https://chat.whatsapp.com/Kqi1tusHnZa6SHgbTgFqlr AYRAAH BY RABI'ATU KABIR ACHADU (FULANI) YOUNG TALANTED WRITER'S ASSOCITION (YOTA) A har kullum ina jinjina a gare ki garkuwar fulani mahaifiya ta abar alfaharina SADAUKAR WA GA ACHADU'S FAMILY Yanda na fara lafiya Allah ya bani ikon kammala shi lafiya FULANI 08082101373 AYRAH PAGE 1 "A hankali take tafiya, tamkar me tausayin kasar da take takawa." "Doguwar riga ce a jikin ta tayi rolling da mayafin ta, sai glass daya ƙara ƙawata fuskar ta." "Idanun ta da suke cikin glass ta ɗago tana ƙarewa wajen kallo, ganin bataga motar gidan su ba yasa ta" ya mutsa fuskar ta. Agogon hannun ta ta kalla tana ƙara bata rai. Gefe ta koma ta tsaya ta zuba wa get ɗin makarantar ta su ido. "Wayar ta ta ɗakko tana shirin kira, taji ana mata horn, kaman bazata ɗago kanta ba sai kuma ta ɗago." Motar ta nufa cikin takun ta na nutsuwa. Kafin ta ƙarasa ya fito yana shirin buɗe mata ƙofar motar. Tana zuwa baya ta shige bata jira ya rufe mata ta rufe da kanta. """ Barka da fitowa hajiya, dan Allah kiyi hakuri wallahi oga umar ne ya tsayar dani""" Kaman bazata yi magana ba sai kuma ƙasa_ƙasa tace """bakomai""" "Har suka zo gida wayar ta take dannawa, sai da taji ana horn sannan ta ɗago daga danna wayar." "Me gadi ne ya buɗe musu get, suna gama parking ta fito." """Nagode"" daga haka ta nufi cikin gidan." "Kofar main parlown ta buɗe babu kowa sai kamshi me daɗi da yake tashi, tafiya kaɗan tayi ta ƙara buɗe" wata ƙofar parlown nan ma babu motsin kowa sai ƙarar ac da ƙamshin turaren wuta da yake tashi. Har zata wuce taga wayoyi da laptop akan 3 sitter fasa tafiya tayi ta dawo ta ƙwashe kayan. "Cikin sauri ta nufa sama, tana cize leɓan ta na ƙasa, hamdala take sosai a ranta koba komai yanzu ta" "samu a abinda zata rama, daman tana ta tunanin mezata masa ta rama abinda yayi mata." "Ƙofar ɗakin ta buɗe, da sallama ta shiga duk da bakowa a ɗakin, kaman zatayi kuka haka take ƙarewa" "ɗakin kallo, ƙwafa tayi a ranta kawai ta samu waje ta ɓoye abubuwan hannun ta ta fito." """Miemie! miemie.. miemie..""" "Tamkar yarinya yar goye haka take kiran sunan, tana nufar ɗakin miemien nata." Kusan karo suka ci a bakin ƙofa. """Kin dawo? Meyafaru kike jera min kira haka? lafiya?""" A jere take jera mata tambayar ba tare data jira amsar ta ba. """ Miemie kina ganin kafin na fita sai da na gyara ɗakina amman kinga yanda akhie ya hargitsa min shi""" Sosai idon ta ya ciko da ƙwalla duk yanda take ƙokarin shanye ta hakan ya gagara sai da ta zubo a kan fuskar ta. """ Narasa meyasa umar yake haka, muje ai yana gidan be fita""" Hannun ta taja suka nufi ɗakin shi tana me ci gaba da mita. Ƙasa suka sakko suka nufi corridon da yake wajen. Knocking miemie tayi ba tare da sun shiga ba. """ Waye anan?"" Ya tambaya daga ciki." "Cikin fushi miemie tace ""fitowa zakayi ka duba" "ai""" Yanajin muryar ta ya fito da sauri. """ Miemie meyafaru? Aida kin kira ni""" Cikin tsare gida ta kalleshi tace! """Meyasa ta gyara ɗakin ta zaka je ka ɓata mata?""" Cikin rashin gaskiya ya fara kame_kame. """Wuce ka gyara mata ɗakin ta malam kafin ranka ya ɓaci""" Babu yanda ya iya haka ya nufi saman yana galla mata harara. "Bata kula shi ba, ta samu waje ta zauna a parlown ta kunna kallo." A kusa da ita miemie ta zauna. """ Ya school ɗin""" """Alhamdullah miemie amman akwai wahala""" Murmushi tayi ta shafa kanta. "Kwanciya tayi ta ɗora kanta a cinyar miemien tamkar meyin bacci, amman idon ta biyu." "Rolling ɗin kanta ta cire mata, da glass ɗin, cikakkiyar suman kanta data sha gyara ta fara shafa mata a" hankali. "Baccin gaske ne ya fara ɗaukar ta a hakan dan dagaske ta gaji, ga kuma abinda miemien take mata a kan." Fuskar yarinyar tata take kalla cike da soyayya irin ta uwa da ɗiyar ta. Yana sakkowa daga benen ya gansu a haka. Kaman ƙaramin yaro haka ya taɓe bakin shi. """Miemie nima zan kwanta a cinyar ki bacci zanyi""" Ɗagowa tayi tana kallon shi da murmushi a fuskar ta. """ Yaushe zaka girma ne umar?""" Murmushi yayi ya shafa kanshi. """ Babu rana miemie""" Kanta kawai ta girgiza. "Zama yayi a wajen ƙafar ta, shima ya ɗora kanshi a cinyar tata." Hannun ta ta ɗora akan lallausar sumar shi tana shafawa. Idon shi kawai ya lumshe yana jin daɗin abinda take masa. Fuskar yaran nata take kalla tana hamdala a cikin ranta. "Kaman su har ta ɓaci tare da juna, bambancin su kawai shi namiji ne ita kuma mace ce." Amman sosai suke kama. Tunda suka fara magana da miemie ta farka daman baccin nata ba wani nisa yayi ba. Sai da ta bari ya sakan kance ta mintsine shi a wuya ba tare da miemien ta kula ba. Ƙara yasaki yana ɗago kanshi da sauri. Wajen yake shafawa yana kallon ta a haka bazaka ce ita ta aikata abinda tayin ba. """Meyafaru Umar?""" """Amman dai miemie kina ganin yarinyar nan ta mintsine ni a wuya na ko""" """Bana son sharri yarinyar da take bacci yaushe ta mintsi neka""" "Miƙewa yayi kawai ya nufi ɗakin shi, yana ayyana wa a ranshi ze kamata ne ai." Murmushi ne ya ƙwace mata ganin ta kore shi daga wajen. ★★★★★ Tafiya yake fuskar shi sam babu alamun rahama a tare da shi. Napep ya tare yace ya kaishi hotoro. Yana sauka daga napep ya tun kari layin da kai daka ganshi basai ance maka na masu hannu da shuni bane. Tun da ya tun karo gidan ya ƙara haɗe ranshi tamkar besan wani abu wai shi fara'a ba. Knocking yayi ya kai a ƙalla 5 minutes a tsaye kafin a buɗe mishi. "Me gadin yana bashi hannu su gaisa, ko bi ta kanshi beyi ba ya samu waje ya zauna." "Be daɗe da zama ba ya fara jin ƙarar takalmi yana tun karo inda yake, be ɗago kanshi ba dan ya riga da" yasan wacece me tafiyar. Tunda ta tun karo shi take sakin murmushi tamkar wawuya. """Baby daman kazo amman baka kirani a waya ba, yanzu da banji a jiki na kananan ba na fito dasai dai" "kayi ta zama a wajen nan""" Kallo ɗaya ya mata ya ɗauke kansa. Daman bata saka rai daze mata magana ba. "Cikin da kakkiyar muryar shi, da babu alamun wasa a cikin ta yace "" gani madam kiran me kike yi min?""" """Shopping zakai kaini daman""" Hannun shi kawai ya miƙa mata. Mukullin motar ta bashi ya karɓa yayi gaba ya barta a wajen. "Bayan shi take bi tana ƙare mishi kallo, tabbas a yanda ta tsani talaka idan har wani yace mata zata faɗa" soyayya da talakan mutumin da bashi da komai bazata taɓa yadda ba. "Ita kanta tasan zuciyar ta bata mata adalci ba, yanda yake wulaƙanta ta ya kamata ace ta haƙura ta rabu" "da shi, sai dai kome ze faru sai ta aure shi." "Wajen driver ya buɗe ya shiga, itama gaban motar ta shiga." Ci kanta be ce mata ba yaja motar a guje suka bar gidan. "Wellcare ya kaita dake nan Obasanjo road, tun da yayi parking ya lumshe idon shi." "Kallon shi take kaman zata cinye shi, harta buɗe motar ta juyo" """babe ka taso mu shiga tare mana""" Mugun kallon daya watsa mata shiyasa ta fita daga motar babu shiri. "Ba wata siyyar arziƙi tayi ba ta fito, daman kawai dan ta ganshi ne ta kira shi tace yazo tana neman shi," "yace mata yana da uzuri, ta haɗa shi da dad ɗin ta, wanda be isa ya tsallake maganar shi ba." Tana shiga motar yaja suka bar wajen. "Duk da kallon da take mishi yana takura shi, amman ya kasa ce mata ci kanta, dan gani yake yiwa" yarinyar magana tamkar ya faɗo ne. Suna zuwa yayi parking kafin ta fito har ya ɗau hanyar bakin get. Tamkar zatayi kuka haka tabi bayan shi da kallo. "Cikin gidan ta nufa tamkar zata tashi sama, cikin zafin rai tayi watsi da kayan data siyo." Mahaifiyar ta da take zaune a parlown ne ta ɗago tana kallon ta. """Meyafaru?""" Kukan baƙin ciki ne ya ƙwace mata...... FULANI 08082101373 https://chat.whatsapp.com/Kqi1tusHnZa6SHgbTgFqlr https://chat.whatsapp.com/Kqi1tusHnZa6SHgbTgFqlr AYRAAH BY RABI'ATU KABIR ACHADU (FULANI) YOUNG TALANTED WRITER'S ASSOCITION (YOTA) A har kullum ina jinjina a gare ki garkuwar fulani mahaifiya ta abar alfaharina SADAUKAR WA GA ACHADU'S FAMILY Yanda na fara lafiya Allah ya bani ikon kammala shi lafiya FULANI 08082101373 AYRAH PAGE 2 "Gaba ɗaya ta kasa magana tsabar kuka, sai ajiyar zuciya da take saukewa." ★★★★ Ganin baccin ta yayi nisa ne yasa miemie tashi ta samata pillown kujera a kanta. Kitchen ta nufa ta ɗora abincin dare. Har ya kwanta ya taso da niyar ɗaukar laptop ɗin shi da wayar shi zeyi amfani da su. Ganin yanda take bacci cikin nutsuwa ne yasa yayi murmushin mugunta. "Fridge ya buɗe ya ɗakko ruwan sanyi ƙarara, buɗe bakin robar yayi tun daga saman kanta ya fara juye" mata ruwan yana dariya. "A firgice ta tashi daga baccin, tana kame jikin ta." Tasan daman babu me mata abin nan sai shi ɗin. Ƙara ta fasa """miemieeeee""" Kafin ma ta fito ta tashi ta biyo shi a guje tana kuka. """Allah akhie sai na rama, Wallahi bazan yarda ba""" "Sosai suke guje guje a parlown tamkar ƙananun yara, sai ya tsaya kaman zata kama shi sai kuma yayi" tsalle ya tsallaka wani ɓarin. Tana kuka shi kuma yana dariya gaba ɗaya sun har gitsa parlown. "Tun ɗazu miemie tana tsaye tana kallon su, tama rasa mezata ce musu, kanta kawai ta girgiza ta koma" kitchen ɗin. Sai da ya tabbatar ta gaji sannan ya riƙe ta. Duk yanda take kokawar ƙwatar kanta ta kasa. "Zama yayi da ita a jikin shi, suna maida numfashi." Ganin ta kasa ƙwacewa ne yasa ta ƙara fashe wa da kuka. """Waike bakya gajiya da kuka ne?""" """Meyasa ka jiƙani toh?""" "Nima ba mintsini na kikayi ba ɗazu ba""" """Amman akhie Kasan bansan ruwan sanyi ko""" Shiru yayi alamun tunani sai kuma yace """bansaniba""" Kwace kanta tayi kawai ta nufi sama tana gunguni. "Wanka ta shiga, ta ɗakko hand driyer ta busar da gashin ta dan ya jiƙa mata." Sai da ya gama huta wa ya tashi da niyyar ɗaukar kayan shi. Sosai yake duba parlown amman kayan suka ce ɗauke ni inda ka ajiye ni. """AYRAH! AYRAH!! AYRAH!!""" "Tana jin shi tayi mishi banza, saman ya hayo kaman ze tashi sama." Handle ɗin dakin ya murɗa. """Ayrah bani kaya na""" Bata juyo ba kuma bata ce masa komai ba. """Ayrah magana nake miki fa""" """ Toh wai akhie ka bani ajiyar kayan ka ne""" Yanda ta tsare shi da manyan idanun tane yasa yayi kan ta kaman ze dake ta. """Wayyo Allah miemiena, miemie kin ganshi ko"" sosai take ihu kuma taƙi guduwa." Jin alamar tawowar miemien ne yasa ya nufi ƙofar da sauri ze saka key sai dai kafin ya saka har ta shigo ɗakin. """ Wai kai wane irin mutum ne umar kai ta biye mata, bafa sa'ar ka bace kabawa yarinyar nan 10 years" "masu kyau amman kaita saka ta kuka, kai wane irin babban kwabo ne""" Kaman zeyi kuka yace """miemie computer ta da wayoyi na ta ɗauke""" """Lah akhie ni yaushe na ɗaukar maka kaya?""" Tana laɓe bayan miemie tana masa gwalo. Rasa abinda zeyi ne yasa ya juya ya bar ɗakin. """Ayrah ina kayan shi suke""" """Ayya miemie""" "Shitttt ta ɗora ya tsanta a leɓan ta, ""ki kai masa abun sa na faɗa miki""" Tura mata baki tayi ba tace komai ba. "Juyawa tayi ta fita tana mita a fili, yara kaman mage da ɓera, basa gajiya da faɗa, indai suna gida bakin ta" kaman zeyi tsini tsabar magana. ★★★★ "Yana fitowa daga layin gidan, napep ya tara yace ya kaishi goran dutse." "Tunda ya tun karo layin ya ƙarawa tafiyar shi sassarfa, dan hankalin shi na cikin gidan." "Mukulli ya saka ya buɗe gidan, da sallama ya shiga, ɗaki biyu ne a gidan, ɗakin ƙarshe ya shiga da" sallama. Duk da yasan ba amsa mishi na ciki zeyi ba. Gaban ta ya dur ƙusa ya riƙo hannun ta. """Sannu ammie na na daɗe ko? Kiyi hakuri nima ba'a san raina na fita na barki ke kaɗai a gidan ba""" "Gyara mata kwanciyar ta yayi, ya tashi ya fita." Duk da gidan beyi datti ba haka ya gyara shi tasss. "Ɗakin ya koma, ɗan ƙaramin flasks ya ɗakko da kofi, kunu ya tsiyaya a ciki, ɗago ta yayi daga kwancen" da take. "Kunun yake bata wani ya shiga bakin ta wani ya fita, yana bata yana mata hira, gyara mata jikin ta yayi ya" kwantar da ita. "Hannun ta ya riƙe yana kallon ta, tamkar zeyi kuka." Allah ya baki lafiya ammie na. "Ya rasa ina ze saka ranshi yaji daɗi, ga damuwar rashin lafiyar mahaifiyar shi, ga takurar yarinyar can." Tuna yarjejeniyar dake tsakanin su kawai ɗaga mishi hankali yake bare ya tuna cewa.......... FULANI 08082101373 https://chat.whatsapp.com/Kqi1tusHnZa6SHgbTgFqlr https://chat.whatsapp.com/Kqi1tusHnZa6SHgbTgFqlr AYRAAH BY RABI'ATU KABIR ACHADU (FULANI) YOUNG TALANTED WRITER'S ASSOCITION (YOTA) A har kullum ina jinjina a gare ki garkuwar fulani mahaifiya ta abar alfaharina SADAUKARWA GA ACHADU'S FAMILY Yanda na fara lafiya Allah ya bani ikon kammala shi lafiya FULANI 08082101373 AYRAAH PAGE 3 Kanshi ya ɗora a gefen katifar ta. """Ammie yace ze temaka min ne kawai akan lafiyar ki idan har na amince zan auri yar shi""" "Shiru yayi yana haɗiye wani miyau me zafi daya tsaye masa a maƙogaron shi, yana wasa da yatsun" hannunta ya ci gaba da magana. """Ammie bana son ta ko kaɗan, kin hanani cewa na tsani mutum amman ammie da nace miki na tsane ta," "tana takuramun da yawa ammie na""" "Hawaye ne yake bin gefen fuskar ta ba tare da ya kula ba, hannun ta ta ɗago da yake rawa sosai ta ɗora" akan sumar shi. Da sauri ya ɗago kan shi yana kallon ta. Kan nashi ta ci gaba da shafa wa hannunta na rawa. "Ganin yanda hannun ta yake rawa ne ya fahimci tana shan wahala motsa hannun ta da take, hannun shi" yasaka ya riƙo hannun ta dake kan shi. "Farin ciki ne sosai akan fuskar shi, ""ammie na kin motsa hannun ki""" Murmushin ƙarfin hali tayi mishi tana rufe idon ta. Gaba ɗaya ya rasa ina ze saka ranshi dan farin ciki. "Tunani yake waya kamata ya faɗa wa wannan abin farin ciki, mutum ɗaya ne yazo ranshi dan haka ya" "ɗakko wayar shi keypard, ba wasu numbobi bane na azo a gani." """ *BUDDY*""" "Jin yanda wayar take ta ringing ba'a ɗauka bane yasa shi jin babu daɗi, iya sanin shi baya nisa da wayar" shi toh ina ya jefa wayar. Ya masa misscalled wajen 4 shida yawan kira ba ɗabi'ar shi bane. Haƙura yayi ya ajiye wayar yana tunanin ko lafiya. ★★★★★ Shirya wa tayi cikin ƙananun kaya ta sakko ƙasa. "Yana zaune yayi tagumi da hannun shi biyu, abin duniya duk ya dame shi, dan yasan kafin ta bashi kayan" shi sai yaji jiki a hannun ta. "Tun da yaji alamun sakkowar ta daga benen ya zuba mata ido, kayan jikin ta sun haska farar fatar ta" "sosai da sosai, chocolate take buɗewa tana tafiya gaba ɗaya hankalin ta na kan abinda take Ko kula da shi batayi ba." """Ukty""" Sai a lokacin ta ɗago kanta ta kalle shi. """Na'am akhie""" Zama tayi kusa da shi tana shan chocolate ɗin ta. """Kiyi hakuri ukty ki bani kayana dan Allah, aiki zanyi, kar abhie ya dawo ban gama zemin faɗa ba""" Ta gefen ido take kallon shi tana shan chocolate ɗin ta hankali kwance. "Kaman bazata yi magana ba ta kalle shi tace ""akhie kasan wani abu?""" Kanshi ya girgiza mata. """Akhie chocolate ɗina sun ƙare, kuma na daɗe ban sha ice cream""" Banza yayi mata. Juyowa tayi gaba ɗayan ta ta marairaice fuska tana kallon shi. Bala'i yake son mata amman yasan a hannun ta yake dole ya lallaɓa ta. """Yanzu idan na siya miki zaki bani?""" """Kanta ta gyaɗa masa tana sakar masa murmushi." Tashi yayi ya fita yana tunanin sanda zata shiga hannun sa. Dariya take ita kaɗai. """Ke lafiyar ki?""" Miemie ta katse mata dariyar tata. """Miemie akhie ne ya tafi siyomin chocolate da ice cream""" """Shine kike dariya kuma""" """Ai miemie ba dan Allah ze siya ba shiyasa""" Kanta kawai ta girgiza ta haye sama. Beyi 1 hour da fita ba ya dawo da leda a hannun shi. Miƙa mata yayi yana kallon ta. Karɓa tayi ta miƙe zata tafi. """Ukty kayana""" """Kar ka biyo ni toh ka jirani, yanzu zan dawo""" Tsayuwa ya ci gaba dayi a wajen yana jiran ta. Sai da ta tabbatar be biyo bayan taba sannan ya shige ɗakin ta da gudu tana murza key. Ice cream ɗin ta ɗakko tana sha cike da nishaɗi. Jin shirun nata yayi yawa ne yasa ya bita ɗakin sedai yana murɗawa yaji da key a jiki. """Ayraah ki buɗe ƙofar nan kafin ranki ya ɓaci""" """Akhie wanka nake fa""" Juyawa yayi ya nufi ɗakin miemie. """Miemie kiyi mata magana ta bani kayana, tace min chocolate take so da ice cream na siya mata amman" "taƙi bani""" Kanta kawai ta dafe daga safiya zuwa yanzu sun kawo mata ƙara har ta gaji dayin shari'ar faɗa. "Miƙewa tayi yabi bayan ta, koda suka je ɗakik nata a buɗe yake bata ciki." """Ayraah kina ina?""" """Miemie nifa ina ƙasa tun ɗazu ina kallo""" A zuciya ya sakko kanta yayi tamkar ze rufe ta da duka. Sosai ta tsorata da yanayin nashi dan da wahala yayi fushi da ita bare har ranshi ya ɓaci haka. "Idonta ta runtse, tana jiran saukar dukan jikin ta." Jin shiru ne yasa ta buɗe idon ta guda ɗaya. Kayan shi dake gaban ta ya kwashe yayi gaba bece mata komai ba. Jitayi duk babu daɗi dan bata ƙaunar abinda ze ɓata masa rai. "Ganin misscalled ɗin da yake wayar shi ne ya saka shi mamaki, a sanin da yayi wa abokin nashi idan yayi" "maka 2 misscalled baka ɗaga ba baze ƙara ba, gashi yayi masa har 4 Allah yasa lafiya ya faɗa yana danna masa kira." ★★★★★ """Ammie zan fita wajen jiran shago da anyi magriba zan dawo ina sha Allah""" Idon ta ta buɗe ta rufe alamun sai ya dawo. Yana shirin fita wayar shi ta fara ringing. Wayar ya zaro yana duba me kiran nashi. Sallama yayi masa. """Buddy fatan lafiya, yanzu na karbi wayar a hannun wancan aljanar yarinyar naga misscalled ɗin ka" "dayawa, Allah yasa lafiya?""" """Lafiya daman kiran ka nayi mu gaisa""" """Gaskiya ban yadda Malam faɗamin meyafaru""" Sai da yayi murmushi Sannan ya faɗa mishi ammien shi ta motsa hannun ta yau. Sosai ya taya abokin nashi murna. "Hira suka ci gaba dayi, har ya ƙarasa shagon da yake jira." "Sallama suka yi, sannan yayi wa me shagon magana." """Ashraff sai yanzu nayi tunanin yau bazaka zo ba""" Cikin yanayin shi na rashin magana yace masa ya tsaya uzuri ne a gida shiyasa ya makara. Fitowa yayi ya bashi mukulli shi kuma ya shiga cikin shagon. "Shagon charge ne da downloading, yana jire mishi shi kuma yana biyan shi, tanan yake samu yana biya" musu buƙatun su wanda be taka kara ya ƙarya ba. Yana zaune be fita ba sai da aka kira sallar magrib ya kulle shagon yaje yayi ya dawo. "Yana buɗe wa yan downloading suka fara zuwa, daman bayan magrib zuwa 11 na dare shine lokacin" cinikin shagon sosai. "Duk da yanda mutane suka rufe shi, hakan besa hankalin shi ya bar kan ammien shi ba, agogo yake ta" "kalla yana jiran me gidan nashi yazo ya karɓe shi, dan lokacin tafiyar shi gida yayi." "Tsaki yake taja yana duba lokaci, gaba ɗaya sai da ranshi gama ɓaci sannan yazo." """Kayi hakuri ashraff naɗan tsaya yin abu ne""" "Bece masa komai ba ya fito, yayi gaba ko sallamar shi be karɓa ba." Kanshi kawai ya girgiza idan da sabo ya riga ya saba da halin abokin aikin nashi. "Da sallama ya shiga gidan, ɗakin ta ya shiga." """Ammie na gani na dawo, kiyi hakuri oga nane be dawo da wuri ba""" "Matsawa kusa da ita yayi yaga ta ɓata wajen da take, ruwan zafi yaje dafa, babu kyankyami haka ya" "gyara wajen data ɓata da jikin ta, turaren tsinke ya kunna take kuwa ɗakin ya fara kamshi." ★★★★★ """Zaki faɗa min kukan me kike ko kuma sena mugun ɓata miki rai""" Cikin muryar kuka ta fara magana tana ɗaga murya tamkar tana magana da sa'ar ta ba mahaifiyar ta ba. """Mom ashraff dad yace ze aura min shi, amman har yanzu shiru, yau a ƙalla shekara nawa dayi min" "wannan alƙawarin amman shiru, meyasa zemin alƙawarin daba ze cika min ba? Koni ma ƙaryar daya" "sabawa mutane zeyi min? Baze yuyu ba wallahi mom dole na auri ashraff""" Gaba ɗaya ta har gitse duk abinda yazo bakin ta furta shi take ba tare da ta tauna ba. "Ji take tamkar ta tashi ta rufe ta da duka, amman tasan dukan ta shine mafi munin kuskure da zata" "aikata, a gidan dan baban ta baze dubi cewar ita ta haife ta ba, tsaff zeyi mata hauka, dole tayi mata banza." Ganin ba ƙara kula ta zatayi ba ne yasa ta wuce sama a guje tana kuka. Murɗa handle ɗin tayi da karfin ta shige ciki. Zama tayi tana kuka tana me ci gaba da cin alwashi akan sai ta auri ashraff koda kuwa meze faruwa...... FULANI 08082101373 https://chat.whatsapp.com/Kqi1tusHnZa6SHgbTgFqlr https://chat.whatsapp.com/Kqi1tusHnZa6SHgbTgFqlr AYRAAH BY RABI'ATU KABIR ACHADU (FULANI) YOUNG TALANTED WRITER'S ASSOCITION (YOTA) A har kullum ina jinjina a gare ki garkuwar fulani mahaifiya ta abar alfaharina SADAUKARWA GA ACHADU'S FAMILY Yanda na fara lafiya Allah ya bani ikon kammala shi lafiya FULANI 08082101373 AYRAAH PAGE 4 "Gaba ɗaya jikin ta yayi sanyi, dan bata ƙaunar abinda ze sa akhien ta yayi fushi da ita." "Koda abhi ya dawo da sauri ta tarbe shi, tana ɗora kanta a kafadar shi, ""abhi nayi kewan ka sosai""" """Nima nayi kewan ki auta na""" "Ɗakin shi ya wuce yaje yayi wanka, sallah suka fita shida farooq, ganin ko kallon ta beba yasa jikin ta" ƙara yin sanyi. "Alwala taje tayi, sallah tayi ta sakko ƙasa, ta riga kowa zama a dianing." Koda suka dawo daga masallaci suma duk wajen suka yo suka zauna. "Miemie ce ta sakko tana ta baza ƙamshi, sosai tayi kyau cikin kwalliyar tata bazaka taɓa cewa itace ta" haifi umar ba. Murmushin ya sakar mata. Itama mayar mishi tayi tana zama a kujerar datake fuskantar shi. Ayraah ce ta tashi tayi saving kowa sannan ta koma ta zauna. Gaba ɗaya ta kasa cin abincin sai jujjuya shi take yi. """Meyafaru auta na, naga kin kasa cin abincin""" """Bakomai abhie kawai na ƙoshi ne""" Be matsa mata ba dan daman sun san abincin ba wani damun ta yayi ba. Kan kujera ta koma ta zauna. "Game take a wayar ta, hankalin ta amman ba akan game ɗin yake ba yana kan akhien ta." Koda yazo wuce ta yayi ba tare da yace mata komai. Tashi tayi tabi bayan shi. Duk da yaji takun ta be juyo ba yaci gaba da tafiyar shi. """Akhie! Akhie!!""" Jin yanda muryar ta take rawa ne yasa shi juyo wa yana kallon ta. "Kunnen ta riƙe duka biyun idon ta taff hawaye tace ""ayya akhie kayi hakuri in sha Allah bazan kuma""" Murmushi yayi yaja hancin ta. """ Ka haƙura akhie?""" """Daman ina fushi dake ne princess nima ramawa nayi ai""" Dariya tayi beauty point ɗin ta ya lotsa sosai dake ɓarin fuskar ta na hagu. "hannun ta yaja suka koma kan dianing ɗin, abinci ya zuba mata yana bata a baki da kanshi." Iyayen nasu murmushi kawai suke suna kallon su. Sai da ya tabbatar ta ƙoshi sannan ya raka ta ɗakin ta ya sakko. Sallama yayi musu ya shige ɗakin shi ya kwanta. Har ta kwanta ta ɗakko littafin ta da kayan zane. "Ganin kayan kawai farin ciki suke sata, zane burin tane, tun tanayi ana hana ta har ta kai ta kawo yanzu" da kan su suke kawo mata kayan zanen. "Tana zanen tana sakin murmushi, bata ɗau dogon lokaci tana yi ba, ta gama kallon hoton take tana" sakin murmushi. Akhie ne a jiki da ita yana bata abinci a baki. "Wayar ta ta ɗakko tayi hoton zanen, a status ta ɗora da rubutu a ƙasa." """My world best""" "Addu'ar bacci tayi ta kwanta, bata daɗe ba bacci ya ɗauke ta." ★★★★★ "Sai da ya tabbatar ya bawa ammien shi abincin ta, sannan yaje yayi wanka da alwala ya kwanta, be daɗe" ba bacci ya ɗauke shi. "Kiran sallar asubar farko ya tashi, ɗakin ammien shi ya shiga." "Itama idon ta biyu, ɗagota yayi ya gyara mata jikin ta tare da alwala." "Komar da ita yayi, ya fice masallaci." "Ana idar da sallar, ya taso ya nufo gidan, dan haka kawai yake jin gaban shi na faɗuwa tun da ya baro" gidan. Da gudu ya shiga jin yanda yake jin kakarin amai na tashi daga ɗakin da ammie take. Ko kafin yaje har ta faɗo daga kan katifar datake. "Ɗagota yayi jikin shi yana kiran sunan ta, sai dai abinda ya gani ne ya ɗaga mishi hankali harya nemi fita" "hayyacin shi, gaba ɗaya jikin shi karkarwa yake........." FULANI 08082101373 https://chat.whatsapp.com/Kqi1tusHnZa6SHgbTgFqlr https://chat.whatsapp.com/Kqi1tusHnZa6SHgbTgFqlr AYRAAH BY RABI'ATU KABIR ACHADU (FULANI) YOUNG TALANTED WRITER'S ASSOCITION (YOTA) A har kullum ina jinjina a gare ki garkuwar fulani mahaifiya ta abar alfaharina SADAUKAR WA GA ACHADU'S FAMILY Yanda na fara lafiya Allah ya bani ikon kammala shi lafiya FULANI 08082101373 AYRAAH PAGE 5 Sosai jikin shi yake rawa ganin yanda take aman jini ta hanci ta baki. "Ya rasa abinda ya kamata yayi ɗagota yayi ya ɗora a jikin shi tana ci gaba da aman, gaba ɗaya ta ɓata" shi amman ko kaɗan hakan be dame shi ba. Cikin rawar murya ya fara kiran sunan ta """Ammie karki tafi ki barni dan Allah ke kaɗai gare ni""" Sosai yake jijjigata yana kiran sunan ta. Kaman wanda aka mintsina haka ya miƙe ya saɓeta a kafaɗar shi yayi waje cikin sassarfa. "Babu kowa unguwar tsitt, saboda ba'a daɗe da idar da sallar asuba ba, a haka ya nufi titi da ita ko" takalmi babu a ƙafar shi. Jefa ƙafar shi yake yana addu'a a ranshi Allah yasa ya samu abin hawa da wuri. Be daɗe ba ya samu cikin sauri ya shigar da ita shima ya shiga ya zauna. Ganin yanayin su ne yasa yaja napep ɗin. """Bawan Allah wane asibiti zan kaiku?""" """Aminu Kano""" "Daga haka be ƙara magana ba, gaba ɗaya hankalin shi, yana kan fuskar ammien nashi da zuwa yanzu ma" kaman bata numfashi. "Har cikin asibitin ya shigar dasu, ze bashi kuɗi yace ya bar shi Allah ya bata lafiya." Kai tsaye emergency ya nufa da ita a kafaɗar shi. "Da sauri nurses suka karɓe ta, suka shiga da ita." Gaba ɗaya ya kasa tsaye ya kasa zaune zagaye kawai yake a wajen yana addu'a. ★★★★★ "Tun da tayi sallar asuba bata koma bacci ba, kitchen ta sakko ta haɗa musu break fast, tana gama wa ta" jere a dianing ta koma ɗakin ta. "Wanka tayi ta shirya cikin riga da wando ta ɗora doguwar riga a sama, batayi kwalliya ba, kwalli kawai" "ta saka idon ta sai white lipstick, glass ta ɗakko ta saka." "Saida taga fuskar tata tayi mata yanda take so, sannan ta nufo ƙasan mayafin ta da jakar ta a hannu." "Ganin babu wanda ya sakko a cikin su ne, yasa ta nufi ɗakin akhie." Knocking tayi mishi ya bata izinin shiga sannan ta shiga da sallama. Murmushi ya mata. """Morning pretty""" """Morning akhie ka tashi lafiya?""" """Alhamdullah har kin shirya?""" """Muna da lecture 9""" Dariya yayi yana kallon ta ganin yanda tayi da fuskar ta. Tashi yayi ya nufi wardrobe ɗin shi tana tsaye ya dawo ya miƙa mata kuɗi. Tsalle tayi ta maƙalƙale shi tana masa godiya. Zare ta yayi daga jikin shi yace a sauka lafiya. Da sauri kam ta bar ɗakin tana jin daɗi a ranta. Dianing ta nufa ta haɗa tea a tsaye ta sha. "Sama ta koma tayi knocking ɗakin miemie, izinin shiga aka bata ta shiga da sallama." Har ƙasa ta tsugunna ta gaida iyayen nata. """Kin shirya auta?""" """Eh abhie""" "Kuɗi ya ɗebo me yawa ya miƙa mata, godiya tayi mishi tayi musu sallama ta fita." "Ɗakin ta ta koma ta gyara fuskar ta tayi rolling, sannan ta fito." Cikin takun nutsuwar ta ta fito harabar gidan. Driver yana hango ta ya taso da sauri. Yana shirin gaishe ta ta tari numfashin shi. """Barka da safiya baba katashi lafiya""" """Alhamdullah madam""" "Ze buɗe mata ƙofa tace ya barshi, ita har ranta bata son hakan, a haife ya haife ta duk seya sa tana jin" kunyar shi. Har suka je makarantar ba wanda ya ƙara magana acikin su. Yana parking tayi masa sallama ta faɗa masa lokacin da zezo ɗaukar ta. "A yanda take tafiya bazaka taɓa cewa tana magana bare tsokana, komai nata cikin nutsuwa take yin shi." Waje ta samu ta zauna batare data kula kowa a wajen ba. "Duka bata fi sati biyu a makarantar ba, toh bata gama sanin kan makarantar ba, kuma ita shiga mutane" ba damuwar ta yayi ba ita dai barta da akhien ta da miemie se abhie. "Malamin da zeyi musu lecture ne ya shigo, hakan yasa ta mayar da hankalin ta gaba ɗaya kan shi." "Suna cikin lecture ɗin ta shigo, fuskar ta sanye da facemask, malamin ta gaisar, ta shigo cikin ajin sosai," sit ɗin da take zaune tazo ta zauna. "Kallo ɗaya ayraah tayi mata ta ɗauke kanta, itama batace mata komai ta mayar da hankalin ta, kan" malamin. Koda malamin ya fita babu wadda ta kula wata a cikin su. "Waje ta fito ta samu waje ta zauna, Akhie ta kira a waya tana ringing be ɗaga ba, sosai ta zumɓuro bakin" ta gaba tamkar yana gaban ta. Game ta shiga tana cikin yi ya kira ta. Cike da shagwaɓa ta fara masa magana kaman zatayi kuka. """Akhie yunwa zata halaka maka ni""" """Kije capteria kici abinci mana""" """Uhm uhm akhie ni cornflask nake so na sha""" Tsaki yaja ya kashe wayar shi. Maida wayar tayi ta ajiye. Jin kaman ana kallon tane yasa ta ɗago kanta. Yarinyar data zo ta zauna kusa da ita ne a kujerar da take facing ɗinta tana kallon ta. "Bakin ta ta tura gaba tana hararar gefe Allah ya gani ita bata son kallo, tana cikin mita a ranta taji wayar" "ta na ringing, dakkowa tayi ta duba me kiran, ganin akhie ne yasa ta ƙara ɓata rai ta ɗaga dan taji haushin kashe mata waya da yayi, ɗaga wa tayi ba tare da tayi magana ba." """Kizo ki karɓa malama ko nayi tafiya ta""" "Murmushin da bata shirya masa bane ya ƙwace mata, da sauri ta tashi ta nufi wajen depertment ɗin" "nasu, tun daga nesa ta hango shi a jikin mota a tsaye." "Tun daga nesa take sakar mishi murmushi, shikam harara kawai yake zabga mata." """Sannu da zuwa Akhie""" "Bai kulata ba ya buɗe bayan motar ya shiga, itama shiga tayi ta zauna, da kan shi ya haɗa mata cornflask" "ɗin ya bata, gaba ɗaya bakin ta yaƙi rufuwa, sosai tayi farin ciki da zuwan akhien nata." Tana gama sha ta ɗora kanta a kafaɗar shi tana lumshe ido. """Akhie bacci""" Buɗe ƙofar motar yayi ya nuna mata ƙofa alamun ta fita. """Bye bye akhie nagode sosai Allah ya bar min kai""" "Cikin makarantar ta koma tana mejin farin ciki a tare da ita, ba wata yunwar arziƙi take ji ba ta kira shi" kawai dan neman magana sai gashi kuma ya kawo mata. "Cikin class ɗin su ta koma ta zauna, bata daɗe da zama ba yarinyar ɗazu tazo ta zauna a kusa da ita," babu wanda ya kula wani har suka gama lecture's ɗim su na ranar. "Tana fitowa taga driver na jiran ta, dan haka babu ɓata lokaci ta shige motar suka nufi gida." ★★★★★ "Da ka ganshi dole ne ya baka tausayi, gaba ɗaya ya fita daga cikin hayyacin shi, tsawon awannin da" "doctor's ɗin suka ɗauka a cikin emergency be zauna ba, haka be saka wa cikin shi komai, idon shi yana" kan ƙofar ɗakin. "Ganin an kashe hasken ɗakin yasa gaban shi tsanan ta faɗuwa, a hankali doctor's tare da nurses suke fito" wa duk sun haɗa gumi a tare dasu. "Kaman wanda ƙwai ya fashewa a ciki haka yabi bayan doctor yana tambayar shi lafiyar ammien shi, kallo" ɗaya doctor yayi masa yace ya biyo shi office ɗin shi. "Tun da doctor ya fara mishi bayani yayi ƙasa da kan shi, hannun shi dafe da ƙirjin shi, dan ji yake tamkar" wuta ce take kamawa a cikin ƙirjin na shi. "Toh kaman dai yanda na maka bayani tun kafin ciwon nata ya tsananta, yanzu ma zan ƙara maimaita" "maka, mahaifiyar ka na cikin tsaka mai wuya, a halin yanzu tana tsakanin rayuwa da mutuwa, idan har kana buƙatar mahaifiyar ka dole ne ayi mata aiki nan da kwana uku, shima saboda aƙwai gwaje_gwaje da za'a sake mata." Shiru doctor ɗin yayi yana nazartar shi ganin yanda ya jiƙe jarkaf da gumi tamkar babu ac a office ɗin. Cikin shaƙaƙƙiyar murya ya tambayi doctor yanzu kuɗin aikin da komai da komai yakai nawa. Cike da tausayi doctor ya bashi amsa da 1.5million. 1.5 million...... FULANI 08082101373 https://chat.whatsapp.com/Kqi1tusHnZa6SHgbTgFqlr https://chat.whatsapp.com/Kqi1tusHnZa6SHgbTgFqlr AYRAAH BY RABI'ATU KABIR ACHADU (FULANI) YOUNG TALANTED WRITER'S ASSOCITION (YOTA) A har kullum ina jinjina a gare ki garkuwar fulani mahaifiya ta abar alfaharina SADAUKAR WA GA ACHADU'S FAMILY Yanda na fara lafiya Allah ya bani ikon kammala shi lafiya FULANI 08082101373 AYRAAH PAGE 6 "Kuɗin kawai yake maimaita wa a cikin ranshi, jargaf haka ya jiƙe da gumi kaman wanda aka watsa wa" ruwa. Shidai likitan kallon shi kawai yake. "Bece masa komai ba ya tashi ya fita daga office ɗin, be zarce ko ina ba se bakin titi a ƙafa yake tafiya," "yana saƙe_saƙe a cikin ranshi, yayi tafiya me nisa kafin ya samu napep ya ƙarasa da shi hotoro, yana sauka ya ƙarasa layin da ƙafa, wani irin bugu yake tamkar ze ƙarya ƙofar." "A firgice me gadi ya buɗe ƙaramar ƙofar, ganin yanayin shi daya ganine yasa ya bashi hanya ya wuce." "Main ƙofa ta gidan ya tunkara cikin sassarfa, be tsaya yin knocking ba ya danna kanshi cikin ƙofar," "matar gidan na zaune, kai tsaye ɓarin me gidan ya nufa." "Tashi tayi tana shirin dakatar da shi, wani ɗan iskan kallo daya watsa mata da jajayen idanuwan sa ne" yasa ta ja da baya babu shiri. "Jin takun tafiya ne yasa gaba ɗayan su juyawa inda me tawowar yake, babban mutum ne ya sha manyan" "kaya, sai tashin kamshi yake, kai tsaye idan ka kalle shi ka kalli ashraff dole ne kasan cewa suna da alaƙa." "Kujera ya samu ya zauna, ya ɗauki jarida yana ƙoƙarin buɗeta." "Gaban shi yaje ya zube, ya haɗe hannayen shi guda biyu cikin alamun roƙo da magiya ya fara mishi" magana Muryar shi cike da rauni. """ Dan Allah uncle ba danni ba badan halina ba kate make ni, ka biya kuɗin aikin da za'ayi a ceto min" "rayuwar mahaifiya ta""" Ƙafar shi ya ɗora ɗaya kan ɗaya yana mishi kallon ƙasƙanci da wulaƙanci. Be damu da abinda yayi mishi ba ya ci gaba dayi mishi magiya fuskar shi na zubar da hawaye. Tamkar baze kula shi ya daure cike da gadara ya tambaye shi nawa ne kuɗin aikin. """1.5million ne""" "Makirin murmushi ya saki a ranshi yace faɗuwa tazo daidai da zama, dan jiyan nan babyn shi tagama" ɗaga mishi hankali akan auren yaron. "Wani ɗan iskan kallo yaje fa mishi, yace ""ka tuna yarjejeniyar mu?""" Kanshi ya gyaɗa mishi. """Toh malam yanzu wane hukunci ka yanke?""" """ Ko yanzu a shirye nake a ɗaura auren in har zaka biya kuɗin nan""" """Idan kuma bazan biya ba fa?""" Shiru yayi masa zuciyar na tarfafasa ta ciki. """Dad kai wane irin mutum ne yace ze aure ni kuma kana maganar idan baka biya kuɗin ba fa?""" Muryar ta ta katse musu maganar tasu. "Gaba ɗaya juyawa sukayi suna kallon ta, kayan bacci ne a jikin ta, rabin jikin ta duk a waje." Da sauri ashraff ya ɗauke kan shi daga kanta. Zama tayi a jikin dad ɗin nata tamkar yarinya ƙarama. """Baby ai kinsan zan bashi kuɗin tunda har yace ze aure ki, kawai dai""" Da sauri ta ƙara katse mahaifin nata. """Kaga dad ya isa haka kawai ka bashi kuɗin, idan na shirya lokacin auren zanyi maka magana sai ayi dan" "yanzu inada abinda nake son ƙarasawa kafin nayi aure""" """Yanda kike so haka za'ayi baby""" "Kallon shi tayi tana shanye idon ta "" babe nawa ne kuɗin?""" "Be kalleta ba ya bata amsa ""1.5million""" "Tashi tayi ta nufi ɗakin mahaifin nata, locker da yake ajiye kuɗi ta saka security ta ɗebo kuɗin ta fito da" su a hannun ta. "Miƙa masa kuɗin tayi, yana miƙi hannun shi ze karɓa ta mayar da su ta ajiye a cinyar ta iyayen nata ta" kalla tace! """ kuɗan bamu waje zamuyi magana""" "Dad ɗin tane ya fara tashi, ganin mom ɗin ta bata da niyar tashi ya jefa mata wani kallo ba shiri ta tashi" tabi bayan shi. Ganin babu kowa a wajen ne yasa ta kalle shi ta nuna masa kusa da ita alamun yazo ya zauna. "Kanshi kawai ya girgiza mata, alamun nan ma ya ishe shi." """Babe Kasan nawa ne kuɗin nan?"" ta jefa mishi tambayar tana juya su a hannun ta." Shi dai kallon gefe yake ba tare daya kalle ta ba. """2 million ne zan baka su, ayiwa tsohuwar ka aikin, amman ina da sharaɗi, dole zaka dinga zuwa zance" "waje na, kuma duk sanda naji ina buƙatar kazo muje outing zaka je, sannan kuma kayan da nake siya maka kana ƙin karɓa ya zamar maka dole ka karɓa, saboda yanzu a matsayin mijin zainab kake bawai" "ashraff ɗan gidan buzuwa ba""." "Tsare shi tayi da idanun ta tana jiran jin amsar shi, ganin bashi da niyar kulata ne yasa ta kwashe kuɗin ta" "miƙe ta kalle shi tace ""duk sanda ka shirya bin umarni na kazo ka karɓi kuɗin""" Daga haka ta nufi stairs............ FULANI 08082101373 https://chat.whatsapp.com/Kqi1tusHnZa6SHgbTgFqlr https://chat.whatsapp.com/Kqi1tusHnZa6SHgbTgFqlr AYRAAH BY RABI'ATU KABIR ACHADU (FULANI) YOUNG TALANTED WRITER'S ASSOCITION (YOTA) A har kullum ina jinjina a gare ki garkuwar fulani mahaifiya ta abar alfaharina SADAUKARWA GA ACHADU'S FAMILY Yanda na fara lafiya Allah ya bani ikon kammala shi lafiya FULANI 9131319938 RABI'ATU ABDULLAHI KABIRU OPAY 300 SAI A TURA SHAIDAR BIYA TA 08082101373 AYRAAH PAGE 7 """Na amince!!!"" Ya bata amsa zuciyar shi na zafi." "Murmushi ta saki tana ayyana wa a ranta, daman tasan dolen shi ya amince idan har yana son ceton" "rayuwar mahaifiyar shi, domin su shaida ne akan ƙaunar dake tsakanin shi da ammien tashi." "Dawowa tayi ta bashi kuɗin, tana masa kallon ƙasan ido." "Karɓa yayi ba tare da yace mata komai ba, gaba ɗaya jikin shi yayi sanyi, da wannan yanayin da yake ciki," shi kansa yasan amince mata da yayi wani babban ƙalu bale ne ya kira wa kan shi. Jiki babu laka ya nufi waje da kuɗin a hannun shi. """Babe""" Chak ya tsaya ba tare da ya juyo ba. "Jaka ta miƙa masa ƙarama, karɓa yayi yasa kuɗin a ciki ya juya ya tafi." Har ya koma asibitin tunani ka kala kala ne a cikin ranshi. "Kai tsaye office ɗin likitan ya nufa da kuɗin, wajen biyan kuɗin ya tura shi ya biya kuɗin komai da komai" suka bashi raciept. "Sai da yaje yaga ammien shi, yaji dama dama a cikin ranshi, tana kwance da kayan asibiti a jikin ta," "hancin ta an saka maka mata oxgyen domin taimakawa numfashin ta, hannun ta ya riƙe ya ɗora kanshi a kai, hawayen shi ne yake ɗiga a hannun na ta, na tausayin kanshi dana mahaifiyar ta shi, ya daɗe a wajen ta sannan ya tashi ya fita daga ɗakin, ya nufi gida domin canza kayan jikin shi da ɗebo musu kayan da" zasu buƙata a asibitin. ★★★★★ "Gefen titi take kalla itama bata san meyaja hankalin ta ga barin danna wayar ta ba ta zubawa titin ido," "dum dum dum haka zuciyar ta take bugawa da matsanancin bugu, hannun ta tasa ta dafe saitin zuciyar ta, duk addu'ar da tazo bakin ta karanta ta take, jin yanda zuciyar tata ta ci gaba da bugawa ne yasa ta" runtse idanuwan ta da ƙarfi hawaye nabin gefen fuskar ta. "Har suka zo gida bata sani ba, bugun zuciyar ta kawai take saurara a cikin kunnuwan ta, jin ƙarar" "tsayawar motar ne yasa ta buɗe idanun ta da sukayi jajir, a hankali take tafiya tamkar mara laka a jikin ta," "babu kowa a parlown sama ta nufa tana haɗa hanya da ƙyar ta kai kanta ɗakin ta, zubewa tayi a kan" gadon ta tana maida numfashi da sauri_sauri tamkar wadda tayi gudun tsiri. "Ta ɗau tsawon lokaci a hakan kafin ta miƙe ta nufi toilet, wanka ta samu tayi tare da alwala ta fito," "ƙaramar doguwar riga ta saka da hijab tayi sallah, zuwa lokacin data idar da sallar zazzaɓi ne sosai a jikin ta." "Zame wa tayi ta kwanta akan daddumar hawaye nabin fuskar ta, tabbas tamanta rabon da ta tsinci kanta" a cikin wannan yanayin tasan yanzu kuma dawowar ta daidai saita Allah kawai. "Miemie ce ta sakko ƙasa tana duba lokaci, ya kamata ace ayraah ta dawo tuntuni amman har yanzun" "shiru babu ita babu alamar ta, ta kira wayar ta kuma ba'ayi picking ba gaba ɗaya bata jin kwanciyar hankali a tare da ita." Wayar Akhie ta kira. """Hello miemie na""" """Akhie har yanzu ayraah bata dawo gida ba, ina ta kiran wayar ta kuma bata ɗaga wa""" """Ki kwantar da hankalin ki miemie ukty tana lafiya, dan ɗazun da kaina na kai mata cornflask makaranta" "kuma banga alamun rashin lafiya a tare da ita ba, zan kira ta yanzu nima""" Badan hankalin ta ya kwanta ba ta ajiye wayar ta zauna ta dafe kanta. "Wayar ta yake ta kira bata ɗaga wa jin yanda shima hankalin shi ya tashi ne yasa shi nufo gidan, ko gama" parking beba ya nufo cikin gidan. Ganin yanayin da ya shigo ne yasa miemie miƙewa tsaye babu shiri. """Akhie meyasa mi yarinya ta?""" "Kasa tsayawa bata amsa yayi ya nufi sama kaman ze tashi sama, da ƙarfin shi ya murɗa handle ɗin ɗakin" "nata, wata wawuyar ajiyar zuciya ce ta ƙwace masa ganin ta a kwance a ƙasa ta dunƙun ƙune cikin hijabi." """Uktyyyy"" yaja sunan yana ɗago ta." Da ƙyar ta ɓude idon ta ta kalle shi sai kuma ta rufe....... FULANI 08082101373 https://chat.whatsapp.com/Kqi1tusHnZa6SHgbTgFqlr https://chat.whatsapp.com/Kqi1tusHnZa6SHgbTgFqlr AYRAAH BY RABI'ATU KABIR ACHADU (FULANI) YOUNG TALANTED WRITER'S ASSOCITION (YOTA) A har kullum ina jinjina a gare ki garkuwar fulani mahaifiya ta abar alfaharina SADAUKARWA GA ACHADU'S FAMILY Yanda na fara lafiya Allah ya bani ikon kammala shi lafiya FULANI 9131319938 RABI'ATU ABDULLAHI KABIRU OPAY 300 SAI A TURA SHAIDAR BIYA TA 08082101373 AYRAAH PAGE 8 """Uktyyyy baki da lafiya ne wai?""" Jikin shi ta shige tana sakar masa kuka. Sai a lokacin yaji yanda jikin ta ya ɗau zafi. "Jin shirun shi yayi yawa ne yasa miemie ta biyo shi saman, ganin ayraah jikin akhie ne yasa ta saki ajiyar" zuciya duk da alamun su bai nuna mata lafiya suke ba. "Ƙarasowa tayi jikin ta a sanyaye ""meyasa meta akhie?""" """Miemie zazzaɓi ne a jikin ta""" "Ɗaga ta yayi ya mayar da ita kan gadon ta, ɗakin shi yake ya ɗakko mata magani ya bata." "Zama yayi ya riƙe hannun ta har tayi bacci, sai a lokacin yaji hankalin shi ya kwanta." Kafaɗar shi miemie ta dafa ɗagowa yayi ya kalle ta. """Kaje kayi wanka ka huta tunda ta samu bacci""" """Toh miemie kece zaki zauna tare da ita?""" """Akhie babu abinda ze same ta ai kaga ta samu bacci insha Allah kafin ta tashi zazzaɓin ya sauka a jikin" "ta""" "Tashi yayi ya nufi ƙofa ta bishi da kallo, tasan daman indai ɗaya bashi da lafiya tare suke jinyar." "Har abhie ya dawo daga aiki gaba ɗaya gidan babu karsashi a cikin shi, daman tunda yaga auta bata ta" "tare shi ba yasan akwai matsala, be ƙara tabbatar wa ba seda aka zo cin abinci yaga duk ƙaunar akhie da" abinci ya kasa ci sai a lokacin ya magantu. """Gaba ɗaya yau banga auta na ba tun da nadawo daga aiki""" """Abhi bata da lafiya fa""" "Ajiye cokalin abincin yayi ya kalli akhie, ""kaci abincin ka kaji akhie zata samu lafiya""" "Kallon abhin yayi kawai yayi ƙasa da kanshi, ukty itace duniyar shi a duk lokacin da wani abu ya same ta ji" "yake tamkar shi abin ya sama, baya san abinda ze taɓa masa lafiyar ta." "Ƙarshe dai haka suka ci abincin babu walwala a tare dasu, gaba ɗayan su ɗakin ta suka nufa sai dai har" "lokacin bacci take kuma alhamdullah zazzaɓin jikin nata yayi sauƙi, haka suka je suka kwanta jiki babu ƙwari, musamman akhie." ★★★★★ "Ji take a yau babu wanda ya kaita farin ciki, duk da tasan taurin kai irin na ashraff amman yanzu ya shigo" hannun ta. Waya take kira tana taka rawa a hankali. """Hello baby"" akace daga ɗayan bangaren." """Kirani matar ashraff kan ki tsaye babe""" """Hmmm na gaji da jin wannan waƙar har na hadda ce ta""" """ A wannan lokacin ashraff ze zama mallaki na, duk abinda ya faru ta zayya newa ƙawar tata""" """Gaskiya zee ban taɓa sanin shashasha bace ke se yanzu, kinyi gangancin bashi kuɗin nan, tunda kinfi" "kowa sanin halin gayen nan, yanzu idan ya canza ra'ayi bayan samun lafiyar mahaifiyar shi dame zaki" "masa taƙama?""" "Ɗifff tayi tamkar ruwa ya cinye ta, tana jin yanda gaban ta yake faɗuwa akan tunatar war da aminiyar" tata tayi mata. Cikin sanyin murya take tambayar ta. """Toh yanzu menene mafita??????" FULANI 08082101373 https://chat.whatsapp.com/Kqi1tusHnZa6SHgbTgFqlr https://chat.whatsapp.com/Kqi1tusHnZa6SHgbTgFqlr AYRAAH BY RABI'ATU KABIR ACHADU (FULANI) YOUNG TALANTED WRITER'S ASSOCITION (YOTA) A har kullum ina jinjina a gare ki garkuwar fulani mahaifiya ta abar alfaharina SADAUKARWA GA ACHADU'S FAMILY Yanda na fara lafiya Allah ya bani ikon kammala shi lafiya FULANI 9131319938 RABI'ATU ABDULLAHI KABIRU OPAY 300 SAI A TURA SHAIDAR BIYA TA 08082101373 AYRAAH PAGE 9 """Taya zaki tsaya tambaya ta mafita bayan kin gama ɓata komai""" """Ki gane babe banyi wannan tunanin ba, wataƙila ma shine abinda dad yaso fahimtar dani naƙi tsaya wa" "na saurare shi, nidai yanzu dan Allah ki faɗa min abinda ya kamata nayi"" ta ƙarasa maganar kaman zatayi" kuka. """A halin yanzu mafita ɗaya gare mu, kuma ita zamu aiwatar""" Cike da zaƙuwa take tambayar ta menene ta faɗa mata. "Bayani tayi mata, har ta gama tsaff tana sauraren ta, seda ta gama tayi mata magana." """Babe abin nan beyi tsauri ba kuwa?""" """Nidai nabaki shawarar da zan iya baki zaɓi kuma ya rage naki""" "Ajiyar zuciya ta sauke tana me na'am da bayanin ƙawar tata, duk da tasan aƙwai ƙura a ƙasan aikata" hakan. ★★★★★ "Yana koma wa gida ya gyara inda ammie ta ɓata, sannan yayi wanka ya shirya ya fita, komai cikin hanzari" "yake yinshi dan burin shi ya koma asibitin, kayan da zasu yi amfani da shi ya ɗiba ya fito, har ze wuce ya fasa ya nufi shagon charging da yake jira, bayani yayi mishi akan ammien shi na asibiti dan haka baze" "samu zuwa ba sai yaga abinda hali yayi tukun nan, addu'a yayi mata da fatan samun lafiya, ya juya ya tafi." "Har ya koma asibitin tananan a yarda ya barta, locker da take jikin gadon ta ya jera musu kayan su, ya" "ɗora yan kananun kwanuka a saman ta, sai da ya gama da komai, ya fita ya siyo musu ruwan sha da" "sabulu klin, sai bayan ya gama da komai ya fara jin yunwa, dan haka ya fita nema wa kanshi abinda ze iya" ci a cikin asibitin. "Cin abincin yake tamkar me cin magani, yana cine kawai dan yayi maganin yunwar cikin shi, bawai dan" "yana jin daɗin abincin ba, yana cikin ci yaji saƙo ya shigo wayar shi, har ze share sai kuma ya ɗakko ya duba." """A wane asibiti sirikata take ina son zuwa na duba ta ne""" "Iya kacin abinda saƙon ya ƙunsa kenan, ji yayi abincin bakin shi ya maƙale ya kasa wuce wa, dole ya ɗauki" "ruwa ya kora, shi yasan zuwan ta baze haifar da ɗa ido me ido ba amman bashi da zaɓi dole ya bata amsa." "Aminu kano, Al Hassan ɗan tata ward." Daga haka ya ture abincin dan ya riga da ya fita daga ranshi kuma. Zama yayi cikin zulumi "da tunanin da wacce zata zo masa kuma, Allah masani, ya kai awa ɗaya a zaune yakasa taɓuka komai yaji" "ringing na wayar shi, wayar ya ɗago yana kallon me kiran har ta katse be samu damar ɗaga wayar ba," wani kiran ne ya ƙara shigo wa sai da ta kusa yankewa ya ɗaga. """ Ina bakin ward ɗin kazo ka shigar dani"" daga haka ta katse kiran." "Juyawa yayi ya zuba wa ammie ido daba tasan wanene a kanta ba, ya ɗau a ƙalla 10 minutes yana" kallon ta sannan ya tashi ya fita. "Tana tsaye tana danna waya, riga da wando ne a jikin ta, sai ƙaramin mayafi da tayi rolling da shi, baƙin" "glass ne a fuskar ta daya kusa rabin fuskar tata, baka ganin koda ƙwayar idon tane." Kallo ɗaya ya mata ya ɗauke kanshi yana jan tsakin dabe san yayi shi ba. Ƙarar tsakin ne yasa ta ɗagowa daga danna wayar ta ta tana kallon shi. "Cike da izza ta kalle shi, ta fara magana." """Ka barni a wajen ina zaman jiran ka bayan kasan na tsani jira, sannan yanzu kazo kana jamin tsaki?""" Be bata amsa ba sai juyawa da yayi ya nufi ɗakin. "Sakin baki tayi tana kallon shi, tamkar bashi ne ɗazun abin tausayi ba, amman yanzu kalli har halin nashi" "ya dawo jikin shi, kar dai maganar babe ta zama gaskiya, bayan shi tabi cikin takun ta na isa, tana kiran sunan shi." Ko juya wa ya kalle ta beba har ya ƙarasa gadon ammien ya zauna. "Glass ɗin idonta ta cire tana masa kallon takaici, ga yanda ya wulaƙanta ta cikin jama'a, tana ganin" yanda mutanen ɗakin suka bisu da kallo. """Ashraff dame kake ta ƙama ne da har zaka min wannan abin cikin mutane, kar ka manta kai ɗin tamkar" "bawa kake a waje na""" Bala'i ta ci gaba da zazzaga masa amman yayi biriss da ita tamkar ba da shi take ba. Ganin yanda ya mayar da ita mahaukaciya ne yasa tayi kan ammie dake kwance. Ta ƙasan ido yake kallon ta yaga me zata aika ta. Oxgyen din hancin ta ta zare tana wuci. "Ai besan sanda ya miƙe yazo gaban taba, kyakkyawan mari ya sakar mata akan fuskar ta, karɓar abin" yayi ya mayar mata da shi. "Shock ne ya hata magana da farko tare da tsananin mamaki, jin yanda ya finciki hannun tane yasa ta" "ɗago idon ta dake zubar da hawaye ta bishi da kallo, sai da suka matsa daga wajen mutane sosai ya saki hannun ta, juyawa yayi ze tafi sai a lokacin tayi magana, cikin muryar kuka." """Akan wannan sauran gawar ka mare ni?""" "Chak ya tsaya, juyo wa yayi ya zuba mata idon shi da yayi jajir saboda ɓacin rai." """Mahaifiyar tawa ce sauran gawa?""" """Eh itace uwa ta ce kuma insha Allah bazata tashi daga wannan rashin lafiyar ba mutuwa zatayi," "sannan...""" Bema barta ta ƙarasa ba ya ƙara ɗauke ta da marin dayafi na farko. "Fuskar ta ta dafe jin yanda abu me ɗumi yake bin gefen hancin ta ne yasa ta kai hannun ta, sosai ta" zare idon ta ganin jini a hannun nata. "Sosai zuciyar sa take masa zafi, ya rasa me zece mata tsabar ɓacin rai, ammien tashi da duk duniya" bashi da kamar ta wannan yarinyar take faɗa wa haka. """Wallahil azim sai kayi danasanin wannan marin da kayi min, zaka san kaɗebo ruwan dafa kan ka, zamu" "gani ta yanda za'ayi wa uwar ka aikin ai bare ta samu lafiya, kuma wallahi ka rubuta ka ajiye aure tsakani na da kai babu fashi, amman hakan baze hana ka girbi abinda ka shuka ba""" FULANI 08082101373 https://chat.whatsapp.com/Kqi1tusHnZa6SHgbTgFqlr https://chat.whatsapp.com/Kqi1tusHnZa6SHgbTgFqlr AYRAAH BY RABI'ATU KABIR ACHADU (FULANI) YOUNG TALANTED WRITER'S ASSOCITION (YOTA) A har kullum ina jinjina a gare ki garkuwar fulani mahaifiya ta abar alfaharina SADAUKARWA GA ACHADU'S FAMILY Yanda na fara lafiya Allah ya bani ikon kammala shi lafiya FULANI 9131319938 RABI'ATU ABDULLAHI KABIRU OPAY 300 SAI A TURA SHAIDAR BIYA TA 08082101373 AYRAAH PAGE 10 LAST FREE PAGE "Fuuuu ta juya ta tafi tana kuka me cin rai, babu wani mahaluƙi dayake mata abinda ashraff yake mata," amman a wannan karon taci alwashin sai yayi danasanin abinda ya aikata mata. Kujera ya samu ya zauna ya dafe kanshi da yake mahaukin sara mishi. ★★★★ "Ba ita ta shi daga bacci ba sai wajen 11:pm na dare, a hankali ta miƙe ta nufi toilet, wanka tayi da ruwan" "ɗumi sosai tare da alwala, sallolin da ake binta tayi, hannayen ta ta ɗaga da niyyar addu'a, hawaye ne sosai yake bin fuskar ta, haɗe hannayen nata tayi ta rufe fuskar ta kuka take sosai wanda da ace wani" yana kusa da ita zeji yanda kukan nata yake fita tun daga ƙasan zuciyar ta. "Ta ɗau tsawon lokaci a haka kafin ta miƙe ta koma ta kwanta, bacci ya ƙaurace wa idanun ta, duk yanda" taso tursasa kanta yin bacci abu ya gagara. "Tashi tayi zaune ta cire ribbon ɗin dake kanta, dogon gashin tane ya baje a jikin ta sosai, baka ganin" koda fuskar tane. "Kaman wadda aka mintsina, ta miƙe ta nufi wardrobe ɗin ta kayan ta take watso wa, bata ga abinda take" "nema ba, gaba ɗaya ta hargitsa ɗakin wajen neman abin da take son ganin." Zubewa tayi akan gwiwar ta tana fashe wa da kuka. "Tunani take sosai akan ina taje fa abin, kaman ance ta ɗaga idon ta sama ta hango wata trolley baby pink" "me kyau, da sauri ta tashi ta hau kan abu ta janyo ta, buɗe ta tayi, ajiyar zuciya ta sauke ganin abinda take nema suna ci." Card board paper ne a ciki masu yawa wadda take saman ta fara ɗakkowa. "Kyakkyawan zane ne na gefen fuskar namiji, sosai sajen shi da sumar kanshi suka fito tamkar a zahiri," kallon hoton take hawaye na zuba a kai. "Gaba ɗaya hotunan ta fito da shi, gaba ɗaya babu wanda cikakkiyar fuskar shi ta fito ajiki, duk rabin" "fuska ne sosai hotunan suka zanu, tabbacin wanda yayi zanen ya ƙware sosai." Rungume hoton tayi tana kuka sosai. "Wata card board paper ɗin ta ɗakko da kayan zane ta farayi, sosai zanen ya fita." Rubutun dake ƙasa take kalla hawaye nabin fuskar ta. "*Adaidai lokacin da gangar jiki take buƙatar hutu, ƙwaƙwalwa take buƙatar nutsuwa, adaidai lokacin ne" "zuciya ta take rasa nutsuwar ta tare da farin cikin ta, zuwa wane lokaci zan ci gaba da zama cikin wannan raɗaɗin? Se yaushe ne zuciya ta zata huta? Tsawon wane lokaci zan ɗauka ina jiran ka? Sai yaushe" hawaye na zai daina zuba akan ka?* *Wanene kai? Yaushe zaka bayyana a gare ni?* "Tambayoyin take wa kanta tana kuka, tana zaune a wajen har a kayi kiran Sallah, Alwala tayi ta gabatar" "da sallah, ci gaba da zama tayi akan daddumar, tuna cewar za'a iya shigowa a same ta haka ne yasa ta" tattare hotunan ta tura su ƙasan gadon ta. "Hijabin jikin ta ta cire, tayi zaman ta a haka." Jin an taɓa handle ɗin ɗakin ne yasa ta juyo ta zubawa ƙofar ido. "Akhie ne ya shigo da sallama, turuss ya tsaya ya zubawa fuskar ta ido, ganin yanda idanun ta suka" "kumbura sukayi sumtum, ga fuskar ta ma ta ɗaga sosai gaba ɗaya tayi ja." "Cikin sauri ya ƙarasa ɗakin, fuskar ta ya riƙe a hannun sa yana kallon idanun ta da suke ƙyallin hawaye." """Meyafaru ayraah?""" Kanta ta girgiza masa hawaye nabin fuskar ta. """Dan Allah ki faɗa min damuwar ki a wannan lokacin na roƙe ki ukty""" "Hannun shi ta riƙe ta ɗora akan saitin zuciyar ta, jin yanda zuciyar tata take bugawa sosai ya tsorata." """Akhie zuciya ta zata fashe tun jiya take wannan bugun, kaina kaman ze rabe gida biyu akhieeee""" Jin yanda numfashin ta yake riƙe wa ne yasa shi janyo ta ya rungume ta a jikin shi. "Numfashi take sauke wa sosai a jikin shi, can kuma yaji numfashin nata ya tsaya, jikin ta ya saki a jikin" shi. "Da bala'in ƙarfi ya zaro ta daga ƙirjin shi yana kallon ta, ganin yanda idanun ta suka kakkafe ne yasa shi" fasa ihu kaman ƙaramin yaro. """Miemieeeee!! Abhieeeee!!!""" """Ayraah ki tashi, uktyyyy""" Kaman ze zare haka yake jijjigata. Kusan rige rigen shigowa ɗakin ake tsakanin miemie da abhie. Ganin autan nasu a haka ne yasa jiri ya ɗibi miemie ta faɗi a wajen itama numfashin ta na ƙoƙarin "ɗaukewa, da sauri abhie ya riƙe ta yana kiran sunan ta." Shikam akhie zuwa lokacin ya fara fita daga hayyacin shi. Ganin yarinyar daya raina da hannun shi kwance bata numfashi a gaban shi. ★★★★★ "Tabbas sai yanzu yaga wautar da yayi na marin yarinyar da yayi amman hakan be dame shi ba, yana jin" ze iya aikata komai ga kowa akan ammien shi koda kuwa hakan na nufin ya rasa rayuwar shi. "Gashi doctor yace masa gobe idan Allah ya kaimu za'ayi wa ammie aiki, saboda jikin ta ƙara rikicewa" yake. "Gaba ɗaya ranar be runtsu ba, sallah yake kawai tare da addu'a akan Allah yasa a wannan karon ayi cikin" Sa'a. Tun yana jiran sakamakon abinda ya aikata wa zainab a daren har ya haƙura ya cire fargabar a cikin ranshi. Sai dai yana da tabbacin shirun su ba Alkhairi bane. "Ƙarfe 11 na safe za'a shiga da ammie ɗakin tiyata, goma da rabi aka shirya ta cikin kayan aikin, nurses" suka zo tafiya da ita yabi bayan su. Ana shirin shiga da ita yaji cikin kaushin murya ance! """Ku dakata""" Gaba ɗaya juyawa sukayi suna kallon me maganar banda shi da yaji yanda zuciyar shi take bugawa tamkar zata faso ƙirjin shi ta fito. """Ku kama min shi""" Yan sanda ne cikin farin kaya suka zagaye shi. """You are under arrest""" Innallilahi wa'inna ilaihir'raji'un kawai yake maimaita wa acikin zuciyar shi. "Sai a lokacin ya juyo yana kallon uncle ɗin nashi, da yar gwal ɗin yar shi da fuskar ta take kumbure" saboda marin data sha a hannun shi. Tashin hankali ne rubuce akan fuskar shi. Wani irin kallo yake wa uncle ɗin nashi me wuyar fassara. Babbar rigar shi ya saɓa ya matso gaban shi. """Kai har kanajin wanene kai da zaka marar min yar?"" Koni ban taɓa ɗora hannun na a kanta ba bare kai," "talakan banza talakan wofi""" """Yanzu yanzu ina son kadawo min da kuɗin da tabaka jiya, wallahi sai dai wannan uwar taka mara" "amfani ta mutu""" "Gaba ɗaya jijiyoyin jikin shi sun miƙe samɓal, tsabar ɓacin rai da tashin hankali." """Zaka dake nine? Ina kuɗi na?""" Cikin shaƙaƙƙiyar murya yace! """Nariga na biya kuɗin aikin""" """Da ayi mata aiki da kuɗi na gwara ace nabar wa asibitin kuɗin"" kai kuma Kasan duk yanda zakayi da ita" "uwar taka""" "Sosai nurses ɗin suke bashi haƙuri, da nuna mishi irin tsananin wahalar da majinyaciyar take ciki, amman" ya rantse akan baza'a mata aikin nan ba sedai ta mutu. "Har ƙasa ashraff ya tsugunna da niyar bashi haƙuri, sai dai kafin yayi magana ya ɗauke shi da mari cike da" ɓacin rai. """Ku ɗauke shi ku tafi da shi... Itama uwar tashi ku biyo ni da ita...." Topha ana wata ga wata ga ƙoshi ga kwanan yunwa. ku biyo alƙalamin yar gidan baba Achadu dan jin yanda zata kasance. FULANI 08082101373 https://chat.whatsapp.com/Kqi1tusHnZa6SHgbTgFqlr