɗai ta san ma'anarsa, ta wuce shi ta tafi kitchen." **** "Daga Naja'atu har Indabo fuskokinsu ɗauke da damuwa, Bunkure tayi ƙwafa ta ce ""Gaba ɗaya hankalina a tashe yake, lallai gaskiyar hausawa, ɗan hakin da ka raina, shi ne yake tsole maka ido, yarinyar nan dai ta dage sai ta ga bayana, idan asirina ya tonu, ban san wane irin kallo zan yi wa al'umma ba. Abdul duk shi ya janyo wannan abun." "P.A ya ce ""Duk ku kwantar da hankalinku, babu wani abu da zai faru, kamar yadda ka yi umarni, dattijon nan zai shiga silent, yanzu uwar yarinyar ta rage, ita muke binciken in da take, kuma ita" "ma zamu ganota in sha Allah, Abdul ma muna daf da gano, wurin da ya ɓoye yarinyar nan""" "Indabo ya girgiza kai ya ce ""Ban san in da Abdul ya koyi wannan baƙin taurin kan ba, magana ta fito fili, an ce a binciki ministocin da muka ƙulla harƙallar kuɗaɗen nan da su, na san kuma dole sai sunana ya fito, wai ya kwashe kuɗin nan, ya yi wa yan ƙauye ayyukan raya ƙasa, na rasa uban abun da ya samu a jikin yarinyar talaka mara galihu, ya nace mata take abun da ta ga dama har" "haka""" "Bunkure ta sauke numfashi ta ce ""P.A ya batun barrister Nabila?""" """Kamar yadda na gaya muku, sponsiring ɗin ta ake yi, na gwada sakawa a kamo mini ita, amma" "hakan ya gagara akwai jami'an da suke bin ta, wanda ba san suwaye ba, kuma da alama ita kanta ba ta san suna bin ta ba""" "Indabo ya ce ""Kar ku ja da nisa, kankarofi ne, babbar buƙatar sa ya ga ya kai ni ƙasa, ya rama" "abun da nayi masa, kuma yayi kaɗan""." ***** "Nabila na zaune a ɗakinta, tunanin ma ta rasa wanne yakamata ta yi, kawai ta ga Nasir ya shigo ɗ" "akin, ba ta ko motsa ba, balle ya sanya ran za ta kula shi." """Nabila""" "Ta ɗaga ido ta kalleshi. ""Da gaske ke ki ka nemi a hana kama Aminu Viper""" """Eh"" ta faɗa a nutse." """Nawa aikin ki ke burin ɓatawa kenan, me nayi miki haka ne?""" "Ta kalleshi ta ce ""Ba kai nake fatan ɓatawa aiki ba, duk wani mara gaskiya sai na ɓata masa aiki. Gaba ɗaya ka canza i miss my old DSP, the only person that understand me"" tayi maganar tana" tashi ta bar shi a ɗakin. "Tana office ɗin ta, tana son zuwa duba jikin malam garba, tana son zuwa wurin 'yan sanda, tana" "son ganin Viper, ga kuma maganar Abba da ta tsaye mata, da ya ce taje ta nemi ubanta, ta bar" masa gida. "Kenan Abba ya goyi bayan ɗan sa, shi ma a wannan karon ya nuna mata, gurbin ido ba ido bane ba." "Turo ƙofar office ɗin aka yi, ta tashi zaune sosai daga kashingiɗar da tayi, tana tunanin ina ta taɓa" ganin baƙon nata. "Ya samu wuri ya zauna, suka gaisa, ya ce ""Baki gane ni ba ko?""" "Ta jinjina kai ta ce ""Gaskiya dai""" """Haka ne, magana na zo mu yi da ke mai muhimmanci""" "Nabila ta ce ""Ok, ina jinka""" """Saƙo ne daga wurin distinguish Ma'aruf Indabo, na zo mu yi magana mu fuskanci juna da ke""" Nabila ta yamutsa fuska tana kallonsa. """Muna yi miki tayin ki fanshi kanki da kanki ne, kan abun da ba a so ya afku""" """Ɗan yi sauri, ina da wurin zuwa""" "P.A ya ce ""Maganar da na zo da ita, ta fi abun da zaki je yi muhimmanci, muna son ki janye" "shari'ar nan ta batun fyaɗe nan, case ne tsakanin ki da Bunkure, kuma ko yanzu kin cika burinki a kanta, akwai maƙudan kuɗaɗe muddin ki ka aikata abun da na ce""" "Nabila ta ce ""Malam na yi maka kama da shashasha ne? Da Bunkure nake case ɗina, meye nasa a ciki? Bibiyar rayuwata da ya saka aka din ga yi, da ƙoƙarin kashe ni, duk bai ishe ku ba, shi ne zaka zo mini da maganar bunkure? Wallahi idan kaga na bar case ɗin nan, to an hukunta ainihin mai laifin ne, kuma muddin wani abu ya same ni, kai ko mutuwa nayi, ina da manya manyan hujjoji a kan sa, da suke a hannun wakilai ne, akwai wanda za su ɗora, in sha Allah sai na bayar da misali a Nigeria, an fara hukunta masu riƙe da madafun iko, da iyalansu, ba wai doka a kan" "talaka kawai ba, everyone is equal before the law""" """Haka ki ka ce?""" """Hala kurma ne kai?""" "Ya ce ""To bari mu gani, yaro bai san wuta ba sai ya taka""" """Na santa farin sani, tun da na ɗaukko ƘARFEN CIKIN WUTA, da ya gagari hannaye da yawa""" "P.A ya kalleta ya ce ""Me ki ke nufi?""" """Zaka fahimta nan ba da jimawa ba""" "Yana fita tayi tsaki, ta ɗauki jakarta ta fita, a nan ta bar motarta, ta hau abun hawa ta tafi gidan" Viper. "Yana tsakar gida, daga shi sai ɗan mama a gidan, suna hira." "Sun daɗe suna kallon juna, sannan ta ƙarasa ciki, ta samu wuri ta zauna ba tare da ta ce masa" uffan ba. "Ya samu abu ya zauna, ya ce ""Ya ake ciki, meye labari?""" """Ko ka neme ni, kwana biyu ina cikin damuwa da tashin hankali, amma ko a jikinka""" "Ya tsuke fuska ya ce ""Menene?""" """Vi""" "Ya Kalle ta, tare da ɗage girarsa ɗaya." """Ka dubi girman zatin Allah, ka tausaya mini, ina ga ciwon zuciya na daf da kamani, kowa ya ja da baya ya juya mini baya, Abba ya yayyaga hotunan nan ya watsa mini, ya ce naje na nemi ubana na bar masa gida, daga shi har yan gidanmu, babu wanda yake kula ni. Gashi a tsakiyar program sumayya ta hau yi mini tambaya a kanka, yanzu ta ko ina mutane sai attacking ɗina suke yi a media, saboda case ɗinka, client ɗina malam garba wai ya yanke jiki ya faɗi na je na duba shi, na tarar wai ya samu stroke, yanzu P.A ɗin Indabo ya bar office ɗina da tashi barazanar, kuma haryanzu ka ƙi gaya mini dalilin da ya sanya Indabo yake bibiyata. Na rasa ya zan yi me zan yi ne? Kamar na gaza, ba wanda zan je na samu duk na gaya wa damuwata, dan Allah Viper ka gaya mini wacece ta jikin hoton nan, ina jin kamar ina da alaƙa da ita, tun da ni dai na san ba ni bace ba, dan" "Allah idan akwai wani abu da ka sani ka gaya mini, atleast na rage wata damuwar""." """Na gaya miki ban san komai ba, 'yan gidanku zaki tambaya""" """Na gaya maka ba zasu gaya mini komai ba, so kake sai na mutu ban san babana ba, idan kana da" "yadda zaka yi ka taimake ni dan Allah, ko hakan ne alfarmar da ya rage da zaka yi mini a rayuwa"" tayi maganar tana haɗa hannayenta biyu cikin sigar magiya." """Ana kiranki a waya""" """Ni ba ta waya nake yi ba, ka taimaka mini dan Allah""" """Ki ɗaga wayarki "" yayi maganar yana kallon ta." "Ta ɗaukko wayar, ta ga lambar barrister Habib ce, ta ɗaga wayar ta ce ""Hello""" """Na duba office ba kya nan, Allah ya yi wa malam garba rasuwa yanzun nan"" miƙewa ta yi tsaye," "ta saki wayar, ta tashi za ta nufi hanyar fita, jikinta yana rawa." "Cikin zafin nama, Viper ya tashi ya riƙe ta, gaba ɗaya ta gigice, ta ce ""Sun kashe shi, wallahi" "kashe shi aka yi""" "Ya ce ""Waye? Waye ya kashe shi?""" """Malam garba, wayyo Allahna, meyasa na karɓi shari'arsa, na janyo ya rasa raywarsa a banza, bani da sa'a wayyo Allah zuciyata"" wata irin miƙa tayi, kamar zata zare, ta fara kokowar ƙwace wa" "daga hannun Viper, tana kallon hanyar waje." "Ya ƙara riƙeta ya ce ""Abla, tsaya ki ji, ki nutsu""" "Magana take son yi, amma numfashinta ya din ga sama yana ƙasa, hannunta da ya riƙe, ya din ga" jin bugun zuciyar ta da sauri-sauri. "Ya ciro wani abu a jikinsa, ya saka mata a gefen wuyanta, gaba ɗaya jikinta ya saki." "Ya kalli ɗan mama ya ce ""Ka kira mutanen nan a waya, su aiko da mota, a kaita Asibiti""" "Ɗan mama yayi saroro ya ce ""A ina ta ajiye motar tata?"" Viper ya ƙura masa ido, ya ce ""Au," "ammm wasu mutanen?""" """A tunaninka duk abun da ka ke yi ban sani bane? Zaka kira su ko ni na kira su?"" Ɗan mama yayi" "wiƙi-wiƙi da ido, cikin tsoro da mamaki""." """Am talking to you, and you are looking at me"" ba shiri ɗan mama ya ciro waya yana kallon" Viper. **** """Abdul yau ka addabe ni, kamar nayi maka dukan tsiya haka nake ji""" """Sorry baby, kin san kullum ke ta musamman ce, i so much love the natural you""." "Ramma ta ce ""Wallahi ka isheni, duk ka dame ni""" """Wallahi wani mafarki nayi da bai yi mini daɗi ba, ya bani tsoro""." "Ramma ta ce ""Maganin wanda baya addu'a""" """Wallahi ina yi, har karatun Alqur'ani nake sakawa fa""" "Ta ce ""To Allah ya bada lada, yanzu ka bani wuri na je nayi wanka, zan yi salla""." "Ya tashi zaune ya ce ""Mu je, daga nan sai ki ɗan dafa mana wani abun, yunwa nake ji""" "Yayi maganar yana ɗagota, daga kwancen da take." "A tsakiyar gado suka din ga ciye-ciye da shi da ramma, suna yi yana tsokanarta, tana gaya masa ba" ƙar magana yana dariya. "Tamkar ya mayar da ramma cikin sa haka yake ji, kuma ya kasa ɓoye mata hakan, suka kwanta ya" "gama damunta, bacci ya kwasheta." "Juyi ta yi zata gyara kwanciyarta, ta ga Abdul a zaune, ya saka wayarsa a gaba, ya ɗora hannu a" "ka, yana wani irin kuka tamkar ɗan ƙaramin yaro." Ayshercool 08081012143 ₦500 ne via 0009450228 Aisha Adam jaiz bank sai shaidar biya ta 08081012143 Wanda za su jira document 1K ne. 90009343 'Yan Nijar ku turo katin airtel na 300fcfa https://whatsapp.com/channel/0029Va9QtrY4dTnBYG1hST2VHADARIN *BRIGHT PENS SECOND BATCH* "Ku kasance da littatafan bright pens, second batch." *ƘARFE A WUTA (AYSHERCOOL)* *MUTALLAB (NIMCYLUV)* HADARIN GABAS (NAZEEFA NASHE)* *ZAYTOON (ZEE KUMURYA)* "Tashi ramma tayi, ta ce ""Abdul, wai menene meyafaru ne?"" Yayi mata shiru ya cigaba da kuka." """Dan Allah kayi magana mana, ko mutuwa aka yi muku?""" "Yayi mata shiru bai yi magana ba, ta kai hannu zata ɗauki wayar, amma ya janye wayar ya kashe." "Kawai ya yinƙura, ya ɗauki mukullin motarsa, ramma ta miƙe ta riƙe shi ta ce ""Ina zaka je ne?""" """Fita zan yi""" """A wannan yanayin da ka ke? Idan wani abu ya sameka fa, dan Allah koma menene kayi haƙuri, zuwa Allah ya kaimu gobe, dan Allah ka haƙura da fitar nan"" jifa yayi da mukullin, ya koma ya" zauna ya cigaba da kuka. "Ta zauna a kusa da shi, cikin damuwa ta cire masa hannunsa da ya rufe idanunsa ta ce ""Abdul," "kalleni menene wai?""" "Ya sake sunkuyar da kai, kamar ita ce baya son haɗa ido da ita. A hankali ya kwanta a jikinta kamar ƙaramin yaro, ta rungume shi sosai, tana shafa kansa ta ce ""Koma menen kayi ta nanata Innalillahi wa Innalillahi raji'un, zaka samu sassauci in sha Allah"" wata irin ajiyar zuciya ya din ga" "yi, wanda sai da ya bata tsoro." """Rahama"" ya kira sunanta da kyar a galabaice." """Dan Allah ko na fuskanci hukunci, kar ki manta da ni, na san koma menene zuwa ki gama" "karatunki, zan fito""" """Tom"" ta faɗa a sanyaye, dan wasu lokutan har tausayi yake bata, gaba ɗaya Abdul ya saduda," duk wannan iskancin da rashin mutunci ba ya yin su. """Rahama kin ce mini kina da yaya da ƙani ko? Har su ina son in ɗauki nauyin su""" "Ramma ta ce ""Ba na gaya maka yayana ya mutu ba, sai ƙanina sani""" """Da gaske ki ke fyaɗe aka yi masa ya mutu?""" "Ta ce ""Oho ina na sani, ba ka ce mini ba a yi wa maza ba, ni kamar haka na so na ji an ce, wai za a samo masa aiki, yaje Abuja aka yi masa, amma mama ba ta taɓa zama ta gaya mini yadda abun ya faru ba, ko tunawa ba ta son yi, idan ta tuno da shi tayi ta kuka""" "Yayi ajiyar zuciya ya ce ""Ban san me zai faru ba, amma dan Allah duk tsanani kar ki rabu da ni, ki" "zama mai yi mini uzuri da tausaya mini dan Allah, Allah ma baya kama wani da laifin wani""" "Ramma ta ce ""Da bana yi maka uzuri, da bana tunanin zamanmu zai zo i yanzu, ka daina wannan" "kukan dan Allah kunya kake bani"" tayi maganar da sigar tsokana." Ya ƙanƙameta ya cigaba da sheshsheƙar kuka. """To ɗan jariri, ya isa haka, cikin dare kawai mutum ya tashi yana kuka, ko ka je ka yi alwala kayi" "salla""." """Ba zan iya ba, ba zan yi karatun sallar dai-dai ba""" """Kaga amfanin ibada ko, idan bawa ya tuna da Allah, lokacin da yake cikin yalwa, Ubangiji yana tuna wa da shi lokacin da yake cikin ƙunci, ka cigaba da addu'a, Allah ya yaye maka damuwar ka" "doctor Abdul yasar"" yayi lamo kamar kyanwa a jikinta, ba tare da ya kuma magana ba." **** "A hankali Nabila tayi juyi, tana ƙoƙarin gyara kwanciyarta kawai ta ga Viper a zaune a kan kujera, yana danna waya. Ta ƙura masa ido tana kallon sa." """Wannan kallon haramun ne, ki daina yi mini wannan kallon"" yayi maganar ba tare da ya kalleta" "ba. Ko ƙifta ido ba ta yi, ta cigaba da kallonsa." "Ya waiwayo sosai yana fuskantar ta, ya ce ""Ya aka yi ne? Ya jikin?""" "Ta ɗaga hannunta, ta kalli drip ɗin da yake shiga, ta ce ""Vi""" """Mmm""" """Ina ne nan?""" """Wurin sayar da mutane"" yayi maganar yana cigaba da danna wayar." "Ta lumshe idanunta ta buɗe, ta ce ""Kamar bacci nake yi, kuma kamar a zahiri ne, dan Allah da" "gaske malam garba ya mutu?""" "Viper ya ce ""Eh, ya mutu""" "Ta girgiza kai, tana kuka daga kwance ta ce ""Ai shikenan, ya mutu bai shaƙi iskar 'yanci ba, ban cika masa alƙawarin da nayi masa ba, da yaya zan kalli iyalinsa? Kullum da shi nake kwana nake tashi a zuciyata, ya mutu da mummunan tabo a zuciyarsa da rayuwarsa, ban cika masa alƙawarin" "da nayi masa ba, na gaza na kasa"" tai maganar tana fashewa da matsanancin kuka." """Ke, wai baki da tawakalli ne? Shikenan ke ba zaki mayar da lamarinki ga Allah ba? Wani ya ce" "ke ki ka kashe shi ne?""" "Ƙara sautin kukan ta yi, ta ce ""Ya ka ji da aka kashe matarka, ya zuciyarka tayi da aka ƙala maka laifin kisanta? Haka iyalan malam garba suke ji, da wannan ɗacin da baƙin cikin ya mutu, kuma ni ban yadda da wani stroke ne ya kama shi ba, wani abun suka yi masa"" Viper ya janyo kujerarsa gaban gadon sosai, ya matsa daf da ita, ya ce ""Ki yi haƙuri"" ta kalli cikin idonsa ta ce ""Kai yakamata na bawa haƙuri nayi alƙawarin saka kotu ta wanke malam garba, a gurfanar da ainihin wanda yayi laifin, amma ya rasa rayuwarsa ina kan ƙadamin aikin, na fara tsorata kamar ba zan" "iya ba Vi""" "Ya girgiza kai ya ce ""Zamu cigaba da ƙoƙari, ba zamu gaza ba, ba zamu sare ba, zamu yi nasara" "in sha Allah, idan kina cewa kin karaya, nima karaya nake yi"" ta ja wata irin ajiyar zuciya ta kalli rigar jikinsa." """Vi""" """Mmm""" """Me kake ɓoye mini ne? Ba irin wannan rigar ka yaga lokacin kana Asibiti ba, mai tambarin" "dragon ɗin nan ba?""" """Ki daina saka ido, kina ƙirga mini kaya, son rigar nake yi"" hararsa tayi ta ce ""Am not kid""" """You are"" yayi maganar very serious." "Wani ne ya shigo ɗakin Nabila, yana shigowa ya ce ""Viperrr"" ya kira sunan yana jan sunan, tare" "da dunƙule hannunsa, ya miƙawa Viper, Viper ya dunƙule nasa suka haɗa." "Ya ce ""Ya madam, ta tashi? Barrister ya ƙarfin jiki?""" """Ba sauƙi"" ta faɗa tana tura baki." "Duka suka kalleta, ya ce ""Subhanallah, ba sauƙi fa, garin yaya meyafaru?""" "Ta nuna Viper, ta ce ""Baya son na warke, bai iya jinya ba sam"" dariya ya yi ya ce ""Maza gumbar dutse, ina Viper zai iya jinya dama, ki manta da shi, zaki samu sauƙi in sha Allah, meyake" "damunki yanzu?""" "Ta girgiza kai ta ce ""Babu komai, ƙirjina ne yake nauyi kawai""" """To ki cire damuwa daga ranki, zai daina in sha Allah""" "Ta ce ""Ok sir, na gode sosai"" yayi rubuce-rubuce a file ɗin hannunsa ya fita." """Vi""" """Mmm""" """Wai ina ne nan? Kuma waye wannan ɗin?""" """Asibiti da likita""" "Nabila ta ce ""Ai na san asibitin ne, ina son tafiya ne, zan je na ga malam garba""" "Viper ya kalleta ya ce ""Kina da abun gaya wa iyalinsa ne?"" Jiki a sanyaye ta girgiza masa kai." """To sai ki daina maganar zuwa""" """To ina son na gaya wa yan gidanmu ina Asibiti, kar a neme ni""" """Wa zaki kira? Wanda ya ce ki bar masa gida ki je ki nemi babanki, ko kuma yayanki da yake yi miki bita da ƙulli? Ko kuma sauran yan gidan da suke yi miki kallon yar hana ruwa gudu? Ba wanda ya damu da ke, mutum ɗaya ne, kuma a halin yanzu an gurɓata masa tunani, na taɓa tsintar kaina a cikin wannan halin. Mata guba ne mai masifar dafi da saurin kashe wanda suka hara. Annabi Sallallahu alaihi Wasallam yayi gaskiya, da ya ce Bai bar wata fitina a bayansa da take cutar da maza ba a bayansa sai mata, banda haka me zai sanya mace ta raba ɗa da uba?"" Yayi maganar jijiyoyin kansa na kumbura, idanunsa suka yi ja, suka ciccika da hawaye, tuna mahaifinsa" da ya yi. """Ni ba guba bace ba, idan ka yi wa dukkan mata ka kira mu da guba, baka yi mana adalci ba, yakamata ko albarkacin jauhar mu ci, ka din ga kallon wasunmu ne gurɓatattu, kamar yadda kuma" "a jinsinku yake da akwai gurɓatattu""" "Yayi shiru tare da sunkuyar da kai, saboda sake soso masa wurin da yake yi masa ƙaiƙayi." **** "Indabo yana zauna yana karyawa, tare da matarsa, kawai Abdul ya faɗo tsakiyar wurin da suke cin abincin." """Meye haka Abdul, baka iya sallama ba baka iya gaisuwa ba""" "Indabo ya ce ""Ko giyar ka je ka sha, ka yi shaye-shaye ne?""" """Na daina shan giya da miyagun ƙwayoyi, tun bayan da rahama ta shigo rayuwata, ta haskar baƙ ar bayahudiyar rayuwar da kuka tarbiyyantar da ni a kai, kodayeke gara ma ni shan giya ne da neman mata kawai, but am so much disappointed on you, nayi dana sanin kasancewar ka mahaifina. Dama a tsatson talakawa na taso, talakawa futuk sai ya fiye mini wannan mummunar" "rayuwa da iftila'in kasancewar ka mahaifina""" """Abdul, uban naka ka ke gaya wa haka? Duk iya ƙoƙarin da yayi na ƙarar da rayuwarsa wurin" "ganin ya gina ku, ka zo gabansa kana gaya masa wannan maganar?""" """Mummy! Wace irin gina rayuwarmu, gangar jikin da aka gina da zunzurutun haramun da jinin mutane? Haba mummy da alama mafitarki kawai ki ka nema, ya sanya ki ka auri Daddy, wallahi mu 'ya'yanki baki yi mana adalci ba, kuma a yau ba sai gobe ba, zan bar ƙasar nan, na nesanta kaina da ku, tun kafin asirinka ya tonu a idon duniya abun da ka yi ya shafe ni, gara in kalli duniya a hukunta ni da laifin fyaɗe da nayi, da a hukunta ni da mummunan laifin da ka aikata, ga waya" "nan ka karɓa ka saurari saƙonka""" "Yayi maganar yana miƙa masa wayarsa, Indabo ya saka hannu ya karɓa, yana dubawa." "Wani audio ya fara buɗewa, sai dai jin muryar wanda yayi message ɗin kawai, ya rikita masa" "lissafi, ya fara gumi hannunsa ya hau rawa." """Wanna saƙon ba naka bane ba, na mahaifinka ne. Duk da ina da access na yadda zan same shi, amma yafi dacewa na tura masa saƙon ta hannunka, sai yafi karɓar sa da muhimmanci. Lokaci yayi da zamu daina buga wasan 'yar ɓuya da kai indabo, zamu yi wasa na ƙeƙe da ƙeƙe, saboda ina daf da barin ramina da nake ɓoye, na cigaba da addabar rayuwar ka ta kowane hali. Idan ka muzgunawa Nabila, tamkar jauhar ka taɓa mini, taɓa jauhar kuwa taɓa zuciyata ne kai tsaye. Dan zan yi wasa irin wanda ka ke so ayi." "Ka so ta zama tarkon da zaka yi amfani da shi ka kamani, shi kuma Allah ba azzalumin sarki bane ba. Ɗanka ya yi wa rahama fyaɗe ƙanwar Nura, da ka lalatawa rayuwa ka kashe, ka ɗorawa wani daban, kuma ka bishi ka saka an kashe shi. Abun da baka sani ba shi ne, ina da cikakkiyar shaidar mummunar ɗabi'ar da ka ke aikatawa, ta lalata rayuwar matasa da sunan sama musu aikin yi." "Sannan ni na saka aka kama ɗanka Jafar, a Mexico in da ya gudu neman mafaka bayan yayi kisan kai, haka zalika yanzu ma da saka hannuna a mayar da shi amurka." "Yanzu haka miyagun ƙwayoyi da hodar iblis ɗin da aka loda maka a jirgin ruwa, za ayi safararsu" "ta ruwa, za a kama su a gaɓar tekun italy. Kamar yadda nayi maka aike na farko, ina tare da Simon kuma shi ya bani wannan saƙon naka""." "Jiki na rawa ya buɗe videon, shi ne a cikin videon, yana ta kokowa da Nura guduma, wasu irin ƙ" "arti majiya ƙarfin gaske, suka riƙe Nura, yana kururuwa yana ƙoƙarin ƙwatar kansa, amma abu ya gagara, kuma ba iya fuskar Indabo ba ce a videon, har da wasu daga cikin manya a ƙasa." "Da ƙyar Indabo ya iya ɗaga ido, ya kalli Abdul, ya haɗiye wani irin abu mai yaji da ɗaci, ya kasa" "magana. Abdul kuma ya ƙure shi da ido, yana jiran ya ji mai indabon zai ce." "Mahaifiyar Abdul tayi shiru, suka yi tsuru-tsuru." """Na tabattar ba sharri aka yi maka ba, kai ne a jikin videon nan, naga baka buɗe sauran audios ɗin ba, amma ya tabattar da cewa, mutum goma ne suke da videon, muddin ka cigaba da takura musu, sai sun sake shi a duniya, kuma sai an ɗauki mummunan mataki a kanka, babban takaicina me zan cewa rahama, yarinyar da nake nema ta yafe mini, ashe akwai babban aiki a gabana jawur, kai kayi silar mutuwar ɗan uwanta, tayaya mahaifiyarta zata yafe mini ta bari na cigaba da rayuwa da" "ita?""" """Abdul ka cigaba da rayuwa da wa? Tona wa mahaifinka asiri zaka yi? Satin bikinka ya kama" "kana nufin zaka yi aure kuma ka ajiye karuwa?""" """Rahama ba karuwa ba ce, aurenta nake yi, kuma yau zan tattara na bar garin nan da ita, da" "wannan abun kunyar da ka aikata""" "Indabo ya ce ""Aurenta ka ke yi kamar yaya?""" SOME MONTHS BACK. "Abdul ne ya shigo, ya tarar da rahama a rakuɓe, a jikin gado, idanu duk sun kumbura saboda kuka." """Wai ba zaki raba kanki da wannan kukan ba? Aikuwa kina tare da wahala, dan kuwa yanzu ki ka" "fara, tashi ga abinci""" "Ta ɗago ta kalleshi ta ce ""Ba na ci, ka ƙyale ni na mutu, ai tun farko cewa kayi zaka kashe ni, menene na ajiye ni kana tozarta rayuwata, saboda kawai ina 'yar talaka? Talauci ne ya saka na fita aikatau, da burin yin karatu, mahaifiyata ba zata iya ɗaukar ɗawainiyata ba, ban da haka killace ni zata yi a tare da ita, ba zata bari ma ka ganni ba balle ka keta mini haddi"" ta yi kneel down ta ce" """Dan girman Allah ka kasheni na huta""" """Ke naji, kin cika mini kunne da koke-koke, zan mayar da ke""" "Ta girgiza kai ta ce ""Ko ka mayar da ni, ba zan yi daraja ba, abar ƙyama zan zama, kawai ka" "kashe ni, ka kaiwa mama gawata dan Allah""" "Abdul ya zauna a kusa da ita ya ce ""Ya isa haka kukan, ki ci abinci zan san abun yi"" kwanaki biyu, tana jiran ya kashe ta, ko ya mayar da ita amma shiru, gashi tun da tayi ɓarin nan, da ya zo mata" "zata fara kuka kamar ranta zai fita, tana yi masa magiyar ya daina wulaƙanta mata rayuwa." "Cikin marairaicewa ta same shi, ta durƙusa a ƙasa ta ce ""Ka ce zaka mayar da ni gida, kuma baka" "mayar da ni ba""" """Rahama ba zan iya mayar da ke ba, zan ta tunaninki ne, kawai na ji ina damuwa da ke, ki haƙura" "kawai"" cikin kuka ta ƙare masa zagi, amma ko a jikinsa." "Washegari ya ɗauki Salim, ko saifu bai gaya wa ba, suka tafi gidan su ramma." "Mahaifiyar ramma na ganin Abdul, ta tashi cikin ƙarfin hali ta ce ""Ina ka kai mini 'ya ta? Ka dawo" "mini da 'ya ta""" "Abdul ya ce ""Mama masalaha na zo muyi, ɓarna an riga an yi ta, dan Allah ki yi haƙuri ki bar" "mini ramma, ki bani aurenta"" Sai da Salim ya kalle shi, dan bai san abun da zai ce kenan ba." """Allah ya tsare, cuta ka riga ka gama cutar da mu, kai da Allah, amma ka dawo mini da 'ya ta""" "Ya girgiza kai ya ce ""Kar mu yi haka, a rufa wa juna asiri, kun ɗauki aure da muhimmanci sosai," "ta ce babu lallai tayi daraja, ƙyamarta za a din ga yi, dan haka ki yi haƙuri dan Allah, ki aura mini ita""" """Wallahi ba zan taɓa aura maka ita ba, gara ayi ta tsangwamarmu, zan riƙa a bata na kula da ita," "kuma zan cigaba da nema mata hakkinta, har zuwa ƙarshen numfashina""" "Ya miƙe ya ce ""Shikenan, tana gaishe ki, ki kwantar da hankalinki, tana cikin ƙoshin lafiya"" ya" "ajiye mata kuɗi suka fice, ta bishi tana ya zo ya karɓi kuɗinsa amma yayi mata banza suka tafi." "Salim ya din ga yi masa masifa a mota ""Amma dai baka da hankali ko? Ka yi wa yarinyar fyaɗe, mu zo gaban babarta mu yi rashin mutunci, kuma mu dawo ka ce zaka aureta, wai ma ka gaya wa" "su daddy ne?""" "Abdul ya girgiza kai ya ce ""A'a, yarinyar ce take bani tausayi irin sosai ɗin nan, virginity is very" "important to woman's, i took it away just like that, she's very young and innocent, ina jin babu daɗ i, na san yadda zan ɓullowa lamarin""" "Tare da Salim suka cigaba da shige da fice, suka samo wani wan baban ramma, Abdul ya danƙara masa kuɗi, babar ramma bata sani ba, aka ɗaura musu aure, sai bayan an ɗaura ya je ya din ga yi wa babar ramma masifa, wai Allah zai rufa wa ramma asiri, amma tana ƙoƙarin tonewa, da ta samu ma mai kuɗi da kyau kamar wannan ya saurari yar ta ta, a wurin ɗan birni kamar Abdul ai" ramma a bar ƙyama ce. "Cikin kuka ta ce ""Wallahi balarabe ba zai yiwu ba, ban san wani zancen aurar da ramma ba," "lokacin da nake wahala ta da ya ta da me ka taimake ni, ina har gonar su ta gado ka cinye""." """Oho miki, koma menene rashin iya takaucinki, da son abun duniya ya sanya ki ka kaita aikatau"" da kansa ya shiga ya kwaso wa Abdul kayan ramma, ya sake ba wa babar ramma kuɗi, ya ɗauki" kaya suka tafi. "Suna tafe Salim ya ce ""Ranar da asirinka ya tonu ban sanka ba wallahi, ko kuma ka gama abun da" "zaka yi, salin alin ka sakar musu 'ya""" "Abdul ya ce ""Ban aureta dan na saketa ba, sai dai ayi wadda za ayi""" "Ya je ya samu ramma, ya kai mata kayanta, da goro da alawa ya ce ""Gashi nan, hankalinki ya" "kwanta an ɗaura mana aure yau"" cikin mamaki ta kalleshi ta ce ""Aure kuma kamar yaya?""" """Ba damuwarki kenan ba? Ke ba zaki auru ba? To an ɗaura yau, yayan babanki wai malam bala," "shi ne ya ɗaura mana aure""" """Wane irin aure ne babu istibura'i? Cewa nayi ina sonka ne ma?""" "Ya ce ""Meye istibura'i?""" """Sai nayi jini uku a addinance, dan tsaftace mahaifata kan ka aureni, tun da zina kayi da ni, kuma" "ni bana sonka""." "Abdul ya kalleta ya ce ""Allah ya nuna mana wata ukun, kuma ni ina sonki ai, Shikenan an wuce" "wurin""." "Ramma tayi kuka a kan wannan wulaƙanci da Abdul yayi mata, da nuna mata tsantsar isa da gadara, ta fara yi masa misbehaving ta daina tsoronsa, amma ko a jikinsa, sai dai zamansu tare ta gane yana da wasu ɗabi'u na tausayi da sauƙin kai, rashin tarbiyya da ilimin addini ne kawai yake" "ɗawainiya da shi, bai sake nemanta ba, sai da ta cika watanni uku, kamar yadda ta buƙata." "Idan tana yi masa masifar ba dan Allah ya aure ta ba, ya kan ce mata ""Ba dan ina sonki ba, babu dalilin da zai sanya na zauna da ke watanni uku ina kallonki, kina gindaya mini sharuɗa ina ƙyale" "ki""." **** "Mahaifiyar Abdul ta ce ""Aure ka yi bamu sani ba Abdul, rashin muhimmancin namu har ya kai haka?""" "Ya kalleta ya ce ""Ko zan mutu ba zaku yadda ku aura mini rahama ba, zaku yi iƙirarin yar talakawa ce, ba tare da la'akari da ɓarnar da na akata mata ba. Kuma sakawa zaka yi a kasheta, sannan mutumin nan da ka saka aka kashe, ba ruwana babu saka hannuna a ciki. Zan ɗauki matata mu bar garin nan, dan Allah kar ka neme ni, takara kuma ka bawa wani, ba zan iya ba"" ya ɗauke" "wayarsa, mahaifiyarsa ta bishi tana ƙwala masa kira, amma yayi waje." *** "Viper ne ya shigo ɗakin da Nabila take, tana zaune ya shigo da waya a kunnensa ya ce ""Eh na je wani wuri ne, ɗan mama ya dawo gidan nan ne, ya gudu na neme shi na rasa, ya kuma kashe wayarsa""" "Walid ya ce ""A'a bai dawo ba, ko laifi yayi maka ka ce zaka hukunta shi?""" "Yayi murmushi ya ce ""Laifi yayi, kuma duk in da ya shiga zan nemo shi, zamu gauraya da ni da" "shi""ya katse wayar ya ƙarasa gefen Nabilaya zauna." """Vi""" """Mmm""" """Wai dan Allah ina ne nan? Ina son na tafi gida ne""" """Ai ba zaki koma gida ba, kin zo kenan""" "Dariya tayi, dan ta zata da wasa yake yi." """Daga fitarka ka sha sigari ko?""" """Eh""" "Nabila ta ce ""Au eh, baka jin kunya wai ka amsa ka tsaye, sai ƙauri ka ke yi, ba na son ƙaurin" "abar nan ko kaɗan wallahi""" "Ya tsura mata ido, ya girgiza kai ya ce ""You can't be her""" """Who?""" "Ya lanƙwasa ƙafarsa ɗaya a kan gadon ya ce ""Jauhar, ba ta taɓa nuna warin sigarina da wiwi yana damunta ba, sai dai ta ce ; Master kar a sha da yawa, dan Allah a sha kaɗan, idan nayi shaye-shaye na dawo, ta bani ruwan wanka, ta bani wankakkun kaya, ta fesa mini turare, sai daga baya na fahimci, warin wiwi ne ba ta so, amma bata taɓa yi mini complain ba. Yanzu bana iya shan komai, na yadda ƙwaƙwalwata da lafiyata suna da amfani, ko dan ganin bayan wanda suka cutar da mu." "Ke kuwa masifaffiya ce, always angry, ki ka gaya mini ina ƙaurin taba""" """Sai na zama irin ta zaka so ni? Gaskiya ba zan iya shiru ba, ni kawai ka daina gaba ɗaya""" "Viper ya ce ""Ai babu wannan maganar tsakanina da ke, na gaya miki ki daina wahalar da kanki""" ya yi maganar yana miƙa mata wayarta. "Karɓa ta yi tana hararsa ta ga sunan sumayya ta ce ""Ba zan ɗaga ba""" """No, ki ɗaga baki san me za ta ce miki ba""" "Ta ɗaga ta saka a kunnenta ta ce ""Ina jinki""" """Nabila kina ina ne?""" """Menene?""" """Kawai malama kina ina?""" """Ki gaya mini meyafaru? Nayi nisa ne""" "Sumayya ta ce ""Mahaifin Viper, ya zo gidan radionmu, ya ce yana son zai yi magana da ke, na ce" "masa zan haɗaku, zan yi miki magana""" "Nabila ta ce ""Are you serious dan Allah da gaske?""" """Wallahi da gaske nake yi miki""" """Shikenan, in sha Allah zuwa gobe in Allah ya kaimu, zan zo zamu haɗu, kin karɓi lambarsa?""" """Eh na karɓa""" """Shikenan in sha Allah zan zo"" ta katse wayar, ta ga wani irin kallo da yake yi mata." """Vi snake, menene? Abunka ne ya zo yana nemana, wataƙila....." """Silent. Kar ki kuskura ki fara, ke gaba ɗaya baki da lissafi, idan wani trap ɗin ne fa?"" Yayi" maganar cikin hargowa. """Bari na zama kamar jauhar, ba zan biye maka ba ai yanzu, hukuma sai da rarrashi, hadari malafar duniya. Tsakanin ɗa da mahaifi sai Allah. Nifa duk da ina da labarin abun da babanna yayi wa mahaifiyata, fata nake yi na ganshi, haka zaka cigaba da rayuwa ba dangi, kaikaɗai sai su oga" "Walid, sai kuma Ni"" ta yi maganar tana murmushi." """Ka bari mu haɗu da Abbu dan Allah, na san maybe nemanka yake yi, so yake ya ganka, haba sweetheart, namijin duniya, kar ka saka muyi babu, kai ba uba nima haka, kayi haƙuri dan Allah, ka manta da komai My Vi. Magana fa nake yi an yi mini shiru, talk mana, ko sarautar ce ta motsa?" "Master magana nake"" tsigar jikinsa ta mimmiƙe ya juya yana kallonta." """Ban taɓa kallon wani abu na ji ina son shi ba, sai kai Vi, duk a dalilinka na rasa ajina da jin kai na 'ya mace. Gashi ka yi ta hantarata, baka tausayina ko kaɗan." "Ɗan nuna mini hoton 'yar madara mana, ko sau ɗaya ne""" """Hotonta mai tsada ne, yarinya mai haƙuri da aji""" """Ni kuma masifaffiya mara aji, daga nan kuma sai me?"" Ya fuskanci kawai kunna shi take yi." "Ya ajiye mata wata leda, ya ce ""Gashi nan, abinci ne, za a kawo miki kaya""" """A'a nifa ban gane ba, gida fa?""" "Ya miƙe tsaye ya ce ""Ba sa buƙatar ki, na fi su buƙatar ki a yanzu, muddin wani abu ya sameki, ni" "aka jiƙawa aiki""" "Nabila ta ce ""Ban gane ba, garkuwa zaka yi da ni?""" """Na ma yi"" yayi maganar tare da ficewa." **** "Hanklin can gidan su Nabila ya tashi, bayan an shafe kwana na biyu, ba a san in da take ba, Abba ya maze kamar ko a jikinsa, amma hankalinsa a matuƙar tashe yake. Nasir ma ya din ga up and down, haka ma sumayya dan sai da ta gaya wa Kankarofi an nemi Nabila an rasa." "Ta gaya wa Nasir cewa, ranar da ta ɓata sun yi waya, bayan la'asar kuma da alama tana cikin ƙ" oshin lafiya. "Nasir ya ce ""Abu ne mawuyaci ace barin gidan nan tayi, wataƙila mutanen da take addabawa ne" "suka sace ta""" "Aka din ga kiran wayarta, amma a kashe." "Kwana na uku, Nasir ya kira wayarta, ta shiga, amma ba a ɗagawa." "Dan haka ya saka layin a tracker, ya fara tracking in da wayar take, sai dai ga mamakinsa, wayar" tana cikin garin kano. **** "Abdul tamkar zai haukace, duk wani lungu da saƙo na gidan ya duba, amma bai ga ramma ba, ya dudduba ko ina da ina, amma bai ganta ba. Ya kira wayarta amma a kashe." "Taka jikinsa ya hau tsuma, ya tabattar da cewa Indabo ne ya saka aka ɗauke ta, jikinsa na rawa ya" "ɗaukko mota ya fito, tare da sakawa a ransa komai zai faru sai dai ya faru, amma sai indabo ya fito masa da matarsa, ko kuma shi da kansa ya tona musu asiri kowa ya huta." **** "Nasir yayi mamakin surƙuƙin wurin da yake indicating in da wayar Nabila take, da shi da abokan aikinsa, ƙarshe ajiye motar suka yi, suka din ga shiga wurin da ƙafa, suna cigaba da dubawa." "A tsaye suka tarar da shi ya juya baya, hayaƙi yana tashi." "Nasir ya ce ""Malam waye kai?""" "Sai da ya ja sakanni, sannan ya juyo a hankali, hannunsa ɗaya da wayar Nabila, ɗaya kuma riƙe" "da sigarinsa, gaban rigarsa ɗauke da sunansa Viper da hoton maciji a jiki." """Al'amin Viper, ko ka ce mai zamani""" Ayshercool 08081012143 ₦500 ne via 0009450228 Aisha Adam jaiz bank sai shaidar biya ta 08081012143 Wanda za su jira document 1K ne. 90009343 'Yan Nijar ku turo katin airtel na 300fcfa https://whatsapp.com/channel/0029Va9QtrY4dTnBYG1hST2VHADARIN *BRIGHT PENS SECOND BATCH* "Ku kasance da littatafan bright pens, second batch." *ƘARFE A WUTA (AYSHERCOOL)* *MUTALLAB (NIMCYLUV)* HADARIN GABAS (NAZEEFA NASHE)* *ZAYTOON (ZEE KUMURYA "Cikin matsanancin mamaki, Nasir ya cigaba da takawa zuwa gaban Viper, ya ɗan bayar da tazara" tsakaninsa da shi. "Nasir ya ce ""Dama kai ne Vipern?""" "Ya ɗan kaɗa kai ya ce ""Ni ne Viper, abun mamaki ko? Haɗuwar mu biyu, amma baka san ni ne ba, haryanzu ina mamakin wane irin aiki jami'an tsaron ƙasarmu su ke yi, kodayeke ƙulafucin cin hanci ne yake rufewa galibinku idanu, ku danne masu gaskiyar cikinku, ko ku sauya musu ra'ayi" "domin neman mafitarku kawai""" "Nasir ya ƙare masa kallo ya ce ""Ina 'yar uwata take? Ina Nabila?""" "Viper ya jujjya wayar Nabila sannan ya ɗagawa Nasir ita ya ce ""Baka buƙatar yi mini wannan" "tambayar, tun da ka samu wayarta a hannuna""" """Tana ina?""" """Tana wurina ƙarƙashin kulawata, na fiku buƙatar ta, ina buƙatar ganinta a raye domin nayi" "surviving, dan haka za ta cigaba da zama a ƙarƙashin kulawata, har zuwa lokacin da ya dace""" "A fusace Nasir ya ce ""A matsayinka nawa, am arresting you, ba zan bar wurin nan ba, sai na kama" "ka""" "Viper ya kalle su gaba ɗaya 'yan sandan su biyar ɗin ya ce ""Bisa wace dokar? Ko bisa umarnin indabo da ka karɓar wa kuɗi, zaka kama ni?. Viper ya zaro takarda a aljihunsa ya ce ""Na sami wannan takardar yau da safe, kai ma kuma ka je ka bincika, kotu ta hana hukumar 'yan sanda da kowace hukuma kama ni, har sai an kammala bincike, dan haka ba ka da wannan ikon, hannunka bashi da ƙwarin ɗaukar ƙarfen cikin wannan wutar, ba zaka jure ba, muddin ka taɓa kuwa, zaka" "yi ƙunar da zata yi dalilin rabaka da hannun""" "Nasir ya fizgi takardar hannun Viper, jikinsa na rawa, ya hau karantawa, tabbas Viper da gaske" "yake, kotu ta bayar da umarnin hana kama shi." "Nasir ya riƙe takardar, ya zaro bindiga a jikinsa, ya ce ""Idan kuma na kashe ka a wurin nan fa, waye ya sani?""" "Viper ya nuna masa mutanen bayansa ya ce ""Ku 'yan sanda ai ba dukkanku ne masu amana ba, wane tabbaci ka ke da shi cewa mutane huɗun nan na bayanka, ba zasu tona maka asiri cewa ka kashe ni ba? Beside kana sakin bullet ɗin bindigar ka, kaima za a kashe ka, tunaninka a banza na" "zo nan na jiraka? na san kana tracking ɗin wayar, shiyasa na jira ka zo ka iskeni""" "Ya ciro ID card ya ɗaga wa Nasir ya ce ""I am an NIA officer, and also a former thug, ni ba da" "bindiga zan yi maka illa ba, ƙarfe zan saka maka, a ɗan daba na zan yi maka illa, ba jami'i ba." "Sauke bindiga Nasir yayi, ya ce ""NIA officer how?""" """Kamar yadda ka gani. Maganar Nabila kuma, bari na gaya maka wani abu, na san kana sonta amma ta haramta a gareka, muddin ina ganin fuskar matata a ta Nabila, aurenta ya haramta a gareka, ba kai ba kowa ma. Nabila tana wurina, kuma zan mayar da ita wurin mahaifinta, wannan" "shi ne tukuicin da zan yi mata, bisa ga jajircewarta da ceto rayuwata""" """Mahaifinta like how? Me ka ke nufi da hakan?""" """Hoton da na bata, ta kai muku ku yi mata bayani, amsar da ku ka bata, ta sanya na yanke" "shawarar yin abun da ya dace"" Nasir zai kuma magana, wani ya ƙaraso wurin da babur, sanye da riga mai tambarin NIA (National Intelligence Agency) Viper ya hau babur ɗin, suka bar wurin." "Dafe kai Nasir yayi, yana tunanin wannan wane irin rikitaccen al'amari ne, tayaya riƙaƙƙen daba ya zama jami'in cibiyar samar da bayanan sirri da leƙen asiri? Ya aka yi kuma ya san mahaifin" "Nabila, anya wannan duk ba wata shiryayyiya ba ce ba?." """DSP yakamata fa mu bar wurin nan, ni gaba ɗaya ban yadda da mutumin nan ba, i don't think we" "are safe here"" bai ce uffan ba, ya yinƙura ya tashi suka bar wurin." **** "Gida Nasir ya nufa, a wahale, cike da damuwa da tashin hankali, yama rasa ta ina yakamata ya" "fara, meyakamata yayi." "Ya za ayi hukuma kamar wannan, ta bar jami'inta yana tafka rashin mutunci son ransa. Yayi shiru yana tunanin yadda wasu abubuwan suka din ga faruwa, ya aikata laifi, amma a bi a goge duk" "wani trace da zai nuna shi yayi, ko kuma a gano shi." "Babban abun da ya ƙara baƙanta masa rai, shi ne umarnin kotu, na hana kama Viper, ana tuhumar" "mutum da laifi, har na kisan kai, amma ace kotu tayi umarnin dakatar da kama shi a kan me?." "A ƙofar gidan su, ya tarar da manya-manyan motoci har da na 'yan sanda, cikin sauri ya yi parking, ya shiga cikin gidan domin ya ga mai yake faruwa, baba magajiya ta sanar masa major ne" yayi baƙi. "Hankalinsa bai kwanta ba, ya nufi ɗakin Abba, dan tabattar da abun da yake faruwa." "Ya tarar da Alhaji mu'zzam kankarofi, tare da wasu jami'an tsaro, da kuma Abba a falonsa." "Abba ya ce ""Yauwwa, ƙaraso Nasir"" ya ƙarasa ya shiga, ya zauna suka gaisa." "Abba ya ce ""Ka gane wannan ai ko?"" Yayi maganar yana nuna masa Alhaji mu'azzam." "Nasir ya ce ""Eh ya je asibiti duba Arfat""" """Ashe babban mutum ne ni ban sani ba, ya ce Nabila tana ƙarƙashin kulawar hukuma, saboda" "rayuwarta na cikin hatsari, wanda take karewa ya rasu, ba a san me zai iya faruwa da ita ba""" "Kamar shashasha Nasir ya tsaya yana bin su da kallo, shi kuma meya kawo shi cikin wannan lamarin? Tare da Viper suke harƙalla kenan? Amma da kamar wuya ace kamilin mutum da ya san" "doka, kamar sa ace yana hulɗa da mutumin banza kamar Viper." """Mu'azzam wada kankarofi, mai bawa shugaban ƙasa shawara na musamman a kan harkar tsaro""" "ya faɗa yana kallon Nasir da ya ga yana yi masa wani irin kallo mai cike da tuhuma""." "Major ya ce ""Haryanzu ina mamaki, da ka ce kai ne dai wada kankarofi, ni na zata suna ne kawai" "ya zo ɗaya""" "Alhaji mu'azzam ya ce ""A'a, ni ne dai, a rayuwata ina son 'yanci da walwala, dan haka ban fiye son takura ba, ko yawo da gayyar jami'an tsaro ba duk in da zani." "Na san ka ɗauki zafi a kan abubuwan da Nabila take aikatawa, na kasada, amma ni burgeni tayi, kuma daga ranar farko da na ganta a law firm ɗin su, nake bibiyarta, nake taimakonta, akwai ire-iren ta, brave citizens, da cin hanci da ƙarfin iko, ya sanya ake tauye su su kasa kataɓus, a kanta na ce bari mu jarraba ayi supporting ɗin ta, mu ga wace irin baiwa da gudunmawa zata bai" "wa ƙasa, and Alhamdilillah ko iya haka tayi rawar gani """ "Major ya jinjina kai ya ce ""Haka ne sir, amma abun da aka yi ya isa haka, ina son a dawo mini da 'ya ta, abun da tayi Allah ya amfana, ni aikin ma a haƙura da shi, tayi aure. Ba zan lamunci zuba mata ido, tana kare rayuwar ɗan ta'adda ba. Aikinta na neman kawo mini rabuwar kai a cikin iyali. Ga ɗan uwanta yana fafutukar neman mai laifi, ita kuma tana kare shi ba. Sunanta ya ɓaci a idon" "duniya ba, ina buƙatar ta dawo a haƙura kawai""" "Alhaji mu'azzam ya ce ""Am sorry to say sir, Nabila ta ɗaukko aikin da kammala shi ne kawai" "mafita, da ceto dubban al'umma, za ta aikata abun da da yawa sun yi yunkurin yi, amma ba su yi" "nasara ba. Bani da ikon dawo maka da ita, umarni ne na musamman kareta da lafiyar ta""" "Abba ya numfasa ya ce ""Na ji, amma Allah ya amfana haka nan, a dawo mini da 'ya ta, ban ga" "dalilin da zai sanya, a ɗaukar mini yarinya ba da iznina ba a ɗaga mini hakali har haka ba""" "Alhaji mu'azzam ya ce ""Na san an yi maka laifi, shiyasa muka zo har gida baka haƙuri, kuma ta ɗ" "an samu mini attack ne mun kaita Asibiti, daga baya kuma muka lura da matsanancin haɗarin da rayuwarta take ciki, ka ɗan bamu lokaci""" "Nasir kamar yayi maganar Viper, amma yayi shiru, kenan da gaske Viper yake shi jami'in sirri ne," ko kuma wata kitumurmurar ce?. "Abba suka yi ta jayya da Alhaji mu'zzam, haka ya haƙura, sai dai bai ji zai yi shiru da maganar" "nan ba, dole a dawo masa da 'yar sa." "Bayan tafiyar su, mutanen gidan suja din ga tambayar meyafaru, Abba ya gaya musu ba wani abu," "a kan Nabila ne, tana wurin hukuma saboda tsaron lafiyarta." "Masu jiran su ji baƙin labari, duk ba haka suka so ba, baba magajiya kuwa addu'a ta cigaba da yi," tare da fatan Allah ya sa Nabila na cikin ƙoshin lafiya. "Sumayya ce ta zo gidan, cikin matsananciyar damuwa, ta tarar da Abba yana shirin fita, suka gaisa" "ya ce ""Kin biyo sahu ko sumayya?""" """Eh Abba, hankalina ya kasa kwanciya, ni har a radio na sanar a tayamu addu'a bamu ganta ba, na" "kasa sukuni gaba ɗaya""" """Ki kwantar da hankalinki, yanzun nan baƙi suka tafi, wai tana wurin hukuma saboda tsaron lafiyarta, wai wani saurayinta da ya zo dubata kwanaki, wai mai bawa shugaban ƙasa shawara a" "kan harkar tsaro""." "Take Sumayya ta gane waye, ta ce ""To Abba ya tabattar maka tana lafiya?""" """Eh, ya ce suna bata kariya ne, ashe ba saurayin ta bane kawai, ni dai kam na gaji da wannan aikin," "ajiye shi zata yi ta fitar da miji, na yi mata aure, ko ni na fitar mata""" "Sumayya ta ce ""A'a Abba ka yi haƙuri, aikin yana da muhimmanci, zan cigaha da kiranta, Allah ya" "sa na sameta""" """Allah ya sa, dan bana tunanin zasu bari ta ɗaga waya""." *** "Ko da Abdul yayi parking a harabar gidan su, bai ko tsaya rufe motar ba, ya shiga cikin gidan" "kamar yayi fuka-fukai ya tashi, ""Mummy"" ya din ga ƙwala wa mahaifiyarsa kira." """Menene wai ka ke kirana haka?""" """Ina Daddy?""" "Ta kalleshi rai a ɓace ta ce ""Ya tafi ya gurfana a gaban kwamitin da aka naɗa, na binciken kuɗin" "da kake neman ka janyo masifa a kansu""" """Mummy ba wannan ba, dan girman Allah ki gaya mini idan shi ne ya sa aka je aka ɗauke" "ramma""" "Sheƙeƙe ta kalle shi ta ce ""Wacece hakan?""" """Matata mana""" """Wai Abdul baka jin kunyar faɗar wannan maganganun ne? Har wani tutiya kake yi dan ka auri" "karuwa? Wannan aure da zaka yi alfahari da shi ne, kana wani matarka?""" "Abdul ya ce ""Mummy, meyasa a ƙasashen ƙetare, ko wasu sassan na duniya, idan suka lalata yarinya, ko su gama watsewar su, suke dawowa su aure su, mu kuma sai mu tafka ɓarna mu koma mu ce zamu yi wa Allah wayo, na san ba zan taɓa auren macen kirki ba, dole ragowar wani zan" "aura, gara wannan ragowata ce koma menene ni na janyo""" """Abdul, ka tsaya a gabana ka ke gaya mini wannan maganganun banzan? Ina uwarka""" """Ni dai dan girman Allah idan ku kuka ɗauke mini mata, ko dawo mini da ita, wallahi ba zan iya" "rayuwa mai daɗi babu rahama ba""" """Innalillahi wa Innalillahi raji'un, ka je kayi duk abin da zaka yi Abdul""" """Mummy dan Allah Daddy ne ya saka aka ɗauke mini ita""" """Ban sani ba, ka bishi Abujan ka tambaye shi"" ta juya ta koma ɗakinta, a matuƙar fusace." **** "Wata irin runguma, Ramma ta yi wa mahaifiyarta, suka fashe da kuka baki ɗaya." """Ramma, kina lafiya bai cutar mini da ke ba?"" Ramma ta jinjina mata kai tana kuka, suka ƙara ƙ" anƙame juna. "Barrister Habib ya ce ""Kukan ya isa haka, a gode wa Allah, dan Allah ku yi wa Nabila Addu'a, da" "ita da malam garba, shi an bishi an kashe a prison ɗin, amma ita Nabila an kauwwameta, ana" "tsaron lafiyarta""" """Innalillahi wa Innalillahi raji'un, sai da mutumin nan ya rasa ransa?"" Maman ramma tayi maganar" cikin tashin hankali. "Jiki a sanyaye ramma ta ce ""Yanzu malam garba ya rasu? Wayyo Allana, Allah ya sa mutuwa hutu" "ce a gare shi""" Suka Amsa da Amin. "Mama ta kalli barrister Habib ta ce ""Na gode sosai da sosai, Allah ya saka muku da mafificin alkhairi, idan ka samu ganinta, ka ce mata na gode, na gode Allah ya saka mata da mafificin" "alkhairi, ya jiƙan magabatanta, yadda ta share mana hawaye, ka da Allah ya bar nata su zuba""" "Ya ce ""Amin, amma ni kuma fa""" """Kai ma haka tare da Alhajin da yake ta ɗawainiya da ni""" "Barrister Habib ya ce ""Amin ya haiyyu ya ƙaiyyum, bari zamu cigaba da magana da jami'an tsaron, za a kama ainihin mai laifin, za a hukunta shi da yardar Allah, duk wata shaida muna da ita" "a kansa"" suka din ga yi masa godiya, ya wuce ya fita." "Suka ƙara rungume juna, mama ta ce ""Lokacin da yarinyar nan take tabattar mini da zata dawo" "mini da ke, ban zaci da gaske take ba, da zan ganta har ƙasa zan durƙusa na yi mata godiya""" "Ramma cikin kuka ta ce ""Mama ina Sani?""" """Mutumin nan da ya saka aka ɗaukkomu, ya kai shi makarantar kwana, ta kuɗi""" """Mama wai waye shi? Meyasa ya ɗaukko ki?""" """Yana da nasa dalilin, amma ban sani ba""" *MONTHS BACK* "Nabila sai sauri take yi, takalminta mai tsini yana ƙara, tana neman network, domin yin magana" "da sumayya, har ta dangana da rukunin ofisoshin da ba kowa a wurin." """Hello, ke Sumayya T ladan, ba network ne, yanzu na samu wuri, ya ake ciki munafukan" "al'umma""" "Sumayya ta ce ""Nabila ki daina ce mana munafukai, aiki muke fa""" """Ba wani aiki, tsegumi wanda aka saka ku, da wanda ba a saka ku ba, duk ku ke samowa ku" "kwatsawa al'unma komai daɗinsa da ɗacinsa""" """Zan ɗura miki ashariya wallahi""" "Nabila ta ce ""Sorry T ladan, masoyiyyar Nabila, bani labari""" "Da sauri Ramma ta ajiye littafin hannunta, jin an ambaci sumayya T ladan, da sauri ta ƙarasa" gaban window tana zura kai. """Baiwar Allah, baiwar Allah kin ganni ta nan baiwar Allah"" Nabila ta hau waige-waige, taga ta ina" ake magana. """Baiwar Allah wadda take waya, dan ki ƙaraso wurin tagar nan""" "Cikin dakewa Nabila ta ƙarasa, ta ragar jikin window Nabila ta ga ramma, ta ce ""Lafiya kuwa?""" "Ramma ta ce ""Ki taimake ni, kamar yadda Allah ya taimake ki dan Allah, na ji kina faɗar sunan" "yar jaridar nan, mai aiki a radio""" "Nabila ta ce ""Eh ya aka yi, kin santa ne?""" """Ban santa ba, taimakona zaki yi, dan Allah ku sanar da jami'an tsaro idan kuna da dama, wani ne yayi mini fyaɗe, ya sace ni ya aure ni, ba da sanin mahaifiyata ba, ban san a wane halin take ciki" "ba""" """Yayi miki fyaɗe ya sace ki? Garin yaya?""" "Nan ramma ta gaya mata komai, Nabila ta ce ""Innalillahi wa Innalillahi raji'un, kin san irin neman da muke yi miki kuwa? Ni nake shari'a a kan case ɗin ki, har ya fita yana yawo da ke, amma baki" "yi masa ihu ba, a ƙwace ki?""" """Tayaya zan yi masa ihu yana aurena? Kuma idan nayi ihu tamkar na ƙara tonawa kaina asiri ne, wanda ya sanni, da wanda bai sanni ba, sai kowa ya san abin da ya same ni, shi ne mai asibitin nan, shi yayi mini fyaɗe, sai an bi a hankali idan ba haka ba, ba zai taɓa rabuwa da ni ba, dan Allah ki" "taimaka mini dan Allah, ina son na je na ga mahaifiyata""" "Nabila ta ce ""Tsaya, yana baki ci da sha, ko yana dukanki da cin zarafi?""" "Ramma ta ce ""A'a, baya yi""" """Yauwwa Alhamdilillah, a ina yake ɓoye ki?""" """Ban san ina ne ba""ta yi maganar tana kuka." "Samo abu na rubuta miki lambata, ki faki idonsa, ko saƙo ki turo mini, sai ki goge, nayi miki alƙ" "awarin zaki kuɓuta in sha Allah""" "Nabila ta bata lambarta, ta nufo hanyar tafiya, tana yi wa Allah godiya, yadda kayanta suka tsinke" "a gindin kaba, saboda tsananin addu'a da take yi." "Daga nan ta koma ƙofar ɗakin Viper, ɗan mama ya hanata shiga." "Kamar yadda suka tsara, Ramma ta yi mata message, Abdul na wanka, Nabila ta bawa Viper, ta ce" "masa wata lamba take so, a duba mata location ɗin ta." "Yana dubawa ya ce ""Wannan ai lambar ɗan gidan indabo ce""" """Waye Indabo?""" """Mutumin da ya kashe mini jauhar""" Nabila ta rufe baki cikin tsananin mamaki. """A ina ki ka sameta?""" "Ta ce ""Kar ka damu, manta kawai"" sai da kanta ya sara, ta ina zata fara yi masa wannan mugun jawabin mara daɗin ji, indabo ya kashe Nura guduma, kuma yanzu ɗansa ya saceta, bayan yayi" mata fyaɗe. "Wurin barrister Habib ta je, ta sanar masa da abin da ya faru, sun daɗe suna mamaki, barrister Habib ya ce ""Wannan lamarin ba zamu miƙa shi kai tsaye ga 'yan sanda ba, dan bamu san a hannun wa zamu danƙa ba, yana buƙatar sirri sosai da sosai, kar wani yayi mana katsalandan ya ɓ" "ata mana aiki""." "Bayan Nabila ta gano Alhaji mu'azzam, shi ya sama musu wanda suka cigaba da tracking in da ramma take, ta hanyar bibiyar lambar Abdul, har zuwa lokacin da aka yi nasarar gano in da take," "jami'an tsaron Civil defense, suka je suka ɗaukkota" **** "Nabila na tsaye na leƙen window, ta kasa gane a ina take, wurin shi ba jeji ba, shi dai gashi nan." "Ta koma ta nemi wuri ta zauna, Viper ya shigo da sallama, ta amsa masa, ya je gabanta ya tsaya," "ya ajiye mata ledar abinci ya ce ""Gashi nan ki ci ki sha magani""" """Vi""" """Mmm""" """Dan Allah ka mayar da ni gida, ina da abubuwan yi da yawa, yakamata na je ta'aziyyar malam" "garba, na rarrashi iyalinsa na basu haƙuri, bisa ga gazawata, dama ni ban taɓa shari'a na samu nasara ba, kullum faɗuwa nake yi, bani da sa'a"" ta ƙarasa maganar cikin damuwa." """Dama yaushe masifaffen mutum zai yi sa'a?""" """Na ji, amma ka mayar da ni gida, ni ban san me ma zan cewa yan gidanmu ba, kwana biyu bana" "gida, dama ana yi mini iƙirarin bin maza, ban san me zan ce musu ba""" "Viper ya ce ""Na gaya miki, na fisu buƙatar ki, zaki cigaba da zama a nan, har sai kin kammala" "aikina""" """Wai na cigaba da zama kamar yaya? Sai in din ga keɓewa daga ni sai kai, ka san dai bai dace ba," "idan mace da namiji suka haɗu na ukunsu shaiɗan ne, ka san bai kamata ba""" "Ya sunkuyo dai-dai fuskarta, ya tsura nata jajayen idanunsa, da suke razanata wasu lokutan, zaro harshen sa yayi waje, wanda sai da ta tsorata, saboda ganin tsayin harshensa. Ya ɗan ja numfashi ya ce ""Lokacin da ki ke sintiri a gidan da nake, kina neman suna, baki yi tunanin na ukunmu shaiɗ an bane sai yanzu? Sai dai kece macen kuma shaiɗaniyar, idan zamu shekara dubu, baki isheni" "kallo ba, wadda take halalina ma, sai da. Sai kuma ya yi shiru." "Ya cigaba da cewa ""Kamar yadda na gaya miki, duk wata mace idan ba jauhar ba, namiji ce a" "idona""" """Katako kake gani ba namiji ba"" tayi maganar cikin ƙunƙuni." """Ban taɓa ganin abin da ya raina ni ba kamar ke? Amm dama zan gaya miki, ina ganin zan canza lawyer, saboda na lura baki da sa'a ko kaɗan, gashi baki wani goge ba, nafi son wanda zai din ga abin da nake so. Idan na biye miki, sai na koma prison, kuma ƙila nima a bini a kashe a can," "kamar yadda aka kashe wannan mutumin, dan haka zan canza lauya""." "Ɗagowa tayi tana kallon Viper, cikin tsananin mamaki da takaicin abin da yake fitowa daga" bakinsa. "Fuskarsa a ɗaure, alamar da gaske yake yi." """Bayan duk wannan wahalar da na riga na sha? Ka san zaka ɗauki wani lauyan, amma ka wahalar" "da ni, nake ta dagewa ina ƙoƙari a kan shari'ar ka na kasa zaune na kasa tsaye?""" "Viper ya ce ""Eh, muddin zaki cigaba da yi mini rashin kunya, tabbas zan sake saka miki ƙarfe" "wataran, kamar yadda na saka miki da farko, na gaji kin kasa kawo ƙarshen lamarin, kullum sai surutu da shirme ki ka iya""" "Tamkar ta kwaɗe shi, haka wani abu ya cunkushe mata ƙirji, kawai ta kifa kanta a kan gwiwarta." """Abla, ɗago ki ga"" banza tayi masa taƙi ɗagowa." """Kin san magana ɗaya nake yi"" ta ɗago idanunta, da suka yi sharkaf da hawaye." "Ya ajiye mata takarda a gabanta, takardar umarnin kotu ce, da ta hana kama shi, ɗagowa tayi ta kalleshi, ta rasa ihu zata yi na murna ko kuma me? Kawai ta cukuikuye takardar, ta jefa masa a ƙ" "irji, ta sauka daga kan gadon tana cigaba da kuka""" "Murmushi ya yi ya tashi ya bi bayanta, cikin kuka ta ce ""Amma a haka kake cewa zaka canza" "lauya?""" "Ya ce ""Sorry, am just kidding""" """A haka ake wasa Vi?, fuska a ɗaure ana zare ido? Tayaya zan gane wasa kake yi?"" Tayi maganar" tana kuka cike da shagwaɓa. "Ya ce ""Viper baya manta halacci, ba kuma ya saɓa alƙawari, ko da zaki yi failing sau dubu, ba zan" "taɓa barin ki ke kaɗai ba, alƙawari ne da na ɗauka""" "Nabila ta ce ""Look at you, i even save your life, amma da haka zaka yi mini albishir da 'yar ƙ aramar nasarar da nayi"" ya girgiza kai ya ce ""Ba ƙaramar nasara ba ce Congratulations, and barrister Habib ya yi miki message, Civil defense sun ɗaukko rahama"" a take ta waro ido ta ce" """Dan Manzon Allah, da gaske?"" Ya jinjina mata kai, alamar eh." "Rikicewa tayi, ta durƙusa tayi sujudu shukur, ta tashi, ta shiga kaiwa tana komowa ta ce ""Alhamdilillah, ko yanzu na mutu, na cika wani sashe na alƙawarin da nayi, Allah sarki malam" "Garba, Allah ya yi masa rahama, ni me ma zan yi ne dan daɗi Vi?""" "Murmushi take yi, tana kuka, tana ta zarya a ɗakin, kamar zata zare, shi kuma sai bin ta yake da" "ido. Ta je ta tsaya a jikin bango, ta jingina tana sauke numfashi." "Ya sake takawa, ya ƙarasa in da take ya saka hannunsa ɗaya ya dafe bango, yana cigaba da" tsareta da ido. """Thank you for saving my life 'yar suga"" duk da ta takura, amma bai hanata yi masa murmushi ba." "Kallonta yake yi, yana tunanin a yaya zata ɗauki ƙaddarar da take bibiye da ita? Ko zata iya jurewa, ko zata gaza kamar yadda yayi? A hankali ya ce ""Wannan babbar nasara ce ki ka samu, kamar yadda nayi tsammani, ba kya gori, kamar yadda Jauhar take, na zata da na ce zan canza lauya, zaki yi mini gori, amma ba ki yi ba." "Akwai tambayoyi da ki ka yi mini a baya, da wasu wanda nake son na yi miki." "Da fari meyasa nayi yinƙurin kashe ki karon farko da na ganki? Meyasa ki ka ga ruɗewa a fuskar liti da walid da suka ganki? Meyasa na din ga korarki idan ki ka zo wurina, nake yi miki barazanar" "mutuwa? Meyasa su liti suka amince su kawo ki wurina, duk da babu mahalukin da suke bawa damar hakan? Meyasa Indabo ya ke ƙoƙarin yi mini tarko da ke? A yanzu ko a baya, ba za a rasa mutanen da suka nuna miki sanayya ba, alhalin baki san su ba right?"" Ta tsare shi da ido tana jiran" amsohin tambayoyin. """And as my lawyer, akwai abubuwan da yakamata na sanar da ke, but before then, Abla ni da ke ƙ" "addara ce mai ƙarfin gaske ta haɗa ni da ke, dan haka dole mu yi haƙuri, mu karɓeta a yadda ta zo mana, saboda pain ɗin da zaki shiga, zai iya fin wanda ni na tsinci kaina a ciki""" Tayi tsuru tana kallonsa. "Ya zaro wani hoto a aljihunsa, ya miƙa wa Nabila." "Hannunta na rawar rashin sanin wace ƙaddarar ce, ta sanya hannu ta karɓi hoton, wata 'yar ƙ aramar ƙara ta saki, ta saki hoton a ƙasa, jikinta yana rawa, ta kalleshi ta ce ""Soka ke sai na haukace sannan zaka daina yi mini wasa da hankali, menene wannan? Ni bani bace wannan, ni yaushe na sanka har muka yi wannan hoton tare?"" Tayi maganar a firgice, tana neman ta raɓa shi ta wuce, amma ya riƙeta a jikin bango, idanunsa suka cika da hawaye ya ce ""Matata ce a jiki, ita ce jauhar, 'yar madarata, mace mafi soyuwa a gare ni, matar da ba zan manta halaccinta ga rayuwata ba, matar aljanna da kullum nake fatan na farka daga mummunan mafarkin da nake yi, na farka na ganta a kusa da ni, Nabila meyasa ki ke kama da matata?"" Jikinta ne yake wata irin" "rawa, ta zazzaro ido tana kallon sa." "Buɗe ƙofar ɗakin aka yi, suka waiwaya gaba ɗaya suna kallon ƙofar, Alhaji mu'azzam ne ya" "shigo tare da barrister Habib, da kuma ɗan mama, da yake laɓewa a baya, yana leƙowa." "Cikin mamaki Viper yake bin Alhaji mu'azzam da kallo, ba tare da ya saki Nabila ba." Ayshercool 08081012143 ₦500 ne via 0009450228 Aisha Adam jaiz bank sai shaidar biya ta 08081012143 Wanda za su jira document 1K ne. 90009343 'Yan Nijar ku turo katin airtel na 300fcfa *BRIGHT PENS SECOND BATCH* "Ku kasance da littatafan bright pens, second batch." *ƘARFE A WUTA (AYSHERCOOL)* *MUTALLAB (NIMCYLUV)* HADARIN GABAS (NAZEEFA NASHE)* *ZAYTOON (ZEE KUMURYA)* """Bana iya gane ina ake, saboda a matuƙar galabaice nake, amma naji a jikina, yakamata ace idan asibiti ne ya ci ace an je, duk da bana sanya ran zan rayu, a maganar da mutanen motar suke yi, jini nake ta fitarwa ta hancinca, ga azabar yunwa da datti, na gidan yari, tufafina tamkar mahaukaci, dan a mazaunin da aka ajiyeni kenan." "Aka yi parking ɗin motar, aka canza mini wata, wadda nake kyautata zaton ambulance ce, dan a ciki aka toshe hancina da bandeji, saboda jinin da nake zubarwa, aka saka mini ruwa, muka cigaba da tafiya. Tun ina jin maganganun da ake yi a motar, tafiya taƙi ci taƙi cinyewa, har na daina gane komai, na buɗe ido na ganni a wani wuri, a kan gadon asibiti, an tuɓe kayan jikina, sai gajeren wando, na tashi a gigice cikin matsananciyar kiɗima, ina ihu saboda ban san meyafaru da ni ba, na farka ina zaton zan ga madaki da jauhar, ina hana shi cutar da ita, wani ɓangaren ina tunanin ko ina prison ne, wani yayi galaba a kaina. Sai dai na ji ni a ɗaure da ankwa dukka hannayena, na din ga ihu saboda yadda naman jikina yake yi mini wani irin azababben zugi, kamar ba zan rayu ba." "Wasu mutane da ban san suwaye ba, suka zo kaina, da allurai suka yi mini, ɗaya daga cikin su ya ce ""A cigaba da kula da shi mu gani, will he survive the poison, duk yadda zaku yi, ku yi ƙoƙarin ceton rayuwar sa"" haka na sake fita hayyacina na farka, sai dai a wannan karon, ban ji wannan raɗ aɗin ba." "Aka cire mini ankwa, aka tashe ni zaune, aka kawo mini abinci, kamar mayunwacin kare, haka na dirarwa abincin nan, kamar zan haɗa da kwanon saboda yunwa, ina ci ina jin kamar ana yayyanaka kayan cikina da wuƙa, amma azabar yunwar da nake ji, ya sanya naƙi daina ci, sai dai ban gama ci ba na din ga amai, haɗe da jini, wai duk cikin side effect ɗin allura da aka yi mini ne, kashe ni aka so ayi." "Ba a sake bani abinci ba, sai ƙarin ruwa da allurai, mutanen wurin ba kowa ke jin hausa ba, ni kuma bana magana, suna bani damar yin salla, aka fara koya mini cin abinci." "Ba wanda na tambaya dalilin kai ni wurin nan, kuma babu wanda yayi mini bayani, a haka har na shafe wata guda cif." "Duk yadda suka so nayi magana, bana yi, sai dai wasu lokutan ina rasa tunanina, na din ga ganin madaki da jauhar a zahiri, na din ga yinƙurin shaƙe duk wanda yake kusa da ni. Sai da na ɗan samu nutsuwa, aka aske mini gemuna da sumar kaina gaba ɗaya, aka kuma saka mini ankwa, aka rufe mini ido, aka sakani a mota, aka bar wurin da ni." "Wani wurin aka sake kai ni, mu huɗu ne a wurin, kowa da wurin da ake ajiye shi tamkar ceil. Na fauskanci nikaɗai ne musulmi babu bahaushe, sai ƙabilu, kullum bayan nayi sallar asuba, da sassafe haka za a kaimu wani wuri, ana bamu training na azabatarwa, wanda ka iya zama ajalin mutum." "Idan muka gama, zamu saka wasu riguna, masu tambarin dragon, za a kaimu wani wuri, in da ake bamu darasi, malamanmu turawa ne, class ɗin mu huɗun nan ne, kowa da computer sa, ayi mana darasi ta online. Waɗanda suke kula da mu, wasu irin zaratan ƙartin sojoji ne, sun kai su goma sha biyu, a kan mu huɗu kawai." "Azaba ta ishe ni, ban ga alamar za a mayar da ni gida ba, na gaji, gaba ɗaya na rasa ina rayuwata" "ta dosa, bani da wani burin da ya wuce na mutu na huta. Za a bamu abinci mai kyau, a bamu abin sha mai kyau, amma azabar da ake mana ta ishe ni. Wataran ana tsaka da bamu training, na fizgi bindigar wani, nayi yinƙurin kashe kaina, suka riƙe ni, aka ɗauke ni aka kai ni wani ɗaki, da ban zaci zan fito da rai ba. Sai da na kwana bakwai a ɗakin, ko class bana zuwa. Ranar na takwas, ogansu ya zo ya same ni, yake tambayata meye matsalata na yi yinƙurin kashe kaina." "Na ce masa su mayar da ni garinmu, ina son ganin matata." "Ya ce mini muddin ina son komawa gida, sai na basu haɗin kai, na yi wa ƙasata aiki, sun san ni yaron dodo ne, kuma akwai amfanin da zan yi musu, dan haka dole na mayar da hankali a kan training da kuma karatun da nake yi, kuɗi aka ware masu nauyi, saboda mu yi wannan karatun." "Na ce ni ba zan yi ba, su kasheni kawai su daina wahalar da rayuwata." "Ya ce ba zasu kashe ni ba, in yi abin da suka umarceni, idan ina son na ga matata. Sai na tambaye shi, matata na raye? Ya ce tana raye, zan ganta idan na daina taurin kai, nayi abin da ake so. Kuma ko ina so ko bana so, ubangidana ne ya nema mini wannan aikin, tun kan ya mutu, dan haka sai dai na mutu a process ɗin, tun da na san sirruka masu muhimmanci da zasu taimaki ƙasa. Na din ga tunanin, wane irin laifi na yi wa dodo, zai zaɓa mini wannan azabar, sai dai tsananin ɗoki, da daɗin bakin zan ga matata, ya sanya na saduda, gashi suka saka mini ido sosai da sosai, saboda suna iƙirarin bani da lafiyar ƙwaƙwalwa, kuma bana ji." "Wata makaranta muke yi a russia, ilimin na'ura mai ƙwaƙwalwa kawai ake bamu, duk da na san abubuwa da yawa ni, ta online muke makarantar, a training ɗin nan aka koya mana duk wani nau'i na haɗawa da wargaza bindiga, ilimin makamai, leƙen asiri, da duk wani nau'i na abin da ya shafi harkar tsaro." "Suka ce mini ƙwazona, shi zai bayar da damar komawata garinmu, har naga matata, na roƙe su ko a waya, a haɗani da matata tun da sun ce tana raye, suka ce ba zasu haɗamu ba, zan ɓata musu aiki." "Na zage damtse, lokutan jarrabawa, ina cikin overollers, ina tashi da points masu kyau, na fara sabawa da wahalar training, jikina duk ya murɗe, sai dai babbar matsalata bana cikakken bacci, bana iya bacci, da na rufe idona, zan ganni a falo, tare da jauhar madaki zai kasheta, gaba ɗaya sai na tubure musu, na hau ihu. Ko abincin da nake ci, bana cin sa ta daɗin rai, saboda damuwa da tunani. Abokan karatuna a kan basu damar shan giya, har mata a kan kawo musu, amma ni duk ba wannan a gabana." "Tun ina lissafi da sanya ran ƙarewar wannan wahala, naga babu rana babu wata, na zauna nayi tunani, babu yadda za ayi, jauhar na raye a gurfanar da ni a gaban kotu, a tuhume ni da laifin kisan kai, naga kawai raina mini hankali suke yi, sai kuma wata zuciyar ta ce mini ai mafarki nake yi, sai dai na rasa wanne ne mafarkin wanne ne zahirin?." "A haka na shafe shekaru a wurin nan, ban taɓa barin kewayen in da muke ba, na rayu da matsanancin ƙunci da damuwa a zuciyata, wasu lokutan sai an yi mini allurar bacci nake iyawa." "A haka muka kammala karatu, sauran ukun aka ce, za ayi posting ɗin su, in da ake son su gabatar da ayyukansu, ni kuma sai an yi settling issue ɗina. Mun zama sojojin leƙen asiri." "Ni dai jinsu kawai na din ga yi, sauran suka din ga murna, aka shirya mana walima, sauran duk sun saba da su, ni duk yadda aka so ja na a jiki, a yi raha da ni, a saba ban yadda ba, dan ni kaina na san rabi mai hankali rabi mahaukaci nake. Abokan karatuna kuwa, basa shiga harkata, dan duk lokacin da ƙwaƙwalwa ta ta haska mini fuskar madaki, a jikin ɗaya, sai na kusa kashe shi, dan duk da training ɗin da aka bamu, na fi su ƙarfi nesa ba kusa ba, kuma ba addinmu ɗaya ba, ba ƙ" abilarmu ɗaya ba. "Sai da na ji haushin dodo, duk da baya raye, na ji ya sakani a masifa, duk da ina fatan sanya indabo, biyan bashin abin da ya aikata ciki har da kisan dodo." "Ana gobe za a mayar da ni kano, ina ta murna zan koma naga jauhar, naga ɗana, dan na san a lokacin ya yi wayo, ban san meyafaru ba, ko me suka yi mini ba, sai farkawa nayi, na ganni a prison. Hakan ya ƙara burkita ƙwaƙwalwa ta, na fara tunanin wani mafarkin na kuma yi, na din ga kiran sunayen shugabbaninmu da suka bamu training, ina cewa su zo su cika mini alƙawarin da suka yi mini, su haɗa ni da jauhar ɗina da ɗana kamar yadda suka yi mini alƙawari, gashi ko za a kashe ni, ban san sunan garin da aka kaini ba." "Gandirobobi, suka yi mini dukan tsiya, wai na cika musu kunne da hauka, matar da na kashe da hannuna, bayan na sha na bugu, na amsa hakan a kotu, yanzu kuma na zo na ishe su da shirme. Suka yi mini dukan tsiya, amma na kasa daina kururuwar kiran sunaye da magiyar su haɗani da jauhar, gaba ɗaya na zama mahaukaci, ni kaina a lokacin na yadda ni mahaukaci ne. Wasu lokutan idan na buɗe jikina, ina ganin tabon raunuka da wahalar da na sha a wancan garin, amma fafur aka nuna hauka nake yi, da sambatun ƙarya." "Tun da suka tabattar mini ni na kashe jauhar, na ƙara rasa tunanina, damuwa da tashin hankali suka koma sabbi fil." "Kusan watanni uku, cikin dare ina kwance, dama ɗakina daban, aka tashe ni aka ce na fito, na fita na bi bayan wanda suka kira ni, aka fitar da ni wajen gate, wai an karɓi court order na tafi." "Na tsaya ina kallonsu, ina mamakin wane mafarkin kuma na sake shigowa, suka rufe gate ɗin prsion ɗin, suka bar ni a tsaye." "Zuciyata ta raya mini maza kafin na farka daga baccin, na je na ga jauhar, ko zan farka dai na ganta." "Na fara tafiya a duhun nan, har garin Allah ya waye. rana ta ɗaga, na isa unguwar mu, ban manta hanya ba. Sai dai Abbu ya tabattar mini da jauhar ta mutu, ni na kasheta, na tafi na bar masa gida. Mutanen unguwa suka din ga kallona, har da masu gudu." "Babu tunanin komai ko tsoro, bayan na je dabarmu, su Walid suka karɓe ni, suka kuma tabattar mini da cewar na rasa Jauhar." "Na burkice musu, amma suka riƙe ni suna kula da ni, kawai sai ga sanarwa daga hukumar 'yan sanda, wai a kamo ni, a raye ko a mace, da fari suka ce na gudu daga prsion, daga baya kuma wai an sake ni ba bisa ƙa'ida ba." "Walid ya ce ""Kome za ayi, ba zasu yadda a sake mayar da ni a kulle ba, sun san ba zan taɓa kashe 'yar madara ba." "Na tarar da su da ɗan mama, na san shi tun da na taɓa yi masa rauni, shi ne ya bayar da gidan da muke zaune muke ɓoye." "Idan nayi kamar na gaya musu, rayuwar da nayi ana bani training, sai na tuna aikin sirri ne, an gargaɗemu a kan haka, kuma bani da evidence ni kaina bani da tabbacin cewa a gaske nayi wannan rayuwar." "Bana iya bacci, bana iya cin abinci, ga azababben ciwon kai, ga nauyin ƙirji, kawai na koma shaye-shaye fiye da da, duk da a wurin training ina shan sigari da wiwi, sai dai bana shan miyagun ƙwayoyi, ko giya." "Amma bayan tabattar da mutuwar jauhar, na cigaba da shaye-shaye ina fatan ko haukacewa nayi, na manta da duk wata rayuwa, wadda nake tunanin gaske ce ko mafarki, amma kayan cajin basa ɗ aukata." "Ganin ɗan mama na din ga yi tamkar Nura, dan ba zai fi sa'ansa ba, ya din ga yi mini biyayya," "hakan ya sanya nake son sa sosai, saboda su Walid kullum cikin faɗa muke, suna hana ni shaye-shaye." "Shi kuwa samowa yake yi ya kawo mini, a hakan idan na bushi iska, sai na tafi gidana na dura ta katanga, na kan yi iya ƙoƙarina nayi kuka, amma bana iyawa, sai dai na yi ta jin ƙunar rai da bugun zuciya." "Na kan yi yinƙurin zuwa na ɗauki fansar abin da madaki yayi mini, amma su Walid su hana ni, suka samo mini waya keypad suka bani incase ina buƙatar wani abu, basa nan, ɗan mama shi yake yi mini duk wata hidima, kawai wannan mutumin ya fara kirana, yana ƙara dagula mini lissafi. Kayan shaye-shayen ya zama basa ɗaukata, sai dai nayi ta tamɓele, suna iya ƙoƙarin su a kaina, amma ba sa yi mini abin da nake so." "Damuwa shaye-shaye suka ƙara tsunduma ni a wani hali, har nake yinƙurin kashe kaina. Ashe duk wannan abun, mutanen nan suna bibiye da ni, da duk wani motsina, na din ga ƙoƙarin jami'an tsaron kawai su kamani, su yi duk yadda za su yi da ni, amma da nayi laifi, dan goge hanyar da za abi a kama ni." "Walid ya zo ya bani labarinki, na ce ƙarya yake yi, cutata zai yi. Bai haƙur ba, ya kawo mini ke, kawai ƙwaƙwalwata ta bani cewar, an haɗa baki da ke an shirya wani abun ne, dan a kuma yi mini wani mugun abun, hakan ya saka na sanya miki ƙarfe ko zan ga ainihin wacece ke, dan na san jauhar ba ta kaiki girma ba, ba ta kaiki waye ba, kuma babu yadda za ayi ta ganni ta kasa gane ni." "Amma da ki ka faɗi, ciwonki ya tashi, sai na ga kin koma ita sak, duk da ina jin haushin mata wasu lokutan, amma a sanadinta nake tausayin su, saboda tunawa da ita, na sai kayan treatment ɗ in ta na asma, nake ajiyewa ina kallo, ina ganin kamar zata dawo. Shigowar ki rayuwata, ya ƙara rikita mini lissafi, Walid ya ce na sanar miki irin kamannin da ki ke yi da matata, na baki labarina, amma naƙi." "Na cigaba da barazanar kashe ki, saboda na kasa tantance jauhar ce ke ko ba ita ba ce, nayi ta ƙoƙ arin avoiding ɗinki, kar na aikata ɓarna, saboda babu in da ki ka bar ta, sai kuma daga baya na ga zuwanki wurina, yana rage mini damuwa, kamar ke kin fahimci halin da nake ciki." "Rigar da ake ta bibiyata da ita, ta wancan aikin ce, dan an tura mini saƙon zasu tafi da ni, na ƙi kulawa, sai daga baya da na amince da ke, na ga dole ina buƙatar security ko dan lafiyar ki, na amince zan tafi nayi aikin, amma sai na samu nasara a kotu. Aka ce za a ɗaukar mini lauyoyi da zasu kare ni, zasu nemi a basu ni, su suyi na su binciken, su yi mini hukunci na ce ban yarda ba, ina da lauya, tsaro kawai nake buƙata a tsare mini lafiyarki." "Suka yarda da hakan, amma da zimmar zan fara yi musu aiki." "Daga nan barrack ɗin kano, suka zo suka tafi da ni, aka bani kayan aiki, ciki har da tab ɗin hannuna, da rigar aiki da ki ke ganina da ita, sai dai ba kowa ya san ma'narta ba, ciki har da su Walid." "A yanzu haka ina karɓar salary, kuma ina aiki da NIA, ƙoƙarin ki ne zai sanya, na yi free na" "cigaba da aikina, akasin haka kuma, zan iya komawa prison ne, babu ranar fitowata, duk da ba zan ce ma ban yi shekarun nan a prison ba, tun da kauwwame ni aka yi, aka hanani dukkanin walwala." "Nabila tayi ƙuri da ido tana kallonsa, cike da tsantsar mamakin duk wannan rashin mutunci, da cin mutuncin doka, a Nigeria ake aikata shi. Wani abun idan bai zo kanka ya faru ba, sai ka rantse da Allah ƙarya ne ba zai faru ba. Har gara shi, da aka fitar da shi daga prison ɗin, taimakon sa" "aka yi ta wani fannin, wasu kuwa canza musu gari ake yi gaba ɗaya, suje su yi rayuwarsu, saboda" "tsabar masifa, a prsion ɗin ma bin sa aka yi za a kashe. Gaba ɗaya rayuwar Viper gaba a baya" "take, sai dai ita ma tata rayuwar kusan haka." """Abla, talk please, jami'an tsaro na nemana, zan je a ɗauki statement, kuma dole sai da ke zamu tafi, dan Allah ki daidaita nutsuwar ki, yanzu rayuwata tana hannun Allah, tana hannunki, nayi rejecting support ɗin da za a bani a hukumance, na zaɓi cika miki alƙawarin da nayi miki, ba zan" "ja da baya na barki ba""" "Ta ɗago idanunta da suke tsiyayar da hawaye ta ce ""Wacece ni? Kuma wacece jauhar?""" """Ki na ji na? Shiyasa tuntuni nake jinjina yadda zan yi miki bayanin nan, ki nutsu ki karɓi ƙ" "addara a duk yadda zata zo miki""" "Nabila ta ware masa manyan idanunta, da suka yi jawur, ta ce ""Ba ni ce jauhar ba, to ni wacece? Ko jauhar 'yar uwata ce? Dan girman Allah ka kaini gidansu na ga ko iyayenta ne, wataƙila muna" "da alaƙa""" "Ya girgiza mata kai ya ce ""Babu tabbacin kina da alaƙa da ita, bata taɓa gaya mini cewar tana da wata 'yar uwa ba, ce mini tayi itakaɗai mahaifiyar ta ta haifa a gidan, ta fita. Amma ke babu abin" "da ki ka sani game da mahaifiyarki, da ahalinta?""" "Ta ja wata irin ajiyar zuciya ta ce ""Idan ya kasance jauhar yar uwata ce, kenan ina da 'yar uwa ban" "taɓa ganinta ba, ban rayu da ita ba? An cutar da ni, wallahi an zalunce ni""" "Viper ya ce ""Kar ki ce haka, ki bari sai mun tabattar tukuna, kuma wannan amsar dole 'yan" "gidanku ne za su bayar da ita, amma mu fara gamawa da wannan case ɗin, kiyi haƙuri""" "Tari ta fara yi, tana kuka ta ce ""Ni gaba ɗaya baka yi mini adalci ba, ka ɓoye mini abubuwa da yawa, da yakamata na sani, sai yanzu zaka gaya mini. Ni ka rabu da ni ma ka ƙyale ni, ina ga" "nima haukacewar zan yi""" "Duk yadda Viper ya sauke jin kansa, yake rarrashinta, ta burkice masa, ta ce idan an ga dama a ɗ" "aure shi da igiya, case ɗin nasa ma ta fasa, ƙarshe haka ya tashi ya rabu da ita." *** """Badi'a, anya ba zan gudu na bar ƙasar nan ba, ina daf da yin faɗuwar baƙar tasa, wannan yarinyar ta dage sai ta ga bayana ta kaini ƙasa, ya zan yi ne?""" "Badi'a ta ce ""Naja, wallahi ki ka bari yarinyar nan ta ga bayanki, kin ɗuma asara""" """Badi'a, kowace hanya ta toshe ta ko ina, duk masu goya mini bayan, sun ce wannan karon" "lamarin yafi ƙarfin su, shi kansa Indabo yana can Abuja, yana fuskantar tuhuma, EFCC sun dakatar da wasu daga cikin kadarorinsa, yana cikin tashin hankali, na rasa yadda zan yi""." """Wallahi kina guduwa asirinki zai tonu, ki jira kiga iya gudun ruwansu, tun da haryanzu ba su ce" "komai ba, ba su tona miki asirin ba""" "Kamar ta fasa ihu ta ce ""Yanzu jira zan yi sai sun fito sun tona ɗin? Ke kin san ba zasu bar ni ba, lallai ɗan hakin da ka raina, shi ke tsole maka ido, babu ƙoƙarin da ban yi na kawar da yarinyar" "nan ba, amma abu ya gagara, amma duk da haka ba zan zuba ido ba, sai na san abun yi""." *** "Abdul kuwa ya yi sintiri tsakanin Kano da Abuja, babu adadi, amma ya kasa ganin Indabo, hakan ya sanya ya tabattar wa da kansa cewar Indabon ne ya ɗauke ramma." "Duk yadda mahaifiyar ramma, ta bugi cikinta, ramma ta nuna mata babu abin da ya faru, Abdul" "ajieta kawai yayi, duk da ya ce ya aureta." "Maman ramma ta ce ""Har na ji sanyi, dole a zo a raba auren nan, dama ba da yardata kawunki ya aurawa wannan tsohon mara mutunci ke ba, saboda kuɗi da tsinannen son abin duniya yayi mini haka. In sha Allah yaron nan sai Allah ya tozarta shi kamar yadda ya tozarta mu, sai Allah ya wula ƙanta shi, kamar yadda yayi mana"" jin Addu'a ramma tayi har cikin zuciyarta, dan sai da cikinta ya" "motsa, tayi shiru bata amsa da Amin ba, ta san duk inda yake yana can hankali a tashe." """Amma ramma, kin tabattar ba abin da ya haɗaki da mutumin nan? Mutumin da yayi miki fyaɗe" "shi ne zai aure ki kawai ya ajiye ki?""" "Cikin tsoro da rashin gaskiy, ramma ta ce ""Eh, ɓoye ni yayi saboda kar asirinsa ya tonu, cewa aka yi da ya kashe ni ma, shi ne bai kashe ni ba. Kuma wai ya biya mini kuɗin makaranta na cigaba" "har jami'a""" """Allah ya kiyaye, ba ma buƙatar duk wani abu daga hannunsa, da haka zai yaudaremu, in sha Allah sai an hukunta shi, barrister nan tayi mini wannan alƙawarin, sai an gurfanar da shi, ya girbi abin da ya shuka, ga kisan kan da suka yi wa wannan tsohon, da suka ƙalawa sharri, Allah dai ya" "watsa shi, daga shi har wanda suke goya masa baya""" "Ramma ta kawar da zancen, ta hanyar cewa ""Mama wai a nan zamu yi ta zama?""" "Ta ce ""A'a, nima wannan Alhajin ne ya saka aka ɗaukko ni wai idan aka bar ni, nima za a iya cutar da ni, ban san zuwa yaushe zamu zauna a nan ɗin ba, amma ina ga da komai ya daidaita sai" "mu tafi"" Ramma ta jinjina kai." "Maman ramma ta bi ta da ido, ganin yadda duk jikinta yake a sanyaye, ta kalli fatar ramma yadda" tayi haske take ta sheƙi. """Rahama""" """Na'am mama""" """Wai me ki ke ci ne a hannun nasa, na zata a wahale zan ganki, ki gaya mini tsakani da Allah idan" "akwai wani abu""" """Mama babu komai fa, nifa tun da ya ajiye ni baya ƙasar, sai masu kula da ni"" mama ta jinjina kai" "kawai, ba ta sake magana ba." "Viper ya haƙura da azabar kishin da yake ɗawainiya da shi, aka yi zama na musamman da shi da Alhaji mu'zzam, da shugabannin sa, aka sake jaddadawa Al'amin, Alhaji mu'azzam tainakonsa yayi, kuma tare da haɗin kan Alhaji mu'azzam komai ya tafi daidai, kasancewar sa babban mutum a ɓangaren harkar tsaro." "Sai kuma aka yi masa alƙawarin ba shi duk wata kariya, da shi da Nabila, tun da haka ya zaɓa," "amma muddin suka yi failing a shari'a a kotu, babu wani abu da za a kuma sake yi masa. Ya ce ya amince, babu gudu babu ja da baya Nabila ce lauyar da zata tsaya masa." "Sai dai Nabila gaba ɗaya ta hargitse, Viper ya kasa gane kanta, gashi an gayyace shi hukumar yan" "sanda, ya je ya bayar da bayani, amma Nabila fafur ta ce ba zata je ba." "Sanarwa kuma ta fita, muddin Viper bai kai kansa ba, order kotu zata koma arrest order." "Nabila na zaune, zuciyarta a cunkushe ta rasa abin da yake yi mata daɗi, lallai tana buƙatar ganin" "Abba, ko ta halin ƙaƙa Viper ba shi da niyyar yi mata bayanin abin da take son ji." "Ta ga wayarta a gefen gadon da take kai, tayi sauri ta ɗauka, ta kunna tana dudduba saƙonni." "A What's app ta tarar da message, wai gari ana ta yaɗa rumors, cewar Viper ya saceta, ba a san in" "da take ba, wasu suna Allah ya ƙara, wasu suna yi mata addu'a." "Ta buɗe message ɗin Nasir, ta saurari voice message ɗin da ya turo mata." """Haryanzu wanda ki ke iƙrarin karewa, bai bayyana a gaban hukumar yan sanda ba, idan ya wuce wa'adin da muka bashi, order kotu zata sauya, ga shela da ake ta yi, na cewar ya sace ki, ba a san in da ki ke ba, ko a nan sunanki ya ɓaci, am did on you." "Knocking aka yi, tayi shiru, dan ta zata Viper ne, ta ajiye wayar." "Wani narkeken mutumi ne ya shigo, tare da barrister Habib, da sumayya, da kuma Walid." "Zama tayi sosai tana kallonsu, sumayya ta ƙarasa ta zauna a kan gadon ta ce ""Nabila, ya kike kina" "cikin ƙoshin lafiya?"" Nabila ta jinjina mata kai." "Mutumin ya ce ""I salute you barrister, kallabi tsakanin rawuna"" yayi maganar cikin gurɓatacciyar" "hauss, amma da alama ya ji hausa." "Ta ɗan yi murmushi yaƙe, ta kalli Walid ta ce ""Oga walid""" """Na'am barrister, ya ki ke ya ƙoƙari?""" """Alhamdilillah"" ta din ga bin su da ido, dan bata san dalilin zuwan su duka ba." "Walid ya ce ""Barrister, na san mun yi miki laifi, tun da fari na so Viper yayi miki bayani, amma ya ƙi, kin san shi wasu lokutan da taurin kai, kuma na san kin yi haƙuri da shi, amma dan Allah ki janye batun cewar ba zaki tsaya masa ba, ki yi haƙuri dan Allah, ba zamu iya jure ganinsa ya koma prison ba, kiyi wani abu a kai, wanda kuke ƙalubalanta, suma ba zasu zauna haka ba, dole zasu yi" "ƙoƙarin yin wani abu suma, ki taimaka""" "Ɗaya mutumin ya ce ""Duk wani support da zamu ba shi a hukumance, yaƙi yarda, ke kaɗai ce" "hope ɗin sa, kar ki ce a'a, kiyi haƙuri, a ƙarasa wannan case ɗin, sai koma menene ya biyo baya""" """Meyasa ya ɓoye mini abubuwa irin wannan?""" """Tsarin aikinmu ne a haka, haryanzu ke kaɗaice lauyar sa, ke ki ka sani, su kansu yanzu da muka zo tare ba komai suka sani ba, ga abokin aikinki, dole kina buƙatar sa, ga ƙawarki kina buƙatar ta," "ga abokansa da sun san komai""" "Barrister Habib ya ce ""Ga case ɗin ramma ma""" "Mutumin ya ce ""Yess, ke fa yanzu idon duniya yana kanki, ba laifinsa bane, kin san ba mai yawan" "magana bane ba, kuma tsarin aikinmu ne, yanzu abin nan da ya gaya miki, zai iya zama da hukuncin kisa a kansa, banda mun san a situation ɗin da yake""" "Walid ya ce ""Yana asibiti ma, ciwon cikin nan da yayi kwanaki ya kuma tayar masa, hantarsa ta kumbura, yana asibitin sojojin nan da aka ɗaukko ki""" "Nabila ta numfasa, ta ce ""Muje zan ganshi, kuma ina son zuwa office ɗina, zan koma aiki""" "Mutumin nan ya ce ""Is ok, zaki koma bakin aikinki, amma a ƙarƙashin kulawar mu, ƙasarmu na" "san rayuwar Viper""" """Amma ku ka bari ya kusa haukacewa, aka ɓata masa suna"" mutumin yayi murmushi ya ce ""We" "are trying our best now""" "Sumayya ta ce ""Nabila ina son magana da ke fa""" """Ni da nake kare ɗan ta'adda, me ki ke so a wurina?""" "Sumayya ta yi murmushi ta ce ""Arfan Abbanta, an buga dake an barki, batutuwa ne masu" "muhimmanci, amma sai kin saukko tukuna""" "A cikin wata rantsatsiyar mota, aka ɗauki Nabila da sumayya, da barrister Habib, suka tafi." "Liti ya ƙarewa ɗan mama kallo ya ce ""Ɗan mama, ni haryanzu mamaki nake yi, yaushe Viper ya" "san wannan mutanen bamu da labari ne? Wai naga sojoji ne suke kula da shi, duk ka munafunce mu""" """Nima ban san meyasa ba""" """Ƙarya kake yi munafiki, ka san komai, meye haɗin Viper da sojoji? Ko ka gaya mini ko na ɓ" "ulaka da wuƙa""" "Ɗan mama ya ce ""Wallahi oga liti muka yi misbehaving, zanemu za ayi daga ni har kai a barikin" "nan, dan Allah kayi haƙuri ka rufa mana asiri""" """Ni haryanzu tsoro nake ji, idan ba haɗa kai aka yi da kai, ake son a kashe mu ba, ko a haɗamu a cikin yan boko haram ace duk su ne ba, gaba ɗaya baka da imani ɗan mama, tsawon lokaci kana" "jakadancin munafunci""" "Suna cikin maganar, su Nabila suka shigo wurin, ba wanda ake bari ya shiga wurin Viper, su liti" ma a waje suke. Aka ce Nabila ce kawai zata shiga wurin Viper. "Ta taka a hankali ta shiga, ta tarar yana kwance, likita yana yi masa allura ta cikin cannula." "Suka gaisa da likitan, ya gama yi masa ya fice, ta zauna ta kalleshi ta ce ""Effect na shaye-shaye" "yana ta bibiyarka"" ya yi shiru yana kallonta." """Idan ɓoye mini waye kai, ba laifinka bane tsarin aikinka ne, ni kuma ɓoye mini wacece ni, laifinka ne da wasa da hankalina." "Ba zan watsar da alƙawarin da nayi maka ba, gobe in Allah ya kaimu zamu je station, zamu bayar" "da statement, amma bisa ga sharaɗi ɗaya da sai ka yadda da shi""" Ya lumshe idanunsa ya buɗe yana kallonta. """Am talking to you""." """Viper zaki sawa sharaɗi?""" """Your freedom depends on me, so watch your tounge""" """Send me back to prsion if you like, i am still Viper, the most dangerous snake""" """A heartless spy""" "Ya yinƙura ya tashi zaune yayi murmushi ya ce ""I admit it, am heartless""" """Dole ka amince da sharaɗina Viper, akasin haka kuma........" Ayshercool 08081012143 ₦500 ne via 0009450228 Aisha Adam jaiz bank sai shaidar biya ta 08081012143 Wanda za su jira document 1K ne. 90009343 'Yan Nijar ku turo katin airtel na 300fcfa *BRIGHT PENS SECOND BATCH* "Ku kasance da littatafan bright pens, second batch." *ƘARFE A WUTA (AYSHERCOOL)* *MUTALLAB (NIMCYLUV)* HADARIN GABAS (NAZEEFA NASHE)* *ZAYTOON (ZEE KUMURYA)* "Shiru tayi ganin irin kallon da ya yi mata, a take jikinta ya hau rawa, ta haɗiye maganar da take" son yi. "Ya jingina yana kallonta ya ce ""Ina jinki, sharaɗin menene?"" Ta girgiza kai ta ce ""Shikenan kawai, yakamata mu fara zuwa mu sake ganin madaki, an ce yana asibiti, a hannun jami'an tsaro," "yakamata mu je mu ganshi, kafin mu haɗu gaba ɗaya a gaban yan sanda""" """Menene sharaɗin naki?""" "Ta ɗan kalle shi ta ce ""Bakomai, ya wuce kawai"" ta yinƙura zata tashi, ya mayar da ita ya zaunar" "da ita, yana bin fuskarta da kallo." """Kawai kin zaɓi ki wahalar da ni, saboda kin ga ina lallaɓaki ko?""" "Ta girgiza kai Viper ya ce ""Haka ne mana, i can give up the trial, na koma prison kawai, i can do" "it""" "Jiki a sanyaye ta ce ""Am just curious to know who i am, ina son sanin mahaifina, da 'yan uwana" "idan ina da su, amma bana fatan ace ina da alaƙa jauhar matarka""" "Da sauri ya ce ""Why?""" """An gaya mini mahaifina yana da mata da yara, ya auri mahaifiyarmu, muddin jauhar yar uwata ce, zai iya yiwuwa cikinmu ɗaya, ta mutu ba tare da na taɓa ganinta ba"" tai maganar tana zubar da" hawaye. """Kin ga babban dalilin da ya sanya, na cigaba da ɓoye miki abubuwa da dama, you will lose" "confidence. Babu tabbacin kina da alaƙa da jauhar, kuma dolena cika alƙawarin da nayi miki, ki kwantar da hankalinki"" kamar ya tunzurata, ta cigaba da kukan." "Yayi ƙasa da muryarsa ya ce ""Bana barin 'yar madara ta zubar da hawaye, muddin kina kuka a gabana, matata nake gani, zan iya rungumarki at any time na ce zan rarrashe ki, ki rufa mini asiri kar ki saka na aikata ɓarna, kin ga daga nan kuma ba lallai na tsaya a nan"" da sauri ta ja da baya" "tana kallonsa, tsaf zaka rantse ka ce baya magana." "Ta ce ""Ammm yaushe zamu je mu ganshi?""" "Viper yayi murmushi ya ce ""Za ayi mini allurai anjima, sai mu je kawai""" "Nabila ta ce ""Ka ji sauƙi ne?""" """Idan aka yi mini allurai ina jin daɗin jikina, daba da shaye-shaye sun yi mini mugun tabo, illoli" "ko ta ina""" """Kayi ta istigfari, Allah ya yafe maka ya sassauta maka, bari na je waje"" ya jinjina mata kai alamar" to. "Ta fito ta tarar da su, ta kalli barrister Habib ta ce ""Yaya, zamu je mu ga ɗaya daga shaidun da" "muke da su ne, gobe in Allah ya kaimu zamu je wurin jami'an tsaro""" "Habib ya ce ""To shikenan, jikinsa sa sauƙi amma?""" Ta jinjina kai alamar eh. "Sumayya ta ce ""Ni dai sonake naga Vipern nan, amma Allah bai yi ba, zan koma ana nemana," "amma Nabila na gaya miki mahaifin sa yana ta sintiri, yana so na haɗaki da shi, neman ɗansa yake ido rufe""" "Jiki a sanyaye Nabila ta ce ""Ki rarrashe shi, yayi mana afuwa zuwa mu kammala shari'ar nan," "Viper ba zai yadda su haɗu yanzu ba""." """Amma Arfa meke damunki ne? Ko wani abin suke yi miki da ba kya so?""" "Nabila ta girgiza kai hawayen da ta ke ƙoƙarin tarewa, suka zubo mata." "Hankali a tashe Sumayya ta ce ""Nabila menene?""" "Nabila ta ja hannunta suka koma gefe, ta ce ""Sumayya, matar Viper da aka kashe, ina kyautata" "zaton ina da alaƙa da ita""" "Sumayya ta ce ""Ta ina?""" """Yanzu na san ko na ce ya bani hotonta, ba zai bani ba, idan ki ga ganta rantsewa zaki yi, ki ce ni" "ce a jikin hoton""" """Ke Nabila bana son shirirta dan Allah, saboda soyayya ta rufe miki ido, har kin fara kalen dangi""" "A hasale Nabila ta ce ""Sumayya yaushe zaki din ga ɗaukar maganganuna serious ne? Kodayeke shikenan, daga baya idan komai ya bayyana, zaki gane idan ma ƙarya nake, idan ma gaskiya nake" "faɗa, ki je kiran da ake yi miki"" Sumayya ta bi Nabila da kallo har ta bar wurin." "Suna tafe a hanya, Nabila take tunanin lokacin da take takurawa Nasir, tana tambayarsa me zata yi, wanda zai saka tayi suna sosai ta zama kamar bunkure, ya ce mata ta nemo masa Viper. Ta din ga bin yadda abubuwa suka din ga faruwa daki daki, ita kanta ta san ƙudura da ikon Allah ne kawai da ya ƙaddara sai ta haɗu da Viper. Da ta din ga lissafa rashin hankali da wautar da ta din ga yi, tana yawon nemansa, yana iƙirarin kasheta, amma tana nace tana bibiyarsa kamar mayya har zuwa" "wannan lokaci, abun lamari ne na Allah kawai." """Amma daga can, yakamata muje ku gaisa da mahaifiyar ramma""" "Ya ɗago ya kalli Nabila ya ce ""Bana son haɗuwa da mutanen da na sani, suna yi mini kallon ɗan" "ta'adda""" "Nabila ta girgiza kai ta ce ""Ba kowa ne yake yi maka kallon hakan ba, abin da yakamata ne," "mussaman da iftila'in nan ya faɗawa ramma"" yayi shiru bai ce komai ba." Har ɗakin da madaki yake aka kai su. "Tare da Viper suka shiga, suka tarar da shi a kwance, duk jikinsa sara da suka, da rauni, ɗakin sai wari yake yi. Babban abin da ya bawa Nabila mamaki bai wuce duk jikin madaki raunukan nan sun yi kore ba, maimakon ja, irin na ciwo. Hatta fuskarsa sara ne, kamanninsa sun sauya daga shi" sai ɗan wando. "Nabila ta dubi jami'an tsaron da suke tsare da shi ta ce ""Yanzu a haka yake? Ana duba shi kuwa?""" """Eh, likitoci na duba shi, yana da ciwon suga ne, dan haka wannan raunukan ba zasu warke ba, sai" "dai ayi ta treatment a haka""." """To wannan tayaya zamu je da shi kotu, yana magana ma tukuna?""" "Madaki ya buɗe ido da kyar, yana kallonsu." "Viper yayi murmushi, dan ya san ba ciwon suga bane kawai, russia da yayi amfani da ita, wurin karya sihirin da yake amfani da shi ne ya janyo haka, duk wani rauni da ya ji, muddin da ƙarfe ne," ba zai warke ba. Wancan karon ma Viper shi yayi sponsoring yanke ƙafar madaki. "Viper ya ce ""Ya kake kallonta, haryanzu kana tunanin wadda ka kashe ce ko? Nayi mamaki da na turo maka ita da farko, ka iya jurewa baka yi wani abu ba. Kodayeke namiji idan ya kai namiji, baya tsoro baya nuna gazawa." "Ina yi maka albishir da sai ka ruɓe a raye, kafin ka mutu, dan idan ka mutu yanzu hutu ne. Naka ƙ arshen ya fi na kowa muni. Baka aikata alkhairi ba, baka bar wani baya mai kyau ba, babu ɗa babu jika, sai tarin zunubi da haƙoƙƙin mutane. Ga lokaci ya ƙure da zaka bi su yawon neman yafiya. Ka zo a banza zaka koma a wofi, ina fatan sunana da yake gadon bayanka ba zai ruɓe ba, zaka koma ga Allah da shi, duk da kome zan yi maka, ba zan huce zaluncin da ka yi mini kashi-kashi ba." "Da farko yayana, na biyu ubangidana, mafi muni kuma matata da ɗa na, wata shari'ar sai a lahira," "duk abin da zan yi maka, ba zan bi wa yar madara hakkinta ba, Allahn da yayi ta shi zai saka mata"" yayi maganar muryarsa na rawa. Madaki ya ƙure su da ido." "Nabila ta girgizawa Viper kai, cikin matsanancin tausayin sa, juyawa yayu yana haɗiye hawayen" da yake shirin zubo masa. """Vi, shaidar da muke da shi, ɗaya yana kwance ba zai ma taɓa yi mana amfani ba, ba magana zai" "yi ba, dole muna buƙatar wata ƙwaƙwƙwarar shaidar""" """Kamar wa kenan? Wa zamu samo?""" """Muna buƙatar, ko daga cikin maƙwabtanku, ko makamancin haka""" "Viper ya ce ""No, ki rabu da wannan mutanen, mu bari gobe in Allah ya kaimu sai mu ga yadda za" "ayi""." """Muna buƙatar iyayen jauhar a case ɗin nan""" """Meyasa?""" """Saboda shaidunmu su zama masu ƙarfi, bana son a ja shari'ar da yawa"" yayi mata shiru bai sake" cewa komai ba. "Nabila har system ɗin ta aka kawo mata daga wurin aiki, barrister Habib ya kawo mata."