𝐙𝐀𝐅𝐈𝐍 𝐖𝐔𝐓𝐀 LABARI ME CIKE DA "BAN TAUSAYI, " "MATSANANCIYAR DAMUWA, KUNCIN CUZIYA, " "SADAUKARWA, " ZAZZAFAR SOYAYYA ME TSAYAWA A RUHI. WRITING BY MARYAM STAR YAR BAIWAR JJRT. MARUBUCIYAR RAYUWAR SAMHAD DAFIN MACIJI A DAREN AURENA AND NOW ZAFIN WUTA PAID BOOK SEASON ONE Chapter 1-5 ميحرلا نمحرلا الله مسب. LEGOS NIGERIA UNGUWAR AGEGE "Wani ƙwararaɓaɓɓen gida ne ginin ƙasa wanda ko arzikin shahen siminti bai samu ba, gida ne ƙarami sosai kuma marar tsayo dan dama waje za'a iya hango kaiwa da komowar mutanen gidan." Da gudu na fito daga cikin kurkukun gidanmu wa ni dattijo biye da ni hannunshi riƙe da zabgegiya bulala irinta "dukan dawakai, gudu ni ke iyakar ƙarfina tare da ihun neman agaji dan saura ƙiris Dattijon ya kama ni damma ina zillewa." "Shawo kwana yai hannu shi riƙe da jakar bakko, lokacin da ni ke ƙoƙarin bige shi insha kwanar nima, caraf na ji anriƙe hannuna da mugun ƙarfi, wa ta iriyar ƙara na saki tare da gantsarewa jin saukar duka a jikina, kafin in aje numfashi na sake jin saukar wa ta bulalar a bayana aiko na sake gantsarewa tare da kai gwuiwoyina ƙasa saboda yanda zafin bulalar ya ratsani, rufe ni yai da duka babu ƙaƙƙautawa yayinda har lokacin ba'asakarmin hannuna ba, birgima ni ke a ƙasa ina bayarda haƙuri tare da neman agajin jama'a amma babu wanda ya kula ta kaina." Sai da wannan dattijon yai min lis yanda ko hannuna ba na iya ɗagawa saboda tsabar yanda na daku sannan ya rabu "da ni, wannan matashin kuma wanda ya riƙe hannuna bai sake ni ba har aka gama dukana, bayan dattijon ya juya ya na sababi kamar ze haɗe harshenshi saboda masifa ya koma ya shige cikin gida ba tare da ya kula da ko hijabi" "babu a jikina ba, daga ni sai doguwar riga irinta shan iska wacce duk ta jeme ta ji jiki, kaina ko atziƙin ɗan kwali babu" "sai baƙin sisilkan gashina da ya sauka har tsakiyar bayana, sanadiyar burkiɗa da nai duk ƙasa ta cika min gashi da jiki. Cike da raɗaɗin zuciya na tashi ina karkaɗe jikina har lokacin ban daina kuka ba kuma hannuna na riƙe da na wannan matashin." "Baice da ni komi ba ya ja hannuna ina turjewa amma bai tsaya ba sai da ya sada ni da cikin gidanmu, a gaban" wannan dattijon wanda ya yi min duka ya sake ni tare da komawa gefe inda wa ta farar matashiyar ma ta ke zaune ta yi tagumi hannu biyu. """Mama barka da wuni, munsame ku lafiya.""" Matashin ya katse ta daga tunanin da ta ke. """Lafiya lau Hashim fatan ka dawo lafiya ya hanya ?""." """lafiya lau Alhamdulillah, ga wannan.""" Yai maganar ya na miƙo ma ta bakkon hannunshi. Cikin sassauta fuska ta amshi ledar tare binshi da addu'a. Amsawa yai tare da tashi ya koma wajen wannan dattijon shima ya gaida shi tare da zaro kuɗaɗe daga cikin aljihunshi ya ba shi tare da faɗin. """Abba ga wannan babu yawa anyi cefane, kuma idan andawo daga sallah idan baku komi ina son muɗan tattauna.""" """Ah bakomi Hashimu yaron albarka, ina gaya maka kaf gidannan babu me hankalinka ubangiji Allah ya biyaka da" "gidan aljanna.""" Ya faɗa tare da zuran kuɗin a aljihun rigarshi. Kallo Hashim yai tare da faɗin. """Mubeenah ki tashi ki yi alwala lokacin sallah ya gabato.""" Cikeda masifa Abba yai caram ya ce. """Yauwa Hashimu gara da Allah ya kawoka a daidai wannan lokacin, wallahi na gaji da halin wannan yarinyar, na gaji" "da nunamin ita yanzu ta kangare ta balage, kullum cikin janyomin hasifa da tashin hankali ta ke, ace yarinya rai ɗaya amma ta addabi rayuwata ta hana ni sakat, banda damar gindaya doka a gidana sai wannan masifatattar ta nuna ban isa da ita ba, to na gaji wallahi ta kaini ƙarshe na ƙure da bango, kodai ta nemi aiki inda za ta dinga ciyar da kanta ko kuma ta fito da mijin aure in aurar da ita in huta, Allah yana gani na gaji da riƙon wannan yarinyar.""" "Ƙaƙƙarfar ajiyar zuciya Hashim ya sauke, a cikin zuciyarshi ya na karanto A'uziyya jin irin kalaman da Abba ya ke jifar" ƴar cikinashi kamar ba shi ya tsugunna ya kawo ta duniyar ba. Fice wa sukai daga gidan zuwa masallacin da ke cikin kayi don gabatar da Sallar La'asar. Mama ce ta tashi daga inda ta ke zaune ta nufi Mubeenah ta ɗago ta tare da kama hannunta suka shiga cikin wani "ɗaki me ƴar ƙaramar ƙofa, akan wa ta jemammiyar katifa ta zaunar da ita, itama ta zauna tare da kama hannun Mubeena cikin na ta, cikin nuna damuwa ta ce." """Mubeenah! tabbas Abbanku baya kyauta, sam abubuwanda ya ke miki ba su dace ba, musamman zafafan kalaman" "da ya ke yawan jifanki da su masu kama da ZAFIN WUTA saboda muninsu, bazan ja da baya ba wajen sake jadadda" "ma ki cewa ki ƙara haƙuri akan wanda kike yi a yanzu, komi zai wuce kamar ba'aiba wuya ko ƙunci basa taɓa" "dawwama, bayan wuya sai daɗi, kicigaba da haƙuri da ƙaddararki, jarabawace Allah ya ke jarabtar ki da ita, idan kika jure nan gaba zakiyi alfahari da hakan, tabbas Ubangiji ya na son ki tunda har ya jarabce ki da rayuwa me cike da tarin ƙalubale gami da tukitattun al'amurra, ki ci gaba da yin addu'a akan Allah ya zaɓa ma ki abin da ya ke alkairi a gare ki, da yardar Allah kina tare da nasara.""" "Zafaffan hawaye ne suke ambaliya akan fuskata, yayinda nike tunanin shi har tsawon wane lokaci zan ɗauka ina" "fuskantar ƙalubalen rayuwa, har zuwa yaushe Allah zai dube ni ya sauƙaƙamin lamurrana kamar sauran mutane, ina so inyi farin ciki kamar kowa, ina so inzama kamar sauran mata sa'annina waɗanɗa ke rayuwa cike da farin ciki." "Shafa bayana Mama ta ke alamar rarrashi, a zuciyarta ta na matuƙar tausayamin da irin rayuwar da na tsinci kaina." Mun ɗauki lokaci a hakan gani da Mama tai lokacin Sallah na ƙurewa ya saka ta lallaɓa ni muka fice a tare dan "gabatar da Sallah akan lokaci, da kanta ta zubamin ruwa a ƙaramar butar da ita kaɗai ta rage mana a gidan, kamar talauci a kanmu ya ƙare, kullum ina Allah wadai da irin hallayar Abba ta mamaƙo da bin diddigi, Abba ya kasance cikin irin mutanenan masu hannun ƴan dambe, ga son banza muddin zai ƙyalla ido ya hangi mutum da ɗan maiƙo ba shakka sai yasan yanda yai wajen haɗa alaƙa da shi ta yanda zai yagi rabonsa." "Shiga banɗakinmu wanda ya kasance ɗan ƙuƙut, sam baya da faɗi sai tsawo shima ba canba, raɓewa naj gefe na" "malala ruwa a ƙasa sannan na biya buƙatata na fito, alwala na gabatar cikin nutsuwa tare da godewa Allah da ya yo ni cikin hasken musulunci, yanda ruwan alwata ke bin muguji ya na gudana haka damuwar da ta cunkushemin zuciya ke kwaranyewa saboda ƙarfafa iymani na da nai a lokacin da nike alwala dan ganawa da mahaliccina." ZAFIN WUTA LITTAFIN KUƊI NE AKAN NAIRA 500 KACAL. TA KU HAR KULLUM MARYAM STAR. 𝐙𝐀𝐅𝐈𝐍 𝐖𝐔𝐓𝐀 LABARI ME CIKE DA "BAN TAUSAYI, " "MATSANANCIYAR DAMUWA, " "KUNCIN CUZIYA, " "SADAUKARWA, " ZAZZAFAR SOYAYYA ME TSAYAWA A RUHI. WRITING BY MARYAM STAR YAR BAIWAR JJRT. MARUBUCIYAR RAYUWAR SAMHAD DAFIN MACIJI A DAREN AURENA AND NOW ZAFIN WUTA PAID BOOK Season two Chapter 5-10 "Bayan na kammala alwalar na yi addu'a kamar yanda manzo ya koyar, sannan na tashi na zubawa Mama ruwa na kai ma ta butar bakin ƙofar bayan gida na juya na wuce ɗan tsukakken ɗakina me kama da gidan Tantabaru, yamusashe abin Sallah na shimfiɗa sannan na janyo daguwar linkakkiyar hijabina wacce ta ke a tsarkake fes sai zuba ƙamshin turare ɗan ɗure ta ke, zura hijabin nai tare da kabbara Sallah na fuskanci Mahaliccina cike da ƙanƙan da kai, wani irin rauni ne ya ziyarce ni lokacinda gaɓoɓin jikina suka taimaka mani wajen yin Sujjada ina ganawa da Ubangijina, addu'a nike jerowa cike da fata da yaƙinin Allah zai kalle ni ya amsamin roƙona." "Bayan na sallame Sallar nai tazbihi gami da azkar wanda Manzonmu ya koyar, na jingina da bangon ɗakin ina" "tunanon irin ƙalubalen da ke baibaye da rayuwata tun tasowata har zuwa yanzu, ko a labaran hausa da nike bibiya ban taɓa cin karo da makamanci labari wanda yai shige da nawu ba, kullum cikin fuskantar sabon babin ƙalubale da littafin ƙaddarata ke buɗe min nike, sam bansan farin ciki ba a rayuwata, abu ɗaya na sa ni shine, tarin ƙalubale da wahalhalun rayuwa." "Ina a zaune ina tunanin yanda rayuwa ke gara ni kamar kwallon ƙafa na jiyo maganar Abba tun daga waje, Abba irin" "mutanen nan ne masu hayaniya waɗanda ba'a sirri da su, idan ya na magana muryarshi na fitowa da ƙarfi sosai, tumbama ace faɗa ya ke wayyo Allah wallahi inada tabbacin har masu wucewa a bakin hanya su na jiyo amon sautinshi, kafin in ankare na ji Sallamarsu a cikin gida shi da Hashim, runtse idanuwana na yi da ƙarfi jikina yahau tsuma kamar yanda nike tsintar kaina aduk lokacinda Abba zai shigo gida, ina jingina shigowarshi da tashin hankalina saboda da zarar ya sako ƙafarshi ya ke fara ƙirƙirar abin da zai saka ya kira ni ya yi min faɗa wa ta ranama harda duka." "Zagi, gori, cin mutunci sune abubuwanda ke maimaita kansu a bakin Abba akaina, nakan cintsi kaina a cikin wasiwasi lokuta dadama idan nai Abba ya jefe ni da mummunar kalma, zuciyata na raya ma ni cewa ba shine wanda yai silar zuwana duniya ba, musamman idan na natsu ina tunani akan yanda ya ke ina nakasa ina naka aje da Sumayya da Habiba, Sumayya da Habiba yayena amma ba uwarmu ɗaya ba, Sumayya Mamace wacce ta haifeta ita kuma Habiba ɗiyar Umma ce abokiyar zaman Mama wacce ayanzu ta tafi da Habiba da Sumayya ganin gida acan Katsina." """Mubeena! Mubeenah!! ke Mubeena wannan wane irin iskanci da raini ne ace kina ji na sai faman kwaɗa kira nike amma kiyimin banza saboda ke ba yarinyar arziƙi ba ce, idan kika bari daƙiƙa biyu ta shuɗe ba tare da kin fito ba" "Wallahil'azim na iske ki a ɗakinan sai jikinki ya gaya ma ki.""" "Tsulum na fito kamar wacce aka hankaɗo na isa gabanshi tare da duƙawa na ce ""Dan Allah ka yi haƙuri Abba wallahi Sallah na idasa, kafin in kwashe abin Sallar ne ka kira ni.""" """Mtswwwww aikin banza da wofi, da anyi magana ki kama sunne kai ke ala dole ta Allah, ki buɗe kunenki da kyau ki ji abin da zan gaya ma ki, Allah ya so ki yayanku ya ceceki daga hukuncin da na zartar a kanki, ya tsaya tsayin daka ya" "nemo ma ki aiki a gidan wasu manyan mutane shahararrun attajirai waɗanda kowa ya san da zamansu a Legos ke harma da sauran ƙasashe da garuruwa, idan kika natsu kika yi aiki me kyau to ba shakka mun warke daga wannan addababen talaucin, idan kuma bakiyi abin da ya dace ba har suka gaji suka koroki kamar yanda akai ma ki a gidan Alhaji Ɗan Gaske to babu makawa zaɓi biyu ne ya rage ma ki, kodai ki auri Samual abokina ko kuma ki fita salin alin kibarmin gidana dan bazan iya ci gaba da riƙe ki ba tunda na lura ke me farar ƙafa ce, daga lokacinda Allah ya haɗa ni da ke na fara fuskantar matsaloli a cikin rayuwata.""" "Ɗif na ji jina ya ɗauke na tsawon lokaci, kwanyata ta shiga maimaita min maganganun Abba da ya ce ni me farar" "ƙafa ce, daga lokacinda Allah ya haɗa shi da ni ya ke fuskantar matsaloli." """Innalillahi wa'inna ilaihi raju'un, Hasbunallahu wa ni'imalwalkil, Allahumma ajirni fi musubati, Abba maimaita min" "maganarka dan Allah ko zan daina kokonto akan abin da zuciyata ke raya min, Abba da gaske ne abin da kake faɗi Allah haɗaka da ni yai, kenan ba kaine ka haifeni ba ko, dan girman zatin Allah ka amsa min.""" "Tsit Abba yai ya na jin babu daɗi akan yanda na fassara maganarsa, harga Allah ba haka ya ke nufi ba, bai zata" "hankalina zai kai ga waɗannan kalaman da suka suɓuce ma shi ba, kafin yasan abin yi muka jiyo muryar Umma da ta shigo yanzu ita da su Habiba ta na faɗin." """Yo Allah na tuba Mubeena miye banbancinki da tsintacciya, ai wallahi baki da maraba da waɗanda ake kaiwa gidan" "marayu waɗanda ake yasarwa a kan kwalta, akaɗa a raya Abban dai shine ubanki wanda za ki yi taƙama da alfahari da shi, domin kuwa ya yi ma ki sutura tunda ya kasance uba agare ki.""" Saurin katse zancen Mama ta yi gudun abin da kan iya zuwa ya dawo idan aka tsawaita zancen. """A,ah Umman yarah kece tafe da la'asar sakaliya, lalle marhaban da isowa, Biba Sumayya ku shigo daga ciki manah kun toge a bakin ƙofa kamar wasu baƙi.""" Taɓe wawakeken bakinta Umma tai tare da jifar Mama da wani banzan kallo sannan ta cire yalolon mayafin cikinta ta sagaleshi a igiyar shanya sannan ta turo ɗan kwalinta gaba ta na faɗin. """Wallahi ko Zainabu kinganni nan yanzu nai ra'ayin isowa, kuma babu wanda ya isa ya mayar da ni, ya muka same ku?.""" Cikin rashin jin daɗin yanda Umma ke gwasaleta idan tai ma ta magana ta ce. """Muna lafiya lau Alhamdulillahi.""" """A,ah kaga uwar gida me Capacity, Hajiya Halima ikon Allah, anbuga da ke ambarki maƙiyanki fadawanki, ke ce ɗaya rak amintaciyya a zuciyar Ibrahima, yo in banda ƙaddara da jaraba irin tawa mi na gano a wajen sauran mata da na" "nace akansu harda fa ƙaro ma ki kishiya, oh ni Iroro jikan Me ƙosai, In sha Allah daga Zainabu na kulle bazan sake yo maki kishiyaba da yardar Allah.""" "Abba yai maganar ya na zuro kanshi ya na leƙa cikin jakar Umma wacce ya ke hango walƙiyar ƴan dubu-dubu sababbi dal, kamar wuyanshi zai ɓalle saboda leƙe." Ita kuwa Umma sai wani fari ta ke da idanuwa tare da ƙara buɗe bakin jakar dan Abba ya samu damar ganin kuɗin da kyau. Cikin rashin jin daɗin abin da Umma ta yi wa Mama ta tashi tare da jan hannun Mubeena da ke duƙe cikin mawuyacin hali ta nufi ɗakinta da ita. "Habiba da Sumayya ne suka shigo su na yatsine fuska a fizge suka gaisarda Abba, cike da fara'a ya amsa ya na musu" sannu da hanya. """Mama bazan iya ci gaba da jurar waɗanan munanan kalaman daga bakin Abba ba, Mama ki tausayawa halinda nike" "ciki ki faɗamin wacece ni? shin dagaske Abba shine wanda ya haifeni, ko kuma ni ɗin ba ƴarsa ba ce, miyyasa ya ke banbanta ni da Yaya Babiba da Yaya Sumayya?.""" "Nai maganar ina me tsareta da rinannun idanuwa waɗanda launonsu ya koma jah saboda kuka, ji nike gaba ɗaya" "rayuwar ta ficemin, duniyar tai min zafi, banajin daɗin komi, ga zafin zuciya ga zafin dukanda Abba ya yi min." PAID BOOK NE AKAN 500 ONLY TA KU HAR KULLUM MARYAM STAR ƳAR BAIWAR JAJIRTATTU WRITERS 𝐙𝐀𝐅𝐈𝐍 𝐖𝐔𝐓𝐀 LABARI ME CIKE DA "BAN TAUSAYI, " "MATSANANCIYAR DAMUWA, KUNCIN CUZIYA, " "SADAUKARWA, " ZAZZAFAR SOYAYYA ME TSAYAWA A RUHI. WRITING BY MARYAM STAR YAR BAIWAR JJRT. MARUBUCIYAR RAYUWAR SAMHAD DAFIN MACIJI A DAREN AURENA AND NOW ZAFIN WUTA *https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341 &mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION* *(J.W.A)* "_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_. " """Jajirtattu mu ne ƙarfi a zuciya, hikima a magana, jajircewa a aiki. Ba mu ja da baya, ba mu faɗuwa. Mu ne tarihi" "da ake ginawa!"" " THE NOBLE WRITER'S TEAM ( DEDICATION IS OUR STRONG ) Typing... PAID BOOK 500 ONLY Season two Chapter 10-15 "Gudu ya ke shararawa a cikin dajin da babu komi sai kukan tsuntsaye da halittu masu firgitarwa, bai tsaya a ko ina ba" "sai nesa kaɗan da wajen wani kogon dutse, kashe motar yai tare da fito a firgice ya tsaya daidai wani waje inda aka aje wasu tsofaffin ƙorai, cikin rawar jiki ya cire kayan jikinshi tas yai tsirara haihuwar uwarshi sannan ya jefarda kayan a saman ƙoran ya rufe idanuwanshi tare da juyawa ya na karanto wasu damatsilan tsafi ya isa gaban kogon, a zahiri kogon baida wa ta ƙofa sai wa ta ƴar huda ƴar ƙarama wacce wani bakin hayaƙi ke fitowa, ci gaba da karanto damatsalan yai har wannan baƙin hayaƙin ya baibaiye inda ya ke tsaye, ɓat ya bace daga wajen bai samu kanshi ba sai a gaban wani shirgegen baƙin mutum me tsananin muni wanda ya ke tsirara haihuwar uwarshi babu ko ƙyalle a jikinshi sai wani jan abu da ya naɗe al'aurarshi da ita, a hankali matashin ya fara ruɗe idanuwanshi bayan jin saukar" "wani ruwa me yauƙi akan jikinsa, buɗe idonshi yai tare da yunƙurawa cikin zafin nama yai Sujjada tare da kirari ga" wannan ƙaton zindiƙin bokan. "Wa ta arniyar dariyace ta cika kogon wanda ke zagaye da abubuwan ban tsoro iri daban-daban, bayan ɗaukewar" sautin dariyar matashin ya ɗago tare da sharce guminda ke tsatstsafo ma shi sannan ya maida hankalinshi akan bokan. """Kamar dai yanda aka saba sadaukarwar wannan karonma tayi kyau, Zuka ya ji daɗin jininda aka bashi yanzu a shirye" "ya ke dan ganin ya biya maka dukkanin buƙatunka.""" Boka yai maganar bakinshi na amayarda tururin baƙin hayaki harda tartsatsin wuta a lokacinda ya ke magana. """Ina godiya Boka uban bokaye, hatsabibi uban hatsabibai, Mutum uban Aljannu, zaka dawwama kana juya duniya" "da mutanen da ke cikinta ta ƙarfin ikon ka.""" Wani mumunan murmushi Bokan ya saki wanda ya sake bayyana munin halittar fuskarshi wacce sam babu kyan gani. """Kana tare da sa'a da nasara saboda biyayyarka agaremu, tabbas akwai shahara a tare da kai burukanka da yawa" "zasu cika saboda ƙarfin iymanin da ka yi da mu.""" "Nan matashi ya zube tare da kwararo godiya sannan ya shiga lissafo abubuwanda ya kawoshi, bayan ya gama" "jawabinshi Bokan ya ɗaga hannunshi sama tare da karanto wasu kalmomi, nan take hanun ya shiga buɗewa har wani dunƙulallen abu ya bayyana, ɗayan hanun nashi me kama da icce ya ɗaga tare da shafa abinda ya bayyana, nan take ya shiga warwarewa yana buɗewa gamida bada tsawo da faɗi, wani madubine ya bayyana." "Mutum ne a kwance kamar gawa, babu abin da ke motsi a jikinshi, babu ko tufafin kirki a jikinshi sai wani farin gyalle" "da aka lulluɓe iya al'aurarshi, jikinshi kamar babu tsoka saboda tsabar yanda ƙasusuwa suka firfito miraran, fatar jikinshima duk ta taƙune ta yamushe kamar tsoho, wani abin mamaki kuma gashin kanshi na nan kwance luf kamar baƙi ƙirin kamar na larabawa ko indiyawa, wani tururin hayaƙi ne ke fitowa daga ƙofofin gargasar da ke jikinshi." Wata iriyar dariyace matashin ya kece da ita tare da faɗin. """Fauzan Shareef Abdallah kaga abin da taurin kai da binciken ƙwaƙwaf ya janyo maka ko, ka ga abin da nike mama gargaɗi akashi ko, indai ZAFIN WUTAR tsafi ne yanzu aka fara, sai na ƙone gangar jiki da ruhinka da ZAFIN WUTA wannan itace makomar da ka zaɓawa kanka, duk wannan iko da dukiyar da kake taƙama da ita sai na yi sanadiyyar ƙarewarsu, sai rayuwarka ta ɗaiɗaice ta wulaƙanta, sai na maidaka abin tausayi a cikin mutane, dole ne in nuna maka nafika tantiranci da hatsabibanci.""" Cike da mugunta ya kalli Bokan bayan ya gama magana a fusace ya ce. """Ya shugabana Boka uban Bokaye ina so ayiwa Aljani Zuka albishirin jinin jinjirin da ƙanwata zata haifa, ina so ya" "sake ninka azabar da yakewa wannan kafaffen Fauzan ɗin azaba me tsanani ta yanda hatta makusantanshi zasu ji tsoron kusantarshi, so nike asa wuta ta dinga ƙona gangar jiki da ruhinshi, ina so hannu ya gagara taɓa jikinshi, ina nufin a ƙone duk wanda zai taɓa shi, sannan ina so a hana gangar jikinshi saurin ƙonewa saboda banso ya mutu da wuri, ina so ya ɗanɗani uƙuba da azaba me raɗaɗi.""" "Dariya Boka ya kece da ita tare da dunƙule madubin sannan ya shafa, nan take ya ɓace hannunshi ya dawo daidai, har zuwa lokacin be daina mumunar dariyarba wacce ke kama da saukar aradu saboda tsananin munin muryarsa." TAKU HAR KULLUM MARYAM STAR Follow the 𝑀𝐴𝑅𝑌𝐴𝑀 𝑆𝑇𝐴𝑅 𝑌𝐴𝑅 𝐵𝐴𝐼𝑊𝐴𝑅 𝐽𝐴𝐽𝐼𝑅𝑇𝐴𝑇𝑇𝑈 𝐻𝐴𝑈𝑆𝐴 𝑁𝑂𝑉𝐸𝐿𝑆 𝐶𝐻𝐴𝑁𝑁𝐸𝐿 channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029Vb5xdoy2975BcTM5m133 I'm on Instagram as @maryamumarkt553. Get the app and follow me https://www.instagram.com/maryamumarkt553 https://ngl.link/maryamstar https://www.wattpad.com/user/maryamumarstar?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=invite friends 𝐙𝐀𝐅𝐈𝐍 𝐖𝐔𝐓𝐀 LABARI ME CIKE DA "BAN TAUSAYI, " "MATSANANCIYAR DAMUWA, KUNCIN CUZIYA, " "SADAUKARWA, " ZAZZAFAR SOYAYYA ME TSAYAWA A RUHI. WRITING BY MARYAM STAR YAR BAIWAR JJRT. MARUBUCIYAR RAYUWAR SAMHAD DAFIN MACIJI A DAREN AURENA AND NOW ZAFIN WUTA *https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341 &mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION* *(J.W.A)* "_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_. " """Jajirtattu mu ne ƙarfi a zuciya, hikima a magana, jajircewa a aiki. Ba mu ja da baya, ba mu faɗuwa. Mu ne tarihi" "da ake ginawa!"" " THE NOBLE WRITER'S TEAM ( DEDICATION IS OUR STRONG ) Typing... PAID BOOK 500 ONLY SEASON TWO CHAPTER 15-20 "Wata jaka ce ta faɗo daga sama ji kake timmm, ɗaukarta boka yai tare da faɗin." """Angaishe da hatsabibi uban hatsabiban aljannu, aikinka ya na kyau.""" "Jakarce ta shiga buɗe kanta, wani farin abu ya bayyana acikin wata ƴar farar roba, fito da abin Boka yai tare da" miƙawa matashin haɗi da yi ma shi bayani akan yanda zai yi amfani da maganin. "Bayan ya amsa yai godiya gamida kirari sannan ya rumtse idonshi, nan take ya ɓace ɓat bai ɓulla ko ina ba sai gaban wannan dutsen da ƙorai ke ajiye, kayanshi ya mayar tare da hanzartawa ya nufi wajen da ya aje motarshi ya shiga ya" jata da mugun gudu dan duhun dare ya fara. BANANA ISLAND "Tamfatsetsen gida ne wanda ya lashe million kuɗaɗe wajen ginashi, tun daga nesa zaka tabbatar da lallai ko waye ya mallaki wannan gjdan tabbas ba ƙaramin me dukiya ba ne." "Wa ta hamshaƙiyar mata ce me tsananin wayewa da gayu ta fito daga wani ɗaki fuskarta da alamar damuwa, yayinda wa ta matashiyar budurwa ke biye da ita a baya ta na zubda hawaye." "Wani haɗaɗɗen ɗaki suka shiga basu tsaya ko ina ba sai gaban gadon da wani marar lafiya ke kwance yana amai, wa ta iriyar ƙara wannan matar ta saki tare da yin baya tai taga-taga kamar za ta faɗi tsabar firgicewa, cike da tashin" hankali ta ke faɗin. """Sulaima kina ganin abin da ni ke gani kuwa, wuta! wuta ce nike gani na fitowa daga bakin Fauzan, please ki ce min" "ba gaskiya bane mafarki ne, tayaya hakan zai faru, ki gaya min tayaya mutum zai dinga amayo wuta daga cikin jikinshi.""" "A firgice ta ke maganar hankalinta idan ya yi dubu y tashi, yayinda hawaye ke zaryar saukowa daga idanuwanta su na" zuba akan kyakkyawar fuskarta. """Mommy! wallahi dagaske ne, dagaske Yah Fauzan ne kike gani a cikin mawuyacin hali, shikenan nasan zamu rasa" "Yah Fauzan, nasan ba lallai ya tashi ba, wayyo Allah ka kawo manah ɗauki, ya Allah ya tashi kafaɗar wannan bawan naka me tsananin biyayya ga umurninka, Ya Allah ka bawa wannan bawan naka lafiya domin ya tashi yaci gaba da bauta maka kamar yanda ya ke yi lokacinda ya ke da lafita, Ya Allah ka yanke ma shi wannan wahalar hakanan."" Kukane ya ci ƙarfinta har jikinta na jijjiga saboda tsabar yanda ta ke kuka." "Cike da juriya, tausayi gami da zazzafar soyayya irinta uwa da ɗa matarda aka kira da Mommy ta taka zuwa inda" "wannan mutumin ke kwance ya na maida lumfashi, yayinda tururin wuta ke fita daga bakinshi da hanci, zama tai a ƙasan gadon glass ɗin da yake a kwance bai ko iya motsi ta na zubarda hawaye, yayinda ta ɗaga hannunta zata ɗaura akanshi wani irin ZAFIN WUTA ya bugo ma ta, da mugun sauri ta janye hannunta tare da sulalewa a ƙasan wajen ta na sakin kuka me ƙarfi , irin wanda ya ke fitowa daga can ƙasan rai, kuka ta ke ta na surutai wanda babu me iya jin abin da ta ke faɗi." "A hankali marar lafiyar ya shiga buɗe idanuwanshi tare da ƙoƙarin juyasu zuwa inda matar ke nuƙe tana kuka, wani" "irin ja da baya Sulaima ta yi tare da fasa ƙara me tsananin ƙarfi ta na nuna marar lafiyar, ɗagowa Mommy tai daga duƙen da ta ke, aiko ta ci karo da abin da ya kusa tsaida bugun lumfashinta." """Yah Fauzan dan Allah ka rufe idanuwanka banason gani, please bana son gani tsoro ka ke bani.""" Sulaima ta yi maganar ta na saka hannayenta ta dafe idanuwanta da ƙarfi. "A hankali wanda ta kira da Fauzan ya fara karkata kanshi zuwa ɗayan sashen, abin mamaki duk sanda wuyanshi ya" "motsa da niyyar juyawa sai wajen ya saluɓe ya ƙone, a maimakon jini ko ruwa ya fito sai hayaƙi ya dinga fitowa daganan kuma sai wuta ta kama kamar wacce aka zubawa fetur ko kalanzir." "Mommy da ke kallon abi da ke faruwa ɗif kukanta ya ɗauke wani irin tsoro, fargaba da tashin hankali ne suka" "bayyana a fuskarta, yawun bakinta ya ƙafe laɓɓanta suka bushe sai ƙoƙarin buɗe baki ta ke dan tai magana amma ta kasa, ko motsi kasawa tai sai idanuwanta da ke sake firfitowa waje." Duk irin azabar da ya ke ji baj daina motsa jikinshi ba sai da ya juyar da kanshi saitin glashin da aka kewaye ɗakin "da shi, ƙur ya ƙurawa ƙwarangwal ɗin fuskarshi ido ya na jinjina girman ikon Allah, yayinda tsoro ya kamashi ganin yanda idanuwanshi da ya sa ni a farare suka juye zuwa launin jah, ga wani tururi da ke fitowa daga cikinsu, duk da ya na jin azaba a duk lokacin da yai ƙoƙarin yin magana amma haka ya daure cikin ƙarfi hali ya ke faɗi a fili." """Inalillahi wa'inna'ilaihi raju'un ya Allah ka ɗauki rayuwata dan sauƙaƙawa mahaifiyata wahalar da ta ke da ni, yah Allah ka yankewa jajirtacciyar uwa hawalar jinyar yaron da ka jarabceshi da cuta, Allah ka ga zuciya ban butulce maka ba akan jarabawar da ta same ni ba, na roƙeƙa ne dan tsananin tausayin mahaifiya me rauni akan ɗanta.""" "Maganace ta gagareshi domin kuwa tuni bakin na shi ya dare tare da saluɓewa, yayinda Sulaima da ke kaklonshi ta" cikin glass ke faɗin. """A,ah Yaya a,a please kadaina kana jiwa kanka ciwo, dan Allah ka daina magana yah Fauzan.""" Ta faɗi ta na kai gwuiwoyinta a ƙasa dan ƙafafuwanta sun gaza bata haɗin kan tsayuwa. Ganin halin da Mommy ke ciki na suman zaune ne ya sakata sake fashewa da wani matsanancin kukan tare da dafe saitin ƙirjinta jin lumfashinta na barazanar ɗaukewa. TAKU HAR KULLUM MARYAM STAR 𝑍𝐴𝐹𝐼𝑁 𝑊𝑈𝑇𝐴 Follow the 𝑀𝐴𝑅𝑌𝐴𝑀 𝑆𝑇𝐴𝑅 𝑌𝐴𝑅 𝐵𝐴𝐼𝑊𝐴𝑅 𝐽𝐴𝐽𝐼𝑅𝑇𝐴𝑇𝑇𝑈 𝐻𝐴𝑈𝑆𝐴 𝑁𝑂𝑉𝐸𝐿𝑆 𝐶𝐻𝐴𝑁𝑁𝐸𝐿 channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029Vb5xdoy2975BcTM5m133 𝐙𝐀𝐅𝐈𝐍 𝐖𝐔𝐓𝐀 LABARI ME CIKE DA "BAN TAUSAYI, " "MATSANANCIYAR DAMUWA, KUNCIN CUZIYA, " "SADAUKARWA, " ZAZZAFAR SOYAYYA ME TSAYAWA A RUHI. WRITING BY MARYAM STAR YAR BAIWAR JJRT. MARUBUCIYAR RAYUWAR SAMHAD DAFIN MACIJI A DAREN AURENA AND NOW ZAFIN WUTA *https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341 &mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION* *(J.W.A)* "_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_. " """Jajirtattu mu ne ƙarfi a zuciya, hikima a magana, jajircewa a aiki. Ba mu ja da baya, ba mu faɗuwa. Mu ne tarihi" "da ake ginawa!"" " THE NOBLE WRITER'S TEAM ( DEDICATION IS OUR STRONG ) Typing... PAID BOOK 500 ONLY SEASON TWO CHAPTER 20-25 Kuka Sulaima ke yi bakin rai bakin fama ta na jijjiga Mommy wacce hankalinta ya gushe daga gangar jikinta. Fauzan ma kukan ya ke amma na zuci dan duk ƙarfin halinshi yanzu baya iya yin kuka saboda tsoron yanda hawaye "ke zuba kan fuskarshi su na ƙona shi, jin shi ya ke bayada banbanci da gawa, azabar da yake ji kaɗai ta isheshi ya ji ya gaji da duniya da abin da ke cikinta." """Fatima! Fatima!! ke Fatima wai kina ina ne haka, wannan kukan daga ina nike jiyoshi ne wai, duk ambi an cika gida" "da iface-iface kamar gidan mutuw """ "Kasa ƙarashe maganar tai yayinda idanuwanta sukai tozali da Mommy a ƙame, Sulaima na kuka tare da jijjigata, a" ɗari da tamanin ta idasa shigowa ɗakin ta na sallati da salallami ganin halinda ta iske Mommy a ciki. """ Na shiga uku ni Salamatu, mi zan gani haka, mike damunta ta ƙafe haka bata ko matsi.""" Dattijuwar matarda zata kai kimanin shekaru sittin ta faɗa a cikin rikewa ganin halinda wacce ta kira da Fatima ta shiga. Kafin Sulaima ta samu damar cewa komi wani itin huci me tsananin zafi ya ɗumame ɗakin lokaci guda ga wani "hayaƙi baƙi ƙirin da ke tashi, cike da ɗimauta Dattijuwar ta ɗaga kanta tai duba idan Fauzan ya ke, wani gigitacen salati ta saki tare da kuka me ƙarfi cikin tashin hankalin ganin yanda Fauzan ke ƙoƙarin juyowa amma jikinshi yaƙi bashi haɗin kai, duk inda ga motsa sai wajen ya kwalje tare da feso wuta gami da baƙin hayaƙi, cike da rikicewa da ƙarfin hali irinna tsofaffi Dattijuwar ta rarrafa da ƙafafuwanta da suka gaza ɗaukarta zuwa gaban gaɗon glashin da Fauzan ke kwance." """Haba Fauzan miye hakan kake ƙoƙarin yi! mi yasa zakai hakan, shin baka tausayin halinda mahaifiyarka ke shiga" "idan ta ganka cikin wannan halin, mi yasa ba zaka yi haƙuri kaɗauki danganaba, ka duba kaga yanda jikinka ke kwaljewa idan ka motsa bayaga haka har wuta ke fesowa, bamusan mi kake ji ba a jikinka amma tabbas munsan kana cikin azaba me raɗaɗi wacce ka zaɓi mutuwa a kanta, ka yi hakuri ka jure ka dogara da Allah zai kawo maka ɗauki, ka ƙara haƙuri da juriya akan yanda mukasanka, tabbas kai ɗin me juriya ne tunda har ka iya shanye raɗaɗi da azabar da kake ciki na tsawon lokaci, in sha Allahu ina ji a jikina sauƙi ya zo, ina ji a jikina samun lafiyarka ya zo nan kusa-kusa, ka jure ka daina motsa jikinka ka ji bawan Allah, duk wanda ke da sa hannu a cikin wannan lalurar ta ka In sha Allahu, Allah bazai barshi ba, dole zai ɗanɗani azaba wacce ta linka wacce kake ciki a yanzu, ina maka fatan Allah ya azurtaka da lafiya dawwamanmiya wacce zaka amfanin masoya da maƙiyanka da ita.""" Da waɗanan kalaman tai masarar dakatar da Fauzan wanda ke ƙoƙarin juyawa ya ga halinda mahaifiyarshi ke ciki. "Da rarrafe Dattijuwar ta ƙarasa wajen Mommy, a hankali ta kwantar da ita ganin jikinta yai sanyi bata ko motsi, kallon Sulaima ta yi tare da faɗin, ""Kawomin ruwa me sanyi."" cikin hanzari ta tashi ta nufi ƙatuwar freezar wacce ke" kafe a cikin ɗakin ta ɗauko ruwan gora tare da miƙawa Datrijuwar har lokacin bata daina kuka ba. "Amsar ruwan ta yi tare da buɗewa ta zuba ahannunta ta dinga shafawa Mommy tare da tofa ma ta addu'a, sai da ta shafa ma ta sau uku a cikon na huɗunne Mommy ta ja ajiyar zuciya me ƙarfi sannan ta shiga buɗe idanhwanta da" suka kaɗa sukai jajur ta na kallon Sulaima data ranƙwafo ta na leƙa fuskarta lokaci ɗaya ta na dariya me haɗe da kuka. Murya ƙasa-ƙasa Mommy ke faɗin. """Sulaima! Fauzan ɗina mutuwa zai yi ko? zan rasashi ko? bazai tashi daga wannan cutar ba ko? Sulaima ina son Fauzan ɗina bana so in rasa ɗaya daga cikinku, bazan iya jure rashinku ba, ina matuƙar ƙaunarku, dan Allah ki yi min addu'a ko zan samu sassauci daga yanda ni ke ji, Sulaima zuciyata ta kusa bugawa, ina jin ciwo me tsananai.""" """Haba Fatima, kar ki zamo me butulci akan abin da Allah ya riga ya zartar da faruwarsa tun farkon asali, cuta ba" "mutuwa bace, In sha Allah Fauzan zai samu lafiya zai tsaya da ƙafafuwanshi kamar yanda ya ke a baya, ki ƙara haƙuri kuma kici gaba da yi ma shiƙ addu'a In sha Allah ƙarshen wahalarshi ya zo.""" "Dattijuwar tai magana ta na kallon Mommy cike da tausayawa, dama ita uwa babu wanda zai kai ta ƙaunar ɗanta, kuma aduk yanda ɗa ya ke fama da lalura zaka samu uwarshi na tare da shi kuma ta na son abinta a haka." Lallaɓa Mommy Dattijiwar ta yi da kalamai masu kwantar da hankali sannan suka kama ta ita da Sulaima suka fice da ita daga ɗaƙi. AGEGE "Zazzaune muku akan tabarma kowa na ci abinci cike da raha irin wacce ake yi a gidanmu, amma ni nayi shiru ina" "kallon gefe ɗaya ina tunani, Mamace ke ƙoƙarin yimin magana idan ta ji shirun yai yawa sai ta ce, ""Mubeenah tunanin mi kike yi haka, ki ci abincinki mana karya huce."" amsa ma ta nike da ""to"". amma badan inajin abinci zai samu muhallin zama a cikina ba, maganganun Abbane ke ta maimaita kansu a cikin zuciya da kwanyata, ga wani irin tashin hankali da ke sake baibayeni gami da tsoro me tsanani." FLASS BACK Bayan dawowar Umma da ƴan mintuna Abba ya bita ɗaki tare da fito da Yaya Habiba da Yaya Sumayya. """Umma wajenki na zo zamuyi magana.""" "Umma ta na wani yatsina gami da shan ƙamshi ta ce, ""Ina jinka amma da banda magana akan kuɗina, dan wallahi" "Allah sisi bazan baka ba wannan karon, sana'a zan nema nima intsaya da ƙafafuwa.""" """Kash ke wallahi kina da matsala, yo Allah na tuba ana gamanar miliyoyin tsabar kudaɗe ke kuma kina magana akan wash ƴan canji, ai ina me tabbatar ma ki nan gaba kaɗan zamu zama shahararun masu kuɗi, wallahi sai mun" "girgiza Agege ke Legos ɗinma gaba ɗaya zamu jijjiga cikin kwana biyu rak.""" """Na shiga ukuna!!! Abba sata ka kidnapping ka fara da kake faɗin wannan maganar?""." Umma tai magana ta na zaro ƙananun idanuwanta waje ta na jiran Abba ya bata amsa. """Daɗina da ke shashanci wallahi, ke kanki hakanan ya ke suluf babu komi cikinshi, in banda hauka da rashin tunani" "tayaya za ki yimin wannan maganar, to ki sa ni arziki kamar nayishi na gama ne, domin kuma kalma ɗaya ce rak ta rage infurta ta inzama cikakken me arziki.""" "Sake waro idanuwa Umma tai, fuskarta cike da tsoron kalama Abba." """kai ni fa ban gane ba, mi kake nufi da kalma ɗaya rak ta rage ka zama me arziki, ni fa ka kulle min kai tamau da kalamanka.""" """Yanzu dai ki nutsu ki ji abin da zan gaya ma ki, sannan sai mu nemi mafita, yaronan Hashimu ne ya zo min da wa ta" "magana, da farko nima na shiga yanayin ruɗu, saboda lamarin me girma ne, kuma abin ya bani tsoro, amma dana natsu nai duba da ido basira sai naga ai faɗuwace ta zo daidai da zama, yo ba dole ince haka ba Umma tun da abin da nike nema ne ya zo kuma sai abin yazo min da alkairi, dama ba komi bane, a can wannan unguwar ya shahararrun masu kuɗi inda shi Hashime ke aiki ne suke neman ƴar aiki wacce zatai jinyar wani toyayye, abin da zai baki mamaki shine wai duk ƴan aikin da ake ɗaukowa da sunje sai suce basu iyawa saboda yanda marar lafiyar ke jin jiki, babu irin ƙasashen ƙetare wanda basu je ba amma abin yaƙi ci yaƙi cinyewa, ance ana buƙayar wacce zatai jinyarshi za'a biyata da maƙudan miliyoyin kuɗin, da yake kinsan yaronan Hashimu ɗan arziƙi ne shine kai tsaye ya amsa ma su da cewar waccan shashashar zata iya, to shine fa suka turoshi dan ya zo ya sanar da mu, sunce daga miiyan ɗaya har zuwa miliyan biyar zasu iya biyanmu indai Mubeena za ta jure tai wannan jinyar.""" """Sai naci abu ta kazan ubanta wallahi mudin ta sake ta kawo mana wargi, yo Allah na tuba wannan ai ba maganar da" "za'a tsaya neman amincewarta bace, wallahi ko bata amince ba mu mun amince ma ta, babu gudu babu ja da baya."" Cewar Umma tare da tattare zanin jikinta ta fara taka rawa ta na sakin buɗa me babu ko kunya." """Dammm"" gabana ya doka da tsananin ƙ arfi, yayinda jikina yai sanyi ƙalau wani irin baƙon yanayi na ji ya na" "baibaye ni yayinda ƙarar sautin buɗar Umma ta daki dodon kunnena, ƙanƙame jikina nai tare da takurewa na sake lafewa saman gadon ƙarfen Mama." "Mama ce ta shigo tare da tada ni dan in fito tsakar gida insha iska saboda zafi, sai ta iskeni a wannan yanayin," "fuskarta da alamun ƴar damuwa ta kamo ni muka fito waje inda su Yaya Habiba ke zaune, ko kallo ban ishesu ba bare su nuna sun san da zamana, haka ko gaida umma basuyiba saima ƙara volume ɗin kallon da suke yi cikin faskekiyar tsadaddiyar wayar Yaya Sumayya, Mama ce ta dinga jana da fira har na ɗan saki jikina muka dinga fira cike da nishaɗi dan kuwa ina son irin labaran da Mama ke bani idan muka zauna zaman fira, Yaya Habibace ta kira ni." """Mubeena zo kiga wani abu nan yo sauri ki gani karya wuce.""" "Yanda tai maganar ne ya saka na kalli Mama ina jin daɗin yanda ƴan uwana suka kula ni, gyaɗa min kai tai alamar inje ingani, na muskuta zuwa inda suke na leƙo da kaina dan kallon abinda Yaya Habiba ke son nuna min, banyi kyakkyawan gani ba, dan kuwa Yaya Sumayya na saka play aka nuno wani waje shiru babu kowa sai wa ta kujera da" "ke lila kanta, sake ware manyan idamuwana nai dan in sake kallo da kyau, aiko na kallo abin da ya saka dukannin" "mutanen gida a tashin hankali, wani mummunan abu ne aka nuna ya taho da gudu kamar ze kamo ni, ban san lokacin da na saka ƙara me ƙarfi ba tare da miƙewa, sai nai tuntuɓe da ƙafar Yaya Habiba hakan ya bani damar faɗuwa ƙasa timm." "Sallati Mama ta saki tare da tashi ta ƙaraso inda nike kwance dan ta tada ni, kai hannunta jikina ko second ɗaya bata" "ƙara ba tai saurin janyewa ta na riƙe hannun wanda ke ƙyarma, idanuwa ta fiddo waje ta na kallona ta na kallon hanuna, yayin da Abba da Umma suka firfito dan sunji ihuna sannan kuma sunji salatin Mama." """Mi zan gani haka, wannan wace irin rayuwace, mi yasa ƴan gidannan kuke da baƙin ciki, yanzu mabuɗin arziƙin nawa ce kuke so ku kashe dan iyayenku.""" "Abba yai maganar tare da ƙarasawa inda Mama ke tsaye riƙe da hannunta, yayinda ni kuma nike yashe a ƙasa kamar" "gawa, duƙawa yai da niyyar taso da ni ya na sababi, amma abin mamaki sai hannunshi na sauka jikina kawai akaga anɗaga Abba sama, ba,a saukeshi a ko ina ba sai a jikin dangar ɗakin umma, cike da razana kowa ya shiga ja da baya- baya ganin lokaci daya na tashi tsaye ƙam, gashin cikina ya mimmiƙe, launin idona ya bace ɓat sai kalar shuɗiya me haske da ta bayyana, kafin suyi wani yunƙuri Mama na zube a ƙasa ta durkushe tare da faɗi cikin wa ta iriyar murya." """Takawarki lafiya sarauniya Zubudiyya ƴar sarki jikar sarki, haƙiƙa kogin Sumalai na ki ne, babu me iko da shi," "takawarki lafiya sarauniyar sanyi da ƙanƙara, ƙasƙantaccen bawa na miƙo gaisuwa a gare ki."" sai Mama ta duƙar da kai a ƙasa kamar ta na gaban sarki, daga haka bata sake magana ba kuma bata ɗago ba, wa ta irin razananniyar dariya na fara wacce tsananin iskar dariyar sai da shanyar da akai tsakar gidan ta dinga kaɗawa da ƙarfi, yayinda wani irin sanyi ya lulluɓe wajen irin me saka maƙyarƙata, abin da ya ƙara tsorata su Abba bai wuce yanda suka ga wasu irin ruwa masu haske da sheƙi na ɓullowa daga kasa ba a daidai saitin da nike a tsaye, sai da ruwan ya zo min har wajen ƙugu sannan ya tsaya da ɓulɓulowa, tafiya na fara yi a cikin ruwan ina shawagi cike da shauƙi, yayinda idanuwana suka shiga sauya launi a hankali, sai kuma ruwan ya fara ɓacewa amma har lokacin ban daina dariya ba amma kuma yanzu sautin yana raguwa a hankali kamar yanda ruwan ke ɓacewa." Ɓat sautin dariyar ya ɓace yayinda ruwan ya ƙafe sannan kuma a hankali yanayin ya dinga canzawa daga sanyi zuwa "yanayinda muke ciki, faɗuwa nai a ƙasa tim ban sake motsiba." "Mama ma ɓingirewa tai daga duƙiyar fadawan da tai, ta shiga sakin munsharin barci." "YANZU ZA'A SOMA CAKWAKIYA, KU KASACNCE TARE DA NI DOMIN JIN YANDA ZA TA KAYA A CIKIN WANNAN" LABARIN. "KARKU MANTA LITTAFINAN NA KUƊI NE, KUMA MUN KUSA KAMMALA FREE PAGES GA WACCE TA SHIRYA BIYA GA" ACCOUNT A ƘASA. 9136291920 MARYAM UMAR OPAY 500 ONLY 𝑣 NI CE TAKU MARYAM STAR YAR BAIWAR JAJIRTATTU WRITERS ZAFIN WUTA Follow the 𝑀𝐴𝑅𝑌𝐴𝑀 𝑆𝑇𝐴𝑅 𝑌𝐴𝑅 𝐵𝐴𝐼𝑊𝐴𝑅 𝐽𝐴𝐽𝐼𝑅𝑇𝐴𝑇𝑇𝑈 𝐻𝐴𝑈𝑆𝐴 𝑁𝑂𝑉𝐸𝐿𝑆 𝐶𝐻𝐴𝑁𝑁𝐸𝐿 channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029Vb5xdoy2975BcTM5m133 𝐙𝐀𝐅𝐈𝐍 𝐖𝐔𝐓𝐀 LABARI ME CIKE DA "BAN TAUSAYI, " "MATSANANCIYAR DAMUWA, KUNCIN CUZIYA, " "SADAUKARWA, " ZAZZAFAR SOYAYYA ME TSAYAWA A RUHI. WRITING BY MARYAM STAR YAR BAIWAR JJRT. MARUBUCIYAR RAYUWAR SAMHAD DAFIN MACIJI A DAREN AURENA AND NOW ZAFIN WUTA *https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341 &mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION* *(J.W.A)* "_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_. " """Jajirtattu mu ne ƙarfi a zuciya, hikima a magana, jajircewa a aiki. Ba mu ja da baya, ba mu faɗuwa. Mu ne tarihi" "da ake ginawa!"" " THE NOBLE WRITER'S TEAM ( DEDICATION IS OUR STRONG ) Typing... PAID BOOK 500 ONLY SEASON TWO CHAPTER 25-30. ميحرلا نمحرلا الله مسب. "Cike da tsoro Umma ta matso cikin sanɗa ta jijjiga Mama gami da kiran sunanta, amma Mama ba ta amsa ba kuma ba ta motsaba, shiko Abban tafe bango ya yi tare da silalewa ƙasa ya zauna ya na maida lumfashi gami da sharce" "gumi, Yaya Habiba ce ta nufi inda ya ke ta na ma shi sannu ganin yanda ya diririce duk ya tsure kamar wanda yai" jinya. "Da ƙyar Abba yai nasarar ƙwato kalmar ""Ruwa."" daga bakinshi, aiko da sauri Yaya Habiba ta ɗebo ma shi wanda ke" "cikin randa, tun da ya kafa kofin bai sauke ba sai da ya tabbatar da yanshe tas sannan ya aje tare da lumshe ido ya na sauraren yanda zuciyarshi ke bugawa da sauri-sauri." "Umma ta tsorata ainun da abin da ya faru hakan ya saka ta haɗa kawunan su Yaya Sumayya tai ɗaki da su," acewarta wai karasu kwashi jangwam. "Shima Abba lallaɓawa yai tare da rarrafawa ya shige ɗakin Umma harda kullo ƙofa, ni da Mama kuma aka barmu" anan kamar kayan banza. "A hankali na fara buɗe idanuwana da sukaimin nauyi, kaina ne ya sara da tsananin ƙarfi wanda hakan ya tilasta ni" "saurin rufe idanuwan nawa, ƙoƙarin tashi na fara yi zaune amma sai naji jikina kamar anyimin tsinannen duka, ko ina ciwo ya ke min, daurewa nai na tashi ina cije baki cike da dauriya dan sosai kaina ke barazanar tarwatsewa, a hankali na buɗe idanuwa da sukai min tsananin nauyi na sauke su akan Mama da ke kwance,mamaki ne ya kama ni ganinta a kwance ta n barci gashi magrib ta kawo kai, cike da jarumta na matsa kusa da ita na shiga tashinta ganin irin kwanciyar da tai, buɗe idanuwanta tai tare da ƙoƙarin tashi, na lura itama jikinta sam babu ƙarfi, bayan ta tashi zaune ne na shiga jera ma ta sannu." """Halan baki jin daɗi, naga kinyi barcin marice, sannu bari imfadawa Abba ya siyo ma ki magani."" Nai maganar ina" kallon yanda Mama ta dafe kanta. Cikin sanyi murya ta furta. """A,ah Mubeenah! lafiya lau kawai naɗanyi barci ne shine jikina yai sanyi, zan warware da zarar nai sallah.""" Sannu na sake yi mata gami da lallaɓawa na tashi tsaye na nufi wajen ruwa na ɗauki ƴar gudaliyar butar gidanmu na "cikata da ruwa na nufi kewaye dan in watsa ruwa saboda rashin daɗin da jikina ke min, raɓewa na yi ta samu na watsa ruwan sannan na fito na fara gabatarda alwala cikin nutsuwa, ina alfahari da yanda ni ke nutsuwa idan zan gana da mahaliccina, ni mutumce me tsananin son ibada da tsoron Allah, bana wasa wajen kiyaye haƙoƙin ubangijina, nakan yi iya bakin ƙoƙarina wajen kaucewa saɓo, da wannan nike kira ga ƴan uwana musulmai da muji tsoron Allah mu kyautata makomarmu, mu dinga kiyaye haƙoƙin Allah dan samun sakamako me kyau a lahirarmh, Allah ya datar da mu Ameen." "Bayan na kammala alwalar nai tasbihi kamar yanda mazonmu ya koyar, sannan na zubawa Mama ruwa a buta na" "shigar ma ta da ita sannan na dawo na shiga ɗakina wanda ko arziƙin fitila babu, gashi babu ko taga se wasu ƴan bulillika da aka jera a can sama, da lalube na ɗauki hijabi da abin Sallah ta, da yake na haddace inda komi ya ke a cikin ɗaki a haka nike gudanar da rayuwata ba tare da na takura ba." "A zaune na gabatar da Sallar saboda yanda kaina ke sarawa, bayan na gama ne na shiga yin azkar ɗin marice da" "bansamu damar yi ba, da yake na riga da na hardace shi tas a kaina, bayan na gama ne na jingina da jikin bango ina sauraren yanda bugun zuciyata ya sauya lokcinda na farka naga na yi barci wanda bansan lokacinda ya kwasheni ba, ina jin sauyi sosai a jikina wanda kafin in kwanta sam banji hakan ba, hakanan kawai na ji a jikina akwai abin da ya faru wanda ban sa ni ba, a gefe ɗaya kuma ina tunani akan abin da ya hana Umma da Abba fitowa yin alwala, ina jiyo tashin muryarsu a ɗakin Umma, hakanan kawai na ji ina so inje in taso su dan suyi sallah ƙila basusan an kira ba tun da ba wani ji ake sosaiba daga masallaci idan aka kira, ni da Mama mune masu ƙoƙarin yin sallah akan lokacinta." "Cikin amincewa da shawarar zuciyata na tashi ina dafe bango na nufi ɗakin Umma, ina tura ƙofar naci burki ganin Abba zaune akan taƙunanniyar dadumar Umma ya na sallah, gefe ɗaya kuma babbar robar Umma ce da buta a jiye" sai wasu ruwa a cikin robar masu datti da alama awala akai ciki. "Cikin shanye mamakina na yi sallama cikin sanyi murya, abin da ya ɗaure min kai be wuce yanda naga firgici da" razana ba kwance akan fuskar Yaya Habiba da Yaya Sumayya waɗanɗa suka salame Sallah. """Innalilahi wa'inna ilaihi raju'un!!! Mubeena lafiya kika zo kikai min tsaye a bakin ƙofa."" Umma ta faɗi da yanayin" tsoro. "Kallon tsaf nai ma ta, ina ganin yanda ta ke ƙoƙarin haɗiyar yawun da ya maƙale ma ta a maƙoshi, idanuwanta da" alamun tsoro ƙarara. Bangama ƙare ma ta kalloba na tsinayo muryar Abba shima a sanyaye ya na faɗin. """Mubeenah lafiya dai ko? ko wani abu kike buƙata."" yai maganar shina maƙogwaromshi na kai komo." """Dama naga baku fito yin sallah ba shine na ce bari inzo in sanar muku."" nai maganar ina kokonto akan yanda naga" su na wani ɗari-ɗari da ni. """A'ah ai da kin barshi ba sai kinzo ba, yau a tasha da zan dawo na siyo sabuwar gora, shine nace ba sai mun dinga yin" "alwala a waje ba mayi a ɗaki kawai tunda tsakar gidan caɓewa ya ke harmu gaza samun wajen kwanciya ga kuma saurayen da ke yo gayya idan wajen ya caɓe."" Umma tai tsulum ta bani amsa." "Haka kawai naji ban yarda da wannan maganar ta ta ba, hakanan ma Umma idan ta bushi iska sai ta tsiro wanki da" "marice dan kawai ta jiƙe inda muke kwanciya ni da Mama, musamman idan ranar ita ke da girki." "Bance komi ba na juya na nufi ɗakin Mama na isketa akan dadduma ta gama sallah, gaishe ta nai cike da" "girmamawa, amsawa tai cike da kulawa tare da tambayata lafiyata, bayan na bata amsa mukai zaman shiru na tsawon lokaci, ganin shirun yai yawa ne yau ko ƴar fira bamuyiba ya saka nace." """Wai Mama yau babu aikin girkin dare ne, naga har yanzu baki ce inhura rushi ba.""" """Da yake kinga Ummanku ta dawo to shine Abbanku ya ce imbar ma ta girkin tunda nata ne dama, ban musaba" "na bata abinta.""" "Mama ta bani amsa ta na ƙoƙarin kunna ragwargwaɓaɓɓiyar redionta wacce taci uban ɗauri da robali, shiru mukai" muna sauraren labaranda ake a gidan redion. Bamu daɗe da fara sauraren labaranba Abba ya aiko Yaya Habiba akan Mama ta fito tai shimfiɗa zamuci abinci. Firgigit na dawo daga tunanin da na tafi. """Mubeena ki ci abincin mana kar ya yi sanyi, wai kodai baki jin daɗi ne tun ɗazu nike lura da ke sam baki da walwala."" Mama tai maganar ta na jiran amsata." """Dan Allah Mama za ki iya gayamin abin da ya faru ɗazu, haka kawai nike ji a jikina akwai abin da ya faru, kinga su" "Yaya Habiba basa kula ni kamarma tsorona suke bayan ba gaka muke ba, Abbama bai yi min faɗa ba yanzu, shiyasa nike son insan abin da ya faru." """Ke ko wannan yarinya kin shiga uku, haka kika koma kuma bayan sa ido yanzu harda bin ƙwaƙwaf kike yi, to ni gaskiya bazan iya ɗaukar wannan rainin hankalin naki ba, tabbas wani abu ya faru kuma ba komi bane face aljannun" "da kika tada kika nemi hallakamu da ruwa, kuma mun riga mun yanke hukunci akanki ni da Abbanku, ba za ki sake ƙara kwana a gidannan ba daga gobe, dan tsaf za ki hallakamu alhalin da sauran lokacinmu, mun shirya tsaf dan mu kai ki aikatau can bariki.""" "Sak kowa na wajen yai jin abin da Umma ta ce, Abba kuwa cike da ƙulewa ya banka ma ta uwar harara ya na" "takaicin hali irinnata na rashin siri, inde tonon sililine to fa Umma ta yi dgree akanshi, sam ba ta da sirri ko kaɗan, sai Abba yajata gefe suyi magana ba tare sanin Mama ba amma mudin za'azauna da Umma sai ta faɗi wannan maganar, ga shi Allah ya ɗaurawa Abba son yin shawara ko sirri da Umma." "Kallon yanda nike kokowa da hawayen da suka dage akan dole sai sun zubo, ni kuma naƙi basu damar hakan Mama" "ta yi, cikin sanyi jiki ta janyo ni ta kwantar akan kafaɗarta ta na jin babu daɗi da maganar da Umma ta faɗa min alhalin ba ita na tambaya ba." "Gyaran murya Abba yai tare da janyo hankullanmu akan zai yi magana kowa ya nutsu, ɗago kaina nai ina son jin abin" da Abban zai faɗa. """Ke Mubeenah ki natsu domin maganar ta ki ce, bayan zuwan Yayanku Hashimu ya yi min wani abishir akan ya samo" "ma ki aikatau a can cikin bariki, na yi murna sosai da hakan dan idan ba ki manta ba nace ma ki, ko dai ki fidda miji in aurar da ke, ko kuma inbawa abokina aurenki ko ki fita ki barmin gida dan na gaji da ciyar da ke hakanan babu wa ta riba, ga matsalolinki da sukafi ƙarfin kanki bare kuma ni Iroro wanda ban aje ba kuma ban bama wani ajiya ba, na rigada na yanke shawara akan gobe da yardar Allah zan ɗaukeki da kaina in kaiki can gidan aikin, mutanen a matse suke da son samun wacce za tai aikin,yanzu abin da nike so da ke shine, ki tattaro dukannin abubuwan da kikasan ki na buƙata ki shirya gobe tun da sassafe zamu kama hanyar tafiya dan kuwa ana so muje kafin wani me magani ya iso, kuma ban amince kiyi magana da Mamanki ba akan wannan aikin, umarni ne na zartar a kanki ban amince kiyi magana da kowa ba akan wannan aikin face ni kaɗai ko Ummanku idan kika yi magana da wani Allah ya isa ban yafe muku ba wallahi, dan ba shawararki na nema ba na riga na zartar da hukunci.""" "Zuciyata ta shiga dokawa da tsananin ƙarfi, ya yinda na gama jin kalaman Abba, hakanan na ji na amince da hukuncin da ya zartar a kaina, hakanan nike ji na gaji da rayuwa a ƙarƙashin innuwar kulawar Abba, na daɗe da gane" "cewa Abba baya so na, ban san daliliba sai tsintar kaina na yi a cikin farin ciki, ban san wane zaren ƙaddara ba ne ya ke jana akan amimcewa da aikin, ni dai kawai ina jin daɗin zan nisanta da Abba na tsawon lokaci, zan yi nisanda zan samu nutsuwar gangar jiki da zuciya, ina buƙatar samun inda zan zauna inyi tunani akan rayuwata tun daga farko har izuwa yanzu da tarin ƙaddarori suka samu muhallin zama a rayuwata." "Bancewa kowa komi ba sai tashi da nai babu alamun damuwa atare da ni na wuce ɗaƙina, Mama ce ta bawa Yaya Habiba ƴar ƙaramar fitilarta ta kawo min, aiko na ji daɗin hakan dan so nike in sadu da ma'ajiyar ƙur'ani na dan" amma duhu ya hana hakan. "Jakar iskamiyya ta na ɗauko na fito da ƙur'ani na izufi sittin, na buɗe shi tare da fatan samun salama da dangana akan ƙaddarar da ke tunkaro ni, a lokacinda na fara karanta alƙur'ani me girma da tsarki, wani irin raunine ya baibaye ni har ban san sanda na fara hawayeba, ban daina karatunba kuma ban daina kukanba, hakanan nike ji a jikina wannan hawayen da nike na samun salama da sauƙin zuciya ne." "Ban daina karatun ba sai da na tabbatar da na samu gamsashiyar nutsuwa, sannan na rufe alƙur'ani nai addu'ata" tare da tashi na gabatar da Sallar Isha'i. "Bayan na gama ne na ta gyara wajen kwanciyata sannan na ɗauki fitilar Mama na mufi ɗakin ta, turus na yi ganinta durƙushe a ƙasa ga Abba tsaye a kant sai huci ya ke, ban ce komi ba na nufi inda ta ke ajiye fitilar na ajiye tare da" "juyawa na fice zuwa ɗakina, azkar ɗin kwanciya narci na gabatar sannan na haye yamusashiyar katifata nai lamo ina jin yanda har yanzu zuciyata bata bar dokawa da ƙarfiba, ban bawa kaina damar tunani akan komi ba haka na kwanta har barci me nauyi yai nasarar tafiya da ni." "Kyakkyawan matashi ne zaune a wa ta kujerar alfarma ya na aiki, sai wa ta mummunar halitta marar kyan gado ta" "zo ta bayanshi ta buɗe mumunan bakinta ta shiga yo aman wuta, juyawa yai ya na salatin jin ZAFIN WUTA amma sai wannan hallitar tai amfani da wannan damar ta sake amayo wa ta wutar me yawa akanshi, sai da halittar ta cike inda matashin ya ke da wuta sannan ta fice da jikin gini, wa ta mata ce ta zo kusa da wamda aka sakawa wutar ta na kuka tare da tattaɓa jikinshi, amma duk inda ta taɓa sai ya kwalje ita kuma sai hanunta ya ƙone, a haka ta zauna ta na ta kuka babu me rarrashi, yayinda muka zo wucewa ta wajen ni da Abba sai muka ga wannan matar shine Abba" ya ja hannuna ya bata ya na faɗin nice kaɗai zan nemo maganin da zai warkar da wannan matashin wanda wuta ke "ƙonawa, hannu biyu matar ta amshe ni tare da yiwa Abba alkairi me yawa ya juya ya barni da ita, da na tunkari inda wannan matashin ya ke, sai ruwa me ƙarfi ya zo ya maido da ni, haka na dage sai na isa gareshi har nai nasarar kama hanunshi, abin mamaki ina kama hanunshi sai wannan wutar ta ɓace ɓat sai de baƙin hayaƙi da ya karaɗe daƙin wanda wa ta murya marar daɗin amo ke faɗin, ""kin yi nasarar rabani da shi amma tabbas zan dawo, zan dawo domin ɗaukar fansa.""" A firgice na farka cikin matsanancin tsoro. "WANNAN LITTAFIN NA KUƊI NE, GA WACCE TA SHIRYA BIYA GA ACCOUNT." 9136291920 MARYAM UMAR OPAY TAKU HAR ƘULLUM. MARYAM STAR Follow the 𝑀𝐴𝑅𝑌𝐴𝑀 𝑆𝑇𝐴𝑅 𝑌𝐴𝑅 𝐵𝐴𝐼𝑊𝐴𝑅 𝐽𝐴𝐽𝐼𝑅𝑇𝐴𝑇𝑇𝑈 𝐻𝐴𝑈𝑆𝐴 𝑁𝑂𝑉𝐸𝐿𝑆 𝐶𝐻𝐴𝑁𝑁𝐸𝐿 channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029Vb5xdoy2975BcTM5m133 𝐙𝐀𝐅𝐈𝐍 𝐖𝐔𝐓𝐀 LABARI ME CIKE DA "BAN TAUSAYI, " "MATSANANCIYAR DAMUWA, KUNCIN CUZIYA, " "SADAUKARWA, " ZAZZAFAR SOYAYYA ME TSAYAWA A RUHI. WRITING BY MARYAM STAR YAR BAIWAR JJRT. MARUBUCIYAR RAYUWAR SAMHAD DAFIN MACIJI A DAREN AURENA AND NOW ZAFIN WUTA *https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341 &mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION* *(J.W.A)* "_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_. " """Jajirtattu mu ne ƙarfi a zuciya, hikima a magana, jajircewa a aiki. Ba mu ja da baya, ba mu faɗuwa. Mu ne tarihi" "da ake ginawa!"" " THE NOBLE WRITER'S TEAM ( DEDICATION IS OUR STRONG ) Typing... PAID BOOK 500 ONLY SEASON TWO PAGE 35 "Ina karanto addu'o'inda Manzonmu ya koyar idan mutum yai mummunan mafarki, zuciyata har lokacin bata daina" "dokawa da ƙarfi ba, sai ma sake tsananta dokawa da tai fiye da baya, hakanan naji jikina yai sanyi sam bani da kuzari ko kaɗan." "Tunanika barkayai suka dinga bijiromin na abubuwanda suka faru da ni tun wayuwar garin yau, idan da sabo ya" "kamata ace na saba da yanda rayuwa ke gara ni kamar kwallon ƙafa, aduk lokacinda zan wayi gari d irin ƙalubalen da zan fuskanta, sam babu wani abu na birgewa a cikin rayuwata, hakanan nike gudanar da rayuwata sam babu farin ciki." "Sake juyawa nai ɗayan sashen ina ji a jikina dole ne in tashi in nemawa kaina mafita, ina buƙatar farin ciki kamar" "kowace mace, ina buƙatar samun ƴancin kai kamar kowace budurwa wacce ke gaban iyayenta, amma ta yaya zan samu hakan? na tambayi zuciyata da take saƙamin tunanika daban-daban." "'Zan samu ƴanci kamar kowa amma sai na cire tsoro, dole sai na aro mayafin juriya na aje na haƙuri dan samun damar cimma muradina, to amma kuma ai Abba ya ce gobe zan bar gidan, ko da yake wannan ma wa ta damace zan samu dan in canza rayuwata, ban san gidan da zan rayu a cikinshi ba, haka zalika bansan wane irin mutanene a cikin gidan ba, zan tsaya imfara karantar mutanen wajen dan insan ta yanda zan gyara rayuwata kamar kowa.'" Ina ta tunani daban-daban da haka har barci ya ɗauke ni me nauyi. BANANA ISLAND "Ƙwance Mommy ta ke a kan katafaren gadonta wanda ya lashe miliyoyin kudaɗe kafin kafuwarshi a daɗin, kallon" "farko zakai me ka gane ba ɗan ƙasar ba ne, ko daga wace ƙasa aka ƙerashi lallai me tsananin tsada ne." "Sulaima ce zaune akan kagon kusa da Mommy wacce Doctor ke duba lafiyarta, fuskarnan ta ta tai jazur" musamman saman hancinta abinka da farin mutun. A gefe kuma wannan Dattijuwar matar ce zaune ta yi tagumi ta na kallon yanda Mommy duk ta bi ta fice a hayyacinta. Bayan Dr. ya gama ba ta taimakon gaugawa ya juyo ya fuskanci wannan Dattijuwar ya na faɗin. """Hajjo, wai dan Allah mi yasa bakwa kiyaye lafiyar baiwar Allarnan, ta na cikin mawuyacin hali yanzu haka, jininta" "yayi mugun hawa, ga ciwon zuciya, mi yasa kuke barinta cikin damuwa har haka, ina Fauzan ya ke ne, nasan shi kaɗaine zai fahimci abin da nike nufi."" Doctor yai maganar fuskarshi da alamun ɓacin rai gami da damuwa." """Kayya dai dakat, ai baka sa ni ba, Fauzan ɗin shine wanda yai silar shigarta wannan halin, ya na can kwance cikin" "mawuyacin hali rai a hannun Allah, kasande akwai shaƙuwa me tsanani tsakanin Fatima da Fauzan, halinda Fauzan" "ɗin ke ciki ne ya asassa ma ta tashin ciwon, wallahi muna yin bakin ƙoƙarinmu wajen ganin mun fitar da ita daga" "damuwa, amma abin ya ci tura, da zarar ta ga halin da ɗanta ke ciki sai jikin na ta ya rikice."" Hajjo tai maganar muryarta na jimanta lamarin." """Wai dama Hajjo har yanzu Fauzan be warke ba, na yi tunanin da kuka fita da shi India ya samu lafiya."" Dr. yai" maganar ya na jimanta lamarin. """Kai de bari Dakta! lamarin Fauzan se du'a'i, yanzu abin ya wuce yanda ake tunani, ciwo sai gaba ya ke ba wani sauƙi" "sai a wajen Allah, da zaka ga Fauzan yanzu na tabbata ƙafafuwanka ba zasu taku ta daɗin rai ba, yaronan yana ganin jarabawar rayuwa, sai de kawai muci gaba da taya shi da addu'a Allah ya yanke ma shi wannan wahala da yake ciki.""" "Jinjina kai kawai Dr. yai cike da jimami, dan bai mance yanda aka kawo Fauzan asibitinsu ba cikin matsanancin ciwo" "da zafin jiki, fatan samun sauƙi yai musu tare da bada shawarwari akan yanda zasu dinga kiyaye lafiyar Mommy gudun samun matsala sannan ya tafi." "Zaman shiru sukai a ɗakin kowa na tunanin zuci, da haka har barci me nauyi yai awon gaba da Hajjo, da wannan" "damar Sulaima tai amfani wajen sulalewa ta tafi ɗakin Fauzan dan ta ƙara ganinshi, sam hankalinta baya kwance, ga tashin hankalin yanda jikin ɗan uwanta ke tsananta, ga guma tashin hankalin yanayin Mommy ke ciki." "Zuwa bakin ƙofar glass ɗin ɗakin Sulaima ta yi, tare da jingina jikinta akan ƙofar ɗakin idanuwanta na zubarda" "hawaye, ta na ɓatuƙar ƙaunar ɗan uwanta, sam batason abin da zai ɓata ma shi rai, ta na kiyaye abin da zai saka yai fushi da ita, shima kuma ya shaƙu da ita, ita kaɗaice abokiyar nishaɗinshi, da ita yake sirri da ita ya ke shawara, ya yarda da ita fiye da kowa." "Ta ɗauki tsawon lokaci a hakan ta na tunani kafin daga bisani ta zabura tare da janyo ƙofar ta fito ta nufi kan stairs, da bibiyu ta ke hawa benen hakan ya bata damar hayewa cikin sauri, wa ta tsadaddiyar waya ta ɗauka akan luntsumemiyar kujerar da ke jere a ƙayataccen parloun, cikin sauri ta buɗe mabuɗan sirrin tare da laluba wa ta numbar da akai save da Pahpah, ta danna calling." Amsa kiran akai daga can ɓangaren tare da furta. """Assalamu alaikum""" """Wa,alaika salam pahpah!฀""" Sulaima tai maganar ta na ƙoƙarin haɗe kukanda ya sake taso ma ta. """Sulaima lafiya dai ko! ina Mommynku ina kuma Fauzan ya na lafiya dai ko, jikin da sauƙi ko!!!.""" Ya jero tambayoyin cike da ruɗewa. """Pahpah dan Allah ka dawo hakanan, wallahi Yah Fauzan ya na cikin matsanancin ciwo, Pahpah kullum abin gaba" "yake sake yi, please idan maganin bazai samu ba ka taho hakanan, banaso yah Fauzan ya mutu bakuyi bankwana ba, Pahpah jikinshi sam babu kyawun gani, yau kwana uku kenan rabon da ya saka koda ruwa ne a cikin !" Sai kuma wani sabon kukan ya sake ɓalle ma ta. "Cike da damuwa Ya fara rarrashinta tare da tabbatar ma ta da yana hanya yau komi dare a legos zai kwana, sannan yai ma ta albishir da ansamu maganin." "Ta ɗanji daɗi jin cewa zai dawo yau, ko babu komi zai tsaya wajen ganin ko yayane Fauzan ya saka wani abu a" "cikinshi, dan kaf a gidan shi kaɗai ne ya isa ya taɓa Fauzan ba tare da ya ƙone ba." 𝑃𝑙𝑒𝑎𝑠𝑒 𝑘𝑢𝑦𝑖 𝑚𝑎𝑛𝑎𝑔𝑒 𝑑𝑎 𝑤𝑎𝑛𝑛𝑎𝑛 𝑤𝑎𝑙𝑙𝑎ℎ𝑖 𝑖𝑛𝑎 𝑏𝑢𝑠𝑦 𝑛𝑒 𝑘𝑤𝑎𝑛𝑎 𝑏𝑖𝑦𝑢 𝑎𝑚𝑚𝑎 𝑖𝑛𝑠ℎ𝑎 𝐴𝑙𝑙𝑎ℎ 𝑑𝑎𝑔𝑎 𝑦𝑎𝑛𝑧𝑢 𝑧𝑎𝑘𝑢 𝑑𝑖𝑛𝑔𝑎 𝑠𝑎𝑚𝑢𝑛 𝑙𝑖𝑡𝑡𝑎𝑓𝑖𝑛 𝑍𝐴𝐹𝐼𝑁 𝑊𝑈𝑇𝐴 𝑎 𝑘𝑎𝑖 𝑎 𝑘𝑎𝑖. 𝐺𝐴 𝑊𝐴𝐷𝐴𝑁𝐷𝐴 𝑆𝑈𝐾𝐴 𝑆𝐻𝐼𝑅𝑌𝐴 𝐵𝐼𝑌𝐴𝑁 𝐾𝐷𝐼𝑁 𝐷𝐴 𝐴𝐶𝐶𝑂𝑈𝑁𝑇. 9136291920 𝑀𝐴𝑅𝑌𝐴𝑀 𝑈𝑀𝐴𝑅 𝑂𝑃𝐴𝑌 TAKU HAR KULLUM MARYAM STAR Follow the 𝑀𝐴𝑅𝑌𝐴𝑀 𝑆𝑇𝐴𝑅 𝑌𝐴𝑅 𝐵𝐴𝐼𝑊𝐴𝑅 𝐽𝐴𝐽𝐼𝑅𝑇𝐴𝑇𝑇𝑈 𝐻𝐴𝑈𝑆𝐴 𝑁𝑂𝑉𝐸𝐿𝑆 𝐶𝐻𝐴𝑁𝑁𝐸𝐿 channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029Vb5xdoy2975BcTM5m133 𝐙𝐀𝐅𝐈𝐍 𝐖𝐔𝐓𝐀 LABARI ME CIKE DA "BAN TAUSAYI, " "MATSANANCIYAR DAMUWA, KUNCIN CUZIYA, " "SADAUKARWA, " ZAZZAFAR SOYAYYA ME TSAYAWA A RUHI. WRITING BY MARYAM STAR YAR BAIWAR JJRT. MARUBUCIYAR RAYUWAR SAMHAD DAFIN MACIJI A DAREN AURENA AND NOW ZAFIN WUTA *https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341 &mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION* *(J.W.A)* "_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_. " """Jajirtattu mu ne ƙarfi a zuciya, hikima a magana, jajircewa a aiki. Ba mu ja da baya, ba mu faɗuwa. Mu ne tarihi" "da ake ginawa!"" " THE NOBLE WRITER'S TEAM ( DEDICATION IS OUR STRONG ) Typing... PAID BOOK 500 ONLY CHAPTER 35-40 .ميحرلا نمحرلا الله مسب "Ajiyar zuciya Pahpah ya saki lokacinda Sulaima ta kashe wayar, kallonshi farin mutum da ke zaune kan sallaya tai tare" da girgiza kai sannan ya ce. """Mudin haskenta ya sadu da ɗanka tabbas ƙarshen wahalarsa ya zo, ita kaɗaice za ta iya karya wannan mugun" "sihirin, sannan kuma ta bashi garkuwa da izinin ubangijinmu.""" "Shiru Pahpah yai tare da zurfafa a cikin tunanin yanda zai sadu da wannan tauraruwa me haske, wacce zata zamo" tsanin takawar Fauzan ta hanyar samun lafiyarshi. """Ka tashi ka je, kana tare da nasara, ka riƙe Allah domin shine kaɗai zai tallafa maka.""" "Wani abin al'ajabi da bammamaki, mutumin na gama maganar sai ya ɓace ɓat kamar be taɓa wanzuwa a wajen ba." "Tsam Pahpah ya tashi ya fice cikim tsoro, direct wajen motarshi ya nufa, bayan ya shiga ya saka drivar ya ja da sauri" suka bar wajen. MUBEENAH AGEGE "Can cikin barci ni ke jiyo muryar Mama sama-sama, ban buɗe ido ba sai juyi da na sake yi ina shirin gyara kwanciyata, sai na ji an jijjiga ni da ƙarfin gaske ana faɗin." """Innalillahi wa'inna ilaihi raju'un, jama'a Mubeenah wai lafiyarki ƙalau kuwa? dan Allah ki tashi hakanan, rana" "har ta fito amma kin gagara tashi, tun asubahi nike tashinki.""" "Zaram na tashi zaune tun lokacin da na ji salatin da Mama ta saki, cikin sauri na buɗe idanuwana, amma abin" "mamaki shine, sun buɗe tar amma sam bana ganin komi, sake kai hannuna nai ina shafa idon dawa, amma abin al'ajabi sai naji ashe a buɗe suke." """Allahu Akbar, kaji ƙudirar Ubangiji mabuwayi gagara misali, me hanawa kuma me bayarwa, Wallahi Allah Mama" "idanuwana basa ganin komi, duhu nike gani, zo ki duba ki gani.""" "Nai maganar cikin jinjina ƙarfin buwayar Ubangiji, me bayarwa kuma me hanawa aduk lokacin da ya so, idan ba Ikon" "Ubangijiba waye zai baka alokacin da ya so, kuma ya amsa a lokacinda ya so?." """Ke Mubeena ban son iskanci, ta gidan ubanwa ke baki gani, alhalin ga idanuwanki nan tarrrr ma sha Allah, ki daina" "wasa ki taso muje kiyi sallah lokaci na wucewa.""" Mama tai maganar ta na hana kanta gasgata cewa da nai bana gani. """To Mama bara in tashi.""" "Nai maganar ina ƙoƙarin tashi, amma mi ta tabbata dai bana gani sam, dan kuwa ina taka ƙafata ban sauke ta a ko ina ba sai cikin kwanon da nike aje ruwa idan zan kwanta, cike da razani na janye ƙafata nai baya ina salati." "Sak Mama ta yi, ta kasa taɓuka komi domin kuwa ko ta so ko kar ta so ya tabbata bana gani." Maganar Abba ce ta yanke min jimamin da na shiga. """Ke Halima! wai har yanzu ita Mubeenar ba ta tashi ba, ki watsa ma ta ruwa manah, kinga rana ta soma yi, kuma" "ana jiranmu dan yanzu na sake yin waya da Hashimu ya sanar da ni cewa, me gidan ya dawo jiya cikin dare, muyi sauri muje dan """ "Maganarshi ta yanke ne lokacin da ya lura da Mama zaune daɓas a ƙasa, kamar ma bata cikin hayyacinda dan ya lura" da yanda laɓɓanta ke motsawa. """Halima lafiya dai ko? ko wani abun ta. """ Bai ƙarasaba ya ji ni na fashe da matsanancin kuka ina faɗin. """Abba kana gani na ko, wallahi Abba ni bana ganinka, na zama makauniya, bana ganin komi sai duhu, dan Allah zo ka" "kama hannuna ka kaini waje inyo alwala banyi sallah ba""." "Wa ta iriyar ashar Abba ya kutuntumo ya watsa wa Mubeenah, sannan ya ɗaura da faɗin." """Ke abu ta kazar ubanki, ubanki ya hwaɗa ya afka ya zunduma cikin makantarnan, ni za ki mayar tsohon banza, na rantse da girman Allah sai kin buɗe idonan, ni za kiyi wa baƙin ciki Mubeenah, ni!! ni!!! Mubeenah.""" "Ya ƙarashe maganar ya na taƙune fuska kamar zai saka iho, ya riga da ya gama tsala lissafin yanda rayuwa zata canza" "mai, ya gama sadaƙarwa a yau zai zama ɗaya daga cikin masu kuɗin a arear unguwar Agege, amma lissafinshi na neman roshewa ganin halin da Mubeenah ke ciki." "Mama ce ta tashi tare da kama ni ta fitar da ni idanuwanta na zubarda hawaye, ni nasan kaf duniyata ba zan samu" "me sona kamar Mama ba, ƙauna tattali gami da kulawa a wajen ta kaɗai nike samunsu, ita ce kaɗai bangon da zan jingina inyi kuka kuma ta rarrasheni cike da kulawa haɗi da tausayi." "Ruwa ta zuba a buta ta kama hannuna muka nufi bayan gida, can inda tasan ina tsayawa ta aje ni tare da ajiye butar" "inda tasan bazan zubar ba, sannan ta fice ta bani waje." "Tsarki na yi kamar yansa na saba, sannan na tafo bango a hankali na fito waje ina sake tabbatarwa kaina na zama" "makauniya, banyi aune ba na ji wani abu ya ja ni, nai baya-baya na faɗa akan kayan zuba ruwanmu, ji kake ""Tinjim."" na afka cikin babban bahon ruwa da yake ƙarami ne bashida tsawo sai faɗi." "Abba ne ya taso daga ɗakin Mama dan ganin abin da ya faru, sai kuwa yai tozali da ni kwance male-male a cikin bahon ruwa." """Yau ni Iroro na ga jarfa, ke dan malafar ubanki shine zaki rasa insa za ki faɗa sai cikin baho, wato ne dole sai kin" "tabbatar min da cewa ki na min baƙin ciki, yo baƙin ciki manah, sarai kin san wahalar da nike sha wajen samo ruwanan, kina can kina barcin asara na je na samo wai dan kiyi wanka idan zamu je gidan da za kiyi aikatau.""" "'Aikatau', na maimaita kalmar a zuciyata, sai kuma na zabura na tashi zaune ina lalube ina faɗin." """Abba bara inje inyi sallah sai in shirya idan har zasu ɗauke ni a haka da makantata ni na amince zanyi aikin.""" Nai maganar wani irin karsashi da ƙwarin gwuiwa na zo min. "ALHAMDULILLAH, MUN KUSA GAMA FREE PAGE, SAURA PAGE BIYU." GA WACCW TA SHIRYA KARANTA LITTAFIN ZAFIN WUTA GA ACCOUNT A ƘASA. 9136291920 MARYAM UMAR OPAY. TAKU HAR KULLUM ME SON GANIN FARIN CIKINKU. MARYAM STAR ZAFIN WUTA Follow the 𝑀𝐴𝑅𝑌𝐴𝑀 𝑆𝑇𝐴𝑅 𝑌𝐴𝑅 𝐵𝐴𝐼𝑊𝐴𝑅 𝐽𝐴𝐽𝐼𝑅𝑇𝐴𝑇𝑇𝑈 𝐻𝐴𝑈𝑆𝐴 𝑁𝑂𝑉𝐸𝐿𝑆 𝐶𝐻𝐴𝑁𝑁𝐸𝐿 channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029Vb5xdoy2975BcTM5m133 𝐙𝐀𝐅𝐈𝐍 𝐖𝐔𝐓𝐀 LABARI ME CIKE DA "BAN TAUSAYI, " "MATSANANCIYAR DAMUWA, KUNCIN CUZIYA, " "SADAUKARWA, " ZAZZAFAR SOYAYYA ME TSAYAWA A RUHI. WRITING BY MARYAM STAR YAR BAIWAR JJRT. MARUBUCIYAR RAYUWAR SAMHAD DAFIN MACIJI A DAREN AURENA AND NOW ZAFIN WUTA *https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341 &mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION* *(J.W.A)* "_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_. " """Jajirtattu mu ne ƙarfi a zuciya, hikima a magana, jajircewa a aiki. Ba mu ja da baya, ba mu faɗuwa. Mu ne tarihi" "da ake ginawa!"" " THE NOBLE WRITER'S TEAM ( DEDICATION IS OUR STRONG ) Typing... PAID BOOK 500 ONLY CHAFTER 40-45 .ميحرلا نمحرلا الله مسب "Tsit Abba yai jin maganar da nai, sai kuma ya was he baki tare da faɗin." """Yauwa Mubeenah, ko ke fa, to yanzu kiyi sauri ki shirya zuwa anjima bayan Ummanku ta gama abin kari sai kiyi" "mu kama hanya dan mu isa da wuri."" ya ƙarashe maganar tare sa taimakamin na fito daga cikin bahon jikina na tsiyayarda ruwa, sake zuba min ruwa yai a buta sannan ya damƙamin a hannuna ya na ta rarrashina gami da lallaɓawa, sai naji jikina yai sanyi ƙalau, duk da ba ganin shi nike ba amma a iya maganar da yai min na fuskanci lallai ya ji daɗin maganar da na faɗa, sai na shiga zargin kaina akan ƙin bin umirninsa da nike a baya, wataƙila hakan ne ya saka ya tsaneni saboda kafiya da baƙin taurin kai irin nawa." "Ban san sanda bakina ya furta. ""Abba dan Allah ka yafe min duk abin da nai maka, bazan sake ba, na yi danasanin" "wanda nai maka a baya, nasan da ace na bi umurninka da na auri abokinka da yanzu nima kana so na kamar yanda kake son su Yaya Habiba, daga yau bazan sake saɓama umuninka ba in sha Allah.""" "Kasaƙe Abba yai jin maganar da nayi, sai jikinshi yai sanyi, duk wanda ya taɓa zuwa gidanmu koda na wuni ɗaya" "ne, to yasan rashin jituwar da ke tsakanina da Abba, tun maƙota na zuwa bada haƙuri idan yana dukana har takai da suk girman unguwarmu babu me ko kallon inda muke idan wani abu ya haɗo ni." "Bai ce komi ba sai juyawa da yai ya shige ɗakin Umma wacce dukkan abin da ke faruwa akan idonta, indai wajen iya" "laɓe da jin ƙwam ne, to Umma ita ce kan gaba, bata yarda gulma ko tsugudidi su wuce ta, a haka ma wai dan a Legos muke ta na tsoron ƴan iskan unguwarmu, dan abu ƙalilan sai ka ji ance ansakawa mutum taya an ƙone shi ƙurmus, musamman idan wani abu ya haɗa yare da hausawa." """Wallahi kar ka yarda da abin da ta gaya maka, yaudara ce kawai, so take tai mana baƙin cikin cin arziki shiyasa ta" "kulle idon, yo ita makantar haukace da zata sameta lokaci ɗaya, ade bincika zaka samu wani abun ta shafa dan baƙin munafurci irin nata."" Umma tai maganar ta na shanye ƙananun idanuwanta irinna kwararrun ƴan gulma da munafurci." """Ubanta ya zurma ya afka ya zunduma ya faɗa cikin shafawa ido wani dan makancewa, ita yanzu dan kutumar abu ta" "kazanta har ta yi wayon sanin makirci, to aniyarta ta bita, na fi ƙarfin ta yaudare ni wallahi, zan gwada ma ta ba abanza nike zaune a legos ba, nima tantirin kaina ne, iskanci sai de mu koyawa wasu badai mu a koya mamu ba."" Abba yafi cikin tada jijiyoyin wuya, daga jin abin da Umma ta faɗa shikenan har ya yarda ya hau kai ya zauna daram,dama ba tun yau ya saba irin haka ba, sau da dama hakan kan kasance, lafiya lau za'ayi magana da shi amma da zarar Umma ta ce ba haka ba babu bincike ba lissafi zai hau kai ya zauna akan yanda ta ce hakanne gaskiya." "Mamace ta zo ta kama ni ta kaini ɗaki tare da yimin shimfiɗa da saka min hijabi, alƙibla ta fuskantar da ni tare da" bani umarnin yin sallah. "Ina kabbara Sallah wani irin rauni ya baibayeni, sai na ji ina buƙatar tsiyayarda damuwata a gaban Mahallicina me" "rahama, nasan zai sauƙaƙamin ta wani ɓangaren, aiko na shiga zubda hawaye masu zafi yayinda nike gabatar da Sallah cikin nutsuwa da kamala, kuka me ƙarfi ya kubcemin lokacinda na duƙar da gaɓoɓina aƙasa nakai sujjadah, kuka da addu'a nai sosai har sai da naji nauyin da ya tokaremin ƙirji ya sauka sannan na ɗago naci gaba da Sallar cikin karsashi har na sallame, bayan na kammala azkar na hau karatun alƙur'ani me girma, da yake harda ce da" "ni, dandanan nishaɗi ya baibaye, tabbas karanta littafi me tsarki babbar rahamace, babu abin da yake saka ni nishaɗi" kamar inji ina karanto littafi me tsarki tiryan-tiryan. "Na ɗauki lokaci me tsawo ina karatu, har sai da muryata ta disashe sosai sannan nai addu'a tare da shafawa nai" "zaune abuna ina nazarin rayuwa, wato Allah alhakim, wa ta hikimace ta ubangiji wannan makantar da ya ɗauramin, godiya nai a gareshi ta hanyar yin tazbihi harma da salatin Annabi, duk safiyar duniya da zan wayi gari da ciwo ko babu sai na yi tarin aiyuka kamarsu, share ɗakin Mama da na Umma, share tsakar gida, hura wutar ɗaura abin kari, wanke-wanke, wankin kayanda aka ɓata, idan ka cire kayan Mama hatta na Abba nice zan wankesu kullum ranar duniya, aƙalla Yaya Sumayya na daka kaya kala uku duk rana, haka zan haɗa in wanke, wani bin Abba ya na zundumamin zagi Umma kuma na mita haka zan zage inyi aiyukana babu me cemin sannu sai ma zagi da nike sha wajen Abba, amma nice yau zaune a ɗaki ina hutawa kamar yanda kowa ke yi, babban abin da yai min daɗi be wuce yanda yau bazanje shago ba, sam bani son zuwa shagonan saboda ƴan iskan da ke wajen, amma banda damar daina hakan, sai gashi yau babu zuwa shago saboda lalurar makanta." "Ban san na ɗauki tsawon lokaci ina tunani ba sai da Abba ya kwaɗo min kira, firgigit na farka daga duniyar tunani da" "na lula, da laluben hanya har na kawo ƙofar ɗakin." """Gani Abba.""" """Amshi wannan kunun ki shanye sai kiyi sauri kizo muje.""" """To Abba nagode.""" "Na faɗa tare da lalubawa har na kai inda hannunshi ya ke na amshi kofin kunun, juyawa yai abinshi, ni kuma na zame na zauna a wajen tare da kafa kofin a baki na shiga shan kunun, ina son abu me ruwa sosai hakan ya bani damar" shanye kunun duka. "Lalubawa na sake yi ina bin bango har nakai wajen jakar da nike ajiye kaya, da lalube ba buɗe ta na ɗauki kedar" "thank you wacce nike ajiye a gefen jakar, laluba ƙasan jakar nai harna lalubo wa ta ƴar siririyar chain, danƙe shi nai a hannuna kamar wani zai ƙwacemin, sannan na saka hannuna na kakkaɓe jakar tawa na janyo ta zuwa jikin bango na aje nima na zauna zaman shiru, har yanzu zuciyata ba ta daina dokawa da matsanancin ƙarfi ba, kuma ina jin wani irin sanyi me kashe gaɓoɓi ya na baibaye ni, ga wa ta iriyar kasala me sakar da gaɓoɓi da ta saukomin." "Shiru nai ina sauraran bugun zuciyata harna tsawon lokaci, ban san adadin mintunan da na kwashe ba, sai da na jiyo" muryar Abba ya na faɗin. """Mubeenah, ke Mubeenah ki fito idan kin gama ke nake jira mu yi mu tafi lokaci ya na ja.""" Zumbur ta tashi kamar dama jiran kiranshi nike. """Abba dan Allah ka taimaka ka ɗaukar min jakar tunda bana ganin hanya.""" "Bai musa ba ya shigo ya ɗauki jakar tare da kama hannuna muka fito, bai saki hannuna ba sai ji nai ya na faɗin." """To Mubeena ga mutanen gidana zasuyi sallama da ke.""" Murmushi nai sannan na ce. """Mama nasan kuka kike yi, dan ina iya jiyo zafin zubar hawayenki a cikin zuciyata, dan Allah ki kwantar da hankalinki babu abin da zai sameni sai alkairi, ina ji a jikina wannan tafiyar ita ce zata zamo tsanin da zan taka wajen ganin na cimma muradai da mafarkaina, haƙiƙa Mama ke uwace a gare ni, a duk inda nike zan kasance cikin kwanciyar hankali matsawar za ki ch gaba da yi min addu'a kamar yanda kika saba, zan yi kewar kulawarki a gareni, Allah ya baki haƙurin jure rashina uwa ta gari me maida ɗiyarta kamar sarauniya saboda soyayya da kulawa฀.""" "Kuka ne ya kubcewa Mama me tsananin ƙarfi, yayinda na matso inda muke ta riƙe hannuna gam ta na faɗin." """Ibrahim ka ji tsoron Allah karka rabani da Mubeenah, wallahi ina jinta kamar ƴar da na tsugunna na haifa, ka ji tausayin halin lalurar da ta ke ciki kabarmin ita, wallahi nayi alƙawarin zan ɗauki dukannin ɗawainiyarta.""" """To munafuka ƴar baƙin ciki me baƙin hali, ai dama batun yau ba nasan kedin munafuka ce, yo munafuka manah idan ba munafurci da baƙin ciki ba, ina ruwanki da shiga sha'anin uba da ƴa, wannan ai kinibibine irin na fulanin" "ruga."" Umma tai zaram ta faɗi jin maganar da Mama ke yi na neman yin tasiri a zuciyar Abba, dan ta lura kamar jikinshi ya ɗan yi danyi." Cike da macin rai Mama ta saki hannuna ta juyo wajen Umma ta na faɗi. """Ke Umma ki kiyaye bakin ki , kisan abin da za ki dinga faɗa, ina ruwanki, wa ya saka da ke, ban san shigar shigula, ki kiyaye ni wallahi kar ki bari in waiwayo ta kanki dan abi ba zai yi maki daɗi ba, ina ɗaga maki ƙafane kawai dan a zauna lafiya amma badan ina tsoronki ba, daga yau kar in sake ji kin tsomamin wannan baƙin bakin na ki me kama da anzunguro kan kare ta taga, ki shiga hankalinki.""" "Mama ta yi maganar ɓacin rai da hasala na bayyana a fuskarta, yayin da Umma tai murus sai walimar idanu ta ke" "yana shege lahira, shi kanshi Abba mamakin Mama ne ya daskarar sa shi a tsaye, dan bai taɓa tunanin ta na da zafi har haka ba, lallai an ƙure haƙurin damo, ya faɗi a zuciyarshi." Juyowa ta yi wajen shi tare da faɗin. """Tabbas ban isa in hanaka zartar da hukunci akan Mubeena ba, amma zan tuna maka gaji tsoron Allah, wannan baiwar da kake wulaƙanta rayuwarka ita ce rufin asirinka, kuma amanace a wajenka, muddin ka zalunceta Allah ba zai barka ba, ka je ka yi duk yanda kaga dama da ita."" Mama na gama faɗin hakan ta zo wajena ta damƙamin wani abu a cikin hannuna sannan ta shafa fuskata ta juya fuuuuu ta shige ɗakinta." Da sauri Umma ta matso kusa da inda muke ta fara jan hannun Abba wanda ke riƙe da jaka ta ta na turamu waje wai kar Mama ta fito ta hanamu tafiya. Ina tuntume da komi haka Abba ya ja hannuna har muka fice sannan ta saki hannunshi ta dawo cikin gida ta kaɗa su Yaya Habiba zuwa cikin ɗaki suka shige harda kullo ƙofa. Ina tuntuɓe da komi haka Abba ke jaye da hannuwana har muka shiga cikin unguwarmu sosai inda mutane keta "hada-hadarsu su na kaiwa da komowa, a Legos babu ƴan zaman banza kowa fitowa ya ke ya nemi na kanshi dan rufawa kai asiri." "Munyi tafiya sosai kafin mu samu abin hawa, nan Abba ya lalubo wayarshi wacce ta ci duniya duk ta sha ɗauri da" lobali ya lalubo number Yah Hashim ya kirashi dan ya yiwa me abin hawan kwatancin inda za'a ajemu. "Hawa mukai bayan mun tsadance muka tafi, har lokacin ban daina jin sautin bugun zuciyata ba a cikin kunnuwana," sannan sanyin jikina sai daɗa ƙaruwa ya ke kamar wacce ta shiga cikin na'urar sanyi. "A daidai farkon shiga BANANA ISLAND aka sauke mu, Abba ya sake kiran Ya Hashim, kafin ya zo sai da muka ɗauki" "mintuna atsaye, tun ina jin daɗin tsayuwar har ta gundure ni, hakan ya saka nace cikin sanyin murya." """Abba dan Allah ka samo mana inda zamu ɗan zauna, na gaji da tsayuwa wallahi.""" "Waige-waige ya shiga yi kamar me neman wani abu, wa ta bishiya me kyau ya hanga a gefenmu, hakan ya saka ya ja" hannuna muka je can muka zauna ya na mitar jimawar da Hashim yai be zo ba. "Ƙungurmin daji ne me cike da munanan halittu iri daban-daban, wa ta iriyar guguwace me haɗi da ƙura ta taso da iska me tsananin ƙarfi, saboda tsananin ƙarfin iskar guguwar sai da halittun da ke wajen suka shiga neman wajen" "ɓuya, sauti marar daɗin ji me kama da tsawa me firgitarwa ne ya cika dajin gaba ɗaya, a daidai wajen wa ta" "tshohuwar bishiyar kuka me rassa da jijiyoyi da yawa wannan guguwar ta tsaya, a hankali yayyafin ruwa ya fara" "sauka a cikin guguwar da ke ɓacewa ta na komawa ruwa, farace tas tas farin har ya yi yawa kai da ganin irin hasken nata kasan ba dai mutum ba sai dai jinsin aljannu, fara ce kuma doguwa me yalwar baƙin gashi da tsananin tsawo ta bayyana fuskarta a murtuke, idanuwana sun kaɗa sun sauya launi zuwa launin shuɗi me haske, cike da ɓacin rai ta buɗe murya cikin amo marar daɗin ji ta kwala kiran." """Zizzau! Zizzau!! Zizzau!!!.""" "A yanda ta ke magana sautinta na fita da amo me tsoratarwa, bakinta kuma na feso da feshin ruwa masu zafin" "gaske, wannan bishiyar kukarce ta shiga girgiza da tsananin ƙarfi, kafin wani hayaƙi ya bayyana wani baƙin gajeren aljani mumunan gaske ya bayyana, duƙawa yai cike da girmama ya fara kirari gami da fadanci." Dakatar da shi wannan aljanar ta yi cike da facin rai ta ke faɗin. """Waye wanda ya aikeka yin aiki akan goɗiyata? tabbas za ka fuskanci hukunci me tsanani saboda saɓa umurnina" "da kuma karya dokar da na gindaya muku akan aiki da waɗacan butulun bil Adaman waɗanda basu san komi ba sai cutar da ƴan uwansu da yaɗa zalunci a doran ƙasa, yanzu-yanzu da ƙarfin ikon ubangiji na baka izini kaje ka karya aikin da kai, sannan kuma kadawo ka kai kanka wajen ruwan hukunci.""" "Bata jira abin da zai ce ba ta ɓacewa daga wajen, nan take ruwan ya ɗauke gaba daya kamar be taɓa wanzuwa ba." "Cikin hanzari wannan baƙin aljanin yai girgiza tare da ɓacewa ɓat, bai bayyana a ko ina ba sai akan bishiyar da Abba" da Mubeena suke zaune su na hutawa. "Shuuuuuuu, wani abu ya gifta ta gefen idon Mubeenah, yayin da baƙin hayaƙi." "SAURA ONE PAGE MU KAMMALA FREE PAGE INSHA ALLAH, BAN YI ALƘAWARIN CI GABA DA SHARE KAMAR" "KULLUM BA, AMMA WAJIBINE INTURAWA DUK WACCE TA BIYA KUƊI SABODA HAƘINTA NE." 09136291920 MARYAM UMAR OPAY TA KU HAR KULLUM MARYAM STAR Follow the 𝑀𝐴𝑅𝑌𝐴𝑀 𝑆𝑇𝐴𝑅 𝑌𝐴𝑅 𝐵𝐴𝐼𝑊𝐴𝑅 𝐽𝐴𝐽𝐼𝑅𝑇𝐴𝑇𝑇𝑈 𝐻𝐴𝑈𝑆𝐴 𝑁𝑂𝑉𝐸𝐿𝑆 𝐶𝐻𝐴𝑁𝑁𝐸𝐿 channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029Vb5xdoy2975BcTM5m133 𝐙𝐀𝐅𝐈𝐍 𝐖𝐔𝐓𝐀 LABARI ME CIKE DA "BAN TAUSAYI, " "MATSANANCIYAR DAMUWA, KUNCIN CUZIYA, " "SADAUKARWA, " ZAZZAFAR SOYAYYA ME TSAYAWA A RUHI. WRITING BY MARYAM STAR YAR BAIWAR JJRT. MARUBUCIYAR RAYUWAR SAMHAD DAFIN MACIJI A DAREN AURENA AND NOW ZAFIN WUTA *https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341 &mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION* *(J.W.A)* "_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_. " """Jajirtattu mu ne ƙarfi a zuciya, hikima a magana, jajircewa a aiki. Ba mu ja da baya, ba mu faɗuwa. Mu ne tarihi" "da ake ginawa!"" " THE NOBLE WRITER'S TEAM ( DEDICATION IS OUR STRONG ) Typing... PAID BOOK 500 ONLY CHAPTER 45-50 .ميحرلا نمحرلا الله مسب "Ya mamaye wajen, tare da iskar guguwa me tsanani, hakan ya yi daidai da tsayuwar jibgegiyar motar da Ya Hashim ke ciki, wasu irin baƙin ruwa masu tsananin azabe suka shiga zubowa daga idanuwana gaba ɗaya hankalina ya gushe saboda ruɗani da kuma azabar da idanuwanta ke ma ta, Abba ne ya juyo ya na kare fuskarshi daga yashin da guguwar ta ɗebo, sai ya ganni a wannan halin, cike da firgici ya soma ja d baya ya na girgiza kai ganin yanda baƙin ruwa ke tsiyaya daga idanuwana." Fitowar Yaya Hashim daga mota ya yi daidai da ɓacewar guguwar haɗe da ɓacewar wannan ruwan daga kan fuskata kamar ba au taɓa wanzuwa ba. "A hankali na ke buɗe idanuwa waɗanda sukaimin nauyi, abin al'ajabi sai na ga Abba da Yaya Hashim tarrrr, sake" "rufe idon nawa nai sai kuma na sake ganinsu, da matsananin sauri na miƙe tsaye zumbur ina dube-dube amma stil ina ganin komi clear." """Allahu akbar kabeeran, Allah na gode maka, Allah kai ne abin godiya, Alhamdulillah, Alhamdulillah.""" Na faɗa ina sake maimaitawa cike da farin cikin yanda ganina ya dawo. "Sakin baki Abba yai ya na bina da kallo me cike da mamaki da kuma tsoro, ga zallar al'abin abin da ya gani yana" zuba daga idona. "Yah Hashim ne ya katse shi ta hanyar dafa kafaɗunshi ya na faɗin ""Wai Abba lafiya?.""" Sannan ya dawo hayyacinshi tare da basarwa ya miƙe tsaye ya na bin shawar da zuciyarshi ta bashi akan b waske kawai ya samu ya rabu da ni lafiya. "A gaggauce Ya Hashim yai mana jagora zuwa gaban motar, har lokacin fuskata ɗauke da annashuwa da farin ciki, cike" "da ɗauki na matsa gaban motar ina jiran ya buɗe min da mota itace ƙarshen abin da nike son hawa a rayuwata, ina bala'in son inganni a cikin mota, amma babu halin hakan, iyakata da ita sai gani daga nesa." "Tun da muka fara shiga cikin tsararriyar unguwar bugun zuciyata ya sauya salo, numfashina na yau shirin ɗaukewa" "amma ban bashi damar ɗaukewarba nike janyo shi da sauri, wato malam duniya da arziƙi su na inda suke, tsayawa baku labarin yanda unguwar ta kai ƙarshe a haɗuwa ɓa ta lokacine, sai dai kawai ince kugi imagin." Daidai wani ƙaton get na alfarma wanda ya lashe maƙudai wajen kafuwarshi Yaya Hashim ya tsaya da motar tare da fito da wani card ya miƙawa ɗaya daga cikin jibga-jibgan jaruman escort ɗin da ke zagaye da get ɗin. "Bayan am bamu damar shiga cikin gidan ta hanyar buɗe manah wannan makeken get ɗin, kai tsaye Yaya Hashim ya" danna kan motar cikin makeken ƙeraren gidan wanda yakai ƙarshe wajen haɗuwa. """Muƙuƙut, maƙwat.""" "Abba da ya hangame baki tare da karkace kai ke ta faman haɗiyar yawu, lissafi da kwancewa kawai ya ke a kwanyarshi, tare sa wasu irin tunanika da ke bijiro ma shi." Ni kuwa sake rakuɓewa nai ina ƙara kallon yanda aka narke dukiya wajen gida wannan gida me kama d aljannar "duniya, tun da nike ban taɓa ganin gida wanda ya kama ƙafar wannan wajen haɗuwa da tsaruwa ba." BANANA ISLAND. "Zazzaune suke su huɗu akan lallausan carpet, gabansu an cike shi da kayan break fast na alfarma, kallo ɗa ya zakai" musu ka gane basu cikin walwala. Nisawa kamulallen mutum yai tare da cigaba da maganar da yake wacce ta saka sauran nutsuwa. """Wallahi hajjo inda kika ga mutumin ba za ki ce ba mutum ba ne, saboda kamala da dattako irin na shi, ya" "tabbatar min da idan har muka samo wacce ta amince zata yi wannan aiki to babu makawa Fauzan zai warke ya samu lafiya kamar kowa, abin da ke bani tsoro yanzu ɗaya ne, shin ta yaya zamu samu wacce za ta amince da aikin alhalin ko mu da muke iyayenshi ba komi zamu iya yi ma shi ba, ni kaina jiya da na kusanci inda ya ke sai da na ƙone wallahi.""" Yai maganar ya na kallon hannunshi da yai jazur ga kuma alamar konuwa ta tashi a hannun na shi. """Ya Allah gareka muka dogara, Allah ka bamu mafita akan yanda zamu shawo kan ciwon wannan bawa naka" "wanda yake cikin matsanancin hali.""" Hajjo tai maganar fuskarta na jimamin lamarin. Mommy ce ta ɗan muskuta tare da gyara kishingiɗar da tai ta buɗe baki cikin ƙarfin hali ta na faɗin. """In sha Allah za'a dace dan kuwa jiya na yi magana da wannan yaron Hashim me wanki da guga akan ina so ya" "binciko min yarinya me hankali da nutsuwa a can cikin unguwanin talakawa, ya amsamin da in sha Allah za'a samu," yanzu haka na tabbatar da su na hanya dan kuwa munyi waya yau da asuba ya sake tabbatar min da ansamu kuma "ƴar uwarshi ce, ya na da yaƙini akan zata iya, to na bashi umarni akan ya ɗaukominsu yanzu da safenan kafin anjima Mu'allim ya zo.""" "Jinjina kawuna sukai a zuciyoyinsu su na addu'ar Allah ya sa a dace, indai kuɗi za su yi aiki to a shirye suke wajen" ganin sun salwantar da ko nawa ne dan samun lafiyar sanyin idaniyarsu. "Bayan isowarmu da kamar mintuna goma, amma shiru babu wanda ya leƙomu, mamaki, gidadanci gami da ƙauya ci sun gama daskare man kawunanmu ni da Abba, idan Abba ya kafe abu ɗaya da ido tofa ba zai janye idonsa ba har" "sai ya gamsu da bayanin da kwanyarshi ke ma shi na adadin kuɗaɗen da abun ya lashe kafin wanzuwarshi, duk da iskan AC da fankoki ma su wurwurawa da tsanani gudu hakan bai yi nasarar hana gumi tsatstsafowa Abba ba, duk bayan sakanni sai ya kai hannunshi ya shafce gumin da ke barazanar jiƙeshi, sai zare jajayen koɗaɗɗun idanuwansa ya ke ya na shege lafiya, lissafi tun ya na yinshi ya na tafiya daidai har busy yaiwa brain ɗinshi yawa ta daina bashi haɗin kai saboda yanda ya takurata da lissafe-lissafe." "Tsinewa rashin siyo calculator ya saka a cikin aljihu saboda irin haka da yayi yafi sau shurin masaƙi, ni kuwa tun" "lokacin da akai mana iso zuwa wannan danƙareren ɗakin na alfarma wanda ya ke cike da kayan ƙawa da more rayuwa jikina yai sanyi, sai na soma tunanin anya kuwa a cikin duniyar mutane mu ke, ko dai duniyar aljannu Yaya Hashim ya kawo mu, tun ina kallon kayan ƙawa da more rayuwar da aka wadata ɗakin da su cikin tsoro, mamaki gami da al'ajabj, har na ware ina bawa idanuwana abinci nima nabi sahun Abba wajen buɗe idanuwana ina kallon kayan ban mamaki, wato malam arziƙi na inda yake, talaka bawan Allah inji hausawa sukace Talaka buzun banza indan ta mutan gari sai ya mutu." "Saƙe-saƙe da lissafe-lisafe babu wanda banyi ba, amma sam hankali da brein ɗina sun gaza lissafo min adadin yawan" maƙudan kuɗaɗen da aka narka wajen gida wannan gida. "Wa ta dattijuwar ma ta ce ta shigo da kayan uniform a jikinta, a bayanta matasan ƴan mata ne suma sanye cikin" "uniform kalar na ta, sai Yaya Hashim da ke biye da su waya kare a kunenshi da alama waya ya ke." Cike da fara'a matar ta ƙaraso inda muke tare da bawa ƴan matan umarnin ajiye treyn da ke hannuwansu wanda ya ke shaƙe tab da kuloli da jug na alfarma. "Gaishe mu tai tare da ƙare manah kallo ganin irin shigar da ke jikinmu, duk da ba kallon raini ko ƙasƙanci tai mana" "ba amma sai naji duk na muzanta, musamman dana ɗaga kai na kalli yanda kayan uniform ɗin jikinta suka sha guga suka kwanta kuf, sannan fatarta luwai gwanin kyau dan harda siririn glashi a idonta, yaƙe kawai nai ma ta ina sinne kaina ina jin wani iri, atamfar jikina na kalla wacce tana ɗaya daga cikin kayan da nike ji da su, Yaya Sumayya ce ta bani ita a wani zuwa da sukai Katsina biki suka dawo da kaya niƙi-niƙi wanda ƴan uwan Umma suka basu, shine ta ɗaukota ta bani saboda rigar ta yi daidai da ni, saboda bani da ƙiba sam sai dai inada cikar jiki da ƙira me jan hankali." "Janye ƙafafuwa nai tare da ƙudundune su a cikin hijabi, dan ina ɗago kai naga matar ta kafe ƙafafuwan nawa da ido," "ba tun yau ba nasan Allah yai mani halitar ƙafa me kyau da tsari, sautari idan na ina ina zaune da Mama takan janyo" ƙafafuwa ta ɗaura a kan cinyarta ta na shafawa wai burgeta suke. "Abbana yai saurin saukowa ƙasa bayan ya amsa gaisuwar matar cike da fara'a kamar bakinshi zai yage, bayan ta" "gabayar mana da waɗanan kuloli wanda na tabbata cike suke da abinci na alfarma, godiya Abba ya shiga zundumawa kamar sabon maroƙi, nannaɗe hannun riga ya soma yi tare da haɗiyar yawu ji kake ""Maƙwat""." "Kiciniyar buɗe food flasck ɗin ya soma amma ya kasa, gudun kar ya je yai ɓarna ya sa ya kalle ni tare da faɗin." """Ke Mubeenah sauko ki buɗe mana coolar muyi mu ci kafin mutan gidan su fito, dan wallahi Allah cikina ya kwakware kamar ban taɓa cin komi ba, dama dai ɗan ruwan kunu ne wanda Umma ta dama kuma kinsan halinta da baƙar ruwar tsiya ɗan kaɗan ta sammin.""" "Banja da nisa ba na sauko, dan nasan halin Abba tsaf zai dalle ni maruka babu ruwanshi dan yasha faɗi da" "bakinshi cewa shi abin kunya gaba ya bashi ba bayaba, iskanci da abin kunya gadonshi sukai." "Da ƙyar na iya buɗe food flask ɗin waɗanda suke ta faman ɗaukar ido da walwali, zazzafan peper soup ne" "wanda ke ta faman tashin ƙamshi me tado tsohuwar yunwa, ɗayar kuma soyayyen dankalin turawa wanda aka soya da kwai, jug ɗin kuma kunun madara ne fari sol sai daƙƙuwa yakemin, ban san sanda nima na bi sahun Abba wajen haɗiyar yawuba." "Abba bai jira na zuba a plate ba ya suri cinyar kaza ba tare da yayi bisimilla ba ya dirar ma ta, ganin haka ya saka" "nima nai maza na zanyo plate na warci ƙirji da fuffuke na saka tare da ɗan tattare hijabina gudun kar ta ɓaci nai bisimilla tare da far ma ta, lokacin da ɗanɗanon naman ya ratsa kwanyata sai da nai hooking na wucin gadi, idan ma rantsuwa nai to bazanyi kaffara ba tunda nike ban taɓa cin kaza me makamancin ɗadin wannanba, ga shi ta dahu luɓus tai taushi gwanin ɗadi wajen ci, ina ci ina jinjina kwarewar wacce ta sarrafa wannan girki, ba maki ɗari ba ni dai har maki dubu ɗari na bata wallahi." "Jug ɗin kunun na janyo na tsiyaya a ƙaramin cup, tare da zuba dankalin shima a plate ɗin da nike cin kaza, harga" "Allah ina da karah da kawaici amma banda wajen abinci, ina bawa cikina muhimmanci sosai, bare nasan idan na tsaya sanya tsaf Abba wai wawure abincinan tas ya barni da haɗiyar yawu, shi yasa nima ban tsaya cutar kainaba na saki jiki na cika tunbina tsaf." "Abin mamaki duk irin mugun cin Abba sai da ya gaji ya ture kazar nan ya koma kan kunun madara, shima ya ɗaɗɗaka sosai amma bai shanye ba, yo ta ina zai iya shanye wannan kayan gara waɗanda ƙamshinsu kaɗai ya isa ya ƙosar da" "mutum bare ace ya ci, wani abu ɗaya da na hasaso shine, tabbas idan dai ɓangaren masu girki za'a ɗaukeni aiki zan zage in koyi irin waɗanan abubuwan dama na daɗe da burin zuwa koyan girki amma sai Umma ta sakamin mugunta, har makaranta abokin Abba ya taɓa samomin ni da ɗiyarshi amma ta shiga ta fita ta hanani zuwa sai aka ƙaƙabamin zaman shago cikin yare." "Duk abin da muke Yaya Hashim na zaune a gefe yana kallonmu, kunya gami da takaicin halin Abba duk ya cikashi," dama yasan za'ayi haka shi yasa koda wasa bai taɓa nuna ga irin gidan da ya ke aiki ba dan yasan dole wa ta rana irin haka za ta faru. "Bayan na gama ne na suɗe hannuna tas kaɗi da lashe pink lips ɗina kamar banci komi ba, sai lokacin hankalina yakai wajen Abba wanda ya wani bararraje kamar gidanshi, duk ya ɗiga musu miya a jikin carpet da gabanshi rigarshi da" ya ɓata kamar wani ƙaramin yaro. "Kunya ce ta kama ni ganin yanda tai, ina tunanin inda zan samo ma shi ko da tsumma ne ya goge jikinshi kafin masu gidan su iso, amma kash na makara dan kuwa ban gama tunanin mafita hancina ya shaƙomin wani irin sanyayyen daddaɗan turare me saukar da nutsu " "IN SHA ALLAH SAURA ONE PAGE MU KAMMALA FREE, SABODA HAKA MAZA-MAZA KU HANZARTA BIYAN KUƊINKU" DOMIN SAMU DAMAR KARANTA WANNAN LABARI. 9136291920 MARYAM UMAR OPAY. KU SAKA SHIADAR BIYA A WANNAN LAYIN 09136291920 Only watsapp TAKU HAR KUKLUM ME SON GANIN FARIN CIKINKU. MARYAM STAR ZAFIN WUTA Follow the 𝑀𝐴𝑅𝑌𝐴𝑀 𝑆𝑇𝐴𝑅 𝑌𝐴𝑅 𝐵𝐴𝐼𝑊𝐴𝑅 𝐽𝐴𝐽𝐼𝑅𝑇𝐴𝑇𝑇𝑈 𝐻𝐴𝑈𝑆𝐴 𝑁𝑂𝑉𝐸𝐿𝑆 𝐶𝐻𝐴𝑁𝑁𝐸𝐿 channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029Vb5xdoy2975BcTM5m133 𝐙𝐀𝐅𝐈𝐍 𝐖𝐔𝐓𝐀 LABARI ME CIKE DA "BAN TAUSAYI, " "MATSANANCIYAR DAMUWA, KUNCIN CUZIYA, " "SADAUKARWA, " ZAZZAFAR SOYAYYA ME TSAYAWA A RUHI. WRITING BY MARYAM STAR YAR BAIWAR JJRT. MARUBUCIYAR RAYUWAR SAMHAD DAFIN MACIJI A DAREN AURENA AND NOW ZAFIN WUTA *https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341 &mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION* *(J.W.A)* "_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_. " """Jajirtattu mu ne ƙarfi a zuciya, hikima a magana, jajircewa a aiki. Ba mu ja da baya, ba mu faɗuwa. Mu ne tarihi" "da ake ginawa!"" " THE NOBLE WRITER'S TEAM ( DEDICATION IS OUR STRONG ) Typing... PAID BOOK 500 ONLY CHAPTER 50-55 .ميحرلا نمحرلا الله مسب "Me saukar danutsuwa gami da nishaɗi, kafin ingama tunani akan daɗin ƙamshi turare wa ta matashi wacce ta" "ƙawatu cikin uban ado kamar wacce za ta je gasar kyau ta bayyana a parloun, gayu iya gayi ta yi shi amma kuma kallo ɗaya nai ma ta na tabbatar da ta na tare da matsananciyar damuwa, fuskarta fayau babu komi akanta sai man leɓe me sheƙi, idanuwanta duk sun zurma can ciki da alama tayi rashin lafiya saboda sautari akan samu irin wannan ramarne wajen wanda yai rashin lafiya, ko me fama da matsananciyar damuwa." "Siririyar sallama ta yi idanuwanta na akanmu, amsa ma ta na yi ina janye idanuwa daga kallonta, kallon secons biyu" "tai mana sannan ta ɗauke kai zuwa inda Yaya Hashim ke zaune, cike da girmama ya zamo daga kujerar tare da faɗin. ""Ranki ya daɗe Hajiya Sulaima barka da wannan lokacin.""" "A taƙaice ta amsa tare da bashi umurnin mu biyo bayanta, babu ɓata lokaci yai manah inkiya akan mu taso da sauri." "Hakanan kawai na ji gabana ya tsananta dokawa da tsananin ƙarfi, sannan kuma kasala ta baibaye ni da ƙyar na" samu na miƙe akan ƙafafuwana. "Abbama tuni ya miƙe ya na ta faman sakin gyatsa da buɗaɗɗiyar muryarshi. Rufawa Yaya Hashim baya mukai har zuwa wa ta ƙofa ta glass wacce akaiwa ado da kalar gorlding, sai ɗaukar ido ta ke, bayan wannan wacce Yaya Hashim ya kira da Sulaima ta shiga muma muka rufa ma ta baya ni da Abba fuskokinmu fal mamakin irin wannan dukiya da aka narka, a wani ƙayataccen makeken parlou wanda ya gaji da gaɗuwa muka ɓulla, su uku ne zaune akan ƙayataccin kujerun alfarwa waɗanda aka ƙawata wajen da su, Dattijuwa ce zaune kusa da wa ta mata wacce taɗan jingina da jikin Dattijuwar, sai wa ni kamulallen mutum zaune a kujerar kusa da su, kusa da mutumin wacce aka kira da Sulaima ta nufa tare da zaunawa ƙasan ƙafafuwanshi." "Cike ca fara'a Dattijuwar ta ke mana sannu da zuwa, yayin da na sake shiga wani irin yanayi marar misaltuwa ga" "zazzaɓi da ke shirin rufar ma ni nan take, a ƙasƙance muka rakuɓe ni da Abba, mu na jinmu wani iri ganin yanda muka samu mutanen wajen kamar sarakuna saboda ado da kwalliya, mu kuma sai na dinga ganinmu kamar bayi duƙe a gaban sarki ko yarima." "Abba kamar zai taune harshe wajen gaisarda su,ni kuwa cike da nutsuwa na gaidasu ba tare da na kallesu ba." "Mommy ce ta ɗago a hankali ta na gyara zamanta tare da kafe ni da ido kamar me kokonto a kaina, sai kuma ta kalli Pahpah wanda shima dai idonshi a kaina ya ke, ita kuma Hajjo hankalinta na wajen Abba wanda ke ta faman" "zare idanuwa ya na ƙarewa duk abin da idonshi ya sauka akanshi kallo, idan ya kalli abu sai ya lissafi idadin kimanin kuɗaɗaɗen da abin zai iya lashewa sannan ya jinjina kai ya koma wajen wani abun, bayan kamar min tuna biyu da zamanma Pahpah ya kalli Yaya Hashim tare sa gyaran murya sannan ya ce." """Masha Allah, Hisham wannan ita ce ƙanwar ta ka ko? gaskiya na yaba da hankalinta sosai, kuma ina da yaƙini" "akan za ta iya, nutsuwarta da kamalarta sun burge ni ainun, sannan ina fatan itace za ta zame mana abin alfahari anan gaba.""" """Dararammm"" ƙirjina ya doka da tsananin ƙarfi, yayinda zuciyata ke kokowar fitowa saboda razani da fargabar da" nike tsintar kaina a gaban waɗanan mutane. "Aje numfashin Pahpah ya yi daidai da tabbatuwar lissafin da zuciya da kwanyar Abba ya haɗe waje ɗaya, tare da" "gamsar da kanshi wannan ita ce sakayyar yanda gobenshi da ta iyalanshi za ta kasance, dan haka sai ya aro bargon nutsuwa ya yafawa kanshi, tare da ƙoƙarin hana idanuwanshi kalle-kallen abubuwan da suke neman caza tunaninshi." Nutsuwarshi ta yi daidai ta kallonshi da Pahpah yai tare da fara yi ma shi magana ya na karantar yanayinshi. Babban abin da ya burge bai wuce yanda naga Abba ya kame kamar ba shi ba ya na zayyano zantuka masu ma'ana "da dattako, sai na ji wani sanyi da farin ciki ya baibaiyane yau ɗaya Abba ya ɓoye hallayarshi a gaban mutane." BAYAN AWANNI BIYU. "Zaune nike akan mafefen royal bed ɗin da ya mamaye ɗakin, ya yinda idanuwa ke zubarda hawaye wanda ni kaina" "bansan na minene ba, amma zuciyata ta tilasta ni amincewa sa lallai Abba baya so na, ban taɓa kawo afkuwar irin wannan lamarin nan kurkusa a rayuwata ba, ban san mi yasa a kaina Abba ya ke kasancewa me son kanshi ba, muddin lamari ya shafe ni to babu makawa sai Abba ya nuna son kai akaina." "Ɗaure fuska na yi tare da furta ""Abba kenan, ina mai tabbatar maka daga wannan karon rayuwata ta canza," "Abba daga yau bazan sake kasancewa cikin baƙin cikin abubuwanda kake yiminba, daga yau zan tsaya tsayin daka wajen ganin na inganta rayuwta kamar ko wace mace."" Na yi maganar kamar Abban na gabana ko ancemin ya na jin abin da nike faɗa." "Rigar da aka aje kusa da ni marar nauyi na ɗauka, sai da na tabbatar da babu me kallona sannan na shiga warware" "ƙaton towel ɗin da aka kawomin wai in ɗaura idan zan shiga wanka, a jikin ƙaton madubin da ke shaƙe da kayan kwalliya na kalla, ina sake ƙarewa surar jikina kallo ta cikin gashin, wani irin daɗi ne da sanyi ne ya baibaye ni domin kuwa ni kaina nasan Allah yayimin baiwar tsarin zubin hallitta me ɗaukar hankali, sai na ji zuciyata na min wasu saƙe-saƙe aiko nai saurin yin A'uziyya tare da hanama kaina sake yarda da yin makamancin wannan tunanin, cikin sauri na zura rigar tare da mulke jikina da lallausan losion wanda naga an jera, ban tsaya jiran komi ba na ɗauki veil ɗin rigar na ɗaure kaina da shi, sai na kawo hijabina na saka, kallon kaina nai a madubi sai naga na yi wani irin kyau na musamman wanda zan rantse ban taɓa yin irinshi ba, tunawa da wannan matar wacce na ji sun kira da Mommy ta ce inyi sauri ta na jirana, ya saka nai hanzarin juyawa dan infita, sai de kuma na mance inda ƙofar ta ke, duk inda na taɓa sai inga ashe ba ƙofar ba ne, tashin hankali ne ya baibaye ganin ƙofa ta ɓacewa ganina, da ƙyar na rarrashi kaina banyi kuka ba, amma kuma daf ni ke da rafka ihu ko za'a samu wanda zai kawo min ɗauki idan ya jiyo ni." "Ƙarar buɗe abu na ji, cikin sauri na ɗaga kaina dan ganin minene, sai na sauke udanuwa akan wacce na ji an" "kira da Sulaima, ajiyar zuciya na saki ina godiya ga Allah da ya kawo min ɗauki." "Guntun murmushi ta sakarmin tare da ƙarasowa inda nike ta na min magana da turanci, aiko gaba na sake tsallen" "bugu, dan harga Allah nasan ina jin turanci amma da na ji yanda ta ke nata turancin cike da kwarewa da iyayi sai na kasa fahimtar mi ta ke nufi." """Oh sorry, Mubeenah ko! dama Mommy ce ta ce ki zo muje idan kin ƙarasa, tun ɗazu muke jiranki amma shiru" "baki fito ba.""" "Zurum na miƙe tsaye ba tare da na yi magana ba, dan sai na tsinci kaina cikin tsoron buɗe baki inyi magana kar inyi" ba daidaiba in kwafsa. "Ganin na miƙe tsaye ya saka ta ɗauke kai daga kallona da ta ke, a ranta ta ke yabawa da irin kyawun da Allah yai min," "sai de rashin gyara da ƙarancin wayewa ya disashe ƙyalin kyawun nawa, amma duk da haka kallon farko za'a sakani a cikin jerin kyawawa." Bin bayanta ni ke kaina a ƙasa har muka isa wani ɗan ƙaramin parlou wanda babu komi a cikinsa saga na'urar Ac sai "ƙaramin fridge me kyau da tsari sai kujeru masu taushi. ganinmu ya saka Mommy da Hajjo miƙewa tsaye, bayan mun ƙarasa na zame na sake gaidasu ta hanyar yin jimla." Bayan sun amsa Hajjo ta matso kusa da ni tare da kama hanuna ta na faɗin. """Mu je jikata yarinyar kirki, Allah ya albarkaci rayuwarki ya haskaka ki da saiken alkairi.""" Amsawa na yi a cikin zuciyata ina yaba karamci irin na waɗanan mutanen. "Mommy ce gaba sai ni da Hajjo da Sulaima a bayanta, sai da tai ɗan jimmm sannan ta tura ƙofar glashin tare sa Bisimilla ta tura kanta ciki, haka Sulaima ta rufa ma ta baya, yayinda Hajjo ta tura kanta tare da janyo hanuna nima" na shiga. "Wa ni irin mummunan bugu ƙirjina yau, wanda saura taƙi ɗaya rak ya ragewa zuciyata ta wuntsilo ta maƙogarona" "zuwa waje, ban san lokacin da na duƙe a wajenba na shiga maida numfashi da tsananin sauri, hannunawa dafe da ƙirjina, dokawar da zuciyata ke yi na barazanar toshe magudanar numfashina, yayin da wa ta iriyar zufa tare da sanyi suka lulluɓe ni lokaci guda, juyowar Mommy da duƙowar Hajjo a kaina ta na jijjigani ya yi daidai ta isowar Pahpah wajen, cikin hanzari ya matso kusa da ni fuskarshi na bayyanar da annuri gami da tausayina a lokaci ɗaya, kafin kowa ya samu damar cewa komi Pahpah ya duƙa tare da kamo hannuwana ya miƙar da ni tsaye, sai da ya tabbatar da na samu nutsuwa sannan cikin taushin murya gami da rarrashi ya ke faɗin." """Ki nutsu! nutsu kinji mah doughter, ki tausayawa halin da ɗan uwanki musulmi, kuma wanda ke amsa suna miji" "a gareki yanzu ya ke ciki, ke kaɗaice za ki iya ceto rayuwarshi da taimakon ubangijinmu, na baki yardata 100% a karo na farko a cikin rayuwata da na yarda da wani mutum na daban har na yi marabada shi a cikin familynah.""" "Duk da yanda ƙafafuwana ke rawa su na barazanar kayarda ni, amma sauraren kalaman da suka ci gaba da fitowa" "daga bakin Pahpah, wanda nike wa kallon mutum me daraja da karamci, sai na ji zuciyata na bani kwarin gwuiwa, hakan ya saka na shiga gyaɗa ma shi kai, ban san wane zaren ƙaddara bane ya janyo ni zuwa cikin waɗannan ahali masu karamci, ban san cewa amincewar da na yi ba zai zama mabuɗin buɗe ƙofofin ƙaddararon rayuwata, haka kawai nike ji a jikina daga yau kuma yanzu rayuwata ta sauya, sauyi sosai wanda ya banbanta da irin faɗi tashi da tarin ƙalubalen da na fuskanta a rayuwata." "Cike da tausaya Pahpah ya janyo hannuna zuwa ainahin cikin ɗakin, wanda shigata cikinshi ya zaftare abubuwa da" "dama daga ratuwa da burukana, ɗakin da ya zama wajen da zan kafa tarihin wa ta rayuwa me cike da rikitattun al'amurra." "Duk taƙo ɗaya da zanyi, ina aje ƙafata ne tare da bugawar zuciya me tsananin ƙarfi, sannan kuma ina jin wani irin" "ZAFI me kama da ZAFIN WUTA ya na fuskanto ni, a daidai lokacin da na sauke takona na ƙarshe, a lokacin ne zuciyata ta tsaya cak da bugawa, gangar jikina ta kafe akan ƙafafuwa, a sa'ilin da idanuwa suka sauka abin abin da ya nemi hargitsa duniyata a lokacinne kwanyata ta shiga maimaitomin tariyar mafarkan da suka addabe ni a cikin barci musamman kwanakinnan " "ALHAMDULILLAH YAU DAI ALLAH YA AMINCE NA KAMMALA FREE PAGE, YANZU ZAMU SHIGA AINAHIN CIKIN" LABARIN BA TARE DA ƁATA LOKACI BA. DOMIN SAMUN DAMAR KARANTA WANNAN LABARI ME RIKITATTUN LAMURRA KI DAURE KI BIYA NAIRA 500 KACAL A WANNAN LAYIN. 9136291920 MARYAM UMAR OPAY. "NICE TA KU HAR KULLUM ME SON GANIN FARIN CIKINKU""MARYAM STAR KE MUKU FATAN" "ALKAIRI """ WAƊANDA SUKA BIYA PAYMENT SAI MUN HAƊU A BOOK TWO... Follow the 𝑀𝐴𝑅𝑌𝐴𝑀 𝑆𝑇𝐴𝑅 𝑌𝐴𝑅 𝐵𝐴𝐼𝑊𝐴𝑅 𝐽𝐴𝐽𝐼𝑅𝑇𝐴𝑇𝑇𝑈 𝐻𝐴𝑈𝑆𝐴 𝑁𝑂𝑉𝐸𝐿𝑆 𝐶𝐻𝐴𝑁𝑁𝐸𝐿 channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029Vb5xdoy2975BcTM5m133 𝐙𝐀𝐅𝐈𝐍 𝐖𝐔𝐓𝐀 LABARI ME CIKE DA "BAN TAUSAYI, MATSANANCIYAR DAMUWA, " "KUNCIN CUZIYA, " "SADAUKARWA, " ZAZZAFAR SOYAYYA ME TSAYAWA A RUHI. WRITING BY MARYAM STAR YAR BAIWAR JJRT. MARUBUCIYAR RAYUWAR SAMHAD DAFIN MACIJI A DAREN AURENA AND NOW ZAFIN WUTA *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION* *(J.W.A)* THE NOBLE WRITER'S TEAM PAID BOOK 500 ONLY BOOK TWO PAGE 01 ميحرلا نمحرلا الله مسب "Kwance ya ke akan bed wanda ya kasance na glass me kwari, gaba ɗaya jikinshi babu kyan gani saboda" "tako'ina ƙonuwace duk ta dalje, yayinta gangar jikinshi ta ke a buɗe sai iya al'aurarshi kaɗai aka rufe da wani ɗan kyalle fari, ba yau na saba ganin ƙuna ba amma wannan da na gani ta bala'in ɗaga min hankali, da ya ke gaf sosai nike da shi hakan ya bawa zafin hucin wutar da ke cinshi fesomin, wani irin jah da baya nai jikina na karkarwa, yayinda harshena yai nauyin wajen furta koda kalma ɗaya ce, da ƙyar nai nasarar" janyo kalmar. """ Innalillahi, ZAFIN WUTA ke fitowa daga jikinshi."" Na faɗi ina durƙushewa ƙasa a daidai saitin inda" "Mommy ta ke tsaye ta na sharer hawayen da suka ƙi tsayawa, kama ni ta yi tare da miƙar da ni tsaye" sannan ta matse min kafaɗun da tsananin ƙarfin ta na jijjiga ni yayinda matsanancin tashin hankali ya baibaye fuskarta. "Wa ta irinyar fizga na yi na kwace kaina daga riƙon da taimin, yayin da nai baya-baya kamar zan faɗi sai" "kuma na tsaya ƙyam akan ƙafafuwana, wa ta iriyar iska me sanyin gaskece ta baibaye ɗakin, yayinda idanuwa suka sauya launi zuwa kalar shuɗi, da wa ni irin hanzari na sada kaina da inda Fauzan ke kwance ya na barcin azaba, ban san y akai ba sai dai kawai na g hannuna ya ɗaga da kanshi bai suka ako ina ba" "sai akan fuskarshi wacce batad maraba da kwarangwal sai fatar dake rufe da ita, saukar hannuna ke da" "wuya wani irin hayaƙi wanda ke fitar da wuta ya tashi yasa, sake yawata hannuna nai a fuskar ta shi, aiko" "duk inda na saka hannuna sai wannan baƙin yahaƙin ya tashi yai sama, idan yai sama sai ya ɓace ɓat, wa ta iriyar ajiyar zuciyar salama Fauzan ya sauke, yayinda fuskarsi tai wani irin haske fayau, wannan baƙin ƙunar duk ya ɓace, a hankali ya fara buɗe idonshi, hanuna nakai saiyin idon na shi na danna da tsananin" "ƙarfi ina sakin nishi da gurnani, sai ga wani abu na tsiyayowa marar kyan ganni." "Mamaki da tsoro ne ya ya baibaye fuskokin Mommy, Sulaima, Pahpah da Hajjo, yayinda suke ganin" "yanda hayaƙi ke fita daga jikinshi ni kuma wannan hallitar wacce na gani a cikin mafarkina ce nike gani a zahiri kwance akan wannan bawan Allan ta na cinye tsokar jikinshi, idan ta cinye tsokar sai ta hura ma ahi wutar cikin bakinshi a wajen sai ta koma wani wajen kuma." "Hannuna nakan fuskarshi jikina ya fara karkarwa, ban janye hannun nawa ba har sai da ƙafafuwana suka" "lankwashe kansu sukai nasarar kayar da ni ƙasa, wani irin turirin sanyi ne ya fara fitowa daga ƙofofin gargasar jikina ya na yin sama ganyar da wannan hayaƙin ya bi, zubewa nai a kasan wajen a sume." A can cikin daji kuma bayan Sarauniya Zubudiyyace ta biyo bayan baƙin Aljani Zuka wanda jikinshi ya "ƙone sosai da sosai, gudu ya ke tsulawa ya na ketawa ta jikin manya-manyan bishiyu amma sai da Sarauniya ɗiyar sarkin ruwa ta cimmashi, ba tai wata-wata ba ta saka ƙafarta me fitar da tururin ƙanƙara ta danna bindinshi, wa ta iriyar ƙarar azaba ya saki wacce sai da ta karaɗe baƙin dajin, aiko nan ƙananun ƴaƴan aljannu da tsunsaye harma da hallitun da ke rayuwa ciki suka dinga guduwa domin neman wajen ɓuya, dan sarai sun san wacece Sarauniya Zubudiyya ƴar sarkin ruwa, ba ta barin bashi ga duk wanda yai ba daidai ba, launin azabobi iri-iri ta dinga ganawa Zuka wanda tun ya na da ƙarfin karewa har ya haƙura ya saduda ta azabtar da shi yanda ya kamata, sannan ta umurci wasu aljannu akan su kai ma ta shi bakin" kogon hukunci. "Duk wannan dambarwar da aka gudanar ina ganin komi a cikin barcina, yayinda a zahiri na shiga yin wa" "ta iriyar jijjiga ina burgima, Hajjo ce ta matso inda nike ta shiga tofa min addu'o'i, cikin ikon Allah na koma daidai na daina birgimar na daina gurnani sai barci me nauyi da yai gaba da ni." Kallon su Pahpah da mamaki ya gama kashe ta yi tare da faɗin. """Ko zo muje da yardar Ubangiji babu abin da zai faru, sai ma nasara da za'a samu""." "Haka Hajjo ta kaɗa kawunansu suka fice suka barmu, bayan kusan mintuna talatin da faɗuwata na" "farfaro, amma jikina ta ko ina ciwo ya ke min, ga hannuna da yai wani irin jawur sai azabar zafi ya ke min." "Addu'ar tashi daga barci na karanto tare da tashi zaune ina murza ido, buɗe idona ke da wuya na ganni" "awannan ɗakin wanda nai zaton mafarki na yi, a sukwane na kai dubana zuwa wajen gadon da wannan bawan Allan ya ke kwance, aiko karaf idanuwana suka sarƙafe a cikin na shi, wani irin hantsalowa zuciyata tai kamar me shirin fitowa waje, ya na nan kwance kamar gawa, jikinshi ko ina yayi baƙi wasu uwaren kuma duk sun kwalje su na fitar da ruwa irin na ƙonuwa, wa ni irin sanyi ne ke fitowa daga rinannun idanuwanshi ya na shiga cikin nawa idon, da kyar na samu na janye idona daga kallonshi zuciyata na dokawa da ƙarfi, ga wa ta iriyar kasala da ta baibaye ni na gagara ɗaga koda hannuna ne, sai de lumshe ido da nai ina sauraron bugun zuciyata da ya haɗu da wa ta zuciyar wacce ba tawa ba suka" dinga dokawa a tare a cikin ƙirjina. "Ɓangaren Fauzan ma haka ya cinci kanshi cikin wani yanayi me wuyar fassarawa, yayin da wa ta iriyar" "nutsuwa ta baibaye ruhinshi, ga wani irin sanyi me daɗi irin wanda ya daɗe ya na buƙatar samu dan samu sassauci daga halin azabar da ya shiga, amma hakan bai samu ba sai yanzu, bugu da ƙari wani irin dokawa da zuciyar ta dinga yi a cikin ƙirjinshi wanda a baya tai ma shi nauyi kamar andanne ma shi ita da ƙaton dutse, sannan kuma kallon wannan kyakkywar halitar ta wa ta saka shi cikin wani yanayi wanda ya" mance da shi a ɗan tsukinan saboda azabar ZAFIN WUTAR da yake barazanar tafiya da rayuwarshi. A hankali ya lumshe idanuwanshi ya na jin wannan sanyin na safkar ma shi da kasala wacce ke barazanar sauya yanayinshi zuwa wani abu daban. Wasu manyan zungura-zunguran jajayen aljannune suka ɗauki Zuka zuwa kogin hutunta wanda yai wa "Sarki ko Sarauniya laifi, ya na turjewa gami da bayar da haƙuri amma sam babu ki babu gani suka" cicciɓeshi suka wular a cikin wannan kogin wanda ke kwance sai lunƙaya ya ke yana fitar da tururin sanyi. "Lokacin da fatar jikinshi ke sulluɓewa saboda tsananin sanyin azabar da ake gana ma shi, lokacin ne yai" alƙawari gami da alwashi akan wasu mutane guda biyu. AGEGE. Tun bayan dawowar Abba wanda Yaya Haisam yai ma shi rakiya saboda yanda ya ruɗe ya kuma tsorata da irin gigitacciyar kyautar da Alhaji Abdallah me gwalagwalai yai ma shi. Rungume ya ke da ɓakar ƙatuwar jakar da aka loda manya manyan kuɗaɗe wanda suke barazanar ɗauke ji da ganinshi KI BIYA 500 A WANNAN LAYIN SAI MU HAƊE A PAID GROUP. 9136291920 MARYAM UMAR STAR Follow the 𝑀𝐴𝑅𝑌𝐴𝑀 𝑆𝑇𝐴𝑅 𝑌𝐴𝑅 𝐵𝐴𝐼𝑊𝐴𝑅 𝐽𝐴𝐽𝐼𝑅𝑇𝐴𝑇𝑇𝑈 𝐻𝐴𝑈𝑆𝐴 𝑁𝑂𝑉𝐸𝐿𝑆 𝐶𝐻𝐴𝑁𝑁𝐸𝐿 channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029Vb5xdoy2975BcTM5m133 𝐙𝐀𝐅𝐈𝐍 𝐖𝐔𝐓𝐀 LABARI ME CIKE DA "BAN TAUSAYI, MATSANANCIYAR DAMUWA, " "KUNCIN CUZIYA, " "SADAUKARWA, " ZAZZAFAR SOYAYYA ME TSAYAWA A RUHI. WRITING BY MARYAM STAR YAR BAIWAR JJRT. MARUBUCIYAR RAYUWAR SAMHAD DAFIN MACIJI A DAREN AURENA AND NOW ZAFIN WUTA *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION* *(J.W.A)* THE NOBLE WRITER'S TEAM PAID BOOK 500 ONLY BOOK TWO CHAPTER 2 ميحرلا نمحرلا الله مسب "Sai faman zare idanuwa ya ke yana shege lahira, gumin ruɗu da farin ciki sai karyo ma shi ya ke tun daga" "cikin kai ya na bin fuskarshi, a tsakiyar gida ya zauna sai ƙara ƙanƙame jakar ya ke kamar wani zai kwace, Umma ce ta fara fitowa kamar wacce aka hankaɗo, zaninta a hannu sai faman ɗaurashi ta ke amma yaƙi ya bata haɗin kai wajen ɗautuwa ta daɗi, ya yinda ta ke ta faman washe washeshen bakinta kamar zai rabe biyu, matsowa ta yi kusa da Abba tare da yunƙurin janyo jakar za ta ƙwace, wani irin wawan" bahagon mari Abba ya sauke ma ta tare da sake ƙanƙame jakarshi ya na juya ma ta baya. "Sak Umma tai jin saukar gigitacen marin da ya kusa tarwatse ji da ganinta, lokaci guda ta kai ƙasa taɓas" ta na ƙifta idanuwanta. Mama na tsaye ƙofar ɗakinta bata ce komi ba dan ita yau ta fita harkar kowa na gidan saboda rabata da "ni da Abba yai, a hakama wai dan batasan abin da ya faruba a can gidan aikatau ɗin." Ganin Abba ya kasa magana ya saka Yaya Hashim fara yi musu bayanin komi dalla-dalla. Abin da ya faru bayan Pahpah ya tabbatar da Abba ne Babana. "Musabaha sukai bakin Abba kamar zai ɓare, sannan Pahpah ya nemi da su keɓe ya na da" "muhimmiyar magana, ba musu Abba ya bishi jiki na rawa." """Amm dama Malam ba komi ne ya saka na nemi keɓewa da kai ba sai wa ta alfarma da nike nema a" "wajenka, nasan abin da nauyi amma kuma insha Allah ina abin zai zama alkairi a goben yaranmu.""" """Haba Alhajin Allah, ai kawai ka yi maganarka kanka tsaye babu kwana, yo Allah na tuba ai kawuce" "neman alfarma a wajen talaka irina sai dai ka bada umurni.""" Jinjina kai Pahpah ya yi tare da nazarin maganar Abba sannan ya nisa ya ce. """Ita yarinyar da za ta yi aikin jinya ƴarka ce???.""" "Sai da gaban Abba yai mummumar bugawa, wa ni tunani ya gifta ta cikin kanshi, sannan ya yi saurin" waske wa ya ce. """Am..ih...ih yarinyata ce, duk duniya bata da wani uba da ya wuce ni.""" """Ma sha Allah, to ina neman aurenta, ka bawa ɗana aurenta.""" Kwalalo ido Abba ya yi tare da zamo ɗuwawunshi daga kan sopa ya shiba in ina kafin da kyar ya ce. """Aure kuma, aure fa kace Alhajin Allah.""" Abba yai maganar wani irin farin cikina baibaye fuskarshi. """Ih aurenta nike nemawa ɗana Fauzan wanda shine za ta yi jinyar, to ganin ita yanzu yarinyace" "matashiya bai kamata ace ta keɓanta da wanda ba muharraminta ba ne, sannan kuma akwai wasu dalilan da ya saka na ce haka, na kuma yaba da nutsuwar ita yarinyar, ka yanke ma ta sadaki daga milion" "daƴa har zuwa inda tunanika ya yanke.""" "Naman fuskar Abba ne ya shiga rawa, yayinda jajayen idanuwanshi suka yo waje, lissafi da kwancewa ya" "shiga yi a kwanyarshi, amma duk yanda ya so ya lissafa adadin da zai faɗa abin ya gagara, da kyar ya fizgo maganar daga bakinshi ya na haɗiyar yawu ya ce." """Alhajin Allah ai ina ganin da kuɗin tambaya da na lefo da sadakin ku bada miliyan biyar kawai Allah" "ya basu zaman lafiya.""" """To babu laifi hakan, zan bada milion goma gaba ɗaya, amma banda lefe wannan kam mu zamuyi ma ta," "yanzu ka sanar da wakilanta da waɗanɗa suka kamata su sa ni, zuwa anjima bayan sallar la'asar sai a" ɗaura auren dan da buƙatar ayi shi cikin gaugawa saboda akwai wasu magunguna da wani babban me "bada magani a India ya bani, kuma ya tabbatar min da idan akai amfani da maganin ta hanyar da ya dace in sha Allah za'a samu dacewa.""" """Allah sarki, to idan babu damuwa mi zai hana a ɗaura ayanzu kawai sai Yayanta Hashimu ya wakilceta," "tunda maganar gaskiya mu ba ƴannan bane, a ƙarance za'a iya ɗaukar sati ɗaya ba tare da an haɗo kan dangi ba saboda kowa da inda ya ke rayuwa.""" "Pahpah amincewa yai ba tare da ya ja zancen ba, shi ta samun lafiyar ɗan shi kawai ya ke." Limamin da ke jan Sallah a cikin masallacin cikin gidan aka kira tare da tsirarun ma'aika masu nutsuwa da "hankali sai Yaya Hashim, su ne waɗanda suka shaida ɗauruwar igiyoyi uku kwarara akan MUHAMMAD FAUZAN ABDALLAH, da amaryarsa MUBARAKHA MUHAMMAD IBRAHIM." "Auren da ya ɗaurewa mutanen da suka shada kai, domin kuwa abin da ɗaure kai musamman da sukaga" "Abba a matsayin uban amarya, a kaf garin Legos babu wanda bai san wanene ABDALLAH ME GWALAGWALAIBA." "Cike da fatan samawa Fauzan mafita Pahpah ke addu'ar Allah ya dawwamar da albarka a cikin aure, tare" "da fatan ƙulluwar alaƙa me tsananin ƙarfi a tsakanin ma'auratan biyu, waɗanda akaiwa kutse cikin rayuwarsu aka zartar da hukunci ba tare da amincewa ko sahalewar su ba, tausayina ne ya luluɓe Pahpah ya na ganin kamar an shiga haƙƙina da yawa, duba da zamanin yanzu da ƴan mata da yawa su" keyiwa kamsu zaɓin abokan rayuwa. Abba bakinan har kunne ya na ta gandala da godiya ga Allah da ya kawo shi wannan rana wacce za ta "kafa tarihi a rayuwarshi, ranar da baƙin talauci me kama da ZAFIN WUTA zai yaye, arziƙi dawamamme ya" "maye gurbinsa, albarkar da ya daɗe da ɗebemin yau ita ce ya ke zundumamin babu ƙaƙƙautawa," "albarkar da niban san yana yi ba, tun da ba agaban idona ya ke ba." Numfashi Yaya Hashim ya sauke tare da satar kallon inda Mama ke tsaye ta na aiko musu da mugun "kallo wanda ya nemi ya hautsina ma shi hanjin ciki, Abbama kallonta ya ke duk jikinshi ya yi sanyi, sai yanzu yaga rashin kyautawar abin da ya aikata ma ta, sanin kanshi ne akaf gidan babh wanda mukai sabo" "da shaƙuwa da shi irin Mama, komi na samo Mama, idan wani abu ya same ni to Mama ce zata zauna" tare da ni. "Umma kuwa dukda cewa ta maru ba kaɗanba, dan Abba ya shammaceta lokacin da tazo karɓar jakar" "hannunshi, ya ƙe ta shiga yi ta na nuna murna da farin cikin auren da aka ɗaura min babu shiri, ta na ganin hakan shine ya dace da ni tunda bani da wani gata." "Shigewa ɗaki Mama ta yi tare da fashewa da kukan baƙin cikin halin Abba, ta tabbata kuɗi ya gani ya" "bayar da aurena haka kamar auren kaza, ta yi kuka harta godewa Allah kafin daga bisani ta shiga jero" addu'oin nema min kariya aduk inda nike 500 ONLY ZA TA BAKI DAMAR KARATUN LITTAFINAN CIKI SALAMA 9136291920 MARYAM UMAR OPAY TAKU HAR KULLUM MESON GANIN FARIN CIKINKU MARYAM STAR KE MUKU FATAN ALKAIRI . Follow the 𝑀𝐴𝑅𝑌𝐴𝑀 𝑆𝑇𝐴𝑅 𝑌𝐴𝑅 𝐵𝐴𝐼𝑊𝐴𝑅 𝐽𝐴𝐽𝐼𝑅𝑇𝐴𝑇𝑇𝑈 𝐻𝐴𝑈𝑆𝐴 𝑁𝑂𝑉𝐸𝐿𝑆 𝐶𝐻𝐴𝑁𝑁𝐸𝐿 channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029Vb5xdoy2975BcTM5m133 𝐙𝐀𝐅𝐈𝐍 𝐖𝐔𝐓𝐀 LABARI ME CIKE DA "BAN TAUSAYI, MATSANANCIYAR DAMUWA, " "KUNCIN CUZIYA, " "SADAUKARWA, " ZAZZAFAR SOYAYYA ME TSAYAWA A RUHI. WRITING BY MARYAM STAR YAR BAIWAR JJRT. MARUBUCIYAR RAYUWAR SAMHAD DAFIN MACIJI A DAREN AURENA AND NOW ZAFIN WUTA *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION* *(J.W.A)* THE NOBLE WRITER'S TEAM PAID BOOK 500 ONLY BOOK TWO CHAPTER 3 ميحرلا نمحرلا الله مسب Yayinda baƙin cikin halayar Abba da Umma ya mamaye zuciyarta har ta na jin kamar ta tashi ta barmusu "gidansu kawai, tunda dama da ita da babu du ɗaya ne, sunan ta na zaune ne kawai amma zaman haƙuri" da jure halin Abba kawai ta ke. "Umma kuwa kwantar da kai ta yi ta lallaɓa Abba ya bita ɗaki, can sukai lissafinsu ba tare da sun nemi" "Mama ba, sai da daddare da lokacin cin abinci ya yi aka aiki Yaya Sumayya ta kirawo ta, da farko kamar ba za ta je ba dan tunanin halin da nike ciki ya ƙi barinta, Abba bai sanar ma ta na warke daga makanta ba, amma ko mi ta gani sai kuma ta tashi ta je, tun da tai sallama ta kai dubanta inda su Abba ke zaune da tarin kayan kwalam da makwalashe a gabansu ta jinjina lallai ba ƙaramar duniya Abba ya samo ba, kaji ne ƙosasshi aka banƙare tare da yi musu kyakkyawar gashi sai sheƙi da ɗaukar ido suke, kusan guda biyar aka jere a ƙaton faranti, sai lemon jarka kaloli shina an jere sai kuma robobin take away da" yogofura. "Mama bata ce komi ba ta shiga ta zauna ba tare da ta kula kowa ba, Abbama bai kulata ba dan ta bashi" "tsoro yanda yaga ta ɗauki lamarin da zafi, bayan anzubama kowa abin da yake so suka shiga ɗibar daɗi babu me tunawa da ni sai Mama." "A slow na lumse manyan fararen idanuwa masu ɗaukar hankali, sai kuma na sake buɗesu warrrr na" "watsasu akan Fauzan wanda har yanzu bai janye idanuwanshi daga gare ni ba, da yake Pahpah ya yi ma shi bayani akan matsayina sai ya shiga tunani a zuciyarshi." "'Ita kuma wannan kyakkyawar halittar zunubin mi ta aikata da za'a haɗata aure da ni, amma dai" "gaskiya ba'ayi ma ta adalci ba sam, kuma wannan ai san kai da tauye haƙƙi.'" "A hankali na tashi zaune ina jin ko ina na jikina na yi min ciwo, jingina na yi a jikin bangon glashin ɗakin, a" hankali cike da tsoro da kuma tsananin tausayin halin da ya ke ciki na sake dubanshi sannan na ce. """Sannu bawan Allah, Allah ya baka lafiya ya sa zakkar jiki ce.""" "Lumshe idons ya yi yayinda sanyi da daɗin sautina ya ratsa har cikin kanshi, kamar ba zai amsa ba sai" kuma ya sake dubana sannan ya ce cikin harshen turanci. """Thank you""." "A taƙaice, kuma bai janye idonshi daga kallona ba." Kamar daga sama na sake jiyo amon raunanniyar muryarsa wacce ta ke fita a hankali kuma can ƙasa sosai ya na faɗin. """Dan Allah ki taimaka min da ruwa d lemo a cikin wancan fridge ɗin""." Ya sake faɗa da turanci. "Ban musa ba a hankali na tashi tsaye ina ji na kamar bazan iya tsayuwarba saboda rashin kuzari, amma" "na daure na tilastawa kaina tsayuwar harma da fara takawa dan cika umurninshi, ina zuwa gaban fridge ɗin kai na yai wa ta irin sarawa, tsikar jikina na mimiƙewa ta na yamm yammm amma haka nai addu'a tare da buɗe fridge ɗin, lemon da ya faɗa min sunanshi na sauke idona a kanshin, amma sai zuciyata ba ta kwanta da shi ba, dan haka sai kawai na sauke hannuna akan wa ta robar lemon tare da ɗauko wa na" ɗauki ruwa na kulle murfin da ƙarfi. "A gaban ɗan table ɗin da ke wajen na ajiye tare da ɗauko cup na shiyaya ma shi ruwa, kallonshi na yi" ina faɗin. """Ga su ammafa da zaka daure ka tashi zaune da sai ka fi jin daɗin sha.""" "Ɗan waro idanuwa ya yi jin abin da na ce, sai ya yi murmushi kawai tare da miƙomin ƙonannen" hannunshi alamar in taimaka in tada shi. "Kamar ba zan yi ba, sai kuma na kama hannun na shi wanda ke fitar da ƙarni da warin ƙonuwa, a" "hankali na ja hannun da niyar in tada shi, amma sai na ji bai ko motsaba, hakan ya saka na yanyo ɗayan hannun shima na janyo shi da tsananin ƙarfi, sai da ya saki nishin azaba, dan na yi nasarar tada shi zaune daga wajen da shi kanshi ya mance rabon da ya ganshi an tada shi, ko mi za'ayi ma shi sai dai a yi ma shi" shi daga kwance. "Saura kaɗan in sake shi inyi baya dan tsoro, duka manyan idanuwana na waro waje ina karanto addu'o'i" a fili tare da kawar da kaina gefe ina bawa hawayen da na bansan da taruwarsu ba damar fitowa. "Ƙarni da wari ne kawai ke tashi a wajen ga fatar bayanshi nan tanƙare a kan glasa bed ɗin, sai tsutsotsi" "da ke ta faman sintiri a wajen, da mugun hanzari na kalli bayanshi wanda ya sille ya saluɓe tas babu ko" fata sai sauran tsokar da ta rage a jikinshi itama tai jajur ga tsutsaotsi nan manya da ƙanana su na sunturi akai. "Wani irin sanyi me sanya nutsuwa ne ya ke safkarwa Fauzan, ga wani irin daɗi da ya baibaiye shi jin na" "raba shi da wannan azabar da yake ciki, yasan za'a iya samun fiye da abin da na gani dan kuwa shi kaɗai ya san mi yake ji a jikinshi, sannan wannan sanyin da tun zuwana ɗakin ya baibayeshi daga azabar da" yake ciki sai yanzu ya gane daga gare ni ya ke. "Cike da ƙarfin zuciya da tsananin tausayi na lallaɓa na janyo shi zuwa ƙasa, sai nishi da shesheka ni ke yi," "na yi ina ƙoƙarina wajen ganin na zaunar da shi, amma abin ya ci tura, ban san lokacin da na cire hijabin" "jikina ba na ɗauki gorar ruwan sanyin da na ɗauko na tsiyaye shi akan hijabin tas, wasu ƴan tuntaye na" "gani a gefe da su na yi amfani na shimfiɗasu agefe sannan na shimfiɗa hijabina a ƙasansu, cike da dabara" na kwantar da shi na gefe tare da tare shi da wannan tuntayen gudun kar ya kwanta ta bayan. A jiyar zuciya ya sauke me ƙarfi tare da lumshe ido ya na jin sanyin abayata na ratsa ƙonannen jikinshi. "Ƙoƙarin zare hannuna daga na shi na yi, amma ya hana hakan faruwa ta hanyar riƙe nawa hannun da" "kyau, saurin kallonshi na yi sai naga idonshi na kan ruwan da na zuba a cup, ni na manta shaf wallahi, dan hankalina sam baya jikina ganin irin halin da yake ciki, da ɗayan hannuna na yi amfani wajen ɗauko ruwa, a hankali na zauna agabanshi na fara yin tofin ayatul shufah a cikin ruwan sannan na yi bisimilla" tare da kaiwa ga busashen bakinshi... ƳAN ALBARKA MASU JIRAN DOCUMENT INSHA ALLAH NAN DA KWANA BIYU ZAI SAUKA DA ZAFINSA AKAN NAIRA 500 KACAL CIKIN SAUƘI RANGWAME DA RAHUSA฀. KU HANZARTA BIYAN KUƊINKU TA WANNAN ACCOUN ƊIN 9136291920. MARYAM UMAR OPAY. TAKU HAR KULLUM ME SON GANIN FARIN CIKINKU. MARYAM STAR KE MUKU FATAN ALKAIRI. Follow the 𝑀𝐴𝑅𝑌𝐴𝑀 𝑆𝑇𝐴𝑅 𝑌𝐴𝑅 𝐵𝐴𝐼𝑊𝐴𝑅 𝐽𝐴𝐽𝐼𝑅𝑇𝐴𝑇𝑇𝑈 𝐻𝐴𝑈𝑆𝐴 𝑁𝑂𝑉𝐸𝐿𝑆 𝐶𝐻𝐴𝑁𝑁𝐸𝐿 channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029Vb5xdoy2975BcTM5m133 𝐙𝐀𝐅𝐈𝐍 𝐖𝐔𝐓𝐀 LABARI ME CIKE DA "BAN TAUSAYI, MATSANANCIYAR DAMUWA, " "KUNCIN CUZIYA, " "SADAUKARWA, " ZAZZAFAR SOYAYYA ME TSAYAWA A RUHI. WRITING BY MARYAM STAR YAR BAIWAR JJRT. MARUBUCIYAR RAYUWAR SAMHAD DAFIN MACIJI A DAREN AURENA AND NOW ZAFIN WUTA *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION* *(J.W.A)* THE NOBLE WRITER'S TEAM PAID BOOK 500 ONLY BOOK TWO CHAPTER 4 ميحرلا نمحرلا الله مسب "Da sauri ya amsa tare da zuƙe ruwa, janye cup ɗin na yi ina tsananin tausaya ma shi, kafin in dire cup ɗin" "na ji wani irin kakari gami da nishi, sauri juyo da kaina na yi, aiko nai arangama da shi ya na sheƙa uban amai, ruwan da ya sha, ya amaye tasss tare da wasu irin abubuwa marasa kyan gani masu fitar da wani irin wari. rasa abin yi na yi sai kawai na fashe da kuka me ƙarfi da sauti, har lokacin ina riƙe da hannunshi" cikin nawa. "Mommyce ta yi taga-taga kamar za ta faɗi, dan dukkan abin da ke faruwa akan idonta, ji ta yi anyi saurin" "taro ta, buɗe rinannun idanuwanta waɗanda suka rine saboda kuka ta yi tare da kallo tsakiyar nashi idanuwan waɗanda ke cike da zallar ƙauna da matsanancin tausayinta, sake shigewa jikinshi ta yi tare da fashewa da kuka me sauti, rarrashin ta yayi tare da kwantar ma ta da hankali, gefe ɗaya kuma ya na jinjinawa ƙoƙarin da nayi, dan shima tun lokacinda yaga tahowarta ya biyo bayanta dama ya tsaya wajen bada umarnin a dafawa Fauzan shari da abu me ruwa wanda zai iya sha, da kanshi ya tsaya ya taho da" "basket ɗin bayan an gama haɗa komi, shine ya tsaya kallon irin ƙoƙarin da nike yi shima." Kamo hannun Mommy Pahpah ya yi tare da ɗaukar basket ɗin ya shigo da iya ɗakin. "Har yanzu kuka nike na rasa yanda zanyi, kaina gaba ɗaya ya kulle da tausayin halin da Fauzan ke ciki, jin" sallamar su Pahpah ya saka na ɗan tsahirta daga kukan amma ba dainawa na yi ba. "Mommy ce ta ƙaraso tare wajena itama ta na zubda hawaye, ba ta jira komi ba ta rungume ni tsam a" "ƙirjinta ta na shafa bayana, mun daɗe rungume da juna kafin daga bisani ta sake ni ta na kissin face ɗina tare da jero min godiya da addu'a cikin harshen turanci." Pahpah ma sannu ya jera min tare da saka min albarka sannan ya miƙomin wani ƙullin magani tare da "basket ɗin hannunshi, bayani ya yi min akan yanda zanyi amfani da maganin sannan ya janyo Mommy da ke zubda hawaye har lokaci suka fice badan ta so ba." "A je kayan hannuna na yi tare da bin wa ta madaidaiciyar ƙofa da na gani a buɗe, ina shiga naga ashe" "toilet ne ƙerarre amma na glashi sai dai shi ba'a iya ganin cikinshi, amma wanda je ciki zai iya ganin abin" da ke waje. "Ruwa na tara cikin wani butiki da na gani, na ɗauki wani towel da aka shanya a jikin hanger, sannan na" ɗauki detergent powder tare da freshner na zuba da moper na fice. Fauzan tun da na tashi daga wajen na shiga toilet ya dainajin wannan sanyi wanda ke saukar ma shi da "nutsuwa, a hankali ya fara jin wannan zafin me kama da ZAFIN WUTA ya na tasowa a hankali a hankali" "har ya fara baibaye dukkan ilahirin jikinshi, runtse ido ya yi yana sauraren yanda azabar zafin ke saƙe" konashi. "Tun da na fito daga toilet na dinga jin wani huci na me haɗi da zafi ya baibaye ɗaƙin, ina tafiya ina jin" "yanda hucin zafin ke nesa da ni, ina ƙara matsawa ya na ɓacewa har ya ɓace ɓat, wa ta iriyar wawiyar ajiyar zuciya Fauzan ya sauke lokacin da sanyin da ke tattare da ni ya baibaye duniyarsa ya na saukar ma" shi da wa ta iriyar kasala da nutsuwa. A hankali na duƙa kusa da inda ya ke na shiga gyara wajen ba tare da na damu da warin da aman ke "fitarwaba, ina yi ina tazbihi gami da godiya ga Allah da ya wadata ni da lafiya, tsaf na gyara wajen sannan na kwashe kayan na kai toilet na zubar da ruwan na kunna shower ta wanke wajen, tap ɗin ruwan zafi na kunna na sirka ruwa daidai misali sannan na fito da su zuwa inda Fauzan ya ke, ba tare da jin ko ɗar ba na duƙa gabanshi na dinga saka ƙaramin towel ɗin cikin ruwa ina matsewa, na shiga goge ma shi fuska" ba tare da na damu da yanda jikinshi ke fitar da ƙarni gwanin kyankyami ba. "Tas na goge ma shi fuskar wajenda ya kwalje kuma na saka maganin da Pahpah ya bani, komawa na yi" "wajen hannuwanshi suma na durje su tasss sukan ba laifin sun ƙone sosai gaskiya dan kusan duka fatar na darje tare da barbaɗa maganin sannan na tashi na canzo wasu ruwan amma wannan karon harda detol na saka a ciki da kuma sumfi na farkon yawa, komawa bayanshi wanda ya caɓe babu kyan gani na yi, tsayawa tunanin ta inda zan fara na yi, dan harga Allah bayan na shi bayu kyawun gani, hakanan na karanto bisimilla tare da aro bargon juriya da haƙuri ina tuna saboda aikin jinyarshi aka kawo ni gidan kuma aka aura man shi ba'a son raina ba, ina tilastawa kaina dole na yi aiki tuƙuru kodan biyan bashin" maƙiden miliyoyin kuɗin da Abba ya tafi da su. "A hankali na naanaa ma shi towel ɗin tare da gogawa, wa ta irin ƙara marar sauti ya saki tare da jujjuya" "kanshi ya na sakin numfarfashin wahala da azaba, cike da tsoro na ja da baya ganin yanda na ɗago da towel ɗin yayi caɓa caɓa da jini da kuma danƙararriyar dauɗa wace ta manne da ƙananun tsutsotsi, kamar ba zan iya ba na aje towel ɗin sai kuma na sake ɗauka na ɗauraye a cikin ruwan na kuma mayarwa akan bayan ba tare da na kalli wajenba, sake wankewa na yi amma wannan karon a hankali ba da ƙarfi ba, sau uku na wanke bayan badan ya fita ba na barshi hakanan sai dan saboda warin da ƙarnin da suka addabe ni, cikin sauri na tashi da kayan na kai toilet tare da sakarma bukitin ruwan shower dan bazan iya wanke su da hannuna ba, na ga worshing machine amma rashin iya amfani da shi ya saka banyi gigin zuwa inda yake aje ba, wanke hannuna nayi sosai sannan na koma na ɗauki maganin na saka" audiga na dinga goga ma shi a hankali a wajen. "A jiyar zuciya na sauke lokacin da na gama saka magananin, sosai na yabawa kaina dan kuwaba kowace" "mace ce zata iya yin abin da na yi ba, wajen basket ɗin na koma na ɗauko madaidaicin cup na shiyayi ruwan tea ɗin da aka zuba a ƙaramin flasck wanda ke ta tashin kayan ƙamshi, na buɗe gwangwanin madarar da aka saka da vornbiter na zuba nai haɗin kauri, babu sugar saboda haka nai amfani da zumar da aka sako cikin wani ɗan ƙaramin cup, juya tea ɗin na yi da tea spoon har na tabbatar da babu zafi sosai sannan na sake matsawa inda ya ke kwance kamar gunki nai bisimilla tare da nufar bakinshi da cokalin da na zuba tea ɗin, bai musamin ba ya buɗe bakin cikin sauri, ganin ya amshi wanda na bashi ya saka na yi dabarar saka mashi cup ɗin abaki dan sauƙaƙama kaina wajen bashi, aiko tunda ya kafa kai bai" "tsaya ba sai da ya zuƙe tea ɗin tas, da yake da yawa na zuba mashi ba laifi " 500 KACAL ZA KI MALLAKI NA KI฀ TAKU HAR KULLUM ME SON GANIN FARIN CIKINMU. MARYAM STAR KE MUKU FATAN ALKARI ZAFIN WUTA Follow the 𝑀𝐴𝑅𝑌𝐴𝑀 𝑆𝑇𝐴𝑅 𝑌𝐴𝑅 𝐵𝐴𝐼𝑊𝐴𝑅 𝐽𝐴𝐽𝐼𝑅𝑇𝐴𝑇𝑇𝑈 𝐻𝐴𝑈𝑆𝐴 𝑁𝑂𝑉𝐸𝐿𝑆 𝐶𝐻𝐴𝑁𝑁𝐸𝐿 channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029Vb5xdoy2975BcTM5m133 𝐙𝐀𝐅𝐈𝐍 𝐖𝐔𝐓𝐀 LABARI ME CIKE DA "BAN TAUSAYI, MATSANANCIYAR DAMUWA, " "KUNCIN CUZIYA, " "SADAUKARWA, " ZAZZAFAR SOYAYYA ME TSAYAWA A RUHI. WRITING BY MARYAM STAR YAR BAIWAR JJRT. MARUBUCIYAR RAYUWAR SAMHAD DAFIN MACIJI A DAREN AURENA AND NOW ZAFIN WUTA *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION* *(J.W.A)* THE NOBLE WRITER'S TEAM PAID BOOK 500 ONLY BOOK TWO CHAPTER 5 ميحرلا نمحرلا الله مسب Ganin ya shanye tea ɗin tas ya saka na janyo food flask ɗin na zuba ma shi joloup ɗin taliyar da akaiwa "tsarariyar dahuwa sai turirin ƙamshi ta ke, a nutse na bashi ya ci, ba laifi ya ɗanci sosai, ruwa na bashi me gauraye da magani, sannan na gyara ma shi kwanciyar na tashi na shiga toilet na ɗauro alwala, ficewa na yi daga ɗakin ina neman ɗakin da na sauka ɗazu gami da ƙarewa babban parloun gida kallo ina yaba kyau da tsarin da ya yi, bayan na gane ƙofar ɗaki na shiga tare da zuwa wajen da aka tanadar dan yi" sallah wanda aka shimfiɗa prayer mate da cazbaha harsa al'ƙur'ani me girma sai ƙaramin littafin azkar. Bayan am fito da Zuka daga kogin azaba wasu aljannun suka ɗauke shi suka yasar a can ƙarahen baƙin "daji, sukai tafiyarsu suka barshi ba tare da tausayin halin da yake ciki ba, da kyar ya daure azabar da yake ji ya ɓace zuwa kogon da boka ya ke ciki, boka na zaune ya na haɗa magungunan surkullensa kawai ya ji faɗowar abu ya na nishi gami da fitar da hucin azaba, ga wani irin zafi da ya fara mamaye kogon, cike da razani boka ke kallon yanda zuka ke fitar da numfashi ga jikinshi duk yayi fari alamar ƙonuwa, zai buɗe baki kenan yai magana kawai Zuka ya feso ma shi wani baƙin hayaƙi daga wawakeken bakinshi, nan take ya faɗi a wajen kamar gawa, cikin matsananciyar azaba Zuka ya kamo hudar gashin bokan ya shiga zazzage ma shi cutar da azabar da ke cikinshi, sai da ya gama juyewa bokan ciwon jikinshi tas sannan ya" tashi a galabaice ya bi ta jikin bangon dutsen ya ɓace ɓat yabar boka kwance cikin mawuyacin hali. ABDFA GROUP OF COMPANY. "Su biyu ne masu tsananin kama da, duk iya kokonton mutum ba zai iya banbance su ba sai dai idan su ne" "suka nemi a gane su, fararene tas masu matsakaicin kyau sai, amma fuskokinsu cike suke da haiba da kwarjini, hannuwansu sarƙafe da juna, hatta takon ƙafafuwa tare suke saukewa kuma au ɗaga a tare, idan suka haɗu da wanda suka sa ni sukan ɗaga ma shi hannu tare da sakar ma shi tattausan murmushi, gaban jibgegiyar motarsu suka nufa, ɗayan ya kai hannu na yaɗewa ɗayan, a maimakon ya shiga shima sai ya koma can ɗayan ɓarin ya buɗewa ɗaya, murmushi suka saki atare dare da zagayowa kowa ya shiga ƙofar da ɗan uwansa ya buɗe ma shi, babu ɓata lokaci driven motar ya ja da wani irin spich suka fice" daga companyn. """My bee, zamuje mu duba jikin friend, kwana biyu kenan bamu je ba, kuma akwai wasu magunguna" "da nike so in gwadawa Pahpah ya gwada yi ma shi amfani da su za'a dace da yardar Allah.""" "Ɗayan ya faɗi fuskarshi da damuwa, numfashi ɗayan ya sauke shima fuskarshi na zancaza zuwa tsananin" damuwa dannan ya ce. """Ok My bee, mu biya mu gaida shi ɗi.""" Babu wanda ya sake magana a cikinsu sai tunani da kowanensu ke yi. "Bayan na gama sallah tare da karatun azkar wani irin nannauyan barci ya kwashe ni, barci nike yi sosai," "ga sanyi AC da rashin hayaniya da ya sake taimakamin wajen yin barci cikin daɗin rai, ban samu farkawa ba sai daf da kiran magrib, shima dan ban saba barci lokacin sallah ba, koda kuwa barci ya ɗauke ni babu jimawa aka kira sallah, tofa haka zan tashi in kakkaɓe barcin, dan sam bana wasa da lokacin sallah, addu'ar ta shi daga barci na yi, gamin daga bisani na tashi na cire hijabin da ke jikina na nufi toilet, ba da niyyar yin wanka na shiga ba, amma dana gwada zuba ruwa a bahon wanka naga sun taru gwanin sha'awa sai na ji ina so inyi wankan, dan haka sai na ɗauki wasu robabi da ake aje turarukan wanka na bulbula sosai a ciki, sannan na cire rigata na sulala ciki, kai arziki rahama, na faɗi a zuci yayinda daɗin ruwan da ƙamshi ya ratsa ni, sai na nemi kasalar da nike ji ta barci na rasa, yayinda na shagala ina wasa da ruwan ina murje lallausar matata wacce na ji ta sake yin laushi dana shiga ruwan, sai ji na yi in kwalla kiran sallah a masallcin da nike da tabbacin daga cikin gidan ya ke, da hanzari na kammala wankan na fito ba tare da na tsiyaye ruwanba, towel na gani ɗan ƙarami sai na ɗauke shi na ɗaura cikin hanzari," "rigar da na cire kuma na jefata a cikin bahon wankan, acewata idan na gama Sallah zan dawo in wanke ta, a gaggauce na yi alwala na fito, turus na tsaya ina tunanin yanzu ya zanyi ga shi banga jakar kayana ba, sai na yanke hukuncin zan ari ɗaya daga cikin waɗanda naga ankawo ɗazu an aje, ban tsaya wata-wata" "ba na buɗe sif ɗin na zaɓo wani lallausan manterial me taushi, na antaya rigar a jikina sannan na shafa" mai tare da fesa turare ina ji na yau wasai. "Hajjo, Pahpah, Mommy da Sulaima su ne zagaye da Fauzan su na ta yi ma shi fira, fuskokinsu cike da" "farin cikin ganin sauye-sauye da dama, sai shi mani albarka suke tare sa gasgata lallai ni ɗin alkairi ce, da yake Pahpah ya basu labarin bayanin da me magani ya yi mashi, akan indai aka samu me irin baiwata" "tabbas zai rabu da lalurar gaba ɗaya, tunda dama sihiri ne akai ma shi da ɓakin aljani." "Fuskar Mommy yau wasai babu kuka sai mumushi wanda ya ƙi yankewa daga fuskarta, ita ko hajjo abin" "ba'a magana iya arziƙin zama lafiya lau ba tare da wannan tururin ya addaba musu ba kaɗai ya isheta farin ciki, a dah daurewa kawai suke su zo duba shi amma Alla-Allah ta ke su fita saboda zafin da ke" mamaye ilahirin ɗakin wanda ke hanata nutsuwa. "Su na ahaka su na firar duk da Fauzan barci ya ke amma basu tafi ba, hakanan sukai zamansu zagaye da" "shi, ana cikin haka ne me kula da shigowar baƙi ta sanar da zuwan wasu baƙi, basu damar shigowa Hajjo ta yi, anan ne suka shigo hannuwansu sarƙafe cikin na juna, ga fuskokinsu faɗaɗe da murmushi." """Ah lalle marhaban da zuwan Al-Hassan da Al-Hussain, kune tafe da yamma haka, ku ƙaraso daga ciki.""" cewar Hajjo cike da murnar ganinsu. "Wa ta iriyar mummunar bugawa zuciyar ɗayan ta yi, ganin Fauzan kwance a ƙasa ga magani a jikinshi," "sannan babu wannan tururin da ke fitowa daga jikinshi, wa ta iriyar muguwar ashar ya kutuntuma acikin" "zuciyarshi, yayin da a fili fuskarshi ta ke normal kamar yanda ta ɗan uwanshi ta ke. " 500 NE KUƊIN IDAN KIN SHIRYA BIYA GA ACCOUNT 9136291920 MARYAM UMAR OPAY. 𝐙𝐀𝐅𝐈𝐍 𝐖𝐔𝐓𝐀 LABARI ME CIKE DA "BAN TAUSAYI, MATSANANCIYAR DAMUWA, " "KUNCIN CUZIYA, " "SADAUKARWA, " ZAZZAFAR SOYAYYA ME TSAYAWA A RUHI. WRITING BY MARYAM STAR YAR BAIWAR JJRT. MARUBUCIYAR RAYUWAR SAMHAD DAFIN MACIJI A DAREN AURENA AND NOW ZAFIN WUTA *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION* *(J.W.A)* THE NOBLE WRITER'S TEAM PAID BOOK 500 ONLY BOOK TWO CHAPTER 6 ميحرلا نمحرلا الله مسب "'Mike shirin faruwa ne, waye ya sakama Fauwa wannan maganin, shin wai tayaya hakan ta faru, ina" Zuka da alƙawarin da yai min???.' "Haka yai ta jera tarin tambayoyi a zuciyarshi, amma babu amsa." Bacin sun gaisa da su Pahpah suka aje ƙatuwar ledar da suka kawo kayan dubiya tare da yi ma shi fatan samun lafiya sannan suka tafi fuskokinsu da jimami. Albarka su Hajjo suka shiga saka musu tare da yabama karanci irin na su. AGEGE ABBA "Durƙushe ya ke a gaban wani gini da aka yi shi da zallar zinariya, ga kudaɗe na ta shawagi a ata ko ina, Ni" "kuma ina zaune a saman kuɗin ina ta sakarwa Abba murmushi, gefe ɗaya kuma wani ƙaƙƙarfan farin mutum ne me ƙira irinta sadaukai tsaye a can bayana ya na aika min da kallon irina so da ƙauna, yayin da wa ta wuta ke tahowa ta bayanshi har ta iso ta mamaye shi gaba ɗaya, wani irin kukan kura na yi tare da" dirkowa daga kan katangar na isa wajen wutar sa dugu na janyo mutum ina kakkaɓe ma shi wutar da ke "ƙona shi ina kuka, yayin da na sauka daga kan katangar wasu mutane masu tsananin kama su biyu suka" "ɓillo ɗaya daga cikinsu na nufo inda ni ke ina kuka tare da yayyafawa wannan mutumin ruwa ina kakkaɓe ma shi wutar, ya na isowa ya shiga taimaka min muka kashe wutar a tare, yayinfa Abba da" ɗayan suka nufi wajen katanfar da aka gina na gold suka haye tare da juya manah baya. "A mugun firgice Abba ya farka daga mafarki da yayi, yayin da ya shiga sakin shehseka tare da ajiyar" "zuciya me ƙarfi, kallonshi ya kai wajen jakar kuɗinshi, sai yaga an canza ma ta yanayin ajiya ba haka ya" "ajiye ta ba, da sauri ya diro daga kan kadon ƙarfen Umma ya na sakin ashar." """Uban ɓarawo ya zurma ya afka ya hwaɗa ya zumduma cikin satar min ƙudi, na rantse da kabarin" "kakana bazan yarda ba."" sai ya buɗe iyakar muryarshi ya kwarara uban ihu tare da nufar jakar ya buɗe ta, ilai kuwa an ɗibi kuɗin sai dai ba sosaiba, ɗaurin dalla ɗaya kaɗai aka ɗauka, ajiyar zuciya ya sauke me ƙarfi tare da rataye jakar a hammata ta shiga kwalla kira har sai da ya tada kowa na gidan." "Zuciyar Umma ce ta hau luguden duku da ƙarfi, sai sharce gumi ta ke, yayinda ta tura hannunta can" "bayan gado ta saki ɗaurin kuɗin da ta sha baƙar wahala wajen satowa, da kyar ta aro baigon jarumtar ɓoye halin da ta ke ciki ta tashi ta na murza idanu kamar me barcin gaski." """Abba wai lafiya zaka tashi mutane a tsohon darenan, wani abu ya faru da kulinne.""" """Inafa lahiya Umma ana neman a yashe ni tsaf, wallahi babu zaman lafiy ga duk wanda ya taɓa kuɗinan" "dan wallahi gidan wannan abokin me dallar Me rauhanai zanje a binciko min wanda ke farautar rayuwata ta hanyar barazanar taɓa min dukiya, na rantse da sittin ta Ubangiji bazan bar ko waye ya" "zauna lafiya.""" "Wa ta iriyar tusar tashin hankalice ta kuncewa Umma, yayinda dana sa nin ɗaukar kuɗin Abba ya" "baibaye ta, ta manta da waye Abba akan kuɗi, Abba zai iya tuɓe riga ya daku da uban kowa akan kuɗinda basu taka kara sun karya ba, nadama ce baibaye ta yayinda zuciyarta ke luguden duka." """Ahaf ai dole ne kiyi hutu Ummakatiti kina can ki na barci za'a yashe ma ki tattalin arziƙin miji, Allah" "kaɗai yasan irin haɗarin da na tsallake wajen samun kuɗinan, amma wani banza ƙaramin ɓatawo me fama da bakin uwa ya zo zai yashe ni, nasan abin da zanyi wallahi bazan zauna hakanan sake ba.""" """Ah..ih...eh wallahi Abba ya kamata asan abin yi tun kafin lamarin yai nisa, ko kuma muje banki gobe da" "sahe mu binne kuɗin a can babu wanda yaji bare ya gani.""" Umma ta yi maganar ta na ƙyafta idanu yana shege lahira. "Mama kuwa duk abin da suke ta na jiyo su, amma ba ta nuna tasan su na yi ba, dan zuwa ta yi ta ɗaura" "alwala ta fara jero salloli ta na kaiwa Allah kokenta, tare da roƙon Allah ya shiryar da Abba akan hanya madaidaiciya, sannan ta jero min addu'ar kariya da taimakon Allah aduk inda nike, ba ita ta gama sallar ba sai da ta ɗauki tsawon lokaci sannan ta shafa tare da tashi ta naɗe kayan da ta yi Sallah ta adana sannan ta haye kan gadonta tana tunanin ranar da zaren ƙaddara ha haɗa ta da Abba har ya janyo ta" zuwa ga wannan rayuwar me cike da son kai. FLASH BACK IKORODU "Anan ne unguwarda Malam Sa'idu ya sauka tun bayan barowarshi daga ƙauƴen Kura, ya sauka a" "unguwar tare da iyalinshi gaba ɗaya, inda suke rayuwa cikin sauƙi kasancewar ya taho da guzurinshi bayan rasuwar mahaifinsu da aka raba gado aka bashi kasonshi, ya na da mata ɗaya me suma Zulai da ƴaƴa uku Halima ita ce babba sai ƙanwarta Zubaida da ƙaninsu Sagiru, Malam Sa'idu mutum ne me tarin ilimin addini, a ƙauyen Kura shine limami a ungursu wanda ya ke jan su sallar juma'a, abin da yai sanadiyar barowarshi daga Ƙauyen har ya shigo duniya shi ne, mahaifinsu na da mata uku sannan akwai ƴaƴa masu yawa kusan ƴaƴa talatin da ɗoriya, Balarabe shine mahaifinsu, mutum ne me tarin dukiyar noma da kiwo, yana ɗaya daga cikin manyan attajiran da ake ji da su a kaf ƙauyen, to kafin rasuwarshi ya bar wasiyya akan abawa Sa'idu babbar gonarshi wacce yake noman shinkafa a cikinta, sannan ya ware wasu daga cikin shanaye ya ce lallai idan ya riga Sa'idu barin duniya to abashi nashi ne halak malak basu cikin gado, nan akai rubutu Balarabe ya rantaɓa hannu akan takarda sannan akabawa me garin garin ya aje a wajensa, babu jimawa Balarabe ya kamu da ciwo wanda ya sha jinya sosai har daga ƙarshe ya riski ajalinshi, bayan sadakar arba'in ƴaƴanshi suka hura wuta akan rabon gado wannan yasa me gari ya zo da kanshi ya warware takarda ya karanta kuma yabawa kowa ya duba, nanfa aka shiga tashin hankali, domin ƙiri-ƙiri saura suka nuna rashin amincewa da hukuncin, me gari bai bi takansu ba ya saka malaman fada suka raba gado sannan aka bawa Sa'idu kasonshi da kuma wasiyyar mahaifinshi, tofa" "wannan wasiyya sa aka bashi ta zama tashin hanƙali ƙiri-ƙiri ƴan uwanshi suke neman rayuwarshi, hakan" ya saka yaje wajen me gari ya damƙa amanar gonarshi da abin da za'a noma tare da isassun kuɗi wanda "zasu isa ayi komi, ya tattara sauran gadonshi ya sayar ya haɗo kan iyalanshi ya yo kudu dan tsira sa rayuwarshi da ta iyalinshi." Halima yarinyace nutsatsiya ta na da hankali sosai ga tarin ilimin Mahammadiya da samu wajen "mahaifinta, bata zuwa ko ina kullum su na gida zaune abinsu, amma wani lokaci takanbi mahaifinta kasuwa inda ya ke saida kayan gwari." Ta na shekara ashirin da biyu wani abokin kasuwanci Malam Sa'idu yaganta ya yaba da halayyarta da "nutsuwarta, nan take yai wa ƙaninshi sha'awar aurenta, bai yi nauyin baki ba ya tari Malam da maganar," ya nuna jin daɗi sosai kuma ya bada goyon baya ɗari bisa ɗari dan ya yaba da karancin Usman ƙani ga abokinshi Abubakar... "WANNAN LITTAFI DAI NA KUƊI NE, IDAN KIKA BIYA 500 ZA KI SAMU DAMAR KARANTA COMPLETE " TA KU HAR KULLUM ME SON GANIN FARIN CIKINKU MARYAM STAR 𝐙𝐀𝐅𝐈𝐍 𝐖𝐔𝐓𝐀 LABARI ME CIKE DA "BAN TAUSAYI, MATSANANCIYAR DAMUWA, " "KUNCIN CUZIYA, " "SADAUKARWA, " ZAZZAFAR SOYAYYA ME TSAYAWA A RUHI. WRITING BY MARYAM STAR YAR BAIWAR JJRT. MARUBUCIYAR RAYUWAR SAMHAD DAFIN MACIJI A DAREN AURENA AND NOW ZAFIN WUTA *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION* *(J.W.A)* THE NOBLE WRITER'S TEAM PAID BOOK 500 ONLY BOOK TWO CHAPTER 7 ميحرلا نمحرلا الله مسب "Ba'a ɗau lokaci ba Abubakar ya sanar da Usman akan ya je ya ga Halima su daidaita, Usman matashi ne" "me biyaya ga umarnin na gaba da shi, hakan ya saka bai ja da nisa ba ya je ya ga Halima, kallon farko ya afka cikin kogon sonta dan kuwa Halima takai a so ta a kallon farko, ta haɗa duk wani abu da namiji me hankali zai buƙata a wajen mace, ga nutsuwarta wacce tai bala'in tafiya da shi, shi mutum ne me son nutsuwa, a ɓangaren Malam Sa'idu ma ya sanar da Halima da zatai baƙo, cike da ladabi ta amsawa mahaifin na ta, bayan zuwan Usman sai ta ga ya kwanta ma ta sosai saboda mutum ne me nutsuwa da" "kamala, sam bashi da hayaniya irinta samarin zamani." Bayan komawar Usman gida ya samu yayanashi Abubakar ya sanar da shi ya na son Halima dan ya yaba "da hankalinta, idan babu damuwa aje kawai ai magana ba sai anja lokaci ba." "Sosai malam Sa'idu ya ji daɗin maganar sa abokinshi ya zo ma shi da ita, bai ja da nisa ba bayan ya koma" "gida ya nemo Halima ya tambayeta akan shin ko ta amince, abinka da mace me kunya da tarbiya bata" "amsa ma shi ba sai duƙewa da ta yi ta gagara ɗagowa ta kalli mahaifin na ta, ya ji daɗin wannan abin da ta yi dan haka ya sallame ta ta tafi ya zanta da mahaifiyarta." "Bayan kwana biyu aka tsaida maganar aurensu nan da wata ɗaya, saboda wani aiki da ya tasowa Usman" "ɗin zai je wanj couse a ƙasar waje, kafin aure wa ta iriyar ƙaƙarfar soyayya da shaƙuwa ce ta ƙulu tsakanin Usman da Halima, sun yarda da junansu sun tsara rayuwa me tsari wacce take cike da soyayya, sai de su na tasu Allah na tashi, tsarinsu kawai suka sa ni, basu san tsarin Ubangiji me kowa me komi ba, shi yasa ake so ɓu rage buruka da shagala da duniya, domin duniya ba matabbata bace, babu wanda ke sa shaida ko alamar dawwama da ratuwarshi, ita mutuwa bata sallama ko aike, idan ta zo ɗauka kawai ta ke, dan haka dan Allah ƴan uwa musulmai mu rage burika, mu dinga tunawa da mutuwa a cikin" "al'amuranmu, kada rayuwar ko ruɗin duniya su shagaltar da mu, Allah ya kyautata ƙarshen mu amin." BAYAN WATANNI BIYU. Bayan auren Usman da Halima da wata ɗaya suka tarkata zuwa chaina dan Usman zai gabatar da wani "aiki wanda aka ɗaukesu su uku a companyn da ya ke aiki, tare da halima suka tafi, acan suka gudanar da rayuwa me tsafta da tsari, sai da sukai shekara ɗaya da rabi sannan suka dawo Nigeria, sosai ƴan uwa da abokan arziƙi waɗanda ke kusa sukai murnanar dawowarsu tare da tarin nasarori, ɗaya bayan ɗaya suka dinga zaga gidajen ƴan uwa na kusa dana nesa, a lokacin Halima na ɗauke da tsohon ciki haihuwa yau ko" "gobe, Usman sai nan nan ya ke da cikin dan kuwa yanzo baya jin nauyi ko junyar kowa wajen bata" "kulawa, ko da gidan Malam Sa'idu suka je haka zai manne ma ta babu ruwanshi da ganin idon surukai." "Wa ta rana bayan dawowarsu daga gidan Abubakar da daddare naƙuda ta tasowa Halima, wanda ya" "saka Usman ya kira gida ya sanar sannan ya tashi ya ɗauki mota ya tado me aikin da ya samo ma ta suka nufi asibiti, sai dai basu samu isa ba Allah yai nashi ikon, a daidai lokacin da wa ta ƙatuwar mota wacce akayo lodin shanu burkinta ya kwanta ta daki motar Usman, a lokacin ne Halima ta samu nasarar sauke abin da ke cikinta zuwa wannan duniyar me cike da tarin al'amurra masu kyau da maras kyau, a lokacin da jinjirar ta saki kukan godiya ga Ubangiji, a lokacin ne numfashin Usman na ƙarshe ya fice daga ƙirjinshi" bayan ya yi nasarar karanto kalmatusha shahada a rarrabe. Halima bata san abin da ya faru ba dan tsoro da firgicin abin da ya faru ne ya saka ta haihu ba tare da ta "sa ni ba, sai farfaɗowa ta yi ta tsinci kanta akan gadon asibiti ƙarƙashin kulawar likitoci, tun da ta farfaɗo ba ta cewa kowa komi ba sai kallon likitocin da ke ta aikin bincike akanta ko akwai wa ta matsala, amma" "cikin ikon Allah babu matsalar komi, hakan ya saka suka sallameta kawai." "Lokacin da suka koma gida babu wanda ta kula dan sam batai magana ba, amma duk wanda ya ambaci" sunan Usman ko hatsari tofa za ta kafe shi da ido ta na kallo babu ƙaƙƙautawa. "Halima bata dawo daidai ba sai da ta kwashi tsawon watanni uku, babu irin maganin da ba'a nemo ma ta" "ba amma ko ina maganar ɗaya ce lafiyarta ƙalau kawai ta shiga halin ruɗu ne wanda ya mantar da ita komi, amma za ta dawo daidai da yardar Allah, hakanan iyayenta suka zubawa sarautar Allah ido su na taya ta da Addu'ar samul lafiya." "A wata rana Mama da Zulaha suka ɗauki Halima da jinjirarta wacce ta ci suna Fatima, zasu kaita asibiti" "saboda zazzaɓin da ta ke fama da shi, akan hanyarsu ta dawowa sun tsaya jiran go slow ya rage wani ɗan ƙaramin gatsari ya auku, inda mashina guda biyu suka yi karo da junansu suka faɗi, wa ni tartsatsi ne ya gifta ta cikin kan Halima, yayinda aka tariyo ma ta yanda sukai hatsari ita da Usman, nan take ta fasa" ƙara tare da kwalla kiran sunan Usman ta ƙarfi sai kuma ta faɗi a sume. CIGABAN LABARI. "Saurin ta shi Mama ta yi jin amfara kiran sallar asubahi, ta na jinjina irin daɗewar da ta yi ta na tunanin" "rayuwarta ta baya, sake tashi ta yi ta je ta ɗauro alwala ta sake jero wasu sallolin kafin a tada asubahi." "Zarya ya ke ta faman yi a cikin makeken ɗakinshi, yayinda ya ke dunƙule annayenshi duka biyun ya na" "saiwa iska naushi a haukace, sai faman huci ya ke kamar kumurcin maciji." """Waye wannan wanda ke wasa da rayuwarshi ta hanyar shiga gonata, wallahi ko wanene sai naga" "bayanshi tunda har yai gangancin shiga hurumin da ba nashi ba, dole ko waye zai biya wannan bashin da rayuwarsa.""" "Ya na gama faɗin gakan ya juya da sauri ya nufi wajen wasu manyan lokoki ya buɗe, ya janyo wa ta jaka," "buɗe jakar ya yi ya shiga fito da wasu ƙullin abubuwa ƴan ƙananu, zuwa ya yi bakin door ya kulle tare da" "batin key ɗin a jiki, sai ya nufi wajen labulaye ya sakesu duka, kashe wutar ɗakin ya yi sannan ya kunna" "hayaƙi tare da yin tsirara haihuwar uwarshi, sannan ya shiga kirari ya na kwalla kiran sunan ZUKA." "Duk abin da ya ke Zuka na tsaye jikin gini ya na kallonshi, sai da ya galabaita da sosai wajen kiranshi" sannan ya buso wani ɓakin hayaƙi me wari sannan ya bayanna a sufar jegare me amon wuta. Sauke numfashi ya yi tare da ɗagowa ya na haki kamar wanda ya tiƙi uban gudu sannan ya ce a galabaice. """Ya zakai min haka! ba haka mukai da kai ba Zuka ba haka mukai yarjejeniya ba, na riga da na gama yi" "maka dukanin abin da kake so, na sadaukar maka da jinin waɗanda suke da muhimanci a rayuwata ta yaya zaka yi haka, waye wa warware aikin, da idona na ga anzuba ma shi magani, kuma yanzu har iyayenshi na can zaune tare da shi su na hira su na raha, bama wannan ne babban abin da ya dameni ba," shin ko kasan har yanzu babu wani ci gaba a company har yanzu banga alamar wancan tsohon banzar zai "miƙa ragamar komi a hannuna ba, na gaji! na gaji!!! na gajiiiiiiiiiiiii.""" Yai maganar da ƙarfi jijiyoyin jikinshi na firfitowa yayin da idanuwanshi suka koma launin jah. Cikin amo marar daɗin saurare gami da firgitawarta Zuka ya fara magana a suffar dabbah. """BA DAGA NI BA NE, SU NE SUKA LALATA AIKIN DAGA WAJENSU, YANZU HAKA TASIRINA YA RAUNATA" "SABODA SUN ƘONANI DA RUWAN KOGIN HUKUNCI, A HALIN YANZU BA ZAN IYA KOMI BA DOLE SAI NA YI JINYA ME TSAWO, SAI DAI KA SA NI BA KOWA NE ZAI IYA IRIN AIKIN DA NA YI MAKA, MUSAMMAN YANZU DA SUKE DA DANGANTAKA DA SARAUNIYA ZUBIDIYYA ƳAR SARKIN RUWA, KUNE KUKA JEFANI A HALIN DA NIKE CIKI YANZU, SABODA HAKA ZAN RABA JINYAR TARE DA KU.""" "Ya na gama faɗin haka ya huro iska me ƙarfi daga bakinshi zuwa jikin matashin, sai da ya suma dan azaba," "ya na suma Zuka ya saka hannunshi ya dafa bayan matashin, nan take wasu abubuwa suka shiga fitowa daga jikin Zuka da ke a suffar Jegare ya na sauka akan bayan matashi." "Bayan ya gama juye ma shi cutar ya tashi ya fice da sama ba tare da ya sake bi takan matashin ba, sai dai" ya tattara kayan ya maida a ma'ajiyarsu tare da buɗe ɗakin. "Barci nike ina juyi cike da nishaɗi, sanyi AC da lallausar katifarda aka shimfiɗe akan gadon na sake" "taimaka wajen saka ni nannauyan barci me cike da nishaɗi, tun bayan da na yi sallar asubahi na koma na sake kwanciya, dan Allah na gani ina mutuwar son yin barcin safe amma sam bana samun damar yi lokacin da nike gida." "Ba ni na farka ba sai wajen sha ɗaya na safe, shima Hajjo ce ta tada ni dan tare muka kwana da ita a" ɗakin sai dai kowa gadonshi daban. "Hajjo dattijuwa ce me tsananin kirki da sanin darajar ɗan Adam, sam banyi tunanin samun karɓuwa a" "wajen mutanen gidan har haka ba, iya jiya kaɗai sun nuna min gata, kulawa gami da godiya akan bajintar da nayi wajen kulawa da lafiyar ɗansu, yanda suke nan nan da ni kaɗai ya tabbatar min da su ɗin na daban ne ko a cikin masu kuɗi, kuma na ji zan iya jure ko wace iri wahala wajen ganin na hidimta musu da gangar jikina, na ɗaura ɗamarar bautata musu ba tare da gajiyawa ba, indai har zasu dawwama su na nuna min kulawa kamar wanda sukai jiya, na taso cikin rashin kulawa a gidanmu, babu me kukawa da ni sai Mama ita kaɗai, to itama wani lokacin ba cikakkiyar lafiyace da ita ba, ina daga cikin mutane masu son kulawa koda ba za'ayi min duka abin da nike so ba matsawar za'a kula da ni to ambiya ni duniya da" lahira LITTAFIDAI PAID BOOK NE ZA KI BIYA 500 NAIRA. 9136291920 MARYAM UMAR OPAY. TAKU HAR KULLUM ME SON GANIN FARIN CIKINKU. MARYAM STAR KE MUKU FATAN ALKAIRI 𝐙𝐀𝐅𝐈𝐍 𝐖𝐔𝐓𝐀 LABARI ME CIKE DA "BAN TAUSAYI, MATSANANCIYAR DAMUWA, " "KUNCIN CUZIYA, " "SADAUKARWA, " ZAZZAFAR SOYAYYA ME TSAYAWA A RUHI. WRITING BY MARYAM STAR YAR BAIWAR JJRT. MARUBUCIYAR RAYUWAR SAMHAD DAFIN MACIJI A DAREN AURENA AND NOW ZAFIN WUTA *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION* *(J.W.A)* THE NOBLE WRITER'S TEAM PAID BOOK 500 ONLY BOOK TWO CHAPTER 8 ميحرلا نمحرلا الله مسب "Tashi na yi na shiga toilet ɗin ɗaki wanda ya gaji da haɗuwa, Allah na gani toilet ɗin ya tashi kaina," "ƙauyanci ko ba'a magana, sai dai intaɓa nan in taɓɓa can inata jin daɗi, ni kaina nasan banada yawan fara'a bare murmushi, idan kaga murmushi ko dariyata to ina gaban Mama ne muna fira, amma wallahi zuwana gidannan jiya na yi murmushi sau babu adadi, iya kalon kayan ƙawar da aka ƙawata gidan kawai" ya isa ya saka ni murmusawa bare kuma yanda aketa ririta ni. FAUZAN "Tun bayan da muka gama firar dare muka yi ma shi sallama tare da fatan samun lafiya, kallona kawai ya" "ke, ga amsa kuwar muryata da ke ta faman yi ma shi gizo a kunnuwa, maganata biyu tun da Hajjo ta ja ni zuwa ɗakin, duk da su na ta saka ni a firar amma sam na ƙi sakin jiki inyi firar, ganin yanda fuskokinsu suka washe da fara'a kawai ya isheni farin ciki, ga Mommy da duk motsin da zanyi sai ta tambayeni ko ina buƙatar wani abu ne, ko ta sakar min murmushi tare da yimin godiya, yanda naga su na ji da Fauzan" sai abin ya burge ni na ji inama ace nima haka nawa Iyayen sa dangi ke so na. "Fauzan tun da muka tafi ya ke ta tunanina, kuma ya lura idan ina waje to wannan sanyin wanda ke sakar" "ma shi da kasala ya kuma saka ma shi nutsuwa yana wajen, amma da zarar na tafi sai ya dainajin sanyi, ji ya yi kamar ya tsaida ni duk da ba magana ni ke ma shi ba, amma kuma sai ya kasa yin hakan, ya na ji ya" na gani na fice banko waiwayeshi ba. "Bayan na gama ƙauyancin na tara ruwa a baho na tuɓe kayana na afka ciki, wani mugun daɗin ruwan ne" "ya baibaye ni, aiko na sake nutsewa ina lumshe ido gami da wasa da hannuna da ruwan cike da nishaɗi, na ɗauki tsawon lokaci a haka kafin daga bisani na yi wankan na fito ina zuba ƙamshin turaren wanka," banga towel ba dan haka na maida kayanda na saka na zumbula hijabina na fito. "Sulaima ce zaune a bakin gado su na gaisawa da Hajjo cikin harshen turanci, mamaki ne ya kama ni jin" yanda Hajjo ta lamkwashe harshe kamar baturiya ta na zayyano turanci tiryan-tiryan a bakinta. Jin sallamata ne ya saka su duka suka juyo su na kallona fuskokinsu da murmushi. """Ƙanwata harkin fito kenan, tun ɗazu na shigo Hajjo ta ce min kin shiga wanka ba ki fito ba.""" Sulaima tai maganar ta na tashi tsaye cike da kulawa ta miƙo min jakar hannunta ƴar madaidaiciya me kyau. """Ih wallahi na shiga wanka ne shi yasa na daɗe ban fito ba.""" Na bata amsa tare da miƙa hannu na karmi jakar. """Kayan da za ki saka ne, kiyi sauri muna jiranki a main parloun zamuyi breack.""" Tai maganar ta na duba tsadadiyar agogon diamond ɗin da ke ɗaure bisa tsintsiyar hannunta. "Kallonta na sake yi cike da burgewa, dan Allah ya sa ni ina matuƙar son mace me gayu da ado, shi yasa" "ko a gida tamu bata zo ɗaya data Umma ba, dan ƙazama ce ta bugawa ajarida, yayinda Mama kuma ta kasance mace me tsananin tsafta, gashidai bata da kayan ƙawa da ada irin na Umma, amma idan ta yi wanka ta caɓa ado kai ka ce ba matar Abba ba ce, dan sam Mama bata yi kala da matar da Abba zai aura" "ba, kalar matan Alhazawan masu kuɗi ne." "Har na aje jakar nufina inje mu karya sannan in dawo in saka, sai kuma na yi gudun kar ace dokar" "gidance haka, tun da ƴan gayu ne ƙila sai anyi ado da kwalliya sannan ake zama cin abinci, ɗaukar jakar na yi ina buɗewa sai naga atamfa ce ɗinkakkiya wacce ta sha guga a linke tsaf, fito sa ita na yi dan insaka, ban san lokacin da n doka tsallen murna ba, Allah ya sa ni ina natuƙar son inyi gayu musamman ace sababin kaya na samu, amma ba damar hakan dan Abba bai damu da yimin ɗinki ba daga sheka sai shekara, haka zanga Yaya Sumayya na caɓa ado abinta, ni ko inta sha'awarta ina binta da kallon burgewa," idan na isheta da kallo kuma tayi ta hantarata ta na zagina wai na isheta da kallo sai kace mayya. "Ɗas ɗinkin goduwar rigar ya zauna a jikina, yayinda gaba da bayan rigar ya ci ado da stons masu sheƙi da" "walwali, wani ƙarin abin burgewa shine atamfar da ɗinkin sun amshi jikina sun zauna ɗass, da ya ke atamfar me ɗan duhu ce sai ta sake fito da ainahin hasken fatata wanda rashin kyara ke barazanar" "disashewa, ban iya stayle na ɗaurin kallabi ba hakan ya saka na kama gashina na gyara na ɗaure shi da" ɗan ƙaramin ribon wanda na siyo a shagon kusa da shagon Abba wanda ni ke tsarewa. "Da kyar na tattare gashin saboda silɓi da tsawonshi sai de bai cika irin yawannan cinkus ba, yafi tsawo" sosai amma babu yawa. Ganin yanda gashin gaban goshina ya kwanta luf ya saka na ɗauki wani mai gaban miro wanda nike "tunanin na gashi ne na zuwa a hannuna sannan na shafe goshin nawa, aiko sai gashin ya sake kwanciya ya lafe tare da yin ƙyalli gwanin burgewa, ban shafa komi ba sai iya turare da na malala saboda ina son ƙamshi, sai na shafa lips glow me danƙo wansa ya taimaka wajen fito da ainahin pink lips ɗina, sake ɗauko jakar da Sulaima ta bani na yi na zazzage, saiga mayafi me shara-shara marar nauyi ya faɗo, tare sa takalma plate masu kyau, ɗuka na yi na safa a saman kai tare da gyala shi ta kafaɗata sai na zura" takalmin wanda ya zauna a ƙafata ɗas gwanin sha'awa. "Juyi na yi tare da ƙara juyawa ina ganin yanda na yi bala'in kyau, ni kaina nasan yau na yi kyan da ban" "taɓa yin irinshi ba tun tasowata, wani sassanyan murmushi ne ke fitowa a fuskata na tsananin murna da jin daɗi, yayin da a zuciyata nike ta yiwa su Pahpah da Mommy addu'a dan wallahi na ji daɗi sosai da sosai." """Ma sha Allah laƙuwwata illabillah, wallahi kinyi azabar kyau Mubeenah.""" "Sulaima da ban san lokacin da ta shigo ɗakinba na ji ta faɗa gami da takowa inda nike, ban ce komi ba" "sai murmushi da na yi najin daɗin yabon da tai min, kama hannuna ta yi muka fice tare da haurawa sama mukai wajen dinning ta na ta yaba kyawun da na yi." Fuskarsu a sake suke kallona yayinda muka isa wajen na zame hannuna daga cikin na Sulaima na "tsugunna ina gaidasu a jimlace, cikin kulawa suka amsa min tare da tambaya ya baƙunta, bance moki ba" "sai murmushi da na yi, wajen Hajjo da aka shimfiɗa ƙaton lallausan carpet, ancija gabanta da kayan kari" "na nufa, zaunawa na yi tare yi ma ta tata gaisuwar cike da bata girma." """Hajjo barka da safiya, antashi lafiya, ya gajiya.""" """Lafiya ƙalau Mubaraka ya gajiyarki, ai kece da gajiya ƴarnan, sannu jiya kinsha fama da marar lafiya," "mun gode sosai Allah yayi albarka.""" Hajjo ta faɗi ta na janyo ni zuwa gabanta. """Hajjo ki kyaleta hakanan ta samu ta karya za ta bawa Yaya Fauzan magani.""" Sulaima ta faɗi ta na dire plate ɗin hannunta wanda ta zubo soyayyar doya wacce ta yi caɓa-caɓa da "kwai da vegetables da yanyanka ƙanana a cikin kwan, sai ɗaukar ido soyayyar doyar ta ke, ga sous da aka zuba agefe da kechop harda yankaken carbege, yanda aka jere komi a cikin farantin kwanin sha'awa, sai kunun cous-cous wanda ya wadatu da madara sai ƙamshin flavor ya ke, ajiyewa ta yi a gabana sannan ta" tashi ta ɗauko tea flask ta ajemin tare da janyo min kwankwanayen kayan tea. """Bisimillah, ki yi ki ci kar surutun Hajjo ya cika miki ciki.""" Sulaima ta faɗi tare da zama itama ta haɗa nata kayan garin. "Murmushi kawai na yi ina hasaso inama ace tare da su Mama zanci wannan kayan alfarmar, duk sai na ji" "jikina ya yi sanyi, kewar Mama na sake bijiromin ina tunanin yanzu ko mi ta ke yi, ko wane hali take ciki." "LITTAFIN ZAFIN WUTA PAID BOOK NE, ZA KI BIYA 500 KACAL DOMIN KI MALLAKI NAKI." 9136291920 MARYAM UMAR OPAY TAKU HAR KULLUM ME SON GANIN FARIN CIKINKU. MARYAM STAR KE MUKU FATAN ALKIRI . 𝐙𝐀𝐅𝐈𝐍 𝐖𝐔𝐓𝐀 LABARI ME CIKE DA "BAN TAUSAYI, MATSANANCIYAR DAMUWA, " "KUNCIN CUZIYA, " "SADAUKARWA, " ZAZZAFAR SOYAYYA ME TSAYAWA A RUHI. WRITING BY MARYAM STAR YAR BAIWAR JJRT. MARUBUCIYAR RAYUWAR SAMHAD DAFIN MACIJI A DAREN AURENA AND NOW ZAFIN WUTA *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION* *(J.W.A)* THE NOBLE WRITER'S TEAM PAID BOOK 500 ONLY BOOK TWO CHAPTER 9 .ميحرلا نمحرلا الله مسب Da ƙyar na kawar da tunanin Mama na wajen ya ɗauka da haka har muka gama karyawa a tsanake cikin tsari da burgewa. "Bayan kowa ya gama ne muka ɗunguma zuwa wajen duba jikin Fauzan, sai da kowa ya gama shiga" sannan na shiga daga ƙarshe ina ɓuya bayan Hajjo. Idanuwansa a kulle suke amma jin wannan sanyin me saka ma shi nutsuwa ya saka shi saurin buɗe "rinannun idanuwanshi, haƙiƙa wannan sanyi rahama ne a gareshi, wannan sanyi ya na taka muhimmiyar rawa cikin rayuwarshi, sannan bugu da ƙari tun daga jiya bai huta ba koda na second ɗaya daga tunanin tsari da zubin halitar wacce ta taryeshi hannu biyu a matsayin mijin aurenta wanda ya ke a mawuyacin hali, haƙiƙa ya yabawa jarumta, haƙuri gami da tawassali irin nata, a halin da yake ciki yanzu haka shi" yasan ba kowa zai so shi ba sai dai aji tausayinshi. "Ɗaya bayan ɗaya suka shiga gaisheshi su na yi ma shi ya jiki, ya na amsa su da kai, da haka har aka zo" "kaina, yayinda a sanyaye na matsa kusa da shi ina kin wani abu da ba daidai ba a wajen, cikin sanyin murya na buɗe baki na ba tare da na kalleshi ba na ce." """Barka da safiya, ya ƙarfin jikin, Allah ya bada lafiya.""" "Bai amsa ba kuma bai daina kallona ba, a hankali na yi niyyar matsawa, amma sai naji saukar hannu me" "ɗumi ya riƙo nawa hannun, wani irin tsale duka ƙirjina ya yi, yayinda na ɗaga idona ahankali na sauke" "akan na shi hannun wanda babu komi sai ƙasusuwa da fata, amma sosai na yi mamakin yanda ya riƙe ni" da ƙarfi sosai. """Kai Fauzan cika ma ta hannu manah, baka ganin aikin zuba maka magani za ta yi."" Mommy ta faɗi ganin" yanda nike ta kiciniyar janye hannuna amma na kasa. "Da wani irin sauri na juya tare da sakin baki galala, ba ni kaɗai ba harsa su Hajjo sun cika da mamakin jin" abin da na ji. """Uhumm, Mommy ina son ɗumin jikinta, pleasw ki ce ma ta karta tafi ta barni.""Fauzan ya faɗi cikin wata" "iriyar haɗaɗiyar murya me daɗin amo, nutsuwa, kamala gami da shagwaɓa duka muryar tasa ta haɗa," "nan take na ji wani abu ya tsaga ta cikin jinin jikina, yayinda sautin bugun zuciyata ya sauya ta koma dokawa a hankali cikin sanyi." Da sauri Mommy ta taso tazo gabana ta kama hannuna tare da matsawa kusa da Fauzan idonta na tsiyayarda hawayen farin ciki ta damƙa hannuna a cikin nashi ta na faɗin. """My lovely son฀, indai har zaka samu lafiya ka dawo cikin farin ciki kamar yanda muke a baya, to ga" "Mubaraka nan na damƙa ma ka ita amana, ka ƙarfafa zuciya da gangar jikinka wajen hana ciwo yin galaba akanka, ga kwarara zuciyarka ta hanyar sakawa wannan baiwar Allar me zuciyar zinare da mafificin alkairi kamar yanda ta sadaukar da farin ciki da ƙuruciyarta ta amince da aurenka sannan ta amince da jinyarka alhalin ko mu da muke makusantanka bamuyi maka wannan sadaukarwar ba, tabar ƴan uwanta da danginta harma da rayuwarda ta saba ta zo cikinmu ta zauna dan kawai ta faranta mana rai ta hanyar kulawa da kai, ga Mubaraka nan na damƙa maka ita ɗin matarka ce kuma amana a wajenka" "da mu baki ɗaya.""" "Mommy ba ta ƙarashe faɗin abin da za ta faɗa ba wani irin raunananen kuka ya ci ƙarfinta, wanda hakan" "ya saka ta ƙanƙame hannuna da nashi wajen ɗaya hawayenta na sauka akan hannuwan namu, Phapha ne ya taso cikin sanyi jiki ya janyeta daga wajen tare da rungumeta ya fice fuskarshi da damuwa, Hajjo ma jan hannun Sulaima da bakinta ya mutu murus dan tsabar murna ta yi suka bar wajen, ficewa sukai" suka barni daga ni sai Fauzan wanda ke ƙanƙame da hannuna kamar wani zai kwace ma sa ni. Cikin sassanyan sauti me taushi na kalleshi tare da falin. """Ammm,,, ɗan cika min hannu zan haɗa magani.""" Na faɗi ina ƙifta manyan idanuwana dan kuka ne ke neman kwace min. """Ni bazan cika ki ba gaskiya .""Fauzan ya faɗi a shagwaɓe ya na janyo ni gaba ɗaya, saura kaɗan in faɗa" "jikinsa amma na hana hakan faruwa ta hanyar dafe ƙasa da hannunawa, fuskata na fuskantar ta shi fuskar wacce tai baƙi saboda maganin da na shafa masa jiya." Bazan iya banbance halitar fuskarshi ba amma yanayin yanda naga gashin kanshi ya kwanta luf baƙi wuluk sai hakan ya saka nike tunanin ko yayane zai kasance cikin sahum maza ƴan kwalisa. "Sauke fararena na yi a cikin nasa, wani irin abu me ƙarfi ne ya ke haɗuwa a cikin idanuwanmu, saurin" sauke kaina ƙasa ƙirjina na luguden duka. "Zare jikina na yi na ja baya tare da tashi cikin rashin kwarin jiki, tashi na yi tare da zuwa wajenda aka" "ajiye waɗannan ledojin da baƙin jiya suka kawo jayan dubiya, raɗau nike ganin shatin yatsun wanda ya riƙe ledar na fitar da baƙin hayaƙi, sannan wani irin wari marar daɗi na tashi, gabana na faɗuwa haka na buɗe ledar ina leƙen abin da ke ciki, sai naga kayan fruit ne wasu duk sun ruɓe wasu kuma nunanun sai walƙiya suke da ɗaukar ido, waɗanda suka ruɓe kuma sai wari suke fitarwa tare da wannan baƙin hayaki, saurin ɗaukar ledar na yi na fitar da ita daga ɗakin, a bakin ƙofa na ajiye ta ina jin tsikar jikina na tashi, juyowa na yi na koma ɗakin sai naji yanzu yamin daidai, ajiyar zuciya na sauke sannan na shiga gyara ɗakin duk da ba wani datti yai ba, kuma yau da sauƙin ƙarnin ba kamar jiya ba, bayan na gama na koma wajen Fauzan ɗauke da ruwan magani wanda Phapha ya bani akan agoge ma shi jiki da shi, ruwa na haɗa masu sanyi sannan na ɗauki tsaftatacen towel fari ƙar na saka a cikin ruwan maganin, ba tare da na ce da shi komi ba na matsa kusa da shi na fara aikina, idonshi ƙur a kaina ya na kallona kamar wanda zai haddace kamanin fuskata, bayan na gama goge ma shi fuska da hannuwa na koma kan wuyanshi zuwa cikinshi, duk inda na ɗaura towel ɗin sai wajen ya kwalje amma banji komi ba haka na ci gaba sa goge ma shi jiki, yau ba kamar jiya ba dan yau ko ina sai da na goge ma shi a jikinshi da maganin sannan na na barbaɗa wanda na barbaɗa ma shi jiya, abin gwanin ban tausayi dan kuda fatar jikinshi ta saɓule tai jajir, ban gaji ba na sake kaɗa ma shi na sha, nai bisimilla tare da kaina saikin bakinshi, kamar me jira haka ya buɗe bakin na shiga zuba ma shi maganin, sai da ya shanye tas sannan ya lumshe ido, ina tsaka da tattare kayan wajen zan tashi naji ya riƙo hannuna da ƙarfi, kafin inyi wani yunƙuri tuni ya shiga kelaya amai kamar dai jiya, sai dai na yau harda jini da wani abu kamar saɓa, duk dauriyata sai da nai kuka dan ba kaɗanba ya bani tausayi, a hankali na dafa kafaɗarshi gudun kar in fama ma shi ƙunar na samu na kwantar da kanshi akan pillow sannan na zare hannuna ina jera ma shi sannu, lumshe ido kawai ya yi" "tare da sake min hannu, a hankali na tashi daga wajen tare da kwashe kayan sannan na gyara wajen tsaf," "bayan na gama ne na koma gefe na rakuɓe nai shiru ina tunanin duniya da irin ƙalubalen da ke cikinta," haka wani kalar nannauyan barci yai gaba da ni. "Sarauniya Zubudiyya ce zaune akan bango ta na kallon dukanin abin da muke yi, yayinda tausayina da na" "Fauzan ya sake kamata, ita ɗin hallita ce me tsananin tausayi, sam bata son zalinci kuma bata shiri da duk wani me aikatashi, daga inda take ta na ganin inda Zuka yayi ajiya a jikin Fauzan, wanda hakan ke taimakawa wajen sake tsananta ciwon na shi, daga inda take zaune ta ziro hannu ta tattaro ajiyar kakaf, hakan yayi daidai da lokacinda na bashi maganin sha, shine ya amayar da sukanin ajiyar, sai ya ji wasai cikin cikinshi kamar an ɗauke ma shi wani nannauyan dutse, cikin sanyin da ta saka min ta huro ma shi" iska wace ta saka shi barcin rahama da salama. ABUJA NG. MAITAMA. Tsaye ya ke agaban makeken frem ɗin da ke ɗauke da hotunan kyawawan ƴan mata guda biyu masu "tsananin kama, babbar ba zata wuce shekaru huɗu ba alokacin da akai hoton, ɗayar kuma jinjirace fara sol kyakkyawar gaske." Idonshi na zubda ruwan hawaye ya ke kewaye daidai fuskar jinjirar ya na shafawa. "Wa ta kyakkyawar ma ta ce me kama da laraba ta shigo ɗakin inda mutumin ya ke, taɗan jima a" "bayanshi ta na kallonshi, fuskarta ɗauke da matsananciyar damuwa irin wacce tafi ƙarfin a bayyanata a baki, tabbas ta na cikin matsananciyar damuwa, amma hakan bai hana ta yi tawassali da Allah ba, domin tasan dukan abin da ya samu bawa to yana rubuce a jikin littafin ƙaddararsa, kuma babu me gujewa ƙaddara face ta biyo shi da mugun gudu, irin gudun da idan har ta cimma masa to kuwa sai ta Allah kawai, ita ɗin mahaifiyace kuma me rauni, akwai raunin da yakai a raɓa uwa da ƴarta tun bata gama tantance iskar duniya ba, akwai raunin da yakai a raba uwa da ƴarta lokacinda ta gama wahalar shayarwa da reno, ita tasan me rauni ce gaba da baya, amma batabawa zuciyarta damar raunana har ta kaita ga samun matsala ba, ta riga da ta dangana, ta bar komi a wajen Allah, mudin rana na fitowa ta na faɗuwa tasan wannan ranar za ta zo, ranar da duk wani ƙulli zai warware kansa da ƙarfin ƙudurar ubangiji, ko da bata raye tasan ta yi babban tanadin zuwan wannan ranar, abu ɗaya kawai take jira," shine wanzuwar ikon ubangiji ta hanyar bankaɗo duk wa ta ajiya da aka bizne a cikin baƙin duhu. Cike da ƙwarin gwuiwa ta taka zuwa inda mutumin yake tsaye ya na ta faman sharɓar kuka tare da shafar fuskokin jikin photon. """Bansan har zuwa yaushe gwarzon jarumina zai yi tawassali da ƙadararda ta daɗe da yanke wannan" "damɓarariyar ƙaunarba, ha isa hakan, ya isa!! yanzu ba lokacin yin kuka ko nuna damuwa bane akan zarenda ƙaddara ta daɗe da yankewa ba, yanzu lokacin farin ciki ne da nuna godiya ga Allah da akan manya-manyan kyaututtukan da ya bamu, zo muje muyi tafiyar da za ta sada mu da farin ciki" "madawwani wanda bazai yanke ba da izinin Ubangiji.""" "Ta ƙarashe maganar ta na janyo hannuwanshi duka biyu kamar ƙaramin yaro me koyon tafiya, haka ta" "dinga janshi ta na tafiya da baya-baya harta cimma ƙofar wani ɗaki, buɗe ƙofar ta yi da ƙafarta sannan ta shiga har lokacin bata saki hannuwanshi ba, a gaban baby bed guda biyu ta tsaya tare da dafo kafaɗunshi ta juyar da fuskarshi ta na faɗin." """Yanzu lokacin farin ciki da godiyar Allah ne da ya azurta mu da wannan gagarumar kyautar wacce" "muka daɗe muna jira, ga makwafin yaranmu da muka rasa Allah ya dawo manah da su, MUBARAKA da MARYAM sun dawo gare mu, kallah!!! kallafa!, kalesu Alhaji.""" "Ta yi maganar ta na ɗago da jariran yaran ɗaya bayan ɗaya ta na nuna ma shi, fuskarta faɗaɗe da" "yalwatacen farin ciki, wanda ya kasance na gidoya ga Allah da ya ake azurtata da ƴaƴa mata waɗanda ta ke fatan su kasance ma ta sanyin idaniya, kuma su mamaye wawakeken ramin da ke zuciyarta na rashin ƴaƴanta da ta yi, waɗanda ba mutuwa sukai ba, kawai ƙaddarace da jarabawa ta Ubangiji ta nesanta" tsakaninsu. "LITTAFIN ZAFIN WUTA PAID BOOK NE, ZA KI BIYA 500 KACAL DOMIN KI MALLAKI NAKI." 9136291920 MARYAM UMAR OPAY TAKU HAR KULLUM ME SON GANIN FARIN CIKINKU. MARYAM STAR KE MUKU FATAN ALKIRI . 𝐙𝐀𝐅𝐈𝐍 𝐖𝐔𝐓𝐀 LABARI ME CIKE DA "BAN TAUSAYI, MATSANANCIYAR DAMUWA, " "KUNCIN CUZIYA, " "SADAUKARWA, " ZAZZAFAR SOYAYYA ME TSAYAWA A RUHI. WRITING BY MARYAM STAR YAR BAIWAR JJRT. MARUBUCIYAR RAYUWAR SAMHAD DAFIN MACIJI A DAREN AURENA AND NOW ZAFIN WUTA *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION* *(J.W.A)* THE NOBLE WRITER'S TEAM PAID BOOK 500 ONLY BOOK TWO CHARTER 10 ميحرلا نمحرلا الله مسب "Durƙushewa ya yi akan gwuiyoyinsa, yayinda kuka da dariya suka haɗe ma sa lokaci ɗaya, sai kuma yakai" "hannayensa cikin bed ɗin ya tattaro yaran waɗanda keta sharar barci abinsu, ya haɗa su a ƙirjinsa ya rungume kamar wani zai ƙwace ma shi su, sai kuma ya shiga jero addu'o'i ya na tofesu, sannan ya shiga sumbatarsu kamar zai cinye su, bai tsagaita ba sai da ɗaya ya motsa ta na yamutse fuska kamar za ta yi kuka, sai ya yi saurin mayarda su ya kwantar shi kuma ya kwanta akan lallausan carpet ɗin da ke" shimfiɗe a ƙasa ya na sakin ajiyar zuciya a jere kamar wanda ya kubto daga hannun abin cutarwa. "Alhaji Umar kenan, shararen gogagen ɗan kasuwa wanda manya-manyan ƴan kasuwa, gwamnati da" "al'umaa ke ji da shi, Alhaji Umar sanannen mutumne wanda tauraruwarsa ke haskawa da tsananin haske, haskenda ke tattare a cikin tarin ƙaddarorin da ya shallake kafin haskakuwarshi a sararin samaniyar duniyar kasuwanci, Alhaji Umar mutum ne wanda rayuwarshi ke cike da tari ƙaddararo mabanbanta, tun tasowarshi ƙaddara ke walagigi d rayuwarsa, amma bai sare ba wajen yin tawassali da kuma rungumar ƙaddarar a duk sa'ilin da ta dumfaro rayuwarshi, yakan tsaya tsayin daka wajen ƙasƙantar da kanshi a wajen Mahalicci me kowa kuma me komi, wanda ke aika dukkan abin da ya so ba tare da shamaki ba, manzon Allah ya yi gaskiya da ya ce a cikin wani hadisi, ""Allah ya na son bawa me" "tsoronshi, me wadata""." Tsoron Allah da kuma ƙarfin iymani irinna Alhaji Umar sune suka taimaka ma shi wajen samun ɗaukaka "a duniya, Allah ya azurtashi da tarin dukiya wacce shi kanshi bai san iya adadinta ba, sannan kuma Allah ya albarkace shi da farin jini a cikin mutane." "Ƙaddara ɗaya ce Alhaji Umar ya kasa haƙuri da dangana da ita, wacce ta ke neman zautar da shi, ya" "rasa ƴaƴansa mata har karo biyu, ba rasuwa sukai ba rasa su ya yi ta hanyar son zuciya da kwadayi irin na" makusantanshi. "A hankali Hajiya Sadiya ta dire tray ɗin da ta ɗauko goran ruwa gami da cup a ƙasa, sai kuma ta buɗe wa" "ta ƴar jaka ta ɗauko kwalin magunguna guda biyu, ta buɗe tare da ballawa ta saka a cup ɗin, haka sauran suma ta saka a cikin cup ɗin sannan ta zuba ruka kaɗan ta dama kamar yanda ake bawa yara magani, bayan ta gama ta aje a gefe tare da gyara zamanta ta ɗauki kan Alhaji Umar ta ɗaura akan cinyarta tare da share ma shi hawayen da ke ta faman silalowa daga kwarmin idonshi, a hankali ta janyo cup ɗin tare da bisimilla sannan ta kafashi akan busashen bakinshi wanda laɓɓan suka bushe kamar wanda yai sati ɗaya ya na tafiya ba tare da ya sha ruwa ba, buɗe bakin ya yi ta juye ma shi maganin ya shanye tas, sannan ta kora mashi da ruwa me rangwamen sanyi ta gyara ma shi kwanciya akan cinyarta ta na shafa sumar kanshi a hankali, sai da ta tabbatar da barci me nauyi ya yi awon gaba da shi, sannan ta ja shi da ƙarfin zuciyarta ta ɗaura shi akan makeken bed ɗin da ke ɗakin ta gyara ma shi kanciya sannan ta fice" daga ɗakin. "Wajen photon ta je ta tsaya ita ma ta na kuka me ciwo ta na shafa fuskokin yaran ta na sambatu, ta" jima a wajen ta na kuka kamin daga bisani ta rarrashi kanta ta tashi ta koma wajen ƴaƴanta da ke kuka ta "rarrashe su tare da shayar da su, kwantar da su ta yi a tsakanin ita da mijinta Alhaji Umar, ta jima a kwance ta na tunanin rayuwa, kafin daga bisani barci me nauyi ya yi awon gaba da ita." A cikin barcinta ta yi mafarki kamar yanda ta saba aduk lokacin da takai kafaɗarta ƙasa da sunan yin "barci, yauma kamar kullum." "Zaune suke a waje ɗaya, cikin wani faffaɗan fili me yalwar bishiyu da ciyayi, fuskokinsu na kallon juna a" "zahiri, amma a baɗini ba junansu suke kalloba ko wacensu na kallon wani abu daban, su na matuƙar kama da junansu sosai, sai de ɗaya ta kasance fara tas ɗayar kuma me matsakaicin haske, amma baza'a kirata da baƙa ba ko wankan tarwaɗa saboda tana da haske dande ba can sosaiba, Yau kuma ba kamar" "yanda ta saba ganinsu su kaɗai ba, yau su biyu ne sannan kuma mazaje guda biyu na gefen kowace." "Da Salati ta farka kamar kullum idan ta yi mafarki, sosai yau zuciyarta ta tsinke da lamarin, sai ta ji yau" "kaɗai ta na so ta tattauna lamarin da wani, to amma kuma wani wah, waye zai dubeta da idon basira ya fuskanci abin da ta ke nufi ba tare da ya yi ma ta kallon mahaukaciya ba, amma kuma ya dace a duba lamarinan gaskiya, wannan mafarkin ta jima ta na yinshi tun shekarun baya, kuma kullum duniya ta kwanta barci sai ta yi mafarkin, ya kamata ace tasan mi wannan mafarkin nata ya ke nufi." "Ita kaɗai ta ci gaba da zancen zucin, ta na lalubawa kanta mafita, kamin daga bisani ta tsaida tunani da" "nazarin wacce ta dace da tayi shawara da ita, tasan za ta fuskanceta kuma ta fahimceta, ba kowa ba ce" face ƴar uwarta Asma'u. LEGOS. MUBEENAH. "Yau satina biyu cif a gidan Alhaji Abdallah me gwalagwala, na murje na yi ɓulɓul abina na ƙara zama" "cikakkiyar budurwa duda kasancewata me ƙaramim jiki da siranta, haske da sheƙin fatata ya sake daɗuwa, ni kaina nakan zauna ina taɓa fatata ina jin daɗin yanda tai laushi gwanin kyau, baƙin gashin kaina wanda daƙyar Mama ke gyara min shi dan sam bana son kitso, yanzu ya sake linka tsayi da baƙi saboda musamman Sulaima ke ware lokaci duk bayan kwana biyu ta gyara min shi tsab, haka nike fitowa kamar budurwar ba'indiya irin masu tashen kyawunan, yanzu kullum zaka same ni cikin ado da kwalliya, ga ƙamshin tsadadun turaruka wanda Pahpah da kanshi ya bani kyautarsu, sannan yanzu na yi wani irin sabo da ƴan gidan, na saki jikina da su sosai, su kuma kullum cikin yaba min suke da godiya akan yanda nike jajircewa akan Fauzan, wanda yanzu jikin na shi yai sauƙi sosai, wannan zafin jikin duk babu shi, kasancewar an canza mashi ɗaki yanzu, da wannan damar na yi amfani wajen saka matakin tsaro daga dukanin abin cutarwa mutum ko aljan, ƙira'a nike sakawa cikin ƙaramin sauti a makeken plasma da aka jingine a bangon ɗaki, sannan da lokacin azkar ya yi da kaina nike canza channel, hakan ya taka rawa sosai wajen dawo da hankalin su Mommy suma suka shiga neman kariyar jiki da neman tsari daga dukkanin abin halitta, duk maricen duniya zaka same su a ɗakin Fauzan su na bin ƙira'ar azkar ɗin da ake yi a Sunnah TV, haka za ka ga kowa ya zauna yana bin ƙira'ar cikin ƙaramin sauti, hatta Pahpah yakan zauna idan ya na gida shima ayi da shi, bayan angama kuma abawa ƴan aiki umurnin cike wajen da kayan" ciye-ciye mu zauna ana fira ana ciye-ciye abin gwanin burgewa. A duk lokacin da na tsinci kaina cikin farin ciki nakan tuno rayuwata ta baya wacce da ni da dabba bamu "da bancin, haƙiƙa na yi rayuwa me cike da rashin ƴanci, kyara da rashin samun sakewa a cikin gidanmu, a" "rayuwata ta baya babu ranar da za ta zo ta wuce ba tare da Abba ya lakaɗa min shege duka ba, sannan" "ya bini da mugayen kalamai masu kama da ZAFIN WUTA, bani da iko da kaina sai abin da aka gindayamin, ba ni sa zaɓin kaina sai wanda aka zaɓamin, a wajen mutum ɗaya nike samun rangwame har in samu" rarrashi da tarairayar da na rasa samu a wajen mahaifina ita ce Mama ita kaɗai ce ke nuna min zallar "soyayya wacce babu surki, takan zauna da ni domin ta ji matsalata, takan tayani ɓakin ciki ko damuwa idan wani abu ya same ni, shi yasa har gobe na kasa cire tunaninta, kasa mancewa da ita, kullum sai na yi" hawayen kewarta. "A hankali na saukar da kaina daga kallon jikin miron da nike, cikin nutsuwa na sagala mayafin kayan da" "na saka, sannan na zira takalmina ina sake daidaita fuskata na fice." "Har yanzu na kasa sabawa da bugun zuciyarda nike tsintar kaina aduk lokacin da na tunkari ɗakin Fauzan," "abu ɗaya ne na kasa sabawa da shi tun zuwana gidan shine, kaifafa idanuwan Fauzan bana sakewa idan ya kafe ni da su ya na kallona, shikuma muddin idanuwansa biyu to ya dinga kallona kenan kamar sabon maye, yanzu haka da nike ƙoƙarin shiga ɗakin sai da naɗanyi jimmm a bakin ƙofar tare da ɗaure fuska sannan na yi sallama cikin ƙaramin sauti na tura kaina cikin ɗakin." "Tun sanda na tsaya jikin ƙofar ƙamshin turarena ya riga ni shigowa ɗakin, da sauri ya buɗe idanuwanshi" "ya na jiran ƙarasowata, da yake yau tun safe da na bashi magani ban sake bi takanshi ba sai yanzu d" nasan kowa na gidan na daf da hallara dan mu zauna kamar yanda muka saba dan gudanar da azkar. "Daddaɗar sautin muryata ne ya ratsa can cikin ƙoƙon kan majiyar sautin kunnuwansa, a hankali ya sauke" "nannauyan ajiyar zuciya, wata iriyar kewar sanyin jikina na baibayeshi, sanyin da ke tattare da ni wanda ke samar ma shi da nutsuwa na mamaye ɗakin." "Kamar kullum wai ma bai amsa sallamar a fili ba, amma naga lokacin da jajayen laɓɓansa suka yi motsi" "kaɗan, da sauri na sauke kaina ƙasa tare da ƙarasawa wajen shi, ba tare da na kalleshi ba na hau haɗa" "ma shi maganin marice, bayan na gama na gyara zamana tare da fuskantar inda ya ke kwance amma fuskata na kallon gefe, na wani maze sannan na ce." """Magana nike so inyi da kai, amma dan hasken musulinci ka daina kallona hakanan, idan kana" "kallona bazan iya faɗin abin da nike so imfaɗi ba.""" "Nai maganar ina cuɗanya ƴan yatsuna, amma koda kuskure ban kalli inda yake ba." """Ki na da kyau me fizgar hankali, bazan iya janye idanuwana akan ki ba muddin zamu kasance waje" "ɗaya, kallonki na rage min zugi da raɗaɗin ZAFIN WUTAR da bai gama hucewa a jikina ba, please ki yarjemin kallonki a koda yaushe.""" "Yai maganar cikin salon da ke saka ni jin wani abu ya tsarga tun daga tafin ƙafata har zuwa ƙoƙon kaina," "mazewa na yi na daure na hana idanuwa da ke ƙoƙarin bani kunya akan satar kallonshi, sannan na ce." """Ban san iya adadin watannin daka shafe a kwance cikin halin ciwo ba, amma kai nasan za ka iya" "tuna lokacin, ina so in tunatar da kai yanzu Alhamdulillah ka samu sauƙi sosai, sai nike ganin ya kamata ace ka fara ramakon sallolin da aka biyoka, ba dole sai ka yi kamar yanda ka saba yi abaya ba, zaka iya yi a kwance ta hanyar ayyanawa a zuciyarka, sai kaga sanadiyar sallar Allah ya sake baka lafiya" "mawadaciya.""" "Tun da na fara magana ya kafe ɗan mitsitsin bakina da kaifafan idanuwansa, ya na kallon yanda nike zaro" "magana cikin amon da ke saukar ma shi da kasala, da wani yanayi me wuyar fassarawa." "Bai ce komi ba amma na jiyo sautin fitar murmushinshi, sai na tsinci kaina da jin haushin shirun da ya yi" "min, dan harga Allah da wannan kallo da yake min gwara ya dinga yimin magana, saboda ina jin daɗin amon muryarsa, sannan ina tsintar kaina cikin matsanancin farin ciki aduk lokacinda ya yi min magana." 𝐙𝐀𝐅𝐈𝐍 𝐖𝐔𝐓𝐀 LABARI ME CIKE DA "BAN TAUSAYI, MATSANANCIYAR DAMUWA, " "KUNCIN CUZIYA, " "SADAUKARWA, " ZAZZAFAR SOYAYYA ME TSAYAWA A RUHI. WRITING BY MARYAM STAR YAR BAIWAR JJRT. MARUBUCIYAR RAYUWAR SAMHAD DAFIN MACIJI A DAREN AURENA AND NOW ZAFIN WUTA *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION* *(J.W.A)* THE NOBLE WRITER'S TEAM PAID BOOK 500 ONLY BOOK TWO CHAPTER 11 ميحرلا نمحرلا الله مسب "Shirun da Fauzan ya yi min ya saka na tashi tare da rufe maganin nai tafiyata nabar shi, bai san zuciya na" "yi ba a tunaninshi wani abin zan je inyi, amma sai ya ji shiru ban dawo ba, har kowa ya hallara wajen yin azkar amma ni shiru babu ni babu alamuna, duk wanda ya zo sai ya tambayi ina naje yau ban fito ba, ko lafiya, amma sai Fauzan yai musu nuni da maganin da na kaɗa na bari, har suka gama azkar aka hau hira cikin raha da mutunta juna amma bandawo ba, Sulaima har dubo ɗakina ta yi danta duba ko wani abu ya" tsaida ni amma ta je ta iske wayam babu kowa. "Ni kuma garding ɗin gidan na nufa wanda ya ke a bayan ɗakin Fauzan, can nai zamana ina shaƙar" "dadaɗar iskar wajen me saka nishaɗi, ina zaune a wajen na ji wa ta iska me tsananin sanyi ta taso," lumshe ido na yi ina shaƙar iskar da kyau ina kuma ƙanƙame jikina saboda sanyi. "A hankali na shiga buɗe idona amma mizan gani, sai na ganni a tsakiyar wani tanƙamemen teku wanda" "ke ɗauke da ruwa masu haske farare tas gwanin sha'awa, firfito da idanuwa na yi waje ina kallon ruwa kuma ina kallon kaina asaman wani dutse da ke tsakiyar ruwan, wani irin tsoro da tashin hankali ne ya baibaye ni, kafin insan abin yi kawai naga wani abu dunƙulalle na fitowa ta ƙasan ruwan da nike, a hankali abin yayo sama gaba ɗaya sai kuma ya shiga shimfiɗe kanshi kamar tabarma, kafin in dawo daga suman mamakin da na yi sai kawai naga wani haske me fitar da tartsatsin ruwa na bayyana akan abin, kafin insan abin yi wa ta zankaɗeɗiyar kyakkyawar hallita fara sol ta bayyana ta cikin haske, zaunawa ta yi ta na fuskanta ta farar fuskarta faɗaɗe da murmushi, cikin wa ta irinyar murya me sanyin gaske ta ce" da ni. """MUBEENAH!!! INA MIKI BARKA DA ZUWA FADA TA, MI KIKE SO INSAKA A KAWO MIKI, KI FAƊI" "DUKKAN ABIN DA KIKE BUƘATA.""" Ta yi maganar tartsatsin ruwa na fitowa daga bakinta. """Wa,,,,,,wah,,,,wa,,wa,, wace,,,,wacece ke!!!!!!.""" Na faɗi da ƙyar cikin inda-indar murya. """NI CE SARAUNIYA ZUBUDIYYA, ƳAR SARKIN RUWA, NI ƊIN ME TAIMAKONKI CE, INDAI INA TARE S KE" "BABU MAHALUƘIN DA ZAI CUTAR DA KE, INA BAKI KARIYA DA ƘARFIN IKON UBANGIJI, INA TSAYA MA KI TA INDA BAKI TUNANI, NI ƊIN MAI TSANANIN TASAYINKI CE.""" "Ta faɗi ta na ziro dogon farin hannunta zuwa inda nike ta shafa kaina, nan take wani irin sanyi me" "tsayar da numfashi ya mamaye ilahirin jikina, sai na faɗi a sume, lokaci ɗaya ruwan ya ɓace ɓat, hakan yayi daidai da zuwan Mommy ita da masu aiki wajen ta na kwalla min kira, ɗan turus ta tsaya ganina a" "kwance ƙasa ina barci, a hankali ta duƙo kaina ta na kiran sunana." """Mubeenah! ke Mubeenah lafiyarki ƙalau kuwa da za ki zo nan ki kwanta da sanyin marice.""" "Tai maganar ta na ƙoƙarin ɗago da ni ganin na buɗe idona, ji na yi kaina yamin nauyi sosai dan haka ban" "samu damar cewa komi ba na shiga kiciniyar miƙewa tsaye, ganin ina tangaɗi sai Mommy ta taimaka min ta ɗago da ni tare da taimaka min muka bar wajen." "Ɗakin Hajjo ta kai ni, sai da ta kwantar da ni akan gado ta rufamin blanked sannan ta fice ta barni." Nannauyan barci ne ya ɗauke ni wanda ban farka ba sai ana gab da tada sallar magrib. "A hankali ya tura ƙofar ɗakin jin shirun ya yi yawa, sannan ya kira wayatshi amma bai ɗaga ba har sau" "biyar, tsayawa ya yi yana bin ɗakin da kallo ganin yanda yaɗan hargitse, ga wani wari marar dadi da ke" "tasowa, da sauri ya ƙarasa shigowa ya na faɗin." """Innalillahi bee mi ke damunka haka, lafiya ƙalau fa muka rabu.""" "Yai maganar ya na kai hannunshi jikin Al-hassan, da mugun sauri ya janye hannun jin wani irin" "azababben zafi da ke fitowa daga jikin Hassan ɗin, bai daddara ba ya sake miƙa hannu da niyyar birkito da shi, amma sai ya sake jin wani irin zafi wanda yafi na farko, ɗago da hannu shi ya yi yana kallon yanda nan take hannun yai jazur alamar ƙonuwa, cike da firgici ya ke kallon ɗan uwan nashi sannan kuma ya" "kalli hanunshi, da wani irin gudu ya nufi wajen freezer ya buɗe ya shiga jido kwalaben ruwan sanyi, ɓalle" "murfin kwalaben ya shiga yi lokaci ɗaya ya shiga juyesu a jikin Hassan idonshi na tsiyayar hawaye, amma" "mi lokacin da ruwan ke sauka jikin Hassan wani irin ""Cuuuuuuuuw"" kake ji kamar anzuba ruwa a tafasashen mai." Cike dafirgici Hussain ya ja da baya ya na fashewa da kuka me tsananin ƙarfi sannan ya tashi da mugun gudu ya fice daga ɗakin. ABUJA. """Wannan wace iriyar rayuwace, wannan zalincin yayi yawa, rashin iymanina bai kai nanba, ya kake so" "inyi da girman haƙƙin da ke ɗawainiya da ni, anya kuwa akwai sauran ɓirɓishin imani a zuciyarka Lawal," "wallahi tallahi ka ji na rantse ba zan sake biye maka inyi abin da zai idasa tarwatsa ɗan ɓirɓishin farin cikin da ya ragemin ba, na gaji!!! na gaji Lawan, bazan iya ba.""" Hamshaƙiyar matar ta faɗi ta na jijjiga kwalar rigar mutumin da ta shaƙe ta na masa magana cikin ihu fuskarta shaɓe-shaɓe da hawaye. "Wani makirin murmushi wanda ta kira da Lawan ya saki tare da kai ma ta shura da ƙafa, nan take ta faɗi" "akan ƙafafuwanta, duƙowa ya yi tare da tallabo haɓarta ya matse da ƙarfi, sannan ciki sanyin sauti ya ke" faɗin. """Fatima Abbas, dolene ki idasa abin da aka fara da ke, idan kin san ba za ki iya ba tun farko mi yasa" "kika fara, na daɗe ina maimaita maki cewa duk wanda ya shigo wannan aiki to babu fita, matsawar kuma kika matsa akan za ki bar aikin, to kema kin san makomarki, mutuwa ita ce makomarki Fatima Abbas."" Ya faɗa tare da hankaɗa ta kan kujera sannan ya bita ya ɗora ƙafarshi ɗaya akan hannun kujerar fuskarshi a" murtuke ya sake faɗin. """Na baki awanni biyu rak, kar ki kuskura ki ƙara koda minti ɗaya akai, maza ki je ki haɗomin waɗancan" "tsinanun ƴaƴan da Sadiya ta sake haifawa Umar, alƙawari na yi akan muddin ina raye to jinin Sadiya da Umar ba zai taka a doran ƙasa ba, sai dai idan na mutu na bar wannan duniyar, kai wallahi koda mutuwa zanyi to sai na tabbatar da naga bayan Umar da dukkan dukiyar da ya tara, wannan alƙawarina ne.""" Ya faɗa ya na murje yatsun hanun Fatima da ƙafarshi sannan na fice ya barta a wajen. "Wani irin kuka ta ke tare da gwara kanta da jikin ƙarfen da aka dasa dan sarƙafe labule, jini ne ya soma" tsatsafowa daga goshinta amma sake gwara kan nata take ta na faɗin. """Kaicona da wannan ƙazamar rayuwar wacce na zaɓawa kaina, Allah wadarar rayuwata, gashi na" "biyewa son zuciyata nayi abin da tsawon shekaru masu yawa ya hanani sakewa, haƙiƙa na aikata aikin dana sa ni wanda ya kulle ƙofofin farin cikina, Sadiya ki yafe min, haƙiƙa na cutar da rayuwarki cutarwa me muni, na azabtar da ke ta hanyar bin son zuciya d kyale-kyalen duniya, Allah ka ɗauki rayuwata kozan" "huta da wannan baƙar azabar wacce na janyowa kaina da waɗannan hannuwan nawa.""" Tai maganar tana dukan kanta da hannayenta tare da sake fashewa da kuka wanda ya kusa saka numfashinta ɗaukewa. "LITTAFIN ZAFIN WUTA PAID BOOK NE, ZA KI BIYA 500 KACAL DOMIN KI MALLAKI NAKI." 9136291920 MARYAM UMAR OPAY TAKU HAR KULLUM ME SON GANIN FARIN CIKINKU. MARYAM STAR KE MUKU FATAN ALKIRI . 𝐙𝐀𝐅𝐈𝐍 𝐖𝐔𝐓𝐀 LABARI ME CIKE DA "BAN TAUSAYI, MATSANANCIYAR DAMUWA, " "KUNCIN CUZIYA, " "SADAUKARWA, " ZAZZAFAR SOYAYYA ME TSAYAWA A RUHI. WRITING BY MARYAM STAR YAR BAIWAR JJRT. MARUBUCIYAR RAYUWAR SAMHAD DAFIN MACIJI A DAREN AURENA AND NOW ZAFIN WUTA *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION* *(J.W.A)* THE NOBLE WRITER'S TEAM PAID BOOK 500 ONLY BOOK TWO CHAPTER 12 ميحرلا نمحرلا الله مسب. Ta na ganin dishi-dishi haka ta miƙe ta saɓi mayafinta da carkey ta fice zuwa parking lot ta ɗauki motarta "ta fice da mugun gudu ta na sharɓar kuka, ga fuskarta kaca-kaca da jini, sai da tai gudu sosai ta tabbatar da ta fita daga garin Abuja sannan ta nemi waje tai parking tare da kwanciya ta baya akan kujerar." SADIYA "Tsaye ta ke ta na bawa masu aiki umurnin yanda zasu shirya abinci, fuskarta gwanin kyau domin kuwa" "kwalliya ta caɓa kamar me shirin zuwa gasar ado da kwalliya, ta na gama sallamarsu ta fice zuwa main" parloun inda ya ke cike da baƙi ƴan barka da taya murnan sake samun rabo bayan tsawon shekaru da ta kwashe bata sake haihuwa ba. """Ai Sadiya baiwar Allah ce, ga kirki da tawassalin ɗaukar ƙaddara, yo idan wa ta ce aka sacewa ƴaƴa" "har karo biyu ai ba zata sake zama da mijinba, musamman yanda ake ta raɗe-raɗe akan wai shike" "sadaukar da ƴaƴanshi ga dodon tsafi."" Wa ta dattijuwar mata ta faɗa cike da gulma, yayinda wace ke kusa da ita itama ta caɓe da faɗi." """Ai babu wai, yo ai daganin wannan farin jini da tarin dukiyar ta Alhaji Umar ku kunsan ba banza ba, a" "yanda ake faɗi fa yanzu shine na bakwai a jerin ƴan kasuwa masu kuɗin Nigeria.""" "Sallamar Sadiya wace ta rigada taji dukan firar da suke, ita ta katse Iya Laraba daga zancen ƙanzon" "kuregen da ta ke, sai kuma tahau burin kunya gami da ƙaƙalo fara'ar dole ta yaɓa akan fuskarta." """Kaga Halimatus Sadiya uwar gida me pacasity a gidan Alhaji Ummaru sarkin ƴan kasuwa, yau dai" "Allah ya nufa bayan tsawon shekaru ashirin kin sake ganin kwanki a duniya, ni Balaraba ina tayaki murna, Allah ya rasa akan sunnar Ma'aiki.""" "Murmushi kawai Hajiya Sadiya ta yi, fuskarta babu alamun komi ta gabatar musu da lemo kafin abinci ya" "sauka, babu kunya suka naɗe lemon a jaka, su na faɗin sayiwa yara guzuri da shi, da yake Baba Laraba ƴar uwar Sadiya ce kuma anan ƙauyen abuja take da zama itada mijinta, sanin halin Alhaji Umar na son baƙi da talakawa ya saka bata kwashe wata guda cir ba tare da tazo gidan ba, idan ta tashi zuwa haka za ta ɗibo gayyar mutanen arziki ta taho da su dan samun abin duniya, dayake karamci a jinin Alhaji Umar ya ke, hakanan yake zagewa ya saki bakin aljihu yayiwa Baba Laraba da tawagarta kyauta ta bajinta da" ban girma. "A wunin ranar haka Sadiya taita karmar baƙuncin ƴan uwa da abokan arziƙi, musamman matan abokan" "kasuwancin Alhaji Umar da ƴan siyasa, yara kuma sunsha kyaututuka sosai a wajen ƴan barka, sai dare Sadiya ta samu kanta, ta je ɗakin barcinsu ta taradda Alhaji Umar na sana'ar ta shi wato tunani, idan ta kalleshi sai zuciyarta ta tsinke saboda yanda ya zama abin tausayi, yayi wani sukuku da shi kamar marar laka a jiki, har yanzu Sadiya bata saba da wannan yanayin nashi ba, ta lura yanzu abin na shi gaba yake sake yi, domin kuwa kullum sai ta lura da wani sabon canji a tare da shi, yanzu bai damu da yayi komi da kanshi ba sai shiga toilet, da kuma zuwa gaban photon yaransu da suka rasa yai tsaye ya na kallonsu ya" "na kuka, alamomi da yawa a bayyane suke waɗanda daga gani tasan ba lafiyar mijinta lauba." "Kife kanta tayi a kan gado wani irin kuka na rashin mafina na kwace ma ta, sai da tai kuka sosai" "kamar ranta zai fice, naman ƙasan idonta yai jajur, su kansu idanuwan na ta sun kaɗa sun koma launin" "jah, sai ta ke jin kamar abin ya mata nauyi ba zata iya ɗauka ita kaɗai ba, da gaskiyar Malam da yace" "akwai rikitattun al'amuura da zasu fuskato rayuwarta masu kama da ZAFIN WUTA, wanda suk juriyarta ba zata taɓa iya jure su ba, dole ne za ta nemi taimako, abin da ta ke yiwa kallon shirka da kanta za ta nemi a aimaka ma ta da shi, ba zata taɓa mance kaifafa maganganun da ya watsa ma ta ba kafin ya" tattare kayanshi yai tafiyarshi. "Zumbur ta tashi kamar wacce aka zabura, sai kuma ta shiga laluben wayarta, bayan ta ganta a saman" "pillow sai ta shiga neman number da ta ɗauki shekaru ta na dannawa delete amma ta saka gogewa, saboda batasan mi gobe za ta haifar ba, da ace ta goge number da tashin hankalin da zata shiga sai ya ninka wanda take ciki." "Gabanta ne ya shiga luguden suka, wa ta iriyar kunya ta baibayeta, sai ta ji duk ta muzanta, ita ta" "koreshi daga rayuwarta, kuma itace ta nemoshi kamar yanda ya ce zata nemeshi idan al'amurra suka" "rikice, wa ta iriyar hantsalowa zuciyarta ta yi kamar zata faso ƙirjinta ta fito lokacin da ta cinkayi sallama" "daga muryarshi, ba zata iya fasalta halin da take ciki ba, sai cintar kanta da ta yi tana faɗin." """Malam!!! Malmam,, Malam na sare, ƙarfina ya ƙare, zuciyata ta karaya bazan iya ɗaukar komi ni" "kaɗaiba, ina buƙtarka a kusa da ni, ina buƙatar taimakonka atare da ni, bazan iya ɗaukar nauyin ba, na raunana yanzu na yi rauni zuciyata ta karaya, badan ni ba badan halayyata ba ka taimaka ta dawo, na yi imani da Allah kaima na yi imani da maganganun da ka gaya min a baya, tabbas wa ta jarabtar ba lallai" "mutum ya iya jureta ba duk kuwa ƙarfin imani da zuciyarsa, na haɗa ka da girman Allah Malam.""" "Kukan da take riƙewa ne ya kwace ma ta ya shiga rero kanshi, yayinda acan ɗayan ɓangaren Malam ya yi" "shiru ya na sauraren kalamanta, sai wani murmushi ya kwace ma shi, yasani ba zata iya ɗauka ita kaɗai ba, abin yayi ma ta yawa, ko a bayama yaga mugun ƙoƙarinta, kuma ya yaba ma ta, ya jinjina da irin ƙarfin da zuciyar mace take da shi, sai ya sauke numfashi yana jin kukanta na ratsa kunnuwanshi, a" hankali cike d rarrashi ya ce. """Haƙiƙa kinyi namijin ƙoƙari, na yaba da ƙoƙarinki Halimatu, kin neme ni da kanki bayan tsawon" "lokaci, ki saka a ranki matsalolinki zasu fara warwarewa tun daga tushen da aka soma gina su, komi ya zo ƙarshe, yanzu yaƙin namu ne, kuma da izinin Ubangiji mune da nasara, zamuyi nasara akan mugaye kuma azzaluman mutane, waɗanda suke azabtar da ruhin ƴan uwansu da ZAFIN WUTA, zan zo gare ki" "Halimatu.""." 𝐙𝐀𝐅𝐈𝐍 𝐖𝐔𝐓𝐀 LABARI ME CIKE DA "BAN TAUSAYI, MATSANANCIYAR DAMUWA, " "KUNCIN CUZIYA, " "SADAUKARWA, " ZAZZAFAR SOYAYYA ME TSAYAWA A RUHI. WRITING BY MARYAM STAR YAR BAIWAR JJRT. MARUBUCIYAR RAYUWAR SAMHAD DAFIN MACIJI A DAREN AURENA AND NOW ZAFIN WUTA *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION* *(J.W.A)* THE NOBLE WRITER'S TEAM PAID BOOK 500 ONLY BOOK TWO CHAPTER 13 ميحرلا نمحرلا الله مسب "Sauke wayar Sadiya ta yi, tana jin wani ƙarfin gangar jiki da zuciya na zuwa ma ta lokaci ɗaya, sai ta tashi" "zumbur tare da kama hanun Alhaji Umar ta nufi toilet da shi, alwala ta ɗauro shima ta taimaka ma shi yayo alwalar suka fito a tare, sallaya ta shimfiɗa musu, nan suka shiga jero salloli babu ƙaƙƙautawa, yayinda take sauke dukkan buƙatunta idan tai sujjada, duka rauninta da gazawa take tattarowa ta roƙi ubangiji ya yaye musu wannan wahalhalun rayuwar da suke fuskata, ya sauƙaƙa musu ƙaddarorin da ke" sake kutsowa cikin rayuwarsu. AGEGE ABBA "Tun ranar da Umma ta satarwa Abba kuɗi ya canza salo, yanzu baya zama da kuɗi a jikinshi, banki ya je" "ya buɗe account har guda uku, ya zuba rabi da kwatar kuɗin, sannan ya bazama wajen malamai ya na neman fassarar mafarkan da suka addabi rayuwarshi, muddin zai kwanta ya rufe ido da sunan barci, to sai yayi mafarki akaina, kuma ya bada sunan Mama akan a karkato da hankalinta gareshi, dan yanzu ta zage sai ɗibar albarka ta ke ma shi, bata ragawa kowa ba yanzu, bata barin bashin magana, sannan kuma ya na so a rufe mashi bakin Umma aka kuɗin da yake so ya bawa Mama wanda Alhaji Abdallah me gwalagwalai ya umurta akan a bata, duk da ba duka zai bata ba amma yasan dole za'ayi rigima da Umma" akan kuɗin. "Ranshi fes ya dawo gida ya ci gaba da gudanar da sabgogin gabanshi, yau dai shiru kukejin bakin" "Umma, ko ƴan kudaɗen da ake damfarar Abba ba'a amsa ba, sai faman kaiwa da komowa take ta na shafce gumi, aikin girki ta ke, amma idan kukaga zanin jikinta kamar me yin aikin ƙuli zanin dawan- dawan da shi kamar tsuman sauke tukunya, takalmi gamin bauta ne ta saka a ƙafarta, sai faman zarya ta ke daga ɗaki zuwa inda ake girki, duk bayan mintuna uku sai kaga ta kamo haɓar zani ta fyace majina," sai ta buɗa tukunya ta jujjuya sannan ta rufe ta koma ɗaki. "Mama ma yau ta na ɗaki zamanta ta ci kwalliya tana girki a gas ɗin sai ƙamshi ke tashi gwanin daɗi," "yanzu Mama idan ba alwala ko shiga bayi ba ba ta fiye fitowa waje ta zaunaba, tafi zamanta a ɗaki ita kaɗai abin ta, duk wanda tsautsayi ya saka yai ma ta ba daidai ba zai fuskanci ɓacin rai, bata shayin kowa" yanzu ta zama masifaffiyar ƙarfi da yaji. ABUJA LAWAN. "Zaune ya ke a gaban wani rami, hannunshi a zura tare ɗauko wa ta ƴar tsana wacce aka ɗaure ƙirjinta da" "wa ta yar tsoka, jikin tsokar an caccaka allurai, wani jini ya ɗauko cikin ƴar ruba ya shiga kwararawa a jikin ƴar tsanar ya na diga cikin ramin, maida ƴar tsanar yayi tare da mayarda ƙasa ya rufe sannan ya maida grass carpet a wajen kamar ba'ayi komi ba, kakkaɓe hannunsa ya yi tare da zuwa gaban tap ya" wanke tsa sannan ya fice daga gardeng ɗin. "Manyan mutane ne zaune a babban parlon su uku su na, ko wannensu da ƙaton tunbi a gaba, ga" "gemunansu duk farin gashi alamar anfara kwana biyu, fuskokinsu a murtuke babu fara'a ko kaɗan." """Barkanku da ƙarasowa manyan giwaye, yanzu nike """ """Dakata Lawan, ba zuwa jin tatsuniyar da ka saba shirya manah ya kawomu nan ba, zuwa muka yi jin" "muye dalilinda yasa baka cika aikin da muka umurceka da shi ba tun shekaru ashirin da ɗaya da suka shuɗe, mufa ba yara bane da zaka zauna kana tsara mu da ƙarairaki, munzo ne muji ta inda ka bari aka" "samu matsala."" Ɗaya daga cikinsu ya faɗi tare da cafar tufa ya gatsa a baki babu ko basmala." """Muƙuttt"" Lawan ya haɗe yawu me kauri, hasashe ya ke wane aiki ne nasu bai cika ba, tun da har suka" "yo tattaki suka suka zo har inda yake a daidai wannan lokacin babu sanarwa yasan ƙiyamarshi na daf da tsayawa, sake bin su da idanu yayi yana ƙare masu kallo a zuciyarshi yana furta." """Ale Dikko Zakin fama, Alhaji Balarabe Basani ba sabo, Alhaji Mas'ud Cinnaka bakasan na gida ba, sai" "na ƙarshensu oga kwata-kwata Alhaji Muhammad Bello Kuraye, manyan mutanenda ake damawa da su a fannin siyaya da kasuwanci, mutanen da al'umma ke yiwa kallon shuwagabanni na kwarai, har talaka" "na yi musu laƙani da baya goya marayu, saboda yanda suke hidimtawa jama'a da aljihunansu, sai de kash," "su ɗin kura ne lulluɓe da fatar akuya, sun kasance masu taka muhimmiyar rawa wajen ƙuntatawa talakawa ta ƙarƙashin ƙasa, suɗin taurarine masu wutsiya ganinsu sam babu alkairi." "Saita kanshi ya yi tare da sake sunkui da kai ya aro bangon nutsuwa ya yafawa kanshi, sannan ya" rausayar da murya yana faɗin. """Kuyi min aikin gafara, nidai a iya sanina ban bar ko ɗaya daga cikin ayyukan da kuka taɓa saka ni," "niɗin tamkar ƙasƙantacen bawa ne a gabanku, na kasance ina jiran umurninku dan biyanku akan halaccin da kuka taɓa yimin, kuyimin aikin gafara saboda ni ɗan Adam ne kuma ajazi, ko zan iya sanin aikin dana kuskure akanshi idan da hali in gyara shi yanzu-yanzu.""" "Wa ta dalleliyar baƙar harare Ake Dikko ya dallawa Lawan, yana jin kamar ya murɗe wuyanshi ya raba" "shi da numfashinsa, sabosa tsabar fusata da abin da ya yi musu." """Shin ko kasan cewa ƴaƴan tsohon amininka Alhaji Umar su na nan raye a duniya, shin ko kasan cewa" "rayuwa da burikanmu su na dab da rushewa ta sanadiyyar sakacinka, shin tayaya yaranda ka tabbatar" "manah d sun mutu suke a raye, ta ina wanda ya mutu zai dawo, shin ko za ka iya faɗa mana ta yanda akai haka ta faru."" Cewar oga kwata-kwata Muhammad Bello." "Wani irin ƙugin tashin hankali ne cikin Lawan ya yi, yayin da idanuwansa suka firfito waje cike da tashin" "hankali gami da firgici, zufa ce ta shiga karyo ma shi daga cikin kai ta na tsiyaya har cikin rigarshi, sau bakwai ya na buɗe baki zai yi magana amma sai maganar ta maƙale ta gagara fitowa sakamakon" numfashinshi da ke barazanar ɗaukewa. Babu ko tausayi a fuskokinsu suka shiga zayyano ma shi kalolin uƙuba da tashin hankalin da zai fuskanta "matsawar bincike ya sake tabbatar musu ƴaƴan Alhaji Umar su na raye, tsallake shi sukayi ba tare da ko" tausayi ba suka fice suka barshi a halin firgici da ɗimauta. "Zarya ya ke tsakanin bango zuwa bango, ya na lissafa ta yanda za'ayi ace yaranda Fatima Abbas ta" tabbatar masa da mutuwarsu za'ace su na raye. """Wait, shin wai ma wacece Fatima Abbas, kuma wacece Sadiya matar Alhaji Umar.""" Ya jefawa kanshi tambayar tare da tsallakawa tunanin abubuwanda suka shuɗe acan baya. "Alhaji Abbas ɗan kasuwa ne babba, ya na kasuwancin siminti da buloluwa, tun farko ya fara ne da gina" "gidan bulon ƙasa, kafin daga bisani zamani ya zo aka fara yin ginin bulon siminti, a wancan lokacin za'a saka Abbas cikin jerin ƴan kasuwa masu faɗa a ji, babu inda simintin Abbas bai zagayaba a Nigeria, yayi aure tun ƙuruciya inda akai masa auren haɗi shi da ƴar uwarsa Hadiza, kasancewa Hasiza nutsatsiyar kamilar yarinya ya saka Abbas fara sonta, dan shi yana son mace me kamun kai da kunya, bayan aurensu sun gina rayuwa me tsari dabin turban addinin musulinci, su na girmama junansu sosai hakan ya sake ƙarfafa soyayyar tsakaninsu ta rikiɗe ta koma zazzafar ƙauna, sun ɗauki lokaci basu samu albarkar aure ba wato haihuwa inda iyayen Hadiza da kansu suka matsa akan ya ƙara aure gudun kar ace matsalar daga Hadiza ne, da farko yaso yai tiejiya amma da suka bashi kwararan hujjoji sai ai na'am da hakan ya kuma basu wuƙa da nama akan su zaɓa ma shi wacce ta dace, sunji daɗin karamcin da yayi musu hakan yasaka mahaifiyar Hadiza ta nema ma shi auren ƙanwar abiyar zamanta, itama ta na da nutsuwa sosai ga girmama mutane sannan ta na da addini dan kusan tare suka taso da Hadiza, ba'awani ɗauki lokaci ba aka saka ranar aure Abbas da Karima, inda Hadiza ta shiga sahun gaba wajen masu murnan haɗin wannan auren da iyayenta sukai, bayan anyi auren Karima da Abbas suka haɗe kansu da Hadiza suka" samar sa wanzajen farin ciki a gidan Abbas. "Bayan shekara ɗaya da aure Karima ta haifawa Abbas ƴa mace, wace taci sunan mahaifiyar hadiza ana" "Fateema ana kiranta da Inno, Hadizama ba'aɗauki lokaciba ta santalo ƴan biyu kyawawan gaske" "waɗanda suka biyo ta, tsakanin Karima da Abbas aka rasa gane wanne yafi farin ciki, dan su suka raini" ƴaƴan iyakar Hadiza da su shayarwa. "Rayuwa na ƙara gaba Abbas na sake samun dukiya da arziƙi me tarin yawa, inda ya baro garin Katsina ya" "dawo Kano da zama yaci gaba da gudanar da harkokinsa, Hadiza nada yara uku yan biyu Hassan da Husaini sai gambonsu Aama'u, ita kuma Karima tun haihuwar Fatima ba ta sake samun haihuwa ba, bayan an yayeta yayar Karima Wasila ta ɗauketa daga yaye ta riƙe ta ce tayi ƴa, bayan dawowarsu kano da shekara biyu Hadiza ta haifo sntaleliyar ƴar auta, wace ta biyo ainahin kamanin maaifinta Abbas, fara me dogon hanci da manyan idanuwa haɗi da sisilkan baƙin gashi, aka saka mata suna Halimatus Sadiya, shaƙuwa me tsanani ce ta shiga tsakanin Sadiya da mahaifinta, inda ya je ririta ta, sosai Karima ke nunawa Sadiya soyayya ta gaske, komi ta samu Sadiya ahankali ta janyota tadawo da ita ɗakinta da" kwana. "Shekaru sun ja da dama, yanzu Alhaji Abbas ya zama babban mutum, kuma ɗan kasuwa wanda ake" "damawa da shi ta harkar kasuwanci, Allah yayiwa Hassan ɗanshi rasuwa sai Husaini da sadiya da Asma'u ne kawai ƴaƴansa, tuni ya barwa Anty Wasila Fatima kyauta halak malak saboda Allah bai basu haihuwaba ita da mijinta, Karima kuma bata ce komi ba akan hakan dan yanzu ida ba sa ni kaiba ba zaka" ce ba ita ta haifi Sadiya da Asma'u ba. "Hussaini yayan Sadiya ya taso d son ilimin islamic, inda ya gaji Kakanshi Malam Iro ta fanin sanin" "magungunan gargajiya da likitanci a musulunci, sannan ya na tare da baiwar gane sihiri ko sammu," "wannan yasaka ace kiranshi da Malam, Malam na matuƙar ƙaunar Sadiya, bayason duk wani abu wanda" "zai ɓata ma ta rai, idan ka ji hayaniyarshi to akan an taɓa Sadiya ne." Sadiya ta gama secondary school Alhaji Abbas ya turata Zaria gidan ɗan uwa kuma babban abokinshi ta "yi kadatu a A B U, a canne Sadiya ta haɗu da Fatima Abbas wacce itama tazo karatu a fanin kasuwanci, ba tare da sanin suɗin ƴan uwa ba ne suka ƙulla ƙawance, koda yaushe su na a tare, duk inda kaga" Fatima to zaka ga Sadiya a wajen. "LITTAFIN ZAFIN WUTA PAID BOOK NE, ZA KI BIYA 500 KACAL DOMIN KI MALLAKI NAKI." 9136291920 MARYAM UMAR OPAY TAKU HAR KULLUM ME SON GANIN FARIN CIKINKU. MARYAM STAR KE MUKU FATAN ALKIRI . 𝐙𝐀𝐅𝐈𝐍 𝐖𝐔𝐓𝐀 LABARI ME CIKE DA "BAN TAUSAYI, MATSANANCIYAR DAMUWA, " "KUNCIN CUZIYA, " "SADAUKARWA, " ZAZZAFAR SOYAYYA ME TSAYAWA A RUHI. WRITING BY MARYAM STAR YAR BAIWAR JJRT. MARUBUCIYAR RAYUWAR SAMHAD DAFIN MACIJI A DAREN AURENA AND NOW ZAFIN WUTA *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION* *(J.W.A)* THE NOBLE WRITER'S TEAM PAID BOOK 500 ONLY BOOK TWO CHAPTER 14 ميحرلا نمحرلا الله مسب "Kowane lactura yasan da zaman Fatima Abbas da Sadiya Abbas, kasancewarsu masu ƙoƙari da maida" "hankali sosai akan karatu, lacturas na alfahari da su sosai saboda ƙwazonsu." "A makaranta ne Sadiya ta haɗu da wani kyakkyawan matashi me ji da naira, ba dalibi bane lactura ne" "shima, shike ɗaukarsu a fanin kasuwanci, tun ranar da ya ɗora idanuwansa akan Sadiya matsananciyar ƙaunarta ta mamaye shi, sam baida sukuni sai yaga Sadiya, gashi ya rasa ta hanyar da zaibi wajen sanar da ita yana sonta, ganin zaiwa kanshi illa sai ya shirya takanas ya je har ƙofar shiga hostel ɗinsu ya nemi a kira ma shi Fateema Abbas, sosai Fateema Abbas tai mamakin jin cewar sir Umar Aminullah na nemanta," "saboda zumuɗi kasa tsayawa tai Sadiya ta fito daga wanka ta sanar ma ta tai, sai kawai ta shiga gyara" "fuskarta ta na fatan ace yazo wajenda da wani abu me kama da soyayya, cike da ɗauki ta fita ta nufi" "wajen da aka kwatanta mata, da zuwanta ta taras da shi tsaye kusa da tsadaddiyar motarsa ya na jifarta da tsadaden murmushi, da kyar ta saita kanta ta dan karta kwafsa, dan sai yanzu ta sake nutsuwa ta na ƙarewa halitarshi kallo, wa ta kibiyar ƙaunarshi ce ta soke ta a ƙahon zuciyarta nan take, murmushin da" yake sakar ma ta ya sake ingizata ta afka cikin kogin ƙaunarsa. Ta na maida ma shi da martanin murmushin ta tsaya tare da yin sallama cikin saura ainahin sautin muryarta wanda itama batasan ya aka yi ta samu kanta da sauya murya ba. "Sai de kash, Umar yayi nasarar dugunzuma tunani da zuciyar Fateema Abbas ta hanyar faɗa ma ta yazo" "ne ta shige mashi gaba wajen samun soyayyar ƙawarta Sadiya, inda ya warware ma ta yanda yake fama" "da gyambon sonta a zuciyarsa, yanzu yakai matakin da ko barcin kirki baya samu." "Wa ta zufar tashin hankali ce ta tsatsafowa Fateema Abbs, yayinda ta ke kokowa da harshenta wajen" "ganin bata dannawa Umar manya-manyan ashariya ba, ta daɗe bata ce komi ba, shiko ganin shirun yayi yawa ya saka shi tunanin ko Sadiyar na da wanda take so, tunanin hakan kaɗai sai da ya dugunzuma" "nutsuwar zuciyarshi, amma yai ƙoƙari wajen saita kanshi." "Fateema bata da wani zaɓi a lokacin sai cewa da tayi karya damu zata tuntuɓi ƙawarta akan zance, duk" abin da kenan zata sanar da shi. Sosai Sir Umar ya ji daɗin wanan zance hakan ya saka yaiwa Fateema kyautar kuɗi masu kauri waɗanda suka sake karyar ma ta da zuciya ta kuma sake jin soyayyarshi na yunƙuron ma ta da ƙarfin gaske. Bayan tafiyar Sir Umar Fateema ba ta koma "hostel ba ta nemi wani ɗan tudu ta zauna ta na sharce hawayen baƙin ciki, ta na nan zaune wasu ƴan" "class ɗinsu gungu guda suka zo wajen, ashe duk abin da ya faru tsakaninta da Sir Umar akan idonsu ne," "hakan ya saka suka taho dan suji gulma, har musayar yawu sukai akan zuwa yai wajenta ya ce ya na sonta, dan Fateema Abbas babu laifi kyakkyawa ce itama, gata doguwa kamar Sadiya." Kuka ne me sauti ya kubcewa Fateema Abbas lokacin da suke tambayarta abin da ya faru suka ga ta na "hawaye ga kuma kuɗi a hanunta, sanna kuma duk sunga zuwan Sir Umar wajenda." "Fateema Abbas sam bata da sirri, tanan wajenne kawai ake jin kansu ita da Sadiya, kwashe komi ta yi" "ta faɗi ma su tana sakw fashewa da kukan takaici da hassada, aiko nan suka zagaye ta suka dinga famfata akan karta yarda ta barwa Sadiya Sir Umar, da ita ya dace ba da Sadiya ba, sannan suka hanata" "faɗawa Sadiya yana sonta, aiko Fateema Abbas tahau kan zugarsu ta zauna, a maimakon ta koma hostel" "sai kawai ta bisu nasu hostel ɗin can suka shantake su na ta firar duniya, da yawa daga cikinsu sun daɗe su na jiran wannan rana da zasu samu damar shiga jikin ɗaya daga cikin ƙawayen, kowa na son mu'amula da su saboda baiwarsu ta karatu, amma Sadiya sam bata bawa mutane fuskar, har gara ma" Fateema Abbas ita takan ɗan kula wasu dan ta na da son mutane. "A ranar Sadiya ta nemi Fateema Abbas amma bata ganta ba, ta yi ƙoƙarin kiranta a waya amma bata" "same ta ba, haka ta ƙarashe wunin sukuku da ita, sun saba duk inda zasu je su na tare, koda fita ta kama ɗaya to dole ƴar uwarta za ta sa ni, Fateema Abbas bata dawo ba sai can cikin dare, lokacin har Sadiya ta kwanta barci saboda ta n tashi tayi karatu cikin dare saboda tunkarowar exam, harara Fateema Abbas ta aikawa Sadiya sannan ta juya baya tai kwanciyarta cike da tunanin Sir Umar har barci yai awon gaba da ita, ba ita ta farka ba sai da asubahi shima Sadiya ce ta tada ita, lokacin da ta buɗe ido tai arba da innocent face ɗin Sadiya tunanin yanda Sir Umar ya karkace ya saki baki ya shiga karanto ma ta yanda yake ƙaunar Sadiyar, nanda nan ta haɗe dai ta kuma daina ganin kyawun fuskar Sadiyar sai wani muni da baƙi da take gani, a yatsine ta tashi ba tare da ta kula Sadiya ba ta shige toilet, koda ta fito ta iske har Sadiya ta gama shirinta ta na shirin ɗaura girkin abin kari, dakatar da ita Fateema Abbas ta yi akan karta haɗa da ita idan ta tashi ta haɗa iya nata, Sadiya bata damu da hakan ba dan tanada fahimta sosai kuma" bata damuwa da abin da ba'a saka ta ba. "Daga ranar Fateema Abbas ta daina shigewa Sadiya sai ya zama dole, yanzu komi da suke yi tare" Fateema Abbas ta ware kanta gefe ita da sabbin ƙawayenta su Zee baby da Ayush ƴar wanka. "Wa ta rana Sadiya na zaune a bakin bishiya ta na karatu gabanta lemo da ruwa ne ta na kurɓa a hankali," "Sir Umar ne ya gifto ta wajen sai ya hangeta zaune ita kaɗai, bai yi wata-wata ba ya isa wajen tare sa sallamarshi a baki, amsawa Sadiya ta yi tare da ɗago ido ta kalli mamallakin wannan muryar, karaf idonta ya sarƙe a ciki nashi idon, inda ya hanata janye nata yayi amfani da damar ya fara aika mata da sakonin da ke cikin zuciyarshi ta idon, cike da kunya Sadiya ta sauke kanta ƙasa tana jin wani yanayi haɗi da faɗuwar gaba a lokac ɗaya, a taƙaice dai ranar Sir Umar yai nasarar jefa kwallon soyayyarshi a zuciyar Sadiya bai yarda ya bar wajen ba sai da ya ɓata lokaci ya kuma tabbatar da ya samu karɓuwa sannan ya" rabu da ita cikin shauƙin ƙaunarta. "Soyayya me tsafta ce ta shiga tsakanin Sir Umar da Sadiya, yayinda Fateema Abbas ta koma gefe ta na" "jinyar zuciyarta tare da ɗaukar shawarar su Zee ta nesanta kanta da Sadiya, sai de kuma hakan ya bawa Sadiya damar sakewa da Sir Umar, babu me takura ma ta, sannan yanzu tafi jin daɗin karatun saboda" "kusan duk weekend su na zama ita da Sir Umar su yi lesson, yayinda kaidin basirarta ya daɗa ƙara" soyayyarta a zuciyar Umar dan ya fahimci ita ɗin daban take da sauran mata. Lokacinda aka yi hutu ne Sir Umar yabi Sadiya har gida Kano ya gaisa da Alaji Abbas tare sa gabatar "mashi da kanshi a matsayin siriki, anan ne Alhaji Abbas ya fahimci Sir Umar ɗan gidan Babban ɗan kasuwa ne wanda ake ji da shi a lokacin, bai yi wata-wata ba ya amince tare da bashi damar turo magabatanshi dan a tsaida magana tunda yanzu Sadiya na ajin ƙarshe." "Babu ɓata lokaci Sir Umar ya sanar da mahaifinshi komi da kuma yanda sukai da Alhaji Abbas, bincike" "Alhaji Ibrahim ya saka akai ma shi akan Sadiya sa mahaifinta, ya ji daɗin sakamakon bincike inda anan ne ya fahimci Sadiya ɗiyar Abbas me siminti ce, babu ɓata lokaci manya suka shiga maganar aka tsaida lokacin aure bayan Sadiya sun yi candy, bayan Sadiya ta koma makaranta bata sanar sa kowa saka ranarta ba, amma ta kusan dayawa sun fahimci soyayya suke ita da sir Umar, hakan sam baiyiwa wasu dayawa daɗi ba, ana cikin haka kwatsam wani mutum ya shigo rayuwar sir Umar, inda ya fara da bin diddiginshi, ananne ya gane ansaka mashi rana da ɗalibarsa, baiyi wata-wata ba ya tsananta bincike akan Sadiya da waɗanda take mu'amala da su, Fateema Abbas ita kaɗaice ƙawa ga Sadiya hakan ya saka ya je" ya sanar sa me gidanshi ansamu mutum ɗaya da take da kusanci da matar da sir Umar zai aura. Sosai Muhammad Dikko ya jinjina ƙoƙarin sabon yaron da ya taimaka ya kuɓutar da rayuwarshi daga hannun ƴan fashi da makami wato Lawan. "Lawan dai almajiri ne wanda tun yana shekara shidda mahaifinsa ya kawoshi almajiranci, amma tunda" "ya dire shi a Kano bai sake waiwayarshi ba, Lawan ya taso cikin matsi da ƙyara daga sauran ƴan uwanshi almajirai, da yawa kanyi ma shi gori akan rashin sanin asalin garinshi ko ƴan uwanshi, tun yana damuwa harya daina damuwa dakanshi ya sanar da su cewa shi ɗan shege ne baida uba, hakan ya taka rawar gani sosai wajen sake ƙyamatarshi, babu me raɓarshi bare yayi abota da shi, ana cikin haka ne wata raba bayan ya girma ya zama tantirin ɓarawo kuma marar ji ya fita sata cikin wata unguwar masu kuɗi, akan hanya ƴan fashi suka tareshi, har sun sait harsashi akanshi zasu tarwatsa ma shi kwanya saiga Muhammad Bello ya zo wajen tare da jami'an tsaro, nan take ƴan fashin suka watse kowa ya shiga gudun ceton rai, saboda ruɗewa sai da Lawan ya suma a wajen, amma sai Muhammad Bello ya bawa securty umurnin su ɗauke shi, nan aka ɗaukeshi aka kaishi asibiti aka duba lafiyarsa, washe gari ya dawo" daidai dama kawai ya shiga ruɗu ne amma babu abin da ya sameshi. "Muhammad Bello ya nemi jin tarihin Lawan, nan lawan ya faɗa ma shi komi, aiko Muhammad Bello" "ya ɗaukeshi aiki, aka bashi wajen zama a gidan aka kuma wadatashi da komi, har malamin da zai dinga yi" "mashi lesson aka samo ma sho, cikin shekara ɗaya ya waye ya goge ya zama gaye, ahankali Muhammas" "Bello ya fara janshi cikin ƴan kasuwa da kuma ƴan siyasa, duk da cewa Muhammad Bello yana gaba da sir Umar a wajen kasuwanci, kuma yafi bada ƙarfi a siyasa, amma da yaga yanda tauraron sir Umar ke haskawa, mutane kuma na yinshi sosai duk da baɗan siyasa bane sai hakan ya tsayawa Muhammad Bello a yuwa, ya dinga shege-shigen malamai akan a durƙusar da sir Umar amma sai aka tabbatar ma shi yaron yanada baiwa me ƙarfi kuma farin jininshi daga Allah ne, sannan kuma bazai yuwu ya koma ƙasan Muhammad Bello ɗin ba kamar yanda yake sakawa ana mallake ma shi sauran ƴan kasuwa da ƴan siyasa su dawo ƙasanshi, sosai abin yai wa Muhammad Bello tsaye a rai, ana nan kwatsam sai ya ji labarin akan wata babbar cibiyar kasuwanci da Alhaji Ibrahim zai buɗewa sir Umar, hakan ya sake tunzura tunzurarren ya shiga neman yanda zai samu dama koda sau ɗaya ne akan sir Umar, tofa nan ne yafara amfani Lawan ya tirashi ya shiga jikim Sir Umar amma sai hakan bai samu ba, yayi masara tunda har su na ɗan gaisawa amma daga hakan sir Umar bai bashi wata damarba, nan ne suka juya alaƙar Lawan ya koma ya shiga jikin Fateema Abbas, shine ya sauketa daga shawarar su Zee ya sake maida ita cikin rayuwar Sadiya, a karo na biyu Sadiya ta sake amsar Fateema Abbas, sai de bata sake da ita sosaiba, sai" Fateema ta ji kamar ta rabu da Sadiyar sai kuma ta yi haƙuri tuno irin maganga da Lawan ya tsara ma ta. Haka rayuwa taci gaba ta gudana Lawan ya samo kan Fateema Abbas inda yai ma ta alƙawarin zai "mallaka ma ta sir Umar harma ta aureshi, toko ta yarda saboda gaban idonta sunsha gaisawa sa sir Umar" ɗin anan ta sake tabbatarda lallai Lawan dagaske ya ke zai haɗata da masoyinta harma suyi aure. "Bayan an yaye Sadiya da Fateema ko wace ta koma gida, anan ne aka shiga shirin biki gadan-gadan" "dan dama takowane fanni ashirye suke kuma auren ƴan gata za'ayi shi yasa kowa ya shirya tunda wuri kafin zuwan lokacin, auren Sadiya Abbas da Umar Ibrahim ya ƙayatar sosai, biki ne akai irinna ƴaƴn gata masu ji da naira, Karima ta shiga ta fita wajen sake gyara Sadiya, sai da ta maida ita ƙayatacciyar" mace sannan kuma a ɓoye Hadizama na nata aikin gyaran ba tare da sanin Karima ba. "Ansha shagulgula sosai a bikin, inda tun a lokacin Malam wato Hussain ya gano irin baiwar da sir" "Umar ke sa ita, nan ne yayi ƙoƙari wajen bashi wasu surrukan tsarin jiki wanda basu kaucewa hanya ba, sir Umar ya sake da Malam sosai inda ya nemi yazo suyi aiki a tare amma sai ya nuna ma shi shiyafi son harkar Islamic medicine kasuwanci sam bai dameshiba, aiko sir Umar ya taka rawar gani wajen Malam, dan shago ya buɗe ma shi ƙato a nan kano sanan ya cika ma shi shi da ingantattun magunguna waɗanda" akayo order su daga ƙasar Saudiyya. "LITTAFIN ZAFIN WUTA PAID BOOK NE, ZA KI BIYA 500 KACAL DOMIN KI MALLAKI NAKI." 9136291920 MARYAM UMAR OPAY TAKU HAR KULLUM ME SON GANIN FARIN CIKINKU. MARYAM STAR KE MUKU FATAN ALKIRI . 𝐙𝐀𝐅𝐈𝐍 𝐖𝐔𝐓𝐀 LABARI ME CIKE DA "BAN TAUSAYI, MATSANANCIYAR DAMUWA, " "KUNCIN CUZIYA, " "SADAUKARWA, " ZAZZAFAR SOYAYYA ME TSAYAWA A RUHI. WRITING BY MARYAM STAR YAR BAIWAR JJRT. MARUBUCIYAR RAYUWAR SAMHAD DAFIN MACIJI A DAREN AURENA AND NOW ZAFIN WUTA *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION* *(J.W.A)* THE NOBLE WRITER'S TEAM PAID BOOK 500 ONLY BOOK TWO CHAPTER 15 .ميحرلا نمحرلا الله مسب "Sosai Alhaji Abbas ya jinjinawa ƙoƙarin da sirinkinshi sir Umar ya yi wajen samawar da Malam shago, tun" "tuni Alhaji Abbas ke fafatukar sama ma shi shagon amma sai hidimomi suka shan kanshi, takanas Alhaji" "Abbas ya je har gidan mahaifin sir Umar Alhaji Ibrahim yai godiyar ban girma akan babban abin alkairin da ɗansa ya yi, hannu bibiyu Alhaji Ibrahim ya tarbi sirikin ɗan nashi." Bayan biki Sir Umar ya aje aikin koyarwa ya tsunduma tsama-tsamo cikin harkar manya-manyan "kasuwanci da taimakon mahaifinsa, a gefe guda kuma ya na tare da Lawan yanda ya zama abokinshi ta ƙarfi da yaji, dan dole yake saka Lawan ɗin a harkokinsa saboda yanda yake shige masa kuma yana yawan bashi shawarwari akan business da sauran harkoki, Muhammad Bello najin daɗin yanda Lawan ke gudanar mashi da aiyukan da yake sakashi, ganin irin kwazon da yake ya saka ya gabatar da shi wajen abokanshi su Ale Dikko Zaki da sauran manyan abokanan shi da suke gudanar da harƙalloli ta ƙarƙashin" ƙasa. "Lawan ya fara fantamawa da manyan kuɗaɗe da kuma motoci, dan yanzu sosai yake ɗaukar kasada ko" "wace iri ce, aiki na biyu da ya gudanarwa su Ale Dikko shine kisan kai, wani ɗan kasuwa da yaƙi basu goyon baya akan buƙatar da suka gabatar ma shi, shine suka gwada Lawan ta hanyar bashi aikin sheƙe mutumin, aiko babu ko ɗar Lawan ya haikewa mutum har sai da ya rabashi da duniya, sannan ya kawar" da suk wa ta sheda da zata iya fallasa shi. "Zaman lafiya gami da zazzafar soyayya Sadiya da Umar suke gudanarwa, Sadiya bata rufe shekara ɗaya" "ba ta samu ciki, inda bayan watanni tara ta sintilo kyakkyawar ƴarta mace ta ci suna Maryam su na kiranta da Miemie, sosai sir Umar yai farin ciki da samun ƙaruwar, bayan haihuwar maryam da watanni kaɗan ƙofafin arziƙi suka sake buɗewa sir Umar, inda yake gudanar da kasuwanci me tsafta anan gida Nigeria da sauran ƙasashen ƙetare, babban abin da ya sake haskaka tauraron sir Umar shine sauki da kayanshi suke da shi, indai daga compnynshi abu ya fito to za'a sameshi tsaftatacce me kyau gami da sassauƙan farashi, ganin yanda lokaci ɗaya sunan Sir Umar ya zagaye Nigeria ya saka su Muhammad Bello juyowa takanshi, dan sun nemi tattaunawa tare da shi akan ya shiga cikinsu su dinga gudanar da haramtattun harƙallolin kasuwanci a tare, amma ya taka musu burki, bazama sukai wajen malama da bokaye akan a disashe tauraron Sir Umar, amma duk inda suka je maganar ɗaya ce, babu wanda zai iya dakushe hasken da ke tare da shi, nan suka shiga neman rayuwarshi ta mabanbanta hanyoyi, amma sai Allah ya ku ɓutar da shi, ganin haka sai suka koma tada wuta ga companys ɗinshi da shaguna, sosai sukai ma shi ɓarna amma abin mamaki, a maimakon ya durƙushe kamar yanda suke so, sai ya daɗa yin sama, inda manyan jiga jigan ƴan kasuwa suka tallafa mashi ya sake bunƙasa kasuwancinshi, harma ya zarce na baya, ga ƙananun customers da suka dinga tayashi da addu'a domin faɗuwarshi tasu ce suma, tun wajenshi suke samun kaya a farashi mai sauki da rahusa, sake bazama su Muhammad Bello sukai wajen manyan bokaye inda suka samo wani boka da zai musu aiki akan sir Umar wanda yanzu ya zama Alhaji, amma yace ba yanzu aikin zai yuwu ba, suɗan jira kaɗan zuwa wasu ƴan shekaru da matarshi zata sake haihuwa, zata haifo yarinya ƴar baiwa wacce taurarinta zasuyi daidai danashi, ita ce zata zamo rauninshi, da ƙarfin soyayyar da zai mata ne zasuyi amfani wajen durƙusar da shi, sunji daɗin wannan bayani sosai, inda suka sake saka Lawan aiki akaro na biyu yasan ta yanda zai shiga jikin matar Alhaji Umar wato Sadiya, a wannan karon yai amfani da Fateema Abbas ne ta hanyar auenta badan tana son shi ba, ta amince da shi ne da ƙarfin asirin da yayi ma ta, bayan aurensu ne ya sake haɗa ta da Sadiya suka koma ƙawancensu, sam Fateema Abbas batason Sadiya yanzu musamman yanda ta ga irin daular da ta ke rayuwa a ciki, ga kyakkyawar ƴarta gwanin sha'awa sannan Alhaji Umar kan ririrta matarshi a gaban kowa, hakan ya saka ta sake ƙullatar Sadiyar a zuci, sannan kuma zugarda Lawan ke ma ta akan yanda yanzu Sadiya ke nuna ita ɗin matar manya ce taf ƙarfin Fateemar ya sanya ta amince da aikin da yace zai bata sannan kuma za ta samu maƙuden kuɗaɗen da harta gama rayuwa ba za iya ƙarar da su, nanfa Fateema Abbas ta sake ruɗewa dan akwaita dason abin duniya kamar yanda ta tashi ta ga uwarta Wasila" na martaba kuɗi "LITTAFIN ZAFIN WUTA PAID BOOK NE, ZA KI BIYA 500 KACAL DOMIN KI MALLAKI NAKI." 9136291920 MARYAM UMAR OPAY TAKU HAR KULLUM ME SON GANIN FARIN CIKINKU. MARYAM STAR KE MUKU FATAN ALKIRI . 𝐙𝐀𝐅𝐈𝐍 𝐖𝐔𝐓𝐀 LABARI ME CIKE DA "BAN TAUSAYI, MATSANANCIYAR DAMUWA, " "KUNCIN CUZIYA, " "SADAUKARWA, " ZAZZAFAR SOYAYYA ME TSAYAWA A RUHI. WRITING BY MARYAM STAR YAR BAIWAR JJRT. MARUBUCIYAR RAYUWAR SAMHAD DAFIN MACIJI A DAREN AURENA AND NOW ZAFIN WUTA *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION* *(J.W.A)* THE NOBLE WRITER'S TEAM PAID BOOK 500 ONLY BOOK TWO CHAPTER 16 .ميحرلا نمحرلا الله مسب "Sanu a hankali zuciyar Fateema Abbas ta fara ƙeƙashewa, ta koyi mugunta da son abin duniya kamar" "mijinta Lawan, yanzu wani lokacin atare suke gudanar da aiki idan oganninshi sun saka shi, ta na yawan yiwa Anty Wasila mahaifiyar Fateema Abbas, yanzu Sadiya da Fateema sun sake ɗinkewa sun zama abokai kamar can baya, musamman da yanzu Fateema kan siyi ƴan abubuwa na sha'awa ta kaiwa Miemie a matsayin kyauta, ance me ɗa wawa, nanda nan Sadiya ta sake amincewa da Fateema ɗari bisa ɗari, ana ahaka ne Fateema ta fuskanci Sadiya nada shigar wani cikin, batai ƙasa a gwuiwa ba ta sanar da mijinta Lawan, inda Lawan ya garzaya ya sanarda ubannin gidanshi, nan suka ɗunguma suka tafi wajen boka, boka ya sake tabbatar musu da wannan damar ce suka daɗe su na jira, nan ya basu umurnin su je su jira har ranar da za'a haihu, su tabbatar bayan kwana uku sun kawar da jinjirin daga duniya tare da" ɗayar yarinyar da aka haifa wato Miemie. Kyautar maƙudan kuɗaɗe suka yiwa Lawan akan ya san ta yanda za'ayi ya salwantar da abin da za'a "haifa, ba tare da sanin oganinsa ba ya bawa Fateema Abbas akan ta tabbatar da ta sato jinjirar Sadiya Abbas ko ta kashe jinjirar, abinka da ido a nera nan da nan Fateema tai na'am da zance ta kuma amshe" kuɗaɗen. Zuciyar Fateema Abbas ta fara karyewa ne lokacin da tai arba da Alhaji Umar ɗauke da kyakkyawar "jinjirar da matarshi Sadiya ta haifa ma shi, farin cikin da bata taɓa gani akan fuskarshi ba shi ta gani, yanda yake ririta jinjirar kaɗai ya isa ka gane cewa lallai ƙauna marar adadi ta wanzu ga wannan uban." "Karo na farko da jikin Fateema Abbas yai sanyi, sai ta ji zuciyarta ta karaya, kasancewar haryanzu Allah" "bai bata haihuwa ba, gashi kuma Allah ya ɗora ma ta son yara, idan taga anyiwa Miemie kwalliya kamar ta sace yarinyar haka take ji." "Cikin sanyin jiki ta zauna tare da gaisar da Sadiya da jiki, gaida Alhaji Umar ta yi tare da satar kallon" "jinjirar wacce idan ba gizo idonta ke ma ta gani ta yi kamar jinjirar ta saki murmushi, miƙa hannu ta yi akan ya bata jinjirar, sai da yayi ɗan jim sannan ya miƙa ma ta, amma kuma bai daina ziro hannu ba yana ma ta wasa, tunda jinjirar ta shiga hannun Fateema Abbas, zuciyarta ta tsinke, ta sauke makaman" "yaƙinta tare da ɗaukar ɗamarar tseratar da rayuwarsu, ranar sukuku ta koma gidanta, jikinta duk a mace, sai ta ji bazata iya akinba amma kuma ba zata nunawa Lawan ba, zata sake sabon tsari wajen ganin ba'a salwantar da rayukanda basu da alhakin kowa akansu, tafi tausayawa Miemie wacce tasan daɗin iyaye kan jinjirar, sabon shiri ta sake ta yanda zata taimakawa ƙawarta ba tare da Lawan sun gano ta ba, asirin da Lawan yai ma ta yanzu ya karye shiyasa take danasanin aurenshi, har gobe ta na mamaki akan yanda" ta aureshi bayan sam bata sonshi ita Sir Umar ɗinsu take so. BAYAN KWANA UKU. "Gudu take tsalawa akan tinti ta na yi tana kallon jinjirar da ke kwance ta na wasa da hannayenta, hawaye" "na kwara a idonta take faɗin. ""Ki yafe min ƙawata bazan iya zuba ido ina kallo a raba ƴarki da rayuwarta ba, hakan da zanyi shine daidai, zan tseratar da ƴarki in nisanta ta daga gareki, hakan ne kaɗai zai ba" "ƴarki damar rayuwa cikin salama.""" "Saida tabar cikin mutane sanan ta fara shiga cikin daji sannan ta yi kira a wayarta, babu jimawa sai ga" "wani mutum sanye cikin jemamun kaya, cikin sauti ta ɗauko wa ta baƙar jaka sannan ta fito, sai da ta tabbatar da babu me ganinsu sannan ta buɗe jakar, kuɗi ne shaƙare a cikin jakar nan ta bawa mutum tare da bude ma shi inda ta aje jinjirar sannan ya ɗauketa, harta tada mota za ta tafi sai kuma ta juyo ta" kalli mutumin ta na faɗin. """Ka tabbatar da ka bar garinan yau ba sai gobe ba, sannan kuma idan kana buƙatar wani abu ka kira" "layin dana baka, sunanta MUBARAKA amma naji mahaifinta na kiranta da MUBEENAH, idan kun isa legos" "ɗin ka kira ni zan haɗa ka wanda zai samo muku masauki."" ta na gama faɗin hakan ta juya tabar wajen" "da mugun gudu, akan haryar komawarta ne ta kira Lawan ta sanar da shi duk inda yake yanzu ya kasance" tare da Alhaji Umar ta aiwatar da aiki na farko yanzu za ta gama na biyu. "Cikin sauri Lawan ya shiga motar Alhaji Umar da ya tada zai je shopping, bayan sun gaisa ne ya nuna zai" "raka shi inda zasu je, babu musu ya amince dan yana cikin farin ciki yanzu da kowa fira yake yana faɗar yanda yake bala'in son jinjirar da aka haifa masa, cikin farin ciki yake zuzuta kyawun yarinyar harma ya nuna photon ta, su na tafiya su na firar yanda taron sunan zai ƙayatar, yayinda Lawan ke murmushin ƙeta a zuciyarsa, a fili kuma ya na ƙara bawa abokin nashi shawarwari akan yanda za'ayi gagarumin taro, da wannan damar Fateema Abbas tai amfani wajen zuwa ta ɗauko Miemie daga school, kai tsaye ta nufi hanyar ƙauyukan da ke kan hanyar Abuja, wani ƙauye ta samu ta tsaya akan hanyar shiga garin, babu jimawa wani mutum ya zo da mashin zai shiga garin, nan ta tare shi tare da bashi jaka cike da kuɗi ta ce so take yakai Miemie gidan me gari yace akan hanya ya tsinceta anyi accodent, mota da mutanen cikinta duk sun ƙone, dama mutumin mayen kuɗi ne, nan take ya amince da buƙatar Fateema Abbas ya ɗauki Miemie ya shiga da ita cikinngarin, gudun samun matsala sai ta kunnawa motarta wuta ta taka a ƙafa" harta fita bakin hanya ta samu ɗan mashin ya kaita inda zata samu motar shiga garin Abuja. CI GABAN LABARI Fateema Abbas na zuwa daidai nan a tunaninta ta fashe da matsanancin kuka har jijjiga jikinta ke yi. Yayinda Lawan shima ya tsaya a daidai nan sai ya fara zarya ya na tunanin kodai amanarshi Fateema "Abbas ta yi bata kashe ƴaƴan Alhaji Umar ba, sai yanzu ya tuna da ai bega gawar yaran da idonshi ba," "kiranshi tai akan ta gama aiki, shi kuma ya sanar da su Muhammad Bello daga nan su kuma suka fara aikn da boka ya saka basu." LEGOS. "LITTAFIN ZAFIN WUTA PAID BOOK NE, ZA KI BIYA 500 KACAL DOMIN KI MALLAKI NAKI." 9136291920 MARYAM UMAR OPAY TAKU HAR KULLUM ME SON GANIN FARIN CIKINKU. MARYAM STAR KE MUKU FATAN ALKIRI . 𝐙𝐀𝐅𝐈𝐍 𝐖𝐔𝐓𝐀 LABARI ME CIKE DA "BAN TAUSAYI, MATSANANCIYAR DAMUWA, " "KUNCIN CUZIYA, " "SADAUKARWA, " ZAZZAFAR SOYAYYA ME TSAYAWA A RUHI. WRITING BY MARYAM STAR YAR BAIWAR JJRT. MARUBUCIYAR RAYUWAR SAMHAD DAFIN MACIJI A DAREN AURENA AND NOW ZAFIN WUTA *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION* *(J.W.A)* THE NOBLE WRITER'S TEAM PAID BOOK 500 ONLY BOOK TWO CHAPTER 17. ميحرلا نمحرلا الله مسب LEGOS "Tun ranar da wanan abin ya faru da ni ban sake zuwa garden ba, sai dai yanzu na rage walwala sosai tun" "wani mafarki da na yi kusan sau uku da wasu mutane rungume da juna su na nuna ni suka kuka, idan na tuno da mafarkin sai inji ina kewar wani abu me muhimmanci a rayuwata, nakanyi nazari da tunani akan minene wannan abin wanda nike jin nayi nisa da shi, amma sai in gaza gane ko minene, hatta su Mommy yanzu sun san ina cikin damuwa, Hajjo ta zauna da ni dan ta ji minene matsalata amma sai na kasa ce ma" "ta komi, da ta takurni sai nace kawai ina kewar gida ne, rarrashina ta yi tare da yimin alƙawari akan idan" muka dawo daga tafiyar da zamuyi zuwa india inda za'ayiwa Fauzan aikin fata da kanta za ta saka a kaini "gida na kwana biyu, na ji daɗi hakan sosai ko babu komi zanje inga Mama." """Yau da na je wajen Fauzan sai na same shi duk wani iri, gashinan dai yayi sukuku da shi, bayan na" "shafa ma shi magani na taimaka mashi ya jingina dan yanzu jikin nashi da sauƙi har tada shi zaune mu jinginar muke yi, sai ya tsaida ni akan zamuyi magana, zaunawa na yi a ƙasan gadon ina saurarenshi amma sai naji ya ce. ""Mubaraka ki matso kusa da ni please, ina so jinyi sanyin jiikinki ko zan samu" "kwarin gwuiwar faɗa ma ki damuwata.""" "Duk da gabana ya faɗi amma sai na dake na kalleshi ta wutsiyar ido naga ni yake kallo a sanyaye, sai na" tsinci kaina da bin umurninshi na tashi na koma kusa da gadon. """Sama za ki hawo tun da ba cinye ki zanyi ba, kuma ma idan cinyekin na yi ai matata ce halal.""" "Ya yi maganar ya na tsume fuska, yanzu alhamdulillah jiki yayi kyau dan yanzu ya fara cikowa da tsoka ba" "kamar da dayake daga ƙashi sai fata ba, ina turo baki kamar ƙaramar yarinya irin shagwaɓaɓunan na ɗan ɗofana mazaunaina akan bed ɗin, amma mi sai bawan Allan nan ya dubi Allah ya janyo ni da ƙarfin zuciya na faɗa kwance mala-male akam jikinshi, zabura na yi zan sauka amma sai naji ya saka hannunshi" "ya zagaye ni, gudun kar in fama ma shi ciwo ya saka na ce cikin murya me kama da zanyi kuka." """Dan Allah Yah Fauzan ka yi haƙuri ka ga ciwo gare ka zan fama ma ka."" Da nasan abin da zai biyo baya" "da bance haka ba, matso da bakinshi ya yi a saitin kinnena ya na huromin iskar bakinshi me ɗumi, ""yammmmm"" tsigar jikina ta shiga mimiƙewa, ji na yi wani abu wanda bansan ko minene ba ya shiga bin cikin jikina, sau uku ina buɗe baki zanyi magana amma na gagara faɗin komi jin hannunshi na yawo a jikina, lumshe ido kawai na yi jin abin na neman fin ƙarfina, jin ɗayan hannunshi na yi yana cire mayafin da na yafa a kaina wanda bana ɗaura ɗan kwali sai de intubke shi, janye ribom ɗin yayi, nan take gashin ya warware kanshi, wani irin numfashi ya sauke lokacinda ƙamshin man kaina ya daki hancinshi, a hankali ya shiga wasa da gashin da hannunshi ɗaya, ɗayan kuma ya na sulalawa da shi zuwa cikin rigata bayan yayi nasarar ɓalle zip ɗin, runtse idona na yi da tsananin ƙarfi tare da riƙe hannun na shi da ahankali gudun kar in fama ma shi ciwo, bawan Allah nan bai daina abin da yake ba saima idasa tura" "hannunshi da yayi cikin rigar tare da sauke shi bisa abubuwanda suka daɗe su na tsole ma shi ido a jikina, tsak kwanyata ta daina aiki na wucin gadi, yayinda zuciyata ta shiga dokawa da tsananin ƙarfi, yayinda jikina ya sake ina karɓar saƙonin da Fauzan ke aiko min, lokacin da tafin hannunshi ya sauka aka fatar breast ɗina kusan shiɗewa ya yi, yayinda ya ɗan damƙesu kaɗan yana murzawa a hankali, yanayin da yake ciki na sake daɗuwa, nishi gami da numfashi me ɗumi ya shiga sakarmin a cikin kunne, duk lokacin da numfashinsa ya sauka cikin kunnena sai tsigogin jikina sun sake mimmiƙewa, wani yanyi gami da kasala ya dinga baibaiye ni, yayinda jikina ya muyu murus na kasa yin kataɓus, yanda ya ke yamutsa gashin kaina ya sakani lumshe ido ina jin wani bahagon daɗi na lulluɓe ni, sai da ya yamutsani kamar ya samu kwaɗon yakuwa sannan na kyale ni ya na sauke numfarfashi, lamo na yi wa ta iriyar kunya na" "lulluɓe ni, a hankali ya birkito da ni sannan ya lalubo kunena cikin kasalalliyar murya ya ce." """Miye hakan ki ka yi min Mubaraka, ke da ke jinya miye na wani haikemin, ko so kike ki ƙarasa ni.""" Ya faɗi maganar ya na sake yamutsa gashin kaina ya na wasa da shi. Ƙanƙame shi na yi amma bada ƙarfi ba ina ɓoye kaina a ƙirjinshi kunya na sake baibayeni. """Mi yasa bakya saka brezia kamar yansa Sulaima ke yi, ko so kike abubuwan su lalace tunda wuri" "alhalin ban mori sadakin da Pahpah ya biya ba."" Yai maganar ya na zugemin zif ɗin rigata tare da sakamin ribom ɗina ya ɗaure min gashi." "Wa ta iriyar kunya ce ta baibaye ni, ban san lokacin da na kwace jikina na kwasa a guje nai ɗakin Hajjo" "ba, ko mayafina ban tsaya ɗauka ba saboda kunyar abin da yai min." "Murmushi kawai Fauzan ya yi ganin yanda na tashi a hargitse na ruga, sai ya lumshe ido ya na jin" "nutsuna na safkar ma shi, yayinda sanyin da yake ji idan ina wuri yau yaji shi a cikin jikinshi, sai kawai ya" "ɗauki mayafina ya ɗaura akanshi ya na shaƙar ƙamshin turarena da ya kama mayafin, a haka barci me" daɗi ya fizgeshi. "LITTAFIN ZAFIN WUTA PAID BOOK NE, ZA KI BIYA 500 KACAL DOMIN KI MALLAKI NAKI." 9136291920 MARYAM UMAR OPAY TAKU HAR KULLUM ME SON GANIN FARIN CIKINKU. MARYAM STAR KE MUKU FATAN ALKIRI .